Chapter 19-20
Imara Part 1 Complete Hausa Novel · about 20 min read
Tafiya kawai take bata ko kallon gabanta, burinta ɗaya ta ƙarasa inda tayi niyyar zuwa, babu kowa a wajen kogin sai mutum ɗaya da ta hanga daga can gefen kogin, ajiyar zuciya ta sauke tayi saurin ƙarasawa inda yake, zama tayi gefensa tana kallon kogin kamar yanda yake shima, sun ɗauki tsawon lokaci a haka kafin ta juyo ta kalleshi, kamar kullum yau ma fuskarsa a rufe dake, numfasawa tayi ta ce"Dodo!" ko kallonta bai yi ba dan babu alamar ma yaji abin da tace, haɗe fuska tayi tana kallonsa ta ce "ba zaka kulani ba?, bakasan an yimin mutuwa ba?, Daddyna ya mutu ya barni, ya tafi, sai ni kaɗai, banida kowa yanzu, Umma ma ta tafi, kuka nakeson nayi, ni so nake nayi kuka, ƙirjina zafi yake min Dodo, ka taimakeni" ta ƙarashe maganar tana fashewa da wani raunataccen kuka, kallonta ya yi sai kuma ya ɗora kanta bisa cinyarsa yana shafa gashin kanta ya ce
"Cry, kiyi kuka, ki yi kuka sosai kinji"
Tamkar yana zugata haka ta sake rushewa da wani kukan, bai yi yunƙurin hanata ba, ta ɗauki tsawon lokaci tana kuka kafin a hankali ta fara sauke ajiyar zuciya, shirun da yaji yasa ya ɗago idanunsa ya zuba mata idanu, yarinya ce ƙarama amma gabaɗaya damuwa ta gama wanzuwa akan fuskarta, ko ba'a faɗa maka ba da ka ganta zaka gane tana cikin jarrabawa, hannunsa ya sanya ya goge mata hawayen fuskarta, lumshe idanunta tayi wasu hawayen suka samu damar sakkowa gefen fuskarta, shiru tayi tana shassheƙar kuka a hankali, har bacci ya ɗauketa, ajiyar zuciya ya sauke shima sannan ya gyara mata kwanciyar ta a jikinsa ya cigaba da kallon kogin da yake. Fitowa Granny tayi hannunta riƙe da tsintsiyar tana cewa
"Amma dai kin cinye abincin nan ko Imara?, dan akwai maganin da zan baki" shiru taji hakan yasa ta ce"ka jimin yarinya, ina miki magana kin yimin shiru?" Juyowa tayi taga wayam babu Imara babu alamarta a wajen, yar da tsintsiyar hannunta tayi ta dafe ƙirji tana salati ta ce "subhanallahi, ina yarinyar nan ta shige ni Asiya?"
"Imara! Imara! Imara!" Jin shiru yasa ta leƙa banɗakin, saidai babu alamar ma wani ya shiga banɗakin, jikin granny na rawa ta ciri hijabi a igiya tayi waje, maƙota ta shiga tana neman Imara amma babu wanda ya ganta, yawo kwararo-kwararo babu inda Granny bata je ba amma bata samu Imara ba, zuwa sannan gabaɗaya jikinta ya yi sanyi, fargaba da tashin hankali ya ziyarceta tunanin inda marainiyar yarinya ta shige, har bayan awa ɗaya bata samo Imara ba, hakan yasa ta dawo gida maƙota suka shigo suna yi mata jaje.
