← Book details Kalbim Part 2 complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 4 OF 8

Chapter 3

Kalbim Part 2 complete Hausa Novel · about 7 min read

Ranar da suka fara fita aiki wuni sukai suna yawo se yamma sosai suka dawo da ledar bread da kosai se ruwan pure water dasu Ammar din sukejinsu kamar ruwan zam zam,
Haka suka kwana washe gari ma suka sake fita modibbo yakaisu gurare kafin ya tafi nasa wasu yan harkokin ya barsu suna sake yawon bincikawa cikin azabar rana da rashin isashen abinci ruwa kawai suke zubawa cikinsu,
A ranar ma haka suka gama yawo suka dawo gida a gajiye suka samu kosai da dankalin hausa sukaci suka hau baccin gajiya da azaba.
Rana a uku wani kamfanin gine gine suka nufa inda wani mutumin modibbo yayi musu hanya suka isa cikeda burin su samu abinda suke so.
Zaman jira suka fara zaune a bakin office din Wanda sukaxo ganin lokaci me tsayi batareda an nemesu ba.
Dago kai Maheer yayi yana kallan koina yana karantar yanayin gurin,
Tsari da yanayin gurin dama mutanen gurin ya saka Maheer da Ammar sauke ajiyan zuciya a Karo na babu adadi sbd Banda rayuwa da sauyin kaddara basuma San akwai kananun kamfani irin wainnnan ba da mutum ma zaiyi tinanin samun albashin da zai riqe kansa harma da wani.
Wani turanci director din gurin ya wuce Yana yi Wanda ya saka Maheer da Ammar kallan juna jiki a mace sbd wannan ko securities dake aiki kamfani ko gadin gidansu sunfi wannan ilimi da lafiyayyan turanci amma wannan ace shine director din da zasuyi aiki a qarqashinsa.
Ammar ne ya bude baki cikin damuwa da takaici yace
"A hakan sunyi degree da Masters zasuce ko?
Numfashi Maheer ya sake saukewa Yana cewa
"Koma basu taba shiga aji ba is their problem mudai mu samu aikin kawai musamu mu dawo field din yanda zamu fara sake gina Zaadens"
Modibbo dayake gefe sosai tsaye sbd baa bari ya shigoba shi tinda bada shine zaa bawa aikinba.
Se bayan sallar laasar suka samu akace su shiga bayan me gidan ya dawo sallah kenan.
Miqewa sukai suna dan sake nutsuwa suka shiga cikin nutsuwa.
Dagowa yayi Yana daga zaune kan kujera ya kallesu Yana amsa sallama da gaisuwansu Yana tinanin kamar yasan fuskokin nasu.
Ganin irin kallan dayake musu ya sakasu sauke kawunansu a tare cikeda jin damuwa na rufesu sbd sunsan tabbas kila ya sansu din koda a jarida da labarai ne tinda sunyi lokacinda babu ranar da a labarai baa fadar irin tarin nasarorinsu da arzikinsu hakama kusan kowa daya sansu yasan labarin kaddarar data samesu,
Wasu sun tausaya musu wasu kuma sunyi Allah wadai dasu,wasu kuma sunyi Allah ya qara musu azaba da kunci dan haka a cikin mutane yanzu basusan da wace fuska kowa ke kallansuba.
Numfashi ya sauke yana nuna musu gurin zama a hankali tareda karban folders din hannuwansu Yana cewa
"Kun dade kuna jira ko? Baqin ne da yawa hakama ayyukan"
A natse Maheer yace
"Ba damuwa ai munsan yanayin ayyukan"
Bude takardun yayi Yana dubawa ahankali
Akan sunayensu ya tsayar da idanuwansa tsawon mintina kafin ya dago ya kallesu a natse tukuna ya sake maida idanuwansa akan takardun Yana dubawa.
Abinda ya ganine a ciki game da irin girman ilimi da tsagwaron karatu da experience da suke dashi ya sakasa jin ganganci ma ne a gurinsa daukansu aiki a gurinsa sbd ba bata lokaci yake ganin zasu dokesa su zarcesa sedai ya koma kallo.
Dan haka ajiyar zuciya ya sauke yana rufe takardun ya kallesu da dukkanin nutsuwarsa yace
"Well gaskia a yanzu ba kowace irin damar dauka aiki tako ina
Mun riga mun cike slots namu Wanda ko zaa samu wata damar ba yanxu kusa kusa ba so ina me baku hakuri sbd Kunyo tafiya me tsayi"
Numfashi me dumi suka sauke ahankali idanuwan Ammar na sauyawa ahankali zuwa ja sbd baqin ciki da damuwa da wani irin sanyin jiki
Maheer ma cikin karfin hali da juriya tareda hadiye damuwarsa ya bude baki yace
"Ba damuwa,thank you so much"
Miqewa sukai suka nufi kofa Ya bisu da kallan tausayi kafin ya bude baki yace
"Kunga ku dawo na fada muku wata damar idan kunaso"
Dakatawa sukai a tare tareda juyowa a natse suka sake zauna suna jiran bayaninsa.
Ajiyan zuciya ya sake saukewa Yana fuskewa kai tsaye yace
