← Book details Imara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 3 OF 5

Chapter 17

Imara Part 1 Complete Hausa Novel · about 16 min read

Kallonta granny tayi ganin yanda ta haɗe kai da gwiwa ta ce"lafiya Imara?" Turo baki tayi tana kallon gefe guda ta ce"ko ba Daddy nakeson gani ba" a shagwaɓe tayi maganar kamar zatayi kuka, girgiza kai Granny tayi ta ce "au daga zuwan naki yau shine zaki ce Daddy kikeson gani?, to ƙaniyarki, kuma babu wanda zaki wahalar sai kinyi sati a garin nan" tsam Imara ta tashi daga inda take ta dawo kusada granny ta fasa ƙara ta kwanta a wajen tana burgima, riƙe baki granny tayi ta ce"nashiga uku ni Asiya, me kuma nayi miki?"


"Ni wlh Daddy nakeson na gani!, ki kira shi a waya ya zo, ni sai ya zo wlh!" Kuka take sosai tamkar wata jaririya gabaɗaya ta ɓata kayan jikinta da ƙasa. Tashi Granny tayi ta shige ɗakinta ta ɗauko wayarta ta fara kiran lambar Mubarak, saida tayi ringing sau biyu sannan ya ɗaga bakinsa ɗauke da sallama, gaisawa suka yi sannan ta faɗa masa abin da yake faruwa, murmushi ya yi ya ce ta bata wayar, kallonta tayi ta ce"ki zo ga baban naki" da sauri ta tashi tana goge hawayenta ta karbi wayar


"Da..Daddy!"


Ta faɗa cikin shassheƙar kuka, murmushi ya yi ya ce"na'am ƴar gidan Daddy mene ne?" "Ni ka zo yanzu!" waro idanunsa ya yi kamar tana gabansa ya ce"yanzu kuma Imara?, me ya faru" kuka ta saka ta ce"ni kawai ka zo yanzu" "kin fasa kwana a gurin Granny ɗin?" girgiza kanta tayi ta ce"nidai ka zo yanzu Daddy, ni ka zo, abu zan faɗa maka" murmushi ya yi ya ce" to ki faɗamin a wayar mana" maƙale kafada tayi ta ce"nidai a'a sai kazo" girgiza kansa ya yi ya ce"to Imara ki bari saida safe mana" fashewa tayi da sabon kuka ta ce"ni yanzu nakeson ka zo Daddy!, yanzu fa" numfasawa ya yi ya ce "shikenan gani nan" murmushi tayi har saida beauty point ɗinta ya loma ta ce"safe trip daddy" murmushin shima ya yi sannan ya kashe wayar. Kallonta granny tayi ganin yanda fuskarta tayi jajur ta harareta da wasa ta ce"kuma ba zaki kwanar min a gida ba, yau saidai ku tafi tare" turo baki tayi tana maƙale kafaɗa" .


***Shigowa ɗakin tayi tana kallonsa da mamaki ganin yana ƙoƙarin saka hula, tsayawa tayi a cikin bango har saida ya gama tsaf sannan ta kalleshi fuska a haɗe ta ce"ina kuma zaka je da daddaren nan?" girgiza kansa ya yi ya ce"wlh wai Imara ce ke kirana, sai kuka take na zo, shine zan je amma ba dadewa zan yi ba"


"Imara na kiranka!?, sai kuka take?, kuma ba dadewa zaka yi ba?. Bangane ba, imaran jaririya ce?, ko kuwa tana da wata lalura ne?, nifa bangane wannan rikitaccen al'amarin ba wlh, tana kuka akan me?" Yana ƙoƙarin ɓalle bottle ɗinsa ya ce"dan tana son ganina shine ai bu?, ko kuwa dan tayi kuka, ko kin manta yarinya ƙarama ce ne?, har kwaya nawa imaran take?, she's just 9yrs old fa"


"And so what?, Ina ruwana da shekarunta?, me ya shafeni?, nagaji da irin waɗannan abubuwan da kake yimin Mubarak!, nagaji wlh! Wulaƙancinka ya fara yawa a gareni, i can't endure it anymore!, kuma wlh babu inda zaka fita, ni zaka rainawa hankali!, kai ka isama!?"


