← Book details Hajar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 5 OF 6

Chapter 49... on Arewabooks..

Hajar Part 1 Complete Hausa Novel · about 129 min read

Click the link below to join my WhatsApp group 👇
💛 HAJAR 💛

{49..}
Thick eyebrows dinsa a haɗe while still staring at her yace "i said give me the keys..", ta juyar da kai gefe tana turo baki tace "ni fa bazan bayar ba..", bata ankara ba taji hannunsa akan nata da ta ɓoye a baya yana ƙoƙarin dawo dashi gaba, ta cije iya ƙarfinta ta sake dunƙule keys din a hannunta, partially ya dubi fuskarta kafin ya murɗa hannun nata ya dawo dashi, ƙara ta fasa ta fara ƙoƙarin fixgewa, tana ji tana gani ya ɓamɓare keys din daga hannunta, ya bita da wani shegen kallo ya juya ya fita daga ɗakin, wani mugun takaici ne ya tokare mata a maƙoshi, ta sulale ƙasa ta rushe da kuka tace "wllh sai na maka rashin mutunci mai wasali, ba dai ni ka murɗewa hannu ba, na rantse da Allah saina rama, dala ba gammo ka ɗakkowa kanka idan baka sani ba saika sakeni zaka cigaba da rayuwa mai daɗi..", taci kukanta ta more ta tashi ta shiga bathroom ta wanke fuskarta da ruwa ta fito, fita tay daga ɗakin tana cika ta batsewa ƙiris take jira a taɓata ta sauke kwandon bala'i, downstairs ta sauka ta nufi kitchen tana cewa "duk abinda kace kar nayi toh yanzu na fara yinsa a gidan nan, dani da kai naga wanda zai sumar da wani, dan wllh tllh ni kaɗai nasan irin ayar da zan gasa maka a hannu..", plate ta ɗauka ta buɗe bucket din dubulan dana chin chin ta zuba, ta fito daga kitchen din, tsaye tayi tana kallon cup din Coffeen da ya ajiye a hannun kujera, Cup din ta ɗauka tana kallon coffen, ta gyaɗa kai ta haura sama da Kofin, a kan mirror ta ajiye plate da cup din taja stool ta zauna, taci dubulan da chin chin dinta tayi nak tana korawa da coffee, sosai combination din ya mata dadi sbd the coffe is creamy and yummy gashi babu sugar sosai sai hakan ya bada wani armashi. Nurain ya ringa kallon inda ya ajiye Coffeen sa wayarsa a kare kunne yana magana da Farooq, zagaye ya ringa yi yana duba each sofa a palourn, Farooq yace "are you listening..?", Nurain yana sake duba hannun kujeru yace "yeah", Farooq yace "alright" ya cigaba da bayanin da yake masa, after 5minutes suka gama wayar, Nurain ya shafa cikakkiyar sumarsa yace "damn it i misplace my coffee" da haka ya haura sama to get ready for work, dakatawa yayi da zuge glass door da ya fara ya kalli ƙofar ɗakinta da ta buɗe ta fito, idonsa ya sauka akan cup din dake riƙe a hannunta, ya ringa kallonta har ta ɓace masa bayan ta sauka ƙasa, slight hiss yayi ya juya ya shiga room dinsa, ƙarfe tara dot ya fito bayan yayi wanka ya shirya hannunsa riƙe da briefcase, ya sauka downstairs ya shiga kitchen ya ɗauki basket din abinci da yazo dashi jiya, bayan ya rufe main door ya isa parking space, ya shiga motarsa ya kunna, a booth ya saka basket din ya koma ya shiga motar tana gama warming ya fara driving ya fita daga gidan Inuwa na ɗaga masa hannu. sai ƙarfe uku Hajar ta fito ɗakinta zuwa kitchen, duk wnn lokacin ba ta ji yunwa ba sbd breakfast din yau ya riƙe mata ciki, ji take dama zata sake samun wnn creamy coffee din, saida ta gama jajjaga attaruhu da Albasa ta zuba a ƙaramar pot ta ɗora kan gas, ta ɗauki lighter ta kunna gas din amma babu wuta, ta canza wani shima dai wuta ba tazo ba, ta koma ta jingina da jikin cabinet tana tunanin yanxu yaya knn, me zata bawa cikinta, ta ringa kallon gas cooker din sai taga ashe akwai electric head ajiki har guda biyu, ta tuna lokacin da take gidan Anty Jamilah dashi ai take amfani most of the time sbd unguwar akwai nepa sosai, Hajar tayi ajiyar zuciya a bit relief, tana murɗa control knob din electric stove din luckily for her sai gashi ya kama, tinda a jone yake da wuta, wani dadi ne ya ratsa Hajar, tini ta hau yin girkinta, cikin kayan gararta ta farke buhun shinkafa ta ɗebi yadda zai mata ta dafa, bayan ta gama dafa shinkafar da ƴar sauce ta palm oil, gaba ɗaya ta juye a plate ta zuba Sauce din akai, ta buɗe fridge ta ɗauki ruwa da haka ta fita zuwa palour, da kyar ta iya cinye abincin, ta kai plate din kitchen, saida ta wanke komai da tayi amfani dashi ta mayar mazauninsa snn ta bar kitchen din ta haura sama, cikinta ɗam ɗam dan ji take ita da abinci kam sai gobe kuma.

