← Book details Jami'in Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 4

Sashe 3

Jami'in Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"
Maida kallonta tayi gareshi kanshi Ak'asa, ga Alama Dai yana kunyar Ammaaa

"Ya Abbas kaidana Jin Kunya ko wani d'ari d'ari everything will be normal bamuda matsala ko gun Daddy bazan Samu matsala ba Domin yana sona kuma Yasan bazanyi Abu Mara Kyau ba, so tashi na nuna maka inda zaka zauna,"

Tashi sukayi suka nufe waje wani parts dake kusa Dasu Yana Rufe ta kaishi d'akin 2 ciki da palour sai kitchen store dama Toilet,

D'akin ya had'u ba datty Komai Pink ne ciki shima,

"Fatan d'akin ya maka,"

"Sosai ma kuwa yayi Kyau musamman tsarinsa da kalarsa Komai Pink Amma na Mata ne ai,"

Dariya Tayi Kafin tace"itace best colors d'ina Pink shiyasa duk Abunda Yake Under control d'ina nakan Masa zab'i irin nawa,"

"Ai Kam dai Yayi Kyau Sosai, Nainaaa"

"Au kasan sunana Ashe,"?

"Habadai sau nawa Aka Kira sunanki gabana? Ai dole na rik'e,"

"Um hakane Bari na Barka kahuta ko, sai Anjima Amma idan kana buk'atar wani Abu kamin Magana Kuma ba shamaki ka iya zuwa part d'inmu Koda bana Nan Ammaaa tana Nan zata yimaka koma meye,"

"Ina godiya sosai da wannan karamcin Nainaaa Allah yasaka da Alkhairi Yabani damar yimiki Abunda Kika min koma fiye da Hakan My Nainaaahh," Yaja sunan Cikin Cool voice d'insa,

Sosai taji dad'in hakan murmushi Kawai tamasa Had'id'a juyawa tafice................................

_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_

WhatsApp number 07064904617
*JAMI'IN SIRRI*
*C~I~D👨‍💻*

_PAID BOOK #300 ONLY_

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK...(24) RUHIN JINN PAID BOOK.. (25) JAMI'IN SIRRI C~I~D PAID BOOK 300 ONLY.
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝```

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *JAMI'IN SIRRI C~I~D👨‍💻*
_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._

_SATURDAY 16/9/2023 SEPTEMBER_

*Free 🅿️ 16 to 20*

_SECON TO THE LAST FREE PAGE IN SHA ALLAH_

*IDAN KINA SO KANA SO KABIYA KI KARANTA CIKIN SALAMA MASU SIYE KU FITARMUN DA BOOK KUDA ALLAH BAMASU KARANTAWA BASU BIYABA SUNAGANIN SUNSAMI BANZA KUMA KUDA ALLAH, BAZAN YIWA KOWA ALLAH YA ISA BA AMMA KUNSAN BAKUMIN ADALCI BA HAKAN YASA NACE KUDA ALLAH,.. 300 NE KAWAI BA YAWA, ALLAH YASA MUDACE AMEEN*

...........Kwanaki sunfara tafiya inda Yanzu satin Abbas 3 Cikin gidan shak'uwa soyayya Mai tsanani tashiga tsakaninsu Musamman Nainaaa sosai take son Abbas ba kad'an ba, Kullum suna tare indai tadawo Aiki ko in bataje ba, Duka Ahlin gidan sunsan da Soyayyar da ke tsakaninsu,,

Yanzuma tana Zaune A garding d'in gidan tana Shan iska laptop ce gabanta tana Magana da Daddy,

"Allah daddy mutumin kirki ne na k'agu kadawo ku had'u Daddy harda Aiki nakeson kabashi, Daddy yaushe zaka dawo,"?

"Oh Daughter Lalle wannnan Yaron kina Sonshi ba kad'an ba, Amma kina ganin Bawata matsala kinsan fa d'an Adam sanin sirrin zuciyar mak'iyi sai Allah, sautari Mutum zai rab'ekane don biyan buk'atar sa dazaran Yasamu saiya gujeka,"

"Daddy shikam ba Haka yake ba, Kuma in Sha Allah had'uwar mu Alkhairi ce nidai da Zuciya d'aya nake tare dashi shima hakan ne in sha Allah,"

"Shikenan daughter nalura dai wannnan Abbas d'in yagama siyemin zuciyar Y'a, in Sha Allah cikin satin Nan zandawo Kinga saina zauna dashi daganan muyi Abunda yadace Ai duk Abunda kikeso shi Zanmiki daughter,"

