← Book details Hajar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 6 OF 6

chapter 61

Hajar Part 1 Complete Hausa Novel · about 514 min read

👇

Arewabooks....

Eager to read go there ☺️
💛 HAJAR 💛

{61..}
Hajar dai kawai kallonsa take da wani irin expression, tama kasa gane me yake nufi bare ta fahimta, har lokacin bai dena kallonta ba thick eyebrows dinsa a haɗe, sai ynxu ya fahimci tmbyar da yayi mata which is meaningless to him, to me yasa ma zai mata wnn tmbyar, ta juya ta cigaba da kallon window da sigar ko in kula, kawai ji tayi ya fixgota ya juyo da fuskarta tana kallonsa, ɗan buɗe baki tayi ta sha kunu tace "ni ka dena taɓani", yace "is there anything to touch...?", ta haɗiyi wni miyau ba tace komai ba ta gasa masa harara, ya ajiye numfashi yace "one day one time" da haka ya kunna motar suka cigaba da tafiya, suna zuwa gida ta buɗe motar ta fita ta wuce entrance, a bakin door ta jirasa har yazo ya buɗe mata ta shiga. shi kam kitchen ya wuce ya haɗa Coffee kafin ya haura sama, saida ya gama shan Coffeen snn ya shiga wanka, after ya shirya cikin Pajamas ya rage wutar ɗakin yabar dim, Laptop dinsa ya dauka ya hau kan bed, operating system din ya fara, after 40mins ya gama abinda zai yi ya kashe laptop din, ya ɗauke remote din AC ya ƙara mata gudu snn ya kwanta ya lumshe ido, buɗe ido yayi bayan minti biyar sai kuma ya miƙe zaune, zuro legs dinsa yayi ya zura room slippers ya tashi tsaye, door ya nufa ya buɗe ya fita, ya ringa kallon ƙofar room dinta bayan ya isa corridor, ya kai hannu jikin handle amma bai murɗa ba, after few seconds kawai ya murɗa handle din ya shiga, a hankali ya saki handle din ya shiga ɗakin making sure baiyi making ko wane sound ba, he spent almost 3mins yana kallon innocent face ɗinta tana bacci, kwance take a inda ta saba kwanciya kan carpet, ta rufe da duvet har zuwa wuyanta tana bacci Calmly, duƙawa yayi kusa da ita still looking at her face. Da asuba Hajar ta farka, ta taƙune fuska ta shafa laushin da ta jita a kai, miƙewa tayi zaune ta fara ƙarewa room din kallo sai kuma ta kalli gadon da take kai, zaro ido tayi ta dafe kanta to yaushe ta hau gado, ita da ta kwanta kan Carpet toh ya ta tashi ta ganta a gado, yaye rufar tayi ta tashi ta kunna fitila ta ƙara hasken ɗakin, ta ringa kallon gadon kafin ta girgiza kanta ta shiga bathroom, alwala tayo ta fito ta shimfiɗa dardumar ta fara gabatar da raka'ataynil fajr. Ƙarfe Shida da ƴan mintina Nurain ya fita compound da car key a hannunsa, Hajar ta gyara tsayuwarta a jikin window ta buɗe curtain din da kyau tana kallon compound, idonta ne ya kai parking space kawai ta hangosa, ta sha kunu tayi sauri ta rufe labulen ta bar wajen tana yamutsa fuska. kafin shida da minti arba'in Nurain ya isa gidansu, Already matafiyan sun zama ready, yana shiga main palour ya tarar da Hajiya da kwanon tuwon alkama da tasa akay mata warming, gaisawa sukay ta amsa masa a takaice sai kuma ta fara tambayarsa Hajar, a fizge ya bata amsa ya wuce ciki, box din Mami yaje ya ɗakko ya fita da ita, Drivern Abba ne ya ringa arranging luggage a booth din motar gidan wacca zata kwashesu gaba ɗaya comfortably, Nurain ne yayi driving motarsu Abba while Drivern Abba yayi driving motar Nurain din, Nurain bai bar airport ba saida su Hajiya suka shiga filin jirgi, car key dinsa ya amsa hannun Drivern Abba ya damƙa masa na motar gidansu. yana komawa gida daman kwanciyarsa yayi ya huta, ko da ya farka abinda ya fara faɗo masa shine wnn workshop din, shaf ma ya manta da wani symposium, slight hiss yayi ya janyo wayarsa yayi booking flight, azabar yunwa ce tasa ya fita eatery yayo takeaway, koda ya dawo gida tsattsakurar abincin yayi ya ture. Tin fitar da yayi kafin azahar ya siyo abinci bai sake fita ba, daman yau Saturday ba ranar aiki bace, Hajar kam ko gilmawarta bai gani ba, itama dai ta fahimci a waɗan nan kwanakin ne yake zama a gida shiyasa bata fiya warkajami ranar asabar da lahadi ba. wajen ƙarfe takwas na dare Hajar ta buɗe ƙofar room dinta, a hankali ta fito ta sauka downstairs, kitchen ta wuce ta buɗe fridge ta dauki bottle water ta fito ta haura sama, tana gama haurawa stairs din shima a lokacin ya fito daga ɓangarensa hannunsa riƙe da empty cup da ya sha Coffee, saukar da idanunta tayi ta wuce ta shiga ɗakinta, binta yayi da kallo lokaci guda brain dinsa ta amsa, ya zaiyi da ita knn.. gobe zai wuce Abuja fa, ƙasa ya sauka ya kai cup din kitchen snn ya koma saman, a palourn sa ya zauna yana neman one Solution, toh ya zaiyi da yarinyar nan, shi dai bazai barta a gida ita kadai ba hkan ma beyi making sense ba gsky, toh ko dai gidan Sakeena zai kaita, girgiza kai yayi don hakan shima bai masa ba, yayi tunanin ya kaita gidan Aunt dinsa Zulaihah, shima dai hakan bai masa ba... toh ko dai yace ta tattara ta tafi gidansu ne kawai, chab duk ciki ma hakan shine worst. wayarsa ya ɗauka ya canza flight din daga na safe zuwa dare bayan yayi booking wani seat din, yayi ajiyar zuciya yayi resting da kujera. washe gari ƙarfe goma Hajar na tsaye kitchen tana dafawa kanta breakfast, bayan ta gama ta zauna kitchen din taci snn ta wanke komai da tayi amfani dashi ta fita, palour ta fita ta fara kakkaɓe cuisine tana arranging trow pillows, yamutsa fuska tayi sbd cikinta da ya murɗa a bazata, ajiye duster din hannunta tayi ta haura sama hannunta dafe da cikinta, tasan ma cramps ne yake shirin antayo mata, haka ciwon ya wuni yi mata saidai bai tsawaita ba shiyasa bata wahala kamar yadda yake mata ba, zaune take kan darduma bayan ta idar da sallar magrib, a ynxun ma dai cikin ne ya ɗan murɗa mata, kawai jira take ayi sallar isha'i ta tashi tayi ta kwanta kawai, ƙofar ɗakin aka murɗa kafin aka buɗe aka shigo, ta ɗaga kai tana kallonsa, tini pure men scent dinsa ya bulale ɗakin, yayi sallama ciki ciki kafin ya ƙaraso cikin ɗakin, yana kallonta yace "ki haɗa duk wani abu da kika san zaki buƙata idan zaki wani wajen kwana...", ta ɗago ta kallesa sai kuma ta ɗauke kanta ba tace komai ba, ya kalli tsadadden agogon wrist dinsa yace "you just have 10mins to do that.." yana gama faɗin haka ya juya ya fita, taɓe baki tayi ta jinginar da kanta da gado, after 15mins Nurain ya sake dawowa ɗakin, zaro piercing eyes dinsa yayi ganinta inda ya barta ɗaxu, kawai gani tayi ya shigo ɗakin ya wuceta ya tsaya gaban makekiyar wardrobe din kayanta, buɗe wardrobe din yayi ya ringa kallon ciki sai kuma ya rufe ya buɗe wani section din, boxes din lefe ya gani an jerasu a ciki, ƴar madaidaiciyar box ya sauke ya ɗora kan bed ya buɗeta, cike take da kaya ya zazzage kayan ya barta empty, daga nan ya fara sauke ragowar boxes din, Abaya set uku ya ɗiba ya zuba a empty box din, sai kayan bacci da ya kwashi wajen set shida suma ya zuba ciki, Hajar dai na zaune inda take tana binsa da ido, ya mayar da boxes position dinsu wacca ke kan bed kawai ya bari, ya sake buɗe section din kayanta ya fara janyo duk wnda hannunsa ya fara taɓawa, haɗe gira tayi ta miƙa tace "meye haka wai, ni ka dena taɓamin kaya..", banza yayi da ita har ya gama ɗebar abinda zai ɗauka ya jibga a box din, bathroom ya shiga ya fito da shower gel da spoonge, ya zuge ƙaramin zip na akwatin ya zuba a ciki, daga nan ya wuce gaban mirror, tsaye yayi yana kallon tarkacen kai ya rasa abinda zai ɗauka don mirror din a cike yake da kayan shafe shafe, juyawa yayi ya kalleta for the first time yace "zo ki ɗauki abinda kika buƙata a nan..", with confusion written all over her face take kallonsa, ya haɗe thick eyebrows dinsa strictly yace "Ba magana nake miki ba... you are wasting my time malama..", saukar da idanunta tayi ta isa gaban mirrorn ta fitar da body lotion din da take shafawa sai perfumes guda huɗu, ya kalleta yace "is that all you need..?", turo baki tayi ta ɗauki hair butter da oil tayi drawing drawer ta ɗakko comb, ya kalleta da gefen ido kafin ya kwashe kayan shafar ya zuba a box din ya zugeta ya ɗauka ya nufi door, juyowa yayi yana kallonta yace "get change right away" da haka ya fita, Hajar tabi ƙofar da ya rufe da kallo tana sauke ajiyar zuciya, toh meye haka ne wai, kawai sai tayi tunanin ko gidansu zai mayar da ita ne, hakan yasa taji wani mugun daɗi ta ringa fatan Allah yasa haka ne, within few minutes ta gama canza kaya, doguwar rigar Abaya ta saka tayi rolling kanta da veil din Abayar, ko 1mins ba tayi da gama shiryawa ba sai gashi nan ya shigo, daga bakin door ya tsaya yace "ki jirani a compound", ba tace komai ba ta wucesa ta sauka downstairs, ɗakin nata ya shiga ya kashe duk wasu kayan wuta snn ya rufe ya fita, daman already ya kashe electric appliances na palour dana kitchen, freezer da fridge ne kawai ya bari a kunne sbd perishable food da suke cikinsu, tsaye ya ganta a dan nesa da balcony, ya rufe entrance door kafin ya nufi inda mai gadi yake zaune, Hajar tabi bayansa da kallo har ya gama mgana da Inuwa snn ya wuce parking lot, dashare haƙora Inuwa yayi ya cusa uban kuɗin da Nurain ya basa a pocket, tashi yayi ya fara zuge gate. a hankali Hajar ta isa parking space din ta tsaya gaban motar, shiga motar tayi ta fakaici kallonsa tace "gidan mu zaka kaini ko..?", baiko kalleta ba ya sauke handbrake yace "close the door", sai a lokacin ta rufe ƙofar, driving Nurain ya fara yi bayan ya dubi agogon dashboard wnda ya haska ƙarfe takwas da minti ashirin na dare, Flight dinsu na ƙarfe tara ne so he have to make it there kafin time din, haka suka bar gidan Inuwa na ɗaga musu hannu. Hajar tana ganin ya fara sharara gudu tace "kabi a hankali dan Allah, unguwarmu akwai yara da suke tsallaka titi..", without looking at her yace "Ohk" amma bai rage gudun ba, can dai taga samm hanyar da suke bi ba tayi kama da ta zuwa unguwarsu ba, shan kunu tayi tace "where are you taking me...? nan fa ba hanyar gidanmu bace", yana driving dinsa yace "Ohk", Hajar ba ta sake mgna ba tana jiran taga destination din da zasu, suna isa Airport yayi parking wajen da ake ajiye motoci, ya bude booth kafin ya sauko daga motar, sauke box din kayanta yayi da bag dinsa, har ya gama Hajar ba ta fito ba tana zaune cikin mota, tini idonta ya ciko taf da ruwa, toh ina ne nan din ya kawota, itafa gida ta saka ran zai kaita, buɗe murfin motar yayi yana kallonta yace "come down", ta sauke kanta ta fito a hankali tana bin wajen da kallo, key din motar ya bawa wni ma'aikacin Airport din masu kula da motoci, da haka ya dubeta yace "wuce muje", zirr hawayen da suke maƙale idonta suka zubo tayi sauri ta goge da bayan hannu tace "dan Allah cewa fa kayi gidanmu zaka mayar dani..", ya ɗage gira yace "ni mukayi haka dake..?", shiru tayi can tace "toh idan ba gidan mu ba ina zaka kaini da kaya..?", yace "siyar dake zanyi dan naga za kiyi tsada..", zaro ido tayi tace "am not a toy aii..", bag dinsa ya rataya ya nuna mata box din kayanta yace "Ja muje", maƙe shoulder tayi ba tace komai ba, box din ya fara ja ya wuce ya barta a wajen, saida taga ya mata nisa sai kuma ta kyalla da gudu tabi bayansa, tana zuwa kusa dashi ta fashe da kuka tace "kawa Allah da manzonsa kazo ka kaini gidanmu..", ya cigaba da tafiyarsa, tana biye dashi tana kuka a hankali, da haka suka isa departure har aka gama musu checking aka tafi da kayansu za a saka a jirgi, sai kace wata jela haka take biye dashi tana kuka mara sauti, gashi har lokacin ba ta fahimci nan din ina ne ba, ya amsar musu tickets snn suka wuce filin jirgi don har jirginsu ya fara boading, sai a lokacin Hajar ta fahimci a inda take bayan taga manya mayan Aeroplane da suke a parke. da haka tabi bayansa suka shiga jirgi, seat dake kusa da window ya samu ya zauna ita kuma ta zaune seat din dake gefensa, babu jimawa aka fara announcing jirgi zai tashi, passengers suka fara fastening seat belts, Nurain ma yayi fastening nasa, ganin ba ta saka nata ba yace "ke.. ba kiji abinda akace ba..?", ta kallesa da idanunta da suka ɗan haura tana twisting pink lips dinta, ɗauke kansa yayi bai sake kallonta ba, har jirgin ya hau runway bata saka belt dinta ba, slight hiss yayi ya ɗaura mata da kansa ya koma ya zauna da kyau a seat dinsa, habawa ai jirgi na takeoff Hajar taji wani zimmm ya tsarga mata, ƴan hanjinta suka baro ciki sukay ƙabe ƙabe a kirji, ba ta san lokacin da ta ruƙunƙumesa ba, saida jirgin yayi labelling snn ta sakesa, ta jingina da seat dinta tana jin wani iri, ji take kamar za tayi amai, ta jima bata dawo daidai ba, throughout the journey idonta biyu, shi kam tinda ya kwama headphones a kunnensa ya saka karatun Alkur'ani ya lumshe ido, lokacin da jirgin zaiyi landing Hajar tafi shiga yanayi a kan lokacin takeoff, bayan ruƙunƙumesa da tayi saida ta kifa kanta a ƙirjinsa, a hankali ta fashe da kuka tace "na shiga uku na lalace", haka sauran passengers suka fara fita daga jirgin, Nurain ya cire headphone din kunnensa ya rage murya yace "ɗagani malama..", a hankali ta sakesa tana turo baki, ya ɗan kalleta kafin ya cire belt ya tashi ya wuceta zai fita, bin bayansa tayi da kallo sai kuma ta goge fuskarta ta tashi ta bisa, luggage dinsu ya amso musu da haka kuma suka fita wajen airport din, Cab ya tsarar musu suka hau suka bar Airport din, after a ride of about 30mins drivern Cab din yayi parking cikin wani danƙareren hotel wnda daman shine location da Nurain ya basa, Nurain ya biya mai Cab kuɗinsa da haka ya wuce zuwa reception, wani worker ne ya shigar musu da kayansu, ID card da wata paper Nurain ya nunawa receptionist din, tini ta gane manyan baƙin da akay musu booking ne tin last week, Keycard ta ɗakko ta basa harda ɗan russunawa, ya amsa yace "thank you", tayi saurin cewa "my pleasure sir", ta elevator suka haura zuwa room din nasu dake 15 floor, workern dake riƙe da luggage dinsu ya ajiye daga bakin ƙofa snn ya bar wajen, Nurain ya saka Keycard ya buɗe room din, the room is huge and luxury with big bathroom, Hajar dai tayi tsaye bakin ƙofa tana ƙarewa room din kallo, Nurain ya ɗauki jakar kayansa ya buɗe closet ya saka, bathroom ya shiga ya ɗauro alwala, ya fito yana jan hannun rigarsa, kallonta yayi yace "are you a soldier..?", tayi rolling eyes tace "yess", prayer mat da ya gani a cikin closet ya ɗakko ya shimfiɗa ya kalli direction din da akay indicating a jikin wall, har ya idar da sallar Hajar na tsaye inda take, Atm card dinsa ya ɗauka ya nufi ƙofa yace "excuse me Captain..", ta ɗan matsa kaɗan, ya kewayeta ya fita, saida ya rufe ƙofar ta fahimci fa ita kadai ce a nan din, ƙarasawa cikin ɗakin tayi ta zauna kan couch, tanata zaune a wajen sai kuma ta tashi ta shiga bathroom tayi alwala, ta fito ta kalli inda ya kalla tayi sallahr Isha'i, Sai 11 ya dawo a lokacin Hajar ta gama cika famm da tsoro, yana shigowa ta miƙe tace "ni karka sake barina ni kaɗai..", ya ajiye ledojin da ya shigo dasu kan carpet yace "are you a kid..", sai kuma ya nuna mata ledar abinci yace "take your dinner..", daga haka bai sake kallonta ba ya bude closet ya dauki Pajamas dinsa ya shiga toilet ya saka, yana fitowa ya matsa gaban makeken bed din da ya sha white bedding ya ɗauki pillow da ƙaramin duvet, kan couch ya hau yayi kwanciyarsa. Da asuba Nurain ya farka, vision dinsa na daidaita ya fara surveying kan gado with his sleepy eyes, wayam yaga bata nan kuma babu alamar an hau gadon, can ya hangota ƙasan carpet ta dunƙule waje ɗaya, har yayi sallah yayi wanka ya shirya bata farka ba don ba ita tayi bacci ba sai wajen 3 na dare, before 7 ya gama shirinsa, har ya kai bakin door da bag din laptop dinsa a hannu sai kuma ya dawo, ya ringa kallonta ganin ta takure kanta ya dawo da baya ya ɗauki duvet din da ya rufa ya lulluɓa mata, da haka ya fita daga ɗakin ya rufe, A restaurant din hotel din yayi mata order both breakfast and lunch, ya gaya musu room din da za a kai da kuma time, shi kuma anan ya zauna yayi breakfast din, da ya gama ya wuce babban conference hall dake hotel din inda a nan za ake duganar da training din.....✍️
💛 HAJAR 💛

{62..}
Bai daɗe da fita ba Hajar ta farka daga baccin da take sakamakon cramps din da yake sukarta a cikin baccin, ta yamutsa fuska ta miƙe zaune tana kallon duvet din jikinta, muttsuke idonta tayi ta kalli couch din ɗakin, ta fara yaye duvet din sai kuma ta tsaya tana kallonsa, a hankali ta kai duvet din hanci perceiving the scent, ta taɓe baki gami da yin wurgi da duvet din kafin ta tashi a hankali, ƙarewa ɗakin kallo kawai take sai kace mai neman wani abun, walking like a chameleon ta isa bakin ƙofar toilet, she want to use it amma kuma tana tunanin may be yana ciki tinda dai bata gansa a ɗakin ba, kara kunnenta tayi da jikin ƙofar wai ko za taji wani sound, ɗipp ba taji anysound ba don haka ta samu courage din murɗa handle, ta shiga toilet din tana jin kamar ana mata ruwan allurai a cinye, daman tin tini haka cramp yake wahalar da ita, ganin she is still clean kawai ta ɗora alwala ta fito, ta gyara rolling dinta da ya sakwarkwace wajen bacci da yin alwala kafin ta kabbara sallah, tana idarwa ta kalli ledojin dake kan carpet har lokacin, turo baki tayi ta fara buɗewa, rolls din satchet of white coffee ta gani wajen uku sai milk sai kuma black coffee, taɓe baki tayi ta janyo wata ledar, anan taga toothbrush and toothpaste da detergent, zamewa tayi ta kwanta ta ringa twisting toes dinta shallow in pain, after 40mins lokacin ma takwas ya gota taji ana knocking door a hankali, ta tashi zaune tana kallon ƙofar, saida aka sake knocking snn ta miƙe ta isa bakin ƙofar, tana buɗewa waiter dake riƙe da park din Abinci cikin leda yace "good morning maam..", tace "morning..", ya miƙa mata ledar hannunsa yace "here is your order", kallon ledar ta tsaya yi bata amsa ba, waiter yace "gashi fa Maam", sai a lokacin ta amsa ta mayar da ƙofarta ta kulle, jingina tayi da ƙofar, after few seconds ta bude ƙofar tana leƙa waje wai ko za taga waitern ta tambayesa whereabout din wnda take jira tin dazu, wayam taga long Aisle din mai ɗauke da ƙofofi rututu, idonta yayi rau rau ta juya ta koma ɗaki, a kan couch ta zauna ta fara buɗe ledar, Irish ne da kidney sauce sai golden yam, ga bottle water da lemon kwali, tashi tayi ta dauki ledar da ta ga toothpaste da toothbrush, without second thought ta farke brush din ta matsa masa paste ta shiga toilet, bayan ta gama brush ta kuskure bakinta da mouth rinks da ta gani gefen sink, fitowa tayi ta zauna taci lafiyayyen breakfast dinta, kuma sosai taci abinda don ya mata dadi, saida ta gama ci ta ajiye ragowar snn ta fara tunanin wanka, sai a lokacin ta dubi box ɗinta dake bakin ƙofa tin daren jiya, ta janyo box din ta shiga da ita cikin ɗakin sosai, a hankali ta zuge zip tana kallon kayan ciki, ta harari kayan bayan ta tina ydda aka haɗasu, zaro ido tayi ganin harda undies sai kuma ta juyar da kai tana turo baki, sponge da shower gel dinta ta ɗauka ta shiga bathroom, tayi amfani da towel din da ta gani a jikin hanger, bayan tayi wanka ta fito ta shirya abinda, zaune tayi kan couch ta idonta ƙif akan ƙofa, tunani iri iri ya ringa zuwar mata ka, toh ko dai nan ya kawota shi yayi tafiyarsa, da sauri ta miƙe ta isa gaban closet ta buɗe, tana ganin bag dinsa taji wani mugun relief, tayi ajiyar zuciya kafin ta rufe closet ta koma ta zauna, ƙarfe sha biyu cleaner mace ta shigo ta gyara ɗakin, Cleaner ta gama aikinta ta fita, Hajar dai ta gaji da zama ta kwanta, saida taga har biyu na rana ta gota amma babu alamar zai dawo, da sauri ta miƙe jin anyi knocking door, har tana harɗewa sbd sauri taje ta buɗe door din, tayi turus tana kallon waitern da ya kawo mata breakfast, this time around ma ya gaisheta kafin ya miƙa mata ledar hannunsa, ta amsa tana jin wani ƙululu ya tsaya mata a throat, har waitern ya juya zai tafi tace "dan Allah ji mna..", ya juyo yana kallonta baice komai ba, da kyar ta ƙaƙalo mganar tace "emm dan Allah wane yace a kawo min wnn...?", yace "daga restaurant ne..", tace "Amm shi ina wnda yace a kawo..?", yace "sorry maam but i don't know aikina kawai shine delivery..", wani irin saki guiwarta tayi tace "Okay" da haka ta rufe ƙofarta, ko buɗe abincin ba tayi ba ta ajiyesa kan mini fridge dake ɗakin, saida tayi sallahr la'asar snn ta ɗan ci abincin kaɗan, tin daga cin abinci sai ciwo kuma ya motsa, ta ringa murƙususu a kan carpet, gashi idan baizo ba toh fa cramps din bazai lafa ba, daga yazo mgana ta ƙare, da kyar ta samu ya lafa mata, ta jingina da jikin gado ta ɗora kanta a guiwa, after few minutes ta ɗago kanta ta kalli door, gani kake sharr sharr hawaye sun fara gudu a cheeks dinta wani na bin wani.

★Ruqayyah ce zaune a Nurse station ta zabga uban tagumi, yau tana shigowa hospital direct office dinsa taje taga baya nan, tin ranar Tuesday last week da tazo bata sake zuwa ba sbd bata jin daɗi, sai yau ne ta samu tazo wajen aikin, Nurse Jiddah ce ta iso station din, tapping Ruqayyah tayi tace "Rukky yada zabga tagumi haka..?", Ruqayyah exhale heavily bayan ta fito daga duniyar da ta lula, Nurse Jidda ta zaune still tana kallon Ruqayyah tace "what wrong friendy you look dull..?", Ruqayyah tayi ajiyar zuciya ba tace komai ba kawai kallon Nurse Jiddah take, Nurse Jiddah tace "Okay idan bazaki gayamin ba shiknn amma dai karki sakama kanki damuwa, naga duk ba kya cikin walwala ƴan kwanakin nan...", Ruqayyah ta dafe goshinta kafin tace "Jiddah", Nurse Jiddah tace "na'am", Ruqayyah tace "yau ke ce ku ka shekara sama da biyu da saurayinki kuna soyayya har an saka muku ranar aure, toh a ranar auren sai wani abu ya tasowa shi saurayin naki wcca a dole sai an fasa aurenku a ranar, sai ya turo miki da message ya baki haƙuri yace ki jirasa yana nan dawowa gareki, dan Allah Jiddah wani hukuncin zaki yanke..", Nurse Jiddah dake kallon Ruqayyah ta saki baki kafin ta tafe hannaye tace "chaɓɗi jam..", Ruqayyah ta gyara zama tace "wani mataki zaki ɗauka...?", Nurse Jiddah tace "toh kamar yadda na bar nonon uwata haka zan barka wllh tllh, nida kai saidai hange daga nesa..", Ruqayyah ta katseta da faɗin "haba Jidda akwai fa soyayyah mai ƙarfi a tsakaninku kun fahimci juna sosai snn ya baki haƙuri fa..", Jiddah ta taɓe baki tace "meye kuma haƙuri, aini bbu wani haƙuri da zaka bani na haƙura don ka gama tozarta ni duniya da lahira, ranar ɗaurin auren mu ka tsallake ka tafi ka barni chab..", Ruqayyah ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Nurse Jiddah, gaba ɗaya karsashinta ya zagwanye gami da tsiyayewa ta guiwarta, tace "toh naji, bayan wani lokaci sai ya dawo daga inda ya tafi, yazo har inda kike ya baki haƙuri bayan wnda ya ringa turo miki ta waya..", wani murmushin rainin hankali Nurse Jiddah tayi tace "hmm Rukky knn, ai na gaya miki kamar yadda na bar nonon uwata haka na barka, kuma soyayyarka wllh na riga nayi fatali da ita akan kwalta..", Ruqayyah tace "nidae idan nice zan haƙura.." Nurse Jiddah tace "sbd kin wurgar da zuciyarki kare ya lashe ko..?", Ruqayyah ta haɗe gira tace "let me land mna malama..", Nurse Jiddah tace "Ohk", Ruqayyah tace "zan haƙura sbd fahimtar da na maka da kuma girman soyayyar dake tsakaninmu..", Nurse Jiddah ta miƙe tana kallon agogon hannunta tace "haka fa... Rukky wnn tmbyar naki is meaningless.. kuma in gaya miki duk wnda zaki tambaya irin amsar dana baki zai bayar.. kinga tafiyata zan duba ward C" tana gama faɗin haka ta bar station din. Ruqayyah ta ciro wayarta dake ringing daga pocket, da sauri tayi picking ganin Momy ce ke kiran, bayan sun gaisa Momy tace "kina jina..?", Ruqayyah da zuciyarta ke racing tace "Eh", Momy tace "toh ki taho gida yau..", Ruqayyah tace "toh", da haka Momy ta katse kiran. bayan Ruqayyah ta gama dutyn ta ta wuce gidan Haj Safiyya, kayanta kawai ta ɗeba ta yiwa mutan gidan sallama ta tafi. tana isa gidansu haka nan saddan taji zuciyarta na bugawa, shahada tayi ta murɗa ƙofar palour ta shiga, tayi sallama a hankali kafin ta shiga, Momy dake zaune palour ta amsa ba tare da ta dubeta ba, Ruqayyah ta ƙarasa cikin palourn ta duƙa ta gaida mahaifiyarta, Momy ta amsa mata a fixge sai kuma ta tashi ta bar palourn, Ruqayyah ta saukar da kanta kafin ta wuce room dinta, wanka ta shiga bayan ta fito ta tarar da missed call from Kulsoom, saida ta shirya snn tabi bayan kiran, kiran na shiga Kulsoom ta ɗaga tace "ina kika shiga sai kira nake..?", Ruqayyah tace "i was taking my bath at that time..", Kulsoom tace "Okay... sai yau Momy ta gayamin kwaɓar da kika tafka.. wai ke wace irin dabba ce da baki san gabanki da bayanki ba bare kisan inda kika dosa, wai sama kike cizo ne ko kuma kin fara tsince tsince a bola bamu sani ba, shi mahaifin naki kika kai ƙara sbd yana ƙoƙarin saita miki rayuwa, banza kawai wcca bata san inda yake mata ciwo ba, toh ai sai a barki da maganar auren tinda daman ynxu ke kin zama tsohuwar guzuma, yo to tsohuwar guzuma mana shekara ashirin da shida kin ƙi auruwa kuma duk ke kika ja ma kanki don Allah ya baki dama kikasa ƙafa kikay fatali da ita... kuma ƙaryar da kika shirgawa Momy akan mganar Dr marmaza kije ki sanar da ita da bakin ki cewa ƙarya kika giggila mata idan ba haka wllh saina tayar miki da mummunan bomb kin ji na gaya miki..", Ruqayyah ta fara girgiza kai tace "Sister wllh bazan iya gaya mata ba, bazan iya ce mata ƙarya na mata akan cewa babu wani sasantawa da mukay da Dr", Kulsoom ta juya hannu tace "oho can ta matse miki a matsematsin matsalarki, ko ki faɗa da bakinki ko na bunka miki bomb nonsense.." tana gama faɗin haka ƙitt ta kashe wayarta, Ruqayyah ta ringa kallon wayarta da idanunta kamar zasu faɗo, tana ɗaga kanta sukay ido huɗu da Momy wacca take tsaye bakin ƙofa tana kallonta da wani irin expression, darammm zuciyar Ruqayyah ta buga da ƙarfi, tini lips dinta suka fara zikiri tana ƙif ƙif da ido, juyawa Momy tayi ta bar dakin without saying anything.

★Hajar ta ɗaga kanta sakamakon murɗa door handle da akay, ta zubawa ƙofar lulu eyes dinta da suka haura, yana shigowa tayi sauri ta miƙe tsaye duk da irin murɗawar da cikinta yayi, kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kai yana taɓe baki yayi sallama ciki ciki, ba ta ko amsa ba sai wata shegiyar harara da ta shiga banka masa, shi ko baima san tana yi ba, Laptop bag dake hannunsa ya ajiye kan couch kafin shima ya zauna yana stretching kansa, ajiyar zuciya yayi ya fara massaging neck dinsa, Hajar ta koma ta zauna don tsayuwar na ƙoƙarin tayar mata da ciwo, after 10mins ya tashi ya buɗe closet, jakarsa ya zuge ya ɗauki black sweat pant da white shirt, bathroom ya shiga ya rufo ƙofar, Hajar na zaune inda take sai kace mage, bayan 15mins ya fito, yayi wanka kuma ya shirya a bathroom din kafin ya fito, sai a lokacin ya yiwa Hajar seconds look tin shigowarsa, yana kallonta yace "an kawo miki abinci..?", ta ɗan kallesa sai kuma ta haɗe rai ta juyar da kanta, ganin he start coming towards her tayi sauri ta gyaɗa kai tace "ai an kawo min fa..", yayi slight smirk murya ƙasan maƙoshi yace "Silly girl", Atm card da phone dinsa ya zura a pocket, Hajar na ganin ya saka takalmi ya nufi ƙofa zuciyarta ta buga, da wani irin zafi nama ta miƙe da gudu ta sha gabansa ta danne ƙofar da bayanta, da mamaki ya ringa kallonta, ta sha kunu tana turo baki, yace "ke.. get out of my Way", lips dinta na rawa tace "saidai mu fita tare... ni bana son zaman nan din, ka mayar dani gida", yace "anƙi ɗin...", cike da tsiwa tace "is that so.. to kwa kaima bbu inda zaka", smirk yayi yana auna ƙarfin halinta, ga ta dai wata ƴar tsugul a gabansa amma sai tsaurin ido, hannu ya kai zai matsar da ita, da sauri tace "haram.. karka taɓani.." tana karkaɗa ɗan yatsanta manuniya irin a'a din nan, kallon slim finger din nata yayi, tsaf zai karyasa idan bari ya riƙesa, girgiza kai yayi don baya son ya biye mata ya bar wajen, powering TV yayi ya zauna a kan couch yana latsa wayarsa, Hajar ta turo baki ta bar bakin ƙofar ta dawo ta zauna, har wani bouncing take wai ita ta hanasa fita, babu jimawa magrib tayi, Nurain ya tashi yana jan rigarsa, wuff mutuniyarku ta miƙe itama, gani tayi kawai ya shimfiɗa prayer mat ya kabbara sallah, hakan yasa taji relief ta koma ta zauna tana kallon Tv, ya idar da sallah ya gama addu'oinsa, yana ƙas ƙas da fingers ya tashi ya koma position dinsa ya zauna, a hankali Hajar ta miƙe tana satar kallonsa, saɗaf saɗaf take tafiya har ta isa ƙofar toilet wai ita a nata tunanin bai lura da ita ba ashe ba tasan yana kallon duk wasu moves dinta ta wutsiyar ido ba, da sanɗa ta shiga toilet din ta rufe ƙofa a hankali, ko second biyu bai ƙara ba ya tashi ya bar room din, bashi ya dawo ba sai takwas da rabi, ya ajiye ledar abincin dinner da ya taho mata dashi, Tv ma take kallo abinta don haka ko ma ƴar hararar ta na kula ba tayi masa ba, yana kallonta yace "hey.. ga dinner dinki..", tace "na ƙoshi", ya ringa kallonta kafin yace "ur cup of coffee", bathroom ya shiga ya canza kayan jikinsa zuwa Pajamas, bayan ya fito ne ya fara ƙoƙarin haɗa sahibin nasa, ruwan zafi ya jona a kettle dake kusa da fridge, a jakarsa ya ɗakko mug da spoon, ya shiga toilet ya wanko mug da spoon din, da white coffee powder da ya siyo da ita yayi amfani ya walwala sahibin, da cup din a hannunsa ya rage wutar ɗakin yabar dim, ya zauna kan couch ya kunna Laptop, Hajar dai har ta ɓingire nan kan carpet amma kuma ba bacci take ba, operating system din yake at same time yana sipping coffee, kallon inda take kwance yayi, kawai ya ajiye mug din hannunsa ya tashi ya isa inda take, ya duƙa yayi tapping dinta, ta buɗe idonta tana zarosu waje don ynxu baccin ya fara figarta, bed ya nuna mata yace "koma can ki kwanta..", ta buɗe baki zatay magana, da sauri ya ɗora yatsansa akan lips dinsa yace "shhhh do what i said ko kuma na fanshe duk rashin kunyar da kikay min", ai kam ba musu ta tashi tana turo baki ta hau gadon ta kwanta daga gefe, pillow da ƙaramin duvet da ya kwanta jiya ya ɗauka ya koma kan couch ya cigaba da abinda yake, har 11 bai kwanta ba yanata danna Laptop. Hajar tayi wani juyi mai kauri sbd azabar cramps, ba ta san lokacin da ta sakko daga kan gadon ba ta fara murƙususu tace "wayyo zan mutu cikina" sai kuma ta fashe da kuka, ture laptop din yayi daga gabansa, ya tashi ya kunna hasken ɗakin sosai, da sauri ya ƙaraso inda take durƙushe ya sunkuya yana kallonta yace "mene ne..?", ta yarfe hannu tana cigaba da kuka tace "wayyo Allah na zan mutu...", haɗe thick eyebrows dinsa yayi ya ɗan ɗaga murya yace "am asking mene ne..?", ganin yadda ta dafe lower abdomen dinta ya fahimci problem din daga ciki ne, ya ɗaga ƴar rigarta sai kawai ta ji soft palm dinsa a bare tummy dinta, tsabar shock da ta shiga ji kake ɗiff ta shanye kukan da take......✍️

Assalamu alaikum beautiful fans 🥰 zan dakata da posting cause I will be having exams insha Allah, please i need your prayers.... 🙏
💛 HAJAR 💛

{63..}
Duk da irin azabar pain din da take ji hakan bai hanata firgita da taji hannunsa a tummy dinta ba, she was very shocked and frightened, ta ja baya tana zaro ido tace "ni ka dena taɓani dan Allah babu kyau" sai kuma ta yarfe hannu ta cigaba da kuka a hankali, a takaice ya kalleta yace "then tell me, me yake damunki..?", ba tace masa uffan ba ta cigaba da murƙususun da take, ya ringa kallonta trying to figure out what her problem is, after yayi realizing matsalar a hankali yace "is it cramps..?", wani irin turo baki tayi ta juyar da fuskarta, hakan da tayi yasa ya gasgata hasashensa, ya tashi ya isa gaban closet ya buɗe ya ɗauki kananan kaya daga bag dinsa, bathroom ya shiga ya cire Pajamas ya saka ƙananun kayan, ya fito ya zura atm card a pocket, wayarsa ya ɗauka yana duba lokaci yaga sha ɗaya da rabi, door ya nufa ya buɗe lock kafin ya murɗa handle, har zai fita sai kuma ya juyo yana kallonta, har lokacin tana durƙushe amma kuma ta dena yarfe hannu da kuka alamar dai ya lafa mata, a hankali ta ɗago kanta sukay ido huɗu, after few seconds of staring at each other tayi sauri ta saukar da idanunta ƙasa, Nurain ya ajiye numfashi yana jan rigarsa ya buɗe ƙofar ya fita, yadda ya fita ya barta haka take a durƙushe sbd zaman ya mata daɗi sosai taji relief, ta samu ta ɗan jinginar da kanta da jikin gado ta lumshe ido, kafin 12 Nurain ya shigo ɗakin da leda a hannunsa, rufe ƙofar yayi ya shiga ciki sosai, kallonta ya ringa yi har ya ƙarasa inda take, ya duƙa gabanta ya ajiye ledar da ya shigo da ita, peacefully take ajiye numfashi idonta a lumshe, ya ringa kallon innocent face ɗinta without blinking, a hankali ya kai dubansa kan small pink lips dinta wanda ya kware wajen tsiwa, tinda yake bai taɓa mata irin wnn kallon ba, sai kace wnda aka tsikara haka ya haɗe gira yace "hey..", ganin bata motsa ba ya kai hannu ya taɓa goshinta, ta buɗe idonta tana kallonsa gashi har lokacin bai cire hannunsa daga goshinta ba, ta muskuta baya tana turo baki gami da banka masa harara, yayi saurin dunƙule hannun da ya taɓa goshinta ya kawar da kansa yace "ki koma kan bed..", maƙe shoulder tayi don bazata iya tashi a gabansa ba don tana farkawa taji alamar abinda yake wahalar da ita for days yazo, ya haɗe gira yana kallonta yace "nace ki tashi daga nan ki koma bed malama...", saukar da kanta tayi tana turo baki ba tace komai ba, chaɓ saidai yayi abinda zai yi ita dai bazata tashi ba gsky, haka kurum ta tashi asirinta ya tonu, miƙewa yayi ya fara ƙoƙarin ɗagota, ta tsala masa wani uban ihu tace "ni dae ka barni a nan, ana dole ne...", ji tayi ya saketa sai kuma ya ɗauki ledar da ya ajiye ya matsar mata da ita gabanta ba tare da ya dubeta ba, wajen ya bari ya koma yayi zamansa kan couch ya cigaba da abinda yake jikin Laptop, after like 10mins ya ɗago kai ya kalli inda take ta saman couch din, zaune ya ganta a yadda ya barta don ko motsi ba tayi ba, ya taɓe baki yana girgiza kai, kashe laptop din yayi ya ajiye, ya tashi ya rage wutar ɗakin kafin ya koma kan couch din yayi kwanciyarsa, saida Hajar taga ya ɗan jima da kwanciya snn ta samu kwarin guiwar miƙewa tsaye, ta ɗan saci kallon couch din kafin ta sunkuya ta ɗauki ledar tana duba abinda yake ciki, wani daram zuciyarta ta buga ganin abinda ke ciki, sanitary pad ce pack uku manya manya, kawai sai taji dama ƙasa ta tsage ta shige, tafi minti biyu a tsaye da ledar a hannunta, a hankali ta fara tafiya cikin sanɗa ta wuce inda box dinta take, ta buɗe box din ta ɗauki abinda zata ɗauka ta rufe, a hankali ta wuce hanyar toilet, tana buɗe ƙofar bathroom taji tayi ƙara, ta zaro lulu eyes dinta sai kuma ta juya ta fakaici kallon couch, ba ta isa ta fahimci bacci yake ko ba bacci yake ba sbd wutar ɗakin ba tada haske, tana shiga bathroom din ya buɗe idonsa yana kallon ƙofar bathroom din, kwanciyarsa ya gyara ya lumshe idonsa, Hajar na gama abinda za tay a bathroom ta fito ɗaure da towel don ta wanke rigar da ta cire da jikinta, wata soft sleeping gown wacca ta tsaya mata iya guiwa ta saka, har ta kwanta kan carpet sai kuma ta tashi tana kallon bed, a hankali tace "uhmm bari na koma kan gadon kar azo ana taɓamin jiki a bati", ta tashi ta koma kan gadon ta kwanta ta rufe da duvet. Da aduba Nurain ya farka, ya tashi zaune yana stretching jikinsa tare da karanto addu'a, shi bai saba da kwanciya a kan couch ba, bathroom ya shiga ya ɗauro alwala ya fito, bayan ya idar da sallah ya shiga wanka tare da kayan da zai saka. tsaye yake bakin mirror yana combing hair dinsa bayan ya fito daga wanka, Hajar ta buɗe idonta, kallonsa ta ringa yi har ya gama combing hair din ya bar gaban mirrorn, wayarsa yayi plugging a charge kafin ya kunna kettle ya fara tafasa ruwa, few minutes ruwan ya tafasa ya haɗa white Coffee ya zauna yana sha a hankali, duk Hajar na ankare dashi, shi kam ko kallon gadon beyi ba harkarsa kawai yake, yana gama shan coffeen ya ɗauki wayarsa da jakar Laptop dinsa, agogon dake wrist dinsa ya kalla yaga bakwai da minti ashirin, Hajar na ganin ya nufi door ta wani hantsilo daga kan gado, da sauri ta sha gabansa ta sha kunu, from head to toe ya kalleta, yayi saurin kawar da kansa after looking at her fresh legs, twisting pink lips dinta tayi ba tare da ta dubesa ba tace "idan tafiya za kai nidae ka mayar dani gida, I don't like it here..", yace "is there anything da akay miki ko kuma akwai abinda kika rasa a nan din ne...?", ta turo baki ba tace komai ba, gani tayi ya koma cikin ɗakin ya buɗe closet, babu jimawa ya dawo inda take da waya a hannunsa ƴar shafal ƙirar Samsung edge, kunna wayar yayi tana gama booting ya shiga call log, yayi long pressing 1 a take wata number ta fito, dialing numbern yayi wayarsa dake pocket tayi ringing, yayi cutting call din yana kallonta yace "if you need anything sai kiyi yadda kika ga nayi ynxu ki kirani.." da haka ya miƙa mata wayar, ƙin amsa tayi ta ringa kallon hannunsa, ya tsuke piercing eyes dinsa yace "take malama...", sai a lokacin ta amsa tana ƙif ƙif da ido, still ya koma cikin ɗakin yayi powering TV kafin ya juya yana kallonta yace "ga kallo nan kiyi idan kinga dama, in kuma ba kya so sai ki zauna kiyi jugum kamar mai zaman makoki..", yana gama fadin haka ya nufi ƙofa ya buɗe ya fita, Hajar tabi ƙofar da kallon na wasu seconds din. bayan tayi wanka ta shirya tana zauna tana kallon tv din dole, ƙarfe 9 aka kawo mata breakfast, zama tayi ta fara ci bayan ta haɗa coffee kamar yadda taga yayi, wajen ƙarfe biyu tana kwance kan couch tana kallon wani american movie da ya ɗebe mata kewa, ta tashi zaune ta zame ƙasa ta dafe cikinta da ya murɗa, can dai bayan taji bazata iya coping ba ta tashi ta ɗauko wayar da ya bata wacca ta yasar akan mirror, ta kunna ta shiga call log ta danne 1, number na appearing tayi dialing, har ta gama ringing ta katse ba a ɗaga ba, ta sake dialing a karo na biyu. Nurain dake zaune a wani makeken conference hall tare da collegue dinsa da suka zo workshop din suma, ya dena kallon abinda aka haska musu a projector ya dubi wayarsa dake kusa da Laptop dinsa da take vibrate a karo na biyu, saida wayar ta katse snn ya tashi daga kan chair dinsa yayi excusing kansa ya ɗauki wayarsa ya nufi ƙofar fita daga conference hall din, a bakin ƙofar hall din ya tsaya ya shiga kiran numbern, Hajar ta kalli wayar hannunta jin tana ringing, har ta haƙura da taji ba a ɗaga ba, a hankali ta kai slim finger dinta tayi picking ta kara a kunne ba tace komai ba, silence ɗin seconds ne ya biyo baya kafin yace "what..?", shiru tayi masa taƙi mgana, ya ciro wayar daga kunnensa ya kalli screen dinta sai kuma ya mayar kunne yace "mene ne...?", tace "ni cikina ne yake min ciwo", jim yayi kafin yace "ohk.. na siya miki drug jiya sai ki sha..", juya lulu eyes dinta tayi tace "ni ban gansa ba..", yace "ohh ba kinyi amfani da abinda na kawo miki jiya at night ba.. so ki duba cikin ledar", Hajar tayi shiru tana tunani mene abinda ya kawo mata tayi amfani dashi, lokaci guda ta tuna ai kam ƙit ta kashe wayar tana turo baki, walking slowly ta isa gaban box din kayanta ta durƙusa ta buɗe, ledar da ta saka ciki ta buɗe ta fara ciro pack din sanitary pad din, a can ƙasa ta hango wata ledar tana buɗewa taga kwalin drug, ta ɓalli 2tablets ta sha da bottle water, ko 3mins ba tayi da sha ba ciwon ya sauka gaba ɗaya babu shi, ta koma ta zauna ta cigaba da watching movie din da take.

★Maama ta fito daga ɗakinta da wata fatattakakkiyar tabarma a hannunta wacca ta gama zarewa tass, inuwar dake gaban ɗakinta ta samu ta shimfiɗa tabarmar ta zauna, Nabilah dake zaune tsakar gida tana tankaɗe tace "Maama wace miyar za a kaɗa kuka ko kuɓewa..?", Maama ta juya hannu tace "duk wacca kika kaɗa..", Nabilah tace "bari na kaɗa kuɓewa kawai don Baba yafi sonta...", Maama dake susar kai ba ji ba gani ta dena susar tace "kuka zaki kaɗamin bana son wata kuɓewar banza kayan zawayi..", Nabilah tace "amma Baba yafi son kuɓewa kuma kinga baya jin daɗi...", Maama ta ƙunduma mata wani ashar harda daƙuwa tace "uban da ya haifeki ya hau fel waya ya diro, ni zaki yiwa tsarin banza, ince baya gidan tin safe ya fita da wani kike cewa baya jin dadi, wnda baya jin dadi ne zai fice tin safe..", Nabilah ba ta sake cewa komai ba ta cigaba da tankaɗenta, Sa'adatu ce ta fito daga ɗaki sai sharɓa uban gumi take, ta zauna kusa da Maama tana sharce zufa tace "kai ɗakin nan akwai zafin bala'i da masifa sai kace gidan burodi wllh..", Maama tace "uhmm tsakar gidan ma ba dama, idan iska ta kaɗo sai ta gama baɗaɗo zafin rana take zuwa sai kiji kamar daga jahannama ta huro", Sa'adatu tayi tsaki tace "shiyasa na tsani zaman gidan nan, zafi da kuɗin cizo ma kawai sun ishi bawa..", Nabilah ta ajiye rariyar hannunta ta juyo tana kallon Sa'adatu sai kuma ta taɓe baki tace "ya za kiyi tinda a nan Allah ya ajiye ki..", Sa'adatu ta hura hanci tace "Maama ki mata mgana kinga dai ban saka da ita ba ko", Maama tace "bari Nabilah..", Nabilah ta gallawa Sa'adatu harara ta juya ta cigaba da aikinta, Maimuna ce ta fito daga ɗaki fuskarta duk kumburin bacci da kwandon soso da sabulu a hannunta, ta wage baki tana zabga hamma babu a'uzubillahi bare ta rufe baki, bokiti ta ɗauka ta ɗebi ruwa ta shiga toilet. tin daga soro Balaraba ta shiga zabga sallama, ayam ta shigo gidan tana kiran sunan Maama, Maama ta turɓune fuska ta juyar da kai, Balaraba ta ƙarasa shigowa tana kallon Maama tace "haba ƙawalli romon jaɓa babu faɗa me ya kawo gaba Rabi", Maama ta haɗe rai tace "lfy zaki shigo gidan matan aure da hayagaga..", Balaraba ta wage baki tace "nidae zuwa nayi biko naga kwana biyu kin ɗauke ƙafa sam bana jin ɗuriyarki..", Nabilah ce kawai ta gaida Balaraba Sa'adatu kam ko kallon arziƙi ba ta mata ba tana danna wayarta, wayar nan da za a buɗe maka gallery ka shiga video to tsaf mutum zai iya makancewa don babu komai a ciki sai videos din batsa da shashanci, Balaraba ta zauna kan tabarma tace "kai wnn ma duk ta ruɓe cin jiki za tay..", Maama tace "da sai ki taho da wacca zaki zauna ai..", Balaraba tace "kyaji dashi dai.. idan da kinsan da mai nazo miki da tini kin fara nan nan dani wllh tllh..", Maama ta taɓe baki tace "haba Balaraba ke har akwai wani abin arziki da za ki zo min dashi har nayi rawar ƙafa nayi nan nan dake.. hmm wane dare ne jemage bai gani ba ai sai na mutuwarsa..", Balaraba tace "da dai kin taso mun shiga daga ciki..", Maama tace "mu shiga daga ciki a ina... dawa za a shiga daga cikin..?", Balaraba ta fakaici kallon Nabilah da Sa'adatu sai kuma ta marairaice fuska tace "haba Rabi ai kya bari kiji abinda nazo miki dashi tukunna", Maama ta tashi tana gyara haɓar zaninta ta shiga ɗaki Balaraba tabi bayanta. Maimuna ta fito daga wanka ta tsugunna gaban rariya tana goge kaushi, Nabilah da ta gama ruɗe tace "Maimuna ki ɗan temaka kiyi wanke wanke babu ko kwanunkan da za a ci abinci da daddare", Maimuna ta girgiza kai tace "chabɗi tin da baki gayamin ba saida nayi wanka..", Nabilah tace "knn dai baza kiyi ba..?", Maimuna tace "kwarai..", Nabilah tayi kwafa ta saka hijab ta fita zata siyo daddawa, Maimuna ta ƙarasa goge ƙafarta ta tashi zata shiga ɗaki, juyawa tayi tana kallon Sabrah da ta shigo gidan yanxu ta dawo daga islamiyya, Maimuna tace "ke zo nan..", a hankali Sabrah ta isa kusa da Maimuna tace "gani", Maimuna tace "ga can kayan wanke wanke wuce ki zauna kiyi", Sabrah ta kalli kayan wanke wanken tace "toh bari na cire kayan makaranta Umma tace ina dawowa na ringa cirewa..", Maimuna ta buɗe baki ta lailayo wata ashariya ta lafta mata tace "zaki wuce ko saina sumar dake shegiya..", Sabrah taja da baya tana ƙunƙuni tace "Umma tace na dena zama da uniform fa..", Sa'adatu dake kallonsu tace "kika tsaya wnn figigiyar yarinyar tana mayar miki da martani, shegiyar yayarta ma haka ta barmu bare wnn ƴar tsituwar, ci uwarta kawai..", babu tausayi Maimuna ta maƙure yarinya ta shiga gaura mata mari, Sabrah ta fasa wata gigitacciyar ƙara sbd har taurari take gani, cikin bacci Umma taji ihun ƴar autarta, ita bata ma san lokacin da baccin ya ɗebeta ba, da sauri ta fito tsakar gida, har lokacin Maimuna ba ta dena wankawa Sabrah mari ba, Maimuna na ɗago kai sukay ido huɗu da Naseer dake tsaye ya harɗe hannu yana kallonta, da sauri ta saki Sabrah ta kwasa a guje zata shiga ɗakin Maama, da sauri Umma da zuciyarta ke tafasa hundred degree Celsius tasa mata ƙafa. Maimuna saida tayi nadamar marin Sabrah da tayi, dan da Naseer ya ringa haskata da maruka saida ya fasa mata baki, kunnenta kam gaba ɗaya signal dinsa ta ɗauke, da kyar Maama ta kwaci Maimuna daga hannunsa, daman yanada cikinta, Umma dai tinda ta janye ƴar autarta ta wuce ɗaki da ita.

★Tini Hajar ta fara sabawa da zaman hotel room din, yau kwanansu huɗu kenan, tin ranar da ya bata waya kullum saita kira Ummanta sun gaisa, da daddare da misalin ƙarfe tara na dare, Hajar na zaune kan carpet tana kallon wani film na comedy mai suna home alone, Nurain na zaune kan couch da pajamas a jikinsa yana operating laptop, wayarsa ya ɗauka ya shiga lalubo numbern wani friend dinsa da sukay karatu tare a India, cikin numbers da yayi saving akan email ya samo numbern abokin nasa da yayi saving da Dr Hammad, dialing numbern yayi ai kam tana fara ringing akay picking, Nurain na sallama Hammad ya ganesa with his voice, bayan sun gaisa Hammad yace "how are you doing yasu Mami...?", Nurain yace "fyn alhmdllh..?", Hammad yace "to masha Allah sai yau aka tina dani kenan", Nurain ya shafa sumar kansa yace "Ai gani ma a garin ku", Hammad yace "really are you in town..?", Nurain yace "yeah, since Sunday ma ina..." shiru yayi jin wata dariya da Hajar ta sheƙe da ita, ya ringa kallonta tana dariyarta her eyes fixed on tv, ta ɗan juyo ta kallesa har lokacin annurin fuskarta beyi fading ba, ganin sunyi ido huɗu tayi saurin tsuke fuska ta juya ta cigaba da kallonta, jin shiru Hammad yace "hello are you there..?", Nurain yace "yeah" suka cigaba da magana, wani abin dariyar aka sake yi a film din, Hajar couldn't help it but to laugh hard, ta toshe bakinta da palm dinta tana ƙoƙarin tsaida dariyar, ta gefen ido ta fakaici kallonsa ai kam taga ashe kallonta kawai yake, ta turo baki tayi twinkling lulu eyes dinta, tashi yayi ya ɗauki remote din TV ya danna off ya koma ya zauna ya ajiye remote din a side dinsa, Hajar ta wani haɗe gira ganin ya kashe mata kallo, juyowa tayi tana kallonsa taga wayarsa ma yake ko a jikinsa, haka kurum don baƙin hali shine zai kashe mata jin dadinta shi kuma ya koma gefe yana wayarsa, wani irin turo baki tayi ganin yayi murmushi kawai zuciyarta ta bata ai da girlfriend dinsa yake waya, miƙewa tayi tana kallon remote din da ya ajiye gefensa, tafiya ta fara yi kamar zata wuce still tana kallon remote din, da sauri ta kai hannu zata wafci remote din, kafin ta kai ga ɗauka shi ya rigata ɗaukewa ya ɗaga sama, ai kam taci tuntuɓe da ƙafarsa gaba dayanta ta faɗa kansa, a gigice ta fara ƙoƙarin ɗagasa ta wani zaro ido, bai bata damar hakan ba yayi saurin dafe bayanta ta sake faɗawa ƙirjinsa, a hankali yace "i will call you back" da haka ya cire wayar a kunnensa ya ajiye gefe, mutsu mutsu kawai Hajar take alan a dole tana so ta sauka a jikinsa, daman da hannu ɗaya kawai ya riƙeta, jin yadda take motsi kawai ya zagayeta da ɗayan hannun, wani irin bugu zuciyarta ta shiga yi hancinta ya cika da ƙamshinsa gashi har saukar numfashinsa tana ji.....✍️
💛 HAJAR 💛

{64..}
Sosai yayi wrapping dinta a ƙirjinsa har saida ta dena mutsu mutsun da take, tayi lamo zuciyarta na tsananta bugu, gaba ɗaya ta gigice ta rasa sukuni, after a while taji ya sassauta riƙon da ya mata, ai kam tayi wuff ta fincike kanta ta ɗagasa, ta koma da baya tana jan fingers dinta murya ƙasa ƙasa tace "wllh bbu kyau haram ne..", tsuke piercing eyes dinsa yayi yana kallonta yace "mene babu kyau..?", ba tasan lokacin da ta galla masa wata shegiyar harara ba tace "me yasa zaka taɓani ai kasan haram ne..", ya haɗe thick eyebrows dinsa yace "Nah.. ohh naga ke kika faɗo kaina young lady or is it a coincidence", ta zuba masa lulu eyes dinta sai kuma ta haɗe rai, yayi slight smirk ya nuna remote din dake gefensa yace "you can take it..", kallon remote din tayi ta wuce ta bar wajen, juyawa yayi yana kallonta ganin ta nufi gado yace "hey ga remote din fa ko kin fasa kallon ne..", banza tayi dashi ta hau gado abinta ta rufa da duvet tana turo baki, taɓe baki yayi ya juya murya ƙasan maƙoshi yace "Silly girl..." ya ɗauki wayarsa ya kira Hammad, tinda Hajar ta kwanta take shaƙar ƙamshinsa da take jinsa a kayanta, ta ringa juye juye tana yamutsa fuska, lokaci guda ta miƙe zaune ta ja siririn hancinta, ko dai ta cire kayan ne ta huta, komawa tayi ta kwanta kawai bata dade ba bacci me nauyi ya ɗauketa wnda hakan yanada nasaba da ni'imtaccen ƙamshin da ta ringa shaƙa ita bata sani ba. da asuba ta farka, a hankali ta fara buɗe idonta jin wata qira'a mai daɗi tana shiga kunnenta, ta fara surveying ɗakin da ido, zaune ta gansa kan prayer mat sautin qira'ar yana tasowa daga wajensa alamar dai shi yake karatun, tarwal Hajar ta buɗe idonta tana kallonsa, a zuciyarta kam mamaki take ai tasha boko kawai ya saka a gaba, ita tinda take ma ta taɓa jin qira'a mai daɗin wnn, gashi kuma ba taga Alqur'ani a gabansa ba alamar da ka yake yi, ta yamutsa fuska a ranta tace ba wani nan ya sayyadi ya fisa, ta lumshe idonta tana tunanin ya sayyadinta wnda ɗaiɗaikun ranaku ne bata tinawa dashi. tashi Nurain yayi bayan ya hattama iya izifin da zaiyi, ya kunna hasken ɗakin sosai, ya ɗan fakaice kallon gado, da sauri ya ɗauke kansa ya wuce ya buɗe closet ya ɗauki kayan da zai saka ya shiga wanka, after 15 minutes ya fito already ya saka kaya a bathroom yana goge cikakkiyar sumarsa da small towel, Hajar da ta buɗe idonta tin bayan shigarsa bathroom tayi sauri ta rufe ganin ya fito, saida yasha white coffee snn ya ɗau jakar Laptop dinsa ya fita wajen bakwai da rabi, yana fita Hajar ta diro daga kan gado, da sauri ta shige toilet tayi wanka, tana fitowa ta kimtsa kanta tsaf don har combing hair dinta tayi, ƙarfe takwas da rabi aka kawo mata breakfast, kaɗan taci abincin don bata jin yunwa sbd tasha coffee, wayar da ya bata ta ɗauko tayi dialing numbern Umma, tana fara ringing Umma ta ɗaga, bayan sun gaisa Hajar tace "Umma yasu Baba da Sabra da Yaya...?", Umma tace "kowa lfy lou alhmdllh, kema ai lfyr kike ko..?", Hajar ta gyaɗa kai tace "uhmm", Umma tace "toh Alhmdllh... Allah yayi albarka sai anjima..", Hajar tace "toh sai anjima..", Umma ta katse kiran. har ƙarfe sha biyu Hajar na zaune kan couch tana kallon tv, daga wnn channel din zuwa wata channel din, ita zaman waje ɗayan nan ya fara isarta fa, ba chass ba Ass saidai kawai taci abinci tayi wanka sai kwanciya, ta dubi agogo taga ƙarfe biyu saura, ita lokacin ma baya mata sauri yanzu, kallon ƙofa tayi jin an murɗa handle, a hankali ya turo ƙofar ya shigo, ido huɗu sukay, da sauri Hajar ta ɗauke kanta, yayi sallama ciki ciki itama ta amsa masa ciki ciki, tini room din ya kaure da pure men scent dinsa, da yake yaune last day na symposium din shiyasa suka tashi da wuri, daman na kwana biyar ne so a yau da take Friday suka gama, tana ganin ya shiga bathroom ta tashi daga kan couch ta ɗauki ledar lunch da aka kawo mata ta koma bakin gado ta zauna ta fara ci, Nurain ya fito daga bathroom bayan yayi refreshing kansa, a fakaice Hajar ta dubesa, lokaci guda ta tsura masa ido tana kallon farar Shirt ƙal dake jikinsa, brain ɗinta ce ta amsa ta fara sinking, kallonsa take babu ƙiftawa tana so ta tina wani abu da yake mata yawo a brain, kamar fa ba lokacin da ya kusan bige yaron nan ta fara ganinsa ba, tabbas da ta ga wnn farar Shirt din tana ƙoƙarin tina wani abu, don ita gaba ɗaya ta manta encounter dinsu ta farko ta biyu da ta uku saita huɗu kawai take tinawa, ya juya ya ɗan kalleta, ganin kallon da take masa ya tsuke ido, wayarsa da tayi vibrate ya ɗauka yaga Hammad ne ke kiransa, bai ɗaga kiran ba ya sake kallon Hajar da har lokacin bata ɗauke idonta daga kansa ba, ya kalli Shirt dinsa wacca ya lura ita take kallo, jan Shirt din yayi kafin ya haɗe gira yace "hey what are you starting at..?", ganin bata amsa ba kuma bata dena kallon nasa ba kawai ya fara tafiya towards her, twisting fingers dinsa yayi a daidai fuskarta wnda ya bada sautin ɗas ɗas, ai firgigit ta dawo daga duniyar da ta lula, haɗe gira tayi ganinsa daf ta ita, ta ajiye spoon din hannunta kan takeaway din abincin da take ci, Calmly yace "what are you starting at..?", ta juya idonta tace "is there anything to stare at..", ya ringa kallon pink lips dinta da take mgana ta wani cokalosu, ya buɗe baki zai mgna knn wayar hannunsa tayi vibrate, ya ɗauke idonsa daga kallon lips dinta ya koma da baya, picking kiran yayi ya kara a kunne yace "ohh Hammad..", from the other side Hammad yace "are you coming..?", Nurain yace "wait ai nace ka turomin inda zamu hadu ko", Hammad yace "Oh c'mon gidana fa zaka zo Dr", Nurain ya sauke ajiyar zuciya yana shafa kansa yace "kawai mu hadu a wani Eatery or Coffee shop haka mna..", Hammad yace "No.. saidai ba ziyarar zaka kawomin ba..", Nurain yace "Alright you know i don't have the Address right...", Hammad yace "ohh i will send it to you right away", Nurain yace "better" da haka ya katse kiran yana sauke ajiyar zuciya, bbu jimawa message din Hammad da ya turo masa da address ya shigo, ya zauna kan couch bayan few seconds ya kwanta ya miƙar da legs dinsa, da hannunsa yayi pillow lokaci guda bacci ya ɗebesa, Hajar na gama cin abincin ta rufe ragowar, itama baccin ne ya tafi da ita daga ɗan miƙewa. Nurain ya farka wajen ƙarfe huɗu, stretching jikinsa yayi bayan ya miƙe zaune, da sauri ya wuce toilet ya dauro alwala gudun lokaci ya ƙure masa, yana idar da sallah ya juya yana kallon Hajar da ke bacci har lokacin bata farka ba, ya sauya kayan jikinsa daga ƙanana zuwa manya, text din da Hammad ya turo masa ya buɗe yana karantawa, shi kam dai yaso su haɗu a wani wajen ba gida ba, dama dai gidansu ne bazai damu ba, wayarsa ya saka a front pocket yace "damn it", ya sake kallon position din Hajar, duƙawa yayi gabanta yayi tapping dinta a hankali, ta buɗe sleepy eyes dinta, da sauri ta miƙe tana murza ido taja da baya, miƙewa yayi yace "hey ki tashi ki shirya.. idan kuma anan zan barki shknn", yana gama faɗin haka ya nufi door ya fita, reception ya wuce ya zauna, after 30mins ya dawo ɗakin ya tarar har ta gama shiryawa, black Abaya wcca bata taɓa sawa ba ta saka, tayi rolling kanta da mayafin Abayan, tanata faman zuge box dinta wacca ta gama shirya kayanta tsaf, tinda taji yace tafiya za suyi taji wani sanyi ya saukar mata don har ga Allah ta gaji da zaman nan din, yana kallon abinda take yace "are you done..?", ta gyaɗa kai tace "Eh" lokacin da ta miƙe tana gyara rolling din da tayi, door ya nufa yace "muje", box dinta ta fara ja tabi bayansa, juyowa yayi yana kallonta, ta saukar da kanta tace "ka manta bag dinka fa..", yace "kema ke kika sa kanki daukar wnn, lokacin da muka zo mu muka dauki kayan", girgiza kai tayi ba tace komai ba, ya buɗe ƙofa ya fita, sakin box din tayi tabi bayansa, bayan ta fito daga room din ya mayar da ƙofar ya rufe, wucewa yayi ya tsaya gaban Elevator tabi bayansa suka shiga tare, suna sauka ƙasa yana gaba tana biye dashi, ganin ya zauna a kujera bayan sun isa reception tayi turus tana kallonsa, shikam wayarsa ya ciro yana duba bolt da ya kira, can kujerar dake nesa dashi ta samu ta zauna, tinda Hajar ta zauna wani gentleman dake zaune opposite dinta ya zuba mata ido, ita kam kanta na ƙasa tana wasa da fingers dinta, Nurain ya ɗago kansa ya kalli mutumin, sosai ya lura da irin kallon da yake yiwa Hajar babu ko ƙiftawa, Nurain ya haɗe gira ya tashi ya koma kujerar dake kusa data ta, ɗago kanta tayi ta kallesa jin scent dinsa, yana latsa wayarsa ba tare da ya dubeta ba ya rage murya yace "baki taho da hijab ba..?", tace "ai baka sako hijab ba da ka haɗa kayan..", ɗago kansa yayi ya ringa kallonta without blinking, ta fakaici kallonsa ganin kallon da yake mata tace "ka dena kallona dan Allah..", yace "ohh really ke da wane idon kika san ina kallonki", tashi tayi ta bar masa kujerar ta koma inda ya taso a hankali tace "ai kallon batin ya isa haka", Nurain ya kalli mutumin a fakaice, gani yayi ya juya akalar kallon nasa zuwa inda ta koma, wani irin murtuke fuska yayi har saida thick eyebrows dinsa suka haɗe, kamar wnda aka fusata haka ya miƙe, babu wani jinkiri ya isa inda ta koma ya figi hannunta ya fara janta suka fita daga reception din, suna fita waje ta fixge hannunta tace "meye haka..", ta fara goge hannun a jikin kayanta, wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke ya shafa fuskarsa da palm dinsa, juyowa yayi yana kallonta from head to toe, wani irin haske ta ƙara barin ma da ta saka black din Abaya sai hasken ya ƙaru, sajen forehead dinta ya kwanta luf luf sai kace balarabiya, ya kalli ƙafarta that is so fair har wani ja take sbd haske ga nails dinta pink, da wata iriyar murya yace "wai ke ko socks baki ɗakko ba..", da mamaki ta kallesa tace "toh wai ni na haɗa kayan ne", idan ba ƙafa da hannu da fuska ba babu inda yake bayyane a jikinta, dressing dinta was more than decent, yana duba wayarsa yaga bolt din da ya kira tazo, a front seat Nurain ya zauna Hajar kuma back seat, da haka suka bar harabar hotel din, Hajar ta ringa kallon window wondering a wani gari take, wata unguwar masu hannu da shuni suka shiga, ƙerarrun gidajen dake unguwar sai kace a ƙasar waje, gaban wani danƙareren gida Nurain yasa mai bolt din yayi parking kafin ya fara kallon wayarsa yana duba house numbern na gidan dan ya tabbatar shi din ne, bayan ya tabbatar yayi dialing numbern Hammad, tana shiga Hammad ya ɗauka, Nurain yace "am at the gate..", Hammad yace "Ohk ka shiga mana Dr", Nurain yace "Amm ai bolt ne..", Hammad yace "Okay bari na yiwa gateman mgana kawai ya shigo ciki da kai", Nurain yace "Alright", babu jimawa aka zuge tafkeken gate din gidan, suna shiga fakeken compound din gidan drivern bolt ya parker motar, Nurain ya yiwa mai bolt transfer din kuɗinsa bayan ya masa doubling, back seat ya buɗe yana kallon Hajar da tayi wani lakur yace "come down", a hankali ta zuro ƙafafuwanta ta fito, daidai lokacin Hammad ya fito daga entrance din gidan, da sauri ya ƙaraso inda Nurain yake sukay hugging juna lightly, sai kuma sukay musabaha bakin Hammad har ear yace "i swear i pick a flag..", Hajar dai kawai kallon Hammad take don bai mata kama da ƴan Nigeria ba, kana ganinsa kaga halfcast, Hammad ya kalli Hajar yace "beauty Noor..?", Nurain ya dubi Hajar ya girgiza kai yace "she is someone else", Hammad yace "ohh", da haka yayi leading dinsu zuwa katafaren palourn gidan, Hajar dai ta samu sofa ta zauna bayan shigarsu palourn, sake gaisawa sukay, Hammad yace "ai this is better, koni da naje kano ai har gida naje muka gaisa kuma na gaisa da Mami..", Nurain yace "ya wajen su Ummi...?", Hammad yace "Ummi taje Yamen", Nurain yace "Ohk", Hammad ya dubi Hajar dake zaune kan sofa yace "Hi.. good afternoon..", Hajar ta saukar da kanta tace "ina yini", yace "lfy lou, how are you doing...?", tace "fine alhmdllh", Hammad yace "good", sai kuma ya dubi Nurain dake satar kallon Hajar yace "bari na kira my Madam tazo ku gaisa" da haka ya tashi ya haura sama, bai jima ba ya sakko ya zauna a position dinsa suka cigaba da fira da Nurain, after few minutes da basu kai huɗu ba matar Hammad Maysha ta iso palourn, she's so beautiful brown skin girl, gaisawa sukay da Nurain snn Hajar, bayan nan Maysha ta tashi ta shiga kitchen ta lafto snacks da drinks tray guda ta kawo palourn ta ajiye, ta sake komawa kitchen ta kawo warmers din abinci, Maysha ganin Hajar bata taɓa komai da ta ajiye musu ba ta ɗebar mata tace tazo su shiga ciki taci, Nurain kam yasha drink sai semosa guda ɗaya, Hammad na kallon Nurain bayan Maysha ta wuce da Hajar ciki yace "Please who is this young lady Dr, is she your wife..?", Nurain ya ajiye glass goblet din lemo da yake sha yace "wife.. no she's not", Hammad yace "then", Nurain yace "yah how will i get marry ban gaya mka ba, kasan zan gaya maka koda bazaka zo ba, kaima lokacin aurenka ina India ai ka gayamin right", Hammad yace "Okay then who is she..", Nurain yace "someone" da haka ya dauki lemonsa yana sipping. sai bayan magrib suka bar gidan wnda da ƙyar Nurain ya yarda ya kai time ɗin, bayan sun dawo hotel sun shiga Elevator Hajar dake riƙe da ledar da Maysha ta bata tace "waini ban gane ba fa me muka dawo yi anan?..", a lokaci na farko da ya dubeta, kamar bazai amsa ba can yace "zama mna", ta wani zaro ido tace "what zama fa kace", ya ɗaga shoulder irin yess, da haka ya fita daga Elevator din don sunzo floor din room dinsu, Keycard ya ciro ya buɗe ƙofar room din ya juya yana kallonta yace "get in", ta maƙe shoulder tana ƙoƙarin danne hawayen da yake shirin zubo mata, kallon few seconds ya mata kafin ya shige ɗakin ya barta tsaye nan, Hajar ta goge hawayen da ya zubo mata da bayan hannu, ajiye ledar hannunta tayi a bakin ƙofar ta juya ta koma cikin Elevator, bayan kamar minti biyar Nurain dake zaune kan couch ya miƙe ganin bata shigo ba, door ya nufa yana zuwa yaga wayam, ya kalli ledar da ta ajiye nan bakin ƙofa, lokaci guda ya kalli dogon Aisle din shima yaga babu kowa, da sauri ya shiga Elevator ya sauka reception, saida ya fara ƙarewa reception din kallo nan ma yaga bata nan, har zai fita daga reception din sai kuma ya dawo ya tsaya gaban receptionist yace "amm excuse me", receptionist din yace "yes sir" Nurain yace "Please ba kaga wata young lady ta fita ba..", receptionist din yayi jim yana tunani, Nurain da hankalinsa ya fara tashi yace "she is in black", receptionist din yace "ohh i saw her going out few minutes ago", Nurain ya juya yana kallon ƙofar fita da mamaki, direct exist door ya nufa ya fita harabar hotel din dake da haske tarwal kamar rana, ya sauke numfashi yana shafa kansa yace "damn it", kawai kalle kalle yake a harabar hotel din ko zai ganta, can ya hangota tana tafiya a hankali har ta kai babban gate din barin hotel din, bai san lokacin da ya fara zabga wani sauri ba ya nufi gate, lokacin da ya isa gate din ita harta jima da fita, hangota yayi har tayi nisa da tafiyar da take gefen titi, wani irin mugun gudu motocin da suke wucewa suke, duk motar da tazo a guje take wucewa, haɗe gira yayi yabi bayanta da sauri, yana daf da zuwa kusa da ita with husky voice yace "Ke!! where are you going are you mad...?", lokaci ɗaya ta dakata da tafiyar ta juyo sukay ido huɗu, tattare ƙasan rigarta tayi ta juya ta kwasa a guje, Nurain ya zaro ido ganin uban gudun fanfalaƙin da take wnda tayi masa muguwar zarra, ai kam bashi da wani option da ya wuce ya bita, gudu take ba ji ba gani, ta waiwayo taga ai ya kusa kamota, ganin zai cimmata kawai tayi crossing road, a lokacin da wata shimfiɗeɗiyar mota ta kwararo with high speed, Nurain yaci wani mugun birki yana jin tamkar an kwaɗa masa guduma a ka, da wata iriyar murya mai diri ya kwala kiran sunanta "Hajar"......✍️
💛 HAJAR 💛

{65..}
Saura ƙiris motar ta kwasheta amma duk da haka saida ta gogeta, wata iriyar hantsilawa tayi ta faɗi ƙasan kwalta, ta dauje a duka guiwoyinta da tafin hannu, da sauri Nurain ya ƙaraso inda take, damtsenta ya riƙo ya ɗagata kamar ƴar kaza, ba karamin tashi hankalinsa yayi ba kuma har lokacin kansa bai dena sarawa ba, tin daga sama har ƙasa ya ringa kallonta fuskarsa a matuƙar murtuke, sakinta yayi kafin yasa bayan hannu ya falla mata mari, bata gama dawowa hayyacinta ba ya sake mangareta, saida Hajar taga stars tsabar gigicewa, ta fashe da matsanancin kuka a gigice tace "na shiga uku", wata tsawa da ya daka mata saida ta koma ta zube a ƙasa sbd yadda ƴan hanjinta suka juya, with stern voice yace "you must be mad, wawuya kawai..", a lokacin drivern motar da ya samu ya tsayar da motar far away from them ya ƙaraso inda suke da ɗan gudu gudu, kana ganinsa kasan ƙuruciya ke ɗebansa don bazai wuce 25yrs ba, duƙawa yayi gaban Hajar dake rusa kuka kamar ranta zai fita yace "am sorry", Nurain ya figi hannunta ya miƙar da ita, sosai ta firgita ta sake fashewa da kuka, young man din yace "should I take her to the hospital...?", a taƙaice Nurain yace "no need" da haka ya ja hannunta suka bar wajen tana rusa kuka, a haka yana figarta har suka koma cikin hotel din, direct elevator suka shiga bayan sun wuce reception, har lokacin Hajar bata dena kuka ba, suna isa room dinsu ya wani wancakalar da ita a kan carpet, da sauri da haɗe kanta da guiwarta da take jin tana mata zugi, ya zauna kan couch ya dafe kansa, ynxu idan da motar nan ta bigeta fa sai yadda Allah yayi, ya ɗago kansa ya kalleta zuciyarsa na ƙuna, slight hiss yayi ya tashi ya shiga bathroom yayo alwala, bayan yayi sallah after taking his bath ya saka pajamas, making coffee yayi ya zauna kan couch, ajiye mug din hannunsa yayi kafin ya kalli inda take, har lokacin kanta haɗe yake da guiwa tana shessheƙa a hankali, ya taɓe baki yace "ke!!", ko motsi ba tayi ba bare ta amsa, ya ɗan daga murya yace "ke!", ta ɗago jar fuskarta ba tare da ta dubesa ba, ya haɗe gira yace "tashi kije ki cire wnn black kayan sai kace a palace din sheɗanu", ba musu ta tashi tana jan ƙafa ta janyo box din kayanta, wata soft sleeping gown ta ɗauka ta shige bathroom zuciyarta tamkar za tay bindiga, yabi bayanta da kallo kafin ya ɗauki mug din coffee ya fara sipping wnda daman haɗasa yayi don ya rage masa takaici, ba ƙaramin ɓata masa rai Silly girl tayi ba, sai kace wacca kwai ya fashewa a ciki haka ta fito daga toilet din, a hankali ta zauna gefen gado after few minutes ta kwanta ta rufe da duvet, babu abinda take hangowa sai irin stars din da ta gani, Nurain na gama shanye coffee ya juya ya kalli gado, lokaci guda ya miƙe ya isa bakin gadon, kallonta ya ringa yi kafin ya zauna gefenta, Hajar ta rintse idonta don ba bacci take ba, duvet din da ta rufe ya yaye, bata motsa ba duk da hakan yazo mata unexpected, tin daga ƙafarta zuwa knees dinta da suke a bayyane ya ringa kallo, ya lura da bruises din dake guiwoyinta, a hankali ya kai dubansa kan hannayenta, bai ga ciwo a hannun ba, ya janyo hannun da ta danne yana dubasa shima, a palm yaga taji ciwo, in banda bugu bbu abinda zuciyarta take, me yasa yake taɓata wai, wani azabar tsoronsa take ji shiyasa taƙi motsi, ya ringa kallon fuskarta musamman ma soft cheeks dinta da ya hango zanen yatsunsa uku, wajen yayi jajur, shiyasa ya saka mata bayan hannu idan da front ya saka mata tsaf zai fitar mata da haƙori, ya kasa withstanding abinda ta aikata ne, the girl is so stubborn, ji tayi ya dafa forehead dinta sai kuma ya tuge mayafin da ta rufe gashinta, tini ta buɗe idonta ta miƙe zaune, tashin da tayi bai hanasa cigaba da duba jikinta da yake ba, hakan ne ma yasa ya fara ƙoƙarin ɗaga ƴar rigarta don ya duba inda rigar ta rufe, wata gigitacciyar ƙara ta fasa ta fara ture hannunsa, ganin ko gezau so yake fa ya ɗaga rigar nan sai ta fara kokawa, haɗe gira yayi ya rutsa hannayen nata da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma ya ɗage rigar yana ƙarewa fresh bodyn ta kallo, ƙoƙarin sauka ta fara daga kan gadon ya hanata don katamau ya riƙe ƴar farka, ai kam ta rushe da kuka jikinta har na rawa tace "wayyo Allahna na shiga uku, dan girman Allah ka dena taɓani, Ummata...", sakinta yayi bayan ya tabbatar bbu ciwo a jikin, da sauri taja rigar ta rufe jikinta tana zaro ido, tashi yayi ya shiga bathroom ya fito da kwalbar Dettol, kwalin tissue dake ajiye kan table ya dauka snn ya koma gefen gado ya zauna, Hajar ta muskuta baya tana turo baki, sam bata bari sun haɗa ido ba, haka nan ya goge mata bruises din da taji a hannu da knees da ruwan dettol, tinda ya zare mata ido ta tsaya bbu wani noƙe noƙe, ya mayar da kwalbar Dettol din bathroom ya fito ya rage hasken ɗakin ya hau couch ya kwanta, wajen ƙarfe ɗaya ya farka, zaune ya miƙe ya ringa massaging neck dinsa da ya riƙe, yafi minti biyar yana massaging neck din, ya juya yana kallon gado, can gefen gadon yaga Hajar tabar space sosai, ya murza sleepy eyes dinsa ya tashi ya koma kan gadon, ya kwanta a other side din gadon ya juya mata baya, da asuba Nurain ya farka yaga Hajar daf dashi sai kace yayi cuddling dinta, kanta bisa hannunsa, sauke sleepy eyes dinsa yayi kan innocent face ɗinta, baccinta take peacefully, ya gyara kwanciyarsa getting even more closer to her, kallon fuskarta yake without blinking musamman cheek dinta, a bazata ya kai other hand dinsa ya shafa cheek din nata, tin daga ƙololuwar kai yaji tamkar ana masa ruwan allurai, yayi ajiyar zuciya a hankali ya zame hannunsa da ta danne making sure bai tasheta ba, ya miƙe daga kan gadon ya nufi bathroom yana ciccilla hannunsa da ta kwanta a kai alamar dai ta daɗe akansa, sai takwas saura Hajar ta farka, tana sauka kan gado ta gansa zaune kan couch already well dressed up yana latsa wayarsa, bata masa second look ba tayi wucewarta ta shiga bathroom, yana ganin haka ya tashi ya bar mata ɗakin, har ta fito wanka ta shirya a tsanake snn ya dawo, ledar takeaway dake kan fridge ya nuna mata yace "ga breakfast", shiru tayi masa ba tace komai ba, ya daka mata tsawa yace "ba kiji me nace ba..?", ta sunkuyar da kanta tana wasa da fingers dinta tace "toh", murya ƙasan maƙoshi yace "Silly girl", kaɗan taci abincin ta ture, yana latsa wayarsa ba tare da ya dubeta ba yace "kin gama haɗa komai naki..?", gudun kar ya sake mata tsawa ta gyaɗa kai tace "Eh", fita yayi bayan minti biyar ya dawo tare da wnda zai fitar musu da kayansu don already bolt na waje tana jira, Hajar na ganin an fita da box dinta taji wani daɗi har cikin ranta, Nurain ya nufi door ya murɗa handle, juyowa yayi yana kallon Hajar da take saka takalminta, tana ɗago kanta sukay ido huɗu, tayi sauri ta saukar da kanta, dawowa yayi ya tsaya gabanta, jin scent dinsa ta ɗaga kanta, a hankali ya kai hannu ya shafa cheek dinta yace "ba kya jin magana..", da sauri taja baya tana juya lulu eyes dinta, ya sauke numfashi yace "wuce muje..", ƙofa ta nufa da sauri yabi bayanta, saida ya rufe ɗakin snn suka shiga Elevator tare zuwa ƙasa, Nurain ya dakata a reception domin checking out ya ajiye key kuma, receptionist ya duba Keycard din ganin numbern room dake jiki ya dakatar da Nurain, wata leda ya ɗakko ya miƙa masa yace "perhaps is this yours..?", Nurain ya ringa kallon ledar snn ya amsa yace "yess", ledar da matar Hammad ta bawa Hajar ce. before 9:50 suka isa Airport don jirgin 10 zasu shiga, Hajar dai na fahimtar wajen ta haɗe rai, tunowa da wahalar da tasha a jirgi tayi, saida suka shiga filin jirji ta ɗan kallesa tace "dan Allah dama mota muka hau", yace "ba nida lokacin tafiya daga Abuja zuwa kano a mota..", bata sake ce masa komai ba har suka hau jirgi, kamar lokacin da suka zo tafiyar ma ga seat dinsa ga nata, tinda suka shiga jirgin take addu'a a ranta, ai kam taci sa'a lokacin da jirgi yayi takeoff ba taji kamar yadda taji da zasu zo ba, da suka isa ma wajen landing yazo mata da sauƙi, suna fitowa Nurain ya amshi motarsa suka bar airport din, sha ɗaya da minti goma Nurain yayi horn a gate din gidansa, tini mai gadi ya buɗe gate, bayan Nurain yayi parking a parking space ya fito daga motar yana amsa sannu da zuwan da Inuwa ke masa, har bakin balcony Inuwa ya kai musu kayansu, Hajar dai na tsaye bakin ƙofa tana jiran ya buɗe masa ta shiga, deep inside her mind taji daɗi da ta ganta a gida, yana buɗe main door ta kai hannu zata ja box dinta kawai taga ya ɗauka ya shiga da ita, bayansa tabi zuwa palour taga ya haura upstairs, slowly ta fara tafiya ta haura saman itama, a bakin ƙofar ɗakinta taga ya ajiye box din, ta buɗe ɗakin taja box din ta shiga ta mayar da ƙofar ta rufe. sai wajen 4 ta sauka downstairs ta shiga kitchen ta nemawa kanta abinda za taci, plain Noodles ta dafa da boiled egg ta ci a kitchen din snn ta wanke komai da tayi amfani dashi, tinda ta koma room dinta bata sake sakkowa ba, ƙarfe tara na dare tayi wanka abinta ta saka kayan bacci, pillow da duvet ta ɗauka tayi kwanciyarta kan carpet, ko minti biyu ba tayi da kwanciya ba aka turo ƙofar ɗakin, waya ce kare a kunnensa yana sake dialing numbern Mami wacca suna cikin waya network ya yanke, bai samu Mami ba don hka ya sauke wayar daga kunnensa yana kallon Hajar, with a repartee yace "ke!! tashi daga ƙasan nan", ta miƙe zaune tana turo baki tace "ni nafi son nan..", ware ido yayi yace "what..?, magana kike min..?", ta shiga girgiza kai sai kuma ta miƙe ta koma kan gado ta kwanta, yace "daga yau kar na sake ganin wani soul ya kwanta kan carpet..", sai kace yana kallonta haka ta shiga bunka masa harara tamkar sabuwar kamu, ya juya ya bar ɗakin bayan ya kashe mata fitila. washe gari da Hajar ta farka abinda ta farayi shine wanka biyu snn ta haɗa da wankin hair dinta tinda ta jiƙasa, nannaɗe gashin tayi da towel ta fito, bayan ta gama rubbing lotion a fatarta ta fitar da kayan da zata saka riga da skirt na atampa, tana gama oiling gashinta ta ɗauki kayan zata saka, zip din riga dai da kyar ya zugu, da tazo saka skirt shi kam zip dinsa bai zugu ba, sakin baki tayi tana kallon kanta a mirror, though ita ɗin ba mai jiki bace don ko chubby ba ta kai ba, amma kuma duk wasu point da yake fitar da kyan mace a jiki toh nata aciki suke dam dam, haƙura tayi da saka riga da skirt din ta saka doguwar riga A-line ta feshe jikinta da 3 different perfumes, tin daga room dinta ta fara shara har ta kai downstairs palour shima ta share ta kaɗe ƙura, bayan tayi mopping ta goge kayan kallo ta jona turaren wuta a burner, haba tini gida ya ɗau harami yana baza ƙamshi, kitchen ta shiga don samawa kanta breakfast, ƙarfe goma da rabi Nurain dake sanye cikin sweat pant da shirt sky blue ya sakko downstairs, ya ringa bin ko ina da kallo yana mamakin yadda yaga guri yayi fes fes, uwa uba kuma ƙamshin da yaji wnda a wajen Maminsa ya sansa, kitchen ya shiga, Hajar dake chopping onion ta ɗaga kai ta ɗan kallesa kafin ta ɗauke kanta ta cigaba da abinda take, sosai yajin albarsa da take yankawa ya addabi Nurain dake jiran coffee dinsa ya kammala, Hajar na ɗago kanta a karo na biyu ta lura da yadda yake micincina ido yana jan pointed nose dinsa, bata san lokacin da wata dariya ta kufce mata ba, ta sunkuyar da kanta tana cigaba da dariya, haɗe gira Nurain yayi lokaci guda ya kashe Coffee makern ya fita daga kitchen din don bazai iya withstanding yajin ba, yana fita kitchen din yayi wani kasalallen murmushi ya haura sama, semosa da meat pie wnda suka ji isasshen nama tayi, daman Hafsah ta koya mata yadda ake yin minced meat a blender, semosa biyu meat pie biyu ta soya ragowar kuma ta ajiye cikin fridge, daga nan ta tafasa black tea mai kayan ƙamshi ta zuba sugar ta fita. bayan Hajar ta idar da sallar azahar ta tuna da wayar da ya bata, box din da ta mayar wardrobe ta dakko, already tin jiya ta kwashe kayanta wayar ce kawai bata dauka ba, ƙaramin zip ta bude ta ciro wayar da charger dinta, ba tayi wata wata ba ta cire sim dinta na cikin wayarta da ta lallace ta ɗora kan wayar, amma dai bata cire na kai ba tinda wayar ba dual bace, numbern Hafsah ta nemo tayi dialing, bata daɗe tana ringing ba tayi picking, bayan sun gaisa Hajar tace "yasu Antyna..?", Hafsah tace "wllh lfy alhmdllh", Hajar tace "amma yaushe zaki zo Hafsah..?", Hafsah ta zaro ido tace "ranar da fel waya tayi gashi..", Hajar tace "ke dan Allah", Hafsah ta fashe da dariya tace "nifa na fadi hakan ne naji me zakice, wllh na ɗauka zaki rufeni da bala'i", Hajar tace "sbd ga jarababbiya dage sarkin faɗa ko..?", Hafsah tace "A'a ni bance ba..", Hajar tace "Toh yaushe zaki zo tare da Humairah..?", Hafsah tace "ina nan tafe karki samu damuwa", fira suka taɓa snn sukay sallama Hajar ta katse kiran, tashi Hajar tayi ta sauka downstairs ta shiga kitchen, store ta wuce ta ɗebo rice flour ta damasa a small bucket ta zuba yeast snn ta rufe da leda da kuma murfin to proof it, daga haka ta koma room dinta, ba ita ta sakko ba sai hudu da rabi bayan tayi sallahr la'asar da azkar da ta saba, tsaye tayi jikin kitchen island tana tunanin da mai zata haɗa abin, deep freezer ta bude ta ɗakko nama, saida ta bari naman ya saki snn ta shiga sarrafa pepper soup, wata daddaɗar aroma ce take tashi a kitchen din, pepper soup din na kan wuta ta ɗakko ƙullun da ta kwaɓa, har ya tashi fumm ya cika bucket din, babu ɓata lokacin ta fara soya sinasir din da tayi amfani da easy way of making it, ƙofar kitchen din taji an buɗe, ta juya sukay ido huɗu dashi, ƙarasowa yayi gaban gas din ya miƙa mata abinda ke hannunsa, ta tattare gira tana kallon hijab dinta da yake bata, amsa tayi tace "what for..?", gaba ɗaya hancinsa ya gama cika da ƙamshin abincin, yace "ki fito palour ku gaisa", yana gama fadin haka ya juya ya fita a kichen din, saida ta sauke wnda ke kan wuta ta kashe gas din snn ta fita, tare da Farooq ta gansa zaune a palourn, walking gently ta ƙarasa palourn ta zauna ta gaida Farooq, da fara'a ya amsa mata yace "how are you doing Amarya...?", Hajar ta saukar da kanta ta amsa a taƙaice, Nurain dai sai satar kallonta yake ya wani haɗe gira, after a while yace "kije ki cigaba da abinda kike" don even with hijab baiso ta zauna a nan din da dai da niqab ne is okay, kitchen ta koma within few minutes ta fito hannunta riƙe da tray na bottle water da drink, kan Centre table ta ajiye, Farooq yayi murmushi yace "thank you..", ba tace komai ba sai murmushi da tayi, Nurain ya haɗe gira yabi bayanta da kallo, Nurain yace "Amm kunyi waya da iron lady kam tinda suka tafi..?", Farooq yace "yeah vid call ma mukay da ita ta wayar Noor", Nurain ya shafa kansa yace "ohh i see", Farooq yace "Dr what exactly my problem is nifa har ynxu lower abdominal pain din nan bai barni ba..?", Nurain ya gyara zama yace "i think i told you... kayi aure kawai", Farooq ya haɗe gira yace "is a different casa malam, tin fa ina yaro wnn ciwon yake har akamin surgery.." jin an buɗe ƙofa yayi shiru, Hajar ce ta fito ta ajiye wani tray din mai ɗauke da two warmer da plates da kuma bowls, ta ajiye saman Centre table, Farooq yace "Ahh harda baƙin yamma..", murmushi tayi ba tace komai ba ta koma kitchen, da plate din nata abincin ta fito ta haura sama, Nurain ya bita da kallo sai kuma ya dubi Farooq yace "Am coming", bai jira cewarsa ba ya haura sama yana tsallake steps da bibbiyu, ƙofar ɗakinta ya buɗe, tana zaune kan carpet tana cin abinci, daga bakin ƙofa ya tsaya girarsa a haɗe yace "karki sake fitowa", ya rufe mata ƙofar, taɓe baki tayi ta cigaba da cin abincinta, tini Farooq ya baje harka ya fara ɗebar dabge, tin kafin Nurain ya ƙaraso palourn yake kallonsa ganin yadda ya tattare hannun riga yana shan pepper soup, Nurain ya zauna position dinsa yace "ynxu pain din ne ya dawo..?", Farooq yace "bari na gama karna ƙware gsky, your wife is a good cook kaji daɗinka dude...", Nurain yayi resting jikin kujera yana latsa wayarsa, bayan Farooq ya gama da pepper soup din da ya zuba yace "dude kai bazaka ci ba..?", Nurain yace "am not eating..", Farooq yace "Alright naka ai special ne, amma dai the food is yummy..", Nurain yace "stop exaggerating..", Farooq yace "am not wollah", Nurain bai sake cewa komai ba, kafin Magrib Farooq ya tashi tafiya bayan sun gama mgana da brother din nasa, Farooq yace "toh kiramin madam muyi sallama", Nurain ya nufi door yace "no need", Farooq yace "toh hka zan tafi without giving her anything, please ka kirata..", firr Nurain yaƙi kiranta sam, haka nan Farooq ya wuce amma yaso ya bawa Hajar kyauta. Nurain ya shigo palour bayan tafiyar Farooq, kallon abincin da Farooq ya rage yayi, lokaci guda ya matsa gaban center table din, spoon ya ɗauka ya buɗe warmer din pepper soup, ya ɗan ɗebi soup din ya kai baki, bari dai yaji me Farooq yaji yake zuba wnn zancen, ji yayi kunnensa ya tsira tamkar an caka masa allura, ya ɗauki tsoka daya ya saka a baki, ɗayar warmer din ya buɗe yaga wainar sinasir, yayi pinching sinasir din ya kai baki, kamar ydda ear dinsa ya tsira lokacin da ya sha soup hakama yayi this time around, ɗaukar warmers din yayi ya haura sama. washe gari Monday Nurain na isa hospital after 40mins ya shiga surgery, wani emergency patient aka kawo wnda yake buƙatar aiki cikin gaggawa, ya tsaye a position dinsa na head of the surgery, Ruqayyah ma na surgery room din tana miƙa instruments, kana ganinta kasan bata jin daɗi, Nurain yace "Artery forcep", yanata jira a basa amma shiru, ga bleeding Artery din da zaiyi clamping sai zuba take, maimakon ta basa Artery forcep saita basa Dissecting forcep shi da ba sutures zaiyi ba, Khaleel dake first assistant yace "A Nurse concentrate or you wanna be a quack", sai a lokacin Ruqayyah ta lura da abinda take miƙawa, da sauri ta mayar ta ajiye ta miƙa masa wnda ya buƙata, ana cigaba da surgery da minti 10 Ruqayyah tayi collapsing, da Nurse Jiddah aka ƙarasa surgeryn, Nurain ya zare hands gloves din hannunsa yayi disposing ya fita daga surgery room din, saida ya cire surgeon gown da soft Clog shoe da yayi surgery dasu snn ya fita gaba ɗaya, bayan Nurain ya koma office dinsa ya kira Khaleel a waya, tambayarsa yayi ina aka kai Ruqayyah, Khaleel yace "Amenity 5", Nurain yace "Ohk" kafin ya katse kiran, ajiyar zuciya yayi ya tashi ya bar office din, yana zuwa ƙofar ward din da Ruqayyah take ya murɗa handle din ya shiga, ya ƙarasa gaban bed din da take kwance yana kallonta, bakinta ya bushe kamar ƙanxo, idonta a rufe tana bacci, a wahale take ajiye numfashi, ya dubi Nurse Amina dake tare da ita yace "anyi checking BP dinta..?", Nurse Amina tace "yess Dr", yace "bring the Bp gauge..", Nurse Amina tace "Okay" da haka ta juya ta fita daga ward din, Nurain dai na tsaye gefen gadon, ji yayi an riƙe hannunsa, ya juya yana kallonta, idanunta sunyi jajir tana kallonsa a sanyaye, da kyar ta motsa lips dinta da suka bushe tace "Dearest".......✍️
💛 HAJAR 💛

{66..}
Nurain ya zare hannunsa da ta riƙe ya tattare girarsa yace "how are you feeling now..?", Ruqayyah dake kallonsa da jajayen idanunta ta girgiza kai tace "not fine... not okay", ɗauke kansa yayi daga kallonta yace "Alright you will be fine insha Allah...", Ruqayyah ta lumshe idonta tana jin suya a zuciyarta, hawaye ya ciko idonta tace "Dearest" sai kuma tayi shiru jin an buɗe ƙofa, Nurse Amina ce ta shigo da Bp gauge a hannunta, a gaban Nurain ta sake gwada Bpn ta nuna masa reading din wnda ya nuna jinin ne yayi low, ita dai Ruqayyah kawai kallonsa take sai kace tsohuwar mayya, shi kam bai sake kallon inda take ba yana kallon Nurse Amina yace "An kira familyn dinta..?", Nurse Amina tace "Eh", yace "Okay... sai a sa mata drip tinda Dr Marwan yasa an mata injection..." da haka ya juya ya fita daga ward din, Ruqayyah ta bisa da kallo tana jin wani hope yana taso mata, lallai an samu cigaba wai Dearest ne ya nuna damuwa akanta, har cikin ranta taji daɗin hakan kuma ba ƙaramin daɗi taji ba, ynxu kam ta samu ƙwarin guiwar da zata fara bar ruwa ga shukarta da ta bushe, Nurse Amina ce ta zauna da ita har Momy ta iso asibitin, Momy ta zauna gefen gadon da Ruqayyah ke kwance, da ladabi Nurse Amina ta gaisheta, Momy ta amsa mata da sakakkiyar fuska sai kuma ta dubi Ruqayyah tace "me yake damunta...?", Nurse Amina tace "sun shiga surgery ne shine ta faɗi, ashe bp dinta ne yayi low..", Momy ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Ruqayyah ba tace komai ba, Nurse Amina tace "Amma alhmdllh she is fine now, an mata allura ga drip nan ma an saka mata...", Momy tace "Alhmdllh, sannu da ƙoƙari Allah yayi albarka", Nurse Amina tace "ba komai, ni zan wuce gida Allah ya bata lfy...", Momy tace "Ameen.. Allah ya miki albarka", Nurse Amina tayi murmushi da haka ta fice daga ward din, Nurse Jiddah ma ta shigo duba Ruqayyah ta tarar tana bacci don haka suka gaisa da Momy kafin ta tafi, tin ƙarfe sha ɗaya Ruqayyah ke bacci ba ita ta farka ba sai biyu saura, tana buɗe idonta taga Momy ga two sisters dinta ma duk sunxo, a hankali Ruqayyah ta miƙe zaune ta jingina da jikin gado, Aisha tace "ya jikin..?", Ruqayyah tace "da sauƙi", Kulsoom dake goye da baby dinta ta ɗora hannu kan forehead din Ruqayyah sai kuma ta kalli Momy tace "babu fever..", a taƙaice Momy tace "Okay ya sauka knn.. saita faɗi abinda za taci ai", Ruqayyah ta sunkuyar da kanta, Kulsoom tace "na kawo miki offals pepper soup za ki ci..?", Ruqayyah ta gyaɗa kai a hankali, zuba mata farfesun kayan cikin Kulsoom tayi a bowl ta bata, Aisha tace "a haɗaki miki shayi..?", Ruqayyah ta girgiza kai tana cin farfesun a hankali, Aisha na kallon Momy tace "wai me yake damunta ne, ita kullum ba lfy..?", Momy tace "yo toh ba dole tayi ta rashin lfy ba ta ɗorawa kanta damuwa, ynxu fisabilillah me ya haɗa Ruqayyatu da hawa da saukar jini", Aisha tace "hawan jini kuma..?", Momy tace "abinda likita yace knn", Aisha ta saki baki ta kalli Ruqayyah da ta kasa cin farfesun gabanta kawai jujjuya spoon din take, Momy tace "dama ta kwantar da hankalinta wllh, ni wnn damuwar da har take ƙoƙarin jawa kanta cuta shine zai sa naji haushinta, ƙaryar da ta yimin wnn bata ƙonamin rai kamar wnn halin da ta tarka ba, tinda dai kanta ta yiwa duk wnda yayi na gari kansa, idan ma mganar Dauda ce toh shima ta sakawa zuciyarta salama don an riga an shafe babinta, shima daman aure ai ba farillah bane ƙarfaffiyar sunna ce, tinda ta nuna bata son auren ai shknn mgana ta ƙare bbu wnda zai mata dole, Daddy ya ajiye lamarinta a gefe, a haka dai dana haifeta sai mu cigaba da zama a gida nida ita muna haɗa kafaɗa, Dr yana shigowa zance ya sallamemu ni baxan yi zaman asibiti ba, ke da Kulsoom duk aure gareku ga kuma yara, nice dai zaman ya duba kuma bazan yi ba", Aisha tace "Ayi haƙuri Momy", Momy tayi tsaki tace "ni bbu abinda tayi min wnn dai damuwar ce da tke jama kanta bana so..", Aisha ta dubi Ruqayyah tace "toh kinji dai, saiki cire duk abinda ke zuciyarki..", Kulsoom tace "ya dai fiye mata". Da yamma aka sallami Ruqayyah don daman rashin lafiyar nata ba chronic bane, Ruqayyah kam tana komawa gida ta fara tsara yadda zata janyo hankalin Dearest dinta ya dawo gareta, wnn damuwar da ya nuna akanta ba ƙaramin tasiri yayi a zuciyarta ba, hakan ya nuna cewa har ynxu yana jinta a zuciyarsa knn, ta lashi takobi duk tsiya duk tsiya tsiya saita dawo da Dearest dinta.