***A hankali ta shiga buɗe idanunta, saurin tashi zaune tayi tana kallonsa taga bama ita yake kallo ba, turo baki tayi cikeda shagwaɓa ta ce"Dodo zan ci abinci" waro idanunsa ya yi ya ce"wane ya ce miki sunana Dodo?" washe baki tayi ta ce"laaa, daman kana magana?" girgiza kansa ya yi bai ce mata komai ba ya tashi tsaye, tashi itama tayi ya kalleta kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce"idan baki zauna ba ina zan kawo miki abincin?" Maƙale kafaɗa tayi ta ce"ai bin ka xanyi, rakaka zanyi" girgiza kansa ya yi ya juya tayi saurin riƙe gefen rigarsa tana murmushi. A bakin wata Range rover ɗin mota baƙa ya tsaya ta kalleshi sai kuma ta kalli motar, buɗe motar ya yi ya ɗauko mata wata leda ya miƙa mata, langwaɓar da kanta tayi ta ce"ayyah ni ka barni na zauna anan" ta nuna motar, bai kalleta ba ya buɗe mata back seat ta shiga tana murmushi. Gaba ya shiga ya zauna ya kunna karatun Alkur'ani a motar, buɗe ledar tayi taga takeaway na fried rice wacce taji wadatattun kayan haɗi sai kaza akanta, ɗayan takeaway ɗin kuma soyayyen dankalin turawa ne sai aka yi garnishing na soyyayn kwai akai, lumshe idanunta tayi ta buɗe fried rice ɗin ta shiga ci tana lumshe ido alamar abincin ya yi mata daɗi. Saida ta cinyeta tas sannan ta ɗauki ruwa ta sha ta mayar da ledar ta ajiye tayi gyatsa tana kallonsa ta ce "nagama" jinjina kansa ya yi sannan ya juyo ya kalleta kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce"tafi gida kar Azo ana nemanki" turo baki tayi ta ce "ni ka tafi dani, nan babu daɗi bana zuwa makaranta, ni so nake na koma makaranta ka kai ni ka ji" waro idanunsa ya yi ya ce a hankali "to ai ni banida kuɗin kai ki makaranta" kallonsa tayi ta ce"kaiiii, wlh kanada shi, gashi har mota ka siya" murmushi ya yi wanda bata sani ba ya ce"wane ya ce miki motata ce?, ta uban gidana ce, ni driver ne kawai" shiru tayi sai kuma ta ce"to ka aramin kuɗin ka kaini makarantar, idan na samu zan biyaka" girgiza kansa ya yi yana jinjina hauka irin na yarinyar ya ce"wane zai bani aran?" murmushi ta yi ta ce"me gidan naka, kace ya ara maka, ni makaranta nakeso, kuma a dutse nakeson makaranta banaso anan garin Allah " murmushi ya yi ya ce"keda za'a arawa kuɗi kece kike kafa sharaɗin makarantar da zaki je?" Turo baki tayi, ya kalleta ta mudubi ya girgiza kansa kawai. Shirin da taji ya yi yasa ta kalleshi ta ce"zaka aramin ɗin?"
"Zan duba nagani"
Ya bata amsa a takaice, taɓe baki tayi ta fashe da kuka, juyowa ya yi ya zuba mata idanu ganin yanda take kuka babu dalili, ganin yanda yake kallonta yasa tayi shiru ta rufe fuskarta da hannayenta tana leƙensa, murmushi ya yi ya ce"Rigimammiya kawai!" kifa fuskarta tayi a cinyarta taƙi ɗagowa, y sanya hannunsa ya ɗago fuskarta yana murmushi ya ce"kema dai kinji kunya, ki je gida kar granny ta nemeki"
"Zaka sakani makarantar?"
Gyaɗa mata kai ya yi, tayi murmushi har saida beauty point ɗinta ya loma ta ce "thank you Dodona" lumshe idanunsa kawai ya yi bai ce mata komai ba, ta ɗauki ledar takeaway ɗin ta sauka daga motar. Saida ya daina hangota sannan ya yiwa motar key ya bar ƙauyen.