★Maama na kallon Maimuna da take ƙoƙarin saka hijab tace "wai ina zaki a haka Mainuna.. jifa fuskarki ko gama saɓewa ba tayi ba..", Maimuna da tayi ɗaurin ɗan kwali har goshi tace "kai Maama ba fa daɗewa zanyi ba, nan nan zanje na dawo..", Maama tace "nan nan ina..?", Maimuna tace "kai jaraba" ta ciro wata fatattakakkiyar dari biyu daga bra ta linƙawa Maama a ƙirji tace "yanzun nan zan dawo..", Maama ta dafe ɗari biyun tace "karki daɗe", Maimuna ta ƙarasa saka hijab dinta ta fita, bayan ta saka takalmanta dake bakin ƙofa tayi soro, can ta gangara cikin lugunsa har ta ɓulla wani lungun, daga nan tayi tafiyar da bata wuce ta minti biyar ba sai gata a wani kango wanda aka zagayesa da blocks sai gate na langa langa, tin kafin ma ta ƙarasa cikin kangon ta fara jin warin kayan zuƙe zuƙe, haka nan ta dake ta shiga kangon, su biyar ne a zaune a kangon matasa dasu babu wanda ya haura ashirin da bakwai a cikinsu, wanda ya fara hangota ya cire cigarette da yake zuƙa yace "ke ubanki kika kalla anan...?", Maimuna tace "ƙwage nake nema..", wani daga can gefe wanda ya fisu shekaru bakinsa baƙi ƙirin ya kalleta a wulaƙance, Wiwin dake hannunsa ya yiwa mummunar zuƙa ya fesar da hayaƙin ta hanci da baki tamkar salansar tsohon babur yace "ke yarinya yane... kin kawomin kanki ne dan na tuɓeki..?", Maimuna tace "haba ƙwage ai kasan nafi ƙarfin ka... harƙalla na kawo maka..", Ƙwage ya tashi ya matsa kusa da ita yace "meye..?" yana cigaba da busa wiwi, ta fara lalube cikin hijab dinta ta ciro kuɗi masu ɗan kauri a ƙalla zasu kai 10k ta miƙa masa, wurgar da ragowar wiwin yayi ya murjeta a ƙasa ya amshe kuɗin, Maimuna tace "kasan Mu'azzam ɗan gidan gini..?", Wani ne ya taso yana kallon hannun Ƙwage yace "kai wnn yaron fa nunar rana take nufi, ke ba ƴar gidansu bace ai naga yayanki ne..?", Maimuna tace "Eh ɗan kishiyar Baabarmu ne..", yace "A'a malama baabarki dai ba tamu ba..", Ƙwage yace "kai zan feɗe ka da rai nace ka sako bakinka ne..?", Bisi ƙwale yace "haba gorun goruba naga harkar nan tare muke yinta ai karka mana eh yane faa..", Ƙwage yayi kwafa yace "ina jinki", Maimuna tace "Shi nunar ranar Mu'azzam nake so ku masa dukan tsiya..", Ƙwage yace "Au abin sauƙi, ai ko cewa kikai mu ƙaddamar masa wllh a yau sai yaro ya ziyarci barzahu..", Maimuna tace "ku lakaɗa masa na jaki..", zuciyar Maimuna ba tada maraba da kindirmon nono sbd fari haka ta koma gida, tana shiga ɗaki ta cire hijab ta bage akan gado, Maama ta bita da idanu tace "har kin dawo...?", Maimuna tace "gashi kin gani", Maama tace "sai naji kamar kina warin Wiwi", a hasale Maimuna ta miƙe zaune tace "wiwi kuma Maama..?", Nabilah dake zaune ɗakin tana tsince shinkafa tace "nima naji wllh...", harara Maimuna ta bisu da ita ta koma ta kwanta tana jan dogon tsaki. Da yamma Umma na zaune bakin murhu tana kwasar tuwo, Mu'azzam ya shigo gidan da sallama, ya durƙusa gaban Umma ya gaisheta, da fara'a ta amsa masa tace "an dawo lfy ya aiki..?", yace "Alhmdllh Umma, yau mun gama da gidan ma har an biya mu zuwa jibi zamu tafi Katsina wani aikin..", Umma tace "toh alhmdllh, Allah ya temaka..", yace "Ameen Umma ga wnn.." ya ajiye mata ledar da ya shigo da ita, tace "toh madallah, Allah yayi albarka, ga can abincinka a ɗaki", yace "toh" ya tashi ya shiga ɗakinta ya ɗauki warmern abincinsa, daga nan ya shiga ɗakinsu, Maimuna dake laɓe jikin window tana leƙensa tayi kwafa ta koma ta zauna, Umma ta gama kwashe tuwon ta ɗauka ta kai ɗaki tare da ledar da Mu'azzam ya kawo mata, ta buɗe ledar taga lemo da Ayaba sai kuma ɗan tsire ne ciki, murmushi tayi ta ajiye kan mirror, Sabra ce ta shigo da gudu tana haki tace "Umma Yaya ya dawo...?", Umma tace "ba zaki dena guje gujen nan ba ko dan kinga Addarki ba tanan ne?", Sabra tace "ya haƙuri Umma", Umma ta shafa kanta ta ɗauki lemo ɗaya Ayaba ɗaya ta bata tace "zauna kici". Mu'azzam na alwala bakin rariya zai wuce masallaci dan daf ake da kiran sallar magrib, yana idar da alwalar ya fita daga gidan, bayan Umma ta idar da sallahr Isha'i tana zaune kan darduma tana lazimi, sallama akay daga soro, Maama da ƴaƴanta babu wanda ya amsa Nabilah kuma da ta ɗan fara shiryuwa sallah take, ga Baba ma baya nan ya fita masallaci, Umma ta ajiye carbin da take lazimi ta fita, daga bakin ƙofar soron ta tsaya, bata kai ga magana ba Naseer ya shigo, gaisawa Sukay da Munkaila wanda shine yayi sallamar, Munkaila yace "ina Baban naku..?", Naseer yace "yana masallaci..", Munkaila ya numfasa yace "toh muje da kai, ban san me ya haɗa Mu'azzam da fitinannun yaran nan ba gashi can sun sassara sa, yanzu haka dai an wuce dashi emergency..." ganin Umma kawai sukay a soron tace "innalillah wa'inna ilayhirraji'un.. wane Mu'azzam din.."

★Nurain yayi parking motarsa a wani babban eatery, fitowa yayi daga motar ya shiga eatery din, a vacant table na two sitters ya zauna, tini waitress ta kawo masa food menu, bayan ya gama order abinda yake so waitress din ta tafi kawo masa, dice watermelon da Orange juice aka fara serving dinsa as a starter, gently yake sipping orange juice din yana latsa wayarsa, Tamkar ɓera a buta hka ta shigo Eatery din tana rarraba idanu, tana hangosa ta nufi table din da yake zaune, ta ja kujera ta zauna gami da zuba masa idanu, ajiye glass cup din lemon yayi ya fara shirin miƙewa, da sauri ta riƙo hannunsa tace "dan girma Allah listen to me ko sau ɗaya ne..", fasa tashin yayi da sigar ko in kula murya ƙasan maƙoshi yace "what..?", duk da Ruqayyah taji haushin yadda yayi treating dinta these days amma bata nuna ba, gyara zama tayi tana kallonsa tace "Dr dan Allah don't take grudge against me, ba wai na tafi bane sbd bana son na aureka, ba a fahimce ni bane from the start..", keenly yace "Ohk, then stop following me..", Ruqayyah ta haɗiye kukan da ya taho mata tace "shknn, nasan har yanxu fishi kake dani Dearest..", yana latsa wayarsa yace "not at all..", tace "nagode da ka tsaya, har yanzu ban canza