★Nurain yayi parking motarsa a parking space din gidansa, ya cire key daga Ignition yana stretching kansa, ledar takeaway da ya siyo ya ɗauka snn ya buɗe motar ya fita, yana shiga palour daman direct sama ya haura ya shiga ɓangarensa, ya ajiye ledar takeaway din kan makeken Centre table dake huge palourn, bedroom ya wuce ya shiga wanka, yana fitowa ya saka ƙananun kaya da yake zaman gida dasu, fitowa yayi daga room din zai sauka downstairs, ya tsaya a corridor yana kallon ƙofar ɗakinta na wasu seconds din kafin ya sauka, ya buɗe ƙofar kitchen ya shiga, wani daddaɗan aroma ne ya fara masa maraba, ya kalli tukunyar dake kan gas wacca wuta take cinta amma kaɗan, plate da spoon ya ɗauka, har zai fita daga kitchen din ya dawo ya ɗauki lemon kwali da cup ya fita, upstairs ya haura ya shiga part dinsa, ledar takeaway ya buɗe ya juye abincin a plate, tinda ƙamshin abincin ya daki hancinsa ya yamutsa fuska, kwata kwata ƙamshin bai masa ba, wai nan saida ya zaɓi babban eatery snn ya siyo abincin a nan, toh ko dai tsanar da ya yiwa abincin siyarwa ne yasa yaji hakan, spoon ɗaya yaci yayi saurin wurgi da cokalin ya zuba lemo a cup ya fara sipping, mayar da abincin yayi cikin takeaway ya rufe ya koma ya jingina da kujera da cup din lemonsa a hannu, after 10mins ya ajiye cup din ya tashi ya fita, yana sauka ƙasa ya buɗe ƙofar kitchen, tsayawa yayi yana kallonta, tana tsaye gaban gas cooker tana serving, da sauri ya ɗauke idanunsa daga kallon bayanta sai kuma ya shiga kitchen din sosai, Hajar ta ajiye serving spoon dake hannunta ta juya tana kallonsa sbd motsin da taji, ido huɗu sukay tayi sauri ta janye nata ta cigaba da abinda take, Nurain ya tsaya daga bayanta yana leƙa tukunyar abincin, yanxu kam ƙamshin da yake tashi yafi na ɗaxu da ya shigo, harɗe hannu yayi ya tsuke fuska yace "har dashi kika dafa dai ko..?", jimm tayi ba tare da ta juyo ba tace "shi wa..?", Nurain ya sake tsuke fuska yace "shi wanda yaxo jiya yaci jagwalgwalon naki..", Hajar ta haɗe gira tace "A'a ba dai jagwalgwalo ba, ni ban iya jagwalgwalo ba" da haka ta rufe tukunyar ta ɗauki plate din abincin ta juyo, kallonta taga yanayi babu ko ƙiftawa, sosai idanunsu suka sarƙe staring at each other na almost 10secs, Hajar ta murguɗa masa baki tace "Please excuse me ni fita zanyi" don kallon nan da yake mata harta tsargu, ya matsa ya buɗe tukunyar, tini ya ajiye murfin sbd akwai zafi, dariyar mugunta Hajar ta tuntsire da ita tace "wa yace ka taɓamin", Nurain ya haɗe gira yana kallon hannun da ya ƙone yace "toh wai daman waye zaici wnn jagwalgwalon naki idan ba Farooq ba, look ki zuba masa zan fita sai na tafar masa dashi" da haka ya bar kitchen din yana yarfe hannu, Hajar tabi bayansa da kallo tana sauke murmushin muguntar da take masa, ajiye plate din hannunta tayi kan island, a medium warmer mai kyau ta zuba abincin, daman wnda ta rage ne za taci da daddare kawai ta zuba masa in yaso ta dafa Noodles da daddaren, Hajar na fita kitchen din da few minutes Nurain ya shigo, yana ganin warmern da ta ajiye yayi sauri ya buɗe, rufewa yayi ya ɗauki plate ya fita ya haura sama abinsa. Da daddare wajen ƙarfe tara Nurain na zaune kan makeken gadonsa, ya rage hasken ɗakin da Laptop a gabansa yana operating, wayarsa da tayi ƙarar shigowar message ya kalla, ɗaukar wayar yayi yaga number ce ta turo text din, bude message din yayi ya karanta, (Nagode sosai Dearest da kulawa..) shine kawai abinda ke rubuce, ajiye wayar yayi ya cigaba da abinda yake, sauka yayi daga kan gadon yana jan farar rigar Pajamas dake jikinsa, room slippers ya zura a soft legs dinsa, walking gently ya buɗe ƙofa ya fita, yafi minti biyu yana kallon ƙofar ɗakinta bayan fitarsa corridor snn ya buɗe, saida ya kai tsakiyar ɗakin kafin Hajar dake ɗaure da towel iya cinya ta lura dashi, fitowarta daga wanka knn, wata gigitacciyar ƙara ta fasa ta durƙushe ƙasa tana kare jikinta, Nurain kam tsaye yayi still yana kallonta ya fara tafiya towards her, Hajar da jikinta ke rawa ta ɗaga kai ganin yana nufota tayi saurin miƙewa, zumbulelen hijab dinta ta yayiba zata saka, kawai gani tayi yaxo kusa da ita aikam maimakon ta saka hijab din saita yaɓa masa a fuska, da mugun gudu ta juya da nufin shiga toilet, unfortunately for her yayi saurin fixgo hannunta bayan ya wurgar da hijab din, da iya volume dinta ta fasa ƙara hakan yasa ya wani fixgota tayi wata ramfa ya haɗata da bango, da sauri ta dafe towel din jikinta sbd kar ya kwance, ya sauke ajiyar zuciya yana kallonta from head to toe ya riƙe hannunta gam, tini ta manne da bango tana ƙoƙarin fixge hannunta daya riƙe don ta riƙe towel dinta da hannu biyu, matsowa kusa da ita yayi har tana jin breathing dinsa, muryarta na rawa tace "meye haka... ni ka sakeni babu kyau wllh Allah", da muryarsa da ta canza amo yace "mene babu kyau..?", yana jin yadda jikinta ke rawa, da kyar ta iya magana sbd yadda muryarta ke rawa tace "taɓani da kake wllh babu kyau haram ne...", sake manneta yayi da bango har jikinsu na gogar na juna, da wata iriyar murya yace "says who..?", ta bude baki za tay magana kenan ya kai hannu ya kashe wutar ɗakin, Hajar na ganin duhu ya gaure ɗakin ta wani zaro ido ta fara turesa da iya ƙarfinta, zagaye ƙugunta yayi ya janyota jikinsa yace "uhmm am asking you.. wane yace babu kyau...?", kasa magana tayi ta ringa ƙoƙarin fixge kanta, ya sunkuyo gami da ɗora goshinsa saman nata, dena kokawar tayi yayinda zuciyarta ta buga da ƙarfi, a bazata taji ya goga pointed nose dinsa a nata snn da muryar da ta tsaya iya ƙirji yace "Am asking you young lady", ina Hajar kasa mgana tayi in banda rawa bbu abinda jikinta yake, Nurain ya lumshe idonsa yana jin wani sabon abu yana kai ziyara brain ɗinsa, ajiyar zuciya ya sauke wcca tasa Hajar saurin lumshe idonta tare da kwarin guiwar hankaɗasa, saidai fa a banza don ko gezau beyi ba, sakinta yayi ya kunna fitila, da sauri ta sulale ƙasa ta tsala wani uban ihu ta takure kanta waje ɗaya, ya mata kallo ɗaya yace "bashi ne ko ba yau ba sai kin bani amsana Silly girl..", yana gama faɗin haka ya juya ya fita daga ɗakin with a hidden smile all over his face. washe gari Nurain ya fito daga ɓangarensa, briefcase ne riƙe a hannunsa, har zai sauka ƙasa sai kuma yaji bazai iya ba, dawowa yayi da baya ya murɗa ƙofar ɗakinta, Hajar dake kwance kan bed tayi sauri ta rufe idonta jin an bude ƙofa ga kuma ƙamshinsa da ya baza ɗakin, ko da idonta yake a rufe amma tana jin kaifin idonsa a kanta, after few minutes taji ya rufe ƙofar, ta mirgina ta kalli ƙofar tana turo baki gami da banka mata harara. Nurain na isa hospital ya wuce office dinsa, postion din secretaryn sa Haleema ya kalla yaga bata nan, that is unusual don kullum tana rigasa zuwa, da haka dai ya murɗa handle ya shiga ciki, tinda ya shiga yayi turus a bakin ƙofa yana kallonta, Ruqayyah ta ajiye frame din hotonsa dake hannunta ta miƙe, bayan oil control powder da ta shafa a fuskarta harda lipgloss da eye pencil, ga wani ɗan uhansun turare da ta baƙaƙa a jikinta, ta yalwata fuskarta da murmushi tace "welcome Dr", Nurain ya haɗe gira without looking at her for the second time yace "what are you doing here..?" sai kuma ya ƙaraso ciki ya zauna a chair dinsa, Ruqayyah ta bisa da kallo tana murmushi tace "Amm good morning", ko kallonta beyi ba yace "what brings you here..?", Mug din da ta ajiye kan table ta ɗauka ta miƙa masa tace "i just wanna say good morning and give this to you", sai a lokacin ya ɗaga kai ya dubi Mug din da take miƙa masa, girarsa a haɗe yace "please get lost my patients are waiting outside", tace "Ohh okay... amma please kasha coffee din", ya ɗaga kansa yana mata wani shegen kallo with stern voice yace "just leave", ta ɗaga shoulder sai kuma ta ajiye mug din kan table da haka ta juya ta fita da tafiyar da take motsa wasu sassan na jikinta, Nurse station ta wuce walking like a cat, tana zama station din tayi wani murmushi tace "yanxu ma aka fara", Nurse Jiddah ce ta fito daga wani room na female Nurses, tana ganin Ruqayyah ta saki baki tace "wai keda baki da lfy jiya har dasu kwanciya shine kike fito aiki yau", Rukayyah tace "dole na fito aiki Jiddah tinda na samu sauqi", Nurse Jiddah tace "toh Allah ya ƙara lfy", Ruqayyah tace "Ameen", Nurse Jiddah ta kalli agogon wrist dinta tace "Ohh nasan ynxu Dr Uthman yaxo bari naje na dauki Vitals din patient din na kai masa", Ruqayyah tace "wane patient..?", Nurse Jiddah tace "patient da ya yiwa aiki jiya, ai dake aka fara aikin baki kai ba hajiyata", Ruqayyah tace "Ohk, bari naje na duba kawai ke ki zauna", Nurse Jiddah tace "Okay tom shknn", miƙewa Ruqayyah tayi tace "A wane ward yake da bed number", Nurse Jiddah ta gaya mata, barin station din Ruqayyah tayi ta tafi ward din da patient din yake, saida tayi recording komai da ya kamata snn ta fito, riƙe da record book din ta kama hanyar office dinsa, daidai corridor da zai kaika office din ta tsaya, ta saka hannu a pocket ta ciro ƙaramar kwalbar turare, sosai take ƙamshi amma ta sake fesa wani, ta gyara wuyan ƙaramin hijab dinta da ya sha guga kamar Nurses Scrub dake jikinta, tana zuwa bakin office din ta tarar akwai patient a ciki don haka taja gefe ta tsaya, few minutes patient din ya fito, patient dake kan layi ya tashi zai shiga Ruqayyah tace "dan Allah ka ɗan jira na fito..", ganin itama ma'aikaciya ce bai mata musu ba, Ruqayyah ta shige office din gami da canza salon tafiya, Haleema dai ta bita da kallo sbd tana shigowa taji ƙamshi, a bakin ƙofa ta tsaya tana kallonsa yana rubuce rubuce, Nurain ya ɗago kansa da zummar ganin next patient sai kawai yaga akasin haka, ya sauke kansa fuskarsa ba yabo ba fallasa, ta ƙarasa walking like a cat ta ajiye record din hannunta kan table tace "here Vital signs na pat..", bata ƙarasa ba ya katseta da faɗin "i think Nurse Jiddah should do that", tayi twinkling eyes dinta tace "amma aikina ne Dr ita tamin handover", girarsa a haɗe ya ɗauki record din ya ajiye gabansa yace "Ohk", har cikin ranta taji daɗi after few seconds ta juya ta fita da shegiyar tafiyar da ta tarki yi.

★Da kyar Hajar ta iya raba kanta da gado, jin kanta take wani odd gani take shknn ta zama ƴar Air, ya za ai ya mata haka fisabilillah, ta samu tayi wanka tayi shafe shafenta, ba tayi attempting saka riga da skirt ba ta saka doguwar riga, ta zo fita kawai ta tsaya kallon bango, a take moment din jiya ya dawo mata fresh, ta runtse idonta ta dafe kanta, da sauri ta kawar da tunanin ta bar ɗakin, a ɗarare ta gama dafa breakfast taci a kitchen din, tana gama ci ta fara wanke duk wasu kwanuka da tayi amfani dasu, tinda ta koma ɗakinta bata sake fitowa ba har akay sallar azahar, bayan tayi sallah ta kira Anty da Ummanta suka gaisa, sai wajen ƙarfe uku ta fara jin yunwa, gashi kuma ba ta son fita sbd karta haɗu dashi, haka kurum ya ringa mata kallon ƴar air tinda ya kalleta jiya, da kyar tayi shahada ta fita, walking like a chameleon ta sauka downstairs tayi wuf ta shige kitchen, har da wani rufe ido da ajiye numfashi, kayan miya tayi blending wnda za tayi sauce, ta silala spaghetti kawai ya fiye mata sauƙi, har ta gama silala taliyar tayi sieving dinta ta zuba a plate, tana cikin zuba Sauce taji an buɗe ƙofa, da ƙarfin gaske zuciyarta ta buga sbd scent dinsa da ta shaƙa, wllh Allah shine, backing ɗinsa tayi amma kuma saita kasa cigaba da abinda take, lokaci guda ta juya ba ta bari ta hada ido dashi ba ta nufi ƙofa zata fita, da sauri ya riƙo hannunta, aikam tana juyowa ta gatsa masa cixo a hannu, yana sakinta ta kwasa a guje ta bar kitchen din.....✍️
💛 HAJAR 💛

{67..}
Nurain ya dubi hannun da ta gatsa masa cixo yayi kwafa ya juya ya kalli abincin da ta fara zubawa, plate din Abincin ya ɗauka ya ƙarasa zuba Sauce din ya soka fork a gefen plate din, saida ya ɗauki ruwa da lemo snn ya fita. da daddare wajen ƙarfe takwas Hajar ta idar da sallahr Isha'i, da kyar ta nannaɗe prayer mat din ta ajiye kan chest of drawers sbd wata azabar yunwa da take kartarta, bathroom ta shiga tayi wanka ta fito tana tafiya a hankali, ji take kamar an yashe mata ƴan hanji, doguwar riga ta kayan bacci mai laushi ta saka ko mai bata iya shafawa ba sbd ydda tayi weak, ta zumbula hijab har ƙasa tana tafiya a hankali ta fita a ɗakin, a hankali ta ringa sauka daga stairs tayi support da railer don ji take kamar iska zata iya ɗebeta, tin kafin ta kai ƙasa taji ƙarar TV, yana zaune palour da mug din coffee riƙe a hannunsa, tinda ya hangota ya dena kallon Tv ya zuba mata idanu, Hajar ta saukar da kanta ta wuce kitchen abinta, neman Spaghetti dinta ta farayi, sama ko ƙasa babu taliya a kitchen, jingina tayi da cabinet sbd bazata iya tsayuwa ba, ko strength din dafa shayi ma bata dashi a halin yanzu, da taliyarta na nan haka zata ci kayarta duk sandarewar da tayi, wani ƙululu ne ya tsaya mata a throat ynxu ina taliyanta, kafin kace me hawaye ya ciko idanunta, door aka buɗe ta ɗaga kai ta masa kallo ɗaya kafin ta saukar da idanunta, mug din hannunsa ya ajiye gaban sink without looking at her for the second time, da haka ya juya zai bar kitchen din sai kuma ya dawo da baya ya tsaya yana kallonta, speaking with a repartee yace "yah.. why are you standing here like one living statue...?", tana ɗago kanta hawayen da suke maƙale idanunta suka hau zarya, tayi sauri tasa bayan hannu ta fara gogewa, tsuke ido Nurain yayi ya ɗan matso kusa da ita yace "what happened..?", ta sunkuyar da kanta ba tace komai ba, ya duƙa ya leƙa fuskarta yace "ke mene ne..?", fashewa tayi da kuka tace "Taliyana na ajiye zan ci kuma ban ganta ba", still Nurain yayi yana kallonta cike da mamaki, ya harɗe hannu still looking at her yace "A ina kika ajiye...?", ta nuna masa kan gas tace "a nan fa na ajiye abuna..", ya kalli kan gas din sai kuma ya juyo yana kallonta, yace "toh ke wa yace ki ajiye a nan, baki san ba a ajiye abinci a kitchen din nan ba, don haka kin rasa Aljanun kitchen din sun cinye daman rabonsu ne", da sauri ta kallesa tace "ban gane Aljanu ba, daman Aljani yana cin abinci ne..?", ya ɗaga shoulder yace "ba gashi nan kin gani ba, so next time sai ki san inda zaki ringa ajiye abincinki...", sulalewa tayi ƙasa ta fashe da kuka tace "na rantse sai sun biyani abuna, ba Aljanu ba ko sheɗanu ne sai sun biyani abuna, su sun isa su cinye min abinci..", Nurain couldn't help it but to smile lightly, she's so childish, tsuke fuska yayi kamar ba shi ya gama murmushi ba yace "Au kina zaune a gidansu zaki ringa musu rashin kunya, idan suka miki wani abun ke kika jiyo... c'mon get up ki nemi wani abin ki dafa kici, ko babu abinci ne a store..?", ta dena kukan tana shessheƙa tace "Ni spaghetti na nake so bxn iya dafa wani ba..", ta ɗora kanta kan cabinet don ynxu strength din mganar ma babu, she start be coming more weak than before, Nurain ya buɗe fridge ya ciro ƙatuwar bottle din sweetened fresh milk, cupboard ya buɗe ya ɗakko glass cup ya wankesa a sink, tini ya ɓalle murfin bottle din saida ya kusan cika glass cup din da fresh milk snn ya mayar da bottle din fridge, ya duƙa gabanta ya ajiye glass cup din madaran, ta ɗan kallesa sai kuma ta dubi cup din madaran, miƙewa yayi yana jan rigarsa ya nufi ƙofa ya buɗe ya fita, after few seconds Hajar ta ɗauki cup din madaran tana turo baki, lokaci guda abinda ya faɗa akan Aljanu yayi hitting brain dinta, sai kace muzuru a lefe haka tabi kitchen din da idanu, ba tasan lokacin da wani ƙarfi yaxo mata ba ta miƙe bayan ta suri cup din madaran ta fita da sauri, still a palour ta gansa kan doguwar kujera yana latsa wayarsa TV da ya kunna tana aikinta ita kaɗai, Hajar dai ta rakuɓe ta zauna gefe guda ta kafa kofin madaran a baki, saida ta kwankwaɗe tass snn ta diri cup din, after 10mins bayan madaran ya faɗa mata ta miƙe ta shiga kitchen, a buɗe ta bar ƙofar ta ajiye cup din a sink ta fito da sauri, walking like a chameleon ta nufi stairs, Nurain ya bita da kallon wutsiyar ido har ta ɓacewa ganinsa, tashi yayi ya zura slippers dinsa tare da jan rigarsa ya kashe kayan kallon da duk wasu kayan wuta na palourn, da haka ya haura sama yana brushing sumarsa with his hand, yana haure stairs ya ganta tsaye bakin ɗakinta jingine da bango, har ya wuceta yaji tace "Ai a kitchen kawai suke ko..?", ya zuba both hands dinsa a pocket ya juyo yace "Su wa..?", tace "Aljanun..", har zai ce mata Eh sai kuma ya fasa don so yake yayi teasing dinta yace "No daman a waje biyu suke a gidan nan, da kitchen da kuma nan" yayi pointing ƙofar ɗakinta, zaro lulu eyes dinta tayi kamar zasu faɗo ta kalli ƙofar ɗakin, da sauri ya sunkuyar da kansa ganin yadda ta zaro ido sai kuma ya ɗago bayan ya haɗe gira, Hajar ta yarfe hannu tace "na shiga uku..", yace "A'a baki shiga uku ba tinda kin iya rashin kunya, don haka saiki zama ready kiga abinda zasu miki tinda kin yiwa ƴan uwansu rashin kunya..", wani irin zaro ido tayi tana girgiza kai tace "wllh ban musu rashin kunya ba, a ina na musu rashin kunya, kawai fa cewa nayi sai sun biyani abuna, kai kaji lokacin da na musu rashin kunyar..?", ya ɗaga shoulder yana taɓe baki, yadda ta wani gigice tana zaro ido ne yake basa dariya, daman gashi tubarkallah akwai idanun bare ta zarosu, tace "kuma ni yanxu ma na yafe musu na bar musu abincin halak malak..", yace "kin bar musu knn..?", ta gyaɗa kai sai kace lizard tace "Eh halak malak", yace "Alright shiga ki kwanta..", ta juya tana kallon ƙofar ɗakin sai kuma ta juyo tace "babu abinda za suyi min ko..?", yace "may be", har ta kai hannu zata buɗe ƙofar sai kuma ta fasa ta juya tace "dan Allah baza suyi min komai ba...", tsaki yayi ya buɗe ɗakin ya shiga yace "kin fi kowa iya rashin kunya da tsiwa amma ga tsoro sai kace me, c'mon malama shigo ki kwanta..", ba musu sum sum ta shiga ɗakin ta nufi gado, ya bita da kallo ganin yadda hijab dinta ke jan ƙasa kamar zai harɗeta yace "ba dai da wnn blanket dake jikinki zaki kwanta ba...?", nan ma ba musu ta kware hijab din ta ajiye ta wuce ta haye gado, saida ya tabbatar ta kwanta ta rufe legs dinta zuwa neck da duvet snn ya nufi switch din ɗakin, kashe hasken yayi ya bar mata dim, kawai sai Hajar taga kamar gaba ɗaya ya kashe wutan don duhu ta gani dunɗum, afujajan ta yaye rufar tayi kneeling kan gadon ta tsala ihu, bai san lokacin da ya bar bakin switch ba ya hau kan gadon ya toshe mata baki, tana jin present dinsa daf da ita ga kuma ƙamshinsa tayi sauri ta faɗa ƙirjinsa ta sakar masa kuka, ba wai a tsaye yake ba bare yace ƙafarsa ne ya shanye ji yayi kamar an zare masa spine gami da caka masa wani allura a ƙwaƙwalwa, bai san lokacin da ya tafi luu ya faɗa kan gadon da bayansa ba ita kuma ta faɗa ƙirjinsa fiye da da, ta wani lafe a jikinsa harda gyara kwanciya don wani secure take jinta a nan ɗin, gani take ba wani harm da zai zo gareta a jikinsa don haka tayi lakur abinta, after a while ba tasan ta yaya ba kawai taji hannunsa cikin rigarta, da sauri ta buɗe idonta da ta lumshe ta fara shirin ɗagasa, yayi saurin mirginasu ta koma ƙasansa, pillow ya janyo ya ɗora kanta a kai ya koma gefe ya zauna zuciyarsa na racing, ta ja duvet ta lulluɓe jikinta don gaba ɗaya rigar baccin ta kwaye, shi dai bai sake kallonta ba yana yaƙi da abinda yake ji, can dai ya juya ya kalleta ganin yadda take sauke numfashi ya rage murya yace "Hajar", sau uku yana kiran sunanta amma no response, ya tashi a hankali ya nufi ƙofa don har lokacin bai dawo normal ba.

★Umma na zaune tsakar gida tana tsince waken alale, Sabra ce kusa da ita da uniform tana cin wainar gero da ƙuli ƙuli da Umma ta bata kuɗi ta siyo, Umma tace "marmaza ki cinye ki tafi karki makara auta", Sabrah tace "toh Umma" sai kuma ta dauki rabin wainar da ta rage ta lunƙuma a baki, ta tashi ta wanke hannunta daga nan ta shiga ɗaki ta ɗakko jakar makaranta, saida ta shiga wajen Baba ta gaishesa ta amso kuɗin makaranta kafin ta wuce makarantar, Umma ta koma bakin rariya tana wanke gwangwanaye, Sa'adatu ce ta fito sai soshe soshe take sbd cixon sauro da kuɗin cizon da ta sha, ta ɗauki buta ta zuba ruwa tana gyatsine, tsaye tayi kan Umma ta riƙe ƙugu tace "malama ban hanya zan wuce", ko kallonta Umma ba tayi ba ta cigaba da abinda take, idan ba iskanci ba ga isasshiyar hanya nan da zata wuce ta shiga banɗakin amma sbd rashin mutunci wai sai ta inda Umma ke zaune zata wuce, har wani girgije girgije take tace "wllh ko a matsamin ko na bi tako ina ma, mutum da gidan ubansa anzo an baza shirgi ta ko ina, can an zube wake nan kuma an baza gwangwanaye, a matsa min ko in taka in wuce..", da sauri Sa'adatu ta waiga jin ana buɗe sakatar ɗaki, Naseer ya fito daga ɗakinsu fuskarsa a haɗe yace "waye yake mgana a tsakar gidan nan?", simi simi Sa'adatu ta kewaye Umma ta wuce toilet tana ƙunƙuni, Naseer ya koma ɗakinsu yana ƙwafa, don aikinsa na kwana ne wllh da sai ya gyarawa marasa kunyar yaran nan zama, tin jiya ma yaso tafiya amma bai tafin ba sbd Baba yace ya jira yau masu neman auren Nabilah zasu zo, Umma ta ajiye soson hannunta zuciyarta na mata zafi, ya za ai yarinya ƙarama ta giggilla mata wnn rashin kunyar, kawai sai Hajar ta faɗo mata, tabbas da Hajar na nan Sa'adatu bazata ci bulus ba saita mayar mata da martani, ynxu tinda babu Hajar akanta za suyi durango knn, daman Maimuna ta fara addabar Sabrah da ƙeta da mugunta. Da yamma Naseer ya shigo gida yana kallon Umma yace "Umma ki bada tabarma inji Baba", Umma dake tankaɗe tace "tom" ta tashi tana kaɗe hannunta ta shiga ɗaki, babu jimawa ta fito da tabarma ta basa, Maama da ta fito daga kewaye ta bi Naseer da kallo har ya fita, After like 20mins Baba ya shigo gidan tare da Naseer, Naseer ya miƙawa Umma tabarma yace "gashi Umma", amsa tayi ta shiga da ita ciki, Baba ya dubi ƙofar ɗakin Maama yace "ina uwar Nabilah", fitowa Maama tayi tana riƙe da labule tace "gani..", Baba yace "Alhmdllh an kawo kuɗin auren Nabilah gasu nan aljihu na..", Maama tayi kasaƙe don bata taɓa tunanin kuɗin ƴarta aka kawo ba amma aka zauna a tabarmar Umma, Maama tace "Amma an yimin adalci knn a matsayina na wacca ta haifi Nabilah", Baba yace "toh ko ke zaki fita ki amso kuɗin auren ne...?", a fusace Maama ta koma ɗakinta zuciyarta na zafi, Baba ya sanar da Umma abinda ya faru ita kuma tayi masa Allah ya sanya alheri. Maama ta kalli Nabilah da take linke kayanta tana jerawa cikin wardrobe tace "ba dai wnn matsolon bane ya kawo kuɗin aure...?", Nabilah ta saukar da kanta ba tace komai ba, Maama ta hangame baki jikinta har ya fara rawa tace "mgana nake miki kika wani sunkuyar da kai sai kace munafuka..", Maimuna tace "Maama dama kin dena ɓaɓatu don wllh shine, Tanimu mai pachi ba", Maama tace "kar dai kice min Tanimu da yake zaune bakin titi mai pachin tayar motoci", Maimuna ta tuntsire da dariya tace "shi fa", a fusace Nabilah tace "Eh shi ɗin zan aura ina ruwanki, ke zaki zauna min dashi iye, bana son shisshigi da kwala kai a faranti", Maama ta shiga tafe hannaye tace "Annabilatuwa ashe ba ki da hankali da tunani, ni kuka kai juyayi kika jajiɓowa kanki, ke mahaukaciyar inace..?", Nabilah ta zumburi baki tace "nidae ina sonsa a haka.. ai gwara ma ni an san sa kuma yana zuwa gida, itafa Maimuna ko layin gidan nan bai taɓa zuwa ba...", Maama ta katseta da faɗin "kin hau fel waya kin diro, shi wnda yake son Maimuna ba mai kuɗi bane, uban me zai haɗasa da layin nan ya shaƙi ɗoyin kwata da maƙaƙin hammatar su Iliya mai awo..", Nabilah ta ajiye kayan hannunta ta bar ɗakin da sauri, Maama ta cigaba da jaraba ita lallai Nabilah ba zata auri Tanimu ba, Sa'adatu kam ko ta tafasa sauke ba tace ba don ba shiri suke da Nabilah ba.

★Murɗa handle din ƙofar office din tayi kafin ta shiga da sallama tana tafiya like a cat, ya ɗaga kansa ya kalleta sai kuma ya haɗe gira, daga lokacin da yazo zuwa ynxu ta shigo office dinsa a karo na uku knn, kuma duk shigowar da zatay saita fesa different turare don haka da different ƙamshi ta shigo a ynxun ma, fuskarta a sake sai kace za tayi murmushi ta ƙaraso ciki ta ajiye file din hannunta kan table, a fakaice Nurain ya kalli file din yace "my secretary will do that", Ruqayyah ta dubi mug din coffee da ta ajiye masa tin shigowarta na farko, ta leƙa mug din tace "Amm baka sha Coffeen ba ai, alright sai mu canza brand tinda dearest baya son wnn..", tana gama faɗin haka ta ɗauki mug din ta nufi ƙofa tana tafiya kamar tarwaɗa, sai 3 Nurain ya bar hospital din kuma daga nan fita sukay da Farooq, ba shi ya koma gida ba sai takwas na dare, direct sama ya haura ya wuce part dinsa, after yayi refreshing kansa wajen ƙarfe sha ɗaya ya sauka ƙasa ya shiga kitchen ya haɗa Coffee, daidai inda ta jingina da cabinet jiya ya ringa kallo, to ko yau ya akay da Aljanu tinda yaga alamar ta shigo kitchen din, yana gama haɗa coffee din ya fita, bayan ya haura sama ya tsaya yana kallon ƙofar room dinta, har ya kai hannu zai murɗa handle sai kuma ya fasa, shi kaɗai yasan yadda yayi controlling kansa jiya, so solution dinsa ɗaya kuma shine to stay away from her, da wnn tunanin ya wuce room dinsa. haka nan kam acikin kwanaki uku bai saka Silly girl a idonsa ba, deep down his mind he want to see her amma action dinta kaɗai ma sosai suke jefasa a halin da bai san inda zai nemo solution ba, ranar Asabar da daddare suka tafi Airport tare da Farooq zasu taho dasu Hajiya da jirginsu yake daf da sauka, sai ƙarfe tara jirginsu Hajiya yayi landing, Hajiya na ganin Nurain abinda ta fara tmbyarsa shine ina matarsa, a takaice ya bata amsa yace tana gida, wajen parent dinsa ya wuce yana musu sannu da zuwan da Hajiya ta hanasa da tmbyar Hajar saida ya bata amsa snn ta barsa, bayan an gama musu checking suka wuce, already Abba part dinsa ya wuce Mami ma haka bayan sun isa gida, Hajiya kam branching tayi a main palour, daman Farooq bai shigo ba suna zuwa ya tafi gida, Hajiya ta daga kai ta kalli Nurain da ya fito daga part din Mami bayan ya shigar mata da kayanta, Hajiya tace "ina matar taka ne Usuman..?", Nurain yace "ohh Hajiya nace miki tana gida fa", Hajiya tace "Auho aini da kace tana gida na sha nan kake nufi, sai kace min gidanta ba wai gida ba..", Nurain yace "toh tana can", Noor ce ta shigo da ƙaramar jakar kayanta, Nurain yace "kayan sun ƙare Noor..?", Noor tace "Eh Yaya", da haka ta nufi hanyar ɗakinta, Hajiya tace "gobe da sassafe ka kawo min ita nan ta amshi tsarabarta don duk rabin kayan da na siyo ita na siyowa, sbd itace ta taimaka min na sakata na wala a kujerar jirgi, da bata shafamin man zafin nan ba ai bazan iya zaman kujera har na daɗe ba, shiyasa da naje Saudiyyar ma duk kayan da na gani ita nake tunawa, gashi nan kam na lafto mata kaya kuma babu wnda zan bawa sai ita, Noor ce ta tayani zaɓa tinda ta fini sanin birni..", Nurain yace "Ai kam saidai su raba dasu Aysha..", katsesa tayi da faɗin "wace kuma Aishan kake nufi wai Shatu..?", Nurain yace "Eh", Hajiya ta tsuke fuska tana kallonsa ta ƙasan glasses dinta tace "ba da wanda zasu raba, idan ta Shatu zan biye da tuni ƙafata ta daɗe da ruɓewa, sam sam wnn ɗiyar ta Ummi bata temaka min wajen shafa man zafi", Nurain ya kalli tsadadden agogon dake wrist dinsa, ganin dare yayi ya tashi ya miƙawa Hajiya hannunsa yace "muje na rakaki ɓangarenki kema ki huta", Hajiya ta kama hannunsa ta miƙe snn ta riƙe sandarta da other hand din tace "Eh gsky rakani nima na yada kwankwasona karka tafi ka barni ni kaɗai nayi ƙuƙi sai kace mayya tinda kowa ya ɗaɗe, su basu yi bacci ba a jirgin ni kuma na ɗan gyangyaɗa..", yana riƙe da hannunta har saida ya kaita ɓangarenta snn ya fito, ya yiwa Maminsa sallama Abba kam tinda ya shiga part dinsa ya kwanta, ƙarfe sha ɗaya da ƴan mintina Nurain ya bar gidansu zuwa gidansa....✍️
💛 HAJAR 💛

{68..}
Washe gari ƙarfe tara da rabi Hajar ta fito daga wanka ɗaure da towel, a hankali ta zauna kan stool tana rubbing lotion, wata doguwar riga armless ta saka bayan ta gama shafe shafenta, ta fesa perfumes masu sanyin ƙamshi, a hankali ta buɗe ƙofar room dinta ta fita tana ƙarewa corridor kallo, after few seconds ta ƙarasa fita ba tare da ta rufe door ba don ba ta so tayi ƙara, walking slowly cikin sanɗa har ta kai bakin door din ɓangarensa, ko takalmi bbu a ƙafarta wai don kar aji footsteps, tafi minti biyu a tsaye kafin ta kai hannu da nufin sliding door din sai kuma ta fasa, ta ciji lower lip dinta painlessly ta kara kunne a jikin ƙofar, wani irin turo baki tayi don ba taji motsi ba, ta juya ta koma room dinta still tana turo baki, toh ko dai ita kaɗai ce a gidan ynxu ne, three days fa ba ta gansa ba ko sau ɗaya, tana barin bakin ɓangaren nasa ya buɗe ƙofa, ya ringa surveying corridorn da idanunsa amma bai ga kowa ba, shi dai he is not mistaking tabbas yaga silhouette din mutum, har ya juya zai koma ciki sai kuma ya fasa ya cigaba da kallon wajen, pointed nose dinsa ya ja don sosai ya shaƙi sassanyan ƙamshin da ya karaɗe corridor din, after a while ya juya ya shiga ciki. Hajar ta zauna kan stool dake gaban mirror tana kallon kanta, toh wai yana ina ne, tsaki tayi a fili tace "ina ruwana ya tafi space ma", hular da ta rufe gashinta ta cire ta warware jelar gashin da ta naɗe, oil hair spray da Maysha matar Hammad ta bata ta ɗauka ta feshe hair dinta dashi, after that ta jiƙa kan da hair butter snn ta fara combing dinsa a hankali, jin an buɗe ƙofa tayi sauri ta ɗaga kanta, ido huɗu sukay dashi hannunsa daya cikin pocket din sweat pant dake jikinsa, miƙewa tayi still tana kallonsa sai kuma ta koma ta zauna, kallonta yake without blinking ya wani tattare thick eyebrows dinsa, Hajar ta saukar da kanta sai kuma ta ajiye comb din hannunta kan mirror, sosai ta masa kama da baby doll sbd armless gown da ta saka da kuma black coiled hair dinta dake a warware, da sauri ya ɗauke kansa speaking with a repartee yace "idan kin gama abinda kike ki shirya zan ajiyeki can wajen Hajiya...", ba tare da ta ɗago ba tana twisting slim fingers dinta ta gyaɗa kai tace "toh", yace "idan kin shirya sai kiyi yadda na koya miki a can garin da wayar da na ara miki..", nan ma tace "toh", bai ko ƙara 1sec ba ya juya ya fita ya rufe mata ƙofar, lumshe idonsa yayi yana sauke ajiyar zuciya sai kuma ya shiga ɓangarensa, saida Hajar ta gama combing din gashinta snn ta sauka downstairs ta shiga kitchen, sharp sharp ta dafa abinda za taci, bayan ta gama cin abincin ta wanke utensils din da tayi amfani dasu ta bar kitchen din, tana shiga room dinta ta bude wardrobe zata zaɓi kayan da zata saka, wata riga da skirt na atampa ta ciro, cikin kayan da Mami ta ɗinka mata ne lokacin da zasu dawo gida, kana ganin atampar kasan me tsada ce, ita dai tunanin ta kar taje sunyi mata kaɗan tinda riga da skirt ne, saidai kuma da ta saka suka mata chas chas harda space sosai a skirt din, har da pendant necklace mai dutsen white pearl ta saka, veil wnda ya dace da zanen flower din atampar ta saka kuma wnda ya rufe mata jiki sosai, ta ciro wayar da tayi plugging a charge babu wani ɓata lokaci ta shiga call log tayi long pressing 1, number na appearing tayi dialing ta kara a kunne, tana fara ringing ya katse few seconds saiga kira ya shigo, picking tayi da sanyin murya tace "Aslm..", can ƙasa taji muryarsa ya amsa, ta juya lulu eyes dinta tace "na shirya", a takaice yace "Ohk.. ki jirani a compound" da haka ya katse kiran, Hajar ta saka wayar a handbag dinta kafin ta tashi ta fita, yana kallon lokacin da ta fito ta glass door din ɓangarensa, tana sauka downstairs ya fito yabi bayanta, saida ya tabbatar ta fita daga palour snn shima ya sauka, bayan ya rufe main door ya zura key din a pocket, tsaye yayi yana kallonta babu ko ƙiftawa, tana tsaye a parking lot waiting, walking majestically ya isa parking space din ya buɗe motar da zai shiga, tana ganin ya shiga itama ta zagayo ta buɗe front seat ta zauna, tini hancinta ya ringa perceiving pure men scent dinsa mai azabar ƙamshi, Nurain ya sauke handbrake ya fakaice kallonta da wutsiyar ido, can after a while yace "saka mayafinki a head", ta ɗan kallesa ba tare da ta yi abinda yace din ba, fuskarsa a murtuke tamau ya kalleta yace "ba kiji me nace ba..", ba musu ta janyo veil din ta saka a ka sai kuma ta kalli window ta ɗaure fuska, har suka isa gidan babu wnda yace da wani ƙala, ita kam Hajar daman tinda ta kalli window ba ta sake juyowa ba, tinda ya ganta da veil yake jin wani suya a zuciyarsa, saidai kuma yasan inda za su zo bbu maza and glass din motarsa tinted ne, yana gaba tana biye dashi suka shiga main building din gidan, sosai Mami taji dadin ganin Hajar, da ladabi Hajar ta zaune ƙasan carpet ta gaida Mami snn ta mata barka dawowa kanta a ƙasa, Mami ta amsa mata da fara'a tana kallonta da kyau, ba taga damuwa a tare da ita ba hakama jikinta, Hajar ta gaida Sakeena da itama take zaune a palour tare da Mami, Sakeena tace "lfy lou alhmdllh Hajar.. ya gida..?", Hajar tace "Alhmdllh", Sakeena tace "toh masha Allah", bayan minti uku Hajar tace "zan je wajen Hajiya..", Sakeena tace "Okay toh wajen iron lady zaki..?", Hajar ta gyaɗa kai tace "Eh" da haka ta tashi ta fita walking gently, Sakeena tace "Mami yarinyar nan na da nutsuwa wllh", Mami tayi murmushi tace "sosai ma kuwa ni na gani da ta zauna a gidan nan", Nurain ne ya fito daga bedroom din Mami don suna shigowa tare da Hajar ya shige ciki. tinda Hajar ta shiga wajen Hajiya ta gaisheta tayi zamanta a can, Noor ce ta shigo tana ganin Hajar tayi murmushi tace "ynxu Yaya take gyamin kinxo..", Hajar tayi murmushi tace "An dawo lfy..?", Noor tace "alhmdllh", Hajiya na kallon Noor tace "wai ni waye zai buɗe min wnn jakar da aka nannaɗe min ita da leda da gam, duk anbi an ƙadabaibaiye min kaya sai kace na sata, daman Sa'udiyyar nan basu da yarda sam, ka bar ganin fatarsu jajir zuciyar ɓaka ce, inba baƙin hali ba meye na rufe min jaka salon dai sai an baka wahala kafin ka buɗe", Noor tace "Iron lady ba sai kin koma can gidan zaki buɗe jakan ba", Hajiya tace "Wane can gidan kuma... ga mai rabin kaya nan tazo mai ake jira, marmaza ki kirawo min wanda zai farke jakar nan na fitar mata da abunta..", Noor tace "bari na kira miki Yaya ya buɗe miki", Hajiya tace "Wai Usuman, toh ai kar naje ya gwada ƙarfi ya tsinke hannun jakar na riga na yiwa Asabe alƙawarinta", Noor tace "Iron lady mene kuma na tsinka hannun jaka kawai fa ledan za'a ɓare, nima don aiki nake a kitchen da ni zan cire miki", Hajiya tace "Au toh..", door aka buɗe Nurain ya shigo da sallama, Hajiya tace "shknn ma ba sai kin kirasa ba gashi nan yaxo", Nurain ya ƙarasa shigowa ciki ya zauna kan Sofa, Hajar na ɗaga kanta sukay ido huɗu dashi, da sauri ta miƙe tabi bayan Noor wacca ta fita ynxu, Noor ta juyo ta kalli Hajar tace "au tasowa kikay..?", Hajar tace "muje na tayaki aikin", tare suka wuce kitchen, Noor ta buɗe oven ta ciro cookies din da ta zuba tace "saura ƙiris ya babbake Hajiya ta riƙeni da surutu", Hajar dai tayi tsaye a kitchen din tana ta kallon Noor dake aikin flour, ta kwaɓa wancan ta soya wancan ta gasa wancan, ita dai tinda ba tasan me za tayi ba saidai ta temaka mata da kneading dough, suna cikin aikin Sakeena ta shigo, tana kallon Noor tace "An ɗora lunch..?", Noor ta girgiza kai tace "Garban bai dawo ba..", Sakeena tace "Alright plxx yana kawo perishable stuff din sai a ɗora", Noor tace "Sure", Sakeena ta kalli Hajar tace "you are here dear..?", Hajar ta gyaɗa kai tana cigaba da kneading dough din da take, Sakeena ta bar kitchen din bayan ta ɗebi doughnut da cookies, few minutes aka kawo perishable stuff din, mai aiki ce ta shiga dasu ta ringa ajiyewa a inda ya dace, Hajar ta matsa gaban sink ta wanke hannunta tace "me za a dafa..?", Noor ta ware ido tace "ke za kiyi girkin..?", Hajar ta ɗauki clean towel tana goge hannunta ba tace komai ba, Noor tace "Anything since you are the cook", Haɗaɗɗen Abinci mai rai da lafiya Hajar ta girka, tana gamawa Noor ta fara serving, ta zubawa Abba da Mami a different warmers, ta zubawa Hajiya potatoes porridge da Hajar din ta mata. Da yamma Mami na zaune main palour tana attending Son din ƙawarta Haj Fati, Noor ta fito daga part din Hajiya ta gaida baƙon dake palour tare da Mami, Mami tace "Noor kawo masa abinci da drink..", yace "A'a alhmdllh zan wuce ne ma..", Mami tace "A'a ka jira", Noor ta tashi ta shiga kitchen, ruwa da lemo sai snack din da ta yiwa boyfriend dinta da zai zo kawai ta ɗebar masa, don ko ƙwayar abinci ba a rage ba, an cinye tass, Nurain kam tana ganin plate biyu yaci, Noor na ajiye trayn ruwa da lemon ta wuce room dinta zata shirya zuwan saurayinta, Nurain ya sauko daga stairs yana ɗabi'arsa na jan riga, ganin Mami zaune palour tare da guest ya dakata, hannu ya miƙawa baƙon sukay musabaha, Mami tace "ka ganesa...?", Nurain yace "Sure" sai kuma ya dubi baƙon yace "Ahmad right..?", yace "yeah", Nurain har zai koma sama sai kuma ya shiga ɓangaren Hajiya, kan rug ya tarar da Hajiya ga Hajar gefenta tana yanka mata papaya, Nurain ya shafa kansa yace "ke da kika ce kin daina shan ta", Hajiya tace "Ai kaɗan zan sha yadda ba zata gundureni ba", yace "Ohk" sai kuma ya fakaici kallon Hajar da kanta ke ƙasa tana yanka papaya, key din mota ya ciro daga pocket ya jefar kan carpet daga kusa da ita, da wutsiyar ido Hajar ta kalli key din, Nurain ya duƙa kamar zai ɗauki key din ya rage murya sosai yadda Hajiya baza taji ba yace "karki fito palour" da haka ya miƙe ya fita, ko yanka uku na papayan Hajiya ba tasha ba tace "fita da ita ƴar nan ta gundureni wllh", Hajar tace "tom", har zata fita sai kuma ta dawo ta ajiye plate din papayan ta rufe, Hajiya tace "du Allah fita da ita", ba yacca Hajar ta iya haka ta ɗauki plate din ta fita, saida tazo tsakiyar main palour snn ta lura da baƙon dake zaune kan Sofa, shi kaɗai ne a palourn Mami ta shiga ciki zata ɗauko masa saƙon da zai kaiwa Mother dinsa, yana ɗago kansa daga latsa wayar da yake sukay ido huɗu da Hajar, sosai zuciyarta ta buga ganinsa a nan ɗin, ya ringa kallonta babu ko ƙiftawa, Nurain dake tsaye can ƙarshen stairs yana kallon palourn ya wani irin murtuke fuska, saida eyebrows dinsa suka haɗe, da sauri ya fara sakkowa daga stairs din, kafin ya kawo ƙasa Mami ta fito daga part dinta da paper bag a hannunta, Hajar ta saukar da kanta ta wuce kitchen da sauri, Ahmad ya bita da kallo wnda ya sake fusata Nurain dake tsaye daga bakin stairs, har wani yaji yaji zuciyarsa ke masa, innalillah babu fa veil a jikinta ya subhanallah, Ahmad ya yiwa Mami sallama bayan ya amshi bag din da ta basa, ya yiwa Nurain ma sallamar wnda ya amsa sama sama da haka ya wuce, Mami ta kalli Nurain ganin yadda ya ɗaure fuska tace "Ah ah Son this is not you, why are you frowning...?", ajiyar zuciya ya sauke ya shafa kansa, Mami tace "Come" da haka ta tashi ta shiga part dinta, bayanta Nurain yabi yana kallon ƙofar kitchen. After 20mins Hajar na zaune palourn Hajiya duk jikinta yayi sanyi sbd ganin Ahmad da tayi, toh ko dai ɗan uwansu ne, ƙofa aka buɗe, Nurain ne ya shigo har lokacin fuskarsa ba ta saki ba, yace "we are going home now", ta gyaɗa kai ba tace komai ba, ya ɗaga murya da ɗan tsawa yace "ba kiji bane..?", ba Hajar ba har Hajiya dake gyangyaɗi saida ta farka a firgice, Hajiya ta micincina ido tace "waye wnn ya ɗauki haƙƙina..?", Nurain ya ajiye numfashin da yafi kama da huci yace "Am waiting outside saura ki daɗe" da haka ya fita yayi banging door, Hajiya ta saki baki tace "bari ubanka ya dawo wllh saina gaya masa abinda kamin, ji fa fuskarsa sai kace tsohon hadari, wai yaushe Usuman ya zama haka ya mayar da fuskarsa ta Sa ƙarfi da yaji". Hajar dai tini ta yafa veil dinta ta ɗauki hand bag dinta, Hajiya ta dubeta tace "ke kuma lfy kike saɓa jaka..?", Hajar ta duƙa tace "tafiya za muyi Hajiya..", Hajiya ta buɗe baki sai kuma ta rausayar da kai tace "toh ai shknn, shiga ƙurya za kiga wasu ledoji gaban madubi ki ɗakko babbar ki kawomin..", Hajar tace "tom" da haka ta tashi ta shiga bedroom din Hajiya, babu jimawa ta fito tana jan ƙatuwar ledar da Hajiya tace ta ɗakko, Hajar tace "gashi Hajiya", Hajiya tace "Ai naki ne ƴar nan tsarabarki ne..", Hajar was shocked ta ma rasa me za tace, wnn uban kayan duka nata ne, ko da ta fara yiwa Hajiya godiya katseta tayi tace "A'a ƴar nan bafa maula kikay ba, lokacin da kike shaƙe yajin man zafi da loko babu wnda yaji babu wnda ya gani", Nurain ya sake shigowa ya tsaya daga bakin ƙofa yace "ke!!..", Hajiya tace "ka fita idona Usuman ya zaka ringa firgita ƴar mutane", yace "Hajiya cewa nayi fa ta fito..", da haka Hajar ta yiwa Hajiya sallama ta fita, ɓangaren Mami ta shiga don yi mata sallama, nan ma dai Hajar da leda ta fito wcca Mami ta bata, saida Hajar ta gayawa Mami cewa Hajiya ta bata kaya, tana fitowa Nurain dake tsaye main palour ya sunkuci ledar da ta ajiye a palourn wcca Hajiya ta bata yayi waje with speed, ita dai tabi bayansa walking gently, ikon Allah da kariyarsa ce ta kaisu gida, don gudun da Nurain ya ringa falfalawa ba a cewa komai, Hajar taga izaya iya izaya kuma taga ƙarshen walagigi a mota, a palour ya dangwarar da ledar da ya temaka mata da ita ya haura sama, Hajar ta taɓe baki ta bisa da kallo, mutum sai kace mai Junnu ko me akay masa oho, ita dai taja ledarta ta haura sama abinta. bata sake fitowa ba har dare yayi, bayan tayi sallar isha'i ta shiga wanka, tana fitowa ta tarar da missed calls from Anty Jamilah, ta zauna gefen gado ta shiga calling back, da sauri ta kalli door jin an buɗe, ta ajiye wayar ba tare da tayi ending call din ba, hijab dinta ta fara wawake zata saka, ya shigo ɗakin girarsa a haɗe yace "A can gidan me nace miki akan fitowa palour...?", turo baki tayi tace "ni ka dena shigo min ɗaki kuma ka dena kallona babu kyau haram ne" da kyar ta ƙarashe tana kallon hijab dinta dake can nesa kuma so take ta ɗakko, kawai ganinsa tayi a gabanta, ba ƙaramin bugu zuciyarta tayi ba ta tashi zumbur ta ja da baya, ganin yadda ya haɗe fuska ta buga ƙafarta a ƙasa tace "wai ni na maka laifi da zaka zo ka huce a kaina, ai Hajiya ce ta aikeni...", ya katseta da faɗin "da Hajiya ta aikeki sai akace ki fito palour without veil or hijab, ko baki san kinada aure ba...", wani kallo ta wurga masa tace "Aure kuma.. wace take da auren..?, toh saidai wata ba ni ba don ni ban taɓa aure a rayuwata ba", tsuke idanunsa yayi yace "really..", tace "yess kar kaga don kace na saka mayafi a ka na saka hakan baya nufin komai..", ba ta ankara ba sai gani tayi hasken ɗakin ya ragu, tana ganin ya taho inda take ta wani zaro ido, da gudu ta kyalla da nufin shiga bathroom amma ina don tini ya fixgota gami da haɗata da jikin wardrobe, ta tsala ihu ta fara turesa da duka hannayenta har da ƙoƙarin cixo, kawai saukar warm lips dinsa taji a nata, tsabar shock da firgita sai ta dena tura san, after few seconds ta dawo daga duniyar daskarewar da tayi, ta daddage da iya ƙarfin da Allah ya bata ta hankaɗasa, idan yayi gezau toh tabbas ya raba lips dinsa da nata, da hannu ɗaya ya riƙe duka hannayen da take kokawar dasu, ɗayan hannun kuma ya zare ribbon din da ta ɗaure gashinta kafin ya nutsar da yatsunsa cikin lallausan gashin nata still kissing her passionately, rawar da jikinta yake ce tasa towel dinta da daman ya fara sakwarkwacewa yabi jikinta ya faɗi ƙasa, da kyar Nurain yayi controlling kansa ya raba lips dinsu, sai a lokacin Hajar ta samu wani chance din kurma ihu, ƙoƙarin zubewa tayi a ƙasa yayi saurin ɗaukarta calak ya ajiyeta bisa gado, tsoron kar ya kalleta a haka yasa tayi saurin rumgumesa ta fashe da kuka tace "wayyoh Allahna na shiga uku na lalace, Ummana", Hajar ba tasan cewa wani ruwan ta janyo ba, Ehen a yau dai an fitar da part one na raini, bai kyaleta ba saida ya tabbatar ya firgita ƴar farka, a hakan ma saida ya kai zuciyarsa nesa don bai mata komai ba, tamkar zata shiɗe haka take jan shessheƙa, ganin zata sauka daga gadon ya janyota jikinsa a kasale, ta sakar masa kuka da dasasshiyar muryanta, bai saketa ba ya kuma rungumeta, da sauri ta ɓoye fuskarta a ƙirjinsa tana shessheƙa, ya ɗora kansa a kan nata hugging her tightly, lumshe idonsa yayi yana shaƙar ƙamshin da gashinta ke fitarwa, ya sauke ajiyar zuciya kafin ya rage murya a saitin kunnenta yace "har ynxun ma baki da auren Silly girl?"......✍️
💛 HAJAR 💛

{69..}
Sam Hajar taƙi ta buɗe idonta bare ta fahimci me ya faɗa, jikinta har rawa yake cause ba tayi tsammanin hakan da yayi mata ba, why did he touches her body that way, sosai yake jin ydda jikinta ke kyarma, tsoron da yake so taji din taji knn, a daidai saitin kunnen nata ya sake mgana yace "ki bani amsana Silly girl... are you still single...?", nan ma dai ta masa banza ta cigaba da shessheƙa a hankali, yace "Alright since you don't have an answer now shima na bar miki bashi, next time dole sai kin bani amsana", yana gama faɗin haka ya saketa ya tashi daga kan gadon, ya nufi door yana buttoning rigar Pajamas dake jikinsa, Hajar na jin fitarsa ta wani irin mirgina ta shige cikin duvet ta rushe da kuka, sabo fil abinda ya mata yake yawo a brain dinta, gashi skin dinta ma ƙamshinsa take bare ta yage ta cillar da ita ko ta samu ta manta, da kyar ta iya miƙewa ta nannaɗe jikinta da duvet ta ɗauki kayan baccinta ta saka, komawa tayi ta kwanta ta dunƙule waje ɗaya sai kace mage. Da asuba ta tashi tayi sallah ta sake komawa ta kwanta, har ƙarfe bakwai idonta biyu bata koma bacci ba, ji tayi an buɗe ƙofa ai kam ta runtse idonta da sauri, walking gently ya ƙarasa shigowa ya isa bakin gadon, kallon fuskarta ya ringa yi sai kuma ya duƙa ya kalli eye lashes dinta da suke rawa, bai san lokacin da wani murmushi ya kufce masa ba ya juya ya bar ɗakin ya rufe mata ƙofa, downstairs ya sauka don daman fita zaiyi yanada appointment da safe daga nan kuma zai wuce hospital. Ƙarfe sha biyu da few minutes Hajar na tsaye gaban sink a kitchen tana wanke utensils da tayi amfani dasu, tana gama wanke wanken ta ciro vegetables daga fridge za tayi blending, stew mai ɗan yawa za tayi saita ajiye a fridge ta ringa amfani da ita na 2days, tana wanke pot da za tayi amfani da ita taji ƙarar bell, fitowa tayi daga kitchen din taje ta buɗe ƙofar, ta waro ido ganin Anty sai kuma ta rungumeta tace "Anty sannu da zuwa", a takaice Anty tace "yawwa", kan Sofa Anty ta zauna tana bin palourn da kallo, Hajar ta duƙa gabanta tace "Anty ina yini", Anty ta amsa a fixge, Hajar ta ɗago kanta sai kuma ta zauna kan kujera tace "yasu Humairah...?", nan ma dai a fixge Anty ta amsa mata, tini Hajar ta fara shan jinin jikinta a hankali ta tashi ta nufi kitchen, Anty ta bita da kallo ganin yadda ta canza, ba iya fatarta ne ya canza ba har jikinta, tayi wani luwai luwai abinta alamar dai hankalinta a kwance yake, babu jimawa Hajar ta fito ta ajiyewa Anty ruwa da lemon da ta ɗakko, Anty tace "sannu Hakima", Hajar dai ta saukar da kanta ba tace komai ba, Anty ta zuge handbag dinta ta ciro wayarta, tana kallon Hajar ta ajiye mata wayar daga gefenta, da sauri Hajar ta ɗago kanta jin muryanta na fitowa daga cikin wayar, conversation dinta ne dashi na daren jiya, muryarta raɗau tana cewa kar ya sake kallonta haram ne, sau ɗaya muryarsa ya fito inda yake cewa ba tasan tanada aure ba ta fito without veil or hijab shima ɗin ƙasa ƙasa, sai na muryarta da ya kusa fasa speaker din wayar tana cewa ita sam ba tada wani aure, daga nan voice din ya ƙare kuma daman anan Anty ta katse kiran, Anty ta ringa kallon Hajar da ta sunkuyar da kai kamar munafuka tace "Daman baki da hankali Hajar, a gidan aure akwai wani abu da yake haram ne, ko ba a kan idona wnn abun ya faru ba inaji nasan cewa da mijinki kike, Islamiyyar da kika je ta tashi a banza a wofi knn, wancan allon naki da ke sargafe ɗakin Umma ba shi da wani amfani, ko a Islamiyyar naku hka aka koya miki...?", Hajar tayi shiru ba tace komai ba zuciyarta na bugu, Anty ta daka mata tsawa tace "Amsa min tambayana shashasha kike wani sunkuyar da kai sai kace ta Allah bayan ga rashin hankalin da kike giggillawa", ba shiri Hajar ta girgiza kai tace "A'a", da faɗa Anty tace "ba haka aka koya miki a Islamiyyar ba knn naki salon iskancin ne a haka, ashe abinda kike aikatawa a gidan mijin naki knn, wnn wane irin hauka ne ka ringa cewa mijinka haram sbd shirme, toh ynxu kallon me zai miki da kika aikata haka, kai tsaye zai kiraki da jahila wacca ba taje Islamiyya ba, bayan wnn ma baki amshi ƙaddara ba, idan da kin amshi ƙaddara kya aikata haka a gidan aurenki, aure an wuce wata ɗaya wata biyu na uku ma an kusa fita daga cikinsa amma kin ƙi ki saukar da kanki, Mijinki na faɗa kema kina faɗa sbd baki da hankali har wni cewa kike baki da aure, wllh tllh Allah ya temake ki zuciyata tayi sanyi da ace jiya na sameki da saina kwakkwaɗa miki mari, kuma dman daga nan wajen Umma da Baban ki zan wuce na wassafa musu abinda ke faruwa kinga sai su san wace irin tarbiyyar kike nunawa a gidanki don wnn tarbiyyar ba nasu bane...", a gigice Hajar ta zamo daga kan kujerar ta fashe da kuka tana yarfe hannu tace "na shiga uku don Allah Anty ki rufamin asiri..", Anty ta murtuke fuska tace "Ja can mara kunya fitsararriya waye zai rufa miki asirin bayan ke kina nan kina tona mana namu asirin", habawa ai a gigice Hajar ta riƙe legs din Anty tace "wayyo Allah dan Allah Anty kiyi haƙuri..", Anty tace "sakarmin ƙafa ko na mangareki, haƙurinki na banza haƙurinki na wofi ni ina ruwana da haƙurin ki, can dai kije ki riƙe carbi ki nemi gafarar Ubangiji dana mijinki don zunubin da kika kwasarwa kanki ba kaɗan bane", saida Anty ta yiwa Hajar wankin babban bargo, ciki da bai ta wanketa fess da sosa da sabulu, Hajar na shessheƙar kuka tace "Anty dan Allah kiyi haƙuri wllh na dena", Anty tace "Allah yasa iya abinda naji kike aikatawa babu wani wanda ban sani ba, toh a ydda kike masa mganar nan gatsal Allah yasa kina dafa masa abinci bare ta kai ga gaisuwa ko sannu da zuwa, ko kina yi ne...?", Hajar ta duƙar da kanta hawaye na zuba cheeks dinta, Anty tace "innalillahi wa'inna ilayhirraji'un abin naki is too much Hajar, tabarbarewar yayi yawa, gsky wnn mijin naki ma mai haƙuri ne wllh don ba ko wane namijin zaka yiwa wnn haukan ya ɗauka ba, da tini ya baki red card ya kaɗaki gidanku, kinga idan kika koma gida sai kije ki zauna dasu Sa'adatu ku ɗora daga inda kuka tsaya, kuma kinci baya a rayuwa don duk macen da tayi sagegeduwa aurenta ya mutu haka nan saddan wllh taci baya, ke bazaki duba liɗifin da Allah ya miki ba, kalli fa gidan da Allah ya baki mai yalwa da wadata, amma kin daddage kina shirin saka ƙafa kiyi fatali da damarki, wllh da jiya na sameki da saina bibbigeki..", Anty na gama faɗin haka ta ɗauki wayarta ta saka a jaka ta miƙe, tini Hajar da hannunta yayi jajir tsabar mutssukasan da tayi ta miƙe har lokacin kuka take tace "Anty dan Allah kiyi haƙuri ki rufamin asiri wllh na dena", Anty taja wani dogon tsaki tace "Abin naki yayi yawa Hajar, saidai kici ki kwanta ko sharar arziƙi ba kya yi a gidan naki ma...", Hajar tace "wllh ina yin aiki Anty ina shara...", katseta Anty tayi da faɗin "rufe min baki da murya sai kace tsanya, ƙarya kike ba kullum kike sharar ba", with serious note Anty tace "this is the first and the last da zan sake zuwa gidan ki na tarar da shirme, wawuya kawai" da haka ta nufi door tana tafiya da sauri, Hajar tabi bayanta tana kuka ta buɗe baki za tay magana knn Anty tace "karki kuskura ki fito, ni da ke munyi hannun riga duk ranar da kika nutsu kika gyara halinki ma shirya...", Anty tayi tafiyarta bayan ta rufe ƙofa, Hajar ta sulale ƙasa ta fashe da kuka, ai da an tsaya anji ta bakinta ai shima yanada laifi, me yasa zata ringa dafa masa abinci bayan yace ita ba matarsa bace and she will never be, me yasa idan ya taɓata baza tace haram ba tinda yace ita ba matarsa bace, me yasa zata ringa gaishesa bayan yace ita ba matarsa bace, tinda bai ɗauketa matsayin matarsa ba itama ba taga dalilin da yasa zata ɗaukesa matsayin miji ba. After 10mins ta tashi ta haura sama zuciyarta na zafi, Abincin ma da take mararin dafawa duk ya fice mata a rai.

★Nurain na fita direct warehouse dinsa ya wuce don kayansa da yayi order from China sunxo, shi dai yana tsaye sai shiga ake da kayan, gaba daya mind dinsa ma ba a wajen take ba ya lula wani planet din, moment din daren jiya ne ya ringa yawo a brain dinsa, har aka gama sauke kayan tass snn ya shiga ya duba, sai ƙarfe tara da rabi ya isa hospital kuma immediately ya fara attending patient dinsa, knocking door akay ya bada umarnin shigowa don shi ya zata next patient ne zai shigo sai yaga akasin hka, kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kai, Ruqayyah ta ƙarasa shigowa tace "good morning Dr", a takaice yace "morning what's up...?", tayi twinkling eyes dinta kafin ta ajiye masa wani envelope a gabansa, kallon envelope din yayi yace "this is not part of your work A Nurse", tace "yeah just to see you" da haka ta juya ta fita, few patient Nurain ya sake gani kafin yasa Haleema ta sallami ragowar don Surgery zai shiga next, walking gently Nurain ya shiga surgery room din, after ya saka hands gloves da nose mask ya tsaya a postion dinsa, Ruqayyah dake tsaya a right dinsa da tray na instruments a hannunta ta miƙa masa scalpel, Nurain ya amsa making sure bai taɓa hannunta ba, lokaci guda brain dinsa ta amsa, moment din da tin safe yake dakonsa ne ya shiga kai kamo a head dinsa, ya lumshe idonsa yana ƙoƙarin yakice abin amma he can't, the way she reacted and cried like a baby ne yafi tsaya masa, must part of it kuma her soft body and lips, her soft hair that's so good in brushing, ganin almost 5mins da basa scalpel bai fara aikin ba Khaleel yace "Dr", Nurain ya sauke ajiyar zuciya ya ajiye Scalpel din, yana kallon Khaleel yace "please call Dr Marwan instead" yana gama fadin haka ya kwaɓe nose mask din fuskarsa snn ya fige cap da ya rufe cikakkiyar sumarsa itama, saida ya cire hands gloves yayi disposing snn ya fita daga surgery room din, Ruqayyah tabi bayansa da kallo wondering me ya hanasa surgery din, wnn shine first time da taga ya fasa surgery, yana komawa office dinsa ya saka laptop dinsa a briefcase da sauran tarkacensa ya fita harabar hospital din, with speed yake driving zuwa gida, a daidai wani roundabout wayarsa ya fara ringing, yana dubawa yaga Mami ke kiransa, picking yayi ya kara a kunne gami da yin sallama, Mami ta amsa sallamar tasa tace "idan ka taso aiki kaxo gida", jimm yayi sai kuma yace "Sure Mami", Mami tace "Okay" da haka ta katse kiran, haka nan Nurain ya juya kan motar ya ɗebi hanyar gidansu, yana zuwa gidan ya shiga part din Mami, mgana sukay da Mami akan auren Noor da ya taho, ranar Thursday ma za a kawo lefe, daman tintini an kawo kuɗinta two years back, zuwa lokacin da ta gama karatu shi kuma mijin ya dawo daga abroad, main palour Nurain ya fito bayan sun gama mgna da Mami, Noor dake zaune palourn tana cin spicy Noodles tace "Yaya ina yini", ya amsa gaisuwar nata yana kallon part din Hajiya yace "Iron lady na nan..?", tace "yeah", part din Hajiya ya shiga da sallama, zaune ya tarar da ita kan rug ga jakar kayanta a gefe, tayi shigarta na asun da asun, Hajiya ta dubi mai aikin gidan dake tattare kwanukan abinci tace "yauwa ke Lauriyya idan kin fita da kwanukan nan sai ki biya kice da driver ya cigaba da wasshagare walle dinsa Usuman ya kaini...", mai aikin tace "tom Hajiya", Nurain ya haɗe gira yace "wane Uthman din..?", Hajiya tace "ga ka nan a tsaye ƙerere da kai nake..", yace "Ah ni gida zan tafi fa", tace "idan ka ajiyeni ka zarce gidan naka..", ajiyar zuciya Nurain ya sauke yana jin dama bai shigo ba, Hajiya tace "in taso mu tafi ne..?", girarsa a haɗe yace "Nope ina zuwa", da haka ya juya ya fita, room dinsa na gidan ya shiga, saida yayi wanka ya canza kaya snn ya fito, ya saka Noor ta zubo masa abinci yaci, saida yaje mosque yayi sallar la'asar kafin ya waiwayi Hajiya, tinda suka fito compound take zabga masa mitar ya shanyata kamar kayan wanki, shi dai baice mata uffan ba ya temaka mata ta shiga motar, with minimum speed yake driving har ya ajiye Hajiya a gidansu Farooq, ko shiga gidan be yi ba ya juya sbd he was so eager ya koma gida, gudunsa ya falfala a mota zuwa gida tinda ya ajiye iron lady, yana parking motar ya fito ya nufi entrance ya shiga ciki, da bibbiyu ya ringa haura stairs, kai tsaye ya buɗe ƙofar ɗakinta, ido huɗu sukay tayi sauri ta janye nata bayan zuciyarta ta buga, ajiye spoon din hannunta tayi ta miƙe afujajan ta shiga bathroom ta banke ƙofar tana turo baki, Nurain ya shafa kansa a bit relief after seeing her ya bar wajen, ƙarfe takwas na dare da few minutes Nurain ya dawo daga masallaci sallar isha'i, a palourn downstairs yayi zamansa bayan yayi powering TV, though ba kallon yake ba wayarsa yake dannawa, ƙarar rufe ƙofa yaji ya kalli stairs, kife wayarsa yayi kan kujera ya tashi ya koma dining section, a hankali Hajar take sakkowa daga stairs sai kace mai taka ƙaya, saida ta gama surveying palourn da ido snn ta wuce da sauri ta shiga kitchen, har wani ɗif ɗif zuciyarta ke mata, ta ajiye plate din da taci abinci ta buɗe fridge ta ɗauki bottle water, da bottle water din hannunta ta fito walking like a chameleon ta nufi stairs, babu tsammani kawai taga yayi blocking front dinta, ba tasan lokacin da bottle din hannunta ta faɗi ƙasa ba, sosai zuciyarta ta buga after their eye contact, tayi ƙoƙarin wucewa ta gefensa ya sake blocking dinta, sake ƙoƙarin wucewar tayi ta other side din nan ma ya hanata, a duk wnn abun kanta na ƙasa taƙi ta bari su haɗa ido, ya zuba mata piercing eyes dinsa yana mata wni irin kallo, ganin bazai matsa mata ba ta fara tafiya da baya tana komawa cikin palourn, duk step din da tayi shima sai yayi hakan yasa ta ringa tafiya da baya har ta kai bakin kujera bata sani ba, ƙugunta ya riƙe snn ya janyota jikinsa, ihu tayi shirin tsalawa yayi wani juyin masa da ita ya zauna kan kujerar ita kuma ta faɗa ƙirjinsa, tini ta fara ƙoƙarin miƙewa ƙarfi da yaji, da kyar ta iya cewa "meye haka ne ni ka sakeni...", kallonta ya ringa yi ganin sam taƙi bari su haɗa ido, yace "me yasa kike guduna young lady...?", haɗe fuska tayi perceiving his pure scent ba tace komai ba, ya sunkuya ya leƙa fuskarta, da sauri ta juyar da kanta gefe tana turo baki, Nurain yayi murmushin da ya tsaya iya lips yace "and why are you avoiding my eye contact..?", nan ma ta masa shiru tana sinne kai, yace "ko wnn ma no answer ya zama bashi..?", lokaci guda yayi wrapping dinta sosai ya kai lips dinsa kunnenta yace "i will not let yesterday's night question slide", wani irin runtse ido Hajar tayi tana jin tamkar ta nutse a wajen, after a while taji ya saketa ai kam ta ɗagasa da sauri, sai kace walƙiya ta haura sama harda tuntuɓe, Nurain ya bi bayanta da kallo murya ƙasan throat yace "Silly girl", wayarsa ce tayi ringing, yayi ajiyar zuciya ya ɗauki wayar ya ringa kallon numbern dake kiransa, tattare thick eyebrows dinsa yayi sai kuma yayi picking ya kara a kunne, muryar mace yaji tace "Aslm Dr, i hope you are doing well tin..." bai bari ta ƙarasa ba ya katse kiran, nan ta shiga kiransa babu ƙaƙƙautawa sai kace masifa, daga ƙarshe ma silencing wayar yayi ya tashi ya haura sama. Washe gari da safe Nurain na tsaye kitchen yana making coffee, buɗe ƙofar kitchen din akay har zata koma ganinsa sai kuma ta fasa ta shigo, ba tare da ta dubesa ba da sanyin murya tace "Ina kwana", lips dinta Nurain ya kalla da wani irin expression, ko dai kunnensa ne yaji ba daidai ba, juyawa yayi yana ƙarewa kitchen din kallo wai ko akwai wani a kitchen din, bai ga kowa a kitchen din ba alamar dai su kaɗai ne, Hajar bata damu da rashin amsawar da yayi ba ta ɗauki abinda zata ɗauka ta fita ta bar Nurain with different thoughts running in his mind......✍️
💛 HAJAR 💛

