Part dinsa kai tsaye nufa dake bangaren Aysha , burinsa kawai yayi toxali da kyakykyawan fuskanta
Laifin Boye Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 48 min read
Phone dinsa kawai ya aje ya watsa ruwa shaf-shaf , koda yafito farar jallabiyace kal yasaka ajikinta sai turare daya fesa , yafito zuwa parlor Dr. Sudais kadai da yusrah yagani wacce Ayshan taroka tasake kwana , hakan yasa shushun wucewa kai tsaye zuwa bedroom din Ayshan
Yanaji sudais din natsokanan akan yayi sauri yafito su mikawa Amarya shi , yai gaba tamkar baiji abnd yake fadi ba
Yana tura kofan ya hangota abakin bed wayane akunninta da alamu da umman ta take mgn, jin yadda tanarke tana zuba shagwaba
Sanye take cikin dogon wando da vest mai karamin hannu tamkar na bra, kayan duka pink color ce illah gaban rigan da akai zanan zuciya
Gashinta sai kyalli yake wanda yaji mayuka masu qamshin gske , gaba daya dakin na fidda wani sanyayyen qamshine maisaka bawa cikin shauki da nutsuwa
Zama yayi kan stool yana karemata kallo zuciyansa na harbawa da karfi , domin bakaramin kyau tai masa cikin shiganba
Tana aje wayan kallo daya taimasa ta dauke kanta tana fadin"sannu da zuwa fuskanta tahadeshi tamkar ba itace tagama waya cikin raha ba"
Bai amsaba illah tashi dayayai tsam yadawo gabanta , hannu yasa ya juyo da fuskanta data waigar gefe guda
Kokarin kwacewa take amma ina sake rungumarta yayi yahade fuskansu guri guda , yana jin yadda bugun kirjinta ke karuwa
Saida yai kissing dinta son ransa kafin yasaketa , cikin kasalalliyar murya yake fadin"smile esha plxx wannan hade ran baidace dakeba
Ko kina kishin yau zan angwance da Amarya ne? Wlh idn bakiso sai inyita kwana nan , kina bani irin cwt din dana dandani zakinsa daren jiya ,
Yakare mgn cikeda zolaya yana kallon cikin kwayar idanunta , "
Kwace jikinta tayi da karfin gske kuka takesonyi sai dai sam bata son yagane weakness dinta ayanxu , hakan yasata yin murmushi wanda iyakansa labbanta kawai
Saida tasanya idanunta cikin nasa kafin tafara fadin "hmm ya shushu kenan taya xanyi kishi don xaka kasance da Amaryan ka , ina tayaka mafarin ciki domin yau xaka dandani wani irin xumane wanda mata suka sha suka barmaka ragowa ,
Ina tayaka farin ciki dazaka sami cikakkiyar soyayyan da aka jima da gogewa gurin nunawa wasunka , taya zanyi kishi alhalin nasan Neesa itace mafarin cikin shureim
Itace macen da ya shushu kematukar burin mallaka , gashi ayau tazama mallakinka har kuna shirin zama abu guda kaida ita , kaga dole intayaka kishi amatsayin ka na yaya kuma miji agareni , wanda duk macen kwarai tana kokarine gurin taya mijinta son abnd yakeso
Bare kuma Aysha da akayi sa'a sam babuma kishin mijin azuciyanta , takare mgn tana duban yadda gaba daya fuskansa yasauya , "
Kafin tacigaba da fadin "mezakai da alawan wacce batada wani matsayi cikin xuciyanka face qanwarka ,nasani bakasona ya shushu sha'awata kakeyi ka kuma nasaran kaudata , batare daka nemi yardata ko amincewa taba kayi abnd kakeso ,
Kana tunanin duk dadin bakin dazaka min ayanxu zaiyi tasirine? Bazan taba amincewa da maganganunka ba , katashi kaje gurinta kabarta itakadai kana bata lokacinka a inda ba'a damu dakai ba"
Karya kikeyi esha karya kikeyi kindamu da shureim , yayi mgn cikin karaji yana riko kafadunta dakarfin gske , idanunsa sun sauya kala yanajin tsananin zafin maganganun datake fada masa
Jijjiga kafadunta yake yana cigaba da fadin"esha tunda zuciyata tafara sonki wlh kema yazama dole kisoni , ki kuma koyi kishina dole kisoni Aysha , domin bazan iya rayuwa babu keba ayanxu
Kidago fuskanki kisanar dani bakisona kifadamin hakan ido cikin ido nace , tsorone yakamata ganin yadda gaba daya yake neman fita nutsuwarsa
Duk yadda taso danne zuciyanta kasawa tayi saida hawaye suka shiga zubo mata , ahnkl ta dubi fuskansa murya narawa take fadin"banson ........ "
Kafinma takarisa yarufe bakinta tahanyar sanya harshensa cikin nata , tamkar zai ballata haka rungumeta , takasa hanashi duk abnd yake aiwatarwa da jikinta , domin sam jikinta babu kwarin yin hakan
Saida yajagulata son ranshi kafin yasaketa yana sauke numfashi , idanunsa gaba daya sun juye xuwa launi nadaban yayinda Ayshan takifa kai tana kuka ahnkl
Tanajin sadda yafice tareda rufo mata kofan , hakan yasata saurin fadawa toilet ta wanka idanunta domin ko yusrah bata kaunar ta fuskanci bacin ran datake ciki , abnd kawai ta kudurcema ranta shine asannu zatayi maganin shushun yagane shayi ma ruwane
Tasani sarai sudais nanan yana jiran fitowanta , hakan yasata daukan hijab tarufe jikinta ta fita falon
Suna zaune shida yusrah babu shushun cikin falon , sai ledojin dake zube bisa center table, Dr sudais ne suka gaisa yana tsokananta da uwar gd sarautan mata , murmushi kawai take yi bata ce uffanba
Shima nasiha yaimata akan takara hakury takuma kai zuciyanta nesa , domin zaman tare dole sai anyi hakury duk da cewa baguri guda sukeba amma yauda gobe sai Allah, ya yabeta sosai akan irin nutsuwanta da hakurinn daya santa dashi
Sosai Ayshan taji dadin nasihansa jikinta kuma yasake yin sanyi sosan gske, gogan ne yafito wannan karon yaboye idanunsa cikin bakin eye Glass , wanda bazaka taba karantar yanayin dayake cikiba illah Ayshan datasan maganganuntane suka fusata shi sukaima zuciyansa illah
Ledoji guda 3 Dr sudais ya kwasa ahannunsa yabarma su Ayshan guda 3 din, har bakin kofa fita part din yusrah da Aysha suka raka su , Aysha ce kefadin"ya shushu Allah bamu alkhairy asha amarci lfy da tauraruwan xuciyanka Aneesa,"
yadda takare mgn tana wani sakin Raritan's yasa shushun juyawa ya kalleta , ransa ne yai dubu yabaci fadi yake azuciyansa lallai nema yarinyan nan bata sonshi dagske , meyasa bata kishinsa kaman yadda yasan duk macen datasan mijinta dole tayi kishin kasancewansa da wata , toko dai don tasan Aneesan famko ce ? Wani tsaki yaja dabaisan sadda yayi shiba saida yaji Dr sudais nafadin "sorry sir basaikayi tsaki zansan ka kosa kayi tozali da gimbiyar ba yakare mgn yana tuntsirewa da dariya su Aysha natayashi
Abnd yai masifan sake bata ran shushu watoma har daman bude hakora tana kwasan dariya agaban sudais takeyi , cikin tsawa yayi mgn yana fadin" oya duka kuwuce ku koma ubanwa ma yabaku izinin fitowa gulma ko me? Kai kuma mai janyo ma mutane raini idn kagama saika sameni acan yakare mgn yana tafiya fuu xuwa part din Aneesan , zuciyansa na matukar yimasa zafi ga azaban son kasancewa da Ayshan daya cika zuciyansa
Koda suka juya har lokacin yusrah bata fasa dariyaba , tana fadin "o su ya shushu angama fidda rai dasamin abn kirki dominyasan koyayi rawan kafa fankoce , shine zainemi yasauke fushinsa akanmu
Bude ledojin kajin dasu gasassun fish wit Irish an onion source mai azaban dadi suka shiga ci , sai Aysha sam turawa kawai takeyi tana biyema yusrah suna santy amma sam bawai don tanajin dadinsa ba
Ita tafara cire hannunta tana karisa shan ruwan lemun , basu kalli youghort dinba bare susha kasancewar sunci kifi
Yusrah ita takwashe sauran xuwa kitchen ta fito ta tadda har Ayshan tashige bedroom
Koda suka kwanta Aysha rufe idanu kawai tayi badon tanaji zata iya rintswaba , tunane-tunane kawai take cikin zuciyanta sai soyayyan mijinta da azaban kishin Neesa datakeji cikin zuciyanta , duk da tayi amanna da wuya shushu ya iya hada shinfida da ita awannan daren ,
Wata zuciyan ketunasar da ita yanafasonta , itama tana sonshi gata gogaggiya ce watakil tanemi kayanta dakanta ma , runtse idanunta tayi zuciyanta na bugawa dakarfi , sautin kukanta keshirin fitowa hakan yasata sauka ta nufi bathroom domin batason yusrah ta farka taganta ayanayin datake ciki
Tajima tsaye jikin kofa tana kuka mai ban tausayi kafin ta rarrashi kanta tashare hawayenta
Alwala tadauro tafito karatun kur'ani taitayi har xuwa 2pm bata runtsaba , sallah tayi tana adduan Allah yasanya hakury da juriya azuciyanta , yabata ikon shnye duk wata damuwa
Yasanya soyayyanta azuciyan shureim yahada kansu da Neesa matukar itadin alkhairi ce cikin rayuwansu
Sai around 4 tasamu bacci ya dauketa cikeda mafarkai barkatai wanda takasa gane inda suka sa gaba
*****A part din Neesa kuwa ........
Ayshat Dansabo lemu 👌🏻
[10:21PM, 5/24/2018] 😃😃 SMILER😄😄😄: *LAIFIN BOYE*
*_Haske writers_* *_association_* 💡
Writing by Ayshat Dansabo lemu 🖊
*56*
******A part din Neesa kuwa koda suka shiga afalo shushu ya zube cikin sofa, yana sauke wata zazzafan ajiyan zuciya , har zuwa lokacin maganganun da esha tafada masa keyawo akwanyansa, zuciyansa nasake daukan zafi
Dariyan datayi da amon muryanta kawai yake sake ji yana masa yawo , meyasa bazata soshi ba ? Meyasa yake jin zafin yadda take nuna hakin ko inkuka da lamuransa?
