← Book details Kalbim Part 2 complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 2 OF 8

Chapter 1

Kalbim Part 2 complete Hausa Novel · about 7 min read

BismillahirRahmannir.
Kumar yanda hausawa ke fada qasar kabari bata kisa sedai ta binne binnannnniya,
Wahala,kunci,talauci,sauyin rayuwa da munin kaddara bai kashe Zaadens a rayuwar da suka samu kansu rana tsaka ba saima karfin imani dana zuciyar karban kowace irin kaddara datazo musu da hannu bibbiyu,
Rayuwa a kauye ta zuwar musu a tsananin da suke ganin kamar bazasu iyaba sbd rayuwa ce da babu ko a mafarki da suka taba jin labarinta bare tsintar kansu acikinta,
Rayuwa ce dataiwa tasu rayuwar nauyin da suke jin kamar bazasu kai koinaba zasu mace a cikinta,
Ammar da maheer sunfi kowa zarewa a cikinta musamman Ammar dayake jin kamar zai zare idan ya bude ido yaga a inda rayuwarsa take,
Bandaki kadai wani abu ne me girma dayake tsananin tsoro sbd ganin yakeyi kamar zai fada dashi,
Ranar farko da suka iso kauyen ya shiga Yana leqa masai/shadda da aka nuna masa anan zaiyi kashi tsutsotsi da kyankyason dayaga sunata yawo da motsi a cikin pool na kashi yanke jiki yayi ya some a jikin garba daya rakosa.
Cikeda mamaki da tsoro garba ya ciccibosa ya fito dashi waje yana kiran jamaa.
Su Dad da jannah ne suka iso da sauri tareda su modibbo hankali tashe kowa na tambayar lafiya.
Maheer bandakin ya nufa da sauri dan dubo abinda yaiwa rayuwar Ammar din barazana yana saka kai ya dawo Yana kasa shiga sbd jirin dayaji Yana dibansa na qaton ramin dayaga bakinsa a bude sbd shi baima leqa ba bare yasan meye shi ramin.
Ruwa masu sauyin gaske garba ya zubawa Ammar yana cewa
"Modibbo nifa inaga gamo yayi a bandakin,Aljanu sunga jan bature duk da ance a hakan ya dafe sosai ko?"
Katsesa modibbo yayi da cewa
"Aikuwa dai da alamar gamon yayi,
Maza ku kawo qauri yanzu a turara musu su duka sbd tsari"
Kawu isiya na jin haka ya kalli garba yace Maza debo jar wuta,
Juyawa yayi shima yaje daki ya dauko wasu manyan jakar dinki na kyallen atampa da wani yadi yazo ya zaro wasu daurin mgani kamar na hayaqin bori ya cika hannu ya zuba a cikin wutar da garba ya kawo suka tura su Ammar din da Maheer Harma da Dad dasu jannah a daki suka ringa turarasu.
Ammar sake somewa yayi sbd tsananin azabar hayaqi dayaji yana shigar masa qwaqwalwa da lungs Harma da neman makancewa.
Maheer tare yakeyi Yana neman mutuwa shima baisan lokacinda ya cara zabga ihun azaba ba Yana neman hanyar fita baya ko gani amma garba ya dafesa yana cewa
"Tsari ne da maganin kowane qwaro zaman kauye saida magani a jikin ku"
Jannah dayake sun dan fara sabo da azabar rayuwa da hayaqin sunsha wuya sosai amma ba kamar su Ammar din ba,
Dad ba shiri aka fito dashi sbd mutuwar da sukaga zaiyi shi da Ummah da jannah amma Ammar da Maheer suna sumewa suna tashi haka suka dannesu saida suka tabbatarda ya shigesu sosai maganin tukuna.
Tsoro da tashin hankali me tsananin gaske Ammar ya samu kansa a ciki bayan dawowansa daidai sbd ganin mutanen yake kamar rayuwar dabbobi ba mutaneba sukeyi.
Maheer ma zawo ya ringa yi amma a bayan Gida a daji sbd baya iya shiga bandakin shima tsoron tsugunawa akai yakeyi amma dayake a prison sun iya tsugunawa cikin grasses kashi da fitsari so sun dan saba,
Shima Ammar dole dajin yake zuwa duk abinda yakeji amma se garba ya rakasa sbd tsoro yakeji koina a kauyen.
Dad ma na acikin tsaka me wuya da rayuwar daya samu kansa a ciki me tsanani da wuya amma ganin Jannah ta jure ta rungumi kaddara ta saba ita datake mace kuma yarinya gashi tfara shiga damuwa da ganin yanayin da suke shiga na samun kansu a inda rayuwa zata qara musu tsanani dan haka ya rungumi jarumta ya karbi kaddarar sabuwar rayuwar da suka samu a kauyen Wanda zai sun dangana sun rungumi rayuwar sun karbeta zasuji dadinta da kuma samun nutsuwar da suka rasa ta shekarun da suka wuce dan haka ya nutsu ya shirya rayuwa a kauyen har lokacinda Allah zai kawo musu wata rayuwar kokuma har karshen rayuwarsa.
Maheer ma a hakan dole ya dangana ya amshi rayuwar duk da akwai abubuwan da bazasu iya adapting nasu da wuri ba se ahankali kamar bandakinsu har yanzu tsoro sukeji basa iya shiga,
Hakama cimarsu da sauran yanda suke gudanar da rayuwar ko zasu saba sai ahankali,
