← Book details Hayatiy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 9

Sashe 9

Hayatiy Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

_*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_
_(Mrs Ɗangote)_

_*HAYATIY:* Labari mai cike da tsantsar Soyayya, Amince tare da Sadaukarwa,sarƙakiya mai ban mamaki_

_*PAGE-16*_

🔚🔚🔚🔚🔚🔙🔙🔙🔙🔙🔙🔙🔙🔙🔙🔙

_Allah ya yi,Labari mafi gajarta acikin arubutuna na littafi,kuma littafi na daban🥲 dole inyi kukan rabuwa da Hayatiy domin mun saba😂🤚amman ya muka iya da kaddarar rayuwa? Suhail ya dauke abar shi_

_*Albishir ku mun murna an mun takwara Aysha ana kiranta Xayyeesherthuo🤚😂kar kuyi mamaki innace kamarmu daya da little Xayyeesherthuo*_

[10/9, 5:28 PM] Xayyeesherthul-humaerath: Farkawa barci ta yi cikin shesshekan Kuka, tana fadin, "Momah kina gani Yaya bai mutu ba ni na ce miki bai mutu ba, Yaya ka tashi."

Sautin Kukanta yasa Momah,Abu da SUHAIL suka fito atare cikin gaggawa.

Suna shiga dakin SUHAIL ta rugume tana shekar kuka, "Yaya Dan Allah kar ka mutu kaji,ina sonka,inka mutu binka zan yi nikam." Ta kara fashewa da kuka.

Rugumeta ya yi yana, "Oh Sorry,kiyi shiru kinji ba zan mutu ba,in Sha Allah zan rayu da Hayatiy na,yanzu fada mana me ya faru?"

Cikin Muryar kuka ta ce, "To ba kai ne,na yi mafarki ka mutu ba."

Daga Momah har Abu murmushi kawai su ka yi.

SUHAIL ya ce, "To ai mafarki ba gaskiya bane,yanzu ba gani kina gani na ba,maza je kiyi addua ki kwanta."

"Uhum,uhumm ni Yaya Ka mun alƙawari ba za ka mutu ka barni ba,kaji,ina sonka,ina sonka Yaya."

SUHAIL ya ce, "Nayi alƙawari in sha Allah to je ki kwanta."

"Uhum yumm ni aa."

Momah ta ce, "miye haka kuma? Ba gashi ba? Maza je ki kwanta."

Kuka ta fara gani take inta tafi ta kwanta yayan nata zai mutu da gaske.

"Yaya Muje Falo mu zauna kaji,ni bana jin barci kuma ba na son Zaman dakinnan, Ni bana so ka mutu,ba zan yi barci ba,ni na daina Barcin ma."

SUHAIL ya ce, "To muje."

Momah za ta yi magana Abu ya dakatar da ita da ido kawai su ka fice.

Ranar kuwa Barcin da SUHAILA ba tai ba kenan ko ta fara cikin sauri zata farka ta kalli Yayanta tare da sake mi shi murmushi.

Washegari kuwa kowa ya sheda daurin auren SUHAIL da SUHAILA.

Anyi shagalin biki na rana daya ba tashin hankali mai ciki da kayatarwa
[10/9, 5:50 PM] Xayyeesherthul-humaerath: An kai Amarya gidanta kowa ya watse daga SUHAIL sai SUHAILA.

Daga mata mayafin fuskarta ya yi tare da fadin, "Alhamdu Lillah tsarki ya tabbata ga ubangijina da ya hallaci wannan tauraruwar tawa."

Daga hannunta tai tare da rufe fuskar ta tana dariya.

"Laaa Hayatiy na jin kunyar Yaya ba za ta bari ya ga kwalliyarta ba,to bara inje waje inga na wasu."

Shagwabe fuska tai cikin sauri ta sauke hannayen nata riko hannun yayannata tai cikin sanyayyar murya ta ce, "Yaya bana so ka kalli kowa,ni kadai za ka na kallo ni ce kawai ka ke so kaji, zan ma duk abun da ka ke so kar ka kalli wata in ka kalli wata zanyi kuka." Ta karasa maganar hawaye na zuba daga idanunta.

Dawowa yaiy ya zauna ya fara goge mata hawayen kan ya ce, "Waya ce miki zan kalli wasu bayan kanwata? Kina tunanin kona kallesu za su min kyau ne kamarki? Ko kwatan yanayinki bana taba gani afuskar wata mace,kanwata tafi kowacce kyau aduniya,kuma ta fi kowacce mace iya murmushi aduniya,ki mun murmushin kinji,ki daina mun asarar hawayenki ina jin zafin hakan har cikin raina Hayatiy."

Murmushi tayi tare da kwanta a kirjin yayan nata.

"Yawwa goog gurl." Cewar SUHAIL ya na shafa bayanta.

"Uhumm ni Yayana ya fi na kowa,ina son shi,ina alfahari da shi,kuma ni ina kishinsa bana so kowa ya so mun shi,shi nawane ni kadai,Yaya kace ni kai nawane ni kadai kaji."