***Taɓe baki Baba Hansatu tayi ta ce"wannan yarinyar akwai fitinanniya ko ina ta baɗaɗa oho!" kallonta kawai granny tayi tama kasa magana, shigowa Imara tayi, saidai ganin mutane a tsakar gidan ya saka ta taja ta tsaya ba tareda ta ce komai, tashi Baba Hansatu tayi zata tafi sukai ido huɗu da Imara, tafa hannu ta shiga yi tana kallonta ta ce"to ga ja'irar yarinyar nan ta dawo" da sauri granny ta miƙe tsaye, wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke lokacin data hango Imara, da sauri ta ƙaraso gabanta ta riƙeta cikin sanyin murya ta ce"Imara ina kika je?, meyasa kika fita baki faɗa min ba?, meyasa!" kallonta kawai Imara tayi bata ce komai ba, Baba Yabi ta ce"ta yiwa mutane shiru kamar wata gunki, yarinyar mai kamada fatalwa" kallonta Imara tayi sai kuma ta fashe da kuka, ta shige ɗaki da gudu. Taɓe baki Baba Hansatu tayi ta ce"lallaima to wlh wannan yarinyar ki binciketa, ji fa harda wata leda ta yan gayu a hannunta, yanda take kamar balarabiyar nan babu wuyar an janyeta, saboda haka ki sanya idanu akanta!" Ta fice daga gidan, bin bayanta sukayi Granny ta bisu da kallo. Numfasawa tayi sannan ta shige ɗakin tana kiran sunan Imara.
Zaune ta sameta gefen katifa tana kuka a hankali, zama tayi kusada ita ta jawota jikinta, rungumeta tayi tana shafa bayanta ta ce"dan Allah Imara karki sake fita baki faɗa min ba, hankalina ya tashi sosai, ki faɗa min ina kika je?, wane kuma ya baki wannan ledar" lamo Imara tayi a jikin granny kasancewar ta mai son jiki, ɗanyatsanta ta sanya a baki tana tsotsa cikin shassheƙar kuka ta ce "ni ba yawo na tafi ba, wajen Dodo naje, shine ya bani abinci, kuma ya ce zai aramin kuɗi ya sani a makaranta" kallonta granny tayi ta ce"har yanzu kina ganin Dodon?, Imara kar fa ki je aljani ne ba mutum ba" saurin ɗagowa zaune tayi tana kallonta ta ce"mutum ne wlh, kuma yanada mutunci, muryarsa mai daɗi, kuma fari ne shima kamar ni, ba aljani bane, ya ce min shi Dodo ne ba'a ganin fuskarsa" murmushi Granny tayi ta ce"ke daɗina dake shirme, Allah ya kyauta dai".
Cikin lokaci ƙanƙani Imara ta saba da Dodonta, kusan kullum sai ta haɗu dashi, har granny saida ta san shi, haka kawai kuma ta ji ta aminta dashi, hidima sosai yake musu, duk wani abun buƙata yana yi musu tun kafin ma su tambaye shi.
Cunkoson daya hanga ya sanya ya tsaya da motar, dan gabaɗaya sun cike wajen babu ta inda zai samu ya shige, ɗan siririn tsaki ya ja sannan ya kashe motar ya sakko, ratsawa ya yi ta gefensu zai shige ya hangeta tana ta masifa kamar bakinta zai yage, tsayawa ya yi yana ganin ikon Allah ganin yanda yarinyar ƙaramar kamarta ta iya tashin hankali. Wata budurwa ce ta kalleta ta ce"ke me kamada aljanu kin ishi mutane, kinsan ai sun rigaki kice sai kin ɗiba, ke ba zaki bi layi ba?" wani banzan kallo Imara tayi mata tana riƙe kugu ta ce"wlh sai na ɗiba, dan wasa zan yi dashi, ai naga ƙaramin bokiti ne, kuma karki sake cemin aljana saidai idan kece aljana ba ni ba" ihu wajen ya ɗauka yara sai dariya suke suna sake tura Imara, hankade bokitan wajen tayi ta saka nata, wani yaro ya ture nata bokitin ya