Chapter 23-24
Imara Part 1 Complete Hausa Novel · about 176 min read
Mikiya writers asso...
A ƙofar gidansu ya yi parking, ya kashe motar ya juyo yana kallonta fuskarsa ɗauke da murmushi. Haɗe gifts ɗinta tayi tana ƙoƙarin buɗe motar ya ce"a'a, ko sallama babu zaki tafi?" hannunta akan handle ɗin ƙofar ta ce"Nagode Sosai Allah ya saka da Alkhairi" ɗan murmushi ya yi ya ce"shikenan, tunda naga gidan zan zo" da sauri ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kanta. Fahima dake kallonsu tun ɗazu ta ce"tom friend, bye, Allah ya ƙaddara saduwarmu" murmushi Imara tayi tana kallonta ta ce"Nagode sosai Fahima sai anjima" murmushi suka yi a tare ta buɗe motar ta sauka. Sauka shima yayi ya ciro mata trolley ɗinta yana murmushi ya ce"sai na zo" ɗan murmushi tayi baya bata ce komai ba ta juya ta shige gida.
Da É—an saurinta ta shiga gidan tana murmushi ta ce"Granny! Granny! Granny!, ki fito na dawo, I'm back" shiru Imara taji hakan yasa ta É—an haÉ—e rai ta ce"grannyyy! kina ina?" Ajiye kayan hannunta tayi akan tabarma sannan ta shige É—akin da sauri
"Granny ina ta kiranki kina bacci, ko zuwa ki ɗaukeni ba kiyi ba" tafada tana faɗawa kan katifar, murmushi tayi ta shiga janye bargon data rufa tana cewa "a wannan zafin kike rufa granny, gaskiya..." Kasa ƙarasa maganar tayi saboda ganin yanda Granny ke rawar sanyi, a firgice ta ce"subhanallahi, bakida lafiya ne Granny, zazzaɓi kike ne?" hannunta Granny ta kama jikinta na rawa ta ce"Fatima" kallonta Imara tayi tana hawaye ta ce"na'am Granny, sannu, bari na kira likita ya duba ki, ko muje asibiti ne?" ɗan murmushi tayi ta ce"ai ciwona bana asibiti bane Imara, kedai ki dinga yimin addu'a kinji, ki daina wannan kukan" tafada tana share mata hawaye, riƙe hannunta Imara tayi tana girgiza kai ta ce"a'a Granny, wlh bansani ba ma dana nemi excuse a school nazo, ki tashi muje asibiti dan Allah, ni banason naga mutum bashida lafiya, barin ma kuma ke, ki tashi Granny" ta miƙe daga kan katifar ta buɗe kayansu ta ɗauko mata hijabi, kallonta kawai granny take tana murmushi mai haɗe da hawaye, dawowa Imara tayi ta saka mata ta ɗagota ta ce"Granny tashi mu tafi, daure kinji" girgiza kanta tayi idanunta na neman rufewa ta ce"a'a Imara, daina taɓa ni, ciwon dake jikina baya son a taɓa shi, akwai wasu maganganu da nakeson faɗa miki.
IMARA ki kula da rayuwa ki yarda da duk ƙaddarar data zo miki ba lallai yanzu ki fahimci abinda yake akwai ba amma tabbas watarana zaki gane abinda nake yawan gaya miki idan kinada rabo zaki iya haɗuwa da iyayenki idan kuma ubangiji bai ƙadarta ba to shikenan ke dasu har abada, hannunta ta sanya cikin samirar dake gefenta ta xaro wata kyakkyawar sarƙa sai kyalli take cikin kakkarwar hannu ta danƙa mata cikin nata siririn hannun tana kallonta da idanunta wanda suka fara rufewa ta ce"wannan ita kaɗai ce ragowar abinda yake mallakinki ki kula da ita karki bari tabar wuyanki IMARA domin ita ɗin ƙaddararki ce ki kul..." Tsit ɗan ƙaramin ɗakin ya ɗauki shiru na wasu sakwanni kafin Imara ta mayar da idanunta kan mahaifiyar tata ta kalleta da son sanin abinda ya sanya tayi shiru saidai yanda taga idanunta sun ƙafe ya sanya ta saki wani razanannen ihu, sakinta Imara tayi ta shiga girgiza kai bakinta na rawa ta ce"granny banason irin wannan wasan, ki bari, ni ki daina yimin, ki tashi kawai wlh" jin tayi shiru bata ce komai ba yasa ta tashi a firgice tayi waje. Makotansu gidan Baba Hansatu ta shiga, zaune ta sameta tana yanka kuɓewa ta ƙarasa cikin tashin hankali ta ce"Baba zo muje ki ganta, granny ce, granny Baba" tashi Baba Hansatu tayi ta ce"mene ya faru?" Waje Imara tayi tana ihu, mayafi ta zara akan igiya tayi waje ƙafarta babu ko takalmi.
Zanin dake gefenta Baba Hansatu ta sanya ta rufe fuskarta, wata zabura Imara tayi ta ƙarasa wajen ta yaye zanin ta rungume granny jikinta sai wata irin kyarma yake, hannunta Baba Hansatu ta kama tana kuka ta ce"kiyi haƙuri Imara, Allah ya yiwa Asiya rasuwa, daman tunda kika tafi makaranta ciwo ya zo ya ci ƙarfinta, gashi kuma yanzu ya yi ajalinta kiyi mata addu'a kawai" girgiza kai Imara ta shiga yi tana sauke ajiyar zuciya dan kuka ma ya gagara ta yisa, tashi Baba Hansatu tayi ta fita dan faɗawa sauran maƙota su shigo ayi mata suttura a kaita gidanta na gaskiya.
*Days later*
Zaune take kan tabarma a tsakar gidan, ta cure jikinta waje guda, tunanine fal zuciyarta, tun ranar da aka kai granny ƙabari bata sake samun nutsuwa ba, shikenan ita yanzu batada kowa, kowa ya tafi ya barta, babu Daddynta babu Umma, babu granny babu Dodo, kowa ya gudu ya barta, ita kaɗai, kuka ne ya ci ƙarfinta ta kifa kanta tana yi babu ƙaƙƙautawa. Sallama aka yi ta ɗago kanta ba tareda ta amsa ba, kwanan abinci ta ajiye mata ta ce"gashi nan in ji baba ta ce a kawo miki" kallon kwanon abincin tayi sai kuma ta kalli yarinyar ta sake sunkuyar da kanta, girgiza kai Asabe tayi ta juya ta fice daga gidan. Haka Imara ta cigaba da rayuwa a cikin gidan ba tareda kowa ba, babu wani mai ɗauke mata kewa ko kuma ya yi hira da ita, gaba ɗaya ta rame saboda damuwa da tayi mata yawa, a haka har akayi arba'in ɗin mutuwar Granny.
Tashi tayi babu ruwa a gidan dan famfon nasu ya daina yi, hakan yasa ta ɗauki bokiti dan ta samo wanda zata yi amfani dashi, tafiya kawai take ba tareda tana kallon gabanta ba, tunani ya yi mata yawa, bata banbance a gida take ko kuma a hanya. Duk irin horn ɗin da suke mata bata ji ba, wani wawan burki yaja dan sauran kaɗan ya kaɗeta, sai a sannan ta dawo cikin hankalinta ta kalli motar dake gabanta. Kallonsa ɗaya na cikin motar ya yi cikin harshen larabci ya ce"lafiya dai?" kashe motar ya yi bai ce masa komai ba ya sauka daga motar, ƙarasawa wajenta ya yi ta ɗan kalleshi a rikice ta ce" I'm sorry dan Allah ban ganku ba" shiru taji ya yi yasa ta sunkuyar da kanta, fitowa ɗayan ya yi yana kallonsa ya ce "wai Maheer mene haka ka manta abubuwan dake gabanmu ne?" ko ta kansa Maheer bai bi ba, sai ma sake kallonta da yake yana murmushi, cikin sanyin murya ya ce"sannunki" kallonsa tayi ta ce"yawwa, kuyi haƙuri na ɓata muku lokaci" ta faɗa tana kallonsa, murmushi ya yi ya ce" ba komai yarinya, ina zaki je haka?" kallon bokitin hannunta tayi ta ce"ruwa zan ɗan ɗebo" shiru ya yi sai kuma ya ce"ɗebo ruwa kuma da kanki?" jinjina masa kai tayi dan maganar ta fara damunta. Murmushi ya yi ya ce"anyway, I'm Maheer bin Fahad al-kuwari, mun zo aiki ne daga Qatar kuma naji ina sonki idan babu damuwa zan aureki" da sauri Imara ta kalleshi sai kuma ta ɗauke kanta tana wasada fingers ɗinta, jin bata ce komai ba yasa ya ce"kefa ya sunanki?, ina ne gidanku?, bakiyi kamada yar nan garin ba kodai kin zo hutu ne?" ɗan murmushi tayi ta ce"a'a anan nake, gidanmu yana can baya babu nisa" numfasawa ya yi ya ce"muje naga gidan to, ki bar ɗiban ruwan za'a kawo muku" toh kawai ta ce dashi sannan tayi gaba yana bin ta a baya. Kallonsa Tareeq ya yi sai kuma ya girgiza kai ya biyo su. A ƙofar gidan ta tsaya ta ce"nan ne gidanmu, amma babu kowa a ciki sai ni kaɗai" dan waro idanu ya yi ya ce"meyasa?, ko sunyi tafiya ne?" gyaɗa masa kai tayi saboda kukan daya tawo mata ta shige gidan ba tareda ta sake cewa komai ba. Da idanu ya bita har ta shige sai kuma ya juyo ya kalli Tareeq, harararsa ya yi ya ce"ai sai ka shige mu tafi ko, nasan meyasa ka biyota ai, koni nayi mamaki sosai, kamar Katalina fa" ɗan haɗe rai ya yi ya ce"bansan ana kiran sunanta ka sani, zan samo information ɗin yarinyar nan da ita zan koma Qatar" tuntsirewa da dariya Tareeq ya yi ya ce"idan kaje tanada wanda take so fa?, har zaka wani yi confirming na tafiya da ita?" tsaki ya yi bai ce masa komai ba ya hangi wani yaro, da hannu ya yi masa alamar da ya zo yaron ya zo yana kallonsa ya ce"akwai manya a gidan nan? ya nuna gidan Baba Hansatu, gyaɗa masa kai yaron ya yi ya ce"Eh akwai, gidan Baba Hansatu ne" ajiyar zuciya ya sauke ya ce"yawwa Boy, cene ana sallama da ita kaji" da gudu ya bar wajen ya shige gidan. Kallon Tareeq ya yi ya ɗaga masa gira, dariya kawai ya yi ya cigaba da danna wayarsa.
Fitowa Baba Hansatu tayi tana wurga idanu ganin jajayen fata, cikin rawar murya ta ce"sann... sannu yaro, Allah dai yasa ba wani abun nayi ba?" murmushi Maheer ya yi cikin harshen Hausa wanda ba zaka yi tunanin ya iya ba ya fara magana "ko kaɗan bakiyi laifi ba Baba, kawai wasu tambayoyi nake son nayi miki idan babu damuwa" jinjina kai tayi ta ce "to...to.naji Allah ya sa na sani" jingina ya yi da jikin wata bishiya yana kallonta ya ce"wannan yarinyar ta gidan nan, wata fara ta cemin ita kaɗai ce a gidan Inason sanin gaskiya al'amarin" girgiza kai tayi ta ce"Imara kake nufi kenan, Allah sarki, ita da kakarta ne a gidan to kakar ta mutu, kai asalima ba wannan ce kakar tata ba, ƙawar kakarta ce, aka kashe iyayenta kakar ta ɗaukota daga birni to itama aka biyota aka kashe shine ta bawa wannan riƙo kuma yanzu Allah ya yi mata rasuwa. Ita kaɗai take rayuwa a gidan ko ƙawa batada ta kammala makarantar sakandire ma" numfasawa ya yi ya ce"Allah sarki, Allah ya jiƙansu da Rahama, yanzu Baba idan inason aurenta wa zan samu kenan?" Zaro idanu tayi ta ce"aurenta zaka yi?" Gyaɗa mata kai ya yi ta ce"da kuwa ka taimaka mata, akwai mijina sai ya zamar mata waliyyi kai kuma ka kawo naka waliyyin a ɗaura auren" murmushi ya yi ya ce"ai kuwa da na gode sosai in sha Allah zuwa anjima zamu dawo" jinjina masa kai tayi tana murmushi ta ce"To Allah ya kaimu lafiya, an gode sosai" kuɗin Nigeria Tareeq ya zaro ya miƙa mata bandir biyu, a kiɗime ta amshi kuɗin jikinta na ɓari ta ce"kai kai kai, yaro an gode muku ku kam, meyasa sai anjima zaku dawo a ɗaura auren?, ai kawai ayi yanzu, malam yana ciki yanzu a ɗaura ku tafi da ita" murmushi Tareeq ya yi ya ce"tom Baba mun gode Allah ya ƙara girma, kira shi ɗin" komawa tayi da sauri kamar zata tashi sama, da kallo Tareeq ya bita sai kuma yayi murmushi.
"Malam!! Malam!! Malam!!" "Na'am" ya furta yana fitowa daga ɗakin, kallonsa tayi ta ce"malam abun arziki har gida, kalli kaga" ta nuna masa kuɗin dake hannunta, ganinsa tayi a gabanta ya yi saurin karɓar kuɗin yana juyasu ya ce "Hansatu ina kika sami wannan maƙudan kuɗaɗen?" dafe haba tayi tana faɗin "kai dai bari malam, ai arziki Allah ya saukar mana, wannan yarinyar wajen Asiya tazo mana da Alkhairi, aurenta za'a yi shine aka bani wannan, muje yanzu za'a ɗaura auren kai ne waliyyinta" naɗe hannun babbar rigar dake jikinsa ya yi ya ce"Allah mai iko, to muje, kawo a ajiye wannan" ya fita yana tafiya kamar zai fadi.
Anan ƙasan bishiyar aka ɗaura auren Imara da Maheer akan sadaki naira miliyan 1, Tareeq ne ya ce"ya kamata a kira yarinyar dan a bata sadakinta a hannunta" girgiza kai Malam ya yi ya ce"a'a, ba sai an kirata ba kawai a bani zan ajiye mata" murmushi Tareeq ya yi ya ce"ai yanada kyau a sanar da ita sannan ta karɓi haƙƙinta da kanta" ba dan ya so ba aka aika yaro ya yi kiranta. Fitowa tayi tana sanye da hijab onion colour, hangosu da tayi yasa ta ɗan tsaya tana waro idanunta, da hannu Baba y yi mata alama da ta zo ta ƙaraso, cikin sanyin jiki ta ƙarasa wajen murmushi ya yi yana kallonta ya ce"yawwa ƴar albarka daman kiran ki aka yi a nuna miki mijinki a kuma baki sadakin ki" cikin rawar murya ta ce"sa...sadaki kuma Baba?, sadakin wa?, mijin wa?" murmushi ya yi ya ce"wannan bawan Allah ne ya aureki yanzu, arziki ya zo miki har gida Imara, yanzu ma dashi zaku tafi" girgiza kanta ta shiga yi sai kuma ta tafi luuu ta fadi ƙasa a sume.
# *Bestnovel*
# *Heart touching 💔*
# *IMARA 💋*
# *Maheer*
# *Nanameera*
# *2025*
08106608363.
https://chat.whatsapp.com/KLWdQLCbhFwJz1pDjuOvYD
*IMARA 💋 💋*
25&26
Mikiya writers asso...
08106608363
A hankali ta shiga buɗe idanunta, a ɗan firgice ta tashi zaune tana ƙarewa ɗakin kallo, turo ƙofar ɗakin a kayi, tayi saurin kallon wajen dan ganin wanda zai shigo. Wata irin bugawa zuciyar Imara tayi sanda tayi ido biyu dashi, ya ƙaraso hannunsa riƙe da tray. A kan table ɗin dake gefen gadon ya ajiye sannan ya zauna kusada ita yana kallonta, saurin matsawa tayi muryarta na rawa ta ce"a'a, lafiya?, ina ne nan?, dan Allah ka mayar dani gidanmu" murmushi Maheer ya yi bai ce komai ba ya zaro wayarsa yana dannawa a hankali, kallonsa Imara tayi sai kuma ta sake kallon daƙin, tayi saurin miƙewa tsaye tana kallonsa ta ce"ni ka mayar dani gida, bangane wannan abun ba" wayarsa ya mayar aljihu ya miƙe tsaye yana kallonta ya ce"ya kamata ki kwantar da hankalinki Imara, ki zauna ki ci abinci" wani kallo tayi masa ta ɗauke kanta tana jijjiga ƙafa, murmushi ya yi ya ce "shikenan, zauna ki ci abinci sai muyi maganar" kallonsa tayi sai kuma ta kalii inda ya ajiye tray ɗin abincin, yunwa take ji sosai hakan yasa ta nemi waje can gefe dashi ta zauna. Kallonta Maheer ya yi ya ɗauko tray ɗin ya ajiye mata a gabanta ya juya ya fice daga ɗakin, da idanu ta bishi sai kuma ta gyara zamanta ta buɗe abincin, Irish potato ne aka soya shi da kwai sai plantain da akayi garnishing da ita. Tea ta haɗa sannan ta fara cin abinci. Saida ta cinye komai tas saboda yunwar dake cikinta, ta yi gyatsa. Kamar jira yake ta gama ci ya shigo ɗakin, wannan karan ya sauya kaya, t-shirt ce white colour a jikinsa sai wando jins blue colour, kallo ɗaya tayi masa ta sunkuyar da kanta tana wasa da fingers ɗinta. Ƙarasowa ya yi ya zauna gefenta, ƙamshin turarensa ya daki hancinta tayi saurin lumshe idanunta, a ɗan firgice ta juyo ganin yanda ya riƙe hannunta cikin nasa, kallonsa tayi taga murmushi yake, saurin janye hannun nata tayi tana turo baki ta ce"akan me zaka dinga riƙeni?" Maheer couldn't help it but smile, above 2mins kafin ya ce"tashi mu je" tana kallon wani wajen daban ta ce"ina zaka kaini?, gida?" girgiza kansa ya yi ya ce"idan mun je zaki gani" taɓe baki tayi ta ce"ni to babu inda zanje" ta faɗa tana tura baki gaba. Murmushi ya yi ya ce"idan bazaki iya tafiya ba sai na ɗaukeki" da sauri ta miƙe tsaye tana zaro ido ta ce"Allah ya kiyaye" da hannu ya yi mata da su tafi, ta kalleshi sai kuma ta kalli hanyar, kamar wacce kwai ya fashewa a jiki haka ta fara tafiya.
A bakin shopping mall ɗin ya yi parking, ta kalli wajen, idan bata manta ba sun taɓa zuwa wajen da Daddynta, sunkuyar da kanta tayi tana jin wata irin kewa, Allah sarki rayuwa ta tabbata idan da Daddynta na raye da zuwa yanzu ba wannan ƙaddarar ce ta afka mata ba, Daddynta bazai taɓa aurar da ita a shekarunta ba. Kallonta Maheer ya tsaya yana yi ganin kamar bata jin abin da yake cewa, taɓa ya yi tayi saurin kallonsa sai kuma ta haɗe fuska,
"Meke damunki?"
Shiru tayi masa, ya ce"mu je ko?" sauka tayi daga motar ta tsaya tana jiransa, kashe motar ya yi ya fito yana kallonta ya ce"muje" tafiya ta fara yi tana kallonsa, suna shiga ya nemi kujera ya zauna, É—aya daga cikin ma'aikatan wajen ce tazo tana kallonsa ta ce"u are welcome sir" jinjina mata kai ya yi ta ce" me ake so?" Imara ya nuna mata ya ce "kaya wanda zai yi mata nakeson ki haÉ—a" cikin girmamawa ta ce"okay sir, ta kalli Imara ta ce"mu je Madam" kallonsa Imara tayi ya gyaÉ—a mata kai sannan tabi bayanta. Kaya sosai aka siya mata masu tsada kafin su bar mall É—in, a wani restaurant ya tsaya ya yi parking yana kallonta ya ce"mu je kici abinci" da sauri ta kalleshi sai kuma ta É—auke kanta tana kallon titi ta ce"bayan wanda naci, ni bana jin yunwa" murmushi Maheer ya yi ya ce"ai tunda rana kika ci abinci, kuma kinga yanzu magrib akayi"
"Nidai a ƙoshe nake, naga ɗazu naci abincin, kawai ka mayar dani gida mana" ta faɗa ba tareda ta kalli inda yake ba. Bai sake magana ba ya sauka daga motar kai tsaye kuma cikin restaurant ɗin ya nufa, binsa tayi da harara a ƙufule ta ce"aikin banza, ko ana dole" .
Bayan minti goma Maheer ya fito hannunsa riƙe da ledoji guda biyu, kallo ɗaya Imara tayi masa ta ɗauke idanunta, har suka je gida babu wanda ya sake magana a cikinsu. Bayan ya yi parking ya kalleta ya ce"ki shiga ciki zan je na dawo" bata ce masa komai ba ta buɗe handle ɗin motar ta sauka, ledojin daya miƙo mata ta kalla sai kuma ta ce"amma nace maka na ƙoshi ko?" murmushi ya yi ya ce"ai ba cewa nayi ki ci ba, ki shiga dashi kawai" ɗan tura baki ta yi sannan ta amsa ta juya ta shige gidan. Da idanu Maheer ya bita sai kuma ya girgiza kansa fuskarsa fal murmushi ya yiwa motar key ya bar gidan.
Imara nashiga ta wuce sama kai tsaye, ɗakin da ta zauna ɗazu nan ta shiga. Ta ajiye veil ɗinta kan gadon sannan ta shige toilet ta ɗauro alwala, tana fitowa ta tsaya jikin mudubi tana kallon veil ɗin data ajiye, ya yi ƙarami da sallah hakan yasa ta buɗe wardrobe ɗin dake ɗakin ko zata samu wani abu, ɗan kwaɓe fuska tayi ganin babu komai a ciki, ta koma ta zauna ta zuba uban tagumi.
Sai bayan sallahr magrib sannan Maheer ya shigo gidan, time ɗin tana zaune bayan ta idar da sallah da veil ɗin nata, sallama ya yi ya turo ƙofar ya shigo, a ciki ta amsa sallamar ya ƙaraso ya zauna gefenta yana kallonta ya ce"tashu muje ƙasa kici abinci" kamar ba zatayi magana ba sai kuma ta ce "sai yaushe zaka mayar dani gidanmu?" numfasawa ya yi ya ce "Imara Inason kibar wannan maganar, idan Allah ya kaimu next week zamu tafi gida, kinsan yanzu ke matata ce, saboda haka ni ne nakeda ikon tafiya dake duk inda zani, kuma bakida wani waje sai inda na ajiye ki, nayi miki alƙawarin zan kula da ke fiye da yanda kike tunani. Zan kai ki cikin ahalina, zan zame miki uwa zan zame miki uba, abinda kawai nakeso shine yardar ki" ya ƙarashe maganar yana dafa hannunta, kallon hannun nata tayi sai kuma ta kalli fuskarsa, haka kawai ta ji ta yarda da Maheer, ta yi shiru na wasu mintuna sannan ta ce"meyasa ka aureni?" murmushi Maheer ya yi ya ce"saboda ina sonki" cikin rawar murya ta ce"zan yarda da kai amma dan Allah karka juyamin baya, karka sakani kuka, ka ɗaukeni matsayin ƙanwarka wacce ba zaka cutar da ita ba, kaji Yaya!"
Da sauri Maheer ya ɗago ya kalleta sai kuma ya yi murmushi ya kamo hannunta ya riƙe cikin nasa ya ce"Thank you" ɗan murmushi tayi har saida beauty point ɗinta ya loma ta ce"nima nagode" hannunta ya kama ya tashi ya ce"muje ki ci abinci" gyaɗa masa kai tayi ya nuna mata hanya, tayi gaba ya bita a baya.
Tun daga wannan ranar suke zaune lafiya da Maheer a kullum shaƙuwa ƙara shiga tsakaninsu take, a haka har suka ƙarasa wannan satin, ranar Lahadi tana zaune bakin mirror tana gyara kanta ya shigo, ƙarasowa gabanta ya yi yana murmushi ya tsaya a gefenta yana kallonta ta jikin mudubi, kallonsa itama tayi tana murmushi
"Madam idan kin kammala muna iya tafiya" tashi tsaye tayi bayan ta yi parking gashin nata ta ce"Eh na shirya" gyaÉ—a kai ya yi sannan ya kama hannunta suka fita daga É—akin. A compound É—in gidan suka tsaya, ya buÉ—e mata backseat ta shiga sannan shima ya shiga driver ya ja motar suka tafi, kai tsaye airport suka shige, not too long kuma jirgin su ya tashi i zuwa Qatar.
Around 7pm suka shigo fadar, babu kowa a babban parlon hakan yasa kai tsaye yaja hannunta zuwa ɗakinsa, haɗaɗɗen ɗaki ne wanda yaji kayan more rayuwa, komai na ɗakin blue colour ne, domin shine favourite colour na Maheer, kallonta ya yi yana murmushi ya ce"yawwa Katalina shiga kiyi wanka, akwai kayan ki zan ɗebo miki" da wani irin mamaki Imara ta kalleshi sai kuma tayi murmushi ta ce"yaya manta sunan nawa kayi?, ko kuma tsokanata kake?" girgiza kai ya yi fuskarsa babu alamar murmushi saɓanin ɗazu ya ce"akan me zan manta sunan ki?, sunan da kika ji na ambace ki dashi shine sunan dana zaɓa miki, kuma muddin kina cikin fadar nan shine sunan da zaki dinga amfani dashi"
Tunda ya fara magana Imara ke kallonsa baki buɗe, kwata-kwata bata gane abinda yake faɗa, ƙwaƙwalwarta ta tunkushe tunani ya yi mata yawa, ganin yana shirin fita yasa tayi saurin shan gabansa tana riƙe rigarsa ta ce cikin rawar murya
"Yaya Maheer bangane abinda ka faɗa ba, ka daina yimin irin wannan wasan, tsoro nakeji, zan daina kula ka wlh, banaso, tsoro nakeji...!" Ta ƙarashe maganar tana fashewa da kuka, ta rungumeshi, ɗan tsaki Maheer ya yi kafin ya janyeta daga jikinsa yana kallon fuskarta wacce ta jiƙe da hawaye ya ce"it's better for you to obey my rules or else..." Ya yi mata gargadi da hannunsa sannan ya fice daga ɗakin.
Zubewa Imara tayi akan tiles É—in É—akin, banda tsuma babu abinda jikinta ke yi, wace irin masifa ce ta tunkarota?, wane hannu ta faÉ—a?, wace Katalina?, me Maheer ke nufi?, ko dai mafarki take, tunanin hakan yasa tayi saurin dukan fuskarta idan ma mafarki take ta farka, amma ga mamakin ta sai taga idanunta biyu. Kifa kanta tayi bisa gwuiwoyinta ta fashe da wani sabon kukan.
Ƙarfe takwas da rabi Maheer ya buɗe ɗakin ya shigo, zaune ya sameta kan tiles idanunta sun kumbura, ƙarasawa ya yi ya sanya hannunsa ya ɗagota yana watsa mata wani kallo ya ce"kee!, ina wasa dake ne?, baki ji abin da na ce miki ba?, kina son ranki ya ɓaci right?" girgiza kai Imara ta shiga yi ta ce"a'a wlh, tsoro naji yaya, dan Allah mu koma Jigawa, ka mayar dani gida, tsoro nakeji, bazan iya zama a nan ba" wani tsaki yaja yana kallonta ya ce"karki sake kiramin sunan wani gari anan, ki shirya yanzu ki sakko ƙasa, nasan kin iya yaren su, dan basa jin Hausa" juyawa ya yi ya fita kafin ta buɗe bakinta. Dafe kanta tayi ta jingina da wardrobe cikin wata raunatacciyar murya ta ce"inna lil lahi wa ina ilayhi raji'un, nashiga uku, wayyo Allahna, meke faruwa da rayuwata ne?, wace irin masifa nashiga?" Rashin sanin wanda zai bata waɗannan amsoshin ya sanya ta sake fashewa da wani sabon kukan.
A hankali tafara taka stairs É—in benan, sanya take da wata Abaya white colour ta yafa veil É—in Abayar tana tafiya tana kallon fadar. Daga can gefe taji ance
"Tabarakallah"
A ɗan firgice ta juya, sai kuma ta hangi jama'ar gidan zaune akan dinning table. A hankali ta ƙarasa bakinta na rawa ta gaishesu cikin harshen larabci, fuska a sake suka amsa mata musamman Shammah, ta kalleta cikin sakin fuska ta ce"zauna mana" ta faɗa cikin harshen larabci, cikin sanyin jiki Imara ta zauna ta sunkuyar da kanta, a hankali ya tura kujerar ya tashi, da sauri suka kalleshi, Immi ta ce"lafiya?" bai ce mata komai ba ya juya ya bar wajen, da idanu duk suka bi shi, banda Imara wacce har sannan kanta yake a sunkuye. Girgiza kai Shamma tayi ta cigaba da cin abincin ta, dakyar Imara taci abincin bayan takurawar da Shamma tayi mata.
12:30am.