{70..}
Wajen ƙarfe goma Hajar ta sauko downstairs ta ɗauki sweeper da packer ta wuce room dinta, sai da ta share room dinta snn ta fito corridor shima ta share daga nan kuma tayi ƙasa, tass ta gyara ko ina yayi fess snn ta zuba turaren wuta a burners tabi kan hayaƙin da freshener mai sanyin ƙamshi, saida ta gama gyara gidan snn ta shiga kitchen ta dafawa kanta breakfast taci, shima kitchen din ta gyara sa bayan ta gama amfani dashi, room dinta ta koma ta kwanta gefen gado, sosai bayanta ya riƙe don aiki tayi tuƙuru mara algus, a hankali ta tashi ta ɗauki wayar aron daya bata ta koma ta kwanta, har wani fargaba ta ringa ji tana tsoron kiran Umma, da kyar dai tayi shahada ta kirata, har suka gama waya da Umma ba taji wani canji ba, Hajar ta sauke ajiyar zuciya tana jin daɗi har cikin ranta knn Anty bata gayawa Umma ba, bayan Hajar ta idar da sallahr Azahar ne ta sake sauka downstairs, direct kitchen ta wuce, tsaye tayi ta jingina da cabinet tana tunanin me zata dafa, at last dai ta ciro froze chicken daga freezer ta fara girkin, before 3 na rana ta gama girkin, wata irin aroma ce ta bulale girman kitchen din, wasu sabbin warmers ta ciro daga kwalinsu ta wanke ta zuba abincin, bisa kitchen island ta jere warmers din, ta juye ragowar abincin a plate da haka kuma ta kimtsa kitchen din ta fita. Sai ƙarfe biyar Nurain ya dawo, kana ganinsa kasan he is exhausted, ɓangarensa ya wuce ya ajiye briefcase din hannunsa, refreshing kansa yayi ya fito daga bathroom yana goge sumarsa da towel, yana gama shirya kansa cikin ƙananan kaya ya fito corridor yana jan rigarsa, kallon few seconds ya yiwa ƙofar ɗakinta kafin ya sauka downstairs, kitchen ya shiga zai dauki ko da fruits ne yaci kafin anjima ya wuce gida yaci solid food, idonsa akan warmers dake jere kan island ya fara sauka, ya ringa kallon warmers din kafin ya ƙarasa ya buɗe, aroman data daki hancinsa kaɗai ma ta isa ta ƙara masa yunwar dake cinsa, tini ya manta da wani batun fruits ya dauki plate ya zuba abincin daga haka ya bar kitchen din. ƙarfe takwas na dare Hajar ta fito daga wanka, tayi shafe shafenta ta fesa perfume mai sanyi kamshi, kaya ƴan sawai sawai ta saka don ba kwanciya za tayi ba akwai abinda za tayi a kitchen kafin ta kwanta, ta saka hula ta rufe baƙin gashinta ta fita a ɗakin, walking gently ta sauka downstairs ta shiga kitchen, tana riƙe da door handle ta ƙarewa kitchen din kallo, surely bai daɗe da fita ba don sosai taji pure scent dinsa, taɓe baki tayi bayan ta lura da coffee maker a jone, murmushi Hajar ta saki bayan ta buɗe warmers din abincin taga kaɗan ya rage, daman abincin ba wani yawa ne dashi ba, tayi kwafa har lokacin murmushin beyi fading a beautiful face dinta ba. Nurain na zaune a balcony yana waya da Mr Lee from China, suna gama wayar Nurain ya tashi ya shiga ciki, ba tare da ya cire airpod din dake right ear dinsa da ya gama wayar ba ya buɗe ƙofar kitchen, coffee dinsa ya tsiyaye a mug ya ɗauka zai fice a kitchen din sai kuma ya juyo jin motsi, Hajar ce ta fito daga store da roba a hannunta, da sauri ta saukar da kanta ta ajiye robar kan cabinet, a hankali tace "ina yini", Nurain ya dawo da baya ya jingina da cabinet ya ringa kallonta without blinking, lokaci guda ya cire airpod dake kunnensa still staring at her, tana ɗago kanta sukay ido huɗu, turo baki tayi ta saukar da kanta, knife ta ɗauka ta fara feraye dankalin da ta debo, da gefen ido ta fakaici kallonsa kawai taji wata azaba a hannunta, ba shiri ta saki wuƙar gami da yin ƴar ƙara, da sauri Nurain ya ajiye mug din hannunsa ya isa inda take, riƙe hannun da take yarfewa yayi yana so yaga inda ta yanke, ƙoƙarin amshe hannun ta ringa yi, lokaci guda ya saki hannun nata ya rutsa flat tummy dinta ya ɗorata kan cabinet, ya riƙe hannunta with care, tamkar robot da aka dannawa remote haka ta ƙame, ta ringa kallonsa without blinking, wnn shine karo na farko da tayi masa wnn kallon, yana ɗago kansa sukay ido hudu, suka ringa kallon juna after few seconds Hajar ta janye idonta, zamowa tayi zata sauka yayi saurin haɗe goshinsu waje ɗaya, tayi saurin runtse idonta, ya sauke ajiyar zuciya yace "Please be more careful..." da haka ya janye goshinsa a nata ya dauki mug din coffee da airpod dinsa ya fita, saida Hajar taji ƙarar rufe ƙofa snn ta samu kwarin guiwar buɗe idonta da ta lumshe, numfashi ta sauke tana turo baki ta diro ƙasa, ta duba finger dinta inda ta yanke taga kaɗan ne ma yankan, ko jini babu sosai sai wnda ya tsattsafo yanxu, ta isa gaban sink ta buɗe tap ta wanke ciwon, kasa yin aikin tayi kawai ta buɗe ƙofa ta fita, tana zuwa room dinta ta saka kayan bacci tabi lafiyar gado, uhmm saidai tinda ta kwanta ta kasa baccin juyi kawai take tana naɗewa waje ɗaya tamkar ƙadondoniya, lokaci zuwa lokaci take turo baki ta juya lulu eyes dinta. Ranar Thursday da yamma Nurain ya isa gidansu, yana shiga main palour ya tarar da baƙi, both his paternal and maternal Aunties na zaune palourn da kuma close friends din Maminsa, da ladabi Nurain ya gaishe da mutanen palourn, Mama Mardiyya ƙanwar Abba tace "Uthman ya iyali...?", yace "Alhmdllh" yana shafa kansa, da haka ya tashi ya wuce part din Mami, Sakeena ya tarar a palour tana sealing envelope da aka cika da sabbin kuɗi, Nurain ya ƙarasa palourn yace "wani abun ake ne naga ƴan uwa..?", Sakeena tace "kai komai baka sani ba, yau fa za a kawo lefen Noory", ya waro ido yace "Oh right... Mami ta gayamin", Mami ta fito daga bedroom dinta da 2 notes na kudi a hannunta ta miƙawa Sakeena tace "suma kisa a envelope", Sakeena ta amshi kuɗin tace "Ohk", bayan Nurain sun gaisa da Mami yace "Abba na nan...?", Mami tace "Nope yaje Abuja sai 7 nake jin zai dawo", Nurain yace "Alright". wajen ƙarfe biyar masu kawo lefen Noor suka iso, aka tarbesu da girmamawa snn aka musu shimfiɗa ta fuska da kuma ta tabarma, da suka tashi tafiya ma aka bisu da abin arziƙi. Da daddare wajen ƙarfe takwas Mami na zaune main palour tare da Sakeena, ga uban kayan lefen da aka kawo zube kan Carpet, Sakeena tace "Our Mami baki ga kayan ba kona ɗaɗɗaga miki...?", Mami tace "No dear zan duba later", Sakeena tace "Tom" ta cigaba da duba box din kayan shafa, Nurain ya fito daga great room din Abba, paper din hannunsa ya miƙawa Mami snn ya zauna kan Sofa, Mami ta kalli papern sai kuma tace "i don't understand, wane calculation ne wnn..?", Nurain yace "kayan da nace miki zasu zo to nasu ne...", Mami tace "Masha Allah, Allah yasa rabo ne yasa albarka", yace "Ameen", Mami ta miƙawa Sakeena papern ta tashi ta shiga great room din Abba don daman so take suyi mgana dashi akan bikin, buɗe baki Sakeena tayi tace "Brother wane irin houses zaka siyamin a Villa..?", ya waro ido yace "irin wnda kike so", Sakeena tayi murmushi tace "Toh wai me kake a hospital?", straight forward yace "Help", Sakeena ta ajiye papern kan kujera tace "saidai hakan", ta cigaba da duba kayan da take, can after few minutes tace "Yauwa bani kuɗin kayan Hajar ma", Nurain ya dubeta ya ɗage gira yace "kayan me?", tace "Outfits da zata saka a biki mna", yace "Outfits kuma is she the bride?", tace "yeah she's your bride wcca kake ma favor" ta ƙarashe tana galla masa harara tace "kaga babu enough time saura 2weeks", yace "2week sukay fixing..?", tace "yeah", yace "ohh account digit", ta gaya masa account digit dinta, bayan ya tura mata ya ajiye wayar yace "done", wayarta ta duba bayan alert din ya shigo, ganin kuɗin daya turo tace "bafa 20set za a dinka ba", yace "sunyi kaɗan ne..?", tace "No sunyi yawa sosai zan maka refunding half", yace "no need", a lokacin Mami ta fito tana kallon Nurain tace "Abba yace zaka wuce China..?", Nurain yace "yeah..", Mami tace "when..?", yace "insha Allah on Monday", Mami tace "hope ba zaka daɗe ba", yace "Sure 10days zanyi", Mami tace "Alright... sai ka kawo Hajar nan..", yace "Tom". Before 10 Nurain ya koma gida, sharp sharp yayi wanka ya saka white pajamas don so yake ya sauka downstairs ya zuba abinci, a gidansu yana ganin ana ci yaƙi ci don ynxu sosai taste din abincinta ya kama masa baki, yana buttoning rigar jikinsa ya sauko downstairs ya shiga kitchen, tini ya ɗauki plate ya fara zuba abincin da yau kwana uku knn sai ya tarar a ajiye, yana gama zuba snow rice ya buɗe warmer din stew, yana fara zuba stew din aka buɗe ƙofa, daskarewa yayi a yacca yake da serving spoon a hannu, Hajar tafi seconds biyar tana kallonsa sai kuma ta taɓe baki ta wuce ta ɗauki ruwa, har ta nufi door zata fita sai kuma ta juyo, wata shegiyar dariya ce ta taho mata ganin ya kasa cigaba da zuba abincin sai jujjuya serving spoon din hannunsa yake, tayi gyaran murya tace "kai ma kana tayasu ci knn...?", haɗe gira yayi yace "what are you talking about...?", Hajar ta fashe da dariya tace "Aljanun kitchen fa na ajiyewa shine ka cinye musu..", Nurain bai san lokacin da ya ajiye serving spoon din ba yace "yah... i was only helping them sai an zuba a plate suke ci ai idan a warmer ne baza....", shiru yayi jin ta tuntsire da dariya, ita za a yiwa wayo bayan ita take wanke plate din da yaci, kallonta yake without blinking har tana riƙe ciki, Nurain yayi blushing ya shafa kansa, ya harɗe hannu yana kallonta, saida ta more dariyarta snn ta ɗago tace "wayyoh Allahna", ganin yana tahowa kusa da ita tayi sauri ta buɗe ƙofar kitchen din ta fita, saidai dariyar da take tayi weakening dinta tasa kafin ta hau stairs yayi nasarar fixgota, ta tsala ihu tace "i know your were just helping them, daman su suke cin jagwalgwalo kai baka ci", sakinta yayi ta haura sama da sauri, yabi bayanta da kallo sai kuma ya juya ya koma kitchen yana blushing, stew din ya ƙarasa zubawa ya ɗauki ruwa da lemo ya fita, a palour ma yayi zamansa yaci abincin, sha biyu da rabi na dare Nurain ya rufe laptop din da yake operating, ya tashi daga kan gadon bayan ya zura room slippers ya fita palour, yayi sliding door ya fita daga ɓangaren nasa, a hankali ya murɗa ƙofar ɗakinta ya shiga walking gently without making any sound, kwance ya ganta kan gado ta rufe da duvet, hasken ɗakin ya rage yabar dim, ya matsa gaban gadon yana kallonta da ɗan hasken ɗakin, a hankali ya kwanta daga bayanta ya ɗora kansa a pillow dinta, yana ɗaga duvet Hajar ta farka don daman baccin nata beyi nisa ba, ganin zata miƙe yayi saurin rumgumota ta baya, scent dinsa da ta shaƙa ne yasa taji relief amma kuma saita fara ƙoƙarin fixge kanta, da taga dai bazata iya kwacewa ba ta marairaice tace "please let go off me this is not proper fa..", ya sake haɗata da ƙirjinsa har tana jin bugun zuciyarsa, lumshe idonta tayi jin saukar numfashinsa a gefen wuyanta tace "dan Allah let me go..", murya can ƙasa yace "No.. sai kin faɗi wa kike yima dariya ɗaxu", turo baki tayi tace "nifa ba da kai nake ba, Aljanun ne suke bani dariya..", tummy dinta ya riƙe ya mirginasu suka koma suna fuskantar juna yace "really.. Aljanun kike yima dariya..?", da sauri ta runtse idonta ta gyaɗa kai don idan tace zata buɗe baki tayi mgana toh tabbas dariya ce zata biyo baya, a bazata taji ya haɗe goshinsu waje guda sai kuma yayi brushing lips dinsu, yace "lokacin da kike dariya ai buɗe baki kikay so now answer me bana son nodding talk Silly girl", tini zuciyarta ya fara racing, ta daddage tana matsawa baya don ta raba goshinta da nasa, da sauri ya tallafo kanta ya hanata raba goshin nasu, tana buɗe baki da shirin tsala masa ihu ya rufe bakin da nasa, this time around ba iya brushing lips dinsu yayi ba he sucked her small lips deeply, tini Hajar ta fashe da kuka jikinta har na rawa tace "Ummana wayyo Ummana...", Nurain yayi murmushi mai sauti yana kallon lips din nata da bai gaji da sucking ba, yace "Shhh in ana dariya ba a kuka fa", ba tasan lokacin da ta shiga banka masa harara ba tace "Ni ka sakeni dan Allah, ni fa ba kai nake yiwa dariya ba", yace "Ohh really su Aljanun da kike jin tsoro kike ma dariya knn..?", da sauri ta gyaɗa masa kai, ehen ai kam da kiss din da ya matuƙar firgitata ya gigitata ya mata tinin ba nodding saidai tayi mgana, yana sakar mata lips ta fashe masa da kuka harda shessheƙa, garin riƙeta sbd fincikewar da take ne ya kasa controlling kansa, abu daga tsokana sai kuma ya fita daga sahun tsokana har ya wuce gejin kiss, firgitar da tayi yafi na ranar nan, don wnn karon anje inda ba'a aje ba ranar nan, da kyar ta samu chance din da ta kwala uban ihu sai kuma ta ja numfashi tamkar zata shiɗe tana kiran Ummanta, sai a lokacin Nurain ya sarara mata, gefenta ya kwanta yana sauke nannauyan ajiyar zuciya, Hajar ta ja rigar baccinta data koma wuya tana shessheƙa, daman ba a maganar bra don ita cilli akay da ita may be ma ta kai gaban mirror, gaba ɗaya jikinta rawa yake tamkar an jona mata shoking, yau ita taga jalala da ƙarshen tashin hankali, hantsilowa tayi daga gadon ta kwanta kan carpet ta ringa rusa kuka kamar ranta zai fita, Nurain ya lumshe idonsa yana jinta, idan yace zai rarrasheta to tabbas ba rarrashi zai yi ba wani kukan zai sakata ko kuma ma ya sumar da ita tinda ya lura matsoraciya ce, after 30mins yaji ta dena kukan saidai shessheƙa time to time, da kyar ya tashi zaune snn yayi buttoning rigarsa, a hankali ya sauka daga gadon ya duƙa gabanta, ya rage murya yace "Hajar... Hajar... Hajar", jin shiru bata amsa ba ya ɗauketa ya mayar da ita gado ya rufa mata duvet, daga haka ya fice walking slowly don ya kunnowa kansa ruwa. Washe gari Hajar tayi gurgumi a ɗaki taƙi fita ko ina, daga taji motsi saita kyalla bathroom, tsoron encounter dashi take har cikin zuciyarta, gashi tana so ta sauka kitchen don yunwa take ji amma kuma bazata taɓa iya fita ba, tin safe ruwa kawai ta ringa ɗurawa kanta, wajen ƙarfe biyu na rana ta miƙe a hankali ta matsa gaban window, curtain din ta yaye ta leƙa waje tana kallon compound, parking space ta kalla taga babu motarsa guda ɗaya, hakan ne ya bata hope din baya gidan knn, ai da sauri ta nufi door ta buɗe ta fita, sharp sharp tayi frying egg ta tafasa black tea, jikinta har wani ɓari yake don tayi sauri ta gama ta fita, haka ta shanye shayin da zafinsa yana ƙona mata baki, tana gamawa ta buɗe ƙofa ta fita, a lokacin shima ya shigo palourn da leda a hannunsa, sanye yake da manyan kaya farare tass sbd yau Friday kuma daga mosque ya dawo, Hajar ji tayi kamar zuciyarta ta koma ciki ganinsa, da sauri ta koma kitchen don hawa saman ma ya mata nisa, ta yarfe hannu kamar zata fashe da kuka tace "na shiga uku", jin an murɗa handle ta koma da baya tana zaro ido, sai taji dama ta iya irin magic din nan na cikin films din da Noor take kallo, da babu abinda zai hana ynxu tayi applying dinsa a wnn taƙin ta ɓace ɓat ta huta, sulalewa tayi ƙasa after realizing tabbas shine ta haɗe kanta da guiwa, Nurain ya ajiye ledan fruit da ya shigo dashi, ya ringa kallonta kafin ya fara tafiya gently towards her, ya duƙa gabanta yace "yau ba gaisuwa?"......✍️
💛 HAJAR 💛

{71..}
Hajar dai taƙi tace masa komai kanta na bisa guiwarta, after a while yace "ko nima na zama masquerade ne...?", turo baki tayi ta gyaɗa kai, Nurain ya waro ido yace "why...? me yasa na zama masquerade all of a sudden..?", ta masa shiru ba amsa, yasa hannu ya ɗago kanta, suna haɗa ido tayi sauri ta mayar da kanta, Nurain yayi blushing ya shafa kansa ya miƙe yace "Alright i know daga yesterday's night na zama masquerade din nan", ta sake takure kanta tana jin dama ƙasa ta tsage ta shige kawai, wai daman yana sane da abun be manta ba, yace "Hajar", ba ta ɗago kanta ba amma kuma ta amsa a hankali, yace "i bought some fruit, make a fruit salad", ta gyaɗa masa kai, after few seconds Nurain ya fita daga kitchen din, saida Hajar ta tabbatar ya fita snn ta iya ɗago kanta ta tashi tsaye, ledan da ya ajiye kan Island ta buɗe ta ringa kallon fresh fruit dake ciki, gaba daya fruit din ta wanke snn ta zuba a fridge bayan ta ɗebi wnda za tayi salad din dasu, within few minutes ta gama haɗa yummy fruit salad din wnda ta jefa guda gudan green and purple grapes a ciki, a tsadadden transparent bowl ta juye ta saka a fridge, daga haka ta bar kitchen din ta koma room dinta, nail cutter ta ɗauka ta zauna tana yanke farcenta da bai wani fito sosai ba, tana gama yanke farcen ta tashi ta shiga bathroom ta wanke hannunta ta dawo ta zauna gefen gado, tana zama aka buɗe door, ta san dole shine don haka ta saukar da kanta taƙi kallon door din, ga kuma pure men scent dinsa da already ya cika room din shima ya tabbatar mata da shi din ne, daga bakin door ya tsaya yana kallonta yace "kin gama making fruit salad din ne...?", a hankali ta gyaɗa kai tana wasa da slim fingers dinta, yace "Ohk then bring it to my room" bai jira amsarta ba ya juya ya fita, Hajar ta ɗago kanta ta kalli ƙofar sai kuma ta turo baki, bata gane ta kai masa room dinsa ba, saida ta gama muhawara da zuciyarta snn ta tashi walking gently ta fita, downstairs ta sauka ta shiga kitchen, a tray ta ɗauro bowl din fruit salad din wnda yayi sanyi ƙau, ta saka spoon kan trayn bayan ta rufe bowl din da marufinsa, walking gently ta fita daga kitchen ta haura sama, tsaye tayi bakin door din part dinsa without making any move, da kyar tayi shahadar knocking a hankali, muryarsa taji yace "Come in", tayi ajiyar zuciya ta shiga kanta a ƙasa, zaune yake kan one of the exclusive Sofas dake palourn, yana kallon monitor din laptop dinsa da ya haska hoton posterior view of the heart, kallo ɗaya Hajar ta masa tayi saurin ɗauke kanta tayi sallama, Nurain ya ɗago daga kallon monitor ya dubeta ya amsa sallamar da tayi, ta ƙaraso ta ajiye trayn saman Centre table dake gabansa ta juya zata fita, da sauri ya riƙo hannunta ya janyota ta zauna kan kujerar daga gefensa, yace "are you eager to leave..?", da sauri ta gyaɗa kai, slight smirk yayi yace "Ke!! sai kin jama kanki ciwo ko..? kina ta wani nodding head sai kace lizard.. ko sai na maimaita abinda na masa last night zai buɗe..?" ya ƙarashe yana kallon lips dinta, da sauri ta girgiza kai tana turo baki tace "Ni fa aiki nake a kitchen", yace "Oh i thought sai na buɗesa za kiyi mgana ai", ɓamɓare hannunta da ya riƙe tayi ta miƙe ta nufi door, Nurain yabi body figure dinta da kallo har ta fice, ya dauki fruit salad din ya fara sha, har wani lumshe ido yake sbd yadda dadin ya shigesa. Kitchen Hajar ta koma ta shiga dafa abinci, before 4 ta gama girkin ta ɗebi nata ta bar masa nasa a warmers ta fita. Washe gari wajen ƙarfe sha ɗaya Nurain ya dawo daga unguwar da yaje, thick eyebrows dinsa a haɗe alamar dai ransa ya ɗan ɓaci, tafiyar da zaiyi ranar Monday ashe jirgin ba ta Kano zai tashi ba tacan Abuja ne, don haka yau Saturday ya kamata ya wuce Abuja ranar Sunday yayi clearing komai a can Abujan kafin ranar Monday da jirginsu zai ɗaga zuwa China, kafin ma ya dawo gida yayi booking flight ticket zuwa Abujan, sama ya haura ya murɗa ƙofar room dinta, surveying ɗakin yayi da ido yaga bata nan, rufe kofar yayi ya wuce part dinsa kawai, after like 20mins ya fito in a hurry ya sauka ƙasa, zai buɗe kofar kitchen knn aka rigasa ta ciki, da sauri ta fito ta basa hanya sai kuma ta dan yi bowing tace "ina kwana..", bata taɓa tsammanin zai amsa mata ba sai gashi ya amsa, wucewa tayi zata haura sama yace "Hajar", ta juyo tare da amsawa a hankali, yana kallonta da kyau yace "kije ki haɗa kayanki zamu wuce gidan Mami", ba tace komai ba ta ɗan kallesa, yace "belongings naki da za kiyi amfani dashi na two weeks", tace "tom" da haka ta juya ta fara hawa stairs, Nurain ya lumshe ido yana sauke ajiyar zuciya sai kuma ya shiga kitchen. haka nan Hajar ta haɗa duk wani abu da tasan zata buƙata a box, kayan sawa har cikin tsarabar Hajiya da ta Mami ta kwashi wasu, tana cikin zuge box din ya shigo, ganin tana fama da zip ya ƙaraso ya zuge mata yace "kin gama packing komai da zaki buƙata..?", tace "Eh", yace "Alright ki fita compound" da haka ya ɗauki box din nata ya fita, Hajar ta ɗauki handbag data saka waya da wasu ƴan tarkacen nata, bayan ta saka well ironed hijab da ta fitar ta nufi ƙofa, saida Nurain ya kashe duk wasu electric appliances na gidan ya rufe ko ina snn ya fito compound hannunsa riƙe da car key, wajen mai gadi ya wuce, da sauri Inuwa ya miƙe ya russuna yana gaishesa, Nurain yace "yawwa mal Inuwa yaushe zaka tafi gidan...?", Inuwa yace "insha Allah gobe da sassafe zan ɗau hanya", Nurain yace "Okay" ya ciro kuɗi masu kauri sosai daga aljihunsa ya basa, hannun bibbiyu Inuwa yasa gami da russunawa can ƙasa ya amshi kudin yace "Allah ya saka da alheri", Nurain yayi murmushi yace "toh Allah ya tsare hanya" bai jira mai zaice ba ya wuce parking space yana kallon Hajar dake tsaye jikin mota tana jiransa, Inuwa dai ya saki baki yana kallon uban kuɗin, jiya fa ya basa Albashinsa yau ma gashi ya ƙara masa wasu, ga kuma kayan abincin da ya basa yace ya kai gida, shiyasa Garba yace aiki gangariya ya samo masa, a gsky kam yayi sa'ar uban gida na gari. Hajar ta bude front seat ta shiga bayan shima ya shiga driver seat, saida motar ta gama warming snn ya fara driving slowly yabar harabar gidan, ko da suka fita main road Hajar tayi mamakin da ba taga yana fella gudu ba, da minimum speed yake jan motar, tinda suka baro gida ya kunna qira'ar Sheikh Abdul Baseet don haka har suka je gidan Abba babu wnda yace uffan, yana gama parking ya buɗe motar ya fita, Hajar ma ta buɗe ta fito tabi bayansa zuwa cikin gidan. Mami tace a kai box din kayan Hajar zuwa room din data zauna lokacin da bata da lfy amma ina tini Noor tasa mai aiki ta kai box din ɗakinta don tace anan zata sauka, Bayan sallahr magrib Nurain na zaune palourn Mami, Mami ta fito daga bedroom dinta tana kallonsa tace "sai yaushe zaka wuce Abujan ba flights din dare bane..?", yace "yeah ynxu zan wuce", Mami tace "Ohk kar dai kayi missing flight", yace "kafin time zan isa Airport insha Allah", Mami tace "ka tafi da warm sweater da Jacket don ynxu China wnn snow din ake musu", yace "Tom Our Mami", tace "ka ringa shafa mentholated cream kar sanyi ya kamaka Nurain kasan dai yadda mura yake maka", yace "Tom Mami". Hajar na zaune kan prayer mat bayan ta idar da sallahr magrib a room din Noor, Noor ta shigo tana kallon Hajar tace "kixo inji Yaya..", Hajar tace "tom" ta miƙe tabi bayan Noor suka fita main palour, Hajar ta ringa bin palourn da kallo don bata gansa ba, Noor tace "meet him outside", Noor na gama fadin haka ta wuce can room din da mai mata gyaran jiki ke jiranta, a hankali Hajar ta fara tafiya har ta fita balcony, Tinda ta fito bai ɗauke idonsa akanta ba, yana zaune cikin motarsa ya bar door a buɗe snn ma legs dinsa ma basa cikin motar kawai dai zama yayi a driver seat din, walking gently yaga ta nufi wajen motar, kallonta yake har ta ƙaraso bakin motar, ta tsaya daga jikin motar without saying anything, after the silent of about 1mins Nurain yayi ajiyar zuciya yace "you will be staying here for the meantime...", ta ɗan kallesa da wutsiyar ido taga ita yake kallo, a hankali ta gyaɗa kai, ya waro ido yace "ko saina buɗe bakin za kiyi mgana", ta sunkuyar da kanta tana wasa da ƙasan hijab tace "Tom", yace "Good... if you need anything don't hesitate to ask Mami", tace "Tom", envelope da ya ajiye kan dashboard ya ɗauka ya fito daga motar, ya tsaya daf da ita leaning against her, tini Hajar ta sake mannewa da jikin motar perceiving his pure scent, hannunta ya kamo ya damƙa mata envelope din yace "if you need anything", sai a lokacin Hajar taji wani iri a zuciyarta tana so ta fahimci wani abu, bata fito daga duniyar tunani ba ya ɗan janyota kamar zaiyi hugging dinta, ya sunkuyo a saitin kunnenta yace "be good Hajar", sosai mganarsa tayi hitting eardrum dinta tare da kai electric shock brain dinta, ba tasan lokacin da ta lumshe idonta ba tana jin breathing dinsa, After a while ya matsa daga kusa da ita yace "you can go", ko 1sec bata ƙara ba ta wuce ta bar wajen, Nurain yabi bayanta da kallo har ta shiga ciki, rubbing face dinsa yayi da palm snn ya shiga motar. Sosai Hajar taji daɗin zaman gidan, sosai take comfortable bbu abinda ta nema ta rasa, yau kwananta na shida knn a gidan, shirye shiryen bikin Noor ake a gidan ka'in da Na'in, ɗaiɗaikun ranaku ne Sakeena bata zuwa su fita tare da Mami, ita dai Hajar tana kallon ikon Allah taga ya masu kudi suke nasu bikin, ita dai tasan an ɓatar da kuɗi wnda zata iya kiransu da mazaje. Da yamma Hajar ta gama cin abincin da ba taci da rana ba sai ynxu, da plate a hannunta ta fito zata kai kitchen, turus tayi ganin baƙi a palour, Anty Zulaihah ce sai Khausar wnda zuwansu knn, Sakeena dake zaune palourn tin bayan dawowarsu da Mami daga kasuwa ce tare dasu, Hajar ta ƙarasa cikin palourn ta duƙa ta gaida Anty Zulaihah da ladabi, Anty Zulaihah na kallonta da kyau tace "lfy lou alhmdllh" sai kuma ta dubi Sakeena tace "Matar Nurain ce ko...?", Sakeena ta gyaɗa kai tace "Eh Anty", sai a lokacin Khausar dake danna waya ta dubi Hajar sai kuma ta ɗauke kanta, though ta taɓa ganinta sau ɗaya ranar da aka kawota amma kuma bata san haka take ba, Hajar ta miƙe ta wuce kitchen da plate din. Noor ta sauko daga upstairs, hugging juna sukay da Khausar, Noor ta gaida Anty din ta ta da ladabi, bayan sun gaisa Anty Zulaihah ta wuce part din Mami, Noor na kallon Khausar tace "banga box naki ba hajiyata..", Khausar ta mata nuni da jakar kayanta tace "gata can ai nazo knn", room din Noor suka wuce tare Khausar na gaya mata ydda suke tsarin cocktail party da friends dinsu, Noor ta zuge closet ta saka jakar Khausar ciki, Khausar tace "ki saka min a ɗaya side din mna nafi more aware and comfortable with it", Noor tace "Oh box din Hajar ne a wajen", Khausar tace "Ohk... wai waccar farar da ta shiga kitchen itace matar Ya Nurain..?", Noor tace "dman baki santa ba..?", Khausar tace "Nope kawai dai ban ganeta ba", a lokacin Hajar ta shigo Khausar ta bita da kallo, Noor tace "Ehmm Hajar meet my sisto Khausar..", Hajar tace "sannu ko", Khausar ta miƙe daga gefen gadon da ta zauna ta kalli Hajar tace "Hi" sai kuma ta nufi door tana cewa "zanje mu gaisa da Mami". after 10mins Khausar ta dawo, Hajar ganin suna firarsu wcca bata shafeta ba ta dubi Noor tace "zanje palour nayi kallo sai kin taho", Noor tace "Ohk". Da daddare Noor ta zubo musu abinci su uku, da farko Khausar cewa tayi baza taci ba sai kuma ta tashi ta fita sai gata ta dawo da plate ta ɗebi nata ta koma gefe tana ci, Noor ta bita da kallo tace "Au you like to eat alone", Khausar tace "yeah you know bana cin abinci sama da mutum biyu", Hajar ce ta tattara plate din da suka gama cin abinci ta fita dasu, tana dawowa ta shiga bathroom don yin wanka cause da wuri take so ta kwanta, Khausar tace "Noor amma the bed will not be enough", Noor tace "sai kace wasu elephants even 4 people can sleep on this bed comfortably", Khausar ba ta sake cewa komai ba ta haye gado bayan ta saka nities dinta, wani irin bararrajewa tayi ta kwashe rabi da quartern gadon, Hajar na fitowa wanka ta bude box dinta ta dauki kayan bcci ta saka, kallon position din da take kwanciya tayi taga Khausar tayi ɗai ɗai tana latsa waya, Noor tace "Khausar matsa zata kwanta ne fa", Khausar ta matsa kaɗan, Noor ta tashi daga position dinta tace "Hajar zo ki kwanta anan", Hajar tace "A'a ku kwanta kawai" da haka ta buɗe closet ta ciro wani blanket da ta gani tayi kwanciyarta kan carpet, babu yacca Noor ba tayi da ita ba akan ta tashi daga ƙasa amma tace she is Okay, Khausar tace "Omo she said it's okay please let her be.. kin san wani yafi son ƙasan", Noor dai ta ɗan haɗe gira ta koma ta zauna, ba ta son wnn acting din da Khausar take gsky, Khausar tace "The bride to be nifa banga Ya Nurain ba, ɗaxu ma da zanje gaida Mami na biya na gaidashi a room dinsa baya nan", speaking with a repartee Noor tace "ohh he is not around yana China", Khausar tace "Ohk when is he coming back...?", Noor tace "i don't think zai ƙara 1week bai dawo ba", Hajar dake kwance kan carpet duk tana jin conversation din nasu, ita sai ynxu ma tasan tafiya yayi ashe baya ƙasar ma, shiyasa bata ganinsa knn. washe gari Hajar ita kaɗai ce a gidan, da wuri Mami suka fita tare da Sakeena da alama dai so suke su gama shirye shirye kafin lokacin bikin ya shigo, Noor ma sun fita tare da Khausar ba dai tasan inda zasu ba, duk da Noor tace tazo suje tare amma taƙi sbd ydda Khausar ta nuna bata so a tafi da ita, ita kam daman ba son fitar take ba. Hajar ta shiga ɓangaren Mami don yi mata sannu da zuwa kamar yadda ta saba, bayan ta musu sannu da zuwan Mami tace "why are you all alone at home baki bi su Noor ba..?", Hajar tace "Eh", Mami tace "Okay.. je ki kawo mna abinci", Hajar tace "tom" da haka ta tashi ta fita, Sakeena ta fito daga small room din Mami inda suke ajiye kayan da suka siyo, wayar Mami kare a kunnenta tace "You catched cold brother", from the other side Nurain da muryansa ta dashe yace "yeah", don yana isa China wani muku mukun sanyi ake, daga airport kafin ya isa masaukinsa anan yayi catching cold, sosai mura ya kamasa ya riƙe masa murya shiyasa bai kira kowa ba, though ya yiwa Mami message yace mata ya sauka lfy, sai ynxun ne da muryan nasa ya bude ya samu ya kira, Sakeena ta miƙawa Mami wayar tace "Nurain ne", Mami na jin muryansa ta haɗe gira tace "ba kayi abinda nace ba ko..?", Nurain ya ja pointed nose dinsa don mganar ya fito sosai yace "No Mother wollah nayi abinda kika ce, tin a plane na saka Jacket dina, akwai sanyi ne sosai Mami", Mami tace "Ohk", suna gama wayar Mami ta katse kiran, saida Hajar ta kawowa Mami abincin da lemo da ruwa snn ta koma room din Noor, wayarta da ta ajiye kan mirror ce tayi haske, tana ɗaukan wayar taga 4 missed calls da number wcca ba ta ƙasar nan ba, Hajar ta ringa kallon numbern kafin ta ajiye wayar ta shiga bathroom don yin alwala. Da daddare wajen ƙarfe tara Hajar na durƙushe gaban box dinta zata ciro kayan bacci da zata saka, Khausar na kwance kan bed tayi rub da ciki tana latsa waya, door aka bude Noor ta shigo ta miƙawa Hajar wayarta tace "Yaya ne", Hajar ta ringa kallon wayar bata amsa ba, Khausar ta taso ta amshe wayar a hannun Noor tace "bari dman za muyi mgana dashi" da haka ta kara wayar a kunnenta ta fita, Noor ta bita da kallo hakama Hajar, Noor ta juya ta fita itama, Hajar ta ƙarasa ciro kayan baccinta ta saka, daga nan tayi kwanciyarta kan carpet ta rufe legs dinta da blanket, bata daɗe da kwanciya ba Noor ta sake shigowa, a hankali Noor tayi tapping dinta tace "Hajar har kinyi bacci", Hajar ta buɗe idonta sai kuma ta miƙe zaune, Noor ta miƙa mata wayarta tace "ga Yaya", Hajar na amsar wayar Noor ta tashi ta fita, a hankali ta kara wayar a kunnenta tayi shiru ba tace komai ba, after a while jin shiru ta ciro wayar tana kallon screen din taga seconds sai tafiya suke alamar dai bai katse kiran ba, turo baki tayi ta mayar kunne, ajiyar zuciya taji ya sauke sai kuma yace "Hajar", ji tayi muryansa ya canza amma still tasan shine, ta haɗe kanta da guiwa da sanyin murya tace "ina yini"……✍️

Please Masu neman complete din Hajar toh ku dena whalar da kanku don bbu complete ynxu nake rubutashi, snn kuma a wajena Ni Nafeesah Yusuf Nagoda (Feenerh feeche) kawai zaki samu book din don nawa ne mallakina.

💛 HAJAR 💛

{72..}
A hankali Hajar ta daga kanta jin an buɗe door, ido huɗu sukay da Khausar wacca ta shigo, Khausar ta haye gado ta cigaba da danna wayarta, Nurain yace "ina wayan dana ara miki ba kya picking call ko..?", Hajar ta girgiza kai kamar yana kallonta tace "A'a ban gani ba", yace "ohh All is well right..?", ta gyaɗa kai ba tace komai ba, ai kam kamar yasan me tayi ya tsuke ido yace "ohh nodding head kikay ba zaki yi mgana ba, idan na dawo fa bxan buɗesa ta sauƙi ba, gwara ma kiyi mgana yarinya", Hajar ta kifa kanta a knees dinta tace "Ni fa bacci zanyi..", wani dogon tsaki Khausar taja ta tashi zaune ta jingina da allon gado don tana jiyo mganarsa sosai sbd the room was so silent, Hajar dai ko kallonta ba tayi ba waya na kare kunnenta, Nurain ya ja nose dinsa yace "hmm your lips are aching surely i must brush them when am back..", wani irin turo baki tayi tace "Allah kuwa Ni bacci zanyi", yayi slight smirk yace "nayi gluing eyes dinki ne", kawai dai latsa waya Khausar take amma all her mind yana kan Hajar ne, lokaci guda ta tashi daga kan gadon taje ta kashe fitila, sosai room din yayi duhu sai hasken wayar Khausar da take latsawa, Nurain yayi ajiyar zuciya yace "you know what Hajar..?", ba ta kai ga basa amsa ba Khausar ta kunna waƙa a wayarta ta ƙure volume, bayan song din data kunna har wani bi take tana ɗaga murya, hakan yasa Hajar ba tajin me yake cewa tinda muryansa ba sosai take fitowa ba, Hajar tace "saida safe" bata jira cewarsa ba ta katse kiran don tasan ko yayi mgana ba ji za tayi ba, snn kuma idan ba ɗakin Noor ba taga inda zata iya waya dashi a gidan ba, Hajar ta ajiye wayar a gefenta ta sauke ajiyar zuciya sai kuma ta kwanta, Khausar ta rage volume din wayar bayan ta lura da kwanciyar Hajar, har bacci ya ɗauke Hajar mganarsa ta ƙarshe take tunawa ko me zai gaya mata. washe gari tinda Khausar ta tashi take wani cin magani, sai wani murtuke fuska take da ƙananun tsaki, har saida Noor ta tmbyeta lfy lokacin da ta kirata yin breakfast, fuska a ɗaure Khausar tace "nothing am just moody today", Noor tace "Ohk ki fito muyi breakfast", Khausar tace "tom am coming", Noor ta juya ta fita, Khausar na fita palour ta tarar da Noor da Hajar zaune kan carpet ga Variety na breakfast a gabansu, Khausar ta zauna ta haɗa shaya a mug, irish da kwai ta ɗeba ta matsa ketchup snn ta fara ci, Noor tace "ga croissant fa", Khausar na shan shayinta ta girgiza kai, Noor tace "akwai cheese sosai fa", Khausar tace "am not eating sister", Noor bata sake cewa komai ba, daman Hajar tinda Khausar ta fito bata ko kalli position dinta ba, ta lura yau ɗaɗɗaga kan nata yafi na jiya, Hajar na gama yin breakfast dinta ta kai plate da cup din kitchen, da ta fito bata zauna a palour ba tayi wucewarta ɗaki, bai fi 20mins da zamanta ba Khausar ta shigo, ta zauna gefen gado ta ɗauki wayarta dake kan bedside tayi dialing number ta kara a kunne, tsaki tayi ta wurgar da wayar kan bed, Hajar ta tashi ta fita ba tare da ta kalli inda take ba, through out the day hka Hajar ta ringa avoiding Khausar, mgnar da ya gaya mata kafin ya tafi ce ta ringa mata yawo a brain wato be good Hajar, idan ta tina saita share lamarin Khausar da take ƙoƙarin fusata ta. wajen ƙarfe biyu Hajar taje kiran da Sakeena ke mata, mai aikin gidan ce tazo kiran ta, Hajar ta shiga room din Sakeena na gidan da sallama, Sakeena dake zaune kan carpet da kaya baja baja zagaye da ita ta amsa, Hajar ta ƙarasa ciki ta zauna, wata leda Sakeena ta bata tace "Outfits dinki ne na biki, nasan size din zasu miki tailor Salmah ce ta miki tinda tasan size dinki amma dai ki gwada", Hajar tace "Toh ngd sosai", Sakeena tace "you're welcome dear", Hajar ta koma room din Noor don ta ajiye kayan, Khausar kawai ta tarar Noor ta tafi ɗakin da ake mata gyaran jiki, Hajar ta buɗe closet ta sauke box dinta zata jera kayan aciki, sosai laces din sukay mata kyau gasu kuma colors din da za suyi fitting dinta sosai, duk kayan da ta zaro saita ɗaga sai kuma ta mayar ta linke ta saka a box, by doing that har ta gane zasu mata ko bata gwada ba, Khausar tayi pausing Movie da take kallo jikin Laptop jin wayarta na ringing, tini tayi picking call din ta kara a kunne tace "Ya Nurain i have been calling you since morning..", sai kuma ta karyar da kai tace "Okay... hope you are not busy now..", tinda Khausar ta ambaci Ya Nurain Hajar ta dena abinda take na almost 10sec kafin ta cigaba, a handsfree Khausar ta saka wayar don ba ta jinsa sosai wnda hakan yasa Hajar ta tsinkayo muryansa ainun, taji yace "what were you saying yesterday lil sis..?", tini Hajar ta ɗauke hankalinta daga kansu ta cigaba da abinda take, ƙasa ƙasa taji sautin dariyarsa sbd tazarar dake tsakaninsu da Khausar, Hajar na ɗago kanta taga Khausar na murmushi sai kuma ta kwanta tace "Am serious fa Yaya", da sauri Hajar ta tutsa ragowar kayan ta dannasu cikin box din, ta mayar da box din cikin closet da haka ta nufi door ta fita kuma har lokacin basu gama wayar ba, Hajar har zata zauna palour sai kuma ta fasa ta tafi wajen Sakeena, ta gaya mata cewa ta gwada kayan kuma sun mata, Sakeena tace "where is Khausar...?", Hajar tace "tana can ɗaki", Sakeena tace "call her for me", har Hajar ta tashi kirantan Sakeena tace ta barshi, a nan Hajar ta cigaba da zamanta har ta taya Sakeena shirya wasu kaya da aka kawo a cikin Souvenirs box, wajen ƙarfe huɗu Mami ta shigo don daman bata nan sun fita da Anty Zulaihah, sannu da zuwa Sakeena ta mata Hajar ma haka, Mami na kallon Sakeena tace "har kin gama da wnn shima...?", Sakeena tace "yeah.. ai nafi so na gama komai ydda zan zama free a lokacin biki", Mami tace "su little Abba na wajen grandma dinsu ko...?", Sakeena tace "Eh", Mami tace "Alright please a ware 100 pieces daban", Sakeena tace "Sure", da haka Mami ta juya ta fita, Sakeena ta kalli Hajar tace "je kici Abinci kiyi sallah sai mu ƙarasa", Hajar tace "Toh" da haka ta tashi ta fita. the same time daya kira jiya ta wayar Noor yau ma haka ya kira saidai ta wayar da ya bata, shi asuba ce a can nan kuma ƙarfe tara na dare, Hajar ta ciro wayar da ta ajiye cikin handbag dinta tin safe jin tana ringing, ta ringa kallon exact number da ta kirata jiya, turo baki tayi bayan tayi wani tunani, gashi da Sim 1 ake kiran snn kuma numbern ba ta Nigeria bace, lokaci guda ta makawa wayar harara ta dannata a silent ta mayar cikin jaka, bathroom ta shige tana turo baki gami da juya lulu eyes dinta, tana fitowa daga wanka ta tarar da Noor na jiran fitowarta, da sauri Noor ta miƙa mata wayar hannunta tace "take it Yaya ne zai kira ynxu" tana gama fadin haka ta fita da sauri don kallon stuff na Kdrama data saba take yi ya kira, gashi yace lallai lallai ta bar abinda take ta kaiwa Hajar waya, tana zuwa ta tarar da Hajar na wanka gashi sai azalzalanta yke sai kace zai fito daga wayar, Noor na fita kiransa ya shigo, Hajar ta ringa kallon wayar har kiran ya katse wani ya sake shigowa, kan mirror ta ajiye wayar ta barta sai ringing take, ta dauki kayan baccinta ta saka tayi kwanciyarta tana ji wayar nata ringing, bayan wani lokaci taji kiran ya dena shigowa, kasa bacci Hajar tayi duk da baccin da take ji, idonta ne kawai a rufe amma ba baccin take ba, jin an buɗe door ta ɗan buɗe idonta, azatonta Khausar ce sai taga Noor ai kam tayi sauri ta rufe ido, Noor ta duba sides din Hajar tana neman wayarta tinda jiya ma anan ta ganta, ganin bata ganta ba saita fara dube duben ɗakin har ta hangota a kan mirror, zaro ido tayi ganin 10+ missed call, wani kiran nashi ne ya kuma shigowa, Noor tayi picking ta kara a kunne tace "Hello", from the other side Nurain ya haɗe thick eyebrows dinsa da muryansa da bata daidaita ba yace "Hey Noor kin kai mata wayar..", Noor tace "wllh na kai mata hand to hand..", ya sauke numfashi yace "where is she..?", Noor ta dubi Hajar da take baccin ƙarya tace "she's already at sleep", yace "wake her up", Noor tace "Ohk" da haka ta durƙusa gaban Hajar ta fara tapping dinta, tamkar sumammiya haka Hajar ta naɗe samm taƙi ta motsa ma, Noor tace "Yaya she's deeply at sleep taƙi tashi fa", yayi ajiyar zuciya tace "ki san yacca za kiyi ki tasheta nan da 5mins" ƙit ya katse kiran, Noor tayi tagumi tana kallon Hajar tace "na shiga uku", ganin lokaci na tafiya Noor ta kai hannu tayi tapping dinta tace "Please Hajar wake up ki rufamin asiri", sau ɗaya ta sake tapping dinta sai ta fara mutstsuka ido kamar gaske ta miƙe zaune, Noor tayi ajiyar zuciya don wani relief taji tace "Sorry Yaya ne yace na tashe ki", Hajar dai sai mutstsuka ido take ta gyaɗa kai, 5mins na cika dot ya kira, Noor tayi picking tace "gata nan na tasheta ynxu zan bata wayar", yace "Better", tini Noor ta miƙa mata wayar, Hajar ta amsa ta kai kunne ba tare da tace komai ba, fita daga ɗakin Noor tayi tana jin daɗi Allah ya rabata dashi, almost 1mins wayar na kare kunnenta taƙi tace masa komai, ya rage murya yace "Hajar are you there...?", shiru ta masa taƙi mgana sam, slight breathing dinta da yake jiyowa ta wayar ne ya basa assurance cewar tana ji mgana ne dai baza ta masa ba, yayi ajiyar zuciya yace "Hajar are you hearing me", ta haɗe gira ba tace uffan ba, babu yacca Nurain baiyi ba akan ta masa mgana amma taƙi, daga ƙarshe yace "i must open that small mouth of yours until you beg for mercy", da haka ya katse kiran, Hajar ta turo baki ta koma ta kwanta zuciyarta wasai. Haka nan two days Hajar taƙi sauraron Nurain, idan ya kira ta wayarta daman bata picking, ta wayar Noor kam zata dauka amma ba za tayi mgana ba, sosai Nurain ya damu da hkan da take masa, lafiyar Allah fa ya baro Silly girl dinsa toh me ya faru ne, wayar da sukay na farko ma harda sassanyan gaisuwar da kwana biyu take masa tayi fa, wai what is exactly happening ne, tini ya fara shirin dawowa 9ja duk da bai gama abinda zaiyi a can ba ya bar Mr Lee zai ƙarasa masa shikam ya kamo hanyar gida Nigeria. Zuwa wnn lokaci gida ya fara cika da ƴan uwa na nesa wnda suka zo biki, gobe ne za'a fara gudunar da ƙananun shagulgulan na bikin wnda Amarya da ƙawayenta ne zasu warwasa. Khausar ta dubi Noor dake zauna kan hannun kujera tace "Please Noor kixo mu tafi wajen Salon din nan don mu dawo da wuri", Noor tace "Hajar nake jira ynxu zata fito", Khausar ta haɗe gira tace "wace Hajar kuma ita amarya ce da sai kunje wajen Salon tare", Noor tace "Yaya Sakeena ce tace muje tare", Khausar tace "Ohk alright amma ai komai na bride is different from others", Noor tayi dariya tace "wankin kai ne fa kawai ba make up ko Outfits ba", Khausar ta taɓe baki ba tace komai ba, Hajar ta fito sanye da hijab da handbag dinta a hannu, da haka suka wuce wajen Salon din bayan sun sanar da Mami. ƙarfe 11 na safe Nurain ya iso gida, direct part din Mami ya wuce wacca ya tarar da ita tayi shirin fita, don haka suna gaisawa Mami ta fita don already driver dinta ma ya gama warming mota, Nurain na fitowa part din Mami ya buɗe room din Noor after knocking for almost 1mins, haɗe gira yayi ya juya ya koma bangaren Mami kuma saida ya duba ko wane room na part din snn ya fito, at last ya shiga kitchen ya duba shima dai baiga abinda yake nema ba, infact ma ya lura da babu kowa a main house din don ko baƙin da suka fara zuwa suna can Cabins din gidan, a ransa ya ayyana may be suna tare da Noor tinda bai ga kowa a gidan ba. Sai wajen huɗu su Hajar suka dawo daga wajen Salon, Noor cewa tayi ba zata shiga ciki ba sai taci abinci, Khausar sai wani cin mur take tin bayan da aka gama musu gyaran gashin, gani tayi na Hajar yafi na kowa kyau duk da cewa assistance din me Salon din ce ta mata, shiyasa tace kar aje da ita ai ga irinta nan nata yafi na amaryar ma kyau, ita dai ce taga hakan don kowa da zubin gashinsa amma na Noor yafi tsada da cin lokaci ai, a palour suka zauna cin abincin, Hajar da Noor eating from the same plate Khausar na cin nata daban, a kusan tare suka ɗago jin an fito daga great room din Abba, wani irin bugu zuciyar Hajar tayi after their eye contact, Khausar ta waro ido tace "Laa Ya Nurain", Hajar kawai yake kallo wacca ta sunkuyar da kanta tana juya spoon din hannunta, Khausar tace "Yaya yaushe ka dawo..?", speaking with a repartee yace "Since 11..", tace "Okay welcome", Noor ta masa snnu da zuwa tare da gaishesa, kaf saida ya amsa gaisuwar tasu banda ta Hajar, da haka ya nufi door hands dinsa zube a pocket don daman mosque zai fita sallar la'asar, tini Hajar taji ta tsani abincin, ta ajiye spoon din ta zuba ruwa ta sha, Noor tace "kin ƙoshi ne?", Hajar ta gyaɗa kai sai kuma ta ɗauki handbag dinta ta shiga ciki. bata sake fita ba sai after magrib da ta ɗakko shoes dinta a motar Sakeena, tinda ta koma ɗaki tayi zamanta sai kace prisoner, yau ko ɗan kallon ma bata fita palour tayi ba, wajen ƙarfe goma ta tashi ta shiga wanka, bayan ta fito ne ta tsaya gaban mirror tana kallon gyaran gashin da akay mata, zaro ido tayi ganin babu ear ring a kunnenta na hagu, sharp sharp ta ƙarasa shiryawa ta saka nities dinta, hijab ta zumbula saman nities din snn ta nufi ƙofa ta buɗe ta fita don ta duba ear ring dinta, main palour kitchen duk saida ta duba ba taga ɗan kunnen ba, tunawa tayi ai ɗaxu ta fita ko wajen ɗakko shoes dinta ta yar a compound, tana buɗe door abinda ta fara ji shine pure scent dinsa, sai kuma ta hango Khausar zaune kan kujera a balcony din, bata fita ba ta ɗan leƙa balconyn ai kam ta hangosa, shima yana zaune kan kujera suna facing juna da Khausar wacca take ta zuba masa zance, ya bata rabin attention dinsa while the other half yana kan wayarsa, and worst part of it the smile on his face, ba shiri Hajar ta juya ta koma ciki, ƙafarta har harɗewa take tayi sauri ta zauna kan tiles, saida abinda take ji ya ɗan ragu snn ta miƙe still ƙafarta na harɗewa ta shiga room din Noor, sulalewa tayi kan carpet tana jin wani iri a zuciyarta, duk yacca taso ta daure amma kasa jurewa tayi, ba tasan lokacin da ta fashe da kuka ba, samm bata iya danne kuka indai ya taho mata toh sai tayi, door aka buɗe Noor ta shigo, da sauri Noor ta ajiye bowl din farfesun kazar da ta shigo dashi ta duƙa gaban Hajar da ta kasa danne kukan da ya ci ƙarfinta, with care Noor tace "Ya salam what happened Hajar...?", Hajar ta girgiza kai tana ƙoƙarin tsayar da hawayen dake zuba cheeks dinta, Noor tace "please tell me Hajar me ya faru..?", da ƙyar Hajar tace "kai na ne yake ciwo", Noor tace "Ayya Sorry bari na kawo miki drug", Noor ta tashi ta fita bbu jimawa ta dawo da glass of water da satchet din Panadol, Hajar na yamutsa fuska haka tasha maganin, zata kwanta kan carpet Noor ta mata dole ta hau gado ta kwanta, sosai zuciyarta take mata wani iri wnda bata san a yadda zata fasaltasa ba. sai wajen ƙarfe sha ɗaya Khausar ta shigo, ta ringa nunawa Noor abinda Nurain ya taho mata dashi daga China, Hajar da idonta ke lumshe duk tana ji tayi sauri ta juya musu baya tana turo baki. Washe gari da safe Khausar ta fito daga kitchen da mug a hannunta, stairs ta dosa zata hau, dakatawa tayi ganin Sakeena na sakkowa daga stairs din, Sakeena ta kalleta a takaice tace "Khausar ina zuwa haka..?", Khausar tace "Ya Nurain ne yace na kai masa Coffee", Sakeena ta ƙarasa sakkowa tace "kawo Coffee din", Khausar tayi jim sai kuma ta miƙa mata mug din, Sakeena ta amshi mug din snn ta miƙa mata paper bag din data sakko da ita tace "take it to Mami", Khausar tace "sure" da haka ta bar wajen, ita dai Sakeena tasan Nurain ba zai sa Khausar ta kai masa Coffee room dinsa ba saidai cewa yayi ta haɗa ta ajiye masa zai zo ya amsa, kamar kwa ta san hkan sukay dashi, har Sakeena ta juya zata koma saman ta hango Hajar ta fito palour, Hajar na ganin Sakeena tayi bowing tace "ina kwana", Sakeena tace "morning how are you doing...?", Hajar tace "Alhmdllh", Sakeena tace "masha Allah, Noor tace jiya kanki na ciwo how are you feeling now...?", Hajar tace "ya dena alhmdllh", Sakeena tace "Ohk toh Allah ya ƙara sauƙi", mug din Coffee ta miƙa mata tace "ki kaiwa Nurain", daram zuciyar Hajar ta buga ta amshi mug din, Sakeena ta ringa kallonta ganin bata motsa ba tace "yana room dinsa..", Hajar ta gyaɗa kai tace "ai bansan room din nasa ba", saida Sakeena taji hakan odd kafin ta kwatanta mata room din nasa, a hankali Hajar ta haura stairs din zuciyarta na ɗif ɗif, tana isa ƙofar room din nasa ta kai hannu tayi knocking a hankali, tafi minti biyu a tsaye amma no respond, tunani tayi may be ma baya ciki don haka bari ta shiga ta ajiye masa idan yaxo ya gani, da wnn tunanin ta murɗa handle ta shiga, ɗakin sanyi ƙau sai kace freezer, kaɗan ta shiga tana ɗaga kanta sukay ido huɗu dashi ta cikin mirror, a tsaye yake bakin mirror yana taje sumar kansa da towel ɗaure a waist dinsa alamar daga wanka ya fito, Hajar ta fasa ƙara ta rufe idonta da other hand dinta, a miliyan ta juya ta nufi door saida tayi karo da bango sbd idonta dake a rufe snn ta wawaki ƙofar ta fita, rabin coffee din kam duk ya zube mata a legs kuma taji zafi sosai, Nurain yayi wani murmushi irin zaki shigo hannu ne, yayi kwafa ya cigaba da combing hair dinsa, zai kamata ne wllh sai ta nemi mercy kamar yadda ya faɗa mata, duk ta gama guje gujenta da zille zillenta ai zasu koma gida ne sai yaga ƙarshen gudu. A gigice Hajar ta sauka stairs kawai taji tayi karo da mutum, Khausar ta hangame baki tana kallon jikinta da Hajar ta wanke mata shi da ragowar Coffeen, Hajar tace "please kiyi haƙuri ban...", katseta Khausar tayi da ɗan tsawa bayan ta ƙarewa palourn kallon tace "Shut up.. I don't need your apology..", Hajar ta maka mata wata shegiyar harara tace "Au haba toh kar Allah yasa ki haƙura sai kije can kisha wankin madara" tana gama faɗin haka ta kewayeta ta wuce gami da jan dogon tsaki, Khausar ta saki baki galala tabi ta da kallon mamaki.......✍️
💛 HAJAR 💛

{74..}
A fusace Hajar ta juyo ta fixge veil dinta tace "Am not single..", murmushi yayi yace "ai ko idan duk jikina kunne ne i will not believe you An mata", bata sake ce masa ƙala ba ta juya ta nufi ƙofar hall din, bai haƙura ba ya sake bin bayanta, Nurain da zuciyarsa take tafasa hundred degree Celsius sai a lokacin ya iya buɗe motar ya fito, ya riga da yayi mistake din farko da ya riƙe mata veil, wnn time din kam hannunta yaso kamowa da nufin tsayar da ita, saidai me bai kai ga riƙe hannun nata ba yaji saukar wani mugun punch a fuskarsa, tini Abokin ango ya riƙe gefen fuskarsa yana jin taste din blood a bakinsa, a gigice Hajar ta juyo tana ganin Nurain jikinta ya hau shivering, da sauri tasa hannu ta rufe bakinta gami da yin ƴar ƙara ganin bakin abokin Ango na zubar da jini, with husky voice Nurain da idonsa ya rine yace "daga yau bazaka sake mistake din riƙema wata veil ba.." da haka ya fixgi hannun Hajar zuwa inda ya yasar da motar, saura ƙiris taci da ka sbd yadda ya finciketa, fashewa tayi da kuka jin kamar zai ɓalla mata hannu tace "ni ka sakeni wayyo Ummana zai karya min hannu", front seat ya buɗe ya cillata ciki ya rufe ƙofar saura ƙiris ya haɗa da hannunta, ya zaga driver seat ya shiga da haka ya fita da motar daga event center din da reverse, wani irin cin taya yayi a kan kwalta snn ya fixgi motar with high speed ya bar area din, Hajar ta fasa ƙara ta haɗe kanta da guiwa don harta saddaƙar yau sai ya kifar dasu, gaba ɗaya Nurain daina ganin gabansa yayi sbd yadda zuciyarsa take tafasa, kawai hango yacca wnn banzan ya riƙe veil din Silly girl dinsa yake, how dare him da zaiyi ƙoƙarin riƙe mata hannu, a lokaci guda ya gangara bakin road ya tsayar da motar gami da kifa kansa ga steering, ya lumshe idonsa trying very hard to control himself, Hajar ta ɗago kanta jin ya tsaya da tuƙin, ta ɗan kallesa har lokacin kansa na haɗe da steering, after a while ya ɗago sukay ido huɗu tayi saurin janye nata, zuciyarta ta hau lugude ganin yanayinsa, Nurain exhale heavily his eye fixed on her, ya dubi dressing dinta da kyau, ji yayi kamar ya wanka mata mari amma bazai yi hakan ba, not in this situation gsky, ko a Abuja da ya mareta yasan bata ji da daɗi ba, toh this time around ma yace zai mangareta wllh sai tayi jinya, dunƙule hannunsa yayi ya sauke ajiyar zuciya, after few seconds ya furzar da iska ya cigaba da driving din, koda wasa Hajar bata sake ɗago kanta ba har suka je gida, a daidai main door ya tsayar da motar ba tare da ya dubeta ba yace "get out", jikinta har rawa yake tayi sauri ta zura takalmanta ta bude ƙofa ta fita, ɓangaren Hajiya ta shige walking gently, Hajiya da har lokacin take tare da Farooq ta kalleta tace "Ah ah ƴar nan har kun dawo daga wajen chasun da wuri haka...?", Hajar ta gyaɗa kai tace "Eh Hajiya", Hajiya ta taɓe baki tace "yo wnn ai ba chasun akai ba du du mintinku nawa da tafiya", Hajar ta ɗanyi bowing ta gaida Farooq, ya amsa da sakakkiyar fuska yace "how are you doing..?", tace "fine alhmdllh", yace "Good anata shan biki..", door aka buɗe aka shigo, Hajar na ganin wnda ya shigo tayi sauri ta shige bedroom din Hajiya, Nurain yayi kwafa ya bita da kallo sai kuma ya ƙaraso ciki ya zauna gefen Farooq ya ajiye masa key din mota, Farooq ya ringa kallonsa ganin ydda ya wani haɗe rai sai kace bai taɓa murmushi ba a rayuwa, rage murya Farooq yayi yace "ka kyauta da ka hana yarinya morewa Dinner", Nurain ya tamke fuska yace "what are you talking about...?", Sosai Farooq yayi dariya yace "Oh yeah ni dae kasan bazaka min wasa da hankali ba..", Nurain yace "Whatever", sai a lokacin Nurain ya kalli Hajiya da tin shigowarsa take kallonsa ta ƙasan glasses dinta, ya waro ido yace "Iron lady barka..", Hajiya ta katsesa da faɗin "kkkk riƙe abinka bana so, Man zafin da ka kawomin ma kazo ka amshi abinka bana so", Nurain ya sauka kan carpet ya zauna gefenta yace "ba kyau fa mayar da hannun kyauta na bar miki", tace "ka matsa daga kusa dani ko na saka sandar nan na raɗe ka wllh", Nurain ya riƙo hannunta yace "ya haƙuri idan kika buga min sanda wa kika kama", Hajiya tace "azabar son da nake yiwa jikoki shiyasa suka sami ƙofar yimin wulaƙanci barin ma kai da Al'ameen", Nurain yace "nidae nace kiyi haƙuri duk da bansan laefin da nayi ba", Hajiya ta rausayar da kai tana micincina ido. ƴan Dinner kam basu dawo gida ba sai wajen 11 don neman Hajar aka ringa yi tin kafin ma a gama Dinnern, Farooq Sakeena ta kira tace masa idan yana tare da Nurain ya gaya masa suxo ba a ga Hajar ba, saida Farooq ya gama cin dariya snn ya gaya mata cewar ai Hajar ta daɗe da dawowa gida. washe gari Friday kuma itace ranar ɗaurin auren, bayan an sakko daga masallaci aka ɗaura auren, zuwa bayan sallar la'asar gida ya kuma cika maƙil da jama'a sbd an shiga sabgar yini, a duk wnn bidiri da ake Hajar na maƙale part din Hajiya, ita dai da safe take zuwa wajen Mami ta gaisheta, Sumayyah ce ta shigo tayi kiran Hajar tace taje inji Mami, Hajar ta yafa veil dinta ta tashi ta fita, ta ringa wuce jama'a tana kutsawa harta samu ta shiga part din Mami, shima nan din a cike yake maƙil da mutane, sai ga Mami nan ta fito daga bedroom dinta, da hannu ta yiwa Hajar alamar tazo, Hajar ta ƙarasa har gabanta suka shiga bedroom din tare, wasu mata su biyu Hajar ta tarar a room din an jere musu kayan abinci, sai kuma Haj Fati da take zaune room din itama, Hajar ta durƙusa har ƙasa ta gaishesu da ladabi, ɗaya daga cikin matan tace "Masha Allah, matar Nurainin ce..?", Mami ta gyaɗa kai da murmushi kwance fuskarta, bayan sun gama gaisawa Mami tace da Hajar ta wuce abinta, har ta tashi zata fita Haj Fati ta dakatar da ita, box din souvenir ta bata tace ta rakata compound dashi, Hajar na biye da Haj Fati da box din souvenir har suka fita compound, Ahmad da yayi parking din motarsa can kusa da gate ya fito ganin mahaifiyarsa, da sauri ya taho inda take da wata leda a hannunsa, Hajar na hangosa tayi still a inda take har ya ƙaraso, sai da yaxo daf dasu snn ya lura da Hajar, Haj Fati tace "Good.. hope baka mnta komai ba..?", yace "Sure Ammie.. Husnah ce ma ta bani", Haj Fati tace "Alright.. ga wnn ka tafar min dashi", da haka ta juya ta amshi box din hannun Hajar ta miƙa masa, ya amsa yana kallon Hajar without blinking sai kuma yace "Hi Hajar..", Hajar ta saukar da kanta tace "good afternoon..", Haj Fati tace "you know her..?", Ahmad ya gyaɗa kai yace "yeah", Haj Fati tace "A ina ka santa..?", yace "ba kin aikoni wajen Mami ba three weeks back", Haj Fati tace "Ohk..", ita dai Hajar na jinsu ba tace komai ba har suka gama mganar snn ta koma ciki tare da Haj Fatin. Sakeena na attending guest dinta da suka zo biki wnda su din in-laws dinta ne, kiran Nurain ne ya shigo wayarta, saida tayi excusing kanta snn ta ɗaga kiran, Nurain ya sanar da ita ai Hammad ne yaxo tare da matarsa suna Mini palour, Sakeena tace "Alright" don daman tasan Hammad, haka nan taje suka gaisa dasu Hammad din snn ta tasa aka kai musu abinci ita kuma ta wuce ta kira Mami don su gaisa, Sakeena ta shiga mini palour tare da Mami, Mami na gama gaisawa dasu Hammad ta koma wajen nata baƙin da suke kan zuwa, Maysha ce ta tambayi ina Hajar don tana so su gaisa, Sakeena ta kira Aysha a waya tace ta kira mata Hajar, su Hammad basu wani jima ba suka tafi don dman suma wani bikin suka zo kano shine suka biyo tanan, Bayan tafiyarsu Hammad Nurain ya dawo daga rakasu ya tarar da Sakeena bakin main door, sosai ya tsargu da irin kallon da take masa, ya ɗage gira yace "why..", Sakeena tace "wai kai har wani extinct kaje sbd taurin kai brother..?, me yasa kake ɓoyewa mutane Hajar matarka ce...?", ya waro ido yace "Nah..?", Sakeena ta haɗe gira tace "bafa wasa nake ba Nurain..", ya zuba both hands dinsa a pocket yace "Nah too, kin san dai mun gama mgnar nan dake", Sakeena ta saki baki tace "i thought ka janye wnn shirmen Nurain", ya ɗaga shoulder yace "kince fa ina da taurin kai so taya za ai na janye", Sakeena ta sauke ajiyar zuciya ta koma ciki. kafin magrib aka hau shirin kai Amarya gidanta, dangin Ango har sunxo daukar abarsu da convoy din manyan motoci, hka aka fito da Noor data sha lafaya daga ɓangaren Abba tana gursheƙen kuka, da kyar aka ɓanɓareta daga jikin Mami snn aka miƙata dangin mijinta, Mami kawai daurewa take don itama harta fara missing ƴarta ta, sai a lokacin Hajiya ta fito tace ita ce nan zata kai jikarta har ɗakin mijinta, ai kam ba wnda yayi musu haka Hajiya ta riƙe hannu Noor har compound, daman duk jikarta mace da akai aurenta toh ita ta kaita ɗakinta, tin daga kan Sakeena ma kuwa, idan kuma namiji ne da ita ake zuwa ta rungumo matar ta kaita har ɗakinta, shiyasa lokacin auren Nurain ta ringa mitar ƙafarta ta cuceta da bata je ta rumgumo matar Usuman ba. Hajar na gani ana ta rawar ƙafar zuwa gidan Amarya ita dai ko a jikinta hasalima guduwa tayi can bedroom din Hajiya tayi kwanciyarta don kanta ke ciwo, har wajen ƙarfe takwas na dare gida bai dawo daidai ba don wasu ma sai a lokacin suke tafiya gidan Amaryar wasu kuma na dawowa, friends din Amarya kam da shiri biyu suka tafi don za ai cocktail party ne bayan an kai Amaryar, ita dai Hajar har tayi bacci ba tasan dawowar su Aysha ba. washe gari kam an gama biki tin safe gidan ya fara bajewa don da yawan mutane da safe suka tafi, kafin yamma tass gida ya ɗaɗe bbu kowa sai asalin mutanen cikinsa, tin safe daman ma'aikata suke ta share share da goge goge suna so su mayar da gidan normal self dinsa. bayan Hajar ta idar da sallahr magrib ta fito main palour da ƴar wayarta a hannu, tini tayi dialing numbern Umma ta kara a kunne, gaisawa kawai sukay da Umma kiran ya katse, Hajar ta sake kiranta nan taji switched off, Contact ta shiga ta nemo number Mu'azzam wnda tayi saving da Yayana, da sauri ta katse kiran bayan tayi realizing wnda ta kira, ashe maimakon ta danna Yayana saita danna Ya Sayyadina a rashin sani, unfortunately for her don kiran ya shiga, Tinda Nurain ya fito daga great room din Abba yake kallonta, don ita bata ma san yana nan ba ta juya masa baya, walking majestically ya matso inda take, tayi sauri ta juyo after perceiving his pure scent, wayar hannunta ce ta fara ringing, ta kalli screen din wayar kawai taga Ya Sayyadina ɓaro ɓaro, tana ɗaga kanta taga Nurain shima yana kallon wayar, a bazata ya fixge wayar daga hannunta yayi picking ya kare a kunne, wani irin sauyawa shimfiɗar fuskarsa tayi bayan ya tsinkayo muryar namiji a wayar, wani mugun yawo Hajar ta haɗiya ta kwasa a guje zata shige ɓangaren Hajiya saidai ina tini ya fixgota da ƙarfi saida ta bige da kujera, girgiza kai ta shiga yi tana son yin mgana amma rawar da lips dinta suke ta hana mganar fita, sosai idon Nurain suka kaɗa ya fara losing control, gaba ɗaya temper dinsa ta tashi, ya buga wayar da ƙasa ta tawarwatse kafin ya daka mata tsawa yace "Waye wnn din..?", Hajar ta numfasa da kyar bakinta na rawa tace "Allah yaso dai wayar taka ce kai kayi asara bani ba", slightly ya buge bakin da bayan hannu, habawa ai tini Hajar ta durƙuse a ƙasa ta fashe da kuka don ji tayi kamar guduma aka buga mata a bakin, ta kai hannu ta shafa lips dinta ai kam ta dangwalo jini hakan yasa ta kuma rushewa da kuka, da sauri Sakeena ta ƙarasa sakkowa daga stairs don akan idonta ya gwabjewa Hajar baki, ta durƙusa ta ɗago Hajar da bakinta ke fitar jini, Sakeena ta zaro ido tace "innalillah", shi ma kansa saida hankalinsa ya tashi da yaga jini, slightly fa ya bige bakin ba da wani ƙarfi ba, idan da yasan za taji ciwo ai bazai bigeta ba, ya cije lower lip dinsa ya haura sama girarsa a haɗe, Sakeena tabi bayansa da kallo sai kuma ta tallafi Hajar da tke kuka har lokacin ta wuce da ita part din Mami, gsky Mami zata gayawa abinda ta fahimta a zaman auren nan nasu, Mami ta ringa furta subhanallah bayan taga fashewar da bakin Hajar yayi, Mami tace "faɗuwa tayi ne..?", Sakeena ta girgiza kai tace "ko ɗaya Nurain ne ya bigeta", Mami was very shocked, Nurain ne ya bigeta kuma, Nurain din har yaushe ya fara duka, Mami ta wuce da Hajar bedroom snn ta shiga da ita toilet tasa ta wanke bakinta da fuskarta, Mami ta zaunar da Hajar daga gefen gadonta tace ta zauna anan, da haka Mami ta fita zuwa palour, Hajar ta kasa zama a kan gadon ta tashi ta nufi ƙofa ta buɗe, bata fita ba ta rakuɓe jikin ƙofar ta jingina da ita, har lokacin Sakeena na zaune palour tana jiran fitowar Mami, Mami na kallon Sakeena bayan ta zauna tace "what exactly happened Sakeena..?", Sakeena ta juya hannu tace "Mami nidae ban sani ba kawai naga lokacin daya bigeta ne a baki", shiru Sakeena tayi after few seconds tace "Mami", Mami tace "mene ne", Sakeena tace "Ni dae a nawa view din ya kamata ayima Nurain mgana akan yacca ya ɗauki auren nan", nan Sakeena ta wassafawa Mami komai, ta gaya mata yadda yace shi favor kawai yakema Hajar don ba choice dinsa bace kuma ita ba type dinsa bace, har yadda sukay jiya da Hammad da Nurain ya ɓoye masa Hajar matsayin mata saida Sakeena ta gayawa Mami, abinda yafi tsayawa Mami shine favor din nan da kuma yacca yake gayawa jama'a ita din ba matarsa bace, Mami ta numfasa tace "Ina Nurain din yake..?", Sakeena tace "yana room dinsa", Mami tace "Abbanku bai fita ba..", saida Sakeena tayi sak kafin tace "Eh banga fitarsa ba", Mami ta yunƙura ta nufi ƙofa, Sakeena tace "Mother dan Allah karki gayawa Abba ke ki masa mgana", Mami ta girgiza kai tace "A'a gara na gayawa wnda ya aura masa ita" da haka ta fice daga palourn. da sauri Hajar ta sulale ƙasa hawaye ya cika mata ido, surely bbu abinda ba taji ba na mganar da Sakeena ta gayawa Mami, ita ba Choice dinsa bace yess tasan da hakan ai kamar yadda shima ba Choice dinta bane, and yess ita ba type dinsa bace sbd ya fita ta ko ina, daman taya za ai ta zama type dinsa bacin irin tazarar da yayi mata, ita ba ƴar gidan kowa bace babanta mai rauni ne wnda sai ya fita kullum yake nemo musu abinda zasu saka a bakin salatinsu, Shifa Babansa is super rich wnda ya bawa talauci baya, ko daga unguwar da suke zaune ai tasan dole yace ita ba type dinsa bace, ita ƴar ghetto area shi kuma ɗan GRA, ta fashe da kuka mai taɓa zuciya, da Ya Sayyadi Nura ta aura bbu ta inda zaice alfarma yake mata, amma fa wai zaman da take duk na alfarma ne, lokaci guda brain dinta ta sarƙe da irin kalaman da ya gaya mata, (never.. i will never imagine you as my wife and you will never be, Amm young lady dman nace miki inada mata ne abinda na sani shine ni banda wata mata a rayuwa). Hajar ta lumshe idonta hawayen da suka taro suka hau zarya bisa kuncinta, bayan kamar minti ashirin saiga Sakeena nan ta shigo, Hajar ta ɗaga kai ta kalleta, Sakeena tace "Come with me", a hankali Hajar ta tashi tabi bayan Sakeena suka fita daga part din Mami, Sakeena ta nufi great room din Abba ta buɗe ta shiga, saida Hajar ta shiga snn ta rufe ƙofar, Abba da fuskarsa ke a haɗe ya kalli Hajar har ta zauna kan carpet kusa da Sakeena, Mami tayi ajiyar zuciya itama dai fuskar nan bbu annuri, Babu jimawa aka buɗe ƙofa Nurain ya shigo, har ya fara shigowa ciki sai kuma yayi still bayan ya lura da Hajar dake zaune kan carpet, ya dake ya ƙarasa shigowa yana satar kallon Mami da ya lura ranta a ɓace yake, Nurain ya zauna kan carpet ya sunkuyar da kansa baice komai ba, fuska ba yabo ba fallasa Abba yace "who is that lady..?", Nurain ya ɗago ya kalli inda Abba ke masa pointing, a hankali yace "Hajar", Abba ya gyaɗa kai yace "and mene matsayinta a wajenka..?", Nurain ya saukar da kansa baice komai ba, Abba exhale heavily ya tashi ya shiga ɗakinsa, few seconds ya dawo da pen da jotter a hannunsa ya wurgawa Nurain, strictly yace "rubuta mata sakinta..", da sauri Mami da Sakeena suka dubi Abba don basu taɓa zaton hukuncin da zai yanke ba knn, Shi kam Nurain wani irin faskarawa kansa yayi tamkar an buga masa guduma, tini zufa ta fara keto masa bbu shiri duk da sanyin Ac da yake busowa, Mami tace "Amma yallaɓai ba..", Abba ya ɗaga mata hannu yace "Please madam ba dai nina ƙulla wnn auren ba toh ni zan warwaresa, ko ke favor nake miki a gidanki..?", sai kuma ya dubi Nurain yace "you are wasting my time Uthman kayi abinda nace", Nurain bai taɓa sanin cewa akwai ranar da hannunsa zaiyi rawa ba sai wnn moment din, da kyar ya ɗauki pen din ya buɗe jottern amma ya kasa rubutu, lokaci guda idonsa ya rine ya juya ya kalli ƙofa yana fatan Iron lady ta shigo, ina ma dai ta shigo kamar ranar da yazowa da Abba batun sakin Hajar tazo ta hana, muryar Abba ce ta dawo dashi daga duniyar fatan da ya afka, Abba yace "ni zaka yiwa favor ba ita ba Uthman, tinda favor kake mata rubutamin sakinta ka bani..", Nurain ya sauke ajiyar zuciya mai karfi ya ɗan kalli Hajar da tinda ya shigo kanta ke ƙasa, Abba yace "i don't want to repeat my self Uthman", A hankali Nurain ya fara rubutu a paper, rubutun da ya ɗaukesa minti 4 yana yi, yana gama rubutawa ya felle papern ya miƙawa Abba, Abba ya amsa yace "Good you can go to any extinct ka auri wcca bazaka yima favor ba Uthman, and as a father na baka go ahead hundred percent..", Nurain ya shafa fuskarsa da palm dinsa ya tashi ya fita da sauri, Abba ya miƙawa Mami papern yace "keep it with you" da haka ya wuce bedroom dinsa, Samm Mami bata so haka ba don ko riƙe takardar ma bata son yi, Sakeena ta miƙawa tace ta ajiye mata a closet dinta, Sakeena tazo amsar papern ta faɗi a ƙasa, Hajar da hawaye yake zuba daga idanunta ta kalli rubutun jiki, lokaci guda taji kamar an cinna mata wuta a zuciya, ba tasan lokacin da ta fashe da kuka ba, Sakeena da jikinta yayi mugun sanyi ta duƙa ta ɗauki papern bayan Hajar ta gama karancewa tass, Sakeena tayi folding papern tana kallon wani position din, da haka ta ɗaga Hajar dake kuka harda shessheƙa suka bar great room din.......✍️
💛 HAJAR 💛

{75..}
Bangaren Mami Sakeena ta wuce da Hajar wcca har lokacin tke kuka a hankali, Sakeena ta shiga bedroom din Mami bayan ta zaunar da Hajar akan sofa, Closet din Mami ta shiga ta ajiye papern snn ta fito palour, gani tayi Hajar ta zamo daga kan kujerar ta haɗe kanta da guiwa still tana kuka, Sakeena ta zauna gefenta tace "please stop crying dear", da kyar Hajar ta tsayar da kukan don wani suya zuciyarta ke mata, Sakeena tace "have you take your dinner...?", Hajar ta girgiza kai tace "Am not hungry..", Sakeena tace "Ohk Alright". wajen ƙarfe tara Mami ta fito daga ɓangaren Abba, har zata shiga nata sai kuma ta juya ta shiga na Hajiya don ta dubata, tarar da Hajiya tayi ta mimmiƙe ƙafafuwa sai matsa su take, Mami ta zauna gefenta tace "Hajiya barka da dare..", Hajiya na cigaba da matse ƙafarta tace "barka dai ƴar nan", Mami tace "ya hidima", Hajiya tace "Ayyo ai kune masu hidima kuka sha gwagwarmaya, ni kam tinda na jaɓe me na aikata in banda miƙa Noor gidan miji, ai kune da sannu Mami..", Mami tayi murmushi tace "ƙafar ne yake ciwo Hajiya..?", Hajiya tace "wllh kuwa kin san bata son whala ko kaɗan, da muka je gidan Noor wai ashe ɗakin nata na sama ni kuma nayi alƙawari saina dangana da ita har ɗakinta, Toh dai in taƙaice miki saida na hau saman nan da kyar ina jinjina da kuma tara tarar jama'a snn na hau..", Mami tace "ya subhanallah Hajiya ai da baku whalar da kanku ba..", Hajiya tace "Ahap ynxu ba gashi ya wuce ba, ni nan ƴar Albarkar yarinyar nan matar Usuman ma nake jira ta zo ta shafa min man zafi ko naji sassauci, tin ɗaxu da ta fita ban sake ganinta ba", Mami tace "tana can wajena ta kwanta bata jin daɗi ne..", Hajiya ta gwalo ido tace "Allah sarki, nidae tinda ake hidimar nan sai naga tana abu lagwai lagwai duk ba tada wani kuzari ko dai ciki ne da ita..?", Mami tace "ina man zafin na shafa muku Hajiya..?", Hajiya ta saƙa hannu cikin ƙatuwar jakarta dake gefenta ta ciro kwalbar man zafin da Nurain ya kawo mata ta miƙawa Mami tace "kinga man zafin Usuman ne ya bani", Mami ta amshi kwalbar ta buɗe ta fara shafa mata a hankali, Hajiya tace "kin san shi Usuman baya son yaga ina cikin farin ciki da walwala sai ya fara kowa abinda zai ɗaga min hankali, nan yaxo yamin ƙerere a ka wai kar na bari ayi saki a gidan nan, toh wane irin saki ana zaune ƙalou salon a tarwatsa kan ahali, saida dai ya ɗaga min hankali wllh, da kyar na rarakasa da sandata na kaɗasa waje, kuma naji daɗi dana samesa a hannu don shammatarsa nayi..", Mami dai tayi shiru tana mamakin Nurain, wato wajen Hajiya yxo bayan ta faru ta ƙare, Mami na gama shafawa Hajiya man zafin ta mata saida safe ta tafi ɓangarenta. Hajar a wajen Mami ta kwana, washe gari da safe wajen ƙarfe goma mai aikin Mami ta kai mata box dinta, wanka Hajar ta shiga bayan ta fito ta fitar da kayan da zata saka, tana cikin shiryawa mai aikin ta kawo mata breakfast, ko da Hajar ta gama shirin bata kalli abincin ba, bata jin zata iya cin wni abu don maƙogoronta ciwo yake, ga idanunta da sukayi luhu luhu suna mata zafi, After 30mins da kawo mata abincin Mami ta shigo, ganin ba taci ba Mami tace "ya baki ci abincin ba dear..?", Hajar ta saukar da kanta ba tace komai ba, Mami tace "ko ba kya son wnn a kawo miki wani..?", Hajar ta girgiza kai tace "A'a", Mami tace "ko a dama miki Oat..?", Hajar ta janyo abincin gabanta tace "zanci wnn..?", Mami tace "Ohk.. eat a lot kinji dear" da hka ta juya ta fita, da kyar Hajar taci abincin kaɗan ta ture, Shayin ma sip baifi huɗu tayi ba ta ajiye, a hankali ta tashi ta saka hijab dinta ta ɗauki abincin zata kai kitchen, bata son Mami ta dawo taga ba taci sosai ba, bata tarar da kowa a palourn Mami ba don haka direct ta nufi door ta buɗe ta fita, main palour ma bbu kowa ta zaga ta bayan kujera ta shiga kitchen, ajiye abincin tayi kan island ta matsa gaban sink ta buɗe tap tana wanke hannunta, door aka buɗe ya shigo ya mayar da door din ya rufe, sak Hajar tayi after perceiving his scent ta kashe tap din ta juyo kanta a ƙasa ta nufi door zata fita, kallonta ya ringa yi without blinking, kwata kwata jiya bai rintsa ba, yacca yaga rana haka yaga dare, bai taɓa shiga ɗimuwa ba irin ta jiya da Abba ya tarfasa yace ya saki Hajar ba, sosai ya shiga damuwar da har wayewar gari bai samu sassauci ba, sosai ya lura da haurawar da idanunta sukay duk da cewa bata kallesa ba, tana zuwa kusa dashi zata wuce yayi saurin riƙo hannunta, da iya ƙarfinta ta fara fincikewa ta wani murtuke fuska, sakinta yayi da wata iriyar murya yace "Hajar", ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta ta fashe da kuka, ya ringa kallon slim fingers dinta da suka ji jan lalle, lokaci guda ya janyota jikinsa ya rumgumeta, da ita a jikinsa yaje ya sakawa door lock kafin ya fara patting din bayanta a hankali, har lokacin kuka take rusa masa don wni irin zafi zuciyarta ke mata, ya sauke ajiyar zuciya a saitin kunnenta yace "Please please stop crying Hajar..", bai saketa ba duk da irin attempting din kwace kanta da ta ringa yi, almost 10mins tana jikinsa stiil yana patting bayanta har saida ta dena kukan ta dawo jera ajiyar zuciya, ya saketa a hankali ya ringa kallon fuskarta kafin ya kai babban finger dinsa ya share mata ragowar hawayen da suke kwance cheeks dinta, hannunta ya riƙe ya nufi ƙofar kitchen din wcca tayi leading zuwa backyard, ya buɗe ƙofar ya fita hannunta cikin nasa, ganin sun fito waje Hajar ta turje, ai kam without second thought ya sunkuceta ya zaga ta baya har zuwa parking space, babu wnda ya lura dasu har ya buɗe motarsa ya sakata, Hajar ta kurma ihu tace "meye haka, where are you taking me..?", tini ya zaga driver seat ya buɗe ya shiga motar da haka ya bar gidan bayan mai gadi ya buɗe masa gate, tin Hajar na bubbuga glass din motar tana cewa ya ajiyeta har ta haƙura ta haɗe kanta da guiwa tana hawaye, habawa ai Nurain saida ya gansu a ƙofar gidansa snn ya samu relief, fita yayi yaje ya buɗe gate ya dawo ya shigar da motar ciki, yana gama parking ya lumshe idonsa yana sauke ajiyar zuciya, ya fakaici kallon Hajar kafin ya buɗe motar ya fita, entrance din gidan ya nufa ya ciro key ya bude main door, dawowa yayi wajen motar ya bude side dinta ya ɗauketa ya nufi cikin gidan da ita, har room dinta ya kaita ya ajiyeta bisa gado yace "we are home Hajar", ta ɗago kanta tana ƙarewa room din kallo sai kuma ta taɓe baki tace "this is not my home and it will never be", ya waro ido yace "really", ta gyaɗa kai tana turo baki tace "everything da ake maka favor dashi there is no way da zaka kirasa da naka..", yayi blushing yace "are you sure Silly girl..?", ta gyaɗa kai tace "Eh dan haka nan din is not my home", Nurain ya kalli lips dinta yace "your lips are aching right", juya masa baya tayi bata sake cewa komai ba. Sakeena ta miƙawa Mami papern hannunta snn ta samu waje ta zauna, a hankali Mami ta fara warware takardar zuciyarta na sinking, gwara dai ta duba taga saki nawa ya mata duk da tasan bazai wuce ɗaya ba, Mami ta ƙanƙance ido bayan ta gama karanta papern, Sakeena dake ankare da expression dinta tace "Saki nawa ne..?", Mami ta miƙa mata takardar without saying anything, Sakeena ta amsa ta karanta, tana gamawa ta kwashe da dariya tace "Abinda ya rubuta knn.. toh ai ni banga saki ba", Mami ta girgiza kai ta sake amsar papern ta karanta, samm bbu alamar saki a jiki don ko ambaton sunan Hajar din ma beyi ba, kawai dai ya cewa Abba he is very sorry amma bazai iya sakin matarsa ba, Mami ta tashi ta fita da takardar a hannunta, ɓangaren Abba ta wuce, a bedroom dinsa ta tarar dashi, ba wani wala wala ta basa papern, saida Abba ya saka glasses dinsa snn ya duba, ya kalli Mami ya kalli takardan yace "what is this..?", Mami tace "Papern da kace na ajiye maka jiya ce..", yace "I don't understand ba divorce paper na baki ba..?", tace "not at All abinda Nurain ya rubuta knn", Abba ya cukuikuiye papern yace "how dare him play with our intelligence, where is your Son Mami..?", Mami ta numfasa ganin Abba na shirin fusata ta saukar da murya tace "yallaɓai dan Allah mubi komai a hnkali Please, tinda kaga Nurain bai saki yarinyar nan ba toh yana son zama da ita wllh, i know him wllh tinda yaƙi sakinta yana son zama da ita..", Abba ya haɗe gira yace "yana son zama da ita ya cigaba da mata favor knn..?", Mami ta girgiza kai tace "No yallaɓai ba dai zaman Alfarma ba, saidai ya zauna da ita don ta isa kuma ta kai a zauna da ita matsayin mata, wnn shine chance dinsa na ƙarshe, please a masa haƙuri this one, i will handle the case now..", Abba exhale heavily yace "daga wnn moment din kar Nurain ya sake cewa favor yake ma my daughter, this is my last warning..", Mami tace "Sure". Mami na komawa ɓangarenta ta tarar da Hajiya zaune kan sofa da sandarta a hannu, Hajiya tace "hankalina yaƙi kwanciya wllh tin jiya da kika ce yarinyar nan ba lfy, gashi yau da safe nayi ta zuba ido naga ta shigo amma shiru kake ji, shine na wanko sayyadata naga yata kwana..", Sakeena ta fito daga room din da Hajar ta kwana tana tattare gira, Hajiya tace "Sakeenatu ya kika fito ke kaɗai ince yarinyar kika shiga kira..", Sakeena tace "bata nan, nasha ma tana toilet na tsaya jira ta fito toh ashe ma bata ɗakin gaba ɗaya", Mami ta kalli Sakeena tace "where did she go..?", Sakeena tace "bari na dubata waje da Kitchen", duk inda ake tunanin Hajar zata shiga a gidan an duba amma bata nan, har ɓangaren Hajiya Sakeena ta sake dubawa wai ko sun samu saɓani amma bbu Hajar, Sakeena ta dawo a bit confuse tana kallon Mami tace "this is weird I can't find her", Hajiya ta ringa salati da sallallami tace "yarinyar allura ce da za a ce ba a ganta ba a gidan nan", Mami ta tashi ta shiga room dinta, wayarta ta ɗauka tayi dialing numbern Nurain, tana daf da katsewa ya ɗaga, Mami bata basa chance din mgana ba tace "where is she Nurain..?", Nurain ya tashi daga gefen gadon ya nufi door da wayar a kunnensa, Hajar tabi bayansa da kallo ta haɗe fuska, Nurain yace "tana gida", Mami tace "wane gida..?", shiru yayi baice komai ba, tini Mami ta sake gasgata hasashenta, strictly tace "i want to see you now" bata jira cewarsa ba ta katse kiran, Nurain ya ciro wayar daga kunnensa tare da sauke ajiyar zuciya. Hajar ta miƙe zaune gami da murje fuskarta a hankali, ba tayi wata wata ba ta buɗe wardrobe ta ɗauki box din da aka kawota da ita, tini ta bude section din da kayanta suke, duk kayan da ta san nata ne wnda tazo dasu gidan saida ta cirosu ta zuba a box din, tana gama kwashe kayanta tass ta zuge box din, bathroom ta shiga ta wanke fuskarta ta fito, da haka ta sauke box din ta jata ta fita daga room din, har wani bugu zuciyarta take tana fatan kar Allah ya haɗata dashi, daga nan sai gidan ubanta inda zata zauna ta sakata ta wala wnda baza ace alfarma ake mata ba, da kyar ta sauka downstairs da box din, direct ta nufi door ta murɗa handle, wani irin bugu zuciyarta tayi bayan taji ƙofar a kulle, ta sake murɗawa ta jita a kulle, wata ball ce ta tsaya mata a throat mai taurin bala'i, da sauri ta shiga kitchen ta duba ƙofar fita backyard ita ma dai taga a rufe take, walking like a chameleon ta fito hawaye ya cika idonta, wllh saita tafi gidansu, tasan ubanta bai aurar da ita don a mata alfarma ba. Nurain na isa gidansu direct wajen Maminsa ya shiga, sallamar da yayi ma Sakeena ce ta amsa, walking gently ya shiga palourn ya zauna kan Carpet, Mami ko kallon position dinsa ba tayi ba her eyes fixed on tv, Sakeena ta tashi ta shiga bedroom da plate din dice pineapple da take sha, Nurain ya shafa kansa yace "Mami barka da rana", ko kallonsa ba tayi ba bare yasa ran zata amsa masa, pen da jotter da ta ajiye a side dinta ta dauka ta miƙa masa tace "saura nima ka rubuta min irin abinda ka rubutawa baban ka", Nurain ya sauke numfashi yana kallon jotter da pen din, Mami tace "take now ka rubuta abinda kaƙi rubutawa jiya", ya shafa kansa yace "Mother wllh bxn iya sakinta ba, i can't do that", Mami ta gyaɗa kai ta ajiye jotter da pen din gefenta don daman so take ya faɗa da bakinsa cewa bazai iya sakinta ba, full attention dinta ta mayar kansa tana kallonsa da kyau tace "kasan bazaka iya sakinta ba shine kake iƙirarin cewa favor kake mata, kasan bazaka iya sakinta ba kake cewa ita ba choice dinka bace, duk kasan da hkan kuma kasan ba type dinka bace amma ka ƙi sakinta", Nurain dai baice komai ba fatansa dai kar a rabasa da Silly girl, Mami wasn't easy on him, saida ta tabbatar ta kwashe masa wnn girman kan tass, don kawai hangowa take ai ƴarta ce mijinta yake cewa ai alfarma yake mata, saida ta sule Nurain tass snn ta ƙare da faɗin "this is the least we expected from You Nurain, babanka bai taɓa sanin zaka watsa masa ƙasa a ido kamar haka ba shiyasa ya amso mka auren yarinyar nan", Nurain yace "Am so sorry Mother", Mami tace "don't mother me Uthman", Nurain ya ajiye numfashi yana jin kamar an watsa masa garwashi a zuciya, Mami ta nuna masa room din da box din Hajar take tace "wuce ka ɗauki box din tinda ka ɗauke me ita, and wnn shine last warning da zan mka akan Hajar, snn kuma Abba na jiranka a great room", Nurain bai iya cewa komai ba ya tashi ya shiga room din ya fito da box dinta, bai tarar da Mami a palour ba koda ya fito, door ya nufa ya fita main palour, yana jan rigarsa sai kace mai son ƙara mata tsaho ya shiga great room din Abba, dman yasan Abba bazai masa wani mgana ba tinda already Mami tayi, as expected Abba bai ce masa komai ba kawai ya amsa apology da ya nema. Hajar dake zaune kan stairs ta ƙurawa ƙofa lulu eyes dinta da suka haura matuƙa, da sauri ta miƙe jin an zura keys a ƙofar alamar za'a buɗe, kallonsa ta ringa yi har ya shigo ya ajiye ledar takeaway da ya tsaya a eatery ya siyo mata lunch don yasan da kyar idan ta dafa, ya sake komawa wajen ya dauko box dinta da ya ajiye a balcony, da haka ya mayar da ƙofar ya rufe ya zare keys din ya zura a pocket, Hajar ta saukar da kanta tace "why did you do that bayan mun sami chance..?", Nurain yayi folding hands dinsa yace "wani chance..?" yana kallon box din da ke gefenta, tace "Chance din da aka baka jiya na datse alaƙar dake tsakaninka da wcca kake yima favor, am not asking for much wllh just a piece of paper can end this relationship", Nurain yayi blushing moving towards the stairs yace "really.. but I can't divorce my wife..", Hajar was very shocked jin abinda ya faɗa, ta ringa kallonsa without blinking kafin ta haɗiyi wani yawu tace "your wife.. where is she...?", harda wani ƙanƙance ido ta faɗi hakan, bai ce mata uffan ba ya fara hawa stairs din, saida yaje step din dake kusa da wnda take kai snn ya dakata, ya ɗora hannunsa kan nata dake riƙe da railer, ta fara ƙoƙarin zame hannunta amma ya hana hkan, a hankali tace "let go off my ha...", maganar bata ƙarasa fita ba sakamakon saukar lips dinsa a forehead dinta, da sauri ta lumshe idonta don hakan yazo mata a bazata, after a while ya janye lips dinsa daga forehead dinta, ya rage murya yace "Delete all those stuffs from your head..", ta haɗe gira tana buɗe baki da shirin yin mgana ya haɗe lips dinsa da nata, and he gave her french kiss din da ya matuƙar firgitata ya kwance mata notin kai wnda ya ratsa har zuwa yatsun ƙafarta, saura ƙiris ta zube a ƙasa amma kuma bata zube din ba sbd riƙon da ya mata, he kissed her for almost a minute kafin ya haɗe forehead dinsu waje guda, ya goga karan hancinsa a nata yace "Tonight i will surely show you that you are my wife", yayi ajiyar zuciya yace "Tonight"......✍️

💛 HAJAR 💛

{76..}

★Bayan sallar la'asar wajen ƙarfe huɗu da rabi Naseer ya shigo gida da sallama, Nabilah dake zaune tsakar gida tana jajjaga kayan miya ta amsa sallamar tasa, tace "Yaya sannu da zuwa..", yace "yauwa Baba ya dawo..?", tace "Eh ya dawo amma ya fita masallaci har yanxu bai dawo ba", yace "Maama fa..?", Nabilah tace "ita tin ƙarfe uku ta fita", Naseer ya jinjina kai bai sake cewa komai ba ya buɗe ɗakinsu ya shiga, Umma ma bata nan don ɗakinta a rufe yake da padlock, Naseer na zaune ɗakinsu yana cin abincin da ya siyo yaji sallamar Baba, saida ya gama cin abincin snn ya tashi ya fita, kai tsaye ya wuce ɗakin Baba ya shiga da sallama, Baba ya dubesa yace "A'a Nasiru har ka dawo..?", Naseer ya zauna kan tabarma yace "Eh Baba", ya ciro wata paper daga aljihunsa ya miƙawa Baba yace "gashi Baba", Baba yaƙi amsar takardar yace "ba sai naga takardar ba yimin bayani kawai", Naseer yace "tom" daga haka ya fara yiwa Baba bayanin filin da aka siyar da kuma adadin kuɗin, Baba ya gyaɗa kai yace "masha Allah... sai a raba kuɗin gida uku, a ɗauki kaso ɗaya a yiwa Nabilah hidimar aure kamar yacca aka yiwa Hajara", Naseer yace "toh Baba sai a cire lissafin katifa ni zan siya", Baba yace "Allah yayi albarka", Naseer ya shafa kansa yace "Ameen", da daddare Baba na zaune tsakar gida bisa darduma yana cin abincin da Umma ta ajiye masa, Maama ta fito daga ɗaki zata shiga kewaye, ɗaga kai Baba yayi ya kalleta yace "Rabi", banza tayi dashi ta ɗauki buta tayi gaba abinta, bayan ta fito har zata koma ɗaki Baba ya sake kiranta, juyowa tayi tace "wai waye yake min shegen kira ne sai kace tsohon makaho", Baba ya rausayar da kai yace "idan kinga dama kixo idan kuma baki ga dama ba kar kizo", ƙasa ƙasa taja tsaki ta nufi inda yake ta zauna kan kujera ɗan nesa dashi, Umma dake zaune tsakar gidan itama ta tashi ta shiga ɗakinta, Maama ta bita da kallo sai kuma ta taɓe baki tace "gani fa mal Adamu", Baba yayi gefe da kwanon abincin yace "A matsayinki na uwar Nabilah nawa kike buƙata wnda zaki tsinto mata tarkacen kitchen da sauran su..?", Maama ta haɗe fuska tace "ban gane ba kuma ban fahimta ba, ji nake an mayarwa da yaron nan kuɗinsa", Baba yace "A sbd me za'a mayar masa da kuɗinsa", Maama tace "sbd ni uwar Nabilah banyi na'am dashi ba, bana sonsa kwata kwata don haka dole a fasa auren nan", Baba yace "toh baki isa ba auren Nabilah ba fashi..", Maama ta hura tukubar hancinta tace "mal Adamu karfa ka wani zaƙalƙale ehe, ita Nabilahr ai cewa tayi ta fasa auren", Baba ya kwalawa Nabilah kira bbu jimawa ta fito bayan ta amsa, ta duƙa gabansa tace "Baba gani", yace "kina son auren Tanimu ko ba kya so", Nabilah tayi shiru ba tace komai ba, Maama tace "Ahap ai na gaya mka", Nabilah ta kalli Maama wcca take ƙifta mata ido wai tace eh, Nabilah ta sunkuyar da kanta, Baba yace "Rabi ki bari yarinya tayi mgana da bakinta", Maama ta rausayar da kai tace "Toh ai gata nan", Baba ya sake kallon Nabilah yace "ba kya so..?", Nabilah ta girgiza kai, Baba ya sauke ajiyar zuciya yace "jeki abinki", Maama ta saki baki tabi Nabilah da kallo harta koma ɗaki kafin tace "amma dai yarinyar nan kin shammaceni... shekaran jiya na gama mgana dake ringiɗi ringiɗi kika ce kin fasa auren mai pachi shine ynxu zaki baɗamin ƙasa a ido", da haka ta tashi tabi Nabilah ɗakin tana sababi, Nabilah kam tayi mata shiru, Sa'adatu kam sai zabga tsaki take don Maama ta cika ɗakin da zance, Sa'adatu da ta gaji tace "haba dan Allah Maama sai ihu kike mna", Maama tace "ba dole nayi ihu ba, kina gani wnn yarinyar mai ƙwaƙwalwar kifi wai har ynxu bata bar mganar Tanimu mai pachi ba, so take tayi auren da zata ringa dawomin tana cewa na bata masara...", Maimuna tace "duk wnda yace zai haɗiyi gatari ai sai a sakar masa ƙota, ba dai ita tace taji ta gani ba", Maama tace "mai pachi fa ƴar nan ta jajiɓo...", Maimuna tace "A'a ai ynxu naga yana ƙulla gawayi ma", tashi Nabilah tayi ta bar musu ɗakin, zama tayi tsakar gida tana share hawayen dake zuba idonta, Baba na gama cin abincinsa ya ajiye kwanon yaje ya wanke hannu, duk yana sane da Nabilah dake matse hawaye. wajen ƙarfe goma Naseer ya shigo gida har zai shiga ɗakinsu ya tarar da Baba a ƙofar nasa ɗakin, Baba yace "Mu'azzam ya shigo..?", Naseer yace "ynxu na gansa wajen mai shayi amma nasan ba zai jima ba zai taho", Baba yace "Toh... Abinda nake so da kai Nasiru ko bayan raina kar a fasa auren Nabilah indai ba da wani ƙwakkwaran dalili ba, wnn wasiyya ce na bari..", Naseer yace "insha Allah ma kai zaka ɗaura auren Baba", Baba yace "ko dai bayan raina kaji dai me nace", Naseer yace "Eh", Baba yace "Port Harcourt din zaka wuce gobe..?", Naseer yace "insha Allah", Baba yace "toh saida safe" da haka ya juya ya koma ɗakinsa.