Kara rungumeta ya yi kan ya ce, "Wayace Yayanki ba naki bane? Yayan HAYATIY ne ita kadai ba kowa,Oyaa yanzu mu tashi muyi sallah mu ci kazarmu ko?"

"Uhumm uhumm ni ba zan ci kaza in ba."

"Sai fa kinci ." Ya fada yana rikota suna saukowa agadon.

Ko da su ka yi sallah suka idar da kyar SUHAIL ta ci naman nan sau biyu.

Nan take kuwa ta bingire da Barcin karya jikin Yayan nata.

Murmushi ya yi azahiri ya ce, "Ayyah Hayatiy ta gaji ko kayan Barcin bata sa ba bara in gama insa mata."

Kara lumshe ido tai domin ko kadan bata so ya fahimci idonta biyu.

Haka ya gama canja kaya ya sa mata har ya kwantar da ita tana ji,kan tai barci.

*Rayuwar Farinciki ta haskaka wannan sabon ahali ta kowanni fanni domin kuwa SUHAILA na samun kulawa fiye da na da wajen Yayanta*
[10/9, 6:17 PM] Xayyeesherthul-humaerath: Bayan Wata Shida, SUHAILA ce ta fito da tsohon ciki tana tafiya da kyar, "Yaya,Yaya kana ina? Ni kazo ka goyani, wallahi na gaji da nauyin cikinnan kazo ka goyani ni humm."

SUHAIL da ke ta typing a system dinsa ne ya dago tare da fadin, "Hayatiy yau abun yazo kainan yanzu dan Allah wa zan goya tsakanin abu uku,Cikin Jikin naki? Kibar taki? Ko kuwa zallan ke din?"

Zama tai agun za ta fara kuka, "To wa ya maidani haka,ina Yayanane? To ni wallahi ka karbi cikinka ma bana so." Ta fara kuka.

Tasowa ya yi ya durkusa gabanta, "in karba in kaiwa wata ta haifamun kenan?".

Da sauri ta ce, "Aa ni bar mun abuna kuma ka bar kallona, ka bar ma kulani."

Dariya SUHAIL ya yi, "To naji kin san dai ba wadda zan kai ma ko,yanzu fadamun abun da kike so muje mu siyo."

"Uhimm chocolate ni ina so."

"Bayan shi fa?" Cewar SUHAIL.

"Yhum sai Yayana kawai ina so."

Rike hannunta ya yi yana kokarin taimaka mata ta tashi.

"Yayanki ai daman naki ne bana kowa ba ko? Ya karasa maganar tare da kai mata kiss."

Dariya ta yi, "zan rama ai."

Akwana atashi har cikin SUHAILA ya kai haihuwa ta sulubo er ta ta mace.

An sanya mata Aisha ana kiranta Xayyeesherthuo

_*Hhhh Fans kumin murna Hayatiy ta mun kara ysn*_

Bayan ta haihu ta karasa karatunta nan take SUHAIL ya nema mata aiki a asibiti , Little Xayyeesherthuo kuwa har ta fara zuwa skul,kar kuji mamaki innace ma ku da ni take kama,hhh lol.

SUHAIL kuwa dukafa ya yi wajen nemawa SUHAILA hakkin mahaifinta da aka danne batare da kowa ya sani ba,sai da ya yi kokarin kwato komai kan ya tara aka sanar da SUHAILA gaskiyar komai

Duk da cewa hakan ya tabata amman bata damu ba kasancewar ta tare da SUHAIL.

Murmushi ta yi tana fadin, "Yaya Allah kan iya kashe wasu arayuwarmu sanan ya Turo mana wasu muyi rayuwa tare domin sune mafi cancanta ga rayuwarmu Ina sonku Momah,Abu,Yaya,Hajiya Kaka."

Suhail ya ce, "Ina alfahari da ke Hayatiy na Allah karawa rayuwarki albarka."

Suhaila ta ce, "To Yaya Agoyani."

Kallonta suka yi duka kan suka sa dariya.

Little Xayyeesherthuo ta zo da gudu, "Aa ammier ni Abhie zai goya."

Alhamdu Lillah💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃

I'm Done💃💃💃💃💃

Ya Allah in nayi kuskure acikin littafinnan ka yafemun🙏

Godiya mai yawa gareku Masoyana🤩 ina maku so fisabillah.

Feel free in kina bukatar magana dani ki dau numberta 08103080717

Masoyan boye da na zahiri tabbas duk ina yinku over🤩

AMEENATOU YAR KAKA is loading 💯 ku shirya kwasan dariya amman paid book ne in kin karanta MATAR POLICE da KUCHAKAR KISHIYA ba sai na ce komai ba kun san salon ai😂🤚 mu tare a Aminatu daure ku siya naki tun wuri.

Urs Xayyeesherthuo
Chapter 9 · 0% Book details