"Akwai securities na gate da masu aikin cikin gida da masu aiki da ake nema a wani kamfani Zaa kai gidan wani baturen Alh da baa qasar nan yake ba,
Masu aiki da securities da ake nema wainda sukeda ilimi me zurfin gaske akeso sbd yanayin familynsa da turancin suka fi ji,
So a taqaice dai masu ilimi irinku ake nema idan zaku iya
Slots din na nan amma sai anyi muku interview so if zaku iya yayi muku zan iya gabatar daku a kamfanin da ake neman"
Zuba masa idanuwa Maheer da Ammar sukai idanuwan na jajir sbd wani irin baqin ciki da qunci daya cike kirjinsu da zuciyarsu da maganganunsa wai securities masu gadi fa kenan kuma har sai an musu interview a gidan wani Wanda bayama kasar gadin gidansa zasuyi abanxa kafin ya dawo din.
Ganin yanda idanuwansu sukai jajir na Ammar hadda wasu zafafan hawayen qunci da dacin zuciya ne suka cikasu
Bude baki yayi sbd ya sake fahimtar dasu yace
"Karku damu aikin ba wani aikine me wahala ko yawa ba
Zakuji dadinsa na tabbatar sbd a bayanin gidan mansion ne sabo da aka kammala a watan nan hakama kwata kwata fa basa qasar,
Matarsa da zai aura ce baturiya shiyasa dole se masu zurfin ilimin irin naku,
Hakama a cikin mansion din akwai bangaren masu aiki da da zaku zauna acikin kwanciyar hankali da wadata tareda jin dadin gaske,
And idan kunada mata ko kanne mata kuma sunada ilimi irin naku duka sauku cike slots din sbd ku samu zaunawa dukanku a cikin mansion din bangarenku na masu aiki sbd samun nutsuwa
Daga karshe kuma albishirin da zanmuku albashin nada tsananin tsoka da girman gaske Wanda duk aikin da zaku samu na kamfani bazaku samu albashi me Kyansa ba"
Ammar kasa cewa komai yayi ya miqe hawayen idanuwansa na gangarowa yafice kirjinsa na masa wani irin nauyi,
Hannuwansa yasaka Yana share hawayensa da suka gangaro Yana jin zancen na sake yankar zuciyar ta yanda bama akansu zancen ya tsaya ba ace wai idan sunada kanne ko mata suzo suyi aikatau dasu,
Tayaya zai iya kallan Jannah a matsayin maid tana aikin aikatau a karkashin wata macen?
Tayaya zasu bari Ummah tayi aikatau a qarqashin wata bayan yanayin lafiyarta ma dasuke lallabawa dan su samu su farfado su nema mata lafiya da duk abinda zasu tara.
Maheer ma dago idanuwansa da sukai jajir yayi ya kalli mutuman ya bude baki ahankali yace
"Mun gode bama buqtaan hakan zamu ci gaba da neman aikin a wani gurin"
Miqewa yayi shima ya fice yana danne radadin da zuciyarsa ke masa.
Modibbo na ganinsu hankalinsa ya tashi jikinsa yayi sanyi sedai kafin ya juya ya bisu secretary din office din yazo yace ana kiransa.
Modibbo na shiga office din ya zube qasa yana gaidasa cikeda girmamawa.
Amsawa yayi kafin ya sake korowa modibbo zancen dallah dallah da irin tarin kudin da zasu ringa samu a aikin kafin ya ciro katinsa ya bawa modibbon yace
"Ga numbern wayata nan idan kunje gida sun sake shawara akan zasuyi saiku nemeni"
Karba modibbo yayi da sauri yana rudewa akan jin kudi da alkhairin da zaa iya samu a aikin idan sunyi.
Kudi ya ciro dubu goma ya bawa modibbon yace
"Gashi ku hau mota sai naji daga gareku,idan kuma kunja lokaci zasu iya rasa damar sbd aikine da duk me wayo ya samu zaiyi gaggawan karba"
Godiya modibbo ya hau yi Yana rawan jiki kafin ya fito yana jin idan badan masu zurfin ilimi da akace ana nemaba da babu abinda zai hanasa tattaro su Garba dasu isiya suzo su karba aikin amma ko su Ammar din wlh ba barinsu zaiyiba sai sun karbi aikin nan koda asiri ne.
Yana fita tini su Maheer sun fice daga kamfanin zuciyoyinsu cikeda daci da radadi me zafi.
Acaba suka tara su uku sukai overload suka wuce masaukinsu kowa zuciyarsa cikeda tinani me nauyi Musamman modibbo daya matsu daya koma ya fayyacewa su isiya wannan samu da rashin dasu Maheer ke kokarin janyo musu dan rashin tinaninsu,
To wlh tsaf zai gama zugasu da takurasu saiya tabbatarda sun karba aikin dukansu har Jannah tinda itama tanada ilimin da akeson gwara suje suyi aikin ai yafi zaman banza.
#MAMUH
#BEST LOVE
#STEEZ
#ROMANCE
#LIMBAS
#ZAADENS
ZAFAFA BIYAR
KALBIM 500
Mamuhgee
KIRJIN ME HANKALI 500
Miss Xoxo
ADUNIYATA 500
Huguma
AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul
09033181070
09032345899*_KALBIM_*
Book 2
Chapter 4 · 0% Book details