Tunda ta fara maganar yake kallonta bai ce komai ba, yana ganin tayi shiru ya ratsa ta gefenta zai fita, jawo shi tayi tana huci ta ce"mahaukaciya ka mayar dani kenan?, wlh babu inda zaka je kaji na faɗa maka!" Tsaki ya yi yana kallon waje ya ce"tun kafin raina ya ɓaci Suhaila ki sakeni, banason nazo nayi abinda zai ɓata mana rai duka, saboda haka let go of me, or else..."


"Kayi duk abin da kake ganin zaka yi, amma wlh babu inda zaka fita, baka is..." Maganar ta tsaya dalilin wasu maruka da ya yi mata, dafe kuncinta tayi nan take hawaye suka fara ambaliya ta kalleshi bakinta na rawa ta ce"ni!?, ni ka mara Mubarak?, ka mareni?"


"Nan gaba idan kika sake yimin irin wannan ba marinki kaÉ—ai zai yi ba, saina karya ki, ni ba sa'an wasanki bane, baki isa ki dinga yimin irin cin kashin da kika so ba!" Ya fice daga É—akin kamar zai tashi sama, da idanu kawai Suhaila ta bishi sai kuma ta sulale a wajen ta rushe da wani irin kuka kamar ranta zai fita.


***Har ya isa ƙauyen ransa a ɓace yake, yana zuwa ya tarar da ita zaune gefen granny tayi shiru, tana ganinsa ta tashi da gudu ta rungumeshi tana dariya, murmushi ya yi yana shafa kanta ya ce "sarkin rigima!" turo baki tayi bata ce komai ba, ta rike hannunsa suka ƙarasa inda aka shimfida tabarma, zama ya yi ya kalleta ya ce"to gani nazo" murmushi tayi ta ce"yawwa Daddy na shiyasa nake sonka wlh, har naji daɗi dana ganka" girgiza kai granny ta yi ta ce"kuma ka tafi da yarka ni bazan iya wannan abun nata ba" juyowa tayi ta kalli Granny sai kuma ta maƙale kafaɗa ta ce"ni wlh anan zan kwana" dariya ya yi ya ce"ai daman ba tafiya zanyi dake ba, ummanki ma ta tafi garinsu ɗazu, ta ce ba zata iya zaman gidan babu ke ba" murmushi tayi ta ce"yawwa Daddy". Nisawa ya yi sai kuma ya ce"me zaki faɗamin?, dare nayi" murmushi tayi ta ce"daman ce maka zanyi ina sonka, i love you Daddynaaaaa" waro idanu ya yi ya kama kunneta ya ce"akan wannan kika taso ni Imara?" gyaɗa masa kai tayi tana dariya, murmushi ya yi ganin yanda take farin ciki ya ce"Allah ya dawwamar miki da farin cikin nan har ƙarshen rayuwarki Baby" "Ameen" cewar granny itama tana murmushi. Har mota ta rakoshi tana murmushi ta ce"Daddy gobe ma kazo kaji dan Allah" murmushi ya yi ya ce"gobe inada abubuwa dayawa, amma in sha Allah jibi zan zo ki ganni" langwaɓar da kai tayi ta ce"Tom shikenan sai ka zo Daddy" Bye bye tayi masa shima ya daga mata hannu sannan ya shiga motarsa, saida ta daina hango motar sannan ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ta koma cikin gidan.


Washegari.