Zaune take gefen gadon ta jingina da jikinsa, tunani ne fal zuciyarta, duk da dare ya yi sosai amma babu alamar bacci a tare da ita, tanada buƙatar ta yi magana da Maheer. Ta kasa gane abin da yake shirin faruwa da rayuwarta. Tana cikin wannan tunanin ya shigo ɗakin yana sanye da wasu pyjames black colour, s hankali ta saki ajiyar zuciya dan har ga Allah taji daɗin shigowar tasa, zama ya yi gefen gadon yana kallonta, gyara zamanta ta yi, tana ƙoƙarin magana ya ɗaga mata hannu.
"Nasan abinda zaki ce, nasan me za ki tambaya, wane ne ni?, meyasa na aureki?, me nake nufi dake?. To bar kiji, ni Maheer ne kamar yanda kika sani, kuma ɗa ga Amir wato Sheikh Fahad bin saleem al-kuwari, na aureki saboda wani dalili, ba lallai bane na sanar dake, the main thing shine ki yi duk wani abu dana umarce ki, daga yau ba irin wannan shigar nakeson kiyi ba, kuma daga yau sunanki Katalina a idona ba IMARA ba, idan har kika kuskura kika ce zaki saɓamin to ba zaki ji daɗin zama cikin fadar nan ba, saboda haka ki kasance yanda nakeso shine kawai abinda zai ceceki.
Kallonsa kawai Imara take tana hawaye, cikin rawar murya ta ce"daman ba saboda Allah ka aureni ba?, daman ƙarya kayimin?, meyasa zaka yaudareni?, meyasa zaka sanya mini soyyarka a zuciya sannan ka cutar dani?, akan me ka rabo ni da dangina?, meyasa! meyasa Maheer!!"
Tashi tsaye ya yi yana kallonta ya ce"ke kika ga zaki iya wahalar da kan ki, kina sona, bakya sona wannan bai dameni ba, abinda nakeso shine kawai abinda nake aiwatarwa, saboda haka zaɓi ya rage naki, kiyi biyayya ki zauna lafiya. Kuma ma da kike magana akan na raboki da kasarku, wa kike dashi a ƙasar?, wane gatanki?, zaman kanki fa kike, ai auranki da nayi taimako ne a gareki, saboda haka ni ba abin rainawar ki bane, fact.
Da idanu Imara ta bishi har ya ɓacewa ganinta, ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, dan kuka ma ya gagareta sai na zuci, komawa tayi ta jingina da gadon tana numfashi sama sama, kafin kuma ta samu ta fashe da wani raunataccen kuka mai shiga zuciyar mae sauraro. Yanda Imara taga rana haka taga dare cikin masarautar Udaid sanda taji anfara kiran sallah asuba ta tashi ta ɗauro alwala ta zauna kan ladduma tana roƙon Allah ya kawo mata mafita.
A haka ta cigaba da rayuwa a cikin gidan cikin takurawar Maheer, ko kaɗan baya barinta ta sake, gabaɗaya ta rame kamar ba ita ba, kullum sai zama a ɗaki tana kuka. Yau ma kamar kullum tana zaune kan kujera cikin ɗakinta ta zuba uban tagumi, akayi sallama aka shigo, a hankali ta ɗaga kanta jin ba muryar Maheer ba, Ameer da ta gani ya sanya tayi saurin miƙewa tana ƙaƙalo murmushin ƙarya ta ce"sannu da zuwa Ameer" lumshe idanunsa ya yi sannan ya buɗe su akanta, cikin rawar baki ta ce"na manta Ameer ka zauna" gyaɗa mata kai ya yi sannan ya zauna gefen gadonta cikin wata kamilalliyar murya ya furta
"Bismillah"
Zama Imara tayi itama tana kallonsa ta ce "Ameer lafiya?" kallonta ya yi da dara-daran idanunsa ya ce"IMARA"
"Na'am Ameer"
Numfasawa ya yi sannan ya ce"nasan zaki yi mamakin abinda zai fito daga bakina, duk da nima abun ya zo mini a bazata, bansan yaushe ba, bansan kuma dalili ba, amma naji na kamu da sonki tun ranar dana fara ɗora idanuna akan ki, inaji kamar ba ranar nafara ganinki ba. Nayi ƙoƙarin ganin na cire tunanin daga raina amma nakasa, inason ki Imara, ina sonki, soyyaya irin wacce bansan iyakarta ba, duk da ke matar ɗana Maheer ce amma ina faɗa miki haka, wlh ina sonki har cikin raina"
A É—imauce Imara ta tashi tsaye tana nuna shi da yatsa amma ta kasa cewa komai, ta shiga girgiza kanta hawaye na zuba akan fuskarta, tayi saurin dafe kanta tana rusa kuka, tashi tsaye Ameer ya yi yana kallonta sai kuma ya girgiza kai ya ce"ban faÉ—a miki sirrin dake zuciyata dan naga hawayen ki ba Lolo, Inason ki zauna kiyi tunani akan magana"
"Tunani?!, tunani fa Ameer?, me zanyi tunani?, ni ce fa IMARA matar Maheer ɗanka, amma ni kake so?, meyasa kuke son ganin ƙarshena ta hanyar irin waɗannan halayen naku, nakasa fahimtar komai, nakasa ganewa, ƙwaƙwalwata tayi ƙarama ba zata iya ɗaukan irin waɗannan tashin hankalin ba, kallon uba mahaifi nake maka nayi tunanin kaima zaka yimin kallon ɗiyarka wacce ka haifa, meyasa kake ƙoƙarin cutar da rayuwarta?, akan me zaka bari sheɗan ya shiga zuciyarka har ya sakaka furta irin waɗannan zantukan. Dan Allah ka tuba tun wuri Ameer, babu wanda zan faɗawa, wlh nayi maka alƙawari, amma karka sake irin wannan maganar. Numfasawa Ameer ya yi idanunsa na kallon ƙasa, s hankali ya ɗago ya kalleta, gabaɗaya launin idanunsa ya koma ja ya girgiza mata kai zai yi magana tayi saurin shigewa toilet saidai kafin ta rufo ƙofar har Ameer ya rigada ya shigo.
Cigaban labari.
Banda kuka babu abinda take yi Mama na taya ta, saida tayi mai isarta sannan ta ɗago kanta tana kukan ta ce "meyasa Mama?, bayan duk wannan wahalar dana sha ya rabu dani, duk wanda ya raɓeni a rayuwa da niyyar naji daɗi sai ya tafi ya barni, kowa baya zama tare dani, nafiso ma na mutu. Ta kalli Mama dake kuka ta ce"dan Allah Mama ki bani abinda zanci ko nasha na mutu, nagaji da rayuwar, banida kowa, banida kowa Mamah! Ni marainiya ce, wacce batada mai sonta, duk sun mutu, meyasa ni nake a raye Mamah?, meyasa!?, dan Allah ki bani abin mutuwa..." Rungumeta Mamah tayi tana shafa kanta ta ce"karki sake cewa haka Imara, kinada kowa, mu zamu zama dangin ki, ba za ki sake maraici ba IMARA, ki daina kuka kinji" ta cigaba da shafa sumar kanta, ajiyar zuciya Abaan ya sauke kafin ya juya ya bar wajen ba tareda ya shiga ɗakin ba.
# *Heart touching 💔*
# *IMARA💋💋*
# *Nanameera*
# *2025*.

*IMARA 💋💋*
27&28.
08106608363
Mikiya writers asso...
Around 7pm Mamah ta turo ƙofa ta shigo hannunta ɗauke da tray, da idanu Imara ta kalleta sai kuma ta sake sunkuyar da kanta. Ƙarasowa Mama ta yi ta zauna gefen bedside drawer tana kallonta ta ce"ki daina damuwa Imara, ko baki yarda dani ba ne?" Ɗago idanunta tayi ta kalleta sai kuma ta girgiza kanta cikin sanyin murya ta ce"na yarda Mamah" shafa kanta tayi ta ce"then ki daina damuwa, banason ganin ɓacin rai akan fuskarki, nan ma gidanku ne" jinjina kai tayi, Mamah ta ce "kici abinci gashi nan, idan kin gama sai ki sakko ƙasa wajensu Jadda tana bada labari" to kawai ta ce tana wasada fingers ɗinta. Kallonta Mamah tayi bata ce komai ba ta tashi ta fice daga ɗakin. Tana jin ta rufe ƙofar ta ɗago kanta, sai kuma ta sake fashewa da wani sabon kukan, gabaɗaya zuciyarta ta ƙi aminta da halin da take ciki, gani take kamar mafarki take wanda zata farka nan bada jimawa ba. Tanason ganin Maheer domin taji dalilin daya sanya ya saketa, kuma tanason sanin halin da Ameer yake ciki, duk da yanzu ita a matsayin wacce tayi kisan kai take a wajensu hakan bai sa taji batasan komawa ba. Sannan zama cikin gidan Mamah ba abu bane mai yiwuwa, dan ta fuskanci ya'yan gidan basu shirya amsarta a matsayin baƙuwa ba. Wadannan tunanin su ne suke damunta a koda yaushe, gabaɗaya ta rame kamar ba ita ba. Cigaba da zama tayi cikin ɗakin tayi har aka kira sallar isha'i ta tashi ta shiga toilet ta ɗauro alwala ta fito ta tada sallah.
Zaune suke sunyi da'ira a falon sai kallon Jadda suke wacce take faman basu labarurruka masu abun dariya, Nanah ce ta tashi daga gefenta tana miƙe ƙafarta ta ce"kai Jadda kuma to ya aka yi ta yarda" murmushi tayi ta ce"ke dalla to ya'yan yanzu da sun ji daɗin gidan miji mantawa suke da abin da ya faru, tuni ta haƙura ta zauna" tuntsirewa suka yi da dariya. Daga bakin ƙofa suka ji an ce
"Ba kusan dare ya yi bane?"
A firgice suka kalli inda yake sai kuma suka sunkuyar da kansu, shigowa ya yi yana sanye da jallabiya hannunsa riƙe da counter irinta zamani yana ja, kallonsa Jadda tayi sai kuma ta taɓe baki tana kallon gefe ta ce"Allah na tuba mutum sai baƙin hali ya ajiye, banda haka ina ruwansa da jikokina. Banza Abaan ya yi mata ba dan bai ji abin da ta ce ba, sai dan baya son ya shiga harkarta. Buɗe ƙofar parlon akayi suka shigo bakinsu ɗauke da sallama, sanye suke duk da jallabiya da alama daga masallaci suke shi ya riga su yo gaba. Zama Abbiey ya yi kan cushion yana kallonsa ya ce"Muhammad lafiya dai?" yana shafa gemunsa ya ce"ba komai Abbiey"
"Yo jaraba ce ta ishe shi, yaro ya girma ya zama babban mutum yana shirin zama tuzuru bai yi aure ba, sa'anninsa duk sun ajiye iyali shi yana nan sai zama a gidan uba, ana dafa abinci ana sammasa, sai shegen girman kai da faÉ—in zuciya. "
Jadda tayi maganar tana harararsa. Murmushi Abbiey ya yi ya kalleshi, ba zaka taɓa cewa da Abaan take magana ba, domin idanunsa a lumshe suke, girgiza kai ya yi ya kalli Jadda ya ce"to ay Jadda dan mutum ya girma ba shine yake nufin sai ya yi aure ba, duk da muna son muga ya yi auren amma dole sai mun yi masa uzuri tunda ba'a san abinda ya hana shi ba. Kame haɓa tayi tana firfito da idanu waje ta ce"aaa wannan rashin adalci ne gaskiya, ka daina haka, wane irin uzuri?, kana goyan bayan ɗanka kawai, amma dai wannan yaron yafi ƙarfin ace ayi masa uzuri." Hawaye ta shiga gogewa da gefen rigarta tana cewa
"Kawai dai so yake har sai Allah ya ɗauki raina sannan, bayason ya yi aure na kalla ya'yansa, rashin yin aurensa yasa babu wani a cikin ƙannensa da yake da niyyar yin aure"
Sai a sannan ya buɗe idanunsa wanda suka sauya launi zuwa jaa ya zuba mata. Murmushi Adeel ya yi ya ce"haba old woman karki wani damu, idan shi bai yi aure ba, ni nakusa yi, zakiga ya'ya na, dan yaya bai yi aure yanzu ba hakan ba yana nufin ba zai yi bane, komai a lokacine" ya ƙarashe maganar yana dariya. Wata uwar harara ta maka masa cikin hayaƙi take cewa"to tattabara, daga an yi maganar aure ya wani fara washe baki, saboda masifa ta masa yawa. To a hir ɗinka ko zaka ruɓe ba zaka yi aure ba sai yayanka ya yi. Harda wani washe min baki"
Tuntsirewa suka yi da dariya suna kallonsa, haɗe rai Adeel ya yi ya ce"lallaima ai sai ki hanani auran to tunda ke zaki ɗaura" kallonsa Abbiey ya yi yana murmushi ya ce"karka sake magana Adeel" sunkuyar da kansa ya yi Nanah ta ce"nima na ƙagu naga auran yaya wlh, kuma kinsan me Jadda?" girgiza mata kai Jadda tayi, ta ce" zan faɗa miki anjima"washe baki Jadda tayi tana kallonta ta ce"yawwa ƴar gari kar a saka mana idanu.
Wani sassanyan hawaye ne ya ziraro kan fuskarta, ji tayi dama ace ita ce take zaune cikin yan'uwan ta irin haka, yanayin yanda suke zaune suke nishadi sai taji ya burgeta.
"Imara"
Da sauri ta juyo sai kuma ta goge fuskarta, hannunta Mamah ta kama taji ɗumi hakan yasa ta taɓa wuyanta. Zafi sosai taji alamar zazzaɓi mai zafi. Cikin sanyin murya ta ce"Imara meya faru?, kukan me kike?" Murmushi tayi tana riƙe hannun Mamah ta ce"babu komai Mamah, kawai naji ina ma ni ce" murmushi Mamah tayi ta ce"zo muje ki zauna".
Kallonsu Jadda ta shiga yi har suka ƙaraso wajen, zatayi magana Abbiey ya ce"Imara zo ki zauna anan" da sauri ta kalleshi sai kuma ta ƙarasa inda ya nuna mata ta zauna a ƙasa, girgiza kai ya yi ya ce"no tashi ki zauna anan" girgiza kanta tayi ta ce"a'a zan zauna anan Abbiey" hannunta Abbiey ya kama ya ɗagota ta zauna kan kujerar dake kusada tashi. Tunda Mamah ta bashi labarinta yake matuƙar tausaya mata, musamman daya kalli yarinya ce ƙarama, wacce bata shige ace tana makaranta tana karatu yanzu ba, amma ta zama bazawara. Kallon Umaima Mamah tayi ta ce"ke ku tashi kuje kuyi sallah, dan na tabbata bakuyi ba kuna nan kuna hira" tashi suka yi Nana ta ce" ni fa Mamah bari nayi idan zan kwanta sai nayi" wata harara tayi mata daya sanya ta shigewa ba tareda ta sake cewa komai ba. Jadda ce ta kalli Abbiey ta ce"ni bangane wannan al'amari ba, wannan yarinyar kuma daga ina?, tun a jirgi muke tafe tare" murmushi Abbiey ya yi ya ce"baƙuwarmu ce Jadda" taɓe baki tayi ta ce"too, Allah ya kyauta". Mamah ce ta kalli Abaan ta ce"doctor ka sama mata magani, tun jiya take zazzaɓi kuma baya sauka" tashi ya yi ya shige ciki ba tare da ya amsa ba, lura da abin da yake nufi yasa Mamah ta kalli Imara ta ce"je ki ya baki magani dear" tashi Imara tayi jiki a sanyaye tabi bayansa. Saida ta bar wajen Jadda ta kalli Mamah ta ce" wace Irin rayuwa ce wannan haka?, ta bishi ina?, akai ta asibiti mana" murmushi Mamah tayi ta ce"ai Jadda gani nayi akwai kayan aiki a gida, kinga ba sai anje asibiti ba ko?" girgiza kai tayi ta ce"wannan ba hujja bace bari kiji, ni ban yarda ba, wannan yarinyar kwata-kwata bata kwanta min ba, saboda haka kar a dinga haɗata da yan gidan nan yawwa" murmushi Abbiey ya yi sannan ya ɗan bata labarin Imara. Allah sarki Jadda harda kukanta ta kalli Abbiey tana share majina ta ce"Allah sarki baiwar Allah, amma taga masifar rayuwa, to yanzu kenan ita batada kowa haka take rayuwa?, baiwar Allah, Allah ya bamu ladan riƙon maraya" murmushi sukayi duka kowa ya ce Ameen.
A hankali ta shiga ɗakin tana kalle kalle, zaune ta sameshi kan kujera yana danna wayarsa, cikin rawar murya tayi sallama kafin ta ƙarasa inda yake, tsugunawa tayi tana kallonsa cikin sanyin murya ta ce"gani" banza ya yi mata ya cigaba da danna wayarsa. Ta gyara zamanta tana kallon ƙasa, saida ya kwashe mintunu biyar kafin ya ajiye wayar hannunsa ya tashi ba tareda ya kalleta ba ya shige bedroom ɗinsa, ɗago idanunta tayi ta bi shi da kallo haka kawai taji ranta yana ɓaci dan a rayuwarta ta tsani mutum ya shareta. Tana nan zaune har bacci ya fara ɗauketa bai fito ba, a hankali ta tashi tana kallon ƙofar ɗakin sai kuma ta tura baki ta ƙarasa wajen, duk da yanda take jin tsoro ganin yanda yake haɗe rai hakan bai hanata tura ƙofar ɗakin ba. Wani irin ƙamshi mai sanyi ne ya daki hancinta wanda ya haddasa mata da mutuwar jiki, a hankali ta jingina da murfin ƙofar tana dafe ƙirjinta. Kamar tasan irin wannan ƙamshin saidai ta kasa tuna inda ta san shi, a hankali ta buɗe idanunta wanda ta rufe su ba tareda ta sani ba. A kwance ta hangeshi ya rufe jikinsa da duvet da alama ma ya manta da wani babin ta. Haɗe fuska tayi kamar za ta yi kuka, ta ƙarasa gabansa. Zama tayi kan bedside drawer ɗin wajen tana kallon bargon daya rufe jikinsa, turo baki tayi sai kuma ta jingina da bangon ɗakin ta lumshe ido nan da nan bacci ya kwasheta a zaune.
Ƙarfe 11:20pm Mamah ta turo ƙofar bedroom ɗin ta shigo. Wani irin ajiyar zuciya ta sauke tana dafe ƙirji kafin ta ƙarasa inda take baccin. Sosai ta bata tausayi ganin yanda take bacci a zaune bata ko tsoron wuyanta ya yi ciwo. Girgiza jikinta Mamah tayi, ta yi saurin buɗe idanu tana kallonta hannunta ta kama suka fita gudun kada su tashe shi. Saida ta kai ta har ɗakinta sannan ta kalleta ta ce"ya ba ki maganin?" Kamar zatayi kuka ta girgiza mata kai, murmushi Mamah ta yi ta ce "shikenan bari na samo miki paracetamol kafin zuwa da safe muje asibiti" jinjina mata kai Imara tayi ta kwanta gefen gadon, ita kuma ta juya ta fita. Bayan ta dawo ta tashe ta ta bata maganin sannan ta gyara mata wajen kwanciya, saida taga ta koma bacci sannan tayi mata addu'a ta bar ɗakin.
2:45am.
Tsaye yake cikin bedroom ɗinsa ya kasa zama sai kai komo yake. Tunda ya saka idanunsa kan yarinyar ya kasa samun nutsuwa tunanin yanda zai ɓullowa al'amarin yake. Amma tabbas ko ta wane hali sai ya san yanda zai sameta. Da wannan tunanin ya koma ya kwanta kafin bacci ya ɗaukeshi.
Yanda Imara taga rana haka taga dare ranar, dan tun bayan fitar Mamah ta buɗe idanunta, tsananin ciwon kai da zazzaɓi shine ya dameta, gefe guda kuma mararta da take mata wani irin azabbaben ciwo. Tana idar da sallahr asuba ta kifa kanta akan gwuiwarta ta fashe da kuka, ganin kukan ba zai kai mata ba ya sanya ta tashi tana dafe kanta ta fice daga ɗakin. Hanyar ɗakinsa ta nufa tana zuwa ta tura ƙofar ta shiga bata ko ganin gabanta, babu kowa a parlon sai ƙamshin turarensa dake tashi. Cikin bedroom ɗin ta shige, zubewa tayi a ƙasa ganin nan ma babu kowa, ta dafe mararta tana runtse idanunta, above 5mins kafin ya buɗe ƙofar ya shigo, kafeta ya yi da idanu sai kuma ya shige ciki, system ɗinsa ya ɗauko ya nemi waje ya zauna bayan ya ɗauko yogurt ya buɗe ya yi bismillah ya fara sha, kafin ya cigaba da danna system ɗinsa hankali kwance. Wani irin ihu da yaji ya sanya ya ɗago kansa, kwance ya ganta a wajen tana kuka tana burgima. Ɗan ƙaramin tsaki yaja kafin ya tashi ya ƙarasa inda take hannunsa riƙe da kwalin yogurt ɗin, tsugunawa ya yi a gabanta ya sanya hannunsa ya ɗago fuskarta yana kallonta ya ce
"Mene?"
Kamar jira take ta sake rushewa da wani sabon kukan tana yarfe hannunta, numfasawa ya yi sannan ya ɗagota zaune idanunsa zube kan fuskarta ya ce "idan bakida abin faɗa tashi ki bani waje" cikin shassheƙar kuka ta ce " ka bani magani, zan mutu cikina ciwo yake, nashiga uku" taɓe baki ya yi ya ce"Allah ya jiƙanki" daga haka ya tashi ya fice daga ɗakin, wata irin kartawa mararta tayi ta saki wata irin ƙara sai kuma ta faɗi ƙasa a sume.
# *IMARA 💋*
# *Nanameera*
# *Bestnovel*
# *2025*
*IMARA 💋💋*
29&30.
08106608363.
Mikiya writers asso...
Durus Abaan ya yi yana kallonta kafin a hankali ya ƙarasa gabanta. Ɗagota ya yi ya zuba mata idanu sai kuma ya mayar da ita, ya tashi ya ɗauko ruwa a fridge ya dawo ya zuba mata. Wata nannauyar ajiyar zuciya Imara ta sauke ta shiga buɗe idanunta a hankali, barin wajen ya yi ya koma kan sofar ya zauna. Da kyar ta tashi zaune ta jingina da jikin gadon tana kallonsa, sai kuma ta fashe da kuka. Tashi Abaan ya yi ya shige toilet ya barta a wajen, duk yanda ta so ta tashi kasawa tayi sai kawai ta sake lumshe idanunta hawaye na sintiri akan fuskarta. Kusan 20mins kafin ya fito daga toilet ɗin sanye da bathrobe, ta gefen ido ya kalleta yaga idanunta a rufe ya mayar da kansa gaban mirror ɗin. Saida ya gama shiryawa cikin wata dakakkiyar shadda Madam gezner black blue, ya ɗora hularsa mai aikin blue, wani irin sihiritaccen kyau ya yi ya fito kamar balarabe, sai a sannan ya juyo ya kalleta bayan ya ɗauki wayarsa ya kalli inda take zaune. Ƙamshin turarensa ne ya sanya ta buɗe idanunta a hankali, sunkuyar da kanta tayi hawaye na zubowa kan fuskarta, girgiza kai ya yi ya ce"tashi muje" daga haka ya juya zai fita. Turo bakinta ta yi cikin wata murya mai rawa ta ce
"To ni bazan iya tafiya ba"
Yanda tayi maganar kamar tana kuka yasa ya juyo ya kalleta sai kuma yaja ya tsaya a wajen, sunkuyar da kanta tayi tana wasada fingers ɗinta. Ɗan siririn tsaki yaja sannan ya dawo inda take zaune ya ya kamata ta tashi tsaye ya ce"to mu je" sake kwaɓe fuska tayi ta ce"ni ba zan iya tafiya ba" ƙura mata idanu ya yi sai kuma ya yi kamar zai sunkuya ya ɗauketa kamar yar Baby ya fita da ita.
A corridor ɗin benan suka haɗu dashi yana sanye da suit black colour daga alama shiryawa ya yi zai tafi aiki, cike da girmamawa ya sunkuya ya ce"Barka da safiya doctor " jinjina masa kai kawai Abaan ya yi sannan ya juya ya bar wajen, kai tsaye kuma ɗakin Mamah ya shiga. Zaune ya sameta gefen gado tana sanye cikin wata embroidery atampa milk da adon baƙi tayi kyau kai ba zaka ce ita ce wacce ta haife shi ba. A gefen gadon ya ajiye Imara ya kalli Mamah cikeda girmamawa ya ce"Barka da safiya" fuskarta ɗauke da yalwataccen murmushi ta ce"ka tashi lpy son?"
"Alhamdulillah"
Ya ce a takaice, jinjina kai tayi sannan ta mayar da kallonta kan Imara ta ce "jikin ne?" faɗawa jikinta tayi ta fashe da kuka, zafin da Mamah taji yasa ta yi saurin kallonsa ta ce "doctor baka dubata ko?" ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce"jiya bacci nayi Mamah ki shirya ta ina apartment ɗin Jadda" daga haka ya fice daga ɗakin cikin tafiyarsa ta ƙasaita. Girgiza kai Mamah tayi tana jinjina hali ko in kula irin nasa, kafin ta kama hannun Imara ta ce"sannu dear" .
***Turo ƙofar ɗakin akayi ta ɗaga kanta daga kwance da take ta kalleta sai kuma ta cigaba da danna wayarta
"Sai yanzu kika ga damar zuwa?"
Ƙarasowa Amrish tayi tana murmushi ta ce"sarkin fushi, ai gani dai nazo, tunda na ce miki zan zo ai kinsan ina hanya" tashi zaune Jidda ta yi ta ajiye wayarta tana kallonta ta ce "nakasa bacci jiya, hankalina ya tashi Amrish, bazan iya cigaba da rayuwa a haka ba, nadawo daga Zaria amma takaicin dana tarar saida na gwammace ban dawo gida ba" numfasawa tayi ta ce
"Kema Jidda, ki daina wani tada hankalin ki, kin sani Abaan yana matuƙar son ki, kuma ba zai taɓa yin abin da zai raba ki dashi ba, tun kina ƙarama yake ɗaukan duk wata ɗawainiyarki. To meyasa yanzu kike tadawa kanki hankali akan abin da yake mallakin ki?, dan kawai jiya bai kula ki ba ai ba hakan yana nufin ya daina sonki ba, kuma kinsan halinsa na shariya"
Girgiza kai Jidda tayi ta ce"you can't understand Amrish, Abaan bafa irin sauran maza bane, kinsan halinsa kuwa?koda sau É—aya kika ga ya sauya fuska to tabbas akwai abin da ba daidai ba, banason matsala wlh"
Dafata Amrish tayi ta ce"don't worry ƙawata, Abaan naki ne ke kaɗai, kawai ki cigaba da son shiga zuciyarsa har kiyi nasara, koma akwai wata wacce yakeda muradi ya ji ta daina burgeshi"
Wani murmushin jindadi tayi wanda ya fito da zallar kyanta ta ce"shiyasa nake sonki ƙawata, yanzu kin san me?, bari na shirya muje muyi breakfast" gyaɗa mata kai kawai tayi, ta tashi daga kwancen ta shige toilet dan yin wanka, da idanu kawai Amrish ta bita sai kuma ta zaro wayarta ta shiga dannawa.
***Washe baki Jadda tayi tana cewa"kaga É—an albarkan jika, shiyasa duk cikin jikokina nafi sonka, saboda yanda kake ji dani" kallonta kawai Abaan ya yi da manya manyan idanunsa ta cigaba da faÉ—in" yawwa yanzu wannan bazawarar daka kawo gidan nan fa?, naga yarinyar tanada kyau, narasa inda nasan me irin kamarta, tana kamada wata wlh" shi dai Abaan sai kallonta yake, zata cigaba da magana Mamah tayi sallama ta shigo falon Imara na biye da ita. Murmushi Jadda tayi tana kallonta ta ce
"Sannu da zuwa yarinya, ya kwanan baƙunta?"
Jiki babu kwari Imara ta tsuguna cikin cool voice ɗinta ta ce "ina kwana" shiru Jadda tayi ta zuba mata idanu, jin bata ce komai ba ya sanya Imara sunkuyar da kanta. Wani irin jiri take jin yana ɗibanta a zaune ga mararta dake mata wata iriyar karta. Tashi tsaye Abaan ya yi ya kalli Mamah ya ce"sai nadawo" daga haka ya fice ba tare da ya sake bi ta kan Jadda ba. Hannun Imara Mamah ta kama ta miƙar da ita tsaye sannan ta ce"ki je kar ya tafi ya barki" jinjina kai kawai tayi sannan ta yi waje tana tafiya a hankali.
***Durus tayi a bakin entrance ɗin falon, sai kallon ko'ina take, yawan motocin data gani yasa ta kasa gane wacce ya shiga. Ganin yanda rana ke facing ɗinta yasa ta tsuguna a wajen tayi tagumi nan da nan hawaye suka fara zuba kamar an buɗe famfo. Tunda ta fito Abaan yake kallonta har zuwa sanda ta zauna, yana zaune cikin backseat ɗin wata baƙar mota ko ba'a faɗa maka ba kasan irin motocin nan ne wanda aka saka kuɗaɗe aka siya. A hankali ya ƙaraso gabanta hannayensa zube cikin aljihu, saurin ɗago kanta tayi saboda inuwar mutum data gani, murmushi Adeel ya sakar mata a hankali ta tashi tsaye bakinta na rawa ta ce
"In...ina kwana?"