daga Ruqayyahn da ka sanni ba, i still remains your first love and only kuma your wife to be, zan aureka Dearest, a shirye nke ko yanxu ma kaje wajen Daddy za ai mana aure Dearest..", a lokaci na farko da ya ɗago kansa ya kalleta kafin ya dauki orange juice yayi sipping yace "Ruqayyah..", murya na rawa tace "Na'am", yace "a lokacin da nayi dating dinki kinsan duk abinda na bari na barsa knn", ta gyaɗa kai idanunta na ciccikowa, yace "snn kin san banida ra'ayin auren mata sama da ɗaya..", nan ma ta gyaɗa masa kai tace "amma why are you saying that bayan baka da aure..?", ya girgiza kai yace "you are wrong" da haka ya kira waitress yace ai masa packaging abincin da yayi order, Ruqayyah dai ta kasa mgn cause tana buƙatar concrete explanation, wayarsa ya saka a pocket ya tashi zai biya bill, cashier ya nufa ya biya bill din ya amshi ledar abincin ya nufi exist, da sauri Ruqayyah tabi bayansa tace "wllh Allah ban fahimci me kake cewa ba, kuma baka bani enough time na maka bayani ba..", yayi ajiyar zuciya yace "i don't like it idan kina bina hka, please stay away from me, i don't have any feelings for you now, snn kuma i am married.. good luck..", da haka ya nufi motarsa ya shiga ya bar Eatery din, Ruqayyah taga kamar birds ne suke yawo a kanta kafin ta fara ganin harabar Eatery din bibbiyu daga nan kuma bata sake fahimtar halin da take ciki ba. farkawa tayi ta ganta a restroom na Eatery din mutum har huɗu akanta, ta miƙe zaune tana kallonsu kafin ta dafe kanta, wata mata ce tace "Alhmdllh sannu ko..", Ruqayyah ba ta iya cewa komai ba kawai binsu take da idanu, wani mutum wanda shima staff ne a Eateryn yace "ki bamu contact din wani naki a kira a gaya musu halin da kike ciki..", a hankali Ruqayyah ta girgiza masa kai tace "no need ngd sosai..", ta miƙe da kyar kanta na sarawa, waitress din da itama ke wajen ta miƙa mata ragowar bottle water da aka yayyafa mata ta farfaɗo tace "ga ruwa ko zaki sha..", Ruqayyah ta girgiza kai tace "nagode.." ta nufi ƙofa zata fita, mutumin ya sake cewa "da dai kin jira an kira ƴan uwan naki hajiya", bata tanka masa ba sbd ita kaɗai tasan abinda take ji, da kyar ta kai kanta bakin titi ta tsari napep, ba ta ma gaya masa inda zai kaita ba kawai ta shiga, saida suka fara tafiya snn ta gaya masa inda zata, Ruqayyah na zuwa gida direct hanyar room dinta ta nufa, Momy dake zaune palour ta bita da kallo tace "baki da lfy ne..?", gyaɗa mata kai Ruqayyah tayi, Momy tace "sannu..", room dinta ta wuce zuciyarta kamar an ɗora mata dutse, tayi wurgi da handbag dinta a kan bed kafin itama ta zube akan bed din, Momy ce ta shigo da plate din abinci da ruwa, ganin Ruqayyah a kwance ta ajiye plate din akan mirror ta iso bakin gadon tana feeling body temp dinta, jikin nata zafi ramm, with care Momy tace "zazzaɓi kike ne Ruqayyah..?", Ruqayyah ta yunƙure ta miƙe hawaye na zuba idanunta wani nabin wani, sosai hankalin Momy ya tashi ta zauna gefen gadon, Ruqayyah ta ɗora kanta a kafaɗar Momy ta fashe da kuka mai ƙarfi tace "Momy kiyi haƙuri, am so sorry".

★Ƙarfe takwas da rabi Nurain ya isa gidansa, basket din abinci da ya taho dashi daga gidansu ya ɗauka kafin ya fito daga motar, ya ciro ledar take away na abinci da ya siya baici ba dan tinda ya saka a motar baima bi takansa ba, Inuwa ya bawa ledar abincin ya wuce ciki da basket na abincin gidansu, upstairs ya haura yayi refreshing kansa kafin ya sakko sanye da white pajamas ya shiga kitchen ya ɗakko plate da spoon da drink, saida yayi powering TV snn ya zauna cin abincin, ko rabin abincin bai ci ba ya ajiye spoon din yana kallon stairs, lokaci guda ya miƙe ya haura saman, toh me tasamu taci bayan ya kashe mata gas, har ga Allah mantawa yayi ya bawa Inuwa ya siyo mata Charcoal ko firewood da safe in yaso sai tayi amfani dasu tayi girkin, still yayi a corridor yana kallon ƙofar ɗakinta, ya haɗe gira ya murɗa door handle ya shiga, yayi sallama ƙasa ƙasa, Hajar ta ajiye wayarta kan mirror ta dubi ƙofar, tin ɗazu take kiran Umma amma no respond, suna haɗa ido dashi ta murtuke fuska ta galla masa harara ta ɗauke kai, duk da ya lura da hakan amma he don't care, with a repartee yace "hey..", bata bari taji sauran maganar ba ta katsesa da fadin "can kaje ka nemo hey dinka nan Hajar ce ba Hey ba", Nurain was more than shock jin abinda ta faɗa, furiously yace "young lady, na fahimci kanki na rawa kuma baki da kunya, amma please enough don't try me..", wani irin yamutsa fuska tayi tace "Au haba, so kake na ɗauki mayafi na kirma a ka na rufe fuskata shine zan zama me kunya ko me.." haɗiye sauran maganar tayi ganinsa a gabanta, ita dai bata san lokacin da har ya taho yazo gabanta ba, wani mugun bugu zuciyarta ta fara yi, ta ja baya da sauri tana zare ido, tana ƙoƙarin sake ja da baya ya kama dukka hannayenta ya mayar dasu baya ya rutsasu duka da hannu ɗaya, riƙo bana wasa ya mata ba don ji tayi kamar shoulders ɗinta zasu karye, turo baki tayi tace "malam ni ka sake..", bata gama maganar ba yasa finger ya ɗalle bakin rashin kunyar, tini Hajar tayi shiru tana jin azaba a lips ɗinta, yana ganin ta fara motsa lips alamar za tay magana ya sake ɗalle bakin, gashi ta gagara motsi babban weapon dinta kuma an hanata amfani dashi wato her mouth, motsa lips din ta sake yi nan ma ya ɗallesa, tini lips din kwa sukay jajir, thick eyebrows dinsa a matuƙar haɗe yake kallon fuskarta, wani yunƙuri tayi zata fixge, da sauri ya kuma matseta ya ɗalle lips din a karo na huɗu, lulu eyes ɗinta ya kalla da suka cika taff da hawaye, lokaci guda tears din suka fara zarya kan kuncinta.....✍️
💛 HAJAR 💛

{51..}
