Sashe 7
Hayatiy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana shiga ya karasa gadon da SUHAILA take ya kwanta ajikinta tare da fadin, "HAYATIY, shin da gaske kike daman zaki tafi ki barni? Da gaske kike kin fi so ki rigani barin duniya? SUHAILA na fada miki kece rayuwata, dan Allah kada ki tafi ki barni, kada ki tafi,ina sonki SUHAILA na ce miki ina sonki ba zan iya rayuwa ba in babu ke, kece rayuwata dan Allah kar ki mun haka ki dawo mu rayu tare kin manta alƙawarin da ki ka mun ne? HAYATIY ki tuna alƙawarin mu zamu rayu tare dan Allah kar ki mun haka ki dawo mu rayu."
Fashewa ya yi da kuka yana kara kwanciya ajikinta.
Ban da fadin Innalillahi-wa inna-illaihir-raji'un ba abun da abou ke yi domin ga Momah can assume SUHAILA ma kwance ,haka SUHAIL hankalin sa ya bar jikinsa.
Ban da sambatu ba abun da yake yi.
Daga karshe bai san lokacin da wani irin barci ya kwashe shi jikin SUHAILA ba
Momah kuwa anfita ita adakin an kaita na hutu domin ana sa ran farfadowarta a cikin mintuna kadan.
Kamar cikin mafarki SUHAIL ya fara jin numfashin SUHAILA tana kiransa a hankali.
Afirgice ya farka da mamakinsa kuwa tana numfashi amman bata kiransa.
Da gudu ya fita yasanar da Doctor,da mamaki kuwa doctor ya tarar SUHAILA na nunfashi.
SUHAIL ya rike hanun doctorn tare da fadin, "Umar dan Allah ka taimakeni koda ni ba zan rayu ba SUHAILA ta rayu acire koma miye nawa asa mata kuma kamin alkawarin cewa ba zaka sanar da su abou ba."
Ba yadda doctorn ya iya domin ya san shaƙuwar SUHAIL da SUHAILA hakan ya sa shi amincewa domin yin wannnan aiki mai tattare da babban hatsari.
Batare da su Abou sun sani ba aka fara shirin aiki SUHAIL yasa hannu nan take aka shigar da SUHAILA da SUHAIL dakin opretion .
Momah na farkawa ta kalli Abou, "Ka ga ni ko? Wai da gaske SUHAILA ta mutu? Da gaske ne? Dan Allah ka ce mun karyane Abou kaji, shikenan asirinmu ya tonu Farincikin ahalinmu ya tarwatse zan mutu nima nasan mutuwa zan yi kawai."
"aa Aisha kiyi masu addu'a duka , wannan ƙaddarar mu ce kuma kada ki yi sako wa Allah gode masa ya kamata mu kasance masu yi akullum."
Shigowar doctor ne ya katse su yana fadin, "Abun mamaki abun al'ajabi SUHAILA na raye kuma in sha Allah ayau zamuyi maganin wannan lalura tata domin yanzu haka anyi nisa wajen yi mata aikin."
Tashi Momah tayi ta zaune tare suka furta. , "Alhamdu Lillah Allah mun gode ma."
Abou ya ce, "to doctor SUHAIL fa yasani?"
Doctor ya yi shiru can kuma ya ce, "E,e yana ma tare da ita yanzu haka."
Abou ya kalli Momah" yanzu abu mafi mahimmanci shine muyi alwala muyi sallah domin nuna godiyar mu ga Allah daman na fada miki Allah na tare da mu kuma shi zai yi mana magani,kinga komai yazo cikin sauki ko?"
Murmushi kawai ta yi tana mai jin dadi aranta.
Zuwan Wani Attajiri ne ya tsaidasu tare da fadin , "Dan Allah ko kai ne Alhaji Muhammad?"
"Eh" Abou ya amsa cike da mamaki.
Murmushi wannan Attajirin Ya yi kan ya ce, "Na san za ka yi mamakin ganina ko? Amman kafin nan ina Suhaila? Ina fatan tana cikin koshin lafiya? Dan naji ance sanadin ta kukazo asibitin nan."
Wani irin kallo Abou da Momah suka ma juna.