Wata zuciyan kesanar dashi sbd batasonka
Duk yadda Dr sudais yayi dashi akan yaje ya fito da amarya Neesa, shushu yi yayi tamkar baimasan yana mgn ba
Ganin zai dameshi yasashi duban idanunsa yana fadin"plzz guy karabu dani kana iya shiga ka fiddo da amma baniba "
Sudais baisake mgn ba illah mikewa da yayi hannunsa rikeda phone dinsa , ya dubi shushun yana fadin"haka kace ok toni nayi nan Allah bamu khairan asha angonci lfy "
Ya fice yana tuntsura dariyan dake taho masa , yabar shushun dajan dogon tsaki shima ya mike ya nufi part dinsa , yabar ledojin da suka shigo dashi aje anan kan table
Kokadan baiyi tunanin duba lfyn amarya Aneesa ba , koda yashiga part dinsa fadawa gado yayi ya kwanta
Byn yacire jallabiyan jikinsa idanunsa alumshe suke , yayinda zuciyansa tayi nisa gurin tunanin yarinyar dake neman sauya tunaninsa lokaci guda , wato Aysha gaba daya zuciyansa takasa hutawa da tunaninta dason kasancewa da ita ,
Wani juyi yayi yanaji ina tana kusadashi ayanzu, ya jita ajikinsa koya sami nutsuwan zuwa da gangar jikinsa dake azabtuwa da shaukin ta
Duk yadda yaso ya danne zuciyansa daga damuwa yakasa , ganin abn zai damesa yasashi daukan wayansa yana danne-danne na bagaira babu dalili
Da kyar bacci yadauke shushu awannan dare , yayi shine kuma cikeda mafarkin Ayshan
Aneesa kuwa tun daga shigowan su shushu har fitan Dr sudais, akan kunnuwanta ne ta Dade tana jiran shigowan angonta
Wanda idanunta ke kwadayin gani , rabonsa dashi tun randa suka rabu zuciyoyinsu babu dadi , ko awaya bata sake jin muryansa ba
Tun tana kallon agogo harta gaji ta yaye rufan dake jikinta , babu alamun shushun zai waiwayota ahnkl takejin hawaye na cika idanunta
Inama bata aikata abnd tayi ta aikatawaba da yanzu tasani yana nan yana tarairayanta , sanin ko itadin wacece da yayi ayanzu yasashi juya mata baya
Kukane mai sauti ya kwacemata mai cikeda tsantsan nadama da danasanin dabazai mata anfaniba , tanason shureim tanajinsa acikin zuciyanta ta yadda bataji zata iya daurewa shariyansa , sai dai ta yaya zata fuskancesa alhali ayanzu ya tsaneta ?
Saida tayi kuka mai isanta kafin ta iya mikewa xuwa toilet, idanunta ta wanke ta fito kayan jikinta ta cire tasanya sleeping gown
Kwanciya tayi amma ko kadan bataji zata iya rintsawa, meyasa wannan daren yazo mata ahaka ? Daren da tadade tana jiran zuwansa domin su faranta ran juna itada shushunta
Idn ta tuna cewa Rufaida ce silan fallasa sirrinta agurin shushun , saitaji gaba daya ta tsaneta tsana bana wasa ba
Atakaice dai sai bacci barawo ne yasace Aneesa a wannan dare
****washegary abangaren Ayshat kuwa a round 10am itace tsaye a dining tagama shirya musu breakfast wanda iyakacinsa bai wuci wanda zasuci itada Rufaida ba
Yayinda Peter yagama shirya na part din Amarya Neesa , yakai musu can apartment din Aneesan
Juyawa tayi zuwa bedroom a zaune ta tadda yusrah kan stool , fitowanta wanka kenan tana shafa kallon juna sukai tareda sakarwa juna murmushi kafin yusrah ta furta "morning my matar ya shushu"
Harara shine abnd Ayshan tasakar mata tana fadin "matsalata dake wlh neman mgn baby ni kinga bari inshiga wanka idn kingama breakfast is ready "
Tayi shigewanta bathroom koda ta fito bata tadda yusrah adakinba hakan yasata zama ta fara shafa
**shushu ne tsaye gaban mirrow yana daura agogon zallan azurfa a tsintsinyar hannunsa, yayi wanka yana sanye da english wears wanda sukai matukar amsansa
Falo yafito kai tsaye dining ya nufa yafara bude kulolin daya gani jera reras , tundaga kalolin abncin yagane ba Aysha bane tayi shi hakan yasashi rufewa ya bar wajen
Yana karisowa cikin falon Aneesa na fitowa wacce taci ado cikin wani hadaddan boyel laces mai shegen kyau
Gown ce wacce tayi asalin zama ajikinta , fitinannan qamshine ketashi ta ko'ina ajikinta , yi yayi tamkar bai gantaba yaci gaba da tafiya
Amon voice dinta yajiyo tana gaida shi , juyawa yayi yashiga karemata kallo mai cikeda ma'anoni daban -daban, tabbas idn yace batai kyauba yayi mata karya sai dai sam yanzu bayaji akwai abnd zatai ta birgesa , ganin ta ayanxu yashiga hasko munanan pics dinta dayaci karo dasu abaya
Wadanda sune silar tarwatsa zuciyansa da dasa kyama da tsananta acikin zuciyansa, idanunsa sunfara canzawa zuwa tsantsan bakin ciki da takaici , fadi yake aransa dubeta tamkar duka kenan
Amaimakon ya amsa gaisuwanta wani dogon tsaki yaja tareda juyawa yafice daga part din baki daya ,ya nufi part din Aysha
Zama Aneesa tayi tasaki kuka maiban tausayi , wani sonsa takeji nasake mamaye zuciyanta , mekenan keshirin faruwa da ita ? Kardai har shureim yadaina sonta ? No ta furta tamkar wata zararriya tana sake barkewa da hawaye masu zafin gske
Yunwa takeji domin rabonta da abnci tunna yamman jiya , da aka sata agaba taci hakan yasata mikewa tanajin kanta nasarawa xuwa dining
Kadan ta iya tsakalan abncin ta ture illah kunun gyada dayai mata dadi , yaji madara shitaita sifing ahnkl harta shanye cup guda
Nan cikin falon takoma ta kwanta tana danna wayanta , kafin daga karshe tayi dialing number din ummanta
****shushu kam yana shiga part din Aysha da yusrah yafarayin tozali , tana kalaci bisa dining hakan yasa kai tsaye yanufi gurin
Gaidashi yusyn tayi ya amsa yana wani tabe mata baki , tareda bin plate din dake gabanta da kallo Danish patotoa ne sai tashin qamshi yake , gefe guda kuma Pepe soup ne na ragowan kajin dasukaci daren jiya , Ayshan tamaida shi pepe soup din
Hannu yakai yadauki plate din zaifara zubawa , wanda kadan yayi saura cikin kulan domin sam esha batayi dayawa ba
Yusrah ce ta dubeshi cikeda mamaki tana fadin"laaah... Ya shushu ragowan na Aysha ne kadai bamuyi dakai ba , bakayi breakfast bane a part din Amaryan? "
Wani uban harara ya zabga mata yana fadin"bansaniba na lura raini yafara shiga tsakanina dake ko baby , be careful wlh zanyi maganinki nidin tsaranki ne ? Koko kinji natambayeki akan abncin bare kifara zubamin sharhi ? "
Yakare mgn yana jan dogon tsaki kafin yacigaba da juye abncin, tareda zuba Pepe soup din wanda duk yawunsa ya tsinke yakisa yakai bakinsa
Sorry Allah yabaka hakury ya shushu, abnd yusrah tagama fadi kenan tacigaba dacin abncinta
Aysha wacce tagama hadewa cikin wasu riga da wando masu shegen kyau , English waers ne rigan karamace matuka wacce tafidda asirin kirjinta
Wandon iyakacinsa guiwanta da kadan yakamata matuka , shape dinta yafito sosan gske rigan pink ce akaimai adon hrt da black sai wandon black , gashinta tayi parking dinsa zuwa baya
Qamshinta mai dadi dakashe zuciyan shureim Aji shike tashi ako wani lungu da sako naji kinta, kanta tsaye ta nufo cikin falon batareda wani tunanin zataga shushun ba
Kanta akasa yake idanunta nakan wayanta ne tana duba text's dake shigowa ta WhatsApp chart , dining din tanufa kai tsaye sai dai me tunda ta dinfari gurin hancinta yafara jiyo mata qamshinsa
Hakan yasata daga ido ta kalli gurin karaf sukai full eyes da shushun wanda yatsareta da manyan idanunsa , wani mayen kallo yake binta dashi tamkar yamike ya tarbota ya rungume kozai sami sassaucin abnd ke fisgan zuciyansa gameda ita haka yakeji
Dauke idanunta tayi tana cigaba da dinfaro wajen , shikam shushu sam yakasa dauke idansa daga kallon kirjinta dasuke tsone idanunsa
Kujera taja kusada yusrah ta zauna sai alokacin tasake duban inda yake , gud morning ya shushu tafurta tana dauke kanta gefe guda
Kulan tabude wayam babu komi ya juye takaicine yarufeta , yarasa gulman dake damun shushu dason kuntata zuciyanta dayake , mekuma yakawoshi part dinta kalaci inba tsabagen yashiga rayuwanta ba
Cikin shagwaba mai cikeda tsiwa take fadin"kai ya shushu me kuma yakawoka nan cin abnci kaida zaka tsaya kuci kaida Amarya
