← Book details Hayatiy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 9

Sashe 2

Hayatiy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon Yayan na ta ta yi cikin sauri ta rungume shi tana, "Ka ce kai Yayana ne ka dai kuma ka cewa Momah ni ba mummuna ce ba ka ji Yayana,ka faɗa mata ni ce ka dai kanwarka ni ka fi so kuma ba ka son kowa."
Maganar take tana dukan girjinsa can kuma ta fara kokarin kuka.

Da sauri SUHAIL ya ce, "Ni Yayan Hayatiy na ne ita Ka dai ba kowa, kuma HAYATIY na kyakkyawa ce ta fi duk matan duniya kyau ni anya ma Ba ke ce sarauniyar kyau ba?"

Washe Baki SUHAILA ta yi tare da yi wa Momah gwalo, "Yayana ne ni ka dai ba kowa."

Murmushi Momah ta yi har aranta tana jin dadin yadda 'ya'yan nata ke nuna tsantsan so da kaunar juna amman duk ran da ta tuna cewa Tabbas watarana dole sai SUHAIL ya rabu da SUHAILA , SUHAILA ta rabu da SUHAIL ji take ranta sam Babu dadi dariyar su ne ya katse mata tunani , "Umm Yaya ka goyani kaji."

"Aa Hayatiy Yanzu fa kin girma kun wuce goyo."

"Ummm,ummm,ummm wallahi sai ka goyani ko sau ɗayane."

Hawaye ne ke kokarin zubowa Momah tai saurin tare su ba tare da ta bari 'ya'yan nata sun fahimta ba,,sum ta shige ɗaki ta sha kukanta son ranta.

_*Ko miye dalilin kukan Momah?*_

SUHAIL kuwa goyata ya yi suna ta zagaye gidan ban da dariya ba abun da SUHAILA ke yi.

Ni shi yake ya ajiyeta saman kan wata farar mota.

"Hayatiy na gaji kin yi nauyi fa, tsabar shan Madara da chocolate ko? Dan dai Wannan na san ba dai abinci ba."

"Ni abinci ina ci fa yaya."

"To rantse in da gaske ne."

Subulewa tai daga kan motar sai da ta ja gemun shi kan ta ce, "Umm umm ni ba kyau rantsuwa Yaya ya hana ni."

Ta shige cikin gidan da gudu.

Bin ta shima ya yi yana dariya.

Tana shiga ta zabga wata ƙara.

A firgice SUHAIL ya Karasa cikin gidan.........

_*A ci gaba ko a tsaya??*_

*More comments more typing*

08103080717
Urs Xayyeesherthu
*HAYATIY حياتي*
2/09/2021
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_
_(Mrs Ɗangote)_

_*HAYATIY:* Labari mai cike da tsantsar Soyayya, Amince tare da Sadaukarwa,sarƙakiya mai ban mamaki_

_*SADAUKARWA*_
_SADAUKARWA GARE KU YAN UWAN KWARAI,BA ZAN IYA MIKU SO KAƊAN BA FARIDA MUSA (SWEERY) ZAINAB SALIHU (SARAUNIYAR KANAWA), ASMA'U ABUBAKAR (JASMEEN) REAL NANA AISHA,HAUPHA,MANAB/YAR BABA,JANNAT M NASIR,RAHMA SABO USMAN,HANNA MUHAMMAD SUHANA._
_*Ku yi yadda kuke so da littafinnan daga farko har karshe naku ne,son so fisabillah🌹*_

PAGE-2

_Bismillahir-rahmanir-rahim_

_*Gajeran Labari ne, dan haka pages din za su rinka zuwa guntu-guntu amman duk da hakan yawan comments yawan typing🤭*_

A guje SUHAIL ya ƙaraso, SUHAILA kuwa tuni ta fara kuka, "Yaya Ɓera,ɓera a kafata, kafata ya hau." Ta ƙara fashewa da kuka.

Mai SUHAIL zai yi ban da dariya.

"Hayatiy ki rasa me za ki ma kuka sai ɓera dan kawai ya hau mi ki ƙafa? Cizon ki ya yi?"

Ya ƙara kyalkyalewa da dariya.

Ɓata rai ta yi ta kalle shi kan ta fara dukan shi a kirjin shi.

"Yaya, ni ka ke ma dariya? Ni ka dai na mun dariya, na ce ka bari kuma ba ruwana ma da kai." Ta fada tana ƙara dukan kirjin shi.