Niko nace anzo wajen.
Cikin dimuwa Momah ta ce, "Shikenan dukkan komai zai bayyana rayuwa ta fara juya mana baya." Ta karasa maganar tana faduwa
ƙasa.
Attajirin ya ce," ....
*†Ahito awasa kwakwalwa,shin wannnan mutumin waye?sannan kuma meke shirin faruwa?†*
08103080717
Urs xayyeesherthuo
*HAYATIY حياتي*
28/09/2021
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```

*https://www.facebook.com/106494781436168/*
_*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_
_(Mrs Ɗangote)_
_*HAYATIY:* Labari mai cike da tsantsar Soyayya, Amince tare da Sadaukarwa,sarƙakiya mai ban mamaki_
*PAGE-12/13*
_*HAKURI MAI YAWA GAREKU MASOYA😫BANA DA LAFIYA NA KASA TYPING,NA GODE DA KULAWAR KU GARENI*_
_*DOMIN KU KADAI MY GROUP MEMBERS INA YINKU HAYATIY FANS GROUP MUJE ZUWA*_
"Banzo dan tada maku hankali ba ko wani abu, nazo ne domin tunatar da ku cewa tabbas wani cikin dangin SUHAILA na raye."
Momah ta Bude baki.
"Dangin SUHAILA Kamar ya?,Ban Fahimta ba, Dangin SUHAILA fa."
Murmushi ya yi kan ya ci gaba da magana.
"Sosai kuma kada kuyi Mamakin Hakan,Nine na rubuto komai na jikin takardar kuma duk labarin SUHAILA Gaskiya ne ba ƙage ko kadan,kar kuyi mamaki innace maku agabana ɗanku ya dauketa kuma ina lura da komai da ke wakana agidanku."
Abou ya ce, "Ikon Allah kenan."
Murmushi wannan dattijon ya yi kan ya ce, "Ina SUHAIL? Ina bukatar ganinsa cikin gaggawa domin da kwai maganar da zamu tattauna da ku duka ayanzu tana da matukar muhimmanci."
Kan Abou ya yi magana SUHAIL ya fito daga dakin operation,ya jima da farkawa amman kasancewar ba yaso su Abou su fahimci komai ya tsaya har sai da ya gama dawowa hayyacinsa.
Ganin Iyayen nasa ne yasa shi kakalo wani murmushi yana karasowa garesu a hankali .
Attajirin ne ya yi murmushi tare da kallon shi yana fadin, "madalla da kai ɗana, madalla da kyawun dabi'u irin naka,in babu damuwa Ina so mu samu waje mu zauna domin tattaunawa."
Kallon Abou SUHAIL ya yi da alamar tambaya.
Murmushi Abou ya yi tare da fadin, "SUHAIL kar ka damu muje mu zauna zaka fahimci komai in sha Allah."
Bangaren da mutane ke zama domin ganin likita suka nufa kasancewar darene ba kowa.
Attajirin ne ya fara jawabi kamar haka, "Kamar yadda kuka sani kuma na sani SUHAILA tamkar haske ce ga rayuwar duk wanda take tare da shi,banzo da niyar kwace maku ita ba, illa sanar da ku wacece SUHAILA, bazan manta da ranar da kuka samu SUHAILA ba domin ni na aje maku ita, kan nan ina so ku sani cewa SUHAIL Ne Mijin SUHAILA akwai bukatar daura masu aure cikin gaggawa,SUHAILA 'Yace ga Wani Hamshakin mai kudi kuma Attajiri mai suna Muhammad Sa'id wanda bai da dangi face matarsa Ramla da cikin da ke jikinta, kwatsam abokan kasuwanci tare yaransa suka haɗa baki domin hallakasa tare da matarsa dan su kwashe wannan arzikin,sunyi nasarar kashe Muhammad Sa'id ya yin da matarsa ta tsere da cikin da ke jikinta aranta tasa cewa ko da ba za ta rayu ba tana son yarta tazo duniya kuma ta rayu kamar kowa,kar kuji mamaki innace maku ni ba BIL ADAM bane."
Abou, Momah da SUHAIL suka tsaya kallon juna cike da Mamaki.
