← Book details Mailaah Part 1 Complete Hausa Novel. Local reading mode
READING PART 3 OF 5

Sashe 3

Mailaah Part 1 Complete Hausa Novel. · about 7 min read

Barci ya ke amma zuciyarshi naga ƴarshi jininshi, wacce yake zargin kanshi akan wofintar da rayuwarta, da ace ya rungumeta ya karɓeta da lalurarta, da rayuwa ba zatai ma ta ƙunci irin haka ba, da ace ya tsaya tsayin daka wajen kula da lafiyarta tare da juriyar nema ma ta magani, da yanzu wataƙila ta samu lafiya, yana matuƙar son ƴarshi MAILAAH, amma bai san dalilinda yasa ya kasa kulawa da ita ba, wani bin yakan mance da rayuwarta sai idan anyi zancenta ko Allah yasa ta fito waje su haɗu, yakan kalli tsakiyar jemamun idanuwanta waɗanda ruwa ke kwance masu sheƙi kamar hawaye, tsaf ya ke karantar rauni da kuma jarumtarta a cikin idonta, yakanji ya tsani kanshi daya kasa inganta rayuwarta, idan yayi niyar janyota jikinshi don ya kyautata ma ta, kuma ya zama inniwa a gareta, sai wa ta doguwar katanga wacce yayiwa laƙani da katangar ƙaddara ta gifta a tsakaninsu, taƙi ɗaya bazai ƙaraba daga inda yake sai de ya farka yaganshi kwance ana saka ma shi drip, tun abin na damunshi harya rasa sukuni har takai daya sadaƙar, yakuma cire hannunshi gaba ɗaya cikin safgar MAILAAH dan yana so ya tsira da lafiyarshi, badan abin baya nuƙurƙusar zuciyarshi ba, kawai de ya janye jikinsh daga ita ne dan samar musu da nutsuwa daga shi har ita.
Bai taɓa zartar da hukuncin da yai danasanin ba irin aurar da MAILAAH, bai samu halartar ɗaurin aurenba, saboda ciwon zuciya daya addabeshi a safiyar ranar, gaba ɗaya guyagunshi sun gama sakewa akan cakuɗaɗɗun al'amurranda ke faruwa da rayuwar ƴarshi, muddin zaiyi hwaɓɓasa akan yi ma ta wani abu babu shakka sai yaji a jikinsa, sau dayawa zuciyarshi kanyi rawa akanta, har yakan ji kamar ya yarda da zancen da ake faɗi akanta na lallai ta haɗa jinsi da Aljannu, amma idan ya tuno yanda yai rayuwa tare da mahaifiyar sai ya tuhumi kanshi, mahaifiyarta itace wadda ta sadaukar da komi nata, ta sallama rayuwarta akanshi, idan zaiyi tunani iri ɗaya da sauran mutane tabbas ya zama butulu, gaba ɗaya kanshi a kulle yake, yanada buƙatar sarari domin ya nutsu yayi tunanin komi tun daga tushe, sai de bai da wannan lokacin, lokaci yayi ƙaranci a gareshi, idan yace zai matsanta kuma, to abubuwane masu tarin yawa zasu ɓullo marasa daɗi.
Haka yaita tunane-tunane har lokacinda barci ya sake ɗauke shi.