★Tinda Hajar ta idar da sallar la'asar take kwance inda tayi sallar, lokaci zuwa lokaci saita turo baki sai kuma ta harari iska, zaune ta miƙe ta kalli box din kayanta da ya shigo mata dasu, da wcca ta hada da kuma wcca ya taho mata da ita daga gidansu, a kan chest of drawers taga ledar abinci da ya ajiye mata wnda ƙamshinsa ya cika ɗakin, a hankali ta tashi taje ta ɗakko ledar ta buɗe, fried rice ce da taji kayan lambu sai rabin peppered chicken a gefe da plaintain, shinkafar kawai ta ɗan tsattsakura ta ajiye don ba tada appetite ma, kan chest of drawers ta mayar da abincin ta koma ta cigaba da kwanciya, bayan sallar magrib ta ɗauki ledar abincin zata kai kitchen don ƙamshinsa ya takura mata, a hankali ta buɗe ƙofa ta ƙarewa long corridorn kallo, bayan ta gama surveying corridorn da ido tayi ajiyar zuciya ta fito, walking slowly ta sauka downstairs, a hankali ma ta murɗa handle da zata shiga kitchen, ta ringa kallon kitchen din ganin shopping bags kan island da cabinet harda wasu ma a ƙasa, ta tsallake ta samu guri ta ajiye abincin da haka ta buɗe fridge, tana buɗe fridge din shima ta gansa a cike, ita dai ta ɗauki ruwa abinta ta zagaye ta fita, tana fita palour ta isa gaban main door ta murɗa, ta ajiye numfashi bayan taji ƙofar a kulle, wani ƙululu ne ya tsaya mata a throat don da a buɗe take kawai fecewa za tay abinta, da takaici ta haura sama ta koma room ɗinta, tin ƙarfe takwas da minti goma dman ta haye gado ta rufe da duvet har kai, hka nan saddan taji gabanta na faɗuwa shiyasa ma ta kwanta da wuri, ji tayi an buɗe ƙofa tayi sauri ta runtse idonta, zuciyarta har wani ɗif ɗif take after perceiving his scent, Nurain yafi minti uku yana kallonta kafin ya juya ya fita, ta sauke ajiyar zuciya bayan taji fitarsa, har goma saura Hajar ta nemi bacci ta rasa a idonta ta ringa juye juye tana so bacci ya ɗauketa amma ta kasa, lokaci guda ta sauko daga gadon, box din kayanta da ta kudurce bazata mayar dasu wardrobe ba har zuwa lokacin da zata samu chance din tafiya gidansu ta buɗe, showel gel da sponge ta ɗauka da haka ta shiga bathroom don yin wanka, gani take wankan da ba tayi bane yasa ta kasa bacci, bayan ta fito ta zauna kan stool, sharp sharp tayi rubbing lotion dinta wnda shima ta fitar daga box, perfume da take shafawa da daddare mara hayaniya ta shafa, tana gama fesa hair spray a gashinta zata ajiye gwangwanin knn aka buɗe ƙofa, sosai zuciyarta ta buga ta kalli ƙofar da sauri, Nurain ya daskare a inda yake tsaye riƙe da handle yana binta da kallo from head to toe, fararen pajamas ne a jikinsa masu riga armless da sweat pant, a gigice ta miƙe ta nufi inda hijab dinta yake, sai dai kafin ta kai ga ɗaukar hijab din har ya shigo ɗakin yayi sama da ita, Hajar ta tsala ihu jinta akan isa tace "Ni bana son haka ka ajiyeni", ko sauraronta beyi ba ya juya ya fita da ita daga ɗakin, bai tsaya a ko ina ba saida ya dangana har huge bedroom dinsa snn ya ajiyeta kan makeken gadonsa da yasha pure white bedding, tini ta hantsilo ƙasa ta miƙe tsaye gami da riƙe towel dinta tamau hannu bibbiyu, Nurain ya zuba hannayensa a pocket yana kallonta yace "Hey a kan wuta na ajiyeki ne..?", idonta har ya ciko da ruwa ta juya tana kallon ƙofa, ai kam kamar yasan abinda za tay shima ya kalli ƙofar, lokaci guda ta kwasa a guje ta nufi door har ta murɗa handle yayi saurin fixgota bayan ya hadata da jikin door din ya rufe, tini ta sakar masa kuka jin ya sakawa ƙofar lock, ya duƙa ya kalli lips dinta da suke rawa yace "Tin ynxu ma kin fara kuka yarinya... even before a kiss that you must beg for mercy", Hajar ta yarfe hannu har ta jiƙa cheeks dinta da hawaye tace "dan Allah dan Allah... ni wllh room dina zan tafi", ya ɗage gira his eyes fixed on her face yace "No you must spend the night here", in banda bugu bbu abinda zuciyarta take, a hankali ta gyaɗa kai tace "Naji toh i need to wear my clothe first", slight smirk yayi yace "you don't need ta wear anything tonight..", ta haɗiyi wani yawu ta share hawayen da yaƙi tsaya mata, sosai ta marairaice murya tace "dan girman Allah da manzonsa... dan darajar iyayenka ka taim...", kafin ta ƙarasa ya ɗora finger dinsa a lips dinta ya girgiza kai yace "don't", da haka ya barta tsaye bakin ƙofar ya shiga huge Closet dinsa, few seconds ya fito da farar Shirt a hannunsa ya ajiye gefen gado, yana kallonta yace "ba dai clothe zaki dakko a room din naki ba toh gashi nan kisa wnn", maƙe shoulder tayi tace "Ni bana son wnn nawa nake so", ya tsuke piercing eyes dinsa yace "ohh really", ya matsa kusa da ita, ba tayi aune ba sai jin hannunsa tayi zai kwance mata towel yace "lets remove this one ma", tini ta zille ta matsa gaban gado ta wafci shirt din sai kuma ta koma can side din gadon tana turo baki, wani muskilin murmushi yayi ya nufi door ya buɗe ya fita ya saka lock ta waje, Hajar ta sauke ajiyar zuciya sai kuma ta kalli Shirt din hannunta, room din ta ƙarewa kallo wnda yayi biyun nata, ga wani mugun sanyi da yake ratsa mata fata, rigar ta warware wcca ta shaƙo scent dinsa, har rabin cinya rigar tazo mata da ta saka, after like 10mins ta gaji da tsayuwa ta zauna gami da takure kanta waje guda, ɗago kanta tayi jin an buɗe door, ya ƙarasa shigowa ciki bayan ya saka lock a ƙofar, ya ajiye hijab dinta da ya biya ɗakinta ya ɗakko a gefen gado, sai kuma ya ajiye ledar da ya ɗauro kan plate a kan carpet, Hajar ta tashi tana kallon hijab dinta da ya ajiye, Nurain ya sauke ajiyar zuciya yabi fresh laps dinta da kallo, ai kam tini Hajar ta zaga ta inda hijab din yake ta dauki abinta ta kirma, shi dai bai ce mata komai ba, taga ya wuce inda ya shiga ɗaxu da zai ɗauko mata Shirt, bai wani jima ba ya fito yana jan hannun jallabiyan da ya ɗora kan Pajamas da alamar ruwa a fuskarsa, ba tare da ya dubeta ba yace "go and perform ablution..", ta wani tsaya sai kace soja tace "Ah ni nayi sallah na", yace "toh wnn is different tare za muyi", ta maƙe shoulder ta koma jikin door tace "dan Allah ka bude min na tafi room dina..", yace "Ohk okay idan kinyi sallah sai na buɗe miki", ta saki baki tana kallonsa zuciyarta na wasiwasin abinda ya faɗa, ta saukar da murya tace "dan Allah idan nayi sallahn zaka budemin..?", ya gyaɗa kai yace "Sure", walking like a chameleon ta dawo ta tsaya kan lallausan carpet din da ya shimfiɗa babbar prayer mat a kai, yana kallonta bbu ko ƙiftawa yace "Ablution..", ta turo baki tace "Ni nayi alwala na", don duk lokacin da tayi wanka da daddare sai tayi alwala, ba dai Sallah ce zata rabasu ba toh taji za tayi sallah ya bude mata ta tafi, kamilar Sallah raka'a biyu ya jasu wcca ya biya surori masu ɗan tsaho, bayan sun idar da Sallahn taga sai Addu'a yake, Alla Alla take ya shafa ya bude mata ta ƙara gaba, saida ya kwashe almost 5mins yana addu'a snn ya shafa, ya juyo yana kallonta, tana ɗago kai sukay ido huɗu ya sakar mata murmushi mai kyau, Hajar was so surprised with that smile ta kasa dena kallonsa, lokaci guda ta saukar da kanta tana wasa da fingers dinta, Nurain yayi ajiyar zuciya ya tashi ya cire jallabiyan jikinsa ya bar ainahin white pajamas, ya buɗe ledar roasted chicken da ya shigo da ita, cinya ya ɗauka ya miƙa mata without saying anything, ta girgiza kai murya ciki ciki tace "Nayi sallahn Please open the door", yace "why would i open the door...?", tini ta ɗago ta kallesa da mamaki, ya ɗaga shoulder yace "Ohh i will only open it idan kika ci wnn", ta girgiza kai lulu eyes dinta suka ciko da ruwa tace "please am begging you ka bude min na tafi", yace "Ohh i will amma eat first", Hajar ta amshi kazar ta riƙe a hannu after few seconds ta kai baki, yaga uku tayi ta ajiye tace "toh open", ya ture ledar kazar daga gabansu ya matso daf da ita har tana jin breathing dinsa yace "have you forgotten Silly girl... i have to show you that you are my wife remember", tini ta fara muskutawa baya ai kam ya riƙo hijab dinta, habawa saita miƙe zumbur unfortunately saiga hijab din a hannunsa bayan ya sule daga jikinta, ta fashe da kuka tace "Allah kuwa ba haka mukay da kai ba, kai fa kace idan nayi sallah zaka buɗe min na tafi", murmushi mai sauti yayi ya miƙe tsayen shima yace "na fasa", tana ganin ya fara tunkararta ta ringa tafiya da baya har saida ta kai bango, still dai taga zai biyota bangon ai kam tayi gefe zata zille amma ina don tini ya riƙota, ta tsala wani uban ihu ganin ya mata rumfa tace "Ummana... wayyoh Ummana", lips dinta da suke shivering kawai yake kallo, ya ajiye numfashi ya riƙo ƙugunta getting even more closer to her, turasa ta fara yi tace "kar fa ka mnta kace am not your wife and I will never be..", ya manna mata kiss a right Cheek da muryarsa da har ya fara canzawa yace "Now i will show you who am i to you... you are my Halal..", kuka take harda shessheƙa ta girgiza kai tace "please No... Hajar ce fa wnn ba choice dinka ba...", ya sake manna mata wani kiss din a left cheek yace "Action speak louder than voice" daga nan bai sake bata damar mgana ba ya haɗe bakinsu waje ɗaya, passionately yake kissing dinta babu wani sassauci, tini ya fara loosing stamina dinsa, tsayuwar ma ta fara gagararsa ballantana ita da daman shi ya riƙeta, don haka ba wani jinkiri ya ɗauketa sai gado, remote control dake kan bedside ya ɗauka ya rage hasken ɗakin ya bar dim, Hajar da numfashinta ya ɗauke na wucin gadi ta danna wani ihu jikinta na ɓari kamar an jona mata mazari, bakin ihun ya rufe snn kuma ya zafafa lamarin, da haka ya rabata da kayan jikinta wnda ma basu samu fita ta arziƙi ba don farkesu akay, daga nan shima ya rasa control, Hajar ta kwallara ƙara bayan taji azabar da bata taɓa jin irinta ba tinda uwarta ta haifeta, bama gentle yabi da ita ba extra gentle ne amma saida taji azaba, lokaci guda ta fara magiya tana haɗasa da Allah amma ina bai ma san tanayi ba, da taga magiyar bazai kaita ba sai ta fara kokawa, anan ya gwada mata ba ƙarfinsu ɗaya ba, cixo yakushi da mintsili bbu wnda ba tayi ba amma a banza an yakushi kakkausa, And at that night bummmm the bomb exploded, ba part one ko part two na raini aka fitar ba, shi rainin gaba ɗaya aka fitar don anyi mai kankat.......✍️

Join my WhatsApp group to read page 77, or go to Arewabooks....

👇
https://chat.whatsapp.com/JQi46zH5Se3IvhrdEGHdIA
💛 HAJAR 💛

{77..}
Nurain ya buɗe lumsassun idanunsa tare da yin ajiyar zuciya, juyawa yayi ya dubi Hajar dake gefensa, ya miƙe zaune ya kunna hasken ɗakin yana kallonta da kyau, kana ganinta kasan tayi laushi tamkar flour da ta sha bugun gardi, shi dai bai san tayi laushi hka ba amma he vividly remember what just happened, yasan shi ya ƙarar mata da strength, ya kalli fuskarta da tayi jajir tare da lallausan gashinta da ya baje kan pillow wnda shi ya hautsinasa, ya lulluɓeta da duvet snn ya tashi ya shiga bathroom, da sauri ya gama kimtsa kansa ya fito yana goge sumarsa da ƙaramin towel, sharp sharp ya saka white singlet da short nicker don so yake ya kula da yarinyar kuma, shi yayi aika aika don haka shi zai gyara, kan gadon ya isa ya zaune gefe yana kallon innocent face dinta, ya shafa cheek dinta da hawaye ya bushe a kansa, a hankali yayi tapping dinta gami da rage murya ya kira sunanta, ko motsi Hajar ba tayi ba bare yasa ran zata amsa, ya kamo hannunta ai kam yaji she's very weak don baya tinanin tana cikin conscious dinta, da sauri ya miƙe daga gadon ya shiga bathroom bbu jimawa ya fito da ruwa a bowl, kaɗan ya zuba ruwan a hannunsa ya yayyafa mata a fuska sai kuma ya hura mata iska ya kira sunanta, haka ya cigaba da mata har saida taja numfashi, yana ganin haka ya ɗora goshinsa saman nata yace "open your eyes baby girl" sai kuma ya ɗago yana kallonta, after few seconds Hajar ta buɗe idonta da suka kumbura wnda suke mata wani zugin barkono, suna haɗa ido dashi tayi saurin kawar da kanta gefe lokaci gudu hawaye suke fara zarya bisa kuncinta, ga wata azaba da ta yanko mata tin daga waist har zuwa laps dinta, ji take kamar ana mata ruwan allurai, tinda yaga ta farafado bai tsaya wani jinkiri ba ya ɗauketa kawai, ya ringa kallon inda ya ɗagata kafin ya wuce bathroom, a wnn dare Hajar taga jalala, ji tayi kamar a ruwan jajjagaggen attaruhu ya sakata, ba iya Umma ta ringa kira ba har yayanta da little sister dinta saida suka sha kira, Nurain pity her don yasan she's in pain, haka dai ya cije ya gasa abarsa don hakan shine zaisa taji dama dama, A kan couch ya ajiyeta tana nannaɗe da bathrobe dinsa, sai jan zuciya take idonta a runtse don tinda ta farka sukay ido hudu bata sake buɗe idonta ba, closet ya wuce ya dauko mata wata shirt dinsa mai laushi, inda take kan couch ya nufa ya kai hannu zai kwaye bathrobe din, tini ta ƙanƙame bathrobe din, sakar mata yayi ya ajiye mata Shirt din akan cinya, ta wani turo baki ta cukuikuiye shirt din a hannunta, upper bedsheet din gadon ya kware ya shiga dashi bathroom, After like 10mins ya fito, idonsa a kan couch ya fara sauka, yaga ta saka rigar ta jinginar da kanta a couch din, walking gently ya isa gaban couch din ya duƙa, ya ringa kallonta without blinking, wato an samu sauƙi tinda gashi bacci ma take saidai kuma har ynxu jan zuciya take, ya tuna ranar daya fara ganinta da rashin kunyar da ta zabga masa a duk wasu encounter dinsu kafin a aura masa ita, yayi blushing bayan ya tina dramas dinta da yasha bayan aure, duk wata rashin kunya da ta masa yaji tayi fading a zuciyarsa don gani yake shafar mai ne akan abinda ya mata, he took away her valuable item her honor her pride wnda a ynxu yasa yake matuƙar ganin kimarta, he found his wife intact wllh, murmushi yayi bayan ya tuna yadda ta kasance ɗaxu a hannunsa, yafi minti goma yana a haka kafin ya miƙe ya ɗauketa gami da haɗata da ƙirjinsa zai mayar da ita gado, Ai kam ta buɗe idonta bayan ya ajiyeta a kan gadon, a gigice ta fara shirin miƙewa har jikinta na rawa, ganin yacca ta tsorata kawai ya rumgumeta ya kwanta da ita a jikinsa, ta fashe da kuka tana ƙoƙarin kwace kanta ƙarfi da yaji don sosai ta firgita, gam ya riƙeta motsin ma ta kasa sai kuka, yayi ajiyar zuciya yace "wollah i will not hug pillow bayan i have my wife" da haka yaja duvet ya rufa musu, ya kai lips dinsa saitin kunnenta yace "let me give you warm baby girl", tayi lamo listening to his heartbeats, lumshe idonta tayi tana jin ydda yke shafa tin daga bayanta zuwa wet hair dinta, few minutes kam ta koma bccinta deeply in his arms. Da Asuba Hajar ta farka ta buɗe idonta a hankali, ta ringa bin room din da bbu wani haske sosai da kallo, sai kuma ta juya ta kalli both sides dinta taga ita kaɗai ce a makeken gadon, da kuzarinta ta yunƙura ta miƙe zaune gami da zuro ƙafafuwanta ƙasa, tana taka ƙafarta a ƙasa taji wata azaba data shallake tunaninta wccca ta ratsa har brain dinta, ta fasa ƙara a gigice sai kuma ta tafi luuu ta faɗa kan gadon da baya, ji tayi kamar ana mata ruwan allurai a laps dinta, lokaci guda brain dinta tayi booting on hawaye suka fara sakko mata, tafi minti biyar a kwance kafin zugin da jikinta yake mata ya ragu still dai bata dena hawaye ba, tana ji aka buɗe ƙofa aka shigo amma bata motsa ba, Nurain ya ƙarasa shigowa ɗakin yana kallon position dinta, a yacca take kwance gefen gadon yasan cewa ta farka ne, yana isa kusa da ita ya tabbatar sbd hawayen da ya gani kwance cheeks dinta, ya duƙa ya kalli lumsassun idanunta da tinda taji shigowarsa ta rufe yace "Hajar", haɗe fuska tayi gami da turo baki sai kuma ta kawar da kanta, murmushi yayi cause yasan fushi take kuma baiga laifinta ba don tayi fishi dashi, ya rage murya yace "let me take care of you baby girl" da haka ya fara tattare hannun button down shirt da ya saka da zai fita mosque sai kuma ya nufi bathroom, ruwan zafi ya tara a tub ya sirkasa kamar na daren jiya. This time around Hajar ji tayi kamar a ruwan jajjagaggen tattasai ya sakata, though ba taji azaba kamar na daren jiya ba amma dai ta ɗanɗana shima, saida ya tabbatar ta gasu snn ya fito ya barta a bathroom din don tayi alwala, walking slowly Hajar ta fito daga bathroom da rigarsa dake jikinta wcca ta tsaya mata a rabin cinya, yana zaune tsakiyar gado yana operating laptop, suna haɗa ido tayi saurin janye nata zuciyarta ta buga da ƙarfi, ji take kamar ta nutse a wajen, bai ɗauke idonsa daga kallonta ba yana lura da yanayin tafiyarta har ta ƙaraso cikin ɗakin, hijab dinta ta ɗauka ta saka without looking at him for the second time ta kalli qiblah, yana ganin ta kabbara sallah ya tashi ya nufi door, after 15mins ya dawo ya tarar har ta idar da sallar tana zaune kan darduma, inda take ya nufa ya duƙa ya ajiye mug din hot chocolate da ya shigo dashi, da sauri ta haɗe kanta da guiwa don bazata iya haɗa ido dashi ba ga kuma azabar tsoronsa da ya cikata, ya kamo hannunta da taushin murya yace "yau ma ba gaisuwa...?", sai kace an ƙunduma mata zagi haka ta fashe masa da kuka bil haqqi, ya waro ido yace "Laa me aka miki..?", ita dai taƙi mgana kawai kuka take kamar an aikota, ganin har ta fara jan shessheƙa yace "stop crying and tell me what happened... ko masquerade din ya sake zuwa ne..?", mganar ma bata fita sosai sbd muryarta ta dashe tace "Ni gidanmu zan tafi... i don't like it here, i want to go home please", yayi blushing don shi da tayi mgana ma daɗi yaji yace "where are you going from your husband's house Silly girl..?", a hankali tace "i don't have one..", ƙoƙarin ɗago fuskarta yayi ya kalli cikin idonta amma taƙi ɗagowa, ya jingina kansa a nata gami da mgana in a whisper yace "you don't have one After last night", turo baki tayi ba tace komai ba, yace "yesterday's night was so amazing, super sweet, i really enjoyed it.. i hope today's night will be more sweeter", yana gama fadin haka ya janye kansa a nata sai kuma ya fara ƙoƙarin ɗago kanta, firr taƙi yarda don har wani shivering take, da kyar yayi nasarar riƙe haɓarta tana jin haka ta faɗa ƙirjinsa snn ta rufe fuskar a nan, tini ya sauke ajiyar zuciyar da bai shirya mata ba, gaba ɗaya sensory nerves dinsa saida suka kai electric shock brain dinsa, mug din hot chocolate din dake gefensu ya matsar sai kuma ya dafe bayanta yana daɗa shigar da ita jikinsa sosai, tayi lamo a jikinsa ita dai she don't care indai za tayi avoiding eye contact dinsa, patting bayanta yke with one hand yace "Thank you for yesterday's night... Sorry for the pain..", ita dai ta lafe a jikinsa sai kace anan aka halicceta perceiving his pure scent, after 5mins yace "baby wife here is your free breakfast" da haka ya zameta a jikinsa, sam bata bari sun haɗa ido ba, mug din chocolate din ya dauka ya kamo hannunta ya damƙa mata, ya ajiye numfashi ya tashi ya nufi door ya buɗe ya fita palour, kan sofa ya zauna yayi resting yana sauke ajiyar zuciya, so yake ya bata hutu don ƙarama ce baya so ya sake taɓata sai tayi healing, iya hugging dinta da yayi ynxu har lissafinsa ya fara kwancewa shiyasa ya bata space snn shima yayi calming kansa down, sai after 1hour ya koma ɗakin, ya tarar ta sha rabin chocolate din ga ragowar nan ta ajiye, ta koma baccinta nan kan carpet, kan gado ya mayar da ita ya rufa mata duvet sai kuma taɓa goshinta to feel her body temp, yeah temp dinta ya ɗanyi high amma ba sosai ba dman dole sai hakan ta faru.

★Maama ta saki baki har miyau na shirin zuba tana kallon Maimuna da ta shigo ɗaki tana yamutsa fuska tace "wai Aman kika sake yi..?", Maimuna da tayi wani lakwam ta faɗa kan gado tayi rub da ciki tace "Eh", Maama tace "gsky ba lfy.. ko dai wnn cutar da ake ta amai da gudawa ce ta kamaki", Maimuna ta girgiza kai tace "Amai kawai nke fa..", Maama tace "na kawo miki kunun tsamiyar za ki sha..?", Maimuna ta girgiza kai tace "A'a na ƙoshi...", Maama tace "wane irin kin ƙoshi iyeeh, yau tinda garin Allah ya waye ubanki kika sakawa cikinki salon dai cutar ta miki muguwar illa", Maimuna da take mgana tana yamutsa fuska tace "zan sha anjima..", Maama tace "Allah ya kaimu anjiman" ta tashi tana baza zani ta fita, wajen ƙarfe sha biyu Maimuna na farkawa daga bacci Maama ta ciko kofi da kunu ta kawo mata, ai Maimuna na yiwa kunu kurɓa ɗaya ta toshe baki sai kuma ta zura da gudu ta fita waje, nan bakin rariya ta durƙushe ta ringa kakarin amai, Umma tayi sauri ta janye robar gwangwanayenta da take wankewa, Nabilah tayi kasaƙe da tsintsiya a hannu tana kallon Maimuna da har lokacin take kakarin amai, Nabilah ta ajiye tsintsiyar ta zuba ruwa a buta ta ajiye gefen Maimuna sai kuma ta koma ta cigaba da tattare tsakar gida, Maimuna ta kuskure bakinta ta tashi sai kace wcca ta shekara tana jinya ta shiga ɗaki, Maama ta tarar ta sauya kayan jikinta tana shirin saka hijab, Maama tace "kar ma ki kwanta saka mayafinta na kaiki Chemist", Maimuna ba tayi musu ba don itama lfyr take nema ta canza kaya, Maama tace "Akwai kuɗi a hannunki..?", Maimuna ta girgiza kai, Maama tace "Au tsimilmilar ma har kanki za ki yiwa, toh ki fito da kuɗin da za'a siya miki mgana dan nidae ɗari biyar ce kawai a wajena", Maimuna tace "wllh Allah ba nida ko kwandala", Maama tace "ina kuɗin da Alhaj din naki yake baki..?", Maimuna tace "Ni yau sati biyar knn rabona dashi wllh, ko na kira wayarsa ma bata shiga", Maama ta ringa kallonta don ta lura gsky take gya mata ba tada kuɗi, Maama tace "dena ɗaukar wayarki yayi...?", Maimuna tace "Eh dman yace min aiki ya masa yawa bxn ringa samunsa ba", Maama ta gyaɗa kai tace "Au toh", tsakar gida suka fita Maama na kallon Nabilah tace "zan kai Maimuna chemist tana fama da masassara", Nabilah tace "toh sai kun dawo", Maama tace "yawwa" da haka ta nufi soro tana riƙe da Maimuna wcca take tafiya a hankali, suna isa chemist Maimuna ta zauna kan benjin dake cikin Chemist din, mai Chemist na gamawa da mutumin da suka tarar ya waiwaye su, ƴan tambayoyi ya yiwa Maimuna ta ringa basa amsa, ya kalli Maama yace "A kaita asibiti su mata gwaje gwaje kawai", Maama tace "kai bazaka iya mata gwaje gwajen ba anan, masassara ce fa take damunta", yace "A'a aje dai asibiti, ni Strip kawai zan iya baku", Maama tace "meye kuma sitirif..?", Strip din ya ɗakko yace "gashi", Maama ta amshi ledar Strip din tace "kai da zaka bani magani sai kuma ka miƙomin robar banza", mai Chemist ya amshi Strip dinsa yace kawai suje asibiti, Maama na sababi suka bar Chemist din tace su tafi wani, Chemist biyu suka je bayan wnn shima dai abinda ake ce musu knn, Maimuna kam har ta jigata ta dawo jan ƙafa, jingina tayi da bango tace "Maama dan Allah mu tsaya gidan Balaraba na huta", Maama ta haɗe fuska sai kuma ta saki fuskar bayan ta tuna har gida Balaraba tazo ta bata haƙuri, gidan Balaraba suka wuce wcca ta saukesu a tsakar gida, Maimuna ta sheme kan tabarma zuciyarta na wani irin hautsinawa, bayan Balaraba sun gaisa da Maama tace "lfy dai na ganku da ranar Allah..?", Maama tace "uhmm tinda kika ga haka ai ba lfy", nan ta gaya mata ai Maimuna ce ba ta jin daɗi shine suka fito Chemist, Balaraba tace "Ayyah Allah ya bata lfy", a kasale Maimuna ta yunƙura tana toshe baki ta nufi gaban rariya, ba tayi aman ba ta dawo ta kwanta, Balaraba ta ringa kallonta kafin ta jinjina kai ta kalli Maama tace "Rabi kawai kuje asibitin", Maama tace "toh idan munje asibitin shekaruna zan lalo na basu, kuma da rana tsage tsage zamu tafi asibitin ma'aikatan lfy da basu da kirki ai sai su kaɗomu..", Balaraba tace "inada kuɗin da aka kawomin ajiya sai na ranta miki ai, ita lfy ai yar sarki ce gwara a nemeta", dubu biyar Balaraba ta rantawa Maama da wajewar nan da sati ɗaya zata biyata kuɗinta, Maama tace "ba zai ma kai sati ba ko gobe sai na kawo miki kuɗinki don ubanta na dawowa zan amso kuɗin a wajensa, amma dai ynxu wani asibitin za mu nufa..?", Balaraba tace "nan nan ma asibitin gangare zasu dubata.. bari na raka ku", haka nan Balaraba ta raka su Maama can wani karamin asibitin gwamnati, kuma suna zuwa aka ɗebi jinin Maimuna za'a mata test din abinda ake zargi, Balaraba na zaune kan benci tare da Maimuna a inda suke jiran result, Maama ta tafi siyowa Maimuna ruwa don tace ƙishi ruwa take ji, wata Nurse ce ta fito da takardar result din test din ta kira sunan Maimuna, Balaraba tace "gata nan", Nurse din ta isa inda suke ta bawa Balaraba takardar tace "nasan dai ku manya ai kun san me yake damunta kawai dai kunxo nan ne dan ku tabbatar", Balaraba tace "me yake damunta..?", ba yabo ba fallasa Nurse din tace "Ciki ne da ita na tsahon sati uku... Allah ya raba lfy", Balaraba da ta gasgata zarginta ta saki fuska kamar ba komai tace "toh Alhmdllh mun gode likita", Nurse din bata daɗe da tafiya ba sai ga Maama nan da ledar pure water biyu, Balaraba ta ringa kallonta har ta iso, Maama ta tashi Maimuna da bacci ya kwasheta don ko zuwan Nurse din bata sani ba ta bata ruwan tasha, duk Balaraba na kallonsu saida ta gama shan ruwan snn tace "mu tafi gida kawai", Maama tace "ai bamu gama ba", Balaraba ta nunawa Maama takardar tace "gashi nan sun rubuta mta magunguna muje gida kawai na miki bayani", haka dai suka sake runtuma suka wuce gidan Balaraba, Maama ta fixge hijab dinta snn ta tuge ɗan kwalinta tana kallon Balaraba da idonta kamar zasu faɗo, ƙiris ya rage ta kurma ihu ta ƙundumawa Balaraba wata mummunar ashariya tace "Ƙarya kike billahillazi la'ilaha illa huwa", Balaraba ta wurga mata takarda tace "toh duba ki gani da idonki idan karya nake ƴarki bata kwaye zani an ɗirka mata ciki ba, dman shiyasa nace mu taho gida don nsan tsaf zaki tonawa kanki asiri a cikin jama'a", kafin kace me gumi ya jiƙa Maama har yana ɗiga, habawa ai da Maama ta wani zabura sai kace wcca aka kaɗo daga dawanau tayi kan Maimuna ta ringa loda mata hannu tana fatali da ita, Balaraba ta ringa ƙoƙarin kwace Maimuna tana cewa "ki rufamin asiri kar kiyi kisan kai a gidana na shiga uku", ina saida Maama ta yiwa Maimuna lilis har ita kanta ta gaji da duka snn Balaraba tayi nasarar amsheta ta wurgata banɗaki, mala mala Maimuna tayi a ƙasan dauɗaɗɗen banɗakin don ba tada maraba da sumammiya, Maama ta ɗora hannu bibbiyu a ka ta kurma wani uban ihu sai kuma tayi rimi tayi zaman ƴan bori a ƙasa ta fara tumami, wiwi ta ringa kuka irin na takaicin nan don ko hawaye bbu sai wata azaba da maƙogoronta ke mata, Balaraba ta juyar da kai tana dariya ƙasa ƙasa don yacca Maama ta zaro harshe tana kuka sai kace Akuya mai naƙuda ba ƙaramin dariya ta bata ba, saida Balaraba ta gama dariyarta wcca Maama bata lura ba snn ta matsa kusa da ita tace "ƙawata ki bani hankalinki nan, mu tone ƙasa mu rufe sirrin nan bbu wnda yaji bbu wnda ya gani kamar yacca muka saba".

★Hajar bata farka daga baccin da ta koma ba sai sha ɗaya da minti goma, a hankali ta miƙe zaune tana mamaki da ta ganta a gado, da kyar tayi shahada ta zuro ƙafafuwanta ƙasa amma kuma sai taƙi taka ƙasa don tsoro take ji kar taji zafi, ta lallaɓa ta miƙe tsaye sai kuma taga ba taji zafin ba, walking slowly ta nufi door ta murɗa handle, wata ajiyar zuciya ta sauke jin ƙofar ta buɗe, ai kam tini ta nufi ƙofar fita daga ɓangaren tayi sliding ta fita, sai kace mai tafiya akan ƙaya har ta isa room dinta, wani sanyi ne ya ratsa mata zuciya sai kace wcca ta shigo inuwa daga rana, ta mayar da ƙofar ta kulle ta jingina da ita, turo baki tayi don ƙamshinsa kawai take ji duk da cewa ta baro room dinsa, lokaci guda ta kalli kanta taga shirt dinsa ce fa a jikinta, bathroom ta shiga ta cire rigar ta daura pink towel, wanka tayi da warm water ta fito, bata iya zama kan stool ba ta zauna gefen gado tayi rubbing lotion, ta ringa kallon inda box din kayanta suke taga basa nan, kamar da wasa ta bude wardrobe ai kam sai ga kayan a jere intact, she was very shocked haka dai ta fitar da wata gown mara nauyi da hula ta saka, lipbalm ta goga a pink lips dinta da sukay pink sosai, sama sama ta fesa perfumes masu sanyin ƙamshi, gyara arrangement din kayan kan mirror din ta fara duk da cewa basu wani hargitse ba, door aka buɗe ya shigo tare da yin sallama, ai ko da wasa bata kalli ƙofar ba, lips dinta suka motsa lokacin da ta amsa ciki ciki sai kuma ta haɗe fuska, ya ƙarasa shigowa ciki ya ajiye ledar hannunsa kan chest of drawers, tini ƙamshinsa ya baza room din, kallonta yake bbu ko ƙiftawa and he was so happy da ya ganta a hka, tinda ya shigo ta kasa cigaba da jera cosmetics din cause hannun nata ma rawa yake, gaban mirrorn ya ƙarasa ya tsaya daff da bayanta har jikinsu na gogar na juna, a bazata ta ɗago kanta sukay ido huɗu ta cikin mirrorn, da sauri ta saukar da kanta tana jin kamar ta nutsu a wajen, zagaye flat tummy dinta yayi yana kallonta ta cikin mirror yace "how are you feeling now..?", ba tace uffan ba ta ringa kallon hannunsa daya ritsa cikinta, ɗan girgizata yayi yace "uhmm ynxu kin dena jin pain din...?", a hankali ta gyaɗa kai tana turo baki, yace "Good, i bought your breakfast.. eat alot kinji baby girl", nan ma kai ta gyaɗa masa, lips dinsa ya kawo saitin kunnenta har tana jin breathing dinsa, ba shiri ta lumshe idonta tana jin kamar an kwara mata ruwan ƙanƙara, yayi pecking cheek dinta lokaci guda ya saketa yace "Sai na dawo" da haka ya fita daga ɗakin, after few seconds da fitarsa Hajar ta sulale ƙasa ta ajiye numfashi. Shi kam direct downstairs ya sauka ya shiga motarsa ya bar gidan zuwa gidansu zaije wajen Abba da yake kiransa, with minimum speed yake jan motar time to time sai yayi blushing a haka har ya isa gida, yana shiga gida dman direct ɓangaren Abbansa ya shiga, suna gama mgana da Abba ya fito da envelope a hannunsa ya wuce wajen Mami, a bedroom dinta ya sameta ya zauna kan carpet ya gaisheta, with care ta amsa masa kmar ba ita bace ya sha faɗa a wajenta jiya ba, ita da Abba hka suke daga sunyi faɗa toh a wajen suke barinsa basa sake tayar da zancen ko kuma su ringa canzawa mutum fuska, No idan abu ya wuce toh ya tafi knn a wajensu, tace "how is my daughter...?", Nurain ya shafa kansa yace "She is great", Mami tace "Masha Allah", sai kuma ta kalli envelope din hannunsa tace "where are you taking that..?", yace "house of assembly", ta gyaɗa kai tace "Ohk baka je work ba..?", yace "yeah", Nurain beyi tunanin zai daɗe a wajen da Abbansa ya aikesa ba, sai yamma liƙis ya dawo gidansu in a hurry kawai zai bawa Abba abinda ya amso ya wuce gida, gaba ɗaya hnkalinsa yayi kan Hajar da ya bari a gida, sharp sharp ya fito daga ɓangaren Abba har zai fita sai kuma ya juya ya shiga wajen Mami don mata sallama kafin ya tafi, ko zama ma beyi ba ya tsaya ta bayan kujerar da take zaune yace "Our Mami saida safe..", Mami ta juya ta kallesa tace "Ohh you are leaving already..?", da sauri yace "yeah", Mami ta ɗage gira tana kallonsa, tace "Ohk.. go in za kaga blue leather bag kan bedside ka kaiwa Hajar... tin jiya Sakeena da zata tafi tace na baka idan kazo", yace "tom" da haka ya shiga bedroom din, after few seconds ya fito hannunsa wayam ba ledar yace "Mami ban gani ba..", Mami tace "A kan bedside din..?", yace "Eh", Mami tace "A kan right bedside fa", bai ce komai ba ya sake komawa ɗakin nan ma ya fito bbu ledar, Mami ta haɗe gira ta tashi ta shiga room din da kanta, bbu jimawa sai gata nan ta fito da ledar a hannunta, ta ringa kallon Nurain da yake ta murza palms sai kace mai jin sanyi tace "where is your sense Nurain..?", ya sauke ajiyar zuciya gami ta shafa kansa yace "ban gani bane Mami", Mami ta girgiza kai ta miƙa masa ledar tace "Goodluck", da kallo ta bisa har ya fita daga palourn nata, ko saurin me yake oho. Daf da sallahr magrib Nurain ya isa gida, da bibbiyu ya ringa tsallake stairs har ya haura sama, kai tsaye room dinta ya buɗe, ya ringa ƙarewa room din kallo don bai ganta ba, saida ya shiga ciki snn yaji ƙarar ruwa a bathroom, juyawa yayi ya fita ya shiga ɓangarensa, kafin yayi wanka ya shirya har an kira sallah don haka sharp sharp ya gama shiryawa ya fito, ya sauka downstairs zai wuce mosque kar sallah ya wucesa, yana dawowa mosque ya shiga room dinta ya tarar ta idar da sallah knn, ya ƙarasa shiga ciki ya duƙa gabanta, tayi saurin kawar da kanta gefe, yace "have you eaten..?", slowly ta gyaɗa kai, yace "me kika ci..?", Calmly tace "Noodles", yace "you cook it..?", ta gyaɗa kai, ajiyar zuciya yayi wato har ma ta iya sauka kitchen tayi girki. Washe gari da Asuba Hajar ta buɗe idonta, a zabure ta miƙe zaune tana tattaɓa gadon da take kai, sai kuma ta fara ƙarewa ɗakin kallo, ita dai tasan jiya da daddare da tayi wanka ba'a nan ta kwanta ba, ita da ta kwanta a ɗakinta toh me ya kawota nan, can ta hangosa kan couch yana karanta Holy Qur'an, tini ta diro daga gadon tana gyara silk sleeping gown din jikinta, sum sum ta nufi door yace "where are you going..?", tini zuciyarta ta hau lugude don wani azabar tsoronsa take ji, muryarta na scratching tace "ɗakina zan tafi nayi sallah", yace "shi nan din ba'a Sallah..?", ta girgiza kai tana jan slim fingers dinta tace "bbu hijab a nan", yace "says who..? wancan ba hijab bane", saukar da kanta tayi ba tace komai ba, after a while ta shiga bathroom tayo alwala ta fito, hijab dinta wnda tinda tin daren shekaran jiya yake room din ta zumbula tayi sallah, Nurain ya cigaba karatunsa, tana gama azkar dinta kanta a ƙasa tace "ina kwana", ƙasa ƙasa ya tsinkayo muryarta, saida ya kai Aya snn yace "morning how was your night..?", a hankali ta amsa don ma bai ji me tace ba, after 5mins ta tashi ta nufi door zata fita don ɗakin da mai shi tsoro suke bata, a hankali ya rufe Al'qur'anin yace "shi hijab din da shi kika zo da zaki fita dashi..?", turo baki tayi ta dawo ta cire ta ajiye inda ta ɗauka, ga hijab nan ita dai bazata zauna ba, sai dai me tana murɗa handle taji ƙofar a rufe, a bazata taji zuciyarta ta buga ta juya ta kallesa, wani murmushi ta tsinta a fuskarsa kamar wnda zaiyi dariya, habawa tini ta fara bubbuga legs dinta a ƙasa kafin kace me hawaye suka hau zarya bisa kuncinta tace "Ni wllh bxn zauna a nan ba room dina zan tafi", saida Nurain ya kusa melting a inda yake tsabar yacca shagwaɓar da take masa ta shigesa, yayi resting kansa gami ta taɓe baki yace "ohh really, toh an riƙe maki ƙafa ne", bata fasa abinda take ba tace "Ni dae ka buɗe min", ya lura ma ko kallonsa ba tayi duk wnn abun amma take cewa ya buɗe mata ƙofa, yace "Na ƙi din", sulalewa tayi ƙasa sai kuma ta fashe da kuka, ya waro ido yayi slight smirk ya tashi ya durƙusa gabanta, idonsa ya sauka akan ƙirjinta da yake sama yana ƙasa, kasa ɗauke idonsa yayi daga wajen, within few seconds har idonsa ya canza, ya ja doguwar ajiyar zuciya ya kai hannu ya riƙe haɓarta ya ɗago fuskarta, tini ta haɗiye kukan ta runtse idonta eye lashes dinta sai rawa suke, ja da baya za tayi ta zille amma ina kawai ya haɗe bakinsu waje ɗaya, igiyar rigar baccin nata ya kunce ai kam rigar ta zame daga jikinta don dman silk ce, sai kuma ya zuge ribbon din da ta ɗaure lallausan gashinta, sosai jikinta ya fara ɓari tasa hannu bibbiyu ta ringa turesa tana so ta kwace lips dinta, wata razananniyar ƙara ta fasa bayan ta samu chance tace "wayyoh Ummana na shiga uku na lalace, dan Allah kayi haƙuri..", ya kalli bare chest dinta don bbu wani abu da yayi masa shamaki duk ya ciresu, tana shirin miƙewa ya janyota ya manna mata wani lafiyayyen kiss a neck wnda ya sake turning dinsa on, daga nan kuma zancen ya sauya bayan yayi jarumtar kaisu gado, this time around gentle yabi da ita ba extra gentle ba, ba kamar encounter dinsu na farko ba wnn karon bai sarara mata ba, yau dai ya ɗanɗana abinda yafi Coffee din safe daɗi, toh wa ma zai haɗa, bayan ƙura ya lafa ya ɗora forehead dinsa saman nata yana jera ajiyar zuciya pleasantly, da wata iriyar murya yace "Hajar" to know if she is conscious, da ragowar strength din da ya rage mata ta fashe da matsanancin kuka......✍️
💛 HAJAR 💛

{78..}
Babu wani pleading word da Nurain bai yi amfani dashi ba wajen consoling Hajar amma taƙi shiru, daga ƙarshe ma juya masa baya tayi ta duƙunƙune da duvet ta cigaba da rusa kukanta, bayan jikinta da yake mata ciwo har zuciyarta ma zafi take, Nurain ya tashi ya shiga bathroom, har ya fito bata dena kukan ba, singlet da short nicker kawai ya saka, wurga towel din da yake tsane sumarsa yayi kan couch snn ya nufi gadon, gefenta ya zauna ya bude fuskarta da ta rufe da duvet, ta muskuta da shirin juya masa baya yayi saurin riƙeta, idonta a runtse yake gamm sai jan zuciya take tamkar zata shiɗe, ya kamo hannunta yace "Baby girl..", ta fincike hannunta sai kuma ta mirgina ta koma can ƙarshen gadon, lokaci guda ta sake rushewa da sabon kuka sbd azabar da taji da ta mirgina din, Nurain ya sauke ajiyar zuciya don yasan ba sauraronsa za tayi ba, amma still ya zagaya ta side din da ta koma ya durƙusa yana kallon fuskarta, ya kai hannu ya shafa lallausan gashinta da ya hargitse yace "Baby wife listen to me..", da sauri ta tankwaɓar da hannunsa daga kanta ta wani turo baki, har lokacin idonta a rufe yake, ya cije lower lip dinsa painlessly gami da sauke wani ƙayataccen murmushi mai sauti, lokaci guda ya kware duvet din daga jikinta, ta tsala wani uban ihu ta cure kanta waje guda, tini ya wuce bathroom da ita don ya tara warm water a tub kafin ya fito, yasan she need warm water don she is still tight, yana ganin ko nan da encounter dinsu na biyar ma saida sitz bath, Hajar ta sha azaba don ruwan na yau sai taji kamar na barkono ne, yana ajiyeta kan gado bayan sun fito daga bathroom ta bige hannunsa daga jikinta, haushinsa take ji na gasken gaske shiyasa ma bata so ya taɓata, murmushi yayi ya kalli hannun nasa da ta bige yace "Eh naji... thank you... you make my morning today Baby wife", ya rage murya yace "it is sweeter than day before yesterday's night..", pecking cheek dinta yyi ya tashi ya fita, sai a lokacin Hajar ta buɗe idonta, ta miƙe a hankali ta zauna a ɗofane don bazata iya zama da kyau ba, room dinta take son komawa, ta miƙe tsaye da kyar tana cije lips, walking slowly sai kace mai taka ƙaya ta nufi door ta fita, tana tafiyar tana hutawa a haka har ta kai kanta ɗakinta, ta zube kan gado hawaye masu zafi na sauko mata, Anya kwa zata iya barin lokacin da ta ƙidaye yaxo kafin ta wanzar da ƙudirinta, Eh sbd favor yake mata shiyasa ya rufe ido ya ɗanɗana mata wnn azabar, sbd favor yake mata shiyasa bai saurari magiya da raƙon da ta ringa masa ba, wato ya gama da salon ɗalle mata baki da gaya mata maganganu ynxu ya dawo azabtar da gangar jikinta kuma, wnn tunanin yasa hawaye suka kasa tsaya mata, idanunta har zugi suke gashi kuma sun ƙanƙance, tana ji aka buɗe ƙofa amma taƙi motsawa zafin da zuciyarta take ya ƙaru, walking majestically ya zauna gefenta yace "Baby girl here is your Coffee", banza ta masa ta wani haɗe gira, yace "the Coffee you like wnda kike shanye min fa.." da haka ya ɗagota, afujajan ta fixge jikinta tana jan shessheƙa tace "please leave me alone", ta koma ta kwanta, yayi slight smirk yace "Ohk then get some rest..", da haka ya miƙe ya fita da mug din coffeen, ɓangarensa ya wuce ya zauna palour yana shan Coffeen, time to time sai yayi blushing sai kace zautacce, ji yake kamar an cire masa wani burden da yake damunsa yana jin kansa sakayau ynxu, yana gama sha ya ajiye cup din ya shiga bedroom, wayarsa dake kan bedside ya ɗauka, missed calls ya gani from 2 people, na Ruqayyah wnda daman ya saba ganinsa don kullum saita kirasa sau goma ko sama da haka, sai kuma missed call din Dr Marwan, na Dr Marwan din yabi, wayar almost 5mins sukay da Dr Marwan kafin Nurain ya katse kiran yana sauke ajiyar zuciya, knn yau sai ya shiga hospital, ya dubi makeken wall clock dake tickling yaga ƙarfe takwas da rabi, ƙarfe tara ya fito cikin shirinsa tsaf da car key a hannunsa ya sauka downstairs, Nearby Eatery yaje ya siyo mata breakfast snn ya dawo, da ledar abincin da kuma wcca Mami ta basa jiya tace ya kawo mata ya shiga palour, direct room dinta ya buɗe ya shiga bayan ya haura sama, ido biyu ya tarar da ita saidai a kwance take, suna haɗa ido tayi saurin janye nata, ya ƙarasa kusa da gadon yana kallonta without blinking yace "how are you feeling now...?", ba tayi niyyar amsa masa ba amma tsoronsa da ya shigeta yasa tace "much better", da kyar ma tayi mgnar ta wani sha kunu, duk yana ankare da yanayinta yaga dai har ynxu fushi take dashi bata sauko ba, don dai sauri yake da sai ya sauko da ita snn zai fita, amma dai bari ya dawo tinda ba wani daɗewa zaiyi ba, yace "Good... gashi Mami tace a baki wnn", ta gyaɗa kai a hankali, yace "i bought your breakfast", nan ma ta gyaɗa kai, after a while ya sunkuyo yayi pecking forehead dinta ya juya ya fita, saida taji ƙarar rufe ƙofa snn ta buɗe idonta, ta kai hannu ta goge forehead dinta inda yayi pecking tana turo baki. Nurain na isa hospital ko office dinsa bai shiga ba ya wuce surgery room, bayan ya gama shirin surgery ya saka surgeon gown ya shiga surgery room din, patient din da zai yiwa aiki har ya zama ready, tinda ya shigo surgery room din Ruqayyah ke kallonsa ta wani haɗe gira, position dinta ta tsaya don yau Vital signs zata ringa dubawa, Nurse Amina kuma ta ringa miƙa instruments, Good 3hours surgeryn ya ɗauka kafin aka gama, tini Nurain yayi disposing hand gloves da nose mask ya fita, throughout the surgery tunanin Hajar da ya bari a gida kawai yake, Allah yaso ma surgeryn ba wanda ake buɗa ciki bane da zai iya barin wani small instrument din a cikin patient, Ruqayyah ta bisa da kallo ta gyaɗa kai, ita da Nurse Amina ne suka mayar da patient din ward, da sauri Ruqayyah ta fita daga ward din bayan ta gama checking Vitals din patient din after surgery, direct hanyar office dinsa ta ɗiba, tana isa bakin office din ta tarar da patients wajen su goma, ta zauna kan silver chair tana jiran ya gama attending patients din kafin ta shiga, wayarta ta ciro daga pocket din Scrub dinta ta shiga messages. Nurain dake zaune office dinsa yana duba patient ya kalli wayarsa da tayi haske, ignoring message din da ya shigo yyi ya cigaba da aikinsa, 1hour ya ɗauka kafin ya gama attending ma patients din, har lokacin kuma Ruqayyah na zaune tana jira, last patient na fitowa ta zura wayarta cikin pocket din Scrub ta shiga office din, ko kallon Haleema ba tayi ba ta wuce ciki, ta mayar da ƙofar ta rufe ta jingina da ita, kallonsa ta ringa yi bbu ko ƙiftawa kafin tace "Assalamu alaikum", bai ɗago kansa daga kallon monitor din laptop da yake ba yana imputing data ya amsa sallamar ƙasa ƙasa, after few seconds din da suka kusa jingine 1mins ta ƙarasa shigowa, kan chair dake gaban huge table din ta zauna, a lokacin ya gama shutting down laptop din don ya gama abinda zaiyi, ya miƙe tsaye yana jan rigarsa, Ruqayyah ta ɗaga kai ta kallesa da mamaki ba dai tace komai ba, taga ya ɗauki car key alamar dai tafiya zaiyi, tace "Dr..", ya ɗan kalleta yace "what's up..?", tace "baka ga message dina ba nace zanyi mgana da kai Please", ya girgiza kai yace "ban gani ba... mene ne akan patient ne or something else...?", tace "please we need to talk", yace "Ohk not now, i will give you time next week Monday.." da haka ya zagayo ya nufi door, tini Ruqayyah ta miƙe tabi bayansa tace "why..?, me yasa ba ynxu ba..?", Calmly ya juyo yace "because my wife is waiting for me.. i can't give you even 1sec from her time" da haka ya buɗe ƙofa ya fita ya barta tsaye nan a daskare, shin da gaske ne wai Dearest dinta yayi aure, na farko da ta bisa Eatery yace mata yayi aure wnda sam sam bata yarda ba, ynxu kuma gashi yace mata ai matarsa na jiransa kuma ba taga wasa a yanayinsa ba. Wajen ƙarfe ɗaya da rabi Nurain ya fito daga wani haɗaɗɗen wajen siyar da wayoyi da wata yellow transparent leather a hannunsa, motarsa ya shiga ya bar harabar wajen, after a ride of 15mins ya isa gida, parking motar yayi snn ya buɗe ya fito, ya amsa sannu da zuwan da mai gadi ya masa kafin ya wuce cikin gida, ya buɗe ƙofar palour ya shiga, Hajar da take ƙoƙarin saukowa daga stairs a hankali tayi saurin kallon ƙofar, ai kam sukay ido huɗu zuciyarta ta buga da wni irin speed, ba shiri ta juya ta koma room dinta ta shiga toilet ta saka lock, wani mugun tsoronsa take ji, bayanta yabi ya haura upstairs din shima, a buɗe yaga ƙofar ɗakinta ya shiga bai ganta ba, ya kalli door din bathroom yyi slight smirk don yasan nan ta shige ya juya ya fita, ɓangarensa ya wuce yayi refreshing kansa ya saka ƙananun kaya riga polo da sweat pant. haka nan Hajar ta ringa gudun Nurain sai kace mage da ɓera har dare yayi, ynxu kam ta dena guduwa bathroom room din nata take rufewa da key snn ta bar muƙullin a jiki, wajen ƙarfe takwas Nurain ya dawo daga mosque sallar isha'i, ya kalli ƙofar ɗakinta yayi slight smirk, kafin ya fita saida ya murɗa handle yaji a rufe, tinda yake da ita a gidan wnn shine first time da ta sakawa ɗakinta key, girgiza kai yayi ya zura both hands dinsa a pocket ya wuce part dinsa, inda ya ajiye spare keys din gidan ya nufa, da kyar ya lalubo na room dinta, da key din a hannunsa ya fito corridor, sau uku yayi attempting saka key din a ƙofar amma yaƙi shiga, sosai yayi realizing ai akwai wani key din a jiki shiyasa yaƙi shiga, ajiyar zuciya ya sauke ya fara knocking door din, tini Hajar dake zaune gefen gado ta miƙe zumbur ta ringa kallon ƙofar, ta haɗiyi wani yawu jikinta ya fara rawa don gani take kamar zai shigo ne, Nurain yayi knocking door din da ɗan ƙarfi yace "Hajar..", idonta kamar zai faɗo ta ringa murza fingers dinta, lokaci guda ta afka toilet ta rufe da keys tana turo baki, after 5mins Nurain ya bar wajen ya sauka downstairs, kitchen ya shiga yayi making coffee ya fito ya haura sama. washe gari da sassafe Hajar ta ringa jin yunwa, jiya ba wani abincin arxiƙi taci ba tin breakfast da ya kawo mata ne acikinta sai kuma plain Noodles da ta dafa, A ɗarare tayi unlocking ƙofa ta buɗe ta fita cikin sanɗa ta sauka downstairs, ynxu kam tana iya tafiya ba taji zafi ba cause sau biyu tana yin sitz bath yau da safe da kuma jiya da daddare, kitchen ta shiga zuciyarta na bugawa don a tsorace take gani take kamar zata gansa a nan, sharp sharp ta tafasa ruwan tea ta haɗa shayi mai kauri ta shanye abinta a kitchen din, bata so ta wuce da cup din room dinta don tasan idan ta koma ta rufe ƙofar kuma sai 12 Noon, tana gama sha ta fito zuciyarta wasai ta haura sama ta shiga ɗakinta, still tayi ta ringa kallon jikin ƙofar ganin bbu keys, sosai zuciyarta ta buga don taji scent dinsa a ɗakin, bata gama lissafin da take ba kawai aka turo ƙofar ta waje, saida zuciyarta ta koma stomach after their eye contact, da baya ta koma sai kuma ta juya a miliyan zata shiga toilet, tini ya fixgota tayi landing a ƙirjinsa yace "Ke... ni Masquerade ne da zaki ringa guduna..?", ta yarfe hannu sai kuma ta fashe masa da kuka tace "wayyo Allahna na shiga uku..", jikinta har ya fara karkarwa don da gaske ta tsorata dashi, ya zaunar da ita gefen gado to calm her down ya duƙa gabanta, ya kamo shaking hand dinta ya riƙe a tafukan nasa yace "look at me Baby wife", kaudar da kanta tayi taƙi ta kallesa duk da yacca ya ringa leƙa fuskarta yana so suyi ido huɗu, yace "Hajar..", ta ɗaure fuska samm taƙi ta kallesa, murmushin kan lips yayi yace "wai har ynxu fushi kike Baby wife, After tough punishment din da kike min, you left me yesterday all alone, i couldn't even sleep comfortably..", ita dai ba tace komai ba, yace "sorry bazan sake ba sai kin gama healing Baby girl, i promise...", fashewa tayi da kuka sosai, wani irin sai tayi healing kuma, shi da zaice ya dena gaba ɗaya sai yace sai tayi wani healing, ta fara ƙoƙarin fincike hannunta amma yaƙi sakinta, murmushi mai sauti yayi don ya gane kukan na mene, yasa palm dinsa ya share mata hawayen yace "i promise you this Baby wife", ledar da ya shigo da ita ya dauka ya dora mata kan laps, ta ringa kallon ledar bbu ko ƙiftawa, yace "Open it", a hankali ta ciro kwalin tsaleliyar wayar daga cikin leda, tin daga kwalin ma kasan wayar me tsada ce, yace "you like it...?", ta gyaɗa kai a hankali sai kuma ta ɗago ta ɗan kallesa, saukar da kanta tayi tace "Thank you.." ta ɗanyi jimm kafin tace "Allah ya saka da Alkhairy", ya ringa kallonta yana jin wani abu mara misaltuwa na figarsa, zamm yarinya nan ta juye irin yacca yake mafarkin matarsa ta kasance, ba tin yau ya fara lura da hakan ba, ta ɗago kanta taga har lokacin kallonta yake, suna haɗa ido ta saukar da kanta, ya kamo hannunta yayi pecking for almost 10secs, a hankali ya ringa murza hannun nata yace "you need anything...?", da sauri ta gyaɗa kai, yace "tell me what is it..?", kanta a ƙasa tace "ina so naje gidanmu dan Allah", yayi ajiyar zuciya yace "Is that what you like..?", ta gyaɗa kai, yace "Ohk then insha Allah on Saturday sai nayi dropping dinki kiga Umma ko..?", ta ɗaga kai ta kallesa, ya sakar mata murmushin da tayi nadamar ɗagowa jin wani abu ya cakar mata zuciya, yace "yeah... Umma da ake kira daga anji wuya mna", turo baki tayi, ya ɗauke kwalin wayar daga laps dinta ya miƙe tsaye sai kuma ya riƙe hannunta ya ɗagota, rumgumeta yayi yana sauke ajiyar zuciya yace "missed you soo much yesterday..", a tare suka lumshe ido, ta kwantar da kanta sosai a ƙirjinsa. Sosai Nurain yayi keeping promise dinsa don bai sake taɓata ba, amma kuma bai sake barin sun raba shimfiɗa ba don baya ma iya bacci sai yayi Cuddling abarsa, itama ƴar farkar tafi jin daɗin bacci a jikinsa, kamar yadda ta saba a da yanzu ma haka take zata dafa abinci ta ajiye masa nasa a warmers, sai dai yanxu ba da kansa yake zubawa ba sai ya kirata ta zuba masa, Abu ɗaya ne yake sukar zuciyarta daga ta tuna cewa favor ake mata, wnn abu sosai ya tsaya mata a rai, ranar Saturday kamar zata zuba ruwa a ƙasa tasha don murna yau zata je gida, kafin ƙarfe goma ta gama duk wani aiki da za tayi, tana komawa ɗakinta ta faɗa bathroom ta fesa wanka, kayan da bata taɓa sakawa ba ta saka cikin na fitar bikin Noor da aka ɗinka mata, ta saka ƙaramin hijab dinta wanda yake tsaya mata a guiwa da kuma Charger din sabuwar wayarta a ƙaramar hand bag da ta fitar, sosai tayi kyau kamar a saceta, ta kalli door jin an buɗe, bai shigo ba ya tsaya daga waje ya waro ido yace "Hey ina zaki da sassafen nan", ta marairaice murya tace "yau ne fa zanje gida", yace "Ohk Okay... Amma dai ba ynxu ba", ta langwaɓar da kai tace "toh Ni yaushe zan tafi ƙarfe goma fa ya wuce", Nurain yayi slight smirk yace "where is my breakfast... bring it to my room". haka nan Hajar ta shiga kitchen ta hada masa breakfast sharp sharp ta kai masa ɓangarensa, ita da ta shirya tin goma da wani abun amma basu bar gidan ba sai sha biyu, Alla Alla take taga sun shiga unguwarsu don yau ma sai taga kamar gudun da yake bai wadaceta ba, Saida ya tsaya wani super market yayi shopping snn suka cigaba da tafiya, wani sanyi ne ya ratsa Hajar lokacin da yayi parking a daidai lungun gidansu, da sauri ta fara ƙoƙarin buɗe motar sai ta jita a kullu, ta juya ta kallesa ba tace komai ba, ya ɗauki envelope din daya ajiye kan dashboard ya miƙa mata, ta girgiza kai tace "Akwai tin wnda ka bani ranar nan", bai saurareta ba ya janyo jakarta ya zuge zip ya saka mata ba tare da ya lura da abinda ke cikin jakar ba, yace "idan na dawo zan shigo na gaida Umma", ta gyaɗa kai a hankali, da haka ya buɗe motar ya sauka, itama sauka tayi taga ya buɗe back seat ya fara ciro shopping bags, yara uku ya biya yace su ɗaukar mata kayan, Hajar ta saki baki tana kallonsa don ba tayi zaton gidansu za a kai ba, saida Hajar ta ɓacewa ganinsa snn ya koma mota yabar unguwar. Nabilah dake bakin rariya tana wanke wanke ta dena abinda take tabi yaran da suka shigo da kaya da kallo, Maama da ta fito daga bayi knn itama kallon yaran tayi baki a sake, Umma na zuba ƙullu cikin gwangwanaye Sabrah na shafa mata manja suma suka dubi yaran, duk cikinsu aka rasa wnda zai yi mgana, walking gently Hajar ta shigo tare yin sallama cikin murya mai sanyi, Umma dai tini ta ɗau muryar ƴarta ta, Sabrah ta micincina ido lokaci guda ta fasa ƙara tace "Addah.." sai kuma ta tashi da gudu taje ta rumgume Hajar, wani kukan farin ciki ne ya tahowa Hajar ta rumgume little sister dinta, Maama ta saki butar hannunta Nabilah kuma ta saki kwanon da take wankewa don sai ynxu suka gane Hajar, da farko sun sha wata balarabiyar ce tayi shigar hausawa, Maama ta dafe ƙirji murya a sama tace "wai Hajara ce", Hajar ko kallon inda take ba tayi ba ta wuce wajen Ummanta ta duƙa ta rungumeta, sai kuma ta fara hawayen farin ciki tace "Umma.. Ummanmu", Umma tayi murmushi tace "Hajara", Hajar na ɗago kai taga Sa'adatu da Maimuna sunyi cirko cirko a bakin ƙofa suna kallonta sai kace tsofaffin mayu sunji yunwa, Maimuna tayi wani baƙi fuska duk ƙuraje sai wata uwar rama da tayi gayau haƙora sun fito sai kace za tayi cixo, tini Umma ta rufe ƙullun alale taja ƴarta sukay ɗaki, gani kake yuuu Maama da ƴaƴanta suka bi Hajar da idanu, Sabrah ce ta ringa kwaso ledojin ta shigar dasu ɗaki, Hajar was more than happy da taga Ummanta, Umma taji daɗin ganin ƴarta ta data canza matuƙa, Hajar dai ta zama wata tauraruwa abar kallo a wajen Maama da ƴaƴanta, da ta fita yin alwala za tayi sallah har saida tayi tuntuɓe tsabar kallo, ita kam ko bi ta kansu ma ba tayi ba don bbu wnda ta kula, da yamma Baba ya shigo gida, Hajar na jin muryarsa ta ji wani mugun dadi, saida ya shiga ɗakinsa snn ta tashi ta fita ta tsaya bakin labule tayi sallama, da sauri Baba ya juya ya kalli labulen don ya gane muryar favorite din ƴar tasa, har ƙasa Hajar ta duƙa ta gaida mahaifinta wnda ya amsa mata gami ta saka mata albarka bayan ya dafa kanta, farin cikin da Hajar tayi a ranar bazai misaltu ba don rabonta da yin farin ciki kamar na yau har ta manta, bayan sallar magrib ne kiran Nurain ya shigo wayarta, dman contact biyu ne a wayar daga tasa wacca ma ko saving ba tayi ba sai na Umma, ita throughout the day ma bata bi takan wayar ba tana wajen Sabrah sai game take, basu wani jima suna wayar ba kawai ce mata yayi yana kan hanya zaizo ya ɗauketa, tace masa toh Allah ya kawosa lfy, after 15mins kam ya sake kira yace mata yaxo yana ƙofar gida, Hajar tayi wani murmushin gefen baki sai kuma ta saka veil dinta ta fita, bata wani jima ba ta dawo, Hajar ta duƙa gaban Umma wacca take zaune kan darduma tana jan carbi tace "Umma yace wai zaku gaisa", daga bakin ƙofar ɗakin Umma Hajar ta shimfiɗa darduma guda biyu, gashi kuma anyi sa'a yau an kyallaro wutar Nepa, Hajar ta fita soro bayan ta gama shimfiɗa darduman, tare suka shigo dashi ya zauna kan ɗaya daga cikin darduman, Umma ta fito suka gaisa kansa a ƙasa, da haka ya tashi ya nufi soro, Maama dai wuyanta kamar zai karye sbd leƙe daga ɗaki, lokaci guda ta koma gefen gado ta zauna sai kuma ta fashe da kukan baƙin ciki. Hajar ta gyara yafen mayafinta tayi hanyar soro, ta tsaya gami da tattaro courage don abinda za tayi sai da courage, ta ajiye numfashi a hankali, walking gently ta ƙarasa inda yake kanta a ƙasa, har ta isa kusa dashi kallonta yake, dukkansu shiru sukay bbu wnda yace komai, shi yayi breaking silence din da faɗin "shall we..?", ta jingina da bango speaking calmly tace "Thank you", ya tattare thick eyebrows dinsa yace "for what..?", ta kallesa a karo na farko tace "for everything... from the beginning till now that is the end", ya gyara tsayuwarsa yana kallonta da kyau, tace "A watanni huɗu da muka zauna tare nasan cewa na maka laifi dan Allah ka yafemin, i know i wronged you many times please forgive me.. however it seems i won't be able to do any of that now, bxn sake zama burden a kanka ba, ngode da favor din da kayimin na good 4months, nsan cewa Babana yamin aure amma ba auren Alfarma ba", Nurain ya tsuke piercing eyes dinsa yace "Hajar", ta haɗiyi wata ball da ta tsaya mata a throat tace "yess, kace zaka nunamin am your wife and you did that, still dai it won't change the fact that you are doing me a favor", kallonta yake bbu ko ƙiftawa, tace "ban san me yasa kake min favor ba ko don sbd ni ba choice dinka bace ko kuma sbd background dina ne i don't know, ngd da ka dawo dani inda ba favor ake min ba...", ta ɗan ja da baya ganin zai riƙo hannunta, ya ajiye numfashi yace "what are you saying Baby wife...?", da kyar tace "Nurain let me go, i will also let you go, from now on we won't own each other anything", tana gama faɗin haka ta juya ta shiga gida.....✍️
💛 HAJAR 💛

{79..}
A tsakar gida Hajar ta tsaya tana jin wata ball ta tsaya mata a throat, har lokacin akwai ragowar pure scent dinsa da ya bari, lokaci guda idonta ya ciko da ruwa, after a while ta juya ta kalli ƙofar soro sai kuma ta saukar da kanta ta shiga ɗakin Umma, wayarta ta amsa a hannun Sabrah ta dannata a Airplane mode ta mayar mata ta cigaba da game dinta, ta cire veil dinta ta koma gefen gado ta zauna, Umma ta kalleta tace "ya kuma naga kin zauna karfa ki barsa a tsaye yana jira", Hajar ta kwakwalo murmushi tace "Laaa ai ya tafi Umma", da mamaki Umma ta dubeta tace "ya tafi kuma...?", Hajar ta gyaɗa kai tace "Eh... ni anan zan kwana", Umma ta haɗe gira tace "bana son sakarci wane irin anan zaki kwana, tin tini baki zo da shirin kwanan ba saida kika zo nan za wani kice a nan zaki kwana, toh maza tashi ki bi mijinta tin kafin ma ya tafi..", Hajar ta marairaice tace "Umma shi yace fa na kwana wllh... kinga daga nan ma Airport zai wuce wani aiki ne ya taso masa, shine yaxo ya gaya min snn ya tambayi ra'ayina yace ya mayar dani gida ko kuma zan zauna a nan, shine nace masa a nan zan zauna, Umma yaushe rabona da ganin ku wllh nayi missing dinku over..", da kyar ta ƙarashe don muryarta har ta fara rawa kar a rafko jirginta, Umma tayi ajiyar zuciya tace "Amma baki taho da komai wnda zaki buƙata na kwana ba", Hajar tace "ba komai Umma, i will manage...", Umma bata sake cewa komai ba, Hajar ta tashi ta buɗe wardrobe inda take ajiye kayanta kafin aure taga kayan Sabrah ne aciki, Hajar tace "Umma an bayar da kayan dana bari ne...?", Umma tace "A'a duba ƙasa zaki gansu..", Hajar ta durƙusa tana duba ƙasan wardrobe din taga kayanta wajen set 7 da ta bari, sosai taji daɗi na ganin kayan, tini Hajar ta cire kayan jikinta ta linkesu ta ɗauki wani material mai laushi cikin kayan ta saka, wajen ƙarfe tara Hajar ta jiyo muryar Mu'azzam a tsakar gida suna mgana da Umma, tashi tayi ta fita tsakar gidan ta tsaya daga bakin ƙofa tace "Yayana...", Mu'azzam ya juya ya kalleta sai kuma ya tsuke ido yace "Wnn kuma daga ina..?", Hajar ta waro ido tace "Yaya ni din ce baka gane ba..?", yace "Eh kwarai..?", Hajar ta turo baki tace "knn ma ba kayi missing dina ba Yaya..", yace "Toh na sanki ne", Umma tayi murmushi tace "shiga ki ɗakko masa kwanon abincinsa wataqila ya tuna wace ce ke", Hajar ta shiga ɗaki ta ɗauko warmer din abincin nasa ta kai masa, ya amsa yace "toh yawwa ngd yar ƙanwata..", Hajar tayi murmushi tace "daman nasan tsokanata kake..", yace "Toh ykk..?", tace "lfy lou Yaya", yace "Toh masha Allah haka ake so" da haka ya shiga ɗakinsu. Washe gari wajen ƙarfe bakwai Hajar ta fita tsakar gida, tinda tayi sallar asuba ta kasa komawa bacci shine da taga Umma ta fita tsakar gida itama ta miƙe tabi bayanta, tasan aikace aikace za tayi don haka ita dai bazata kwanta ta bar Uwarta na aiki ba, tini Hajar ta kama aikin da Umma za tayi, ta share tsakar gida snn ta haɗa kwanuka tayi wanke wanke, Charcoal ta hura ma wuta ta dora ruwan shayi, yana tafasa ta juye a flask ta koma ɗaki ta tarar da Umma na tsince wake, zama tayi tana tayata tsintar waken, Sabrah na tashi Hajar ta ciro kuɗi a jakarta ta bata tace ta siyo musu bread da kwai, murna a gun Sabrah ba'a cewa komai ta tafi siyowa, Hajar na zaune kan kujera gaban Mangal tana soya kwan da Sabrah ta kawo, Maimuna ta fito daga ɗakin Maama tayi zugum tana kallon wainar kwan yawunta na tsinkewa, cikin bacci taji ƙamshin kwan ai kam a duniya taji shi kawai take son ci, Maama ta fito daga ɗakin itama da ɗaurin ƙirji, wani irin yamutsa fuska tayi ta kalli Hajar sai kuma ta zubawa Maimuna wani mugun ranƙwashi ta ƙunduma mata ashar tace "Shegiya wuce ɗaki kona ɓarar dake, yau kika fara cin wainar kwai da zaki fito ki tsira mata idanu sai kace tsohuwar mayya, da wata ƙonanniyar fuskarki", Maimuna ta juya ta shige ɗaki da sauri tana sosa inda Maama ta rankwasheta, babu ranar da rana zata fito ta faɗi Maama bata rankwasheta ko kuma mintsili ba, wataran har marinta take ko kuma ta fasa mata baki, Maama ta ja wani dogon tsaki tamkar tsohuwar tsaka tana hura hanci tace "ko wa za'a nunawa wata shegiya wainar kwai" ta shige ɗakinta tana baza zani, Hajar na gama suyar kwan ta tashi ta shiga ciki, Shayi mai kauri ta haɗa musu da kayan shayin data zo dasu jiya. Da yamma Maama na tsaye a soro sun keɓe da Balaraba da tazo, Balaraba tace "ke ni wata fa na gani kamar balarabiya a ciki", Maama ta taɓe baki tace "hmm ba wata balarabiya wnn shegiyar yarinyar ce yar wajen Faɗima..", Balaraba tace "wai Hajara ce yar kishiyarki..?", Maama tace "Uhmm itace wllh tllh... nima da tazo jiya ban ganeta ba", Balaraba tace "jar uba amma dai ba'a ƙasar nan suke da zama ba ko..?", Maama ta taɓe baki tace "Wllh a ƙasar nan suke anan garin ma kuwa", Balaraba tace "Chabɗi jam ai ƙafarta na gani kamar bata taka ƙasa wata irin fara ƙal ƙal ƙal sai kace tumatir", Maama tace "gidanta fa sama da ƙasa tayal ne, ga lantarki ta ko ina kamar zata fasa fitilu ba dole ki ganta kamar daga ƙasar waje ba, yoh gidan nata ma kika shiga ydda kika san a ƙasar wajen", Balaraba ta gyaɗa kai tace "Wnn dama malamin makarantar ta aura wllh tllh..", Maama ta sauke ajiyar zuciya tace "Ni hankalina ma duk ya tashi tsaye cur wllh, so nake na haɗa kuɗin nan muje a ɓarar da cikin jikin Maimuna kona samu nayi bacci da munshari, snn kuma zan koma wajen malamin nan na tsamiya da ƙudi masu kauri don so nake yayi min aiki mai kyau, wnn shegiyar yarinyar a kaɗota daga gidan mijin sai a manna Maimuna a wajenta, ni dai ynxu burina a fige cikin Maimuna kar ya bayyana na shiga uku", Balaraba tace "Gsky dai kiyi da jiki ƙawata tin kafin lokaci ya ƙure miki, kamata yayi ma tin ynxu a cire cikin don ya haura wata ɗaya, snn kuma baki da labarin Malamin tsamiya ya haukace watanni biyu da suka wuce..", Maama ta dafe ƙirji tace "na shiga uku ynxu wa zai min aikin kaɗo wnn yarinyar daga gidan mijin..?", Balaraba tace "Oho can ta matse miki a matsematsin matsalarki, ina ruwana duk inda zaki ki nemo malami sai kije ki nemo, nida ke anyi ta yanke anyi ta gille indai akan harkar malami ce, wancan karon ma haka kika wulaƙantani kika tijartani kika yagani sbd kince aikin da akay miki bai ci ba, ynxu ni ba ruwana dake akan wnn lamarin wllh" ta ƙarashe da jan guntun tsaki, Maama tace "Toh shknn... ynxu dai bazaki temaka min ba Balaraba, kina gani zan zama abin dariya a bainar nasi..", Balaraba tace "kinga ni tafiya zanyi bani kuɗina na ƙara gaba..", Maama ta sosa kanta tace "Wllh bani dasu banida dalilinsu kiyi haƙuri ki ɗaga min ƙafa zuwa wani lokacin", Balaraba ta saki baki tace "ban gane ba, haka mu kayi dake tsakani ga Allah, cewa fa kikai a washe gari ma zaki dawomin da kuɗina, kuma na gaya miki kudin nan ba nawa bane na mutane ne suka kawomin ajiya..", Maama ta juya hannu tace "haƙuri za kiyi Balaraba..", Balaraba tace "ni dae ki bani kuɗina tin muna shaida juna Rabi", Maama tayi kasaƙe tana kallonta kafin tace "Toh shekaruna zan lalo na baki iyee", Balaraba bata sake cewa komai ba ta juya ta fita fuuu kamar zata tashi sama, Maama ta taɓe baki ta juya ta koma gida.

★Walking slowly Nurain ya sauko daga stairs da farar Shirt a jikinsa da black sweat pant, kitchen ya shiga ya jona coffee maker, jingina yayi da jikin cabinet yana ƙarewa kitchen din kallo, haka nan yaga tana masa gizo a ko wane angle na kitchen din, ya dafe kansa da yayi masa nauyi gami da lumshe idonsa, daren jiya bai rintsa ba even a nap bai samu yayi ba, shi kansa saida yayi mamakin yacca idonsa ya soye ya kasa bacci, sai wajen biyu snn ya ɗora alwala ya fara yin sallah ganin bacci yaƙi zuwa, har asuba bai rintsa ba haka ya wuce mosque yayi sallah ya dawo, a tunaninsa zai iya bacci da safe ashe ba haka bane, daga karshe shine ya taso zai haɗa Coffee ko zai samu relief, ya dauki mug din Coffee ya fice daga kitchen din bayan ya gama haɗawa, direct sama ya haura ya shiga ɓangarensa ya zauna kan Sofa, after a while ya ɗauki mug din Coffeen ya kai baki, yana sipping yaji ɗaci sai kace ruwan bitter leaf, lokaci guda ya sauke cup din ya kalli Coffee din, sai da yaga baƙin Coffeen snn ya tuna ashe fa bai zuba milk da sugar ba haka nan ya haɗa tsura, ya haɗe thick eyebrows dinsa sai kuma yayi slight smirk bayan ya tuna ranar da ya ɗura mata irin wnn coffeen, yacca ta ringa yamutsa fuska and she cried tace Allah sai ya sakamin da ka bani maɗaci nasha... wayarsa dake kan Centre table ya dauka, ya shiga call log ya kira layinta a karo na ba adadi, abinda aka kwana ana gaya masa yaji wato switched off, Nurain bai ƙara ko 2hours a gidan ba ya fita, gaba daya gidan ya zamar masa wani empty, gidansu ya wuce kuma yana zuwa bbu wnda ya lura dashi don haka kawai ya haura upstairs ya shiga room dinsa, sai a lokacin ya samu bacci, ba shi ya farka ba sai ƙarfe biyu na rana, abinda ya fara yi shine daukar wayarsa ya sake kiran layinta, ajiye wayar yayi yana sauke ajiyar zuciya murya ƙasan maƙoshi yace "Baby wife". wajen ƙarfe huɗu da rabi Nurain ya shigo main palour ya tarar da Farooq suna gaisawa da Mami, ƙarasawa yayi ya miƙawa Farooq hannu sukay musabaha snn ya zauna kan Sofa, Mami ta ɗan kallesa tace "ka ɗauki Abincin da kace a zuba mka..?", Nurain ya gyaɗa kai yace "Eh..", Mami tace "Ohk then..", da haka ta tashi ta nufi ɓangaren Hajiya, Nurain ya dubi Farooq yace "kaxo tafiya da Amaryar taka ne...?", Farooq ya gyaɗa kai yace "Sure ita ta tasoni fa..", Nurain yace "Ohk" sai kuma ya koma yayi resting da kujera yana shafa kansa, Farooq ya gyara zama yace "That girl.. umm I can't recall her name daughter din sister din Mami..", Nurain yace "what about her..?", Farooq ya shafa kansa yace "what's that her name..?", Calmly Nurain yace "Khausar..", Farooq ya gyaɗa kai yana maimaita sunan, after few minutes of silence Farooq ya ɗago kansa daga latsa wayar da yake ya ringa kallon Nurain yace "Dude...", Nurain yace "why Punk..?", Farooq yace "you look dull and moody..", Nurain ya girgiza kai yace "Am perfectly alright", yasan idan ya gayawa Farooq damuwarsa toh sai ya masa dariya ma kafin ya basa solution, toh shi a wnn Mood din dariya ce baya so a masa, Nurain na jin alamar Hajiya zata fito ya tashi ya bar palourn ya shiga na Mami, definitely yasan saita masa mganar Hajar shi kuma baya so a ringa taɓo weak point dinsa a ynxu, haka nan Hajiya ta bar gidan tare da Farooq da yxo ɗaukarta, Washe gari Monday da wuri Nurain ya isa hospital, first abinda ya fara yi shine cancelling duk wni surgery da akay scheduling da zaiyi, ina zai iya wani surgery a wnn halin da yake ciki, patient kawai yake attending suma ba wasu da yawa ba ragowar yace Haleema ta sallamesu su dawo gobe, wajen sha ɗaya da minti hamsin ya gama duba patients din da zaiyi, wajen Haleema ya fita yace ta kira Nurse station yana son ganin A Nurse, da haka ya koma office dinsa ya zauna, after 10mins aka buɗe ƙofar office din Ruqayyah ta shigo, walking gently ta ƙarasa shigowa ta zauna kan kujera dake gaban table dinsa, Nurain ya taso daga chair dinsa ya ja kujerar dake kusa da wcca ta zauna, saida yayi nesa da kujerarta snn ya zauna opposite to her yana fuskantarta yace "Good afternoon A Nurse", ta ɗan kallesa tace "Afternoon" sai kuma ta saukar da kanta tana wasa da ring din hannunta, speaking calmly yace "You wanna to talk to me right...?, nace i will make time for you on Monday ko, so now ina jinki", sosai Ruqayyah tayi mamaki don bata taɓa tunanin zai kirata akan hakan ba, ita tasha ma ya manta ashe ba haka bane, A hankali tace "Dr ba sai na tsaya maka wani dogon jawabi ba kasan dai duk akan me nake binka, so nake kayi haquri akan laifin da nayi mka dan Allah", Nurain ya sauke ajiyar zuciya yace "If that's the case toh na haƙura, please stop disturbing my slumber..", har cikin ranta taji daɗi kuma hakan ya nuna a fuskarta, tace "Thank you very much Dearest..", ya girgiza kai yace "Take that name off your mouth Ruqayyah, ki manta da duk wani abu da ya wuce Ruqayyah, ba wai na haƙura bane sbd don mu dawo da relationship din mu na baya ba A'a na haƙura ne na abinda kika min, Ruqayyah bana so a ta dalilina kiyi ruining rayuwarki, ni na riga nayi moving on nayi aurena and ina zaune cikin farin ciki da matana, sai a ynxu nasan cewa ban dace dake ba from the start Ruqayyah, ina so kema ki ajiye komai kiyi moving on don gyara future dinki, wollah Ruqayyah I don't have any feeling left for you, kuma har abada bazan sake waiwayenki ba just know that, ki dena ɓata golden time dinki wajen yin abinda bazai fissheki ba", hawaye wasu nabin wasu haka suka fara zarya akan cheeks dinta, Nurain ya figi tissue paper ya miƙa mata, a hankali ta amsa ta goge hawayen, tana gogewa wasu na sauko mata, shi dai gsky ya gaya mata gwara tasan inda dare yayi mata tin wuri, After a while ta ɗago tace "Thank you for letting me know what is in your mind... ngd da ka yafemin laifin da na mka, tabbas some opportunities comes once in life, nima opportunityn aurenka sau ɗaya tazomin a rayuwa amma nasa ƙafa nayi fatali da ita, insha Allah Ni Ruqayyatu ba zan sake shiga rayuwarka ba Dr..", Nurain yace "Better", a hankali ta tashi ta nufi door har lokacin hawaye bai dena sauko mata ba, ta juya tana kallonsa sai kuma tace "Allah ya baka zaman lfy with your wife..", speaking with a repartee yace "Ameen.. please Shut the door", ta gyaɗa kai a hankali tace "Tom" da haka ta fice ta kullo masa ƙofar. Ƙarfe tara na dare Nurain na kwance kan doguwar kujera a palourn Maminsa, ceiling kawai yake kallo ya ɗora left hand dinsa a forehead, thick eyebrows dinsa a haɗe thinking of what to do, toh ynxu idan yarinyar ta gayawa parent dinta da wne idon zai kallesu, bama wnn ba Babanta wane irin kallo zai yiwa Abba, shiyasa ya rasa courage din zuwa gidan nasu don bai san me zai tarar ba, kuma shima rashin zuwan nasa matsala ne, wayarsa dake side dinsa ya ɗauka ya ringa kallon screen dinta, after few seconds ya ajiye ba tare da yayi komai da ita ba, don yasan ma idan ya kira switched off zai ji, lumshe idonsa yayi gami da sauke ajiyar zuciya, Mami da ta fito daga bedroom ta ringa kallonsa without blinking, ƙarasawa kujerar da yake kwance tayi ta kai hannu forehead dinsa tace "Are you sick Son..?", ya buɗe lumsassun idanunsa sai kuma ya miƙe zaune yace "No", Mami tace "Ohk amma ya baka tafi gida ba ko baka san dare yayi ba..?", ya kalli clock yace "ban san dare yayi haka ba", Mami tace "Alright sai ka tashi ka tafi dare na kuma yi, ka bar ƙaramar yarinya a gida", yace "Toh" da haka ya tashi yana jan rigarsa yace "Saida safe", tace "Allah ya tashemu lfy", ta bisa da kallo har ya fice, definitely tasan akwai abinda yake damunsa, ko ta tmbyesa ma ba gaya mata zaiyi ba sbd shi lamba ɗaya ne a fannin zurfin ciki da taurin kai, da kansa zaizo ya gaya mata idan abun ya ishesa dman haka yake.