Gsky nifa ana takuramin ana shiga rayuwata haba "
Takare mgn tana mikewa fuu zuwa kitchen , gaba daya jikinta na kadawa wanda yasa shushun yakusa kwarewa , bugun zuciyansa ne yakaro yanajin wani abu namasa yawo cikin jikinsa
Saidai tabacewa ganinsa kafin ya maida hnkln sa kan abncin , baby yusy ne ta mike yabar wajen tana danne dariyan dakeson taho masa
Ganin yadda yayan nata yashiga wani moment nadaban, saibin Ayshan da mayataccen kallo yake
Bisa sofa tayi kwanciyanta tashiga buga game din candy crush a phone dinta ,
Shushun ne ya mike tsaye byn ya kammala cin breakfast din , kai tsaye kitchen da Ayshat tanufa zuciyansa ke ingizashi yabita domin baigaji da ganin wannan wankan dake neman zautashi ba
Tsaye yayi abakin kofan yana kallon yadda take fere Irish , qamshinsa ne daya cika wajen yasa Ayshan sanin yashigo gurin , amma sam batako yi yunkurin duban bakin kofanba
Aikinta kawai takeyi tagama tsane Irish din , gas takunna ta dora mai yana zafi ta juye , egg takada cikin bowl ta soya ta aje
Tana kokarin kwashe irish din sai jitayi anrike kugunta ta baya , saura kadan tasaki ludayin mai ya fallatsa mata tasaki wani kara
Saurin sakinta yayi yana fadin"sorry my cwt plxx yana wani langabar dakai "
Harara tarwatsa masa tana fadin"wai miye haka ya shushu yanzu dakasani nakone fa? Koda yake bakada asara tunda kabare sabuwa aleda tayi mgn tana sake tamke fuska "
Wani murmushi yayi natakaici domin sarai yagane bakar mgn ce take yimasa shagube da ita , kuma tabbas hakan nabakanta ransa
Juye abnta tayi cikin plate tana kokarin rabawa tawuce shi , sai dai taku daya yayi ya damkota zuwa jikinsa

*57*
A plastic chair dake girke cikin kitchen din yai musu masauki , plate ya amshe daga hannunta ya aje gefe guda ,
Kokarin kwacewa take daga rikon dayai mata amma saiya sake matseta ajikinsa, yana shakan qamshinta mai dadi da gigitashi tareda kunna wutan sha'awarta azuciyansa
Hannu yasa yadago fuskanta bai jira komi ba yahade bakunansu guri guda , sai dai hawayen dayaji yana zuba daga idanunta , da yadda take kokarin kwace kanta yasashi sakin bakinta bawai don yagaji da tsotso ba
Bakinsa yamayar saitin kunnuwanta cikin wata iriyar murya yake fadin
"plxx esha kibarni nasami nutsuwa mana wlh idn kika sake kokarin raba jikinki danawa Allah ya isa, sai yaushe zaki gane zuciyata ayanzu tana tsananin bukatan kulawanki ?
Meyasa bazaki amince shushun najinki har cikin jinin jikinsaba? Haba my cwt yakamata kifara kaunata wlh I luv u my baby"
Dagowa tayi suka hada idanunsu waje guda cikin rawan murya take fadin"bazan taba amincewa da wannan kalmanba ya shushu , alokuta da dama kalman I luv u bayana nufin namiji na kaunar mace da zuciya guda bane,
Bakasona ya shureim ninasani jikina kawai kakeso wlh sha'awata kawai kakeyi ya shushu
Takare mgn tana fitarda sautin kukanta ahnkl "
Sake matseta yayi gam cikin jikinsa yanajin yadda sautin kukanta ke taba zuciyansa, cikin karfi hali yayi mgn yana fadin
"shikenan esha zan nunamiki ba jikinki kadai nakesoba ke nakeso , bazan sake neman wani abu ajikinki ba harsai kece kika amince da hakan , amma kisani kowani hali nafada kece sila domin ayanzu nakai munzilin dabazan iya rayuwa babu mace ba , esha inasonki ina kuma tsananin bukatar kibani kulawa domin kare martabata ,
Zanci gaba da azabtuwa da sonki tareda adana sha'awarki har zuwa lokacin dazaki amince shureim yana kaunarki sonki ne yahaifar da tsananin bukatarki agareni cwthrt , kedin dabance esha "
Yakare mgn yana sake rungumarta sosai tareda kai baki yasunbaci wuyanta , hannu yasa yana wifing tears din dake xuba afuskarta
Plate din chips dinta ya dakko yashiga bata abaki , ba musu take amsa domin yunwa takeji saidata kauda kai alamun takoshi sannan ya kyaleta
Yana rikeda hannunta suka fito daga kitchen din gaba daya jikinta yayi mugun sanyi , son shushun kesake kassara zuciyanta har tanaji anya zata cigaba da gujemasa tamkar yadda ta tsarawa kanta wahal da zuciya da gangar jikinsa?
Dining yanata yahada mata ruwan shayi wannan karon taki yarda yabata abaki , dakanta ta karba tanasha shikuma idanunsa akanta yake harta kare
Atare suka mike hannunta yakama murya can kasa yake fadin"babyna zani gdn momy plxx anjima ki shirya launch dani kinji my cwt"
Dauke kai kawai tayi byn ta kwace hannunta gaba tai zuwa bedroom dinta tabarshi tsaye , yana murmushi shikadai wani sonta yakeji nasake karuwa cikin zuciyansa
***karfe 3pm yusrah tabar gdn shushu Aysha jitayi tamkar karta koma domin bakaramin rage mata damuwa zamanta keyiba
Sai dai tasani momy bazata taba amincewa da dawowanta gdn baki dayaba , yanzuma kwanakin da tayi don kawai tana tausayin Ayshan ne
Dawowa Aysha tayi ta kule cikin bedroom dinta , hawayen daba tasan kona miyeba ke zuba a idanunta
Maganganun shushun 1by1 kedawowa cikin kwakwalwanta , tanajin wani irin tausayinsa da soyayyarta cikin zuciyanta , sai dai takasa amincewa shushu yakamu da sonta
Side drawer dinta tajawo wanda wani karamin diary dinta ke ciki , shita dakko tareda bude wani shafi domin yin rubutu
Inda tafara rubutun kamar haka" **ya *shureim sonka akullum yana kara illah ta dukkanin zuciya da gangar jikinane, domin nasani sonka yariga da yazama jinin jikina , narayu dasonka ne tunbansan miye soba harna fahimci kayi wa zuciyata mummunan kamu , bansake sanin bazan iya rayuwa babu kaiba saida muka zama abu guda , inasonka mijina ina tsananin kishinka sai dai sam zuciyata takasa amincewa da kana sona ya shushu*
*
*Nakasa yadda ba sha'awata kesaka furtamin kalman soba ...... Takasa karisa rubutun sakamakon karan bude kofansa da shigowansa dataji* "
Dasauri ta cusa diary din karkashin pillow domin duk wani sirrin soyayyansa datake yana rubuce cikinsa , sai dai abnd batasani ba yariga yagani
Dagowa tayi idanunta na zubda hawaye ganin irin kallon dayake mata yasata saurin sunkuyar dakanta hawayen da takasa tsaidasu nacigaba da zuba
Ahnkl yake karisowa har yasami bakin gadon yazauna , hannu yakai ya janyota tareda daga pillon da hannu guda
Diary din yadauke yana juyashi ahannunsa , Ayshat ce tayi saurin kwace jikinta tana zuba masa magiyan yabata abnta , kada yakarnce mata sirrin dake cikin sa
Harara ya watsamata yana fadin"akwai wani sirrin da mata zata boye ma mijinta ne esha , ko zakiyi kuka najini yau saina karance sirrin dake cikin wannan littafin
Nasan dai baiwuce sirrin soyayyan guy din dakike so bako , yayi mgn ne cikin jin zafi da tsananin kishi shiyasa kotakan irin gunjin kukan datake masa baibiba ya tsallake ta zuciyansa na tafasa yabar part din kotakan launch din daya shigo domin sa baibi ba
****apart din Neesa kuwa kwance take afalo ta kunna TV domin yarage mata damuwan datake ciki , sai dai zuciyanta ba akan kallon da takunna yake ba , tayi nisa ne cikin tunanin angonta shureim wanda ayanxu take hango tsananta karara acikin kwayar idanunsa
Tayi wanka tasake sauya kwalliya dakaya masu daukar hnkl, jikinta dakuma ko ina nadakin na fidda qamshi ne mai matukar dadi
Ko lunch din da aka kawo takasaci sam tanan kwancen cikin tunani taji karan bude kofan falon
Hakan yasata daga idanunta ta hangosa shureim Ko sam baiko dubi inda takeba ya shige cikin part dinsa, yanayinsa kadai zai baka tabbacin baya cikin nutsuwan zuciyansa
Lumshe idanunta tayi tanaji tamkar tabi bayansa tabashi hakury , tasanar dashi ta tuba ayanxu shikadai take bukata cikin rayuwanta , sai dai bazata iyaba
Amatsayinta na amarya wacce yadace ace shine yake tarairayanta ayanxu , wata zuciyan kesanar mata taya zai tarairayeta alhali yasan Irin LAIFIN data dinga aikatawa a BOYE
Lumshe idanunta tayi hawaye nasauka ahnkl yanzu shikenan haka zatai tazama tamkar hoto miji bayako bi takanta ?