Hajar tafi minti ashirin tsaye bakin titi tin fitowarta daga gida kafin ta samu abin hawa, ta gayawa mai napep din inda zai kaita, bayan tafiyar rabin awa suka iso, ta sauka daga napep din ta buɗe hand bag ta ciro 1k ta basa, ya bata canji da haka ta shiga gate din asibitin, can jikin wata bishiya ta tsaya ta ciro wayarta tayi dialing numbern Umma, Umma na picking Hajar tace "Umma kuna emergency room ko..?", Umma tayi jimm kafin tace "badai fitowa kikay ba Hajara..?", Hajar ta sunkuyar da kanta tace "fitowa nayi gani ma a asibitin..", Umma tayi ajiyar zuciya tace "toh kinga dai yanzu ni ina gida ban taho ba amma mal da Nasiru na nan..", Hajar tace "toh bari na shiga kafin kizo.." da haka ta katse wayar, wani worker ta tmbya ina Emergency room yayi leading dinta, gradually ta fara duba ko wane bed bayan shigarta E.R din, Naseer ta fara hangowa aikam ta nufi wajen, tana zuwa gaban gadon da Mu'azzam yake ta durƙusa har ƙasa ta gaida Baba, Baba ya amsa yana ƙare mata kallo, ta gaida Naseer ma, yace "lfy lou Hajar ykk, ygida..?", tace "lfy lou Yaya, ya aiki..?", yace "alhmdllh..", tashi tayi tana kallon Mu'azzam dake jingine da gado, shima kallonta yake, hankalinta ya mugun tashi ganin condition dinsa, ta dubi Naseer tace "Yaya hatsari yayi ne..?" don Umma bata gaya mata ainahin me ya faru ba kawai tace mata bashi da lfy suna asibiti, Naseer yace "ke karki ɗaga mna hankali..", ta ringa kallon Mu'azzam idonta ya ciko taf da ruwa tace "sannu Yaya". babu jimawa da zuwan Hajar saiga Umma tare da Sabra, da gudu Sabra taje ta rungume Hajar, Hajar tayi murmushi a takaice tace "ashe dai kina sona ƴar kanwata..", Baba ya tashi daga kan kujerar da yake ya ciro kuɗi daga aljihu ya bawa Umma yace "ko za a buƙaci wani abun", Umma ta karɓa tace "tom", yace "sai anjima..", Naseer ya tashi shima don tare zasu tafi da Baban yace "Umma saina dawo da daddare, zanje wajen police din ma akan case din, ya kamata a kama yaran nan...", Umma tace "toh Nasiru, Allah yayi albarka..", yace "Ameen" snn ya bar room din, Hajar tace "Umma hatsari yayi ne naji Yaya Naseer yace zaije police station...", Umma tace "ba hatsari yayi ba ƴan daba ne suka farr masa..", Hajar ta zaro ido tace "innalillah wa'inna ilayhirraji'un", sai kuma ta dubi Mu'azzam tana kallon inda aka sassaresa a jiki, Umma ta rausayar da kai ta buɗe ledar abinci da ta zo da ita, ta zuba masa abincin, da kanta ta ringa basa yana ci sbd karayar dake hannunsa. wajajen ƙarshe uku da rabi sai ga Anty Jamilah tare da Abdallah dake riƙe da basket, Anty suka gaisa da Umma ta mata ya me jiki, Abdallah ya russuna yace "Umma ina wuni, ya me jiki...?", Umma tace "alhmdllh, ya kasuwa..?", yace "alhmdllh..", Umma tace "madallah..", da mamaki Anty take kallon Hajar da ta gaisheta, Anty ta riƙe haɓa tace "ita kuma wnn har ta fara fita..?", Hajar ta sunkuyar da kanta ba tace komai ba, Umma tace "nima dai hka nagani, yanzu nke shirin ce mata ta tashi ta tafi ban kai ga gya mata ba sai gaku..", Anty tace "ai ya kamata dai ki tashi haka Hajar, ina ma laifi dan ma dai ɗan uwanki ne ba lfy..", wani tashin hankali ne ya baibaiye Hajar, ji take kamar ta kurma ihu tsabar baƙin ciki, itafa bazata koma gidan nan ba wlllh tllh, ko wace walle walle za ai ayita ta ƙare, da kyar ta iya cewa "ana yin sallar la'asar zan tafii..", Anty tace "ai la'sar din ta kusa..", tashin hankalin Hajar bai linku ba saida taji kiran sallah, Anty ta shimfiɗa dardumar da tazo da ita ta kabbara sallah, tana idarwa Umma ta miƙawa Hajar ƴar purse ɗinta tace "riƙe min nayi sallah". Hajar ta saka ƴar purse din a hijab, a hankali ta zuge zip dinta ta fara lalube, can ƙasan purse din ta jiyo keys, ta ciro keys din ta buɗe tata jakar ta saka a ciki, Umma na idar da Sallah tace "toh Hajara ayi harama..", Hajar tace "toh Umma bari nayi sallah..", tana idar da sallar tayi musu sallama ta fita, tana fita taji ance "Hajar..", ta juyo taga Anty ce, Anty ta ƙarasa har inda take tana mata kallon tsanake tace "Hajar Allah yasa dai baki ɗaga hankalinki a gidan ki ba.. idan da akwai matsala ki gaya min..", Hajar tayi rau rau da ido ta shanye kukan da yake shirin taho mata tace "A'a Anty babu wata matsala faa kawai dai nayi missing su Umma ne..", Anty tayi ajiyar zuciya tace "toh alhmdllh, toh ki kwantar da hankalinki kinji, karki sawa kanki damuwa ko wace mace a haka ta saba da gidan mijin, ai kowa yana son gidansu..", Hajar ta gyaɗa kai don huɗubar Anty bata shigeta ba bare tayi tasiri, abinda ta ƙulla shi zata warzar yanzu ma kuwa, tace "toh Anty ki gaida min da Hafsah" da haka sukay sallama, Hajar na fita bakin titi ta tsari napep tace "Dala zaka kaini..", mai napep ya gyaɗa kai ya gaya mata kudi, a bakin layin gidansu ta sauka bayan sun zo unguwar, a hankali ta shiga lungun ta wuce gida, da ido Maimuna da ta fito daga wanka ta bita tana taɓe baki, Hajar ko kallon inda take ba tayi ba ta wuce ƙofar ɗakin Umma ta ciro keys din da ta ɗauka ta buɗe padlock din ta shiga, rufe ƙofar tayi ta saka sakata, ta faɗa kan gado tana sauke ajiyar zuciya. Maimuna ta shiga ɗaki tana kallon Maama tace "ko me tazo yi oho..", Maama tace "wa knn..?", Maimuna tace "Hajara mna gata can ta buɗe ɗakin uwar ta shiga ta rufe..", Maama tace "ita Hajarar ce tazo gidan nan", Maimuna ta taɓe baki tace "ita fa", kwandon kayan shafa ta ɗakko ta zauna ta buɗe BSC cream ta lafta a fuska. saida aka kira sallar magrib Hajar ta fito tayi alwala ta sake komawa ɗakin ta rufe, ta haɗe kanta da guiwa bayan ta idar da sallar isha'i. wajen takwas da rabi Umma ta dawo, ta buɗe ƴar purse dinta zata ɗauki muƙulli, wayam taga babu alamar mukulli a jakar, ta kunna torch light din wayarta don babu nepa a gari tana haska alhargar ƙofar taga a buɗe, sai a lokacin ta lura da hasken dake ɗakin ta jikin window, jikin windown ta isa ta bankaɗa labule tana kallon cikin ɗakin tace "waye a nan", Hajar ta kalli window ta tashi ta buɗe ƙofar, Umma ta ringa kallonta don ta rasa ma me zatace mata, Sabra tace "laa Adda anan zaki kwana..?", Hajar dai na tsaye a inda take tamkar wacca aka dasa, Umma ta shiga ɗakin ta samu gefen gado ta zauna still idanunta na kan Hajar, Hajar ta sulale ƙasa daga nan inda take ta fashe da kuka tace "Umma... Umma.. bazan iya zaman auren nan ba wllh.."

