Sashe 1
Hayatiy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*HAYATIY حياتي*
1/09/2021
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```

*https://www.facebook.com/106494781436168/*
_*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_
_(Mrs Ɗangote)_
_*HAYATIY:* Labari mai cike da tsantsar Soyayya, Amince tare da Sadaukarwa,sarƙakiya mai ban mamaki_
_*SADAUKARWA*_
_SADAUKARWA GARE KU YAN UWAN KWARAI,BA ZAN IYA MIKU SO KAƊAN BA FARIDA MUSA (SWEERY) ZAINAB SALIHU (SARAUNIYAR KANAWA), ASMA'U ABUBAKAR (JASMEEN) REAL NANA AISHA,HAUPHA,MANAB/YAR BABA,JANNAT M NASIR,RAHMA SABO USMAN,HANNA MUHAMMAD SUHANA._
_*Ku yi yadda kuke so da littafinnan daga farko har karshe naku ne,son so fisabillah🌹*_
PAGE-1
_Bismillahir-rahmanir-rahim_
_*Gajeran Labari ne, dan haka pages din za su rinka zuwa guntu-guntu amman duk da hakan yawan comments yawan typing🤭*_
Wata yarinya ce ƙarama da ba zata wuce Shekara biyu zuwa uku ba aduniya ba tare da wani matashin saurayi da aƙalla zai kai shekaru goma sha biyu zuwa uku,sanye da uniform,tarin kayan wasa ne birjik gaban su kai kace shagon kayan wasa aka tara,ban da dariya ba abun da yarinyar ke yi ganin yayan nata ya tashi tsaye yana ta rawa, "Anything you need yes I'm your guide.
I only wanna keep you satisfy.
I just wanna be there for you.." Waƙar da yake ta yi mata kenan ita kuma tana jin dadi tana ƙara kyalkyalewa da dariya.
Cikin Tsamin Muryarta na yarinta ta ce, "Yaya."
Sai kuma ta yi shiru.
Ganin shirun nata yasa shi matsawa kusa da ita tare da fadin, "Na'am HAYATIY."
Ta kama kunnensa kan ta raɗa masa ,"Ina Shon Yayana."
Kallonta ya yi kan ya ce, "Nima ina son HAYATIYna,ina ba za ki bar sona ba?"
Ta girgiza kai alamar "Eh"
Ya ce, "To HAYATIYN waye?"
Dariya ta yi kan ta ce, "Ayatin Yayane."
"SUHAIL, SUHAIL ba ka ji na ne ? Za ka makara fa ka zo ka tafi skul." Cewar Momah da ke kitchen
"Naam Momah da HAYATIY zan tafi nikam yau bana so ta yi kuka."
Da sauri Momah ta fito domin sarai ta san halin SUHAIL kan SUHAILA zai yi mafiyin hakan ma.
"Ka yi hakuri ka ga za ta ji yunwa kuma kai karatu za ka yi,wai ma ka manta alƙawarin da ka ma HAYATIY ne? Ba ka ce za ka yi karatu ka yi kudi kamar Abu ba kuma ka sata a makaranta ta zama Likita? In baka je skul din ba ta ya za ka mai da HAYATIY likita?"
SUHAIL ya kalli kanwar ta shi da tun da aka fara maganar ta zuba mi shi ido duk da kasancewar ba ta ma san me suke faɗa ba, murmushi ya sake mata kan ya ce, "Momah Hayatiyna likitace kuma ni zan biya mata da kai na natafi byeebyeee.".
Hannu ya ɗaga mata yana kokarin fita ganin tana kokarin fara kukane ya sa shi saurin fita yana goge hawaye.
In da sabo Momah ta saba duk sanda SUHAIL zai tafi skul da kuka suke rabuwa da SUHAILA ,shi yana yi ita tana yi.
Shaƙuwar SUHAIL da SUHAILA na matuƙar ba mutane mamaki hatta iyayen na su ma.
Lokacin dawowar SUHAIL na yi za ka ga SUHAIL tsaye abakin get bata san Lokaci ba,kuma bata ma iya dubawa ba amman lokaci indai na dawowan SUHAIL ne SUHAILA ta sani .
