Chapter 12
Imara Part 1 Complete Hausa Novel · about 56 min read
Wani irin abu ne ya tokarewa Imara a ƙirjinta, batasan sanda ta saki takardar hannunta ba, gaba-daya jikinta rawa yake, runtse idanu tayi wasu zafafan hawaye suka fara sintiri kan fuskarta. Batasan sanda ta silalo daga kan gadon ba ta yi zaman dirshan a ƙasa, wani zazzaɓi ne ya rufeta wanda yakeda nasaba da abinda idanunta ya gani, dafe ƙirjinta tayi jin yadda zuciyarta ke wani irin bugu daya zarce misali, ƙoƙarin take tayi kuka amma bakinta ya gagara, hawayen ma ya ƙafe daga idanunta, sai bin ɗakin take da kallo tamkar wata zararriya.
"Mamah wai..."
Turus ya yi ganin wata kyakkyawar budurwa zaune ta zubawa kofar idanu, bai san da zuwan Imara gidan ba hakan yasa shi yayi mamakin ganin fuskar da bai sani ba a ɗakin Mamah. Ƙarasawa ya yi yana kallonta ya ce"Hyy, where is Mamah?" jin tayi shiru yasa ya ɗan haɗe rai yana zare idanu ya ce"kee..baki jina ne?" Shirin da yaji ta sake yi masa ya sanya ya ƙarasa dab da ita ya taɓa ta, ga mamakinsa sai yaga ta tafi luu ta faɗi ƙasa sumammiya. Saurin ja da baya Khalil ya yi ya shiga girgiza kansa daidai nan Mamah ta buɗe kofar ɗakin ta shigo da mamaki take kallonsa sai kuma ta kalli Imara wacce ke kwance ƙasa tamkar tana bacci, cikin hanzari ta ƙarasa gabanta ta shiga jijjigata amma shiru babu alamar tana jin abin da take cewa. Tashi Mamah tayi ta fice daga ɗakin ba tare da ta sake bi ta kan Khalil ba, tana fita ya koma inda Imara ke kwance ya tsugana ya zuba mata idanu
"Woww Beautiful"
Khalil ya samu kansa da furta hakan yana sakin wani yalwataccen murmushi, ya saba ganin kyawawan ƴan mata amma bai taɓa ganin mai kyau irin Imara ba. Yana cikin wannan tunanin ta buɗe kofar ta shigo ta dawo inda take, not too long shima ya shigo ɗakin yana sanye da wata jallabiya ash colour, gaba-daya gashin kansa ya rufe fuskarsa da alama daga wanka ya fito dan babu alamar gyara a kan nasa. Tafiya yake a hankali kamar ba wanda aka yiwa reporting ciwo ba
"Abaan mene haka?, bakaga halin da take ciki bane?"
Bai ce komai ba sai hannunsa daya sanya ya ɗan hargitsa gashin kansa kafin ya tsugana daidai inda take, hannunsa ya kai ya taɓa wuyanta, ya yi kamar zai mike tsaye sai kuma ya sunkuya ya ɗauketa tamkar Baby ya yi waje da ita.
*45, Zaria road Kaduna*
***Zaune take gefen gadon ta zubawa kanta idanu, wayarta ce ta shiga ringing ta kalli wayar ta taɓe baki ta cigaba da kallon fuskanta, saida akayi 4missed calls kafin ta ɗauki wayar ta sanyata a flymode ta yi cilli da ita kan gadon. Turo kofar ɗakin akayi wanda ya sanya ta juya dan ganin wanda ya shigo mata ɗaki, murmushi ta sakar mata tana ƙarasowa ta ce"har yanzu shirin ne baki gama ba?, Kin fison sai babanki yazo yana jiranki ko?" mikewa tsaye tayi tana gyara zaman veil din jikinta ta ce"nafa gama Mom" numfasawa tayi ta ce"yanzu sai yaushe?" langwaɓar da kanta tayi ta ce"ke da kika koreni, wlh saina daɗe ban zo Kd ba" murmushi Mom tayi ta ce"Allah ya huci zuciyar Mamana, ba korarki nake ba, halin mahaifinki nasani banason ya yi miki faɗa ko ya yiwa mahaifiyarki shiyasa amma ke kinsan I'm gonna to miss you alot" rungume small Mom ɗin tata ta yi tana turo baki ta ce"me too Mom" shafa bayanta tayi ta ce"muje kar kuyi missing flight.
Tsaye suke a farfajiyar gidan, "A'isha! A'isha" juyowa tayi ta kalleta ta ce" lafiya dai?" Murmushi tayi tana kallon yar uwar tata ta ce"yau Aunty Jidda zata koma Kano fa" wani tsalle A'isha tayi ta rungumeta tana dariya ta ce"kai amma naji daɗi, alhamdulillah, mun rabu da jaraba in Sha Allah ba zata sake dawowa gidan nan ba" buɗe baki tayi zata yi magana taga ta fito tana jan troley dinta, sanye take da wata doguwar rigar Egyft Abaya coffee colour ta sanya wani sun glasses a idanunta hannunta ɗaya riƙe da hand bag ɗinta sai taunar cew gum take. Ta gabansu ta zo zata shige suka kalleta ba tare da sun ce mata ko a dawo lafiya ba suka shige cikin gidan, yanda basu nuna sun ganta ba haka itama bata nuna ta gansu ba kanta tsaye ta shige bayan mota driver ya jata zuwa Airport.
*Kano state*
Murmushi Mamah tana kallon Jadda bata ce komai ba. Riƙe haɓa Jadda tayi tana ƙanƙance idanu ta ce"au sallamammiya kika mayar dani ko me?, Ina faɗa miki abin da matar nan tayi min amma kina min dariya? Eh lallai! bari shi wanda na isa dashi ɗin ya dawo, wlh sai na saka ya saketa idan batayi wasa ba". Girgiza kai Mamah tayi cikin cool voice ɗin ta kamar koda yaushe ta ce"ki dai yi hakuri Jadda, maybe gajiyar tafiya yasa bata zo ta gaisheki ba"
"Babu wani gajiya rashin arziki ne irin nata, kuma zata san dani take zancen ba dai É—ana take aure ba!" Jadda ta faÉ—a cikin faÉ—a, Ita dai Mamah bata sake cewa komai ba gudun kada itama tayi wani laifin.
A hankali ta shiga buɗe idanunta wanda suka yi mata nauyi, ɗakin da take ta ƙarewa kallo kafin ta fara yunƙurin tashi zaune, kallon hannunta tayi taga an saka mata drip a hankali memeries ɗin abin da ya faru ya fara dawo mata, wani irin raunataccen kukane ya kwace mata ta shiga rareshi kamar ƙaramar yarinya, saida tayi mai isarta sannan ta tashi da niyyar fita daga ɗakin daidai nan ya buɗe wata ƙofa ya shigo, kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kai ya nufi gaban gadon, drip din hannunta ya cire sannan ya ɗago yana kallonta, saurin ɗauke kanta tayi wasu hawayen na biyo fuskarta. Taɓe baki Abaan ya yi bai sake bi ta kanta ba ya juya ya fice daga ɗakin gabaɗaya. Da idanu Imara ta bishi sai Kuma ta sake fashewa da wani sabon kukan tana bubbuga ƙafa.
***Da gudu ta tawo ta rungume mahaifiyar tata tana murmushi ta ce"Mom nayi missing naki" murmushi itama tayi ta ce"nima haka Jidda, ya hanya?" Bata ba ta amsa ba sai kallon ƙofar ɗaya apartment ɗin da take, ganin abun take kamar a mafarki hakan yasa ta kasa ƙarasawa gurinsa ta juyo ta kalli Mom tata bakinta na rawa ta ce"Momm...Mom ya Abaan ya dawo?" wani kallo Mom ta watsa mata kafin ta ce"yadawo mana, mene haɗinki da dawowarsa?, ko har yanzu akwai wani abu a zuciyarki ne?, karki fara cewa zaki yi abin da zai sakani a bakin duniya Jidda, ki fita harkarsa a daina yi mana kallon waɗanda basu kai ba idan kuma ba haka ba..." Sakar baki Mom tayi ganin Jidda tayi hanyar Apartment din Babu ma alamar tana sauraren abin da take faɗa.
"Jidda! Jidda!"
Tamkar ba ita da ita take magana ba dan ko juyowa bata yi ba ta shige apartment ɗin, tsabar takaici kasa motsi Mom tayi ta dinga kallon ƙofar ko zata ga Jidda ta fito amma shiru babu labarinta
"Mom lafiya?, ina Jiddah?"
Kallonta tayi bata ce komai ba, ta juya ta bar wajen, da idanu Suhaila ta bita sai kuma ta ɗaga kafaɗarta irin bai dameta ɗin nan ba tayi waje tana riƙe da car key ɗinta. Kai tsaye Jidda sama ta haye dan babu kowa a parlon kasancewar lokacin duk suna gurin aiki, ƙofar dakinsa ta buɗe ta shiga bakinta ɗauke da sallama, shiru taji da alama ma baya ciki, dan haɗe fuska tayi s shagwaɓe ta ce"ina kuma yaje to?" Juyawa tayi zata fita taji an buɗe ƙofar bedroom ɗin an fito, da sauri ta juyo bakinta ɗauke da murmushi saidai abinda ta gani yasa ta yi saurin haɗe fuska kamar ba ita ba, kallonta Imara tayi da idanunta wanda suka kumbura saboda kukan data sha bata ce mata komai ba ta zo zata shige ta gefenta. Kasa jurewa Jiddah tayi ta jawo rigarta tana watsa mata wani banzan kallo ta ce
"Hyy, what brought you here?, Ina mai ɗakin yake?" Kallonta kawai Imara ta yi badan batasan abin da ta ce ba, yin shirun nata ya sake ɓatawa Jiddah rai cikin masifa ta ce"keeee! Wane ubanki a garin nan da har ina yi miki magana kina jina?, me kike taƙama dashi?" Numfasawa Imara ta yi ta sake yunƙurin fita a karo na biyu, a fusace Jidda ta jawota kafin tayi aune ta sauke mata wani lafiyayyen mari daidai nan Abaan ya buɗe ƙofar ɗakin ya shigo, da idanu ya shiga bin su Jidda tayi saurin ƙarasawa inda yake tana murmushi ta ce"Yaya daman ka dawo?" kallonta ya yi bai ce mata komai ba, tasan me yake nufi hakan yasa ta haɗe ranta tana kallon Imara wacce ke tsaye hannunta ɗaya bisa kuncinta ta ce"wai ina yi mata magana tanaji tayi min banza, kasan ni kuma bana ɗaukan raini" ta ƙarashe maganar tana haɗe hannayenta a ƙirji. Kallon Imara kawai ya yi sannan ya kalli Jiddah cikin cool voice ya ce"get out" kallonsa Jidda ta yi nan da nan hawaye ya kawo idanunta ba ta ce komai ba ta juya ta fice daga ɗakin tana banko ƙofar, girgiza kansa ya yi kawai sannan ya ƙaraso gabanta, wuyanta ya taɓa yaji sanyi klao da alamar zazzaɓin ya sauka,
"Je ki wajen Mamah ta baki abinci"
Abin da kawai ya faÉ—a kenan ya shige bedroom É—insa, da idanu Imara ta bishi kafin ta juya ta fice daga É—akin har sannan hawaye bai bar zuba daga idanunta ba.