takashi ya fashe, wata iriyar ƙara ta saki ta fadi s wajen ta shiga burgima a cikin ƙasa. Baya yaran wajen suka yi suna cewa wai aljanunta sun tashi, ganin abun nata bana ƙare bane yasa ya ƙaraso wajen, darewa akayi ya ƙarasa inda take kwance ya ɗagota, kallonsa tayi sai kuma ta sake faɗuwa ta cigaba da kukanta, bai ce komai ba ya sunkuya ya ɗauketa kamar jaririya ya bar wajen da ita, mota ya sanya ta sannan ya yiwa motar key ya bar wajen. A ƙofar gidansu ya yi parking har sannan kuka take, ya kalleta fuska babu annuri ya ce"ke yimin shiru" tsit ta daina kukan sai ajiyar zuciya data shiga saukewa tana kallonsa, saida yaga tayi shiru sannan ya ce "meya kai ki wajen ɗiban ruwa bayan akwai famfo a gida?, ke bakison zaman lafiya ko?, duk inda ake tashin hankali sai kin je wajen ko?, Allah yasa na sake ganinki a wajen sai nayi miki duka" tura baki ta shiga yi tana kallon gefe, girgiza kansa ya yi ya ce"sauka ki tafi gida, idan kin shiga ki kiramin Granny" a ƙufule ta ce"batanan!" murmushi ya yi ya ce"to sauka ki ban waje, ko bana ce miki karki sake shiga harkata ba?" kallonsa tayi da idanunta wanda hawaye ya kwanta ta ce"ai bani na kula ka ba, ni babu ruwana da kai, na daina kulaka har abada" kafin ya yi magana ta sauka daga motar ta shige gida da gudu. Fitowa ya yi daga motar daidai nan Granny s fito daga cikin gidan, gaisawa suka yi ya ce"daman kayan makarantar Imara ne, in sha Allah ranar Monday zata fara zuwa, akwai driver da zai dinga zuwa yana ɗaukanta in sha Allah" murmushi Granny tayi ta ce"Allah sarki, ubangiji ya biyaka ɗawainiyar da kake mana, Allah ya saka maka da Alkhairi ya kula da naka ya'yan, na daɗe ban yi farin ciki irin na yau ba, Nagode sosai" murmushi ya yi ya ce"Ameen Granny, amma babu godiya tsakanina da Imara, duk wani abun da kika ga nayi mata, nauyi ne a kaina nayi mata shi, wanda kuma idan har banyi ba Allah zai iya tsaidani akan haka, Imara tamkar 'ya take a wajena, ita ɗin AMANATA ce, nauyinta a wuyana ya rayata saboda haka ki daina min godiya dan Allah" murmushi tayi ta ce"duk da dai bansan alaƙarka da ita ba, zanyi shaidarka a ko'ina, idan alƙawari ka yiwa wani zaka kula da ita to tabbas ka cika alƙawarinka, idan kuma ita ɗin jininka ce to ka kasance ɗan uwa nagari, Allah ya albarkaci rayuwarka" ajiyar zuciya ya sauke ya ce"Ameen ya rabbi, idan kin shiga ki ce tazo" to ta ce masa sannan ta karɓi kayan ta shiga gidan. Zaune ta hangeta kan tabarma tana shassheƙar kuka, ƙarasawa tayi ta zauna kan kujerar dake gefen tabarmar tana kallonta ta ce"to ɓaure sarkin kuka, ki je ana kiranki" kallonta tayi tana kuka ta ce"ni bazani ba, wlh ba zani ba, na daina kula shi, shima ya daina kulani, babu ruwana dashi" murmushi granny ta yi ta ce"shikenan, ya zo da abin daɗi ya ce kije zai baki chocolate" da sauri ta kalleta sai kuma ta ce"amma wlh bazan masa magana ba, kawai karɓowa zanyi na tawo gida, na daina kula shi" jinjina kai tayi ta ce"je ki to" tashi ta yi ta fice daga gidan.
# *Bestnovel*
# *heart touching 💔*
# *IMARA 💋*
# *Dodo*
# *Nanameera*
# *2025*.
*IMARA 💋💋*
Mikiya writers asso...
