← Book details Hayatiy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 9

Sashe 5

Hayatiy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Riƙe hannun Abou ta yi suka fita tare.

SUHAILA da SUHAIL sun tsaya bangare guda.

Momah da Abou ma haka.
Kaka kawai ake jira domin har mai gadi ya tsaya abangaren su Abou

SUHAIL ta kalli SUHAIL.

"Yaya, ina so yau mu cinye Abou da Momah, mu ci su goma fa kasan Ba iya ball su ka yi ba."

Abou ya ce, "tabbas yau za ki ga iya ball domin sai mun ci ku ashirin ma ba goma ba, ko ba haka ba madam?" Ya ƙarasa maganar yana kallon Momah.

"Sosai ma Ogana, zamu basu mamaki ai."

Fitowar kaka ne ya dakatar da su.

Abou da Momah , SUHAIL basu san sanda suka tintsire da dariya ba.

SUHAILA kuwa harda faduwa akasa.

Gabadaya yanayin kaka ya chanja ga gajeran wando ka katuwar rigar ball gabadaya yawo take acikin kayan.

Takalmin kuwa ko daure igiyar batai ba

Wata irin tafiya take tamkar wanda ya yi kashi awando domin takalmin ba karamin nauyi ya mata ba.

Kallonsu ta yi tare da wage kafa kan ta ce, "Oyaaaaaa boleeeeeeee."

_hhhhhhhh kaka za abuga ball_

Urs xayyeesherthou
*HAYATIY حياتي*
8/09/2021
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_
_(Mrs Ɗangote)_

_*HAYATIY:* Labari mai cike da tsantsar Soyayya, Amince tare da Sadaukarwa,sarƙakiya mai ban mamaki_

_*SADAUKARWA*_
_SADAUKARWA GARE KU YAN UWAN KWARAI,BA ZAN IYA MIKU SO KAƊAN BA FARIDA MUSA (SWEERY) ZAINAB SALIHU (SARAUNIYAR KANAWA), ASMA'U ABUBAKAR (JASMEEN) REAL NANA AISHA,HAUPHA,MANAB/YAR BABA,JANNAT M NASIR,RAHMA SABO USMAN,HANNA MUHAMMAD SUHANA._
_*Ku yi yadda kuke so da littafinnan daga farko har karshe naku ne,son so fisabillah🌹*_

PAGE-7

_Bismillahir-rahmanir-rahim_

_*Gajeran Labari ne, dan haka pages din za su rinka zuwa guntu-guntu amman duk da hakan yawan comments yawan typing*_

SUHAILA ce ta damƙe dariyar tare da fadin, "Kaka ke fa golarmuce ni da Yayana, ke zaki dun ga tare ball in su Abou sun turo kar su cinyemu,kinji."

Kaka ta ce, "oh na gane aiko ba za su taba cinyemu ba SUHAILATU afara kawai."

Gwananin sha'awa cike da nishadi tare da fara'a afuskar dukka ahalinnan suka fara buga ball din.

Abou na kokarin zura kwallon raga caraf Kaka ta bararraje agun ta tare tare da fadin, "aradu kunyi kadan sai mun cinye kwallon yau dinnan."

haka aka ta fama d kaka harda rungumar ba, mai gadi kuwa ya washe baki tuni SUHAIL ya wurga ya cinye masu.

Daga karshe dai 3/0 aka tashi SUHAILA da kaka sai dariya ana yiwa su Abou gwalo.

Hoto suka dunga yi, kowa dariya da ka gan su zaka san Farinciki na mussaman ya ziyarci zukatansu.

Momah ce ta kasa daurewa sai kuka .

Da sauri SUHAILA ta karasa gun Momah ta fara goge mata hawaye, "Momah na, menene ya sa ki kuka? Ba kya so mu ci ne? Tam kiyi hakuri kinji ni kam mun bar ma ku cin dan Allah ki daina kuka ki daina in kina yi nima zan yi." Ta karasa maganar tana fashewa da kukan ita ma.

Da sauri Momah ta rungume ta, "SUHAIL ba zan iya rayuwa ba bu ku ba dan Allah kar wanin ku ya bar ni."