Mamah na zaune kan kujera idanunta maƙale cikin glasses tana kallon show ɗin da ake haskawa a TV Jiddah ta sakko daga saman, da idanu ta bita har ta ƙaraso gabanta ta tsuguna
"Mamah ina yini"
"Saukar yaushe Hauwa'u?"
Ɗan murmushi Jiddah ta yi ta ce"zuwana kenan, shine naga motar Ya Abaan na biyo shi" jinjina kai Mamah ta yi ta ce"toh sannu da hanya yasu Jamilan?" "Suna nan klao Alhamdulillah, Ina Jadda?" Murmushi Mamah ta yi ta ce"tana ciki, tunda ta dawo taki komawa apartment ɗinta" dariya Jidda ta yi ta ce" Jadda rigima, let me take shower sai nazo na gaisheta" okay Mamah ta ce Jidda ta tashi ta fita. Abbiey ne ya sakko daga cikin shigarsa ta manyan kaya kamar koda yaushe, kallonsa Mamah ta yi ta ce"yau ka makara yallaɓai" rollex ɗin hannunsa ya kalla ya ɗan yi tsaki ya ce" ban san time ya tafi haka ba, ina Abaan yake?" tashi Mamah ta yi ta ce"yana ciki, kasan halinsa dai, maybe jira yake hutun daya ɗauka ya ƙare ya koma bakin aiki" girgiza kai Abbiey ya yi ya ce"no munyi magana dashi ai, ya ce yanason a gama komai na asibitin ne kafin ya koma Abuja so kinga dole a sake bashi lokaci" numfasawa Mamah ta yi ta ce"Jadda na nemanka tun ɗazu" dafe kansa ya yi ya ce "ya rabb, har zan manta na fita" "ai kuwa da ka dawo yanzu" ta faɗa tana murmushi, girgiza kansa ya yi shima yana murmushin ya yi hanyar part ɗin da take.
Yana barin wajen Imara ta sakko tana tafe a hankali, kallonta Mamah ta yi ta ce "daughter kin tashi?" jinjina mata kai tayi dan bakinta yayi nauyi, kama hannunta tayi tana kallon fuskarta ta ce"lafiya?, me ya sami fuskarki?, who slapped you?" girgiza kai Imara tayi tana aro dauriya gudun kada tayi kuka ta ce "babu kowa, bigewa nayi" shiru Mamah ta yi ba dan ta yarda da abin da ta ce ba, sai dan batasan ƙureta,
"Muje kiyi breakfast"
Girgiza kai tayi ta ce"na ƙoshi yanzu" haɗe rai Mamah ta yi ta ce" da kika ci me?" sunkuyar da kanta ƙasa tayi tana wasada fingers ɗinta, tallafo habarta Mamah ta yi ta ce"ki daina ɓoyemin komai, muje ciki Inason magana dake" kallonta Imara tayi hawaye na taruwa a cikin idanunta ta ce"Tom Mamah".
***Zaune ya sameta tana jan cazbaha saida ya bari ta idar sannan ya gaisheta,
"Jadda lafiya kike nemana?" Girgiza kai Jadda ta shiga yi tana kallonsa ta ce"wai kamarni! Kamarni za'a yiwa irin haka ko?, kana sane da matarka bata zo ta gaisheni ba tunda na dawo daga asibiti?, yau ko zaman kafurci muke da ita ai ya ci tazo ta dubani ko?, amma wlh matar nan shiru bata zo ba, ina jin sanda suka dawo daga bikin amma ta kasa shigowa ta cemin sannu ya jiki, haka ake rayuwa Fadeel?, an kyauta min kenan?, haka taga Fatima nayi?, kullum cikin ɗawainiya take dani yarinyar nan bata taɓa gazawa ba, shine ita zata dinga wulaƙantani?, me nayi mata?, me na mata Eh?!..." Ta ƙarashe maganar tana goge hawaye da hijab ɗin jikinta. Shiru Abbiey ya yi na wasu sakkani, gabaɗaya ransa ya gama ɓaci koda wasa bai yi tunani bata zo ta duba mahaifiyarsa ba, duk da tasan abin da ya sameta, a hankali ya kamo hannunta cikin son kwantar mata da hankali ya ce "dan Allah Jadda kiyi haƙuri, zan yi mata magana, kuma in sha Allah hakan ba zata sake faruwa ba, zan sanda yanda zanyi da wannan matsalar, amma kar ki damu kanki wani ciwon ya sake kamaki kamar da, kiyi mani wannan alfarmar" jinjina masa kai tayi ta ce "babu komai, ni kawai faɗa maka nayi, amma ban riƙe kowa a zuciyata ba" ajiyar zuciya ya sauke ya ce"Nagode Jadda, bari naje" "Allah ya tsare ka, ya yi maka albarka, ya kula dakai da yaranka" murmushin jin daɗi ya yi ya ce"Ameen ya rabbi Jadda".
***A fusace ta buɗe ƙofar parlon tana zuwa ta faɗa kan mahaifiyar tata tana fashewa da kuka, girgiza kai Mom tayi cikin ɓacin rai ta ce"dana gargaɗeki ai baki ji ba Jiddah, kinyi tunanin ko ya sauya ne?, da dai Abaan ya so ki amma tuni aka shiga tsakaninku, saboda haka tun wuri na faɗa miki ki fita hanyarsa!, ki daina zuwa in da ma yake kada ke ma ayi miki wani mugun abun" cikin shassheƙar kuka ta ce"wlh Mommy ina son Abaan kuma ni shi xan aura, wlh shi nakeso, shine wanda zuciyata ta zaɓa mini kuma zaɓinta zan bi, ki taimakeni Mommy, ki taimaka!" Ta ƙarashe maganar tana sake rushewa da wani sabon kukan, shiru Mommy tayi dan abun nema yake yafi ƙarfinta, tsayin lokaci tana neman yanda zata raba wannan al'amari amma abu yaƙi yiwuwa, tana cikin wannan tunanin ya buɗe ƙofar ya shigo, da sauri Jiddah ta tashi ta shiga goge hawayen fuskarta ta tsuguna kanta a ƙasa ta ce "ina yini Abbiey" saida ya ƙare mata kallo sannan ya ce"lafiya klao" daga haka ta tashi ta shige ciki.
"Yanzu abinda kika aikata daidai kenan?, mahaifiyata ita ce abar rainawarki?, daga ke har yayanki babu wanda ya iya zuwa ya gaisheta?, kunsan kuma batada lafiya daga jin ya ta dawo, to bari kiji idan har kina son zama cikin gidan nan ƙarƙashina to dole sai kin girmama mahaifiyata, idan kuma ba haka ba wlh zan ɗauki mummunan mataki akan ki, zaki san dani kike!" Yana gama faɗar haka ya juya ya fice daga ɗakin kamar zai tashi sama, da idanu Mommy ta bishi sai kuma ta taɓe baki
"Allah na tuba matar da ba son ganina take ba me zan je yi mata?" Ta faÉ—a a fili tana danna wayarta.
***Kallonta Mamah tayi ganin yanda jikinta ke rawa ta ce"nutsu Imara, faɗamin me yake faruwa, me kika yi masa ya sake ki?" Batasan sanda ta faɗa jikin Mamah ta fashe da wani raunataccen kuka mai taɓa zuciya ba, kuka take irin mai fitowa tun daga ƙasan zuciya, kukane wanda ke nuna zallar damuwar da take ciki, kuka ne irin wannan ke nuna komai ya ƙare min a rayuwa, yanda take jan numfashinta yasa Mamah tayi saurin rungumeta tana shafa kanta
"Ma...Mamah...ya sakeni,. Maheer ya sakeni, baya sona, meyasa Mamah?, me nayi masa?, ya yimin laifi kala-kala amma na haƙura, meyasa shi ba zai iya haƙura ba idan nayi masa laifi?, ni kawai son sa nake Mamah, amma shi kuma ya faɗa min baya sona, meyasa!, meyasa Mamah!!, wlh bani na kashe Ameer ba!, ban kashe shi ba Mamah!, meyasa zan kashe Ameer bayan shine wanda ya ƙaunaceni a lokacin da kowa ya juyamin baya?, meyasa zan kashe mutumin da al'umma ke maraba da samunsa a cikinsu?, bazan iya kashe koda ƙwaro ba ballantana mutum kamar Ameer, bani ba ce! Wlh ban aikata ba Mamah!, ban kashe Ameer ba!, nima inason Ameer!, IMARA nason Ameer, amma ya mutu, ya mutu ya barni a wannan duniyar me cike da ruɗani da tashin hankali, wlh bazan iya ba, so nake na mutu Mamah!, mutuwa nakeso, kowa ya mutu ya barni, na rasa Mama, na rasa granny, narasa Dodona, na rasa Maheer, na rasa Ameer, banida kowa! Banida kowa Mamah!..."
Wasu zafafan hawayene suka shiga sintiri kan fuskar Mamah, duk da batasan labarin Imara ba amma tayi matuƙar tausaya mata, shekarunta sun yi kaɗan wajen ɗaukar waɗannan matsalolin, rayuwarta abar tausayawa ce, wa ta kashe?, wani irin tashin hankali ne ya saukarwa Mamah, ta ɗago fuskarta tana goge mata hawayen ta ce" tell the truth Imara, wace ke?, me ya sami rayuwarki?, bani labari!" Lumshe idanunta tayi wasu hawayen suka sakko mata ɗan ƙaramin bakinta wanda ya yi jajur dashi duk ya jiƙe ta shiga buɗewa cikin wani irin yanayi ta ce" zan baki labarina Mamah, zan sanar dake abin da ya sameni da kuma irin tawa ƙaddarar".
# *Bestnovel*
# *Heart touching 💔*
# *IMARA 💋*
# *Nanameera*
# *2025*.
08106608363.
*IMARA 💋💋*
Mikiya writers asso.