*Chapter 21-22*
Tsaye ta sameshi jikin motarsa yana danna wayar dake hannunsa, ƙarasawa tayi daf dashi ta miƙa hannunta ɗaya ta ɗauke kanta tana kallon gefe sai jijjiga ƙafa take yi, juyowa ya yi ya kalleta sannan ya kalli hannun nata, ɗan murmushi ya yi ya ɗauke kansa ya cigaba da danna wayar. Shirun da Imara taji ya sanya ta ɗan juyo tana kallonsa ta gefen ido, ganin kamar ma bai san tana wajen ba yasa ta juyo gaba ɗaya tana turo baki ta ce "ka bani zan tafi gida" ta miƙa masa hannunta, wayarsa ya zura aljihu ya juyo yana kallonta, kwaɓe fuska Imara tayi tana kallonsa, hannunsa ya harɗe a ƙirji yana kallonta ya ce"lafiya?" kamar zatayi kuka ta ce"chocolate ɗin zaka bani, ni tafiya gida zan yi ka bani kawai"
"Who stop u?", ya furta yana kafeta da idanunsa dake cikin glasses, wani kwarjini ya yi mata wanda ya hanata sake faÉ—ar wata kalmar, ta juya zata koma gida. Taku É—aya ya yi ya kamo hannunta ya dawo da ita gabansa yana kallonta ya ce"sarkin rigima!" shiru tayi masa tana sake haÉ—e fuska tamau ita bata yarda ba fushi take dashi, murmushi ya yi ya ce"shikenan yi murmushi na baki wani abu" kallonsa tayi hawaye ya zubo idanunta, hannunsa ya sanya ya share mata hawayen yana cewa"wannan hawayen naki daraja gare su, ki daina bari suna zuba koda yaushe" faÉ—awa jikinsa tayi ta fashe da kuka, murmushi ya yi kawai ya shiga patting bayanta har saida yaga tayi shiru. ÆŠago kanta tayi tana kallonsa bakinta na rawa ta ce
"To ba kai bane, ka ce ka daina kulani, me nayi maka?, kuma kasan banida kowa, ni Daddyna ya mutu, banida ƙawaye, ni kaɗai nake zama sai Granny, na daina kulaka nima, babu ruwana da kai" ta dunƙule hannunta tana dukansa, sake rungumeta ya yi yana dariya ya ce"shikenan I'm sorry babyn Dodonta kiyi haƙuri kinji, yanzu ina kulaki, bazan sake faɗa dake ba, kinsan me?" Girgiza kanta tayi har sannan tana ƙirjinsa sai sauke numfashi take a hankali, murmushi ya yi ya ce "Monday zaki fara zuwa school" wani tsalle tayi tana barin jikinsa, ta tafi ƙofar gidansu ta tsaya ta rufe bakinta tana dariya, kallonta ya shiga yi yana murmushi shima, dawowa gabansa tayi ta ce"ina kayana?, ka ara kudin?" shiru ya yi yana kallonta ta langwaɓar da kai ta ce" kake kallona haka?, to wa zai dinga bani kuɗin makaranta?, kaga banida kuɗi" numfasawa ya yi ya ce "ke zaki dinga biya mana" shiru tayi sai kuma ta ce"ai kasan banida kuɗi, duk ka ranta min, kuma ka siyomin abinci, ni da abinci nake tafiya makaranta" murmushi ya yi ya ce" Tom duk za'a baki," daga haka ya buɗe back seat na motar ya ciro wasu ledoji, miƙa mata ya yi ta karɓa cikin sanyin murya ta ce"Nagode sosai " harararta ya yi ya ce"bar nan" murmushi tayi sannan ta juya ta shige gida da sauri, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya shiga motar ya bar unguwar.