Shikam shushu tunda yashige anan sofa ya kwanta cikin falonsa , jikinsa har wani rawa yakeyi yakosa yasan meke kunshe cikin wannan diary din
Ahnkl yafara karantawa harya kare hawaye nake hangowa suna zarya akuncinsa , tsananin son Aysha da tausayinta ke cika zuciyansa, dama Aysha shine mutumin datakeso ? Meyasa yakasa nuna mata so awancan lokacin
Meyasa bata sanar dashi shine muradin rantaba? Meyasa har ayanxu tacigaba da boye son tana wahal da zukatansu baki daya?
Abubuwan daya dingayi mata narashin kyautawa ne suka dinga dawo masa, gaba daya jiyayi yatsani kansa , wutan soyayyan ta kesake ruruwa cikin zuciyansa
Afili yake fadin"ina sonki esha yana kaunarki zan kuladake zan mallaka miki dukkanin zuciya da gangar jikina , zanbaki kulawa tareda tsantsan soyayya esha
Wlh inasonki matata ina sonki zankuma rayu dake har karshen numfashina , rungume diary din yayi tamkar Ayshan ce rungume akirjinsa
Hawaye yakeyi sosai natsananin tausayinta ahaka har baisan sanda barci yasace shi , cikeda mafarkin wai gashi suna shinfida kyakykyawar rayuwa da eshan ba

*58*
*5* *DAYS LATER*
Cikin wadannan kwanakin daya kasance 6days dakawo Neesa cikin gdn shushu, babu abnd ya hadasu domin sam bata gabansa , hasalima bayi son ganinta sam
Tunani da tsananin damuwa yasata rama sosan gske illah haske data karayi , ayau dai takudiry aniyan fuskantansa ayi wacce za'ayi domin tagaji
Misalin 10nadare taji shigowansa part din nasa, sanye take cikin sleeping gown wacce batada maraba da kyallen tatan koko
Babu abnd baka hangowa na halittar kiran jikinta , qamshi ketashi ta kowani lungu da sako na jikin nata
Batadamu data sanya hijab ko zani akan shigan nataba, domin so take tajanyo hnklnsa ya biyamata kwadayin dake addaban zuciyanta, domin tana cikin kewa da bukatuwan hakan , domin ayanxu babu mai debe mata kewan hakan
Shureim yafito daga bathroom kenan yana sanya jallabiya , dakin gaba daya sanyi da qamshi ke fita daga dakin
Ya aje kwalban turaren daya gama fesawa kenan ya juya zuwa beddinsa, yaji karan murda handle din kofa
Baidamu sam daya san kowayeba illah daukar phone dinsa dayayi , yana turawa sahiban zuciyansa ayanxu wato esha
Qamshin dayake shakane yake karuwa a kafofin hancinsa, hakan yasa ya aje wayan byn yatura mata sakon , mai dauke da kalamai masu matukar nauyi dasace zuciyan duk wacce yakamu da kaunarsa
Idanunsa yasauke akanta wacce ke tsaye takasa karisowa , domin yadda tasami kirjinta na tsananin bugawa
Dauke kansa yayi yakwantar bisa pillow tareda maidasu ya kulle , batareda ko kwakwkwaran motsi yasake yiba , illah hancinsa dahar yanzu ke shako masa wani irin sassanyan qamshi
Ahnkl Aneesa take takowa har zuwa bakin bed din tazauna , zuciyanta ya tsinke bugun kirjinta yakaru
Cikin wata irin murya tafara mgn tana fadin"shureim ina rokonka gafara dakayafemin kadaina tsanata, wlh duk abnd na aikata sharrin shaidan ne da kuma tsananin bukatar aure wanda mahaifina yakasa bani goyan baya
Kaji tausayina ka tallafi rayuwata kona ji dadin yin tabbatacciyar tuba shushu, nasani kana kyamata ka kuma tsaneni , wlh shureim son ka gab yakeda ya illah tani inasonka , inajinka har cikin jikina
Idn baka yafemin ka dawo gareniba jinake tamkar zan iya rasa raina ko inkoma ruwa ,plzz ya sh.......... "
Wata razananniyan tsawan da shureim yadaka matane yahanata karisa kalamanta , idanunsa gaba daya sun sauya launi yake dubanta , byn yasa hannu ya hankadeta daga kusa dashi
Kasan carpet ta zube tana gunjin kuka cikin kausasasshiyar murya yafara mgn"yimun shiru kazama mayaudariya kawai harni zaki sakoma wannan dan iskan kayan kishigo inda nake kina fadamin wadannan banzayen kalaman ?
To bari kiji Aneesa duk iya sonda nakemiki ayanxu natsaneki Neesa, bazan iya rayuwa dake cikin wannan kazamar rayuwan dakika aikata ba
Na gwammaci sonki yayimin illah akan insake baki zuciyata , kitashi kibarmin daki tun ban miki wulakanci mafi muni cikin rayuwanki ba
Wato kega 'yar iska mara aji ko ? Kinbiyo miji har turanka sa domin tsabagen jarabar da kikeda shi wannan wani Irin rashin ajine da akuyanci haka ?
Koda yake bazanyi mamakiba idn nayi la'akari dake din wacece , wani tsawan yakuma daka mata yana mai runtse idanunsa bayi kaunan kokadan yasake daura idanunsa asuranta don karma ta haddasa fitinan datake buri cikin zuciyansa
Fadi yake I said get out Plzz , kada kibari insake repeating words dina akanki , stupid gal "
Kaman kasa ya tsage haka Neesa keji don tsananin kunya datakaici , bata taba tunanin shushunta zai iya rintse ido yaci mutuncinta har hakaba
Wani bakin cikine ya turnuke zuciyanta aguje ta fice daga dakin tana kuka wiwi gawani tsananin sha'awansa da sonsa dake addaban zuciyanta
Tabbas ayadda takejin zuciyanta dazata sami wata abokiyar har ka bataji zata iya hana kanta aikata koma miye domin samin nutsuwa, wa'iyazubillah
Dukkaninsu haka suka kwana xuciyoyinsu sam babu dadi ko kadan
****Washegari tun safe shureim kejin sa cikin wata iriyar nishadi domin ayau zai tattara yakoma part din cwt dinsa Aysha
Misalin 11am yafito anan falo ya tadda Neesa , kallo daya yaimata yaga yadda idanunta suka tasa har abn yaso ya dami zuciyansa
Kisameni a part din my cwt wifey ya furta batare daya tsaya amsa gaisuwan dayake mata ba ya fita
Kai tsaye part din eshan yanufa cikeda dokin son ganinta , domin rabon dayasata a ido tun randa ya kwace mata diary dinta
Koya shiga part din bata yarda sam suhadu dashi harya gaji yabarta domin yasan rananshi nazuwa , yau kenan dayake jinsa tamkar sabon angone shi
A falo yasameta kwance rikeda waya ahannunta gama kalacinta kenan , tadawo cikin falon ta kwanta tana sanye cikin skin tight pencil skat wanda idn tamike tsayinsa da kadan yazarce guiwanta
Sai wata guntuwar top milk color yayinda sakat din yazama black , fadin kyawun datayima bata bakine gashinta yakwanta abayanta sai qamshi take zabgawa kawai abnta
Tunkafin yayi sallama qamshinsa ne yafara iso mata , hakan yasata sake gyara kwanciyanta byn ta amsa sallaman ahnkl
Karisowa yayi idanunsa nakanta harya iso yazaune kusa da ita byn yasa hannu ya kwashe kafafunta dake mike
Yadda tadauke kai tana gaidashi ne yasashi kai hannu yadagota gaba dayanta , bai mata masaukiba sai akan jikinsa yana kokarin sanya idanunsa cikin nata
Gud morning ya shushu tafurta ahnkl tana tunzure baki , tamkar zata fashe da ihu bai amsa ba sai kawo yadago da fuskanta ya sunbata
Kansa yamayar ya cusa akirjinta yana shakan fitinannen qamshinta dake jefashi cikin shauki
Ahnkl yakai bakinsa kunninta yana fadin"I really miss u my cwt esha meyasa kikeson wahal da zuciyoyinmu bayan dukkaninmu munsan bazamu iya rayuwa batareda junaba umm? Baby I luv u .... Ya furta cikin wata irin murya daya tada tsigogin jikin eshan baki daya , yana sake cusa kansa akirjinta tareda sauke ajiyan zuciya
Sallaman Neesa da shigowanta yasa Ayshat saurin kallon bakin kofan , ganin wacce ketsaye ta harde hannuwanta akirji tana kallonsu , tunda kujeran dasuke yana facing bakin kofanne
Kokarin kwace jikinta takeyi amma sam shushun yaki bata daman hakan, kallonsa yakai ga Aneesan yana fadin "bismillah mana yayi mgn yana Hade fuska tareda gyarawa Ayshan zama ajikinsa "
Saida Aneesa tayi matukar danne zuciyanta kafin ta iya karisowa tazauna , murmushi ta kakaro tana fadin"ina kwana Anty Aysha"
Sosai eshan taji tausayinta domin tana karantar yanayinta , tareda hango kishi karara akwayar idanunta , itakanta bataso Neesa tagansu cikin irin yanayin dasukeba , domin dole zuciyanta yasosu
Saidai tagane laifin shushun ne da gayya yasake matseta ajikinsa domin yabakanta ran Aneesan, cikin sanyin murya Aysha ke amsa gaisuwan da fadin
"Lfy lau Amaryanmu ya kadaici ? "