*Chapter 13: The beginning*
*17yrs ago, 7:30pm*
*Daƙayyawa, Jigawa state*
Drivern yake hankalinsa kwance, gefensa wata kyakkyawar balarabiya ce hannunta riƙe da yar ƙaramar yarinya mai kama da ita sak, murmushi ya yi yana kallonsu ya ce"da alama kin fi son yarinyar nan dani ko?" girgiza masa kai tayi tana kwaɓe fuska ta ce"kaiii! Janaan, wlh ba haka bane kai ma kasan ina sonka ai" yanayin maganarta zai tabbatar maka da ba asalin bahaushiya ba ce, murmushi ya yi ya ce"ni na isa na ce baki sona?, cewa nayi kin fi son yarki yanzu akaina" rau-rau tayi da idanu kamar zata yi kuka ta ce"to tunda hakane ka karɓeta ai kai ma naga yarka ce" ta faɗa tana turo masa baki, tuntsirewa ya yi da dariya yana kallonta ya ce"au hakama zaki ce?, bari mu ƙarasa sai na karɓeta." Har suka ƙarasa ƙauyen hira suke basu yi shiru ba, bayan ya yi parking ya karɓi yarinyar ya ɗagata sama yana kallonta ya ce"kinsan me?, diz girl dake kawai take kama wlh, ni bata yo ni ba" dariya tayi ta ce"na fika ƙarfin jini shiyasa" harararta ya yi bai sake magana ba su kayi sallama cikin ɗan ƙaramin gidan, tarba sosai tsohuwar matar tayi masu, bayan sun ci abinci ya kalleta fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce "Granny kin fara tsufa fa" daƙuwa tayi masa da hannu ta ce"ka ji min ɗa, to bazan tsufa ba kake nufi ko me, dan ma inada tsawon rai ne, kalli fa mahaifiyarka ta rasu ta barni, Allah dai ya jiƙanta da Rahama" jikinsa a sanyaye ya ce"Ameen ya rabbi" kallon matar tasa tayi ta ce"banda ikon Allah kaje ka auro balarabiyar mata, kai Ahmad kanada ɗaukowa kai, ita kuma ta bar iyayenta ta biyo ka!" Haɗe ransa ya yi sanin halinta ya ce"wai granny mene haka?" Hannunta ta ɗora a bakinta ta ce"tuf! tuf, babu ruwana" murmushi Madiha tayi tana kallon granny, yarinyar hannunta Granny ta kalla ta washe baki tana dariya ta ce "a'a kaga ƴar Baba, yama sunanta?" "IMARA" Madiha ta faɗa tana murmushi, karbar ta Granny tayi tana yi mata wasa ta ce "yo ai sunan ne irin naku, ni ina zan wani riƙe" girgiza kai Kawai ya yi bai sake cewa komai ba. Sai bayan magrib sannan suka ɗauki hanyar dutse, kafin suke gida har anyi sallar isha.
***Shigowa ɗakin tayi bakinta ɗauke da sallama, amsawa ya yi yana cigaba da abin da yake, ƙarasawa gabansa tayi ta haɗe rai, ɗagowa ya yi ya kalleta sai kuma ya yi murmushi cikin sakin fuska ya ce"wai me aka yiwa matar ne?" kamar zatayi kuka ta ce"ni wlh sai na bika" riƙe ƙugunsa ya yi kamar mace ya ce"dan Allah ki bar maganar nan, Granny fa kawai zan mayar gida, beside kuma dare ya yi fa, sannan kinsan Imara batajin daɗi ai bai kamata ki fita ba, ki bar maganar please!" Tsura masa idanu tayi ba ta ce komai ba sai hawaye da ya kwanta a kurmin idanun, tausayi ta bashi sanin cewa ta bar nata dangin saboda kawai tayi rayuwa tare dashi, numfasawa ya yi ya ce"shikenan ɗauko veil ɗin ki" sai a sannan hawayen ya samu damar sauka a kan fuskarta, kamo hannunta ya yi cikin sanyin murya ya ce" to kuma ba nace ki zo muje ba, mene na kukan?" Ya goge mata hawayen ya ce"shirya ki fito maza" ya fice daga ɗakin, da kallo ta bisa sai kuma ta shiga shiryawa, saida tagama tsaf sannan ta gyara Imara. Tashi tayi ta buɗe wardrobe ta ɗauko wani ɗan box a can ƙasan kayanta, buɗewa tayi ta zaro wata sarƙa ta diamond sai sheƙi take, wasu zafafan hawayene suka shiga sintiri kan fuskarta haka kawai taji tana missing rayuwarta ta da, above 5mins kafin ta goge hawayen ta dawo inda Imara ke zaune tana wasada fingers ɗinta lokacin tana wata na sha biyar, da haihuwa, kallonta tayi sai kuma ta yi murmushi ta saka mata sarkar a wuya. Sosai sakar tayi mata kyau duk da cewa tayi mata yawa, ɗaukanta tayi ta mata kiss sannan ta ajiyeta tana dariya ta ce" yar kyakkyawar ƴata".
**Fitowa tayi hannunta ɗauke da Imara, ta shirya cikin wata Abaya black colour, kallonta ya yi yana murmushi ya ce"enyeee kinyi kyau" dariyar ta mai kyau tayi ta ce"kaima haka" Granny ce ta fito tana kallon su bata ce komai ba, kallonta ya yi ganin bata shirya ba ya ce "Granny wai na ganki haka dare fa ya yi, gobe fa da safe zamu tafi Abuja Kinga babu tym ɗin da zan kai ki gida" harararsa tayi ta ce"to ni bansan hanya bane?, nafasa tafiya yau ɗin sai gobe wlh" sakar baki ya yi yana kallonta Madiha tayi murmushi ta ce"yawwa Granny daman wlh banason ki tafi, ki zauna ki cigaba da bani labarin" washe baki tayi ta ce"kaji ƴar gari, shine zai kaɗani ya ce na tafi gida to bazan tafi ba" girgiza kansa ya yi ya ce "nifa Granny ban koreki ba, cewa kikayi yau zaki tafi, shine nikuma zan kai ki amma Allah ya baki haƙuri ya kaimu goben da rai da lafiya" Ameen " tayi saurin faɗa. Tashi ya yi ya ce"bari naje zanyi magana da guards ɗin nan" "Tom yallaɓai sai ka dawo" jinjina mata kai ya yi sannan ya yi waje, karɓar Imara tayi tana murmushi ta ce "ke ƴar gidan soja, gaki kyakkyawa dake tubarkallah Masha Allah shiyasa babanki ya maƙalewa babarki sai ya aureta dan ya haifi irin kyau, duk da dai shima da kyansa" tuntsirewa da dariya Madiha tayi ta ce"hajya Granny tamu, bari naje ciki ina zuwa" toh ta ce mata sannan ta shige apartment ɗin da aka bata.
*Around 3am*
A hankali ta shiga buɗe idanunta, duhu sosai ɗakin hakan yasa ta kunna bedside lamp ta shiga kallonsa, baccinsa yake hankali kwance tashi tayi ta shige banɗaki ta ɗauro alwala ta dawo ta fara gabatar da sallolinta na dare, kamar wacce aka tsikara haka ta tashi ta buɗe wata ƙofa, ta shiga wajen tana hango ƙasan gidan, sosai tayi mamaki ganin duk tarin securities ɗin gidan babu kowa, sake matsawa tayi without making any sound, saurin toshe bakinta tayi ganin wasu mutane sun rufe fuskokinsu da baƙin kyalle sai janye ragowar securities ɗin dake bacci suke, buɗe ƙofar tayi a hankali ta koma ɗakin da gudu ta ɗauki wayarta da niyya kiran jami'ai, text message ne ya fado tasa wayar da wata unknown number
_Major Ahmad how far?, na turo maka saƙo gidanka fatan zaka karbesu hannu bibbiyu._
Sakin wayar ta yi ta shiga kiran sunansa tana kuka, cikin tashin hankali ya farka yana kallonta ya ce"Madiha lafiya?" Wayar data faɗi ƙasa ta shiga nuna masa hannunta na rawa, ɗaukan wayar ya yi ya karanta sakon ya yi saurin miƙewa tsaye, hanyar fita ya yi tayi saurin riƙe shi tana kuka kasa ƙasa ta ce"ba wannan ne abun ji ba, yarmu Janaan, kar wani abun ya samu IMARA, dan Allah kayi wani abun" riƙe hannunta ya yi yana jinjina mata kai ya ce"in sha Allah babu abin da zai sameku duka" waje ya yi tana biye dashi, ƙofar parlon farko suka ji ana ƙoƙarin buɗewa ta sake fashewa da kuka ta ce" ka zo muje wajen Granny, kar wani abun ya same su, ta tafi da Imara Major!" girgiza mata kai ya yi ya ce"dare ne fa Madiha, kikasan abun da zai same su idan suka fita?, karki manta ni jami'i ne dole na kare iyalina" girgiza kanta tayi tana kuka ta ce"duk da haka nidai bari naje" jin sun buɗe ƙofar farko yasa tayi apartment ɗin granny da gudu, bashida wani zaɓi wanda ya shige ya bita. Tashin Granny sukayi cikin tashin hankali miƙewa tayi tana salati, goya mata Imara tayi tana kuka ta ce"dan Allah Granny ki kula min da ita, karki bari tayi kuka a rayuwa, ku bar garin nan, indai suka san da ita zasu kasheta, ku tafi dan Allah" kuɗi ya miƙa mata a jaka cikin rauni ya ce"Granny ku tafi, akwai ƙofa ta baya ku bi ta can, ki kula da *IMARA* ki kula da ita, idan Allah ya yi zamu sake haɗuwa a rayuwa, idan kuma bai yi ba ki sanar da ita iyayenta na ƙaunarta" kuka ta saka tana kallonsu ta ce " me yake faruwa ya'yan nan?, ku ina zaku je?" "Babu lokacin wannan maganar Granny muje na raka ku" Madiha ta faɗa tana riƙe hannun Granny. Fitowa suka yi daga ɗakin suka shiga wani lokacin har sun buɗe ɗaya ƙofar sun baza suna nemansu, buɗe musu ƙofar tayi ta can bayan gidan tana kuka kamar ranta zai fita ta ce"dan Allah Granny ki kula da ita, ki sanyata farin ciki dan Allah, batada koda sai ke a halin yanzu, nan gaba akwai wanda zai dinga Zuwa yana dubata ki yarda dashi, shi ɗin jinina ne!, bazai cutar da ita ba, karki bar IMARA haka ki sakata makaranta! Kuɗin zai isheku ko ba mai tsada ba, ki kula Granny, ki kula, ku tafi..Idan ta girma ki faɗa mata iyayenta suna sonta sosai... Ki ce mata mahaifiyarta na sonta! Tana ƙaunarta..." Ta yi saurin sakin hannunta saboda har bin da ta jiyo, da gudu Granny ta fice daga gidan duk da shekarunta. Komawa gidan tayi da gudu tana ta tarar sai harbinsu yake duk da shima sun harbeshi a ƙafa, daskarewa tayi a wajen tana bin su da kallo dan tama gagara ko yin kuka, harbi wani ya yo inda take da gudu ya ƙarasa ya rungumeta harbin ya sauka a gadon bayansa, ƙara ta saki tana kuka ta ce"dan Allah Major! Mene haka meyasa kayi haka?" Shafa fuskarta ya yi kawai yana murmushi dan gaba ɗaya lokacin ƙarfinsa ya fara ƙarewa, batasan sanda ta karɓi bindigar hannun nasa ba ta cigaba da kai harbin itama, wani harbin aka sake yo wa daidai saitin zuciyarsa ƙarasawa wajensa tayi ta kare shi harbin ya sauka akan zuciyarta, wani tari tayi mai haɗe da gudan jini ta fadi a wajen, wata irin kururuwa ya yi ya ƙarasa wajenta ya rungumeta yana sakin wani irin kuka mai tsuma zuciya, har bin sa shima akayi ya faɗi ƙasa nan kusada ita. Ɗaya daga cikinsu ne ya zaro wayarsa ya ɗaukesu hoto, ya tura masa
"Kallon hotunan ya yi, sai kuma ya ce"ina ƴar tasu?" "Bamu sami kowa ba bayan waɗandan yallaɓai" girgiza kansa ya yi yana kallonsa ta cikin video call ɗin ya ce"akwai yarinya, duk yanda za'a yi ku samota, a kasheta!" Jinjina masa kai ya yi sannan ya kashe wayar, ya yi musu alama da su biyo shi suka fita daga cikin gidan, sai a sannan mutane suka fara shigowa dan suna jin ƙarar harbe-harben da akayi tsoro ya hana kowa fitowa daga gidansa, sai lokacin aka kira hukuma aka sanar musu.