★Yau kwanan Hajar uku a gida, sosai take jin daɗin zamanta da Ummanta da little sister dinta, lokaci zuwa lokaci abinda ta ajiye ƙasan zuciyarta ke tsikararta kuma nan da nan take yakice sa daga ranta, tinda tazo Baba bai mata mgana akan kwana ba sai yau, kuma shima cewa yayi ta tafi gidanta ko mijin nata bai dawo ba, da ta koma ɗaki tana kumbure kumbure ma Umma bata goyi bayanta ba tace ai tayi na Allah da ma'aiki kawai ta tafi, gashi bata gayawa Umma ainahin me ya faru ba, haka dai ta ƙudurce a ranta yau da daddare zata sanar da mahaifiyarta gskyr lamari, Hajar na zauna kan darduma tin bayan da ta idar da sallar magrib, daga tsakar gida taji Umma na yiwa Sabrah mgana tana cewa "baza kije ki kai mata wayarta ba iye... kullum waya na hannunki sai game kike bbu kama ƙafar yaro", Mu'azzam dake tsakar gidan shima yace "Ai wcca ta bata ce ba tada hnkali... bata san tsadar wayar bane shiyasa, Samsung ce fa ynxu ta faɗi screen dinta ya fashe sai taja kuɗi sama da dubu ɗari wllh... a Samsung din ma fa tata babba ce..", Umma ta riƙe baki tace "wuce ki kai mata wayarta", Sabrah tace "Toh", sum sum sum ta tashi ta kaiwa Hajar wayar, Hajar ta amsa tace "Anjima kaɗan saina baki ki cigaba da game din", Sabrah tace "Toh Addah" sai kuma ta juya ta fita, Hajar ta kalli wayarta ta a karo na farko tinda garin Allah ya waye, sam sam bata bi takanta don har Chargi ma Sabrah ce take sakata idan an kawo wuta, kuma tinda ta sakata a Airplane mode bata cire ba, a hankali ta kai hannu ta kunna wayar, tattare gira tayi bayan taga notification din messages, da sauri ta janyo labulen wayar ai kam taga ba a Airplane mode take ba, Sabrah ta cire garin danne danne, Hajar ta kwanta tana kallon messages din amma bata buɗe ba, ta sauke numfashi a hankali ta kai hannu ta buɗe guda ɗaya, saida zuciyarta ta buga kafin ta fara karanta message din, guda biyu kawai ta karanta taji idanunta sun ciko da ruwa, lokaci guda hawaye suka fara gangaro mata ta kife wayar don bazata iya cigaba da karantawa ba, ko minti goma ba ai ba wayar ta fara ringing, ita tsorata ma tayi don tayi nisa cikin tunanin da take, ta ɗago wayar tana kallon screen dinta ba tare da tayi picking ba, a haka har kiran ya katse wani ya sake shigowa, ta kai hannu za tayi rejecting call din amma ta kasa, ba tasan lokacin da tayi picking ba sai kuma ta kasa kaiwa kunne, a hankali ta kara a kunnenta ba tace komai ba, ta jiyo muryarsa yace "Baby wife..", turo baki tayi ta masa banza, yace "Hajar..", tayi jimm kafin tace "Na'am", ajiyar zuciya taji ya sauke tayi sauri ta lumshe idonta tana jin tsigar jikinta na mimmiƙewa, yace "har ynxu baki huce ba Baby wife..?", ta masa banza tana wani turo baki, yace "please talk to me", nan ma shiru ta masa, Calmly yace "Am sorry Hajar, i shouldn't have said All that stuff, delete All that stuff from your head please, Am sorry Baby wife", Sosai jikinta yayi sanyi ta kasa ce masa uffan, hawaye ya cika idanunta, yace "Can i come for you now..?", ta girgiza kai kmar yana kallonta tace "No..", yace "Why..?", tace "Sbd kaxo ka tafi dani ka cigaba da min favor ko", ya sauke numfashi yace "Hajar.. wollah i take back all what I said", tace "Okay good night...", yace "Toh can i come and pick you tomorrow..?", katse kiran tayi without answering, nan ya ringa kiranta taƙi yin picking, message ta shiga ta tura masa Yess, daga hka ta danna wayar a Airplane mode. Washe gari sai yamma liƙis Hajar ta cire wayarta a Airplane mode, dman tace da Umma ai yau ma zaizo su tafi ya dawo daga tafiyar. wajen ƙarfe takwas na dare kiransa ya shigo wayarta, tana picking yace "how are you doing Baby wife..?", tace "Alhmdllh", yace "Good, Am here already", tace "Ohk" sai kuma ta katse kiran, Umma ta shigo ta ajiye warmer din abincin hannunta gefe guda snn ta kalli Hajar tace "baizo bane..?", Hajar ta girgiza kai tace "yaxo yana ƙofar gida", Umma tace "toh tashi ki tafi mna kin barsa yna jira", Hajar tace "Umma ba muyi sallama da Baba fa", Umma tace "Topa kin san dai ba ynxu zai dawo ba sai Anjima", Hajar tace "nidae zan jirasa", Umma ta buɗe baki knn saiga sallamar Baba, yace "Ina Hajarar ne..?", Umma ta fita tsakar gida tace "gata nan mal", Hajar ta tashi ta tsaya gaban mirror zata ɗauki handbag dinta, zuge handbag din tayi ta ciro duka kuɗin da suke jakar ta ajiye kan mirrorn ta danne da robar mai, ta kalli Sabrah da ta bita da ido tace "Shhh karki gayawa Umma", da haka Hajar ta fita tsakar gida Sabrah tabi bayanta, Hajar ta duƙa gaban parent dinta tana musu sallama, Baba ya dafa kanta yana saka mata albarka kamar yacca ya saba, tini hawaye suka cika idon Hajar don ji take kmar idan ta tafi bazata dawo ba, Maama da ke tsaye tsakar gidan itama tace "Au ai na sha kaɗota akay da naga kwana biyu ta zaune a gida", daga Baba har Umma bbu wnda ya tanka mata, Sabrah kam fashewa tayi da kuka ita sai tabi Hajar, Hajar kam ta cake tace ta ɗakko kayanta su tafi, Umma tace A'a makaranta fa, Baba kam daman bai yarda ba tin farko ya girgiza kai, Hajar tace "A cewa Yaya na tafi", Umma tace "zai ji". Walking slowly Hajar ta nufi soro zuciyarta na wani irin harbawa tamkar zata fito, tin daga bakin soron taji ƙamshinsa da tayi mugun missing, ta saukar da kanta ta ƙarasa fita, ko da wasa bata kalli position dinsa ba ta tsaya nesa dashi, ta ɗanyi bowing tace "ina yini", kallonta yake without blinking sai kuma ya sauke ajiyar zuciya, one thing came to his mind cewa bata sanar da parent dinta ba. The ride was so silent bbu wnda yace uffan a cikinsu, ita kam Hajar window ta kalla ta ringa kallon titi, suna tsaye a wani traffic kafin a basu hannu Nurain ya juya Ninety degree yana kallonta, sosai taji kaifin idonsa a kanta amma taƙi ta juyo, slowly ya kamo hannunta ya ringa murzawa a tafin nasa, ta ɗan juya ta kallesa, yayi pecking hannun nata yace "kinyi shiru", ta saukar da kanta ba tace komai ba, ya sake pecking hannun nata ai kam ta ɗago ta kallesa, yace "ko saina buɗe bakin", turo baki tayi zata fixge hannun yaƙi ya sakar mata, da haka ya juya ya cigaba da driving don an basu hannu, da hannu ɗaya yake driving din ɗayan hannun kuma yana riƙe da nata, suna shiga palour bayan sun isa gida Hajar ta nufi stairs, da sauri Nurain ya ajiye ledar roasted chicken da tsire daya siya a hanya ya riƙota, kan kujera ya zaunar da ita yace "Are you still mad at me..?", ta girgiza kai, ya duƙa gabanta yace "Hajar bana so ki haura upstairs baki huce ba..", Kneeling yayi yace "please forgive me Baby wife", tini ta zamo ƙasa daga kan kujerar ganin abinda yayi tasa soft palm dinta ta toshe masa baki tace "wllh na haƙura", lokaci guda ta faɗa ƙirjinsa ta sakar masa kuka tace "Wllh na haƙura.. nima kayi haƙuri", tini yayi wrapping dinta sosai tamkar zai ɓallata, ta lumshe idonta tana sauraron bugun zuciyarsa tana kuka a hankali wnda ta rasa dalilinsa, in a whisper tone yace "I missed you Baby wife"......✍️
💛 HAJAR 💛

{81..}
Saida Hajar taji fitarsa masallaci da asuba snn ta buɗe idonta, a hankali ta muskuta ta sauko daga gadon tana ƙarewa kanta kallo, rigarsa ce a jikinta wcca ta tsaya mata a rabin laps, bata san lokacin da wani murmushi ya kufce mata ba, sai kuma ta saukar da kanta tana jin wata azabar kunya, ilahirin jikinta ya kwaso ainahin ƙamshin mijinta mai sanya nutsuwa, sleeping gown dinta dake yashe kan tiles da ribbon dinta ta dauka ta nufi door da sauri, bata so ya dawo ya tarar da ita a room dinsa cause bazata iya haɗa ido dashi ba, room dinta ta wuce direct ta shiga bathroom ta dauro alwala, tana idar da sallah ta koma gefen gado ta zauna don har ynxu tana jin slight pain, gaba ɗaya memory din last night ne yake mata yawo a brain, komai fresh yake dawo mata, ai kam ta ringa zabga murmushi ba kama ƙafar yaro, tana ji aka buɗe ƙofa amma taƙi ɗagowa cause tasan shine, Nurain na riƙe da door handle yana kallonta without blinking, murmushi yayi ya shafa cikakkiyar sumarsa still yana kallonta, bayan watanni huɗu da aurensa sai yanxu kyallin Angonci yake haskawa a goshinsa, kulle ƙofar yayi ya ƙaraso har inda take ya duƙa, da sauri ta kawar da kanta tace "ina kwana...", Calmly ya kamo hannunta yace "Good morning Sweet pie..", ta saukar da kanta sam taƙi bari su haɗa ido, yayi blushing yana lura da yanayinta yace "how was our steamy night...?", da sauri ta amshe hannunta ta kwanta ta cusa kanta cikin pillow tana jin wata azabar kunyarsa, tafin fararen ƙafarta yabi da kallo sai kuma ya kai hannu yabi zanen ƙunshin da akay mata da bikin Noor wnda har ynxu bai gama ficewa ba, Hajar ta janye ƙafarta jin yana mata tafiyar tsutsa ta turo baki, lower lip dinsa ya ciza painlessly, hawa gadon yayi ya ɗagota lokaci guda ya cire zumbulelen hijab din dake jikinta yace "I hate this blanket..", ta zaro ido tana turo baki tace "Ni ka bani abuna..", cilli yayi da hijab din har saida ya kai gaban mirror snn ya juya ya zubawa chest dinta idanu, yace "Toh ina ne ban gani ba... abarni na kalli properties dina ehe..", ji tayi kamar ta nutse a wajen, ta ɗaga kai ta kallesa suna yin ido huɗu ta saukar da kanta tana murmushi, ta turo baki tace "Ni dae ka bani abuna..", yace "wollah baza a rufemin properties dina ba..", tini ta fara ƙoƙarin sauka daga gadon ya fixgota yayi wrapping dinta a ƙirjinsa, ya cusa kansa a wuyanta ya ringa shaƙar ƙamshinta, after a while ya sauke numfashi yace "Toh muyi fira about our sweet yesterday's night" da haka ya sauke mata wni hot kiss a neck, ba shiri ta maƙe wuya ta shige jikinsa tana ajiye numfashi don wni electric shock ne ya ratsa veins dinta, ya kai lips dinsa saitin kunnenta yace "shall we have one romantic morning.." da haka yayi kissing kunnen nata, ta maƙe shoulder tace "Ni dae A'a...", yace "please Baby wife..", nan ma ta maƙe shoulder, bai sake cewa komai ba ya ɗago kanta yayi kissing lumsassun idanunta, sai kuma yayi kissing karan hancinta, murmushi tayi idonta a lumshe ta riƙe rigarsa gamm, kallon lips dinta yayi sai kuma ya sunkuya yayi brushing dinsu da nasa, ta tamke riƙon da ta yiwa rigarsa tana ajiye numfashi, kallon fuskarta yayi na few seconds sai kuma ya sake sunkuyawa yayi sucking lips dinta deeply, tini ya fara fita daga duniyar itama yana ƙoƙarin fitar da ita, da kyar ya janyo pillow ya kwantar da ita slowly, daga haka kuma ya fara smooching dinta a hankali, tayi masa lamo ta riƙe rigarsa gamm as if her life depend on that, saida taji yana ƙoƙarin rabata da ƴar rigarta snn ta farga, ai kam tini ta hantsila gefe ta gyara rigarta da ta tattare tana turo baki, ita fa har ynxu azabar tsoronsa take ji har cikin ranta, ita kaɗai tasan azabar da take sha idan ya taɓata, last night ma saida ta ɗanɗana don ruwan citta ta shiga, Nurain ya sauke ajiyar zuciya sai kuma ya tashi daga kan gadon yana buttoning rigarsa, blushing yayi yace "Ohk then bari na nemi alternative...", ya zagayo ta inda take ya duka yana kallon fuskarta, turo masa baki tayi, yayi murmushi yace "Au duk da na kyaleki shine kike turamin baki, tinda ban samu morning Coffee from you ba bari naje nayi making na alternative..", ta saukar da kanta ba tace komai ba, slowly ya kamo hannunta yace "you want some...?", ta gyaɗa kai a hankali, yaja hancinta yace "Ohk Coffee or Chocolate...?", ta langwaɓar da kai tace "Coffee..", yace "Alright" da haka ya tashi ya nufi door hannunsa zube a pocket, Hajar tabi bayansa da kallo sai kuma tayi murmushi tana juya lulu eyes dinta, After 15mins taji ana knocking door, tashi tayi taje ta buɗe ƙofar, yana riƙe da 2 Coffee cups a both hands dinsa, ya miƙa mata ɗaya yace "here..", ta amsa tace "thank you..", ya ɗaga cup din hannunsa yace "Enjoy.." da haka ya juya ya wuce ɓangarensa, Hajar ta rufe ƙofarta a hankali, gefen gado ta samu ta zauna ta ringa sipping coffee din, sosai ya mata daɗi don har wni lumshe ido take fuskanta a sake, tass ta shanye ta tashi zata kai cup din kitchen, bai ɗauketa wni lokaci mai yawa ba ta gama gyara kitchen da downstairs palour, daga nan ta haura room dinta shima ta gyara snn ta baza turaren wuta a ko ina, towel ta ɗaura ta faɗa wnka, yau yadda ta tattale jikinta na musamman ne, kolacca da humra da Sakeena ta bata tin lokacin da taje gidan ta ɗakko, ta shafe jikinta da kolaccan bayan tayi rubbing lotion dinta, snn tabi kan kolaccan da humra itama mai azabar sanyin ƙamshi, tayi Oiling gashinta snn tayi parking dinsa ta saki jelar da ta sauka har mid back, ta tsaya gaban mirror tana ƙarewa kanta kallo bayan ta saka gown din da ta fitar, sosai tayi kyau snn kuma body figure dinta sun fito sosai duk da cewa kayan ba kwasassu bane, wall clock ta kalla taga takwas saura, zaro ido tayi ta saka takalminta ta nufi door, tini ta shiga kitchen ta fara shirya breakfast, tana tsaye gaban sink tana wanke dankalin da ta feraye aka buɗe ƙofar kitchen din, bata juya ba don tasan shine tinda tayi perceiving pure scent dinsa, saida Nurain ya zagwanye a tsaye tsabar yacca ta masa kyau, kawai kallon back view dinta yake without blinking wata kasala na ratsasa, ajiyar zuciyar da bai shirya mata ba ya sauke lokaci guda yaje ya rumgumeta, Hajar ta zaro ido tace "What are you doing...?", ƙamshin da yayi perceiving ne a jikinta yasa ya cusa kansa a wuyanta perceiving it even more, gaba ɗaya Hajar sai taji ta kasa cigaba da abinda take, ga tap din ruwa da ta buɗe yanata zuba, da kyar ta iya cewa "dan Allah ka bari kaga fa aiki nake..", a kasale yace "Continue what you're doing am not stopping you Baby wife...", yana gama faɗin haka ya kwantar da kansa a nata har dasu lumshe ido, ta kalli ydda ya ritsa cikinta da hannayensa, a hankali tace "But i can't work like this..", yace "Ohh really toh abar aikin nidae bxan rabu da partner dina ba..", murmushi tayi ta ƙarasa wanke Irish din ta bar sa a colander zai tsane, buɗe idonsa yayi jin ta cigaba da aikin yace "Baby wife...", tace "Uhmm", ya shafa flat tummy dinta yace "I think yesterday's night I left something precious here.." ya ajiye mata wni combo kiss a neck yace "right..?", runtse ido tayi tana jin kamar ta nutse a ƙasa ta huta kawai, wai shi baya jin kunya ne, ta wni irin turo baki lokaci guda ta fara bubbuga ƙafarta a ƙasa da muryan shagwaɓa tace "Kaga bana so..", yyi blushing yace "Eh mna..", bubbuga ƙafar ta cigaba da yi tace "Ni A'a ba haka bane", sakinta yayi sai kuma ya sunkuceta sai kace baby yace "Muje upstairs sai kimin shagwaɓan da kyau snn kuma ki bani amsana da others ma da nake binki bashi", da haka ya fita daga kitchen din da ita sai ciccilla ƙafa take tace "Ni fa girki zanyi", yayi pecking lips dinta yace "let feed on each other... symbiotic mode of nutrition..", direct ɓangarensa ya wuce da ita bayan sun haura sama.

★Ƙarfe biyar da wni abu na yamma Maama na tsaye kan Maimuna dake zaune gefen gado ta toshe baki da duka hannayenta, Maama ta zuba mata wani mugun ranƙwashi tace "cinyesa shegiyar banza, wllh bxa ki fita ki tona min asira a bainar nasi ba saidai ki cinye amanki..", Maimuna dai ta guntse baki hawaye na zuba idonta don amai ne cike a bakinta ta kasa haɗiyewa, bazar bazar Balaraba ta afko ɗakin bbu ko sallama, Maama dake ƙundumawa Maimuna ashar ƙasa ƙasa ta juyo ta kalli Balaraba, lokaci guda Maama ta haɗe rai tace "A'a lfy zaki bankaɗo min ɗaki ba sallama..", Balaraba da ta wani murtuke fuska tace "Ke Rabi bani kuɗina..", Maama ta yamutse fuska tace "Ah aha toh meye kuma na miƙo hannu bayan abin rabo ya ƙare, kuɗi dai zan biya amma ba ynxu ba sbd bani dsu", Balaraba ta kalli sama tana jinjina abinda Maama ta faɗa snn tace "kut melesi.. billahillazi la'ilaha illa huwa bazan bar gidan nan ba sai kin biyani kuɗina Rabi..", Maama da ta fara fusata ta baza zani tace "na ƙarfin arnan da ne ehe.. idan kinada ƙarfi saiki kwata..", kafin kace me cacar baki ta kaure a tsakanin Maama da Balaraba, Balaraba ta cokalo kallabinta gaba ta daddage ta dungurewa Maama kai tace "Ai saina nuna miki ƙarfin arnan da din idan shi kika zaɓa", saida Maama tayi taga taga kamar zata faɗi tsabar yacca kan nata ya dunguru don har saida wuyanta ya amsa tamkar zai karye, Maama ta mulmulo ashar bayan ta gama recover, ba tayi wata wata ba ta cukuikuiye Balaraba ta tankaɗata waje, nan suka shiga musayar mugayen kalamai suna laftawa juna, Nabilah da take tsakar gida tana tankaɗe tayi kasaƙe tana kallonsu, Maama tace "Dalla malama fitar min daga gida..", Balaraba ta buga cinya tace "Ahayye riii ba dai kince kuɗi na ƙarfin arnan da bane toh kwa zaki gani", Maama ta zage ta ringa ƙoƙarin tura Balaraba soro amma firr taƙi fita, Umma ta fito daga ɗakinta jin hayaniya taƙi ta ƙare, Balaraba na ganin Umma tace "yawwa Faɗima..", nan Balaraba ta bankaɗa sirrin Maama wnda tayi asiri lokacin bikin Hajar har aka fasa aurenta da Ya Sayyadi Nura, Balaraba tace "Itace nan munafuka algunguma annamimiyar da ta shiga ta fita aka fasa auren Hajara wai duk don sbd karki cigaba keda ƴarki, Toh da aka fasa auren ma ba kyaleki da ƴarki tayi ba don tinda ta kyallara ido taga gidan yarki da maiƙo ta gigice tana neman hanyar da zata bunka wani asirin don a sako ƴarki ita kuma ta manna tata ƴar", sosai Umma ta sha mamaki ta tsinci kanta da furta "innalillah wa'inna ilayhirraji'un..", Balaraba tace "kuma ƴarta ta da tayo cikin shege...", sai a lokacin Baba da bai daɗe da dawowa ba ya fito yana kallon Balaraba yace "Fita..", Balaraba tace "Toh mal Adamu ko baka san cewa ƴarka Maimuna ta kunshi cikin shege ba ita da uwarta suka ɓoye, ynxu ma haka neman kuɗin da za'a cire cikin suke kafin ya fito fili", gaba ɗaya Maama gigice tayi ta wani susuce tamkar psycho, jikinta har rawa yake ta rasa mai zata yiwa Balaraba, sai dukanta take da guiwar hannu amma Balaraba taƙi yin shiru, daidai nan Huzaifa ya shigo gidan, jiya ya dawo gida sbd an musu hutun session, Nabilah ta matso inda yake tace "Yaya dan girman Allah fita da wnn matar..." shiru tayi sakamakon bangazar da Maimuna ta mata wcca ta fito daga ɗaki da gudu, ko bakin rariya Maimuna bata iya kaiwa ba ta durƙushe nan tsakar gida ta shiga kwarara amai, duk mutanen da suke tsakar gidan suka ringa kallonta kowa da abinda yake saƙawa a ransa, hatta Maama tsayawa tayi tana kallon Maimuna wcca har lokacin take kakari, Balaraba ta taɓe baki ta buga cinya tace "ga zahiri nan kun gani ehe, cikin shege dai gashi nan a jikin ƴarku...", wata kururuwar baƙin ciki Maama ta kurma ta rarumo bokitin ƙarfe ta ɓaurawa Balaraba a goshi, tini jini ya tsinke a goshin Balaraba, Maama ta sake ɗaga bokitin zata buga mata a karo na biyu Huzaifa ya amshe, da haka yayi waje da Balaraba dake ƙundume ƙundumen ashar tana cewa "Ni kika fitarwa da jini ko... kwarankwatsa dubu saina rama baza kici bulus ba", a sukwane Maama ta juya ta kalli Baba lokaci guda ta rushe da kuka tace "ƙarya take yi wllh tllh... masharraciya ce algunguma..", Baba da yake jin ƙirjinsa kamar an cinna masa wuta ya juya ya shiga ɗakinsa yana dafe bango, Umma ta kalli ɗakin Baba sai kuma ta saukar da kai ta shiga nata, wnn wni irin bita da ƙulli ne hka, dman Maama ce ta kawo tangarɗa lokacin auren Hajar, Maama tayi zaman ƴan bori a ƙasa tana rusa kuka kamar ranta zai fita tana cewa "ƙarya take wllh tllh..", Nabilah ta ringa ƙoƙarin ɗagata amma taƙi tashi, a fusace Huzaifa ya dawo gida bayan ya kaɗa Balaraba har kusa da lungun gidanta, fuskarsa a ɗaure ya dubi Maimuna da har lokacin take durƙushe ta kasa tashi yace "Ke durƙushen me kike yi anan da bazaki koma ɗaki ba..?", a kasale Maimuna tace "bazan iya tashi ba", wata irin fusata Huzaifa yayi da tace haka, don a zafin zuciya ya linka Naseer, wani harbi ya kai mata a ruwan ciki, dga nan ya zare belt ya ringa shauɗa mata kamar Allah ne ya aikosa, ihu Maimuna take tana neman agaji amma daga Maama har Nabilah bbu wnda ya ceceta, ta ko ina Huzaifa ya ringa sauke mata ruwan belt yace "dan uwarki ni zaki gayawa ba zaki iya tashi ba..", tin daga soro Sa'adatu da ta dawo gidan ynxu ta ringa jin ihun Maimuna, leƙowa tayi taga abinda yke faruwa ai kam ta koma ta rakuɓe a soron tana raba ido tamkar ɓera a buta, Maimuna ta rasa inda zata sosa a jikinta sbd duk inda Huzaifa ya samu lafta mata belt yake, da sauri Umma ta fito jin duka yaƙi karewa ta riƙe belt din hannun Huzaifa, sai a lokacin Maimuna ta samu chance ta rarrafa ta shige ɗaki tana jin wni abu mai ɗumi yana bin cinyoyinta, gaba ɗaya Umma ta kasa sukuni tin bayan da Baba ya shiga ɗakinsa, Ai kam tana shiga ɗakin nasa ta tarar ba lfy don Baba har ya fita hayyacinsa, a gigice ta kira Huzaifa suka koma ɗakin tare, ranga ranga Huzaifa da Mu'azzam suka wuce da Baba Asibiti Emergency, tini aka amshi Baba domin basa taimakon gaggawa, saidai me kamar ana zubawa wuta fetur ne don bbu wni cigaba da aka samu don jikin Baban ma yafi sauƙi a gida, BP dinsa ne ya haye fiye da kima ga kuma zuciya da itama ta motsa sosai, ƙarfe bakwai na dare Naseer ya iso asibitin shima don dman yana kan hanya Mu'azzam ya kirasa a waya ya gaya masa, bayan minti ashirin da zuwan Naseer suna zaune a bakin Emergency room din da likitoci sukace a basu guri, wata Nurse ce ta fito tayi describing Baba tace ana buƙatar relative dinsa guda ɗaya ya shiga, wata gudumar tashin hankali ce ta doka akan Naseer bayan ya hango gadon da Baba yake kai, da sauri ya ƙarasa gaban gadon yana kallon Baba da already an lulluɓesa har kai, Naseer bai san lokacin da ya zauna kan kujerar dake gaban gadon ba, a hankali ya kai hannu ya buɗe fuska mahaifin nasa wcca tayi kamar ta mai bacci cikin nutsuwa, after a while ya rufe masa fuskar yace "innalillah wa'inna ilayhirraji'un", ya saukar da kansa hawaye na sauko masa yana jin wata ƙuna a zuciyarsa, Dr din da yake cikin duba Baba har Allah ya masa rasuwa ya dafa shoulder din Naseer, Calmly Dr din yace "Allah ya gafarta masa..", After 15mins Naseer ya fita daga E.R din, Huzaifa na zaune kan kujera ya dafe kansa with both hands, Mu'azzam kam sai zagaye yake ya kasa zama don Umma ce take ta sirfa masa kira, dman da kyar ta yarda suka barta a gida, tinda suka zo asibitin yake lafta mata ƙarya don ta kwantar da hankalinta, da sauri Mu'azzam ya nufi Naseer yace "Yaya ya jikin nasa...?" sai kuma yayi shiru ganin yacca idon Naseer din yayi jajur, Huzaifa ya taso shima yana tambayar jikin Baba, Naseer yana kallonsu duka yace "Allah ya yiwa mahaifinmu rasuwa".

★Nurain ya dubi wayarsa da tayi ring wcca take side dinsa, dakatawa yayi da operating laptop da yake ya ɗauki wayar, ganin Abba ne ke kiransa ya duba lokaci yaga ƙarfe goma saura, picking yayi ya kara a kunne, ko minti biyu ba suyi ba suna wayar, Abba ya gaya masa cewa Allah ya yiwa mahaifin Hajar rasuwa gobe zasu fita jana'izarsa, shi ma Abba yana zaune yaga an turo masa message ta numbern din Baba, toh anan yaga rasuwar wnda Naseer ne yayi amfani da wayar Baba ya tura message ga duk Contacts din Baba don a samu sauƙi wajen sanar da mutane, Nurain ya tashi da sauri ya nufi door yana jan rigarsa, corridor ya fita ya buɗe ɗakinta, tarar da ita yayi tana linke hijab din da ta idar da sallah, already har ta saka kayan baccinta riga da wando, kallonta ya ringa yi without blinking sai kuma ya shiga ɗakin, ajiye hijab din tayi bayan ta gama linkewa, ta ɗaga kai ta ɗan kallesa, suna haɗa ido ya sakar mata murmushi, ta saukar da kanta tana twisting slim fingers dinta, ya ƙaraso inda take yace "Sweet pie have you eaten..?", ta gyaɗa kai, yace "hope da yawa kika ci little love ma ya samu nasa...?", turo baki tayi ta juya masa baya, murmushi mai sauti yayi ya rumgumeta ya shafa tummy dinta yace "idan kinyi denying bbu a daren jiya toh yau da safe fa..?", ƙoƙarin fixge kanta ta ringa yi don kar ya yiwa kunnenta fyaɗe, ya sauke ajiyar zuciya yace "where is your phone...?", ta nuna masa kan bedside, sakinta yayi yaje ya ɗauki wayar ya zura a pocket, ita dai ta bisa da idanu ba tace komai ba, yace "Muje ki kwanta Dear..", gado ta nufa tace "Anan zan kwanta ni..", bai saurareta ba ya riƙo hannunta yace "Toh ni kuma fa pillow zanyi hugging tonight...", yana riƙe da hannunta har suka isa ɓangarensa, kwantar da ita yayi kan gado ya gyara mata pillow, yaja duvet ya rufa mata zuwa shoulder, pecking forehead dinta yayi yace "Sleep tight.." da haka ya nufi door ya fita, yana fita palour ya ciro wayarta daga pocket, ya tarar bbu message ko missed call, ajiyar zuciya yayi don yasan ba'a kai ga kiranta daga gida ba, but yasan dole za'a kirata kuwa, da shike sim din Hajar sabo ne kuma bbu wnda yasanta dashi sai Umma da Mu'azzam, kuma a cikinsu bbu wnda ya kira. gaba ɗaya daren nan Nurain bai rintsa ba yana gadin Hajar, ko motsi tayi sai ya sani don sosai yayi cuddling abarsa, sau uku yana jin tana firgita, sai jikinta yayi wani karrr kamar mai jin sanyi, yawan firgitar da ta ringa yi ne yasa ya fara mata karatun Alkur'ani a kunne, ai kam bata sake firgitar ba, wajen ƙarfe uku Hajar ta farka sakamakon Cramps din da yake kartarta har cikin bacci, mutsu mutsu ta ringa yi don sosai cikin ke mata ciwo, Nurain ya buɗe lumsassun idanunsa yace "Mene ne..?", a hankali tace "Cikina", tashi yayi da ita a jikinsa ya kunna hasken ɗakin, yace "ina ne yake ciwon..?", ta masa pointing lower abdomen dinta hawaye ya ciko idanunta, wani magani ƙwalli ɗaya tak ya bata ta haɗiya, ai kam ɗipp taji ciwon ya ɗauke ta koma ta kwanta, bata sake farkawa ba kuma sai asuba, Tinda ta tashi da asuba gabanta yake yankewa yana faduwa haka nan saddan, har wni jiri jiri ta ringa ji tsabar ycca gabanta ke faɗuwa, a haka dai tayi sallar asuba bayan ta idar ta haɗe kanta da gado tana Azkar, Nurain na dawowa masallaci ya duba ɗakinsa yaga bata nan don haka ya biyota room dinta, ya ƙaraso inda take jigine da gado ya duƙa gabanta, da sanyin murya tace "barka da Asuba...", Calmly yace "Good morning how was your night...?", tace "lfy alhmdllh..", yace "Masha Allah... ya ciwon cikin..?", tace "ya dena", ya ringa kallonta ganin kamar tayi weak, ya sauke numfashi a takaice sai kuma ya ɗagota ya zaunar da ita gefen bed, a gefenta ya zauna ya kamo hannunta with care yace "Hajar..", tace "Na'am..", slowly yake murza hannunta yace "kin san dai duk wni mai rai mamaci ne, kuma Allah baya barin wni don wani muddun sa'insa yaxo ko..?", wni irin bugu zuciyarta tayi ta ringa kallonsa bbu ko ƙiftawa, ta gyaɗa kai a hankali, yace "ki shirya zamu fita tare before 7 kinji..", shida da rabi Nurain ya sake dawowa ɗakinta ya tarar har tayi wnka ta shirya, amma kana ganin yanayin kasan a tsorace take snn ga gabanta da yake ta faɗuwa, mug din da ya shigo dashi mai ɗauke da thick tea ya miƙa mata yace ta shanye yana dawowa, Hajar ta zauna da nufin shan tea din amma ƙiri ƙiri ta kasa haɗiya, da ƙyar ta iya shan rabi, next dawowar da Nurain yayi da car key a hannunsa, hijab din data fitar ta ɗauka tasa akan doguwar rigar jikinta ta atamfa, A motar ma lallaɓarta ya ringa yi yana gaya mata maganganu masu taushi, ita dai kawai jinsa take don har ynxu bai gaya mata ainahin me ya faru ba, tini zuciyarta ta karye a karo na farko da tayi mgana tace "dan Allah me ya faru...?", tayi saurin goge hawayen da suka hau zarya kan cheeks dinta without her consent, Calmly ya kamo hannunta yace "Ba komai, just say Allahumma ajirni fi musibati wa aklufuli khairan minha..", wnn ne time na farko da Nurain yaji yana shakkar faɗar abu, bai san how she will react bne idan ya gaya mata kai tsaye, baya so ya karya zuciyar Baby wife dinsa, Hajar taji zuciyarta ta dawo maƙogoro har tana jin bugunta a kunnenta bayan taga inda motarsu ta tsaya, wni irin kyarma jikinta ya fara wnda ya ratsa har zuwa lips dinta, tini ta zare hannunta daga nasa ta juya ta ɓalle murfin motar ta fita, tini shima ya buɗe motar ya fita don da zafin nama ta amshe hannunta snn ta buɗe motar wnda bai san tana dashi ba, har wani gurɗewa ƙafafuwanta suke ta nufi lungun gidansu, habawa ai tini Hajar ta kwasa a guje don gani take tafiyar bazata kaita ba, bata ma lura da mutanen da suke soro ba kawai ta afka cikin gida, shima tsakar gidan a kusan cike yake da mutane, da ƙarfi ta ƙwala kiran "Umma..!!" sai kuma ta afka ɗakin Umman, Anty dake riƙe da Umma wcca ba ta san inda kanta yake ba ta ɗaga kai ta kalli Hajar, shima ɗakin Umman a cike yake da ƴan uwanta, Anty da idanunta sukay jajir ta dubi Wasilah da Hafsah tace "ku riƙeta..", Hajar kam tinda taga Ummanta a wnn halin zuciyarta ta fahimci me ya faru, ji tayi mararta ta wani mugun ɗaure tamkar zata tsinke ta fita daga jikinta, ta fasa wata ƙara har saida kunnenta ya dauɗe, lokaci guda ta sulale ƙasa idanunta suka wulƙile.....✍️
💛 HAJAR 💛

{82..}
Ana idar da sallar juma'a aka sallaci gawar Baba, abinda yasa aka jinkirta jana'izar sbd ƴan uwansa na Yola da suka roƙa a ɗaga musu ƙafa suma su samu jana'izar dan uwansu, jana'iza kamila aka yiwa Baba kuma ya samu ɗumbin mutane, daga nan aka wuce dashi gidansa na gsky, Sosai mutuwar Baba ta wujijjiga mutune musamman ma dai iyalansa, Hajar na kwance ɗakin Umma bata ma san inda kanta yake ba tin bayan da aka fitar da gawar mahaifinta, suman da tayi na farko bata farfaɗo ba saida aka yi ta yayyafa mata ruwa ana mata fifita, tini fashin watanta yaxo bayan ɗaurewar da mararta tayi don it was behind the corner, ta samu dai taga fuskar mahaifinta kafin a fita dashi, kawai Allahumma ajirni fi musibati wa aklufuli khairan minha take furtawa, don bakinta ya kama addu'ar tin a mota da yace ta ringa faɗa, addu'ar ce tasa ta ɗan ji sassauci amma hakan baisa ta dena rusa kuka ba har saida ta fita daga hayyacinta, Umma kam har aka fita da gawar Baba ba ta san inda kanta yake ba, Nabilah kam wni lungu ta shige ta ringa kukan rashin mahaifinta kamar ranta zai fita, gaba ɗaya ta tsani ganin Maama da Maimuna da ita kanta Sa'adatu don gani take su suka kashe Baba, shiyasa ma taƙi zama a ɗakin Maama don bata son ganinsu, wajen ƙarfe biyu ana cikin jimamin mutuwa sai ga Balaraba ta shigo da wasu mata police biye da ita, fuskar nan ta Balaraba ta suntuma suntum kamar an buga mata iska da ƙatuwar bandage a goshi, idonta ɗaya saida ya nutse tsabar yacca fuskarta ta kumbura, tini Balaraba ta ringa kallon mutanen dake tsakar gida tana neman Maama, da bata ganta ba ta wuce ɗakinta da police women din biye da ita, ɗakin Maaman bbu wasu mutane sosai don ba tada wasu shaƙiƙan ƴan uwa duk karume karume ne, Balaraba ta kyallaro idonta da ya nutse ciki ta kalli Maama wcca tayi wni wujiga wujiga don sosai mutuwar Baba ta taɓata, shekaru talatin da wni abu sune tare da bawan Allahn nan, Balaraba tayi nuni da Maama tace "gata can..", ɗaya daga cikin ƴan sandan tace "Baiwar Allah zamu tafi dake can police station sbd muna tuhumarki da ƙoƙarin kisan kai", wata daga cikin karumen ƴan uwan Maama mai suna Jummai tace "ku kam ba ku san gidan mutuwa ba, baiwar Allahn nan fa mijinta ne ya rasu ko dawowa daga kaisa...", ƴar sandar ta ɗaga mata hannu tace "mu hukuma kawai aikinmu muke, an bamu umarnin kamota daga sama dole mu wanzar da aikinmu", haka nan ƴan sandar nan suka kaɗo Maama daga ɗaki tana rusu kuka kamar ba gobe tace "Dan girman Allah karku gwadamin wnn rashin imamin, ku barni da jimamin rashin mijina mna..", Balaraba tace "Ni imamin kika gwada min da kika tsiyayarmin da ruwan ido..", kuka wiwi Maama take tana turjewa don tini ƴan sandan suka fara janta, gashi jama'a bbu wnda yace uffan kawai kallon Maama suke suna taɓe baki, toh daman wa zai ce wni abun halinta ne yaja mata, gashi bata zauna lfy da maƙota ba bare su dubeta, da kyar Maimuna ta rarrafo daga ɗaki ta maƙale jikin ƙofa, ilahirin jikinta shatin belt ne da Huzaifa ya lakaɗa mata duka, ga kuma cikinta dake azabar ciwo kamar zai tsinke, lokaci zuwa lokaci kuma tana yin bleeding kuma shima tin jiya, Sa'adatu ma maƙalewa tayi daga jikin window tana kallon yadda ake jan Maama sai kace Akuya, Balaraba na cewa "Ni kaɗai nasan irin nakasta ni da kika yi, saida na zubar da jini yafi gwangwani huɗu ga uban ɗinkin da akay min ruɓi shida a goshi..", haka nan ƴan sandar suka tisa ƙeyar Maama daga gidan tana kuka Wiwi, hijabinta ya wani waskace ya koma gefen kunne sai haɗa gumi take tamkar tsohuwar kuturwa, Maama ta haɗa hannayenta tana kallon Balaraba tace "ki duba irin halin da nake ciki Balaraba kar kisa a kaini chaji Ofis da ɗanyen mutuwar mijina..", Balaraba ta taɓe baki ta kalli yan sandan tace "Ofisa ku kaɗata du Allah" don so take a kai Maama police station a sakata a cell, kuɗi sosai Balaraba ta biya domin a zane Maama idan an kaita cell. Sai yamma liƙis snn Naseer yayo bailing Maama, ko da yaje police station din sai ya tarar sun jibgi Maama sai kace jaka, da yayi mgana akan dukan sai suka ce ai gardama ta musu, saida Naseer ya biya dubu ashirin don Balaraba cewa tayi sai an bata kuɗin da ta kashe na magani, Balaraba dadi har cikin ranta don ta sami kuɗin da zata biya bashin da ta ciyo ta bawa ƴan sanda don su nakaɗawa Maama duka, ranta washar tinda an jibgi Maama. Sai a washe gari snn Umma ta fara watsakewa, ynxu kam har tana iya amsa gaisuwar wnda suka zo mata ta'aziyya ba kamar jiya ba, Hajar ta ɗan samu kuzari amma ba wni sosai ba, bata iya jimawa a zaune saita kwanta, manyan idanunta duk sun ƙanƙance kuma still bata dena kuka ba, gsky ta amshi tsumangiyar mutuwar mahaifinta, da yammacin ranar saiga Mami tare da Sakeena, a ɗakin Umma Anty ta saukesu, bayan sun gaisa da Umma suka mata ta'aziyya, Hajar dake zaune ɗakin ta gaida Mami, Mami ta amsa with care snn ta mata ta'aziyyar mahaifinta, Hajar suka gaisa da Sakeena snn ta mata ya dadin haƙuri, sosai Sakeeena taji wni mugun tausayin Umma da Hajar don saura ƙiris kukan da take dannewa ya taho mata, bayan wni lokaci Sakeena ta dubi Mami tace "Mami su shigo ynxu..?", Mami na kallon Anty da ta kawo musu ruwa ta zauna gefen Umma bayan sun gaisa tace "Za'a shigo a muku gaisuwa", After few minutes Nurain ya shigo shi da Farooq, suna gaisawa dasu Umma snn suka musu ta'aziyya, Farooq ya dubi Hajar ya mata gaisuwa, ta amsa kanta a ƙasa don ita ko gaisuwar ma aka mta sai ta fara kuka, ynxun ma dai kukan ne ya taho, Nurain ya sauke numfashi yana kallonta da wutsiyar ido, gaba ɗaya jiya bai samu ya ganta ba don tinda akai jana'iza suka wuce gida tare da Abba, da yamma ma dai da ya dawo bai samu ya ganta ba har ya tafi after magrib, gashi wayarta na wajensa though yasan ma ko tana wajenta bazata ɗauka ba, Farooq ne ya fara tashi snn Nurain ya bisa suka fita, su Mami basu wni jima ba suka tashi zasu wuce, Umma tace "Toh mun gode sosai..", Mami tace "Allah ya kara muku hƙuri shi kuma ya masa rahasa yasa can tafi nan..", Umma tace "Ameen..", Sakeena ta matsa kusa da Hajar tana mata mgana a hankali, kawai gyaɗa kai Hajar take tana share hawayen dake zuba cheeks dinta, Umma ta ringa kallonsu hakama Anty, Sakeena ta saki hannun Hajar da ta riƙe tace "sai munxo gobe dear... Allah ya ƙara haƙuri..", Hajar ta gyaɗa kai sai kuma ta miƙe, Mami tace "yi zamanki daughter kinji..", Hajar ta saukar da kanta ta koma ta zauna, zaune kan tabarma su Mami suka tarar da Nurain da Farooq a soro, Farooq yabi bayan Mami da har ta fita, Nurain ya rage murya yana biye da Sakeena yace "Sister please how is she...?", Sakeena ta juyo ta kallesa tace "Toh partially..", ya sauke numfashi ya ciro wayarta da yake ta yawo da ita a pocket ya miƙawa Sakeena yace "please ki bata kafin mu wuce..", Sakeena ta amshi wayar ta juya ta koma cikin gida, bbu jimawa ta fito bayan ta kaiwa Hajar wayar. Da daddare wajen ƙarfe takwas Anty ta shigo ɗakin Umma, direct gado ta nufa inda Hajar ta duƙunƙune waje ɗaya, tapping dinta Anty tayi don tasan ba bacci take ba, Hajar ta miƙe zaune sai kuma ta kai hannu ta goge hawayen cheeks dinta, Anty ta girgiza kai tace "kinci Abincin kuwa Hajar...?", Hajar ta gyaɗa kai tace "Na ci", Anty ta duƙa ta bude plate din abincin sai kuma ta ɗago ta dubi Hajar, Hajar ta saukar da kanta ba tace komai ba, Anty ta sauke ajiyar zuciya tace "tinda kin ƙi cin wnn toh me zaki ci..?", Hajar tace "na ƙoshi ne..", Anty ta ɗan haɗe gira tace "A'a wne irin kin ƙoshi Hajar, na kawo miki kunun gyaɗa da Umma ta rage...?", Hajar ta saukar da kanta sai kuma tace "Toh..", Anty tace "yauwa bari na kawo miki tare da maganinki..", Anty na fita Hajar ta juya tana kallon wayarta da ta fara ringing, da fitilar wayar ta haska ɗakin don bbu Nepa, gashi kuma ana zafi shiyasa duk su Umma suka fita tsakar gida sai ita kaɗaice a ɗakin, tana ɗaukar wayar kiran ya katse, bbu jimawa wni kiran ya sake shigowa, a hankali tayi picking ta kara a kunne, da dasasshiyar muryanta tayi sallama, Nurain ya lumshe idonsa don he can feel the bitterness in her voice da sanyin murya yace "Baby wife...", ta saukar da kanta ta amsa a hankali, yace "please can you come out..?", ta gyaɗa kai a hankali sai kuma ta ajiye wayar bayan ta katse, saukowa tayi dga gadon ta gyara hijab dinta, Anty ta shigo da cup din kunu ganinta a tsaye tace "Ina zaki...?", Hajar tace "shine yaxo..", Anty tace "Ohk.. idan kin dawo sai kisha kunun kinji...", gyaɗa kai Hajar tayi walking slowly ta fita tsakar gida, ta duƙa gaban Umma da ke zaune kan tabarma, ga Sabrah kusa da ita tayi bacci, ta gayawa Umma zata fita ƙofar gida, Umma ta jinjina kai a takaice, Hajar ta tashi ta nufi soro tana tafiya a hankali, bbu kowa a soron don tin bayan sallar magrib masu zama a nan din suke watsewa, su Naseer kuma ta gansu a cikin gida, ta saukar da kanta ta shiga soron da ya gama cika da pure scent dinsa, Nurain dake riƙe da wayarsa ya haska soron ya ringa kallonta without blinking, ta ɗan tsaya nesa dashi, with cracking voice tace "Ina yini...", ya juya ya kalli waje sai kuma ya ƙarewa soron kallo, lokaci guda ya janyo hannunta ta tafi gaba ɗayanta ta faɗa jikinsa, a hankali ya shiga patting bayanta yace "Ya haƙuri Baby wife..", ta kwantar da kanta hawaye na zarya cheeks dinta, ai kam tini ta jiƙa masa gaban riga da ruwan hawaye, haka ya cigaba da consoling wife dinsa har saida ya tabbatar nauyin zuciyarta ya ragu, tana jin bbu wanda ya mata rarrashin da ya shigeta kamar na mijinta, surely ta rarrasu don more than 60 percent na raɗaɗin da take ji ya ragu, ya kai soft palm dinsa ya goge mata ragowar tears din yace "please stop crying Allah ya jiƙan Abba..", sai wajen takwas da rabi Hajar ta shiga gida da bag din kayanta da ya taho mata dasu, other hand din nata kuma ledar kayan ciye ciye ce. Washe gari akay sadakar uku tinda kwanan keso Baba yayi, wajen sha daya na safe sai ga su Mami harda Hajjaju Hajiya da Noor da kuma Umminsu Farooq da Aysha, suka zo da uban abinci kala kala na sadaka, Anty da Umma ba ƙaramin mamaki suka sha ba ganin yacca surkan Hajar suke sonta, ga Iron Lady da suka ga tana mata wni tarairaya na musamman, Umma har cikin ranta take jin daɗi da Allah ya kai ƴarta gidan da ake sonta, yoh toh so mna idan dangin miji basa yi da kai ta ina zasu ringa maka irin wnn mutuncin, bayan 20mins da zuwansu Mami Anty Zulaihah ma tazo don tasan gidan tinda tare da ita aka zo ɗaukan Hajar, Khausar dake biye da mahaifiyarta ta ringa bin gidan da kallo tana yamutse fuska, tinda taji cewa gidansu Hajar Anty Zulaihah zata zo shine tace itama zata zo, Hajar ta duƙa ta gaida Anty Zulaihah wcca ta amsa mata da sakakkiyar fuska snn ta mata ta'aziyya, Khausar dai bata ko kalli Hajar ba bare ta mata gaisuwa, Hajar na lura da yacca ta ɗauke kai da ta ganta, ita kam bata damu ba don duk wnda ya wanko ƙafa yaxo gidansu sbd mutuwar Babanta ya gama mata komai, Hajar na kallon Khausar tace "Sannu Khausar", Khausar ta ɗan kalleta tace "Ya ƙarin haƙuri, Allah ya jiƙansa..", Hajar tace "Ameen..", ko 10mins su Anty Zulaihah basu ƙara ba suka tashi zasu tafi, zuwa lokacin har Khausar ta fara fifita da handbag dinta tana yamutsa fuska, kafin sallar Azahar su Mami ma suka tafi. Da yamma lokacin jama'a sun rage tururuwar zuwa Mu'azzam ya shigo gidan, kwaraɓaɓɓen kitchen din gidan da basa amfani dashi duk ya mutu sai uban shirgi ya buɗe, girgiza kai yayi ya bar bakin kitchen din, ɗakin Baba ya buɗe ya shiga bayan wni lokaci ya fito, wajen Naseer dake tsaye bakin titi tare da Huzaifa ya wuce, Mu'azzam na kallon Naseer yace "Yaya saidai a ajiye a ɗakin Baba a ynxu dai kafin a gyara kitchen din", Naseer yace "Tom.. ku shiga dasu", tini Huzaifa da Mu'azzam suka ringa ɗaukar Foodstuffs din da suke shaƙure a ƴar ƙurƙura suna shiga gida dasu, bayan sun gama kwashe uban kayan Abincin tare da ƴan tayi Naseer ya bisu gidan shima, duba yadda suka ajiye kayan yayi snn ya rufe ɗakin Baban ya bawa Sabrah muƙullin yace ta kaiwa Umma, Maama da akan idonta aka ringa jibgi Foodstuffs din don tana tsakar gida ta dubi Naseer da wni irin yanayi bayan taga ya bawa Sabrah key yace ta kaiwa Umma, Maama tace "Nasiru..", Naseer ya dubeta a karo na farko tin shigowarsa gidan, tace "Zo nan ina son ganinka" da haka ta tashi ta shiga ɗakinta tana ɗingishi, har ynxu ƙashin cinyarta ciwo yake sbd bugun da ta sha a hannun police, Naseer da zuciyarsa take zafi don har cikin ransa ya tsani halin mahaifiyarsa, da ƙyar ya tausashi kansa ya bita ɗakin, kallo ɗaya ya yiwa Maimuna dake malelekuwa a ƙasan leda tana murƙususun ciwon ciki, Sa'adatu ta cusa wayarta da take dannawa ƙarƙashin pillow ta hau baccin ƙarya, haɗe fuska yayi don ya lura da ita, ya duƙa gaban Maama yace "Gani..", Maama ta ringa kallonsa jin yacca yayi mgnar a daƙile, ta girgiza kai tace "Nasiru na lura kai da Huzaifa da Nabilah kun ƙullaceni a cikin ranku, kar ku manta dai ni uwarku ce ko da kuwa tsince tsince nake a bola..", Naseer ya sauke numfashi yace "ba hka bane Maama..", tace "Ai ni ba mahaukaciya bace da za kace min ba hka bane Nasiru, toh ba dai a canzawa tuwo suna, idan ma gani kuke ni na kashe mahaifinku toh wllh ba ruwana, lokacinsa ne yyi snn kuma dukkanku na fiku sonsa don tare kuka ganni dashi..", shi dai Naseer yayi shiru baice komai ba, Maama ta gyaɗa kai tace "Wccan Uban kayan abincin tuli guda a ina ku ka samosa..?", yace "Abokin Baba ne ya kawo..", Maama ta micincina ido tace "Abokin Baba kuma...?, ina mal yaga Aboki mai arziƙin da zai nannago uban kayan abincin nan ya bamu..?", Naseer yace "Alhj Muktar fa", nan ma Maama ta ƙanƙance ido tace "waye hka..?", yace "Surkin Hajar", saida zuciyar Maama ta koma ciki tsabar ruɗu amma bata nuna ba ta rausayar da kai tace "ba shakka shiyasa ai ka damƙa mukulli hannun masu abincin", Naseer ya shafa kansa yace "zan koma soro kar azo ana nemana..", bai jira cewarta ba ya tashi ya fita with speed, takaici ma bazai barsa ya gaya mata sauran Alkhairyn da Abba ya musu ba, ga kuɗi masu yawa ya bayar yace su riƙe a hannunsu snn yace duk abinda ake buƙata a gidan Naseer yaje ya samesa ya gaya masa, a wnn lokacin ai da wuya a samu mutum irin Abba wnda zai waiwayi iyalan Abokinsa bayan rasuwa, kowa ta kansa yake nafsi nafsi. Hajar ta raka Zainab da tazo mata gaisuwa har soro, Hajar tace "Ngd sosai Zainab..", Zainab tayi murmushi tace "ba komai Hajar, Please karki manta ki kirani anjima sai nayi saving number dinki tinda bakya amfani da wncan..", Hajar tace "insha Allah.. ngd sosai Zainab ki gaida Ummi dan Allah..", Zainab tace "zata ji". Hajar na gida har saida akai bakwai, kullum Nurain sai yaxo to check on her, gashi kuma suna waya frequently, yau ne akay sadakar bakwai, da yamma bayan gida ya watse bbu kowa don da yawan mutane sunxo sunyi gaisuwarsu, Anty ce tare da Umma a ɗaki, tin ranar uku Anty ta tafi gidanta sai ranar biyar da ta kuma zuwa sai kuma yau bakwai da tazo, Anty tace "Yau gashi har Baba yayi kwana bakwai a ƙasa, Allah ya jiƙansa ya gafarta masa yasa aljanna ce makomarsa..", Umma da Hajar suka amsa da Ameen, Anty tace "Addah saidai wni hanzari ba gudu ba, zaman gidan nan a gsky ba naki bane ya kamata mu fara tunanin inda zaki koma, baza ki cigaba da zama da waccar matar mai zuciyar kafurai ba..", Umma ta numfasa tace "gskyr ki Jamilah, tabbas bazan cigaba da zama da Rabi ba a gidan nan, zanyi tunani akan hakan..", Anty tace "Yauwa kar ki ja tunanin nan ya daɗe don ni ko sati biyu bana so ki ƙara nan gaba wllh, wccar matar abin tsoro ce tsakani ga Allah", Umma tayi shiru ba tace komai ba, Anty tace "idan gidan Iya zaki koma toh..", Umma tayi saurin girgiza kai tace "A'a bazan koma gidan Iya ba gwara na tafi Yola kawai..", Anty ta zaro ido tace "Yola kuma Addah, wajen wa zaki a Yola..?", Umma tayi murmushi tace "haba Jamilah ya kike mgana sai kace wasu marasa dangi, wajen Gwaggo Habiba zan tafi..", Anty ta sauke ajiyar zuciya tace "haka ne Addah, wllh Gwaggo Habiba tana son mu kuma na tabbata bazata ƙi zama dake ba, lalurar da take da itace ma tasa bata zirga zirga wajen zuwa inda muke wllh", Umma tace "zan dai yi tunani Jamilah", Anty tace "Toh", tini idanun Hajar suka ciko da ruwa jin Ummanta za tayi nesa da ita, Anty ta kalli Hajar tace "ke kuma yaushe zaki koma gidanki..?", Umma tace "Ni nasha ma yau zata koma wllh..", Hajar ta saukar da kanta ba tace komai ba, Anty tace "Ya kamata dai ki tafi tinda anyi bakwai kar kuma a shiga haƙƙin aure..", Hajar bata iya cewa komai ba sai gyaɗa kai, Anty tace "Hajar na jinjina miki Allah ya miki Albarka, yadda naga dangin mijinki na tarairayarki suna ji dake nasan cewa kinyi riƙo da tarbiyyan da mahaifanki suka baki, Allah yasa ki cigaba da ɗorewa a haka kuma kar kiyi sagegeduwar da soyayyar nan da suke nuna miki zata ƙare..", Hajar tace "Insha Allah..", Daf da magrib Hajar na zaune kan kujera gaban rariya tana alwala don ynxu she's clean jiya tayi wankanta, Nabilah tazo ta ɗebi ruwa a buta ta durƙusa nan kusa da Hajar itama za tayi alwalan, Hajar dai bata ko kalli inda take ba ta cigaba da alwalanta a hankali, a hankali Nabilah tace "Hajara..", Hajar ta ɗaga kai ta kalleta sai kuma ta cigaba da alwalanta, Nabilah ta sake kiran sunanta a karo a biyu, da mamaki Hajar ta kalleta sai kuma tace "Na'am..", Nabilah da idonta ya ciko da ruwa tace "ya haƙurin mahaifinmu..", Hajar tace "Mun gode Allah..", Nabilah ta ɗanyi jimm sai kuma tace "Toh ayi haƙuri da duk wni abu da ya faru a baya, irin saɓanin da muka samu a matsayinmu na ƴan uwa, dan Allah kiyi haƙuri komai ya wuce Hajara..", Hajar tace "Ni kam a cikinku bbu wnda na riƙe a raina Nabilah, nice ƙarama acikinku amma kuka nuna bakwa sona a koda yaushe cikin kyarata kuke, snn kuka ringa haɗemin kai samm ba kwa nuna cewa ni ƴar uwarku ce..." sai kuma tayi shiru kafin tace "bazan manta ba shegiya kuke kirana duk da cewa ubanmu ɗaya, bbu damuwa komai ya wuce ni bbu wnda na riƙe a cikinku Nabilah..", Nabilah ta goge hawayen da ya zubo mata tace "haƙiƙa ba mu yiwa mahaifinmu adalci ba, ke kam bbu ruwanki sbd mu muke fara janyo duk wata fitina, duk wata matsala mu muke janyota wllh, dan Allah Hajara kiyi haƙuri mu manta da komai ko don mahaifinmu..", Hajar tace "ba komai kema kiyi haƙuri don ƙarfe ɗaya baya amo" tana gama fadin haka ta wanke ƙafarta ta tashi ta shiga ɗaki. Washe gari Umma tace da Hajar ta shirya ta tafi da wuri ido na ganin ido ba sai dare ba, haka nan Hajar ta hau shirya ƴan kayanta a jaka jiki a sanyaye, wajen sha biyu Abdallah ya kawo saƙo yace inji Anty kuma saƙon na Hajar ne, ai kam Umma bata buɗe ledar ba haka ta miƙawa mai ita, ita dai Hajar ta amshi ledar tana tunanin mene ne a ciki, Abdallah ko zama beyi ba yace zai wuce don kasuwa zai tafi Anty ta bashi saƙon ya kawo, bbu jimawa da tafiyar Abdallah kiran Anty ya shigo wayar Hajar, bayan sun gaisa Anty tace "Abdallah ya kawo miki sako ko..?", Hajar tace "Eh..", Anty tace "Ohk.. akwai paper acikin ko wanne wcca aka rubuta ydda ake amfani dashi..", Hajar tace "Toh ngd Anty" duk da bata san mene ne abinda Anty take mgana akai ba, Anty tace "Yau din zaki tafi..?", Hajar tace "Eh insha Allah da yamma..", da haka sukay sallama. Hajar ta saka hijab dinta a hankali, duƙawa tayi ta saka wayarta cikin bag din kayanta, idanunta cike taff da ruwa ta juya ta kalli Umma, da sauri ta tafi ta faɗa jikin Umma ta fashe da kuka tace "Umma dan girman Allah karki tafi Yola ki barni..", Umma ta daure tace "A'a bazan tafi ba Hajara..", Hajar ta ringa rusa kuka don mikin mutuwar ne ya wani taso mata, ynxu shknn bazata sake ganin Babanta ba, indai tazo gida bazata ga Baba ba, Mu'azzam ne ya shigo ɗakin ya tsaya yana kallonsu, sai kuma yace "kin fa bar mutum yana jira Hajar..", Hajar ta zame jikinta daga na Umma tana jan zuciya, Mu'azzam ya ɗauki jakar kayanta ya fita da ita yana cewa "ki fito hka nan..", haka nan Hajar ta fito tsakar gida da ledar kayan da Anty ta bata a hannu, Umma na biye da ita tace "Allah ya kaiku gida lfy..", Hajar ta kalli Nabilah dake zaune a ƙasa bbu ko tabarma ta zabga uban tagumi sai kace me fama da cutar depression, walking gently Hajar ta isa inda take ta duƙa gabanta tace "Nabilah..", Nabilah tayi firgigit don tayi nisa a tunanin da take, Hajar tace "Ni zan tafi sai na sake zuwa kuma..", Nabilah ta numfasa tace "Toh Allah ya kaiki gida lfy, zan amshi lambarki a wajen Umma sai mu ringa gaisawa..", Hajar ta gyaɗa kai da haka ta miƙe, hannun Umma ta riƙe tace "Umma na tafi..", Umma tace "Allah ya miki albarka Hajara ya kaiku gida lfy..", Hajar tace "Ameen Ummanmu..", Nabilah ta ringa kallonsu tana jin dama ta ta uwar ce a hka. Har bakin mota Mu'azzam ya raka sister dinsa, sai a lokacin Nurain ya amshi bag din kayan daga hannun Mu'azzam ya saka a booth, kafin ma ya gama saka jakar tini Mu'azzam ya juya ya shige lungunsu, Nurain ya zagayo side din da Hajar ta tsaya, ta ɗan kallesa sukay ido huɗu, murmushi ya sakar mata sai kuma ya kai hannu ya buɗe mata front seat, saida ta shiga ya rufe snn ya zaga driver seat ya buɗe ya shiga, ya rufe murfin motar sai kuma yayi stretching kansa sosai yace "Alhmdllh..", bai kunna motar ba ya juya yana kallonta, sosai ya lura da kumburin da idanunta sukay, ya sauki wni boyayyen ajiyar zuciya, Calmly ya kamo hannunta yace "Baby wife..", ta kallesa a takaice tace "Ina yini..", yayi pecking hannun nata yace "Ni har ynxu ba nida suna", ta saukar da kanta ba tace komai ba, ya sake pecking hannun nata na almost 10secs har saida ta ɗago ta kallesa, yace "Uhmm ba nida suna a wajen matana har ynxu..", ta kalli hannunta dake cikin nasa, yasa other hand dinsa ya riƙe haɓarta ya ɗago kanta, kallon eye balls din juna kawai suke, ya lumshe idonsa ya sake buɗasu a kanta, kashe mata ido daya yayi yace "A taimaka min da suna..", yacca ya kashe idon sai kace wni abu ne ya faɗa masa da kuma yacca yayi mganar ne ya bata dariya, bata san lokacin da wni murmushi ya kufce mata ba, ta ɗora forehead dinta kan hannunsu dake maƙale tare still tana murmushi, yaushe rabonta da wni abu wai shi murmushi, shima murmushin yayi ya ɗago kanta ya haɗe forehead dinsu waje guda yana murza hannunta yace "I like it when you smile"......✍️
💛 HAJAR 💛

{83..}
Good 4 days Nurain ya dauka yana cheering Baby wife dinsa up, sam baya barinta ta zauna jigum bare ta shiga damuwa, a kullum yana tare da ita though yana fita aikinsa amma baya daɗewa aikin 3hours kawai yake ya dawo, daga nan zai zauna da ita a gida har sai yamma snn yaje gidansu ya gaida parent dinsa, a gida yake sallar magarib da isha'i ma, bayan nan kuma sai ya ɗauketa su fita su zaga gari, hka nan suke dawowa gida da uban kayan maƙulashe da ya siya mata, kullum da Asuba kam tare suke yiwa Baba Addu'a, sosai Hajar ta sake raɗaɗin zuciyarta ya ragu saidai kuma ciwone da bazai taɓa warkewa ba a zuciyarta har itama ta koma ga mahaliccinta, Addu'a ba kama ƙafar yaro take yiwa Babanta cikin duka kamsu salawat da take gabatarwa. walking gently Hajar ta fito daga bathroom da towel ɗaure ribs dinta ta yafa wni a shoulder dinta, lulu eyes dinta ta sauke akan gadonta sai kuma tayi murmushi ganin har ynxu yana kwance a nan din bai tashi ba, tin Asuba da ya shigo nan din ya kwanta, A ɗakinsa suka kwanta itama da asuba ne ta taho nan, gashi dai har ta sauka downstairs ta kimtsa komai, har part dinsa ma ta gyara ta gama breakfast amma bai farka ba, a tunaninta kafin ta fito dga wnka zata tarar ya tashi sai kuma ta tarar bccin yke har ynxu, gaban mirror ta zauna ta shiga rubbing lotion, tana shafe shafenta tana kallon gado ta cikin mirror, da hka dai ta gama ta bar gaban mirrorn wni sassanyan ƙamshi na tashi a jikinta, a hankali ta buɗe wardrobe without making any sound ta ɗauki kayanta, tana gama saka kayan ta kalli agogo, ƙarfe tara da rabi ta gani, ta zaro ido toh ko dai yau bazai fita bane, ita dai bazata tashesa ba gsky, kallon gadon tayi lokaci guda ta isa gaban gadon, ta sauke idanunta a kan fuskarsa, kallonsa ta ringa yi without blinking, zama tayi gefen gadon a hankali ta sunkuya daidai fuskarsa tana kallonsa, wnn shine karo na farko da ta masa irin wnn kallon, dman haka mijinta yake, words can't express handsomeness of her husband, kawai ganin idonta tayi a cikin nasa, wani irin bugu zuciyarta tayi, ya subhanallah kar dai ya kamata tana kallonsa, wayyoh Allah ta shiga uku, tini ta ɗaga kanta tana inda inda, sai kuma ta ɗan kallesa, kallonta taga yanayi with his sleepy eyes, ta kalli gefe da murya ƙinƙina tace "Amm... daman.. naga.. lokaci..", murmushi yayi ya mirgino ya ɗora kansa kan cinyarta, yana kallonta da kyau yace "daman me Baby wife...?", ta ringa kallon thick eyebrows dinsa sai kuma ta girgiza kai tace "ba komai..", pink lips dinta ya kalla da tayi mganar yace "ban yarda ba", ita dai bata kalli cikin idonsa ba kawai thick eyebrows dinsa take kallo, ta girgiza kai ba tace komai ba, shiru ne ya gifta for some seconds, slowly ya riƙo hannunta ya ɗora kan forehead dinsa, ta ɗan yi tsam kamar zata janye hannun daga goshinsa sai kuma ta fasa, ya gyara kansa sosai a laps dinta yace "Toh gashi dai na kama wata yarinya tana kallona, So ynxu sai a bani suna..", juya lulu eyes dinta tayi tace "A mafarki ko..", ya tattare girarsa yace "Nope in reality mna..", ba ta san lokacin da tasa finger ta fara shafa eyebrows dinsa ba tana bin zanenta, lumshe ido yayi yana jin ydda take yawo da slim finger dinta a girarsa, after a while ya buɗe idon yana kallonta, wni abu yaji yana sukar masa zuciya ya kasa dena kallonta, ta turo baki ganin kallon da yake mata sai kuma ta rufe masa idanu da palm dinta, murmushi yayi gami da sauke ajiyar zuciya, ta turo baki still bata bude masa idanu ba tace "Ni ka dena kallona haka..", ya rutsa tsintsiyar hannun data rufe masa ido ya fara ƙoƙarin zamar da hannun nata daga idonsa, ruff ta sake rufe masa idon ta hana ya buɗe, ai kam ya haƙura da buɗe idon amma kuma bai sakar nata hannu ba yace "Ohh really, Toh ni da aka mayar dani TV fa..", murmushi tayi tace "Allah Ni karka hango muni na kamin dariya..", murmushi mai sauti yayi yace "Nope... you know there's no water in desert..", a hankali ya zamar da hannunta ya buɗe idonsa yace "right..", ta langwaɓar da kai tace "yau ba aiki naga 9 ya wuce..?", da sauri ya miƙe zaune ya kalli clock, ya sauko daga gadon yana jan rigarsa yace "Omo me yasa baki tasheni ba wife...?", ta sauka daga gadon itama tace "Toh ai bacci kake ni bazan iya tashinka ba..", room slipper dinsa ya zura ya matsa daf da ita, cheek dinta yayi patting with one hand yace "really..", ta gyaɗa kai, soft smile yayi ya ja pointed nose dinta a hankali yace "bari na shirya.." da haka ya nufi door ya fita, Hajar tayi ajiyar zuciya sai kuma ta saka nata room slipper din da ya siya musu jiya irin ɗaya ta fita, downstairs ta sauka ta shiga kitchen, breakfast din da ta dafa ta fiddo dinning tayi setting table, palour ta dawo ta zauna kan Sofa tana jiran fitowarsa, after 10mins ta kalli stairs sai kuma ta tashi ta haura upstairs, ɓangarensa ta shiga da sallama, direct ta nufi bedroom ta buɗe ta shiga, tsaye ta gansa gaban mirror yana ƙoƙarin saka maɓallin riga, ta saukar da kanta ta matsa inda yake, dakatawa yayi da saka maɓallin ya juya yana kallonta, tayi murmushi ta matsa daf dashi, sosai tayi ɗage don ya kere mata a tsaho ta kai hannu ta ɓalle masa maɓallin, ta ɗauki Links dake kan mirror ta saka masa shima, tana ɗaga kanta taga kallonta yake, ta waro ido tace "Za fa kayi letti..", ya sunkuyo yayi pecking lips dinta lightly yace "Thank you", tare suka sauko downstairs tana riƙe da briefcase dinsa, duk da tasan sauri yake amma haka ta jasa dinning tace sai yaci abinci zai fita, tini tayi serving dinsa golden yam da offals pepper soup da ta dafa as breakfast, sharp sharp yaci fiye da rabin abincin, a kullum daɗin abincin matarsa ƙaruwa yake, har balcony ta rakasa tana riƙe da briefcase dinsa bayan ya gama, da haka ya wuce parking space bayan yayi pecking both cheeks dinta, Hajar ta juya ta koma ciki, ragowar abincin da ya rage a plate ta ɗauka ta kara kaɗan a kai taci, tea ma a mug dinsa ta haɗa tasha, bayan ta gama tayi clearing tables din ta haura sama tinda ta gama gyara gidanta tin sassafe, wayarta ta ɗauka tayi dialing numbern Umma, daman kullum ne saita kira Ummanta take samun sa'ida, suna gama waya da Umma ta kira Anty ma suka gaisa, saida suka gama waya da Anty ta tuna da abinda ta bata, ita bata san mene ne ba shiyasa bata basa wni muhimmanci ba, tashi tayi ta dauko ledar inda ta ajiyeta, ɗaya bayan ɗaya ta ringa duba robobin da suke dauke da wasu gari sai kace herbs, wni tunani ne yaxo mata, ko dai maganin ciwon mara ne Anty ta bata tinda taga azabar da tke sha, wnn tunanin yasa ta wuce kitchen da ledar tarkacen, bbu wnda bata ɗiba ta sha ba, wni soaking ake a ruwan zafi snn a sha wni kuma a zuba a madara, har wnda ta ajiye a fridge da yake liquid ne ta buɗe tasha, ita dai fatanta ciwon marar nan ya lafa mata, kafin ma ta bar kitchen din taji canji a jikinta don ba ƙaramin gabje gabje ta yiwa kanta ba, she don't care don ita gani take ai wni maganin sai anji zafi yake aiki, upstairs ta koma ta shiga ɗakinta ta kwanta kan gado don bacci take ji tinda bata koma ba tin Asuba.

★Ruqayyah ce ƙarshen fitowa bayan sun gama surgery din wajen ƙarfe biyu da rabi, slowly take tafiya tana kallon soft Clog shoe din ƙafarta, tasan cewa wnn shine last surgery da za tayi tare da Dr Uthman inba wni ƙudiran na Allah ba, Scalpel din hannunta ta kalla sai kuma tayi murmushi, slowly ta nufi washroom ta wanke hannunta da liquid soap, snn shima Scalpel din ta wankesa, wnn shine kaɗai memory din da zata bari nasa, wnn Scalpel din shi zata ringa gani ta tuna da abinda ya mata muguwar zarra a rayuwa, abinda a da nata ne amma tayi fatali dashi sbd rashin Sa'a, surgeon gown din jikinta ta cire ta zura Scalpel din cikin Scrub dinta, da haka ta nufi Nurse station, Nurse Jiddah ta tarar a station din tana rubutu jikin record book, Nurse Jiddah tace "kun fito daga surgery din..?", Ruqayyah tace "Neh..", Nurse Jiddah ta gyaɗa kai tace "how was it..?", Ruqayyah tace "Alhmdllh it was successful, you know Dr Uthman work..", Nurse Jiddah tace "Alhmdllh", Ruqayyah ta shiga wni room nasu na female Nurses da suke amfani dashi, bayan kamar 10mins ta fito ta saka black Abaya saman Scrub dinta da handbag a hannunta, Nurse Jiddah ta ɗaga kai ta kalleta tace "Are you leaving Rukky..?", Ruqayyah ta ja kujera ta zauna tace "Neh..", Nurse Jiddah tace "Ohk ai ya kamata ki huta gsky..", Ruqayyah tayi jimm sai kuma tace "Jiddah please can you move to our team..?", Nurse Jiddah tace "Laa toh bayan ga ki me zanyi a team din...", Ruqayyah tace "Am transferring from here, am leaving this hospital..", with weird facial expression Jiddah tace "Transfer..?", Ruqayyah tace "Eh kinga daga yau ma bazan sake zuwa ba, tin ranar Monday ma ya kamata na dena zuwa amma na ƙara lokaci..", Nurse Jiddah ta ajiye pen din hannunta tace "But why Ruqayyah..?, Salary dinki fa mai tsoka ne anan Asibitin..", Ruqayyah tayi ajiyar zuciya tace "Na sani Jiddah, muddun na cigaba da zama a asibitin nan toh ba zanyi moving on ba, zan ta zama ne wayaƙifa ba wni cigaba, barin asibitin nan shine salamata Jiddah", Nurse Jiddah dai duk jikinta yayi sanyi amma bata tmbayi Ruqayyah dalilinta na barin aikin ba, may be tanada wni personal issue ne daya danganci aiki a asibitin, haka dai ta yiwa Ruqayyah fatan Alkhairy jikinta duk a sanyaye, sunyi zaman lafiya da Ruqayyah wllh don batada wata matsala ko baƙin hali, ko irin gulmar nan ta asibiti da Nurses ke yi ita Ruqayyah ba ruwanta, gata da mutunci bata taɓa jin anyi faɗa da ita ba, snn kuma patients basu taɓa complain da ita ba duba da yadda Nurses suke zuba rashin mutunci a asibiti sai kace na ubansu, Ruqayyah tace "ngd sosai Jiddah insha Allah zamu cigaba da zumuncinmu..", Jiddah tace "Insha Allah kuwa..", Ruqayyah tace "Toh ya kin amshi position din nawa..?", Jiddah tace "Toh waye zai ƙi shiga surgery team din Dr Uthman, it's my pleasure wllh", Ruqayyah tayi murmushi don sosai taji daɗi da Jiddah ta amshi position dinta. saida Ruqayyah tabi duk colleagues dinta that were around a lokacin ta musu sallama, walking gently ta nufi office din last person da zata yiwa sallama, cike da nutsuwa ta shiga office din, ta dakata suka gaisa da Haleema, Ruqayyah tace "Dr yana ciki..?", Haleema tace "yeah..", da haka Ruqayyah ta nufi door din office din ta buɗe ta shiga da sallama, Nurain dake tsaye gaban table yana packing kayansa don gida zai wuce ya amsa sallamar ba tare da ya juya ba, daga bakin door Ruqayyah ta tsaya tace "Are you leaving Dr..?", yace "Yeah A Nurse is there any problem..?", ta girgiza kai tace "Not at All.. kawai dai zan maka sallama ne sbd na bar aiki a asibitin nan nayi transfer zuwa wni..", ya ɗan tattare thick eyebrows dinsa sai kuma ya juya yana kallonta da kyau yace "Why..?", ta saukar da kanta trying very hard not to burst into cry tace "Dr in other to move on i have to leave this hospital", ya ɗan kalleta na few seconds kafin yace "Ohk.. wish you best of luck A Nurse..", tace "Thank you Dr.." da haka ta juya har zata buɗe ƙofar ta fita sai kuma ta dawo tace "B Nurse, i mean Nurse Jiddah will take my position..", ya gyaɗa kai yace "Alright she is not bad..", tace "Sure Goodluck.." tana gama faɗin haka ta buɗe ƙofar ta fita, wata ball ce ta tsaya mata a throat kawai taji tears a cheeks dinta, da sauri tasa hannun ta goge, walking slowly ta bar wajen ta kama hanyar fita daga department din, Khaleel ta hango sai zabga sauri yake da file a hannunsa ya nufi hanyar wards, ta dan ɗaga murya ta kirasa, dakatawa yayi har ta iso inda yake tace "Saurin me kake..?", yace "Ohh kamar fa naji ana kiran Code blue ne..", ta ɗan yi murmushi tace "i think you need hearing aids fa..", ya shafa kunnensa yace "Koh.. ba wni Code blue da aka kira knn..?", ta gyaɗa kai tace "yeah kunnenka ne gsky..", ya sake shafa kunnensa yace "Dole a nemo hearing aids..", tace "Toh nidae da haka da hka sai nace sai wataran...", ya gyara tsayuwarsa yace "Department aka canza miki ne..?", ta girgiza kai tace "Ko ɗaya na bar aiki a hospital din nan ne..", shima dai kamar sauran bai ji daɗi ba, yace "What about our team..?", tace "B Nurse ta cike spot dina". Da yamma Ruqayyah ta shiga room din Momy, Ruqayyah na kallon Momy dake neman abu drawer din bedside tace "Momy me za'a dafa for dinner..?", Momy tace "Tuwon semo koh..?", Ruqayyah tace "Sai ayi Okra soup cause Daddy yafi sonta", Momy tace "Okay..", har Ruqayyah ta kai bakin ƙofa Momy tace "Amma are comfortable da canjin wajen aikin nan Ruqayyah daga Federal zuwa State..?", Ruqayyah tace "Ba komai Momy banbancin fa kaɗan ne shima wajen salery ne kuma kinga wnn hospital din da aka dawo dani yafi kusa da gida, few minutes ride naje bbu nisa..", Momy tace "Okay fine", Ruqayyah ta juya ta fita.

★Da daddare wajen ƙarfe goma Nurain na zaune palourn ɓangarensa da bowl din fruit salad da Hajar ta haɗa masa yana sha, kallon door yayi a wajen karo na uku, daga bari taje ta dawo shine har ynxu shiru almost 30mins da fitarta, ajiye bowl din fruit salad din yayi ya tashi ya nufi door ya fita, direct room dinta ya buɗe ya shiga, he automatically get froze ya kasa ƙarasa shiga, kawai kallon freshness of her body yake hancinsa na shaƙar ni'imtaccen ƙamshin da yake tashi a room din, Hajar dake zaune kan stool gaban mirror ta saukar da kanta ta cigaba da shafa manta, Nurain ya sauke ajiyar zuciya yana kallon duk inda ya bayyana a jikinta, ita dai tinda sukay ido huɗu ta ɗauke kanta, scratching kansa yayi sai kuma ya ɗauke idonsa dga kanta yace "Am waiting for you Baby wife..", ta ɗan kallesa tace "Toh", juyawa yayi ya bar wajen zuciyarsa na racing, yau fa 11days knn rabonsa da matarsa, he miss her over wllh, zaune yayi palour yayi resting da Sofa snn ya lumshe idonsa, fruit salad din ma ya haƙura da sha, shi a ynxu baya son komai sai Baby wife dinsa, after like 10mins ta shigo, saukar da kanta tayi ta ƙarasa shigowa ciki, can edge din kujerar da ya zauna ta zauna itama, ya bita da kallo cause rigar baccin da ta saka ƴar ɓingila ce, bowl din fruit salad din ya ɗauka ya matsa kusa da ita yace "want some..?", ta kalli bowl din ganin bai sha da yawa ba tace "baka sha ba... ko wnn bai maka daɗi ba..?", ya tattare gira yace "Wollah ba fruit salad nke so ba", ta waro ido tace "Toh me kake so naje na dafa mka..?", sosai ya matsa kusa da ita har jikinsu na gogar na juna, bai san lokacin da ya lumshe ido yana kallon wuyanta ba, Calmly yace "I need you wife..", turo baki tayi tana ƙoƙarin matsawa ya sauke mata wni chilled kiss a wuya, tini taji wni shock ya ratsa mata jiki tayi ajiyar zuciya, bata gama daidaita ba ya sake manna mata wni yana fesa mata numfashinsa a wuya wnda shima yke sake sakata shiga yanayin da bata shirya masa ba, muryarta na rawa tace "ka bari dan Allah..", ya ɗago kansa yana kallon fuskarta sai kuma ya amshe bowl din hannunta ya ɗora kan Centre table, yace "Okay fine.. gsky ina jin bazan ƙarasa baki labarin jiya ba..", ta langwaɓar da kai da muryar shagwaɓa tace "please ka ƙarasa min..", ya maƙe shoulder yace "Naƙi din" da haka ya tashi ya nufi bedroom, murmushi tayi sai kuma ta tashi ta bisa bedroom din, zaune ta gansa kan makeken gadonsa ya jingina da allon gadon yana latsa wayarsa, walking slowly ta isa gefen gadon ta zauna, ya ɗan kalleta sai kuma ya cigaba da latsa wayarsa, after a while bbu wnda yace uffan a cikinsu, ita dai tini sanyi ya fara ratsata, bata jurar zama a room din ba tare da ta lulluɓe ba, rubbing damtsenta ta ringa yi tana zuƙar baki, ya ɗan kalleta yayi slight smirk, tashi tayi daga gadon da nufi komawa room dinta, tini ya riƙo hannunta ya fixgota jikinsa, ai kam tini ta lafe ta kuma shige masa, yace "i can give you warm Baby wife..", ta lumshe idonta perceiving his scent, zamar da hular kanta yayi snn ya fara shafa soft hair dinta a hankali, ya kashe wayar ya ajiye kan bedside, lips dinsa ya kai saitin kunnenta ya raɗa mata wni abu, ɓoye fuskarta tayi a ƙirjinsa tace "Allah bana so..", yace "Ni ina so..", ta maƙe shoulder ba tace komai ba, yace "Okay only this.." da haka ya ɗago kanta ya fara kissing dinta slowly, he kissed her for almost 2mins, ta masa lamo bata hanasa ba duk da electric shock din da yake shigarta, ya haɗe forehead dinsa da nata yana ajiye numfashi, itama numfashin take ajiyewa a hankali, tini ya mirginata ta koma ƙasansa ya shiga kissing neck dinta, jin bata hanasa ba tayi masa lamo ya ɗago ya dubeta, sosai ya fahimci tana amsar saƙonsa ne, ya goga karan hancinsa a nata in a whisper yace "May I..?", a hankali ta gyaɗa kai sai kuma ta runtse idonta, saida taga yayi nisa snn tace "please off the lights..", da muryarsa da ta canza yace "No i wanna see my properties...", tace "Ni A'a..", ganin idan bai kashe fitilar ba zata masa gardama kawai ya danna control din lights din dake daf da gadon ya bar dim, lips dinta ya haɗe da nasa, lokaci guda ta zagaye wuyansa da dukka hannayenta ta mayar masa da martani a hankali, Uhmm At that night saida Nurain ya zagaye The Nine planets, ba karamin susucewa da zaucewa yayi ba, shima bai barta ba saida ya kaita har Pluto bayan ya zaga da ita sauran Planets din, bbu kalan sunan da bai kirata ba har dasu Empress, kyautar da ta sha kam ba a cewa komai don kaff arzikin duniyar ya mallaka mata. washe gari samm ta kasa haɗa ido dashi don wata masifaffiyar kunyarsa take ji, ga last night dinsu ya kasa barin brain dinta, memories din fresh suke dawo mata kwanya, bayan sunyi sallar asuba tare don yau a gida yayi sallahn sbd yana ma Alwala aka kabbara sallah a mosque, shiyasa yayi tare da matarsa a gida, yau kam gaisuwar ma juya masa baya akayi, shi dai sai blushing yke yana binta da kallo, gado suka koma suka kwanta, har yayi bacci ita kam ta kasa komawa, a hankali ta buɗe idonta taga fuskarsa daff da ta ta hakan yasa ta kafesa da idanu, After a while tayi murmushi sai kuma ta zame daga jikinsa a hankali, ta sauka daga gadon ta nufi door walking slowly, room dinta ta wuce ta faɗa kan gado, daga ita har shi saida Ni Feenerh feeche na yankar musu ticket a dawanau don na kasa gane wane irin murmushi suke tin wayeyar gari. ƙarfe takwas da rabi ta gama gyara gidan har breakfast ma tayi, room dinta ta dawo ta shiga wanka, bayan ta fito daga wankan tayi shafe shafenta, wardrobe ta buɗe ta ɗakko kayanta ta saka, gaban mirror ta koma ta yiwa gashinta boy and girl, da haka ta feshe jikinta da perfumes tana kallon yacca armless gown din ta mata a jiki, soft room slipper dinta ta zura ta fita, saida ta dubi door din ɓangarensa snn ta sauka downstairs, kitchen ta shiga after few minutes ta fito, tsaye tayi tana kallon stairs jin footsteps, saura stairs biyu ya kawo ƙasa ya dakata yana kallonta, ta riƙe ƙugu da hannu ɗaya ta langwaɓar da kai tace "Good morning My husband..." sai kuma ta sakar masa wani murmushi mai kyau, step ɗaya ya ƙara ya sauko, tsabar mamaki ya kasa cewa komai, Anya ba kunnensa ne yaji ba daidai ba, buɗe mata hannaye yayi alamar ta taho, ai kam da sauri ta isa inda yake tayi ɗage ta zagaye wuyansa tana murmushi, ƙugunta ya rutsa yayi hugging dinta sosai, lumshe idonsa yayi ya fara ɗan juyi dasu yace "please say it again Baby wife..", ta sake ƙanƙamesa snn tace "My husband..", tamke riƙon da yayi mata yayi tamkar zai ɓallata, lokaci guda ya rabata da ƙasa yana dariyar da bata taɓa jin yayi irinta ba......✍️

💛 HAJAR 💛

{84..}
After a while ya direta ya ringa kallonta without blinking, har lokacin murmushi ne kwance fuskarta, ya tallaɓi both cheeks dinta snn ya matso yayi pecking forehead dinta, lumshe idonta tayi a hankali ta ɗora hannunta kan nasa da ya tallaɓi cheeks dinta, slowly ya janye lips dinsa yana kallon eye ball dinta yace "Morning Sweet pie, how was your night..?", tace "fine alhmdllh..", yana patting cheeks dinta yace "Good..", da haka ta saki hannunsa da ta riƙe ta janye fuskarta ta juya ta shiga kitchen, bayanta yabi shima ya shiga kitchen din, Hajar ta juyo jin motsi a bayanta, ya ɗage gira yace "you need any help...?", ta waro ido sai kuma tayi ƴar dariya tace "No..", warmers biyu ta dauka akan Island ta nufi door, tana zuwa kusa dashi ya amshi guda ɗaya, tare suka kai warmers din dining, kitchen ta sake komawa zata dauko ragowar warmer din da plate da cup, footsteps taji a bayanta, ta ɗan juya ai kam taga shine biye da ita, tayi murmushi tace "why are you following me.?", yace "Cause you are my heart beat, I can't live without you..", ta ɗan kallesa sai kuma ta saukar da kanta ba tace komai ba, plates da cups ta miƙa masa ita kuma ta ɗauki warmer, da haka suke sake fita daga kitchen din zuwa dining, Chair ta ja masa tace "Sit", tini tayi serving dinsa abinda ta dafa snn ta haɗa masa tea, tana gamawa dashi ta ɗauki wni plate din ta zubawa kanta, duk abinda take yana kallonta kuma bai fara cin abincin ba, Chair din dake kusa dashi ta ja ta zauna, ta kai hannu zata ɗauki plate din abincin da ta zubawa kanta yayi sauri ya janye ya ɗaga plate din ya juye abincin cikin nasa, ta ringa kallonsa without saying anything, ya tura plate din tsakiyarsu yace "Eat alot..", ta dauki fork tana juyasa a hannunta tace "you too" da haka ta fara ɗeban abincin tana kaiwa baki, time to time suke haɗa ido su sakarwa juna murmushi, ita ta fara gamawa ta dauki shayinta tana sipping, tass ya cinye ya ture plate din yana hamdala, tashi yayi yace "let's me make A call upstairs..", ta gyaɗa kai tace "Ohk", yana haurawa sama ta tashi tayi clearing table din, gaban sink ta tsaya ta wanke duk kwanukan da suka ɓata, da haka ta haura upstairs itama, direct ɓangarensa ta wuce, bata tarar da shi a palour ba don haka ta nufi bedroom, shima nan din ba ta gansa ba, door din balcony ta gani a buɗe ai kam ta nufi wajen, tana leƙa balconyn ta gansa with Airpod still making a call, ya mata alama da hannu, ta girgiza kai ta dawo cikin ɗakin, dman nan ne kawai bata gyara ba don hka ta fara ɗame gado, kawai jinta tayi a kan iska an ɗagata sama, tayi ƴar ƙara tace "please let me down..", kan mirror ya ajiyeta ya tsaya daf da ita yace "yah... ba kya gajiya da aiki", ƙoƙarin sauka tayi daga kan mirrorn ya hanata, ta turo baki tayi pointing clock tace "Kaga..", ya kalli agogon sai kuma ya juyo yana kallonta yace "Mene..?", tace "ba kaga time ba ko yau ba aiki..?", ya ɗage shoulder yace "Nope bbu aiki a waje amma akwai a gida..?", ta ɗan juya lulu eyes dinta tace "Aikin mene a gidan..?", ya kwantar da kansa a chest dinta yace "you wanna me to show you..?", ta gyaɗa kai ba tace komai ba don sosai ta zama uncomfortable, After few seconds ya ɗago kansa ya ringa kallonta, itama kallon nasa take don haka tini idanunsu suka sarƙe staring at each other, ba tasan lokacin da ta kai hannu ba ta shafa thick eyebrows dinsa tare da kwantaccen sajensa ba, lumshe ido yayi snn ya sake buɗasu a kanta, tana shirin janye hannunta daga fuskarsa ya riƙe hannun ya cigaba da yawo dashi a fuskarsa da kansa, da haka ya kai hannun nata lips dinsa yayi pecking a hankali, ya sauke ajiyar zuciya yace "Am all yours wifey... and you're mine too..", ta saukar da kanta tana jin yadda zuciyarta ke racing, ya ɗago kanta da ta saukar lokaci guda ya kai babban ɗan yatsansa lips dinta ya fara shafawa a hankali, tana ganin ya fara kusanto da fuskarsa ga ta ta tayi sauri ta lumshe idonta, slowly lips dinsa yayi landing akan nata, gently ya fara kissing dinta kafin ya zama passionate, ta sake rutse idonta ta damƙe rigarsa da hannun bibbiyu, lokaci guda ta sauko daga kan mirrorn kafin ta shiga mayar masa da martani, tini ya dafe kan mirrorn don ji yayi kamar zai zube a wajen, habawa ai tini kiss ya koma french, after almost a minute ya haɗe forehead dinsu waje ɗaya yana ajiye numfashi, ita kam wni murmushi ne kwance fuskarta, ya ɗago ya kalli cikin eye balls dinta yace "I Love you", kawai kallonsa take tana jin kamar an saka zuciyarta a gidan ƙanƙara, ya tallaɓi cheeks dinta yace "I Love you so much my wife..", ɗage tayi snn ta fada jikinsa tana murmushi. A cikin sati huɗu da suka shuɗe wata narkakkiyar soyayya wcca ta amsa sunan ƙauna suke gwadawa junansu, yoh toh ƙauna mna don ta wuce a kirata da soyayya, within that period Hajar ta fahimci mijinta sosai tasan me yake so da kuma wnda baya so, ta lura cewa he is a simple person ba shi da da damuwa, ashe da don bata fahimcesa bane shiyasa take ganinsa rude, A fanin Nurain kam ynxu yasan cewa Hajar was more than his choice and type, tayi fice snn kuma tayi zarra a ycca yke son matarsa ta kasance, she's so good in every aspect, wajen Abincin kam ba'a cewa komai don she can cook varieties, ga kuma tsafta da take da ita ba'a cewa komai, snn kuma ga ƙoƙari wajen kula da bedroom things, a kullum kuma sai yaji taste din da bai taɓa ji ba shiyasa he can't get enough of her, kullum cikin sabon sauƙinta yake sai kace sabon Ango, yoh ko sabon Angon bazai nuna masa farin ciki ba. A tare suke saukowa daga stairs suna dariya, Hajar dake riƙe da briefcase dinsa ta waiga ta ɗan hararesa tace "you are teasing me...", ya ɗage gira yace "should I show you..", ya matso zai kamota, da gudu ta zille ta ƙarasa sauka daga stairs din tana dariya tace "Don't..", ya ƙarasa saukowa shima yace "please Baby wife be careful, kinga our little love beyi kwari ba...", dariya tayi har dasu riƙe ciki tace "Stop dreaming fa... ba wani little love", ya haɗe gira yace "ke wa ya gaya miki bbu..?", ta langwaɓar da kai tace "kai wa gaya maka akwai..?", waro ido yayi sai kuma ya nuna kansa yace "Am A Doctor you know..", tayi murmushi tace "Fake Dr ba" da haka ta juya ta buɗe ƙofa ta fita balcony, bayanta yabi ya fita balconyn shima yace "ba zaki dena denying ba..", collar din rigarsa ta gyara masa tace "Am not denying", ta matsa daf dashi ta saukar da kanta, slowly ya sunkuyo yayi pecking forehead dinta, da haka ta miƙa masa briefcase din tace "Allah ya tsare My Moon..", yace "Ameen Baby girl", har ya juya zai tafi tace "Amm Moon..", ya dakata, ta ƙarasa inda yake tace "Na manta ban gaya mka zan shiga nan neighbor house na yiwa matar gidan barka ba..", yace "Ohk Okay..", tayi murmushi tace "A dawo lfy". Wajen ƙarfe sha ɗaya na safe Hajar ta shirya zata shiga ta yiwa makwabciyar ta ta data haihu barka, 3 week da suka wuce ne ta samu ta shiga makwabtan nata suka gaisa, Ashe ma sun sha zuwa zasu shigo sai ace musu matar gidan bata nan, wataran kuma da suka zo ko mai gadi basu tarar ba, da suka gaya mata lokacin sai taga ai lokacin bikin Noor ne da kuma lokacin da suka tafi Abuja, daman tin farkon kawota abinda yasa taƙi shiga makwabta sbd gani take gidan ba wajen zamanta bane don haka mene na shiga neighbors, ynxu kam mene zai rabata da mijinta ai saidai mutuwa, Hajar na isa gate mai gadi ya buɗe mata door bayan ya gaisheta ta amsa, gidan da ke opposite din nata tayi knocking, A madaidaicin palourn gidan da yake kamshin turaren wuta ta zauna, few minutes matar gidan wacca ake kira Oum Sulthan ta fito, tana ganin Hajar ta mata murmushi snn ta zauna suka gaisa, Hajar ta mata barka, Oum Sulthan tace "Wanka ake yiwa Babyn..", Hajar tace "Okay tom.. ina Boy..?", Oum Sulthan tace "wai Sulthan yana Schl..", Oum Sulthan da kanta taje ta kawowa Hajar Babyn bayan an gama mata wnka, Hajar ta ringa kallon Baby girl din tana jin kamar ta tafi da ita, the Baby is so cute amma kuma ba fara bace, kana kallonta kaga Maamanta don kamarsu ɗaya, Oum Sulthan baƙa ce ƴar Maiduguri amma kuma kyau ba'a cewa komai, Hajar na shafa soft cheeks din Babyn tace "kamar na tafi da ita wllh..", Oum Sulthan tace "Na bar maki ki tafi da ita, indai Sulthana ce ko 1hour ba za tayi ba zaki nemi hanyar nan gidan..", Hajar tayi murmushi tace "wnn cutie din ce za ace tana rigima..", Oum Sulthan tace "Uhmm shiyasa nace ki tafi da ita kinga idan ta nuna miki halin shknn", Hajar ba ta wani daɗe ba ta yiwa Oum Sulthan sallama ta tafi gida bayan ta ajiye mata ledar da ta shigo da ita. Da daddare wajen ƙarfe takwas da rabi Hajar na tsaye gaban wardrobe tana mayar da boxes din da ta fiddo ta ɗauki new Sleeping gowns, slowly take yin aikin tana humming song, buɗe ƙofa akay Nurain ya shigo, daga bakin door ya tsaya hannunsa ɗaya cikin wandon white pajamas dake jikinsa yace "Baby yau ba kallo naga lokacin fara Stuffs dinki ya kusa..?", tace "Am coming My Moon", yace "Ina downstairs palour..", ta ajiye abinda ke hannunta ta nufi inda yake walking like a cat, tana zuwa kusa dashi ta zagaye wuyansa with both hands ta ɗan yi kissing karan hancinsa tace "Mr Coffee..", yace "Neh Sweet pie..", tace "yau ma akwai wnn yummy coffee din..?", ya goga karan hancinsa a nata yace "shi little love yake so knn..?", tayi twinkling eyes dinta ta gyaɗa kai, ita dai tasan bbu wni little love kawai ta gyaɗa kai ne don ta sha coffee din, sosai ta hango annuri a fuskarsa, yace "do you like it with Popcorn...?", ta gyaɗa kai, yace "Ohk..", A hankali ta janye hannunta daga wuyansa tace "Thank you Cappuccino..", murmushi yayi kafin ya kullo mata ƙofar ya sauka downstairs, tini Hajar ta ƙarasa mayar da kayan, gaban mirror ta matsa ta sake shafe jikinta da turare bayan wnda ke jikinta, room slipper ta saka ta nufi door, Walking gently ta sauka downstairs, palourn bbu haske ko ɗaya sai na TV dake aiki, ta kalli kan Centre table taga Popcorn, ta zauna kan Sofa gami da daukar remote ta canza channel zuwa wacca take so, cup din Popcorn ta ɗauka ta fara watsawa a baki, kamar wcca aka mintsila haka ta ajiye Popcorn din ta tashi da sauri ta nufi kitchen, tana buɗe kitchen din ta gansa yana tsiyaye Coffee din a mug, a hankali ta mayar da ƙofar ta rufe ta koma palour ta zauna tana murmushi, she's very proud of her husband wnda sam ba shida rawanin tsiya wato girman kai, After like 2mins ya fito daga kitchen din, a kusa da ita ya zauna ya miƙe mata Mug din, ta amsa da murmushi a fuskarta tace "Thank you..", Shi dai yana zaune palourn ne amma ba kallon yake ba danne danne yake jikin laptop, ita ce take kallon tana shan Coffee dinta, time to time yake kallonta sai kuma ya cigaba da abinda yake, wnn dai haɗin sai aikin little love ace Popcorn with coffee, kuma ya lura daɗin abinta take ji, saida taci wajen rabin Popcorn din ta juya tana kallonsa tace "Moon", yana operating laptop yace "Uhmm", tace "baka ci ne..?", ya juyo yaja hancinta yace "sai Baby love ya ƙoshi..", guda ɗaya ta ɗauki Popcorn din ta kai saitin bakinsa tace "Haaa", ya buɗa baki ta saka masa, hka nan ta cigaba da yi indai za taci shima sai ta basa, dena operating laptop din yyi snn yayi gefe da ita yace "This is not romantic..", Cup din popcorn din ya amsa, ita dai ta bisa da kallo, Uhmm ai kam tini ya fara gwada mata romantic one.