★Nurain yayi folding din takardar da ya gama karantawa ya saka a pocket, ajiyar zuciya yayi yana kallon stairs kafin ya tafi ya haura, room dinta ya buɗe ya shiga to make sure, ya ƙarewa ɗakin kallo yaga dai babu alamarta anan, har bathroom ya buɗe ya duba, har zai fita daga ɗakin sai kuma ya dawo ya buɗe wardrobe, baiga alamar ta dauki kaya ba, fita yayi daga ɗakin ya sauka downstairs, ya shafa cikakkiyar sumarsa maganganun Abba na yawo a brain dinsa, compound ya fita thinking of what to do, ya sake shafa kansa kawai ya nufi ɗakin mai gadi, sallama ya masa, Inuwa ya fito ya russuna yace "Alhj", Nurain yace "kamar ƙarfe nawa ta fita daga gidan nan..", Inuwa yace "Hajiya..?", Nurain yace "Eh..", Inuwa yace "wajajen ƙarfe biyu..", Nurain ya gyaɗa kai yace "buɗe min gate..", Inuwa yace "tom" ya tafi ya fara buɗe gate din, Nurain ya nufi parking space, motarsa ya buɗe ya shiga, yafi minti biyar zaune a motar kafin ya kunnata, driving slowly ya fita daga compound din, yana hawa saman titi ya take accelerator, with speed yake driving, yana shiga unguwar ya rage gudun cause kwaltar a ragargaje take, gefen titi ya samu ya parker motar yana kallon lungun, unguwar duhu dunɗum sbd babu nepa sai fitilu na masu shagon chajin waya da provision, bai san wane bayanin zaiwa Abba ba hakan shine one Solution dinsa, buɗe motar yayi ya fito yana ƙarewa unguwar kallo, gently ya fara tafiya ya shiga lungun, tsaye yayi a ƙofar gidan, luckily for him yaga wani yaro zai wuce, kiran yaron yayi yace "shiga nan gidan kace Hajar tazo...", yaron yace "tom" ya shiga gidan da gudu, Umma na tsaye bakin ƙofar ɗakinta tare da Naseer da yake mgana ƙasa ƙasa kar Maama ta jiyosa, Umma tace "yanzu an kama yaran..?", Naseer yace "an kama mutum biyu saura uku, tinda an kama Ogan nasu suma za'a kamosu ɗaya bayan ɗaya..", Umma tace "dan Allah Nasiru a musu kwatankwacin abinda sukama yaron nan..", Naseer yace "ai sai sun ɗanɗana kuɗarsu Umma, na bawa ƴan sandar wani abu..", Umma ta gyaɗa kai tana jin wani sanyi a ranta tace "yauwa..", yace "bari na tafi asibitin..", Umma tace "toh da yake ma Abdallah na can tare dashi..", a daidai nan yaron ya shigo yace "wai Hajar tazo inji wani..", Naseer ya kalli Umma yace "daga asibitin nan tayo..?", Umma tayi ajiyar zuciya tace "Eh.." sai kuma tayi shiru ta rasa abin faɗa, Naseer yace "ai saita fito ko mijin tane yazo tafiya da ita.." sai kuma ya dubi yaron dake tsaye yace "kace gata nan..", yaron ya fita da gudu, har lokacin Nurain na tsaye bakin ƙofa ko soron bai shiga ba, tunani yake is he doing the right thing, ɗari biyar ya damƙa a hannun yaron yace "good boy", Naseer ne ya fito bayan ya yiwa Umma sallama, yana ganin Nurain a ƙofar gidan ya miƙa masa hannu sukay musabaha, kallon Nurain yake a tsanake yace "ko kaine kake kiran Hajar..?", Nurain yace "yeah..", Naseer yace "kai ne mijin nata..?", Nurain yace "yeah..", Naseer yace "kayi haƙuri fa na cika ka da tmbya, duba da yadda auren ya kasance shiyasa nake tamby tinda ban sanka ba, anyway ni yayanta ne..", Nurain yace "Okay nice to meet you..", Naseer ya sake miƙa masa hannu yace "same" sai kuma ya kalli cikin gida kafin ya koma ciki. Umma na kallon Hajar da take ta sharar hawaye tace "toh ni yanzu ya zan miki Hajara, na tmbayeki dalili kince min ba komai, komai fa saida dalili, haka kurum bazan tunkari mal nace akashe miki aure ba, yanzu idan kika gyamin dalili kinga na samu hujjar da zan goya miki baya a wajen mal, ba kiji farin cikin da mahaifinki yake ba da wnn auren, yace Allah ya zaɓa miki miji na gari, juma'ar da ta wuce mijin naki da mahaifinsa suka zo har nan yaron ya gaida mal, nutsuwa da hankali ai suna bayyana kansu, mal yace shi dai baiga aibun wanda ya aura miki ba, kema yanxu na tambayeki kin ƙi bani amsa, kin san dai mahaifinki ba lfy ya cika ba idan kina so ciwonsa ya tashi ta dalilinki toh maza ki ɗau harama Hajara..", Hajar ta cigaba da sharar hawaye nan ma ba tace komai ba, Umma tace "A zamanin da haka ake auren, toh kema mahaifinki ya miki zaɓi amma kina ƙoƙarin bijire masa, idan kina samun wata matsalar ne a gidan naki ki faɗa in yaso sai iyaye su shiga idan zaman naku bazai yiwu ba sai a raba, akwai matsala ne..?", Hajar ta girgiza kai, Umma tayi ajiyar zuciya tace "toh shknn, zan turo Jamilah kuyi magana da ita, mal din ma zan masa mgana, kinga ynxu hankalinsa ba a kwance yake ba, tashi ki tafi kar ya dawo ya sameki a gidan nan .." Naseer da ya shigo gidan ya tsaya bakin window yace "ke Hajar kin bar mutum a tsaye fa..", Umma tace "gata nan". saida Hajar ta share minti uku wajen saka hijab da ɗaukar jaka, kamar wata chameleon haka take acting, murtuke fuska tayi ta fita soro, tin kafin ma ta kai bakin ƙofa hancinta ya shaƙi scent dinsa, yana ganinta yaji wani relief cause he can't imagine abinda Abba zai masa, ba tare da ta dubesa ba tace "takardar ka kawo..?", yace "yeah ita na kawo miki..", wani sanyi taji har cikin ranta, ta juya ta zuba masa lulu eyes dinta ta miƙa hannu tace "kawo..", duk da duhun dare saida ya lura da hasken hannun nata da taimako hasken farin wata, yace "ohk, ai takardar na mota idan