***Tun da Granny ta baro gidan take kuka, bayan ta samu waje ta zauna, har sannan Imara bacci take, gaba ɗaya ta fice hayyacinta sai kallon jakar hannunta take, har akayi sallar asuba tana wajen a zaune, saida taga gari ya fara haske sannan ta tashi ta cigaba da tafiya, madadin ta nemi motar barin garin kamar yanda suka ce mata sai ta nemi motar komawa Daƙayyawa ta hau, tana tafe tana kuka har ta sauka daga motar, bata shiga gidanta ba sai ta shiga gidan ƙawarta aminiya wacce ke baya kaɗan da gidanta. Zaune ta sameta tana cin abinci tana zuwa ta zauna ta fashe da kuka
"Inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun, Maryama lafiya kike kuka?, me ya sameki na ganki haka?" Kasa magana Granny ta yi ta cigaba da kukanta, saida tayi mai isarta sannan ta bata labarin duk abin da ya faru, fashewa da kuka Asiya tayi ta ce"an shiga uku, meyasa mutane basa tuna lahirarsu idan zasu aikata abu?, me Ahamdu da Matarsa suka yi musu?, yaro mai biyayya marayan Allah, Allah ka yafe mana?" Cigaba suka yi da kukansu saida aka ɗauki lokaci sannan suka haƙurƙurtar da ransu, kallon Imara ta yi da ke bacci har sannan ta ce"Allah sarki, Allah ya kula da rayuwarki, ya sadaki da iyayenki, ya kare shi daga sharrin zamani" Ameen Granny ta ce jikinta duk a sanyaye, miƙewa tayi ta ce"bari na barta a nan Asiya, zan je gida yanzu, wannan kuɗin iyayenta ne suka bani na kula da ita zanje na ajiye su" cikin damuwa ta ce "Tom sai kin dawo Maryama" fita Granny tayi tana tafiya kamar zata faɗi.
Turo ƙofar gidan nata tayi ta shiga bakinta ɗauke da sallama, turus Granny tayi jikinta na rawa ganin wasu irin mutane tsaye a cikin gidanta, ɗaya daga cikinsu ne ya ƙaraso inda take yana kallonta ya ce"sai gashi har mun rigaki zuwa gidan" ja da baya Granny ta fara tana karanto addu'a a zuciyarta, taku ɗaya ya yi ya ƙarasa gabanta ya shaƙe mata wuya yana kallonta ya ce"ina yarinyar take?, tana ina?" Girgiza masa kai Granny ta shiga yi idanunta na fitowa waje, watsar da ita gefe ya yi ya ce"ba zaki faɗa mana inda take ba kenan?" Hawayene kawai ke zuba daga idanunta ta riƙe wuyanta wanda har yanzu take jin kamar hannunsa na kai, gyaɗa kansa ya yi yana kallon yaran nasa ya ce"ku a cikin ku wane ya keson ya more ta?"
"Ai wannan ta zama guzuma boss" ɗaya daga cikinsu ya faɗa, tuntsirewa suka yi da dariya wani narkeke ya ce"A'a nifa inaso dan babu ruwana da tsufanta" jinjina kai ya yi ya ce " ga tanan, muna jiranka!" Girgiza kai Granny ta shiga yi cikin sanyin murya take faɗin "kai yaro ka duba tsufana da shekaruna karka yimin irin wannan tozarcin, Gara ka kasheni kawai" ko ta kanta basu sake bi ba ya shiga lalata da ita. Fita ɗaya daga cikinsu ya yi ya koma bakin ƙofar gidan ya yi shiru, hangota ya yi yana tawowa hannunta riƙe da Imara wacce take kuka da sauri ya girgiza mata kai yana yi mata alama da ta koma, kallonsa ta shiga yi tana kuma kallon gidan
"I said go back!"
Ya faɗa a tsawace, da gudu ta koma gidan nata ta saka sakata a ƙofar fuskanta ɗauke da tashin hankali.
"Kai da wa kake magana ne?"
Boss ya faɗa da ƙarfi, dawowa ya yi ya ce"wasu yara nagani shine na korasu" jinjina kai ya yi, kallon granny ya yi wacce ke kwance jikin jini idanunta a rufe hawaye sai zuba yake, gaba yayi yana kallon na gefensa ya ce"kill her" harbinta ya yi a ciki sannan suka fice daga cikin gidan, motarsu suka shiga suka bar unguwar. Asiya na gidanta ta jiyo bindiga ta zauna ta rushe da kuka kamar ƙaramar Yarinya, tasowa tayi ta fito daga cikin gidanta dukda yanda take jin tsoro ta shiga gidan Granny, ƙarasawa gaban Granny tayi bakinta na rawa ta ce"mar...Marya...Maryama!" a hankali Granny ta buɗe idanunta wanda ke gab da rufe wa ta ce cikin rawar murya
"Da...Dan.. Allah Asiya ki kula da Imara, idan ta girma ki faɗa mata Iyayenta suna ƙaunarta, wataƙila ta sake ganinsu a rayuwarta, wataƙila kuma saidai a lahira, akwai sarƙa a wuyanta mahaifiyarta ta ce duk sanda danginta yaga wannan sarƙa zai ganeta karki bari ta bar wuyanta, ki ɗauki kuɗin nan ki sakata a makaranta dan Allah Asiya..kimin alƙawari" Jinjina kai tayi tana kuka tama kasa magana.
"Ki sanar da ita sunanta na gaskiya Fateemah, ki kula da ita... Ki kul..."
Cak maganar ta tsaya sai wani numfashi da ta ja, hannunta dake jikin Asiya ya saki, kallonta ta shiga yi sai kuma ta kalli cikinta kafin ta rusa wani raunataccen ihu.
# *Bestnovel*
# *Heart touching 💔*
# *IMARA 💋*
# *Nanameera*
# *2025*.
*IMARA 💋 💋*
Mikiya writers asso...
*Chapter 14*
*4:30pm*
*Daƙayyawa*
Zaune take kan kujerar katako tana tuƙin tuwo, gabaɗaya hankalinta baya wajen aikin da take, har yanzu mutuwar Granny bata saketa ba, wani yaro ne ya yi sallama ya shigo yana gara taya, amsa sallamar tayi ya ce"wai ana sallama da matar gidan nan" "sallama kuma?" Tafada tana kallon yaron, "Eh haka ya ce" tashi tayi ta rufe tukunyar tana kallonsa ta ce"je ka ce ina zuwa" da gudu ya fita daga gidan, hijab ta ɗauko a ɗakin, ta tsaya tana kallon Imara wacce ke zaune tana wasa ɗaukanta tayi ta ce"sarkin haƙuri muje ki rakani" kallonta kawai Imara ta yi ta shiga taɓa mata fuska, murmushi goggo Asiya tayi sannan tayi waje. Tsaye ta sameshi jikin bishiyar ƙofar gidan ya juya mata baya, sallama tayi ya amsa yana juyowa, zabura goggo Asiya tayi ta koma cikin gidan da gudu tana rufe bakinta da hannunta kukan na neman cin ƙarfinta, shigowa gidan ya yi tayi saurin shigewa ɗaki ta saka sakata cikin kuka ta ke faɗin
"Dan Allah kayi haƙuri, ka barmu da ran mu, wannan yarinyar bata san komai ba, kada ka cutar da rayuwarta, kun kashe kowa nata ku barta ta rayu da wannan baƙin cikin kawai, dan Allah kayi mata wannan alfarmar... Ka taimaka yaro... Dan...Allah!..."
Ta ƙarashe maganar tana rushewa da wani sabon kukan, tsaye yake har sannan a tsakar gidan hannayensa zube cikin aljihu sai kallon gidan yake ta cikin glasses ɗin dake maƙale a fuskarsa. Shirun da Goggo Asiya taji yasa ta tsagaita da kukan har sannan tana rungume da Imara wacce tafara kuka, a hankali ta buɗe ƙofar ta fito, turus tayi ganinsa zaune kan tabarmar dake shinfiɗe a ɗan tsakar gidan, jikinta ne ya fara rawa tana ƙoƙarin komawa ya ce"da kin tsaya kin ji abin da ya kawo ni baba" cak ta tsaya jin sunan daya anbaceta dashi da kuma sanyin murya irin nasa, cikin rawar murya ta ce
"Me zaka cemin yaro?, dan Allah kar kace zaka kasheta" É—an murmushin gefen baki ya yi idanunsa na kallon gabansa ya ce
"Idan da naso kashe yarinyar nan da tun ranar na kasheta, idan da banso cetar rayuwarta ba da bazan ce miki ki gudu ba, ban zo nan da niyyar cutar da ita ba, saboda haka ki zauna ki saurareni dan Allah!"
Shiru Goggo Asiya tayi dan gabaɗaya jikinta ya yi sanyi, tabbas ta yarda ta maganganunsa da yaso cutar da Imara shine zai nuna inda take, zama tayi a hankali har sannan Imara na jikinta, hannunsa ya miƙo ya ɗauki yarinyar kasancewar ta saba da ɗaukar babanta ta wangale masa baki tana dariya, murmushin shima ya yi yana kallonta ya ja mata kumatu. Zaunar da ita ya yi kan cinyarsa ya ɗauko mata chocolate a aljihu ya miƙe mata, karɓa tayi tana wasada ita, sai a sannan ya mayar da hankali wajen Goggo Asiya wacce ke kallonsu tun ɗazu.
