← Book details Kalbim Part 2 complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 5 OF 8

Chapter 4

Kalbim Part 2 complete Hausa Novel · about 10 min read

Suna isa gida Maheer jin yayi gabaki daya garin ya fita ransa kauye ma kawai yake son komawa sbd zuciyarsa ta huce daga radadin datake masa,
Ammar ma jin yayi kamar ya hakura da neman aikin gwara su fara wata sanaar su fara Gino kansu daga nan sbd baa taba cin fuska da mutuncinsu kamar yau din ba da zaa kalli girman takardunsu da babu inda ko a ido zaa samu ganin irinsu ba ace wai zaa basu aikin securities a matsayin masu gadi Jannah da suke gwagwarmayar neman komai dan inganta rayuwarta data Ummah ace suma a matsayin masu aiki,wace irin cin mutunci da tozartawa ce wannan?
Modibbo ganin yanayin da suka shiga ya saka ya dakata daga musu magana ya bari sai sun koma gida tukuna amma kam wannan aikin shi a gurinsa kamar anyi an gama ne Banda rashin godiyan Allah irin nasu tayaya zaka samu aiki irin wannan ka tsaya wani duba darajar kai da duba girman iliminka,
Banda sun samesu masu zuciyar tausayi da duba zumunci uban me zai saka su karbesu su basu gurin zama Harma da abubuwa da yawa harda gurin nema da basu damar sanaa tinda su a lokacin da suke cikin daularsu basu taba tinawa ma da akwai dangin kakarsu kakarsu a kauye ba saida suka hadu da qwallon shegen da baya barwa Allah ya fisu zama dan ta'adda ya ruguxasu tukuna suka nemesu.
Har dare babu me walwala a cikinsu sunyi sanyi sosai haka suka kwana bama tareda sun nema wani abincin kirki sunciba.
Washe gari suka so komawa amma Maheer ya daure ya dangana suka sake fita neman aikin Wanda kamar hadin baki babu inda suka samu komai sai wulaqancin dayafi na farkon dan akwai inda aka daukesu amma wai shi Maheer din driver shi kuma Ammar security a kamfani.
Modibbo ganin hakan yasa suka aje maganar aiki suka bisa sabgar kasuwancinsa data kawosa suka koma yawon kasuwannin hatsi da dabbobi a haka suka cike kwanakinsu suka tattaro suka dawo.
Dan abinda ya rage musu na canjin da suka samu a kasuwa tareda modibbo suka siyowa Jannah da Ummah sabin takarmi da dogayen riguna masu dan kyau da turare da sabulun wanka me kyau da toothbrush da sabon brushes na dukkaninsu su biyar sbd iya kokarinsu basa son Jannah ta rasa kyan sigarta ko yayane bazasu iya bari ta koma abar tausayi ba tinda sun fito zasu nema komai su kuma qarar da koman akanta da Ummah.
Jannah ce ta fara samun labarin isowansu a bakin yaran gidan daketa ihun modibbo ya dawo dan haka ta wanke hannunta ahankali daga gama gyara daure dogon gashinta da fatma ta gama mata kitso me kyau.
Kofar shigowa bangarensu ta kalla daidai lokacinda Ammar ya fara sako kai da sallama ta sake murmushi me kyau da nutsuwa na farin cikin ganinsu zuciyarta na sanyi me dadi ta karbi babbar jakar hannunsa tana cewa
"Welcome Ammar Zad"
Sanyi daya mamaye zuciyarsa ne na saukan muryanta kunnensa da yanda haryanxu take kiransa yake kashesa akanta take quncinsa ya narke yabar kirjinsa murmushinsa me kyau shima ya bayyana yana qarasawa ya zauna a kujeran data tashi Yana cewa
"Thank you Jan,
Yaya kauyen nan?
Ina Ummah
ne ta shiga?
Hannu ta miqawa Maheer suka gaisa Ya jata zuwa shimfida suna kokarin zama Ummah ta fito dgaa daki tareda Dad da zai fita suna ganinsu Ummah ta sake fuska sosai tana kallan Ammar da shima ita yake kalla Yana nuna mata gefensa taxo ta zauna ya fidda Apple Guda biyu daya siyo mata ya miqa mata Yana cewa
"Ci wannan kiji yafi wancan mangwaron nasu garba me shegen tsami da saka ciwon ciki"
Cikin farin ciki me tsanani Umman tace
"Da gaske kake?
Wannan yafi wancan dadi kace??
