← Book details Hayatiy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 9

Sashe 8

Hayatiy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yayin da SUHAIL ya kyankyame SUHAILA duk da yunwar ds take ji nan take ta daina kuka madara abou ya siyo da kan shi ya bata tasha sosai har ma tai barci.

Ko da Momah ta farka Abou ya mata bayani tayi farinciki ds hakan sosai,abu daya ne ya dameta sanar da su ciwon SUHAILA da likita yayi sun san cewa SUHAIL na sani za a shiga matsala domin bashi kadai ba su kansu Allah ya jarabesu da matuƙar kaunar SUHAILA.

Madara aka ci gaba da bai wa SUHAILA har girmanta.

Ya yin da Abou ya fara juya wannan dukiyar da tai sanadin arzikinsa.

Tunda Momah ta haifi SUHAIL duk cikin da ta samu sai ya zube.

Wannan har ya kai wata biyar shima ya zube wanda yazo da hadari ina bukatar mata aiki ajuya mahaifiyar tare da wankin ciki,amman basa da halin wannan.

Ci gaban labari...

Attajirin ya ci gaba da magana, "Ina maku fatan Alkairi."

Daga wannan maganar ya bace.

Ya yin da SUHAILA ta farka....

*SHIN ME KUKE TUNANIN ZAI FARU?*

Urs xayyeesherthuo

*HAYATIY حياتي*
1/10/2021
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_
_(Mrs Ɗangote)_

_*HAYATIY:* Labari mai cike da tsantsar Soyayya, Amince tare da Sadaukarwa,sarƙakiya mai ban mamaki_

PAGE-14

*HAYATIY FANS🙏NA SAN KUNA HAKURI AMMAN DAN ALLAH KU KARA WANNAN FEJINMA GUNTU NE KAWAI NAYI NE DANKU KU CI GABA DA MUN ADDUA ALLAH BANI LAFIYA DA IKON YI MAKU MAI YAWA*

SUHAIL ta fara kira abakinta.

"Yayana,Yaya Ka zo ka ji, Yaya ka zo." Tana Maganar tare da mika hannunta idanunta arufe.

Likitanne ya yi saurin zuwa ya sanar da su domin SUHAIL yaje suhaila ta farka.

Ko da ya shigan ma shi kawai take kira.

Saurin karasawa gareta ya yi tare da riƙe hannunnata.

Nan take ta bude ido tana fadin, "Ina Sonka Yayana,ba zan iya rayuwa ba in babu kai kar ka tafi ka barni kaji."

"Nima Ina Sonki SUHAILA,ina kaunar ki,kece Farinciki na kinji."

"To ba ka ce ba zaka tafi ka barni ba."

"Ina so na rayu da ke kuma bana son in tafi in barki kinji Hayatiy na, yanzu ki bar surutu haka kinga ba kya da lafiya."

Kwanan SUHAILA biyar aka sallameta a asibiti.

Tsantsar So da Kauna tare da tausayin SUHAILA ya kama su fiye da,babbar matsala da damuwarsu a yanzu shine yadda za a tinkari SUHAILA da maganar Auren SUHAIL.

Zaune suke afalo Abou ya fara magana .

"Yawwa daman ina son magana daku, SUHAIL kayi girman da dole akwai bukatar fadama kai wanene ,bana so ko fatan na bar duniya ba tare da na sanar da kai sirrin da muka binne shekara da shekaru ba."

Nan Abou ya kwashe duk abun da ya faru da SUHAILA ya mai da shi ga SUHAIL.

Hawaye ta fara ta tashi ta karasa gun yayan nata tare da rike masa hannu tana , "Yaya kayi Hakuri kar ka yi kuka kaji, Dan Allah kar ka yi kuka, nikam na bar ma Abou da Momah kyauta har ma da Kakata, Yayana ina sonka kar ka ce zaka bar mu kaji sorry."

Ta fashe da kuka tana rungumarsa.
SUHAIL ma ya rungumeta yana murmushi, "Shikenan ai ni ban yi kukan ba kinyi ina zan yi kuka kin bani aron Abou da Momah Oyaaa smile HAYATIY."

Ya fada yana share mata hawaye.

Murmushi tai ta ce, "Umm ba Aro ba na baka kyauta kaji."