"Banida kalaman da zanyi magana dasu wajen baki haƙuri, ita rayuwa ba kai kake da ikon zaɓawa kanka yanda zaka yita ba, nasan abin da aka yi ba'a kyauta ba kuma ba daidai bane, amma haka Allah ya ƙadarta, wannan yarinyar Allah ne kaɗai yasan abin da ya ɓoye a cikin rayuwarta, naji sanda mahaifiyarta ke yiwa kakarta wasiyyar ta kula da ita, na barsu sun tafi dukda na hangesu kuma inada ikon na kashe su a wannan lokacin, wannan sana'ar tawa ba abun arziki ba ce, ban taɓa nadama ba sai a lokacin da naga yanda mahaifiyar yarinyar nan ke kukan rabuwa da yarta, an kashe su ba tareda sun aikata wani laifi ba, tun daga sannan nayi alƙawarin barin wannan harkar ta kashe-kashen rayukan al'umma, na biyo su ƙauye ne dan ganin inda yarinyar take kuma na taimaketa idan nasamu dama, sai gashi cikin ikon Allah nasamu damar tseratar da rayuwarta" numfasawa ya yi sannan ya cigaba da faɗin
"Inason na nemi alfarma a wajenki, dan girman Allah ki bani yarinyar nan na riƙeta koda hakan zai sanyayamin zuciya, munyi aure da matata shekaru biyar baya amma ko ɓatan wata bata taɓa yi ba, ki taimaka ki bani yarinyar nan na kula da ita, zan sakata a makaranta kamar yanda mahaifiyarta ta bada wasiyya, nayi miki alƙawarin babu abinda zai samu rayuwarta muddun ina raye, sannan lokaci zuwa lokaci zan dinga kawo miki ita ki ganta"
Tunda ya fara magana Goggo Asiya ke kuka, kallonsa tayi taga shima kukan yake idanunsa zube akan Imara da keta wasa da ledar chocolate, cikin shassheƙar kuka ta ce"wlh tsoro nakeji, wannan yarinyar amana ce a wajena, amanarta aka bar min, idan har nayi abin da zai cutar da rayuwarta Allah bazai barni ba, kuma nima bazan yafewa kaina ba, bazan iya kare kaina ba a ranar lahira, duk da zan zo tayi ilimi kodan ta ɗauki fansar abun da aka yiwa iyayenta amma wlh ina tsoron baka ita, bansan wace rayuwa zata je tayi ba, yarinya ce ƙarama wacce ta gamu da ƙaddarar rayuwa tun tana yar ƙaramarta, wa yasan me gobe zata haifar?, bansan wace rayuwa zata faɗa ba idan ta bar hannuna ne, wane wanda zai zame mata bangon da zata jingina?, dan Allah kayi haƙuri!..." Ta ƙarashe maganar tana fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya.
Tashi ya yi ya tsuguna akan gwuiwarsa ya haɗe hannayensa biyu waje guda alamar roƙo yana kuka ya ce
"Ki taimaka ki yimin wannan alfarmar, ki bani yarinyar nan na raineta, ki taimakeni na aikata wannan koda shine kaɗai abin Alkhairin da zanyi a rayuwa, ki rufamin asiri kamar yanda Allah ya rufa miki, nayi miki alƙawarin ni zan zame mata bango wanda zata jingina, zan bata kariya da rayuwata, zan bata farin ciki iyakar iya wata, dan Allah ki taimakeni na fito daga cikin wannan ƙangin, ki taimakeni na aikata aikin Alkhairi "
Ya ƙarashe maganar yana kuka, above 5mins kafin Goggo Asiya ta kalleshi cikin sanyin murya ta ce"shikenan zan baka ita, amma dan Allah karka barta tayi kuka a rayuwa, kuma a duk sanda kaga ka gaza da rainonta ka dawo min da ita, zan cigaba da kulawa da ita, ita ɗin*AMANATA* (upcoming novel) ce, kaji yaro" . Gyara zamansa ya yi yana kallonta ya ce"Nagode sosai Baba, in sha Allah zan kula da rayuwarta kuma zan kawo miki ita a duk sanda kika buƙata, ni a cikin garin Dutse nake zaune kinga bamuda nisa Kenan, zan baki lambata da address ɗin gidana ko dan halin rayuwa" jinjina kai tayi ta ce" tom shikenan, Allah ya baka ikon sauke nauyin da ka ɗauka" murmushi ya yi ya ce"Ameen ya rabbi" tashi tayi ta shiga ɗaki ta ɗauko jakar kuɗin da granny ta bata ta fito, ajiye masa tayi a gabansa ta ce" wannan iyayenta ne suka bayar saboda a kula da rayuwarta, ka tafi dashi duk abin da take buƙata ka siya mata" murmushi ya yi ya tura mata jakar gabanta ya ce" cewa nayi zan ɗauki nauyin ta, idan har na karɓi kuɗinta kenan ba ɗaukan nauyin nata zanyi ba, ki ajiye mata wannan kuɗin watarana idan ta girma zai mata amfani, amma yanzu dai babu buƙatar su" girgiza kanta tayi ta ce"to, Allah ya yi maka albarka yaro, amma ya sunanka?" Murmushi ya yi ya ce"sunana Mubarak" "to, Allah ya rayaka kaima" "Amen ya rabbi" kuɗi ya zaro a aljihunsa ya ajiye mata yana tashi ya ce"Baba gashi ba yawa" girgiza kanta tayi kafin tayi magana ya ce"karki damu wannan ba kuɗin da ake bani bane, wannan da gumina nake nemosu, dan Allah kiyi amfani da su " murmushi kawai tayi dan daman abin da take tunani kenan, ɗaukan kuɗin tayi ta ce"To Allah ya biyaka" "Ameen " ya faɗa yana murmushi. Ɗaukan Imara ya yi a hannunsa ta rako shi har ƙofar gidan sannan suka yi sallama ya tafi bayan ya bata lambar wayarsa. Ajiyar zuciya ta sauke sanda ya shige motarsa ya bar ƙofar gidan, girgiza kanta tayi ta ce a fili
"Dan Allah Maryama ki gafarceni, ina nema mata kyakkyawar rayuwa ne".
Zaune yake a ƙasa yayinda shi kuma yake zaune kan kujera yana kaɗa ƙafa
"Sir duk abin da ka umarce mu muyi mun aikata shi, yanzu babu wani abu wanda ya danganci Major Ahmad wanda bai zama tahiri ba" murmushi ya yi yana kallonsa ya ce"good job, yarinyar da aka gudu da ita akan kamota?" Shiru ya yi sai kuma ya jinjina masa kai ya ce"yes sir, mun kasheta harma da wacce ta tafi da itan" wani killer smile ya yi ya ce "haka nakeson ji" wata jaka ya ɗauko ya ajiye masa a gefensa ya ce" ga shi nan kowannensu ya ɗauki 5millions, kai kuma ka ɗauka 7m" durƙusawa ya yi yana murmushi ya ce"godiya muke mai gida, Allah ya ja zamaninka, duk wanda zai shigo hanyarka sai mun tabbatar da cewa mun kawar dashi, mu naka ne har abada oga" jinjina masa kai ya yi ya ɗauki wani glass cup dake gefensa ya ce"you can leave" tashi ya yi ya ɗauki jakar ya sake masa godiya sannan ya yi waje.
Tun da ya fara magana take kallonsa har ya gama, tashi tsaye tayi hawaye fal idanunta ta ce"yanzu me kake nufi Mubarak?" cikin sanyin murya ya ce"ina nufin mu raineta har ta girma tunda mu Allah bai bamu haihuwar ba!" Girgiza kanta ta shiga yi tana kuka ta ce"wato abin har ya kai haka?, saboda ban haihu ba!?, dan har yanzu ban haihu ba shine kaje ka ɗauko tsintacciyar yarinya kace na raina?" With so much surprised Mubarak ke kallonta zai yi magana ta cigaba da faɗin " bafa zaka rainamin hankali ba Mubarak!, kai kayi kaɗan, ni bari kaji ma wlh ban yarda iyayenta ne suka mutu ba saidai idan can kaje ka yi cikinta wata ta haifeta yanzu ta baka yarka, ni kuma na zauna haka har ƙarshen rayuwata saboda kawai ina sonka to wlh bazai yiwu ba!, baka isa ba!, na rantse bazan riƙe ta ba!"
"Inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun, Ni Suhaila!?, Ni!, Ni kikewa kallon mazinaci?" Turo baki tayi tana harararsa ta ce"to ai abune a duhu wa ya san abin da kake aikatawa" ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce"abar wannan maganar, ni ba tashin hankali nakeson muyi dake ba, bance sai kin shayar da ita ba, zan dinga siya mata madara har ta isa yaye, amma dan Allah ki dinga yi mata wanka kina saka mata kaya, ta zauna a wajenki idan na fit..."
"Na rantse da Allah bazan yi ba!"
Ta katse shi kafin ya ƙarasa faɗar abin da ya yi niyya. Rasa me zai ce mata ya yi kawai ya tsaya yana kallonta, harararsa ta yi cikeda tsiwa take faɗin
"Bari kaji, idan kanason zaman lafiya dani to ka fita da wannan yarinyar daka cikin gidan nan, idan ko ba haka ba zakaga abin da zan yi yanzun nan" tashi tsaye ya yi yana kallonta ya ce"me zaki yi?" Kallonsa ta yi ta ce"babu abin da ya dameka da abin da zan yi, kuma ba sanar dakai zanyi ba, abin da nakeson ji shine zaka fita da ita ko bazaka fita ba?"
"Bazan fita da ita ba!"
Ya faɗa yana kallonta, waro manyan idanunta tayi tana kallonsa, tunda suke bai taɓa yi mata irin haka ba, baya taɓa zallake maganarta saboda irin yanda suke son junansu, sai gashi yau suna faɗa akan IMARA. Kuka Imara ta saka ya juya yana kallonta, zaune take kan kujera tana sanye da wasu sabbin kaya daya siya mata, ɗaukanta ya yi yana jijjigata, ƙarar da cikinta ya yi ya tabbatar masa da yunwa take ji ya dafa cikinta cikin sanyin murya ya ce
"Sorry marh gurl, muje na siya maki madara" daga haka ya fita daga cikin parlon ba tareda ya sake kallon Suhaila ba, da gudu ta shige É—aki tana kuka kamar ranta zai fita.