★Ranar da akai Arba'in din Baba a masallaci akai Addu'a snn akay sadaka, Hajar ma taje gida a ranar kuma da wuri Nurain ya ajiyeta, washe gari Huzaifa ya koma schl don tintini ma hutunsa ya ƙare, Sa'adatu kam tafi sati uku rabonta da gidan kuma ranar arba'in ma ba tazo ba, Maimuna kuma cikin jikinta ya tsiyaye wnda hkan ya haifar mata da wni azababben ciwon ciki, Nabilah kuma har yau zaman doya da manja suke da Maama da Maimuna, gaba ɗaya ta ɗauke musu wuta sam bata shiga sabgarsu, a fannin Umma kam bata samu wata matsala ba sam a gidan, don Maama bata shiga huruminta saidai kallon banza, Abincin ya wadata a gidan don ko rabin wnda Abba ya kawo ba suci ba, Naseer ne yke bada kuɗin cefane. Umma na zaune kan darduma bayan ta idar da sallar la'asar Nabilah tayi sallama, Umma ta bata izini snn ta shigo, Nabilah ta sunkuya tace "Umma tsintsiya zan ɗauka zanyi shara", Umma tace "Toh ga ta nan a bayan ƙofa", Nabilah ta tashi ta ɗauki tsintsiyar snn ta fita, Umma tabi bayanta da kallo sai kuma ta girgiza kai, ynxu yaushe rabonta da shara da wanke wanke duk Nabilah ce ke mata, bbu jimawa da fitar Nabilah sai ga Mu'azzam ya shigo, ya duƙa ya gaida Umma da ladabi, Umma ta amsa snn tace "yau da wuri aka taso aiki knn..?", ya shafa kansa yace "Eh ai ba ma aikin naje ba..", Umma tace "Au toh..", Mu'azzam ya gyara zamansa sosai yace "Umma kwanakin baya nace zan siya miki gida idan Allah ya bani iko, Toh Alhmdllh yau Allah ya bani iko na siya miki gida Ummanmu" ya ƙarashe yana ciro keys daga Aljihunsa, hannunta ya kamo ya damƙa mata keys din, Umma ta sauke ajiyar zuciya tana kallon keys din, Addu'a sosai ta masa ta saka masa Albarka sai kuma ta girgiza kai tace "Ibrahim sai ka ƙunduge kuɗin da kayi shekara da shekaru kana tarawa ka siya min gida, A'a Ibrahim ka ajiye gidan..." da sauri ya katseta da faɗin "Dan girman Allah Ummanmu..", Umma dai na riƙe da keys ta kasa cewa komai. Sabrah na dawowa daga islamiyya Umma ta aiketa ta siyo mata katin waya, tini Umma ta loda katin a waya ta shiga kiran Anty, Anty na picking bayan sun gaisa Umma ta gaya mata komai, Anty tace "Alhmdllh Allah yayi masa Albarka ya buɗe masa hanyoyin samunsa ta ko ina..", Umma tace "Ameen..", Anty tace "kinga shknn mgnar inda zaki koma da zama ta mutu ynxu kawai gida za muje mu gani sai mu saka ranar tarewa...", Umma tace "tarewa kuma Jamilah A'a nikam nafi son na gama takaba a nan..", Anty tace "Haba Addah a sabon gidan ma ai zaki cigaba da takabarki, wllh kwata kwata zamanki da wnn matar beyi min ba kullum cikin fargaba nake", Umma tace "Wllh bbu abinda yake haɗani da ita, ba ruwan kowa da kowa", Anty tace "Ah a fa muka san me take ƙullawa tinda Allah ya kawo miki liɗifi ɗan albarkar yaronki ya siya miki gida toh ba zaki cigaba da zama a gidan nan ba", kwana biyu bayan nan Anty tazo ta amshi muƙulli taje ta gano gidan tare da Mu'azzam, Tinda Anty ta dawo takewa Umma santin gidan, ɗan madaidaici ne mai 2 bedrooms da palour sai kuma wni ƙaramin ɗaki a soro, sosai Anty tayi mamaki da taga anyi furnishing gidan da funiture masu rangwamin kuɗi, wnn funiture kam da kuɗinsu na gado shi da Hajar aka siyesu, tini aka tsayar da ranar tarewar Umma nan da kwana biyu, ranar tarewa kuwa tin wuri Umma ta shirya ta shiga makwabta ta musu bankwana, kayan sakawa kawai suka ɗauka, gwalegwajin funiture din Umma kam an fita dasu an siyar dasu a hka duk da cewa ba suyi wata daraja ba, Mu'azzam ya shiga ɗaki ya ɗauki jakar kayansu zai fita da ita, kasaƙe yyi yana kallon Nabilah dake zaune kan cement din ɗakin tana kuka Umma sai bata baki take, shi dai yayi waje abunsa da jakar kaya, Umma tace "Toh Nabilah nace kije ki dauko kayanki mu tafi...", Nabilah na sharar hawaye tace "Wllh Maama bazata barni ba..", Umma tayi ajiyar zuciya tace "bari na gwada sa'a ta na tmbayeta", da haka Umma ta nufi ƙofa ta fita, bakin ƙofar ɗakin Maama ta tsaya tayi sallama, Maama ta kalli labulen tace "waye ne..?", Umma tace "Nice..", Maama ta fito da ɗaurin ƙirji tana hura hanci tace "Ince dai lfy..?", Umma tace "zaman tare dai ya ƙare tinda Allah ya ɗauke wnda ysa muke zaune a tare, Ni zan tafi ina miki fatan Alkhairy, zaman da akay tare kuma a yafi juna..", Maama ta yamutse fuska tace "Au toh Alla raka taki gona can ƙauyen naku zaki koma..?", Umma tace "dan Allah ina roƙonki wata alfarma guda ɗaya a rayuwa..", Maama tayi kasaƙe tana kallonta, Umma tace "ki bani Nabilah na tafi da ita", wni kallon hadarin kaji Maama ta mata kafin tace "Eh ba shakka da yake ke kika durƙusa kika haifarmin ita dole kice hka, lokacin da na leƙa lahira na haifeta kina wajen ne, ko an gaya miki ƴar kyanwa ce da za kice na baki, yoh Allah na tuba ko ɗan karena bazan baki ba ballantana ƴar ciki na", Umma ba ta sake cewa komai ba tabar wajen, daman dai karambani tayi don tasan ko sama da ƙasa zasu haɗe Maama ba yarda za tayi ba, Nabilah kaf taji abinda ya faru ai kam ta sake fashewa da kuka, Sabrah sai binta take da kallo, Umma ta bawa Nabilah muƙullin ɗakin nata tace ko za tayi amfani dashi, Umma na hawaye ta kama hanyar soro Sabrah biye da ita, Nabilah dake kuka sosai sai kace uwarta ce zata barta ta wafci hijab akan igiya zata fita, Maama dake tsaye tsakar gidan tace "Alqur'an kika fita saina tsine miki albarka", Nabilah ta durƙushe wajen tana hawaye, har ga Allah Umma kawai take gani a gidan nan ta samu salama.

★Nurain ya juya yana kallon Hajar wcca take bubbuga ƙafarta a ƙasa tana kuka wnda yasan na shagwaɓa ne, ya sauke numfashi yace "Baby girl what now..?", ta buga ƙafarta a ƙasa tace "Ni dae zan bika..", yace "gidan Mami fa zanje, ki bari idan na dawo sai na kaiki kici seafood ai kinji daɗin na rannan ko..?", ta maƙe shoulder tace "Ni gidan Mami nake son zuwa..", yayi slight smirk ya haska mata agogon wrist dinsa yace "kinga fa ynxu ƙarfe huɗu da rabi before 6 insha Allah zan dawo", habawa ai tini hawaye suka hau zarya cheeks dinta tace "dan Allah Moon ka tafi dani..", ya sauke ajiyar zuciya yana kallon yacca ta jiƙa fuskarta da ruwan hawaye, ya girgiza kai yace "you're for real Baby wife ɗakko veil dinki", da sauri ta juya ta fara hawa stairs, yace "be careful fa..", ta juyo ta kallesa sai kuma ta juya ta haura saman, few minutes sai gata ta dawo sanye da hijab da handbag a hannu, ya ringa kallonta sai kuma ya girgiza kai yace "kin fiya rigima Baby wife..", ta turo baki ta wuce ta nufi door don kar ma yace ya fasa zuwa da ita, bayanta yabi ya rufe gidan da key snn suka wuce parking space, saida ya gama warming mota suka bar gidan, with minimum speed yake driving din, ya ɗan kalleta yace "kin ce dai ba kya son seafood din ko..?", ta girgiza kai tace "A'a ni bance bana so ba fa..", yace "what do you mean..?", tace "Ni dae cewa nayi ina son zuwa wajen Mami amma bance bana son seafood ba", yace "Uhmm ni zaki yiwa wayo yarinya", ta kyalkyale da dariya tace "kaga idan muka dawo daga gidan Mami da daddare sai muje yawo ma..", yace "hmmm yarinya ai yau kam kinci taliyan ƙarshe..", Nurain yayi parking bayan sun isa gidan, tana biye dashi suka nufi entrance, buɗe ƙofar palourn yayi ya shiga da sallama, da sauri Khausar dake zaune ita kaɗai a palourn da Laptop gabanta ta amsa sallamar, ta ɗan yi murmushi ta buɗe baki za tayi mgana knn ta hango Hajar, lokaci guda ta ɗaure fuska ta ɗauke idonta daga kallonta.......✍️
💛 HAJAR 💛

{85..}
Khausar na kallon Nurain tace "Ya sannu da zuwa, ina yini...", a takaice yace "lfy lou Lil sis.. yaushe kika zo?", tace "ɗaxu da safe..", ya gyaɗa kai ya nufi part din Mami, Hajar tabi bayansa da kallo sai kuma ta kalli Khausar da ta cigaba da abinda take jikin laptop, Hajar tace "Hi Khausar...", ko kallonta Khausar ba tayi ba tace "Sannu fa", Hajar bata sake mata mgna ba ta zagaye ta shiga part din Mami, bata tarar da kowa ba a palourn Mamin don hka ta samu kan carpet ta zauna, kawai saita fara tunanin shin me ta yiwa Khausar ne da take mata haka, ita dai a iya saninta tasan bbu abinda ya taɓa haɗasu tin farko, ta taɓe baki ta zuge handbag dinta ta ciro wayarta, ƙofar bedroom aka buɗe Mami ta fito Nurain na biye da ita, Mami ta karkaɗa ɗan yatsa tace "kaga Nurain ka fita daga idona na gaya maka..", ya shafa kansa yace "Please our Mami just this one..", Mami ta haɗe gira tace "No" da haka ta ƙaraso cikin palourn tana kallon Hajar fuskarta ƙumshe da murmushi, Hajar ta ɗan russuna tace "Mami barka da fitowa...", Mami tace "yau daughter.. sai kuma kika zauna a ƙasa", Hajar tace "ba komai nafi son ƙasan ne", saida Mami ta zauna kan Sofa snn Hajar ta gaisheta cike da ladabi da nutsuwa, Mami ta amsa mata tana tmbyarta ya take, Nurain dai yana tsaye ta bayan kujerar Mami sai kallonsu yake, ƙofar palourn aka buɗe Khausar ta shigo da sallama hannunta riƙe da Laptop, ta ƙaraso ta zauna kan Sofa ta ɗora Laptop din kan laps dinta, Mami tace "rubutun project din ne dai..", Khausar ta langwaɓar da kai sai kuma tace "Eh.. wllh duk na gaji Mami..", Mami tace "Bature ne ya riga ya bar mu da kazar whala..", Nurain yace "project take yi ne..?", Mami tace "Eh... gashi kuma next week zasu fara exams shiyasa akay tafiyar bbu ita", Nurain ya gyaɗa kai yace "Su Aunt Zulaihah sun tafi knn..?", Mami tace "yeah yau da safe suka wuce", ya kalli Khausar yace "A chapter na nawa kike..?", tace "Two", zagayowa yayi ya zauna kujerar dake kusa da nata yace "Muga Chapter 1..", tace "Ohk" da haka ta fita duba inda Slide din yake, Mami tace "yauwa ka duba mata kafin tayi submitting...", Hajar dai na zaune palourn tana kallon wayarta, Khausar na nemo Chaptern ta miƙe masa Laptop din ya fara duba mata, ta zauna hannun kujerar da yake, Hajar ta ɗaga kai ta kallesu sai kuma ta kaudar da kanta, knocking door akay mai aikin Mami ta shigo, saida ta gaishe da kowa na palourn har Hajar snn tace "Hajiya an kawo kayan marmarin..", Mami tace "Ohk.. An gama haɗa garin kunnun..?", Laure tace "A'a shi dai nake haɗawa..", Mami tace "Jeki ki cigaba da aikinki don gobe da safe zanyi amfani dashi insha Allah..", Laure tace "Toh Hajiya" da haka ta tashi ta fita. Bayan sallar magrib Mami na zaune kan prayer mat da ta idar da sallah a bedroom dinta Khausar ta shigo, a hankali ta ƙarasa ciki ta duƙa gaban Mami, Mami na kallonta tace "ya akai daughter..?", Khausar ta saukar da kanta tana twisting fingers tace "Mami dman cewa nayi zanje gidan Yaya sbd na samu ya ringa dubamin chapters din dana rubuta, ko 5days nayi sai na dawo kafin mu fara exams..", Mami tayi ajiyar zuciya tace "Toh shknn ai kam sai kinfi samun lokacinsa a can gidan nasa tinda nan sai yamma yake zuwa, kin gaya masa ne..?", Khausar ta girgiza kai tace "No i ask you first..", Mami tace "Alright i will tell him..", Khausar tace "Toh" da haka ta tashi ta fita. Nurain na dawowa daga mosque sallar isha'i yaga Hajar ta shiga kitchen, murmushi yayi ya bita kitchen din, tarar da ita yayi ta buɗe fridge ta ɗauki ruwa tana zubawa a glass cup, ya ƙarasa inda take ya rutsa cikinta, sosai ta firgita don ba taji shigowarsa ba, ta zaro ido after perceiving his scent tace "This is not proper nan fa gidan Mami ne...", yayi kissing neck dinta yace "Toh mu tafi gidanmu..", zaro ido tayi don gani take tsaf wni zai iya shigowa ya gansu, ta marairaice tace "Moon ka bari please... Allah wani zai iya shigowa", ya sake manna mata wani kiss din yace "Toh ina ruwana, nida matana", habawa ai tini ta fara ɓamɓare hannunsu daga cikinta, sakinta yayi sai kuma yayi Chuckling yace "bari na yiwa Mami sallama sai mu tafi" yana gama faɗin haka ya juya ya fita, tana ganin ya fita ta sauke ajiyar zuciya, ta ƙarasa tsiyaya ruwan ta sha. Direct Nurain ya wuce part din Mami don yi mata sallama, bai sameta a palour ba don hka ya shiga ɗaki, sallah ya tarar tana yi, kawai ya ɗan kwanta rigingine a kan gado yana jiran ta idar, tana idar da sallahr ta juya ta kallesa sai kuma ta fara jan counter, Nurain ya ɗan ɗago kansa sai yaga ashe ta idar, Mami ta gaya masa cewa Khausar zata bisu gidansa, ɗan jimm yayi bai ce komai ba, Mami tace "Any problem with that..?", ya girgiza kai yace "No.. not at all..", tace "Okay", Hajar ma ta shigo ta yiwa Mami sallama snn ta ɗauki handbag dinta ta fita compound don already Nurain ya fita yana jiranta, a mota ta tarar dashi, ta buɗe front seat ta shiga snn ta kullo ƙofar, ya kamo hannunta yace "Baby wife..", ta juya ta kallesa tace "Moon..", yayi murmushi yace "Tare da Khausar zamu tafi, i hope baki da damuwa akan hakan ko?", ta girgiza kai tace "Ba komai ƙanwarka ce fa", babu jimawa sai ga Khausar nan ta fito da jakar kayanta a hannu, back seat ta buɗe ta saka jakar snn itama ta shiga, Nurain ya juya kaɗan yace "baki manta komai ba ko..?", tace "Eh i think so", slowly yaja motar suka bar harabar gidan, suna hawa saman titi ya ɗan kalli Hajar yace "Sweet pie mu siya seafood din ne..?", da mamaki ta dubesa sai kuma ta gyaɗa kai tace "yess", yace "Okay" da haka ya ɗauke kan motar ya canza hanya, firarsa kawai yake da matarsa cikin farin ciki da ƙaunar juna, Khausar dai na maƙale a baya tana danna wayarta amma fa kunnuwanta na kan firarsu, haba ai Nurain har sakin layi yke don a zahirin gsky ya mnta da wata Khausar a motar, Hajar ta juya idanunta ta matsa kusa dashi ta rage murya tace "Moon akwai fa back sitter..", sai a lokacin ya farga ya shafa kansa yana murmushi, bayan sunyi tafiya mai nisa yayi parking a katafaren wajen da foreigners din suke siyar da seafood, kashe motar yayi yace "what do we do... muci anan ko kuma muyi takeaway..?", Hajar tace "Takeaway..", yace "Okay", tace "with lot of Shrimp Moon", ya ja hancinta ya rage murya yace "shi Baby love yafi so knn..?", ta turo baki ba tace komai ba, Khausar dake back seat ya kalla yace "Lil sis kema kina cin seafood..?", Khausar tace "Eh Yaya", yace "Ohk", buɗe motar yayi ya fita, After 5mins Hajar tace "Khausar duk ciki Shrimp yafi daɗi ko..?", Khausar tace "Nope ni kam Octa yafi min daɗi..", Hajar tace "Ohk ni kam Shrimp din nafi so", Khausar ta taɓe baki tace "Toh ke kam ai ynxu bazaki gane wanne yafi daɗi ba tinda yaushe ma kika fara cin seafood din, nasan ba ci kike ba a da, koda yake a inama kika gansa bare kici, Ai sai kayi kamar 1yr haka kana ci kake gane best..", samm Hajar bata gane mgana Khausar ta gwaɓa mata ba, tace "Okay", 15mins Nurain ya ɗauka kafin ya fito, leda biyu yayo shi da Hajar sai kuma na Khausar ita kaɗai, Tara da rabi suka isa gida, Hajar tini ta wuce ɗakinta don so take tayi wnka saita zauna zaman cin seafood din, Khausar ta ƙarewa palour kallo sai kuma tace "where am I staying..?", Nurain ya nuna mata hanyar guest room yace "that room..?", ta gwalo ido tace "Na shiga uku, ni kaɗai zaku bari a downstairs..", yace "Ashe matsoraciya ce... Alright come with me..", da haka ya nufi stairs, ta ɗauki jakar kayanta tabi bayansa, extra room dake upstairs ya nuna mata yace "Are you Okay with this one..?", ta buɗe ɗakin ta leƙa sai kuma ta juyo ta gyaɗa kai tace "Sure", yace "Akwai bedsheet da blanket a closet, and if you need anything let me know...", ta gyaɗa kai tace "Toh", ta ɗauki jakar kayanta ta shiga ciki, ɗakin Hajar ya buɗe bai ganta ba, motsinta ya jiyo a bathroom don haka ya juya ya fita. Ƙarfe goma da minti shida Hajar ta sauka downstairs, hijab ne har ƙasa a jikinta wnda ta ɗora saman kayan bacci da ta saka, kitchen ta shiga ta buɗe fridge ta ciro lemon kwali da bottle water, ta ɗauki plate ta ɗora kan tray tare da ruwa da lemon, tana fitowa kitchen din taga Khausar na saukowa daga stairs, Khausar na matsawa kusa da Hajar taji wni shegen ƙamshi yana tashi a jikinta, Khausar tace "Amm ina house help room dina is so dusty inaso a sharemin..?", Hajar tace "we don't have one..", Khausar ta rumgume hannaye tace "ban gane ba toh waye yake aikin gidan...?", Hajar tace "Nice nake gyarawa", Khausar ta taɓe baki tace "chab snnu ni kam bazan iya donkey work din nan ba, anyway maybe kin saba da whala shiyasa", Hajar ta ɗan kalleta sai kuma tace "Uhmm ko baka saba da whala ba ai dai ka gyara gidanka", Khausar ta juya idanunta tace "Ohk ni ynxu wane zai gyara min ɗakin ina so na kwanta ne..?", Hajar tace "wa kwa zai gyara miki ke zaki gyara abinki ai" da haka ta zagayeta ta nufi stairs, da sauri Khausar ta sha gabanta tace "kince fa ke kike gyara gidan so ki gyara min room din mna", Hajar tayi ɗan murmushi ta wurga manyan idanunta tace "kin shekara ba'a gyara miki ɗaki kin kwanta ba, ki shiga kitchen a store akwai broom da packer da Mop ki gyara abinki Khausar, idan kuma hka zaki kwana ba gyaran saiki rubuɗa a ƙura..", Hajar na gama faɗin haka ta haura sama abinta, direct kuma turakar mijinta ta shige, haka dai Khausar ta ɗauki kayan shara taje ta gyara ɗakin fess. Washe gari as usual bayan Hajar ta idar da sallar asuba ta fito ta gyara gidanta, ta bulala masa turaren wuta mai mugun ƙamshi, ynxu samm ba tada case a fannin ƙamshi don Oum Sulthan makwabciyarta sana'ar siyar da turaruka take na gida da kuma jiki, turarenta kam ba'a cewa komai sbd ƙamshi, har na Sudan India da sauran ƙasashe da suka san turare tana siyarwa. Hajar na gama gyaran gidan ta shiga kitchen ta shirya lafiyayyen breakfast, dining ta kai ta ajiye snn ta wuce room dinta ta fesa wnka, daga hka ta wuce ɓangarensa don taimaka masa wajen shiri tinda yau zai fita aiki, tare suka sauko downstairs tana riƙe da briefcase ta cokala hularsa a kanta, dining suka zauna ta zuba masu Irish a plate ɗaya, sai kuma ta ɗauki bowl ta zuba masu Offals pepper soup, da haka ta ja kujera ta zauna, yace "Heartbeat ina Khausar..?", tace "ina jin bata tashi ba..", yace "Ohk", tace "Na ajiye mata nata a kitchen..", yace "Thank you..", tayi murmushi tace "Eat alot", ta ƙarƙashin table din ya zura hannu ya shafa tummy dinta yace "you too, baby love ma yaci da yawa", ta juya idanunta ba tace komai ba, jin footsteps alamar ana saukowa daga stairs ta fara ƙoƙarin cire hannunsa daga tummy dinta, Khausar ta ƙarasa saukowa ta ɗanyi bowing tace "Good morning Yaya", yace "Morning how was your night..?", tace "great Alhmdllh", ita dai Hajar abincin ta kawai take ci, juyawa Khausar tayi zata koma saman Nurain yace "come join us..", walking gently Khausar ta isa dining din taja kujera ta zauna, sai a lokacin Hajar ta ɗago kanta ta ɗan kalli Khausar tace "kin tashi lfy..?", a takaice Khausar "Eh lfy..", Nurain ya tura mata warmers din abincin gabanta, Khausar ta buɗe ƙaramar warmern tana kallon farfesun da yake fitar da wani ƙamshi mai daɗi, tini yawunta ya tsinke amma saita yamutsa fuska ta rufe, warmer din Irish da kwai ta buɗe itama ta rufe, cup ta ɗauka ta haɗa shayi ta fara sha, Khausar ta ringa satar kallon Hajar don har ynxu hularsa ce a kanta, ganin Khausar na shan shayi bata zuba abincin ba Nurain yace "ki zuba abinci fa..", ta girgiza kai tace "Amm bana cin offals..", ya gyaɗa kai yace "Ohk then, you should cook something else karki zauna da yunwa...", tace "No am okay with the tea", bai sake cewa komai ba suka cigaba da cin abincinsu, Hajar ce ta fara gamawa don haka ta jirasa har ya gama, miƙewa yayi ya riƙo hannun Hajar itama ta miƙe, ya kalli Khausar yace "saina dawo sai muyi karatun ko..?", tace "Toh a dawo lfy..", tabi hannunsu dake riƙe cikin na juna da kallo kafin ta cigaba da shan shayinta, suna fita balcony ya rage tsaho ta ciro hularsa dake kanta ta kafa masa, hannunta dake cikin nasa ya murza yace "stay safe wife..", ta matsa gaff dashi ta sunkuyar da kanta, a hankali ya sunkuyo yayi pecking forehead dinta, yace "Then your turn..", tace "What..?", ya taɓa lips dinsa yace "Peck", ɗaya daga cikin kujerun dake balcony din ta taka ydda zata kamo tsahonsa, murmushi tayi ganin yacca ya wni lumshe ido wato yana jira, saida ta goga karan hancinta a nasa snn ta basa light peck a lips, da uban gudu har dasu tuntuɓe Khausar dake maƙale jikin ƙofa ta koma ta zauna kan sofa, Hajar ta shigo da murmushi a fuskarta, kallo ɗaya ta yiwa Khausar ta haura upstairs tana humming song. Hajar ba ta sake sakkowa ba sai sha ɗaya da rabi, kasaƙe tayi tana kallon palour, an wurgo da kaf throw pillows din kujeru kan carpet, ga ɓawon Abaya da seeds din Apple kaca kaca a ƙasa, Khausar ce zaune kan doguwar kujera ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, ga Orange nan a gefenta tana sha ta tara ɓawon akan hannun kujerar, ko a jikinta kawai typing dinta take a jikin laptop, Hajar tafi 50secs tana kallonta kafin ta juya ta shiga kitchen, turus tayi a bakin kitchen din ganinsa kamar anyi yaƙin badar, gaba ɗaya cupboard a buɗe suke, ga uban kayan wanke wanke da suka cika sink, everywhere was untidy, 30mins ta ɗauka tana gyara kitchen din, toh wai hka ake girki ko kuma dai wulaƙanci ne, gaba ɗaya an ƙone tukwanen da akay girkin, da tazo mopping kam saida tayi da gaske don wni uban vegetables oil ne malale kan tiles, saida ta gama gyaran kitchen din snn ta ɗora lunch, snow rice din da tayi draining ta mayar kan wuta don tayi steaming, fita tayi daga kitchen din, at that time Khausar bata nan, Hajar ta girgiza kai tana kallon palourn lokaci guda ta duƙa tayi picking ɓawon Ayabar ta kai dustbin, throw pillows din kuma ta mayar dasu kan kujera, room dinta ta koma tayi sallar Azahar, downstairs ta sauko don tasan shinkafar ta gama steaming, Khausar ta tarar A palour still dai Laptop take operating, sukay ido huɗu, Khausar ta ɗauke kanta kamar bata ganta ba, itama Hajar din bata kulata ba ta wuce kitchen, sosai tayi mamaki da taji kitchen din ya cika da ƙauri, gani tayi an ƙure wutar gas din bayan kuma ta rage sosai, da sauri ta isa gaban gas din ta kashe wutar a bit confuse, sama sama ta yaɗe shinkafar wcca bata ƙone ba ta juye a warmer, Allah yaso ba tayi ƙauri ba. Wajen karfe uku Khausar taji ƙarar bell, tsallake throw pillows din da ta sake wurgowa ƙasa tayi ta nufi door ta buɗe, murmushi tayi ta koma gefe tace "Yaya sannu da zuwa", ya amsa kafin ya shigo yana ƙarewa palourn kallo, wnn shine karo na farko da ya shigo gidansa ya tarar da hka, sai ya fara neman matarsa a palourn don ya saba idan ya dawo ta taho da gudu ta rumgumesa tana masa snnu da zuwa, tini ya nufi stairs yana cewa "Baby wife.. Sweet pie.. Honey" da haka ya haura saman. Tinda ya dawo Khausar take zuba ido taga ya sauko don suyi karatun amma shiru, ai kam sai wajen sallar la'asar ya sauko shima kuma mosque zai fita, da kansa yace ta jira idan ya dawo zai duba mata, bbu jimawa Hajar ma ta sauko ta haura sama da kayan abinci, sake saukowa tayi ta ɗauki ruwa da lemo daga nan bata sake dawowa ba. Da daddare Hajar na naɗe jikinsa tana kallon stuff dinta, A hankali yake shafa lallausan gashinta yace "Baby wife wai su duk kamarsu ɗaya wadan nan mutanen..?", tayi ƴar dariya tace "A'a fa kowa da kamarsa", kallon Tv yayi yace "Ga wni can kamar Mr Lee", ta ɗaga kai ta kallesa tace "Wanne..?", yace "the one in black and red..", tace "Chab ai shine boss..", yace "Ohh toh a bani spoiler so that i can catch up..", zaune ta miƙe ta fara surfa masa bayani, shi dai kawai kallonta yake yana nodding head don ba fahimta yake ba, shi dai kawai daɗin kallonta yake ji a haka, ya shafa kansa yace "Mene ne ma kika ce sunan actor din..?", ta gaya masa, tuntsirewa yayi da dariya harda jingina da kujera yace "wnn wane irin suna ne sai kace za'a zura da gudu..", dariya tayi ta kwanta a ƙirjinsa listening to his heart beat tace "kaga fa sunansa da daɗi..", yayi wrapping dinta sosai yace "wollah ba daɗi", a hankali ta ɗagasa ta kalli Tv, yace "ita kuma Actress din fa..?", ta maƙe shoulder tace "dariya zakamin wllh..", yace "Toh idan ban san sunansu ba taya zan gane series din", sai da tayi gyaran murya snn ta gaya masa, pointed nose dinsa ya ja ya gyaɗa kai sai kuma ya zuƙe lips don baya so yayi dariyar da ta taho masa, ai gwara ma sunan Actor din, Hajar ta ƙura masa ido without blinking tana jiran reaction dinsa, ya miƙe daga kan kujerar ya nufi door yana jan rigarsa, tini ta tashi tasha gabansa, bai san lokacin da dariyar ta kufce masa ba, ya ɗora forehead dinsa saman nata da haka ya fara turata har saida ya kaita bango still yana dariya, ta turo baki tace "daman nasan dariya zakamin..", ya ɗago ya kalli eye ball dinta yace "you're the best sweet pie..", ta juya kwayar idanunta ta fara wasa da rigarsa tace "Moon... kawai dai baka son sunan nas..", slight kiss ya sauke mata a lips yace "bari na dawo sai a gayamin sunan supporters suma.." da haka ya bar wajen ya nufi door, downstairs ya sauka, sosai yayi mamakin ganin Khausar, yace "Ohh baki kwanta ba..", ta sosa forehead dinta tace "Eh", yace "Ohk" ya buɗe ƙofa ya fita, After 10mins ya dawo, har zai wuce sama Khausar ta miƙe tace "Yaya don Allah ko zaka ƙarasamin chaptern ynxu in yaso gobe sai mu buɗe fresh, i only have 4days left..", ya ɗanyi jimm sai kuma yace "Ohk" ya dawo palourn ya zauna. Hajar ta kalli door a wajen karo na biyar sai kuma ta kalli agogo, almost 2hours fa da fitarsa, tashi tayi ta nufi door tana tare hammar da ta yanko mata, tana isa gaban stairs ta hango haske sosai a palour kafin ma ta sauka, step ɗaya ta sauka ta hangosu, tafi 50sec a tsaye kafin ta juya ta koma saman, 11 dot Nurain ya haura sama bayan ya gama da Khausar, itama ta haɗa komai nata ta tafi zata kwanta, yana shiga palourn sa ya tarar Hajar tayi bacci kan kujera, ajiyar zuciya yayi don yaso ya cigaba da cin dariyarta, duƙawa yayi gaban kujerar ya ringa kallon fuskarta, daukarta yayi ya shiga bedroom da ita ya kwantar da ita kan gado snn ya rufa mata duvet, ta ɗan motsa ta gyara kwanciyar. Washe gari da Asuba ya shigo ya tarar da ita ta idar da sallah knn, suna haɗa ido ta juyar da kanta tace "Ina kwana..", still yayi a inda yake don ba haka ta saba gaisuwar ba tana haɗawa da My Moon or something romantic, ƙarasowa yayi ya duƙa gabanta, tayi gefe da fuskarta don bata so su haɗa ido, Calmly ya kamo hannunta, a hankali ta amshe hannunta sai kuma ta miƙe tare da prayer mat din da tayi sallah, miƙewa yayi yace "Baby wife", ta juya masa baya ta fara linke prayer mat din.......✍️
💛 HAJAR 💛

{86..}
Ya dawo ta gabanta yana ƙoƙarin leƙa fuskarta ta sake juya masa baya, lower lip dinsa ya ciza painlessly ya riƙo hannunta zai juyo da ita, afujajan ta fixge hannunta kawai ta faɗa kan gado ta takure waje ɗaya, ajiyar zuciya yayi ya hau gadon ya kwanta side dinta, tana jin present dinsa daf da ita ta muskuta zata matsa, da sauri ya riƙota ya janyota jikinsa yace "Me nayi da aka ƙi kulani..?", ji tayi kamar ta rushe da kuka wato ma tmbya yke me yayi, idonta yayi rau rau hawaye suka cikosa, hijab din ya tattaro ya cire mata, duk tana jinsa amma bata motsa ba, duvet ya janyo ya lulluɓa musu tare don yasan bata resisting sanyin ɗakin, a hankali ya fara brushing gashinta da yatsunsa, ta lumshe idonta sai kuma ta fara ƙoƙarin kwace kanta, gam ya riƙeta motsin ma ta daina, ya kai lips dinsa saitin kunnenta yace "Baby wife please talk to me", kamar mai koyar mgana tace "Ni bacci zanyi", yayi pecking forehead dinta sai kuma ya ɗora kansa saman nata yana sauke numfashi a hankali yace "sleep tight Baby girl.." da haka ya lumshe idonsa yana cigaba da brushing hair dinta, ta gyara kwanciyarta perceiving his pure scent tana jin daɗin taɓa gashinta da yake, buɗe idonta tayi don bata so ta koma bacci, idan ta kuskura ta rufe ido toh ynxu zata jita a jihar barno don komai rashin baccin da take ji daga yayi cuddling dinta yana mata hka bacci yake zuwa, bayan ta tabbatar ya koma bacci ta zame jikinta a hankali ta sauka daga gadon, ta ɗauki hijab dinta ta saka ta buɗe ƙofa ta fita, downstairs ta sauka, tsayawa tayi tana kallon palourn da yayi uban datti, palournta bai taɓa datti kamar yau ba, har da noodles ta gani akan kujera da marmasasshen biscuit, a hankali take aikin don wta kasala take ji, kitchen ma ba laifi a ɓace yake saidai bai kai na jiya ba, da rashin kuzari take aikin harta gama, breakfast din da ta dafa sai taji ƙamshinsa yana tayar mata da zuciya, da kyar dai ta juye a warmers ta fita, daga nan room dinta ta koma ta shiga wanka, bayan ta fito tayi shafe shafenta snn ta baza turare a jikinta, doguwar rigar atampa mara nauyi ta saka, ta hau gado ta kwanta ta lumshe ido, time to time take buɗe idonta ta kalli agogo, ƙarfe takwas da rabi taji zuciyar nata ta dena tashi kuma bata jin kasala kamar ɗaxu, bathroom ta shiga ta kuskure bakinta da mouth rinks ta fito, walking gently ta fita ta nufi ɓangarensa, tana shiga bedroom ta gansa gaban mirror already dressed up yana combing hair dinsa, ta cikin mirrorn suka haɗa ido tayi sauri ta saukar da kanta, beyi buttoning rigarsa ba snn ma bai saka links ba don wnn aikin na Baby wife ne, ta ƙarasa gaban mirror din kanta a ƙasa, ya ajiye comb din ya juyo yana kallonta, bata bari sun haɗa ido ba sai juyar da kai take, tayi ɗage kamar yacca ta saba ta ɓalle masa buttons din, shi kam kawai kallonta yake without blinking har ta gama, ta ɗauki links din ta kamo hannunsa ta saka masa, Calmly ta saki hannunsa bayan ta gama saka masa links din, ta juya zata bar wajen, ya sauke wta ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ya riƙe damtsenta ya fixgota, gaba ɗaya ta taho kamar zata faɗi ƙasa sbd yacca ya fixgotan, saidai bata faɗin ba don tini yayi wrapping dinta cause ya fixgota ne sbd hkan, tayi ƴar ƙara cause ta tsorata sai kuma ta fara mutsu mutsu zata fixge, yace "fushi kike dani wife...?", ta girgiza kai tace "A'a", yace "Hmmm i know you are angry at me", ta juya idanunta tace "please let go off me if not kayanka za suyi squeezing..", tamke riƙon da yayi mata yayi yace "let them be", After a while ya saketa sai kuma ya juyo da ita ya tallaɓi cheeks dinta yace "Look at me wife", ta ɗaga kanta ta kallesa a taƙaice, yace "Am sorry I left you all alone last night", ta saukar da kanta tace "It's Okay..", lokaci guda ta ɗago kanta ta ringa kallon eye ball dinsa, ɗage tayi ta zagaye wuyansa sai kuma ta turo baki tace "Ai baka amsa gaisuwana na yau ba", murmushi yayi ya rutsa ƙugunta zuwa bayanta yace "say it again..", tace "Good morning My Moon..", ya goga karan hancinsa a nata yace "Morning Baby girl..", ya daɗa haɗata da ƙirjinsa ya haɗe lips dinsu waje guda ya shiga kissing dinta, lumshe idonta tayi after a while ta shiga mayar masa da martani, hannayenta dake zagaye da wuyansa tasa ta fara wasa da sumarsa, da sauri ta janye lips dinta don tasan ynxu sai abun ya girmama, yayi murmushi snn ya rumgumeta yace "I Love you..", ta cusa kanta a wuyansa tace "I Love you more". Downstairs suka sauka tare as usual, zaune suke kan dining suna yin breakfast a tare, loma biyu tayi ta ajiye spoon din hannunta don tini zuciyarta ta hau tashi, ganin ta dena ci yace "what's wrong wife..?", ta girgiza kai tace "Na ƙoshi..", tini shima ya ajiye spoon dinsa yace "Why ba kya son wnn ne..?", ta gyaɗa kai snn ta ɗauki spoon din ta damƙa masa tace "Noodles zan dafa later ynxu bana jin yunwa..", yace "Ohk ita Baby love yake so", ta langwaɓar da kai tace "Yeah" ita ynxu ma dai kawai biye masa take aje a hkan, ina taga wni abu wai shi ciki a ynxu, Khausar ce ta sauko daga stairs tana tafiya a hankali, fuskarta duk kumburin bacci don bata daɗe da tashi ba kuma shima ƙishi ruwa ne ya tasheta, hijab ne a jikinta har ƙasa, ta ɗanyi tafiya towards dining din da suke kai, sosai tayi bowing ta gaida Nurain, ya amsa yana tmbyrta ya ta kwana, tace "fine alhmdllh..", da haka ta juya zata shiga kitchen, yace "Khausar..", ta juyo sai kuma ta dawo position din da ta tsaya tace "Na'am", thick eyebrows dinsa ya haɗe yace "Kin gaisheni baki gaisheda matana ba ko baki ganta bane..?", Khausar ta ɗago ta kalli Hajar sai kuma ta dubi Nurain tace "Yaya ai mun gaisa da ita ɗaxu..", ya kalli Hajar da ta saki baki tana kallon Khausar yace "Sweet pie hka ne..?", Hajar na kallon cikin idon Khausar tace "A'a wllh ni kam ynxu ma na ganta tinda garin Allah ya waye...", sosai mamaki ya cika Khausar don ba tayi tunanin Hajar zata ƙaryata ta ba, Nurain ya ringa kallon Khausar snn yace "Then do it now..?", wata ball ce ta tsayawa Khausar a throat, da kyar ta buɗe baki tace "good morning..", Hajar ta juyar da kai tace "Morning..", Nurain yace "karki sake maimata wnn mistake din, respect My wife as you respect me...", ta saukar da kanta tace "sure" sai kuma ta juya ta shiga kitchen, though yasan ta girmi Hajar tinda Sa'ar Noor ce amma dai hkan bazai bata ƙofar raina masa mata ba, wnn ai raini ne ya tabbatar idan Noor ce baza tayi hkan ba, ko da Hajar ƙarama ce still dai matar Elder Brother dinsu ce, yana sane ma yaƙi inviting dinta yau wajen yin breakfast don sarai yasan me tayi jiya, sai wni yamutsa fuska take tana aibata yummy abincin matarsa, saida Hajar ta rakasa har balcony tana masa Allah ya tsare, ya tambayeta da me zai taho mata, finger dinta ta zura a baki ta rutsa da haƙoranta tana tunani, lokacin guda tace "Rake..", ya waro ido yace "Sugarcane..?", ta gyaɗa kai tace "Eh shi nake so..", yace "Ohk then.. saina dawo". Noodles din ma da Hajar ta dafa wajen ƙarfe goma kasa ci tayi, kitchen ta kai bayan ta tsattsakura ta rufe, room dinta ta koma ta kwanta, ko 10mins bata ƙara ba wni mugun bacci yayi awon gaba da ita, ba ita ta farka ba sai 1 da wni abun, wasai taji jikinta, duk da cewa ba taci abinci ba sai taji bata jin yunwa, ganin lokaci tayi sauri ta shiga bathroom tayo alwala ta gabatar da sallar azahar, tana idar da sallar ta fita don yau ta makara bata ɗorawa mijinta abinci da wuri ba, da shigarta kitchen din ta wni mugun daskare, har yafi jiya ɓaci don na yau da manja akai badaƙalar, jingina tayi da bango tana tunanin ta ina zata fara, ga palour can shima ya sha nashi hargitsin daidai gwargwado. Ƙarfe ɗaya da minti ashirin Nurain ya dawo gida, haɗe thick eyebrows dinsa yayi ganin palourn a hargitse kafin ya haura sama, direct room dinta ya buɗe ya shiga, ya ajiye ledar Sugarcane da ya taho mata dashi kan chest of drawers, saida ya tabbatar bata ɗakin snn ya fita ya shiga ɓangarensa, wanka yayi ya shirya cikin ƙananan kaya na zaman gida, room din nata ya sake dubawa a karo na biyu still dai bata nan, kawai sai yaji hakan Odd gashi ya kirata tin yana hospital bata ɗaga ba, yana fitowa daga room din nata Khausar ma ta buɗe ƙofar room din da take ta fito, gaishesa tayi snn ta masa snnu da zuwa, a takaice ya amsa kafin ya tmbyeta ko taga Hajar, ta girgiza kai tace "No ban ganta ba ni tin ɗazu ina ɗaki kum..." bai tsaya sauraronta ba ya gangara ya sauka ƙasa, Khausar ta ɗan taɓe baki tace "shegiya mayya... tinda nake da Yayana bai taɓamin faɗa ba sai a kanki, banza ƴar ghetto kawai", can gaban sink a durƙushe Nurain ya hango Hajar bayan ya buɗe ƙofar kitchen, bai san lokacin da ya ƙarasa inda take durƙusa ba ya ɗagota, hawaye ya jiƙa cheeks dinta tana yarfe hannu a hankali, ba ƙaramin rikicewa yayi ba yace "My Hajar.." sai kuma ya fara tattaba fuskarta yace "mene ne Baby..?", ta fashe da kuka ta damƙe hannunsa tace "Cikina..", miƙewa yayi ya miƙar da ita itama, ta koma ta naɗe a ƙasa tace "i can't..", without second thought ya sunkuceta ya fita da ita daga kitchen din, baki a sake Khausar dake tsaye palour ta bisa da kallo har ya haura sama, kuka kawai Hajar take don ji take kamar mararta zata tsinke, gaba ɗaya Nurain rasa inda zai sakata yayi, ji yake kamar ya kwashi ciwon nata ya dawo dashi jikinsa, gashi dai Dr amma tini ya zama quack, wni magani kwalli ɗaya tak ya bata, after 5mins da shan mganin tana murƙususu a jikinsa taji dama dama, lamo tayi tana sauke numfashi har dasu gumi ya tsattsafo mata a goshi, sannu kawai yake jera mata, a hankali ta zame dga jikinsa ta kwanta sosai a kan gadon, hannunsa ya kai tummy dinta yace "Sorry", kwalam yaji cikin nata har ya rufta, ya kalli yacca take ajiye numfashi a hnkali yace "kin ci abinci kuwa..?", ta gumtse baki don wni amai ne ya taho mata da ya ambaci kalmar Abinci, ya dafa goshinta yace "Love you need to eat something..", ta girgiza kai kawai, yace "Toh me kike son ci..?", nan ma ta girgiza kai, she must eat gsky cause in ba haka ba zata sha whala, yayi ajiyar zuciya yace "Toh zaki sha Sugarcane din dana kawo miki.?", tayi shiru sai kuma ta gyaɗa kai, yace "Aha bari na kawo miki..", ya shafa kanta da haka ya juya ya nufi door, room dinta ya shiga ya dauko ledar Sugarcane din da ya ajiye ya sauka downstairs ya wuce kitchen, ya ƙarewa kitchen din kallo sai kuma ya ɗauki plate ya juye raken ya wanke a sink, da plate din ya fito, saida ya kai daf da stairs snn ya juya ya kalli Khausar yace "Khausar kina zaune a guri duk datti, c'mon tashi ki gyara and do the dishes shima kitchen din ki gyarasa.." with comand ya ƙarashe mganar ya haura sama, Khausar tayi still zuciyarta kamar za tayi bindiga, bbu yacca ta iya haka ta tashi ta gyara palourn da ta ɓata da gayya, tana wanke wanke tana tsaki, bayanta har riƙewa yayi sbd tsayuwa, haka dai taci uban wanke wanke da ta tara snn ta gyara kitchen din shima, hannun rigarta ya jiƙe sharkaf da ruwa, fuska a matuƙar murtuke ta fito ta haura sama don ta cire rigar. Sai kace wni nama haka Hajar ta dilliƙi Sugarcane dinta, sosai ta sha ta rage ragowar wai sai Anjima, shi dai kawai kallonta yake don tini yayi confirming zarginsa, sai dai kuma yana so ya tabbatar, Calmly ya kamo hannunta yace "how are you feeling now...?", tace "Much better", yace "Good Alhmdllh, taso muje hospital Baby", ta kallesa ta turo baki tace "Ni am Okay", ya kwantar da murya yace "We have to Baby wife, kinga zasu rubuta miki drugs wnda zaki ringa sha sbd ciwon cikin, ynxu pain reliever ne na baki kar muje later ciwon ya dawo..", ta langwaɓar da kai tace "Ni bana son hospital... kai ka dubani a gida", murmushi yayi ya ɗora hannunsa a chest dinta yace "This is my field, i only chop hearts..", daga ƙarshe yayi convincing dinta ta yarda suje asibitin, hijab dinta ya dauko mata a room dinta da takalminta, wni private hospital ya kaita kuma ya buƙaci test kawai yake so a mata, tini wata Nurse ta dauki blood sample dinta ta wuce dashi lab, bai ɗauki wni 30mins ba result ya fito, bai tsaya bin wni procedure ba ya amshi result din test din suka bar asibitin, basu koma gida ba saida ta gaya masa me take son ci ya siya mata snn suka wuce, suna isa gida ta wuce room dinta ta kwanta, kasalar da ta tashi da ita ce ta dawo mata amma dai bata jin ciwon komai. Nurain ya ciro papern result din daga pocket snn ya zauna kan kujera, ya shafa fuskarsa da both palms dinsa sai kuma ya kalli papern, sai kace me shakkar ganin abinda ke ciki hka ya shiga buɗe papern, yana ganin result din ya sauke wni ajiyar zuciya, ya koma ya jinjina da sofa yace "Alhmdllh... Am going to be a Father..", lokaci guda ya dauki takardar ya fita, kwance ya ganta kan gado bayan ya shiga room dinta, ya ƙarasa gaban gadon ya ƙura mata ido, a hankali ya kai hannu ya kwashe rigarta ya ringa kallon fair tummy dinta, Hajar ta buɗe lumsassun idanunta a hankali, yana ganin haka ya zauna gefen gadon ya ɗagota ta zauna, ita dai kawai kallonsa take don wni yanayi mara misaltuwa ta hango a fuskarsa, bbu inda beyi kissing ba a fuskarta, ita dai tayi lakwan tana ganin iko Allah, duk hkan bai masa ba ya sunkuceta ya fara hajijiya da ita a tsakar ɗakin, saida yayi me isarsa snn ya ajiye a kan gado ya rumgumeta very tight, ya kai lips dinsa saitin kunnenta yace "Congratulation Baby girl you're going to be a Mother..", shiru ta masa don har ynxu hajijiyan da yayi da ita bai gama sakinta ba, a hankali ya rabata da jikinsa ya dauki takardar ya bata, ta kalli content din ciki wnda ya nuna cewa she's 4weeks pregnant, ya riƙe haɓarta ya ɗago kanta ya kalli cikin idonta yace "ynxu kin yarda na cilla kwallon kin caɓe..?", ta saukar da kanta wni murmushi na shirin kufce mata kawai ta faɗa ƙirjinsa, ya rumgumeta sosai yana patting bayanta yace "I Love you..", after few seconds tace "Me too". Tarairaya na musamman Nurain yake gwadawa Hajar, daga tayi motsi zai tmbya me take so, ita dai tin tana mamaki harta dena don taga abin nasa azimun ne, toh wai daman hka maza suke yiwa matansu idan sunada ciki ko kuma nata mijin ne yake mata hka, ta lura ma lfyrta yafi damuwa da ita snn kuma he also love the unborn baby. ɓangaren Khausar kam tin tna jiran yaxo ya duba mata chaptern da ta gama rubutawa jiya har ta gaji ta haƙura, ga takaicin uban wanke wanken da tayi, sai pass 11 snn Nurain ya tuna da wata Khausar, gashi fitar da yayi zuwa mosque da siyo ma Hajar abinda take so bai ganta ba a palour, tinda gobe Friday kuma ba zai fita ba sai ya duba mata. Washe gari Khausar na zaune palour ita kaɗai sai kace mayya, yau kam palourn tsaf tsaf don bata hargitsa ba tana tsoron kar Nurain yace ta gyara, gashi yau tinda ta sauko palour ba taga Hajar ba, Nurain din ma tin safe da suka haɗu a kitchen yana haɗa coffee ita kuma taje dafa breakfast bata sake ganinsa ba, ƙarar mota taji alamar an shigo compound, da sauri ta wurgar da wayar da take latsawa ta kunna Laptop dake side dinta, dman da zai fita mosque yace idan ya dawo zasu cigaba, after 10mins taji ƙarar bell, da sauri ta tashi ta nufi door ta buɗe, ga mamakinta sai taga ba shi bane Hajjaju Hajiya ce riƙe da sandarta a bakin ƙofar bayanta kuma Farooq, Farooq ya ringa kallon Khausar da mamaki don bai taɓa zaton zai ganta a nan din ba, Hajiya ta kalli Khausar ta saman glasses dinta tace "Ah a ya naga hka, baƙa matar Usuman din ta koma ne...", Farooq yace "A'a wnn ai ba ita bace Khausar ce fa... ya dai idon naki Amarsu wnn din ma ai ba baƙa bace", Hajiya tace "Akan matar Usuman ai baƙa ce", Khausar ta ɗan russuna tace "Hajiya snnu da zuwa", Hajiya tace "fara bani hanya na wuce idan na yada kwankwasona ma gaisa", tini Khausar ta matsa gefe, Farooq na bawa Hajiya support da kuma sandarta ta samu ta shiga palourn, Khausar ta mayar da ƙofar ta rufe, a hankali Hajiya take takawa tana cewa "kar ka jani da sauri mai gidan, yanxu sai kaga ƙafafuwan sun lankwashe duk holoƙwayen banza ne..", Farooq dai bai ce komai ba ya kaita har kan sofa ta zauna, ya ajiye mata jakarta a gefenta, Khausar ta ƙaraso ta zauna kan carpet ta gaida Hajiya, Hajiya ta kafeta da ido kafin ta amsa, Khausar ta gaida Farooq wnda yake ta kallonta ta ƙasan ido, Farooq ya amsa snn yace "yasu Umma..?", tace "Suna lfy alhmdllh", yace "Masha Allah... ya karatu..?", tace "fine alhmdllh..", yace "Good" daga haka bai sake cewa komai ba, bayan wni lokaci Khausar ta tashi ta shiga kitchen Hajiya ta bita da kallo, few seconds ta fito da tray mai dauke da ruwa da lemo ta ajiye musu, Hajiya na kallon trayn ruwa da lemon tace "Wnn aiki ai na matar gida ne, tinda nazo banga gilmawarta ba..", Khausar tayi murmushin yaƙe tace "Ai tin safe bata sauko ba Hajiya", Hajiya tace "Au tun safe bata sauko ba... ke din nan kika kwan..?", Khausar ta gyaɗa kai, Hajiya tace "Eh ba shakka", Farooq ya ciro wayarsa yayi dialing numbern Nurain, tana fara ringing Nurain ya ɗaga yace "Why punk..?", Farooq yace "We are here already..", Nurain yace masa ai ya kusa isowa, Ai kam bbu wani jimawa Nurain ya shigo palourn, Hajiya ta dire kofin ruwan da take sha tace "Au toh ashema Usuman din shima bayanan", Nurain ya ƙaraso inda take ya gaida ita, bata ma amsa ba tace "Ina matar taka ne Usuman naxo gida tin ɗaxu ban ganta ba..", Nurain ya kalli stairs sai kuma ya juya ya miƙawa Farooq hannu sukay musabaha, bayan sun gaisa da Farooq ya tashi ya haura sama, bai sameta a part dinsa da ya barta tana bacci ba don haka ya nufi room dinta, zaune ya sameta kan stool tana rubbing lotion, ya sakar mata murmushi yace "kin tashi Baby..?", ta gyaɗa kai tana kallon manyan kayan jikinsa, ya isa inda take ya dafa goshinta yace "you're okay..?", ta gyaɗa kai, yace "Iron Lady tazo tana jiranki a ƙasa", tace "Tom", ya sunkuya yayi pecking cheek dinta snn ya fita, sharp sharp Hajar ta gama shiryawa ta saka hijab dinta ta fita, walking slowly take sauka daga stairs duk da garau take jin kanta, Khausar ta ɗan kalleta sai kuma ta ɗauke kai, direct wajen Hajiya Hajar ta nufa, Hajiya ta ringa kallonta har ta iso gareta, cike da ladabi Hajar ta gaida Hajiya, Hajiya ta amsa tana kallonta da kyau tace "ya naga kina tafiya lagwai lagwai sai kace mara laka ince dai lfy ƴar nan...?", Hajar tace "lfy na lou Hajiya..", Hajiya tace "Toh madallah ai ita ake so ta daure", sai a lokacin Hajar suka gaisa da Farooq, Hajiya ta kyallaro Khausar dake can ƙarshen carpet lokaci guda ta kalli Nurain tace "Wai Usuman in ma hutun za azo gidanka ai sai ƙanana suzo ba wai firɗa firɗa ba, toh ita matar taka nawa take da za a kawo mata gansamemiyar budurwa ta zauna da ita, wnn ai sai a rasa matar gidan a cikinsu, ina ma dai laifin yara ƙanana kamar na Sakinatu wnda baza a sa yarinya whla ba, idan ta sulala musu ƴar taliya ma suka ci shknn, amma an kawo mata wcca saita zage damtse kafin ta dafa mata abinda za taci, sai kace daga garin gaɓa gaɓa", Nurain ya shafa kansa yace "Hajiya karatu ne muke yi tare da ita", Hajiya ta kallesa tace "Toh wai kai din malamin makaranta ne, naga dai farke cikin bil Adama ka karanta", yace "Eh ai nima zan iya duba mata..", Hajiya tace "A gsky ana ƙwarar yarinya, ya za ai a kawo mata gardiya cikin gida haka kurum fisabilillah", tini Khausar ta sulale ta bar palourn ta fita compound, Farooq ya bita da kallo bayan ya lura da reaction dinta, murmushi Nurain yayi da yaga Khausar ta fita, lallai ba tasan Hajiya ba, ai ba a ɗaukar maganar da ta faɗa personal in ba haka ba ka sha haushi, Hajar dai ta saukar da kanta don wata dariya ce ta taho mata wai gansamemiya, Hajiya ta cigaba da zuba sababi wai Khausar tayi girma da zama a gidan, shi dai Nurain tin yana ƙoƙarin nusar da ita har ya gaji ya dena don yaga ba fahimta za tayi ba, toh mene don Khausar ta zauna a gidansa, shi dai baiga aibun haka ba, ko shekara za tayi shi dai bazai ce ta tafi ba, Farooq ya tashi zai fita, Nurain yace "ina zuwa..?", Farooq yace "just a minute" da haka ya buɗe ƙofa ya fita, Hajiya ta janyo jakarta ta ciro kwalbar man zafi tana kallon Hajar tace "yi taimakon da kika saba wllh kamar zasu tsinke". Can jikin flowers Farooq ya hango Khausar bayan ya fita compound, har ya isa kusa da ita ba ta sani ba, handkerchief ya miƙa mata fuskarsa a sake yace "forget about what Iron Lady said and don't take it personal", ta ringa kallonsa sai kuma ta amshi handkerchief din ta goge hawayen da suka zubo mata......✍️
💛 HAJAR 💛

{87..}
Bayan tafiyar su Hajiya Hajar ta haura sama abinta, don tare suka fita da Nurain shi kuma zaije gidan Mami, ita da Khausar kawai aka bari a gidan, kuma daman tinda ba shiri suke ba meye na zama tare da ita, tsaf zata iya irga mganar da sukay da ita tin zuwanta gidan, room dinta ta shiga ta dauki wayarta dake kan chest of drawers, tana kunna wayar taga missed call din Oum Sulthan, tini tabi bayan kiran, kiran na shiga Oum Sulthan ta ɗaga, bayan sun gaisa Hajar tace "ya baby Sulthana..?", Oum Sulthan tace "Arigimatu gata nan na samu tayi bacci", Hajar tace "bana kusa da wayar ne lokacin da kika kira", Oum Sulthan tace "Ohk it's fine, daman cewa zanyi kayanki sun zama intact, jiya da daddare ragowar kayan suka sauka..", Hajar tace "Okay toh..", Oum Sulthan tace "na bawa mai aikina ta kawo miki ynxu..?", Hajar tace "Eh", Oum Sulthan tace "Okay ynxu zan turota..", Hajar tace "Toh ngd sosai..", Oum Sulthan tace "nice da godiya", da haka suka gama wayar, tini Hajar ta tashi ta buɗe ƙofa ta fita ta sauka downstairs, Sofa ta samu ta zauna bata ko kalli position din Khausar ba, wani dogon tsaki Khausar taja ta wni ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, ina irin itace mai palourn tana yiwa ƴan aiki izza, daman haushi take ji tin jiya da ta sha uban wanke wanke, sosai yin wanke wanken nan ya mata ciwo, gashi kuma yau Hajiya taxo tana wni ce mata gardiya, amma sai wni lallaɓa Hajar take sai kace wata ƴar shugaban ƙasa, ƴar ghetto area din mai kai a tukunya ake lallaɓawa, ita dai Hajar ba tace mata ta tafasa sauke ba, in dai tsaki ne ta shekara tana yi tinda ba fito mata zaiyi a jiki ba, kamar yacca Anty da Umma sukay mata nasiha akan tayi haquri a gidanta kar ta bari soyayyar da dangin mijinta suke mata ta kufce toh ko insha Allah zata kamanta, wnn dai mai shafaffen ƙirjin sai kace Allon mayya ba zata zame mata cikas a dangin mijinta ba, ta riga ta zuba banza a kwandon shara, Hajar dai na zaune palourn tana jiran mai aikin Oum Sulthan, after 10mins da zamanta sai ga ƙarar bell, Hajar ta tashi taje ta buɗe mata, da ladabi mai aikin ta gaisheta snn ta miƙa mata ledar hannunta, Hajar ta amshi ledar tace "kice mata ngd", mai aikin tace "Toh" da hka ta juya ta tafi, Hajar ta kulle ƙofarta, tana juyowa taga Khausar ta zuba mata ido, ba tasan lokacin da ta juya manyan idanunta ba ta wuce ta haura sama abinta, room dinta ta shiga ta buɗe ledar, sosai turarukan suka tafi da imaninta sbd ƙamshinsu, turaruka ne ta siya a wajen Oum Sulthan kala kala, na gida da nata da na kabbasa snn da kuma na gashi sai kuma na tsugunno, ga kuma humra wajen kala shida duk ta siya, ita dai burinta tayi ƙamshi ita da gidanta, tin last week tayi ordern kayan a wajen Oum Sulthan kuma tini ta biyata kuɗinta cash, tanada kuɗi sosai a wajenta don duk month sai ya ajiye mata envelope ta kuɗi kuma ba ƙadan ba, kawai ajiyesu take don bata san amfanin da za tayi dasu ba tinda bata rasa komai ba, burner din dake room din ta jona ta ɗebi turaren ta zuba, haba ai kafin kace me wni ƙamshi mai dadi ya fara tashi, da kwalbar turaren ta fita ta shiga ɓangarensa ta zuba turaren a burners din bedroom da palour, da haka ta fito ta sauka downstairs, shima dai hka ta jona burner din palourn ta zuba turare, ƙamshi na fara tashi Khausar tayi gyaran murya sai kuma ta tashi tace "meye hka ina zaune a waje kinzo kin bunka min hayaƙi, bana son turaren wuta...", Hajar ta juya idanunta tace "Oho idan ba kya so sai ki tashi ki bar wajen don baki isa ki hanani sakawa gidana turaren wuta ba", Khausar ta haɗe fuska tace "dalla malama kashe wnn ƙaurin..", Hajar tace "you can't tell me what to do in my house, ki bari idan kinje nki gidan sai kiyi yacca kike so amma ba dai a gidan mijina ba" tana gama faɗin hka ta maka mata wata shegiyar harara ta haura sama, da sauri Khausar ta matso bakin stairs din tana cewa "hey come back here and face me ba wai ki haura sama ba", Hajar ta juyo tace "A'a wllh ni inada aure bazan biye miki ba" tini ta ƙarasa hawa stairs din ta shige ɗakinta, a matuƙar fusace Khausar taje ta fige burner din daga jikin socket, hakan bai mata ba ta ɗaga burner din ta damfara da ƙasa. Wajen ƙarfe biyar da rabi kiran Nurain ya shigo wayar Hajar, turo baki tayi ta kara a kunne, yace "how are you doing My Baby..?", ta juya idanunta tace "fine alhmdllh My Moon", yace "have you eaten..?", ta girgiza kai tace "Ni na ƙoshi..", yace "Toh me kike so na taho miki dashi..?", tace "Algwaluma da green guava..", ya waro ido yace "Baby wife wnn fa duk ba solid food bane", da muryan shagwaɓa tace "Uhmm ni su zanci..", ya sauke numfashi yace "Toh shknn... Please Baby ki zaɓi wni abun ko kinaso Baby love ta zauna da yunwa..?", tayi murmushi da taji yayi inkiyar mace toh wa yasan mene ne ai tukunna dai, tace "Zanci Noodles", yace "Good you want me to order it for you ko kuma da kanki zaki dafa?", tace "zan dafa da kaina", yace "Ohk.. take care of yourself for me", tace "Sure", yace "I Love you..", tayi murmushi tace "Same". Sai ƙarfe shida snn Hajar ta wuce kitchen da nufin dafa Noodles din da tace, tana shiga kitchen din taji bata son cin Noodles din ta fita daga ranta, fridge ta buɗe ta yanko watermelon ƴar madaidaiciya ta yanka ta zuba a cikin blender, madaran gari mai yawa sosai ta zuba da Sugar kaɗan, ta haɗa ta markaɗe with high speed bayan ta zuba ice block, A kullum sai tasha wnn haɗin banda jiya da shekaran jiya da ta rasa appetite, Milk shake din tasha tayi nak don taji daɗinsa sosai. Da daddare wajen ƙarfe takwas da minti goma Hajar ta sauka downstairs walking gently, waro ido tayi ta ƙarasa cikin palourn tace "Moon kana nan daman..?", yace "yeah kin gama gyaran..?", tace "Eh" da hka ta juya ta shiga kitchen, bata jima ba ta fito da plate da kuma green guava da ya siyo mata ɗaxu, kusa da shi ta zauna ta fara cin guava din, ya ɗan kalleta yayi murmushi, few minutes saiga footsteps ana saukowa daga stairs, ita dai Hajar ko kallon stairs din ba tayi ba tana cin guava dinta a hankali, Khausar ta ƙarasa saukowa da shirin fita, black Abaya ce a jikinta da handbag, cikin palourn ta iso ta zauna opposite to them, tace "Yaya dman ina so in gaya mka ne zanje shopping akwai abubuwan da zan siyo...", Nurain ya kalli makeken agogon palourn yaga ƙarfe takwas da minti ashirin, yace "ke kaɗai zaki fita shopping din..?", tana wasa da ring din hannunta tace "Eh ai baxan daɗe ba, bolt din da ta kaini ce ma zata dawo dani insha Allah..", yace "Ohk.. kin kira bolt din..?", tace "A'a ynxu dai zan kira", yace "Ohk" sai kuma ya juya ya kalli Hajar "Baby wife ko zamu fita shopping ki siyo chocolates..?", sai a lokacin Khausar ta kalli Hajar sai kuma ta taɓe baki, Hajar ta ɗan fakaici kallon Khausar sai kuma tayi murmushi tace "i like it Moon..", yace "Ohk alright get ready..", tace "Tom", Nurain ya juya ya kalli Khausar yace "bari mu fita shopping din tare", tace "Ohk", Nurain da Hajar suka haura sama Khausar tayi zaune palourn tana jiransu, shi ya wuce part dinsa ita kuma ta shiga room dinta, wni tunani tayi kawai ta buɗe ƙofa ta fita ta shiga ɓangarensa, a palour ta tarar dashi da waya kare kunnensa, kawai ta wuce bedroom, Closet dinsa ta nufa ta buɗe, komai intact tinda yau 4days knn da ta gyara masa, section din shirts ta buɗe ta ɗauki wata fara ƙal snn ta rufe ta fito, still dai wayar yake bai gama ba, ya kalli hannunta bai dai gane abinda ta ɗauka ba, Hajar na shiga room dinta ta faɗa wanka, bata wni jima ba ta fito ɗaure da towel, da kolaccan da humran da ta siya wajen Oum Sulthan tayi amfani ta shafe jikinta, habawa ai tini wni mahaukacin sassanyan ƙamshi ya bulale ɗakin, ta warware gashinta tayi boy and girl, uhmm maimakon ta saka manyan kaya tinda fita za suyi saita dauki white shirt dinsa da ta dauko ta saka, a rabin cinya shirt din ta tsaya mata, ta kalli kanta a mirror snn ta shafa tummy dinta tayi murmushi, ita tasan me ta shirya shiyasa take wnn murmushin, ta feshe jikinta da perfumes kafin ta nufi door walking like a cat, tana buɗe ƙofa taga Khausar ta nufi hanyar bangarensa, habawa ai da gudu tasha gabanta tayi banga banga a bakin ƙofar ɗakin ta riƙe ƙugu tace "malama ina zuwa hka kanki tsaye..?", Khausar ta gyara tsayuwarta cike da mamaki take kallon Hajar from head to toe, ta haɗe fuska tace "hey... kin isa ki hanani shiga wajen Yaya na..", Hajar ta buɗe baki da irin rainin hankalin nan tace "Ayyah a iya sani na nasan mijina bashi da wata ƙanwa da ta wuce Noor don hka ja jiki wllh bazaki shigar min turakar miji ba", Khausar was more than shock tama kasa cewa komai, can dai tace "ba a auro wcca zata hanani zuwa wajen ɗan uwana ba wllh, before I count 10 ki matsa kafin nayi smashing dinki..", Hajar ta taɓe baki tace "kiyi tafiyarki shopping dinki ke kaɗai ni Mijina baya fita da daddare, may be kafin ki gama irgen kin isa compound" tana gama faɗin hka ta zuge door din, Khausar ta kai hannu zata hanata aikam ta haɗa da hannun nata, ƙara Khausar tayi ta koma da baya, Hajar ta ɗan buɗe ƙofar tace "Am not a psycho da zan bar gardiya ta shiga ɓangaren mijina", ta banke door din snn ta saki curtain ta bar wajen tana juya lulu eyes dinta, wllh ba za aje shopping din nan ba, saita nuna mata limit dinta, ita ta isa tazo gidanta tana mata iya shege da ƙirjin sai kace babe, da tafiyar mage ta nufi bedroom, tsaye tayi bakin ƙofa tana kallonsa, tsaye yake gaban bed already dressed up, ta kalli kayan jikinsa taga dai ba Pajamas bane, ya juyo ya ɗan kalleta yace "Baby wife ya baki shirya ba..?", shiru ta masa ta kalli gefe, ta turo baki sai kuma ta rufe ido ɗaya da bayan hannu ta fara shessheƙa, ya waro ido yace "what happened..?", nan ma bata tanka masa ba ta cigaba da shessheƙar kuka, ya zauna gefen gado yace "come and tell me Baby", a hankali ta taho tana murza idonta da bayan hannu, tana zuwa ta ɗale kan cinyarsa ta rufe fuskarta a ƙirjinsa ta cigaba da kukan, ya ajiye ajiyar zuciyar da bai shirya mata ba bayan ya shaƙi ƙamshinta, ya shiga patting bayanta yace "Mene ne..?", a hankali tace "Ni cikina ne yake ciwo", ya zura hannu cikin rigarta ya shafa cikin yace "here..?", ta gyaɗa kai, yace "Sorry.. gashi baby love bata fara kicking ba bare nace ita ta takura miki", tayi shiru ba tace komai ba tana sake shigewa jikinsa, shi kam gaba ɗaya ƙamshinta da laushin jikinta ya fara saukar masa da kasala, yayi ƙoƙarin ɗagata amma taƙi ta sake komawa ta kwanta, yace "magani fa zan dauko miki Baby wife..", ta maƙe shoulder tace "Ni A'a", yayi chuckling sai kuma ya miƙa hannu ya janyo pillow ya koma da baya ya kwanta, tini tabi jikinsa ta kwanta itama, after few minutes ya ɗago kanta yana kallon fuskarta, wni irin juyi yayi ya kwantar da ita kan gadon ya haɗe forehead dinsa da nata, daga nan kuma zance ya sauya. Tin Khausar na jira har ta haƙura ta koma ɗakin da aka sauketa, ba ƙaramin haushin Hajar ta shaƙa ba a wnn ranar, tinda take ba'a taɓa mata abinda ya ƙona mata rai kamar hka ba, zaune tayi kan gado bayan ta saka pajamas dinta ta cire Abayan, wni ƙululu mai shegen tauri ya tsaya mata a throat, ba tasan lokacin da hawaye ya fara zarya a cheeks dinta ba, ta koma ta kwanta ta rufe fuskarta da pillow tana hawaye. Washe gari ranta busu busu ta tashi, tayi zamanta a ɗaki taƙi fita sai kace wata sabuwar Amarya, tabbas idan ta fita ta haɗu da Hajar toh wllh saita tata mata rashin mutunci mai wasali, wajen ƙarfe sha ɗaya Khausar ta tashi ta shiga wanka, tin ƙarfe takwas da ta tashi take zaune tana latsa wayarta, tana gama shiryawa ta buɗe ƙofar ɗakin ta fita, kanta tsaye ta sauka downstairs, sosai taji daɗi da taga bbu kowa a ƙasan don haka ta buɗe kitchen ta shiga, tsaye tayi bakin ƙofa tana kallon Hajar dake tsaya gaban gas, Hajar kam da taji ƙarar ƙofa tasha shine ba tare da ta juyo ba tace "Moon har ka siyo sausage din..?" sai kuma ta juyo, ido huɗu sukay da Khausar, Hajar ta ɗauke kanta ta cigaba da juya soup din dake kan wuta, Khausar ta taɓe baki ta ƙarasa ciki, cabinet ta buɗe ta ɗakko small pot ta wanke snn ta kunna tap ta zuba ruwa rabin pot din, gaban gas kin ta matsa ta jera da Hajar wcca ba ta sake mata second look ba, Khausar ta kama handle din tukunyar dake kan wuta tinda na plastic ne ta ajiye gefe, pot din da ta zuba ruwa ta ɗauka ta dora a wajen ta koma gefe, mamaki yasa Hajar ta saki baki sai kuma ta juya ta kalleta, Khausar ta rumgume hannaye tana wni karkaɗa kai, haɗe gira Hajar tayi ta juya ta sauke tukunyar ta mayar da ta ta, Khausar ta sake matsowa ta dauke ta mayar da ta ta, saida sukay haka sau uku, A karo na huɗu Hajar tace "meye hka..?", Khausar taja wni dogon tsaki tace "Abinda yayi hka shi yayi hka, a nan nayi niyya zan dafa abinci...", a fusace Hajar ta juyo tace "wllh baki isa..." sai kuma tayi shiru sbd Nurain da ta hango a bakin ƙofa, zuwansa knn wajen, da sauri Hajar ta saukar da kanta tayi kamar bata gansa ba, Khausar kam ta juyawa ƙofar baya don hka bata san yana wajen ba, Khausar tace "baki isa kimin gage a gidan Yayana ba na gaya miki, ke asuwa bloody witch, ke kin isa zanyi girki ki hanani, naga dai Yayana ne ya sayi Foodstuffs din kuma yayi refilling gas, ba daga wnn slum din aka kawo ba, i mean wnn rubabben gidan naku...", Hajar ta rufe fuskarta da hannayeta kamar gaske ta fara shessheƙa a hankali tace "Khausar me na miki kike gayamin wnn mganar..?", Khausar ta taɓe baki tace "Ai ba ƙarya nayi ba, kinxo kin wani bararrashe a gidan Yayana sai kace na ubanki, just know this cewa nan ba gidanku bane da zaki ringa wni zaƙewa, anytime za'a iya kaɗaki ki koma can ghetto area a cigaba da tallan gyaɗa...", habawa ai Nurain kasa withstanding wnn words da take sukar matarsa dasu yayi, tini ya daki ƙofar kitchen din ya shigo ya daka mata wata tsawa mai burga ƴan hanji, ita kanta Hajar saida ta tsorata ta koma can karshen bango tana rarraba ido, tini jikin Khausar ya hau ɓari har lips dinta ma rawar suke, Nurain was burning in and out don wllh yafi Hajar din ma jin zafin maganganun, ya tsuke piercing eyes dinsa yana kallon Khausar yace "Are you talking to my wife that way..?", ta girgiza kai tace "Yaya please let me explain... i.", da ɗan ƙarfi ya gwaɓe mata baki yace "Shut up... you must be Mad", tsabar azaba saida Khausar ta ɗaga ƙafa ɗaya sai kace mai shirin kwaso shoki ta kai both hands ta rufe bakinta da take jin tamkar zai faɗo ƙasa, kukan ma kasawa tayi sbd azaba don ji take kamar harshenta ya datse gida biyu, Hajar na maƙale da bango sai zaro ido take, kawai saita tuna ita azabar da ta sha lokacin daya gwabje mata baki, amma tasan Khausar sai ta fita jin jiki, Khausar ta haɗiye jinin da ya taru a bakinta ba tare da tasan ta haɗiye din ba kafin ta rushe da kuka, nan ma wata tsawar ya daka mata ya nuna door yace "get out...!!", da mugun gudu Khausar ta nufi ƙofa tana zabga tuntuɓe ta fita, Nurain ya juya ya kalli Hajar da tayi wni tsilli tsilli, da sauri ta saukar da kanta, after few seconds ya fita with speed, a ƙasa mala mala kan tiles ya tarar da Khausar tana gursheƙen kuka, da ɗaci a muryarsa yace "pack your belongings now and leave my house..", Khausar ta tashi ta nufi stairs cikin sauri tana gurɗe ƙafa, yabi bayanta da wni mugun kallo, yau da ace same parent suke da Khausar Allah kuwa saita ɗanɗana kurenta, wnn wane irin rashin hnkali ne, ko wata yaji ta yiwa irin wnn mganar sai ya tsawatar mata ballanta beloved wife dinsa, few minutes saiga Khausar da jakar kayanta ta rufe fuskarta da hijab din data saka still tana kuka, Nurain ya shafa pocket dinsa ya ciro car key, kallon key din yayi sai kuma ya haura sama don ya dauko na other car din, Hajar dake maƙale jikin ƙofar kitchen ganin ya tafi sama Khausar ce kawai ta fito, tashin farko wata dariya ta tuntsure da ita tace "Yayan naki ne da kansa ya kaɗaki gida knn, Allah sarki ynxu ai kin tantance tsakanin tsakuwa da Aya, shi Yayan naki ya gwada miki value dina, from now henceforth kar na sake ganin tsumman ƙafarki in my house, Gorilla kawai..", da haka ta koma kitchen din ta rufe ranta fess, Nurain ya sauko da sauri thick eyebrows dinsa a haɗe, ya nuna door yace "i said get out nonsense", da sauri Khausar ta fita, saida ta fita snn yabi bayanta, ya rufe ƙofar ya wuce parking space, a hankali take bin bayansa tana kuka, ya nufi motar da zai shiga ya buɗe, tana isowa yace ta shiga back seat ita da jakarta, bazata zauna a spot din wcca ta gama wulaƙantawa ba, da reverse ya fita da motar daga gidan, few minutes of ride suka isa gidansu sbd uban gudun da ya falfala, a bakin main building din gidan nasu ya tsaida motar with stern voice yace "Get out", Khausar ta lalubi handle ta buɗe ta fita, tana fita ya juya kan motarsa ya bar gidan, Khausar ta shiga main palour da gudu, lokaci guda ta zube a ƙasa ta kurma wni uban ihu sai kuma ta fashe da wni matsanancin kuka, Mami da Noor wacca zuwanta knn suka miƙe a tare, Mami ta nufi Khausar tana tmbyarta lfy, ina kawai kuka Khausar take rusawa kamar ranta zai fita, Noor tayi sauri ta tsugunna gabanta tace "What happened sister..?", Khausar ta kasa cewa komai, Mami ta ƙaraso wajen tace "What happened My daughter?"........✍️
💛 HAJAR 💛

{88..}
Noor ta ɗago Khausar ta temaka mata ta koma kan kujera, gefenta Mami ta zauna tana tmbyarta lfy, har lokacin Khausar kuka take kamar wacca uwarta ta mutu, Noor ta kalli Mami tace "ba gidan Yaya ta tafi ba..?", Mami tace "Eh can taje sbd karatunta..", Mami ta saukar da murya ta dafa kan Khausar tace "Tell me what happened dear..?", da kyar Khausar ta tsaida kukan tace "Matar Yaya ce..", shiru Mami da Noor sukay suna kallonta don basu fahimci me take nufi ba, Noor tace "wai Hajar..?", Khausar ta gyaɗa kai tace "Eh ita", Mami dai kawai kallon Khausar take kafin tace "me Hajar din ta miki..?", Khausar ta nuna bakinta da ya fara suntuma gashi yayi jajir tace "kunga fa abinda ta min" sai kuma ta sake rushewa da kuka, Noor ta kalli Mami don taga reaction dinta, Mami tayi ajiyar zuciya don bata gane me Khausar ke nufi ba amma dai taga bakinta ya kumbura alamar ya fashe, Mami tace "Khausar ki nutsu ki gayamin me ya faru", Khausar ta ɗan tsagaita kukan tace "hankaɗoni tayi daga sama shine na faɗo na fasa baki and my ankle is also paining me...", Mami ta zaro ido tace "innalillah... was it a coincidence or intensional..?", Noor dai kasaƙe tayi tana kallon Khausar da mamaki, kawai ji tayi bata yarda da mganar ba, Hajar ba zata turo Khausar daga stairs ba gsky saidai idan wni abun ne ya faru, Khausar ta girgiza kai tace "No Mami tana sane ta turoni sbd mun sami slight misunderstanding kuma na bata haƙuri ashe bata haƙura ba, gashi tinda naje gidan ta mayar dani house help, nice nake komai ita nata kawai girki kullum tana upstairs, bata bani abinci idan ta dafa saita kwashe ta kai room dinta, idan Yaya ya dawo ya tmbyi naci abinci sai tace Eh, shine ni kuma na fara shiga kitchen ina dafawa da kaina, da ta lura ina shiga kitchen din shine ta rufe store ta wuce da key din, most of the time saidai nasha tea ko kuma naci biscuit dina dana tafi dashi, shine yau ta manta bata rufe store ba ni kuma na samu chance na dafa Noodles, zan wuce sama da Noodles din na tarar da ita zata sauko, shine tace wai me yasa na shigar mata kitchen ni kuma na bata haƙuri, bayan na gama cin Noodles din ne zan kai plates din kitchen ashe tana bayana shine ta hankaɗoni ƙasa..." ta fashe da kuka tace "ban san me ya faru ba kawai Yaya yace na haɗa kayana na bar masa gidansa tinda matarsa nake yiwa wulaƙanci, am very sure itace ta haɗamin sharri a wajensa..", Mami tace "ya isa.. sorry ki dena kuka kinji", da haka Mami ta shiga share mata hawayen cheeks dinta, deep down her mind tana jujjuya mgnar Khausar, Noor dai tsabar shock ta kasa cewa komai, Mami ta shafa kan Khausar tace "kinyi breakfast ko a kawo miki..?", Khausar tace "A'a..", Mami ta ɗanyi shiru tana wni lissafi, ynxu fa tace mata ai ta dafa Noodles shine ma abinda yasa suka samu misunderstanding da Khausar, Mami tace "Ohk... bari a kawo miki kinji, wuce part dina ki zauna kafin a kawo miki..", Khausar tace "Toh" ta tashi a hankali ta wuce part din Mami, Mami ta bita da kallo hakama Noor, Noor ta ɗan kalli Mami sai kuma tace "Our Mami plxx karki yanke hukunci sai kinji ta bakin both parties..", Mami tayi ajiyar zuciya tace "ki haɗawa ƴar uwarki breakfast ki kai mata..", Noor tace "Sure", Mami ta tashi ta shiga great room din Abba, Noor kam kitchen ta shige, Laure ta saka tace ta jere mata breakfast a tray, tini Laure ta gama haɗa komai, Noor ta ɗauki trayn ta fita dashi, part din Mami ta shiga ta tarar da Khausar kwance kan doguwar kujera, Noor ta ajiye trayn tace "sister ga abincin..", Khausar ta miƙe zaune tace "Thank you", Noor tace "na haɗa miki shayin..?", gyaɗa kai Khausar tayi, tini Noor ta haɗa mata tea mai kauri ta miƙa mata, Khausar ta amshi mug din ba tare da ta sha ba tace "yaushe kika zo..?", Noor tace "ban daɗe da zuwa ba..", Khausar tace "Ohk.. ya husby naki..?", Noor tayi murmushi tana cire veil din Abayarta tace "fine Alhmdllh shi yayi dropping dina ma, bai daɗe da fita sun gaisa da Mami ba kika shigo", Khausar ta gyaɗa kai ba tace komai ba, Noor tace "sister kin dai ƙi yarda da Aliyu ko..?", Khausar ta yamutsa fuska tace "waye kuma Aliyu..?", Noor tace "Aliyu fa abokin Abdul dina..", sai a lokacin Khausar ta gane kuma har waya ma suna yi kwanaki amma dai ynxu tayi blocking contact dinsa, Noor tace "he is a good person sister", Khausar tace "Ohk i will think about it" da haka ta kai cup din shayin baki tayi sipping, habawa ai da sauri ta mayar dana bakin nata cikin cup din shayin tsabar azabar da taji, kamar fatar bakinta zata ɓaɓɓako haka taji, tini ta ajiye cup din idonta ya ciko da ruwa, Noor tace "ba zaki iya shan shayin ba..?", da sauri Khausar ta gyaɗa kai tace "it is paining me so much, I can't take the tea", Noor ta ringa kallonta, can dai tace "Sister are you sure about what you told Mami earlier..?", Khausar tace "Sure..", Noor ta gyara zama tace "Ni dman tintini nasan jininku bai haɗu da Hajar ba sister, a time din bikina dai kece me kawo problem kina mata abubuwa amma ban san this time around me ya faru ba..", Khausar ta ɗanyi tsam tace "Toh me na mata lokacin bikin naki..?", Noor ta juya hannu tace "Nope bance kin mata komai ba amma ke kinsan yacca kikai mata", a ɗan fusace Khausar tace "wai me kike nufi ne..?", Noor tace "A gsky sister baki kyauta ba, koda abinda kike faɗa gsky ne toh baki kyauta ba, Mami fa uwar Mijin Hajar ce me yasa za ki faɗi irin wnn maganganun akanta a gaban Mami, kin san irin fitinar da hakan zai kawo..", a bit pissed up Khausar tace "Ohh i see dman ko time din bikin naki na lura ita kike backing, ynxun ma kinaso kice laifina ne knn?", Noor tace "Not at All.. kawai dai you shouldn't have told Mami all this...", Khausar tayi tsaki tace "Enough sister, ni dai kawai ki barni, ki bari idan ke aka fasawa baki sai kice hakan nagani" tana gama faɗin hka ta miƙe ta fita, ba ta jima ba ta dawo da jakar kayanta ta shiga room din da take zaune a gidan. Sam Mami bata kira Nurain ta tmbyesa ba'asi ba, tasan definitely zai zo da yamma toh saita masa mganar, kuma dman ita bata yanke hukuncin cikin fishi saita huce, gashi kuma wnn abune da ya faru na farko don hka dole sai ta tabbatar kafin ta ɗauki wni action din, 6 months knn da Hajar ta kasance daughter in law dinta bata taɓa jin wata matsalar daga gareta ba sai wnn moment din, daga side din ƴan uwa ma ba taji an faɗi aibunta ba saima kirkinta da ake faɗa, Iron Lady ma kaɗai ta isa hujja don ita tamkar littafi take bata ɓoye komai, gashi dai tinda take da Hajiya ba ta taɓa kawo mata complain din Hajar ba, jikokinta kam kullum sai tace ga abinda wane yayi mata, Mami dai bata sake yiwa Khausar mgnar ba tana jiran yamma Nurain yaxo, ai kam biyar saura few minutes Nurain ya iso gidan, ko a fuska Mami ba ta nuna masa komai ba har suka gaisa kamar kullum, ta tmbyesa Hajar, yace mata tana lfy, bayan wni lokaci Mami ta nisa tace "Sai kuma baka kira kaji ya yarinyar mutane tazo gida ba", ya ɗan tattare gira cause bai gane ba, har ga Allah ya manta da wta halitta wai ita Khausar, Mami tace "Khausar da ka kora daga gidanka baka kira kaji lfy tazo ba..", Nurain ya sauke numfashi baice komai ba, Mami ta haɗe gira tace "ka taɓa jin ranar da Abbanku ya taɓa korar ɗan uwansa daga gidansa ko kuma ni ka taɓa jin nasa ya kori wni nasa...?", ya ajiye numfashi yace "A'a Our Mami..", tace "wato baka taɓa ji ba sai kai tattabara sarkin ƴan aure shine zaka kori ƴar uwarka a gidanka sbd matarka ko..?", yayi ajiyar zuciya yace "Mami please do you know what happened..?", tace "if i didn't know how will I asked you such question Uthman..", ya shafa kansa bai ce komai ba, nan Mami ta zayyana masa kaff ƙaryar da Khausar ta giggilla mata, tsabar mamaki saida wni murmushin gefen baki ya kufce masa, Mami ta murtuke fuska tace "You think it's a joke ba..?", ya girgiza kai yace "Ƙarya take... wllh ƙarya take Mami, store din nan kullum a buɗe yake infact ma bbu key a jikin door din, keys din na wajena, kuma ina shiga kitchen din anytime to make a coffee ban taɓa ganin store a rufe ba, mganar abinci kam ƙarya take da kanta take dafa abinda take so taci, mganar ma ta cillota daga stairs ƙarya take nine na bigeta, mganar ta zama house help ƙarya take shima sau ɗaya ta taɓa share kitchen da palour kuma shima nina sakata, All what she said is a lie", Mami ba tace komai ba kawai kallonsa take, tashi tayi ta shiga room din da Khausar take, tana tare da Noor a room din, Mami ta kalli Khausar tace "kin iya shan Oat din..?", Khausar tace "Eh na sha da ya huce..", Mami tace "Ohk come with me..", a bazata Khausar taji zuciyarta ta buga haka kurum, da kyar tace "Toh", Noor tace "Mami kamar naji muryan Ya Nurain shine yaxo..?", Mami tace "Eh", Noor tace "bari naje mu gaisa" da haka tabi bayan Mami suka fita, ita kam Khausar wani irin kullewa cikinta yayi da taji Mami tace Nurain yaxo, da kyar tayi shahada ta fita walking slowly, kanta a ƙasa ta shiga palourn ta zauna kan carpet kusa da kujerar Mami, a fakaice ta kalli Nurain da suke mgana da Noor tace "Yaya ina yini..", bai ko kalleta ba yace "lfy", After few minutes Mami na kallon Khausar tace "Dear ki faɗi duk abinda kika gayamin da safe, me ya faru da kike je gidan Nurain ki faɗa shima yaji don yace bai sani ba", daram zuciyar Khausar ta buga ta sunkuyar da kanta, Nurain kam tini ya zuba mata piercing eyes dinsa yana jiran tayi mgana, sam Khausar taƙi cewa komai sai murza hannu take, Mami tace "Uhmm talk now..", nan ma Khausar tayi ƙumus, Noor ta ɗan kalleta sai kuma ta tashi ta bar palourn ta koma ɗaki, ba yacca Mami ba tayi ba akan Khausar tayi mgana amma taƙi, shi dai Nurain kawai kallonta yke cike da mamaki, shiru palourn ya ɗauka, Mami kam tini ta rafko jirgin Khausar, Nurain yace "Ohk Mami since she won't talk let me tell what exactly happened...", Mami was more than shock ta ringa kallon Khausar bayan Nurain ya gaya mata me ya faru, Khausar ta fashe da kuka tace "Yaya dan Allah kayi haƙuri wllh sharrin shaidan ne..", ta haɗe kanta da kujera tana cigaba da rusa kuka, Mami tayi wni nazari akan hkan da Khausar tayi, tabbas ta gano dalilin da yasa take yiwa Hajar hka, Mami ta sauke numfashi tace "you may leave", Khausar ta miƙe kanta a ƙasa ta shiga ɗaki, after few seconds Nurain yace "Mami dman nace miki ƙarya take..", Mami ta numfasa tace "Naji... Amma am not in support da dukanta da kayi akan matarka Uthman, yess bata kyauta ba bai kamata ta yi wnn furucin ba, and karka sake korar ɗan uwanka daga gidanka just like that, both of them are young kamata yyi ka yiwa Khausar din faɗa ka nuna mata kuskurenta ba wnn tough action din ba", ya shafa kansa don shima sai daga baya yaga bai kyauta ba, yace "insha Allah hkan bazai sake faruwa ba Mami", tace "ywwa itama Khausar din zan mata faɗa ba kyaleta nayi ba..", Nurain yayi ta attempting sanar da Mami cewa Hajar is pregnant amma kunya ya hanasa, hka dai ya tafi bai gaya mata ba, Ai kam da daddare Mami ta samu Khausar ta nuna mata kuskurenta, bai dace ba abinda tayi snn kuma worst part of it ƙarya, snn kuma ta gaya mata cewa ynxu Hajar is part of them tinda tayi aure cikin family nasu, ynxu Hajar kamar daughter dinta take, little sister din Noor, Mami taji daɗin yacca Khausar ta amshi laifinta kuma tace bazata sake ba sharrin shaidan ne, ita dai Mami tasan bbu wni sharrin shaidan sharrin kishi ne tinda yarinyar taso Nurain a baya kuma tana tunanin son nasa ne yaja abinda take yiwa matarsa.

