Sashe 5
Mailaah Part 1 Complete Hausa Novel. · about 2 min read
Kamar kullum fuskata a lulluɓe ta ke ruf cikin niƙabi, wanda bada son raina nike saka shi ba sai dan babu yanda zanyi, da taimakon hasken farin watan daya haske ko'ina nike ganin gabana, ina jin yanda sautin takalmin kwalbar ƙafata ke amsakuwa saboda shirun wajen.
A daidai bakin ruwan na tsaya, ina jin nutsuwa na safko min, lumshe idona na yi dake rufe ina shaƙar ƙamshin ƙasar wajen, zan iya rantsuwa cewa tun daga ranar da ƙafata ta dira a garin ban taɓa samun nutsuwaba kwatankwacin wacce nike samu idan ina a bakin ruwa, nayi iya yina wajen ganin na hana kaina juyawa kallon ƙasar bishiyar, amma abu yaci tura, sai da na juya na kalli wajen, kamar kuma ko yaushe idan na kalli wajen gabana kan doka da ƙarfi, yanzuma ina iya jiyo sautin yanda zuciyata ke tsallen bugu kamar zata faso ƙirjina, a hankali na fara takawa zuwa inda yake a zaune yana kallon ƙafafuwana, kamar meson haddace wani abu.
Zillo zuciyata ta yi a daidai lokacin da na tsugunna agabanshi ina kallon fuskarshi wacce nagaza gane yanayin da yake ciki, ban damu da yanda zuciyata ke dokawaba na tsinci bakina na faɗin.
"Mi kake yi anan, inane gidanku, kaci abinci miyasa bakayi wanka ba, bakada lafiya ne ko wani ya biyoka?." na dinga jera mashi tambayoyi muryata a karye, danakai dubana zuwa ƙafarshi bansan sanda na zauna a ƙasa tare da kama ƙafar tashi wacce nike iya ganin dauɗar da tayi ta cikin hasken farin watan, idona na tsiyayar hawaye ta cikin niƙabina na ce.
"Ya Allahu ya Rahama!!! a ina kaji ciwo, akwai zafi ko, sannu, sannu kaji bara inje gida in ɗauko maka magani, jirani mintuna biyu yanzu zan dawo."
Na faɗi muryata na sarƙewa saboda kuka, a hankali na aje ƙafar tashi tare da tashi da hanzari na fara tafiya gudu-gudu, har naɗanyi nisa sai kuma na dawo da sauri ina faɗin.
"Kaci abinci, ko kanajin yunwa bara in taho maka da tuwo ban saniba ko zaka iya ci tunda bakada lafiya." Sai kuma na sake juyawa na tafi da hanzari.....✍️
KU BIYO NI DAN JIN YANDA ZAMU WARWARE ZAREN SARƘAƘIYAR LABARIN.
KUYI HAƘURI BA YAWA INA BUSY.
MARYAM STAR⭐....✍️