***Around 8am ya shigo gidan hannunsa riƙe da Imara sai wasa take da doll ɗin daya siya mata, siyayya sosai ya yo mata ta kayan sakawa da mayuka sannan ya siyo mata madarar dan baiga alamar tana cin wani abu ba, a parlon ya ajiyeta ya shiga kitchen ya haɗo mata madarar ya dawo ya zauna yana bata, tunda ta kafa kanta jikin feedar bata cire ba sai da ta shanye tass, cirewa tayi ya kalleta yana murmushi ya ce" a ƙaro?" Kamar taji me yace ta gyaɗa masa kai tana ƙura masa idanu, wata ya sake haɗa mata ya bata tasha. Tana gama sha kamar wacce ke jira tafara bacci hankalinta kwance, tashi ya yi ya kai ta ɗaki sannan ya shiga ɗakin Suhaila amma ga mamakinsa sai ya samu bata ciki, fita ya yi ya dawo dan duk zatonsa tana banɗaki saidai har yayi wanka ya shirya ya dawo Suhaila bata fito ba, sunanta ya kira yaji shiru hakan yasa ya tura ƙofar banɗakin amma sai yaga wayam babu ita babu dalilinta, duk inda ya kamata ya duba a gidan saida ya duba amma bai ga Suhaila ba, har maƙota ya shiga bai ganta ba hakan yasa ya dawo gida ya ɗauki waya ya shiga kiranta, ringing ɗin duniya bata ɗauka ba daga ƙarshe ma sai ta kashe wayar tata. Zaunawa ya yi a parlon ya dafe kansa ko ba'a faɗa ba yasan Suhaila gidansu ta tafi, dan damar gwanar ƙorafi ce. Daren ranar haka ya kwana a parlon ba tareda ya yi bacci ba, da yaga lokaci na tafiya a banza ya tashi ya ɗauro alwala ya fara salloli yana roƙon Allah ya gafarta masa zunubansa, har akayi sallar asuba yana zaune sai a sannan ya tashi ya leƙa ɗakin da Imara ke kwance, bacci ya tarar tana yi har sannan sai kawai ya rufe mata ƙofar ya fito harabar gidan wacce batada girma ya shimfida sallaya ya bi jam'in anan.
***Around 9am ya yi parking a ƙofar gidan, a hankali ya fito daga motar ya shiga gidan yana tunanin abin da zai je ya tarar, a babban compound ɗin gidan ya tsaya ya aika mai gadin domin ya yi masa iso,saida aka ce ya shigo sannan ya shiga. A parlon Daddy aka kaishi bayan sun gaisa ya kalleshi ya ce"Mubarak me ya haɗaka da Suhaila?" Cikin ladabi ya bashi labarin duk abin da ya faru, Daddy bai ce masa komai ba yasa akayi kiranta suka shigo ita da Mommy idanunta ya kumbura da alama taci kuka, bayan sun zauna Daddy ya kalleta ya ce"yanzu Mamana mene a ciki dan kin riƙe marainiya?, kinsan ladan riƙon maraya kuwa?" fashewa tayi da kuka ta ce "ni wlh Daddy bata yimin ba, kuma kawai ya mayar da ita wlh indai ni ce bazan riƙeta ba!" Kallonta Mubarak ya yi bai ce komai ba, Daddy ya ce"ya maidata ina?, ki ma bar wannan maganar, kawai magana ɗaya ce yanzu kai Mubarak tunda kanason ka riƙe yarinya to ka samo mata mai aiki wacce zata dinga rainonta har zuwa sanda zatayi hankali ke kuma ki koma gidan mijinki"
"Ta koma ina?, wlh babu inda zata je!, indai har bazai mayar da wannan shegiyar yarinyar da ba'a san asalinta ba saidai ya saketa!".
# *Bestnovel*
# *IMARA 💋*
# *Lolo*
# *Nanameera*
# *2025*.
*IMARA 💋💋*
Mikiya writers asso...
*Chapter 15*
Da sauri Mubarak ya ɗago idanunsa yana kallon Mommy, harararsa tayi ta ce"Eh ka kalleni da kyau!, wlh saidai ka zaɓa ko Suhaila ko kuma yarinyar kaji na faɗa maka!" Ta ƙarashe maganar tana haki, girgiza kai Daddy ya yi yana kallon Suhaila ya ce"ke tashi ki bi mijinki, kai kuma Mubarak ka nemawa yarinyar mai raino kamar yanda nafaɗa maka" har ƙasa ya sunkuya cikeda ladabi ya ce"Nagode sosai Daddy, Allah ya ƙara girma" "Ameen" cewar Daddy yana cigaba da kallon labaransa, tashi ya yi yana kallonta ganin yanda take tura baki gaba kallon iyayen nata tayi sannan ta yi waje fuu kamar zata tashi sama. "Gaskiya yallaɓai wannan ba shawara ba ce ya yarinya zata kawo kuka miji ya yi mata abin da bai dace ba sannan ka ce mata ta koma without taking any action, nan gaba idan ya sake mata abu ai ba zata ji kwarin gwiwar dawowa gida ba"
"Kwarin gwiwar!?, au daman akwai wata kwarin gwiwa a yin yaji?, mene ne abun tashin hankali anan?, dan ya ce zai riƙe yarinya shine ya yi laifi?, tunda su Allah bai basu haihuwar ba, ba zasu ɗauki na wasu su raina ba kenan?, saboda ku mata ƙwaƙwalwarku ƙarama ce!"
"Amma yallaɓai..."
"Kar na sake jin bakinki akan wannan maganar, na rufe babinta" shiru Mommy ta yi ba tareda ta so hakan ba.
***Yana gama parking ɗin motar tayi waje kamar zata tashi sama da, da idanu Mubarak ya bita har ta shige gidan, ya girgiza kansa kawai sannan ya gyara parking ɗin motar ya fito. A parlon ya sameta tana zaune ta haɗe kai da gwiwa tana kuka, zama ya yi gefenta yana kallonta ya ce "Suhaila nayi tunanin komai ya wuce ai?" Tashi tsaye tayi tana watsa masa wani kallo ta ce"ya wuce yaje ina?, to bari kaji babu abinda ya wuce wlh, muddin wannan yarinyar na cikin gidan nan to ka dinga gamuwa da ɓacin rai kala-kala kenan, idan kai baka fasa ba nima bazan fasa ba!" ta juya ta bar parlon, dafe kansa ya yi na rashin sanin abin yi, tunawa ya yi da Imara hakan yasa ya tashi ya ɗauki car key ɗinsa ya yi waje. Gidan maƙotansa ya yi sallama bayan an yi masa iso ya shiga, zaune ya samesu suna hira Imara kuma na gefenta sai wasa take abin ta, zama ya yi suka sake gaisawa sannan yayi musu godiya, murmushi Sulaiman ya yi ya ce "haba ai babu komai Mubarak, duk abinda Suhaila zata iya maka ai Fatima ma zata yi maka shi" jinjina kansa ya yi yana murmushi ya ce"ai ko Nagode sosai, yanzu daman wata alfarma nake nema a wajenki Fatima"
"Alfarma kuma?"
Jinjina kansa ya yi ya ce, "Eh, dan Allah idan babu damuwa inason ki samo min wacce zata dinga rainon Imara, amma irin babba mai hankali nakeso wacce zata riƙeta da amana" murmushi Fatima tayi ta ce"indai wannan ne babu damuwa bari yanzu na kira wacce take kawo min yan aiki naji", ajiyar zuciya ya sauke ta samun sauƙi, ko babu komai zai bawa Imara irin kulawar da yake son bata, duk da zuciyarsa cike take da tunanin yanda rayuwarsa zata kasance muddin oga ya gane baya tare da su, har aka kira wayar yana wannan tunanin, bayan matar ta bata tabbacin za'a samu, sosai ya yi farin ciki sannan ya gode musu ya tashi zai ɗauki Imara
"Tunda dai nasan yanzu Maybe fita zaka yi to wajen wa zaka barta a gidan?" Fatima ta faÉ—a tana kallonsa, girgiza kansa ya yi fuskarsa É—auke da damuwa ya ce"to ya zan yi, da tafiya zanyi da ita" girgiza kai tayi ta ce"a'a a wannan sanyin, kawai ka barta anan zan kula da ita har anjima mai rainonta ta zo" murmushi ya yi ya ce"Nagode sosai da karamci Fatima" murmushi ta yi bata ce komai, sukayi sallama da Sulaiman sannan ya fita yana tunanin ina ma Suhaila ce ta ke yin haka.
Washegari da safe bayan sun gama breakfast ya shiga gidan Sulaiman ya samu har mai rainon ta zo, babbar mace ce kuma kana ganinta kaga mai hankali, da alama ba yar ƙauye ba ce dan babu alamar hakan a tattare da ita tsananin kuncin rayuwa ne kawai, zama ya yi ya lissafa mata abubuwan da yakeson ta dinga yi wa Imara kuma ta amince da hakan, sannan ya danƙa mata Imara a hannunta. Godiya ya sakewa Fatima sannan suka bar gidan, a corridor ɗin gidan ya nuna mata wani part suka shiga, parlon ne madaidaici sai kitchen a cikinsa sai wani ɗakin kwana mara girma da banɗaki a ciki, kallonta ya yi ya ce "yawwa Baba nan ne inda zaku dinga zama" jinjina kanta tayi ta ce"tom Alhaji mun gode" murmushi ya yi ya ce"babu komai, zuwa anjima zan fita nayi muku siyyayar abinda zaku ci da kuma na amfani, nidai fatana kawai ki riƙe yarinyar nan da amana dan marainiya ce" girgiza kanta tayi ta ce"Allah sarki, Allah ya jiƙan iyayenta, in sha Allah ba zaka samu wata matsala daga ɓangarena ba zan kula da ita iyakar iyawata in sha Allah" sosai ya ji daɗin haka ya yi mata sallama ya fita. Kai tsaye ɗakinta ya shiga tana tsaye jikin curtains ɗin ɗakin ta kalleshi murya kasa ƙasa ta ce" wace wannan wacce ka shigo da ita?" yana cire agogon hannunsa ya ce"wacce zata raini Imara ce tunda ke ba zaki iya ba!" harararsa tayi tana taɓe baki ta ce"Eh bazan yi ba tunda ba dolena ba ce, ba zan raini ƴar da bansan taya aka haifeta ba" a fusace ya ɗago yana kallonta cikin wata kakkausar murya ya ce"ki dinga sassauta kalamanki akan yarinyar nan Suhaila idan ba haka ba zan baki mamaki wlh"
"Me zaka yi!?, Na ce me zaka yi?, zaka sakeni ne?, idan zaka iya sakeni Mubarak!, na ce ka sakeni!"
Kwafa ya yi sannan ya juya ya bar wajen ba tareda ya tanka ta ba, harararsa tayi sannan ta fice daga É—akin itama.