Tunda gari ya waye ta caɓa uban ado, gwala-gwalai ne keta walwali a jikinta, ga wani haske da kyau da tayi kamar wa ta sarauniya, ba tun yau ba, ba jiya ba, ba shekaran jiya ba, tun shekaru masu dama da suka shuɗe zuciyoyin ilahirin mazauna gidan ALHAJI SHA'ABAN ke rawa akan matarshi ta biyu me suna SALIMA, ba kyawunta da kullum yake ƙaruwa ne ke rikita tunaninsu ba, hatta izza da kwarjinin da take da shi abin zargi ne a wajensu, amma kamar an saka kwaɗo an kulle bakunansu, haka suka kasa tattauna zancen koda a tsakaninsu ne.
Kamar yanda al'adar gidan ta ke na haɗuwa kowace safiya a ranakun aiki tun ƙarfe bakwai domin karyawa, yauma hakan ce ta faru, rankatakaf iyala Alhaji Sha'aban wanda suke kira da Alhaji ne zazzaune akan dogon dinning table, mecin mutane sama da ashirin, kowa ka gani daga matan har mazan shirye suke a cikin shirin fita aiki, yara kuma kowanne sanye da uniform, sai hayaniya ke tashi kamar gidan biki, da zuwanta wajen kowa yai tsit, hatta yaran du suka kama bakunansu suka nutsu, Hajiya Salima ta saki murmushi cike da ƙasaita sannan cikin izza da taƙama ta zauna akan kujerar da aka ware dan zamanta ita kaɗai, lokaci ɗaya suka haɗe bakunansu wajen gaisar da ita, sai da ta ƙare musu kallo one by one, sannan ta saki murmushin ƙasaita, tai amsawa ɗaya, daga nan kowa ya shiga sarving kanshi, tsit dinning ɗin yayi bakajin komi sai ƙarar cokulla, fuskokin mazauna wajen du sun nuna alamun ƙosawa da takura, muddin Hajiya Salima ta bayyana a waje wannan yanayin ne zai bayyan a fuskokinsu, basa sakew sai ta wuce ta basu waje, wannan ya saka idan ba dole ba babu me zama a kusa da inda ta ke, ita a wajenta tana ganin hakan kamar kwarjini ne, yayinda su kuma suke ɗaukar hakan a matsayin takurawa.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆
Dummmm!! haka na ji kaina na sarawa da tsananin ƙarfi, yayinda na saka hannayena na dafe kan ina jujuyashi cike da azaba, idan akwai abin da nikewa zullumi, bai wuce gusowar dare ba, ni kaina bana iya tantance ainahin abin da nike ji, amma dazarar duhun dare ya kusanto, ina shiga matsanancin tashin hankali, zafin abu biyu kacal na sani, daga zafin azababben ciwon da kaina ke yi, sai zafin baƙar azabar da bansan yanda zan kwatanta ko misaltata ba, kwanyata bata aiki sam, hasalima bana iya tantance wacece ni karan kaina, amma nakan tantance nau'o'in azabar da a kullum dare nike kwana a cikinta.
Buɗe idanuwa na da suka rine zuwa jajaye na yi, ina jin kamar in ciresu in huta saboda ciwon kan da nike ji har cikinsu, ban sauke su ako ina ba sai a saman farar fuskarshi wacce ke zagaye da lallausan saje, "ɗin,ɗinn,ɗinn". na ji wannan sautin ya doka a ƙoƙon kaina, a daidai lokacin da nayi tozali da ɗigo-ɗigo ɗin jinin da bansan ta inda yake fitaba a jikina, ya ɓata gaban farar rigarshi, ban san mi nike yi ba, amma naga hannuna ya miƙe zuwa kan ƙirjinshi a daidai saitin da jinin ya ɗiga, bazance ga abin da nike yi ba, sai kawai naga hannuna na zagaye inda jinin ya ɓata, caraf ya riƙe hannayena, tare da buɗe idanuwanshi ya watsosu a kaina.
Wani tartsatsin haske ne me cike da tarin abubuwa waɗanda ke cakuɗe da hayaniya suka gilma ta cikin idanuwa, acikin abubuwanda suka gilma min nai nasarar cafke wani hoto, a cikin duhu ne a bakin ruwa, ina a tsaye yana a zaune ƙarƙashin bishiya na juya ma shi baya ina jefa ƙananun duwatsu a cikin ruwanda ke gabana, idan ruwan ya yo tsallo yalle sa'ilin da na jefa dutsen yakan fallatsa da ƙarfi har saman fuskata da ke a rufe ruf ba'a iya ganin komi, daga nan hoton ya yanke, sai kawai na damƙi gaban rigarshi da ƙarfi tare da rintse idona, ban san abin da zanyi kuma ban fahimci komi ba amma hakanan naji ina so in idasa ganin wannan hoton daya gilma min.

Wa ta iriyar mummunar dokawa ƙirjinsa yayi, babu shiri ya rintse idonshi da ƙarfi, jijiyoyin da suka zagaye saman kanshi na sake fitowa raɗo-raɗo, wa ta iriyar zufa ta shiga karyo ma shi daga saman kai tana bin fatar fuskarshi, lokaci ɗaya jikinshi ya mutu murus, dama gashi ba wani isashen ƙarfi ne da shi ba, ko ina ciwo yake mashi a jikinshi, sake rintse ido yayi yana tunano mawuyacin halin da yaganni a ciki jiya da daddare.

A CIKIN DARE
Kwance ya ke kamshi na kallon sama, duda baya iya ganin komi saboda duhun da yayiwa ɗakin ƙawanya, tun da yaga yanda na firgita da ganin haske sai kawai ya kashe hasken yana tariyo maganganun kamikin mutumin da tun da yai tozali da shi, ya kasa mancewa da yanayinda yaganshi a ciki, zai iya ganewa idan wani na cikin damuwa koda kuwa yaso ya ɓoye hakan, kallon farko da yaiwa mutumin da aka sheda mashi ya zama suruki a gareshi, ya karanci tarin damuwa me ɗumbin yawa kwance akan fuskarshi, ya kasance cikin mutanen nan waɗanda basu damu da kowa ba, amma bai san yanda akai yaji ya damu da yanayinda yaga mutuminba, kalamanda yai amfani da su wajen yi mashi magana basada tsawo, amma sun samu wawakeken muhalli sun zauna daram a zuciyarshi.
"MAILAAH ƴata ce, ka riƙe min ita amana, ka kula da ita, ka zame mata garkuwa kuma kariya ga dukanin wani abu dazai kusancet walau na cutarwa ko akasin haka, suna yi ma ta kallon mahukaci, sai de ba haka bane ƙaddarce ta mayarda rayuwarta haka, idan ka riƙeta amana nan gaba kaɗan zaka yi alfahari da ita, MAILAAH yarinya ce ƴar baiwa, wacce take rayuwa da ikon Allah kaje na miƙ ragamar rayuwarta a hannunka, Allah ya baka ikon kulawa da ita amin."
.........✍️MARYAM STAR⭐

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/HbYjxC6ucFxK95Gxo1yN9i

🥀🌹MAILAAH🌹🥀

WRITE BY
MARYAM STAR ⭐ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*

PAID BOOK
BOOK ONE
FREE PAGE

بسم الله الرحمن الرحيم.

Chapter----------- 5 & 6
Chapter 3 · 0% Book details