← Book details Haqqi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 5

Sashe 5

Haqqi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

“Meke faruwa ne aaramma?" Baban su ishaq ne ya tambayi jagoran nasu, yana huci yace “alan-guro wani yaro a gidan nan ya mari d'an uwan mu daren jiya dan yazo yayi bara, yanzu a haka yaron yana can a kwance ba lafiya toh wallahi tunda ya gudu sai mun d'auki fansa" yana kai aya a zancen sa yace “kai kuzo mu tafi" baban su ishaq da sauran jama'a su kayi ta basu haquri amma ina sun kafe a kan magana d'aya sai sun d'auki fansa.

Nine ban dawo gida ba sai bayan sallah'r magharib. A nan ne aka labarta min komai, a cikin daren baban mu ya nemo min kud'in motan zuwa maiduguri akan naje can nayi zama na a gun k'anin sa after magana ya lafa sai na dawo gida saboda idan na tsaya naki tafiya zasu iya dawowa ako da yaushe kuma babu shakka zasu d'au fansar su.

Dama banyi kwana biyu da yin d'aurayan kayaki na ba, wad'anda suke da datti baza su wuce set biyu bane a ciki, da asuba na kin-kimi jaka ta na wuce tashar motoci terminors.

A maiduguri nayi spending 2 months bayan komai ya lafa harma na manta da rikicin daya koro ni daga garin *biu* jiki na ya fara kumburi da naga cewa abun baya yin sauk'i sai na tattara na dawo gida gudun kada jikin nawa yayi worst bana gaban mahaifana.

Abu kamar wasa Duk asibitin da muka je sai ace mana wannan bana asibiti bane, na gargajiya ma idan muka je sai ace mana muje asibiti har muka gaji da yawuce-yawuce, daga nan dai aka yiwa baban mu kwatancen gidan wani malami yana can a unguwar nasarawa muka je, baban mu yayi masa bayanin dukkanin abunda ya wakana malamin ya jin-jina kai ya kalle ni sannan yace “kana d'auke-d'auke ne?.

“A'a bana d'auke-d'auke"
malamin yayi shiru yana nazarin wani abu finally yace “kayi tunani dai, baka ta6a d'aukan kayan wani ba?" Same answer na basa, ya sauk'e sassanyar ajiyar zuciya yace “ba shakka wannan kumburin naka yana da nasaba da wani, amma babu wani abu daya shiga tsakanin ka da wani?" “Allah gafarta malam a gaskiya kusan kullum sai munyi rigima da jama'ar unguwar mu kafin lalurar nan ta same ni".

“Toh ya zama dole kaje ka bisu d'aya bayan d'aya ka nemi tuba idan Allah yasa wanda yayi ma wannan d'anyen aikin yaji tausayin ka zai war-ware insha Allahu, bayan kwana biyu in kuka babu wani canji sai ku dawo" godiya sosai muka yi masa sannan muka fice. Haka kuwa aka yi duk sai dana bisu d'aya bayan d'aya na nemi gafarar su, alhamdulillahi duk wanda na tunkare shi da maganar yafiya cewa yake ya yafe min duniya da lakhira.

Bayan kwana biyu babu alamar canji sai muka koma gidan malamin. shiru yayi yana nazari, sosai ya 6ata lokaci a haka daga bisani yayi ajiyar zuciya yace “lallai al-amarin nan babba ne".

“amma kayi tunani da kyau dai" nayi shiru ni gaba d'aya nama manta da wancan almajirin, ina tunowa da shi naji gabana ya fad'i ras! Take hawaye ya gan-garo min baki na yana rawa nace “ba shakka akwai bare-baren almajirin dana mara kwanakin baya har sai da ya suma, kuma y'an uwan sa sunyi ikirarin cewa sai sun d'auki fansa".

“Ba-barbare? Tab! Babbar magana" malamin ya fad'a a d'an razane hakan yasa jiki na yayi sanyi matuka “a gaskiya bani da kokwanto suna da alaka da wannan ciwo naka, kuma in kana son lafiya ya zama dole kaje ka nemi yafiyar su dan wallahi kanuran nan suna iya yiwa mutum abunda yafi naka ma, amma kayi tattaki izuwa makarantan nasu ka nemi gafarar su shine kawai mafita a gare ka" godiya sosai mu kayi masa mahaifi na yayi masa d'an dunkuli sannan muka tafi.