Kumatun ta ya rike yana, "Thank you Hayatiyn Yaya,amman kin san miye? Zan yi kuka in baki yarda da wani abu ba."

Shagwabe fuska tai tana, "Yaya Kar ka yi kuka ni bana so kar kayi kaji,kar ka yi fadamun zan yarda ni bana so ka yi kuka."

Rike hannunta yaiy tare da tashi, "Zo muje muyi magana sirrine bana so Momah da Abou su ji."

Murmushi Momah da Abou ,tare da kaka su ka yi lokaci guda kasancewar sun san maganar da SUHAIL zai ma SUHAILA.

Gwalo tai wa kaka tana, "Ba dai za ki ji me za mu ce ba."

Kaka ta ce, "Yoo me za ku ce da ya wuce maganar doyar turawa."

Suna fita wajen dai da suka saba zama domin tattaunawa suka nufa.

"Hayatiy kina son Yayanki?"

Ta girgiza kai alamar eh

"Zaki iya Auren Yayanki?"

Wani irin faduwar gaba SUHAILA ta ji
Nan da nan hawaye ya fara zubo mata.

SUHAIL ya ce....

*ME KUKE GANI SUHAILA TA AMICE KO KUWA A'A?*

*XAYYEESHERTHUO*

*HAYATIY حياتي*
3/10/2021
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_
_(Mrs Ɗangote)_

_*HAYATIY:* Labari mai cike da tsantsar Soyayya, Amince tare da Sadaukarwa,sarƙakiya mai ban mamaki_

*PAGE-15*

*SADAUKARWA GAREKU HAYATY FANS GROUP❤️*

*AMEENATOU YAR KAKA YANA HANYA IN SHA ALLAH KU GYARA ZAMA🥰*

"Hayatiy in bakya sona ki fada kinji,ba zan miki dole ba kuma ba wanda zai miki dole domin zabinki shine Farincikin ki."ya karasa maganar yana share mata hawayen da ke fuskarta.

Dagowa tai ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kai,cikin sanyayyar Muryarta ta ce, "Ni Yaya Ina so,kuma ni Bana son kowa."

Murmushi SUHAIL ya yi, "Hayatiy indai wannan maganar zata sa ki takura tare da jin kunyata. To kawai abari in nemo miki Anty."

Bata rai tayi ta dago tare da shagwabe fuska, "Yaya ni bana so, bana so, Ni ni ni kadai ka ke so,kuma ni kadai za ka.....

Sai tayi shiru.

Suhail ya ce, "Karasa Mana."

"Uhum,uhumm , uhumm ni." Ta fada tana kokarin tashi.

Dasauri ya rike hannunta yana, "ni sai kin fada ko nai fushi."

Cikin shagwaba ta ce, "Yaya hannuna zafi ka sake mun zan zauna kaji."

Sake mata hannun ya yi yana, "Sorry Hayatiy."

Kamar zata tauna sai kuma ta tashi ta zura aguje har taje kofar falo kan juyo, ta ce, "Yayana Zan Aura."

Ta shige ciki da gudu.

Murmushi SUHAIL ya yi yana hamdala aran shi yake fadin, "Tabbas SUHAILA ce rayuwata in ba ita ba zan iya komai ba,ina sonki HAYATIY."

Tana shiga ta dane cinyar Momah tana dariya.

SUHAIL ya biyo baya yana, "zan kama ki ai."

Abou ya yi gyaran murya kan ya ce, "To yanzu sai akiyaye, ina tunanin mu bari SUHAILA ta karasa karatunta kan afara maganar aure."

SUHAIL ya fara sosa kyeya,yana so ya yi magana amman ya kasa.

Kaka ta kalleshi.

"To fa akwai magana tunda kaga ya fara sosa kyeya kamar kunkurun karkara."
Abou ya kalli SUHAIL kan ya ce, "Meya faru in hakan bai ma ba ka fada."

Ya ci gaba da sosa kyeya , "um Um Abou daman Wai,in da Haline Ayi Yanzu."

Kaka ta ce, "yoo ga magana nan ta fito ai daman nasani kuna ganin shi da ido kamar gurjiya."

Murmushi kawai Abou ya yi kan ya ce, "Shikenan ba matsala ku fara shirin biki nan da sati in sha Allah, tunda angama gina sabon gidan can ma."