Cikin sanɗa ta fito daga ɗakin gudun kada granny ta ji ta ta ɗauki tulun ɗiban ruwa tayi waje da gudu, tana tafe tana yan waƙe-waƙenta na yan makaranta har ta ƙaraso kogin, lumshe idanu Imara tayi haka kawai taji tana ƙaunar zuwa wajen ruwan, Tsugune take bakin Kogin tana ƙoƙarin ɗiban ruwa tana jin sanda yazo ya tsaya a bayanta hakan yasa ta miƙe tana kallon fuskarsa da take a rufe ta ce" yauma ka sake zuwa ko?, wai ya sunanka?" da idanu kawai taga yana binta hakan yasa ta tura baki gaba tana harararsa ta ce"wannan kaman kurma baya magana, kai kana jina? Yayane sunanka?" Shiru nan ma taji ya yi mata ta galla masa harara ta ɗora tulunta aka tashige ta gefensa saida tayi nisa sannan ta tsaya ita kaɗai take cewa" to kodai nayi masa turanci inaga baya jin Hausa" da wannan tunanin ta koma inda yake tsaye har sannan tana kallonsa ta ce" kai what's ur name? Kanajin turanci? Ni sunana Imara gurin granny na nazo wannan ƙauyen kai ya sunanka? ko kai bature ne? nima mama ta ce inada kyau kai kaga kyan?" Ganin har sannan bai ce mata komai ba kuma bai buɗe fuskarsa ba ya sanya ta haɗe rai tana ƙoƙarin fashewa da kuka ta sanya hannunta a baki cikeda shagwaɓa take cewa"sai kai ta tsaiwa nonse kawai ni babu ruwana ma dakai aljani kawai". Shiru ya yi mata kamar rannan hakan kuma ba ƙaramin ɓata mata rai ya yi ba, dan a rayuwarta ta tsani ta yiwa mutun magana ya yi mata shiru, tulunta ta ɗauka ta harareshi sannan ta bar wajen tana tafe tana mita. A ƙofar gidan taga mota hakan yasa ta shige gidan da sauri tana murna ganin yau ma Daddynta yazo, turus tayi ganin ba shi bane, amma data hango ummarta sai ta tafi da gudu ta faɗa jikinta tana dariya, murmushi Umman tayi dukda yanda jikinta yake a sanyaye ta ce cikin sanyin murya" ɗiban ruwa kika tafi?" gyaɗa mata kai tayi tana murmushi, shafa kanta Umma tayi ta ce"tashi ki ɗauko hijab ki zo zamu tafi"


"Tafiya kuma Umma?, meyasa?, ni fa ba yau zan koma ba" kallonta granny tayi ta ce"ai zuwa zamu yi mu dawo" kasancewar Imara nada saurin fahimtar abu yasa ta ce"to me akeyi da zamu je?" murmushi Umma tayi ta ce"wani abun mamaki ne fa, kedai idan mun je zaki gani" juya kanta tayi kawai sannan ta tashi ta É—auko É—an baby hijab É—inta ta É—ora kan rigar jikinta tashi Umma suka yi ta kama hannunta suka fito daga gidan, shiga motar suka yi, ganin abokin Daddynta yasa tayi murmushi ta gaisheshi, amsawa ya yi cikin sakin fuska sannan suka bar unguwar.


# *Bestnovel*
# *Heart touching*
# *IMARA 💋*
# *Nanameera*
# *2025*.


*IMARA 💋 💋*


Mikiya writers asso...


*Chapter 18*


Motar nagama parking Imara ta fito, ɗaya bayan ɗaya take bin mutane dake tsaye a ƙofar gidan da kallo, ɗan turo baki tayi ta riƙe gefen rigar Umma kasancewar batasan taron mutane. Hannunta Umma ta riƙe suka shiga cikin gidan, cak Imara ta tsaya duk da jan hannunta da Umma ke yi, abinda idanunta suka hango mata shine ya hanata yin gaba, zare hannunta tayi daga jikin Umma ta shiga takawa a hankali idanunta kamar zasu faɗo, jikinta na rawa ta ƙarasa inda ta hangi Suhaila tsugune tana zuwa ta dafata bakinta na rawa ta ce"Mommy meya faru?, wane ya mutu?, ina Daddyna?" Wani sabon kukan ne ya kwacewa Suhaila tayi saurin kifa kanta ta shiga rera shi gwanin ban tausayi, tsugunawa Imara tayi hannunta na rawa ta riƙe gefen likkafanin, runtse idanunta tayi sannan ta yaye fuskar, wa iriyar ƙara ta saki tana yin baya, da sauri Umma ta ƙaraso ta rungumeta, ɓuya tayi a jikin Umma bakin na rawa amma ta kasa furta komai sai girgiza kanta take yi, kowa na wajen saida Imara ta bashi tausayi dan gaba ɗaya ta fice hayyacinta har aka fita da Mubarak bata sani ba.