★Hajar ta fito daga Kitchen da plate din gasasshiyar kazar da tayi warming a microwave, ga kuma fresh milk ta ciko glass cup da ita, ko good 2hours ba tayi da cin abinci ba gashi ynxu ma ta kwaso wni za taci, shima abincin ma kwaɗayi take ci, har mamakin kanta take, kan carpet ta zauna ta baje ta fara aika kazarta tana korawa da fresh milk, ita kwaɗayin nata ma sai ita, rannan ta haɗa Popcorn da Coffee yau kuma Kaza da madara, yanka uku taci taji har ta fara ƙoshi kuma, wayarta ta ɗauka ta buɗe data ta shiga whatsapp, message ne suka fara shigowa, chat dinta da Hafsah ta buɗe don taga ma ta turo mata wni saƙon kuma voicemail ne, Online ma Hafsahn take, Hajar ta kunna voicemail din tana ji, dariya tayi ta shiga kiran Hafsah video call, tini Hafsah ta ɗaga don dman Online take, Hajar tana ganin fuskar Hafsah a screen ta sake fashewa da dariya tace "sister nidae ban gane voicemail din nan ba ki gayamin ta nan..", Hafsah ta tashi daga palour da take zaune ta shiga ɗakinsu ta kulle da key, kallon Hajar tayi tace "Wllh duk ke kika ja min..", Hajar tace "wai me naja miki bayan ban gane me kike nufi ba..", Hafsah tace "ba kin sa nayi unblocking dinsa ba da naxo gidanki..?", Hajar tace "Toh wai shi wa..?", Hafsah tace "Ahmad mna..", Hajar tayi murmushi tace "Okay ngane", Hafsah tace "Wai ɗan mutumin nan dan yaga ina ɗan saurararsa muna gaisawa har wataran muyi fira, in gaya miki shine yayi min diren mikiya, ban san dai yacca akayi ba ɗan mutumin nan kawai ya wni turo uncles dinsa wajen Abba, ban san hawa ba ban san sauka ba jiya daddare Anty da Abba suka kirani suna tmbyata wai nasan wni Ahmad, ni dae nace musu na sansa shine suka ce in tashi in tafi, sai daga baya Anty take tmbyata wai ko nice na basa chance ya turo ni kuma nace A'a, toh dai in taƙaice miki zance Abba yace zaiyi bincike a kansa idan bashi da matsala sai magabatansa suxo da kuɗin aure..", Hajar tayi wni kyakkyawan murmushi tace "Alhmdllh wnn lamari yayi min daɗi..", Hafsah ta haɗe fuska tace "Toh ni cewa nayi ina sonsa da zai min hka..", sosai Hajar tayi dariya tace "ba sai kin faɗa ba mu mun gani..", Hafsah ta juya idanu tace "Ni shiyasa ma na kashe wayar tin jiya don kar ya kira don haushi nke ji..", Hajar tace "Ah a meye haka dan Allah.. Allah yasa ma Abba yace ya turo next week Friday, mu sha biki nan kusa wllh, nan gidana zaki taho inada Oum Sulthan wcca zata mayar dake kamar kwai, ƙamshi kam ko gonar flowers albarka", Hafsah tayi kasaƙe tana kallon Hajar sai kuma tace "Uhmm nidae ban yarda ba", sun ɗan jima suna fira kuma duk tsahon lokacin nan Hafsah taƙi yarda cewa tana son Ahmad, bayan sun gama wayar Hajar tayi murmushi tace "ƴar farka zama ki saukar da kai ne", sai kuma ta tashi ta nufi kitchen. Da daddare Hajar na tsaye gaban wardrobe zata fitar da kayan bacci ta saka don already tayi wnka kwanciya za tayi, Nurain ne ya shigo, ta juya ta kallesa, kananun kaya ta gani a jikinsa instead of pajamas, ta kalli agogo taga ƙarfe goma saura, ƙarasowa yayi ya tsaya daga bayanta yace "me zaki saka ne..?", tace "night wears..", ya buɗe section din manyan kayanta ya ciro Abaya ya miƙa mata yace "wear this..", ta kalli kayan tace "dasu zan kwanta..?", ya shafa cheek dinta yace "we are going out Baby wife..", tace "Ohk", tini ta zura Abayan ta koma gaban mirror tayi rolling veil, shi dai yana tsaye yana jiranta har ta gama shiryawa, ya riƙe hannunta suka fita ɗakin tare, ita dai tasha ƴar fitar daren da suka saba ce a siyo kayan maƙulashe, compound suke fita zuwa parking space, ya buɗe motar snn ya buɗe mata front seat ta shiga, ya zaga driver seat ya shiga, kallonsa ta ringa yi har saida ya juyo sukay ido huɗu, ya ɗage gira yace "why..?", ta girgiza kai tace "bkomae", ya kamo hannunta a hankali ya shiga mirzawa sai kuma yayi pecking, tayi murmushi tace "where are we going..?", ya mayar mata da murmushin yace "you will see", da haka ya fara driving slowly suka bar gidan, tafiyar almost 20mins sukay snn yayi parking gaban wni katafaren building, shi ya fara buɗe motar ya fita snn itama ta fita, ta ɗaga kai ta karanta sunan wajen wato Baby's World, kana ganin wajen kasan sabon buɗewa ne kuma wajene da ake siyar da kaya designers masu kyau da aminci haka zalika kuma wajen ƴan ƙarya ne masu aljihu da nauyi, yace "muje Baby wife..", siyayya sosai sukay ta kayan baby from infant size zuwa 6months, ita dai Hajar ba ita tayi zaɓen ba shine ya ringa kwasar kayan, kuma duk ɓangaren da yaje sai yace a bashi na baby girl maimakon unisex tinda har yau ba'a san gender din babyn ba, uban kayan kam sai kace na triple, saida suka je wajen cashier ya biya bill snn aka musu packaging kayan, har mota aka kai musu kayan, saida suka hau saman titi Hajar tace "Moon wai wne yace mka mace ne..?", ya ɗan kalleta yace "i have strong feeling about that..", almost 11:30 suka isa gida. Washe gari Nurain ya shiga room din Hajar bayan ya dawo daga mosque, kwance ya ganta kan gado, ya ƙarasa gaban gadon yana kallonta, scent dinsa da ta shaƙa ne yasa ta buɗe idonta, ya zauna side dinta ya kwaye duvet din da ta lulluɓa, rigarta ya ɗaga ya sunkuya yayi kissing flat tummy dinta yace "Good morning princess".......✍️
💛 HAJAR 💛

{89..}

6 MONTHS LATER

★Hajar na zaune room dinta cikin doguwar rigar Atampa wcca aka yiwa ɗinkin maternity, girman rigar ya rufe turtsetsen cikinta dake da wata bakwai, sosai cikin ya amsheta don bai muzanta mata kamanni ba sai ma wni kyau da ta ƙara, tayi wni irin haske mai kyau snn jikinta ya sake cika ta ko ina musamman ma ƙugunta, plate ne akan cinyarta mai ɗauke da dice fruits, a hankali take cakar fruits din da fork tana sha, saida ta gama shanyewa snn ta kalli agogo, ƙarfe sha ɗaya da rabi ta gani, tashi tayi daga gefen gadon da take, saida ta miƙe snn cikin nata ya sake bayyana, ta gyara rigarta da ta tattare ta nufi door da empty plate din da ta gama shan fruits, downstairs ta sauka walking gently, duk da girman da cikinta yayi bata jin nauyin jikinta, haka take sintirinta tsakanin sama da ƙasa kamar ycca ta saba kafin cikinta ya girma, ko ina na gidanta tsaf tsaf ƙamshi ya ratsa ko ina sbd azababben turaren da take bunka masa frequently, kitchen ta shiga ta wanke plate din kafin ta kife ta fito ta haura sama, room dinta ta wuce ta buɗe wardrobe ta ciro hijab da ya shiga da flowers din kayanta ta saka, wayarta ta saka a handbag ta ɗauki handbag din ta nufi door bayan ta saka flat shoe, ɓangarensa ta shiga da sallama, ya fito daga bedroom knn ta shigo, ta turo baki tace "Allah ka daɗe..", yayi murmushi yace "Afwan Momma princess", ƙarasowa yayi inda take ya riƙe hannunta ya jata zuwa kan Sofa, gefenta ya zauna yana kallonta yace "Ohh yarinyar Umma duk sanda za'a je wajen Umma tin asuba ake fara shiri", ta juya idanunta gami da turo lips dinta da suka sake ciza color dinsu, yace "Toh bari muyi daily routine namu kafin mu wuce ko..?", ta gyaɗa kai, tashi yayi ya shiga bedroom after few minutes ya fito da rechargeable Bp gauge, ya koma position dinsa ya zauna snn ya fara measuring Bp din nata, kullum ne sai ya duba cause yana sane da lokacin da jininta ya hau, farkon aurensu har ta zauna gidan Mami, Alhmdllh a kullum zai duba BP din nata yaga normal, ynxun ma dai normal din ya gani as usual, ya ɗage hijab dinta ya shiga shafa turtsetsen cikin nata yace "Hi Princess..", shafa cikin itama tayi tace "Hi Prince..", yayi chuckling yace "Princess give her a slight punch if she call you prince again..", tayi ƴar dariya tace "Ah am telling you is a boy", ya ja hancinta yace "ni kuma nace girl", ta ɗauke hannunsa daga cikinta ta gyara hijab dinta, sosai ake shan musu a tsakaninsu akan gender din unborn baby din nasu, shi yace girl ita kuma tace boy, To prolong the musu shiyasa ba'a duba gender din babyn ba a ciki wai idan yaxo ya raba gardama, shi kam yace idan baby boy ne zai bata presence, sai ƙarfe sha biyu saura suka fita compound, saida suka ɗauki hanyar gidan Umma yace "bamu siyawa Sabrah sweet ba..", tace "Ohh ai sauri muke sai next time kuma", yace "A'a fa we have to get her something", ai kam saida suka tsaya wani bakery suka sayi snacks snn suka cigaba da tafiya, Nurain yayi parking a ƙofar gidan Umma yace "Greet Umma well later in na dawo zan shigo mu gaisa", Hajar ta gyaɗa kai tace "Toh" da haka ta ɗauki ledar snacks din da handbag dinta, ya matso yayi pecking lips dinta yace "Take care..", tace "Sure Allah ya tsare Moon..", yayi nodding head yace "Ameen" sai kuma ya buɗe motar ya fita, zagayowa yayi side dinta ya buɗe mata ƙofa ta fito, tace "Moon i can do this", yace "No let me do it" da haka ya rufe murfin motar, tace "Thank you" da haka ta nufi ƙofar gidan walking slowly, saida ya tabbatar ta shige snn ya zaga ya shiga driver seat ya bar layin. Umma ta fito daga ɗan madaidaicin kitchen din gidan dake tsakar gida jin sallama, sakin baki tayi tana kallon Hajar da ta shigo, Hajar tayi murmushi tace "Ummanmu..", Umma ta kalleta from head to toe tace "La'ilaha Hajara..", Hajar ta ƙarasa ciki ta rumgumeta tace "Na'am..", Umma ta janyeta daga jikinta tana sake kallonta tace "Hajara kinyi nauyi bazaki zauna a gida ba ko..?", Hajar tace "Wata fa wajen biyu banzo ba", Umma tace "Toh ke ba kiga halin da kike ciki ba", Hajar tace "A'a Ni ba komai" da haka ta wuce ƙofar palour, Umma ta bita da kallo, Hajar na shiga palourn ta cire hijab dinta, Sabrah ta leƙo daga ɗakin Umma tace "Addah snnu da zuwa..", Hajar tace "yauwa... fito mna kike laɓewa a jikin labule", Sabrah tace "wanka nayi zansa kaya", Hajar tace "Okay", Umma ta shigo palourn ta zauna bayan ta ɗora sanwar rana, Hajar ta gaida Ummanta da ladabi, Umma ta amsa tana tmbyarta ya take, bayan wni lokaci Hajar tace "Yaya fa..?", Umma tace "Mu'azzam ya tafi Abuja wni aiki", Hajar ta waro ido tace "Abuja..?", Umma tace "Eh ai kinsan ynxu aikin nasa ba iya kano bane har wasu garuruwan suna zuwa aiki", Hajar ta gyaɗa kai tace "Toh Allah ya dawo dashi lfy", Umma tace "Ameen", Hajar tace "Nabilah ta tafi ne..?", Umma tace "Tin yaushe ai shekaran jiya ma Bappa yaxo aka ɗaura aurenta anan masallaci bayan sallar juma'a, bbu wni taro da akay sbd uwar baso take ba, haka akay komai lami bbu wni shagali sai kace ba auren budurwa ba, ƙannen mahaifinku mata suka miƙata gidan mijin", Hajar tace "Ynxu anyi auren Nabilah... Umma kinje gidan nata toh..?", Umma ta girgiza kai tace "A'a banje ba gsky sai nan gaba insha Allah zan dai daure naje idan tayi sati", Hajar tayi shiru ba tace komai ba tana wni tunani, toh ko ya labarinsu Maimuna da Sa'adatu, Allah yasa dai suma sunyi hankali kamar Nabilah, Sabrah ta fito bayan ta gama shiryawa suka gaisa da Yayarta, Hajar ta bata snacks da suka siya mata, sosai Sabrah ta dashare haƙora tace "ngd Addah", Hajar ta mata murmushi sai kuma ta kalli Umma tace "Umma dan Allah yau ma ki bani aron Sabrah na tafi da ita..", Umma ta girgiza kai tace "yaushe ta dawo daga gidan naki, daga ke har ita ku ka yaudareni dan sati ɗaya nace tayi ta dawo gida amma saida ku ka cinye sati uku..", Hajar ta marairaice murya tace "plxx Umma wnn karon baza mu ƙara ba..", Umma ta girgiza kai tace "A'a wai ance miki bayar da ɗa sauki ne dashi iyeh, ki bari idan kin haifa akace ki kawo sai kiji yacca akeji", Hajar tayi murmushi tana hasaso ycca take son unborn babynta tin kafin ma yaxo duniya, ta rasa a tsakanin ita da uban ɗan wane yafi son babyn, so da dama idan ta kissima yacca za tayi raising babyn bayan yazo duniya idan kuma taji yacca uban yake mararinsa sai taga kamar ya fita son babyn, toh dai mgnar Umma gsky ce don itama fa da alama rowar ƴaƴan nan za tayi, ko zata bayar toh fa tsaf Nurain zai hana. Ƙarfe uku da minti hamsin Umma taji ana sallama a soro, ta san ko waye don ta gane muryarsa, tashi tayi ta fita tsakar gida tana cewa "ka shigo mna Naseer sai kace wni baƙo..", Naseer ya shigo yana sake yin wata sallamar, Umma tace "saika tsaya a soro sai kace baƙo... Bismillah shigo ciki" da haka ta juya ta shiga palour, Naseer ya ajiye doyar da ya shigo da ita snn ya ƙarasa palour da ƙatuwar ledar hannunsa, ya zauna kan kujera yana shafa kansa, da sakakkiyar fuska Umma tace "Sannu da zuwa..", ya russuna yace "Umma barka da yamma", Umma ta amsa with care snn tace "ya hanya..?", yace "Alhmdllh ai kwana na uku da dawowa sbd auren Nabilah..", Umma tace "Eh fa hka ne, Allah ya sanya Alkhairy", yace "Ameen..", tashi Umma tayi ta shiga ɗakinta, ta kalli Hajar dake zaune kan darduma tana zaman tahiya tace "idan kin idar da sallar kixo ga Yayanki.." da haka ta juya ta fita, Hajar na idar da sallah ta miƙe ta fita palour, Naseer ya ɗaga kai ya ɗan kalleta sai kuma ya mata murmushi, Hajar ta samu guri ta zauna tace "Yaya ina yini", yace "lfy lou Hajar... ykk ygida...?", tace "lfy alhmdllh", yace "Masha Allah hka akeso", tayi shiru ba tace komai ba, Umma tace "kawo masa abinci da ruwa", Hajar tace "Toh" snn ta tashi ta fita, Umma ta maida dubanta ga Naseer tace "Allah yyi Albarka naga doya", ya shafa kansa yace "ba komai", tace "ya can wajen Huzaifa ba wata uku ya rage masa ba a karatun..?", yace "Eh ai ya gama ma... saidai yace bazai dawo ba don ya samu aiki mai kyau a can", Umma tace "Masha Allah shi kam ya fita da Sa'a wllh ace kana gama mkaranta ka samu aiki..", Naseer yace "Wllh kam ai da offer dinsa ya fito", Umma tace "Masha Allah..", ya janyo ledar da ya shigo da ita yace "ga wasu kayan ma", Umma ta ja ledar kusa da ita tace "Alhmdllh Naseer ai ka kusa gama haɗa lefen ma", ya waro ido yace "bafa a siyi kayan shafa ba", tace "Toh ai anyi mai wuyar tinda an haɗa sutura da takalma da jakunkuna, kayan Shafa ba masu wni whala bane..", ya shafa kai yace "gani nake kamar kayan basu da yawa", Umma ta riƙe baki tace "Lalala siff dita ai ta zama kantin kwari, kaya kam ka haɗasu ba kaɗan ba Naseer, bari Hajar ta kawo mka abinci kaci saina fiddo mka kaga yawansu..", yace "A'a kar a fiddo in na gansu zan iya shagala", Umma tace "Toh shknn, ai kayi mai wuyar ma wllh, ka gama gini tass har an sakawa gida padlock, a marrar nan ka samu gidan kanka ai ba ƙaramin luɗifi bane", a lokacin Hajar ta shigo masa da abinci a plate da kuma jug din zoɓo mai sanyi. Biyar da ƴan mintina Nurain ya kira Hajar a waya yace mata yaxo, Hajar ta fita palour don da za tayi wayar ɗaki ta shiga, har lokacin Naseer bai tafi ba don dman idan yxo yana jimawa sbd sai ya daɗe baizo ba, tini Hajar ta gayawa Umma cewa zai shigo su gaisa, Umma tace "Toh kawomin hijab dina", Hajar ta koma ɗaki ta kawowa Umma hijab dinta snn ta fito, bbu jimawa suka shigo tare da Nurain, Nurain ya gaida Umma da ladabi, Umma ta amsa da sakakkiyar fuska, bayan sun gaisa da Umma ya juya ya miƙawa Naseer hannu sukay musabaha, Nurain ko minti biyu bai ƙara ba ya yiwa Umma sallama ya fita, Umma tace "marmaza ki shirya ku tafi karki barsa yana jira", Hajar ta shiga ɗaki ta ɗakko handbag dinta ta fito, tace "Umma na tafi, idan Sabrah ta dawo Islamiyya zan kira", Umma tace "Allah ya kaiku gida lfy, saura kuma na sake ganin ƙafarki nan kusa", Hajar ta turo baki tace "next week ma zanzo..", Umma tace "karma ki kuskura na gaya miki", Hajar ta dubi Naseer tace "Yaya ka gaida gida", yace "Aha, Allah ya kaiku gida lfy", tace "Ameen" da haka ta nufi tsakar gida ta fita, cikin mota ta tarar dashi don haka ta buɗe front seat ta shiga, kallonta kawai yake har ta rufe ƙofa ta gyara zamanta, ta ɗan kallesa sai kuma ta buɗa lulu eyes dinta tace "how was your day My Moon..?", yace "Totally dull without you by my side", ya kamo hannunta ya kissing deeply yace "I missed you", tayi murmushi ta sarƙe yatsunta cikin nasa tace "Same", Ai kam hka ya fara driving ba tare da ya saki hannunta ba, saida suka hau saman titi yace "bari mu tsaya mu sayi chocolates ba..?", tace "Ai basu ƙare ba", yace "yeah it is better mu ajiye extra kar ya yanke mna Princess ta mna rigima", tayi ƴar dariya tace "Ohk", A wani mall suka tsaya, tana gaba yana biye da ita suka shiga cikin mall din, direct Aisle din Chocolate da Crunchy biscuits suka tsaya, ya bata basket yace ta ɗebi wnda take so zai duba wni abu, Hajar ta fara dubawa tana ɗebar abinda take so tana sakawa a basket, kukan baby ta jiyo daga jikin Aisle din da take, ai kam da sauri ta zagaya, wata mata ta gani durƙushe a ƙasa tana kwashe kayan da suke zube tana zubawa a basket, babyn da yake hannunta sai tsanyara kuka yake tana ɗan jijjigasa, Hajar ta isa inda take ta ajiye basket din hannunta, matar ta ɗago ta kalli Hajar, Hajar tace "ya Baby yake kuka" da haka ta sunkuya ta amshi babyn ta fara jijjigasa, ai kam tini yayi shiru, Mamansa ta ƙarasa kwashe kayan ta miƙe tana kallon Hajar tace "ngd", Hajar tayi murmushi tace "mention not" sai kuma ta ciro babyn daga shoulder dinta zata miƙawa Mamansa, ba ta miƙa mata ba ta tsaya tana kallon fuskar babyn wcca ta mata kama da fuskar wni mutum da ta sani a rayuwa, muryan namiji suka ji ance "Habibty are you done..?", Matar ta juya gun wanda yayi mgnar tace "Eh Habiby..", Hajar ta ringa kallonsa still tana riƙe da babyn har ya ƙaraso, shima kallon nata yake bbu ko ƙiftawa, Hajar ta saukar da kanta sai kuma ta ɗan russuna tace "Ya Sayyadi ina yini", ya ringa kallonta yace "Hajar Adam Gini..?", Hajar ta gyaɗa kai, Nura ya kalli kyakkyawar matarsa Maryam yace "Ɗalibata ce", Maryam ta kalli Hajar tace "Allah sarki sannu ko", Hajar tace "Ashe matar Ya Sayyadi na kawowa temako..", Maryam tayi murmushi tace "Ai kuwa dai", har Nurain zai wuce Aisle din da suke ciki sai kuma ya dawo sbd ya hango Hajar, ya shigo Aisle din walking majestically, saida ya kusa zuwa kusa dasu snn yace "Baby wife..", Hajar ta juya tana ganinsa tayi wni kyakkyawan murmushi tace "My Moon", shima murmushin ya mata kafin ya ƙaraso ya dafa shoulder dinta yace "what are you doing here..?", tace "Ya Sayyadin Islamiyyarmu da mukay sauka a hannunsa ne..", Nurain ya kalli Nura for the first time yace "Okay" sai kuma ya miƙa masa hannu sukay musabaha, briefly suka gaisa, Nurain ya kalli Hajar yace "let go wife..", tace "sure" da haka ta miƙawa Maryam baby boy din tace "Allah ya raya", Maryam ta amshi babyn tace "Ameen ngd", Hajar ta sunkuya zata ɗauki basket din da ta ajiye amma tini Nurain ya rigata, ya riƙe hannunta suka bar wajen, shopping din suka ƙarasa snn suka bar mall din. Haka rayuwar ta cigaba da garawa Couple din cikin jin daɗi da annashuwa suna rainon unborn dinsu tare, kuma har zuwa wnn lokacin ba a duba gender din babyn ba kuma suma basu dena musu ba, kowa yana kan bakarsa, shi yace baby girl ita kuma tace boy, a haka cikin Hajar ya shiga wata tara, saida ya shiga wata na tara ne snn ta fara jin nauyin jikinta, ba ta iya wnn hawa da saukar kamar da amma dai ta kan sauka downstairs twice a day. Yau da wuri Hajar ta kwanta cause tin safe take jin slight pain sai ynxu ta samu ya lafa mata shine ta kwanta, tana kwance kan gado shi kuma Nurain yana zaune kan couch yana aiki jikin laptop, wajen ƙarfe sha ɗaya Hajar ta farka, ba tasan lokacin da ta kwaye duvet din jikinta ba tana so ta miƙe zaune amma ta kasa, ji take kamar bayanta zai ɓalle, ta shafa both side dinta wai ko za taji present din mijinta, tana jin wayam ta buɗe idonta tarwal tace "Moon", da sauri Nurain ya taso ya isa gaban gadon, ya ɗagota yace "Mene ne..?", ta shiga yarfe hannu don ciwon gaba gaba yake, kawai girgiza kai take sideways ta kasa cewa komai, hasken ɗakin ya kunna sosai, Hajar ta muskuta tayi kneeling kan gado sai kuma ta kwallara wata ƙara tace "Nurain..!!", da sauri ya dawo ya zauna, ta riƙe hannunsa da iya ƙarfinta tace "ka ciremin wnn cikin.. Princess ce ko Prince ni dae bana so na bar maka", habawa ai tini Nurain ya fahimci cewa labor ne, ya tashi ya fita daga ɗakin yana jin yacca take kwala masa kira, bai wni jima ba ya dawo, gani yayi har ta kifo daga kan gadon, ya duƙa gabanta ya fara ƙoƙarin cire mata rigarsa dake jikinta, kawai daurewa yake don har ya fara rikicewa, ita kam Hajar kawai cewa take Nurain ka cire Princess din na bar maka, da kyar yayi jarumtar saka mata ƴar shawalwalar rigarta da ya ɗakko mata, ya mayar da ita kan gado yana jera mata sannu, ƙoƙarin hantsilowa take yayi saurin riƙeta, ta fashe da kuka tace "wayyo na shiga uku na lalace nace ka ciremin", da kyar ya samu ya cire hannunsa a nata ya fita, box din da ya shirya 2weeks ago mai ɗauke da duk wani abu na baby da mother sbd zuwa asibiti ya ɗauka ya fita, bai wani jima ba ya dawo bayan ya kai box din mota, da bibbiyu ya haura stairs, a ƙasa ya sameta malala ta sake sakkowa daga gadon, da ita da turtsetsen cikin nata ya haɗa ya ɗauka, ko gidan ma bai iya rufewa ba ya ajiyeta gaban mota ya kwantar da seat din, gida biyu hankalin Nurain ya rabu, ɗaya yana kan tuƙin da yake ɗayan kuma yana kan Hajar da take cikin raɗaɗin ciwo, da haka suka isa private hospital din Dr Mansoor, tini Midwives suka amshi abarsu aka wuce da ita labor room, Nurain ya ringa shawagi tsakanin ƙofar labor room din, After 20mins wata Midwife ta fito, Nurain yace "how is my wife..?", Midwife din tace "Sir please go in your wife need you..", bai ƙarasa jin ta bakinta ba ya buɗe ƙofar labor room din ya shiga.......✍️

Read page 90 and 91
👇
https://chat.whatsapp.com/CjtDNv3iMzmFhMVE9jTZzW
💛 HAJAR 💛

{90..}
Nurain na shiga labor room din ya tarar da Hajar kwance kan gado, ya ƙarasa gaban gadon ya shafa fuskarta, ta buɗe idonta a hankali, duk gumi ya tsattsafo mata a goshi tana ajiye numfashi a hankali, ya kamo hannunta yana murzawa with care yace "Sorry wife", hawaye ne suka fara sauko mata tace "Nurain bana son nan wajen ka kaini wajen Ummana", ya shafa kanta yace 'Sorry, Allah ya saukeki lfy wife", lumshe idonta tayi ba ta sake cewa komai ba, wata Nurse ce ta shigo instead of Midwife tace "Amm za'a mayar da ita ward tinda labor din ya tsaya..", Nurain ya dan yi jim duk da cewa yaji abinda Nurse din ta faɗa, yace "idan laborn ya dawo sai kuma a dawo da ita nan..?", Nurse din tace "Sure", ya girgiza kai don bai yarda ba duk da yasan cewa hka tsarin hospital yake, gsky ba za a wahalar masa da mata ba a ringa wni walagigi da ita, yace "A barta a nan din har zuwa ta haihu mna..", Nurse din ta rausayar da kai tace "Ohk" sai kuma ta juya ta fita, Nurain ya janyo kujera ya zauna ya sake kamo hannunta ya riƙe, a haka bacci ya ɗan kwashe Hajar, shi kam yana zaune tunkurkur yana gadi don dman ya saba, ya ciro wayarsa ya duba lokaci yaga 12:30 na dare, yana nan tare da matarsa, duk bayan 20 to 30mins sai Midwife ko Nurse sun shigo to check on Hajar, ƙarfe huɗu da rabi lokacin asuba ta kunno kai toh a lokacin ne Hajar ta farka, kuma kai tsaye naƙudar ta taho mata gadan gadan, An sha gumurzu iya gumurzu, daf da sallar asuba Hajar ta silloɓo ƙatuwar baby girl dinta bayan ta leƙa lahira, gidan glass kam saida ta shigesa sbd girman ƴar, a duk wnn gumurzun Nurain na room din don hannunsa ta yiwa mummunar riƙo da haihuwar tazo, tini aka gyarata ita da baby dinta aka mayar dasu Amenity ward, bayan fitar Nurse da Midwife din da suka kula da ita Nurain ya taka gaban gadon, ya ɗaga fuskarta da tayi jajur, pecking forehead dinta yayi, ya ɗago yana sake kallonta yace "Thank you so much wife", ita dai ba tace masa komai ba sai aukin lumshe ido, yayi pecking hannunta deeply yace "Thank you for making me a Father..", ya sake pecking hannun yace "Thank you for giving birth to my child..", a kasale ta masa murmushi sai kuma ta lumshe idonta, sai a lokacin Nurain ya ɗauki babyn tasa dake kwance kan gadon jarirai, ya ringa kallon fuskar babyn wcca tke baccinta peacefully, kumatunta a cike ɓul ɓul ga kuma nauyi tubarkallah sai kace ba first born ba, rumgumeta yayi sosai a jikinsa for a while, bai mayar da ita kan gadon jariran ba ya kwantar da ita kusa da Mother dinta wcca baccin whala ya kwasheta, sai a lokacin Nurain ya samu chance din kiran Mami, ai kam bugu ɗaya ta ɗaga tinda asuba tayi, Mami kam da taga kiransa saida gabanta ya faɗi, tini ya sanar mata abin alkhairy da ya faru, ta tmbyesa suna gida ko asibiti yace asibitin Dr Mansoor daga hka suka katse wayar, Saida ya kira Nurse ta tsaya a room din tare da Hajar da babyn sa snn ya wuce mosque dake kusa da hospital din don yin sallah. Ƙarfe shida da minti sha biyar na safe Mami ta iso asibitin tare da Sakeena wcca a harabar asibitin suka haɗu itama tazo, Mai aikin Mami ta shigo da basket din abinci, Nurain ya tashi daga kan kujerar da yake zaune yana kallon Hajar da baby dinsa da suke bacci har lokacin yace "Mami snnu da zuwa", Mami tace "yawwa" sai kuma ta matsa gaban gadon tana kallon fuskar Hajar, Sakeena ta ƙarasa shigowa ta ɗauki Babyn ta zauna gefen gado tana kallonta, sai kuma ta kalli Nurain tace "Mace ko namiji..?", yace "Baby girl..", Sakeena tace "Masha Allah, Ya ilahi wllh kamarku ɗaya brother..", Mami ta juyo ta kalli Nurain tace "Tin yaushe take bacci..?", yace "Tin Asuba", Mami tace "Ohk", saida Mami ta zauna a position din da Nurain ya bata snn Sakeena ta kawo mata Baby, Mami ta ringa kallon Babyn snn tace "Tubarkallah Masha Allah..", Babyn kamarta ɗaya da ubanta bbu abinda ta bari, har thick eyebrows dinsa saida ta kwaso saidai ita komai nata na mace ne, even complexion na ubanta ta ɗakko saidai ynxu akwai hasken jinjirantaka shiyasa tayi haske, Sakeena ta tsaya daga gefen Mami tana cigaba da kallon Babyn, the baby is so cute, gata ƙatuwa masha Allah, duk da cikar fuskarta da cheeks amma hancinta bai nutsu ba, hancin ya fito sosai gashi ɗan ɗos masha Allah, wani motsi babyn tayi ta yamutsa fuska har saida dimple din da take dashi ya bayyana kansa for the first time, Sakeena tace "Woah Masha Allah har da dimple...", Mami tayi murmushi tana jin son yarinyar, Nurain dai ganin gaba ɗaya hankalinsu na kan Babyn kamar ma sun manta dashi ya duƙa ya gaida Mami, Mami ta kallesa da murmushi kwance fuskarta ta amsa snn tace "An samu ƙaruwa.. Toh Allah ya raya mna ita bisa sunnar manzo..", ya shafa kansa bai amsa ba, Sakeena ce tace "Ameen", After 30mins Hajar ta farka, Sakeena ta haɗa mata shayi mai kauri ta kai mata, ganin taƙi shan shayin Mami tace "ko ba kya son wnn dear..?", Hajar ta ɗago idonta da suke a kumbure tace "A'a", Sakeena tace "ko ya miki zafi ayi diluting..?", Mami tace "A'a da zafin sai yafi.. try and take it even small daughter..", a hankali Hajar ta fara shan shayin, har saida taji ɗuminsa a cikinta da take jin tamkar an yashe mata ƴar hanji, Nurain ne ya shigo ya ajiye ledar da ya shigo da ita, sosai yaji daɗi ganin ta farka, ya matsa gaban gadon yana tmbyrta how she is feeling, Mami tace "kira likita ya dubata", yace "sure", ya nufi door ya fita, bai jima ba ya dawo tare da Nurse da Dr, both the Mother and the Baby were fine haka likitan ya faɗa, snn yace nan da 12 idan an sake tabbatar da lfyrsu za a sallamesu. Kafin ƙarfe takwas su Umma suka zo tare da Anty da Hafsah, tini Sakeena ta miƙawa Anty babyn bayan sun gaisa, Hajar ta gaida Umma da Anty, Umma dai kawai kallon ƴarta ta take, Hafsah ta koma kusa da Hajar ta zauna tace "Sannu sister..", Hajar tayi murmushi kawai, daga kan su Umma bbu wnda ya sake zuwa, don duk wnda ya kira yace zaizo Mami take cewa ya wuce can gidan suma gasu nan dawowa, Hajjaju Hajiya ma can gidan Mami tasa aka wuce da ita, kamar yacca Dr ya faɗa hakan kuwa akay, 12 aka sallamesu bayan an tabbatar bbu wni matsala, gidan Mami aka wuce da Hajar snn aka bata ɗaki guda, kafin kace me ɗakin ya cika sai zuwa ake ganin baby da duba Hajar, Umma dai bata biyosu gidan ba ta wuce gida duk da cewa tana son kasancewa da ƴarta, taso ace an bata ƴarta ta tafi gida da ita amma kuma kawaici yasa tayi shiru, ai suma taga yacca suke taraiyar Hajar din suna bata kula ta musamman, ai soyayya ce ta jawo har suka tafi da ita, Hajar na zaune kan gadon ɗakin, Anty kuma na zaune kan kujerar room din, Hajiya ce ta shigo tana dogara sandarta, Anty ta tashi daga inda take tace "Hajiya ga waje..", Hajiya ta zauna kan kujerar tace "yewwa" sai kuma ta kalli Hajar tace "Sannu Hajaru.. haihuwar fari ki haifo wnn narkekiyar ƴa ai dole a miki sannu", Hajar dai ta saukar da kanta ba tace komai ba, Sakeena ce ta shigo da Babyn a hannunta wcca take tsanyara kuka don ta farka ne, Hajiya tace "A'a lfy..?", Sakeena na jijjiga babyn tace "Tashi tayi ne Hajiya", Hajiya tace "miƙata ga uwarta ta bata Nono", Sakeena ta miƙawa Hajar Babyn, Hajar bata amshi Babyn ba tayi kamar bata san ana miƙo mata ba, amma kuma har cikin ƙahon zuciyarta take jin kukan yarinyar, Sakeena ta ajiye mata ita akan laps tace "feed her", Hajar ta saukar da idanunta tana kallon babyn, tinda taxo duniya sai ynxu ta kalleta da kyau, wni gurmi ne taji ya buɗe a zuciyarta wnda wnn shine karo na farko da ya buɗe, ta ringa kallon jinjirar dake wutsil wutsil a cinyarta tana ƙishin ƙishin, lokaci guda ta fara kuka, ɗaukarta tayi ta sakata a shoulder ta ringa shafa bayanta, still dai babyn bata dena kuka ba, Anty ta zauna kan gadon tana kallon Hajar da kyau tace "ki bata mna", Hajar ta saukar da kanta tace "Ni me zan bata", Hajiya ta caɓe zancen tace "ki bata Nono ko saita shiɗe ne..", firr Hajar ta kasa feeding babyn a gaban mutane, yama za ai tayi feeding gaban mutane, Sakeena tayi murmushi don ta gane manufar Hajar, itama haka tayi wnn wautar a haihuwarta na fari, Sakeena ta amshi babyn daga hannunta, feeder dinta na ruwan zam zam ta dauka ta zauna tana bata ruwan, daidai nan Mami ta shigo, Mami ta kalli Sakeena tace "ya take kuka har ynxu..?", Sakeena tace "Mami a siya mata formula first ynxu naga kamar ruwan mimin bai zo ba", Mami tace "Ohk bari na yiwa Nurain mgana ya kawo mata madaran..", Hajiya ta kalli Mami tace "yau naga jaraba, wace irin madara ana zaune ƙalou, jaririya da Nonon uwarta sai ace a siyo mata madarar kanti, ku bar ganinta ƙatuwa indai ku ka fara bata madara toh wllh duk saita tsiyaye, wnn kumatun da tazo dashi duk saiya zazzage wllh, kar a wni bata wata madara Nonon uwarta ne kawai zaisa jikinta ya cigaba da ɗorewa...", Mami ta saukar da murya tace "Hajiya ai ba madaran za'a bata ba, na wni lokacin ne kafin abincinta yaxo", Hajiya tace "Toh ta yaya zaizo bayan ba'a barta ta zuƙa ba, sai tana ja snn zaizo da wuri, snn kuma jegon zamani na shirme wai sai a bawa mai jego wni banzan shayi ina muka bar kunun kanwa", Mami tace "Toh sai a mata kunun kanwar..", Hajiya tace "Eh da yafi, jinjira sai tsanyara ihu take", da haka Mami ta fita zata saka a damawa Hajar kunun kanwar da Hajiya tace. bayan sallar la'asar Hajar ta fito daga bathroom Anty biye da ita, wanka Anty ta taimaka mata tayi da ruwan zafi snn kuma tayi deep sitz bath tinda bata samu tear ba, Hajar ta kalli babynta dake kan gado tana bacci, tin ɗaxu da aka bata madara take bacci abinta, Anty ta ciro mata kaya cikin box din kayansu, Hajar na gama saka kayan Anty ta shaƙe mata bowl da chicken pepper mai bitter leaf da Anty Zulaihah ta kawo mata, knocking door akay snn aka buɗe, Nurain ne ya shigo, ya ƙaraso cikin ɗakin snn suka gaisa da Anty, ido huɗu sukay da Hajar ya sakar mata murmushi, tayi sauri ta ɗauke idonta ta cigaba da shan pepper soup dinta, Anty ta buɗe ƙofa ta fita, tana fita Nurain ya matsa kusa da Hajar ya sunkuya yana kallonta, ta ɗan kallesa sai kuma ta turo baki tace "Why the look..?", yace "Mamah bear how are you doing..?", ta turo baki tace "bayan wnn princess din taka ta bani whala..", yayi ƴar dariya sai kuma ya zaga side din da babyn take ya ɗauketa, ai kam yana ɗagata ta wni tsanyare da kuka sai kace wcca aka kunna da remote, waro ido yayi snn ya mayar da ita ya ajiye, habawa ai tini Hajar ta taso saura ƙiris tayi fatali da pepper soup din, ɗaukar babyn tayi ta fara jijjigata, saida babyn tayi shiru snn ta zauna gefen gado ta ajiyeta a laps dinta tana kallonta, Nurain ya zauna kusa da ita yana kallon babyn shima, ya taɓa small soft lips din babyn yace "Finally dai Princess ce..", Hajar ta ɗan kallesa sai kuma tayi murmushi, koma dai mene ne ita tana son abarta.

★Ruqayyah na zaune tsakiyar gado ta haɗe kai da guiwa sai rusa uban kuka take, ɗakin nata cike yake da ƴan uwanta, Meema dake kusa da ita tace "haba Ruqayyah wai bazaki dena kukan nan ba, yau fa ranar murna da farin ciki ce a wajenki amma ki zauna kina kuka", Ruqayyah dai ba tace mata uffan ba ta cigaba da rusa kuka, tabbas murna ya kamata tayi a wnn rana amma kuma zuciyarta zafi take, Meema ta taɓe baki tace "Toh Allah ya kyauta" daga haka bata sake cewa komai ba, bbu jimawa Kulsoom elder sister din Ruqayyah ta shigo, sakin baki tayi tace "what is this, wai ba tayi wankan ba..?", Meema tace "yeah", Kulsoom ta zauna gefen Ruqayyah ta dafa shoulder dinta tace "Ruqayyah ki tashi kiyi wnka mna.. dangin Angon fa sunxo", wani tashin hankali ne ya sake baibaiye zuciyar Ruqayyah, Kulsoom ba ta bar ɗakin ba saida ta tabbatar Ruqayya ta shiga wanka, saida Ruqayyah ta kwashi lokaci mai yawa snn ta fito, tini Kulsoom ta kawo mata lafayar da zata saka da kuma kayan ciki, Meema ce ta taimaka mata wajen shiryawar, Ruqayyah ta saka hannunta da yaji zanen ƙunshi ta goge hawayen dake sauko mata, Haj Safiyya ce da ƙanwar Daddy suka shigo ɗakin tare, da haka suka fita da Ruqayyah da aka lulluɓe mata fuska da lafaya, wajen Momy aka kai Ruqayyah domin ta mata faɗa snn suyi bankwana, Momy ba ta iya cewa komai ba bayan fatan Alkhairy da tayi mata da zaman lfy a gidan mijinta, daga wajen Momy aka kai Ruqayyah Amarya wajen Daddy shima ya saka mata Albarka, wajen dattijan gidan aka kaita daga ƙarshe snn aka miƙata hannun dangin mijinta da suke jiran a basu ita, gursheƙen kuka kawai Ruqayyah take har aka fita da ita, aka sakata a motar da take matsayin ta Amarya suka bar gidan da convoy din motocin rakiyarta. Finally Ruqayyah tayi aurenta cikin aminci, a sabon asibitin da ta dawo aiki ne Allah ya haɗata da mijin aure, Mijin nata babban Likitan yara ne, tinda ta fara aiki a asibitin ya nuna interest akanta, farko dai sharesa ta ringa yi har zuwa wni lokaci ta ɗan fara kulasa, da haka har ta basa digit dinta da address din gidansu, soyayya mai tsafta Dr Sa'eed yake yiwa Ruqayyah, ita dai Ruqayyah kawai dai tana kulasa ne ba wai don zuciyarta naso ba, she wants to move on din, ranar da Daddy ya ganta tare da Dr Sa'eed ai kam a ranar ya masa mgana, da yake Dr Sa'eed ba da wasa yaxo ba da gske aurenta zai yi aikam tini ya turo magabatansa, aka saka lokacin auren ba mai tsaho ba cause Dr Sa'eed yace a shirye yake, har week din aure ya kama abin mamaki shine Ruqayyah ba taji tana son wnda zata aura ba, kwata kwata ta kasa buɗe zuciyarta ta bada ƙofa wni ya shigo, ga dai Dr Sa'eed din bashi da wni matsala ga kyan hali saidai kuma ba yaro bane don ya haura hamsin, snn kuma yanada matarsa har da manyan ƴaƴa ma, Ruqayyah dai tayi accepting dinsa ne sbd ta goge black spot din da tayi a wajen parent dinta, kuma don dole ma ta amshesa sbd bazata taɓa samun abinda take so ba, ya riga da ya mata nisa nisan da bazata iya kamosa ba, amma dai ta ɗauki hkan a matsayin darasi mai ƙarko da inganci na rayuwa, yeah some opportunities comes first in life, toh itama hkan ne, sau ɗaya damar auren wanda take so tazo mata amma tasa ƙafa tayi fatali da ita, wnn ya zame mata izina snn kuma ta dauki lesson har ma ta zama teacher, zata iya koyar da duk wcca taga ta dauki step irin nata don ta taimaka mata kar ta aikata abinda za tayi nadama a nan gaba.......✍️

Wanda basu samu sun shiga group ba don ya cika kuma suna son karanta 91 and 92 suyi joining wnn 👇👇

https://chat.whatsapp.com/HOOyHDJCXyO8Uxz5VFhVSU
💛 HAJAR 💛

{91..}

★Sosai Hajar ta saɓe tayi luƙui abinta ita da baby, gata ta ko wace kusurwa ake gwada mata, mijinta ya mata haka zalika ma yan uwansa, ga nata ƴan uwan suma, ƴan uwan Umma ma da suke nan kano duk saida suka zo, yau kwananta huɗu da haihuwa, yau ma Ummanta taxo tare da Iya da Wasilah da kuma Nabilah, Nabilah na riƙe da babyn tace "Masha Allah... Allah ya raya", Anty tace "Ameen", Wasilah tace "Ni kam na sha zasu bamu itane mu tafi da ita tinda dai hka al'adar haihuwar fari take..", Anty tayi ajiyar zuciya tace "Toh dai gashi nan din ma bbu abinda ta rasa na uwa, wllh suna kamantawa", Iya tace "yoh wne kamantawa kuma.. kawai su bamu ɗiyarmu mu wuce da ita gsky..", Umma duk tana jin su ba tace kanzil ba, Anty tace "Ni kam banga aibun hkan ba wllh, duk so ne fa yasa suka riƙeta..", Iya ta gyaɗa kai tace "sai dai hkan, amma dai gsky ya kamata a duba uwar ƴa", Umma dai ba tace komai ba hakama Nabilah dake riƙe da baby, ƙofa aka buɗe Noor ta shigo da fara'arta, da ladabi ta gaishe da mutanen ɗakin, ta ƙarasa wajen Hajar tace "Hajar..", Hajar tayi murmushi tace "kun dawo..?", Noor ta amshi babyn daga hannun Nabilah ta zauna gefen Hajar tace "Azalzalansa nayi muka taho, hka kurum ayi suna bbu ni..", Noor ta shafa cheek din babyn tace "Masha Allah so cute" sai kuma ta rumgumeta tace "Hajar ki bar min ita..", Hajar tayi murmushi kawai, Noor ta rage murya sosai tace "Hajar ya kika ji a labor room..?", Hajar tayi wni murmushi tace "words can't express the pain na rantse, kawai dai na ganni a gidan glass", Noor ta kyalkyale da dariya tace "Na shiga uku..", kawai hango kanta take nan da wata biyar, Mami ce ta shigo ta samu waje ta zauna suka gaisa dasu Umma bayan gaisawar da sukay ɗaxu, Sakeena ce ta shigo ma'aikata gidan mata biye da ita da kayayyaki, boxes ne aka lubge da kaya masu yawa a tsakar ɗakin, su Umma dai suka bi kayan da kallo bbu wnda yace wani abu, tini Mami ta musu bayani cewa kayan barka ne, kaya iya kaya aka zubawa Hajar da Babynta masu uban tsada, bbu abinda babu na kayan baby, har da set din danƙareren gold aka sakowa Hajar cikin kayanta, itama baby an saka mata ɗan kunnen gold guda biyu masu kyau. Daren ranar Nurain ya shigo kamar yacca ya saba, babyn sa ce rumgume a hannunsa yana kallonta, Hajar tace "Papa bear..", ya kalleta yace "Uhmm Mamah bear..", tace "daman Noor ce tace tana son na bar mata baby, ni kuma i can't say no to her nace tazo ta ɗauka..", tini Nurain ya haɗe gira yace "She must be crazy, my princess is not a toy..", Hajar tayi murmushi don tasan za'a kwata, wnn yarinya mai rabata da ubanta a ynxu ai sai Allah, wayar Nurain ce ta fara vibrate, ya karkata yace "Mamah bear help me with my phone..", Hajar ta zura hannu cikin aljihunsa tana cewa "ka ajiye wnn princess din mna", yace "A'a saidai kar a ɗaga wayar", tana ciro wayar yace "Who..?", ta kalli screen din tace "Punk..", yace "Ohk", tace "In ɗaga..?", yace "Sure Farooq ne", picking tayi snn ta kara masa a kunne, ita dai kallon mamaki take masa, toh wai don an ɗauki baby shine baza ayi amfani da hands ba, ko dai nasa salon ɗaukar yaran ne hka, suna gama wayar yace "Farooq zai shigo..", tace "Okay", ta tashi ta ɗauki zumbulelen hijab dinta ta saka, sai a snn ya ajiye babyn kan gado ya tashi ya fita, bbu jimawa ya dawo tare da Farooq, Farooq ya samu guri ya zauna kan kujera, gaisawa sukay da Hajar snn ya mata barka, ita dai kanta na ƙasa ta amsa a taƙaice, Nurain na zaune position din da ya tashi ya rumgume baby, Hajar ta ɗan saci kallonsa ganin bai bawa Farooq ita ba, Farooq yayi gyaran murya yace "Dude..", Nurain ya kallesa da gefen ido yace "why..?", Farooq ya murtuke fuska yace "The Baby..", Nurain yace "ka makara duk wnda bai zo ba 2days ago to ba ganin baby", Farooq yace "i was not in town you know..", Nurain ya miƙe da babyn a hannunsa yace "really" sai kuma ya miƙa masa ita, ashe Farooq bai iya ɗaukar jarirai ba gwara ma Nurain, ai kam ya riƙe babyn a hnkali don gani yake idan ya riƙeta da kyau zai iya ɓallata, babyn ta ɗan karkace a hannun Farooq, habawa ai da sauri Nurain ya taro abarsa sai kuma ya amsheta, Farooq yayi dariya sosai yace "riƙe abunka..", Nurain ya koma ya zauna yace "ko baka faɗa ba", Farooq yayi slight smirk bai ce komai ba, few minutes after that Farooq ya ɗauki wayarsa yayi dialing numbern da yayi saving da Baby with love emoji, kara wayar yayi a kunne yace "Baby where are you..?", daga ɗaya ɓangaren da muryar mace aka ce "Ohh Darling muna gaisawa ne da Mami..", yace "Ohk you have to be fast kar Ummi tace munyi dare..", tace "Alright am coming.." da haka ta katse kiran, few minutes aka buɗe ƙofar ɗakin, da sallama ta shigo kafin ta ƙaraso ciki, tinda ta shigo Farooq yake kallonta, ita dai sau ɗaya ta kalli position dinsa ta ɗauke kai, sosai tayi bowing tace "Yaya ina yini..", Nurain ya ɗan kalleta yace "lfy lou Khausar... how are you doing...?", tace "fine Alhmdllh" sai kuma ta kalli Hajar tayi murmushi tace "Ina yini Maman baby", Hajar ta mayar mata da murmushin tace "mun yini lfy", Khausar tayi murmushi tace "lfy alhmdllh.." da haka ta ajiye medium ledar hannunta ta amshi babyn a hannun Nurain, bbu jimawa Khausar ta kwantar da babyn ta ɗauki ledar da ta ajiye ta miƙawa Hajar tace "Allah ya rayata", Hajar ta amshi ledar tace "Ameen thank you", sosai Hajar tayi mamakin yacca Khausar ta sauya mata, ba tin yau ta fahimci hkan ba, ynxu suna gaisawa cikin mutunci bbu wni ɗagawa, Khausar tace "Yaya saida safe" da haka ta nufi door, Farooq ya tashi ya ciro note din ƴan ɗari biyar biyar ya ajiyewa Hajar snn ya fita. bayan tafiyarsu Farooq Nurain ya kamo hannun Hajar yace "you need anything Love..?", ta gyaɗa kai, yace "Name it Baby wife..", ta kwantar da kanta a shoulder dinsa tana turo baki tace "Seafood", yace "Ohk", ta ɗaga kanta tana kallonsa, yayi kissing lips dinta lightly yace "let me buy it for you", ya duƙa yayi pecking cheeks din baby kafin ya fita, bayan fitarsa da few minutes Hajar taga babyn ta fara saƙa da hannunta alamar ta tashi, ɗaukarta tayi ta fara breastfeeding dinta, tana gama breastfeeding dinta ta sakata a kafaɗa, after few minutes ta kwantar da ita don har ta koma bacci. Ranar suna gida cika yayi maƙil da ƴan uwa da abokan arziki na both side, yarinya taci suna Nanerh Khadijah amma ana kiranta Nanerh sbd sunan Mami ne, gsky an zuba shagali mai lasisi, Hajar har ta gaji da kyau sai shiga take tana fita cikin sabbin ƴan ubansun kayan da aka ɗinka mata, kyau mai sanyi tayi don bata kwaɓa kwalliya ba, komai nata natural ta barshi, kitso kawai akai mata sai jan ƙunshi, sosai Hajar taji daɗin zuwan Oum Sulthan da sauran neighbors dinta. Daren ranar sunan ne Nurain ya shiga part din Maminsa da take kiransa, a bedroom dinta ya tarar da ita, Mami tace "What is your next plan after the naming ceremony..?", ya shafa kansa yace "Nothing Mother..", Mami tace "Okay, sai Hajar ta tafi gida ta ƙarasa 40days dinta", habawa ai tini Nurain ya zubawa Mami idanu, shi da yake so a basa matarsa da ƴarsa su tafi gida ya yaji ana mganar 40days, Mami tace "kasan dai hkan al'ada ne ko, kuma nasan suma iyayenta kawai kawaici sukay mna ta zauna a nan na sati guda, bana so a shiga huruminsu da yawa, itama nasan tana so taje wajen mahaifiyarta..", Nurain dai ya kasa cewa komai don ji yake kamar ana zare masa spine, Mami tace "Any problem with that...?, idan fa kace baka so toh ba zata ba", ya girgiza kai, Mami tace "ba kace min zaka tafi China ba ko ka fasa ne..?", ya girgiza kai yace "A'a zan je", Mami tace "Ohk... shknn ma kaga kayi tafiyarka lfy bbu wni burden ita kuma taje gidansu ko?", ya gyaɗa kai yace "Toh shknn our Mami... yaushe zata tafin..?", Mami tace "ko gobe sai a kaita", yace "Toh". Nurain na barin wajen Mami direct ɗakin da Hajar take ya wuce, ta fito daga wanka knn ya shigo, rabonsa da ita tin safe a palour da akay musu hoto da baby dinsu, yace "where is our princess..?", tace "An tafi da ita wajen Hajiya za'a mata wanka", ya sauke ajiyar zuciya yace "yau an bata whala ko..?", Hajar tayi ƴar dariya tace "whala kuma..?", yace "Eh mna, nasan an ta ɗaukarta ne, duk yawan mutanen nan sai suce sai sun ɗauki baby", tace "A'a fa Hajiya ce tasa aka goya ta so duk wnda zai ganta saidai ya ganta a baya", Nurain ya sauke ajiyar zuciya yace "better", ƙarasawa yayi inda take, tayi sauri ta saka kayan baccinta riga da wando, saida ta gama sa kayan snn ya gaya mata mgnar zuwa gidan Umma, sosai yaga farin ciki ya bayyana bisa fuskarta, ya riƙe hannunta gami da sarƙe yatsunta da nasa, ƙoƙarin kwace hannunta ta ringa yi amma yaƙi ya saketa, ta marairaice tace "wani fa zai iya shigowa", yace "wnda ya shigo shi yaga duhu, kowa yasan am with my wife" da haka ya riƙo ƙugunta ya janyota jikinsa ya bata wni kiss a lips, ta zaro ido sai kuma ta fara turasa, ya ɗago hannunta da ya sarƙe da nasa yayi kissing, murya ƙasan maƙoshi yace "i will miss you", suka ringa kallon eye balls din juna, yaja hancinta yace "Silly girl..", ba ta san lokacin da wni murmushi ya kufce mata ba, kawai ta faɗa ƙirjinsa ta kwantar ta kanta gami da lumshe ido tana shaƙar pure scent dinsa. Haka kuwa akay washe gari Anty Zulaihah da Sakeena suka raka Hajar da baby Nanerh har gidan Umma, Umma never expected that don haka a fili ta nuna farin cikinta, Hajar ma dai taji daɗi sosai saidai tasan za tayi kewar mijinta. Duk wadanda basu samu sunje barka da suna ba nan gidan Umma suka biyo Hajar, Sosai Hajar take jin daɗin zama a wajen Ummanta, ga Sabrah anyi ƴa kullum ta goye Nanerh har yarinyar ta saba da baya, gashi mimin Uwa ya amsheta sai narka ƙiba take don yacca tazo ƙatuwa haka ta ɗora, kullum Nurain sai yaxo da yamma ko da daddare, a haka Hajar ta cika sati biyu da a gidan Umma, yau ma dai ta shirya tsaf tana jiran Nurain da yace zaizo, sai ƙarfe 8 na dare ya ƙaraso, ya shigo suka gaisa da Umma kafin ya wuce ɗakin soro wnda yake matsayin sitting room kuma ɗakin Mu'azzam, Hajar ta shiga ɗaki ta amso Nanerh wacca take hannun Sabrah tana mata wasa, Hajar tace "har ynxu dai babyn naki bata isa fara dariya ba ai Anty Sabrah", Sabrah tace "idonta biyu shiyasa nake mata wasa kar tayi kuka", Hajar ta wuce ɗakin soro, shiga tayi tace "Sannu da zuwa My Moon", yace "you're welcome Baby wife", ta ƙarasa ciki, Nurain ya amshi Nanerh yana kallonta, a kullum yarinyar ƙara girma take da kyau, ya jima yana kallonta kafin ya ɗauki wayarsa dake hannun kujera, ya kalli Hajar yace "Come", ta taso ta zauna kusa da shi, kunna wayar yayi snn ya kunna data ya shiga wni page, yayi ƴan danne danne snn ya miƙa mata yace "which one do you like?".......✍️

read 92 and 93... 👇

https://chat.whatsapp.com/HOOyHDJCXyO8Uxz5VFhVSU
💛 HAJAR 💛

{92..}
Hajar ta amshi wayar ta kalli screen din, a hankali take scrolling tana duddubawa, bayan ta duba ta ɗan kallesa tace "Moon ai ni duk sun min kyau..", yace "wnda yafi miki kyau zaki nunamin..", ta gyara zama harda harɗe ƙafa tana dubawa, after like 5mins ta haska masa wayar tace "This One..", ya amshi wayar yana kallon wnda ta zaɓa da kyau, ya gyaɗa kai yace "Alright.." sai kuma ya ajiye wayar, Nanerh dake hannunsa wacca take wurwurga idanu ce ta fara kuka, Hajar ta lakace mata hanci tace "Ai daman nasan sai tayi halin", ai kam baby kamar tasan me ake ta sake tsanyarewa da kuka, Nurain ya waro ido yace "Baby wife anya ba kiyi rigima ba kina ƙarama", Hajar ta waro ido tace "A'a fa ni banyi rigima ba, daman da kai take kama har rigiman ma kai kayi", Nurain ya zame hular baby Nanerh ya fara rubbing small head dinta wnda yake cike daff da suma kamar gonar audiga, Hajar kam wayarsa ma ta ɗauka ta fara buga game ta barshi da rigimammiyar ƴarsa yana aikin rarrashi, daga tayi shiru kamar abin arziƙi sai kuma ta sake callarewa da kuka, Nurain ya ɗaga yarinya ya ringa dudduba jikinta wai ko wni gurin ne yake mata ciwo shine take kuka, ya kalli Hajar yace "Baby wife tana kukan dare ne..?", Hajar ta gyaɗa kai tace "Sosaima", ya miƙa mata ita, ta amsheta ta fara feeding dinta, yace "let take her to hospital", Hajar ta ɗaga kanta daga kallon Nanerh ta dubesa tace "Umma tace lfyrta lou fa", ya ɗan shafa kansa yace "Yeah, amma dai muje asibitin taga Dr", murmushi Hajar tayi ta shafa kan Nanerh da take ta aukin cin abincinta tace "Okay, let me inform Umma", yace "Ohk", saida ta gama feeding Nanerh wcca ta koma bacci snn ta basa ita, da haka ta shiga cikin gida, A palour ta tarar da Umma tare da Sabrah suna kallo tinda gidan akwai Solar wcca Mu'azzam ya haɗa 2 months earlier, Hajar ta saukar da murya tace "Umma dman cewa yayi zamu kai Nanerh asibiti sbd kukan daren da take..", Umma tayi murmushin manyan tace "Toh shknn, nasan dai bbu abinda yke damunta", Hajar tayi shiru ba tace komai ba, Umma tace "yanxu asibitin zaku tafi..?", Hajar tace "Eh", Umma tace "Toh sai kun dawo", Hajar ta shiga ɗakin da take kwana ta ɗan kimtsa snn ta fito, ta kalli Umma tace "mun tafi" da haka ta nufi ƙofa ta fita, ɗakin da Nurain yake ta shiga, ya kalleta from head to toe yace "shall we..?", ta gyaɗa kai, yace "Ohk, take her", ta ƙarasa inda yake ta amshi Nanerh, yana biye da ita suka fita ƙofar gida inda yayi parking motarsa, ya buɗe mata front seat ta shiga ta zauna kafin ya rufe ƙofar, driver seat ya shiga, yayi stretching kansa yana sauke ajiyar zuciya, kunna motar yayi snn ya kashe Ac sbd Nanerh, a hankali yke driving suna fira da matarsa har suka isa wni private Pediatric clinic, suna zuwa ya yankar musu card, few minutes after that Hajar ta shiga consultation room din bayan wcca take ciki ta fito, Hajar ta zauna kan kujera tana fuskantar female Pediatrician din dake room din, a hankali Hajar tace "Ina yini", Pediatrician din ta amsa da sakakkiyar fuska, tini ta tmbyi Hajar me yake damun babyn nata, Hajar ta ɗanyi jim kafin tace "tana yin kukan dare snn ma idan idonta biyu tana kuka", Pediatrician din ta gyaɗa kai tace "Tana yin bacci..?", Hajar tace "Eh", Pediatrician din ta amshi Nanerh to check on her, baccinta kawai take abinta, ta ɗaga rigarta pink snn ta ɓalle overall dinta, cibiyarta ta duba tana haskawa da pen torch, ta haska both ears dinta suma, murmushi Likitan tayi snn ta mayar da buttons din overall din ta ɓalle mata, a hankali ta ɗagata ta ringa ɗan jijjigata don so take ta tashi, ita dai Hajar kawai kallon Likitan take, ai kam baby Nanerh ta fara yamutsa fuska sai kuma ta fara wutsil wutsil, lokaci guda small pink lips dinta suka fara karkarwa alamar za tayi halin, tini ta tsanyare da kuka da iya ƙarfinta, Hajar dai da ba don a kan idonta akai komai ba da zata iya cewa mintsilar mata ƴa akay, ƙofar aka buɗe, Nurain ne ya shigo da sauri don zamm ya jiyo kukan babyn tinda tsaye yake jikin ƙofa, ƙarasowa yayi ciki yana kallon Likitan yace "Dr what's wrong with my daughter..?", Likita tayi murmushi tace "Relax your daughter is perfectly fine, bbu abinda yake damunta, lfy ma har yaso ya mata yawa...", Nurain ya sauke wni ajiyar zuciya yace "Toh amma wnn kukan fa", tace "rigimammiya ce kawai amma bbu abinda yake damunta", sosai Nurain da ita kanta Hajar suka ji dadi, Nurain yace "Thank you Dr", Likita tace "you're welcome, kawai dai haƙuri za ayi da kukan nata tinda Arigimatu ce", Nurain ya gyaɗa kai yace "Sure", Hajar ta amshi Nanerh a hannun Likitan snn suka fita, bayan sun bar asibitin ne Hajar tace "Moon ynxu wnn princess din taka ta kyautamin knn..", murmushi yayi ya juyo ya kalleta sai kuma ya ɗauke hannunsa daga jikin steering ya shafa cheek dinta yace "zata dena, i promise you this tinda kema kin rage kukan rigima..", ta turo baki tace "Ah ni kam banyi rigima ba", yayi slight smirk yace "Ni dae kin yi min, da fa kullum sai kin yi min kuka, ko kin manta ne..", ta juya idanunta tace "Alright, amma dai nawa da dalili ita kuma Princess dinka mara dalili take", yayi dariya ya juya ya kalleta yace "kema mara dalilin kike min, shknn ma My Princess avenge that for me", ta sake rumgume Nanerh a jikinta tace "her father's daughter", slowly ya kamo hannun Hajar while still driving yace "Te Amo..", ta ɗan yi still don bata gane me yace ba, ya sake cewa "Te Amo", tace "translate..", ya murza hannunta dake cikin nasa yace "I Love you", tayi murmushi tace "Nado Sarang hae", yayi chuckling yace "translate", tace "I Love you too", sukay dariya a tare, sai tara da minti hamsin suka isa gidan Umma, shi dai bai shiga ba amma saida ya tabbatar Hajar ta shiga gida snn ya koma mota ya tafi. Haka nan rayuwar ta cigaba da mirginawa har Hajar tayi wata guda a gidan Umma, kwana huɗu knn Nurain bai je gurinsu ba sbd aikin da ya saka a gaba yake so ya kammala kar lokaci ya ƙure masa, so yake nan da sati guda a hattama komai, China din ma da yaso zuwa tini ya janye tafiyar ya maida hankalinsa akan abinda yake, tinda bai samu yaje wajensu ba hakan yasa suke yin dogon video call, A tsakanin lokacin nan Anty ta fara yiwa Hajar aike na magunguna masu kyau, Hajar kam ta ringa ɗirke abunta don ynxu tasan amfaninsu, gashi ta siyo babbar robar dilke a wajen Oum Sulthan, sosai gyararriyar fatarta ta sake kyau matuƙa, ga sabbin turarukan da take tsuma jikinta dasu wnda a lokaci guda jikin nata ya ɗau ƙamshi mai sanyaya zuciya. Ranar Wednesday Hajar na zaune a palour suna cin abincin da ta dafa musu, shinkafa da wake wcca ta sha haɗin lettuce salad da soyayyen kifi, da kuma zoɓo mai sanyi, bayan sun gama cin abincin Hajar ta fita da kwanukan ta dawo ta zauna, knocking door akay, Sabrah dake riƙe da Nanerh suna zaune palourn ta tashi ta ajiye Nanerh snn ta fita buɗe gida, Sabrah ta dawo tana cewa "Umma Yaya Nabilah ce", daidai nan Nabilah ta shigo da sallama, Umma tace "Ah a Nabilah ce..?", Nabilah ta zauna kan carpet tace "Eh Umma nice", Umma tace "sannu da zuwa", Nabilah tace "Yauwa Umma ina yini", Umma ta amsa snn ta tmbyeta ya take da mai gidanta, Nabilah tace "lfy alhmdllh" sai kuma ta juya ta kalli Hajar wcca take kallonta da sakakkiyar fuska, gaisawa sukay da Hajar a mutunce, Nabilah tace "ya Nanerh..?", Hajar ta nuna kan kujera tace "gata can", Nabilah ta leƙa fuskar Nanerh tace "bacci ma take kar na ɗauketa ta tashi", Hajar tace "Okay toh ynxu tayi bacci da idonta biyu", Nabilah ta saukar da kai tace "Umma daman zai shigo ne ku gaisa", Umma tace "Mai gidan naki..?", Nabilah ta gyaɗa kai, Umma tace "Bismillah shigo dashi", Nabilah tace "Toh" da haka ta miƙe ta fita, Hajar ta tashi ta shiga ɗaki, Umma ta saka hijab dinta, babu jimawa Nabilah ta shigo tare da mijinta, bayan sun gaisa da Umma Hajar ta fito suka gaisa, bai wni jima ba ya tashi ya tafi ya bar Nabilah a nan, har yamma Nabilah na gidan, Umma dai taji daɗin yacca taga Nabilah, kana ganinta kasan tana jin daɗin gidan mijinta, tayi kyau tayi ƙiba abinta don hankalinta a kwance yake, daidai gwargwado mijinta yana kula da ita da iya ƙarfinsa, Nabilah ta gayawa Umma cewa zasu koma Bichi da zama, Umma ta kalli Nabilah tace "kamar ya Bichi..?", Nabilah tace "Ai daman acan garinsu Bichi yake gini kuma ynxu ginin ya kammala, kuma daman wnn gidan da muke ciki na haya ne..", Hajar tayi shiru tana kallon Nabilah don ba ta so komawarsu Bichi ba, haka zalika Umma ma ba ta so tafiyar Nabilah ba amma kuma gidan kai yafi na haya, Umma tace "kun sa ranar tariyar ne..?", Nabilah tace "Eh nan da sati biyu yace", Umma tace "Toh Allah ya kaimu, Allah ya haɗaki da mutanen kwarai a can din", Nabilah tace "Ameen", Umma tace "kina dai zuwa wajen mahaifiyarki ko..?", Nabilah tayi shiru, Umma tayi ajiyar zuciya tace "ba kya zuwa ko..?", Nabilah tace "Naje dai sau biyu", sosai Umma ta yiwa Nabilah nasiha mai shiga jiki, a take Nabilah taji ta ɗan sauko akan haushin Maama da ƴan uwanta da take, ta ƙudurce a ranta zata gidan kafin su koma Bichi. Washe gari Hajar ta je gidan Anty tare da Sabrah, a nan take jin cewa ashe bikin Hafsah ya matso saura 2months, ita ta sha ma bikin saura 4months ashe ba haka bane. Ranar Saturday ne Hajar zata koma gidanta, jiya da Nurain yaxo Umma tace ranar asabar yaxo ya tafi da matarsa, tin safe Hajar take haɗa kaya, sosai take zumuɗin komawa gidanta, saida Umma ta kamata snn ta nutsu kunya ta rufeta, Umma dai ta rausayar da kai ta fita ta barta, Umma ce ta yiwa Nanerh wanka ta shiryata, Hajar ma ta shirya cikin riga da skirt na atampa mai laushi, sosai tayi kyau ɗaurin ɗan kwalinta ya zauna a kanta das das, Sabrah ganin Hajar na shiri ta fara harhaɗe rai, Hajar tace itama ta shirya su tafi, Umma na jin hka tace A'a bbu inda zata, hka dai Sabrah tayi ta matsar kwalla gashi ta saba sosai da Nanerh, ƙarfe uku Nurain yaxo, ya kira Hajar ya gaya mata cewa yazo, saida ya shiga suka gaisa da Umma, already daman sun fito da kayansu palour don haka ya ɗauka ya fita dasu ya saka a booth, yana tsaye jikin mota Hajar ta fito kanta a ƙasa tana riƙe da Nanerh, saida ta ƙaraso snn ya leƙa fuskarta yaga idanunta sunyi ja, eyelashes dinta a jiƙe, yayi slight smirk yace "Uhmm halin ko", ta juyar da kanta, saida suka shiga mota snn ya amshi Nanerh yayi pecking cheek dinta yace "Hi Princess", after a while ya miƙawa Hajar ita, Hajar ta ɗago ta kallesa don wni mugun kyau ya mata, ta lura ma kayan jikinsa sababbi ne kamar yadda nata suke sababbi, ta ringa kallonsa without blinking, twisting fingers dinsa yayi a saitin fuskarta yace "Where are you..?", ta sauke numfashi tace "here". kai tsaye gidan Mami suka wuce, sosai Mami taji daɗin ganin yacca Nanerh ta canza, yarinyar sai girma take alamar tana samun kulawa, Mami ta kaiwa Abba Nanerh don yana gidan itama Hajar din ta shiga great room dinsa suka gaisa, A nan gidan Mami sukay sallar la'asar, immediately Nurain na dawowa daga mosque yace Hajar ta fito, already a cikin mota ta samesa don haka ta shiga suka bar gidan, suna isa unguwarsu Nurain ya rage gudun motar suka shiga layin gidansu, Hajar ta tattare gira tana kallon gidan da Nurain yake danna horn a gaban gate dinsa, Wnn ai ba gidanta bane, ta cikin mirror ta hango gidan Oum Sulthan opposite to gidan da suke da niyyar shiga, hakan ne ya tabbatar mata da cewa eh wnn position din gidanta ne amma fa an canzasa don wnn yafi nata girma, ta juya ta kallesa taga ashe kallonta yake, murmushi ya sakar mata kafin ya juya ya shigar da motar ciki don mai gadi ya zuge gate, nan ma dai Hajar sake sandarewa tayi, anya wnn gidanta ne, an fa canzasa, canzawar ma zuwa high class, ta dubi makeken compound din da suke wucewa har suka isa tafkeken parking space da ya ninka na da, Nurain yayi parking motar ya juya yana kallonta gami da sauke ajiyar zuciya, Hajar dake leƙen window tana kallon gidan ta juyo ta kallesa with mixed facial expression, da cracking voice tace "Moon nan din kuma ina ne..?", yace "Home sweet slum, welcome to your home Baby wife"........✍️
💛 HAJAR 💛

{93..}
Hajar dai kawai kallonsa take har lokacin da wni irin expression, kashe mata ido ɗaya yayi wnda bai iya ba ya buɗe motar ya fita, zagayawa yayi ya buɗe mata yace "get down Baby", ta gyaɗa kai, Nanerh dake laps dinta ya ɗauka ya sakata a shoulder, Hajar ta fito still tana ƙarewa compound din da ya sha wasu flowers masu kyau da ƙara lfyr ido kallo, rufe motar yayi ya danna lock kafin ya riƙo hannunta suka nufi entrance din gidan wnda a ynxu ya canza position, ita dai kawai binsa take like one living status, gsky tana buƙatar fashin baƙi, suna isa entrance door ya ciro key a pocket ya buɗe snn ya murɗa handle yace "go in Baby", taƙi shiga sai kuma ta ɗaga kai, ta buɗe baki knn za tayi mgana ya dafe bayan Nanerh ya sunkuya yayi kissing karan hancinta lightly yace "No more words just go in", a hankali ta shiga ciki kamar wcca kwai ya fashewa, yabi bayanta ya rufe ƙofa, Hajar ta ringa kallon makeken palourn da aka sauyawa matuƙa, sauyi ma kam mai lasisi wnda ya jirkitasa daga ainahinsa na da, Hajar dai was speechless at that moment, Nurain duk yana lura da ita, ya kamo hannunta suka nufi stairs wnda shima taga kamar an canza masa position, kamar yacca tayi tunanin za taga sauyi a saman hakan ce ta kasance, wata huge door ya buɗe sai gasu a wni palour wnda a da bbu shi, Hajar tayi wni murmushi tace "Woah", ta cire hannunta daga nasa ta fara zaga palourn, ya kwantar da Nanerh kan kujera, yasa trow pillows guda uku ya kareta, wajen Hajar da take aukin santin palourn ya nufa, yace "you like it..?", ta juyo ta kallesa ta gyaɗa kai tace "yess i like it wllh", yayi murmushi yace "more are coming", ta cikin palourn yabi da ita suka shiga wata ƙofa ai kam sai gasu a wni huge bedroom, tsabar girman bedroom din daga can nesa kake hango gado wnda shi kaɗai ne a babban ɗakin sai chest of drawers, yace "This is your room..", a fili take nuna masa farin cikinta, bakinta yaƙi rufuwa tsabar murna, ynxu room dinta ba mai wardrobe bane makekiyar Closet ce da ita wcca ta ƙunshi duk wni kayan shiri da zata buƙata, ta wata glass door zaka wuce ainahin bathroom dinta wnda suka opposite da closet din, daga nan ɓangarensa suka wuce, shi kam dai ba a sauyasa ba amma kuma an canza furniture, sosai ko ina ya tafi da imanin Hajar kuma ta ringa appreciating, saida suka gama da ɓangarensa suka fito snn ya kalleta yace "kin san duk wnn da kika gani ba suyi kyau ba..", ta waro ido tace "says who..?", ya koma ta bayanta ya rufe mata idanu da palms dinsa, tace "but what are you doing Moon..?", yace "yeah... i will lead you to the Empire..", tayi murmushi mai sauti tace "Then", yace "ready..?", ta gyaɗa kai tace "sure", a hankali suka fara tafiya yana leading, ita dai sai wani wawaken iska take da hannu sai kace makauniya, tace "Moon karfa na ƙume da bango", yace "how will that happen remember am your saviour", after walking for a minute taji ya buɗe ƙofa snn suka shiga wni guri, a hankali ya zame hannunsa daga idonta, ta buɗe idonta tana ƙarewa wajen kallon, baby room din da a tv kawai ta taɓa ganin irinsa ta gani, yace "My Princess room", ba karamin kyau baby room din yayi ba, komai na ciki pink and white ne, ga wallpapers da stickers masu kyau anyi design nasu an rubuta Princess, bango guda aka cika da sunan Princess with different wall stickers, ragowar wall din kuma Papa's bunny pet pie da dai sauransu, ga teddy bears nan kaca kaca a ɗakin suma duk pink and white, babu abinda bbu na buƙatar baby a room din, ga crib din mai kyau with soft mattress, baby rocker, bassinet, walker duk akwai, majority ma bata isa amfani dasu ba, shelves and drawers ma na ajiye kaya duk a cike suke damm da kaya, sosai Nursery din yayi kyau, sun jima a nan din kafin suka cigaba da zagayen, palourn da suka bar Nanerh suka koma, Hajar ta leƙa fuskarta taga har lokacin bacci take, ta sauke numfashi tace "better". Da daddare wajen ƙarfe tara da rabi Nurain ya shiga room din Hajar, ƙarewa room din kallo yayi yaga bata nan, can ya hangi Nanerh kwance cikin bassinet dinta tana bacci, closet ya shiga ai kam ya tarar da ita tana shirya kayan da ta dawo dasu, bata ma san ya shigo ba cause tayi backing dinsa, ya ƙarasa inda take yayi hugging dinta ta baya, ƴar ƙara tayi don ta firgita, pure scent dinsa ta shaƙa snn tayi murmushi tace "you scared me", ya fige hular kanta ya cusa kansa cikin sumarta gami da shaƙar ƙamshinta, with a husky voice yace "why..?", ƙoƙarin raba kanta da jikinsa tayi amma ya riƙeta, tace "Ai ban san ka shigo ba", shiru ne ya gifta na almost 1mins snn ya rage murya yace "I missed you", ba ta ankara ba taji ya sauke mata wni combo kiss a wuya, ba shiri ta juyo ta fuskancesa tana turo baki, yayi brushing lips dinsu ya zagaye ƙugunta yace "i missed your cooking sweet pie", tayi ɗage ta zagaye wuyansa tace "then should i cook something for you..?", yace "yeah", tayi pecking karan hancinsa tace "i also missed your coffee", yayi dariya mai sauti itama tana tayasa, tace "give and take", yace "Ohk", slowly ta zame jikinta a nasa ta amshi hularta ta saka, yana biye da ita suka fita bedroom, direct ta nufi door, ya tsaya yace "Princess", ta juyo ta kallesa taga ya nufi bassinet din Nanerh, ta tsaya tana kallonsa, yana zuwa gaban bassinet din ya juyo ya kalli Hajar yace "ita ka ɗai zamu bari a nan..", Hajar ta rumgume hannaye tace "yess tinda ba zamu kitchen da ita ba", ya kalli Nanerh yace "idan kuma ta tashi tayi kuka fa", tace "ba zata tashi ba ai bata tashi a wnn time din sai dare ya raba..", yace "Are you sure", ta gyaɗa kai, ya duƙa yayi pecking cheek din babyn kafin ya bar wajen, Hajar dai kawai kallon mamaki take masa, wnn wane irin so yake yiwa ƴar nan ne, downstairs suka sauka, Hajar ta murɗa handle din door din da take tunanin nan ne kitchen ta shiga, shima dai kitchen din anyi renovating dinsa to the extent din da ya canza kamanni, har expanding dinsa akay alamar an shigo da wni filin cikinsa, saida ta gama santin kitchen din snn ta fara tunanin me zata dafa masa sharp sharp wnda ba zai ɗauki time ba, ta kallese tace "Ohh Allah yasa akwai perishable Stuffs", yace "Ermmm i think there is", tace "Ohk", ta buɗe fridge ai kam taga kayan miya fresh ones kamar ma yau aka siyosu, freezer ta buɗe itama taga nama da chicken da fresh fish, yace "i refilled them today…", tace "Okay", ta durƙusa ta dauko pot ta matsa gaban sink ta fara wankewa, yace "Baby wife me zaki dafa ne..?", ta dakata da abinda take ta juyo ta kallesa tace "spaghetti and sauce", ya ɗage gira, tace "irin wnn fa wcca Aljanu suka cinyemin ka taimaka ka bani milk", ya waro ido yace "You", ta kyalkyale da dariya tace "ka tuna", ya matsa kusa da ita yana murmushi yace "ya bxn tuna ba bayan nine babban Aljanin", a tare suka kwashe da dariya ita kam harda riƙe ciki, ya tsaya yana kallonta tana cigaba da dariyar ita kaɗai, idan da akwai abinda yake bata dariya a dramas dinsu ta baya toh bai wuce case din Aljanu ba, ƙiri ƙiri ya cinye mata abinci sai yaxo yace wai Aljanu ne, saida ta gama dariya snn ta cigaba da abinda take, ta ɗora ruwa taliyar a gas, fridge ta buɗe ta ɗebi Attaruhu da tomatoes, yace "Ohh just come with me", ta ajiye robar da ta zuba vegetables din tabi bayansa suka fita palour, ƙofar fita taga ya nufa, bai buɗe ƙofar ba ya tsaya ta ƙaraso, this time around ma rufe mata ido yayi, tace "Another surprise dear..?", yace "sure", saida numfashin Hajar ya ɗauke na wucin gadi bayan tayi tozali da abinda ta gani a gabanta da ya buɗe mata ido, A car, tsaleliyar mota dunƙulallariya fara tass, ta rufe bakinta da both hands dinta, ta juya ta faɗa ƙirjinsa hawayen farin ciki suka ringa sauko mata, rumgumeta yayi sosai yace "As promised, the gift for giving birth to a Princess and for you being my beloved wife", lokacin da suka koma kitchen kam ruwan taliya ya kusa ƙonewa saida ta ƙara wni. New page New Chapter na sabuwar rayuwa Hajar da Nurain suka buɗe, ga Princess dinsu a gefe wcca ta ƙarawa sabuwar rayuwar tasu armashi, yau sati biyu knn da dawowarsu, a cikin sati biyun nan Nurain ya fara koyawa Hajar driving, a compound yake koya mata snn kuma da tasa motar suke amfani, ai kam tini Hajar ta kwashe don she is a fast learner, sabuwar motarta kam kullum sai ta shiga ta bata wuta snn take jin daɗi. Ranar Monday Nurain ya fita aiki, wajen ƙarfe sha ɗaya Hajar ta sauko downstairs da Nanerh a shoulder dinta, baby rocker dinta ta kunna mata ta sakata a ciki don idonta biyu, kitchen Hajar ta wuce ta fara yin snacks za ta ajiye a fridge tinda na fridge din sun ƙare, a buɗe ta bar kitchen din sbd Nanerh dake palour ita kaɗai, lfyr Allah Hajar ta fara aikinta, Nanerh na cikin rocker dinta wcca take bouncing da ita lightly, sai bin toys din jikin rocker din take da kallo kuma hakan ne yasa ba tayi rigima ba, ƙarar bell Hajar taji, tayi still don ba tayi expecting visitor ba, wanke hannunta da ya ɓaci da flour tayi snn ta fita ta buɗe ƙofa, Oum Sulthan ta gani, tini Hajar ta bata hanya tayi welcoming dinta in, Hajar ta miƙawa Sulthana hannu, yarinyar ta maƙe shoulder don ƙiwa take, Hajar tayi dariya tace "Toh shknn bazan baki sweet dina ba..", nan ma dai Sulthana ta maƙe shoulder, Oum Sulthan ta ɗauki Nanerh dake cikin rocker dinta, Hajar tace "Ina shirin shigowa sai kuma kika rigani", Oum Sulthan na kallon Nanerh tace "ba komai ai", Hajar tace "An dawo lfy, ya ku ka baro mutanen Maiduguri", Oum Sulthan tace "Lfy lou muka barosu", Hajar tace "Alhmdllh, Falmata bata biyoki ba..?", Oum Sulthan tace "Ai makaranta", Hajar tace "hka ne kuma", Hajar ta tashi ta shiga kitchen ta kawowa Oum Sulthan snack da lemo, Oum Sulthan tace "ynxu watan Nanerh nawa..?", Hajar tace "biyu zata shiga na uku", Oum Sulthan tace "Masha Allah wllh kamar ƴar wata biyar", Hajar tayi murmushi, Oum Sulthan tace "kuma kince bata shan madara ko..?", Hajar ta gyaɗa kai tace "Eh", sai sha biyu da rabi Oum Sulthan ta tafi, fira sukay sosai da Hajar. Da yammacin ranar Hajar ta kira Umma suka gaisa don yau bata samu ta kirata da safe ba, suna gama waya da Umma ta kira Nabilah, bayan sun gaisa Hajar tace "ya mganar tafiyar naku..?", Nabilah tace "saura kwana biyu mu tafi", Hajar tace "Okay... Allah ya kaimu, wai ƴar uwa kinada bank kuwa..?", Nabilah tace "Opay ne dani", Hajar tace "Aha, sai anjima", Nabilah tace "mu jima da yawa ngd da kulawa", Hajar tace "ba komai" da haka ta katse kiran, transfer na kuɗi masu ɗan tsoka Hajar ta yiwa Nabilah, ta tura mata text tace ta siyi wni abun ba yawa, after 20mins sai ga Nabilah na kira don taga kuɗin, Nabilah tace kuɗi sunyi yawa Hajar tace ba komai wllh ta riƙe, sosai Nabilah ta ringa surfawa Hajar godiya kamar za tayi kuka, Hajar tace ai yiwa kai ne. Da daddare Hajar ta shiga ɓangaren Nurain da jug din fresh coconut juice, da sallama ta ƙarasa shiga ciki, Nurain na zaune kan carpet da Nanerh gefensa wacca take kwance kan floor mattress dinta yana mata wasa, Hajar ta ajiye jug din kusa da kayan abincin da ta jere a carpet, yace "Baby wife zo ki gani ynxu fa Princess ta gama yimin dariya", Hajar tace "A'a saidai ta ƙuda ai bata isa fara dariya ba", yace "No ynxu fa tayi dariyan", tace "Eh ta ƙuda ba" da haka ta ɗauki cup ta tsiyaya coconut juice din ta miƙa masa, ya ɗago daga wasan da ya cigaba da yiwa Nanerh ya amshi juice din, lafiyayyar sakwara da green veggies soup with fresh offals da smocked fish ta zuba masa, habawa ai yana ganin abincin ya gyara zama, ta ɗan kallesa da wutsiyar ido cause yau favourite dinsa ta dafa, spoon ta miƙa masa ya amsa, ya gutsiri sakwarar ya dangwali miyar ya kai baki, ta riƙe hannunsa tace "Bismillah fa", yace "Ohh Bismillah", ta sakar masa hannu ya fara cin abincin, as usual yau ma santin ya ringa zuba mata, ita dai saidai tace uhmm tana cika masa cup da juice daga zarar ya shanye, bayan ya gama cin abincin ta kwashe kwanukan ta fita dasu, da ta dawo ba ta tarar dashi a palour ba ya shiga ciki, ta ɗauki Nanerh ta wuce da ita ɗakinta ta mata wanka ta saka mata overall dinta, breastfeeding dinta tayi har saida tayi bacci snn ta kwantar da ita a bassinet dinta itama ta shiga wankan, tana fitowa daga wankan ta shiga closet, rubbing lotion tayi kafin ta mulke jikinta da night secret, night secret wata breath taking humra ce mai shegen ƙamshi wcca ta siya wajen Oum Sulthan, hair spray ta fesawa gashinta, da haka ta ɗauki silk nightgown ta saka, ta fito bedroom da shirin kwanciya, dakatawa tayi ganin fitulu a kashe sai iya na bedside ne a kunne, kan gado ta kalla ta gansa zaune ya jingina da allon gadon yana latsa waya, yace "kawomin envelope din da na baki ajiya", tace "Toh" ta juya ta koma Closet, ta ɗakko envelope din da ta ajiye ƙarƙashin kayanta ta fito, ta kai masa ya amsa ya fara buɗewa, zagawa tayi ɗaya side din gadon ta janyo bassinet din Nanerh daf da ita, Addu'a da ta saba yi mata duk dare kafin su kwanta ta mata, bayan ta gama mata addu'ar ta janyo cap din bassinet din ta rufeta, juyawa tayi ta kalli Nurain da yake duba abinda ke cikin envelope din da ta kawo masa, ya ɗaga passport dinta da ya fito 1week earlier, ita dai kawai kallonsa take sai kuma ta ja duvet ta kwanta, ganin ta kwanta yace "Mama bear bacci...?", ta gyaɗa kai tace "Uhmm", ya ja hancinta yace "yau fa ba bacci", ta mirgina da shirin juya masa baya, ya fixgota ta faɗa jikinsa, ya mata raɗa a kunne, tayi lamo tana sauraronsa, lokaci guda ta ɗago tace "really..?", yace "Sure", ta fara shafa thick eyebrows dinsa tace "when..?", yace "ba zai kai nan da 1week ba, i can't leave you and my princess behind, let's go together", ta ɗora forehead dinta saman nasa tace "Together..", ya gyaɗa kai yace "yhap"....….✍️
💛 HAJAR 💛