Shushun ne yayi gyaran murya kafin yafara mgn dafadin"to ina godia ga Allah daya hadamu awannan guri amatsayin ma'aurata
Dukkaninku kunzamo akarkashin ikona ne ina fata zaku hada kawunanku domin bani dama insauke nauyin dake kaina
Ke Aneesa inaso ki girmama esha amatsayinta na babba kibata girmanta , domin koda wasa bazan amince da raini da rashin kunya ba
Ke kuma baby ga qanwarki nan ku zauna lfy nasani bakida matsala , so duka kuriki juna kuzauna lfy domin hakan shizai haifar da kyakykyawan zamantakewa atsakaninmu
Mgn kwanaki nayanke kwana bibbiyu atsakani idn akwai wacce keda mgn o namanta mgn girki ,ga Peter nan kukune ke esha ba bako bane agareki
Shizai cigaba da girki yakaiwa kowani bangare duk mai sha'awan girkawa mijinta dakanta tana iyayi idn akwai mgn kuna iyayi
Yakare yana kallon Neesa data saukar dakai kasa tamkar wata mara gsky "
Jin sunyi shiru yasashi duban Ayshat yana fadin"my cwt any matsala ? "
Girgiza kai tayi ahnkl ta furta "babu ya shushu Allah yahada kanmu yabamu zaman lfy
Allah yakauda shaidan atsakanin mu yabamu ikon yimaka biyayya ameen"
Maganganunta sun masa dadi matuka hakan yasa yasunbaceta yana fadin"ameen my cwt Allah yai muku albarka "
Duban Neesa yayi yana fadin"Amarya kina iya tafiya dama mgn kenan "
Ahnkl Neesa tamike jikinta yayi sanyi kalau tabbas tayi babban kuskure data salwantar da mutuncinta atiti
Yau gashi gaban idanunta shushun ta kenunawa wata so da kulawa , wacce abaya yasha sanar da ita baya sonta zabin mom dinsace, tabbas namiji dan kuna mane wasu zafafan hawayene suka shiga sintiri afuskanta
Adaddafe ta isa part dinta ta zube bisa sofa tareda sakin wani irin kuka mai ban tausayi
****Abangaren Aysha kuwa Aneesa nafita tayi kokarin zame jikinta , hannu yasa yarike kugunta yana fadin"baby plxx kibarni naji dumin jikinki ina bukatar hakan plxx karki hanani kinji babyna "
Lakwas tayi tareda maida kanta takwantar akirjinsa , saida ya jagulata son ransa bata hanashi ba sam domin itama zuciyanta na bukatan hakan
Yana rungume da ita akafadunsa yabata zuwa dining yana rada mata cewa shifa yunwa yakeji baiyi break fast ba
Dakyar yashawo kanta taciyar dashi saiwani narke masa take , shikam gaba daya yasake susucewa akanta yake
Aysha jitake tamkar kada wannan moment din yawuce , domin gani take tamkar ba shushun ta ba yadda yake mata wasu Irin abubuwa dake sata jin nauyinsa
Yana kammalawa yasanar mata zaifita yadawo kuma ta tabbatar tasake yimasa kwalliyar datafi wannan kyau
Itadai da murmushi tabishi batareda ta iya furta ko kalma gudaba
Hmmm
#team shushu #

*59*
Da dare misalin karfe 9pm Aysha ce zaune gaban mirrow tana shafa , tagama shafa lotion kadan a lallausar fatarta, tana gyara sumanta data shafe shi da mayuka masu qamshin gske
Towel ne kadai daure akirjinta tana cikin fesa body spray ne shushun yaturo kofar dakin yashigo
Ta jikin mirrow din take hango yana sanye cikin milk color din jallabiya , murmushi ne dauke afuskarsa harya kariso inda take
Kokarin tashi take tasaka sleeping gown dinta , amma yamaidata ya zaunar wasu turarukan ya shiga sake feshe mata
Kafin yadauketa itada towel din yadire kan gado , bani rigata ya shushu plxx Aysha ta fadi cikeda wani salo na shagwaba
Baice komiba saida ya haye bisa gadon sannan ya kai bakinsa kunnuwanta yana fadin"no baby indai ni za'a sakawa bana bukata "
Yana mgn ne hannuwansa gaba daya yana yawo ajikinta , Duk iya yadda taso hanashi raba jikinta da towel din takasa
Light up yai musu byn yajanyo ta yahade jikinsu gurin guda , akunnuwanta yake mata mgn yana fadin"meyasa kikaita dakon soyayyata batare dakin sanar dani nine muradinki ba baby? Sannan sbd tsabar mugunta kikaso kicigaba da wahal da zukatanmu alhali kin rigada kinsan muna son junako"
Hannu tasa tarufe bakinsa alamun yayi shiru batason mgn, hakan yabashi daman cigaba da sarrafata yadda takeso
Awannan daren shushu yasami wani irin nutsuwan dabai taba tunanin akwaita aduniyaba, sun faranta ran junane tareda nuna junansu yadda suke matukar kaunan kansu
Aysha bakaramar dauriya da jarumta ta nunawa shushun ba , wanda akarshe rungumeta yayi tsam akirjinsa yana hawaye , wata sabuwar kaunanta kesake mamaye zuciyansa
Kalamai masu matukar nauyi da tsayawa azucci yake fada mata , wacce ita Ayshan batasan ma Yanayi ba domin baccinta takeyi sbd yadda tagalabaita
Da asuba itace tafara farkawa tazare jikinta xuwa bathroom , tana cikin wankan saigashi ya shigo
Atakaice dai tare sukai wankan suka fito shiya jasu sallah , byn sun idane Ayshan tacigaba dazama harsai da gari yayi haske tana azkar da karatun Qur'an
Wanda takeyi abayyane cikin sanyin muryanta , koda ta ida komawa tayi kan gado inda shushun ke kwance idanunsa fes akanta
Ganin tana kokarin komawa can karshen gadon takwanta , yasashi ware mata hannuwansa alamun ta taho
Noke kafada tayi irin Wanda yara kanyi insunajin daru , cikin tun zure baki taje can karshen gadon ta kwanta
Mirginawa yayi yacinmata baijira komiba yaimata masauki akirjinsa, murya can kasa yake fadin "karki kara yunkurin yimin gardama nida jikina anason adinga min rowansa ko, irin kukan shagwaban dataita mai adaren jiya yafara tsokananta dashi
Matsananciyar kunyansa ne yarufeta hakan yasata boye kanta akirjinsa tana fadin" plxx ya shushu kaga kabari banso wlh kuwa"
I luv u..... My esha ina matukar kaunarki tayadda bazan iya rayuwa babu kega , plxx ki kuladani na baki amanan kaina baby
Ahnkl takai bakinta kunnuwansa tana fadin "I luv u too ya shureim esha nakaunarka fiyeda yadda kake kaunarta domin dasonka narayu tunbansan miye son ba ,
Taya zan iya rayuwa batareda kaiba ? Kaine farin cikin esha ya shushu , plxx ka rike amanata kasoni koda rabin sonda nakema ne kaji mijina
Takarishe mgn tana sake shigar da jikinta cikin nasa"
Yadda taji yasake matseta very tightly ajikinsa ya tabbatar mata mahanganunta sun shigesa matuka
Kin sameni my cwt indai zuciyata kikeso inaso kisa aranki kinsameta , sai yadda kikai da ita esha, kifadi duk abnd kikeso afadin duniyan nan nayi miki alqawarin yimiki shi , koda hakan na nufin shine Abu nakarshe dazan gabatar cikin rayuwata baby
Fadi kome kike bukata agareni my cwthrt "
Shiru tayi akirjinsa tanajin yadda sonsa kesake mamaye zuciyanta, hawayen farin ciki take zubarwa tareda yima Allah kirari cikin zuciyanta , daya mallaka mata zuciyan shureim din alokacin data fara cire rai da samunsa
Ahnkl cikin cool voice dinta tafara fadin"banison komi ya shushu tunda harna sami soyayyar dana dade ina nema daga gareka
Abu daya nakeso kadaukar min alqawari bani fatan kace bazaka iyaba my luv , "
Cikin saury yake fadin "fadi koma miye esha zan yi miki fadi bukatar ki kawai "
Inaso kabawa Aneesa duk wata kulawan da mace ke bukata agun mijinta ya shushu
Inaso kasauke duk wani hakkinata dake kanka , kanasonta nasani haryanzu ya shureim , meyasa bazaka yafemata ba ? Banaso ka kasance cikin mara adalci atsakaninmu , banso katashi ranan lahira da shanyayyen sashi , domin kafifitani akanta ko kashiga hakkinta asanadina
Don Allah ya shureim kacikamin alqawarin kula da ita , kasani bijere mata da juya baya agareta babban barazanace ga rayuwanta ayanxu
Aneesa tana matukar kaunarka duk wanda zai kalli idanunta zai hango sonka kwance cikinsu ,
Nasan zafin so nasan yadda zuciya kan shiga cikin garari alokacin da wanda kake tsananin so yajuya maka baya
Baka tunanin karta koma ruwa ? Nasan bukatata yai maka tsaury amma babu yadda zanyi ya shureim , wannan itace soyayyan dazan nuna maka kayi adalci atsakanin mu , kasauke hakkinmu dake wuyanka "
Tunda tafara mgn shushu kejin yadda xufa ke keto masa, meyasa Aysha zatai masa haka meyasa xata bijiro masa da wannan bukatan nata ?
