← Book details Haqqi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 5

Sashe 3

Haqqi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

😊мr. мεισdγ🍉

[5/17, 15:33] Umar Dalha: *LITTAFI* HAQQI☠

✍🏾mr. melody💥

🌙april-2017

Page5⃣&6⃣

*dedicated to my beloved sisters ummi-aysha & fatimah-bintu👩‍👧*

Tausayin sa ya dad'a lullu6e mata zuciya bata ma san lokacin data fara zubda hawaye ba.
Duk'ar da kaina nayi k'asa wasu zafafan hawaye nake tsiyayarwa na d'an ta6a aliyu nufi na ya tashi mu tafi amma sai ya gyad'a min kai alamun a'a ba yanzu ba, ni kuwa zuciya ta baza ta iya jure ganin muh'd da mahaifiyar suna kuka ba, hakan yasa na tashi zan fita aliyu ya rik'o min hannu ba yadda na iya dole tasa na zauna.
“Muh'd na yafe maka duniya da lakhira, Allah ya baka lafiya ya kuma yima albarka" tayi maganar cikin kuka gami da d'ago sa daga durkushen da yake ta rungume shi shima yayi hugging nata back yana kuka tana bug-buga bayan sa yana cewa “nagode mama Allah ya saka miki da gidan Aljannah, lallai kin cika uwa ta gari" sun d'au lokaci mai tsawo a rungume da juna finally tayi breaking hug d'in a hankali. “mama?" Yayi exclaiming d'in sunan ta da sark'ak'iyar muryar sa “na'am muh'd?" “mama Ina su aisha, fatima da aunty?" Hawayen dake rolling on her both cheeks ne tasa hannu tayi wiping off sannan tace “sun tafi talla, me kake so suyi ma?" “Ba abunda nake so suyi min face gafara, domin na zalince su a rayuwa" ya kare maganar da kuka. Lallai rayuwar muhammad tana k'unshe da darussa bila adadin, wanda mu matasa ya kamata muyi duba ga yadda rayuwar muhammad take a daa can baya, shan kwaya bashi da wani fa'ida kuma ba abunda baya haifarwa, yanzu wani abu da yake damun mu, mu matasa shine wai idan kai baka shan drugs, cigarrete, wiwi, oris da shi-sha (pot) muddin dai baka shan d'aya daga cikin wad'annan haramtattun ababen wai kai baka cika gaye ba, a'uzubillahi, toh kada Allah yasa na cika gayen in dai sai nayi shaye-shaye ne. Wato wani abu d'aya da har yanzu mutane basu fahimta ba shine, turawa sun k'irk'iro shi-sha ne ba dan komai ba sai dan su lalata mana tarbiya wanda iyayen mu suka 6ata shekara da shekaru suna bamu ita. Da farko abunda za muyi la'akari da shi a nan shine: shi-sha da oris duk kamshi d'aya ne dasu sai dai shi oris kamar taba yake a nannad'e, karfa ku manta shi-sha tsani ne wanda mutum zai bi a sauwak'e ya fara shan taba wiwi da sauran su ba tare daya sani ba, kullum ka saba shan shi-sha kana sayan flavor 350 ranar da baka da kud'in sayan flavor'n kuma kana kwad'ayin shan shi-sha cewa za kayi “ba gara naje na saya oris naira goma ba na sha tunda duk kamshi d'aya ne dasu" toh daga ranar da tunanin haka ya fad'owa mutum a rai wallahi tasa ta kare domin shaye-shaye zai fara gadan-gadan kuma dan Allah dear readers ku duba ku gani 80% cikin 100% na mashayan yanzu matasa ne, 70% cikin 100% kuma daga shi-sha suka fara shaye-shaye har suka fara shan wasu kwayoyin, dama shi-sha foundation ne na koyan shaye-shaye wanda turawa suka kafa dan lalata tarbiyan y'ay'an musulmai, yanzu ma abun harta 6aci akwai turare mai kamshin flavor'n shi-sha wai (straw-berry) har mutane suna saya su shafa a jikin su dan rashin hankali, yo! Baka sha amma idan ka had'u da wanda bai san cewa turare bane shikenan kimar ka ta zube a idanun sa, kai bada girki ba amma da warin hayak'i. Allah ka kare mana imanin mu ameen ka kuma tsare mu da muggan abokai domin masu iya magana suna cewa zama da mad'aukin kanwa shike kawo farin kai. Masu sha Allah ya shirye su mu kuma da bama sha Allah ya dad'a tsare mu ameen thummah ameen.