{94..}
Within 4days Nurain ya gama processing komai na tafiyar tasu, Viser dinsu ma ta fito, har flight ticket ya saya tare da lap baby ticket na Nanerh don nan da 2days ne tafiyar, ya rage kwana ɗaya da zasu wuce Abuja ne ya kaita ta yiwa Umma sallama, har wajen Mami suka je, Mami sai tmbyar Nurain take shin ba a sanyi a inda za sun don idan ana sanyi bbu inda zasu da takwararta saidai su tafi su kaɗai, Nurain yace bbu sanyi ai ynxu summer ce a can, sai a lokacin Mami ta dena surfa masa tmbya. Washe gari da sassafe suka wuce Abuja, Nurain bai kama musu hotel ba gidan Hammad suka wuce cause ƙarfe 12 ne zasu koma airport, Maysha ta tafi da Hajar side dinta bayan ta rumgume Nanerh, breakfast mai rai da lfy Maysha ta jerewa Hajar, Hajar dai tabi kayan abincin da kallo don a ƙoshe take, kafin su baro gida saida ta musu abinci, ganin Hajar ba ta taɓa abincin ba Maysha ta kwantar da Nanerh da take ta riƙo ta fara zuba mata abincin, Hajar tace "Laa Please dama baki zuba ba wllh am full", Maysha tace "please ko kaɗan ne ki ci", Hajar ta ɗauki fork tayi loma biyu ta ajiye ta sha ruwa, Maysha sai ririta Nanerh take tana mata wasa, ji take kamar a bar mata ita, tana azabar son babies. Nurain kam yana tare da Hammad acan sashensa, wani yaro da bazai wuce 8yrs bane ya shigo palourn, yaron fari ne sosai kamar an bursuna masa hoda, gashin kansa baƙi siɗik kuma coily, kana ganinsa dai ka san ba ƴaƴan hausawa bane amma dai yafi kama da ruwa biyu wato halfcast, wajen Hammad ya taho yana murza idonsa, Hammad ya zaunar da shi gefensa yace "Ashraaf", yaron ya ɗaga idanunsa da ƙwayarsu take light ash wacca ta sake bambamcesa da ƴan Nigeria ya kalli Hammad yace "Mommy... Uncle where is my Mommy..?", Hammad ya shafa kan yaron yace "Boy your Mommy will be here soon insha Allah, don't worry uhmm", yaron ya gyaɗa kai, Hammad yace "have you eaten..?", Ashraaf yace "Am not hungry", Hammad yace "No my boy you must eat something if you want your Mommy ta come back", Ashraaf yace "Okay, will i see my Mommy if i eat..?", Hammad yace "Insha Allah..", shi dai Nurain na zaune palourn yana kallonsu, Hammad ya nuna Nurain sai kuma ya kalli Ashraaf yace "show your respect my boy..", Ashraaf yayi taku uku towards Nurain kafin ya tsaya ɗan nesa dashi yace "Good morning", Nurain yace "Good boy... what's your name...?", Ashraaf yace "Ashraaf", Nurain yace "let shake hands boy", walking slowly yaron ya isa gaban Nurain snn ya zura hannunsa cikin na Nurain da already ya miƙa masa, a hankali Nurain yayi shaking hands din nasu, Hammad yace "go to your Aunt", Ashraaf yace "yess" da haka ya nufi door ya fita, Hammad ya bisa da kallo hakama Nurain, Nurain yace "i like the boy, yaron waye..?", Hammad ya sauke ajiyar zuciya yace "he is my son, ɗan ƙanwata Azeeza ne", Nurain ya gyaɗa kai don yasan siblings din Hammad din by name tinda bai taɓa ganinsu ba, Umminsu kawai ya taɓa gani, Hammad ya sauke numfashi yace "something terrible happened, an nemi Azeeza an rasa..", Nurain ya tattare girarsa ya gyara zama yace "An nemeta an rasa... ɓata tayi..?", Hammad yace "sure ɓata tayi tinda duk inda ake tunanin zata je an duba ba'a sameta ba, Yemen Uk zanzibar duk anje nemanta ba a samu ba, her husband General Talba bbu inda bai sa an bincika ba a faɗin Nigeria amma no any trace of her, 3 months knn ana abu ɗaya", Nurain yace "ya subhanallah amma Hammad me yasa baka gayamin ba even a little i can help", Hammad yace "i wasn't my self all through Dr", Nurain yace "Innalillah, Ashraaf shi ka ɗai ne yaronta..?", Hammad ya gyaɗa kai yace "Yeah shi ka ɗai ne, and he is the only male child of General Talba shiyasa ya ɗauki son duniya ya ɗora akan Ashraaf, nima da kyar ya bani yaron na taho dashi sbd yaron ya ringa kuka sai ya biyoni, Ummi ma taso ta amsosa amma uban ya hana wai da mai zai ji da rashin Azeeza ko kuma dauke masa yaro da ake shirin yi, kawai dai wni irin bauɗaɗɗen mutum ne he is rude and arrogant amma kuma yana son Azeeza, son da yake mata ne ma yasa har yau bai haƙura da nemanta ba", Nurain yace "Allah Ubangiji ya bayyanata", Hammad yace "Ameen ya rabbi". Maysha ta ɗaga kanta daga wasan da take yiwa Nanerh ta kalli door jin anata faman murɗa handle, tashi tayi ta buɗe ƙofar, ta kalli Ashraaf dake tsaye bakin ƙofar tace "boy..", ganin Nanerh a hannunta sai ya fara ɗage yana son ya hango fuskarta, Maysha tayi murmushi ta riƙo hannunsa ta shigo dashi ciki snn ta rufe ƙofar, ya nuna Nanerh da finger yace "Baby", Maysha tayi nodding head tace "uhmm Baby", murmushi Ashraaf yayi, Maysha ta shafa kansa tana jin daɗi har cikin ranta, yau kwanan yaron huɗu a gidan amma bai taɓa murmushi kamar wnn ba, zama tayi kan carpet ta ɗora Nanerh a laps dinta, ai tini Ashraaf ya zauna kusa da ita ya ringa kallon Nanerh, cheeks dinta da suke a cike ne suka ja hankalinsa har ya kai farin hannunsa sol ya shafa cheeks din, Maysha tace "you like the baby Ashraaf..?", ya gyaɗa kai yana cigaba da taɓa Nanerh, Maysha ta ɗaga kai ta kalli Hajar dake kallonsu, Hajar tayi murmushi tace "sai a dage a yiwa boy ƙanwa tinda dai yana so", Maysha tayi ƴar dariya tace "A'a mu wnn za'a bar mna", Hajar tayi dariya tace "Toh shknn na bar muku", kamar abin arziƙi ana zaune qlou da Nanerh ba rigima, lokaci guda ta tsanyare da kuka sai kace wcca aka kunna da remote control, Ashraaf ya ringa murza kanta wai nan lallashinta yake har saida hularta ta cire, ganin taƙi shiru Maysha ta tashi ta miƙawa Hajar ita, Ashraaf kuma ya fita da gudu Maysha na tmbyarsa ina zasa, after like 5mins lokacin Nanerh tayi shiru tana hannun Hajar tana feeding dinta Ashraaf ya dawo ɗakin da horse toy a hannunsa, slowly ya nufi Hajar snn ya zauna kusa da ita, Hajar ta ringa kallonsa, ya kamo hannun Nanerh ya saka mata toy din, ai kam toy din ya faɗi ƙasa don Nanerh ba tayi wayon riƙe abu ba, ya sake ɗauka sai kuma ya ɗora a cikinta ya juya ya kalli Maysha yace "Aunt i gave her my toy she will not cry again right...?", Maysha tace "Sure... come here", ya tashi ya tafi wajenta, ta riƙe hannunsa sai kuma ta kalli Hajar tace "ina zuwa please, zan basa abinci ne", Hajar tace "Toh", Maysha na riƙe da hannun Ashraaf wnda yake waiwayen Nanerh dake hannun Hajar suka fita. Before 12noon su Nurain suka isa Airport bayan sun baro gidan Hammad, bayan sun gama bin duk wata procedure suka shiga jirgi, seats din kusa da window suka zauna don dman business class ne, Nurain yasa flight attendant ta kawo musu bassinet sbd Nanerh, ana fara announcement jirgi zai tashi Nurain ya amshi Nanerh, Hajar tayi fastening seat belt dinta gami da runtse ido tana karanto duk addu'ar da tazo mata baki, har yau tana jin tsoron tashi da saukar jirgi, bayan jirgi ya keta hazo ya gama leveling a sararin samaniya Nurain ya kwantar da Nanerh a bassinet din da aka basu, Hajar ta cire seat belt dinta ta gyara zamanta sosai, bbu jimawa bacci ya ɗauketa don dman shi take ji, throughout yester night ba tayi wni baccin kirki ba sbd zumuɗi, a shoulder din Nurain ta kwantar da kanta, shi kam headphone ya saka a kunnensa ya kunna karatun Alkur'ani ya lumshe ido, saida aka fara raba abinci snn Hajar ta farka, ta kalli Nurain dake side dinta, ya cire headphone din yace "kin tashi", ta gyaɗa kai sai kuma ta kalli bassinet din gabansu, wayam ta gani bbu Nanerh, ta zaro manyan idanunta waje ta zaburo sai kace mai shiri miƙewa tsaye tace "My baby", Nurain yayi tapping dinta sai kuma ya nuna mata mutumin da ke gabansu jar fata, a hannun mutumin ta hango Nanerh, saida ta leƙa fuskarsa taga fari ne sosai, ta rage murya tace "kamar ɗan China", Nurain yace "yhap shine". After the journey of 8hours suka isa Hong Kong, lokacin ƙarfe 4 na dare, suna fitowa daga filin jirgi Nurain ya tsare musu Cab, wayarsa ya kunna ya shiga language translator App, da Language translator App din sukay communicating da drivern Cab din tinda shi dai bai iya Chinese ba su kuma basa jin turanci, hotel mai cab din ya kaisu kamar yacca sukay da Nurain, bayan Nurain yyi amfani da currency dinsu da ya taho dasu a hannu ya biya kuɗin transport din suka shiga hotel din, Suit room sukay lodging, wanka Hajar ta shiga bayan ta fito ta yiwa Nanerh ma, daga nan ta jero sallalolin da suka wuceta snn tayi ta asuba da ta ƙarato ynxu, Nurain ya musu order din abinci room service, nan Hajar ta kasa cin abincin, snacks din kawai ta iya ci ta haɗa da drink, bayan sun gama cin abincin Nurain ya fita, Hajar da Nanerh kuma baccinsu sukay sosai, sai sha biyu da wni abun Hajar ta farka, ganin da sauran lokacin sallah bai ƙarato ba ta wuce bathroom ta wanko fuskarta ta fito, a hankali ta isa gaban the wall to wall glass windows that viewed the skyscrapers of Hong Kong city, ɗan buɗa baki tayi in an excited way tana kallonta perfect view din da bata taɓa gani ba a rayuwarta, sosai ta shagala da kallon city din tana jin daɗi, ba ta ma ji ƙarar buɗe ƙofar da akay ba, Nurain ya tsaya yana kallonta ganin duk sallamar da yake batama ji ba, ya ƙarasa inda take yace "me ake gani..?", ta juya ta ɗan kallesa tace "birni nake gani", yace "you like the view from here", tace "Sure.. daman haka China take", yace "All the same amma nan Hong Kong ne", ta tattare gira tace "Ohh", yace "Nanerh ba ta tashi ba..?", tace "Eh", Lunch ma a nan cikin hotel din ya musu order, sai da daddare yasa ta shirya zasu fita yin dinner snn suga gari, tini Hajar ta shirya snn ta shirya Nanerh cikin baby jeans carpenter masu kyau, Hutong restaurant suka je one of the top traditional restaurant in Hong Kong, traditional food and modern one akay seving dinsu, Nurain yasa aka kawo musu seafood, spicy lamb ribs Hajar ta fara taɓawa, bon appetit the food is so yummy saidai seasoning din basu ratsa taste dinta ba, ai kam ta ciro guzirin maggi da tayi ta ringa barbaɗawa tana cin abincin, bayan sun gama yin dinner a Hutong restaurant ba hotel suka koma ba, babban Disneyland of Hong Kong ya kaita, daman wajen yafi daɗin zuwa da daddare, ita Hajar yadda taga mutane garin sunfi hulɗa da daddare ne yafi bata mamaki, sai kace wasu ƙannen aljanu, sosai Hajar taji daɗin Disneyland din, ta zaga ko ina tana shan cotton candy da Nurain ya saya musu, sai 12 na dare da wni abun suka koma hotel. Washe gari kuma da wuri suka fita ya kaita Victoria peak da kuma Ocean park, a Ocean park ne suka hau speed boat suka zaga farkon ruwan wajen, A washe gari kuma bbu inda suka je hutawa akay sai next day suka je Wong Tai Sin, shi kuma wajen kawai natural abubuwa ne suke tsawa and it is a top tourist spot, a ranar nan din kawai suka je sbd wajen nada girma da ɓangarori daban daban, Lantau Island ne ƙarshen wajen da suka je a Hong Kong, daga nan kuma ya kaita malls yace su sayi kayan tsaraba.........✍️
💛 HAJAR 💛

{95..}
Satinsu ɗaya a Hong Kong suka wuce China, A Beijing suka sauka kuma anan ne Nurain ya gabatar da ɗayan shirin nasa na zuwa China, kullum sai ya fita sun haɗu da Mr Lee, idan ya dawo da daddare ko yamma su fita da Hajar, A cikin sati biyu ya gama abinda zai yi, a washe garin da ya gama aikin suka shirya zuwa Shanghai City, Shanghai shima babban birni ne a ƙasar China snn akwai wajajen buɗa ido a garin, by train suka tafi Shanghai din tinda miƙaƙƙiyar tafiya ce daga Beijing, Woah a Shanghai city ma sun zaga ba ƙarya, Hajar ta buɗa ido iya buɗawa, duk wni guri da baƙi suke zuwa saida suka je, Yu Garden suka fara zuwa, anan Hajar taga ƴaƴan itatuwan da bata taɓa gani ba, fruits da vegetables ba a cewa komai, har watermelon mai purple flesh ta gani, da tayi tasting taji zaƙi zau kamar zuma, next inda suka je shine The Bund, shi kuma historical place ne, shima dai wajen ya burge Hajar sosai, da suka bar Bund suka je Museum da daddare, Shanghai Ocean Aquarium ne a ƙarshe a inda suka ziyarta a Shanghai city, kamar Hong Kong a nan din ma one weeks sukai, daga Shanghai next inda suka je shine Guilin, waoh nan din ya share komai da Hajar ta gani cause duk yafi birgeta, Guilin is so natural with breath taking scenery, hotel din da suka sauka ma a garin Guilin na traditional ne, seven places suka ziyarta a Guilin, reed flute cave, Elephant trunk hill, Lijiang, Fubo mountain, Yulong river, Chuanshan park and the last one Li river. Beijing suka koma suka fara shirin komawa Nigeria, ya rage saura kwana biyu su tafi ya kaita taga The great wall of china wnda yake nan garin Beijing, watansu ɗaya da sati biyu knn da baro Nigeria, ranar da zasu tafi Hajar ta shirya snn ta shirya ƴarta Nanerh wcca ta ƙara wayo don ynxu ta cike 3months old har da ɗoriya, Hajar na shiryata tana ɓangala mata dariya don ynxu yarinyar ta koma sarkin dariya, ƙarfe tara na dare suka isa Airport, bayan sun bi duk wata procedure suka shiga jirgi, kamar a zuwa wnn karon ma Hajar bacci tayi, da sassafe suka iso Nigeria Abuja, a take Nurain ya yankar musu flight ticket na zuwa kano, ai kam suka biyo jirgin da zai taho kano, bayan sun fito daga filin jirgi Nurain na riƙe da Nanerh wacca take ɓangalawa duk wnda ta gani dariya, ai kam mutane da yawa sai kaga suna murmushi wasu kam basa iya jurewa sai sun mata wasa. Tinda suka fito ta zuba musu na mujiya, lokaci guda ta miƙe daga kan kujerar da take jira bayan ta tabbatar da fuskar Nurain, har yaxo ya wuceta bai lura da ita ba, Hajar na gefensa sun jera suna tafiyar tare da farin ciki madawwami a fuskokinsu, Ruqayyah ta kasa jurewa ta juya tace "Dr..", at first Nurain bai tsaya ba saida ya sake jin an kira inkiyar tasa a karo na biyu snn ya juyo, Ruqayyah ta ƙaraso inda suke da murmushi kwance fuskarta tace "inata mgana baka ji ba Dr" ta faɗi hakan ne tana kallon Nanerh dake hannunsa wcca ta hau ɓangala mata dariya, Nurain yace "Ohh A Nurse", Hajar ta kalli Ruqayyah da wni irin expression, sosai Ruqayyah ta fahimci cewa wnn yarinyar ta hannun Nurain ƴarsa ce sbd kamarsu da ta ɓaci, Nurain yace "how are you doing A Nurse..?", Ruqayyah tace "great Alhmdllh... long time no see", Nurain ya kalli Hajar snn ya dubi Ruqayyah yace "Meet my beloved wife..", Ruqayyah tayi murmushi tana kallon Hajar tace "sannunki", Hajar da a lokaci guda taji bata son Ruqayyah tace "yawwa sannu", Ruqayyah ta amshi Nanerh tace "your daughter is so cute Dr", Nurain yace "thank you", Hajar ta juyar da kanta tana kallon wni position din, da gefen ido Nurain ya kalleta, Ruqayyah tace "naxo tarbar mai gidana ne", Nurain yace "ohh that's good" da haka ya amshi Nanerh yace "Toh na gaisheki A Nurse byee", da haka sukay sallama a mutunce, Ruqayyah ta koma ta zauna ta cigaba da jiran mai gidan nata Dr Sa'eed, bbu laifi sosai take jin daɗi zama da mijinta don kamar yacca na faɗa a baya ba shida matsala. Kwanan su Hajar 6 da dawowa aka shiga bidirin bikin Hafsah da Ahmad, Samm Nurain ya hana Hajar ta ringa kwana don shi lamarin biki ba burgesa yake ba, hka kurum wasu mazan su kalle masa mata, ai kam hka kullum Hajar take sintirin zuwa gidan biki saidai hakan bai dameta ba don da motarta take tafiya, though har ynxu hannunta bai faɗa ba amma kuma ta iya ba laifi, ansha biki iya biki don an zuba bajinta from both side, outside event biyu akay bayan na gida, ranar Juma'a akay ɗaurin aure, da yammacin ranar dangin ango suka xo tafiya da abarsu, har da Mami cikin wadanda suka zo ɗaukar Amarya don Maman ango close friend dinta ce, su Mami suka ɗauki Hafsah da aka shiryata cikin shigar amare na lafaya, Hajar tabi ƴan kai Amarya ta bar Nanerh a wajen Umma. Gidan Amarya Hafsah saidai muce masha Allah don kwa ya haɗu iya haɗuwa gashi danƙarere, Hajar ta shiga makeken bedroom din da aka ajiye Hafsah bayan rurumar ƴan kawo Amarya sun ragu, friends din Hafsah ne kawai a room din, Hajar ta durƙusa gaban Hafsah ta leƙa fuskarta dake a rufe, Hajar ta kyalkyale da dariya tace "Yau ga Hafsah a gidan Ahmad", Hafsah ta janyo Hajar ta rage murya tace "Na shiga uku na, wllh Allah ni tsoronsa nake ji..", Hajar ta waro ido tace "Mijin naki kike jin tsoro", Hafsah ta gyaɗa kai tace "wllh tsoro yake bani, ni dae gidanmu zan tafi", Hajar tayi dariya tace "A haba dai yarinya tin ynxu za wani kice kina jin tsoronsa, toh ki riƙe tsoronki zuwa nan gaba sai kiyi mai hujja..", Hafsah tayi ƙwal ƙwal da ido lokaci guda hawaye suka taru cikinsu tace "Na shiga uku", Hajar tace "wai ke meye haka", Hafsah ta yarfe hannu tace "ba zaki gane ba Allah kuwa..", Hajar tace "Ni kwa na gane tinda ni nan jiyau ce" ta ƙarashe tana dariya ƙasa ƙasa sai kuma ta zauna gefen gadon, hand bag dinta ta buɗe ta ciro wata leda ta amshi jakar hannun Hafsah ta saka ledar a ciki, Hafsah ta bita da kallo tace "meye wnn..?", Hajar tace "turaren sitz bath ne da musk soap", Hajar ba ta so kaiwa lokacin da Angwaye zasu zo ba amma Hafsah ta riƙeta, ai kam Angwayen na zuwa aka fita da Hafsah palour, sosai Hajar ta sha mamakin jin yadda hannun Hafsah dake cikin nata yana karkarwa, toh wai me yake damun Hafsah, ita bata ma kaita ba aka mata auren, Hajar na shirin zaunar da Hafsah kan kujera bayan sun iso palour Ahmad dake zaune palourn da friends dinsa su biyar ya taso, ba wani wala wala ko wata aba kunya ya taso ya rumgume Hafsah, wni irin zaro ido Hafsah tayi bayan ta shaƙi scent dinsa da ya tabbatar mata shine tinda fuskarta a rufe take, afujajan ta fara turasa, yayi murmushi mai sauti a saitin kunnenta yacca bbu wnda zai ji yace "Halal hug.. welcome home Baby", jikinta yayi lagwas ta dena tura san, Abokan ango suka hau ihu yayinda friends din Amarya suka hau shewa, Hajar kam kamar lips dinta zasu yage sbd murmushi, Finally dai ga Hafsah a gidan Ahmad as his lawful wedded wife. Washe gari da yamma Umma na zaune tare da Anty a palour, Anty ta ringa kallon Umma with a weird facial expression, Umma tayi kicin kicin da fuska tace "A gsky ni barin unguwar ma zanyi, tinda don masifa da bala'i da bita da ƙulli har inda nake ya nemo, wnn wni irin masifa ne da dogon wuya, maza yan bala'i ne ko uban wa yake tantance musu tsakanin mai aure da bazawara", Anty ta kwantar da murya tace "Toh ai mu hka muke so Addah, wnn ai rufin asiri ne babba, Kawu na Yola kawai zansa Iya ta yiwa mgana", Umma ta saki baki ta karkaɗa ƙafa tace "goɗai goɗai dani kike min mganar nan Jamilah, uhmm ai ni kam na gama aure har abada ma kuwa, nayi aure har na samu ribar cikinsa, Allah ya bani ƴaƴa har uku na gari wnda zasu kula dani, na rabu da mijina lfy snn na masa takaba cikin aminci, toh bayan wnn me nake nema a wni aure kuma, ai kawai a cigaba da gurgura rayuwa haka Allah ya bamu sa'a mu koma garesa da imaninmu", Anty ta buɗe baki da nufin convincing Umma, tini Umma ta shata mata layi tace bata son mgnar, hakan yasa Anty tayi gumm da bakinta ba ta sake cewa komai ba. Rayuwa ta cigaba da garawa Hajar cikin kwanciyar hankali da jin daɗi, daga kitchen Hajar ta fito da ƙaramin bowl mai ɗauke da plane Noodles with boiled egg, wajen Nanerh dake wasa cikin keken yaranta ta nufa, Nanerh na ganin Mamanta ta fara miƙa mata hannu tana so ta ɗauketa, Hajar ta ajiye bowl din noodles din kan hannun kujera snn ta durƙusa ta cicciɓo ƙatuwar ƴarta ta, ta zauna kan kujera ta ɗauki bowl din noodles ta fara bawa Nanerh, tini Nanerh ta hau zuƙulƙular noodles, 5months take da shi amma sosai ta kama abinci, bbu abinda bata ci bayan abincinta na gwangwani, daya daga cikin ma'aikatan gidan ce ta fito daga kitchen, ta zuba guiwoyinta gaban Hajar tace "Anty na gama aikin", Hajar tace "Ohk sannu, ina Binta..?", mai aikin tace "tana can ɗakinmu", Hajar tace "Ohk ayi noon duty", mai aikin tace "Toh" da haka ta tashi ta fita ta ƙofar kitchen zuwa backyard din gidan ta wuce boys quarters inda nan ne ɗakinsu, bbu jimawa mai aikin ta dawo tare da ƴar uwarta suka hau aikinsu, within few minutes suka gama gyara ko ina na downstairs din wnda daman a gyare yake, Hajar na zaune tana feeding Nanerh har suka gama, iya kacin aikinsu downstairs don ko hanyar upstairs bbu wnda ya taɓa bi, ita take gyara part dinta dana mijinta, Hajar na gama feeding Nanerh ta haura upstairs da ita, room dinta ta shiga da ita ta mata wanka ta sauya mata kaya, kafin ma ta gama shiryata har ta fara gyangyaɗi hakan yasa ta kwantar da ita ta cigaba da baccin, Hajar ta wuce part dinta tayi wankan itama, turare ta baza as usual ta saka wasu kaya na neman fitina, bom short ne wnda ko rabin cinya baixo ba ta haɗa crop wcca ta bayyana cibiyarta, As usual ta tarbi mijinta, tana riƙe da briefcase dinsa suka haura sama, yace "where is my Princess..?", tace "tayi bacci", saida ya shiga room din Nanerh ya dubata yayi pecking cheeks dinta snn ya wuce part dinsa, a kullum upgrading son da yake yima ƴarsa yake, after yayi refreshing kansa yayi wnka Hajar ta kawo masa abinci, ya zabga uban tagumi yana bin duk wasu moves dinsa, gaba ɗaya yaji ya tsani abincin kawai kallonta yake, walking like a cat ta iso inda yake ta zauna kan cinyarsa ta zagaye wuyansa tace "Cappuccino me zan zuba mka..?", ya haɗe thick eyebrows dinsa yace "No ni ba abinci nake so ba", ta waro ido tana wasa da sajensa tace "Toh me kake so...?", ya zagaye ƙugunta yayi kissing karan hancinta yace "i need you", ta noƙe fuskarta tana murmushi sai kuma ta maƙe shoulder, lokaci guda ta ɗagasa, wayarsa ce tayi ring, ya ɗauka ya kalli sceen din, tini yayi picking don Sakeena ce ke kiranta, ko 2 mins ba suyi suna wayar ba, ya ajiye wayar ya kalli Hajar yace "Noor ce ta haihu", Hajar tace "Masha Allah...", yace "bari naci abinci sai mu tafi ba", ta gyaɗa kai tace "Tom"…..……✍️
💛 HAJAR 💛

{96..}
Hajar na gama zuba masa abincin ta tafi room dinta, closet ta shiga ta sauya kaya, saida ta gama saka kayan snn ta sauka downstairs zuwa kitchen, catfish pepper soup din da tayi ɗaxu ta saka a microwave tayi warming dinsa, with few mins ta jera abincin da zasu kai asibiti a basket, sama ta haura ta shiga room din Nanerh, baccinta take lakadan cikin crib dinta, Baby Carrier Hajar ta ɗaura kafin ta ɗauki Nanerh ta haɗata da chest dinta snn ta ɗaure belts din, ɓangarensa suka wuce, already ma ya gama cin abincin ita yake jira don haka suka fito, bayan sun sauka downstairs Hajar tace "Moon zamu kai musu abinci yana kan Island", yace "Sure.." da haka ya shiga kitchen ya dauko basket din abincin, parking space Nurain ya wuce Hajar kuma ta zaga backyard zuwa boys quarters, masu aikinta su Binta ta gayawa cewa ta fita, Allah ya tsare sukay mata, tace Ameen da haka ta bar wajen, Other car din Nurain suka shiga ba wcca ya dawo da ita ba, ko nisa ba suyi ba suna tafiyar Nanerh ta tashi, ɗago kanta tayi tana kallon Hajar sai kuma ta ɓangala dariya har saida rabbit tooth da both dimples dinta suka fito, Hajar ta fara mata wasa ita kuma ta ringa kyalkyala dariya har da ƙoƙarin shiɗewa, Nurain ya kallesu ya shafa kan Nanerh yace "Princess", shima ta basa nasa kason na dariya sai kuma ta fara miƙa masa hannu wai ya ɗauketa, da taga yaƙi ɗaukarta sai ta fara mimmiƙewa za tayi kuka, Hajar ta ɓalle belt din Carrier ta juyar da Nanerh ta kalli window, hakan yasa ta haƙura da zuwa wajen Abban nata da yake driving ta ringa kallon motoci, Nurain yace "Wifey mene burinki a karatu?", da sauri Hajar ta kallesa don bata taɓa tunanin zai mata mganar cigaba da karatu a yacca yke da mugun kishin nan ba, ya kalleta yace "Uhmmm kinyi shiru baby wife", Nanerh ta fara gantsarewa ta ringa ƙoƙarin juyowa don taji muryan Abbanta, Hajar ta hanata juyowar ai kam ta saka kuka, saida Nurain ya dauketa snn suka samu salama, ɗaukarta da yayi bai hanasa cigaba da tuƙi ba tunda bata takura masa ba, tinda ya ɗauketa daru ya ƙare, sai a snn ya samu chance din cigaba da tmbyar Hajar akan karatunta, tace "dana gama secondary school Nursing school ita nake da burin zuwa, sai dai kuma ban samu na shiga ba..", yace "Nurse kike son zama baby wife...?", ta gyaɗa kai tace "shine babban burina a karatu", yace "Okay... kin taɓa applying ne...?", ta gyaɗa kai, yace "Ohk i see, in dai school of Nursing ta kano state ce nasan ba tada kyau, siyasa kawai suka saka a gaba, basa bada Admission sai kanada hanya idan yarinyar ka ma ta shiga schl din akwai wni exams da suke yi su zubar da yara, ita exams din ba qualifications din yaro suke dubawa ba cause siyanta ake da kuɗi ko kuma hanyar ƴan siyasa..", Hajar ta zuba masa manyan idanunta, yace "I heard that from integrate person wnda ko ban gani ba amma na yarda, So you will not go to that bushy school a bar musu kwalinsu, i will find the best Nursing school for you insha Allah", wni sanyi ne ya ratsa zuciyar Hajar, wai itace zata koma schl abinda bata taɓa kawowa ba, Nurain ya kira Sakeena ta sake tuna masa sunan hospital da Address, gab da magrib suka isa hospital din, bayan Nurain yayi parking ya kalli Nanerh yace "weldon Princess kinga kin sa mun daɗe a kwalta", dariya ta ɓangala masa, ya kashe motar snn ya zare key daga ignition, da zafin nama Nanerh ta kaiwa key din cafka, gamm ta riƙe key din da ƙarfinta taƙi saki, ya bar mata a hannunta ya buɗe motar ya sauka, Hajar ta fito ta ciro basket daga booth suka shiga cikin asibitin, Mami da Sakeena sai Aunties din Abdul mijin Noor biyu suka tarar, Hajar ta ajiye basket din hannunta ta gaida kowa da ladabi, Nurain ya miƙawa Mami Nanerh ya amshi cute baby boy din Noor dake hannun Sakeena, after 3mins ya mayarwa da Sakeena babyn yace zai fita sallah ne tinda magrib yayi, Mami tace "Wnn ba key din motarka bane hannun takwarata..?", yace "Eh shine", Mami tace "Ohk toh amshi abinka kar ta cilla wni gurin da za ayi ta nema", yace "Toh" ya ƙaraso zai amshi key din, ai kam tini Nanerh ta gantsare zata saka kuka, sakar mata yayi ta cigaba da wasanta yace "Ai kuka za tayi ne fa", Mami tace "Au kuka za tayi, shknn idan ta wurgar ai ka yanko wni", ya juya ya fita yana shafa kansa, wato ya yarda ya yanko wni ɗin da Princess dinsa tayi kuka, Hajar dai ta amshi baby ta koma gefen gadon da Noor ke kwance tana bacci ta zauna, tinda ta haihu take bacci don long labor tayi, almost 48hrs tana labor, sai bayan sallar isha'i snn Noor ta farka, Mami tasa Hajar ta haɗa mata shayi mai kauri, Hajar ta miƙawa Noor mug din shayin tace "Sannu", Noor ta numfasa ta amshi mug din, Hajar ta zauna gefenta tace "ynxu kin gane gidan glass din da nake gaya miki..?", Noor ta sauke wni ajiyar zuciya tace "gidan glass ɗaya ma knn, ke nifa nan da kika ganni na buga final insha Allah", Hajar ta guntse dariyar da ta taho mata tace "A haba dai nan da 1yr ki silliɓo wta please", Noor tace "tsakani ga Allah tawa ba irin taku bace Hajar, na samu tear fa sosai", Hajar tace "Ayya sorry, ai kwalliya ta biya kuɗin sabulu your baby is so cute..", Noor tayi murmushi, Sakeena ta kallesu tace "wai ƙus ƙus din me kuke ku ka wni haɗa kai..?", Noor tace "ba komai", Sakeena tace "Toh maza ki shanye tea din". 2weeks Later Hajar na zaune palourn downstairs tare da Sabrah wcca ta ɗakkota shekaran jiya, Sabrah sai wasa take yiwa Nanerh da toys dinta da take zaune baja baja a cikinsu, kayan wasa gareta masu yawo sai kace abinci, a cikin kayan wasan harda horse toy da Ashraaf ya bata, shine ma a hannunta tanata gasa masa cixo da rabbit tooth dinta, Sabrah tace "Addah na ga Yaya Maimuna akan titi tana bara a cikin almajirai", Hajar ta dakata da latsa wayar da take tace "wace Maimunar..?", Sabrah tace "Maimunan Maama ta tsohon gidanmu", Hajar ta tsuke ido tace "Maimunan kika gani tana bara..?", Sabrah ta gyaɗa kai tace "Eh idan zanje schl nke ganinta akan titi", Hajar was very shocked amma kuma bata gamsu ba, Maimunan ce zata fito kan titi tana bara, a haba dai wnn ai impossible ne, Hajar tace "kawo min kayan abincin Nanerh naga kamar cikin yayi ƙasa", Sabrah tace "Toh", gwangwanin cereal food din Nanerh da Vacuum flask Sabrah ta kawo mata, tini Hajar ta damawa babynta cereal food dinta a ƙaramin silicone bowl dinta, Hajar ta ɗauki Nanerh ta fara bata abincin, ana yi ana wasa, don idan ba a wasan nan saita ƙi ci next action kuma kuka ne, bell din door aka danna, Hajar tace "Open the door Sabrah", Sabrah ta tashi da sauri ta buɗe ƙofa, Hajar ta buɗa baki ganin wcca ta shigo, Khausar ta ƙarasa shigowa ciki tare da friends dinta biyu, Hajar ta tarbesu, bayan sun zauna suka gaisa a mutunce, Khausar ta ɗauki Nanerh tana mata wasa, Hajar ta saka Sabrah ta kawo musu ruwa da lemo, Khausar tace "Ohh Hajar ynxu fa zamu wuce", Hajar tace "daga zuwa... ai kwa bari ku huta", Khausar tace "driver na jiranmu ai, daman IV card na kawo mki har gida", ɗaya daga cikin friends din Khausar ta ciro cards daga handbag ta miƙawa Hajar tace "ba ki gane ni ba ko..?", Hajar ta tsuke idonta tana so ta tuna inda ta taɓa ganinta, friend din Khausar tace "Banafsha ce", Hajar ta buɗa baki tace "Na gane... ykk Banafsha..?", Banafsha tace "fine Alhmdllh", su Khausar basu wni jima ba suka yiwa Hajar sallama suka tafi, sai bayan tafiyarsu Hajar ta duba cards din, nan da kwana shida ne bikin, ashe har lokaci ya taho, ranar sunan babyn Noor taji ana mganar bikin Khausar din amma bata yi tunanin yaxo kusa ba, komai mai wucewa ne indai kabi duniya da sauqi wai yau Khausar ce ta tako har gidanta ta kawo mata katin bikinta, baya ga haka ynxu sun ƙulla da Khausar suna zuba friendship dinsu sai kace tin da sun san juna. Daga hka aka shiga bikin Khausar da Farooq, sosai bikin ya zama na musamman don ya haɗa both side, ga ɓangaren Mami ga kuma ɓangaren Abba, bikin Farooq da Khausar yayi armashi ba ƙarya, gashi zumunci ya sake ƙulluwa, daman Mami da Ummin Farooq zaman lfy suke ba wni mganar facalanci shiyasa lokacin da Farooq ya jewa da Umminsa da mganar Khausar kai tsaye tace ta amince, kuma daman tasan wace ce Anty Zulaihah ƙanwar Mami, A ɓangaren Farooq Ango sam bai ɗagawa babban amini ɗan uwansa kuma abokinsa ƙafa ba akan sabgar biki, duk irin noƙewar da Nurain ya ringa yi hka Farooq ya ringa jajiɓosa suna shiga sabga, ɓangaren Hajar da Nurain kam drama aka ringa bugawa a wajen events, shi Nurain ya shige cikin Abokan ango wnda duk ƴan uwa ne, ita kuma hakimar tasa tana daga cikin friends din Amarya, duk inda Hajar tayi Nurain na ankare da ita wai kar wni yayi mata mgana, ita kam shigarta ma was more than decent don ba irin na bride mates bane. Hajjaju Hajiya ma ta baza capacity dinta daidai gwargwado, tace bikin Angonta ake don haka dole ta raƙashe, nan fa jikokinta suka yoh mata caaa da tsokana wai batada kishi za a mata kishiya tana murna, Hajiya kam tace ba komai ai wadata ce tasa yayo mata kishiyar, da za a tafi dauko Amarya Hajiya ce a gaba, daman tace indai tana raye kuma da lfyrta toh duk wata jikarta mace ita zata kaita ɗakin miji, haka zalika idan namiji ne itace zata ɗauko masa matar ta kai masa gidansa, ai kam a hannun Hajiya aka damƙa Khausar, Hajiya ta riƙo hannunta gam zuwa mota tana cewa "Allah yasa ki zama kamar matar Usuman, yarinya ƴar albarka irin albarka, ba sakawa bare aje ga fitarwa, nutsuwa hankali ga kawaici duk ta haɗa, ga uwa uba tarbiyya, Allah yasa kema irinta ce". Hajar dai ana shirin tafiya gidan Amarya ita kuma ta wuce gidanta don a zahirin gsky ta gaji snn kuma ga rigimar da Nanerh take mata itama ta gaji, Sabrah ma har ta gaji da rainon, wajen ƙarfe takwas na dare Hajar tayi wnka, ta lallaɓa Nanerh har tayi bacci, gashi dai bacci take ji amma ta kasa sbd mijinta bai dawo ba, a zabure ta miƙe zaune a kan gadonta ta janyo wayarta ta shiga kiransa, missed call biyu tai masa no response, habawa ai tini ta diro daga gadon ta hau shawagi ta cigaba da doka masa kira, sai a kira na huɗu ya ɗaga, tace "Moon", ƙasa ƙasa taji muryarsa yace "Wifey", daga nan bata sake jin muryarsa ba amma kuma taji alamar kamar driving yake, katse kiran tayi ta sake kiransa, an ɗaga amma kuma sai taji muryar mace, ji tayi tamkar an kwaɗa mata guduma a ka don har wani baƙi ne ya gilma mata.......✍️
💛 HAJAR 💛

{97..}
Sauke wayar Hajar tayi daga kunnenta ta wurgarta kan gado ba tare da tayi ending call din ba, wata irin tafasa zuciyarta ta ringa yi har jiri na neman ɗibanta, ta ja ƙafa ta hau kan gado ta kwanta ta cusa fuskarta a pillow, tunanin zuƙa zuƙan friends din Khausar da suke shige da fice a bikin ta ringa yi, bayan friends dinta ga cousins dinta na ɓangaren uba suma masu yawa kuma kyawawa, Hajar ta suntuma tayi famm saura ƙiris ta fashe, idonta ya soye don duk uban baccin da take ji ya gudu, duk bayan 10 to 15 mins saita ɗaga kai ta kalli agogo, har ƙarfe goma ya wuce Nurain bai dawo ba, ita abinda yafi ƙona mata rai shine da bai sake kiranta ba, tashi tayi ta fita palournta na upstairs, ta kalli Sabrah wacca ta barta tana kallo amma kuma tayi bacci ynxu, daman ita da Nanerh ne suke kwana a bedroom din Hajar ita kuma Hajar ta kwana a turakar mijinta, a yau ba ta jin zata kwana a turakar tasa don wnn fitowar da tayi sbd ta rufe ƙofa ne, tana cikin wnn tunanin aka buɗe ƙofa Nurain ya shigo, ɗaga kai tayi ta kallesa nan ta sake jin wni raɗaɗi a zuciyarta, abinda yasa taji raɗaɗin shine kyan da yayi, lokaci guda pure and breath taking scent dinsa ya cika ɗakin, ya mayar da ƙofa ya kulle yana kallonta yace "Baby wife", ba ta ko kallesa ba ta ƙarasa gaban center table ta ɗauki remote ta kashe kayan kallo, kawai gani tayi har ya matso kusa da ita, da sauri taja da baya ta zille masa, ta juya da gudu ta shiga bedroom dinta, lokaci guda hawaye ya ciko idanunta, ai tini Nurain yabi bayanta, kwance ya sameta kan gado ta rufe da duvet har kai, ya sauke ajiyar zuciya ya ƙarasa gaban gadon ya zauna gefenta, Calmly yace "Baby girl.." sai kuma ya kai hannu ya kwashe duvet din, ta sake janyowa ta rufe kanta, saida sukay haka sau uku, yace "Me nayi kuma Baby wife...?", a ɗan fusace ta miƙe ta zuro ƙafafuwanta ta sauka daga gadon, ganin ta nufi hanyar closet yayi sauri ya tashi ya riƙota don yasan next action din nata, bathroom zata shige kuma duk bala'i ba zata buɗe ba, ƙoƙarin fixge kanta ta ringa yi, ita so take ta gudu taje tayi kukan da take dannewa, ganin yacca ta haƙiƙance ya juyo da ita ya rumgumeta tsam a jikinsa, hakan yasa ta gagara motsi, with cracking voice tace "please let go off me", yace "I will not", fashewa tayi da kuka tace "Ni ka kyaleni ka tafi can wajen sabuwar girlfriend din da kayi", ya waro ido yace "wollah bbu wata girlfriend da nayi Baby wife..", ta fara jan shessheƙa tace "Ai naji muryarta kuma har dasu bata waya tamin mgana", yace "No ba haka bane Baby", turasa tayi ita a dole sai ya saketa, ya kai lips dinsa saitin kunnenta yace "don't cry and listen to me..", yana rumgume da ita ya fara tafiya zuwa gefen gado, ya zaunar da ita snn ya duƙa gabanta gami da riƙo hannayenta cikin nasa, ta saukar da kanta ta wani sha kunu, shiru ne ya ratsa room din, shi kam kawai kallonta yake yana auna salon nata kishin, ta ɗago sukay ido huɗu, ta haɗe gira tace "Toh idan ba girlfriend kayi ba wce ta ɗauki wayar..?", ya sauke numfashi yace "Sumayyah ce fa", ta zuba masa ido tabbas sai ynxu ta ɗan gane muryar Sumayyah taji, ya murza hannunta dake cikin nasa yace "muna tare da Iron Lady xan kaita gida ne kika kira baby wife, Hajiya ta hanani yin wayar wai baxan kifar da ita a mota ba, tace wai ina driving ina waya ai baxai yiwu ba, shine na bawa Sumayyah wayar nace ta miki mgana tinda har da ita zan kai gida tare da Iron Lady...", Hajar tayi ajiyar zuciya a bit relief, yace "ina kaisu gidan zan kiraki Charge dina ya ƙare" da haka ya ciro wayarsa ya nuna mata taga tabbas ta mutu bbu Charge, ta juya lulu eyes dinta gami da turo baki tace "Amma baka dawo da wuri ba", yace "Punk... ya hanani sakat saida muka rakasa gidansa snn na samu na gudo", tayi shiru ba tace komai ba tana jin duk raɗaɗin zuciyarta yana zagwanyewa, yace "Daman nace Princess a wajenki ta koyi rigima...", tace "Ai ni nawa da dalili", ya waro ido yace "Ina dalilin anan, har an kusa bani though punishment daga an kira waya anji muryar mace", ta ɗan hararesa, murmushi mai sauti yayi ya janyota yayi kissing idanunta da suka kumbura yace "My ƴar rigima". Washe gari ƙarfe takwas Hajar ta sauka downstairs da Nanerh a hannunta, kawai ƙamshin turaren wuta da freshener ne yake tashi don masu aikinta har sun gama aikinsu, sosai take jin daɗin zama dasu sbd suna jin mgana snn ga tsafta, idan ta gaya musu abu sau ɗaya shknn, saida ta bawa Nanerh abinci ta sakata a kekenta snn ta shiga kitchen ta hau shirya musu nasu abincin, Sabrah ce ta shigo kitchen din, Hajar tace "kin gama shiryawar?", Sabrah ta gyaɗa kai tace "Eh... Addah me zan kama miki..?", Hajar ta bata cabbage tace "ki yanka sa ƙanana", Sabrah ta amshi cabbage din tace "Toh", Hajar tace "kiyi a hankali karki yanke", Hajar ta buɗe fridge ta ciro marinated chicken ta fara mata yankan tsayi tace "Sabrah ranar nan kina gayamin kinga Maimuna tana bara, kin tabbata ita kika gani..?", Sabrah tayi shiru tana tunani, Hajar tace "ba ita bace ko..?", Sabrah tace "Ni wcca nake gani har fuskarta baƙa ce, ita kuma Maimunan Maama fuskarta fara ce ƙafarta da hannunta baƙaƙe", Hajar ta girgiza kai, wnn bai isa ya zama hujja ba don Maimuna bleaching take ta iya yiwuwa ita Sabrah ta gani, Sabrah tace "kuma har ciwon da Maimuna take dashi a goshi na gani", Hajar ta numfasa ta kawar da zancen, kawai dai sai taji ta kasa samun sukuni ne, bata son ahalin Babanta a irin wnn rayuwar, she wish sauran ƴan uwanta su nutsu su koma kamar Nabilah.

★Da kyar Maimuna take jan ƙafarta da ta mata mugun nauyi sbd cikin jikinta da ya girma, tayi wani mugun baƙi sai kace wacca ta shafa gawayi, wata fatattakakkiyar roba sai kace ta kwasar kashi ce a hannunta, tayi wata iriyar rama sai kace wcca ta shekara goma tana jinya, gida ta shiga wanda a ynxu ya sake ruɓewa, tana shiga soro ta tsaya ta janyo duƙunƙunannen hijab dinta da ya koɗe ta goge hawayen da suke sauko mata, wucewar da za tayi wajen shagon Iliya mai awo aka samu wni mutum ya gwaɓa mata mgana, da haka ta shiga gida tana jan ƙafa, sororo tayi tana kallon Maama dake sanye cikn wasu ruɓaɓɓen kaya duk sun zama tsumma, Maimuna tace "Maama..", Maama ta ɗago ta kalli Maimuna sai kuma ta saukar da kanta, Maimuna tace "Na shiga uku... Maama mai ya faru dake", Maama tace "ciwon Sa'adatu ne ya tashi tayi min duka", Maimuna ta ƙarasa ciki tace "Tana ina..?", Maama tasa haɓar zani ta toshe hancinta da ke yoyon jini tace "da kyar na samu na rufeta a ɗaki", Maimuna ta ajiye mushiyar robar dake hannunta ta matsa gaban windown ɗakin da Maama ta rufe Sa'adatu, malelekuwa kawai Sa'adatu take a ƙasar ɗakin da ko leda babu, gurnani take sai kace mage lokaci guda kuma saita kurma wni uban ihu, Maama ta leƙa robar da Maimuna ta ajiye sai kuma tace "yau baki samo komai a wajen maular ba..?", Maimuna tace "Na samo naira talatin", Maama ta fara matsar kwalla tace "yau ko na kwakin bamu samu ba knn... innalillah wa'inna ilayhirraji'un", rabonsu da abinci tin shekaran jiya kuma shima dai garin kwaki ne suka jiƙa bbu sugar suka ci, su duka ukun rabin gwangwani suka sha sbd shi suka samu, Maimuna ce mai fita tayo bara saita samo musu na kaiwa baki, toh ynxu itama Maimunan idan ta fita ba samo abincin take ba, Sa'adatu kam hauka take tuburan lokaci zuwa lokaci, idan haukan bai motsa ba sai kaga ta zauna waje ɗaya tanata kuka, idan kuma ya motsa saita ringa doke doke, abin nata dai sai kace shafar aljanu, kuma idan ta tashi doke doke akan Maama take durango, tana dukanta tana kuka tana mata Allah ya isa da Allah wadai, Maimuna tace "kin bata ruwan tofin..?", Maama tace "shi naxo bata ta cafkeni ta lakaɗa min na jaki", Maimuna tayi zaman daɓaro a ƙasa ta rasa abinyi, rana zafi inuwa ƙuna, wnn wace irin rayuwa ce suke yi, tinda Allah ya yiwa Baba rasuwa duniya ta juya musu baya, ashe da cikin wadata suke da rufin asiri amma ruɗin zuciya ya hanasu gani, haƙiƙa mahaifiyarsu ta cucesu matuƙa, ta sabauta musu rayuwa, ta musu gurguwar tarbiyya ta hanasu bin ta mahaifinsu ta gsky, Maimuna ta miƙe ta nufi soro, Maama tace "ina zaki..?", Maimuna tace "zanje in nemo abinda zanci ne Maama, wllh yunwa nake ji kamar zan mutu, ƙirjina ma ciwo yake" tana gama fadin haka ta fita, bata bi ta hanyar shagon Iliya mai awo ba ta zaga ta baya, da ƙyar take jan ƙafarta bata ma san inda ta dosa ba, kawai ganin mutum tayi a gabanta, ya busa mata hanyaƙin wiwi da yake sha a fuskarta, Maimuna na ɗaga kai taga Bisi Ƙwale, ja da baya tayi ta zagaye zata wucesa, ya kashe wutar wiwin da yake sha a goshinta snn ya buɗa murya yace "kere na yawo zabo na yawo don haka dole su haɗu, yau bbu abinda zai hanani kakkafaki a nan wajen", Maimuna ta hau sosa goshinta da ya kwaile sbd wutar da Bisi Ƙwale ya manna mata, juyawa yayi ya leƙa kangon da suke zama ya kira Ƙwage, yana juyowa yaga bbu Maimuna a gabansa ta gudu, can ya hangota har ta masa nisa, ai kam tini ya saki iskar wandonsa yabi bayanta, Ƙwage ma da ya fito ya rufa masa, Allah ya taimaki Maimuna ta afka cikin gida, tana ƙoƙarin saka sakata Bisi Ƙwale ya banko ƙofar, ai kam gaba ɗaya ƙofa ta sauka daga jikin gini don ta gama ruɓewa, da gudu Maimuna ta shige cikin gida, Maama na tmbyarta lfy ina ba amsa, Bisi Ƙwale ya ɗauki wni icce da ya gani ya rufesu da duka, Ƙwage ya ɗauki wata murgujejiyar taɓarma, tashin farko ya saukewa Maama ita a cinya, Maama ta zube ƙasa cikin gunjin azaba, Maimuna ta rarrafa banɗaki Bisi Ƙwale ya bita yana sauke mata itace a gadon baya, ihu Maama da Maimuna suke suna neman agaji, Ƙwage yace "tsinanniyar yarinyar nan da tasa aka kaini gidan kaso..", Bisi Ƙwale yace "mu ƙaddamar musu kawai", Sa'adatu da ta ɗan dawo hankalinta ta leƙo ta window, ai kam Ƙwage ya hangota, ya saka taɓarya ya bige ɗan ƙaramin kwaɗon da aka rufe ɗakin ya shiga, saida ya shemar da Sa'adatu snn ya murguza mata tabaryar a baki gaba ɗaya haƙoranta na gaba guda shida suka sabauce, uku suka zube a take ragowar ukun kuma suka shige cikin dadashi, tini Sa'adatu ta sume don haka Ƙwage ya rabu da ita, Bisi Ƙwale ya fito daga banɗaki da ya tarfa Maimuna yana zazzare ido bayan yaga ta dena motsi, Ƙwage ya ɗaga tabarya ya ɓaurawa Maama a goshi, Bisi Ƙwale yace "Zo mu ware", da sauri suka fita daga gidan bayan sun wurgar da makaman da sukay aika aikar............✍️
💛 HAJAR 💛

{98..}

★Hajar ta fito balcony zata kira Sabrah da ta fito da Nanerh tana mata wasa, a tsakiyar compound ta hangosu suna kallon gate, daga ƙofar gate din kuma Binta ce mai aiki da Inuwa mai gadi, mai gadi yayi kane kane a bakin ƙofa alamar wni ya hana shigowa, Binta tace "ka ga Inuwa don Allah kaɗata wnn wace irin almajira ce mai nacin tsiya", daga waje Maimuna da hannunta ke nannaɗe da tsumma hawaye na bin kuncinta tace "dan girman Allah ku barni na shiga wajen ƴar uwata", Binta ta mata wni kallon tara saura kwata tace "wace ƴar uwar taki", Maimuna tace "wllh ni ƴar uwar matar gidan ce ubanmu ɗaya...", Binta tace "Chasss kuji mahaukaciya ke kin isa ki zama ƴar uwar matar gidan nan, ke asuwa..", Maimuna ta fashe da kuka tace "dan Allah ku bar ni na shiga..", Binta tace "kaga Inuwa bani hanya na koyawa jakar nan hankali", Inuwa yace "A'a bari ni na koya mata, wllh idan bata bar ƙofar gidan nan ynxu ba saina sumar da ita", Binta tace "barni da ita kawai, kar ka taɓata ace ka taɓa mai rai, wnn idan ka taɓata ai sai ka mata mummunar illa", Inuwa ya matsa daga jikin ƙofar, Binta ta maye position dinsa tana kallon Maimuna tace "baiwar Allah tin muna shaida juna ki tafi", Maimuna tace "ku dubi girman Allah...", ko jin sauran maganar Binta ba tayi ba ta zage ta hankaɗata tace "ke kin san girman Allahn da muka haɗaki dashi kika ƙi tafiya", Binta ta banke ƙofar gidan ta bar wajen, cikin gida ta dosa, Hajar dake tsaye balcony bayan ta saka Sabrah sun koma ciki da Nanerh tayi kiranta, da sauri Binta ta tafi wajen Hajar, tana isa gabanta tayi bowing tace "Anty gani..", Hajar tace "me ya faru a bakin gate na ganki a can kuna hayaniya...?", Binta tace "Wata mata ce wai saita shigo, irin Almajiran nan masu kama da tubabbu, wai cewa tayi ke ƴar uwarta ce shine ta bani haushi na kulle ƙofar", Hajar ta kalli gate din sai kuma tace "ta tafi ko tana nan...?", Binta tace "Wllh ba sani ba, amma da kyar idan ta tafi don irin wadan nan mutanen akwai baƙin naci", Hajar ta kunce mayafin doguwar rigarta da tayi ɗan kwali dashi ta yafa a wuyanta, walking a bit fast ta nufi gate, Binta tabi bayanta tace "Anty kar kije wajen wnn matar ba a rasa cuta a jikinta ba", Hajar bata tanka mata ba ta cigaba da tafiyarta har ta isa gate, tana zuwa gate din kam tasa Inuwa da ya koma kan kujera ya buɗe mata, ana buɗe ƙofar Maimuna dake maƙale da gate zaune rashadan a ƙasa ta ɗago kanta tana kallon Hajar, Hajar ma ta ringa kallonta tana ƙanƙance ido don bata ganeta ba, da rarrafen hannu ɗaya Maimuna ta rarrafa ta riƙe ƙafafuwan Hajar tace "ƙoƙon bara da maulata na kawo miki Hajara, dan girman Allah ki temaka min", Hajar ta ɗan ja da baya tana kallon Maimuna, Binta ta ɗauki farar kujerar da mai gadi yake zama ta tura Maimuna da ita tace "ke karki sake taɓata, muka san wace irin cutar ce a jikinki", Maimuna bata haƙura ba ta sake rarrafowa ta riƙe ƙafar Hajar tace "kar ki duba halina Hajara, kar ki duba halin mahaifiyata, kar ki duba halin ƴan uwana, ki duba girman Allah da Manzonsa, dan darajar Allah da ma'aiki ba dan ni ba ki taimaka mna Hajara, duniya ta mana ruku'un dila, masifa da bala'i ta ko ina Kunno mana kai suke, ƴan uwanmu duk sun gujemu, makwabta babu wnda yake jin kukanmu bare ya jiƙanmu, ke kaɗai ce wcca nake tunanin zaki taimaka mna...", Binta ta ɗaga kujera zata mangare Maimuna Hajar tace "rabu da ita Binta", Maimuna ta rushe da kuka tace "ki duba mahaifinmu Hajara", kukan ma da kyar Maimuna take yi sbd galabaita, ko mai cutar kwasheko ya fita kyan gani, Hajar taji wata ball ta tsaya mata a throat, Allah sarki Baba tabbas yaga jarabawa akan Maimuna da Sa'adatu da uwarsu Maama, ya haifi fanɗararrun ƴaƴa da suka zama annoba cikin al'umma, da ɗacin murya Hajar tace "idan tukunya tayi ɓori...", Maimuna tace "haƙiƙa kanta take ɓatawa", Hajar ta dubi Inuwa da Binta tace "ku fitar min da ita", wni azabar haushin Maimuna taji bayan ta tuna yacca suka gallazawa Baba, yadda Baba ya sha wahala akansu, ba ta jin zata iya taimakon su Maimuna bayan abinda suka yiwa Baba, habawa ai tuni Inuwa ya figi Maimuna ya jata ƙiyyy Binta na taimaka masa, Hajar ta juya da nufin komawa ciki amma saita kasa tafiya, tana jin Maimuna nata ihu, katamau Maimuna ta riƙe jikin gate su Binta na janta, Hajar tayi wni tunani saita juya tana kallon Maimuna, ai wni yana cin arzikin wani, Naseer da Huzaifa da Nabilah duk ƴan uwan Maimuna, tsakanin Naseer da Huzaifa bbu wnda ya taɓa mata wulaƙanci duk kallon ƙanwa kuma ƴar uwa suke mata, Nabilah ma a ynxu tana alfahari da ita kuma zata nunata a ko ina a matsayin ƴar uwarta, a da ne suka saɓa amma ynxu komai ya wuce, uwa uba kuma mahaifinsu ɗaya da Maimuna wnda ko taƙi kota so jini guda ne yake gudana a jijiyoyinsu, Hajar tayi ƙarfin halin yin magana ta dakatar dasu Binta, Maimuna ta sake rarrafowa har guiwarta ta dauje fatar wajen ta kwaile tace "ko kuɗin zuwa asibiti ne ki taimaka mna dashi, ga Maama can a gida ƙafarta zata ruɓe, ta karye a cinya har yau ba'a ɗorata ba, Sa'adatu kuma bakinta zai ruɓe haƙoranta duk sun shige dadashi". Can boys quarters Hajar ta kai Maimuna, ta saka Zaituna ɗayar mai aikinta ta kaiwa Maimuna ruwa da abinci, hannu baka hannu ƙwarya Maimuna ta rufa kan abinci, abincin da ta ci ko gardi albarka, Hajar ta ɗauko kaya cikin kayanta da ta fitar na bayarwa ta kaiwa Maimuna tace ta shiga toilet dake nan boys quarters din tayi wanka ta canza kayan jikinta, ko don ɗoyin da take bazata shiga da ita cikin gidanta ba, Maimuna ta shiga wanka Hajar ta fito daga boys quarters din ta shiga main building, a palournta na upstairs taga Sabrah tare da Nanerh da ta baza mata kayan wasanta, Hajar ta wuce bedroom dinta, wayarta ta ɗauka ta shiga kiran Umma, Umma na picking bayan sun gaisa Hajar ta wassafa mata me ya faru, Umma ta jinjina wnn mganar snn tace "ynxu haka ita Maimunan tana nan gidanki..?", Hajar tace "Eh, wai da zuwa anjima saina kaita gida...", Umma ta katseta da faɗin "ki kaita gida sbd ke kika kawota ko...?, karki kuskura ki fita daga gidanki akan wasu can mutanen da mutunci bai ishesu ba, kuma ynxu ba sai anjima ba ta bar miki gida", Hajar tace "Toh Umma, tace Maama da Sa'adatu na kwance ba lfy", Umma tace "Toh Allah ya basu lfy... ynxu ki tashi ki sallameta", Hajar tace "Tom" da haka ta kashe wayar, yadda Umma tace haka Hajar tayi, haka nan ta sallami Maimuna bayan ta bata kuɗi tace ta kai su Sa'adatu asibiti, Maimuna kamar zata haɗiye harshenta wajen yiwa Hajar godiya sai kace wacca ta bata arziƙin duniya. Umma suna gama waya da Hajar bata ajiye wayar ba ta kira Naseer, har ta gama ringing ta katse bai ɗaga ba, tana ƙoƙarin sake kira sai gashi ya kira, da ladabi Naseer ya gaida Umma, ta amsa masa kafin tace "Allah yasa dai baka koma Lagos din ba..?", yace "Ai kam dai ban koma ba gobe ne zan juya", Umma tace "Toh ina son ganinka yau din nan, idan ma zai yiwu ka taho ynxu", yace "Tom Umma". After like 40mins bayan nan Naseer ya iso gidan, da yaji Umma na nemansa urgent shine ya bar abinda yake ya taho, ita kanta Umma saida tayi mamakin yacca ya iso cikin ƙanƙanin lokaci, gaisuwa ya sake tisa mata duk da sun gaisa a waya, Umma tace "ban dai matsaka ba ko Naseer..?", yace "A'a ba damuwa Umma", Mu'azzam ne ya fito daga ɗakin Umma, Umma ta kallesa tace "ka ganshi..?", Mu'azzam yace "Eh" yana gyara agogon hannunsa, Naseer ya kalla yace "Yaya ina wuni", Naseer yace "lfy lou Mu'azzam... ya aiki..?", Mu'azzam yace "wllh Alhmdllh", Naseer yace "Toh yayi kyau Allah ya taimaka", Mu'azzam ya dubi Umma yace "Umma na fita", tace "Toh sai ka dawo Allah ya tsare hanya...", yace "Ameen" da haka ya fita, Umma ta ɗan sauke ajiyar zuciya tana kallon Naseer da kyau tace "ya wajen ƙannenka su Maimuna da Maama kuma..?", ya shafa kansa yace "suna nan lfy", Umma ta girgiza kai tace "A'a ba lfy ba Naseer, Anya kwa kana zuwa inda suke", ya saukar da kansa baice komai ba, Umma tace "baka zuwa knn..?", yayi ajiyar zuciya yace "Ina gudun fushin mahaifiyata ne, Maama ƙoƙarin yimin baki take akan abinda bai taka kara ya karye ba, ina yin iya ƙoƙarina na ganin na sauke haƙƙinsu a kaina amma Maama bata gani, indai naje gidan sai Maama ta faɗi mganar da zata min illa a rayuwa, ita da kanta tace idan na sake zuwa inda take saita tsine min, wnn dalilin ne yasa na jima banje gidan ba..", Umma ta girgiza kai tana auna gidahumanci da jakanci irin na Maama, Umma tace "Naseer ka daure kaje wajen mahaifiyarka, na tabbata ynxu bazata tsine maka ba, wncan karon ma faɗi kawai take amma baza tayi ba, bbu wata uwa da ta tsani ɗan ta har zata tsine masa bayan ya kasance mai mata biyayya", Sosai Umma ta gayawa Naseer mgana mai daɗi wcca tasa ya sauko daga dokin fushin da ya hau, har saida ya mata alƙawarin daga nan zai wuce wajen Maama. Ko da Naseer yaje gidansu wajen Maama kai tsaye taxi ya kirawo aka ɗura su Maama zuwa asibiti, ita kanta Maimuna data ɗan dawo hayyacinta bayan ta dawo daga gidan Hajar asibitin a kai da ita, shi dai Naseer kawai bin Maimuna yake da kallo ganin turtsetsen ciki a jikinta, ana kaisu asibiti aka shiga da Sa'adatu Theater aka ciro haƙoran da suke shige mata dadashi, Maama kam babban aiki aka shirya yi mata sbd karaya biyu ta samu a ƙashin cinya kuma ƙafa ɗaya, in banda kuka babu abinda Maama take tana cewa Naseer ka kiramin Nabilah da Huzaifa na gansu, zuwa washe gari akace za a yiwa Maama aiki a ƙashin cinya, likitoci sunce idan ya wuce gobe to saidai a datse ƙafar, Naseer ya kira Huzaifa yace ya kamo hanya, shi daman Huzaifa dan i don't care ne ga kuma zuciyar tsiya, tintini yayi watsin uwar watsi da lamarin su Sa'adatu da ita kanta Maaman, gashi Naseer ya gaya masa yacca sukay shiyasa ya sake fusata, a daren ranar kuwa Huzaifa ya iso Kano daga Dutse, saida ya fara duba Maama a ward din ƴan karaya snn ya wuce ward din da Sa'adatu take don itama tana jin jiki, Nurse ya tarar tana bata Yoghurt kasancewar bbu mai kula da ita mace, Huzaifa ya ringa kallon Sa'adatu kafin yace "wane ya fille mata kunne ɗaya..?", Nurse tace "A haka muka ganta dashi". Washe gari an shiga da Maama surgery knn saiga Nabilah, Umma ce ta kirata a waya ta sanar da ita abinda yake faruwa, itama Umman Naseer ne ya gaya mata yace duk an kwantar dasu a asibiti, Saida aka yagalgala tsokar Maama snn aka samu yi mata ɗorin ƙashi, wai nan ma don asibiti ne, baiwar Allah Nabilah ita ta ringa ɗawainiya da uwarta da Sa'adatu, Maimuna kuma Huzaifa ya kaɗata gida sbd tsohon cikin da take dashi, daga shi har Naseer sosai wnn cikin nata ya tsaya musu a rai, Maimuna da aka kaɗa gida ce take jagwalgwala abincin da ake kaiwa asibiti...........✍️
💛 HAJAR 💛

{99..}
Kwanansu Maama uku a asibiti aka canza Sa'adatu zuwa na mahaukata, lokaci guda ciwon nata ya tashi ta fara dukan Nurses, allurai aka ringa garƙama mata a asibitin mahaukatan, da aka mata gwajin kwakwalwa Sai aka ga kwakwalwar nata lfy lou bbu cuta, gida aka mayar da ita aka duƙufa neman mgani na Aljanu tinda ana tunanin su suka shafeta, Maama kam satinta biyu a asibiti tana jinya, ranar da ta cika sati biyu da kwana biyu aka sallameta, Naseer Huzaifa da Nabilah ne suke ta tiri tiri da ita. Washe gari Maama na zaune tsakar gida akan tabarma ta miƙe ƙafar data karye, Nabilah ta kawo mata abincin da ta dafa, Maama ta kalli Nabilah da idanunta da suka cika da ƙwalla tace "Allah ya miki albarka Nabilah", Nabilah tace "Ameen", Maama ta janyo ƙasan rigarta ta ringa goge hawayen da suka shiga sakko mata, da yammacin ranar Naseer ya shigo, tabarmar da Maama ke zaune tana jinyar ƙafa ya nufa, ya duƙa gabanta yana tambayarta ya jiki, kawai saita fashe da kuka wiwi, nadama da dana sani ne fal cike da zuciyarta, Naseer yace "Maama ki dena wnn kukan dan Allah..", Maama ta fyace majina tace "dole nayi kuka Nasiru, ban yiwa kaina adalci ba, ban yiwa mahaifinku adalci ba, ban yiwa ƴaƴan da na haifa adalci ba, haka zalika ban yiwa mutanen da na zauna dasu adalci ba, haƙƙin mutane ma kawai ya isheni, da baƙin cikina da na ƴaƴana da na yiwa gurguwar tarbiyya mahaifinku ya rasu, Nasiru dole nayi kuka idan na tuna haukan dana tafka...", dai dai nan Huzaifa ya shigo da ledar fruit da ya siyowa Maama, Huzaifa ya zauna kan dokin ƙofa yayi kiran Maimuna, daga ɗaki ta fito tana jan ƙafa, rama sosai ta ƙara gashi ta wani ɗashe kamar bbu jini a jikinta, ta samu guri ta zauna da kyar tace "Yaya gani", Huzaifa ya kalleta da ɗacin rai sai kuma ya dubi Naseer yace "Yaya ya za muyi da wnn...?", Naseer ya sauke ajiyar zuciya yace "Ai saita faɗi waye ya mata cikin", Huzaifa ya murtuke fuska yana kallon Maimuna yace "Ke..!!", Maimuna ta sunkuyar da kanta, Huzaifa ya daka mata tsawa yace "ba kiji mai akace ba", Maimuna tasa bayan hannu ta shaɓune hawayen dake sakko mata tace "wllh ban sani ba", Huzaifa yace "baki sani ba kamar ya, a ruwa ake sha..?", Maama tace "Maimuna kiyi mgana mna, nan ƴan uwanki da kika gani masu ƙwato miki haƙƙi ne", Maimuna tace "Billahillazi la'ilaha illa huwa ban sani ba, fyaɗe aka min" ta rushe da kuka. Tsakar dare naƙuda ta kama Maimuna, tun tana jurewa ita kaɗai har ta ja jiki ta tashi Nabilah, Nabilah da taga bazata iya da Maimuna ba ta tashi Maama, ga Maama ba ƙafa saidai jan buttocks, Maama tasan naƙuda ce ta tahowa Maimuna, mgana ake ta tsakar dare bbu abin hawa ballantana a kaita asibiti, Naseer da Huzaifa ne suka tafi neman abin hawan, Maama ganin haihuwa ta taho don har Maimuna ta fara nishi kan ɗaya ya taho ta kalli Nabilah tace ta bata reza, Nabilah ta lalubo reza a jakarta wcca ta taɓa amfani da ita sau ɗaya, a duk wnn zazzafar wainar da ake toyawa Sa'adatu bata san anayi ba, kawai bacci take sai kace mushe, cikin azaba Maimuna ta haihu, ta haifi ƴa mace, saidai kuma tana haihuwar jini ya ɓalle kamar an yanka rago, wata mummunar tear ta samu tin daga sama har ƙasa ta yage, Nabilah ta naɗe jaririyar ta ajiyeta a ƙasa, gaba ɗaya sun gigice ganin yacca jini yake malala, cikin azaba da raɗaɗi Maimuna tace "wayyoh Allahna Maama, ƙirjina zai fashe", Nabilah ta rushe da kuka ta fita a guje ba tare da tasan ina ta nufa ba, lokaci guda Maimuna ta fara convulsion idanunta suka ƙaƙƙafe, hakan tasa Maama ta manta da karayar cinyarta ta miƙe a gigice ta nufi ƙofa, da ƙarfi ta taka ƙafar ai kam ɗorin ya goce, ƙashin ya huda tsokarta ya ɓillo waje, azaba tasa Maama ta tafi luuu ta faɗi a ƙasa bayan kanta ya daki dokin ƙofa. Nabilah kam ashe maƙota ta je ta ringa bubbuga ƙofa, cikin sa'a gidan Mukaila suka buɗe ta taho tare da matarsa, suna zuwa suka tarar da Maimuna Allah ya amshi abarsa, Maama kuma ta sume, kukan jaririyar Maimuna ne kawai yake amsa ƙuwwa a gidan.

★Wajen ƙarfe 10 na safe Hajar ta shiga part din Nurain, direct bedroom ta wuce, bata gansa a bedroom din ba don haka ta shiga closet, ta ɗan waro ido ganin kayan da yake sakawa tace "fita za kayi Husband..?", yace "Uhmm", tace "Ohk" sai kuma ta ƙarasa ciki ta tsaya daf dashi tace "fatan dai ba a min nawa aikin ba..?", yayi murmushi yace "yeah", ya miƙa mata links din da yake shirin sakawa, amsa tayi ta maƙala masa snn ta ɓalle masa buttons din riga, tace "Wai ina zaka yau fa Saturday..?", yace "you know Hammad..?", tace "Eh", yace "shine ya kirani ya bani location yace na samesa a wajen, sunxo kano ne sbd sunji labarin wani yaga ƙanwarsa Azeeza da ta ɓata anan garin", tace "Mother din wnn yaron da muka gani a gidansa..?", yace "Ashraaf... Eh Mamansa", tace "Allah ya bayyanata..", yace "Ameen", Hajar kawai Ashraaf take hangowa, har yau horse toy din da ya bawa Nanerh yana nan tana wasanta dashi, tace "breakfast is ready, sai kaci zaka fita ko..?", yace "Eh", tare suka fito, Hajar ta wuce ta sauka downstairs, shi kam room din Nanerh ya buɗe, kan floor mattress dinta mai faɗi ya ganta ga toys nan iri iri zagaye da ita, yayi murmushi yace "Princess", tini Nanerh ta jefar da toy din hannunta ta rarrafo da sauri inda yake tana ɓangala masa dariya, ya sunkuya ya ɗauketa ya ɗan cillata sama, nan ma ta kyalkyale da dariya, pecking cheeks dinta yayi, sai ƙamshin baby colories da perfume take, fess da ita kamar uwarta, an kama mata cikakkiyar sumarta da cotton band, Hajar na tsaye dining section tana serving abinci taji saukowarsu, ta ɗaga kanta ta kalli Nurain da Nanerh take wawurar hancinsa yana kaucar da fuska tace "Ehen ka ɗaukota ta hanamu cin abinci ko bayan ita ta cika stomach dinta", ya ƙarasa dining din ya zauna a kujerarsa sai kuma ya ɗora Nanerh kan table suka cigaba da wasansu, Hajar na gama zuba masu abinci ta shiga wani room dake downstairs, few secs ta fito da keken Nanerh, ta ajiye keken daga gefen kujerarta snn ta amshi Nanerh a hannunsa ta sakata cikin keken, ta ɗago kanta sukay ido huɗu dashi, ta ɗan turo baki tace "wnn uwar hidimar ce zata bar mu muci abinci lfy, ynxu zata baddala table din", da haka suka fara cin abincin, Hajar na bawa Nanerh wnda zata iya ci cikin abincin. Ƙarfe 11 da wni abun Hajar na closet dinta tana sake kimtsata duk da cewa a gyare take, tana aikin tana humming song, bayan ta gama aikin ta fito, wayarta da ta ajiye gefen gado kusa da Nanerh da take bacci ta ɗauka, 5 missed call from Umma, haka kurum taji gabanta ya faɗi, kiran Umma tayi, bayan sun gama wayar Hajar ta zauna gefen gado ta dafe kanta tace "innalillah wa'inna ilayhirraji'un". A ranar Hajar taje gidan rasuwar ta tarar da Umma acan, duk wnda yaji irin mutuwar da Maimuna tayi sai zuciyarsa ta karye, mutuwa ce ta shahada, ƴarta na nan goye a bayan Nabilah, wujijjigar da Maama tayi ba a cewa komai, bayan an kaita an gyara mata ɗorin da ya sake ɓarɓarcewa tace a dawo da ita gida bazata zauna a asibiti ba, sai ranar sadakar uku snn Hajar ta sake zuwa gidan rasuwar, abinci mai kyau ta kai wnda ta saka su Binta sukay, gidan rasuwar a ɗaɗe yake mutane ƙalilan ne suke zuwa, Hajar na zaune can gefe a tabarma ɗaya da Nabilah wacca take bawa ƴar Maimuna madarar da Huzaifa ya siyo mata, Ita Hajar jira take Umma tazo sai su tafi tare, ai kam bbu jimawa Umman tazo tare da Mu'azzam da Sabrah, Umma ta yiwa Maama ta'aziyya, Mu'azzam ma ya mata, Maama saidai ta gyaɗa kai don bata iya mgana tsabar yacca mutuwar ta daketa, Naseer ne ya shigo Umma ta masa ta'aziyya hakama Hajar, ya tashi zai fita Maama tace "Naseer karka fita, ka kirawo Huzaifa ma", Naseer yace "Toh", ya ciro waya ya kira Huzaifa wnda shima yana kusa, bbu jimawa kam ya shigo, Maama ta ɗan yunƙura tana kallon Mu'azzam tace "Mu'azzamu a bakacin Maimuna ni ina nema mata yafiyarka, dan Allah ka yafe mata abinda ta maka", Mu'azzam ya shafa kansa yace "Na yafe mata duniya da lahira", Maama ta kalli Umma tace "Faɗima dan girman ki yafemin abinda na miki, haƙiƙa na cutar dake ban barki kin zauna lfy a gidan mijinki ba, na cutar dake haka zalika na cutar da ƴaƴanki", Umma ta numfasa tace "na yafe miki, Allah ya yafe mana duka", Maama ta share hawayen da suke zubo mata tace "kowa da yake zaune nan nasan bbu wnda bashi da tabona, ku yafemin ba don halina ba", shiru tsakar gidan yayi bbu wnda yace komai, Sa'adatu ce ta fito tana cewa "Maama ni baki nemi gafarata ba bayan kece kika sabautamin rayuwa, duniya ta min ruku'un dila, duniya ta min gwatson kyanwa, duniya ta min juyin kwaɗo, duk kece sanadi Maama, Allah sarki Maimu Allah ya jiƙanta ya gafarta mata, ni bazan ce komai ba akan mummunar laifin dana tafkawa mahaliccina ba saidai zan dawwama yin istigfari har na koma garesa, ina masu hali irin nawa..?, ƴan mata, zawarawa, matan aure wnda suke aikata abinda yafi zina bala'i suke neman jinsinsu, ina kira da masu irin wnn hali nawa dasu tuba tin kafin lokaci ya ƙure musu, duniya ba wajen tabbata bace lokacinta ƙalilan ne, Zeenatu Mabaruka Teema da tsinanniyar shugabarmu mai ƙungiya naga darisa akansu da kuma kaina, bbu wnda acikinmu wnda bai amshi hukunci ba, nima na amshi nawa, ƴar uwa ki tina ba'a nan masifar take ba sai mutuwa ta riski bawa, rayuwar kabari har lokacin da zata tsaya gaban mahaliccinka domin amsar hukunci, Ni Sa'adatu nayi nadama kuma ina kira da masu irin halina su gyara tin kafin lokaci ya ƙure musu....", daidai nan ta zube ƙasa ta fara haukan nata tana kuka, Huzaifa ya jata ɗaki ya kulle tin kafin ta fara doke doke. Mijin Nabilah yayi kawaice sosai don baice ta dawo gida ba har Maama taji sauƙi, toh saidai ace sauƙi amma kuma ba sauƙi ba don ƙafar shanyewa tayi ta warke a haka, Maama bata iya tafiya saidai da sanda ko kuma ta hau keken guragu, ƴar Maimuna da aka mayar mata da sunan uwarta Nabilah ce ke kula da ita, Sa'adatu an ɗan samu waraka ta dalilin rubutun da ake bata. Da Nabilah tazo tafiya tace zata tafi da Maimuna ƙarama, Maama tace A'a ta bar mata ita wnn yarinya a jikinta take ganin kurwar Maimuna kuma gashi tana kama da uwarta, da kyar Maama ta shawo kan Nabilah akan yarinyar tace bata san ya dangin mijinta zasu amshi yarinyar ba snn kuma bata so wni abun ya haɗata da mijinta. Life continues... Naseer da Huzaifa suka haɗa hannu suka canzawa mahaifiyarsu gida ta bar unguwar dala, gwara ta bar unguwar ta koma inda ba a santa ba inda za a santa da sabon kyakkyawan halinta na yanxu, bil ƙalbi warruhi Maama take kula da Maimuna ƙarama da taimakon Sa'adatu wcca taji sauƙi sosai saida ta nakasta ainun don ba tada haƙoran gaba da kunne ɗaya, haka abun yake shegiya dai Maama ta ganta a kanta, yacca take kiran Hajar shegiya a da ynxu itace take rainon shegiya, shegiyar da take masifar mutuwar so. bayan watanni biyar akay auren Naseer inda ya auri ƙawar Hajar wacca sukay Islamiyya tare wato Zainab, idan kaga yacca Umma da Maama suke ynxu kai ka ɗauka basu taɓa zaman hatsaniya ba, sosai Umma ta shiga bikin Naseer akay da ita, Alhmdllh arziƙin Naseer ya ƙara burunƙasa don ynxu ba direba bane, acan dry port ta Lagos da Port Harcourt ya samu babban aiki, murna a wajen Hajar ba a cewa komai da Yayanta ya auri ƙawarta Zainab, Huzaifa ya baro Dutse ya dawo Kano da aikinsa, shima an kai kuɗinsa wajen budurwarsa dake dutse, Mu'azzam kam tukunna dai don tasa wife to be din Insha Allah bata isa aure ba, Anty tace ta basa Humairah, ita kuma Umma tace ta bawa Abdallah Sabrah, hakan zai sa zumunci ya ƙara ƙulluwa snn dangin ya ƙara girma......✍️
💛 HAJAR 💛

{100..}

Hajar ta shirya snn ta shirya Nanerh don yau juma'a ranar Umma zata tare a sabon gidan mijinta, bayan ansha gwagwarmaya Umma ta amince tayi aure, Kawunanta ne suka haska mata hanya yayinda Anty ma ta nusar da ita, tabbas aure shine rufin asirinta da na ƴaƴanta, ba a cewa uwarsu zaman kanta take ba ko kuma a kirasu da ƴaƴan mace, gashi kuma daman ba wni tsufa tayi ba don a shekara arba'in biyar kawai ta ɗora a kai, Babban mutum Umma ta aura wnda ya samu kyakkyawar shaida, danƙareren gida ya mallaka mata wnda anan ne zata zauna a gidan da yake matsayin nata, hakan tasa Umma ta tafi da yaranta biyu da suke gabanta, Mu'azzam da yake wni ɗan noƙewa wai shi babba tini ya saki jikinsa domin kwa a zahirin gsky mijin mahaifiyarsu mutumin kwarai ne kuma har ya fara musu riƙo irin na uba, tin safe sai yamma Hajar ta koma gida bakinta har kunne, ƴan uwanta sai samun cigaba suke a rayuwa, Ummanta ma has move on. Rayuwa mai mugun azabar daɗi da tsafta Hajar da Nurain suke shimfiɗawa, Happy family knn, shekarar Nanerh ɗaya Hajar ta yayeta daga mama, bbu wnda suka gayawa anyi yayen tsakanin Umma da Mami sbd kar wani yace a kaita wajensa, Nurain ne ya kissifa wnn shawarar don baya son a rabasa da Princess dinsa ko da kuwa na kwana ɗaya ne, Hajar ma tayi na'am da hakan don ita bata so a rabata da ƴarta, yarinyar akwai shiga rai da kyau kamar a sace, Hajar ba ta sha wni wahalar yaye Nanerh ba don already yarinyar ta kama abinci, tin kafin ma ta yayeta bata fiya shan mimin ba sai an bata, Nanerh na nan chubby da ita sai ma kyau da ta ƙara bbu wata rama na yaye. A kusan tare Hafsah da Khausar suka haihu, Khausar ce ta fara haihuwa ta haifi baby boy snn Hafsah da itama ta haifi baby boy, Nabilah kuma har yau Allah bai kawo haihuwar ba duk da cewa ta riga Khausar da Hafsah aure, komai iri ɗaya na kayan barka Hajar ta bawa Hafsah da Khausar, Hajar da taje barkar Hafsah sai taji dama ta kwana kawai sbd Nurain baya nan ya tafi Lagos wni workshop, amma dai bata kwanan ba tinda mijinta bai bata wnn damar da zai tafi ba, ranar da zai dawo tin asuba Hajar take shirin tarbonsa, kunshi da kitso daman tin jiya aka mata, favourite dinsa ta dafa iri iri, wajen sha ɗaya ya iso gidan, habawa kaga rige rigen zuwa tarosa tsakanin ƴa da uwa, Nanerh har dasu tuntuɓe, Hajar ta cake taƙi ƙarasawa ta tsaya kallon Nanerh, Nurain ya ɗauketa snn ya cillata sama, dariya kawai Nanerh ke ɓaɓɓaka masa, yayi pecking cheeks dinta yace "Princess", Hajar ta riƙe ƙugu kamar gske tace "wnn yarinyar..", Nurain ya ajiye Nanerh kan kujera ya wuce gurin Hajar ya rumgumeta, tace "Sannu da zuwa My Moon", yayi kissing lips dinta lightly yace "yawwa wifey". Bayan sallar la'asar Nurain yace Hajar ta shirya zata rakasa unguwa, veil da jaka kawai taje ta dauko tinda a shirye take, bata zama a hargitse a gidanta gsky, Nurain har ya ɗauki Nanerh sun fita compound, Hajar na fita compound ta nufi parking space ta buɗe front seat din motar da suka shiga, Hajar ta kalli Nanerh dake zaune a spot din da yake nata tana shan sweet, Hajar tace "ke Papa's bear or Princess kike that's my spot", Nurain ya ɗauke Nanerh daga kan kujerar, Hajar ta shiga ta gyara zamanta ta rufe ƙofa, sai a snn ya miƙa mata Nanerh, saida suka isa gidan Anty Zulaihah snn Hajar ta san nan din zasu ita tasha ma wni gurin ne daban, bayan sun gaisa da Anty Zulaihah wcca ta dauki Nanerh tana mata wasan kakanni Hajar ta tashi ta shiga ɗakin da Khausar take, tare ta ganta da Farooq wnda yake riƙe da babynsa, shima zuwansa knn, ai da tasan tare suke da Farooq da baza ta shigo ba amma kuma tayi knocking door Khausar tace ta shigo, Khausar tace "barka da zuwa Oum Nanerh", Hajar tayi murmushi tace "yawwa Maman boy", Hajar suka gaisa da Farooq ya tmbyi Nanerh, tace masa tana wajen Anty Zulaihah, Nurain ne ya shigo, firr Farooq yace Nurain bazai ɗauki baby ba ai ya makara, Nurain dai baice uffan ba don ya gane rama abinda ya masa yake, Hajar da ta gane itama ta ringa murmushi, basu wani jima ba suka tafi, gidansu Nurain suka wuce don daman yana son zuwa ya gaida parent dinsa tinda yau ne ya dawo daga Lagos, Hajar na zaune a main palour tare da Noor wcca ta kawo ɗanta Anaab wajen Mami yaye, Hajar tace "kai Noor yanxu yaushe Anaab din ya isa yaye, he is too young", Noor tace "na ji da wnda yake womb dina ma", Hajar ta riƙe haɓa sai kuma tayi dariya tace "har kin manta gidan glass din knn..?", Noor tace "ina fa na manta, da planning fa a jikina", Hajar tace "ikon Allah", Noor tace "Ai canza wani zanyi bayan na haihu", Hajar tace "Toh Allah ya raba lfy", Noor tace "Ameen... ya kamata a yiwa Nanerh ƙanwa gsky", Hajar tayi dariya tace "ba gashi nan zaki mata ba, ga Anaab ma already an mata, very soon Anty Sakeena ma zata mata wani", sai after isha'i su Hajar suka bar gidan Mami, Nurain ya rage gundun motar jin wayarsa tayi ring, wayar da bata wuce ta minti biyu ba yayi ya ajiye wayar, Hajar ta ringa kallonsa ganin expression din fuskarsa ya sauya, ta bude baki zata tmbyesa lfy knn yace "ɓatan mutum bbu daɗi wllh, har yau su Hammad basu haƙura da neman ƴar uwarsu ba, wai ynxu ma Kano zasu sake zuwa to check on other places da ake tunanin za a iya samunta...", Hajar tace "kamar ina.?", yace "Psychiatric hospital, Gidan gajiyayyu and Mortuary", tace "Allah ka bayyanata wnn karon", yace "Ameen", Nurain ya sauke ajiyar zuciya yana tuna Ashraaf, may be har yaron ya haƙura da neman mahaifiyarsa, ya kalli Hajar da itama tunanin da take knn yace "ko mu siyo spicy seafood..?", ta gyaɗa kai tace "Sure, i like it", ɗauke kan motar yayi ya canza hanya, bayan sun sayi seafood din suka juya, Hajar ta kalli agogon dashboard taga ƙarfe tara saura, ta kalli hanyar da suke shirin wuceta tace "Dan Allah Moon muje wajen Iron Lady", yace "sai dai next time kinga yanxu dare yayi", tace "Toh Allah ya kaimu", ya kalleta a taƙaice, samm bata masa musu abinda yace tayi shi take yi, kai tsaye bbu musu ta haƙura da zuwa wajen Hajiyar, murmushi Hajar tayi ganin yayi reverse ya shiga layin gidansu Farooq, ta back door inda direct zaiyi leading zuwa ɓangaren Hajiya suka bi bayan sun shiga gidan, Nurain ya saɓa Nanerh da tayi bacci tin a gidan Mami a shoulder, Hajiya na zaune kan darduma dake saman carpet ta mimmiƙe ƙafafuwa, ga nan kayan sa ranar Aysha da aka kawo yau zagaye da ita, Hajiya ta ɗaga kai ta kalli ƙofa jin an shiga, ta saman kantamemen glasses dinta ta ringa kallon su Hajar da suka shigo, Hajiya tace "su waye waɗan nan da tsoho daren nan, duu Allah ku fita ai an gama ganin kayan sai kuma gobe idan Allah ya kaimu, yoh ina dalili tin ido na ganin ido baku zo ba sai yanxu salon ku ƙuma mana sata", Nurain ya haɗe gira ya kalli Hajar yace "kin gani ko, toh gashi nan tana koramu harda sharrin ce mana ɓarayi", Hajar ta ƙarasa ciki ta zauna kusa da Hajiya da ta bita da kallo tace "Hajiya mune fa..", Hajiya ta micincina ido tace "Ah aha ashe su Hajaru ne, ai nayi zaton mutanen unguwa ne magulmata, tinda aka kawo kayan nan suke shige da fice sai kace lefe, kayan sa rana ne fa", Nurain ya ƙaraso ciki, Hajiya tace "Ajiye wnn shagwaɓaɓɓiyar nan kan kujera ka tareta da matashi, Allah yasa kar ta tashi har ku tafi don ƴar nan taku akwai hidima ynxu saita baddala lissafin kayan nan", Hajar tace "ina yini Hajiya..", Hajiya tace "lfy lou ƴar albarka", Nurain yana kwantar da Nanerh ta tashi, ai kam saida ta baddalawa Hajiya palour kafin su tafi wajen ƙarfe tara da rabi, a haka ma Hajiya tace gsky su tafi lada ya isa haka, wnn ƴan tasu ko fura nan ta barta wajen cika ciki. Washe gari Hajar na dusting kayan kallo Nurain ya shigo palourn, ajiye duster din hannunta tayi tana kallonsa ganin ya ɓoye wani abu a bayansa, yace "guess what..", tace "Chocolate", ya girgiza kai yace "No", tace "Sweet", ya sake girgiza kai, tace "Rose", nan ma ya girgiza kai, langwaɓar da kai tayi tace "i can't guess", ya ƙarasa ciki ya ajiye brown envelope din da ya ɓoyo kan doguwar kujera, Hajar tayi kasaƙe tana kallon envelope din, daman wnn shine abinda yake cewa tayi guess, ita ina zata gane wni envelope, kamo hannunta yayi ya zaunar da ita kan kujerar shima ya zauna suna fuskantar juna, envelope din ya buɗe ya ciro papers guda biyu ya ajiye mata akan laps, ta kalli papers din sai kuma ta kallesa, ya mata alamar ta duba, a hankali ta kai hannu ta dauki paper daya ta karanta, tini facial expression dinta ya canza zuwa na annashuwa, har wni rawa hannunta yake ta dauki ɗayar ma ta duba, paper daya ta aikin hajji ce, dayar kuma ta schl wcca har an gama mata komai lectures kawai zata fara shiga, sai sun dawo daga hajj din ne zata fara zuwa schl, ita dai tasan kwanaki ya amshi credentials dinta amma bata san schl yake mata processing ba, tini hawaye ya ciko idanunta, ta rasa wne words za tayi amfani wajen gode masa, zagaye wuyansa tayi da hannayeta ta haɗe forehead dinta da nasa tace "bbu wni words da tayi fitting na mka godiya mijina, Allah ya saka maka da mafificin alkhairy", ya goga karan hancinsa a nata yace "you deserve more than this my wife..", tace "you're the most kind of blessings that happens to me, i cherish every second with you", yayi murmushi mai sauti yace "Hajar i Nurain take you as my wife, Mother of my child and unborns, to have into hold from the day i met you forward, for better for worse", tayi murmushi tace "for richer, for poorer", ya goga karan hancinsa a nata again yace "in sickness and in health", tace "Till death do us apart..", yayi ajiyar zuciya da murmushi a fuskarsa yace "Until death do us apart", sukay dariya a tare snn suka haɗa baki suka ce "Once and for all", ta raba goshinsu a hankali, ta kai hannu ta ringa shafa kwantaccen sajensa, ya haɗe lips dinsu waje ɗaya ya fara kissing dinta passionately, The kiss last for almost a minute, tana kallon cikin idonsa tace "Na gode Allah da ya bani kai matsayin miji", yace "Nima na gode Allah da ya zaɓamin ke as my wife", ta kwantar da kanta a shoulder dinsa......

Nima Feenerh feeche nace Allah na gode maka daka bani dama na sauke wnn Littafi....

Alhamdulillah.. Alhamdulillah.. Alhamdulillah.

A nan na ajiye Alƙalamina a cikin wnn littafi mai taken HAJAR, kuskuren dake ciki Allah ka yafemin Ni dana rubuta da ku masu karatu... darussan dake ciki Allah kasa al'umma suyi amfani dashi.

As you read the book Hajar kinji daɗi kin samu nishaɗi da annashuwa, Ni Feenerh feeche abu ɗaya nake buƙata a gareki da zaki biyani, dan girman Allah ki karanta suratul Iklas ga Mahaifina, Allah ya kai ladan ƙabarinsa ya gafarta masa....😭 da wnn kaɗai zaki biyani ƴar uwa.

My diehard fans gaisuwa ta musamman a gareku da irin ƙwarin guiwar da ku ka bani through the journey of Hajar.... ngd sosai...

Hau'wa Yunusa, Nafisa Ummu Readone, Maryam Shehu Usman, Zainab A Aliyu, Khadija A Taheer, Zulaihah Bint Saeed, Maryam Adamu Bappah, Sulaymstiches, Maryama, Aeesha, Saadat Baba duk da dai late comer ce, Hajar namesakes, Nafisa Sasaal partner, da sauran fans da ban jeru sunansu ba da ƴan bayan katanga toh duk ina miƙo gaisuwa. Team Hajar 💛 jinjina ta musamman a gareku wllh ina yinku wujiga wujiga, Team Nurain ❤️ kuma ina yinku ba laifi.

Taku har kullum... Nafeesah Yusuf Nagoda (Feenerh feeche...✍️)

Mai son complete Document can Ping me Via my WhatsApp digit, but there is payment it is not free.... 👉 08141826023

BISSALAM....

********************** **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
************************* **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > [email protected]

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

WhatsApp Number: 08138873799


Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafinmu ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** **************************
Chapter 6 · 0% Book details