← Book details Ingarman Namiji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 6

Sashe 5

Ingarman Namiji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yazeed na hangensu sunfito yakafesu da,Ido gabanshi na tsananta fad'uwa anty lele cetayi saurin k'arasawa wurin wani Dr tana tambayar sa sumayya kutafarka.. murmushi yayi Mata tareda cewa"munsamu nasarar samo numfashinta yanzu tana bacci ne sabida allurar bacci damuka Mata.. alhmdllh tace kamun tasakeyin wata magana Dr yace Mata "Wannan ne mujinta? Kallan yazeed anty lele tayi kana tace "ah,ah yayanta ne.."ok kusameni a office yace tareda barin wurin.

Yajima awurin kamun yamik'e yashiga office d'in anty lele nabiyedashi..da sallamah yashiga office din akan labb'ansa.."wa, alaikassalam Dr d'in ya,amsa tareda bashi hannu sukagaisa kana yanunai wurin zama anty lele ma zamanta tayi tana kallansu.

Y"anrubuce,rubecen dayakeyi ya,Ida kana yazare glass din idoshi ya,ajiye tareda duban yazeed yace "yallabai abisa cinciken damukayi mungano cewa k'anwarka akwai abunda tasha metada Sha,awa sosai Wanda hakanne yatada Mata matsanan ciyar Sha,awar tareda ciyon Mara har yagalabaitadda ita Wanda hakanne yayi sanadiyyar sumanta Amma yanzu insha Allah bakomai data farka zata samu sauk'i sedan abunda ba,arasaba..tinda Dr yafara magana yake sauke ajiyar zuciya dajin ba,abunda yake tinanibane..kallanshi kawai yazeed keyi cikin mmki abunda yakeji ta,aikata tomihakan kenufi? Mitasha Kuma? Duk yarasa mimazeyi tinani akai..nisawa yayi tareda yiwa Dr d'in godiya suka fita zuwa room dinda aka,ajiyeta kallan anty lele yayi kana yace "kishiga kizauna maryam nizanje nabiyasune kana nad'auko Miki hajiya mama ke seki koma gida..ok yaya sekadawo Allah yatsare hanya.. ameen y rabbil alameen ya amsa kana yatafi itako tanufi d'akin..

Jejin barno

Zaune take yau acikin kogonnan nata tana kallan wasu picture dake hannuta tana kuka kamar ranta zefita bayan tayi kukanne me isarta kana tamayarda pic din ma,ajinda tayimusu akogon kana tafito tana sawokai taji motsin tafiya Kuma kamar tawaga ne komaminene ba,abu d'aya bane yalla mutun ko dabba komawa tayi ciki tayi zamanta domin batasan cutarda kowa..tana zama taji anafad'ar kuduba ko,Ina karkubari sutsira..Jin abunda akefad'ane yasa takara b'oyewa cikin tashin hankali da fargaba...andad'e tanajin motinsu kana tadenajin komai amalar sunbar wurin kenan asa,annan tasauke nannauyan ajiyar zuciya taname Kara godewa mahaliccinta daneman kariya daga gareshi.

Unguwar Gama B acikin garin kano

K'ira,ar karatun Alqur,ani ketashi a cikin babban perlon gidan cikin zazzakar murya medad'in seraro *k'arasawa nayi cikin perlon Dan daukomuku rahoto masu karatu😜*

Wata budurwace kezaune da zumbulelen hijabinta gawasu Yara sunkai 6 kewayeda ita daga gefe kuwa wasu matane kezaune suwajan 4 kowacce da littafe ahannuta.

Jiyowa nayi inakallan Wannan buduwar dakanta kek'asa tana karatunta cikin gwaninta tareda bawa kowanne harafi hakkinsa saura,rar karatun Nima nazauna domin agaskiya Yana ratsa zuciya seda takai ayar dazata ajiye kana tarufe Al,qur,aninta tareda d'ago kanta.