Gyada kai yayi yana dariya
Juyawa tayi ta kalli dad ddaa farin ciki sosai a fuskanta alamar hakane
Yana dariya cikeda kulawa da wani irin sanyin kaunarta dake cikeda zuciyar Dad din ya gyada mata kai yace
"Yes kici zakiji"
Maheer ta maida kallanta akansa har lokacin farin cikinta a bayyane yake
Dariya shima yayi Yana gyada mata kai alamar eh
Zata kalli Jannah
Jannah din Tai saurin karbewa tana cewa
"Bara na wanke muji ko Ummahna"
Da sauri Umman ta miqa mata dayan tana cewa
"Wanke duka mu cinye"
Maheer dake kusa da ruwa ne ya miqo musu Yana cewa
"Ba kudine ai da ansiyo da yawa tinda nasan Ummah zata so shi sosai dan nima bana son suna shan mangwaron nan kwata kwata"
Jannah cikin kulawa ta bawa Ummah tana cewa taci.
Dad ne ya kalli Maheer Wanda shima shi din ya kalla kafin suka kalli Ammar suka miqe dukkaninsu suka fice zuwa waje.
Suna fita Jannah ta bisu da kallo sbd tin shigowansu taga damuwa boye a tattare dasu.
Suna fita masallaci suka fara nufa sukayo sallar laasar kafin suka dawo a hanya Maheer yakewa Dad bayanin abinda ya faru.
Shiru Dad yayi zuciyarsa na sanyi da damuwa kafin yace
"To Allah yasa hakan shine mafi alkhairin ya kuma kawo mana wata mafitar"
Amin" suka amsa dashi suna qarasawa gida.
Abinci suka ci da daddaren kafin suka fidda siyayyr da sukayo musu,
Fira suka hau yi hankalinsu kwance cikeda kulawa da juna har dare sosai kafin kowa ya shige.
Da sassafe Garba ya shigo bangaren yayi sallama ya sanarda Dad su Modibbo na son magana dashi.
Fitowa Dad din yayi daga daki Yana saka hular sanyi a Kansa sbd akwai sanyi ya fice Maheer na bayansa Ammar be tashi ba hakama Jannah da Ummah.
Tin daga nesa Maheer ganin irin kallan dasu kawu ke jeho musu da irin yanda suka zauna babu me faraa a fuska ya san akwai inda aka samu matsala.
Dad a natse ya qaraso yai musu sallama ya nema guri ya zauna suna gaisawa.
Maheer ma gaidasu yayi cikeda girmamawa kafin ya zauna dga gefe kan dutse.
Shiru gurin yayi tsit kafin Kawu Jibo ya bude baki yace
"Dzad kasan da labarin su Mahe sun samu aiki me kyau da asirinka da nasu harma da namu zai rufu sunqi karba sbd girman kai da ganin sunfi karfin hakan?
Kai tsaye Dad yace
"Wane aikin ne wannan??
Modibbo ya karbe da cewa
"Aikin securities me kyau da albashi me tsokar gaske"
Numfashi Dad ya sauke yace
"Ni bana takura yarana akan abinda basaso ko basuyi niya ba sbd kawai ina cikin talauci,
Idan har tin acan since bazasu iyaba to shikenan din bazasu iyaba"
Wani kallo kawu isiya yayiwa Dad din cikeda mamaki da siqewa tareda takaici yace
"Kenan dai sun fada maka kuma ka goya musu baya?
Harkar samu?
Harkar ci gaba sbd kada mu lasa arziki shine kuka taru kuka yanke shawarar bazasuyiba"
Kawu Jibo daya gama cika shima da baqin ciki kai tsaye yace
"To Ni kawai aban kudina dana bayar bazan iya wannan kayan baqin cikin ba tin yanzu anfara kafin ayi nisa,
Dubu sittin cif a miqomin abuna yanxun nan inada abin yi dasu"
Kawu isiya ma cewa yayi
"Eh gaskia indai bazaa karba aikin da aka gani a kasa ba nima aban kudina bazan iya jira ba dan ba ranar samun wani aikin gwara aban na fara wata sanaar dasu kawai"
Modibbo daya rasa abin fada kallan dad yayi ya gyara zama Yana tattaro nutsuwarsa yace
"Dzad ka nutsu ka duba lamarin rayuwar dake gudana a yanzu,
Kai din baya ba kai bane a yanzu
Hakama yayan naka da sunan da mutuncin da matsayin duka basu bane a yanzu,
A baya idan akace Zaadens magana ake ta masu qasa da wajen qasar ma amma ka duba a yanzu a ina kake?
A ina rayuwa ta dawo da kai.
Maheer ya kalla yace
"Kai Mahe inace cewa kukai zaku sake farowa daga farko ku sake gino Zaadens da guminku da gwagwarmayar da duk ya kamata,
Idan da gaske hakan ne to banga dalilin qin karban aiki kowane irri bane indai bana haram bane ko sabon Allah,
Aikin nan fa bana dindindin bane ku karba ayi na dan lokaci ana samun abin Gina kai saiku ajiye ku fara duk kasuwanci ko aikin da kukeso,
Dan haka xabi dai anan biyu ne kodai ku karba aikin nan ku samu damar fara kafa kanku kokuma ku tabbata anan kauye cikin wannan rayuwar da bakwason ku mutu a cikinta,
Hakama dukanmu idan lamarin bazai yiyuba muna buqtaan kudinmu a cif cif ba bata lokaci"
Shiru Dad da Maheer sukai jikinsu a mace zuciyoyinsu a jagule da maganganun su Kawun.
