← Book details Haqqi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 5

Sashe 4

Haqqi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau take monday muna da general exam na english paper 1-3 Tun 9:30am sai 4:30pm muka kammala. Bayan mun dawo gida so exhausted tare muka ci abinci da aliyu bayan nan ya wuce gida yin wanka nima na fad'a a family bathroom na gidan mu dan watsa ruwa.
30 minutes after sai ga shi ya taho sanye cikin kananan kaya white t-shirt ne mai style da y'ay'an beads da ¾ amry trouser ni kuwa jallabiyar makkah na zurmud'a sannan muka wuce gidan su muh'd dan jin karashin labarin nan nasa. Kai tsaye muka fad'a cikin gidan da sallamar mu matan gidan suka amsa muka gaisa dasu sama-sama sannan muka shige cikin dak'in a inda muka tarar da mamar sa tana bashi abinci a baki.
“Ina yini mama?" muka fad'a tare da aliyu yayin da muke kokarin zuwa kasa “lafiya qalau, sannun ku da zuwa" “yauwa mama, ya mai jikin?" Ajiyar zuciya tayi gami da cewa “wallahi jikin nasa ba wani alamun sauki, jiya iyau koma ince sai dad'uwa yake" na d'ago idanu na, na zuba su kan muh'd wanda tun shigowar mu ya jingine a jikin bango idanun sa a lumshe suke sunyi kanana mini-mini dasu tsabakin kumburin da yayi har za kayi tunanin cewa idanun nasa basa bud'ewa ne. “Allah ya sauwake" cewar aliyu “ameen ya Allah, throughout yau baku zo wurin d'an uwan naku ba sai yanzu, lafiya dai ko?" Murmushin yak'e kawai nayi nace “munje zana jarabawa ne wallahi shi yasa bamu zo ba" “toh Allah ya baku sa'a yasa ku fito da flying colour" da ameen muka bata amsa sannan ta fice. Duk muka yi shiru ba wanda yace koda uffan aliyu ya duk'ar da kansa k'asa kamar me nazarin wani abu, kwallafa idanu na nayi a kan muh'd ina kallon shi cike da tausayawa shi kuwa har yanzu idanun sa a lumshe suke wasu siraran hawaye na gani sun gangaro masa a hankali ya fara yin kuka mara sauti tausayin sa daya min yawa yasa na kasa appeasing d'in sa kamar yadda aliyu ma ya kasa. Yayi kuka mai isar sa ba wanda ya lallashe sa a cikin mu saboda kukan nadama ya keyi bai kamata mu lallashe sa ba, kukan da yayi zai sa ya d'anji sauqi koda kad'an ne a cikin zuciyar sa. Cikin rawar murya yace “sannun ku da zuwa" aliyu ne ya amsa mai da “yauwa" shi d'in ma cikin shesshek'an kuka ne, ya d'aura da cewa “sannu muh'd, Allah yaye ma wannan musiba" kai yake kad'awa a hankali ga kuma hawayen da suke rolling on his cheek “musa baza kayi min magana bane?" Cike da tausayawa na matsa kusa da shi nasa hannu na share masa hawayen da suke sauka kan kumatun sa nace “yi hakuri, sannu kaji? Allah ya baka lafiya ya kuma sa kaffara ne" kukan da nake matsewa ne ya kwace min, gefe na koma na zauna ina matsar kwalla, sai da duk muka saita kawunan mu sannan muh'd ya sauke sassanyar ajiyar zuciya ya kalle ni ya kalli aliyu yace “mu d'aura daga inda muka tsaya jiya ko?" da sauri aliyu ya gyada masa kai gami da cewa “eh".
Muh'd ya sauke sassanyar ajiyar zuciya a karo na biyu gami da gyara jinginuwan sa a jikin bangon ya fara da cewa “as usually dama bani da wani aiki sai dai naje ghetto nayi shaye-shaye sai nayi d'ub nake shigowa cikin unguwa duk yaron dana had'u da shi dukan sa nake tamkar aiko ni aka yi daga sama jama'ar unguwa su kayi ta min magana amma kota kawunan su bana bi sai ma ashar d'in da nake ta faman kwararo musu, baban su usaini ne yazo ya sameni ina langa6e a jikin bango sai wani lumshe ido nake saboda yadda na shawu over, yazo ya sameni ne akan na lakad'awa inusa duka kanin usaini har sai da na fasa masa baki “kai muh'du yanzu abunda kayi ya dace kenan?" Cikin yanayi na shawuwa na kalle shi da ido d'aya nace “daga yau kada ka sake kira na da muh'du, kana ji ko?" Duk da cewa a shaye nake amma da sane na nake fad'in hakan, “yo! Ai sai kaje ka fad'awa uban ka wanda ya rad'a ma sunan kace baka so, ina mai gargad'an ka daka fita a idona na rufe dan wallahi zan sa a daure min kai a garin nan" kallo tara saura quarter nayi masa sannan na tsartar da yawu nace “sunana john daga yau in kuma ka sake kira na da muh'du zaka gane cewa shayi ruwa ne, dan wallahi sai y'ay'an ka sun kasa shaida ka balle matar ka" ya tafa hannun sa yace “innalillahi wa'innaillaihir raju'un!, yanzu kai haukan naka har ya kai kace kai sunan ka john? sunan kafiri?" Tsaki naja na bar wurin sai wani layi nake sai kace mahaukacin jaki, shi kuwa bina kawai yayi da ido baki a wangale. Haka dai a dolen-dole na koma arne in ka kira ni da muh'd na kwararo ma ashar in kuwa john kace sai mu zauna lafiya. Wallahi har yau wasu da john suke kira na wasu kuma da shi suka sanni abun yana bani haushi matuk'a amma ba yadda na iya saboda *NI NAIWA KAINA*. A nan ya fashe mana da kuka yana cizon le6en sa dan takaici, in between crying yace “wallahi shaye-shaye ba abu bane ma kyau, da ban fara shaye-shaye ba, da duk ban tafka rashin hankali dana tafka a duk tsawon rayuwata ba. Nothing is hurting me more and more! like the way that i treated my only mumy harsly like this" kukan nasa ya fad'ad'a Ya sake cewa “peoples are saying what you sow is what you reap either good or bad, yes of course they are right because i have now started reaping all bad things that i have been sowed since" yana kaiwa nan a zancen sa ya duk'ar da kansa kasa yana wani irin kuka mai karya zuciya yana maimaita astagfirullah! Wa'atubu ilaihi Astagfirullah! wa'atubu ilaihi!!...