Ba karamin dadi SUHAIL ya ji aranshi ba domin gani yake in aka ja bikinnan za a kwace mi shi Rayuwarshi.

,,,,Nan da nan aka fara shirin biki ba kakkautawa ya yin da Momah ta dauke SUHAILA agidan ta maidata gun kawarta domin gyarata.

Kullum SUHAIL ban da kewar SUHAILA ba abun da ke damunshi itama haka,ba yadda suka iya haka sukayi hakuri domin hatta wayarta Momah ta kwace ta ce baza su hadu ba har sai ranar daurin Aure.

Wasa-wasa akwana atashi yau ta kasance ranar daurin auren SUHAIL da Hayatiy.

Ya gama shirin shi tsaf za a tafi daurin aure ya wuce dakin Hayatiy.

Ganinta ya yi bakin gado zaune tayi shiru tana ganinsa ta tashi da sauri ta rungumeshi.

Zaunar da ita ya yi kan shima ya zauna.

"Yaya Da gaske kai ne mijina? Da gaske kai zan aure? Zamu rayu har karshen rayuwa,ina sonka Yayana ka mun alƙawari ba za ka rabu dani ba dan Allah,dan Allah kaji."

Ta karasa maganar tana kuka.

"Hayatiy ina sonki fiye da tunani ko zatonki,ina so inyi rayuwa da ke fiye da kowa afadin duniyarnan kullum ina fada miki kece rayuwata da gaske hakan ne ba wasa ba,kimun alƙawari za ki kulamun da kanki duk rintsi duk wuya,ki rikemun mutuncinki da kimarki na 'ya mace ina miki so fiye da zaton kaina."

"Yaya nima ina sonka kuma ina so mu rayu tare,ina sonka sosai ba kadan ba,ko nama laifi karka rabu dani kaji,ina sonka."

"Ko da bana duniya zuciyoyinmu na san suna tare kuma zasu kasance cikin farinciki, Kanwata, rayuwata,kuma farincikina, haka kuma matar da nake burin aure ina matukar kaunarki Hayaty."

Ta kara rungumeshi, " nima ina matuƙar kaunarka Yayana kaji,na fi kowa sonka aduniya kuma ni kai yayana ne kadai ba na kowa ba,yayan Hayaty ne ko?"

Taji shiru.

Ta kara magana, "Yaya ina kai nawane Ni kadai ko?"

Har yanzu dai shiru.

Ta fara shagwabewa zata yi kuka, "Yaya kamun magana zanyi kuka fa,ina kai yayana ne ni kadai?"

Ta fara jijjiaga shi ba alamar motsi atattare da SUHAIL, kuka ta fara tana, "Yaya ka fadamun kace Ni ƙanwar kace ni kadai kar kace kadaina sona dan Allah,ina sonka kaji,yaya kadai na wasannan kamun magana,ni kamun magana, ka tashi kamun magana kaji."

SUHAIL ya bingire kan gadon ba numfashi kuma ba motsi

Innalillahi-wa inna-illaihir-raji'un

_*dukkan mai rai mamacine*_

Dukan kirjinsa ta fara tana, "Dan Allah yaya ka mun magana ,bana so,na ce ma ni bana so kumun magana dan Allah,zan yi kuka,wallahi kuka xanyi yaya ka tashi,nq ce ka tashi."

Gani tai bai da alamar magana ko motsi

Wata irin kara tai da sai da ta kauraye gidan kaf

"Yaya ka tashi,ka tashi dan Allah, kwanciya ajikin sa tai tana kuka."

Tuni jini ya fara fita ta hanci, da bakin .

Momah ce ta fara shigowa sannan yan biki abayanta SUHAILA ta dago tana.

"Momah dan Allah kicewa Yaya ya tashi bana son wasannan ni bana so,wallahi ina son yayana, Kuma shi nawane ni kadai."

Wani irin jirine ya Fara ketowa Momah.

SUHAILA kuwa nan take ta fadi sumammiya.

*DOMIN SHARHI KO TSOKACI KU TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER,08103080717*

Urs xayyeesherthuo

*HAYATIY حياتي*
9/10/2021
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*
Chapter 8 · 0% Book details