Kamar yadda malamin nan ya shawarce ni da naje can makarantar nasu neman tuba, haka kuwa nayi amma da naje tsangayar da mamaki na, naga babu kowa a makarantar alamun sun tashi kenan, zubewa nayi kasa on my knees ina kukan fitan rai dan kuwa yanzu na dad'a tabbatarwa da kaina cewa ciwo na yana da alaka da wad'annan mutanen ne. A garin ba inda bamu neme su ba amma sam koda d'uriyar su bamu ji ba.

Gaba d'aya tausayin sa ya shige mu sai tsiyayar da kwalla kawai muke dan wallahi ban ta6a ji ko ganin haka ya faru da wani ba koda kuwa a film ne ballantana a history. “Allah yasa kaffara ne ya kuma yaye ma wannan bala'i shine kawai addu'ar, yanzu dai maghariba ya karato kuma ya kamata mu kyale ka hakan nan kaima ka huta" aliyu yayi maganar yayin da yasa hanky yana wiping off na hawayen sa.

“Ameen thummah ameen, nagode! Nagode!! Kwarai da gaske da irin kulawar da kuke nunawa a gare ni, Allah ya saka da alkhairi ya kuma bar zumunci" da “ameen" muka amsa masa sannan muka fice bayan munyi sallama da mahaifiyar sa da sauran mutan gidan. *(Allahu akbar! Ashe dai sallamar mu ta karshe kenan Allah sarki rayuwa, Allah kasa mu cika da imani ameen)*.

The following day muna da exam na mathsmatics from 9:30㏂ sai 3:00㏘ muka fito daga hall so exhausted ga kuma wani irin fad'uwan gaban da nake ji tun shigan mu cikin hall d'in har muka fito bai daina ba kuma ban san dalili ba, a haka dai muka tsaya da sauran friends namu muka d'an has-haska pictures, a hanya ma muka idar da sallah'n la'asar sannan muka wuce gida. Muna zaune akan d'an benching dake kofar gidan mu nida amini na aliyu sai muka hango keke napep ya shigo layin zuciya ta, ta buga da karfi mai mashin d'in yana wucewa a gaban mu na saki salati saboda mahaifiyar muh'd na hango tana rik'e da tea flask a hannun ta da tabarma.

Not long enough muka jiyo karan jiniyar amblance yana shigowa ashe tun tafiyar mu makaranta aka d'ebi muh'd sakamakon jikin nasa ya tsananta fiye da kima. Salati kawai muka rinka yi har aka wuce da gawar sa.

Muka d'ugunzuma izuwa makabarta tare da y'an unguwa, wallahi bakwa bina bashin rantsuwa in dai iri na za'a binne a cikin kabarin wallahi sai dai mutum biyu. Bayan an kawo mamacin ramin yayi masa kad'an ta saman kafad'ar sa sai da aka yi ciko da duwatsu sannan aka jera itatuwa followed by gany'e da kwa6a66iyar kasa da busasshiya sai bayan sallah'r i'sha muka baro makabartan. Allah yasa aljannah ce makomar ka muhammad ameen thummah ameen.

Allah yasa mu anfana da wad'annan darussa ameen. Allah muna rok'on ka da kasa mu fi karfin zuk'atan mu, mu kuma cika da kalimatil *la'ilaha il-lal-laa muhammadun rasulullahi sallallahu alaihi wasalam* ameen

```dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah shi kad'an sa malikil quddus, wanda ya ciyar damu, ya shayar damu, ya tufatar damu, ya isar mana. Na rubuta wannan littafi ne dan isar da sako kuma alhamdulillahi na isar, Allah yasa masu irin halayyar sa su gyara dama wad'anda suke yunk'urin bin wannan hanyar ameen. Ya Allah ina neman afuwar ka gare ni bisa kuskure ko tun-tu6en harshe da nayi a bisa rashin sani a dukkanin lamura na, ka bani ladan abunda na fad'a dai-dai ka kuma karamin kaifin basira na rubuta abunda d'umbin jama'a zasu anfana da shi ameen```

мυsα м sαεεd
(mr. melody)

*```WABIHAMDULLAH```*

Complied by Princess Aysha Muhammad (Humaira)
Chapter 5 · 0% Book details