*6yrs later (Bayan shekaru shidda)*
Zaune take tsakar gidan tana wanke-wanke, banda taɓa kwanukan babu abinda take yi dan babu alamar tama iya wanke-wanken, gashin kanta ne duk ya rufe mata fuska hakan ya sa ta miƙe tsaye tana tsalle sai kuma ta fashe da kuka, da gudu ta fito tana kallonta ta ce"Imara lafiya?, me ya saka ki kuka?, wane ya sakaki wanke-wanke?" Ƙarasawa wajenta tayi tana kuka ta ce a shagwaɓe "Umma gashina ne!, gashina ne!, ni ki haɗe min shi" ta ƙarashe maganar tana bubbuga ƙafa, murmushi tayi ta ce"Allah ya yaye miki wannan rigimar" turo baki tayi, girgiza kai Umma tayi sannan ta haɗe mata gashin kan nata irin na larabawa sak ta ɗaure mata waje guda, nan fuskarta ta fito sosai, kyakkyawa ce ajin farko dan ko ba'a faɗa maka ba kasan ma jinin yan Nigeria ba ce ba, kallon idanunta wanda suka kasance manya tayi sannan ta ce "me ya sameki a fuska?, naga tayi ja?" Turo baki ta yi ta ce "ba Aunty ce ta dakeni ba, kuma ta ce nayi mata wanke-wanke, kuma ta ce idan na faɗawa Daddy sai ta yanka niii!"
"What!?"
Suka ji saukar muryarsa a bayansu, girgiza kai Imara ta shiga yi ta rufe bakinta da ɗan ƙaramin hannunta, ƙarasowa gabansu ya yi ya kama hannunta cikin sanyin murya ya ce"me Aunty tayi miki?" Girgiza kanta ta yi, ya daka mata tsawa. Fashewa tayi da kuka ta shige jikinsa jikinta na rawa, rungumeta ya yi yana shafa bayanta ya ce"shikenan ya isa faɗamin me tayi miki?, laifi kika yi mata?" Girgiza kanta tayi cikin shassheƙar kuka ta ce"indomie nakeso shine kuma babu anan, na shiga ciki zan ɗauka shine ta mareni ta ce nayi mata wanke-wanke, amma dan Allah Daddy karka faɗa mata ta ce idan nafaɗa maka sai ta yanka ni, ni banason na mutu Daddy!!" Sosai ransa ya ɓaci bai ce komai ba ya kama hannunta suka shiga gidan, zaune suka sameta tana cin cake tana kallon draman da ake a MBC Bollywood,
"Me tayi miki da har zaki ɗauki hannu ki mareta?, a matsayinki na wa?, akan me zaki sakata aikin da yafi ƙarfin shekarunta?, ke koma aikin da zata iya ne ki a matsayinki na wa zaki sanyata aiki?" Tashi tsaye tayi tana kallonsa baki a buɗe,
"Bari kiji bakisan wahalarta ba, baki raineta ba, babu abin da ya haɗaku saboda haka karna sake jin kin shiga harkarta, idan ko haka ba wlh saina ɓata miki rai!"
"Okay, saboda na saka yar da ake riƙo a gidana aiki shine laifi?, ko kuwa dan na hukuntata?, kenan babu wanda ya isa ya gyara mata idan tayi ba daidai ba?, naga..."
"Akwai mana!, akwai mutanen da suka dace su gyara mata idan tayi kuskure, amma ke bakya É—aya daga cikinsu, bakida wannan damar, baki isa ba!, ke baki kai ba, saboda haka ki kama kanki, idan har kika cigaba da irin wannan nuna kin isan da ita zan baki mamaki!"
Yana gama faɗin hakan ya kama hannun Imara suka yi waje, part ɗinsu ya mayar ya daina ya zauna yana kallonta ya ce"kiyi haƙuri kinji, bari zan fita sai na siyo miki man zafi, kinyi karatu sosai a school ko?" Murmushi tayi har saida beauty point ɗinta ya loma ta ce"Eh Daddy, uncle John ya ce nafi kowa ƙoƙari a class ɗin mu, naji daɗi Daddy" murmushi ya yi ya ce"yawwa, that's my girl, keep it up kinji, inason kiyi karatu sosai ki zama lawyer "
"Lawyer kuma Daddy?, why not Doctor?" Girgiza kai ya yi ya ce"No, lawyer nakeson ki zama kinji" gyaÉ—a masa kai tayi ta ce"your command is my wishes Daddy" girgiza kansa ya yi yana dariya ya ce"yawwa Baby na, yanzu bari naje nayi wanka, zan zo muje shopping" tashi tayi tana tsalle ta ce"yehh, daman inason siyan chocolate da Pringles" murmushi ya yi ya ce"oyha je ki shirya ki zo mu tafi " da gudu ta shige bedroom É—in ya girgiza kansa sannan ya yi waje.
***Kallonta tayi ganin har sannan batayi shiru ba ta ce"wai ke idan ba zakiyi shiru ba ki tashi ki bar nan, tunda kika zo kike kuka, nayi miki maganar duniya kin yimin banza, tun da ba zaki fadi abin da ya kawo ki ba sai ki tashi ki bani guri" shassheƙar kuka ta fara tana kallonta ta ce"Mommy wlh nagaji, nagaji da abin da Mubarak yake yimin akan yarinyar nan, kwata-kwata baya kulani, idan kinga ya yi min magana to saidai akan yarinyar nan, yana fifitata akan komai Mommy, ni bansan me nayi masa ba, kuma ban isa na hukunta yarinyar ba sai ya hau yimin bala'i kamar zai dakeni, ya zanyi Mommy?, ya zan masa, nagaji wlh, idan babu dama sai na haƙura da auren nasa!"
"Ki haƙura!?, ki haƙura fa kika ce?, bama kida hankali, kenan wannan yarinyar da aka haifeta a gabanki ita zata fitar dake daga gidan mijinki, to idan kin fito sai ki auri wa?, kinsan dai babu mai aurenki bakya haihuwa shima ɗin saboda yana cin arzikin ubanki yake zaune dake, amma badan haka ba tuni wani zancen ake. Ke bakida wayo, cikin ruwan sanyi zaki fitar da ita, akwai wata ƙawata wacce ta taɓa sakawa aka yimin aiki akan Alhaji naga bai ci ba na haƙura bari na kirata ta zo ta rakamu muje ayi ta ta ƙare"
Goge hawayenta tayi ta ce"ni Mommy so nake kawai a kasheta kowa ma ya huta, ko kuma a haukatar min da ita".
# *Bestnovel*
# *IMARA 💋*
# *Heart touching 💔*
# *Nanameera*
# *2025*.
*IMARA 💋💋*
Mikiya writers asso...
08106608363
*Chapter 16*
Murmushi Mommy ta yi ta ce"karki damu, wannan duk nasan abin da ya kamata a yi musu duka, yanzu kedai ki koma gidanki ki zauna karki nuna wani abu ma ya faruwa, ina mai tabbatar miki zakiga abun da zai faru" rungume mahaifiyartata tayi ta ce"shiyasa nake sonki Mommy, Nagode sosai".
***Da gudu ta shigo gidan tana kwalawa Umma kira, fitowa Umman tayi daga kitchen tana kallonta ta ce"Imara lafiya kike min wannan kiran?" Turo baki ta yi tana ajiye school bag É—inta ta ce"ni Daddy nake nema zan faÉ—a masa abu" girgiza kai Umma ta yi ta ce"amma ai kinsan bai dawo ba ko?, shine ni zaki dameni?" kallonta tayi da dara-daran idanunta kamar zatayi kuka ta ce"to kira min shi a waya, magana zan masa fah" haÉ—e rai ta yi ta ce"ita maganar ba zaki iya jira sai ya dawo ba?, bansan fa rigima Imara" tashi Imara tayi bata sake ce mata komai ba ta shige bedroom tana zuwa ta faÉ—a kan gado fashe da kuka tana burgima. Shiga É—akin Umma tayi ta tsaya tana kallonta kafin ta nisa ta ce"me aka yi miki na kuka kuma?"
"Ni Daddy zan faÉ—awa abu!, ki kiramin shi!"
Ajiyar zuciya Umma ta sauke ta ce"bari na ɗauko wayata to" daga haka ta fice daga ɗakin, tashi zaune Imara tayi ta shiga goge hawayen fuskarta tana shassheƙar kuka. Umma na fita ɗaukan waya ya yi sallama ya shigo, murmushi ta yi ta ce"Allah ya kawo ka ma shikenan na huta" murmushin shima ya yi ya ce"meya faru?" "daga dawowarta daga makaranta ta hanani sakat sai an kiraka wai abu zata faɗa maka" girgiza kansa ya yi yana dariya ya shige bedroom ɗin, zaune ya sameta har sannan tana shassheƙar kuka tana ganinsa ta tashi tsaye ta rungumeshi, zaunar da ita ya yi gefensa ya ce"mene ya faru?, wa ya taɓa min gimbiyata?" murmushi ta yi ta ce "Daddy daman anyi mana hutu ne, shine nakeson naje ƙauye wajen granny" waro idanunsa ya yi ya ce"ƙauye kuma?, A'a, ki bari sai anyi hutun third term kinga shine mai tsayi sai ki tafi, kina dawowa ki shiga primary 4 ko?" Girgiza kanta tayi tana kwaɓe fuska ta ce"ni yanzu nakeson naje, ka kaini gobe Daddy!, gobe Daddy, dan Allah" numfasawa ya yi ya ce"shikenan, Allah ya kaimu goben sai na kai ki amma one week zakiyi ki dawo gida" gyaɗa masa kai tayi alamar ta yarda ya shafa kanta ya ce"ohya tashi kiyi sallar magrib kizo muyi karatu" jinjina masa kai tayi sannan ta tashi da gudu ta shige toilet ɗin, girgiza kansa ya yi ya tashi ya fita. A parlon ya samu Umma ya ce ta haɗa mata kayanta sannan ya yi waje.
***Zaune yake a katafaren parlon ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, hannunsa riƙe da system yana dannawa a hankali kuma yake sauraren abin da yake faɗa masa,
"Sir, munyi nasarar gano inda Mubarak yake, yanzu kawai muna jiran muji daga bakinka ne, wane hukunci za'a yanke masa na juya mana baya da ya yi?"
Murmushi ya yi yana cigaba da abin da yake ya ce"inason ka gayyato min shi nan, inason magana dashi" sunkuyawa ya yi ya ce"angama sir" jinjina kansa ya yi kafin ya ce "shikenan je ka".
Washegari.
Fitowa tayi da hannunta riƙe da trolley ɗin, kallonta ya yi ya ce"ina Imara?" girgiza kai Umma ta yi ta ce"ta tsaya ɗaure takalmi nace ta sanya wani amma taƙi" murmushi ya yi ya amshi jakar ya ce"kira mu tafi kar mu makara" komawa Umma tayi ta sameta zaune kan kujera tana fama da takalmin har sannan bata ɗaura belt ɗin ba, bata ce komai ba ta ƙarasa ta tsuguna ta sanya mata takalmin sannan ta tashi ta kama hannunta suka fito, sanye take cikin wata Abaya white colour an yi mata rolling veil ɗin abayar akanta, tayi wani irin kyau kamar ba ƙaramar yarinyar ba, da gudu ta ƙarasa ta buɗe motar ta shiga ta leƙo tana kallon Umma ta ce"Bye bye Umma sai nadawoooooo" murmushi Umma tayi ta ce"ki tawomin da tsaraba" gyaɗa mata kai tayi kawai, har suka fita daga gidan tana ɗaga mata hannu, saida suka tafi sannan Umma ta girgiza kanta tana murmushi ta koma ciki.