Kamar kullum tsaye take bakin get cikin mintuna kadan kuwa sai ga mota ta shigo SUHAIL ne da drive ,"Oyoyo Yaya,Oyoyo,Yaya,Yayan Ayati Oyoyo." Tsalle take tana waƙa.
Yana fitowa ya rungumeta tare da faɗin, "Oyoyo HAYATIYna
Daukanta ya yi su ka shige cikin gida ban da washe baki da dariya ba abun da SUHAILA ke yi.
Da Sauri SUHAIL yaje ya canja kaya ya dawo falo da ya aje HAYATIY ,Hajiya Kaka ce ta kalle shi cikin gyatsina baki, "Kai SUHAILU ince wai ba ka da Lokacin kan ka sai na Yarinyar nan ne? Duk kunbi kun shagwaba 'Ya"
HAYATIY ce ta ɓare baki za ta yi kuka jin abin da kaka ke faɗa da kuma kallon da take Mata.
Nan da nan SUHAIL ya bata rai ya dau HAYATIY yana, "Kaka mun bar kukaki wallahi tunda zaki samun HAYATIY na kuka,ni ba ruwana da ke kuma bana kulaki."
Duk da kasancewar SUHAIL ƙarami amman ya ɗauki HAYATIY tamkar rayuwarshi haka ita ma, gata ƙaramar Yarinya sosai amman in tayi wani abun kan SUHAIL sai asha mamaki.
Hatta barci SUHAILA bata taba yi sai jikin SUHAIL,haka ma abinci in ba shi zai bata ba ba ta taba ci
Akwana atashi SUHAILA ta ta ƙara girma baki ya dade budewa hakan yasa Dady yanke shawarar sata a primary school haka kuwa akayi SUHAIL ya ce sai school din da yake ba yadda ya iya haka aka sata yana Jss2 SUHAILA na Nursery 1
Kullum SUHAIL sai ya raka SUHAILA aji ya mata wasa kan ya tafi na shi, lokacin tashin su kuwa nayi yake ɗaukota ya dawo da ita ajinsu.
In anaso aga fada da bacin ran SUHAIL to ko zagine ayiwa SUHAILA bare kuma ataba lafiyarta.
Baya taba wasa da karatun SUHAILA domin tana primary, lokacin yana Ss class abun yan secondry yake koya mata ,abun mamaki SUHAILA na ɗauka sosai fiye da zaton kowa.
Har ya gama school amman ya koma domin ya ce shi ba zai bar SUHAILA kadai tana tafiya sai ya jira harta gama kan su shiga jami'a tare
Wasa wasa Abu ya fahimci cewa in Bai mai da SUHAILA makarantar kwana ba SUHAIL ba zai ci gaba da karatu ba, kamar yadda ya fada,hakan Aka yi ba da son ran Momah da Abun ba amman sun raba su domin ci gabansu duka.
Daga SUHAIL har SUHAILA sai da suka yi ciwon rabuwa sosai kamar ba za su rayu ba.
Tunda ta tafi
Kullum ban da video call ba abun da suke in ba ta aji,dan dole Abu ya nemi izinin bai wa SUHAILA waya cikin makarantar domin sun lura cewa rayuwar 'ya'yan nasu tamkar gudace a gangar jiki biyu.
SUHAIL ya gama karatun shi kuma har ya samu aiki ya yin da SUHAILA ke JSs3
Ta dawo gida domin hutu, sunyi jarabawa.
Tun daga kofar get kamshi ya fara dokar hancinsa ,Wani irin numfashi ya yi tare da sake murmushi azuciyarsa ya ke fadin, "Tabbas Kanwata ta dawo gidannan."
Ita ma da ke kichen tana girki yana shigowa falon kamshin turaren jikin sa ne ya fara dukan hancinta, Shagwabe fuska tayi sannan ta fice aguje tana faɗin, " Yayana."
Juywar da zai yi ta Ƙara Shagwabe fuska tare da tsayawa cak tana kallon shi.
