← Book details Haqqi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 5

Sashe 2

Haqqi Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

😊мr. мεισdγ🍉

[5/17, 15:33] Umar Dalha: *LITTAFI* HAQQI☠

✍🏾mr. melody💥

🌙april-2017

page3⃣&4⃣

*Dedicated to my beloved sisters ummi-aysha & fatima-bintu👩‍👧*

Yau take sunday ban fita wurin aiki na ba kasantuwar ina hutu, bayan nayi wanka around 9㏂ na kira aliyu a waya not long enough sai gashi yazo muka wuce al-arfat
shopping complex muka d'anyi sayayyan drinks daga ciki akwai maltina, bitter lemon, exotic, fresh milk da sauran su, a k'alla dai munyi spending kud'i 1k sannan muka wuce gidan su muh'd. Kamar kullum yau ma mahaifiyar sace zaune a gefen sa da kanta take feeding d'in sa break fast da soyayyan doya mai kwai sai black tea. “yau Kune a gidan namu da safe haka?" “hmm eh wallahi mama, ina kwana?" Muka fad'a tare da aliyu yayin da muka durkushe har k'asa “lafiya qalau y'ay'an nan, ya su maman ku da sauran yaran?" “kowa lafiya qalau wallahi mama, ya mai jiki?" “toh ga mai jiki dai, sai addu'ah" “Allah sarki, Toh Allah ya bashi lafiya ya kuma sa kaffara ne" da “ameen" ta amsa mana sannan ta fice ta bamu wuri muka zauna gami da ajiye shopping d'in da muka yo masa a gefen sa. Kallon sa kawai na tsaya yi saboda naga kumburin nasa ya dad'u ba kamar na jiya ba, “sannu muh'd, Allah ya baka lafiya" abunda aliyu ya iya fad'a kenan “ameen aliyu, ina gajiya musa?" “ba gajiya wallahi, kana cin abinci muka katse
ka ko?" fake smile yayi “no karku damu dama i'm
platefull kawai dai ta matsa min dana ci ne that's all" ajiyar zuciya aliyu yayi sannan yace “Allah ya kyautata
karshen mu" mu duka muka ce “ameeen" daga nan dak'in ya dauk'i shiru na wasu y'an dak'ik'u kamar ba halittu a cikin sa duk munyi zugum, chan! aliyu ya nisa sannan yace “anya muh'd zaka iya cigaba da bamu labarin nan kuwa?" “why not?, insha Allahu zan iya don't bother yourself" "toh shikenan muna sauraron ka" na fad'i hakane yayin da nake gyara zama dan
sauraron labarin da kyau.
bayan na fara samun sauk'i daga dukan da su
hamza suka min na d'an fara fita waje dan shan iska, as you know already mahaifin mu jobless ne bashi da aikin fari balle na bak'i, yau shine wannan
gobe shine wancan da ky'ar yake iya samo mana na abinci balle y'an kud'ad'en da zamu biyawa
kawunan mu bukatu dasu, duk da rashin da muke fama da shi na talauci amma a haka idan maitana ya tashi wato kwad'ayin shaye-shaye na idan ya motsa tisa shi nake a gaba har sai ya bani kud'i, wani lokacin ya bani 500 wani lokaci kuma 200 saboda ni kad'ai ne namiji babba a gidan mu shi yasa bana tambayan abu na rasa kamar yadda nima bana tambayar abunda nasan yafi karfin gidan mu. Ta sanadiyar wannan gatan da yake nuna min ne yasa na 6aci dan har yau ban iya wani aikin hannu ba infact ban ta6a yin wata sana'a ba kullum mahaifina ne ke bani kudi, shi kuwa idan na tambaye shi kud'in bani kawai yake yi baya tambayata me zanyi dasu ni kuwa sai naje can ghetto na kashe mana kud'in tas! a kan kayan maye tare da abokai na, na banza.
Wata rana mahaifin mu ya dawo daga gona, gonar