***Da gudu ta ƙarasa ta rungumeta tana tsalle, murmushi Goggo Asiya ta yi ta ajiye rariyar hannunta ta ce"yau kuma ziyara aka kawo min?" zama Imara tayi a gefenta tana dariya ta ce"Eh mana Granny, harda Daddy fa muka tawo na gudu na barshi a waje" ta ƙarashe maganar tana tafa hannu, girgiza kai Goggo Asiya ta yi ta ce"ai kam dai ki daina gudu yarinya, dan kamar ki basa gudu anan, idan ba haka ba samari su yi miki dariya"
"Samari kuma?, su wane samari??"
Sallamar da Mubarak ya yi ta katse musu maganar, ya shigo hannayensa riƙe da ledoji, tashi Goggo Asiya ta yi ta sanya masa wata tabarmar ya zauna tana murmushi ta ce"lale maraba da zuwa", murmushi ya yi ya gaisheta ta amsa cikin sakin fuska, tashi Imara tayi ta koma inda yake ta zauna tana kallonsa ta ce"Daddy ina jakata?, na kawowa Granny chocolate" murmushi ya yi ya ce"tana mota, ki bari idan zan tafi sai a ɗauko miki" shiru tayi bata sake cewa komai ba. Bayan ya sanar da Goggo Asiya dalilin zuwanta ya tashi saboda kar ya makara a wajen aiki, ledojin hannunsa ya tura mata ya ce"babu yawa Baba" girgiza kanta ta yi ta ce"ɗan nan baka gajiya da hidima?, Allah ya saka da Alkhairi " murmushi ya yi ya ce"babu komai Baba, Allah dai ya saka da Alkhairi, Nagode sosai " har waje suka rakoshi ya tafi sannan suka koma gidan. Imara na shiga ta buɗe trolley ɗinta ta fara firfito da kaya har saida ta ciro ledan shopping ɗin da ya yi mata, ta buɗe, tarkacen biscuits da chocolate ne a ciki ta kalli Goggo Asiya tana murmushi ta ce"granny ki ɗauka ke na kawo wa" murmushi ta yi tana cigaba da tankaɗenta ta ce"ina ni ina wannan kayan zaƙin Imara?, ai sai ke ɗin" langwaɓar da kai tayi ta ce"dan ma na kawo miki, shikenan."
***Tun daga nesa ya hangosu tsaye a bakin gidansa, a hankali ya yi parking motar ya fito yana kallonsu da mamaki, ƙarasowa ogan ya yi yana murmushi ya ce"Alhaji Mubarak!" shiru Mubarak ya yi bai ce komai ba, ogan ya cigaba da faɗin "haka kawai sai muka daina ganinka babu wani notice, what a surprised?" haɗe rai Mubarak ya yi yana kallonsa ya ce"kaga ni yanzu banida wani business daku, na rigada na bar wannan harkar, zan cigaba da neman abincina ta hanyar halal, duk wani abun more rayuwa zanyi na daidai ƙarfina ba tareda nafaɗa halaka ba, saboda haka dan Allah ku bar ƙofar gidan nan" sigarin hannunsa ya yar a ƙasa yasa ƙafa ya murjeta yana girgiza kansa ya ce"kenan daman ka shirya munafuntarmu, akwai wani abu a zuciyarka, ko kuma akwai wanda ka kewa aiki" girgiza kai ya yi ya ce"ni babu wani wanda nake yi wa aiki, kawai na fita daga cikin irin wannan sabgar ta saɓon Allah ne, har abada bazan sake cutar da wani rai ba, ina rokon ubangiji laifukan dana aikata a baya ya yafemin" tuntsirewa ya yi da dariya, ya juya yana kallon sauran suma suka sheƙe da dariyar rainin hankali, haɗe rai ya yi lokaci ɗaya ya ɗaga musu hannu, kowa yayi tsit. Kallon Mubarak ya yi ya ce"kaci Sa'a oga da kansa ya ce yana son ganinka, amma da ni da kaina zanyi maganinka, saboda haka shige muje"
"Babu inda zan je ni!, na fita daga wannan harkar kuma har abada bazan koma ba, wannan shine abinda na yankewa rayuwata, kuma babu wanda ya isa ya sakani na sauya!" Numfasawa Ogan ya yi ya ce"kaii!, nutsu, umarnin oga ne kuma dole ka bi, ko ka tafi ko kuma mu kaika da kanmu" baki buÉ—e Mubarak ke kallonsa, ganinsa irin kallon da yake masa yasa ya yi yaran alamar su zo da hannu, tawowa suka yi duka, ya ce"ku saka shi a mota" kafin kiftawar ido suka cacimeshi suka zura cikin mota suka bar bar unguwar.
***Girgiza kai Goggo Asiya ta yi ta ce"a'a Imara bakisan kogin nan ba, ni banason ma ki je wlh, ki bari nasamu yaro a aika ya ɗebo min" turo baki gaba tayi ta ɗauki tulun ta ce"ni wlh ni zan je nafa sani Granny, kawai ki barni na ɗebo miki, yanzu zan dawo" murmushi ta yi ta ce"uwar kafiya, je ki, Allah ya tsare" da gudu ta fita daga gidan tana dariya, girgiza kai Goggo Asiya ta yi ta cigaba da kunna wutar da take. Tana tafe tana yan waƙoƙinta har ta kai kogin, murmushi tayi har saida beauty point ɗinta suka loma, ta ƙarasa gabansa ta tsuguna tana kallon ruwan wanda yake gwanin ban sha'awa, sunkuyawa tayi ta ɗebi ruwan, zata miƙe ta hangi wani mutum fuskarsa a rufe daga can wani gefe na kogin, murmushi tayi a fili ta ce "laa shima ya zo ɗi ban ruwa" daga haka ta ƙarasa inda yake, sunkuyawa tayi daidai gefen fuskarsa wacce take a rufe ta ce"Hello" shiru ta ji ya yi mata hakan yasa ta ce"ko Hausa kake ji, kuma na ganka fari irina, ya sunanka?, kaima Granny ɗinka zaka ɗibarwa ruwa?, Eh?" Shirun da taji ya yi har sannan yasa ta kwaɓe fuska ta ce"to kai baka ji ne?, ko baka magana irin peter na school ɗin mu, ni sunana IMARA kaifa?" Sai a sannan ya juya ya kalleta, fuskarsa a lulluɓe take baka ganin komai sakamakon glasses ɗin daya sanya akan idanunsa kuma lulluɓin ya rufe har goshinsa, hannunsa kuma sanye suka da safar hannu, murmushi Imara ta yi ta ce"kai ya sunanka?, ka zama abokina mana" bai ce mata komai ba sai tashi da ya yi daga zaunen da yake ya zuba hannunsa a aljihu ya shiga kallon kogin, haɗe rai tayi ta tashi tsaye itama, gabaɗayanta bata kai ƙugunsa ba, ta ɗaga idanu ta kalleshi sai kuma ta harareshi tana murguɗa baki ta ce"wai dan ya fini tsayi, to ni wlh karka ganka babba ko duka nakewa mutane, kuma nama daina kulaka Dodo kawai" tana faɗin haka ya juyo ya kalleta, da gudu ta bar wajen, ta koma inda a ajiye tulun ruwanta ta ɗauka ta bar wajen tana tafe tana sheƙar da ruwan har ta ƙarasa gida. Ajiyewa tayi tana riƙe ƙugunta ta ce"wash! nagaji granny" girgiza kai Goggo ta yi ta ce"to ba dole ba, ji yanda kika jiƙa jikinki" murmushi tayi tana kallon jikin nata ta ce"to ai dodo nagani shine na gudo kar ya kamani"
"Dodo kuma Imara?, bansan shirme fa"
Ƙarasowa tayi kan tabarmar ta ce"wlh granny dodo ne baya magana fa, gashi fuskarsa a rufe" ta tuntsire da dariya tana tafa hannu, girgiza kai Goggo tayi tana murmushi ta ce"shikenan tashi ki cire waɗannan kayan ki sauya wasu, a kuma zuwa ɗiban ruwan ai" tashi tayi ta shige ɗakin tana dariya.
*Dutse*
*12:43pm*
Zaune yake kan kujera yana karkaɗa ƙafa yayinda su kuma suke zaune a ƙasa, idanunsa kan Mubarak wanda ke kallon wani waje daban fuskarsa a haɗe kamar bai taɓa dariya ba, girgiza kai ya yi yana murmushi ya ce"kuma shikenan Mubarak sai ka ɗauke ƙafarka baka sanarwa da kowa ba, ka daina kula kowa tsawon waɗannan shekarun?" Kallonsa ya yi ya ce "nayi hakane saboda kada ma a dakatar dani, saboda tsakanina da Allah na shiryu kuma, kuma ina yi muku fatan shiriyar gaba ɗaya" tashi Ogan nasu ya yi ya shiga zagaye ɗakin kafin ya juyo ya kalleshi ya ce "yanzu kenan ka bar cikinmu kake nufi?, kuma ba zaka dawowa ba?" Jinjina masa kai ya yi ya ce"Eh ka nemi wani" murmushi ya yi ya kalli shugabansu ya ce"Papa ku mai dashi gida, sannan ka bashi kuɗi naira miliyan biyu ya samu yaja jari ya yi wata sana'ar " tashi Mubarak ya yi ya ce"a'a zan koma da kaina, sannan Nagode amma bana buƙatar kuɗinka, Allah ya rufamin asiri, Nagode da kyautatawa " yana gama faɗin haka ya juya ya fice daga parlon, da idanu kawai ya bishi sai kuma ya yi murmushi ya koma ya zauna yana kallon Papa kafin ya yi magana ya ce"yallaɓai ya zaka barshi ya tafi?, idan kuma ya tona mana asiri fa?, nifa nafi tunanin wani yake wa aiki wlh" lemon dake ajiye akan table ya tsiyaya yasha sannan ya kalleshi ya ce"to kai da mene tunaninka?, na hana shi tafiya?, ai bazai yiwu ba, ku barshi ya je gida, duk wanda ya fara aiki dani to dole ya ƙarashe rayuwarsa a tare dani ba'a juyamin baya, ku barshi ya huta na yau, zuwa gobe Inason naji labarin mutuwarsa s gidajen rediyo da kafar sada zumunta" sunkuyar da kai suka yi duka suka haɗa baki wajen faɗin
"Angama"