Ammar ma sbd kwanciyar hankalin Jannah yayi kokari sosai ya fara karban rayuwar kauyen Ammar ko fitsari baya iya zuwa se tareda garba wanda ya zama kamar bodyguard dinsa kuma abokinsa hakama abokin fadansa sbd kullum sai sunyi fada amma koina Ammar baya iya motsawa yaje seda garba sbd garba akwai karfi da jarumta kuma baida tsoro ko kadan dan haka ko sunyi fada Ammar yayita zaginsa da turanci haka zai koma ya nemesa su shirya dole tinda baida yanda zaiyi.
Maheer ya ari jarumta da gabacin da ko yaushe shine yake dauka a Zaadens ya fara bin su kawu daji gidan shanunsu masu tarin yawa garke Guda da ake harkar fidda nono dasu manshanu da madara da taki dai sauransu harma da kulawa da shanun da kuma kasuwancin abincin dabbobi da sukeyi na hada harawa.
Fara binsu yayi Yana shiga aikin kamar sauran yaran dake aiki yana dan samo yan kudin da zasu riqa ciyar da kansu sbd Jannah ce har yanzu me dan sanaar dake suke dan ci baa maganar sha sbd sunyi kwanaki biyu a kauyen cikin azabar kishirwa karfin suka fara shan ruwan kauyen sbd direct daga kogi ake debosu,
Da farko sunyi fama da yawan ciki da yanayi na rashin kyan ruwan kafin cimarsu kafin ahankali cikinsu da jikinsu suka saba,
Fara fitar Maheer aikin wahala da nema ya dan sake kawo sauki da sassauci a rayuwarsu sbd su modibbo tini suka gama hidimar kwana biyu dasu suka dena kowa tasa ta fisshesa.
Tinda Maheer ya fara fuskantar aikin karfi da wahala ya sake jajircewa gurin neman abinda zai hana rayuwarsu shiga kunci da takura a rayuwar kauyen cikin rufin asiri,
Ammar ya kasa sabawa yanda ya kamata duk yanda yaso kokartawa kawai dai shima Yana jurewa Yana bin garba da abokansa nasu ayyukan daji sedai ya bige da mangwaro yake debowa shi yake siyarwa a kofar gida duk da mangwaron ma baya iya hawa ya debo sedai su garba dinne suke debo masa kuma su tayasa siyarwar sbd suna kaunarsa da tausayinsa duk da Yana shan wuya a hannunsu sbd tsoronsa suke sake rikitar dashi shikuma dole ko yaushe Yana biye dasu yana zagi da turanci.
***Rayuwa taja musu a kauyen wanda lokaci ma yaja Wanda ya saka abubuwa da yawa faruwa ciki harda sake samun tsananin hadin kai da sabuwar kauna me karfi a tsakanin Zaadens,
Hakama a cikin manyan alamarin da suka faru shine AUREN DZAD DA UMMAH da aka daura akan kauna da shakuwa da kusancin da suka samu me tsanani a tsakaninsu duka da Umman data maye gurbi na uwa da aka rasa a Zaadens din,
Kaunar me girma da tsaftar dake tsakanin Umma da Jannah yasaka ta shafi duka ahalinta Musamman Ammar da kusan shima kaunar uwa da kulawan uwa yake tsananin so da buqata tin Yana qanqani shiyasa Mimi ta kasance ta maye ta cike masa wannan gurbin shiyasa rashinta kusan yafi tabasa akan kowa sai kumaa yanzu da Ummah take cike masa wannan gurbin ahankali sbd kaunarta da kulawanta Kansa kamar Miminsa.
Dukkaninsu ahankali suka sani suka fahimci ciwon Ummah Wanda sukai accepting dinta ahakan cikeda zuciya daya da kauna me girma tareda cike ahalin Zaaden da ita ayanzu datake uwa gaba daya a Zaadens dan haka ahalinsu a yanzu y dawo biyar a maimakon su hudu,
Sabuwar kauna me karfi da shakuwa me girma ce take sake gudana a tsakaninsu wanda Ammar yake sake dagewa gurin takurawa modibbo akan aiki dayakeso ya samo musu a birni shi dayake yawan zuwa binnin kuma ya dan San mutane,
Yanda yake tsananin son su samu aikin da Maheer da Jannah da Ummah zasu dena aikin azaba a kauyen yasa ko aikin gadi ko ban ruwa ko wanki da guga ne binni yanason su samu dan haka kullum modibbo ya dawo binni seya samesa da maganar aikinsu,
Ta bangaren modibbon shi Kansa yanason ya samo musu aiki me kyau koda bana office ba Kona gadin ne a manyan guri tinda sunada ilimi me girma d yawan gaske dan haka zaa samu kudi me tsoka dasu dan haka ya dage sosai Musamman dayaga da gaske sunason aikin kowane iri ne dan haka yakeson y samo musu aiki a guri daya.
Maheer ma dayaji ana neman aikin duqufa ya sake yi da nema sbd su samu abinda zasu dan samu gurin zama acan binnin idan ta kama.
#MAMUH
#THE STORY BEGINS
#BEST LOVE
#BEST ROMANCE
#LIMBAS
#ZAADENS
#NEW LIFE
ZAFAFA BIYAR
KALBIM 500
Mamuhgee
KIRJIN ME HANKALI 500
Miss Xoxo
ADUNIYATA 500
Huguma
AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul
09033181070
09032345899*_KALBIM_*
Mamuhgee
Book 2
Chapter 2 · 0% Book details