Bai amsa mata ba sai murmushin da ya cigaba da yi, ganin haka ya sanya Imara ta sunkuyar da kanta ƙasa tana wasada fingers ɗinta wanda suka kasance dogaye, numfasawa ya yi sai kuma ya ce"me kike anan Imara?" buɗe baki tayi zata yi magana ta hangeshi tsaye ya kafeta da idanunsa, saurin maida kanta ƙasa tayi dan bata iya jurar haɗa idanu dashi. Ganin inda ta kalla ya sanya Adeel ya juya, rissinawa ya yi cikin ladabi ya ce"Barka da safiya yaya" Cikin sakin fuska ya ce"Ka tashi lpy Adeel?" Jinjina kai ya yi ya ce "Alhamdulillah" gyaɗa kai kawai ya yi sannan ya kama hannunta ya bar wajen.
Wani Kallo Jidda ta bisu dashi har suka shiga motar bayan ya amshi key ɗin ya zauna a driver seat ita kuma ta zauna a gefensa, ta lumshe idanunta. Ya yiwa motar key ya bar gidan da gudu kasancewar kwalta ce a ciki. Saurin riƙe hannun Amrish tayi bakinta na rawa ta shiga nuna mata inda suka tafi, hannunta Amrish ta kama suka shiga mota ta amshi key ɗin dan tasan ba lailai tayi driving ɗin ba. Saida suka hau kan titi sannan ta kalleta ta ce"wacece wannan yarinyar?" murmushin yaƙe Jidda tayi ta ce"nima bansani ba, na ganta a ɗakinsa rannan, nd yau kuma naga ya fita da ita, koma wace i must find out sannan kuma zan mata abun da ba zata taɓa mantawa dani ba"
"Me za ki yi mata?"
Girgiza kai Jidda tayi ta ce"karki wani tambayeni, ki bari idan na aiwatar sai kowa ya gani, amma wlh sai tayi danasanin shigowa gidan nan" murmushi Amrish tayi ta ce"bana jin ki ƙawata, nasan za ki yi abin da ya dace, amma karki yi abin da zai yi causing problem" kwafa tayi ta ce"babu wanda zai haddasawa matsala sai wanda ya jawo matsala da kansa, sai na tabbatar da na wulaƙanta ta, domin wlh babu wacce ta isa ta raɓi Abaan, koda kuwa bayan raina ne" ajiyar zuciya Amrish tayi tana kallon titi ta ce
"Ina muka nufa?"
"Muje Novo kawai".
***A bakin wata ƙaton asibiti na KFJ ya yi parking, iya ka haɗuwa asibitin ya haɗu dukda babu wasu masu shige da fice a cikinsa da alama ma ba'a kai ga buɗeshi ba. Buɗe motar ya yi ya sauka sannan ya zagayo ta inda take ganin kamar bacci take, handle ɗin ƙofar ya buɗe ya taɓa kanta ya ji har sannan da zafi sosai, ya tashe ta sannan ya shige ciki, a baya ta biyo shi har cikin asibitin. Lift suka hau sannan suka je second floor na asibitin, ɗakuna ne birjik sai threater ya buɗe wani office ya shiga, babban office ne wanda ya gaji da haɗuwa ko a asibitocin ƙasar waje iya kar abin da za'a yi masa kenan. Ya ƙarasa ya ajiye wayarsa sannan ya juyo ya kalleta ya ce"zauna" waje ta samu ta zauna kan wata kujera ya juya ya fita. Bayan 5mins ya dawo hannunsa riƙe da injection da drip tana ganin haka tayi saurin langwaɓar da kanta jikinta na rawa, a kusada ita ya zauna ya haɗa allurar sannan ya tashi ya tattare hannun rigarsa yana kallonta ya ce"gyara" ya faɗa a takaice, rawar jiki ta fara yi tana kallonsa nan da nan wasu sabbin hawayen suka sake wanke mata fuska. Ikon Allah Abaan ya tsaya yana kallo kafin ya haɗe rai lokaci ɗaya ya ce
"Hey! Cry cry baby, ce miki a ka yi banida wani abin yin ne?, ki gyara nayi miki injection"
Sake rushewa tayi da kuka ta sanya hannayenta biyu ta rufe fuskarta tana girgiza masa kai, baki buɗe yake kallonta sai kuma ya ce"Ke, Imara ke ki ko wa?, wa za ki yiwa yarinta anan wajen?, ki nutsu kin ji ko!" Cikin shassheƙar kuka ta ce"dan Allah kar ka yimin, tsoro nakeji wlh, zan mutu ni, wayyo Allahna" zuba mata idanu Abaan ya yi kafin ya ajiye injection ɗin a gefen desk ya kalleta sai kuma ya ja kujera dake facing tata ya zauna yana kallonta ya ce
"Shikenan na ajiye"
A hankali ta shiga zare hannayenta daga kan fuskarta tana leƙensa, hannunsa ta kalla taga babu injection ɗin hakan yasa ta yi saurin buɗe fuskarta ta shiga share hawaye wanda ya yi mata kaca -kaca da fuska harda majina. Ɗan murmushi ya yi har saida beauty point ɗinsa suka loma kafin ya ce
"Bakison injection ko?"
Saurin gyaɗa masa kai tayi tana kwaɓe fuska kamar yar Baby, haɗe rai ya yi ya ce
"Bakida baki?"
"Ina da shi"
"Shine kike min maganar kurame"
Murmushin da bata yi niyya ba tayi ta ce"dan Allah karka yimin allura ka ji ko, bana sonta, tun da ma banaso, tun ina yarinya"
"Oh, yanzu kin girma a haka?"
Da sauri ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kanta ta ce"na girma mana, kuma Dodona ya cemin zan yi saurin girma gashi yanzu na girma sosai" shiru ya yi yana kallonta ta sake cewa
"Tunda ya tafi ya barni a makaranta bai sake dawowa ba, koma ya sani Umma ta rasu?, bayasona, bayan ya ce ba zai taɓa tafiya ya barni ba, shine ya gudu, ina jin tsoro sosai, inason na sake ganinsa, inason ganin fuskarsa, shima ya ce min yanada kyau irina. Kamar kai kuma sannan..."
Ɗago idanunsa ya yi ya kalleta sai kuma ya ce"ki cigaba mana" langwaɓar da kai tayi ta ce"kawai bana son shi ne, na daina kula shi. Koda na ganshi babu ruwana dashi, tunda ya saɓa alƙawari, ni Maheer nakeson gani."
Wani zazzafan numfashi Abaan ya sauke sannan ya ce"to kika sani ko ya yita nemanki bai ganki ba" girgiza kanta tayi hawaye na kawowa idanun ta ce"bai nemeni ba, ya tafi ya barni bai sake zuwa ba, yana sane ya tafi. Saboda ya ce a dinga bani abinci, bai san halin da na shiga ba a sanda ya tafi ya barni, ya ƙarya alƙawarinsa, saboda haka babu ruwana dashi. Har abada!" Ɗan murmushi Abaan ya yi ya ce"shikenan, ke bakida yafiya?, anyway tashi muje na saka miki drip ko shi ma bakya so" tashi tayi tabi bayansa suka fita daga office ɗin, wani ɗaki a gefen office ɗin ya shiga. Akan gado ta zauna ya haɗa ruwan sannan ya sanya mata bayan ta saka kukan shagwaɓa, a cikin drip ɗin ya sanya allurar wacce ta haddasa mata da bacci lokaci guda. Zama ya yi gefenta ya ƙura mata idanu yana kallonta, a ɗan firgice ta ɗago ta ɗora kanta akan cinyarsa cikin baccin tana faɗin
"Babu ruwana dashi ai!, ya tafi ya barni"
Shafa kanta kawai ya yi ya shiga yi mata addu'o'i. Murmushi ya yi yana kallon yanda ta kwaɓe fuska ko a cikin bacci bata huta da rigima ba ya dafa kanta ya ce
"I'm here for you".
# *IMARA 💋*
# *Dodo*
# *Bestnovel*
# *Nanameera*
# *2025*
*IMARA 💋💋*
31&32.
08106608363.
Mikiya writers asso...
***Turo ƙofar parlon tayi ta shigo tana jan jakarta, Jadda dake zaune kan kujera ta hakimce tana taunar nama. Zama Umaima tayi akan kujera ta ɗan zame jikinta ta kwanta. Wani banzan kallo Jadda ta watsa mata sai kuma ta ce
"Ke kam wannan yarinya an yi malalaciya, ji yanda kika wani kwanta kamar ruwa, yara duk kun saba da sangarta to ki sauya hali"
A fusace Umaima ta tashi zaune ta kalleta kamar za ta yi kuka ta ce"to dan Allah ina ruwan ki dani Jadda?, Saboda bakisan wahalar dana sha ba. Tun safe nake yawo a school amma shine nadawo za ki kama ki rufeni da faÉ—a. Saboda daman kin tsaneni"
Umaima ta tashi daga falon tana goge hawaye. Riƙe baki Jadda tayi tana cewa
"Karki yarda ki yimin sharri, yaushe nayi miki faÉ—a?, salon ubanku ya dawo ya ji kisa ya tsaneni, to ta Allah ba ta ki ba wlh" Umaima bata sake bi ta kanta ba ta haye sama kai tsaye kuma É—akinta ta shiga.
***Kallonta Amrish tayi ganin sai juya smooth É—in gabanta take ta ce"wai me kike tunani kuma ?" girgiza kai tayi tana cire hannunta daga kan smooth din ta ce"nakasa yarda da abin da nagani ne wlh!, Gaba-daya yanzu tunanina ya ta'allaka akan na gano wacece wannan yarinyar. A ina Abaan ya santa?, Me yasa kuma take biye dashi and he can't scold her, why?" Murmushi Amrish ta yi bayan ta ajiye pork É—in hannunta ta ce
"Jidda! Jidda! Jidda, ki daina sakawa kan ki damuwa. Kinsan dai yana yin lafiyarki, karki manta an rigada an yi miki baiko keda Abaan, so probably zaki aure shi, wannan kina damun kan ki ne a banza kawai. Wacece wannan yarinyar, a ina ya santa?, Duk bai dame ki ba, tunda kina da tabbacin Abaan ba mai kule-kulen mata bane, saboda haka dan Allah ki daina damun kan ki kawai ki ja mana masifa"
Numfasawa tayi ta miƙe ta ɗauki car key ɗin ta tana kallon agogon hannunta ta ce"yamma ya yi already, tun safe muka fito gida zan tafi. Nasan maybe yanzu Abaan ya dawo, zan je na ganshi ne"
Ta shi itama tayi ta ce"haka ne, muje sai ki ajiye ne a Tahir saboda mun yi da Alhaji zamu haÉ—u acan"
Taɓe baki Jidda ta yi ta ce"to Allah ya kyauta" .
***Ƙarfe 7:04 Jidda tayi parking ta fito kai tsaye kuma apartment ɗin su ta nufa. Tana shiga ta sami Mommy zaune ta ci uwar kwalliya sai taunar chew gum ta yi, murmushi Jidda ta yi ta ƙarasa ta zauna gefen ta ta ce"Hajiya Mommy irin wannan kwalliya haka?" Kallonta Mom tayi sai kuma ta harareta ta ce"ke fita a idona, ki je kiyi wanka ki shirya ina nan ina jiran ki" langwabar da kai tayi ta ce"okay Mommy".
Wani kallo Umaima ta watsawa Nana kafin ta ce"ina ruwan ki da ita?, A kanki take?, Wlh ki shiga taitayinki kinsan dai wanda ya kawota gidan" turo baki Nana ta yi ta ce"to ai gaskiya nafaɗa, kawai ta zo ta takura mana, ni wlh bata yimin ba" harararta Umaima tayi ta ce"tunda a rayuwa kana zaɓar wanda ya yi maka da wanda bai maka ba. Ki je kiyi ta yi, watarana sai kin jawo masifar da zata dame ki wlh"
ÆŠaga kafaÉ—a Nana tayi irin bai dame ta É—in nan ba, ta tashi zata fita.
"Da wannan shigar za ki fita?"
Kallon kayan jikinta ta yi, t-shirt ce baka sai wani jeans 3-quarter wanda ya tsaya iya gwuiwarta, ta tufke gashin kanta ya zubo har bayanta. Turo baki ta yi ta ce"to me shiga ta tayi?, Naga wajen Jadda zan je" gyaÉ—a kai Umaima ta yi ta ce" Allah ya taimaka" fita Nana tayi ba tare da ta sake magana ba.
Kallon inda ya yi parking ta yi sai kuma ta sunkuyar da kanta, bai ce mata komai ba ya sauka daga motar hakan yasa ita ma ta sakko tana binsa da idanu. Kai tsaye cikin mall É—in ya nufa ita kuma ta bi bayansa, bayan ya shiga wata ma'aikaci ta zo tana murmushi ta ce
"Welcome sir"
"Kaya na budurwa kamar ta, banda ƙananun kaya, I mean only Abaya"
Jinjina kai tayi sannan ta juya ta bar wajen. Imara na nan wajen a tsaye har aka kai kayan cikin mota ya bada atm card suka cira sannan ya juya ya bar wajen. Tun da suka shiga Mota ta shiga share hawaye tana kuka, Abaan na lura da ita amma bai ce komai ba har suka ƙarasa gida. Bayan ya yi parking ya kalleta sai kuma ya fito daga motar ya shige gida dan daman saida ya yi sallar isha'i sannan ya shigo, a falon ya samesu suna kallo Jadda na fam zuba kamar yanda ta saba,
"Sannu da zuwa yaya"
Wata razananniyar tsawa ya daka mata, wacce tasa ta bar falon da gudu tana kuka. Tsaki ya yi Sannan ya kalli Mamah ya ce"wace irin shiga ce wannan yarinyar ta ke yi ne haka?, nd kuma kina kallo ba za ki yi mata magana ba?"
"Yanzu Abaan ba gashi ka yi mata ta ji ba, nayi maganar amma Jadda ta hanani wai na rabu da ita"
"Muhammadu Rasulullahi, ni za ki yiwa sharri, to keda Allah, kana ji wlh babu ruwana, yo yarinya ce bata jin magana shine kawai na hukunta ta"
Ko kallonta Abaan bai yi ya bar wajen. Ajiyar zuciya Jadda ta sauke sai kuma ta kalli Mamah ta ce
"Karki sake yimin irin haka a gabansa, ba kiga yanda ya haÉ—e rai ba ne"
Girgiza kai Mamah kawai tayi, ta tashi ta bar wajen. Sai a sannan Imara ta yi sallama ta shigo parlon, kallon Jadda ta yi sai kuma ta sunkuyar da kanta ta gaisheta cikin rawar murya.
"Yarinya ya ma sunan ki?, Sannu da dawowa, zo nan ki zauna" a hankali Imara ta ƙarasa ta zauna kusada Jadda ta jingina da jikin bango. Tashi Jadda ta yi ta ce"na ajiye wata fura bari na kawo miki ki sha" daga haka ta bar parlon. Imara na ganin ta shiga part ɗin ta ta tashi ta haye sama tana tafiya cikin sauri. Tura ƙofar ɗakin ta yi ta ganshi tsaf dashi da alama an sake gyarawa. Zama tayi gefen gado ta jingina dashi ta shiga kukanta wanda tun ɗazu yake cin ta. Above 5mins Umaima ta buɗe ɗakin ta shigo, turus tayi ganin yanda Imara ke kuka kamar ranta zai fita. A hankali ta ƙarasa gabanta ta zauna gefenta ta dafata. Ganin bata daina kukan ba yasa ta ce
"Imara me aka yi miki?, Meyasa ki ke kuka?, Wani abun yaya ya yi miki?" Imara couldn't help it but cry, ta cigaba da kukanta. Riƙota Umaima tayi ai kuwa kamar jira take ta faɗa jikinta tana kuka, sosai ta bawa Umaima tausayi kai da ka ganta kasan tana cikin jarrabar rayuwa gata kuma da ƙananun shekaru. Shafa kanta ta shiga yi cikin lallashi ta ce
"Ki daina kuka, addu'a ita ce mafita a koda yaushe, ki dinga faɗawa Allah buƙatar ki, tabbas nasan zai share kimi hawaye. Kin sha wahalar rayuwa Imara amma hakan ba shine dalilin da zai sanya ki maida damuwa abokiyar rayuwarki ba"
"Tsoro nake ji, naji tsoro, irin haka Maheer ya kai ni ya siyamin kaya, ya ce zai zauna dani, ba zai taɓa barina ba, zai zame mini garkuwa, ba zan sake kuka ba. Amma hakan bai faru ba, Maheer ya gujeni, Maheer ya barni daga ƙarshe kuma ya sakeni. Shi ma yanzu ya siyomin kaya, ina tsoron na bar gidan nan, dan Allah ki taimakeni, tsoro nake ji"
Rungumeta Umaima tayi, sai a sannan ta san dalilin kukan nata, dafata tayi ta ce"babu abin da zai faru sai alkhairi Imara. Na tabbata tun da yaya Abaan ya kawo ki gidan nan ba zai bari a cutar dake ba, dan ya siya miki kaya hakan ba yana nufin ya shirya korarki ba, muna nan, gidan nan ya zama gidanki. Ki daina damun kan ki, kada kuka yasa wani ciwon ya sameki Imara"
Haka Umaima ta yita rarrashinta har saida taga tayi shiru, ta É—ago fuskanta tana kallonta ta ce"je ki wanke fuskarki ki zo muje, Jadda ce ta aikoni na kira ki" gyada mata kai Imara tayi sannan ta tashi ta shiga toilet ta wanko fuskarta kamar yanda Umaima ta ce mata, murmushi Umaima ta yi ta ce"yawwa, kinga har kin yi kyau, muje" bin bayanta Imara tayi tana tafiya a hankali.
Tun da ya hango su ya zuba mata idanu yana kallonta, Murmushi Umaima ta yi ta ce"Barka da dare yaya" murmushin shima ya mayar mata ya ce"yayan Mamah" dariya ta yi ya kalli Imara ya ce"Barka da dare baƙuwa" sunkuyar da kanta ta yi cikin sanyin murya ta ce"ina yini" lumshe idanu Khalil ya yi ya ce"lafiya klao, beuaty" shiru Imara tayi, Umaima ta ja hannunta suka bar wajen. Zaune suka sami Jadda tana bawa Nana labari, tana ganinsu ta kalli Imara ta ce
"Shine nace ki tsaya kika tafi ko?, Ko furar tawa ce bakya so?, Yarinya ba abun mutuwa zan saka miki ba" murmushi Imara ta yi ta ce"alwala naje nayi Jadda" jinjina kai tayi ta ce"to har naji daɗi, zauna maza na zuba miki" zama Imara ta yi akan carpet tana kallon su. Haɗe rai Nana ta yi kamar zata yi kuka tana kallon Jadda ta gama zubawa Imara furar ta miƙa mata, amsa Imara tayi tana murmushi ta ce"nagode Jadda"
A hankali ta fara shan furar tana lumshe idanunta saboda daÉ—in ta, Umaima ce ta kalli Jadda ta ce"Granny nifa?" wani banzan kallo Jadda ta yi mata ta ce"waye zai baki, Allah na tuba, ai nafaÉ—a miki wannan da kike gani ta babban gidan nan ce daman shi na ajiyewa" murmushi Umaima ta yi ta ce"to wane ya ce miki yaya zai sha?"
"Ubanki ne ya faÉ—a min Æ´ar nema"
Tashi Umaima ta yi ta ce"Allah ya huci zuciyarki, Allah yaso muma Abbiey yana siyo mana yogurt kuma ba za ki sha ba" riƙe haɓa Jadda ta yi ta ce"iyeeee, to uwarki ita kika yi wa ba ni ba" ko kallonta Umaima ba ta yi ba ta haye sama da sauri. Taɓe baki Nana ta yi ta ce"ai shikenan Jadda tun da kin fifita wata akan jikarki" girgiza kai Jadda ta yi ta ce"ke ba'a haka, baƙuwa ce shiyasa, kuma kina ji aka ce mijinta ne ya saketa gashi marainiya ce ai kinga akwai samun lada cikin riƙon maraya" a fusace Nana ta ce"to nan gidan ai bai yi kamada gidan yan gudun hijira ba, ko kuma gidan zawarawa, dan batada iyaye ai ba haka ke nufin batada dangi ba, ni banason takura wlh" hannunta Jadda ta kama ta ce"ke ba'a haka, ki sauya hali" tashi Nanah ta yi ta bar parlon kamar zata tashi sama. Imara dake saurarensu tun ɗazu ta sunkuyar da kanta, tabbas haka ne dan batada iyaye ba haka ke nufin batada dangi ba. Amma saidai batasan su wanene dangin nata ba, da wannan tunanin ta ajiye cup ɗin furar ta miƙe zata bar wajen.
"Ina kuma za ki je baki shanye ba yarinya?"
Gudun kada Jadda taga hawayenta yasa ta ƙi juyowa cikin rawar murya ta ce"na...naƙoshi Jadda" kafin Jadda ta buɗe bakinta Mamah ta fito daga kitchen tana kallonta ta ce"yawwa daughter je ki kitchen akwai tray na abincin Abaan ki kai masa" to kawai Imara ta ce ta shiga kitchen ta ɗauko tray ɗin ta hau sama.
A corridor ɗin ɗakunan nasu ta ganshi yana ƙoƙarin rufe ɗakinsa, kallo ɗaya ta yi masa ta juya zata bar wajen.
"Imara!"
Ta ji Khalil ya kira sunanta, ba tare da ta juyo ba ta ce
"na'am"
Ƙarasowa gabanta yayi ya zuba hannayensa a aljihu yana kallonta ya ce "ina za ki je?" kanta a ƙasa ta ce
"Mamah ce ta aikeni"
Kallon agogon hannunsa ya yi sai kuma ya ce"okay tom je ki, karna tsayar dake" kamar jira Imara take ta bar wajen da sauri, tana zuwa ta tura ƙofar ɗakin nasa ta shiga, da idanu Khalil ya bita sai kuma ya juya ya sauka ƙasa.
Zaune ta hangeshi kan kujera yana danna system ɗin sa wacce koda yaushe ba'a raba shi da ita. Sallama ta yi sannan ta ƙarasa ta ajiye tray ɗin a gabansa ta tashi zata fita.
"Wane ya baki izinin fita?"
Da sauri ta juyo tana kallonsa taga har sannan danna system ɗinsa yake, a hankali ta dawo ta tsuguna daga can gefe, tana goge hawayen dake zuba akan fuskarta. Saida ya kammala abin da yake sannan ya rufe system ɗin ya ɗago ya kalleta, ƙura mata idanu ya yi sai kuma ya ce"ɗaukon ruwa a fridge" tashi ta yi ta buɗe fridge ɗin ta ɗauko ruwan wanda ya yi sanyi sosai sannan ta ɗauko glass cup. Dawowa ta yi ta miƙa masa har sannan kanta yana ƙasa, karɓa ya yi, sannan ya buɗe ruwan ya zuba a cup ɗin, ga mamakinta sai taga ya miƙo mata, kallonsa tayi sai kuma ta karɓi ruwan ta kafa kai ta shanye tas, miƙa masa cup ɗin ta yi ya sake zuba mata, nan ma ta amsa ta shanye sai kuma ta shiga sauke ajiyar zuciya. Saida yaga ta nutsu sosai sannan ya kalleta ya ce
"Zo nan"
Hannunsa ta ga ya miƙo mata, ta ɗora nata akai ta miƙe tsaye ta zauna gefensa inda ya nuna mata. Numfasawa ya yi sai kuma ya ce
"Me aka yi miki?"
Shassheƙar kuka tafara ya girgiza kansa ya ce"kuka na ce kiyimin dama?" cikin kuka ta ce"dan Allah Inason na tafi" waro idanunsa ya yi a kanta sai kuma jingina da kujerar har sannan yana kallonta ya ce"ki je ina?"
"Jigawa"
"Wajen wa?"
Ya faÉ—a a takaice, shiru Imara ta yi dan tabbas babu wanda zata je wajensa a Jigawa tunda babu wanda ta sani, jin ba ta ce komai ba yasa ya ce"I'm talking to you"
"Kawai zan koma gidan mu da zama, banason nan"
"Ko?"
Jin yanda ya yi maganar a hasale yasa ta kalleshi taga ya haɗe rai, sunkuyar da kanta ta yi ta ce"nan ai ba gidan zawarawa bane, Inason na tafi na nemo dangina, zan zauna a cikin su koda kuwa basa ƙaunata, bazan taɓa ƙorafi ba,k kuma..." Kasa cigabawa ta yi saboda kukan da ya ci ƙarfinta. Shiru Abaan y yi na ɗan lokaci sai kuma ya ce
"Ki shirya gobe za'a kai ki makaranta, nd kiyi concentrating akan karatun ki, banda wasa okay?"
Baki buÉ—e Imara ta kalleshi sai kuma ta ce"wace makaranta?"
"Za ku je skyline University, ke da Nana"
Da sauri ta ɗago ta kalleshi sai kuma ta girgiza kanta ta ce" dan Allah banaso, dan Allah, kayi haƙuri, banason karatun"
"Ji kika yi na tambayeki kina so ko bakya so?, did I asked you?"
Fashewa ta yi da kuka ta tashi ta zauna a ƙasa tana kuka, shiru Abaan ya yi mata ya shiga danna wayarsa, saida ta yi mai isarta sannan bacci ɓarawo ya ɗauketa a wajen. Saida ya gama abin da yake gabansa sannan ya ɗago jin ta yi shiru. Gani ya yi ta yi bacci a wajen, girgiza kansa ya yi sai kuma ya yi murmushi har saida haƙoransa suka fito. Tashi ya yi ya ɗauketa kamar baby ya fita da ita daga ɗakin, ɗakinta ya kai ta ya kwantar da ita ya yi mata addu'a sannan ya ƙaro gudun AC ɗin ya juya ya fita.
Wani zazzafan numfashi Khalil ya sauke lokacin da yaga Abaan ya fito daga É—akin, zuciyarsa a cunkushe ya juya ya koma É—akinsa ya kashe fitila.
# *IMARA 💋*
# *Bestnovel*
# *Heart touching 💔*
# *Nanameera*
# *2025*.
*IMARA 💋💋*
33&34.
08106608363
Mikiya writers asso...
Washegari da wuri Mamah ta shigo ɗakinta, zaune ta sameta gefen gado tana ninke kayan da Abaan ya siya mata jiya. Tana ganin Mamah ta tsuguna ta gaisheta, fuska a sake Mamah ta amsa ta zauna gefenta ta ce"inyee kayan sun yi miki kyau?" gyaɗa mata kai tayi kanta a ƙasa. Murmushi Mamah ta yi ta ce"shikenan ajiye wannan aikin, ki tashi ki shirya za'a tafi kai ki school" da sauri Imara ta kalleta sai kuma ta tuna da abin da Abaan ya ce mata jiya.
"Mamah ni banason school É—in dan Allah"
Waro idanu ta yi ta ce"meyasa?, bakison ki zama babbar mace?, karatu shine gatanki Imara" buÉ—e baki ta yi zata yi magana Mamah ta dakatar da ita ta ce
"Banason sake jin wannan maganar a bakin ki, ba kece kika ce kina son zama lauya dan ki gano su wane suka kashe iyayenki ba?, saboda haka karatu ya zamar miki dole, maza je ki shirya kinji"
Imara bata sake cewa komai ba, ta tashi ta shige toilet tana tafiya cikin sanyin jiki. Ajiyar zuciya Mamah ta sauke sannan ta kwashe duk kayan ta zuba a wardrobe ta juya ta fita. Bayan mintuna goma ta fito, ajiyar zuciya ta sauke ganin Mamah batanan, shiryawa ta fara, duk da har cikin ranta batasan zuwa makarantar amma ba zata iya musu da Mamah. Tana cikin rolling veil ɗin ta Umaima ta buɗe ɗakin ta shigo. Sanye take cikin wata rigar atampa Holland coffee mai manyan zane, ta yafa veil babba akanta, kallon Imara ta yi sai kuma ta saki murmushi. Umaima kyakkyawa ce irin sosai ɗin nan, da ka ganta kasan suna da jiɓi da wata ƙabilar wacce bata hausawa ba, amma duk da kyanta Nana ta fita, ita kawai rashin kirki ne fal a cikinta.
"Imara!"
Murmushi Imara ta yi ta ce"Aunty Umaima" waro idanu Umaima ta yi ta ce"wace Aunty?, banaso, ba ki girmeni ba?" Kwaɓe fuska Imara ta yi ta ce"a yaushe na girmeki dan Allah?" Yanda ta yi maganar kamar za tayi kuka yasa Umaima tuntsirewa da dariya, ta ce "shikenan, cry cry baby, tashi mu je mu yi breakfast za'a tafi school" ɗan yatsine fuska tayi sai kuma ta ce"ke wace makarantar kike?"
"Maryam Abaca nake zuwa, ina karantar computer science"
"Nima nafison wacce kike zuwa"
Imara tafaɗa kamar za ta yi kuka, dafata Umaima ta yi ta ce"no makarantar ku tafi tamu Imara, nima kawai dan can nakeso shiyasa, ki je makaranta kuma ki yi karatu da kyau, ban da wasa, banda kula kulen ƙawaye. Karatu ya kai ki, karatu kawai za ki yi, dan Allah kar a samu matsala dake kinji"
Sosai Imara ta ji daÉ—in furucin Umaima, hakan yasa ta yi murmushi ta ce"Tom in sha Allah, zan yi yadda kika ce" jan kumatunta Umaima ta yi ta ce"yawwa beauty, tashi muje maza" ta shi ta yi suka fice daga É—akin.