"Wash wayyo Allah kirjina." SUHAIL ya faɗa yana gyatsine fuska.

Da sauri SUHAILA ta ɗago, "menene Yaya? Zafi ya ke ma? Sorry na daina kaji ko? Sorry."

Ta fada tare da tashi a jikin sa.

Da sauri SUHAIL ya tashi yana mata gwalo

Ƙarasawa falo ya yi.

Ita ma ta bi shi da gudu tana, "wayo kamun ko yaya? Kuma zan rama nima ai."

Kaka ce ta fara magana

"Ke Salamatu yayan na ki kike ma rashin kunya? Oh ni Jikar Ubana wannan wace irin yarinyace."

Kallonta SUHAILA ta yi kan ta ce, "Kaka ni ba salamatu ce ba,kuma ai ba yayanki bane ."

SUHAIL ya ce, "Hajiya kaka yaushe ki ka ji tamun rashin kunya?"

"Aa bata ma ba SUHAILU Ni na zageka ma kaji,ai yar gwal bata laifi." Cewar Kaka tana gyatsina baki.

Tashi SUHAIL ya yi tare da riƙe ma SUHAILA hannu suka fita domin ya san sarai nan da anjima Kaka zata iya sa SUHAILA kuka.

"Mtseww, oh Ni ina ganin salabe Aduniyar nan, yara kamar Masu rayuwa da ran juna ba dama ataɓa ɗaya,muje zuwa ai dole zaku rabu kije can kima mijin naki shirme da shagwabar banza,bari uban naku ma ya dawo walllahi aure zan sa ya miki."

Karaf a kunnen SUHAILA

Tsayawa ta yi cak.

SUHAIL ya ce, "HAYATIY muje kinji rabu da kaka."

Buɗe bakin da zata yi kawai sai kuka, "Yaya kana ji wai za arabani da kai,wai aure zata sa Abou ya mun? Yaya ni bana son auren ba zan yi ba,ka fadawa Kaka kar arabani da kai, Yayana ni nace bana so, bana so wallahi,ni ba zan yi auren ba." Shiɗewa ta yi nan da nan numfashinta na kokarin ɗaukewa.

Wani irin kira da SUHAIL ya yi ma SUHAILA ne yasa kaka da Momah saurin fitowa tare da ƙarasowa gare su.

"HAYATIYNA ba za amiki na fada miki ba za arabani da ke ba,kinji kar ki tafi ki barni,nima bana son rabuwa da ke,wasa kaka ta ke miki, kaka ki fada mata wasa ki ke mata kinji bana so wani abu ya samu Hayatiy na."

Cikin ruɗun yanayin da kaka taga SUHAILA ya sa ta saurin faɗin, "SUHAILATU wasa na ke miki wallahi wallahi aradun Allah, na rantse ba za kiyi auren ba,ba zan fada mi shi ba." Kuka kaka ta fara harda majina

_Duk tsitar da kaka ke yiwa SUHAILA aranta ba wadda ta ke so kamar ta, Amman tace shagwabar ta ce ke bata mata rai._

A hankali numfashin SUHAILA ya fara dawowa kallon yayan nata ta Yi, "Ina ba za ka bar ni ba?"

Fuskar ta ya shafa tare da sake murmushi, "Alƙawari ba zan ba HAYATIY na ba,da ke zan rayuwa yar uwata."

Ita ma Murmushin ta sake kan ta kalli kaka ta murguɗa baki.

"Kuma daga yau na daina kulaki ma."

Kaka ta yi guntuwar dariya, "Yo ni indai zaki rayu baki kulani ba ai ba komai bane in kika mutune nasan nima zan iya binki SUHAILATUta."

Dariya Momah tai kan ta ce, "To dai Yanzu Alhamdu Lillah mai yaya ta dawo seti, SUHAIL ka tafi masallaci SUHAILA ki zo muje muyi sallah da kaka."

"Tab, tab ni dai ba zan yi sallah da kaka mai majinar kuka ba, yaya ina tare za muyi waje?"

Dagata yayi kan ya rike mata hannu, "eh muje Rayuwata."

Juyowa ta yi tanama kaka gwalo, "hee tsohuwa tayi kukan majina."

"Yar baɗo zan kamaki ai."

Sallah su ka yi tare kan SUHAIL ya ƙara mata karatu tayi.

""""""

Zaune suke zasu ci abincin dare duka haɗawa aka yi, Abou ,Momah, kaka, SUHAILA, SUHAIL domin tare suka saba ci.