ma ba tasa bane daukan sa haya aka yi wato
barema, ko gida ban kyale sa ya shiga ba na tare
shi a bakin kofar gidan ba tare dana kar6i icen da ya d'auko ba balle nace masa sannu da zuwa. Kai
tsaye nace “baba bani da kud'i fah kuma ina jin
yunwa" “toh baka ci abinci bane ko basu girka bane?"
fuska na 6ata “ni in za'a bani a bani ba wai a tisa ni a gaba da tambayoyi ba, in kuwa baza a bani bane let me know shine kawai ehe!" sai daya d'an 6ata lokaci yana kallo na finally ya d'an karkace ya zaro 1k yace “toh gashi kaje ka kawo min 800 yanzu" kar6an kud'in kawai nayi ba tare da nayi godiya a gare shi ba sai ma y'an kumbure-kumburen dana keyi, reason nayin hakan kuwa shine 200 ya min kad'an. Ghetto na wuce wallahi sai dana ga bayan 200 d'in nan a kan kayan maye sannan na dawo gida.
Rannan mahaifiya ta tana toya awara wa kanne na a kitchen suna kaiwa godiya private school na diro mata ba sallama shiru tayi min gudan kada tayi magana nayi mata wani abun, matsami na
dauk'a na kwashi awara a cikin man tuyan na zuba a plate sannan na barbad'a yaji a kai. Duk abubuwan dana keyi bina kawai take da ido “wai ya da kallo hakane? Ko sai na bad'e idanun da barkono ne sannan zaki daina kallo na?" nayi maganan ina mai zare mata ido kai kace da y'ata nake maganar bada MAHAIFIYA TA ba. “yi hakuri ka jeka, babu komai ai duniya ce" doguwar tsaki naja sannan nace “lahira ce ba duniya ba iskanci kawai" ina kaiwa nan na shige cikin dakin ta na zube a kan single couch nata na d'aura plate na awaran bisa cinya ta sannan na hau awaran da chi like there's no tomorrow. Bayan na cinye awaran sai kuma naji kwad'ayin shaye-shaye na ya motsa and my pocket was dried nan fa na shiga chaje mata dak'i da kwanuka amma ban samu koda kwandala d'aya ba, zuciya a dak'ule zan fita kenan sai kuma nayi step backward kasantuwar mahaifiyar tawa uwar adashe ce sai na karasa kan gadon ta na d'aga pillow, wani jaka na gani irin wanda ake daurawa a k'ugu mai d'an girma haka, nan fa zuciya ta tayi haske ban tsaya wata-wata ba na bud'e jakan, dubu-dubu, dari biyar-biyar sai y'an dari bib-biyu na gani a ciki wanda ni kaina ban san ko nawa bane, tattara su nayi kaf! Zan fita dasu kenan sai kuma naji tausayin ta ya kamani “yanzu idan na tafi da kud'ad'en nan ai zata iya rasa rayuwar
ta ko?" Tambayar da na yiwa kaina kenan, take imani ya ziyarci ruhi na, 200 kachal! na dauka a cikin kud'in na mayar mata da sauran cikin jakan na tura shi karkashin pillow'n kamar yadda yake as before wanda baza tayi tunanin wani ya ta6a mata kud'i ba.
Ghetto na wuce nayi ta shaye-shaye wanda har sai da zama ya gagara tsayuwa ta gagara, a ghetton ma na kwana tsabakin yadda na shayu na gama ficewa a hayyaci na gaba d'aya.
Hmm muh'd yayi murmushin takaici sannan yace “wannan fah ina
baku labarin aika-aikan dana keyi a cikin gida ne
dan wallahi hatsabibanci na ya wuce nan." Wannan karon ni ko aliyu ba wanda yayi hawaye a cikin mu sai sauraron sa kawai da muke yi, aliyu yace “toh muna sauraron ka muh'd, ka bamu labarin kato6aran
daka tafka a waje amma kafin nan ga wannan ka d'an sha" yayi maganar ne yayin da ya bud'e ledan drinks d'in da muka taho masa da shi ya d'auko maltinan gwan-gwani ya bud'e sannan ya mik'a masa, kad'an ya sha ya ajiye sauran.