A dinning area suka sami kowa na gidan banda Jadda da Abaan, wanda daman wajen ba gurin zamansu bane. Murmushi Mamah ta yi ganin yanda suka fito a nutse ta ce"yawwa ku yi sauri ku gama" É—aya bayan É—aya Imara ta gaisheda duk mutanen falon, Khalil kam ya kasa É—auke idanunsa daga kanta, kallo É—aya ta yi masa ta É—auke kanta ta gaishe shi, cikin sakin fuska ya amsa ta zauna. Abbiey ne ya kalleta ya ce"Imara kina son makarantar dai?" murmushi ta yi ta ce"Eh Abbiey" jinjina kai ya yi ya ce"Masha Allah, to ki yi karatu da kyau kinji, duk abin da baki gane ba sai ki tambayi Nana tun da ajin ku É—aya, itama this year ta shiga" Tom kawai ta ce sannan ta fara cin abincin ta.
Ƙamshin turarensa ne ya gauraye falon, juyawa suka yi suka kalleshi banda Imara wacce take cin abincinta a nutse, cikin sakin fuska ya gaisar da iyayen nasa sannan ƙannen nasa suka gaishe shi. Da idanu Umaima ta bi Imara ganin kowa ya gaishe shi a wajen banda ita, girgiza kai ta yi ba tare da ta ce komai ba ta ja kujera ta tashi, hand bag ɗinta ta ɗauka tana kallonsu ta ce"nidai na tafi kar nayi late, Imara sai kin dawo" ɗaga mata hannu Imara ta yi tana murmushi. Kai tsaye apartment ɗin Jadda ya nufa, dan babu ranar banza da zai fita daga gidan ba tare da sun gaisa ba. Tana gama ci ta tashi, Mamah ta kalleta ta ce
"Maza ki je mota Imara, kar yazo yana jiranki"
Da sauri ta tashi ta fice daga falon, tashi Nana ta yi ta fice ita ma. A compound ɗin gidan ta hangeta tsaye jikin wata flower ta yi shiru, wani mugun kallo ta watsa mata sai kuma ta ƙarasa gabanta. Veil ɗinta ta ja yasa Imara ta juyo, ta kalleta sai kuma ta yi murmushi
"Nana"
"Riƙe sunanki bana buƙata, Inason na sanar dake wani abu ne, kar ki ga za'a kai ki makarantar da nake ki yi tunanin ke kin kai matsayina, koda wasa kar ki kuskura ki nuna kin sanni a makaranta, idan ba haka ba wlh sai na wulaƙantaki a gaban mutane. Ke ba yar uwata ba ce, babu abin da ya haɗani dake!"
"Nana"
Da sauri ta juya sai kuma ta yi murmushi ta ce"Aunty Jidda" ƙarasowa Jidda tayi tana sanye da wata Abaya maroon colour ta sanye wani glass mai manyan idanu, hannunta riƙe da car key ɗin ta.
"Lafiya?, wacece wannan?"
Ta faɗa tana kallon Imara, taɓe baki Nana ta yi ta ce"wai Yaya ne ya tsinceta shine ya kawota" wani kallo Jidda ta yiwa Imara sai kuma ta ce
"Ke baki iya gaida mutane ba?"
Cikin sanyin murya ta ce"ina yini?"
"Bansani ba, look kin san wace ni?, kinsan gidansu wane wannan?, kinsan wane ne mai gidan nan?, behave ur self, ki kama kanki, nan ba gidan matsiyata bane, kuma ki fita a harkar Abaan kin ji ko?"
GyaÉ—a mata kai Imara ta yi, Jidda ta ja wani uban tsaki ta ce
"Tsintacciya kawai!"
Runtse idanu Imara ta yi, ta sake jingina da flower gudun kada ta faÉ—i. Murmushi Nana tayi jin ta ci mata mutunci ta ce"Aunty ki yi dropping É—ina mana" okay Jidda ta ce sannan ta yi gaba, Nana ta bita da sauri.
Suna barin wajen ta tsuguna a ƙasa ta fashe da kuka kamar ranta zai fita.
"Kee"
Abaan ya faɗa yana tsaye a kanta, ƙin ɗago kanta tayi saida ya maimaita sau uku sannan ta ɗago ta kalleshi da idanunta wanda suka yi jajur, girgiza kansa ya yi ya ce"tashi anan wajen" tashi tsaye tayi har sannan kuma shassheƙar kuka take. Kallon veil ɗin jikinta ya yi sai kuma ya ce"da wannan za ki fita?" kukanta kawai take bata ce masa komai ba, ganin kamar ba za tayi magana ba yasa kawai ya ja hannunta suka bar wajen. Bayan ya sun fara tafiya ya kalleta yaga har sannan kukan take ba tada alamar yin shiru. Bai ce mata komai ba ya cigaba da driving ɗinsa a nutse, a wani boutique ya yi parking ya fita, not too long ya dawo hannunsa riƙe da wata leda babba. Har suka ƙarasa makarantar ba tayi shiru ba, saida ya yi parking sannan ya kashe motar ya juyo ya kalleta ya ce
"Ba ki da niyyar jin shiru ne?"
Kamar wanda ya tunzurata haka ta sake fashewa da kuka, ta rufe fuskarta da hannayenta. Numfasawa ya yi sai kuma ya ce a hankali
"Imara!"
Banza ta yi masa ta cigaba da kukanta, hannunta ya kama ya riƙe cikin nasa ya ce"ya isa faɗa min meya faru?, me aka yi miki?, ke dawa?uhm?" cikin shassheƙar kuka ta ce
"Ni banason makarantar, Jigawa nakeson zuwa, ni gida zan tafi" waro idanu ya yi sai kuma ya sanya hannunsa ya zare hannayenta daga fuskarta yana kallonta ya ce"wani abun aka sake miki?, shikenan zan kai ki Jigawan, amma not today kinji" ɗan buɗe idanunta ta yi ta kalleshi sai kuma ta turo baki ta ce"to ni banason zama a gidan, ka maidani garinmu, bazan zauna anan ba Allah" murmushi ya yi ya ce"to naji, amma yanzu ki fara zuwa school, ko kin manta alƙawarin da kika yiwa wani?, kin ce za ki yi karatu ki biya shi kuɗin da ya ranto miki, ba ke kika faɗa ba?" kwaɓe fuska ta yi sai kuma ta ce"ai to ya tafi ya barni, koda na gansa ma bazan kula shi ba, kuma ba zai gane ni ba" kallonta kawai ya yi sai kuma ya ce"duk da haka, amma ai alƙawari kika ɗaukar masa, kuma kinsan alƙawari kayane, sannan wane ya ce miki ba zai dawo ba?"
"Ni ce nafaÉ—a saboda banason ganin shi"
Girgiza kai ya yi ya ce"anyway, sauka muje" buɗe ƙofar tayi ya ce
"Wait"
Juyowa ta yi tana kallonsa ya buɗe ledar gefensa ya ɗauko hijab ya miƙa mata. Kallonsa ta yi sai kuma ta kalli hijabin ta buɗe, babba ne sosai dan zai rufe mata har ƙafafunta. Turo baki ta yi ta ce"ni wannan ai ya yi min girma" bai ce mata komai ba ya sauka daga motar hakan yasa itama dole ta sauko bayan ta zura hijabin, tafiya ya fara yi tana bin bayansa sai turo baki take tana jan hijabin.
***Saida aka kai ta aji sannan ya bar makaranta. Zaune ta hangi Nana ita da ƙawayenta wanda kana ganinsu kaga ya'yan manya. Wani desk ta gani babu kowa a kai ta ƙarasa ta zauna ba tare da ta kalli kowa ba. Tana nan zaune har wani lecture ya shigo, bayan ya gama yi musu karatu ya kalleta cikin harshen turanci ya ce "sabuwa ce ke?" Gyaɗa masa kai ta yi ya ce"bakya magana ne?" kamar za ta yi kuka ta ce"Eh"
"What's ur name?"
"Imara Ahmad"
Da sauri Nana ta juyo ta kalleta sai kuma ta taɓe baki. Murmushi Sir Jawad ya yi ya ce"wow, nice name" dan murmushi ta yi sannan ya juya ya fita.
***Wani kallo Jidda ta yi musu sai kuma ta taɓe baki ta ce " nifa dama yarinyar bata taɓa burgeni ba, amma yanzu da naji Abaan ya kawota gidan, naji tsanar da nake mata ta nunku, kuma wlh sai na koreta daga gidan!"
Murmushi Majida ta yi ta ce"ke kam mene abun ɗaga hankali?, an fa saka ranar auranki dashi, kuma ke ɗin zaɓin iyayenku ce, damuwa da kishi ba naki bane?"
"Ke ai banza ce Shiyasa"
Cewar Amrish tana kallonta, kwafa Jidda tayi kawai ta miƙe ta ɗauki jakarta ta ce"ni dai na tafi gida, tun an gama lecture sai gobe kuma" daga haka ta fice daga ajin dan batason cigaba da maganar.
***Wajejen Ƙarfe 4 suka tashi daga school, Nana ce ta fara fitowa suna hira da ƙawayenta. Tana ganin driver ya zo ɗaukansu ta kalli ƙawarta Maryam ta ce"yawwa dear sai gobe an zo ɗaukata" ɗaga mata hannu ta yi sannan ta bar wajen, Imara na ganin ta yi wajen motar ta biyo bayanta tana tafe da takardu a hannu, Nana na kallonta ta shige motar ta sauke glass tana kallon drivern ta ce " muje" kasancewar umarninta drivern ke ji yasa ya tada motar Ba tare da ya kalli Imara wacce ke tsaye ba. Da idanu kawai Imara ta bisu har suka fice daga makaranta, shiru ta yi hawaye na kawowa idanunta. Rashin sanin yanda zata yi ya sanya ta fara tafiya toward direction ɗin fita daga makaranta. Saida ta zo gate sannan ta zubawa titi idanu, akwai abin hawa dayawa a wajen, saidai batasan inda zata je ba, dan ko sunar unguwar bata sani ba, gashi babu ko sisi a hannunta. Wannan tunanin ya sanya Imara fashewa da kuka ta maƙale jikin gate ɗin makarantar, kasancewar babu ruwan kowa da wani yasa babu wanda ya je inda take bare ya tambayeta abin da ya dameta. Tunawa ta yi da takardar hannunta wacce aka bata a office ɗin director, tayi sauri ta buɗe tana duba inda aka sanya address,
"No 106. Nassarawa G.R.A"
Shine sunan da ta gani a rubuce, da sauri ta ƙarasa wajen wani mai saida man fetur da ta gani cikin sanyin murya ta yi sallama. Amsawa ya yi ta ce"dan Allah Baba ina ne Nassarawa G.R.A?" shiru ya yi sai kuma ya ce "nan ma dai Nassarawa ce, amma idan wajen G.R.A kike tambaya to adaidaita za ki samu ki faɗa masa sai ya kai ki". Shiru Imara ta yi sai kuma ta ce"to Baba dan Allah ko zaka aramin kuɗi na hau mota, gobe idan zan zo makaranta sai na kawo maka" waro idanu ya yi ya ce"yarinyar kin ganni nan nima fafutuka nake na samu abin da zan je na bawa iyalina, banida kuɗin da zan ara miki, amma za ki iya tsaida mai napep idan ya kai ki unguwar sai ki shiga gida ki karɓo" to kawai ta ce sannan ta bar wajen, titi ta tsallaka ta tsaida adaidaita kamar yanda ya ce mata sannan suka tafi.
Wani haɗaɗɗen hadari ne ya haɗo, lokaci ɗaya gari ya yi wani irin jaa, sosai Imara ta tsorata ta shiga kwaɓe fuska dan idan akwai abin da ta tsana to ruwan sama ne. Yayyafi aka fara da ƙarfi, tsayawa mai adaidaitan ya yi ya ce
"Wai ba'a zo ba ne?"
Cikin rawar murya ta ce"ni bansani ba, bansan gidan ba"
Wani tsaki ya ja ya ce"sauka to, ni juyawa zan yi" tsoro ya bata yasa ta sauka, cikin kuka ta ce"to ai sai mun je gidan zan baka kuɗin" wani mugun kallo ya watsa mata ya ce"lallaima kin raina ni, kinsan da bakida ko sisi kika hawo min mota?" Girgiza kai kawai ta shiga yi jikinta na rawa saboda sanyin daya fara yi mata yawa. Tsaki kawai ya ja sannan ya juya ya shiga adaidaitar ya bar ta a wajen. Wani sabon tsoro ne ya kama Imara, ta fashe da kuka ta tsuguna a wajen ta dunƙule jikinta tana kuka.
***Umaima ce ta shigo ɗakin tana kallonta ta ce"ki je inji Mamah?" Nana dake danna wayarta ta ɗago ta ce"okay". A hankali ta shiga takowa falon tana kallonsu sai kuma ta ƙarasa inda Mamah ke zaune ta ce"Mama gani"
"Ina Imara to?, Umaima je ki kirata"
Okay Umaima ta ce sannan ta koma saman, not too long ta dawo ta ce"Mamah ai batanan, kamar ma bata dawo ba fa"
"What?" Abbiey ya faɗa yana sake kallon Umaima, Mamah ce ta kalli Nanah ta ce"ke ba tare kuka dawo ba?, ko ta fita ne?" murya ƙasa ƙasa ta ce"ni ba tare muka dawo ba Mamah, ni kaɗai driver ya ɗauko"
Rufe bakinta ya yi daidai da sakkowar Abaan ya kalleta cikin wata kakkausar murya ya ce"me kika ce?, acan kika barta kenan?" kuka ta fara yi ta shiga girgiza kanta. Waje Abaan ya yi ba tareda ya sake kallon kowa ba, wani wawan mari Mamah ta sakar mata, sosai ta gigice ta shiga kuka tana riƙe kuncinta. Murmushi Jidda dake zaune gefen Jadda tayi tana addu'ar Allah yasa kar a ganta.
# *IMARA 💋*
# *Bestnovel*
# *Nanameera*
# *2025*.
*IMARA 💋💋*
35&36.
08106608363.
Mikiya writers asso...
Kai tsaye makarantar su ya nufa, har sannan kuma ruwa ake sosai. Shiga makarantar ya yi har office ɗin director saidai bai same shi ba, dan ya fita, shiru Abaan ya yi sai kuma ya fito daga gate ɗin makarantar. Mai saida man fetur ya gani ya ƙarasa wajensa ya yi sallama cike da girmamawa ya ce
"Baba dan Allah ba kaga wata yarinya ba?, yar fara haka"
Shiru ya yi sai kuma ya ce "to ina yawan ganin fararen yara suna fitowa daga makarantar nan, amma da zan ga koda hotonta zan iya shaidata"
Wayarsa ya ciro ya nuna masa wani hoton Imara wanda batasan ma an dauke shi ba. Saurin jinjina kai ya yi ya ce "Eh tabbas naganta. Yarinyar ta zo take tambayata hanyar da za ta yi ta kai ta Nassarawa G.R.A to na ce dai ta samu me Napep ya kai ta, kuma ina ganinta ta hau Napep" shiru Abaan ya yi sai kuma ya yi masa sallama ya koma motarsa. Indai har ta shiga motar zuwa Nassarawa to tabbas tana cikin unguwar kenan.
***Banda kuka babu abin da Nana ke yi ta takure waje guda, kallonta Mamah ta yi ta ce"za ki gane bakida wayo, saboda rashin hankali ki tawo ki barta acan bayan kinsan yarinyar ba yar nan ba ce. Duk abun da ya sameta ai mune a ciki tunda baƙuwarmu ce"
"A'a Mamah maybe fa ko ganin yarinyar ne ba ta yi ba, kuma kinga an tashi daga makaranta ai mutum so yake ya dawo gida, ko Nana?"
Da sauri Nana ta É—aga kai tana kallon Jidda ta ce"A'a Aunty Jidda ba haka bane, na ganta fa, na ce mata ta taso mu tafi ta yimin banza, sau uku ina kiran sunanta ko kallona ba ta yi ba saboda lokacin tana tsaye da wani É—an ajin mu, daman ko a aji bata nuna ta sanni ba, shiyasa kawai na tawo na barta"
Ta ƙarashe maganar tana kuka, cikeda masifa Jidda ta ce"ni daman nasan wlh akwai saka hannun ta, saboda tun da naga yarinyar naga tanada rawar kai" tsaki Mamah ta yi ta ce"ba sai ki kira waya ki faɗa ba, ai idan aka yi mata magana za ta tawo ko?" Tashi Jadda ta yi ta kama hannun Nana tana cewa
"Karki wani ce za ki yiwa yarinya masifa, tun da ita waccen ce taga tafi ƙaunar zama a makaranta. Ke mu je ciki" daga haka ta ja Nana suka bar parlon, shidai Abbiey shiru ya yi bai ce komai ba yana kallonsu. Umaima kuwa girgiza kanta ta yi dan ta tabbatar Nana ƙarya take, babu yanda za'a yi Imara ta ƙi yarda ta dawo gida, tunda bata da inda ya fi nan.
***Wani burki ya ja ganin ya kusa karo da wata mota, ya yi tsaki sannan ya sake kunna motar, ƙin tashi ta yi ya gwada har sau uku taki koda motsi. Sauka ya yi lokacin ruwan ya daina zuba sai yayyafi, tayar motar ya kalla yaga ta yi faci ya ja tsaki. Kasancewar ya kusa gida yasa ya fara tafiya yana kalle kallen hanya ko zai hangota. Can gefe ya hangeta a tsugune fuskarta a rufe, babu ko haufi ya ƙarasa inda take ya dafata, a razane ta ɗago tana wani irin numfashi. Tsungunawa ya yi a gabanta ya shiga girgiza ta, faɗawa tayi jikinsa tana wata iriyar karkarwa, rungumeta ya yi tsam a jikinsa ya shiga shafa kanta cikin cool voice yake faɗin
"Sorry dear, I'm here, nutsu kinji"
Ko kaÉ—an Imara ba ta jin abin da yake cewa, dan gabaÉ—aya hankalinta baya jikinta. Tashi ya yi da ita a jikinsa ya yi mata É—aukan jarirai, bata da nauyi ko kaÉ—an hakan yasa ya fara tafiya toward direction É—in gidan.
Har sannan suna zaune a parlon babu wanda ya tashi, da sauri Mamah ta ƙarasa inda yake tana kallonsa ta ce"lafiya?, meya sameta?" bai ce mata komai ba ya shige ciki da ita, ajiyar zuciya Mamah ta sauke tana dafe ƙirjinta, murmushi Umaima ta yi sai kuma ta shige ciki da gudu itama. Jidda da baƙin ciki ya isheta taji ƙirjinta ya fara yi mata nauyi ta yi saurin fita daga apartment ɗin, da idanu Abbiey ya bita sai kuma ya ce
"Alhamdulillahi"
Murmushin jin daÉ—i Mamah ta yi ta ce"har naji daÉ—i wlh" jinjina kai kawai ya yi sannan ya tashi ya bar parlon. Shi kuwa oga Khalil wani irin abu ne ya zo ya tokare masa zuciya, idan ya buÉ—e idanunsa babu abin da yake gani sai Imara kwance a jikin Abaan, takaici yasa ya bar falon without looking at anybody.
***Fitowarsa kenan daga wanka ya kalli inda take a kwance, har sannan bacci take, numfasawa ya yi sannan ya ƙarasa gaban mirror ya shiga gyara jikinsa. Saida ya shirya tsaf cikin wasu kananan kaya, riga armless milk colour sai wanda cargon 3-quater baƙi, gashin kansa yasha gyara sai sheƙi yake, ya feshe jikinsa da turaren roja. Fita ya yi daga ɗakin ya zauna a parlon yana kallon Al-jazeera. Yana nan zaune har lokacin magrib ya ƙarato, kasancewar ruwan ya sake dawowa yasa basu fita masallaci ba kowa ya gabatar da sallah a gida.
A hankali ta shiga buɗe idanunta tana kallon inda take kwance, tashi zaune ta yi tana jin jikinta na wani irin ciwo, ga kuma zazzaɓi wanda har sannan bai saketa ba. A hankali take sauke numfashi saboda yanda ƙirjinta yake a cure, tuna abin da ya faru ta yi sai kuma ta fashe da kuka, wanda hakan ya yi daidai da shigowarsa. Kallo ɗaya ya yi mata ya ƙarasa inda take ya kama hannunta ya zare drip ɗin, bai kalleta ba ya juya zai fita.
"Ni ka mayar dani gida, wlh bazan sake zama anan gidan ba, banaso, bazan sake zuwa makarantar ba!"
Juyowa ya yi ya watsa mata wani shegen kallo wanda ya sanya ta sunkuyar da kanta ya juya ya fice ba tare da ya ce mata komai ba, sake rushewa tayi da wani sabon kukan na shareta da ya yi ta kwanta akan gadon tana burgima.
Sai wajen ƙarfe 8:30pm sannan ya dawo ɗakin, lokacin ta yi shiru sai kalle kalle take a kwance, zama ya yi gefen gadon ya kalleta ya ce"ke tashi anan" tashi zaune ta yi ta tana kallonsa, cikin whiskey voice ya ce
"Koda wasa kar na sake jin kin ce wai ba za ki je makaranta ba, ko ke baki son makaranta, dole ne ki je makaranta, dole ne kiyi karatu, kuma dole ne ki zauna a gidan nan. Sannan irin haka banason ta sake faruwa ki tabbata kun dawo tare kullum, idan ita tanada baki ke bakida shi ne!?"
Yanda yake maganar babu wasa ya sanya ta sunkuyar da kanta tana hawaye kawai. Turo ƙofar ta yi ta shigo tana sunkuyar da kanta, zama ta yi a ƙasa ya kalleta ya ce
"Khadijah!"
Cikin rawar murya ta ce "na'am Yaya"
"Nasan abin da kika faɗa ba shine abin da ya faru ba, kece kika tawo ki ka barta, koda ban je na tambaya ba nasan abin da za ki iya aikatawa, ita ɗin ki ɗauketa matsayin ƴar uwarki kuma ƙawarki, ba zaku shige shekaru ɗaya ba saboda haka banason jin tashin hankali, duk ranar da irin haka ya sake faruwa ko kuma kika yi mata gori zan tabbatar da cewa na hukuntaki kamar yanda na faɗa miki. Saboda haka ku zauna lafiya, ku je makaranta tare ku dawo tare, tashin hankali ba naku bane, banason faɗa banason baƙar magana kin ji ko?" Cikin rawar murya ta ce
"In sha Allah bazan sake ba, Imara dan Allah kiyi haƙuri" ta faɗa tana kallonta, shiru Imara tayi tana kallonta ita ma
"Ba ki ji abin da ta ce ba?"
Murya can ƙasa ta ce"na haƙura, kema ki yi haƙuri" tashi Nana tayi ta zo ta rungumeta, murmushi suka yi a tare ya kallesu ys ya ce "ku tashi ku je" jan hannunta Nana ta yi suka fice daga apartment ɗin nasa. Akan idanun Khalil suka fito daga ɗakin, kwafa kawai ya yi sannan ya bar wajen. Ɗakin Nana suka shiga, ita dai Imara sai bin ta take da kallo, ganin ta tsaya yasa Nana ta ce"ki zauna mana, bari na kawo mana abinci" a gefen gadonta Imara ta zauna ita kuma ta fice daga ɗakin.
***Ɗago kanta ta yi tana share mata hawayen ta ce"Jidda, ki daina wannan kukan, kinsan dai ni a rayuwa banason naga abin da zai saka ki kuka, in dai Abaan ne ki daina damun kan ki" cikin shassheƙar kuka ta ce"wlh Mommy banason ganin yarinyar nan, ni kawai so nake na daina ganinta. Ko kuma Abaan ya daina ganinta, ko dai ta bar gidan ko kuma ni da Abaan mu bar gidan, kawai a dawo da maganar saka ranar auren nan dan Allah Mommy, ki faɗawa Abbiey, nagaji da jiransa, dan Allah Mommy wlh idan ba haka ba za'a samu matsala, zan iya kamuwa da ciwon zuciya" saurin rufe mata baki ta yi ta ce"kar na sake jin kin fadi irin wannan maganar, ki saka a ranki kamar an yi auren ki da Abaan an gama. Za ki aure shi nan da ɗan lokaci wanda ko ke ba kiyi tunani ba"
Goge hawayen ta shiga yi ta ce"Nagode Mommy, nasan duk abin da nakeso za ki yimin" shafa kanta ta yi ta ce"zan yi komai saboda ke gudaliya ta"
Washegari da wuri suka shirya driver ya ɗaukesu, tare duk suka tafi aka fara ajiye su sannan aka ƙarasa da Umaima, yau a waje ɗaya suka zauna saɓanin ji da suka raba wajen zama. Kasancewar duk suna da kokari yasa suka iya karattunka su na ranar ƙarfe 4 suka fito daga lecture kamar jiya. Suna tafiya a second floor ya hangesu, ƙarasowa ya yi suka gaisheshi, murmushi ya yi ya ce"Imara ko?, ya kike ya gida?" cikin sakin fuska ta ce"Alhamdulillah sir" jinjina kai ya yi ya ce"ba dai gida za ki tafi ba?" gyaɗa masa kai tayi kawai ya ce"to mu je sai nayi dropping naku" kallon Nana tayi sai kuma ta girgiza kanta ta ce"a'a driver ya zo ɗaukar mu yana ƙasa, Thank you" ɗan murmushi ya yi ya ce"okay tom sai gobe" sallama suka yi masa sannan suka cigaba da tafiya. Saida suka sauka ƙasa Nana ta kalleta ta ce"wato daga zuwan ki makaranta har kin yi saurayi ko?, sai na faɗawa Uma" kwaɓe fuska Imara tayi tana kallonta ta ce"mene haka dan Allah, kina gani fa malami ne, wane ya ce miki cewa ya yi yana sona?" Tuntsirewa da dariya Nana ta yi ta ce"ai idan kaga kare na shinshinar takalmi to ɗauka zai yi, wlh ko kaffara bazan yi ba sonki yake, kinsan yanda yake ignoring mutane kuwa, taɓ" turo baki Imara tayi ta ce"to nidai babu ruwana, dan ni ba yar iska ba ce, karatu nazo yi ba soyyaya ba" dafata Nana ta yi ta ce"kin ga Malama lokacin abu a yi shi, idan mun je gida ki cewa Yaya ko Abbiey a siya miki waya saboda assignment, kinga sai ku dinga gaisawa ko?" kallonta Imara kawai tayi sai kuma ta shige mota ba tare da ta bata amsa ba.
***Driver na yin parking ta buɗe motar ta fito tana riƙe da takardun ta, a ƙofar entrance ɗin gidan ya ganta tana ƙoƙarin shiga
"Imara"
Juyowa ta yi sai kuma ta ƙara inda yake zaune ta sunkuya ta gaida shi, murmushi Khalil ya yi ya ce"an dawo?" gyaɗa masa kai ta yi ya ce"sannu, fatan dai kina ƙoƙari?" gyaɗa masa kai tayi tana murmushi, daidai nan Nana ta ƙaraso wajen ta kalleshi ta ce"yawwa yaya dan Allah ka siya mata waya, ana bada assignment kuma batada ita" murmushi ya yi ya ce"to shikenan kuje ku huta, idan anyi magrib sai muje shopping right?" Tsalle Nana ta shiga yi ta ce"yawwa shiyasa nake sonka" ta janye hannun Imara suka shiga gidan.
Mamah ce zaune a parlon sai Jadda tana faman aikin bada labari, tana ganinsu ta ce"an dawo?" murmushi Nana ta yi ta ce"kuma yunwa muke ji Mamah"
"To acici ke wannan yarinya wanda ya aureki ya gamu da wahala, ba zaki bar masa abinci ya huta ba"
Kallon Jadda ta yi sai kuma ta murguɗa mata baki ta ce"to ai naga Abbiey ne dai ya siyo abincin" sakar baki Jadda tayi sai kuma ta ce"Muhammadu Rasulullahi, au gori za ki yimin, to ai ko shi uban naki da ban haifeshi ba bazai samu dukiyar da har kike taƙama da ita ba" ɗaga kafada Nana tayi tana tafiya ta ce"ai ko baki haifeshi ba wata zata haifeshi" kwafa Jadda tayi ta ce"za ki zo har nan ki sameni" .
Kallon Imara tayi wacce ke tsaye ta ce"yawwa Æ´ar albarka je ki É—akina ki daukon wata roba a kusada gadona ki zo na baki abin daÉ—i" to Imara ta ce sannan tayi apartment É—in Jaddan, Murmushi kawai Mamah tayi tana binsu da kallo.
Around 7pm Umaima ta shigo tana kallon su ta ce "naga kun yi shiri ina za ku je?" Nana dake rolling mayafi ta ce "unguwa"
"Unguwa kuma?"
Umaima ta maimaita.
"Eh Yaya Khalil ne ya ce mu shirya zai kai mu shopping"
Turo ƙofar ɗakin ya yi ya shirya cikin wata shadda gezner blue colour sai zuba ƙamshi yake. Kallonsu ya yi ya ce"kun gama?"
"Eh Yaya mun gama"
Kallonsa Umaima ta yi ta ce"okay su kaɗai za ka kai shopping ɗin kenan?" rankwashinta ya yi ya ce"sai na ce miki ki shirya" murmushi tayi sai kuma ta fita daga ɗakin da sauri dan itama ta shiryo. Kallon Imara ya yi wacce take zaune gefen gadon, ba wata kwalliya ta yi ba dan atampa ce a jikinta ta sanya hijabi milk colour har ƙasa, murmushi ya yi sai kuma ya juya ya bar ɗakin.