"Yawwa Sweet Daddy Inasonka Sosai, bay bay," ta k'atse Kiran

Duk Abunda take Yana hangosu ta window d'in d'akinsa domin tanan garding d'in yake, murmushi Kawai yake zubawa Had'id'a cizar lip's d'insa,

Komawa yayi ya zauna Yajanyo wata jaka Naga ya fidda wata laptop Yasoma dannawa Yajima Yana Aikin sannan ya Rufe, Jin motsinta zata shigo yasa Yayi sauri b'oye laptop d'in da jakar duka Yadawo Cikin sauri ya kwanta Had'id'a rufe idanuwansa Kamar Mai bacci,

Da sallama tashigo Ganin Yana bacci yasa tayi murmushi Had'id'a juyawa tafice,

A parlourn ta tarar dasu Duka suna fira gwanin Sha'awa itama ta zauna Suka soma tanajin inama Ace su Daddy da Ummeen tane haka?

Saurin kawar da tinanin tayi domin zai iya sakata damuwa Kuma Babu Abunda ta rasaga Ammaaa, itadai batasan dad'in Uwa ba hakama Mahaifinta batasan shak'uwa ba Saidai suyi waya ko video call on WhatsApp tana wata bataga mahaifinta A Zahiri ba, batasan Aikin me Yake fita ba, Always Yana k'asar waje Abun Yana damunta Amma Batada yarda zatayi,

*SU WAYE SU NAINAAA?*

Alhaji Salman Cikakken d'an kasuwa ne Wanda duniya tasan da zamansa Yana had'akar kasuwa da mutane daban daban Cikin kasuwancin nasa ya had'u da Alhaji Sale Mai gold suka Soma kasuwanci tare, sosai suke Samun riba kuma Ahankali Aminci yake k'aruwa tsakaninsu, hakan Yasa sale Mai gold yabawa sale Mai gold yabawa Salman Auren k'anwarsa Hajara bayan tanuna tana sonshi shima Haka, Sosai Aka Sha biki saidai Abunda Basu sani ba Alhaji Salman Yanada mata A b'oye batare da Yafad'a musu ba Wadda ko iyayensa basusan da Aurenta ba, zaman lafiya suke cikin wasu Y'an Shekaru Tasami Ciki ta haife Y'arta Mai Suna Nainaaa zo kaga murna tattali kulawa soyayya wadda Daddy yake yiwa Nainaaa Domin sunan mahaifiyarsa data rasu Aka samata,

Duk wata k'addara tashi dawasu company wad'anda Yasami ta k'ark'ashin Alhaji Sale Mai gold yayan Hajara duk ya mallaka Komai da Sunan Nainaaa,

Koda d'ayar matarsa Mommy taji hanakalinta Yayi Mugun tashi ganin ta Shekara dashi Kuma ga d'anta Namiji Amma ba'a yimasa wannnan Kyautar ba sai waccan Mai kamada Aljanu, hakan Yasa taja k'awarta Suka garzaya Bak'in daji inda bokan Tsauni sukayi Mugun Asiri ga Alhaji Kuma ranar ta kwaso kaya suka dawo gidansu Nainaaa,

Suna Zaune palourn itada Alhaji suna fira Cikin Soyayya y'arsu naga Hannunsa Yana mata Wasa A Lokacin Bata Wuce wata 3 ba,

Kwatsam saiga Mommy tafad'o d'akin ko sallama Babu tafara masifa, "Lalle Alhaji wato Saboda ka Aure Y'ar masu Kud'i Shine zaka walak'anta mu to muma mundawo Nan da Zama ba inda zamu,"

Mik'ewa tsaye Ummee Tayi Cikin mamaki tace,"Baiwar Allah lafiya Zaki shigowa mutane cikin gida Haka kina d'aga Muna murya,"

"Ke dakata kada ki fad'amun maganar Banza Ni Nan dakike Gani Ni matarsa ce wannnan Kuma d'ansa sai d'an k'aramin cikinsa dake jikina yanzu haka, dama Bai fad'a Miki Yanada mata ba ya Aure ki,"?