Woww Masha Allah a gaskiya yarinyar tahad'u itama dumin kumai hassadar mutun be,Isa yace gamunintaba bafara bace Amma chocolate ce tanada hanci sosai Masha Allah hakama bakinta Dan madedeci dashi kuma jajir yake kamar tashafa janbaki saman goshinta dagefen kunneta kuwa wani gargasa ne kwance awurin gwanin Sha,awa gatada manyan idanuwa sewani lumshewa sukeyi.."to bara mutsaya anan ko hanifa? idan kuka iya gobe se mud'ura ko? Tafad'a tana kallan yaran.."eh anty..ok tokutashi kuje..to sukace tareda mikewa suka fice. kallan matannan tayi kana tace "anty aiku base nak'ara makubako? Kubari seda dare allah latti zanyi tafad'a cikin shagwaba.. murmushi d'ayar tayi taceto "shikenan SAURAT adawo lpy badamuwa.."yeee yawwa my lovely anty bara najeko tafad'a tana kallan sauran..eyee mudaba lovely ba ace mu mutu d'ayar tafad'a tana harararta. Gwalo tamata kana tareda wucewa tana dariya tashige bedroom dinta.

A hospital kuwa yazeed ne yadawo tareda hajiya mama shigowarsu kenan sukaji wani Amon sauti me anshi sosai natashi dagacikin room d'inda sumayya take cikin sauri suk'arasa tareda bud'e d'akin suna shiga Aiko akayiwani....

Happy Friday all my lovely sister's 💃🏽💃🏼 💃🏽💃🏼💃🏽💃🏼💃🏽💃🏼💃🏽💃🏼💃🏽

Free page yakusa k'arewa befi page 3 ba yakare idan kinshirya karatun *INGARMAN NAMIJI* to kihanzarta sayan naki tahanyar datadace #500 ne kachal👌idan kintashi siya Zaki iya yimun magana tawannan nomber 07037092176 inkinsan basiya zakiyiba karki batawa kanki lokacin nemana kokice namuki ragi ko akasin hakan domin bazanyiba karkiyi kice namiki wulakanci bana wulakanta kowa Amma banasan reni maganin Bari Kar,afara..

*KARKIBARI ABAKI LABARI* akwai chakwa kiya agaba 😜😜💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽

Autar ahairi ✍️✍️

*ALHERI WRITERS ASSO*

A.W.A

https://www.facebook.com/100186388252056/posts/

_______________

🐎 *INGARMAN NAMIJI* 🐎

Page 15 & 16

__Akayi wani mugun ihu da gurnani me firgitarwa cikin tashin hankali suka Ida kutsakai ciki Dan ganin mekefaruwa.. sumayya ce atsaye tsakiyar d'akin tad'aga gadon d'akin sama da hannu d'aya tana gurnani idanuwanta duka sunjuye tanashirin dokawa anty lele shi aka..cinkin matsanancin sauri yazeed yayi cikinta tareda rik'e hannayenta duka suka D'ora zagayen d'akin dagadon ahannusu..cikin firgici hajiya mama kefad'ar nashi ukku 🙆 ni hajara mizangani haka yazeed saketa karta illataka saketa nace..ah,ah mama ba,abunda zefaru kufice daganan inasan sauke bed dinne.."ah,ah fa yazeed.."no mama kufitanace yafad'a dad'an d'aga murya sabida ganin tanasan jefama wani acikinsu cikin hanzari suka fice hajiya mama naciro wayarta tadannawa abba kira itako anty lele duk tarud'e tamarasa mizatayi itama wayar taciro takira anty amarya tagaya Mata abunda kefaruwa..atake kuwa cikin tashin hankali anty amarya taje sashen big mom tagaya Mata Dan ita bazatajeba sabida kawaici..itama big mom hankalinta yatashi sosai batako tsaya Kiran abbu ba tafito tana fitowa taga Salman da Ahmad gayamusu tayi tareda cewa sukaita hospital din hakako akayi suka nufi asibitin cikin gaggawa.