kina so kizo ki amsa", yana gama faɗin haka ya juya ya fara tafiya, tabi bayansa da harara sai kuma ta bisa walking slowly, yana fita bakin titi ya tsaya kusa da motar yana jira ta ƙaraso, tana ƙarasowa ya danna mabuɗin motar da keys din hannunsa, cike da tsiwa tace "bani", ya buɗe front seat ya ciro papern dake aljihunsa ya ajiye kan seat yace "pick it..", ta wani galla masa harara ta wuce ta ɗauka, da sauri ya koma ta bayanta ya turata cikin motar, ta zabura zata bar wajen hakan yasa yayi wrapping dinta a ƙirjinsa, tana shirin kwala ihu ya toshe mata baki, within few seconds ya sakata a motar ya kulle, saida ya zaga driver seat snn ya sake buɗe motar ya shiga, dukan glass din motar ta fara yi tana cewa "malam ka buɗe min ƙofa na fita", Nurain kam resting yayi da kujera yana sauke ajiyar zuciya, a hankali yace "damn it", tana jin ya kunna motar ta kwala wani uban ihu sai kuma ta fashe da kuka ta haɗe kanta da guiwa, shi dai baice mata ƙala ba ya fara driving dinsa, a wani eatery ya tsaya yayi take away snn ya fito, back seat ya buɗe ya ajiye ledar abincin kafin ya shiga driver seat, har suka je gida Hajar bata dena kuka ba, bayan yayi parking motar ya buɗe ya fito, ledar abincin ya ɗauka ya zaga side din da take ya buɗe yace "come down..", a hankali ta zuro ƙafafuwanta ta sakko, ya mayar da ƙofar ya rufe snn ya kulle motar, hannunta ya figa suka wuce ciki, saida ya haura har sama da ita snn ya saketa bayan sun shiga har room dinta, ledar abincin ya ajiye nan kan chest of drawers yace "ba takardar saki kika ce na baki ba toh ai gata nan na baki..", Hajar ta dubi papern da ta dunƙule a hannu sai kuma ta ɗago tana kallonsa, ya ɗaga shoulder ya fita daga ɗakin, da sauri ta shiga warware papern hannunta har na rawa, kawai ta tsinci rubutunta a jiki, wurgi tayi da ita ta sulale ƙasa ta fashe da kuka, ji tayi hijab dinta na ƙamshinsa, ta tashi ta cire hijab din ta shiga bathroom ta wanke fuskarta, sai kuma taji tana son tayi wanka, saida tayo wankan snn ta fito da wata azababbiyar yunwa, tin safe babu abinda ta zubawa cikinta ko ruwa, turo baki tayi ta ringa kallon ledar abincin da ya ajiye mata, ta saka kayan bacci snn tazo ta ɗauki ledar ta buɗe. washe gari da safe Nurain na zaune palourn downstairs yana shan Coffee, ga laptop gefensa yana operating, Hajar ce ta sauko ƙasa da ledar abinci a hannunta, kallo ɗaya ta masa ta ɗauke kanta, kitchen yaga ta shiga, ya ajiye coffee cup din ya tashi ya bita kitchen din....✍️
you can join my WhatsApp group by clicking the link below
💛 HAJAR 💛

{52..}
Hajar ta ajiye ledar hannunta kan cabinet, juyowa tayi jin motsi a bayanta, ba tare da ya dubeta ba yayi folding hands yana kallon gas cooker yace "kin iya amfani dashi..?", ta kalli gas cooker din sai kuma ta dubesa tace "A'a saika koyamin..", nodding kansa yayi don ya gane kalar amsar da ta basa, now bazai biye mata ba, without looking at her yace "alright.." ya ƙarasa gaban gas din ya ɗauki lighter ya kunna sai kuma ya dubeta yace "like this.. idan zaki rage wuta da ƙarawa duk da control knob din za kiyi amfani.. kin gane..?", ta juya lulu eyes dinta tace "Eh nagane.." yace "fyn" ya bude fridge ya ɗauki raspberry drink na kwali, cupboard ya buɗe ya ɗauki glasscup, har zai bar kitchen din sai kuma ya dakata yace "i told you babu gage a nan duk abinda kika gani a kitchen din nan idan kina so ki dauka kici.." da haka ya buɗe ƙofa ya fita, ta taɓe baki ta riƙe haɓa tace "nida jangwangwan ai dole ka tmbyeni na iya amfani da gas sbd kaje gidanmu, toh koda nake ƴar malam shehu naje makaranta, koda ilimina ai na kunna shege gas..", Noodles ta dafa ta zauna nan kitchen din taci, tana gama ci ta buɗe fridge ta ɗauki ruwa ta sha, saida ta gyara kitchen din ta wanke komai snn ta fita, har lokacin Nurain na zaune palourn, daman ko gigin kallon position din da yake ba tayi ba ta haura sama, ya tashi ya shiga kitchen din yana ƴan dube dube, komai na nan a mazauninsa babu alamar anyi girki, ya fito kitchen din ya zauna yayi crossing legs ya cigaba da aikinsa jikin Laptop. Hajar ta kimtsa ɗalinta sama sama kafin ta shiga bathroom, ruwan zafi ta tara a bucket ta fito tana jiran ya kai yadda take so, wayarta dake jone a charge ta cire ta shiga kiran Umma, Umma na picking Hajar tace "Umma ina kwana..", a takaice Umma ta amsa tace "kunje gida lfy..?", Hajar tace "Eh Umma ya jikin Yayan..?", Umma tace "jiki alhmdllh..", Hajar tace "toh Allah ya ƙara afuwa..", Umma tace "Ameen, Allah ya miki albarka..", da haka suka katse kiran, Hajar na shirin ajiye wayar ta tina da ruwan zafin da ta tara a bucket, tsabar sauri bata iya ajiye wayar ba ta tafi da ita bathroom din, ai kam ruwan ya cika bucket din dam, ta zaro ido ta tafi zata kashe, wani irin santsi ne ya ɗebeta suuu tana shirin sulewa a ƙasa tayi sauri ta dafa kan pampo, pressure da ta bayar a pampon yasa wayar hannunta ta suɓuce ta faɗa cikin bucket din ruwan zafin, gwalo ido tayi tana shirin kelayar da ruwan zafin sai kuma ta fasa sanin hakan babu kyau, ga wayarta tsamo tsamo ta lume can ƙasan bucket din, bowl din diban ruwa ta ɗauka ta kanfato ruwan tare da wayar, da