***A hankali ta shiga buɗe idanunta wanda suka yi mata nauyi, surutu taji sama-sama a ɗakin, ta tashi zaune tana bin ƴan tsirarin mutane dake ɗakin da kallo, Umma ce ta ƙaraso inda take ta zauna gefen kujerar tana kallonta ta ce"kin tashi Imara?" jinjina mata kai tayi, sai kuma ta tashi tsaye kamar wacce aka tsikara ta ce"wajen Daddy zan je" idanun Umma ne ya kawo ruwa cikin sanyin murya ta ce"ba yanzu ba Imara, Daddy baya nan, dawo ki zauna" maƙale kafaɗa tayi kamar zatayi kuka ta ce"ni Allah wajensa zanje, abu zan faɗa masa fa, wani mafarki nayi fa Umma" kamo hannunta tayi ta ce" mafarki ƙaryane Imara, Daddy baya nan, ba sai kin faɗa masa ba, kiyi addu'a kawai" kallonta Imara tayi da dara-daran idanunta, saurin sunkuyar da kai Umma tayi saboda hawayen dake zuba a fuskarta. Shiru Imara tayi kamar mai nunanin wani abu sai kuma ta tashi ta fice da gudu daga ɗakin, tashi Umma tayi ta bita da sauri gudun kar ta yi wani wajen saidai ganin ta nufi hanyar cikin gidan yasa ta tsaya a wajen har sannan kuma bata daina kuka ba.


"Daddy!, Daddy!, Daddy!" Da idanu mutanen ɗakin ke bin ta, Suhaila ta taso tana kallonta ta ce"wa kike nema Imara?" cikin saurin baki ta ce"Mommy Daddy, Daddy nake nema, zan faɗa masa wani abu" fashewa Suhaila tayi da kuka ta kama hannun Imara tana girgiza mata kai, Mommy ce ta ƙaraso wajen fuskarta a haɗe kamar bata taɓa dariya ba ta ce"ke lafiya?, meya faru kike kuka kuma?" kasa magana Suhaila tayi sai hannun Imara data kama, saurin fizge hannun Mommy tayi ta hankaɗa Imara, kasancewar jikinta babu wani kwari yasa ta fadi a ƙasa, yarfe hannu Imara ta shiga yi hawaye na zubowa kan siririyar fuskarta. Baki buɗe Suhaila ke kallonta cikin shassheƙar kuka ta ce"Mommy mene haka?"


"Tambayata kike mene haka?, to ban sani ba!, nace ban sani ba!" Ta maida idanunta kan Imara wacce ke kallonta ta ce"abinda ya haɗa ya raba, Mubarak ya kawo ki gidan nan, babu yanda bamu yi ba mu fitar dake abu ya gagara, Yanxu kuma wanda ya kawo kin baya duniya, saboda haka babu abinda ya haɗaki da ita, ke tsintacciya ce, wacce ba'a san ma su wane iyayenki ba, kin ci albarkacin Mubarak daya kafe sai ya raineki saboda haka yanzu babu shi bakida wata alaƙa da gidan nan ko mutanen cikinsa, ke je can ki nemi iyayenki, idan kinada rabon ganinsu kenan, idan kuma a duniya aka sameki sai kema ki ɗora daga inda suka tsaya!" Tunda ta fara magana Imara ke kallonta, duk abubuwan data faɗa ta fahimta kuma ta haddacesu a ƙwaƙwalwarta, abu daya ne yake mata yawo arai, daman ba mafarki tayi ba?, da gaske Daddynta mutuwa ya yi?, saurin girgiza kanta tayi ta miƙe tsaye da niyyar fita saidai wani jiri ya ɗabeta ta fadi ƙasa sumammiya. Da gudu Suhaila ta ƙarasa ta ɗagota jikinta haka kawai taji tana tausayin yarinyar, jijjigata tashiga yi amma shiru babu alamar tana numfashi, shigowa Umma tayi Granny na biye da ita da sauri suka ƙarasa wajen Imara suka karɓeta. Ƙarasowa Mommy tayi ta janye Suhaila tana yi mata wani mugun kallo ta ce "karna sake ganin kin taɓa ta, shashasha kawai, bansan yaushe kika zama haka ba" kuka ta saka tana riƙe rigar Mommy ta ce "yarinyace ƙarama Mommy, kar wani ciwon ya sameta, me ɗawainiya da ita ma kaɗai duniya ne, dan girman Allah ki sassauta mata, Mubarak baya nan, bana jin haushin yarinyar nan ko kaɗan wlh, na tabbata zai yi farin ciki idan yaji na kula da rayuwarta bayan ransa kuma..."