Abou ne ya yi saurin datse batun Momah da fadin, "Madam me ya kawo maganar rabuwa kuma? A tunani ban ji wani abu zai iya rabamu ban da ƙaddarar rayuwa, Ummyna kuyi shiru kinji ,Momahnki kukan farinciki take."

Jikin kowa dai ya yi sanyi amman sai da Abou ya san yadda ya yi ya kawar da tunanin komai azukatansu.

"Ummyna yunwa muje muyi break na san yanzu komai ya kammala ."

Rike hannun yayanta ta yi suka shiga cikin gidan duka tare.

Bayan sun gama break ne Abou ya yi gyaran murya tare da fadin, "Yawwa Ummyna daman ina so ki dawo karatu gida, ki bar boarding ki koma day,tun da daman can rashin barin yayanki ya sa dole muka turaki can kuma Alhmdu Lillah yanzu ya kammala har aiki yake, saura ke, zaki dawo gida na gama magana da Pcn ku kuma ya fahimta ba ma da matsala a yanzu."

Dasauri ta tashi tare da rungume Abou, "Thank you, Abou, thank you so much،ina sonka daman na fi son zaman gidan ya fi dadi."

Murmushi ya yi, "to yanzu ga shi anyi an gama, kullum in yayanki za shi Office zaina sauke ki, lokacin tashi ma inya dawo sai ya daukoki ko?"

Kiss ta ma Abou kan ta kara cewa, "Thank you Abou."

Ta dawo gun SUHAIL tare da ja mi shi gemu, "Yayan Ayati za ka kai ni ko?"

"Dole na in ban kai Hayatiy ba wa zan kai?"

Tsalle ta fara tana murna.

"Yaya anjima zamu lallen da kitson ko?"

"Eh in sha Allah،muje amiki kifi Hajiya kaka kyau."

Kaka ta taɓe baki, "Yo tun da dai Ba gani zai ba ai kuta fina kyan, ba zan yi kishi da lutiya ba, Tunda Malam har ya mutu bai taba son lutaye ba."

"Yaya ka ga Kaka ko? Ka ce mata ai nima kuma zan rame, kuma ina na fita kyau?"

SUHAIL ya ce, "tabbas ana maganar indiyawa wake na hausawa yan Nigeria."

SUHAIL ta kyalkyale da dariya tare da yi ma kaka gwalo .

SUHAIL na kokarin magana kenan jini ya fara zuba daga bakin sa.

Aman jini.

Wani irin firgita SUHAILA ta yi.....

Urs xayyeesherthou
*HAYATIY حياتي*
14/09/2021
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_
_(Mrs Ɗangote)_

_*HAYATIY:* Labari mai cike da tsantsar Soyayya, Amince tare da Sadaukarwa,sarƙakiya mai ban mamaki_

*PAGE-8*

Da sauri Momah ta tashi ta ɗibo ruwa da audiga tare da tallafawa SUHAIL ya daga kan sa sama.

SUHAILA kam suman zaune ta yi, ban hawaye ba abun da ke sauka a idanunta ya yin da ta kurawa Yayan nata ido.

Cikin ikon Allah Jinin ya daina zuba, da taimakon Momah da Abou.

Hajiya kaka ma kuwa sake ido tayi kawai tana kallon abun al'ajabi,amman da ka ganta za ka fahimci cewa a tsorace take.

Murmushi SUHAIL ya yi tare da dagowa ya kalli SUHAILA, yana bude hannayen sa alamar ta zo.

Da sauri ta karasa tare da rungumesa a lokacin sautin kukanta ya fara fita.

Cikin lallashi ya fara shafa bayanta yana, "Hayatiyna ba komai bane fa, sorry kinji."

Abou ya ce, "SUHAIL ya aka yi hakan? Shin ma hakan me ke nufi ne wai?"

Murmushi SUHAIL ya yi yana, "Abou ban san dalili ba wallahi amman na fi tunanin normal ne ba matsala watakil zafin rana ne ya janyo mun hakan."

"Uhumm uhumm Yaya ni ban yarda ba,ni bana so,ba na so jininka yana zuba, ka daina bari yana zuba ka ji." Cewar SUHAILA.

"To Hayatiyn Yaya, Smile ."