Cikin tashin Hankali ta juya ta kalle Daddy da kansa ke k'asa ya kasa magana Saboda Kunya

Tace"kenan Abunda wannnan Matar ta fad'a Gaskiya ne,"

Kasa magana Yayi

Dariya Mommy ta shek'a tace"Taya ko zai fad'a Miki tinda bakece gabansa ba tinfarko saboda Tara dukiya ya Aureki yanzu Kuma muntara to saiki k'ara gaba, Kai Alhaji Salman ka saketa Tak'ara Gaba,"

"Kije na sakeki saki d'aya Hajara, Kuma ba Wanda zai rabani da Y'ata Wllh duk duniya," Yana Gama maganar Yawuce d'auke da Yarsa,

Kuka ya kwacewa Ummee tana danasanin Auren Daddy, Haka Mommy tasa d'anta Sagar yama Ummee walak'anci ya korata waje bako takalmi,

Tana kuka tabar Gidan, ba kalar wahalar da Bata Sha Saida tasamu wani gida Aka d'auketa Ai katau Sannan tasami Kud'in komawa gida labari tabawa yayanta tana kuka, Abun yayi matik'ar k'ona Ransa Shida d'ansa Na'if Kuma ya kullace ganin bayan Daddy,

Koda sukayo bincike ba inda Basu duba ba Amma ba ko Alamar Daddy ya kwashe komai nasa yabar gari, Bayan yabasu wata takarda Mai d'auke da shaidar mutuwar Nainaaa,

Hakan yak'ara d'aga hanakalin Ummee har Rashin Lafiya tayi Domin tana masifar son Y'arta, da kyar Asami ceto Rayuwarta Bayan wasu shekaru ta Aure wani mutum Saidai koyaya ne Zuciyarta nagun Salman Allah baisawa Auran Albarka ba suka Rabu,

A yanzu duk Iyayen Salman sunjima da rasuwa Y'ar Uwarsa Binta ce kawai tarage Ammanaaa tana Auren talaka yaronta d'aya Hassan Domin Hussain d'in sa ya rasu, mijinta bamai k'arfi bane hakan Yasa Alhaji Salman ya maidasu Sabon gidansa daya Gina A Abuja suka tare Dukansu Nan yabata Nainaaa Rik'o domin Mommy Tace Wllh bazata Rik'a taba,

Ammanaaa tayi fad'a Sosai ga d'an Uwanta na wannnan Abun dayayi Amma baice Komai ba Domin kuwa sihiri Yana yawo Kanshi,

Ammanaaa tarik'e Nainaaa tamkar itace ta haifeta kulawa Sosai take bata, duk iya k'ok'arin Mommy ganin taga bayan Nainaaa da Ammaaa Abun ya faskara Hakan Yasa ta d'aura musu muguwar tsana A gidan,

Tayi duk Abunda zatayi Wanda ko Labarin Hajara Daddy baison Yaji Kuma ya damfareta Kud'i Masu nauyi yakawo gida Mommy ta kwashe, tayi sama da Fad'i Dasu Amma ya kasa magana,

Abunda duk Basu sani ba tindaga Kan Rabuwarsa da Ummeeen Nainaaa zuwa Kud'insu daya damfara duk Aikin sihiri ne Mommy Tayi Kuma Sagar dayake ma kallon d'ansa yana kashe Masa duniya ba d'ansa bane d'an bokanta ne can tasamo cikin Amma ta Nana Masa Batareda ya sani ba, Hairat ce kawai Y'arsa Shiyasa take k'aunar Nainaaa...

*MUNDAWO LABARIN.....*

Tsaf suka shirya ita dashi gwanin burgewa suka fito,

"Wai nikam Ina Zamuje ne my Nainaaa,"?

"Oh my Abbas bafa saidaka Zanyi ba,"

"Hahaha Inama Zaki iya Saida gudan jinin Masoyin ki,"

Dariya tayi tana bud'e Masa motar "yau Kai zakayi driving d'inmu,"

"Laaaa My sister and brother Shine zaku fita badani ba? Aikuwa Allah ya kawoni Dan Dani Za'a," tana Gama maganar tashige bayan motar

Dariya sukayi duka suka shiga Suma Suna fira,

"Ina muka nufa ne wai,"

"Wannan Mall d'in kasan gobe Daddy zai dawo shine nakeson muyi siyayya,"

Cije lip's d'insa Yayi cike da Samun nasara Yace"Amma kuwa nayi farinciki da Zan had'u da Daddy zakuyi surprise Ashe,"

"Surprise kuma,"?
Chapter 3 · 0% Book details