A compound ɗin gidan suka sameshi yana tsaye jikin motarsa, ƙarasawa suka yi Ita dai Imara a hankali take tafiya, murmushi ya yi ya ce"wannan hijabin fa Imara?" kallon jikinta tayi sai kuma ta sunkuyar da kanta. Murmushi Umaima ta yi ta ce"Yaya ai kasan hijabin yafi mata kyau" jinjina kansa ya yi ya ce "to muje", gaban motar ya buɗe mata ta kalleshi sai kuma ta shiga a hankali. Shiga baya sukayi sannan shima ya zagaya ya shiga sannan suka bar gidan. Glasses ɗin idanunsa ya zare ya tashi daga saman benan ya juya ya koma ɗakinsa.
# *IMARA 💋*
# *Bestnovel*
# *Nanameera*
# *2025*.*IMARA 💋💋*
37&38.
08106608363.
Mikiya writers asso...
Shopping sosai suka yi, kowa sai É—aukar abin da yake so yake, bayan sun kammala ya biya sannan suka baro wajen. Wani shago na saida wayoyi ya tsaya ya yi parking yana kallonta ya ce"mu je ko?" gyaÉ—a masa kai kawai tayi sannan ta sauka daga motar. Biyo bayansu Nana ta yi ita kuwa Umaima ta yi zamanta a mota tana danna wayarta, wayar iphone 13pro max ya siya mata sannan suka bar wajen. Basu dawo gida ba sai wajen 9:45pm, babu kowa a parlon sai tv dake faman aiki, kallonsu ya yi ya ce"oya dare ya yi aje a kwanta" murmushi Umaima ta yi ta ce"mun gode Yaya" harararta ya yi sannan ya shige ciki ya bar su a wajen, Imara na ganin ya bar wajen ta zare hijabin jikinta. Kallonta Nana ta yi ta ce"muje muyi sallar isha'i sai mu kunna wayar muga, kinga yanzu koda ya tambayeki numbern waya kinada ita"
"Waye zai tambayeta?"
Kallon Umaima tayi sai kuma ta ce"idan aka tambayeta a school fa" okay ta ce sannan ta É—auki ledarta ta bar parlon.
***Washegari suka shirya dan tafiya makaranta, ganin tana ƙoƙarin saka hijabi yasa Nana ta ce"wai kullum hijabi za ki dinga sawa kenan?" gyaɗa mata kai Imara ta yi kawai ta ɗauki jakarta ta fice daga ɗakin. Ta ƙofar ɗakinsa ta zo shigewa, haka kawai ta ji tana son ganinsa, tura ƙofar ɗakin ta yi a hankali ta shige. Babu kowa a parlon sai tashin ƙamshi da alama Mamah ta shigo ta gyara masa, yogurt ta gani akan table ta ƙarasa ta ɗauka ta zauna kan kujera ta ɓalle murfin ta fara sha. Saida ta shanye tas sannan ta yi gyatsa ta miƙe tsaye tana gyara zaman hijabinta
"Kece kika ajiye da kika É—auka?"
A razane ta juyo dan ba tayi tunanin yana wajen ba, turo baki ta yi tana wasada fingers ɗinta ta ce"yunwa nake ji shiyasa" kallonta ya yi sai kuma ya ƙaraso gabanta. Zama ya yi kan kujerar har sannan idanunsa na kanta, sunkuyar da kai Imara ta yi tana kwaɓe fuska.
Wayarsa ya É—auko ya shiga dannawa ba tareda ya sake ce mata komai ba, juyowa ta yi taga ba ita yake kallo ta sunkuya ta É—auki jakarta zata fita.
"Kina fita daga É—akin nan za ki gane bakida wayo"
Kamar za ta yi kuka haka ta dawo ta zauna a ƙasan carpet, wayarta ce ta fara ƙara ya juyo ya kalli jakar tata. Ciro wayar ta yi taga sunan Nana, za ta ɗaga kiran ya karɓe wayar ganin an saka Nana yasa ya ɗaga ya saka a handsfree
"Kina ina ne Imara?, ki fito Yaya Khalil zai yi dropping namu"
Kashe wayar ya yi kawai ya ajiyeta gefensa, kusan 5mins bai ce komai ba ta kalleta murya can ƙasa ta ce
"Na tafi?"
Idan kujerar da Abaan ke kai ta yi magana to tabbas shima ya ce wani abu, ganin haka yasa Imara kifa kanta akan gwuiwarta ta yi shiru tana tunani. Saida yaga dama sannan ya ajiye wayar tasa ya É—ago yana kallonta ya ce
"Wane ya baki izinin fita jiya?, wa kika tambaya?, wane ya baki waya?"
A hankali ta É—ago kanta tana kallonsa ta ce"Cewa ya yi muje ya kaimu, kuma naga duk su Nana sun shirya "
"Ko?"
Sunkuyar da kanta ta yi ganin ya haÉ—e rai. Cikin kakkausar murya ya ce"daga yau duk ranar da wani ko wata zasu je wani wajen kika ce za ki bisu ko a kace ki zo aje dake kika tafi za ki gane bakida wayo!" GyaÉ—a masa kai kawai Imara ta yi ya tashi ya shige bedroom É—insa.
Fitowa ya yi bayan ya sauya kaya zuwa wani yadi mai shara-shara coffee colour ana ganin farar singlet É—in daya sanya a ciki. Kallo É—aya ya yi mata ya É—auki car key É—insa ya fice daga É—akin, biyo bayansa tayi da gudunta.
Babu wanda ta samu a parlon duk kowa ya fita Jadda kuma bata fito zama ba ranar, waje ta yi da sauri lokacin har ya shiga motarsa, ƙarasawa tayi ta buɗe front seat ta zauna, saida ya yi warming motar sannan suka bar gidan. Sun yi nisa sosai ta ji cikinta ya fara murɗawa saboda yunwa, jakarta ta buɗe ta ɗauko biscuit wanda ta siyo jiya ta fara ci, ta gefen idanu ya kalleta sai kuma ya cigaba da tuƙinsa, ga mamakinta sai taga ya yi parking a cikin asibiti. Kallonsa ta yi sai kuma ta langwaɓar da kai tana taunar biscuit ɗinta, sauka ya yi daga motar ya fara tafiya, da idanu kawai ta dinga bin sa har ya ɓacewa ganinta. Saida ta cinye biscuit ɗin tas sannan ta ɗauki ruwa ta sha, sosai taji ta ƙoshi dan daman ita batada yawan cin abinci.
Tana nan zaune har sama da awa ɗaya ba taga ya fito, zuwa lokacin ta gaji da zaman, buɗe motar ta yi ta sakkowa tayi daga motar ta gyara hijabinta. Rufe motar tayi da makulli sannan ta fara tafiya, kasancewar ta gane inda ya kai ta rannan yasa batasha wahala ba, tana zuwa ta tura ƙofar office ɗin, zaune ta hangeshi yana danna system ɗinsa. Ƙarasawa tayi ta zauna kujerar kusa da shi kamar za tayi kuka ta ce
"Na makara fa"
Ganin bai kalleta ba yasa ta tashi ta koma inda yake zaune ta shiga jan rigarsa, sai a sannan ya É—ago ya zuba mata idanu, sunkuyar da nata idanun ta yi dan ba zata jure kallon cikin idanunsa ba.
"Mene kuma?"
Zumɓura baki ta yi ta ce
"Ni na makara, kawai ka bani kuÉ—i na hau napep, ko kuma ka bani key É—in motar na tafi kawai" ta faÉ—a tana yarfe hannu. Girgiza kansa kawai ya yi ya ce"ai kin daina zuwa makaranta"
Waro idanu ta yi ta kalleshi sai kuma ta kwaɓe fuska ta ce"dan Allah ka bari, ni inason na je makaranta, kaji" ture hannunsa ya yi daga jikinsa ya harareta ya ce"karki sake taɓani"
"To meyasa?"
"Ban sani ba"
Yanda ya faɗi maganar ya sanya ta tuntsirewa da dariya tana kallonsa, murmushi Abaan ya yi kawai ya ce"tashi mu je" da sauri ta tashi sai ta kalleshi ta kalli hijabin jikinta, langwaɓar da kai tayi ta ce"ni wannan ya isheni wlh, na cire?"
Girgiza mata kai ya yi yana rufe system ɗin sa, buga ƙafa ta shiga yi tana kallonsa ta ce"to ya isheni ni, zafi nakeji, kowa mayafi yake sakawa fa"
"Wane ya ce miki ke kowa ce?"
Murmushi ta yi ta ce"Eh ni ba kowa ba ce, ni Imara ce yar gatan Allah sai kuma Mamah sai kuma..."
Kallonsa ta yi ya ce"sai kuma me?" Girgiza kia ta yi ta ce"ba komai" taɓe baki ya yi, bai sake magana ba ya fice daga office ɗin,
Ganin inda yake tafiya daban yasa ta ce"ba school É—in zaka kai ni ba?"
"Eh".
Ya faɗa a takaice, turo baki ta yi ta ce"to kayi haƙuri kaji"
Shiru ya yi mata, ta ce"ni banason ana yimin shiru fa, ka ce ka haƙura" banza ya sake yi mata ai kuwa ta fashe da kuka, tsaida motar ya yi yana kallonta ya ce"ko kiyimin shiru ko kuma ranki ya ɓaci" ƙara volume ɗin kukan ta yi ya kalleta ya ce
"Ki bari na ce!"
Banza ta yi masa ita ma, ganin ba zata yi shirin ba yasa ya ce"shikenan ki yi shiru gobe za ki je school ɗin, na haƙura".
Goge idanunta ta yi kai ba zaka ce ita ce wacce ta yi kukan ba, murmushi ta yi ta ce"ni to ka dinga bani kuÉ—in makaranta"
Cigaba da tafiya ya yi yana kallon titi ya ce"me za kiyi da kuÉ—i?"
Washe baki tayi ta ce"tarawa zan dinga yi, har sai sun kai na siya gida na koma" jinjina kai ya yi yana murmushi ya ce"au gida ma za ki siya kenan".
"Eh, babban gida nakeso, harda yan aiki su dinga yimin girki nikuma ina kwance"
Murmushi Abaan ya yi yana jinjina yarinta irin ta IMARA, ganin bai ce komai ba yasa ta ce"ayyah, ai zan bar mai gadi ya buɗe maka idan ka shigo. Saboda Dodo ya taɓa cemin kada na saka Alkhairi da sharri, to ai kaga kaima ka yimin Alkhairi tunda ka kawoni gidan ku kuma ana bani abinci ko?"
Dariya mara sauti ya yi ya ce"Ni za'a barni na shigo kenan?" GyaÉ—a masa kai ta yi ya ce"kenan kina yarda da maganarsa?" Saurin gyaÉ—a kai tayi ta ce"Eh mana, to ai shima yana sona, kuma shine ya kai ni makaranta, inason na ganshi"
"Rannan kuma kika ce bakya son ganinsa"
Turo baki ta yi ta ce"ai idan na ganshi ba magana zan yi masa ba, tunda ya tafi ya barni, kuma Umma ta mutu bai zo ba. Kuma nazo aka aura min Maheer nan ma bai zo ba. Ya barni na sha wahala, kuma gashi Maheer ya sakeni, yanzu kuma babu wanda zai aureni ko?"
Tunda ta fara magana Abaan ke kallonta dan parking motar ma ya yi, hawaye ya gani akan fuskarta ya sanya hannunsa yana goge mata. Da sauri ta kalleshi sai kuma ta kalli hannun nasa, murmushi ya yi ya ce"kika sani ko wani babban dalili ne ya sanya shi ya tafi ya barki?" Girgiza kanta ta yi ta ce"amma ai da ya faÉ—a min, kowa haka yake cemin banida dangi kuma da gaske banida kowa, ni kaÉ—ai ce kawai. Ni nafison na mutu ma wlh "
Zuwa sannan kuka sosai Imara ke yi, jawota jikinsa ya yi ya rungumeta yana shafa kanta. Yana jin tana shassheƙar kuka
"Ki daina kuka kin ji, ba gani nan ba uhn, bazan bari wani abu ya sake samunki ba, ki daina kuka kinji"
GyaÉ—a masa kai ta shiga yi, suna nan zaune a haka har bacci ya É—auketa. ÆŠago fuskarta ya yi yana kallonta sai kuma ya yi murmushi ya ce"cry cry baby".
***Ƙarfe 4:56pm Jadda ta tafi daga apartment ɗin ta tana ƙwalawa Mamah kira, fitowa daga kitchen Mamah tayi tana kallonta ta ce"gani Jadda"
"Maza maza kira min Fadeel a waya, duk inda yake Inason ganinsa yanzu" cikeda damuwa Mamah ta ce"Jadda lafiya dai?"
"Malama banason tambaya kiyi abun da nace miki kawai" da idanu kawai Mamah ta bita sai kuma ta hau sama ta ɗauko wayarta, ringing ɗaya Abbiey ya ɗaga bayan tayi sallama ta sanar dashi saƙon Jadda, sosai ya yi mamaki rashin sanin dalilin kiran yasa ya ce ta ce mata gashi nan. Ala dole ya tashi daga abin da yake driver ya ɗauko shi zuwa gida.
***Zaune ya sameta a falo tayi shiru, zama ya yi gefenta ya ce"Jadda lafiya?"
"Fadeel! Fadeel! Fadeel!, sau nawa na kira ka?"
A mamakance ya ce "sau uku Jadda". Numfasawa ta yi ta ce"to so nake a yi auren yaron nan Abaan da Jidda!, kuma banason auran ya shige wata É—aya, ina fatan za'a aikata abin da nace "
"Aure kuma Jadda?, amma naga yanzu ba shine lokacin daya dace ba ko..."
Dakatar dashi ta yi ta ce"banason jin wata magana da Fadeel, idan har na isa dakai, kai kuma ka isa da Jidda da Abaan to Inason ka shirya maganar aurensu daga nan zuwa ƙarshen wannan watan da muke ciki, idan kuma kai ma zaka wulaƙanta ni ne kamar yanda ɗan uwanka ya yi to shikenan, sai na san haihuwa bata yimin rana ba"
Girgiza kai Abbiey ya yi yana kallonta ya ce"Allah kar ya kawo ranar da za ki umarce ni da yin wani abu na gagara aikatashi Jadda, in sha Allah zan haÉ—a su aure, amma idan Abaan da yawo zan ji ta bakinsa"
"Wane bakin nasa?, kenan sai yanaso zaka aikata, idan ya nuna baya buƙata a haƙura ko?, to bari ka ji banason wani ji ta bakinsa, kai ne ma ɗaurin aurensa saboda haka kawai a ɗaura aure koda yardarsa ko kuma babu"
Wani irin bugu ƙirjin Mamah yake yi, an ya kuwa Jadda lafiya klao take?, tasan me take cewa?, ya za'a yi Abaan ma ya yarda?!, wannan tunanin ya sanya ta fara kiran innalil lahi a cikin ranta.
Ajiyar zuciya Abbiey ya sauke ya ce"shikenan Jadda, yanda kikeso haka za'a yi in sha Allah" jinjina kai tayi daidai lokacin Abaan ya yi sallama ya shigo Imara na biye dashi.
# *IMARA 💋*
# *Bestnovel*
# *JADDA*
# *Nanameera*
# *2025.*
*IMARA 💋💋*
39&40.
08106608363.
Mikiya writers asso...
Ajiyar zuciya Abaan ya sauke yana kallon Abbiey ya ce"Abbiey why?" Girgiza kai ya yi cike da damuwa ya ce"Muhammad abun ne ya fi ƙarfina ka dai san halin kakarka, bansan mene ya sameta ba da har ta yanke irin wannan hukunci, ba zan iya yi maka dole akan auren Jidda ba amma ina tunanin abin da zai je ya dawo. Shiru ya yi yana kallon Abbiey kafin ya miƙe tsaye ya yi hanyar fita daga parlon
"Ka aikata abin da Jadda ta umarceka Abbiey"
Da sauri Abbiey ya juyo ya kalleshi zuwa sannan kuma ya fice daga falon. Ajiyar zuciya ya sauke yana godiya ga Allah domin da Abaan bai yarda da auren nan ba bai san abin da zai ce da Jadda ba.
***Tun da ta shiga ɗaki ta nemi waje ta zauna, haka kawai ta ji ba ta jin daɗi zuciyarta na bugawa da ƙarfi, buɗe ɗakin a kayi ta ɗaga idanun ta kalli Nana wacce ta shigo ɗakin, zama ta yi gefenta tana murmushi ta ce"shine yau ki ka ƙi zuwa makaranta ko?, muna ta jiranki baki fito ba" cikin sanyin murya Imara ta ce"to ai na je wajensa ne kuma shine ya ce ba zan je makarantar ba"
"Wane haka?"
Turo baki ta yi ta ce"wannan mana, babban yayan gidan nan" tuntsirewa da dariya Nana ta yi ta ce"wai Yaya?" Gyaɗa mata kai ta yi, Nana ta ce "lallaima, to Yaya Abaan sunan sa, Babban soja ne da kike ganinsa kuma ba ɗan ƙasar nan bane" taɓe baki Imara ta yi, kamar an tsikareta kuma ta gyara zamanta tana kallon Nana ta ce
"Ki ka ce Soja ne?"
Gyaɗa mata kai Nana ta yi, Imara ta tashi tsaye ta fara tafiya a ɗakin tana murmushi, biyo bayanta Nana ta yi tana kallon ikon Allah, ganin kamar ta samu matsala yasa ta ɗan dafata can ƙasa da murya ta ce
"IMARA"
Juyowa ta yi sai kuma ta rungumeta tana dariya ta ce"wlh ina son shi, shi nakeso ni, ina sonshi sosai wlh, kuma shi zan aura"
A fusace Nana ta ture ta daga jkinta tana yi mata kallon kin yi hauka ta ce"me ki ka ce?, kina cikin hayyacinki kuwa?, Yayan ki ke so?, Yaya Abaan É—in?, kinsan kuwa wane shi?"
ÆŠaga kafaÉ—a Imara tayi irin bai dame ta ba ta ce"ni fa babu ruwana da ko wane shi, jami'in tsaro nakeso na aura kuma gashi na same shi, I'm so lucky wlh"
Nana was speechless, sai bin Imara take da kallo tamkar wata zararriya. Girgiza kanta kawai ta shiga yi dan da alama wasu aljanun sun shiga jikin Imara ba tare da kowa ya sani ba.
***Around 9pm ya shigo hannunsa riƙe da wasu ledoji guda biyu, kai tsaye apartment ɗin Jadda ya shige, zaune ya sameta kan ladduma tana jan tsazbaha, zama ya yi a ƙasa kusa da ita har sai da ta idar sannan ta juyo ta kalleshi, murmushi ya yi ya ce"Jadda" ajiyar zuciya ta sauke ta shafa kansa ta ce"Abaan, sannu ka ji, sannu da ƙoƙari, Allah ya yi maka albarka" lumshe idanunsa ya yi ya ɗora kansa bisa cinyarta, sosai ta ji tausayin sa, a duk san da ya yi mata haka ta gane kewar mahaifiyarsa yake. Shafa kansa ta shiga yi tana karanto masa addu'o'i, tana jin yanda yake sauke numfashi a hankali har bacci ya yi gaba da shi.
Sanye take cikin wata doguwar riga ta atampa, a-shape ta rufe gashin kanta da wani veil ya zubo ta bayanta, a hankali take tafiya fuskarta fal murmushi. Zaune ta sami su Umaima suna cin abinci ta zauna a kusa da Umaima tana kallon Nana wadda ke yi mata wani irin kallo kamar me tsoronta. Dariya Imara ta yi, Umaima ta kalleta ta ce"Lafiya dai Imara?" Nuna mata Nana ta yi wadda ke faman zare ido. Dariya ita ma Umaima ta yi ta ce"lafiya me aka yi mata?" shiru Imara tayi har sannan murmushi take. Harararta Nana ta yi ta ce "ni ki daina kallona" gwalo ta yi mata ta ce"na kalla É—in, ni zo ki ga" a hankali Nana ta taso ta dawo inda take zaune ta zauna ita ma, kallo Umaima ta kunna a wayarta hakan yasa suka fasa aikin suka maida hankalinsu kan kallon da suke. Kiran wayar Umaima a aka yi hakan yasa ta tashi ta bar wajen, murmushi Nana ta yi ta ce"ki ce masa ina nan ina jiransa a Naija" harararta kawai ta yi ta shige kitchen da sauri. Kallon Imara Nana ta yi ta ce
"Wai ke ina wayarki ne?"
Taɓe baki ta yi ta ce"ya kwace min, ni so ma nake na ganshi" harararta Nana ta yi ta ce"wlh ki fita a harkarsa tun kafin ki jawowa kan ki Tom, gwara ma ki cigaba da magana da sir sai ya fi miki, ɗazu ma na ganshi ya shiga apartment ɗin Jadda kuma har yanzu bai fito ba" zumbur Imara ta miƙe ta bar wajen, da idanu kawai Nana ta bita sai kuma ta girgiza kanta.
***Wani ihu Umaima ta saki wanda y saka Nana shiga kitchen É—in da sauri. Tana ganinta ta rungumeta tana dariya ta ce
"Yaya ya dawo, Yaya ya dawo Nana, I'm so happy wlh" ihu suka sake saki a tare daidai nan Mamah ta shigo kitchen É—in, kallonsu ta yi ta ce
"Mene haka?, meke damunku?"
"Mamah Yaya Kamal ne ya dawo daga Uk kinga kuwa dole mu yi murna, yanzu ma zamu fara tunanin abin da zamu yi masa gobe idan ya zo ne"
Numfasawa Mamah ta yi ta ce"to sannun sa da dawowa, amma dare ne wannan ihun ya yi yawa, ku je ku kwanta" to kawai suka ce sannan suka yi hanyar fita.
"Ina Imara ne?"
"Taje apartment É—in Jadda"
Okay Mamah ta ce sannan ta cigaba da abin da take.
***A hankali ta tura ƙofar falon ta shiga bakinta ɗauke da sallama, zaune ta hangi Jadda, shi kuma har sannan yana kwance akan cinyarta. Murmushi Jadda ta yi ta ce"au Yarinyar kirki ke ce anan?" gyaɗa mata kai Imara ta yi sannan ta ƙaraso inda take ta zauna tana murmushi ta ce"daman zuwa nayi na gaisheki Jadda"
"Da gaske, kai amma na ji daɗi sosai Yarinya, Allah ya yi miki albarka" murmushi kawai Imara ta yi, Jadda ta ce"kuma ina da wani alkaki da aka yomin, gashi wannan sangartaccen yaron ya zo ya wani kwanta min a jiki" dariya Imara ta yi ta ce"to ki tashe shi Jadda man" girgiza kai Jadda ta yi ta ce"a'a fa, ai ba'a tashin sa yana bacci tun yana yaro" jinjina kai Imara ta yi sai kuma ta leƙa fuskarsa, haɗe rai ta ga ya yi ta ɗago ta kalli Jadda ta ce
"Wlh Jadda yana ji ba bacci yake ba, kinga ya motsa ko?"
Da sauri Jadda ta kalli inda Abaan yake sai kuma ta ce"ke bacci man yake, ina jin saukar numfashinsa É—azu"
"N rantse Jadda ya tashi, bari kiga" tana faɗin haka ta tashi ta koma daidai inda fuskarsa take ta kwalla ƙara. Da sauri Abaan ya tashi zaune ya shiga bin ta da idanu. Tuntsirewa ta yi da dariya tana kallon Jadda ta ce"kin gani ko, wlh ya tashi daga baccin fa" kallonta Jadda ta yi sai kuma ta kalle shi ta ce"kaga ƙaton banza, kai yanzu da ba baccin gaske ka ke ba ka bi ka taushe min ƴar ragowar cinyar tawa" langwaɓar da kai ya yi kamar ƙaramin yaro ya ce"Jadda bacci fa nake ji"
"Sai ka tashi ka je É—akin ka ka kwanta ai. Amma da ka bi ka danne ni, ga nauyi kamar me Allah na tuba. Yarinyar kirki na gode miki, zauna anan na kawo miki abin daÉ—i"
Gyaɗa mata kai Imara ta yi tana murmushi, kwafa Abaan ya yi ya kalleta kawai bai ce komai ba, wata robar dambun kaza Jadda ta kawo mata, ta ajiye a gabanta. Ganin yanda yake ganin robar yasa Jadda ta ce"tashi ki je kitchen ki ɗauko leda ki ɗan sammasa ko kaɗan ne kar mu shiga haƙƙinsa ido guba" kallonsa Imara ta yi taga ya yi murmushi, turo baki ta yi batasan yi wa Jadda musu ya sa kawai ta tashi ta shiga kitchen ɗin. Miƙewa Abaan ya yi ya kalli Jadda ya ce"sai da safe, na tafi" riƙe haɓa ta yi ta ce"au ba zaka ci dambun kazar ba?" Kallon robar ya yi sai luma ya saka hannu ya ɗauke duka ya yi waje, daidai nan Imara ta fito daga kitchen hannunta riƙe da farar leda. Kallon Jadda ta yi ta ce"Jadda ina ya tafi dashi kuma?"
"Bishi duk in da ya yi, karki kuskura ya cinye ya bar ki"
Da gudu Imara ta bi bayansa, saidai bata same shi ko a falo ba, hakan yasa ta haye sama da sauri. Zamewa ta yi, tayi baya zata faɗi ya riƙe ta, ɗagowa tayi ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kanta ta ce "ina yini"
"Lafiya klao Imara, wannan gudun fa?, so ki ke sai kin ji wa kan ki rauni?" Girgiza kai ta yi ta ce"abu na zan amso, bana son ya cinye ina zuwa" daga haka ta shige ta bar Khalil tsaye a wajen. Ƙofar apartment ɗin Abaan ya ga ta shige sai kawai ya ja ya tsaya a wajen yana jiran fitowarta.
***Babu kowa a falon hakan yasa kai tsaye ta shige ɗakinsa, dan ba baƙonta bane, kama ƙugu ta yi ta rike ganin nan ma baya nan, ƙarar zubar ruwan da ta ji a banɗaki ya sanya ta nemi waje ta zauna a gefen gadonsa. Above 10mins kafin Abaan ya fito daga wanka yana sanye da bathrobe, sarai ya ganta sai kawai ya ɗauke kansa ya ƙarasa wardrobe ɗinsa, wasu pyjames White colour ya ɗauko sannan ya dawo gaban dressing mirror ya fara gyara gashin kansa, tana zaune har sai da ya kammala duk wasu abubuwan dake gabansa sannan ya sanya rigarsa. Runtse idanu Imara ta yi ta sanye hannayenta duka biyun ta rufe fuskarta, duk abin da take yana kallonta ta mudubi bai kula ta bar ya kammala nan da nan ɗakin ya ɗauki wani sassayan ƙamshi. Remote ya ɗauka ya ƙaro gudun AC, lumshe idanu Imara ta shiga yi tana jin wani bacci na sanɗarta. Fridge ya buɗe ya ɗauko ruwa ya sha sannan ya dawo ya zauna akan sofar dake ɗakin ba tare da ya kalleta ba, ganin yanda ya shareta ya sa Imara ta taso ta dawo kan kujerar da ya zauna ta zauna itama tana kallonsa ta ce"ka bani dambuna in ji Jadda"
"Mene haka?"
Kwaɓe fuska ta shiga yi tana shirin fashewa da kuka, rangwashinta ya yi akai ya ce"babu kyau mutum zai saka kaya a dinga zama a ɗakin kin ji ko?" Gyaɗa masa kai tayi jin yanda ya riƙe mata kunnenta. Cikin rawar murya ta ce"ni ka bani dambuna na tafi, bacci nake ji" da hannu ya nuna mata inda ya ajiye robar ta tashi da sauri ta ɗauko sannan ta dawo inda yake zaune. Amsa ya yi ya buɗe ya ɗebo da yatsun hannunsa ya miƙo mata, da idanu kawai Imara ta bi shi bai ce mata komai ba ya girgiza kai ya kai bakinsa, lumshe idanunsa ya yi saboda daɗin da dambun ya yi masa. A nutse ya cigaba da cin abin sa ba ta re da ya sake kallonta ba. Ganin yana shirin cinyewa ya sanya ta jawo masa riga hawaye na zuba akan fuskarta ta ce"ka bani na ci to" kallonta ya yi kawai ya sake ɗiba ya kai bakinsa. Fashewa tayi da kuka ya ɗebo ya zuba mata a baki. Tsit Imara ta yi shiru ta shiga tauna naman, sosai ya yi mata daɗi itama, a haka suka cigaba da ci yana bata a baki saida ya rage sauran kaɗan ta yi saurin karɓe robar tana taunar naman ta ce
"Ni ka bar min wannan, ai ni ce ƙarama"
Harararta ya yi ya karɓe robar ya ce"tashi ki tafi to" kallonsa ta yi kamar ta faɗa masa abin da ke zuciyarta sai kuma kawai ta tashi tayi hanyar waje. Murmushi ya yi ganin ba ta sake magana ba ya miƙe tsaye, taku ɗaya ya ƙaraso inda take ya juyo da fuskarta yana kallonta, sunkuyar da kanta ta yi ya ɗago fuskar yana murmushi ya ce "tafiya babu sallama?"
# *IMARA 💋*
# *Bestnovel*
# *Nanameera*
# *2025**IMARA 💋💋**IMARA 💋💋*
41&42.
08106608363
Mikiya writers asso...