"Ki kula da wa?, hala hauka kike yi?, a matsayinta na wa zaki kula da ita?, yar ki ce?, ko ƴar mijinki ce?, ko ƙanwarki ce?, to bari ki je keda yarinyar nan har abada wlh!" Tana kallon su Granny ta nuna su da yatsa ta ce


"Ku É—auketa daga nan, sannan kuma har abada karna sake ganinta, nan gidan bana Mubarak bane, gidan mijina ne ya basu aro su zauna, kuma yanzu ya mutu saboda haka dole ta bar cikin gidan nan, tunda ba yar sa ba ce, batada gadonsa, ke koma tanada shi to wlh ba za'a bata ba, balle ma tsintacciya ce mara asali da tushe, shima Mubarak É—in dan Suhaila ta matsa sai ta aure shi ne amma kwata-kwata ni ba yimin ya yi ba, kuma shima bashida wasu dangi wanda zai nuna ya ce nasa ne, wama ya sani ko a abokan nasa wani ya kashe shi. Dan haka ku tattara yanzu ba sai anjima ba ku bar gidan nan, Allah ya raka taki gona" banda kuka babu abinda suke yi, domin babu kalar cin mutuncin da Mommy bata yi musu ba, basu kaÉ—ai ba harma Mubarak É—in, tana yi yan uwanta na tayata.


Girgiza kai Granny tayi tana kallonta ta ce"babu komai Hajiya, riƙonma da ya yi mata Allah ya saka da Alkhairi, daman ba dolensa ba ce, amma zan so ki bari ayi sadaƙar uku sai mu tafi da ita, ko ba komai nasan akwai ƙawayenta wanda zasu zo yi mata ta'aziyya, idan bata nan ba zasu samu damar ganinta ba, ki yi mana wannan alfarmar" tsaki Mommy tayi cikeda masifa take faɗin


"Ke ɗin banza, wlh yau kuma a yanzu sai kun fita daga cikin gidan nan, ku ba danginsa bane, kai ko ku danginsa ne zan iya korarku tunda ba gidansa bane, saboda haka yanzu ku ɗauketa ku bar cikin gidan nan, tun kafin nasa a naɗa muku duka kuma sannan na koreku" murmushin takaici kawai granny tayi ta ƙarasa inda Umma ke tsugune da Imara tayi mata alama data tashi, tashi Umma tayi ta goya Imara a bayanta suka yi waje, da sauri Suhaila ta biyo su Mommy tayi saurin riƙeta tana harararta, cikin kuka ta ce"wannan ba daidai bane Mommy, dan girman Allah ki bari naje inda suke, ki bari ko numbern wayarsu na karɓa, idan ta tafi babu yiwuwar na sake ganinta har ƙarshen rayuwata"


"To sai me idan baki ganta ba?, na ce sai me?, ai daman ba dolenki ba ce ita, bakuda wata alaƙa wacce zaki ce dole sai kin sake ganinta a rayuwa, wlh bazan bari ku sake haɗuwa ba Suhaila kinji har na rantse miki!"


Zubewa ƙasa tayi ta fashe da wani raunataccen kuka, Mubarak ya tafi ya bar baya da ƙura, ya rabu dasu a lokacin da suke tsananin buƙatarsa, ya fara aiki da ƙareshi saidai Allah, ya tafi ya bar su marayu.