sauri ta tsame wayar ta hau bibbigeta a hannu, ta fito daga toilet din still tana bibbige wayar, ta zauna gefen gado tana gogeta da ƙasan rigarta, ta danna switch ta kunnata, sai gashi ta kawo few seconds da kawowarta sai kuma ta fara farfaɗiya daga nan kuma ta ɗauke gaba ɗaya, babu irin dabarar da Hajar bata gwada ba amma waya taƙi kamawa, daga ƙarshe ta ajiyeta kan mirror a daidai saitin AC, gaba ɗaya jikinta yayi sanyi yanxu idan wayarta bata tashi ba dame zata ringa communicating da ƴan uwanta, bathroom ta shiga tayi wanka da ruwan da ta tara don har ya huce, tana fitowa ta sake gwada kunna wayar amma bata tashi ba, ta gama shiryawa tsaf bayan ta saka wata doguwar riga material wacca akaiwa ɗinkin tsuke baby armless da tail, sai kace wata yarinya haka kayan suka mayar da ita. tanata zaune a ɗaki abin duniya ya isheta ƴar wayar da take rage mata zafi ma ta margaya, a haka har akay sallar Azahar ta tashi tayi, linke dardumar da hijab din tayi ta ajiye, ta gyara hular kanta ta fita daga ɗakin, a hankali ta sauka daga stairs tana jin kamar ta kurma ihu sbd a maƙoshi lalacewar wayar ya tsaya mata, tana kaiwa tsakiyar palour aka buɗe ƙofa aka shigo, tsaye tayi tana kallonsa don ita a tunaninta baya nan, kallon da ta lura yana mata ne yasa ta dubi kanta, wani irin gwalo idanu waje tayi ta ruga da gudu ta koma sama, Nurain ya taɓe baki ya ƙarasa shigowa ciki, yau Saturday babu inda yaje yanxun ma daga masallaci ya dawo, kan doguwar kujera ya hau ya kwanta ya miƙar da legs dinsa, a haka yake amfani da wayarsa, stairs ya duba jin footsteps, lokaci guda ya ɗauke kansa ya cigaba da kallon wayarsa, a zuciyarsa yace what is she covering, Hajar na shiga kitchen ta tattare hijab din da ta zumbula ta fara tunanin me zata girka, bai ɗauketa wani lokaci mai yawa ba ta fara sarrafa wata haɗaɗɗiyar jollof rice wacca ta zuba mata isasshen kifi da kayan miya exclude tomato. Nurain ya tashi daga kwancen da yake yana kallon ƙofar kitchen din, da hannu ya ja pointed nose dinsa jin wani aroma da yake hudasa, hancinsa ya ringa perceiving aroman ba ƙaƙƙautawa, ji yayi stomach dinsa na shaking ya tashi da sauri ya zura room slippers dinsa ya wuce sama. Hajar na gama girkinta tayi serving kanta a plate, ta juye ragowar a warmer ta haura sama da ita. wajen ƙarfe biyar da minti huɗu tana zaune kan stool tana combing hair dinta, gwara dai ta yiwa kanta qiyamul layli tinda ynxu ba ta gida bare Umma ta taimaka mata, don idan ta bari kanta ya danƙare saita gane kurenta, slowly take combing hair din tana yamutsa fuska, wai ma a hakan saida ta jiƙasa da oil, ƙofa aka buɗe aka shigo tare da sallama ciki ciki da murya mai zurfi, ɗaga kanta tayi sukay ido huɗu dashi, ta haɗe gira ta ajiye comb din hannunta kan mirror tace "nifa ka dena shigo min babu notice..", yayi folding hands dinsa a ƙirji yace "bayan sallamar da nayi akwai wani abu bayan ita ne..?", ta miƙe tsaye tana mayar da gashin daya rufe mata fuska baya tace "Amma dai kasan babu kyau, kai ba muharrami na bane dan haka bai kamata ka ringa shigo min ɗaki babu sanarwa ba..", yace "Ohh really, su iyayen naki basu gaya miki me suka miki ba kafin a kawoki nan din", ta yamutsa fuska tace "me kwa aka min din.. nidae ka dena shigomin ɗaki ehe..", sai kuma ta fara gunguni ƙasa ƙasa tana cewa "hka kurum zai kalleni a bati", zamm yaji abinda ta faɗa don yanada sharp hearing mechanisms, yace "ke!! kinje islamic school kuwa..?", cike da tsiwa tace "A'a jira nake kazo ka kaini aii..", tana ganin ya fara tunkarota tayi baya tana turo baki, ya ajiye wayarsa kan mirror, kafin ta ƙara one step backwards yayi wuff ya cafke hannunta, yace "idan bazaki gaji ba nima bazan gaji ba..", tana jin zai ɗaure mata hannaye a baya ta fara ƙoƙarin kwatar kanta, nan ya gwada mata ba ƙarfinsu ɗaya ba, duka hannayenta ya riƙe da hannu ɗaya ta bayanta, ɗalli ya kaiwa lips dinta yace "do i look like your mate ba..?", tini ta guntse lips din ta mayar dasu ciki yadda bazai iya ɗallesu ba, sakinta yayi yace "da kin cigaba dai..", ja da baya tayi tace "karka sake taɓani dan ni ba ƴar iska bace..", slight smirk yayi yace "ƴar iska ce mna tinda gaki nan zaune gida ɗaya da namiji..", ta gwalo idanu tace "chaɓɗi jamm wllh ni ba ƴar iska bace, dole akamin nake zaune a nan..", wani mugun kallo ya watsa mata ya ɗauki wayarsa ya nufi door, har zai fita sai kuma ya juya yace "thank God wanda suka kawoki sun san ina ne nan din a wajenki which is gidan aure..", habawa ai wani irin tafashe Hajar taji a zuciyarta, tini fuskarta ta canza tamkar wacca aka saukarwa da wahayin mutuwa, zuciyarta ta harzuƙa iya harzuƙa, sosai Nurain ya fahimci wnn sauyin don shima saida yaji tasa azabar da ya faɗi hakan amma ya lura ita har ta fisa shiga shock, muryarta na rawa tace "meye kuma wani aure.. wa aka kawo gidan aure.. kaika sansa wllh tllh ni kam banida wani aure, aure a ina.." sai kuma ta durƙusa ƙasa ta fashe da kuka tace "ƙarya ne wllh Allah, ba wani aure da aka min..", ya taɓe baki yace "Silly girl" yayi fitarsa daga ɗakin. downstairs ya sauka ya fita compound, parking space ya isa ya shiga motarsa ya bar gidan zuwa nasu.