SUHAILA na zuwa ta ɗane cinye SUHAIL , "Yaya ina jin yunwa."

Kaka tai karaf ta ce, "wallahi har tausayin SUHAILU na ke inn SUHAILATU ta dawo gidannan bai da sukuni kamar jinjirar kuliya yake kiwo."

SUHAILA ta shagwabe fuska, "Abou Ka ga kaka ko? Yau sai mun masifa tana ta yi,kuma ina Yayana ne ba nata bane ita ma anemo mata yayanta."

Murmushi kawai Abou ya yi.

Haka aka ta fama da SUHAILA duk da tace tana jin yunwa amman da kyar ta ci kaɗan hakanma ta ga Momah na gunne.

A jikin SUHAIL SUHAILA tai barci sai da ya kaita ɗakinta ya mata addu'ar ya shafa mata, kan ya fita adakin shi ma yaje ya kwanta.

Washe Gari

SUHAIL zai wuce masallaci dakin SUHAILA ya shiga barcinta take hankali kwance murmushi ya yi kan ya durkusa dai dai kunnenta a hankali ya ke faɗin, "HAYATIY HAYATIY HAYATIY." Kiran na ukun ta Amsa " *Alhamdu Lillahil- lazi Ahyana ba'adama Amatana wa ilaihin nushur*

Murza ido tayi tana kallon yayan nata.

"Oya Aje ayi alwala ayi sallah, kiyi wanka, sannan kisa kayan sport dinki Kan na dawo."

"Ok Yaya."
Ta fada tare da nufan toilet din.

Kan SUHAIL ya dawo kuwa har SUHAILA ta shirya cikin kayan sport din ta ja mai ratsin fari rigace da kuma wando har ƙasa dai dai jikinta,sai wata farar hula akanta mai adon stons ba ƙaramin kyau ta yi.

Shi ma yana dawowa haka ya shigo cikin shigar kayan sport din sak irin na SUHAILA.

Tsayawa ya yi tare da ɓata rai, "hijabin fa?"

"Yaya ba sai nasa ba fa ni bana son hijabinnan damuna yake."

SUHAIL ya ƙara bata rai , "wuce ki dauko hijabin kisa nace."

Ganin yadda yake mata maganar yasa ta san ba wasa tuni ta ɗauko tasa.

Karamin farin hijabine iya kafadarta ya tsaya.

Kallonta ya yi kan ya sake murmushi, "Yawwa Yar lukutar HAYATIYNA Kin fi kyau a haka."

"Ni unmm umm, morning Yaya."

"Morning Hayatiy,Da gaske fa muje kan gari ya yi haske, ke ba cin abinci ba ma narasa dalilin wannan kibar ta ki,ina ga dai madarace ke huraki."
Maganar yake suna fita.

Gudun suka fara abinsu a hanyar su na dawowa gida SUHAILA ta kafe.

"Yaya Walahi ni na gaji sai dai ka goyani."

"Hayatiy awaje muke fa taya katuwa da ke zan goyaki sorry tashi mu karasa kinji."

Bajewa tayi akasa tana bubbuga kafa, "ni ai yayana kuma ba ruwana da kowa,ni ka goyani yaya ni na gaji ba zan iya ba, yaya ka goyani."

SUHAIL ya ce....

*_more comments more typing_*

08103080717

Urs xayyeesherthu
*HAYATIY حياتي*
3/09/2021
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_
_(Mrs Ɗangote)_

_*HAYATIY:* Labari mai cike da tsantsar Soyayya, Amince tare da Sadaukarwa,sarƙakiya mai ban mamaki_

_*SADAUKARWA*_
_SADAUKARWA GARE KU YAN UWAN KWARAI,BA ZAN IYA MIKU SO KAƊAN BA FARIDA MUSA (SWEERY) ZAINAB SALIHU (SARAUNIYAR KANAWA), ASMA'U ABUBAKAR (JASMEEN) REAL NANA AISHA,HAUPHA,MANAB/YAR BABA,JANNAT M NASIR,RAHMA SABO USMAN,HANNA MUHAMMAD SUHANA._
_*Ku yi yadda ku ke so da littafinnan daga farko har karshe naku ne,son so fisabillah🌹*_

PAGE-3

_Bismillahir-rahmanir-rahim_

_*Gajeran Labari ne, dan haka pages din za su rinka zuwa guntu-guntu amman duk da hakan yawan comments yawan typing🤨*_
Chapter 2 · 0% Book details