"Ummm umm ni ba zan yi ba sai ka mun alƙawari, promise?" Ta karasa maganar tare da nuna mai hannunta.

Rike hannun nata ya yi kafin ya ce, "Yes Promise In sha Allah HAYATIY."

"Na gode Yayana,ina sonka,kar ka daina sona kaji."

"Ina sonki HAYATIY ba zan daina sonki ba kinji."

"Ku dalla kun dameni da surutan banza to waye bai son yan uwansa daman? Ku mana shiru kullum maimaita magana daya agun." Cewar Kaka.

SUHAILA ta kalli Yayanta, "Yaya ka ga kaka ko, ni bana kulata fa."

"bar Hajiya kaka kishi take da haushin rashi tashi kiga muje in kai ki gidan lallen kinji Hayatiyna."

"Uhumm uhumm, Yaya ni na fasa tunda baka da lafiya."

Zaro ido ya yi.

"Iyee? Waye ce miki ban da lafiya? Lafiyana Lau muje in kai Ama Hayatiy na Ado ta Kara fin Hajiya Kaka kyau."

"Yaya Allah ba zani ba ni,mu zauna agida na fasa."ta karasa maganar tana shirin kuka.

Zama ya yi yana, "Shikenan amman kan ki ba zai zauna haka ba,dauko kayan kitsonki in miki."

Da sauri ta tashi tana tsalle tare da kai wa yayan nata kiss.

Wani karamin kid ta dauko na kayan kitsonta.

_duk da kasancewar SUHAILA ta fara girma amman hakan bai sa an daina yi mata kitson yara mai kyalkyali da adon beat ba, abun mamakin anan shine sanadin SUHAILA ,SUHAIL ya iya kitso, aduk san da za akaita kitso da kuka suke rabuwa hakan ya sa shi cewa zai mata kamar wasa kuwa gashi ya iya yi mata kalaba da twistin , kitso biyunnan da yake mata kuwa shi ke kasancewa akanta ko Bata gida,ko da ba shi zai mata ba cewa take ita irin kitson yayanta za amata, SUHAIL ya zabi murmushin SUHAILA fiye da komai, hakan yasa baya taba gajiya da duk wani abu nata_.

Abou, Momah,da kaka kuwa inda sabo sun saba hakan yasa ba wanda ya kulasu.

Tana ɗaukowa ta dire gabansa tana, "Yaya daman ka dade baka mun kitson ba fa."

......

Urs xayyeesherthou
*HAYATIY حياتي*
15/09/2021
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_
_(Mrs Ɗangote)_

_*HAYATIY:* Labari mai cike da tsantsar Soyayya, Amince tare da Sadaukarwa,sarƙakiya mai ban mamaki_

*PAGE-9*

_*Ashe Hayatiy na da fans haka ban sani ba🤔wato laɓewa kukai, godiya sosai da soyayyar ku gareni😍, Xayyeesherthou na maku so tamkar wanda SUHAIL ke ma SUHAILA😂kun yarda ai ko? Tabbas da gaske son so fisabillah*_

_*Masoyan gaskiya ba sa fushi su kan juri jira komin rintsin dadewa🤩😘*_

Kama gashin ya yi, ya kitse mata shi tsaf da kalaba.

Sai da suka gama kan ya jera mata beat din.

Abun ka mai gashi, ban da sheki ba abun da kan keyi,ba karamin kyau kitson ya yi ba

SUHAILA ta kalli Momah, "Momah ku cewa Yaya Thank you,kuma ku ce kitsona ya yi kyau kunji."

Murmushi su ka yi duka.
Kan Abou ya ce, "Gaskiya kitson Ummyna ya yi kyau."

"Thank you, Yayan Ayati, tunda ance dole mu gode." Cewar Momah.

Kaka ta ce, "Tab ni da tsidigu kai kamar farantin hausawa."

"Uhum uhumm Yaya Ka ga Anty Kaka ko? Zan daina ce mata Anty fa."

"Yoo ki daina mana bakina ya huta da tsugudidin ki ai."

Kallon yayan nata ta tsaya yi.

"Sorry RAYUWATA kin san Halin Hajiya Has dinnan dai na nan kuma duk dan nace bana sonta ne,ta shi mu ta fi abun mu."
Chapter 5 · 0% Book details