Amma bashida mafita daya wuce cika alqawary domin shine ya tabbatar mata dacewa tafadi komiye zai cika matashi
Ahnkl takeji yana zare jikinta daga nasa , tareda juya mata baya cikin wani irin murya mai matukar rauni yake fadin"why esha? Meyasa zaki zabi wannan ki canza koma miye amma banda wannan, cika alqawarinki na nufin harda kusantar Neesa byn nidake munsan itadin wacece"
Matsawa tayi tareda kwantar da kanta akafadunsa tabaya , cikin murya can kasa take fadin nasani ya shushu kuma wannan itace kadai abnd zakamin insan cewa kana kaunata, zakuma ka iya bani farin cikin danake burin samu daga gareka
Aneesa macece mai rauni datake bukatan kulawanka , ta aikata laifi wanda bafa kai taimawaba tsakanin ta da Allah , ashe kenan bakada hujjan dazaka kasa yimata uzuri da yafiya dukanmu agurinsa muke neman tuba domin muma masu aikata laifine
Karka manta iyayenmu sun aikata sama da abnd ta aikata , meyasa su muka yafe musu ? Muka kasa juya baya agaresu plxx ya shureim kada kabari kasake zama silan jefa rayuwanta cikin wani hali , domin sai Allah ya tambayeka
Ayanxu kiwanta yana hannunka da sauke duk wani hakki nata dake wiyanka ,
Kadaure kamance abnd yafaru abaya mugina sabuwar rayuwan dazamu samu tsira ranan dabama nunfashi "
Takare mgn yanajin saukan hawayenta , duk iya yadda yaso danne hawayen sa kasawa yayi , hakan yasashi juyo da ita suna fuskanta juna
Wani irin runguma yaimata yana jin tamkar yamaida ta cikin jikinsa, tabbas ya amincewa zuciyansa Aysha tadabance cikin mata , irin ta sunyi karanci sosan gske yarasa same zai saka mata dashi domin ta tunasar dashi abnd yashige masa duhu ,
Baisan afili yake mgn ba Saida yaji tana fadin"kasoni har karshen rayuwanmu ka kuma kula damu wannan shine kadai abnd zaka sakamin dashi ya shushu "
Ahnkl ya furta "kinsamu my life inasonki inasonki Ayshat..... "
Daganan wata duniya suka sake fadawa tamkar zasu cinye da juna, sbd tsananin soyayya da kyar suka iya rabuwa da juna
Yinin ranan babu inda shushun ya iya fita suna nane da junansu , komi tare sukeyi
Akwana dayan daya rage masa apart din eshan , fadin irin rayuwan dasukaima alkalamina bazai iya rubutawa ba
Ayshat ta gamsu takuma amince ayanxu shushu nasonta , tagama mallakan zuciyansa sosan gske
Ranan dazai koma part din Neesa kuwa tamkar ansaukar mai dawani bacin rai haka yakeji , Aysha duk tana lura da yanayinsa
Hakan yasata tadinga lallabashi harsuka rabu Lfy , itama cikin karfin hali takeyin komi tana kishinsa sai dai batada daman dazata nuna hakan , dole tadanne matukar tanason yazama mai adalci atsakaninsu
******A part din Neesa kuwa around 6nayamma ne shushun ya shigo anan falo yasameta kwance da wani novel ahannu tana karantawa
Sallaman da yayi yasata dagowa tasauke idanunta akansa, wani mugun kyau taga yasake yimata gashi shagan dayayi ya kara fiddo da kyawunsa
Dauke kai tayi byn ta amsa sallaman ahnkl tareda maida hnklnta kan karatun datake, shima baibi ta kantaba kaitsaye bangarensa yawuce
Baisake fitowaba sai dake kiran magrib, koda yafita baisake shigowa gdn ba sai around 10 , hakan yasashi fadawa bath room ya watsa ruwa
Farar jallabiya kar yasaka yafito falon sai qamshi yake , baiyi zaton zai sameta ba sai ganinta yayi kwance tana kallon wani korean series
Dining ya wuce kai tsaye domin cin abnci ,jallof din cous cous yaxuba sai patotoa salad dayaji liver
Lemun zobo yaxuba cikin cup sai dai kurba daya yayi , yagane banbancin dadinsa dana cwt dinsa, hatta dandanon abncin yaji daban haka dai ya tsakala ya mike
Amaimakon yakoma part din nasa sai zama yayi cikin parlorn , remote control yadauka yacanza channel ya shiga kallo
Abnd yasa Aneesa tashi tsam tayi shigewanta bedroom , byn ta yabi da kallon yana sakin karamin tsaki
Akqawarin daya daukarwa eshan sane yake dawo masa ,ahnkl yakejin wani bacin rai nataso masa tareda kewan eshan har yanaji bazai iya runtsawa bai sanyata cikin idanunsaba
Kaman wanda aka tsikara ya mike yai waje
******koda ya isa knocking yayi akofar falon esha nazaune, suna chart da yusrah gefe guda kuma karan TV ne yake tashi
Cikin shirin kwanciya take tsaf cikin mitsitsiyar sleeping gown babu abnd baa gani na surar jikinta , bata dora komi akaiba illah dai-dai datayi sanyin air-condition na ratsata , domin akwanakinnan garin na Abuja zafi ake sosai
Knocking dayake ne yasata mikewa tana tunanin waye awannan lokacin kuma , saida ta tambaya waye ?
Nine my cwt bude yafadi duk ya zaku tabude kofan , tana budewa ta sauke masa murmushi cikin zolaya take fadin"angon Neesa ya kuma da daren nan ,? "
Harara ya aikamata byn ya ida shigowa kafin yakai hannu yamurde kunninta , kara tasaki cikeda shagwaba take fadin"kai ya shushu dazafi fa"
Saida yadau keta cak xuwa cikin sofa kafin yadireta acinyansa , yana fadin"to bake bane kike tsokanata wato niba angonki bane na Neesa neko ?
Byn tunaninki ne yahanani sukuni nazo adan bani abnd zanji sanyi-sanyi shine ake nema abata raina ko?
Yakare mgn yana wani narke mata tamkar karamin yaro "
Bakinta takai ta sunbaci fuskansa ahnkl take fadin"sorry my chapman aini yanzu bani da abn baka , sai dai kanwata Neesa "
Tureta yayi alamun yayi fishi itako dariya takeyi sosai kafin , tasake hawa kansa tana fadin"haba my habibi harda su turewa to aidai gsky nafadi , kaga yanzufa duk cikin lokacinta muke plxx ya shushu muje narakaka , nima idn akamin haka gsky bazan lamuntaba "
Bai yadda yabarta ba saida yayi abnd zaiji dadi kafin yasaketa , gaba daya saiyaji ya sake kunna wa zuciyansa wutan sha'awantane
Dakyar tarakashi yabar part dinta lokacin 11 hartayi tama wuce
*********koda yashiga kaitsaye part dinsa ya wuce wacce yahango kwance kan gadonsa ne tasa zuciyansa baci
Aneesa ce tayi kwance cikin shigan da dole ta tsokano fitina , pant ce kadai ajikinta sai siririyar bra daba marabanta da babu
Qamshinta gaba daya yacika dakin , sam bataji shigowansa ba domin bacci yafara daukanta , shureim kam tamkar gunki haka yakoma tsaye yayi akanta yana kare mata kallo , wani abu daya dade yana kokarin dannewa azuciyansa ne yataso , dama gashi cikin bukatan kasancewa da mace yake domin eshansa tagama kunnosa
Ahnkl yake rage tsayinsa haryakai bakin beddin yazauna jiyake tamkar ana ingizashi , ahnkl yakai hannu yashafi kirjinta wanda hakan yasata ta motsa
Saurin janye wa yayi ganin tafara bude ido , ganinsa yasata sunkuyar da kanta byn tatashi zaune
Wani kallo yawatsa mata yana fadin"ubanwa yabaki izinin shigowa kikwanta min adaki ? "
Dagajin yadda yake mgn ma Neesa tasan tarkonta yafara aiki , wani far tayi da idanunta tana fadin"haba my shushu laifine don mata tabiyo mijinta ? "
Tsaki yaja yana fadin "okey ! Okey nagane mekike nema "
Sake kwanciya tayi ta juya masa baya , wani abu yaji ya sake sukan shi akirji kashe hasken dakin yayi zuwa mai duhun haske , tareda rabawa ya kwanta
Tsayin mintuna zuciyansa nacigaba da bugawa , qamshin dayake shaka nasake kashe jikinsa , ahnkl Aneesa ke matsowa garesa harta kawo kusada shi
Jikawai shushun yayi tafado kansa tareda rungumeshi , wani irin bugun zuciyansa ne yakaru , sam yakasa tureta daga jikinsa
Hakan yabata daman hade fuskansu guri guda tana sake goga kirjinta anasa, duk yadda shushu yaso ya kaucewa faruwan wani abu atsakaninsu yakasa
Lokaci guda Aneesa tacire duk wata kunya tafara sarrafashi da kalolin wasnnin dasuka gigitashi, harbaisan lokacin daya fara maida martaniba ,
Alokacin dakai afkuwa zata afkune Neesa taraina kanta , domin karon farko kenan dazata fara sanin namiji arayuwanta
Kokadan ya shushun bai saurara mata ba ta gurzu matuka ahannunsa ,lokacin daya dawo hayyacinsane ya dubi Neesan wacce ke kuka na irin axavan datasha
Tureta yayi daga jikinsa tareda juya mata baya , zuciyansa ne yafara tariyo masa munanan pics da kazamin vedion daya gani
Bakin kici ne yamamaye zuciyansa alokacin daya tuno yadda yashigeta, sam baisha wahalan daya kaman lokacin dazai mallaki eshansa ba
Uwa uba sam baiji tsananin gamsuwa daga Aneesan ba , duk da dai yakashe abnd kedamun zuciyansa , wani mugun son eshansa ne da wani martaba nadaban data sake samu acikin zuciyansa
Tabbas Aneesa ta bata wayonta , yanaji azuciyansa zai cigaba dasauke mata hakkinta na aurene badon yasami cikakkiyar gamsuwaba,