***A ƙofar gidan suka tsaya Umma ta kalleta ta cikin kuka ta ce"yanzu mu kaita asibiti daga nan sai ku wuce gida, zan nemo bayanai wanda zai ɗebo kayanta" kasa magana granny tayi sai kuka ta dake kamar ƙaramar yarinya, tausayin rayuwar Imara take, duk wanda ta riƙe shi a matsayin majingina sai ya rabu da ita, mutuwa nayi mata yankan ƙauna, ta gamu da jarrabobin rayuwa tanada ƙananun shekaru, Allah ne kaɗai yasan abin da ya shiryawa rayuwarta. Tana wannan tunanin ya ƙaraso gabansu da mamaki ya ce


"Umma ina kuma zaku je?, daga kai shi ƙabari?" cikin sanyin murya ta ce"Bashir asibiti zamu kai Imara ta suma ne, ko zaka taimaka ka kai su a motarka, ni zan samu ɗan dako ne" "ɗan dako kuma?" ya maimaita yana kallonta, miƙa masa Imara tayi ba tareda ta sake cewa wani abu ba ya karɓeta ya sakata a mota, Granny ta shiga sannan suka bar ƙofar gidan. Wani private hospital ya kai su a Dutse bayan likitoci sun dubata suka tabbatar da ta kamu da ciwon zuciya saidai bai yi ƙarfi sosai ba, iyaka tashin hankali Granny ta shige shi tayi kuka kamar ranta zai fita, tausayin yarinyar ya cika mata zuciya, a daddafe suka yi kwana uku kafin ta dawo hayyacinta saidai har sannan bata cewa komai sai kallo da idanu, a haka aka sallame su kai tsaye kuma Daƙayyawa suka shige.


One week later (bayan sati É—aya)
10:29am

Fitowa tayi daga ɗakin hannunta riƙe da tsintsiyar laushi da alama shara tayi, kallonta Granny tayi ta saki baki ganin yanda ta zubawa abincin idanu, ajiye tsintsiyar hannunta tayi ta ƙarasa gabanta tana kallonta ta ce"Imara meyasa baki ci abincin ba?" shirin da taji tayi mata yasa ta taɓa ta a firgice ta kalleta, girgiza kai Granny tayi ta ce"ba na hanaki tunani ba?, so kike sai wani ciwon ya sameki wanda zai dame mu?" kallonta Imara tayi da idanunta wanda suka faɗa, gabaɗaya ta rame ta zama so silent kamar ba ita ba, cikin sanyin murya ta ce"Granny da gaske Daddyna ya rasu?, ya ce min zai dawo shine ya tafi ya barni?, granny ina iyayena?, meyasa Mommy ta ce min tsintacciya?, me nayi granny?, wane..." Tari ne ya turnuƙeta, da sauri Granny ta miƙo mata ruwa girgiza kanta tayi tana cigaba da tarin ta, kallonta granny tayi gwanin ban tausayi ta ce"da gaske Daddynki ya mutu Imara, amma ki sani hakan ba wai yana nufin dan kin yi wani abu bane, koda da tasa ƙaddarar, kuma yanda Allah ya hukunta maka haka zaka rayu, Allah ya yi ba zaki tashi da iyayenki ba shiyasa ya ɗaukesu tun kina ƙarama, kada kiyi fushi, ki cigaba da addu'a watarana sai labari, rayuwarki zata zama abar sha'awa ga kowa in sha Allah IMARA!" Kwanciya tayi akan cinyar Granny ta shiga sauke ajiyar zuciya a jere, shafa kanta Granny ta shiga yi zuciyarta fal tunanin mafita a haka har ta fara jin saukar numfashinta alamun bacci ya ɗauketa. Gyara mata kwanciyar tayi kasancewar lokacin ana zafi yasa bata shiga da ita ɗaki ba, sun ɗauki lokaci mai tsawo a haka kafin ta tashi ta koma ciki dan ƙarasa aikin da ita, tana tashi Imara ta buɗe idanunta, kamar wacce aka tsikara haka ta miƙe tsaye duk da jikinta babu kwari ta fice daga gidan.


# *Bestnovel*
# *heart touching 💔*
# *IMARA*
# *2025*
# *Nanameera.*


*IMARA 💋 💋*


Mikiya writers asso...
Chapter 3 · 0% Book details