Girgiza kanta ta yi, sai kuma ta janye fuskarta a hankali ta ce"sai da safe" hannunta ya kama ya ɗora mata robar naman ya ce"Allah ya tashemu lafiya, karki manta ki yi addu'a" gyaɗa masa kai Imara ta yi sannan ta fice daga ɗakin. Ajiyar zuciya Abaan ya sauke ya koma ya cigaba da aikin gabansa. Ko kaɗan ba ta lura da Khalil ba ta tura ƙofar ɗakinta ta shiga tana wasa da robar hannunta. A gefen gado ta ajiye robar sannan ta shige toilet dan watsa ruwa, tana fitowa ta sanya sleeping dress ta ɗaure gashin kanta sannan ta kwanta akan gadon ta lumshe idanunta.
***A hankali ta juya da niyyar komawa ɗaya ɓangaren, rufar da ta gani ya sanya ta s buɗe idanunta, a firgice ta tashi zaune tana kallon mutumin dake tsaye a kanta. Baya ta fara yi tana girgiza kanta gabaɗaya jikinta rawa yake, ganin yanda ta tsora ta ya sanya Khalil kunna hasken ɗakin, kallonsa ta yi sai kuma ta saki ajiyar zuciya ta dafe ƙirjinta. Sai da ya ga ta nutsu sosai sannan ya ce"ki yi haƙuri na tsorata ki" Imara ba ta ce masa komai ba ta sauka daga kan gadon ta ɗauko ruwa a fridge ta ɓalle murfin, sai da ta kusa shanyewa sannan ta ajiye ta dawo ta zauna can nesa dashi. Sun ɗauki mintuna babu wanda ya ce wani abu, Khalil na son aiwatar da abin da ya kawo shi sai dai yana fargabar yanda Imara za ta karɓi al'amarin. Turo baki ta yi dan bacci ta ke ji gashi ba za ta iya ce masa ya bar ɗakin ba, can ƙasa da murya ta ce
"Yaya Khalil dare ya yi sosai fa, kuma gobe da safe ina da makaranta"
Zazzafan numfashi Khalil ya sauke kafin ya juyo ya kalleta ya ce"Na sani Imara, yanzu ne lokacin da ya fi dacewa na zo inda ki ke shiyasa" ƙura masa idanu Imara ta yi tana mamakin furucin bakinsa. Numfasawa ya yi sai kuma ya ce
"Imara tun ranar da idanuna suka yi tozali dake ki ka shiga raina, ki yi haƙuri da abin da zan faɗa amma har cikin zuciyata ina ƙaunarki, nasan ba lallai ne na zama wanda ya fara faɗa miki haka ba, amma ina da tabbacin zan yi nasara akan su duka. Ina da niyyar mallakar ki matsayin matata ta sunna, ina fatan ba za ki juyamin baya ba Imara"
Ras! Haka Imara ta ji gabanta ya faɗi, tashin hankali ƙarara ya bayyana akan fuskarta, cikin rawar murya ta fara cewa
"Yaya amma ni ai kamar ƙanwarka nake, kuma ma kaga kai saurayi ne, ni kuma na taɓa aure. Ina jin tsoro, dan Allah a bar maganar nan"
Ɗan murmushi Khalil ya yi ya miƙe tsaye ya ce"sanin haka yasa na fallasa miki asirin zuciyata, nasan ba za ki ƙini ba, ina da wannan tabbacin Imara. Zan baki lokaci ki yi tunani, amma ina fatan samun babban matsayi cikin zuciyarki." Da idanu kawai Imara ta bi shi har ya fice daga ɗakin, wani irin gumi ta ji yana tsatstsafo mata, duk da Ac dake kunne a ɗakin, me Khalil ya ke nufi?, idan har ya furta yana son ta a gaban mutane ba za ta iya bijirewa ba kodan hallacin da mutane gidan suka yi mata, haka kuma ba za ta iya haƙura da soyyayar Abaan ba!. Da wannan tunanin ta koma ta kwanta, sai dai duk yanda ta yi da bacci ya ƙi zuwar mata, daga ƙarshe kawai ta tashi ta shige toilet ta ɗauro alwala, sallar nafila ta hau yi, kafin daga bisani ta zauna tana roƙon Allah ya zaɓa mata abin da ya fi Alkhairi a rayuwarta.
***Haka Imara ta cigaba da rayuwa a cikin gidan, duk yanda Khalil yake son magana da ita haka take avoiding É—insa, domin bata fatan abin da zai haÉ—a su. A haka har suka fara exams ta first semester a makaranta.
Zaune suke cikin wani ɗan ƙaramin restaurant dake cikin makarantar, da idanu Nana ta bi Imara wadda ta zuba tagumi tun shigowar su. Har aka kawo musu abin da suka yi order Imara ba ta sani ba, tsaki Nana ta yi sannan ta ɗan daki table ɗin gabansu, a ɗan firgice Imara ta kalleta sai kuma ta shiga murje idanunta. Harararta Nana ta yi ta ce
"Wannan tunanin babu abin da zai haifar miki sai wahala Malama, it's better for you to stop it"
Numfasawa Imara ta yi ta ja lemonta ta sha sannan ta ce"ni ce miki na yi tunani nake?" taɓe baki Nana ta yi ta ce"a'a ban sani ba!" Murmushi Imara ta yi ta dafata ta ce"haba ƙawar I'm sorry, zan daina in sha Allah" murmushin ita ma Nana ta yi ta ce"ohyaa mu yi saboda akwai paper a gabanmu" gyaɗa kai Imara ta yi sannan ta cigaba da shan lemonta.
Ƙarfe 4:20pm suka fito daga paper, dafe kai Imara ta yi ta ce"wayyo uwata, nagaji wlh" dariya Nana ta yi ta ce"za ma ki yi bayani ne Hajiya, gobe ma akwai paper" zaro idanu Imara ta yi ta ce"Allah gamu gareka"
Taɓo ta Nana ta yi da hannu, maida idanunta ta yi ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kanta, ƙarasowa gabansu ya yi ya kalleta ya ce"Imara ya exams ɗin?" cikin sakin fuska ta ce"wlh sir exams Alhamdulillah, kuna bamu wuta" dariya Ya yi ya ce"ku yi haƙuri, a ƙarasa a haka" girgiza kai Nana ta yi ta ce"kai sir, ai shikenan, da dai an tausaya mana" dariya ya ce "Khadijah rigima, kawai ku yi karatu, nasan bamu da matsala daku" murmushi su ka yi ya ce"tafiya za ku yi?" gyaɗa masa kai Imara ta yi ya ce"to mu je na sauke ku?" Girgiza kai ta yi ta ce" ai za'a zo a ɗaukemu, ka ga idan muka tafi za'a neme mu a gida" jinjina kai ya yi ya ce"haka ne kuma, to sai goben ku" ɗaga masa hannu su kayi ya juya ya bar wajen. Jan hannun Nana ta yi ta ce" mu je ni nagaji"
Waro idanu Nana ta yi ta ce"kai, kinga Yaya Khalil ne ya zo ɗaukar mu fa" da sauri Imara ta kalli motar, shiru ta yi suka ƙarasa, fitowa ya yi yana kallonsu ya ce"yan makaranta" dariya Nana ta yi ta ce"kai yaya, akwai wahala school wlh" dariya ya yi yana kallon Imara ya ce"beauty wai haka?" gyaɗa masa kai ta yi tana murmushi, Khalil ya ce"to ai sai ku dage ku yi passing, idan kun gama exams za mu je yawo" tsalle Nana tayi ta ce"shiyasa nake mugun son ka Yaya" dariya kawai ya yi sannan suka shiga mota suka tafi. Sai da ya biya dasu mall ya siya musu chocolate sannan suka tafi gida. Yana gama parking Imara ta sauka da sauri ta shige gida gudun ka da ya yi kiranta, da idanu kawai Khalil ya bita sai kuma ya yi murmushi. Turus ta yi ganin akwatina na kaya a zube a parlon, Jadda da wasu tsofaffi sai buɗe kayan suke.
"Jadda wannan kayan fa?"
Nana da ta shigo ta tambaya, washe baki Jadda ta yi ta ce"yawwa yaran kirki ku zo ku ga, irin wannan abun arzikin nakeson kuma a kawo muku" cikin ɗaurewar kai Imara ke kallon Jadda dan kwata-kwata ba ta fahimci abin da take nufi. Shiru Nana ta yi sai kuma ta ce"ko kayan Aunty Jidda ne?" Gyaɗa mata kai Jadda ta yi ta ce"Eh, ɗazu aka shigo dasu, wannan yaron ya yi kaya ba ƙarya"
"Bikin wa za'a yi?"
Imara ta tambaya tana kallon Nana. "Yaya Abaan man, Aunty Jidda zai aura, gashi har an kawo kayan lefe"
Wani irin abu ne ya tokarewa Imara a ƙirji, ta kalli Nana sai kuma ta sake kallon tulin akwatinan, girgiza kanta ta yi muryarta na rawa ta ce"Jad... Jadda wai haka?"
"Eh mana, ashe baki sani ba, Aure zai yi kuma kwa huta, yaro ya girme a gida ya zama magidanci babu aure" tamkar wadda aka zarewa laka haka Imara ta ji jikinta, ba ta sake cewa komai ba ta shige ciki tana tafiya tana haÉ—a hanya. Da idanu Nana ta bi ta sai kuma ta girgiza kai tana tausaya mata domin tasan abin da ke cikin zuciyarta.
***Imara na shiga ɗaki ta nemi waje a ƙasa ta yi zaman dirshin, kuka takeson yi amma ko kaɗan babu wani ruwan hawaye da ya rage a idanunta, gabaɗaya ƙwaƙwalwarta ta tunkushe waje ɗaya, ajiyar zuciya ta shiga saukewa tana maimaita furucin Jadda. Daman aure zai yi ya barta?, ba ta ko samu damar sanar dashi sirrin zuciyarta ba shine zai yi aure ya bar ta?. Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke sai kuma hawaye ya biyo kuncinta, ta shiga rera kuka a hankali.
***Da gudu Jidda ta shigo kitchen ɗin ta na zuwa ta rungume Mommy tana dariya ta ce "Mommy gaskiya Nagode sosai, an kawo kayan aurena fa, kuma yaya Adeel ya ce wai sati uku za'a saka. Gaskiya nayi farin ciki, wannan malamin aikinsa yana yi" girgiza kai Mommy ta yi tana dariya ta ce"da ai kina ɗauka ba zan iya ba, sai gashi ta cikin ruwan sanyi mun buraɗa tsohuwar yanda ita kuma za ta tada musu hankali, kinga yanzu kin zama surukar babban gida" tuntsirewa da dariya Jidda ta yi ta ce"wlh kam naga aiki, yanzu dai kina ji Mommy ba wannan ba, ni banason zaman wannan yarinyar a gidan nan please, idan mun koma wajen mutumin nan zan yi masa bayani. Haka kawai na ji hankali bai kwanta da zamanta cikin gidan nan ba wlh" taɓe baki ta yi tana wanke kayan miya ta ce"to ke mene na ki na damuwa da ita?, ke da za ki bar mata gidan?, ai sai ta yi ta zama a cikinsa, ke da za ki tafi gidan aurenki?" Kwaɓe fuska ta yi ta ce"ni a'a wlh Mommy, na riga da nayi alƙawarin sai na fitar da ita daga gidan nan, saboda haka Allah hankalina ba zai taɓa kwanciya ba muddin ina ganinta. Kuma Jadda sai wani jan ta take a jiki" murmushi Mommy ta yi ta ce"shikenan, idan mun koma sai a yi masa maganar ta, ko kuma ki bari mu gama da maganar aurenki, saboda dai kinsan me ya faru, dole ne kiyi abin da ya dace" jinjina kai tayi ta ce" Haka ne Mommy, sannan kuma ni sai an dawo da hankalin Yaya Abaan kai na, dan ko magana fa ba ya wani yimin, idan na kula shi kuma sai ya dinga amsawa sama-sama, inason ya daina yarda da maganar kowa sai ta wa, ya daina ganin ko wace mace a gabansa sai Jidda" murmushi Mommy ta yi ta ce"ke a tunaninki zamu bar shi haka ne?, ai kawai ki zuba min idanu, ni nasan abubuwan da zan aikata" rungumeta ta sake yi tana murmushi ta ce"shiyasa nake ƙara ƙaunar ki Mommy" murmushi ta yi ta ce"nima haka Jiddona, duk wani abu da zai sanyaki farin ciki shine abin da nake mudarin yi, zan yi komai domin farin cikin ki".
(Ba dai-dai bane a rayuwa uwa ta ce za ta yi wa ɗiyar ta duk wani abu da take so koda kuwa hakan ya saɓawa shari'a ko kuma Addini, Iyaye mata a dinga kiyayewa, farantawa yaro abu ne mai kyau, amma ban da saɓawa mahalicci wajen faranta ran ɗa. Allah ya sa mu dace)
Washegari ko karyawa Imara ba ta yi ba ta fice, dan ko Nana ba ta jira ba. Tana zuwa ta samu waje ta zauna ta zuba uban tagumi, koda Nana ta fito ba ta sameta ba ta yi tunanin ko ta wuce hakan yasa ita ma ta tafi. Zaune ta hangeta ta ɗora hannu akan fuska da alama ta yi nisa a cikin tunanin da ta ke yi, ƙarasawa Nana ta yi ta zauna gefenta ta zuba mata idanu. Above 5mins amma Imara ba ta san Nana ta zauna inda take ba, taɓa ta ta yi, ta ɗago a firgice tana kallonta.
"Imara kinga yanda ki ka rame kuwa?, daga jiya zuwa yau, kar ki saka damuwa a ran ki ki zo ki cuci rayuwarki akan abin da ba za ki samu ba, Yaya Abaan ya riga da ya yi miki nisa Imara. Ka da ki manta Aunty Jidda ita ce wacce zai aura, ina da tabbacin ba za ta taɓa bari ya aure ki ba. Kuma kema kin san da haka, saboda haka ki maida hankalin ki akan karatun ki, shine kawai abin da zai taimaki rayuwar ki, kina da buƙatar ki yi karatu Imara, domin shine kawai gatanki"
Goge hawayen fuskarta Imara ta yi tana kallon Nana ta ce"Nagode Nana, amma ba zan iya cire shi a raina ba. Amma kamar yanda kika faɗa zan maida hankalina akan abin da yake rayuwata, tunanin wani abu bana mara gata irina ba ne, tunanin wani zai so ni ba abu bane mai kyau. In sha Allah zan cire shi daga raina, zan yi ƙoƙarin ganin na gina rayuwata"
Dafa ta Nana ta yi ta ce"ni burina bai shige na ga kin kammala karatun ki lafiya ba" murmushi ta yi ta ce"in sha Allah zan yi haka Nana".
***Tun daga wannan ranar Imara take gujewa kanta duk wani abu da zai haɗata da Abaan, da zarar ta dawo daga makaranta take shigewa ɗaki ba za ta sake fitowa ba sai gobe idan zata tafi makaranta. Ko da Mamah ta yi cigiyarta sai ta ce karatune ya rike ta a haka har suka kammala jarrabawar aka basu hutu, lokacin kuma sauran sati ɗaya bikin Abaan da Jidda. Zaune take kan kujera ta zubawa tv idanu duk da ba fahimtar abin da ake cewa take ba. Ƙamshin turarensa ta ji nan da nan bugun zuciyarta ya sauya, da idanu Mamah ta kalleshi ganin kamar ba shi ba ta ce"Son lafiyarka kuwa?" girgiza kai ya yi ya ce"ki bada abinci a kawomin Mamah" sosai ta yi mamaki ganin yau da bakinsa ya ce a kawo masa abinci, tashi ta yi ta shiga kitchen ta haɗa masa tray na abincin sannan ta fito parlon. Zaune ta iske Imara har sannan bata ko motsa ba
"IMARA"
*IMARA💋💋*
43&44.
08106608363
Mikiya writers asso...
***A hankali ta tura ƙofar ɗakin ta shiga bakinta ɗauke da sallama. Babu kowa a parlon sai ƙamshin turare mai daɗi dake tashi, lumshe idanu ta yi kafin ta ƙarasa ta ajiye tray ɗin akan ɗan centre tables ɗin dake tsakiyar parlon, zama ta yi kan kujera tana tunanin rabonta da shigowa ɗakin, a ƙalla ta kai wajen sati uku ko magana ba ta haɗata da Abaan ba. Tura ƙofar da a ka yi ya sanya ta ɗaga idanunta tana kallonta, da wani irin kallo ta shiga bin Imara kafin ta ƙaraso gabanta, taɓe baki ta yi fuska babu walwala ta ce"ke uban me ki ke yi a ɗakin nan?" kallonta Imara ta yi sai kuma ta ɗauke kanta ba ta re da ta ce komai ba, baki buɗe Jidda ta kalleta sai kuma ta yi kwafa ta ce"kee!, har kina jin ke wata ce da ina yi miki magana za ki yimin shiru?, wane uban ki a ƙasar nan?, dame ki ke taƙama?"
"Duk abin da za ki yi, ki yi shi a kaina, amma kar ki kuskura ki sake sako ubana a ciki, idan kuma ki ka sake wannan gangancin wlh sai na yi miki abin da ba ki taɓa tunani ba!"
Imara ta faɗa tana huci, mamaki ya hana Jidda magana, har ita wannan yarinyar za ta tsaya tana faɗawa magana, kwafa ta yi sai kuma ta ɗaga hannunta da niyyar marinta, riƙe hannun ta ji an yi, ta juya tana kallonsa. Sanye yake cikin wata t-shirt black colour sai wando 3-quater blue a jikinsa, gashin kansa sai wani sheƙi yake. Cikin rawar murya ta ce"dan Allah ka ci ka min hannuna, na rantse da Allah sai na hukunta ta" kallonta kawai ya yi sai kuma ya saki hannunta ya ƙarasa kan kujera ya zauna ya shiga danna wayarsa, ban da huci babu abin da Jidda ke yi, ko da yau ba ta hukunta ta ba, to ta ɗauki alƙawarin yi mata abin da har abada ba za ta taɓa mantawa da ita ba. Ganin Abaan bai ce mata komai ba ya sanya ta juya ta fice daga ɗakin kamar za ta tashi sama. Da idanu kawai Imara ta bi ta sai da taga ta bar ɗakin sannan ita ma ta juya zata fita.
"Zo nan"
Abin da kawai ta ji ya furta kenan, turo baki ta yi sai kuma ta dawo ta zauna a ƙasan in da yake zaune ta sunkuyar da kanta, sai da ya gama danna wayarsa sannan ya ajiyeta a gefe ya kalleta ya ce"da me ki ke tunani?, kin korar min mata shine kuma kema za ki tafi" fashewa da kuka Imara ta yi ta rufe fuskarta, murmushi kawai Abaan ya yi sannan ya kamo hannunta, janyewa ta yi ya sake riƙeta ya dawo da ita gefensa, hannunsa ya sanya ya ɗago fuskarta ya zuba mata idanu, ɗauke idanunta ta yi tana kallon wani wajen tana hawaye.
"Mene ne?, ke dawa?"
Sake fashewa ta yi da kuka kawai ta rungumeshi, murmushi kawai Abaan ya yi dan ya san abin da take wa, yana jin tana kukanta bai hana ta ba sai da ta yi shiru dan kanta. Ɗago fuskarta ya yi ya kalleta ɗauke kanta ta yi tana tura baki, girgiza kai ya yi ya ce "kin gama kukan?" janye hannunsa ta yi daga fuskarta cike da shagwaɓa ta ce"ni bana kula ka, tafiya zan yi" murmushi ya yi har sai da beauty point ɗin sa suka loma, kafeshi da idanu Imara ta yi, ya ja kumatunta ya ce"meyasa na daina ganin ki?, kina karatu dayawa ko?" Cikin tsiwa ta ce"ni ba zan sake zuwa makarantar ba, na daina zuwa wlh" waro idanunsa ya yi ya ce"saboda me yasa?, idan ba ki je makaranta ba me za ki yi?"
"Nima aure zan yi!"
Ta yi maganar a fusace, dariyar da Abaan ya daɗe bai yi ba ta sanya ya yi, ya kalleta fuskarsa cike da fara'a ya ce"to aure kuma?, wa za ki aura?" Murya can ƙasa ta ce"nima ban sani ba, amma ni aure zan yi, tun da kaima auren ka za ka yi, ni ba zan zauna a gidan nan ba!" Abaan couldn't help it but smile, sake haɗe rai Imara ta yi ta tashi daga jikinsa, jawota ya yi ya zaunar da ita kan cinyarsa yana murmushi ya ce"shikenan, tunda baki son karatu, zan aurar dake, akwai abokina dake neman mata kawai sai na aura masa ke"
"Shima soja ne?"
Imara ta faÉ—a da sauri, girgiza kai Abaan ya yi, ta haÉ—e rai ta ce"to ba zan aure shi ba, nima soja kawai zan aura" murmushi ya yi ya ce"to me yasa sai soja za ki aura?, shi da baya zama a gida "
"Saboda idan wani ya yimin abu zan faÉ—a masa ya rama min, nikuma daman na zama lawyer kaga babu wanda zai dinga yimin abu. Kowa zai dinga jin tsorona"
Tuntsirewa da dariya Abaan ya yi yana jinjina shashanci irin nata, turo baki ta yi kamar za ta yi kuka ta ce"yanzu kai aure za ka yi ko?, kuma wannan Jiddar za ka aura?, ni bana sonta" haɗe rai ya yi ya ce"kar na sake jin kin ce bakya son mutum, ba'a cewa haka" gyaɗa masa kai ta yi kawai ta yi shiru ba ta ce komai ba. Janyeta Abaan ya yi ya tashi ya buɗe food flask ɗin, tuwon shinkafa ne miyar egusi wadda ta ji wadatattun kayan haɗi, serving kansa ya yi sannan ya zauna a ƙasa ya tankwashe ƙafafunsa ya yi bismillah ya fara ci, Imara na nan zaune har ya kammala cin abinci sannan ya tashi ya shige bedroom ɗinsa, da idanu kawai ta bi shi sai kuma ta fashe da kuka, ta sunkuyar da kanta akan kujera. Bayan mintuna ashirin ya fito cikin wata sabuwar shigar, kallonta ya yi ganin yanda ta kifa kanta, bai ce mata komai ba ya juya ya fice daga ɗakin, ya rufe ta ta waje.
***Zaune ya samu Jadda a parlon ita da su Umaima tana basu labari kamar yanda ta saba, Jadda na ganinsa ta washe baki ta fara cewa "ango kasha ƙamshi, ina zuwa haka?" Kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce"idan zan fita sai na faɗa miki inda zani?, ki daina gulma" harararsa ta yi ta ce"ubanka ke gulma bani ba ɗan nema" tuntsirewa da dariya Umaima ta yi tana kallon Jadda ta ce"Jadda Yaya fa zai biya ta wajen siyarda nama"
"Haba?"
Ta faÉ—a tana washe baki, gyaÉ—a mata kai Umaima tayi, ta kalli Abaan wanda ke juya mukullin motarsa ta ce"Allah sarki yaron kirki, Allah ya dawo da kai lafiya, dan Allah idan ka tashi siyomin banason naman nan mai romo, nafison wannan mai dan yaji-yajin wanda zan daÉ—e ina ci"
"Ko?"
Abaan ya faɗa, bai sake kuma bi ta kan Jadda ba ya yi waje abin sa. Yana shirin fita daga gidan shi kuma ya shigo, kallo ɗaya Abaan ya yiwa motar sai kuma ya ɗauke kansa, a compound ɗin gidan ya yi parking ya fito, sanye yake da wani farin yadi mara nauyi, yanayin kwalliyarsa zaka gane akwai arziki a tare dashi duk da kasancewar sa baƙar fata. Fuskarsa kamar gonar audiga haka ya ƙaraso wajen Abaan yana zuwa ya tuntsire da dariya. Tsaki Abaan ya yi ya ce
"Mahaukaci kawai"
Sake tuntsirewa ya yi da dariya ya ce"kaga mutumin, ango kasha ƙamshi, kaga yanda ka ke wani glowing, ko dai har Amaryar ta fara kula da kai ne?" Duka Abaan ya kawo masa ya kauce yana dariya ya ce"ai wlh kai ma kasan wuce nan"
"ÆŠan iska, dallah ni matsa na shige"
Gwalo ya yi masa, yana yin yanda suke wasa da dariya zai tabbatar maka da akwai shaƙuwa mara misaltuwa a tsakaninsu. Girgiza kai Abaan ya yi ya ce"kai baka da hankali shiyasa, ni kaga tafiya ta, dariya ya yi ya jawo hannunsa ya ce"haba Dude mu je tare, ina za ka je na raka ka?" kallonsa kawai Abaan ya yi sai kuma ya shige mota, a ɓangaren mai zaman banza ya zauna. Murmushi kawai Kamal ya yi sannan ya zauna a driver seat, yana kallonsa ya ce"sarautar taka zaka nuna min kenan?, Allah ya so nima dai Babana Sarki ne, ba iya ku kaɗai ku ke da sarauta ba"
Banza Abaan ya yi masa ya shiga danna wayarsa, murmushi kawai Kamal ya yi sannan suka bar gidan.
****Tsaki Amrish ta yi ta ce"amma ke ma ba kida wayo, da ki ka ga tana ɗakin shine za ki yi zuciya ki fito?" fuska a haɗe Jidda ta ce"nasan dalilin daya sanya na fito, ki barni da yarinyar, wlh a cikin ruwan sanyi zan dafa ta, ai idan na nuna ban ji maganar da Abaan ya yimin ba. A gabansa ba zan sake nuna wani abu ba, amma a tsakanina da ita wlh sai na yi mata abin da har abada ba zata manta da wa ce Jidda ba!" Jinjina kai Ta yi ta ce"ai dan ke ce za ki yi maganinta, ke kar ma ki barta ta zauna a gidan nan fa tom!, ko da kin yi aure ki fitar da ita daga gidan nan, saboda ai ko da kin yi aure shi zai dinga zuwa gidan a lokutan da ke bama ki sani ba, kuma wlh duk inda wannan yarinyar take nasan akwai son Abaan a cikin zuciyarta" wani killer smile Jidda ta yi ta ce"ni nasan abin da nake shiryawa, a daren da zan bar gidan nan da sunan aure a daren ita ma zata bar shi wannan alƙawarina ne!"
***Sai bayan magrib sannan ta farka daga baccin daya ɗauketa, tashi ta yi ta sake ƙoƙarin buɗe ƙofar, amma ta sake jin ta a rufe. Hawaye ta fara yi dan gabaɗaya ta gaji da zaman ɗakin, ta juya ta koma ciki, abincin da ya rage ta zuba ta fara ci, tana lumshe idanu dan ba karamin daɗi tuwon ya yi ba, kuma daman gata masoyiyar tuwo. Tana gama ci ta kwashe kayan ta kai kitchen ta wanke sannan ta fito, rasa abin yi ta yi hakan yasa ta shiga gyara ɗakin duk da ba datti ya yi ba, bayan ta kammala gyara parlon ta shiga bedroom ɗin domin shima ta gyara shi. Sakewa gadon bedsheet ta yi sannan ta kunna turare, Zama tayi a kan bedside drawer tana kalle-kalle. Kamar wadda aka tsikara haka ta tashi ta shiga buɗe drawer, takardu ne duk a ciki. Tsaki kawai ta yi sannan ta rufe, tana shirin mayarwa wani envelope ya fado, ɗaukansa ta yi ta buɗe, hotuna ta gani a ciki a kuwa ta gyara zamanta ta shiga buɗe su. Hoton farko wasu yara ne mace da namiji a tsaye, daga gani namijin shine babba domin ya fita tsawo da jiki nesa ba kusa ba. Murmushi ta yi sannan ta sake ciro wani hoton, nan ma hoton yaran ne sai dai wannan karan akwai ƙarin wani babban mutum daga gani kasan mahaifinsu ne, kai daga ganin hoton kasan asalin larabawa ne, sake ware idanunta ta yi dan gani ta yi kamar ta taɓa ganin irin fuskar sai dai ta manta in da ta santa. Ɗaya hoton kuma hoton Abaan ne sanye da kayan sojoji, gefensa kuma wani babban mutum ne shima sanye da irin kayan nasa, da alama gaba yake dashi ko a wajen aiki. Murmushi kawai Imara ta yi dan ba ƙaramin kyau hoton ya yi, haka kawai ta ji hoton ya burgeta, turo ƙofar ɗakin da a kayi ya sanya ta yi saurin mayar da hotunan ba tare da ta kammala kalla ba. Da idanu Abaan ya bita sai kuma ya ƙaraso in da take zaune, zama yayi gefen gadon yana kallonta ya ce"kin gaji ne?" Saurin gyaɗa masa kai ta yi kamar za ta yi kuka ta ce"ni ka buɗe min na fita" ɗan murmushi kawai ya yi sannan ya tashi ya fara cire agogon dake hannunsa yana ƙoƙarin shiga toilet ya ce"ai yau anan za ki kwana!"
# *IMARA 💋💋*
# *Bestnovel*
# *Nanameera*
# *2025*.
*Sauran posting 3 na kammala book 1, and book 2 paid book ne ₦500, wanda suke yin payment kafin na kammala book 1 zasu bada ₦400 a matsayin promo, nan da kwana biyu zan kammala book 1, saboda haka a cigaba da payment na book 2 kafin lokaci ya ƙure, nafison a fara da kowa, a tura kuɗi ta wannan account ɗin 7041901078 Hauwa Adamu lawan opay, sai a turo shaida ta number ta, 08106608363 Nanameera, Nagode.*

45&46
08106608363.