Bayan fitarsu hajiya mama kuwa danbene yakaure tsakanin yazeed da sumayya Dak'yar yasamu Kai bakinshi kunneta yafara reramata karatun Al,qur,ani cikin suratul baqarah cikin dakiya da jarumta..gurnanin datakeyine yak'aru tareda karak'aimi wurin San lahantashi..shiko yarik'e hannayenta da,iya k'arfinshi..cikin Jin zafin karatun dayakeyi akejijjigasu taredasan kwacewa Amma Ina abun yacitira hakan yasa sukayi jifada gadon suka jiyo gareshi..shikuwa yazeed jiyowarda tayi yabashi damar mird'e hannuwan tareda jefata akan gadon.

Aiko yazumbur tayi zata Mike yayi saurin danneta tareda sake Kai bakinshi kunneta yacigaba da karatun dayajeye..

Acan waje kuwa tuni su big mom suka k'araso anan suka Sami Abba da abbe Amma dady bezoba suna zuwa hajiya mama tacewa Ahmad "Kai shiga ka temakawa Dan uwanka kada su illatashi..cikin sauri yanufin d'akin yad'ora hannusa kenan yaji ance dakata Ahmad.

Dakatawa yayi sabidan Jin muryar data dakatardashi tareda duban memaganar ummy yagani tafe mahaifiyar sadeeq itada siyamah...k'arasowa tayi tana fadar "barsu dashi karkashiga..kamarya karyashiga zainab? Kinajifa abunda kefaruwa inta jimasa ciwofa tinda ba karfinta bane.."to hajiya mama inya temakeshi yanzu gabafa Waze temakeshi ai gara yasaba tin yanzu..shiru hajiya mama tayi Bata sake maganaba yayinda Ahmad Kebin anty tasu dakallan mmki.

Ad'akin kuwa

Mutanen na sumayya ganin yazeed naneman k'onasu yasa suka fara magana cikin wani sauti me firgitarwa maraddad'in sauraro "kabarmu karka konamu kasani idan kak'onamu bazamu taba barinkaba daga Kai har ahlinka sumayya tawace ni kad'ai duk lokacin daga sake Bari taga wani abun asashen jikinka harya burgeta to wlh Niko senaga bayanka nine kawai Wanda zatakalla yabirgeta nine kawai nata itad'in tawace nikadaiiiiii.. yak'arasa zancen cikin hargagi

Shikuwa yazeed ko,ajikinshi katan kawai yakeyi bebi takan zantukan dasukeyiba ganin k'onasu zeyi bilhak'k'i yasu fita bashiri sunafar karyasake Bari yarab'e sumayya tareda jadda da Masa zasu dawo..gabaki d'aya sumayya zubewa tayi ajikinshi dama akwance suke agilme tamatseshi ajikin bango yanzuko duka jikinta yasake senumfashi take saukewa ahankali alamar bacci takeyi..shiko kallanta kawai yakeyi ana tinanin ai doline tasamu gayyar fasinjoji kodan Wannan Rashin Jin nata sun dad'e ahakan sumayya mak'alle ajikinshi shinfed'eta yayi gefe kana yatashi yagyara jikinshi kana yafita..atare duka suka k'araso suna tambarshi Yaya jikin nata musamman hajiya mama datake cewa "yayadai son hope dai ba,abunda sukama ko? Tafad'a tanashafa gefen fuskarshi Allah yasani tana mugun San yazeed dudda ba,ita ta haifeshiba.. murmushi yayimata kana yakwantarda kasan akan kafad'arta bayan tazauna bakin gadon da sumayya kekwamce Yana fadar"am okay my mama ba,abunda yasameni tareda sumbatar hannuta..itadai big mom murmushi kawai tayi domin tana ganin zallar sonda hajiya mama kewa yazeed ak'wayar idanta Wanda take tinanin ko itadata haifeshi iya son dazata Masa kenan.