Da kyar na samu nayi convicing na aliyu ya tashi muka tafi gida da sharad'in cewa zamu dawo by 8pm dan jin karshen labarin kasantuwar yau babu zuwa majalis. Haka kuwa aka yi 8pm bayan munci abinci muka wuce gidan. Kai tsaye muka zarce dak'in nasa wannan karon k'anwar sa fatima ce ke gefen sa a zaune tana taya shi hira. Cikin girmamawa ta gaida mu, muka amsa sannan ta tashi ta fice muka zauna.
Da fara'a kwance a fuskar sa yace “Sannun ku da zuwa" “yauwa, ya kaji da jikin naka kuma?" a cewar aliyu “hmmm" kawai yayi ba tare da amsa ba “amma muh'd baza ku koma asibitin nan ba kuwa?" Na fad'i hakan ne yayin da nake kare mai kallo dan wallahi babu alamun sauki a tattare da shi saima abunda ya karu. “eh toh abunda yake kaimu asibitin dama magungunan cin abinci ne da kuma irin abincin da doctor yace ina ciki" “haa'ah, kamar ya? Dama basa duba jikin naka ne duk zuwan ku asibitin?" aliyu yayi maganar da mamaki “eh dama tun kafin jikin nawa yayi tsanani likitan ya shaidawa baban mu cewa ciwo na bana asibiti bane kamar yadda binciken su ya nuna bana d'auke da wata cuta daya sa nake wannan kumburin" ajiyar zuciya nayi sannan nace “kun gwada na gargajiya ne?" Ruwan dake gefen sa a cup ne ya d'aga ya d'an kur6a kad'an ya ajiye ya nisa sannan yace “har gombe an kaini amma bamu dace ba, nifa ina ji a jiki na bazan tashi ba" da sauri nace “subhanallahi, bai kamata ka furta wannan kalmar ba, sai kace ba musulmi ba? ka tuna fa cewa ba abunda ya gagari Allah, Allah gagarau ne saboda haka ka cigaba da addu'a muma cikin yima addu'ar muke a kullum kuma insha Allahu zaka samu lafiya" “toh Allah yasa, nagode Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci" nida abokina aliyu muka masa da ameen. “Toh aliyu ne dama ya matsa min akan lallai-lallai muzo ka karasa mana labarin, zaiyu ka karasa mana yau ko kuwa mu hakura sai gobe?" Lumshe idanun sa yayi a hankali kamar mai jin baci yace "gaskya da zaku hakura sai goben da yafi, saboda ina jin kaina yana sarawa ga kuma baccin da nake ji tun dana gabatar da sallah'n magharib" “kash! Subhanallahi Allah ya yaye, ka sha magani kuwa?" aliyu ya tambaye shi “a'a, ban sha ba amma da zarar na samu nayi bacci zan tashi babu ciwon kan" “toh Allah ya baka lafiya, mu zamu wuce gida sai goben in Allah ya kaimu" na fad'i hakanne yayin da muke mik'ewa tare da aliyu “Allah ya kaimu da rai da kuma lafiya, nagode! Nagode!! Allah ya saka da alkhairi ya kuma bar zumunci" da ameen thummah ameen muka amsa masa sannan muka fice bayan munyi sallama da mahajfiyar sa.

😊mr. melody🍉

[5/17, 15:33] Umar Dalha: *LITTAFI* ☠HAQQI☠

✍🏾mr. melody💥

🌙April-2017

Page7⃣&8⃣

*dedicated to my beloved sisters ummi-aysha & fatimah-bintu👩‍👧*
Chapter 3 · 0% Book details