Wannan yanaga eshansa ita kadaice sirrinsa , ayanxu bayaji zai iya hada soyayyanta guri guda dana Neesa, tabbas ada yasota sonda baitaba tunanin kaifinsa zai iya dakushewa ba ,
Koda asuba tayi bathroom yashiga yai wanka , baiko bi takanta ba ya wuce ya tada sallah ,idarwansa yayi daidai da fitiwan Neesa daure da towel
Ficewa tayi zuwa bedroom dinta zuciyanta dajikinta sunyi sanyi , ganin yadd shushun kema ta wani wulakntaccen kallo
Tabbas rashin kai budurci babban masifane ga diya mace , saidai wani gefe nazuciyanta yasake cika da matsananciyr soyayyan shushun ne
Harta idar da sallah takoma ta kwanta , zuciyanta asanyaye yake tasani da'ace yasameta acikakkiyartane zuwa yanzu dayananan yana tarairaya da lallashintane
Danasnin da bashida sauran anfani shita dingayi har bacci yasake daukanta
*Agurguje plxx*
*One month later*
Zaman lfy tareda kwanciyan hnkl ne kewanxuwa agn shushun, Aneesa da Ayshan sun hada kansu suna wani irin zamane , mai cikeda girmama juna da kuma fahimta
Aneesa ta kwantar dakai tana bin Ayshan tateda bata girma , sam basa kishi irin na jahilan matan yanzu , wanda son zuciya darashin wayewa kedamunsu
Kowacce kokarin kwantar da hnkln mijinta take , tareda kokarin ganin takafa gwamnatinta mai karfi
Babu laifi shushun na kokarin bawa Aneesan duk wace kulawa , daganin ya kwatanta adalci
Saii dai eshan itace tauraruwan dake haskawa cikin zuciya da gangar jikinsa , irin yadda take nuna masa so da tarairaya nadabance , ya gama amincewa kowace mace da baiwanta ake halittanta
Acikin wannan lokacin ne kuma akasanya baikon Dr sudais da yusrah , wanda akasa 4weeks kacal
*******
Bayan sati guda wanda yakasance yau din weekend ne saturday, Ayshan ce gaban madubi tana kallon kanta tundaga sama har kasa , tasake cika haskenta yakaru matuka babu abnd kedamunta irin yadda kirjinta suka sake cika matuka , kugunta yasake budewa itakanta tasan tayi kyau bakadan ba
Riga da zani tasaka wanda zanin idn kaganshi ajikinta zakayi tsammanin skat ne , kayan sunkamata sosan gske mayafi takeson hafawa gogan nata yashigo
Murmushine dauke a fuskansa har ya kariso inda take tsaye,itama murmushin take maida masa , kansa yakwantar akafadunta yana sunsunan qamshinta mai dadi
Hannuwansa duka na rikeda kugunta ne ahnkl ya sunbace ta yana mata rada a kunni yana fadin"babyna kinganki kuwa yadda kike sake cika , anya ko banyi ajiyata ananba , yana mgn ne hannuwansa nashafa shafaffen cikinta zuwa maranta "
Rike hannuwansa tayi cikin shagwaba take fadin"nikam babu wani ajiyan ka anan nagama shirin mujeko kada Aneesa taita jira kaga babu dadi"
Dunguremata kai yayi yana fadin "kaji mai wayau nida sonayi mudaga fitan zuwa dare , domin yau ...... Akunni ya ida fadamata sauran kalaman"
Tureshi tayi dakarfi tana hararansa yana dariya mai ban sha'awa,tayi gaba shikuma ya sungumi handbag dinta data barshi ya biyo bynta
Atsaye yasamesu daga ita har Neesa wacce itama tagama hadewa cikin doguwar rigan laces tayi kyau matuka, tasake fresh da kyau abnta
Gaba sukayi yana biyedasu rikeda jakan eshan wanda yahanata rikewa, itadai Neesa binsa kawai take da kallo , lokuta da dama takanyi mamakin yadda Ayshan tayi kane -kane azuciyansa
Duk da yana iya kokari gurin takatsantsan din boye son afili idn suna tare , amma hakan baihana Aneesan gane ayanzu Ayshan tayimata zarrah ba
Gdn momy suka fara zuwa daganan suka wuce gdn su Ayshan, sun jima sosai sai dare yazo yadaukesu ,
Aysha sunzanta da ummanta inda take sanar mata da mgn neman auren dayake azaria , wanda zaayi da zaran gadawo daga checkup din daya tafi kasar England
Kwantar mata da hnkl eshan takeyi tana hawaye wanda umman ta tsareta domin jin ma'anansa, anan tafallasa mata sirrin datasani na abnd su Abban suka dade suna aikatawa a BOYE
Umman Ayshan tashiga kwantar mata da hnkl , takara da cewan auren dazaiyi ita shine kwanciyan hnklnta
Bakaramin abu umman tahadawa Neesa ba tundaga kan turaruka , da atamface zuwa tsadaddun sarkoki fashions , tayaba da yadda suka hada kansu suna zaune lfy da juna
Koda suka isa gd kowa part dinta tawuce , inda hakasance Ayshan keda shushun aranan , hakan yasa suka nufi bangaren Ayshan yana tallabe da ita akafadunsa
******cikin satin da akashiga aka sanya ranan auren dady da maryama , wacce takammala istibra'inta hakan yasa aka sati 2 kacal , ana gama nasu da 2 weeks sai ayi na yusrah
Maryama dai haifaffiyar gwarinpa ce , iyayenta sun rasu tun tana 10yrs hakan yasa rukonta yadawo hannun mallam Audi , wan mahaifinta agurinshi ta tashi wanda suke kirada kawu
Duk wata tarbiya ahannun sa da matarsa karima tasameshi , wacce bata taba haihuwaba , har kawo lokacin da maryama tagirma , umma karima ta taka rawa sosai gurin lalacewan tarbiyan maryama
Bakaramin dukiya dady yasakar musu ba domin hidima , momy da yusrah sune suka hada lefen maryaman
Duk iya yadda yusrah da esha suka tsani maryama haka suka danne , aka shiga hidima domin basuda yadda zasuyi hasalima auren nata ita yusrah shine rufin asirinsu da Ayshan baki daya
Domin ko abaki zaifi dadin fadi akira maryaman da matar dadyn , da akirata da dadironsa
Hajiya kubrah ce da hajiya safiya ne zaune abedroom dinta , aranan da aka kai lefen maryaman
Suna zantawane akan irin yadda mazajen nasu suka dade sunacin amanansu a BOYE
Cikin tsananin takaici umman eshan kefadin"momyn yusrah kinsan ba babban bakin cikina irin yadda salman yayi tarayya da karuwan mahaifinsa wacce yasha alwashin aure , wannan abu yayimin ciwo dole mudanne duk wani kishi mukauda kai suyi auren matukar zasu daina bibiyan 'ya'yan iska

*60*
*END*
******
Ana gobe daure auren dady da maryamane Rufaida ta iso garin Abuja domin kawowa Aneesa ziyaran bazata
Aysha tun safe tabar gdn domin sunata shirin biki wanda ita abn yahade mata 2 ne, harda tsare-tsaren bikin yusrah wanda shinema kan gaba
Tabar Aneesa zata taho daga baya , Neesa harta gama shirin ta tsaf tana kokarin fitowa daga part dinta sai ganin Rufaidan tayi
Kirjintane ya buga da karfin gske domin ita harta fara mantawa da ita , akokarinta na shafe alakansu da ita dasukayi abaya , wanda ayanxu burinta ta dawwama cikin gdn aurenta, da shushunta ganin Rufaida ya bata mamaki domin tadauka har abada sun rabu kenan da juna
Murmushin yake shita kirkira tana fadin " oyoyo yau kice nake ganin tamkar amafarki "
Rufaida kallon Aneesa take tun daga sama harkasa , tayi kyau tasake zama cikakkar mace kana kallonta zakasan hutu da jin dadi sun zauna ajikinta
Bata hanya tayi tana gaba Rufaida nabinta abaya har zuwa falonta , cikin lokaci kadan Aneesa tacika gaban Rufaida da kayan motsa baki
Veil din dake kafadunta tacire tana zama kusada Rufaida , sake gaisawa sukayi Rufaida nafadin"gsky aure ya amsheki aminiya wannan irin kyau haka "
Aneesa tadan gimtse fuska tana fadin"Rufaida kema yakamata zuwa yanzu kitsaida guda cikin tarin masu sonki da aure , kiyi aure kidaina aikata irin rayuwan damukai abaya
Bansake nadaman jefa rayuwata cikin wannan kazamar harkanba sai dana shigo gdn aure na babu mutuncin dazanyi tinkaho dashi ,
Na fuskanci wulakanci daga shushu Rufaida , duk yadda yake sona saida yajuyan baya ,
Don girman Allah kima kanki fada Rufaida , bareke da kike tarayya damaza da mata "
Rufaida data tsare Aneesa da idone ta sauke cup din datakeshan juice , kafin tafara fadin"gsky ne Aneesa zanyi kokarin hakan domin gsky nayi sha'awanki sosai
Matsalan wanda nakeso bazai taba amincewa ya aureni ba , duk da cewa shida ubansa duka tantiran ashararaine , amma ya rintse ido yana sanar dani bazai taba aurenanba alhali dashi nafara sanin dadin maza"
Aneesa ce take fadin"kardai kice saurayinki salman dana dade inajin sunanshi abakinki ? "
Rufaida ta kada kai tana fadin "shinake nufi aminiya kinsan kowaye salman Adam kuwa? "
Aneesa ta jijjiga kai alamun rashin sani
Rufaida ke fadin"salman yayan kishiyarki Aysha ne matar shushu , mahaifinsa da mahaifin shureim duka marasa kamun kaine da suka dade suna aikata munanan LAIFUKA a BOYE
Ahnkl Rufaida take sanar da Neesa abnd tasani nadaga ashararancin da surukanta suka aikata aboye
Takare mgn tana fadin ita kanta yarinyar dayake shirin aure bakowa bace face dadironsa "
Jikin Aneesa yayi sanyi matuka tausayin shushun takeji , yadda yafito salihi sai gashi mahaifinsa yana aikata barna , meyasa ita yakasa yimata uzuri abaya ?