Ajiyan zuciya Dad ya sauke kafin ya kalli su Kawun yace
"Ba damuwa inshallah zamuyi shawara muga abinda zai yiyu gameda biyan kudin"
"Ah ah bawai shawara ba muji shiru,
Aikin nan dai modibbo yace kada a wuce dan lokaci Idan ba hakan ba zaa rasa dan haka ayi me yiyuwa asan nayi"
Kawu Jibo ya fada hakan Yana sake matse fuska.
"Inshallah zaa kokarta kafin lokacin" Dad yace Yana miqewa yabar gurin Maheer na bin bayansa.
Suna isa ciki babu Wanda yayi magana saima shiri da sukai suka fice bayan sun karya da madara da zafi da waina
Se yamma sosai suka dawo,
Dare nayi suka ci abinci gabaki dayansu a tare kafin Dad da Maheer suka sanar da Ammar abinda yake faruwa da kuma tafiyar da zasuyi goben hadda Dad su sake bazama neman aiki koda bana office ba koda na manyan shaguna ne haka ko supermarket ganin sukeyi gwara shi akan aikin gadin.
Washe gari tinda sassafe suka sake Aron kudi a gurinsu modibbo suka wuce.
Tinda suka tafi Jannah ta maida hankalinta ta duqufa a gurin adduar Allah ya zabar musu abinda yafi zaman alkhairi koda aikin gadin ne sbd ta jima da ajiye matsayinta na princess Jannah Zad koina ne indai zata zauna ta rayu da familynta cikin kwanciyar hankali batada damuwar komai.
Kwanansu Dad goma sha shida suka dawo babu Hasken komai a tafiyar sbd duk inda suke saka ran samun wata mafitar babu,
Aiki harna tsaron shaguna da wasu guraren sun nema basu samuba gashi duk bashin da suka laftawa kansu ya qare ba aikin.
Bayan dawowansu su kawu suka sake bude wuta akan a basu kudinsu har abin yakai anfara samun matsala da damuwa sbd tini abin ya koma hadda gori da fade.
Dad ne ya samu su Kawun a Karo na ba adadi cikin nutsuwa ya sake rokonsu akan su qara musu lokaci.
Budar bakin Garba dake tsaye cewa yayi
"Baba ni idan zaka yadda inason Jannah a bani aurenta na bada dukiyar aure se abiya bashin da dukiyar Harma ayi canji"
Wani Amai ne me karfin gaske ya kubcewa Ammar dayake bayan Dad tsaya jin maganar Garba kamar saukar Mummunan qarnin kifin daya kwana cikin ruwan jini.
Maheer ma dagowa yayi yana yiwa Garban wani mummunan kallan baqin ciki me tsananin gaske.
Dad su kawun ya kalla yaga babu Wanda ya shiga mamakin zancen da alamar sun dan da maganar dan haka take yaji gabaki daya kauyen ya fita ransa fit sbd gwara mai aikin gadi daya nakasta rayuwar Hasken idaniyarsa.
Bude baki modibbo yayi yace
"Daman ta isa harta wuce aure kuma kila sbd itane basason aikin gadin sbd bazasu iya barinta ba hakama bazasu iya barin taje aikatau ba dan haka gwara AUREN nima na amince dashi"
Kawu Jibo ma kai tsaye yace ya amince shima.
Dad kuwa idanuwansa ne sukai jajir ya saukesu akan su Kawun sbd ya gama fahimtar toxartasu kawai suke son yi sbd suna rabe a gurinsu dan haka gwara ma su tattara din su qara gaban,
Bude baki yayi zaiyi magana Ammar da idanuwansa sukai jajir hannuwansa na rawa sbd wani irin azababben kishin dayaji Yana neman kashesa take ya riga Dad cewa
"Dad pls mubar nan koda a aikin gadin ne zan iya mutuwa idan naci gaba da zama anan"
Maheer ma kai tsaye ya amince da hakan Wanda shima Dad ya gwammace su tattara su tafi gurin aikin tinda zasu zauna gabaki dayansu guri daya cikin aminci.
#MAMUH
#BEST LOVE STORY
#AZIZ AY LIMBA
#ZAADENS
#JANNAH LIMBA
ZAFAFA BIYAR*_KALBIM_*
Mamuhgee
Book 2
Chapter 5 · 0% Book details