"Naji kamar suna magana minene suke fad'a son? Cewar abba.."no bakomai Abba shirmensune kawai.."to allah yabata lpy yace. suka amsada ameen y Allah..kuzo muje gida domin Dr yace baze sallameta yauba se gobe ke hajara kizauna da,ita tareda yazeed kaiko Ahmad ku,ajiye Maryam gidanta Allah yabamu alkhairi..."Abbah gobe jirginmu zetashi fa karfe 9:00am..sadeeq yafad'a yanakallan abba..to ai bawani abun seyakoma gida da,assuba sabida Wannan matsalar bazeyu hajara tazauna da,ita ita kad'aiba..seku shirya Masa kayansa idan kunkoma kamun yazo..too sukace dukansu tareda yin abunda yace.

Gidansu sulaiman

Dareyayi sudai Dan yanzu karfe 2:00am Marwan ne tsaye yana sallah bayan ya idar yadad'e zaune Yana addu,a tareda kokawa Allah damuwarsu yad'au tsawon lokaci yanayi kamun ya kwanta.

Dakin shatu kuwa kwance suke itada baba lado cikin bacci baba lado yarik'a jiyo kukanta tashi yayi Yana dubata zaune yaganta akan sallaya tad'aga hannayenta duka biyu tana addu,a tana kuka..k'arasowa yayi kusanta tareda tallabota jikinshi Yana shafa bayanta alamar rarrashi dauriya irinta baba lado yau shima seda yayi k'walla Amma yayi sauri sharewa kada matarsa taga rauninshi..ahakan yalallab'ata sukaje suka kwanta tareda yimata nasiha meratsa zuciya akan d'aukar kaddara me kyau ko akasinta tareda karfafa Mata gyiwwa akan muradinsu.

Washe gari

Lpy qalau suka kwanada sumayya ba,abunda yafaru Dan bacci matakeyi har yanzu bata farkaba.. yazeed kuwa tin asuba Ahmad yazo yad'aukeshi suka tafi gida tareda yiwa hajiya mama bankwana..addu,a tayi musu sosai dafatan nasara akan abunda suka sakama gaba..sunji dad'in addu,ar tata sosai kana sukayi Mata sallamah suka tafi..suna fita masallaci suka nufa bayan sunyi sallah suka shiga gidan kowanne yashiga shiryawa Dan sufita da wuri gaya sulaiman yace subiya sad'aukeshi Dan direban gidansu bayanan Marwan Kuma zeje school tin 7 balle yayiwa baba lado magana yakaishi..zaune yake bayan yagama shirinshi tsab Kaya kawai zesaka seya tuna Wannan zuwan dasukayi beduba abunda yafaruba bayan sunyi waccan tafiyar atake yajawo computer shi mehadeda cc vt ze.....

Tofa 😂😂 yazeed nidai nayinan🏃🏃

Free page yakusa k'arewa befi page 3 ba yakare idan kinshirya karatun *INGARMAN NAMIJI* to kiyihanzarta sayan naki tahanyar datadace #500 ne kachal 👌 idan kintashi siya Zaki iya yimun magana tawannan nomber 07037092176 inkinsan basiya zakiyiba karki batawa kanki lokacin nemana kokice namuki ragi ko akasin hakan domin bazanyiba karkiyi kice namiki wulakanci bana wulakanta kowa Amma banasan reni maganin Bari Kar afara..

*KARKIBARI ABAKI LABARI* akwai chakwa kiya agaba 😜😜💃🏽💃🏼 💃🏽💃🏼💃🏽💃🏼

Autar alheri✍️✍️

*ALHERI WRITERS ASSO*

A.W.A

https://www.facebook.com/100186388252056/posts/

________________

🐎
*INGARMAN NAMIJI*🐎

Page 17 & 18
Chapter 5 · 0% Book details