Mikiya writers asso...
Da idanu kawai ta bisa har ya shige toilet ɗin, tashi ta yi ta buɗe drawern ta zari hoton da yake tare da wani ta yi saurin barin ɗakin. Kai tsaye ɗakinta ta shige tana zuwa ta buɗe wardrobe ɗinta ta saka shi can ƙasan kaya sannan ta mayar ta rufe, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta juya ta fita zuwa wajen Jadda. Zaune ta hangesu a parlon suna hira, ƙarasawa ta yi tana kallonsa ta ce"ina yini" murmushi Kamal ya yi ya ce"lafiya klao Imara, ya gida ya shirye-shirye?" "Lpyklao Alhamdulillah" jinjina kai ya yi yana kallon Umaima ya ce"sauran na mu ko?" sunkuyar da kai Umaima ta yi. Murmushi Imara ta yi ta ce"dan kuwa mun ƙagu a zo auren Uma" dariya Kamal ya yi ya ce"ai duk na fi ku ƙaguwa Imara, ni yau zan wa Abbiey magana kawai na bada sadaki a ɗaura yau, sai a haɗe shagalin dana Doctor" rufe baki Imara ta yi tana dariya ta ce"da kuwa mun ji daɗi Yaya" dariya kawai ya yi ta juya ta shige apartment ɗin Jadda".
Tana barin wajen ya kalli Umaima ya ce"ko ya ki ke ce beb?, na haɗa ki da Raheena" haɗe rai ta yi ta ce"ni ba zan aureka ba ai" langwaɓar da kai ya yi kamar yaro ya ce"ayyah yarinyar kirki so ki ke a kai ni asibiti ko?" turo baki ta yi kamar za ta yi kuka ta ce"kai da kana da matar ka har da yarka taɓ!" Dariya Kamal ya yi ya ce"to ai saboda kin yi ƙarama ne shiyasa lokacin ban aure ki ba Uma, da ke zan aura ba Raheena ba" kallonsa ta yi sai kuma ta ɗauke kai tana harararsa.
****Girgiza kai Abbiey ya yi yana kallon Khalil ya ce"amma ka yi magana da ita Khalil?, yarinyar ta amince?, kar a yi abin da ba ta so" numfasawa ya yi ya ce"gaskiya dai bata bani amsa ba Abbiey, duk da dai na faɗa mata" shiru Abbiey ya yi sai kuma ya ce"to ai kaga ni ba zan yanke hukunci akanta ba ko?, beside kuma ba budurwa ba ce yanzu, saboda haka tana da damar zaɓar mijin da take so. Saboda haka ka je ka sami yardarta, idan ya so ko bayan auren Abaan ne sai a yi maganar nata" jinjina kai ya yi ya ce"Tom Abbiey nagode sosai Allah ya ƙara girma" shafa kansa ya yi ya ce"Ameen, Allah ya yi albarka"
****Zaune ta samu Jadda tana cin nama, tana ganin an turo ƙofa ta yi saurin naɗe ledarta, sai da taga Imara ce sannan ta mayar ta ajiye tana washe baki ta ce"au, na yi tunanin wannan zilamammiyar yarinyar ce ashe ke ce" zama ta yi tana murmushi ta ce" ni ce Jadda, Barka da dare" sai da ta kai tsokar nama bakinta sannan ta ce"sannu da zuwa yarinya, ya shirye-shirye?, na ji ɗazu wannan 'ya ta ce wai gobe za'a fara bikin" ɗan murmushi Imara ta yi ta ce"ban ma sani ba Jadda, Allah ya sanya Alkhairi" . Girgiza kai Jadda ta yi ta ce"oh Allah dai ya yarda, wannan aure kamar ba za'a yi shi ba, ai gara ma ya yi auren shima ya huta, duk sa'annin suna da iyali shi ya tsaya ko me yake jira ohho?" Shiru Imara ta yi sai kuma ta ce"to Jadda kuma yana sonta?" Kallonta Jadda ta yi sai kuma ta yi murmushi ta ce"sanda tana yarinya ba'a taɓa ta saboda Abaan, ba ya son yara amma yanda yake kula da yarinyar abin da sai da ya fara bawa kowa mamaki, tun tana ƴar ƙaramarta yake sonta, oh lokacin an ga abu, idan tana kuka Abaan ko zama ba ya yi, idan kuwa suka yi faɗa da Adeel ya daketa to ranar Allah ne kawai zai kwaci Adeel a hannunsa."
Tun da ta fara magana Imara ke kallonta har ta gama, ba ta ce komai ba ta tashi zata fita,
"A'a har kin gama zaman ko naman ba ki ci ba?"
Girgiza kai kawai Imara ta yi sannan ta fice daga É—akin, da idanu kawai Jadda ta bita sai kuma ta ce"oh, kome ke damunta Allah masani"
Ba ta tarar da kowa a parlon ba, haka ita ma bata tsaya ba, kawai ta haye sama kai tsaye kuma ɗakinta ta shiga. Tana zuwa ta faɗa kan gado ta fashe da kuka, ina ma bata tambayi Jadda ba, ina ma ba ta sauka ƙasan ba, kenan Abaan yana son Jidda har haka?, kenan auren soyayya zai yi?. Sake rushewa ta yi da kuka ta dafe kanta, tana nan zaune ta ji an turo ƙofar, da sauri ta kalli ƙofar sai kuma ta shiga goge idanunta. Zama Mamah ta yi gefen gadon tana kallonta ta ce"lafiya ki ke kuka?" can ƙasa da murya ta ce"kaina ne yake ciwo"
"Ciwon kan ki ke wa kuka Imara?, ko da wani abun ya sameki?, nasan bakya ɓoyemin abu ki sanar dani me ya sameki?" Girgiza kai ta yi ta ce"babu komai Mamah kawai ciwo kaina yake, amma yanzu na sha magani" ajiyar zuciya Mamah ta sauke tana murmushi ta ce"Tom Allah ya sawwaƙe, daman wata magana ce nakeson muyi dake Imara" gyara zamanta ta yi tana kallon Mamah ta ce"Tom ina ji" numfasawa ta yi ta fara magana
"Imara daman ina neman wata alfarma ne, kuma sannan ina son na baki shawara, Imara nasan Khalil ya yi magana dake wattanin baya, sai dai har yanzu ba ki ce komai ba, ban sani ba ko kin ji bai miki bane, ko kuma kina gudun faɗawa irin hannun da kika faɗa a da. Ina son na baki shawara a matsayina na mahaiyarki, ki nutsu ki zaɓi mijin aure wanda zai dace da rayuwarki, ki auri mijin marainiya wanda zai kula da ke koda yasan ba kida kowa. Ki auri wanda yake sonki tsakani da Allah wanda ba za ki yi danasanin aurensa ba, nasan halin Khalil, idan har ya furta yana son wani abu to tabbas yana son abun ne, idan har da dama Imara Inason ki yarda da Khalil ki yi aurenki ki cigaba da karatun ki cikin ɗakin ki. Na tabbata ba za ki yi dana sani ba"
Wasu hawayene suka shiga sintiri akan fuskarta, girgiza kai Mamah ta yi ta kama hannunta ta ce"a'a Imara, idan har kinsan akwai wani a zuciyarki ki bar wannan maganar, ba wai dole zan miki ba kin ji" fashewa ta yi da kuka ta shige jikin Mamah, rungumeta Mamah ta yi itama tana hawaye ta shiga shafa kanta. Cikin shassheƙar kuka Imara ta ce"ni babu kowa a zuciyata Mamah, idan ma akwai to na yarda ƙaddara ta raba mu, zan ɗauki duk wata shawara da ki ka bani, sannan zan karɓi Yaya Khalil hannu bibbiyu, na tabbata ba za ki yi abin da zai cutar da ni ba Mamah, ina da wannan yaƙinin, kawai ki dinga yimin addu'a, Allah ya yaye mini damuwata dan Allah Mamah" jinjina kai Mamah ta yi ta ɗago fuskarta tana goge mata hawayen ta ce"in sha Allah Imara, za ki yi farin ciki a rayuwa, komai zai mana tarihi, karki damu kin ji" gyaɗa mata kai ta yi sannan ta sake rungumeta.
Washegari da safe Nana ta shigo É—akin, zaune ta sameta tana kallon hoto, zama ta yi gefenta ta ce"a ina ki ka samu hoton yaya?" murmushi ta yi ta ce" a É—akinsa mana"
"ÆŠakinsa kuma?, me ya kai ki É—akinsa?"
Kallon Nana ta yi ba ta ce komai ba ta tashi ta mayar da hoton inda yake sannan ta dawo ta zauna. Girgiza kai Nana ta yi ta ce"ki tashi mu tafi, kinga gara mu dawo da wuri, anjima za'a yi cocktail" kwanciya Imara ta yi akan gadonta ta ce"ni ba zani ba" baki buɗe Nana ke kallonta sai kuma ta ce"Mamah ce fa ta je mu je, shine za ki ce ba za ki je ba?, ko kuma duk cikin kishin ne?" Banza Imara ta yi mata ta lumshe idanunta kamar me bacci, sai dai ita kaɗai tasan irin ƙunar da zuciyarta ke mata. Nana ba ta sake cewa komai ba gudun kada ranta ya ɓaci ta tashi ta fice daga ɗakin, a corridor ta haɗu da Umaima wadda ke sanye da riga mai mayafi, ganinta ita kaɗai ta yi yasa ta ce"ina Imaran?" Taɓe baki ta yi ta ce"cewa ta yi wai ba za ta je ba"
"Ba za taje ba kuma?, akan me?"
Ɗaga kafaɗa Nana ta yi alamar ba ta sani ba, girgiza kai Umaima ta yi sannan ta koma ɗakin Imara. Kwance ta sameta ta yi ruf da ciki, ƙarasawa ta yi ta zauna gefen gadon ta taɓa
"Imara"
Saurin goge hawayenta ta yi sannan ta tashi zaune tana kallon Umaima ta ce"na'am"
"Mene haka Imara?, ki tashi mu tafi, ko kin fi so mu makara ne?, idan mun je da wuri ai da wuri zamu dawo gida, kinga ai ya fi" dafe kanta ta yi ta ce"ni bana so fa, ku je kawai, ni ba zan je ba" haɗe rai Umaima ta yi za ta yi magana wayar hannunta ta fara ƙara, kallon screen ɗin ta yi sai kuma ta ce"kinga har an fara kiranmu ko?, ki tashi mu tafi mana" girgiza kai Imara ta yi ta ce"na ce miki kawai ku tafi, ni banaso ba zan je ba" . Babu yanda Umaima ba ta yi da ita ba amma ta ce ba za ta je ba, daga ƙarshe ma ta tashi a ta shige toilet. Gajiya Umaima ta yi ta tashi ta fita, tsaye ta hangeshi jikin bene yana danna wayarsa, da sauri ta ƙarasa fuskarta babu walwala ta ce"Yaya" ba tare da ya kalleta ba ya ce"mene ne?"
"Ka yiwa Imara magana, wai ta zo mu je gyaran kai da ƙunshi wai shine ba za ta je ba, tun ɗazu ta ƙi fitowa" ɗago kansa ya yi ya kalleta sai kuma ya ce"call her" da sauri ta koma ɗakin nata. Zaune ta sameta gefen gado ta kifa kanta, ƙarasawa ta yi ta ce "ki je in ji Yaya Abaan" ɗago kanta ta yi ta kalleta sai kuma ta sake sunkuyar da kanta, Umaima ba ta sake cewa komai ba ta fice daga ɗakin, tsaye ta same shi inda ta bar shi tana zuwa ta ce"na faɗa mata yaya" idanunsa maƙale cikin glasses ya ce"to je ki" sauka tayi tana juyowa ta ga ko ta fito. Above 5mins kafin Imara ta fito, tana sanye da wata Abaya maroon colour ta yafa veil ɗinta akai, a hankali take tafiya kamar wadda kwai ya fashewa a jiki, ta ƙaraso ba tare da ta kalleshi ba ta ce"gani" sai da ya ƙarasa abin da yake sannan ya mayar da wayar aljihu ya ɗago ya kalleta kamar ba zai magana sai kuma ya ce"why?" turo baki ta yi ta ɗauke kanta tana jin wasu sabbin hawayen na son zubo mata. Zuba mata idanu ya yi yana kallonta, cikin rawar murya ta ce"ni bana so ba zan je ba"
"Ko?"
Ya faɗa yana kallonta har sannan, sunkuyar da kanta ta yi ta goge hawayen da ya zubo mata, taɓe baki ya yi sannan ya ƙaraso gabanta, ɗago fuskarta ya yi ya ce"kukan me ki ke?" hannunta ta sanya za ya janye nasa hannun, sai dai ta ji ta kasa dan ba ƙaramin riƙo ya yi mata ba. Girgiza kai Abaan ya yi sai kuma ya ja hannunta suka sauka daga saman, zaune suka sami Khalil sai Jadda dake faman bada umarni, da idanu kawai Khalil ya bisu yana ganin yanda Abaan ya riƙe hannunta cikin nasa, bai kula kowa ba ya fice daga parlon. Mota ya shiga ita ma ta shiga sannan suka bar gidan, zazzafan numfashi Jidda ta sauke sai kuma ta bar wajen, kai tsaye kuma ɗakinta ta shiga, wayarta ta ɗauka ta kira ƙawarta bayan ta ɗaga ta ce mata ta jira ta tana nan zuwa daga haka ta kashe wayar ta shige toilet.
****Wani saloon and spa ya kaita, kai daga ganinsa kasan gurin kashe kuɗi ne, ɓangaren maza ya shiga ya zauna kafin ɗaya daga cikin matan ta zo ta tambayeshi yanda za'a mata, bayani ya yi mata yanda zata gane sannan ya bada atm ɗinsa, da idanu kawai Imara ta bi shi sai kuma ta ce "ni kar ma ka bada kuɗinka ko an yimin sai na lalata shi wlh" dariya sosai ta bashi amma ya dake fuskarsa a haɗe ya ce"me ki ka ce?" shiru ta yi tana zumɓura baki gaba.
****Tsaki ta yi tana kallon Jidda ta ce"to yanzu ke me ki ka yanke?" shiru Jidda ta yi sai kuma ta ce"gobe za mu koma wajen wannan malamin inason zan masa maganarta sai shi ya san yanda zai min da ita" tsaki Munceey ta yi ta ce"amma ke banza ce wlh, wato za ki jira har sai sanda boka ya yi miki maganinta kenan?, ke meyasa ba ki da wayo ne?" cike da damuwa ta ce"to Munceey me zan yi?, me ki ke so nayi?, ai zan faɗa masa ne so nake ta bar gidan kafin ni na bar shi, dan wlh ranar da zan tare da Abaan ranar za ta bar gidan mu " murmushi kawai Munceey ta yi ta ce"ki bari zan yi miki text message duk abin da ya kamata mu yi za mu yi, ke kinsan halina dan haka ki bar komai a hannuna zan yi miki maganinta" rungumeta Jidda ta yi ta ce"shiyasa nake ƙara son ki wlh"
Around 3pm ya yi parking a compound É—in gidan, kallonta ya yi ganin yanda ta yi shiru ya sa ya ce"fasa lalatawar ki ka yi?" Turo baki ta yi sai kuma ta ce"ai dai ni ban kula ka ba, kuma kai ma ka daina kula ni" murmushi ya yi ya ce"ke da zan É—auka Æ´ar zaman É—aki idan na yi aure shine za ki ce kin daina kulani?" saurin kallonsa ta yi sai kuma ta ce"lailaima, ni wlh ba Æ´ar zaman É—aki ba ce, nima ai aurena zan yi ni da yaya Khalil"
"Me ki ka ce?"
Juyowa ta yi ta kalleshi ta ga ya haɗe ransa kamar ba shine yanzu yake raha ba, turo baki ta yi ta ce"haka Mamah ta ce shi zan aura, kuma shima ya ce yana sona, kai ma ai Jadda ta cemin kana son Jidda sosai tun tana 'yar ƙarama shiyasa yanzu..."
"Get lost my friend!"
Abaan ya daka mata wata tsawa wadda ta sanya jikinta ya fara rawa, bai sake ce mata komai ba ya buÉ—e Æ™ofar ya fice daga motar, sauka ita ma ta yi ta bi shi da kallo har ya shige ciki. Harararsa ta yi sannan ita ma ta yi hanyar gidan, zaune ta same su a parlon kowanensu da Æ™unshi ja da baÆ™i a hannunsa, saÉ“anin ita da iya ja aka yi mata dan Abaan hana wa yayi a yi mata baÆ™in, Æ™arasawa ta yi ta zauna bayan ta yi sallama, kallonta Nana ta yi ta ce"au ashe kuma kin je?" da idanu kawai Imara ta bita sai kuma ta É—auke kanta, murmushi Umaima ta yi ta ce"mu ga Æ™unshin?" Æoye hannayen nata ta yi, Umaima ta dawo inda take ta buÉ—e hannayen, ba Æ™aramin kyau Æ™unshin ya yi akan hannunta ba, kasancewarta fara tas ya sanya jan Æ™unshin ya yi kamar an dasa shi a hannunta. Suna nan zaune suna hira har uku da rabi hakan yasa suka tashi dan fara shin tafiya cocktail.
# *IMARA 💋*
# *Bestnovel*
# *Nanameera*
# *2025*.
*Sauran posting 2 na kammala book 1, kamar yanda nafaɗa book 2 paid book ne ₦500, an fara payment tuntuni saboda haka wadda ba ta yi ba ga account number nan 7041901078 Hauwa Adamu lawan opay, sai a turo shaidar biya ta wannan numbern 08106608363, Yanzu mu ka fara tafiyar, akwai abubuwa dayawa a gaba💃kar ki bari a yi babu ke sister, ki biya ₦500 ɗin ki kacal na tabbata ba za ki yi danasani ba, taku har kullum Nanameera.**IMARA 💋💋*
47&48.
08106608363
Mikiya writers asso...
Ƙarfe 5:20pm Umaima ta fito cikin wata Abaya black colour, sosai rigar ta haskata ta yi kyau duk da ba wata kwalliya ta yi ba, ɗakin Nana ta shiga ta sameta tana ƙoƙarin saka agogo, irin rigar Umaima ce a jikinta da alama ita ce kalar kayan cocktail ɗin. Kallon agogo ta yi sai kuma ta ce"Imara ba ta fito ba ko?" gyaɗa mata kai Nana ta yi tana cigaba da shirinta, girgiza kai Umaima ta yi sannan ta fice daga ɗakin. Kwance ta hangi Imara ta yi ruf da ciki babu ko alamun tana shirin fita, ƙarasawa Umaima ta yi ta daketa, tashi zaune ta yi tana murza idanunta, Umaima kamar za ta yi kuka ta ce"yanzu Imara ba ki ma shirya ba?, lokaci fa na tafiya, so ki ke mu makara?" da mamaki Imara ke kallonta sai kuma ta ce "shirin me zan yi?" ɗan tsaki Umaima ta yi ta ce"shirin cocktail mana" taɓe baki Imara ta yi ta ce"ni ba zan je ba" zaro idanu Umaima ta yi kafin ta ce"look Imara dan Allah kar ki ɓata mana lokaci, ki tashi mana, kinsan dai babu yanda za'a yi ki ce ba za ki je ba ko?" Tashi tsaye ta yi tana kallon Umaima ta ce"to ni babu in da zan je wlh, ni bana son zuwa, kawai ku tafi mana. Kuma dan Allah karki cewa Mamah komai, Allah ya tsare" tana gama faɗin haka ta shige toilet abin ta. Da idanu kawai Umaima ta bita sai kuma ta juya ta fice daga ɗakin. A corridor suka haɗu da Nana, ganin yanda ranta yake a haɗe yasa Nana ta ce"cewa ta yi ba zata je ba hala?" Gyaɗa mata kai Umaima tayi. Murmushi kawai Nana ta yi ta ce"karki sake ce mata komai, ki zo mu tafi dan Allah"
"Amma Nana ya za'a yi a ce bata je ba?, akan wane dalili?" jan hannunta Nana ta yi ta ce"kin ga fa, ba dole ne sai mutum ya je ba, maybe bata ra'ayin zuwa irin waÉ—annan tarukan tunda kinga bata da shiga mutane, just leave her"
"Wa za'a bari?"
Suka tsinkayi muryar Mamah a bayansu. Girgiza kai Nana ta yi ta ce" ba kowa, wai daman Imara ce ta ce ba zata je partyn yau ba, shine na ce a ƙyaleta, maybe bata saba bane" shiru Mamah ta yi na ɗan wasu sakkani sai kuma ta ce"ku je kawai, bari na yiwa Abaan magana maybe shi ta ji maganarsa. Idan bata je ba ai sai ya zama abin magana" murmushi Umaima ta yi dan har ga Allah tafi son ace Imara taje wajen.
****Zaune ta sameshi kan kujera ya tankwashe ƙafafunsa idanun zube bisa system ɗin dake gabansa, zama ta yi kusa da shi tana murmushi ta ce"amma dai kasan yanzu ba lokacin wannan aikin bane ko?" ɗago kansa ya yi ya zuba mata idanu, murmushi ta yi ganin yanda idanunsa suka faɗa yasa ta ce"ba ka cin abinci ko?, sai yaushe zaka daina irin wannan abun ne Abaan?" langwaɓar da kansa ya yi kamar wanda aka yiwa dole ya ce"Mamah nagaji" dafa kansa ta yi ta ji zafi, girgiza kai ta yi cike da tausayinsa ta ce"sannu, kaga har zazzaɓi zai kamaka, ka tashi ka yi wanka, lokaci na tafiya, kar azo ana jiran ango bai zo ba" kamar zai yi kuka ya ce"Mamah ni fa nagaji wlh" dungure masa kai ta yi ta ce"banason shashanci, maza ka tashi, zan aiko Imara ta kawo maka ruwan tea kasha sai ka zo ka tafi. And kuma ka yi mata magana ance ta shirya taƙi wai ba zata je ba" bai ce komai ba ya rufe system ɗin ya tashi ya shige bedroom ɗinsa, da idanu kawai Mamah ta bishi sai kuma ta fice daga ɗakin.
****Zaune suke gidan makeup ɗin bayan an gama yi mata, sosai ta yi kyau dan daman da kyanta Masha Allah. Murmushi Amrish ta yi ta ce"ke matar nan kin yi wani irin kyau wlh" dariya Jidda ta yi ta ce"da gaske?, ki ce zan tashi kan mijina" tuntsirewa da dariya Raheena ta yi ta ce"ba dole ba, ai kedai ki bar komai a hannuna, wlh sai kin mallakeshi a tafin hannunki, babu boka babu malam" numfasawa Jidda ta yi sai kuma ta ce"nikam ina tsoro wlh, saboda malamin da muke zuwa wajensa ya ce yanada riƙon addini kuma asiri zai wahala ya ci shi" taɓe baki Xahra ta yi ta ce"ni banga wanda asiri ba ya ci ba, kawai dai ba zai iya bane, ki bari sai bayan auren akwai wajen wanda zamu je wlh duk taurin kan namiji sai ya dawo ɗan boyi-boyin ki. Ke duk rashin mutunci irin na Abbas sai da aka ladabtar min dashi, yanzu ko tsinke na ajiye na ce kar ya tsallake wlh ba zai iya tsallakawa ba, kuma ni ke juya dukiyarsa" ajiyar zuciya Jidda ta sauke kafin ta kalleta ta ce"ni fa ba wai inason na dinga juya dukiyarsa ba ne ko wani abun, kawai ni ya so ni, ya fifitani akan komai nasa, mu yi zama na lafiya da soyyaya wlh ni shine kaɗai burina"
Tsaki Xahra ta yi ta ce"ke banza ce ai shiyasa, to ai muddin yana sonki dole ya yi miki biyayya, mazan wannan zamanin idan ba da haka ba babu inda zamu kai labari, musamman miji irin naki mai kyau da kuÉ—i wlh idan ki ka yi sake kina zaune za'a kawo wata cikin gidan"
Saurin dafe ƙirjinta ta yi, lokaci ɗaya Imara ta faɗo mata arai, girgiza kanta ta yi tana kallon Xahra ta ce"Allah ya kiyaye, ni wai ina Munceey ta shiga ne?" tsaki Amrish ta yi ta ce"daga cewa fa gatanan kinga har mun gama abin da muke bata dawo ba, kawai mu tafi wlh"
"To mu je ina?, ai sai ango ya zo da motoci ya É—auki amarya ko?" Girgiza kai Jidda ta yi ta ce"a'a bari dai mu jira su, ai kinga bai san mun gama ba inaga"
****Fitowa ta yi daga kitchen hannunta riƙe da ɗan ƙaramin tea flask wanda Mamah ta bata, Jadda dake zaune kan kujera ta shiga bin ta da kallo kafin ta ce"ni ko wa nake gani haka kamar Imara?" a sanyaye ta ce"ni ce Jadda"
"Muhammadu Rasulullahi, ina wajen bikin?, ko ke ba ki je ba?, nima kinga jira nake angon ya fito mu tafi tare" girgiza kai Imara ta yi ta ce"ban shirya bane Jadda"
"Akan me?, je ki shirya na yi dropping ɗinki" Khalil dake tsaye a bayanta ya yi maganar, kamar za tayi kuka ta ce"ai yaya Khalil kaina ciwo yake shiyasa" girgiza kai ya yi ya ce"ayyah, sannu to, idan muka tafi a hanya sai na siya miki magani ko?" shiru ta yi ba ta sake cewa komai ba. Taɓe baki Jadda ta yi ta ce"yawwa, ni idan za ku tafin ma sai mu tafi tare, tun da na fuskanci shi wancan yaron ba shida niyyar sakkowa mu shige" murmushi kawai Khalil ya yi sai kuma ya ce"Tom Jadda bari na shirya, na kira Adeel ma ya cemin wai yana wajen"
"Sallamammen yaro mai halin uwarsa, nan fa na zauna ina jiran yaron nan sai cemin ya yi wai mota zai kai a sakowa fetur, shine ya yimin zamba cikin aminci ya gudu" ba Khalil ba hatta Imara dake tsaye sai da ta yi dariya, ya kalleta ya ce"Tom Jadda ni zan kai ki karki damu, Imara je ki shirya" da idamu kawai Imara ta bishi dan tama rasa abin da za ta ce masa dan kuwa ba zuwa za tayi ba.
****Tura kofar ɗakin tayi a hankali, babu kowa a parlon hakan yasa ta shiga ta ajiye flask ɗin, tana shirin fita ta ji wayarsa tana ƙara, kallon ƙofar bedroom ɗin ta yi sai kuma ta kalli screen ɗin wayar, babu suna hakan yasa ta ɗauki wayar ta ɗaga ta kai kunne.
"Hello Yaya, mun gama fa, kai muke jira kawai"
Saurin ajiye wayar ta yi ba tare da kashe ba, da idanu kawai Abaan ya bita ya ƙaraso wajen, ɗaukar wayar ya yi ya kai kunnensa, bai sake kallonta ba ya shige kitchen. Da idanu kawai Imara ta bi shi sai kuma ta tashi tsaye tana shirin fita.
"And who give u the permission?"
Cak ta tsaya sai kuma ta juyo ta kalleshi da idanunta wanda ruwa yake kwance a cikinsu. Bai mata magana ba ya zauna kan kujera ya haɗa tea ɗinsa, gajiya ta yi da tsaiwar ta nemi waje ta zauna a ƙasa ta kifa kanta akan gwuiwarta, sai da ya shanye shayin sannan ya ɗago ya kalleta, numfasawa ya yi kafin ya ce"mene dalilin rashin zuwan?" ɗago kanta ta yi a hankali bayan ta goge hawayen da suka zubo mata ta ce"ni kawai bana son zuwa" gyara zamansa ya yi yana kallonta sosai ya ce"saboda akwai abin da ke cikin ranki?, Imara kar ki koyawa kan ki wata ɗabi'a wadda ba taki ba, ki daina wannan abun da ki ke, kar na sake ji ko kuma ganin irin wannan dabi'ar, banason a sake kawomin ƙararki kin ji abin da nace?" Saurin gyaɗa masa kai ta yi tana ƙoƙarin ɓoye kukan dake shirin kwace mata. Tashi tsaye ya yi ya ce"ki tashi ki je ki shirya, Khalil zai tafi ya tafi dake, kuma ina sake faɗa miki kar a sake kawon ƙararki daga yau har ranar da za'a gama bikin nan" daga haka ya fice daga ɗakin ya barta zaune.
Duk wani taku da Abaan ke yi masifa ce a gurin Imara, tana jin kamar yana tafiya da rayuwarta, duk yanda take ƙoƙarin cire son shi daga cikin zuciyarta abun ya gagara, burinta bai shige ta ganta zaune kusa da shi ba, idan dare ya yi har Allah Allah take gari ya waye domin tayi ido biyu da shi, amma da alama duk abubuwan da take a banza suke tafiya, da alama Abaan bai lura da halin da take ciki ba ballantana tayi tunanin samun abin da take so daga gare shi.