Duk da hakan bataga laifinsa akan irin wulakancin dayai ta mata abayanba, tunda gashi suna zaman lfy ayanxu ,
Tausayin esha ne yakamata tana jinjina yadda mahaifinsa yayi dacen haihuwanta , tafito maisanyin hali , nutsuwa sannan uwa uba tasan darajan mutum Aysha kishiyar ce amma hakan bazai hanata fadin kyawawan halayenta ba
Fatan shiriya tai musu dukansu domin bata da bakin data isa tace Allah wadai dasu , domin duk kanwar jace tsakanin LAIFUKANSU da nata banbancin kadan ne"
Hira suka cigaba dayi sosai inda Rufaida keji inama zata sami galaba akan Aneesan data dan huta da ita kona mintunane , sai dai bataga faces din hakanba
Sunanan zaune har around 2:30 shushu yadawo daga masjid , tunda yashigo ya hangi bakuwar mota hakan yabashi tabbacin sunyi baki
Yana shigan part din Neesan yafara jiyo amon muryan Rufaida , muryan da har abada bazai manceshi ba
Sallaman dayayida shigowansa falon ne yabasu daman kallon kofan shigowan, saida gaban Aneesa yafadi ganin yadda yahade fuska tamkar bai taba dariyaba
Fuu yawuce zuwa part dinsa batare da ya tsaya amsa gaisuwan da Rufaida kemasaba
Hakan yasa zuciyan Aneesa yai kololuwa gurin tashi , jiki asalibe tabi bayansa zuwa bedroom dinsa, ganinsa tayi yana kaikawo cikin dakin
Ahnkl takarisa shiga ciki tana fadin"sannu da zuwa ya shushu "
Bai amsa ba illah tambayan daya watso mata "uban me yakawo wannan kazamar cikin gd na ? Metazo yi miye alakan dake tsakaninki da ita ayanxu ? "
Duk ya jero mata tambayoyin cikin tsawa wanda yasa jikin Neesa daukan rawa,
Cikin rikicewa take fadin"wlh babu abnd ke tsakanina da ita shureim , ina shirin fita zuwa gdn momy sai gata , kaga baidace infita bamu gaisaba
Ka amince dani mijina wlh abnd zaka zarga har abada bana fatan sake aikatashi , ta kare mgn tana hawaye "
Hakan yasa jikinsa yin sanyi hannu yasa ya dagota daga durkuson datayi , yana share mata hawayen fadi yake "its okey wlh natsaneta ne baniko son ganin kazamar nan cikin gd na , don haka kiyi gaggawan sallamnta kuma wannan yazama karo nakarshe dazata sake takomin cikin gd na right? "
Ahnkl ta gyada kanta sakinta yayi yafice tana sauke ajiyan zuciya, Rufaida tagani tsaye rataye da jakarta alamun ita kawai take jira
Karisowa tayi tana kokarin kakalo murmushi , take fadin"badai tafiyaba aminiya ? "
Tafiya zanyi Aneesa sai kuma wani lokacin , wata leda maidauke da turaruka ta aje mata kan kujera, godia Aneesa tayi tarako Rufaida har gurin mota sannan takoma
Afalo tasamesa rikeda wannan ledan da Rufaida ta aje yana juya turarukan dake ciki , wadanda akalla kowani guda zai zarce 12k
Asanyaye takariso tana kallon yadda yake jifanta da mummunan kallo , kafin ya furta "miye ma'anan wannan kyautar anya ko ba biko tazoba , tokisani bazakiyi anfani da wannan turarukanba , ya fice dasu kai tsaye baba mai gadi yaba yace yakaiwa iyalinsa
Shiya sauketa agdn momy kafin wuce gurin Dr sudais
*2* *weeks later*
Aka daura auren maryam alqasim da Alhaji shu'aib akan sadaki 50k , bawani shagulgula akaiba amarya ta tare adaya cikin gidajensa dake wuse
Ko kadan momy bata takan wannan auren bare kuma yusrah da shirye-shiryen bikinta yasha musu kai itada Aysha
Hakan yaba dady samun daman cin amarcinsu da tsohuwar kilakinsa maryama , wacce tasha gyara ciki da waje bakaramin morewa juna sukaiba
Tunda bikin yusrah yakasance saura one week babu ranan da Aysha bazata gdn momy ba , bakaramin korafi take sha agun shushunta ba harsai da momy tai masa fada sannan yagaji yadaina mita
Ranan saturday dubban mutane suka shaida daurin auren Dr sudais da yusrah akan sadaki 100k
Aka zarce da shagulgulan biki wanda ana kai amarya aka zarce gurin hadaddiyar dinner , fadin kyawun da yusrah tayi ita da angonta ba'a mgn
Esha da shushunta da kuma amarya Aneesa ne zaune guri guda , sunci ado nakece raini lokacin da aka kira amarya da qawanyenta domin dansewa ne eshan tamike tsaye domin zuwa filin
Hannunta shushun yariko yana fadin "baby ina zuwa badai gurin can zaki shiga kina juya jiki kartan banza nakallemin keba ?
No sam ban aminceba my cwt "
Bata fuska tayi ta shagwabesa tana fadin"haba mana habibi manni kadaifa zanyi mata , to idn kana kishi ne let's go together
Takare mgn tana riko hannunsa tareda kai masa sunba , saukan flash tako'ina sukeji batare da sunsan hnkln masu daukan nakansu ba
Tana rungume abarin damansa yayinda hannunsa daya rikeda dana Aneesa , haka suke keta mutane har suka shiga filin rawan
Kudi bana wasaba suka kikema yusrah dinner yakayatar matuka , byn antashine aka mika amarya dakinta
Dake son city anguwa daya da aminiyan nata , sai dai su sunshiga ciki sosai bakaman shushu da suke daga farko ba
*After 3 month*
Aysha da salman da kuma hajiya safeeya ne akan Alhaji Adam, wanda yadawo daga England watanni 2 da suka wuce
Tunda yadawo babu lfy jiki yarikice , yau 2 days kenan da faduwansa a toilet yasamu mutuwan barin jiki
Wanda hakan yashafe zancen aurensa da sameera yarinyar dayake shirin aure, sameera itama bawata mai kamun kaibace abokin kawalancinsu ne yayi masa hanyarta , har yaji tayi masa aka kulla zancen aure
Saidai tunda taji abnd yasamesa tace babu ita babu shi ,
Sam baisan wanda ke kansaba hakan yasa dukansu ke zuban hawaye , Aysha tafi kowa shiga cikin wanihali gani take tamkar bazai tashiba
Washegarin ranan salman da shushu dakuma dady da umman Ayshan ne suka daga dashi zuwa Dubai
Domin ganin kwararrun likitoci , kwanan shushu da dady 2 suka jiyo alokacin Alhaji Adam yadawo hayyacinsa yana sanin wanda ke kansa saidai sam babu baki baya mgn
Umman da salman aka bari domin kula dashi , tunda suka tafi Aysha tasoma ciwo itama , awashegari momy da Aneesa ne suka kaita hospital , byn gwaje -gwaje ne aka tabbatar masu da cewa tana daukeda juna biyu 2 month
Momy gdnta tawuce da ita duk da cewa Aneesa tayi magiyan zatakula da ita amma fir momyn taki amincewa dahaka
Ranan su shushun suka sauka a 9ja shida dady , tun a airport yake neman line din eshan sa amma akashe , hnklnsa bakaramin tashi yaiba
Itakuma Neesa yayi ringing harya tsinke bata dagaba, tana can tana shirya masa abnci , domin ayanzu itama koyi take Ayshan ganin bata yadda shushun yaci girkin Peter
Dady kansa yana lura da son dinsa sam hnklnsa ba'a kwance yakeba , dady aka fara saukewa ko gdn shushu baishigaba yasa driver yawuce dashi gd , domin hnklnsa nakan cwt dinsa
Koda suka iso kai tsaye bangarenta ya nufa sai dai akulle yake , hakan yasa hnklnsa yasake tashi