*Monday*
7:15am
Tsaye take ƙofar ɗakin hannunta riƙe da wani ƙaramin mudubi tana kallon fuskarta, Granny ne ce ta fito tana murmushi ta kalleta ta ce"oh, su oh'oh za'a fara zuwa makaranta" murmushi Imara tayi tana kallon mudubin ta ce"ya kika ganni?, nayi kyau?" jinjina kai granny ta yi ta ce"ai daman kinada kyanki, kin yi kyau Masha Allah" dariya ta yi ta ce"yawwa, kuma granny naga har yanzu bai zo ba?, ko ba shine zai kai ni ba?" Dafe kai tayi ta ce"yau naga hayyatacciyar yarinya, ba sai ya gama abin da yake ba zai zo?" langwaɓar da kanta tayi ta ce"ai sauri nake ne"
"Sai ki tashi sama ai" granny ta ce tana barin wajen, turo baki tayi ta ajiye mudubin ta shiga gyara akwatin dake gabanta, ganin har ta gama bai zo ba yasa ta koma kan tabarma ta zauna ta zuba uban tagumi kamar wacce aka yiwa mutuwa. Ƙarfe bakwai da rabi daidai granny ta fito daga ɗakin hannunta riƙe da rediyo tana jin kanun labarai, wani abu ne ya zo ya tokarewa Imara a ƙirji ganin kamar ma granny bata damu da lamarin nata ba, kujera granny ta samu ta zauna tana sauraren labaranta hankali kwance.
Kwantawa tayi a kan tabarmar ta shiga burgima tana kuka, kallonta granny ta shiga yi baki buɗe, tana ƙoƙarin yin magana aka yi sallama aka shigo. Tsam ta tashi zaune ta shiga share hawayen nata, tabarma granny ta shinfiɗa masa ya zauna bayan sun gaisa ya ce"me aka mata kuma?" jiki a sanyaye granny ta ce"wai saboda baka zo ba shine take kuka" kallonta ya yi yaga tana share hawaye, murmushi ya yi ya ce "in dai makaranta ce sai ta gundireki, keda zaki je ki zauna a can?" turo baki tayi bata ce komai ba, suka yi sallama da Granny sannan ya tashi ya fita. Tashi itama tayi tana kallon granny, da gudu ta faɗa jikinta tana kuka, granny was couldn't help it but cry, gaba ɗaya tausayin yarinyar ya kamata, tunanin yanda zatayi rayuwa a makaranta na tsawon wani lokaci. Saida sukayi mai isarsu sannan ta rakota har bakin mota, ta shiga tana ɗaga musu hannu har suka ɓacewa ganinta.
Secondary school (Hadejia) boarding section.
Murmushi ya yi yana kallonta ganin yanda ta fara mitsi mitsi da idanu ya ce"ohya tafi mana" turo baki tayi tana shirin yin kuka ta ce "ni anan zaka barni?" jinjina mata kai ya yi yana zura wayarsa a aljihu ya ce "Eh mana, kiyi karatu da kyau kin ji ƴar albarka" fashewa tayi da kuka ta rufe fuskarta da hijab ɗin jikinta, kallonta Directorn ya yi yana murmushi ya ce"ƴar Baba me rigima, ke da zaki shiga secondary school kece kike kuka?, ai murna zaki yi, babu abin da za'a yi miki a school ɗin nan, zaki yi rayuwarki kamar a gida, kuma ai time to time zai dinga kawo miki ziyara" tashi tayi ta fice daga office ɗin tana kuka, tashi shima ya yi yabi bayanta. Tsaye ya sameta jikin wani