Ya ci gaba da magana, "Kada ku tsorata kuma kada ku sa komai aranku domin ni banzo dan cutar da ku ba koda wasa, yayin da Mahaifiyar SUHAIL ta samu damar tserewa yayin da ta gama jigata ba mai taimakonta sai Allah domin daji ta shiga wanda ba ta san gabansa ba bare bayansa, alokacin Allah ya kawoni ta tsaka da nakuda,na matukar tausaya mata, hakan yasani taimakonta har ta haihu sannan ta fada mun dukkan abun da ya faru a karshe ta bani mukudan kudaden da kuka tsinci suhaila tare da su,kuma wa innan kudaden ko kwata ga arzikin Mahaifin SUHAILA bai kai ba,in manta ba ajikin takardar nan na sanar da ku cewa yarinyar ta jigata sosai kan tazo duniya akwai bukatar ta ga likita,wanda shine musabbabin ciwon nan da ya kamata har da yau akai mata aiki,ina sane da bawa likita ya dubantan da kuka yi har zancen cewa aboye ws SUHAIL, ni ba Mutum bane kamar yadda na sanar da ku hakan ya sani fidda SUHAILA awannan dajin yayin da mahaifiyarta ta rasu,kuma na kawota wancen asibitin ba wai dan bana Sonta ba,illa nasan cewa ba zata iya rayuwa cikin Jinsin da ba nata ba,in ma ta iya to tabbas na kwareta,sannannake so ka auri SUHAILA ba illa tamkar garkuwa take arayuwarka,kai ne mafi dacewa tayi rayuwa da shi hakan yasa ba wanda ya ganta illa kai domin da kai tafi cancanta ku rayu tare, lokaci ya yi, lokacin da zanxo ne Yayi domin suhaila tana matuƙar so da kishinka, abu daya ke tarwatsa mata tunani cewa ku yan uwan junane,dan haka na san kai ma kana sonta ka ma fi kowa sonta aduniya ,abu daya nake so kumin kada ku taba bari SUHAILA ta san cewa ita ba yarku ba ce,ina so ya kasance kun nuna mata cewa SUHAIL ne ba danku ba,domin nuna mata cewa ku ba iyayenta bane tamkar barazanace ga rayuwarta har ma da taku,ina so wannan sirrin ya kasance iyaka ni da ku."
Numfasawa Momah tai ya yin da Abou ya tafi dogon tunani.
*WAIWAYE*
Wata rana juma'a da afkuwar Jarabawa tare Alkairi ya kasance duk ga wannan ahali
Momah ce rangaranga ba lafiya,ban da jini ba abun da ke gangarawa daga jikinta bakin asibiti kasancewar basa da kudin aikin da za ayi mata.
Abou zaune gabanta ya yi tagume ya rasa abun fadi ban da hawaye ba abun da ke kwarara a idanunsa.
Yanayin da SUHAIL keta zagaya asibitin.
Kwatsam ya ga jaririya cikin ciyayi tana kuka gefenta wata tsimmace tare da takarda.
Ihu SUHAIL ya yi tare da fadin, "Abou ga Babyn Momah anan bata mutu ba."
Dasauri Abou ya ƙaraso mai zai gani jaririyace abar tausayi ban da kuka ba abin da take,tausayinta yasa shi saurin mantawa da damuwarsa tare da daukanta,abun mamaki sai ga makudan kudi da wata farar takarda sun fado kasa.
Takardar abou ya fara karantawa
"Wannan 'ya amanace ga duk wanda ya tsince ta,kuma wannan kudaden Mallakinta ne,sannan ya hallarta ga duk ahlin da suka tsince ta zasu iya rayuwa da su kuma rayuwa mai inganci, alƙawari daya kada abari ta zubda hawaye mara dalili ita din amanace,akaita asibiti aduba lafiyarta domin ta sha azaba kafin zuwa duniya,bata da suna amman kuna da damar sanya mata suna, kuma tabbas watarana ina zuwa."
Alokacin Abou ya daga hannu sama tare da godiya ga Allah domin kuwa an samu warakar Momah cikin sauki ga kuma ɗiya da suke da matukar bida.
Nan da nan Abou ya biya kudi aka fara yiwa Momah aiki nan take.