Kai jama'a Allah yasa mu dace, matasa dan Allah mu kiyaye shaye-shaye bashi da wani anfani sai ma cutar da lafiyan d'an adam da yake yi. Likitoci sun bayyana cewa shaye-shayen cigarrete, wiwi ko shi-sha yana ru6ar da huhun d'an adam, yana ta6a lafiyar kwakwalwa sai kaga mutum shi kad'ai yana ta surutai, yana jawo cutar daji wato cancer, uwa uba kuma yana zubarwa da mutum mutuncin sa a idanun al ummah. Su kansu masu company'n me suka ce? Cewa su kayi (the federal of ministry of health warns that smokers are liable to die young) abunda suka rubuta a jikin kwalin kenan, abu mai kyau ba sai an fad'a maka cewa wannan abun mai kyau bane kai kanka ka sani, ai ido ba'a nuna masa bacci. Sanadin shaye-shayen nan kwanaki a damaturu na samu labarin cewa wani matashi da bai wuce 22 years ba yaje sha kwaya ya dawo gida ya hallaka mahaifan sa duka biyu har hoton sa na gani, dan Allah me anfanin shaye-shaye ya y'an uwana matasa? bakwa bukatan karin haske ku kanku kun karanta labarin kunji me late muhammed abdullahi ya aikata, kar kuyi zaton ko fictitious story ne wallahi it is true. Bani da ta cewa sai dai nace Allah ya jikan sa da rahama yasa tuban sa kar6a66iya ce mu kuma Allah ya kyautata karshen mu ameen thummah ameen.

😊mr. melody

🍉
[5/17, 15:33] Umar Dalha: ☠HAQQI☠

🌙April-2017

.

✍🏾mr. melody💥

Page9⃣&1⃣0⃣

*```this page is dedicated to you my besty <aliyu garba-ALi baii> ana mugun tare wallahi nawan```*

Bayan yayi ta istigfari daga bisani yayi murmushin yak'e sannan yace “a rana mai kamar ta yau monday itace babban ranar nadama a gare ni, kuma babban ranar farin ciki a gare ni domin ta sanadiyar wannan ranar na nema gafarar *MAHAHAIFIYA TA* kuma ta yafe min masha Allah, my only mum may Allah (s.w.a) reward you jannatul fiddaus ameen thummah ameen i really so much love my momma you are one in a billions".

“I thought ranar da muke zaune a chamber'n kofar gidan mu tare daku muke zaune ko?" zallan Kai kawai muka gyad'a mai alamun a'a ”no bad yau za kuji komai" ya fad'i hakan ne yayin daya d'an kora ruwan faro saboda an hana shi shan ruwan randa kona fan-fo sai swam ko faro.

WAto ranar misalin karfe 8 bayan sallah'r i'sha, kwance muke a chamber muna shan iska kasantuwar zafi ake sosai, wani almjiri ne wanda da kyar ya kai 13 years ya shige cikin gidan mu yayi ta bara yak'i fita ni kuwa abun ya bani haushi sai na harzuka na shiga cikin gidan na fito dashi na wanke shi da gigitacciyar mari take ya fad'i kasa sumamme y'an uwan nasa da suka ga haka sai suka kira manyan su suka tafi dashi makarantar su.

Wannan yaron dana mara ba-barbare ne (kanuri) Haka y'an makarantar nasu ma duk kanurai ne harda malaman. Haka dai na kwana lafiya a wannan ranar kamar maye yaci shirwa. Safiya nayi guraren karfe goma zuwa sha-d'aya da y'an kai, zaune muke a chamber muna break fast da fara da mai (garau-garau) wanda mamar su shukura take yi na sayar wa.

Garadan makarantar su almajirin dana mara daren jiyan ne nayi tozali dasu sunyo gayya kwannen su yana rik'e da allon sa sun nufo kan mu, ganin hakan yasa na tuno da abunda na aikata jiya. Gida na shiga na biya ta kofar baya na gan-gara kasan kwari na gudu.

Da zuwan su chamber'n suka tambayi abokan yaron dana mara d'in cewa “a cikin wad'annan wanne ne ya mari baana?" Yaran duk suka kid'ime suka kasa tunano fuskata sai suka nuna modu, modu na ganin an nufo kan sa da saran allo yasa ihu yana cewa “wallahi tallahi bani bane wanda ya mare sa ya gan-gara k'asan kwari ya gudu".

Wani babba daga cikin su yace “ya gudu?, toh wallahi baza mu kyale shi ba sai mun d'auki fansar d'an uwan mu" jama'ar unguwa su kayi chaa! A gun kowa naso yaji meya faru. Many'an unguwa suka karaso jama'a suka bub-bud'a musu suka shigo inda garadan nan suke.
Chapter 4 · 0% Book details