block ta rufe fuskarta sai kuka take, ƙarasawa ya yi, ya sanya hannu ya tallafi fuskarta yana murmushi ya ce"bansan rigima fa Imara, school ɗin ne kuma baki so yanzu?" cikin shassheƙar kuka ta ce"ni ba school ce bana so ba, ni bazan kwana ba, ni a gida zan dinga kwana, banason boarding, ka maidani gida Dodo, wlh indai nan ne banaso to" shiru ya yi yana tunanin hanyar da zai ɓullo mata, above 5mins kafin y ce" idan har baki yarda kin zauna a school ɗin nan ba, bazan sake zuwa inda kike ba, ba zaki sake ganina ba har abada, zan rabu dake ne" ɗago runannun idanunta tayi ta zuba masa ido, ɗauken kansa ya yi yana kallon gefe ya ce"shige mu je" goge hawayenta tayi ta yi gaba, numfasawa ya yi sannan yabi bayanta, ga mamakinsa sai yaga tayi hanyar inda aka kwatanta musu hostel ɗin nasu, cigaba ya yi da bin ta har suka je ƙofar hostel ɗin sannan ya ga ta tsaya. Kallonta ya shiga yi ta juyo a hankali tana sake goge idanunta ta ce"ka tafi kawai, zan zauna anan, koda bazan ji daɗi ba, zan yi karatu mai yawa kodan nasamu na biyaka kuɗin ka, zan zauna karka damu, Daddyna kafin ya mutu ya cemin na karɓi duk abin da ya zo min a rayuwa, ta iya yiwuwa wannan shine Alkhairin nawa, in sha Allah zan karbe shi hannu bibbiyu" . Tunda ta fara magana yake bin ta da kallo, kalamanta sun fi ƙarfin shekarunta, tanada kaifin basira sosai kuma ta iya faɗar magana, ya ɗan nisa kafin ya ce"idan kinga baki son makarantar nan sai na sauya miki Imara" murmushi tayi mai haɗe da hawaye ta ce"Karka damu kanka, zan zauna anan, Nagode sosai" ba dan ransa ya so ba, sai dan baya son yana dinga ja in ja da ƙaramar yarinya ya yi murmushi ya ce"shikenan, kiyi karatu da kyau kinji IMARA " jinjina masa kai tayi tana murmushin itama. Sallama suka yi ya bar makarantar ita kuma ta shiga hostel ɗin nasu. Tun daga wannan ranar Imara ta maida hankalinta kan karatu, duk wani abu da za'a yi na cigaban makaranta zaka sameta a gaba, hatta malamai saida suka shaidata akan wannan, saidai batada ƙawa ko guda ɗaya, rayuwarta take ita kaɗai batasan mene ne zama ayi hira da ƙawaye ba, iya ka cinta da ƙawa a gaisa. Tun daga wannan ranar kuma Dodonta bai sake zuwa ba, tun tana saka ran zata ganshi har ta fara cirewa, saidai duk sanda ta samu dama ta zauna tayi kuka, dukda bata taɓa rasa abun buƙata ba, dan duk wani abu wanda zata buƙata da ma wanda bai zama dole ba saida ya wakilta wanda zai dinga bata, lokaci zuwa lokaci granny ta kan kawo mata ziyara ta tawo mata da wani abun itama. A haka rayuwa ta cigaba da garawa mintuna na shuɗewa yi zuwa awanni, awanni na shuɗewa i zuwa kwanaki, kwanaki na shuɗewa i zuwa watanni, watanni na shuɗewa i zuwa shekaru har Allah ya kawota ajin ƙarshe, kuma satin ƙarshe.