Murmushi ya sake mata,tuni ta kawar da kai tare da faɗin , "Ni fushi na ke kuma Ni ba zan ƙaraso ba ka ƙara so ni,kuma ka bani hakuri."
Kasancewar ya san halin ƙanwar tasa sarai ya sa shi ƙarasawa gareta cikin sauri.
Yana zuwa ya durkusa tare da rike kunnuwansa, "Am so sorry Rayuwata,kar ki ci gaba da fushi dani kin ji ko?ko ki na so inyi kuka ne?"
Idanunta ne suka fara cika da hawaye tamkar za ta yi kuka.
Da sauri ya miƙe tare da rungumeta,nan da nan ya birkice cikin sauri ya ce, "Rayuwata me ya same ki? Me aka miki? Kar ki zubarmun da hawayenki kinji dan Allah faɗamun kar kiyi kuka."
Cike da Shagwaba take maganar, "Ni to ban ce yayana ya kama kunne ba kuma wayace ya kama ni bana so bana so yayana." Ƙarasa Maganar ta yi cikin muryar kuka.
Fara share mata hawayen ya yi kan ya ce, "amman ba na hana rayuwata kukan nan ba? Kuma ai ke ki ka ce ki na fushi dani na miki laifi shi yayan ba a hukunta shi ne?"
"Ummm to ba kai ne ka ƙi zuwa ɗaukana ba? Kuma ka san yau zan dawo daga skul ka tafi office dinka."
"To kiyi hakuri kin ji,na so zuwa aiki ne dole sai dani kuma kema Kin san ba zan so barinki ke ɗaya ba shi yasa na tura drive,yanzu dai muje yunwa nake ji ina kewar girkin Rayuwata."
"Tam muje,kuma sai ka cinye duka ni."
Murmushi ya sake mata kan ya ce, "To muje."
Riƙe Hannunshi ta yi sai da suka je har falo ta zaunar da shi kan ta ce, "Ka jirani ina zuwa karka tashi fa."
Dariya kawai ya yi mata ba tare da ya ce komai ba
Sinasir ne hadadde da vegetables soup ya ji hanta ta ta zuba mi shi a plate tana kai wa
Ya ce, "Wooooo Rayuwata gaskiya zanci sosai."
Ta shagwabe , "Ummm umm Zan dai baka sosai bude bakin tom."
Ba gardama ya bude domin yasan ba ƙaramin abu bane yanzu Suhaila ta fara kuka.
Ba shi take ta yi yana cewa ya koshi zata turɓune fuska da niyar fara kuka.
Sai da ya cinye biyu ras kan ya ce, "Yawwa Alhamdu Lillah yanzu saura rayuwata tun da dai Yayanta ya koshi ko?"
"Ummmm,Ummm ni na koshi bana jin yunwa,Momah ta dafa mun doyana na ci."
Ɓata rai ya yi, "ban yarda ba na san halinki ai sarai ki ci abincinnan ko mu ɓata."
Yana gama maganar ya ƙara bata rai tare da ɗaukan wayarsa.
Fuskarshi ta juyo da ita gabanta a sanyaye ta ce, "Zan ci kaji yayana bani."
Murmushi ya sake , "Yawwa ɗiyar albarka buɗe bakin."
Yana ba ta ɗaya ta tashi ta gudu,haka ya bita suna zagaya ɗakin tana dariya yana dariya yana bata ahaka har ta ci abincinnan.
Sallamar Momah ne ya katse su "Ai shikenan yanzu Kuma andawo rigima zata ci gaba."
Kawar da kai SAHLA ta yi cike da Shagwaba.
SUHAIL ya yi Murmushi tare da fadin, "Momah Sannu da fitowa."
"Yawwa SUHAIL ,kai dai ba ka gajiya da halin HAYATIYN ka ko?"
SUHAILA ta taɓe baki, "Umm Ai dai Yayana ne ba yayan Momah ba kuma Yayana ne ni ka dai."
Ta ƙarasa maganar tana kallon Yayan nata, wanda murmushi kawai ya sake mata.
Momah ta ce, "SAHLA kwana nawane? Tabbas na kusa haifawa SUHAIL kani very soon Kyakkyawa ba mai kama da ke ba."