****Around 7pm suka yi parking a wajen event ɗin, kallonta Khalil ya yi ganin yanda ta yi shiru ya ce"sannu, kan ne har yanzu?, ko dai mu fara zuwa mu siyo maganin?" girgiza masa kai tayi cikin sanyin murya ta ce"naji sauƙi sosai" girgiza kansa ya yi ya ce"a'a Imara, idan da kin ji sauki ba haka za ki yi ba, bari a tashi sai muje koda su Umaima ne a siya miki magani kinji" gyaɗa masa kai kawai tayi, sannan ta sauka daga motar. Yana sauka ya haɗu da su Kamal hakan yasa ya kalleta ya ce"maza je ki shiga Imara" gyaɗa masa kai ta yi sannan ta fara tafiya. Tana shiga hall ɗin ta hangeta can saman stage sanye da fararen kaya, yayinda duk wata budurwa dake wajen ta saka baƙar riga, hakan yasa suka yi kyau ba ƙarami ba. Kallo ɗaya ta yiwa Abaan dake zaune kusa da ita yana sanye da suit farare gashin kansa wanda ya sha gyara sai sheƙi yake, dafe ƙirjinta ta yi sai kuma ta nemi kujera acan bayan ta yi zamanta. Tana zaune aka dinga tashi ana zuwa rawa da amarya, Jidda ba zaka ce bikinta ake ba dan sakar jikinta ta yi tana rawarta hankali kwance. Tana kallon sanda su Umaima suka je kan stage aka dinga liƙa kuɗi kamar ba'a san zafinsu ba, tashi Imara ta yi ta fita daga hall ɗin ta nemi can wani dandamali ta zauna.
Sai wajen ƙarfe 9pm sannan aka fara fitowa daga wajen, har sannan tana zaune a wajen, ta dunƙule jikinta saboda wani zazzaɓi da ya rufe ta. Har sun shiga mota Khalil ya ƙaraso wajen yana kallonsu ya ce"ina Imara?" Da mamaki Umaima ta ce"Imara kuma?, ai ba ta zo ba" zaro ido Khalil ya yi ya ce"wane irin bata zo ba, ni ne nan na kawota wajen nan, na ce ta shiga ciki, kuma akan ido ta shiga ciki yanzu kuma ku ce bata zo ba" girgiza kai Nana ta yi ta ce"wlh to Yaya bamu ganta ba, mu muna tare da yaya Adeel" jinjina kai Adeel ya yi ya ce"gaskiya bata zo inda suke ba, koma ta shigo ɗin" da sauri Khalil ya bar wajen ya shiga dubata sai dai iya dubansa ban ganta ba. Can ya hangi su Abaan tsaye suna magana da Kamal, ƙarasawa ya yi yana kallonsu, ganin irin yanda yake kallonsu ya sanya Kamal ya ce"Khalil lafiya dai?, meya faru?" girgiza kai ya yi ya ce
"IMARA!"
# *IMARA 💋*
# *Bestnovel*
# *Nanameera*
# *2025*.
*Sauran posting 1 na kammala book one, ƴar uwa har yanzu ba ki yi payment ba??, kina son ganin yanda abun zai kasance kuwa?, da a baki labari ai gara ki bayar saboda haka maza-maza ki yi payment ta wannan account ɗin 7041901078 Hauwa Adamu lawan opay, sai ki turon shaidar biya ta lambata 08106608363, ₦500 kacal, karki bari ayi babu ke, daga gobe ne💃💃, taku har kullum Nanameera**IMARA 💋💋*
49&50.
End of book 1
Mikiya writers asso...
Babu irin neman da ba'a yiwa Imara ba amma basu sameta ba, zuwa lokacin hankalinsu ya yi matuƙar tashi. Tsaye Abaan yake jikin mota sai bin su yake da kallo, koda wasa bai ɗaga ƙafarsa daga inda yake ba, Kamal ne ya ƙaraso yana kallonsa ya ce"wai ya na ganka a tsaye?, ba fa aga yarinyar nan ba" gajiyayyun idanunsa ya zuba masa ba tare da ya ce komai ba. Tsaki Kamal ya yi sanin halinsa ya ce"wai mene haka?, idan kasan inda yarinyar nan take dan Allah ka faɗa"
"Saboda ni na saceta?, ko kuma ni na kawota gurin nan?"
Girgiza kai Kamal ya yi ya ce"ba haka nake nufi ba, anyway kai ma ka shigo a nemeta da kai mana" É—auke idanunsa ya yi yana kallon gefe, can kusa ya zura wayarsa a aljihu ya yi gaba ya bar Kamal a wajen. Girgiza kai kawai Kamal ya yi sannan ya bi bayansa.
A hankali yake tafiya toward direction ɗin flowers ɗin, Kamal ne ya biyo bayansa yana kallon inda yake shiga ya ce"haba malam, me zai kai mutum nan wajen?, ka zo muje wani wajen dan Allah" tamkar wanda yake magana da dutse haka Abaan ya yi masa banza ya cigaba da tafiya. Bin bayansa Kamal ya yi gudun kada wani abun ya same shi. Shassheƙar kukanta ya juyo hakan yasa ya ƙarasa inda take tsugune, wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta, waro idanu Kamal ya yi sai kuma ya ce"Imara" a firgice ta ɗago ganin mutane akanta ya sanya ta tashi tsaye ta shiga goge idanunta.
"Me ki ke anan?, ba kisan dare ba?"
Buɗe baki ta yi za ta yi magana ta ji an sauke mata wasu lafiyayyun maruka har guda biyu. Ba Imara ba hatta Kamal sai da ya dafe kuncinsa saboda yanda ya ji ƙarar marin, Abaan bai sake kallon kowa ba ya juya ya bar wajen. Tafiya tayi luu zata faɗi Kamal ya yi saurin tare ta, ta faɗo hannunsa sumammiya. Ƙarasowa wajen Khalil ya yi ya kalleta sai kuma ya kalli Kamal a rikice ya ce "lafiya dai?, me ya sameta?" girgiza kai kawai Kamal ya yi ya ɗauketa suka bar wajen. Koda suka je basu tarar da Abaan ba da alama tafiyarsa ya yi ba tare da ya jira koda amaryar ba.
****Turo ƙofar ɗakin ya yi ya shigo, tsaye ya samu Mamah sai kai da komo take a cikin ɗakin, ya ƙarasa ya tsaya kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce"lafiya dai Mamah?"
"Lafiya?, tambaya ka ke lafiya Abaan?, abin da ka aikata ka yi daidai kenan?, akan me zaka mari ƴar mutane?, me ta yi maka?, waɗanda suka sha wahalar nemanta ba su mareta ba sai kai?, me ka ke taƙama dashi?, kodan kana jin kai ne silar zuwanta gidan nan?. Yarinyar ba tada lafiya aka yi insisting ɗinta akan sai ta je, shine kuma ta je har ka daketa?, ko matar aurenka zaka saka hannu ka daka?, ka bani mamaki wlh!, na yi shiru da maganar nan ne saboda baƙin dake cikin gidan nan, da kuma arzikin aurenka da ake amma da wlh sai ranka ya ɓaci"
Tunda ta fara magana Abaan ke kallonta, rabon da Mamah ta yi masa faÉ—a irin haka tun yana É—an shekara goma sai gashi yau ta sake masa irin sa akan IMARA. Bai ce mata komai ba ya juya ya bar É—akin, da idanu kawai ta bi shi sai kuma ta nemi waje ta zauna jin jiri na neman É—ibanta. Abaan na fitowa kai tsaye É—akinsa ya shige, yana zuwa ya faÉ—a kan gado ya yi ruf da ciki, a hankali wasu zafafan hawaye suka fara sauka akan fuskarsa abin da ya daÉ—e bai yi ba cikin rayuwarsa, domin ko da yana yaro shi ba ma'abocin kuka bane. Gajiya ya yi da kwanciyar hakan yasa ya tashi zaune, drawer dake gefen gadon ya buÉ—e ya ciro pictures É—in dake ciki. ÆŠaya bayan É—aya ya shiga kallonsu, wani hoto ya ciro yana zaune akan cinyar wani babban mutum, gefensa kuma wata kyakkyawar budurwa ce tayi dariya. Shafa fuskarta ya yi hawaye na zubowa daga idanunsa cikin rawar murya ya ce
"I'm sorry, double sorry Janan, na gaza, ba zan iya ba, nagaza cika alƙawarin dana ɗauka. Ki hukunta Janan, dan Allah Janan"
Yanda yake kuka kamar ƙaramin yaro zai tabbatar maka da halin da yake ciki, tabbas akwai wani ɓoyyayen abu wanda yake damunsa, rungume hoton ya yi yana cigaba da kuka.
****A hankali ta shiga buɗe idanunta wanda suka mata wani irin nauyi, tashi zaune tayi tana ƙarewa ɗakin da take kallo, tunanin wanda ya dawo da ita gida ta shiga yi, wani irin raɗaɗi taji fuskarta na yi mata hakan yasa ta tashi da sauri ta shiga toilet ta zuba ruwa a fuskar, hannunta ta kai fuskar ta ji wani irin abu, da sauri ta kalli mudubi, shatin yatsunsa ne kwance akan fuskarta. Gaba ɗaya fuskar tayi wani irin jaa kasancewarta fara, sai a sannan ta tuna da marukan da Abaan ya yi mata. Wasu zafafan hawayene suka zubo akan fuskarta, fitowa tayi daga toilet ɗin ta dawo ta zauna gefen gado har sannan hannunta na maƙale kan fuskarta. Turo ƙofar ɗakin a kayi ta juya ta kalleta, sanye take da sleeping dress fara ta ɗaure gashin kanta, ƙarasowa Nana ta yi ta zauna kan bedside drawer tana kallonta, tausayi Imara ta bata hakan yasa ta girgiza kai cikin ƙasa da murya ta ce"Imara Inason zan yi magana dake"
Kallonta kawai Imara ta yi bata ce mata komai ba, amma yanda ta maida idanunta kanta ya nuna tana saurarenta. Numfasawa Nana ta yi cikin sanyin murya ta fara magana
"Imara inason ki fita a harkar yaya Abaan dan girman Allah, ki kalli abin da yake gabanki, kinga dai abin da ya faru dake yau, na faɗa miki wani abu?, yaya Abaan baya ƙaunarki, ke babu wani alamu dake nuna yana sonki, bayan haka ma bai damu dake ba. A sanda kowa yake ƙoƙarin nemanki ɗazu shi tsayawa ya yi yana danna waya, sai da kowa ya gaza nemanki sannan Yaya Kamal ya yi masa magana. Saboda haka ki dawo daga wannan duniyar da ki ka shiga, ki fuskanci abin da yake gabanki, ki riƙe maraicinki Imara, ki maida hankali akan abin da zai amfani rayuwarki. Bari na faɗa miki gaskiya wlh! Wlh! Abaan ba zai aureki ba, saboda shi kwata-kwata mata basa burgesa, ke hatta Jidda saboda furucin Jadda ya yarda da auren ba wai saboda yana sonta ba, kuma kema shaida ce na yanda yake yi mata. Ki cire kan ki daga cikin al'amuran rayuwarsa, tun kafin wani ya gane halin da ki ke ciki ya kamata ki dakata haka. Ki daina baƙin ciki ko kishi dan zai yi aure, ki shiga a yi komai dake, ki sani ba za ki taɓa auren mijin da ba naki ba, dole mijinki shi za ki aura. Dan Allah ki ɗauki shawarata ki saki ranki a ƙarasa bikin nan lafiya ki cigaba da karatun ki, ki ka san abin da Allah ya tsara miki?"
Goge hawayen da suka zubo mata tayi, ta kalli Nana cikin shassheƙar kuka ta ce"Nagode sosai da shawarwarin ki Nana, Nagode sosai, zan yi amfani da abin da ki ka ce in sha Allah, zan yi gwagwarmaya domin na samarwa da kaina kyakkyawar rayuwa, ba zan sake shashancin son wani a zuciyata ba, na yadda kowa baya sona, kowa guduna yake, zan rayu ni kaɗai in sha Allah, ba zan sake creating wata matsalar a cikin ahalin nan ba"
Shiru Nana tayi tana kallonta sai kuma ta kamo hannunta ta ce"ba haka nake nufi ba Imara, ya za'ayi ki ce babu wanda yake sonki, how comes?, dole ki sami wanda yake sonki domin ba kida mugun hali, kar ki yiwa maganata mummunar fahimta dan Allah"
Murmushi tayi duk da hawayen dake kan fuskarta ta ce"ko kaÉ—an wlh Nana ban yi miki mummunar fahimta ba, na san gaskiya ki ke faÉ—amin, kuma na yarda dake" ajiyar zuciya ta sauke ta ce"tom Nagode sosai, ki tashi muje É—akina mu kwana, gobe akwai dinner kuma za ki je" gyaÉ—a mata kai kawai Imara ta yi sannan ta tashi, duk da yanda kanta ke mata ciwo hakan bai hanata bin Nana ba.
Zaune suka sami wasu yan mata su biyu suna hira, da idanu kawai Imara ta bisu, ƙarasawa Nana ta yi tana murmushi ta ce"yau kwanan hira zamu yi, ga Imara a gidan nan take. Imara ga Maimoon ga Fadeela cousins ɗina ne ya'yan ƙanwar Mamah ne" ɗan murmushi Imara ta yi ta ce"sannunku" murmushin suma suka mayar mata sannan suka gaisa. Ita dai ta nemi waje ta zauna tana jin yanda suke hira gwanin ban sha'awa.
Washegari da wuri suka tashi saboda aikin da ake a gidan, sosai aka taru dan duk yan uwan Mamah sun zo, kowa sai harkarsa yake, rashin sabo irin na Imara ya sanya ta koma ɗakinta ta yi zamanta dan ita ba gwanar surutu ba ce. Tana nan zaune har aka yi sallar azahar Nana ta shigo tana kallonta ta ce"wai ke mene haka?, kin wani dawo ɗaki kin zauna. Ki tashi to kiyi wanka zamu tafi gidan make-up ance mu je da wuri saboda muna da yawa" a sanyaye Imara ta ce"make-up kuma?, ni banason makeup wlh" wani kallo Nana ta yi mata sai kuma ta ce"to ba faɗata ba ce, Mamah ce ta saka saboda haka sai ki je ki sameta ki faɗa mata ke bakya so" langwaɓar da kai Imara ta yi ta ce"ayyah Nana, dan Allah karki faɗa mata" ba ta ce mata komai ba ta fice daga ɗakin bayan ta ɗauki abin da ya kawota. Tashi Imara ta yi ta shige toilet ba dan ranta yana so ba.
****Ƙarfe 7:50pm suka fito daga gidan kwalliyar, gaba ɗayansu aka yi musu kwalliyar har da Imara, sun saka wani uban su lace mai kyau, kai kana gani kasan da kuɗi aka siya lace ɗin, Imara dake ta ƙoƙarin gyara rigar jikinta Nana ta kalleta ta ce"wai me ki ke haka?" Kamar za ta yi kuka ta ce"ni wlh banaso, duk na matsu" tuntsirewa da dariya suka yi gaba ɗayansu Maimoon ta ce"lailaima ke ɗin nan, wannan kayan ne kin matsu?, baki san kayan da ake matsuwa ba ma" turo baki Imara ta yi ta ce"wlh ni dai sun isheni, kuma wannan mayafin ya yi ƙarami" waro idanu Nana ta yi ta ce"to malama sannunki, to bari ki ji koma me suka yi a haka za ki saka su" ɗauke kanta ta yi tana kallon gefe. Dafata Umaima ta yi ta ce"kinga Imara mu je ki rabu dasu"gyaɗa mata kai tayi suka shiga motar sannan sauran ma suka shiga.
A bakin ƙofar shiga suka tsaya saboda sune masu shiga da amarya, bayan amarya ta fito da ƙawayenta wanda suma suka sanya lace irin nasu Nana wanda ke nuni da ankon lace ɗin aka yi, tsara su aka yi yanda ya kamata sannan suka shiga da amarya. Banda Imara wadda ana shiga ta zame ta fita daga layin, cika sosai aka yi a wajen dan kusan kowa na dangi ya zo bikin, sai liƙa kudaɗe ake kamar ba gobe. Suna nan zaune har aka kira yan cikin gidan domin su zo su yiwa amarya da ango liƙi, tashi suka yi Nana ta kalleta ganin tana zaune ta ce"nan ɗin ma ba za ki taso ba?" langwaɓar da kai Imara ta yi ta ce"dan Allah Nana ku je kawai, ni banason shiga wlh" tsaki Nana tayi ta ja hannunta suka ƙarasa wajen. Khalil ne ya miƙo musu wrapper na yan dubu-dubu, aka saka musu kiɗa suka fara liƙi, Imara kasa motsi ta yi dan ta rasa wanda za ta liƙawa kuɗin, dan Jidda na ganinta ta haɗe rai, haka kuma ba zata iya zuwa inda Abaan yake ba dan ta yiwa kanta katanga dashi. Tunda ta tsaya yake kallonta hakan yasa ya tako har inda take ya riƙo hannunta, wrapper dollars ya zaro a aljihunsa ya buɗe ya shiga liƙa mata. Da idanu kawai Jidda ta shiga bin su, ganin ita ko biyar bai liƙa mata ba, tasowa abokansa suka yi dasu Khalil suka zo inda yake tsaye suka shiga yi musu liƙe, ganin haka ya sanya suma su Umaima suka dawo inda ake liƙin, gaba ɗaya sai kallo ya koma wajen, ya rage sai Jidda tsaye ita kaɗai tana binsu da kallo. Amrish ce ta taso ta zo ta riƙe hannunta ganin tana shirin kuka yasa ta yi mata magana can ƙasa ta ce"karki kuskura ki zubar da mutuncinki, ki bari a koma gida" jinjina kai Jidda tayi tana sauke ajiyar zuciya. Har aka tashi daga wajen ba ta sake koda dariya ba, suna fitowa ta shiga motar Amrish suka bar wajen domin tasan ba Abaan ne zai kai su gida ba.
Amrish na parking ɗin motar ta fita daga gudu kai tsaye kuma apartment ɗin Jadda na da ta shiga, biyo bayanta Amrish ta yi tana zuwa ta sameta kwance kan gado sai rusa kuka take. Zama tayi gefenta tana rarrashinta amma ko saurarenta Jidda ba tayi ba, shigowa sauran su kayi, Munceey ta ƙaraso inda take tana murmushi ta ce "ki kwantar da hankalinki, yau dai ranki ya ɓaci, amma gobe ranta ne zai ɓaci, irin ɓacin ran da zata ji kamar ta kashe kanta. Irin ɓacin ransa da zai yi sanadiyyar barinta gidan nan, na rigada nagama shirya komai saboda haka ki kwantar da hankalinki ki kuma goge hawayenki. Keda kuka sai na farin ciki Jiddo" ɗago kanta tayi tana kallonta ta ce "kina fa kalla, kina fa kallan abin da aka yimin, wlh saidai idan akwai abin da Abaan yake ɓoyewa akan yarinyar nan, idan badan haka ba wlh ko kallonta ba zai dinga yi ba, ni daman tunda ya kawota ban yarda da ita ba" dafata Xahra tayi ta ce"to ba gashi za'a yi maganinta ba, koma wani abun ne ai ya zo ƙarshe, ki daina wani damun kan ki. Kina da masu share miki hawaye" goge idanunta tayi sannan ta saki ranta.
Ranar kusan kwanan zaune suka yi suna hira, Imara ta saki jikinta duk da ba sosai take maganar ba amma idan akayi abun dariya za tayi. Sai da aka kusa sallahr asuba sannan suka kwanta, ita kuwa ta tashi ta ɗauro alwala ta zo ta fara gabatar da sallah. Da safe gidan ya cika sosai da mutane, dangi da abokan arziki kowa ya zo, ƙarfe 10:30am aka ɗaura auren Jidda da Abaan a masallacin dake gidan, daga nan kuma duk mazan suka shige reception. Sai wajen ƙarfe 12pm sannan suka dawo, sanye duk suke da fararen shadda wadda ita ce aka yi ankon ɗaurin auren. Kamar za tayi kuka ta kalli Nana wadda ke janta ta ce"dan Allah ki cikani ni wlh banason hoton" ko saurarenta Nana ba tayi ba ta cigaba da janta har compound ɗin gidan. Taron jama'ar da ta gani ya sanya Imara sunkuyar da kanta, ita a rayuwarta bata iya shiga cikin jama'a ba. Murmushi Umaima tayi ta ce"sai wani sunkuyar da kai ki ke kamar ke ce amaryar" turo baki ta yi ta ce"ayyah ni wlh nagaji kaina ciwo yake" dariya Nana ta yi ta ce"ki bari a yi mana hotuna da amarya sai ki tafi" da sauri ta kalli Nana kamar za tayi magana sai kuma ta yi shiru. Ƙarasowa gabansu ya yi yana murmushi ya ce"kaga ƙannen ango kuma ƙannen amarya" dariya suka yi banda Imara, Nana ta ce"ai Yaya wani shagalin sai ranar bikinka" murmushi Kamal ya yi ya ce"kedai bari mutuniyar, ku zo muje ayi hotuna daku mana" toh suka ce sannan suka bi bayansa har inda ake hotunan, kallo ɗaya Imara ta yiwa Jidda wadda ke wani shishshigewa Abaan, tana sanye da farin lace mai adon golden ta yafa mayafi golden akanta tayi kyau Masha Allah. Ƙarasawa suka yi Imara ta tsaya daga can baya dan ko da wasa bata zuwa inda Abaan yake, hotuna aka shiga ɗaukansu banda ita dan tana tsaye daga can gefe. Kallo ɗaya Abaan ya yi mata sai kuma ya ɗauke kansa, kamar wanda aka yiwa dole haka ya ƙarasa inda take ya jawo hannunta, a kusada shi ya tsayar da ita hannunta na cikin nasa aka ɗaukesu hoto, Jidda fita tayi daga hoton ganin yanda ake ɗaukarsu kamar ita ce matar tasa, juyawa tayi ta bar wajen kamar za ta tashi sama.
****Tunda Imara ta shiga ɗaki bata sake fitowa ba har aka yi sallar la'asar, Nana ce ta shigo ta sameta a kwance, tashinta tayi ta ce"ki tashi ki yi wanka an fara shirin kai amarya har ƙarfe 6pm" dafe kanta tayi kamar za tayi kuka ta ce"kaina ciwo yake Nana, ni ba zan iya fita ba" dafa kanta tayi taji zafi sosai hakan yasa ta ce"sannu to, ki yi zamanki idan zamu koma sai ki je, mu mun tafi" gyaɗa mata kai kawai Imara tayi sannan ta koma ta kwanta. Kiran sallar magrib da ta ji ya sanya ta tashi ta shiga toilet ta ɗauro alwala. Sallah tayi sannan ta fito daga ɗakin, bata sami kowa a main parlon ba, da alama duk an tafi kai amarya. Fitowa compound ɗin gidan tayi tana leƙe ko zata samu wani.
"Imara!"
A ɗan firgice ta juya, Jidda ta gani tsaye a bayanta, murya can ƙasa ta ce"na'am" murmushi Jidda ta yi ta ce"dan Allah muje zan baki tea ki kai wa Yaya Khalil, ya ce a kai masa to ni kuma tafiya zan yi" kamar ba za tai magana sai kuma ta ce to, Jidda tayi gaba ita kuma ta bi bayanta. A bakin ƙofa Imara ta tsaya tana kalle-kalle, lokacin gari ya yi duhu dan har an kusa fara kiran sallar isha'i, fitowa Jidda tayi hannunta riƙe da wani ɗan ƙaramin tea flask, tana murmushi ta miƙa mata, amsa Imara ta yi, ta ce"yawwa dan Allah idan kin je sai ki saka masa cup akai, If possible ki tsaya ya shanye please" toh kawai Imara ta ce sannan ta juya ta bar wajen, murmushi kawai Jidda ta yi sannan ta koma ciki.
Babu inda Imara ba ta duba a ɗakinsa ba amma baya nan babu ma alamar akwai mutum a ɗakin, fitowa tayi hannunta riƙe da flask ɗin tana shirin sauka ta ga wata maid ta hawo, a sanyaye ta ce"dan Allah ina Mama take?, da Yaya Khalil?" cike da girmamawa ta ce"Hajiya Mamah ta fita, shi kuma Khalil yana ɗakin babban yaya ɗazu" jinjina kai kawai Imara tayi sannan tayi hanyar ɗakin Abaan. Tura ƙofar tayi ta shiga, babu kowa a parlon sai tv dake faman aiki ita ɗaya, ƙarasawa tayi ta ajye flask ɗin akan table ta tsaya tana haki. Tunowa ta yi da hotunan rannan hakan yasa ta tayi hanyar bedroom ɗinsa da gudu. Tana shiga Abaan ya fito daga kitchen yana sanye da armless milk da alama bai daɗe da fitowa daga wanka ba. Tea flask ɗin ya gani hakan yasa ya ƙarasa, dan ya yi tunanin Mamah ta manta dashi ma. Cup ya ɗauka ya tsiyayi shayin sannan ya fara sha. Tsayawa ta yi ta rike ƙugunta kamar za tayi kuka, dan babu inda ba ta duba ba amma bata samu hotunan ba. Turo baki tayi ta juya zata fita ta hangi wata jaka akan mirror, ƙarasawa tayi ta buɗe jakar, wata ajiyar zuciya ta sauke ta zaro envelope ɗin, murmushi ta yi ganin hotunan ne, ta yi zaman dirshan a wajen ta cigaba da buɗe hotunan. Wata mata ta gani tsaye a kusada Abaan lokacin bai fi shekara 18 ba, waro idanu Imara tayi ganin matar tana tsananin kama da ita, sake ɗaukan wani hoton tayi nan ma taga matar ce tsaye sai Abaan gefensu kuma wata yar ƙaramar yarinya.
"Joda!"
Imara ta faɗa cikin tashin hankali da mamaki, tabbas wannan Joda ce, koda basa ga maciji da ita amma tagane kamarta, baza hotunan tayi a ƙasa ta shiga zarowa tana kallo, a firgice Imara ta tashi tsaye tana girgiza kanta bakinta na rawa ta shiga furta
"A'a, no ba shi bane, ba Ameer bane!, me hoton Ameer yake a gidan nan?" Tamkar wata zararriya haka take magana, wani hoton ta É—auko wanda ya sanya ta yi baya tana shirin faÉ—uwa, gabaÉ—aya mutanen cikin masarautar Udaid sune a cikin hoton, idanunta ya sauka kan Maheer wanda ke tsaye kusada Abaan, runtse idanunta tayi abubuwan da suka faru suka shiga dawo mata É—aya bayan É—aya, saurin yada hoton ta yi, ta fice daga É—akin da sauri za tayi waje. Tsaye ta same shi a parlon idanunsa a lumshe. GabaÉ—aya jikinta rawa yake cikin rawar murya ta fara magana
"Waww...wane kai?, ka faÉ—a min gaskiya, a ina kasan Ameer?, daman turoka suka yi ka kasheni?, wlh ba ni ce na kashe Ameer!, ban kashe shi ba!, bani ba ce!, kar ka cutar dani, zan bar gidan nan yanzu dan Annabi!"
Ɗago idanunsa ya yi ya zuba mata yana kallonta, saurin ja da baya Imara tayi ganin yanda idanunsa suka yi wani irin Jaa jijiyoyin kansa suka tashi, a hankali ya fara takowa zuwa inda take tsaye. Baya Imara ta fara yi har sai da taje jikin ƙofa hakan yasa ta maƙale a jikin ƙofar cikin tashin hankali take faɗin
"Mene haka?, ka matsa daga kusadani, ni tafiya zan yi, wlh ba ni ce na kashe shi ba!, zan yi maka bayani kar ka cutar dani" runtse idanu Abaan ya yi ba tayi aune ba ta ji ya ja hannunta, kai tsaye kuma ɗakinsa ya shiga da ita, bai lura da tarin hotunan dake zube akan carpet ba ya cillata kan gado jikinsa na wani irin rawa, sai haɗa gumi yake, Imara ta kasa gane abin da yake nufi, gabaɗaya tunanin ya tsaya cak, me Abaan ke shirin aikata mata?, me ya sameshi haka har ya fita daga cikin hayyacinsa?. Fashewa tayi da kuka ta tashi da niyyar guduwa, sake hankaɗata kan gadon ya yi sannan ya bi ya danneta, zuwa sannan ko numfashi ƙwakwakwara bata iya wa, ganin yanda yake abu a gaggauce ya sanya ta runtse idanunta, duk yanda ta so ta kwaci kanta a wajen Abaan kasawa tayi, tana ji tana gani ya rabata da kimarta ta ya mace wadda ko mijin daya aureta bai aikata hakan a gareta ba.
A hankali ya buɗe idanunsa ya zuba mata yana kallonta, gabaɗaya bata cikin hankalinta dan ko numfashi bata yi. Dakyar ya iya tashi daga kwancen da yake ya ja jikinsa zuwa inda take, bugar ƙofar da yaji an yi yasa ya ɗago yana kallon ƙofar cikin tashin hankali
"Abaan!! Abaan!! Abaan!!"
"Mamah!??"
*End of book 1💃💃💃*
*Kina son sanin wane Abaan?*
*Wace IMARA?*
*Wace ce wadda ke kamada IMARA?*
*Wane hali IMARA zata faÉ—a bayan abin da ya faru?*
*Wane Ameer?, yana raye ko ya mutu?*
*Wane Dodonta?, zai dawo ko kuma ya tafi kenan?*
*IMARA zata tashi ko a'a?*
*Mene dalilin Maheer na aurenta da kuma sakinta?*
*Wa zai taimaketa??*
*Duka wadannan amsoshin suna nan cikin littafin IMARA book 2, wanda kuma ba Free bane, za ki biya ₦500 ta wannan account ɗin 7041901078 Hauwa Adamu lawan opay sai a tura shaidar biya ta lambata 08106608363, zamu cigaba da book 2 ranar Monday in sha Allah, kafin nan duk wanda bai biya ba sai ya yi ƙoƙari ya biya, taku har kullum Nanameera.*