***Zaune suke a ƙasan wani block wasu suna riƙe da wayoyi, wasu kuma suna faman hira, Imara kuwa na can gefe kusada wasu ciyayi ta zauna, tunani ne fal ranta, babu abin da take marmari sai komawa gida, Allah Allah take su ƙarasa papern yau wacce ta kasance catering craft ce ta koma gida, tana cikin wannan tunanin ta zo ta dafata. Zama tayi gefenta tana murmushi ta ce"Mrs so silent, ke koda yaushe shiru abin ki?, yau fa zamu yi candy amma kin kasa sakar jikin ki da kowa?, kina gani anata ɗaukan pictures an zo da zafafan wayoyi amma ke kina nan zaune kina tunani, wai meke damunki ne?" ɗan murmushi Imara tayi cikin wata daddaɗar murya ta fara magana
"Ni banga aibu da na zauna ni kaɗai ba, beside ma kinsan ni I'm not familiar with people, nafison na zauna ni kaɗai a kammala exams muyi assembly na tafi gida" taɓe baki Fahima tayi ta ce"taɓ, kina koko, bar ma wannan, sai yaushe zaki bawa brother na dama ne Imara?, kinsan yanda yake son ki kuwa?, wlh mun kasa gane kan yaya basheer saboda ke, kowace mace sai ya ce bata yi masa ba, kinsan daman shi a tsarinsa yana son auren mata kyakkyawa, irin shuwa haka, kema kuma gaki da kyau kamar balarabiya, fatan dai ba wani kika rigada kika mallakawa zuciyar taki ba, dan nasan babu wani namiji da zai ganki ya gyale", kallon Fahima kawai tayi ta ɗauke kanta tana wasada fingers ɗinta wanda suka kasance dogaye masu kyau, sanin halinta yasa Fahima tayi dariya ta ce"to bebiya, tunda ba zaki yi magana sai ki tashi muje an kawo paper" "tom, mu je" taji Imara ta furta bayan ta miƙe tsaye, girgiza kai kawai tayi ta ce"Allah ya shirye ki"
12:45pm
Shiru wajen assembly ɗin ya ɗauka kasancewar Directorn da aka sauya mace ce kuma mafaɗaciya, bayan ta kammala jawabai aka fara kiran ɗaliban da suka kasance masu hazaƙa a cikin makaranta. Sunan Head girl aka fara kira wato Imara Ahmad, tafi wajen ya ɗauka wasu na fito, kowa ya yarda Imara ta cancanci girmamawa daga makaranta, bayan an bata kyaututtuka aka yi musu hoto da malamai sannan aka sallami kowa. A bakin gate kowa ya samu danginsa sun zo tafiya dashi, da idanu Imara ta bisu tana tunawa da Daddynta ta tabbata da yana raye shine zai fara zuwa kafin uban kowace Yarinya,
"Barka dai yammata"
A ɗan firgice ta juya, tsaye yake cikin wasu kananan kaya na riga da wando ya sanya glasses baƙi a idanunsa, ɗan dogon namiji ne amma bashida haske saidai kana ganin fatar tasa kasan a wuce yake, ganin kamar ta ɗan yi nisa yasa ya kyasta hannunsa, kallonsa Imara tayi sai kuma ta ɗauke kai, murmushi ya yi ya ce"ko bakya magana ne Imara?" ɗan sunkuyawa tayi ta ce"ina yini" murmushi ya yi ya ce"lafiya klao, an gama exams lafiya?" "Alhamdulillah" ta furta a gajerce. Fahima ce ta ƙaraso gurin tana murmushi ta ce"Yaya mu tafi na matsu naga Mommy" kallonta ya yi ya ce"Tom yar gidan Mommy, mu tafi mu bar ƙawar taki?" kallon Imara tayi ta ce"haba mu tafi tare sai mu kai ta gida" ta jawo hannun Imara ta ce"muje friend" girgiza kai Imara tayi tana sake ƙanƙame gifts ɗin hannunta ta ce"no zan tari napep ya kaini kawai ku je, Nagode" harararta Fahima ta yi ta ce" dalla banason irin haka, ki shige muje na ce" murmushi kawai Imara tayi dan idan batayi niyyar yin abu ba babu wanda ya isa ya sanya ta tayi, ganin ta cake yasa Basheer ya ce"rabu da ita Imara, saboda Allah shiga na sauke ki, karki daɗe baki je gida ba, ko bakison kiga relatives naki ne?" gyaɗa masa kai kawai tayi sannan ta bude motar ta shiga, a boot aka sanya trolley ɗin nasu sannan suka bar makarantar.
# *Bestnovel*
# *IMARA 💋*
# *Dodo*
# *Granny*