← Book details Jami'in Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 4

Sashe 2

Jami'in Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Amma Ammaa baikamata laifin Daddy ya shafeni ba Dan ya rabu da ita Bai kamata Nima ta watsar Dani ba, kawai sainakejin Ni banida wata Uwa kece Kawai Ammaaa,"

"Nainaaa kinsan fa idan Aka rabu tsakanin miji da mata idan mijin Mai Kud'i ne tofa da wuya yabar yaransa gurin matar, Kuma Koda ya barsu idan zatayi Aure Dole fa sudawo gidan nasu Uban, to Balantana yarda Daddyn ki yake Sonki ai bazai iya Bari tayi wani Auren taje dake Agolanci ba bayan ke ganaki Gidan Uban,"

"Hummmmmmm Ammanaaa kenan nadai gano kinayin Ummeena da yawa shiyasa, Nidai bazan daina Fad'in Bata Sona ba kawai ta sallamani tinda ta rabu da Daddy," mik'ewa tayi tafito d'akin ta nufa iya tsaruwa d'akin ya tsaru komai pink

Toilet ta fad'a tayi Wanka tayi sallah taci Abincin sannan ta fito parts d'in ta nufa Koda ta Shiga can sainaga Wanda tafito Ashe bama Kyau bane Domin wannnan kam ba'a maganar had'uwa Anzuba dukiya Sosai,

Zaune ta tarar da Mommy ta d'aura k'afa d'aya Kan d'aya Tana Danna waya k'afafunta kuwa Y'an Aikinta suna Mata tausa

"Ina wuni Mommy"

A walak'ance ta dubeta Kamar bazata ansa ba sai Kuma Tace"Uwar gantali sai Yanzu kikaga damar zuwa gaida ni, kunacen keda wannnan Muna fukar Matar Kuna gulmarda kuka Saba ba, hunmm ai wllh nakusa maganin ku duka, Ni tashi ficemin A palourn Mai Bak'in hali da naci," Mtssswww

Itadai kanta k'asa duk da tanajin zafin zagin Amma batace Komai ba, kawai Dan takasa sabo da cin mutuncin Mommy ne amma ba Randa Bata zaginta musamman idan Daddy bai Nan sauk'in ta d'aya tanada Ammaaa da Tabbas zaman gidan saiya gagareta,

"Haba Mommy Dan Allah ki sassautawa Baiwar Allah Nan ,"

"Iyee Haira Ni kikewa fad'a? Wato gaki ke sallamammiya ke Mai Y'ar uwa ko? To wllh har ke Zan had'a dake nayi maganin ku banza shasha kawai,"

Mik'ewa Nainaaa Tayi tafice cikin sauri Haira tabi bayanta tanajin Mommy na zage zage Amma Bata dawo ba,

Rik'o hannunta tayi tace"Dan Allah sister na kiyi hak'uri bansan meke damun Mommy ba Amma dai ko Yaya ne kada wannan matsalar ta shafeni nidai wllh ke Y'ar Uwatace Kuma duk rintsi Muna tare, Kawai ki k'ara hak'uri,"

Murmushin yak'e kawai tamata tareda cire hannunta daga nata tawuce,

Saida ta b'acewa ganinta sannan tadawo palourn lokacin Sagar yayanta Yadawo Suka had'e sukamata Tass itadai Bata tankasu ba Kuma tasa A Ranta ba Wanda zai rabata da Nainaaa wllh..

Tana komawa d'akinta tashiga tafad'a Kan gado tana tinanin rayuwa tana kuka har dai bacci B'arawo ya sace ta......

To nace Assubah tagari................................

_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_

WhatsApp number 07064904617

*JAMI'IN SIRRI*
*C~I~D👨‍💻*

_PAID BOOK #300 ONLY_

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK...(24) RUHIN JINN PAID BOOK.. (25) JAMI'IN SIRRI C~I~D PAID BOOK 300 ONLY.
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝```

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *JAMI'IN SIRRI C~I~D👨‍💻*
_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._

_Friday 15/9/2023 September_

*Free 🅿️ 11 to 15*

.....Jimawar da tayi batasami baccin ba Hakan yasata makara,

"Daughter Wai bazaki fita Aiki bane Yau,"