Sanin kanku ne musa, a daa lokacin ina ji da kaina iskanci babu wanda bana yi, fannin mugunta da cin zali kuma kowa ya sallama min dan ba'a barni a baya ba. Wata rana da yamma muna zaune chamber ni, ali, hamza, dauda, abdullahi da kuma yusuf muna hira sai ga hassan mamar sa ta aike sa shagon abbo siyan flower, yazo wucewa kenan na kira sa “kai hassan zo nan" ya waiwayo ya kalle ni ba tare da yana zuwa ba, “wai baza ka zo bane?" na fad'a a tsawace still yak'i zuwa na tashi a fusace nayi kansa “kai dan uwarka ba kiran ka nake yi ba?" kuka ciki-ciki ya fara yi na zabga masa tafi yasa ihu “dan uwarka kayi kukan da tushe, in uban ka ya kira mu bama zuwa ne?" Da wannan na kyale shi yayi kwana abin sa, sai da yayi nisa kad'an yayi min dak'uwa yana cewa “kaci uwar shege tsinanne munafiki mugu azzalimi kawai" “ni ka zaga?" na fad'a da d'an ihu gami da pointing na kaina “eh kai d'in mugu kawai, kuma wallahi Allah ya isa na" “ai kuwa yaro ka zama nama dan wallahi idan na kama ka sai naci uwar ka" a haka fa na hana yaro zuwa aike, da isar sa gida bai jima ba sai ga mamar sa ta fito dama bata da hakuri idan ka ta6a mata y'ay'a, daru mu kayi da ita sosai finally abun ya bani haushi nace da ita “sai dai in bazai na fita waje ba, amma wallahi muddin na rik'e shi sai naci uwar sa" “au! Rashin kunyar taka har ya kai kace zaki ci uwar d'ana? Lallai yaron nan mahaukaci ne kai" Da kyar su hamza suka bata hakuri ta amince, dan cewa tayi sai ta kira min police su tafi dani, duk da cewa ina tsoron zuwa bayan canter amma sam! ban nuna mata a fili ba sai dad'a kurari nake.
Haka dai rayuwa ya cigaba da tafiya kullum cikin rikici nake, na daki d'an wannan na daki d'an wancan har y'an unguwa suka kai report wa babana cewa na fita hanyar y'ay'an su ko kuma su dauk'i matakin daya dace, ni dai bana kwa6uwa dan kuwa sai dai ayi ta min surutu amma duk a banza na riga na zama fitinanne na kin karewa idan naje nayo shaye-shaye na dawo gida duk wanda na samu mahaifiya ta ko kanne na sai na jibge su iya son raina baban mu baya cewa komai sai dai idan su hamza ne suka min duka a bisa dukan mamata ko kanne na da nayi. Ina mai tabbatar muku cewa mahaidiya ta, ta kamu da ciwon hawan jini nine ta sanadiya ta. A nan ya fashe mana da kuka yana zubar da hawaye zafafa, in between crying yace “dan Allah aliyu ka kira min *MAHAIFIYA TA* na sake neman gafarar ta" wallahi da wannan furucin nasa ya karya min zuciya ban san lokacin da hawaye suka fara rolling on my both cheeks ba. Kamar yadda ya bukaci aliyu daya kira mai mamar sa not long enough suka shigo tare gaba d'aya hankalin ta ya gama tashi a zaton ta jikin nasa ne ya tashi, a gaban ta muh'd ya zube on his knee gami da duk'ar da kansa k'asa yace “dan Allah dan annabi mama ki yafe min, ki gafarce ni ba dan hali na ba, ban kyautata wa kaina ba ko kad'an, wallahi kaicho na!!" ya kare maganar da kuka mai tsuma zuciya a hankali ya sulale k'asa ya kama kafafun ta yana neman tuba sai kukan da yake yi mai sauti.
Chapter 2 · 0% Book details