Mik'ewa Tayi Tace"wllh Ammaaa yau baccin ne Yakasa barin Idanuwana,"

"Daughter Dole bacci yasaki gaba, Baki kwantawa da wuri ga Yawan tinani kada kijawa kanki wani ciwon daban, Yanzu tashi kiyi Wanka kizo kiyi break fasts,"

Mik'ewa Tayi tashiga toilet Already tayi sallah shiryawa Tayi tafito parlourn harta zauna zata Soma cin Abincin wayarta tafara k'ara doctor San tagani Rubuce

Tana d'agawa Tace"I'm so sorry doctor but I'm coming now" tana Gama Fad'in hakan ta k'atse tareda mik'ewa

"Ah tafiya zakiyi bakici komai ba,"?

"Ammaaa kin manta Inada patient Kuma better tinkan Akirani Yakamata na kasance wurin, Amma Asamin A baskets sainje Masa dashi ma,"

Delu Mai Aikinsu tazuba Mata takai mata mota Sannan tashiga tawuce,

Parking motar tayi sannan ta d'auke basket d'in tashiga ciki, direct office d'inta tashiga saida tagama settling komai nata sannan tafito office d'in doctor San taje but Yana Rufe hakan yasa tanufe D'akin da Aka kwantar da mutumin

Tura k'ofar Tayi da sallama tashiga

Dukansu Ido suka zuba mata bama kamar guy d'in domin ta burgeshi Sosai Komai nata slow cikin natsuwa da Hankali

Doctor San Yace"Kin manta Damu ba Kuma inatason naje gida Amma ba dama,"

"Dan Allah kayi hak'uri wllh na makara ne Amma Yanzu gani Yaya Ake Ciki kayi Magana da doctor najib d'in,"?

"Eh yazo tin jiyan ma Kuma yaduba komai normal Saidai eh Yasami loosing memory d'insa Saidai idan yaga wani Abu daya shafe Rayuwarsa tabaya to zai iya tinawa ya dawo daidai,"

"To Amma doctor San Maganar tasa kuma fa,"

Hahahaha"kinzata Wai Bai magana Yanzu ma Saida mukayi magana dashi yace ruwa Saidai na lura miskiline na K'arshe shiyasa duk Magana inbatazama dole ba tofa bazai yi taba,"

Maida kallonta tayi kansa saitaga ya d'auke Kansa yawani had'e Rai

Matsawa Kusa Dashi Tayi ta zauna Had'id'a zuba masa Abincin da tazo dashi pepper soup ne da shinkafa mik'amasa Tayi Tace,"Kaci Abinci kadaina B'ata Rai bafa da gangan na bigeka ba, Ni banma San na bigeka ba Kawai saiganin ka nayi kwance idan za'ayi tuhuma Kai Zan tuhuma d'an Samari," tak'arasa maganar tana wani farr da idanuwanta

Murmushi ya sub'uce Masa Dan shi harga Allah dariya tabashi,

"Yawwa idan kanayin magana da murmushi to Zan fasa tuhumarka, Yanzu kaci Abinci ka Huta Kafin nagama da Sauran patient d'ina sainazo Muyi Magana dakai," Bata jira Ansarshi ba tawuce dama doctor yajima da fita,

Saida tafita sannan ya d'auke Abincin yaci,

Tajima Kafin tagama tadawo Zaune ta tarar Dashi ya jingina da gadon,

Sallama Tayi Ai kuwa ya Amsa Ahankali Saida taji wani iri dajin saukar Muryarsa,

Zama tayi daga cikin kujerun d'akin Tace"Sannu bawan Allah yajikin naka,"

"Da sauk'i" Yafad'a Atak'aice idanuwansa na rufe

"Masha Allah A yanzu dai kasami sauk'i kaga Yakamata Asallameka so Ina zankaika Ma'ana Ina Ahlinka suke,"

Shuru harta cire ran Zaiyi magana Sannan ya Ware manyan idanuwansa kanta cikin sanyi da Alamar tausayi Yace"bansani ba nima bansan kowa ba saike, Ni ba d'an Nan garin bane Amma namanta Ina nake bansan Komai game Dani ba Yanzu," Wasu Hawaye Suka Soma silalo Masa

Cikin Jin tausayinsa Ta matso inda yake tace"kada kadamu Akai nice silar faruwar Komai Dan Allah ka yafemin zanje dakai gidanmu ka zauna Kafin Allah yasa Katina Komai naka, Amma ya sunanka,"?

"Sunana Abbas Shine Kawai Zan iya tinawa saboda Naga wannan tare dani, karancin passport d'auke da sunan Abbas Akai, Amma hakan zaiyu kuwa? Iyayenki zasu Bari na zauna daku bayan basusan Ni kowaye ba, ko Ni bansan waye Ni ba balantana nayi musu bayani idan Suka buk'ace hakan,"

"Kada kadamu Kan wannnan idan nayi musu bayani zasu fahimta Kuma ma Daddy na bayanan A Yanzu Amma nasan very soon zai dawo, Yanzu ka d'auki duk Abunda kake buk'ata Kazo muje kawai," tana gama maganar tafice

Binta Yayi da kallo Yana Aiyana Abubuwa dayawa Aransa Had'id'a sakin murmushi,

_NI DAI MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 KALLON IKON ALLAH KAWAI NAKE NAKASA FAHIMTAR KOMAI GAME DA WANNNAN MUTUMIN,"

Saida tagama Komai sannan Sukayi Magana da doctor San ya rakosu har mota suka wuce shikuma ya koma,

Kallon hanya Kawai yake har Suka Isa bawanda Yayi magana

Bayan Tayi parking ta fito tareda Kiran Mai gadi da Sauran masu kula da Gidan Tace,"kunga wannnan bak'ona ne, so Yanada ikon Shiga ko fita duk Sanda yatashi idan Kuma wani yanemi Wani Abu kanshi kawai kuce yasameni, banason sa'ido ko Shiga hurumin da baishafe mutum ba, Ina fatan kun fahimce Ni,"

"Eh madam munfita Kuma in Sha Allah zamu kiyaye,"

"Yawwa Masha sunanshi Abbas, so Shine kawai zaku iya komawa Kan Aikinku nagode,"

"Muje ciki ko Abbas"

Binta Yayi Suka Shiga parlorn

Kallo Yafara k'arewa palourn

"Zauna Bari Nakira Ammanaaa ku gaisa"

Gyad'a kansa Kawai Yayi tareda zama, itakuma tahaye sama

D'aga kansa Yayi Yana kalle kalle can idanuwansa suka fad'a kan wani photo k'ato Dake manne A bango, Itace cikin shigarki Likitoci da Sauran mutane gefe sai sai wani mutum data rik'e shima Yana rik'e da ita suna dariya ga A Ward's tsakansu,

"Ba shakka wannnan Shine," Ya fad'a cikin zuciyarsa tareda cije lip's d'insa na sama,

Jin Alamar Ana saukowa k'asa yasa da sauri yakoma ya zauna,

Fitowa sukayi tareda wata mata,

Sauka yayi k'asa Yana gaida Matar

Cikin fara'a ta Ansa Tace"A'a tashi ka zauna Abbas ai tafad'a mun komai kada kadamu bamuda matsala kasake ranka kaji ka d'auka kamar gidanku, Kuma itama ka Zama yayanta idan kaga tayi kuskure kamata fad'a ta Gyara, Ai Nainaaa mutuniyar kirkice tanada tausayi fatanmu Allah yabaka lafiya Kawai,"

"Ameen Ameen Ammaaa Ngd in Sha Allah zanzamo Nagari gareku," kansa A k'asa yake Maganar

K'uramasa Ido tayi tana murmushi itadai Yana burgeta Wllh,

"To kin fad'ama Daddyn ki Saboda gudun matsala"

"Ammanaaa kinsan samun wayar Daddy it's not easy Always he is busy but I will trying to charts on WhatsApp,"

"Hakane Amma kiyi gaggawar fad'a Masa kinsan Yanayin gidan naku dai," Tak'arasa Maganar tana mik'ewa

"Ammanaaa Ya Hassan ya kirani yace gobe zasu dawo fa,"

"Eh Nima sun fad'amun Allah ya dawo Mana dasu lafiya kawai,"

"Ameen Ameen, Zan Nuna Masa inda zai zauna"

"Eh Hakan ya kamata kam,"
Chapter 2 · 0% Book details