★Ruqayyah na kwance kan gado tunani iri iri ke yawo a brain dinta, babu abinda take tunawa sai time din da sukay sharing da Dearest, ba ƙarya sun zuba soyayya mai danƙo mara algus, soyayyar da take ganin zata kaisu ga aure, soyayyar da take ganin bazata taɓa mutuwa ba, toh me yasa wnn soyayyar take ƙoƙarin tabarbarewa ne..?, me yasa dearest zai gaya mata magana mai zafi irin wnn, wai yana da aure, shin yanada auren ne ko kuma kawai so yake ya ƙuntata mata, a lokacin da ya gaya mata wnn mummunar kalmar tayi tunanin zuciyarta ta buga ne don ji tayi tamkar an ɗauki wuƙa mai shegen kaifi an tsagata gidan biyu snn aka barbarɗa mata gishiri, tin shekaran jiya batada wani kuzari tana kwance ne kawai a ɗaki, jiya ma ko aiki bata je ba duk da cewa tanada night duty, wasu hawaye suka cika mata idanu, lokaci guda suka fara bin gefen fuskarta suna shiga ramin kunnenta, door akay knocking kafin aka murɗa handle aka shiga, da sauri Ruqayyah ta goge hawayenta ta miƙe zaune tana kallon Momy da ta shigo, Momy ta dubeta tace "ya jikin..?", Ruqayyah tace "da sauƙi sosai..", Momy ta gyaɗa kai tace "Ohk sannu your father is calling...", Ruqayyah ta ɗan zaro ido tace "Momy lfy..?", Momy ta nufi ƙofa tace "idan kinje kya ji.." ta buɗe ƙofar ta fita, sakkowa Ruqayyah tayi daga kan gadon ta saka hijab dinta ta fita, palourn Daddy ta shiga da sallama tana rarraɓewa tamkar munufuka, kanta a ƙasa ta zauna kan carpet a hankali tace "Daddy ina yini..", Calmly yace "lfy..", tayi shiru tana wasa da laushin carpet, Daddy yace "Ruqayyatu..", sai a lokacin ta ɗago kanta tace "na'am Daddy..", Ruqayyah na kuka wiwi ta fita daga palourn bayan Daddy ya sanar da ita ya amshi kuɗin aurenta da Dauda, fagam fagam ta wuce room din Momy tana kuka, Momy dake gyaran wardrobe ta ajiye gogaggun kayan hannunta tace "ke lfy kike gursheken kuka haka...?", Ruqayyah ta jingina da bango tana kuka sosai tace "Momy na shiga uku na lalace da rayuwa, wllh da na auri Dauda gwara na mutu..", Momy tace "ce miki akay auren Daudan za kiyi ne..?", Ruqayyah ta tsagaita kukan tace "Daddy ne ya amshi kuɗin auren Dauda..", Momy ta tsuke ido tace "Daddyn ne ya gaya miki haka..", Ruqayyah ta gyaɗa mata kai, Momy ta fita daga ɗakin, zaman dirshan Ruqayyah tayi a ƙasa ta ringa rafsa kuka tamkar wacca uwarta ta mutu, after like 10mins Momy ta dawo ɗakin ranta busu busu, don basu wanye da Daddy ta arziƙi ba, cewa yayi yaga alamar so take ta shiga tsakaninsa da ƴaƴansa, duk wani hukunci da yayi ƙoƙarin zartarwa saita kawo nata tawilin wnda ada ba haka take masa ba, shi ya gaji da zama da Ruqayyah a gida ɗaya aurar da ita zaiyi, goɗai goɗai da ita me zai hana a aurar da ita tinda tanada manema ba babu ba, Momy ta zaune gefen gado tana jin tinda take da Daddy basu taɓa samun matsala kamar yau ba, Ruqayyah ce causative agent, tin farko ita taja komai don haka she must harvest what she planted, Ruqayyah ta rarrafa gaban Momy tayi kneeling tace "Momy kin basa haƙuri ko..?, ya haƙura bazai aura mim Dauda ba ko..?", tureta Momy tayi tace "na gaji Ruqayyah, kawai ki haƙura ki auri Daudan shine zaman lfy na da kuma naki..", daɓas Ruqayyah ta koma ta zauna ba shiri tana girgiza kai, ta wawaki ƙasa ta miƙe ta fita da gudu ta bar ɗakin, dole ta nemawa kanta solution, don wllh tllh bazata auri Dauda ba, safa da marwa ta ringa yi a ɗakinta tamkar wacca ta shirgawa sarki ƙarya, wata babbar dama ce tazo mata kwanya, shi kaɗaine zai iya dakatar da Daddy, gobe goben nan zata kama hanyar Kaduna da yardar Allah, yanzun ma dan yamma tayi ne da babu zai hanata ɗaukar hanya.

★Abba na kallon Nurain yace "ranar Monday zaka amso mna passport din..?", Nurain yace "tom Abba.. zuwa wani lokaci Visa zata fita..?", Abba yayi resting da kujera yace "bazata wuce nan da 3weeks ba insha Allah..", Nurain ya gyaɗa kai yace "harda Hajiya ne..?", Abba yace "yeah..", Nurain ya jinjina kai yace "alright.. can i excuse myself..?", Abba yace "sure", tashi Nurain yayi ya bar great room din, bayan sallar isha'i Nurain na zaune palourn Mami, Mami tace "dan ma dai angama processing komai ne aida da Hajar zamu wuce..", Nurain ya kalleta bai dai ce komai ba, Mami ta numfasa tace "Son i hope all is well..", ajiyar zuciya yayi yace "yeah Mami..", Mami ta ringa kallonsa don yayi losing weight, ba haka yake ba, tace "toh cut down on coffee yasa kana ramewa fa..", ya zaro ido yana shafa fuskarsa yace "Mami coffee ne zai ramar dani", tace "toh idan bashi ba mene ne, bayan ma kullum anan sai kayi ƙat da abinci..", dariya yayi wacca ta tsaya iya throat, Mami ta kalli Tv tace "toh ga gaskiya..", Noor ce ta shigo da box din doughnuts da tayi order a hannunta, ta ajiye box din tace "Mami ga doughnut..", Mami ɗauki one piece cikin pieces shida dake cikin box din mai filling din foam milk with chocolate, Noor ta ɗauki box din ta ajiye kusa da brother dinta tace "Yaya fa..", ya girgiza kai yace "A'a", tace "toh na kawo maka cake" bata jira cewarsa ba ta tashi ta fita, da plate ta dawo palourn mai ɗauke da variety na cake, akwai red velvet with whipped cream, milk coconut cake, sai kuma chocolate cake, miƙa masa plate din tayi ya amsa yana kallon abin ciki, spoon dake gefe ya ɗauka ya fara ci a hankali, Noor ta zauna gefensa tana cin doughnut ita kuma tace "Yaya ya kaji cake din...?", yace "not bad..", tayi murmushi tace "nifa nayi..", yace "gashi nan kam har kin fara shirga kiba tinda kin durfafi cin wnn tarkacen..", ta zaro ido tace "aikam basa sa kiba Yaya.." sai kuma ta fakaici kallon yadda yake cin cake din tace "Yaya na dakko system din..?", ya ajiye plate din yace "Au bribery aka bani knn.. toh am leaving..", ya tashi ya yiwa Mami sallama, kafin ya nufi door ya kalli Noor, ta fakaici kallon Mami tayi sauri ta ƙifta masa ido, fita yayi daga ɗakin, yana fita da kamar minti biyar Noor ta ɗauki plate din cake da ya ajiye tace "bari na mayar da abuna fridge.." ta tashi ta fita tana kallon Mami da wutsiyar ido, da sauri ta wuce kitchen ta zuba abinci a warmers ta jera a basket, ɗaukar basket din tayi ta buɗe ƙofar kitchen din ta baya ta fita, ta zagaya zuwa parking space, tana zuwa ta bude front seat ta ajiye basket din ta duƙa tace "kaga fa ni ba ruwana Yaya, gobe ka ƙarasamin gyaran dan Allah..", yace "ke close the door and get lost..", ta turo baki ta rufe ƙofar ta wuce cikin gida, tara saura Nurain ya isa gida, yana shiga main palour ya fara tunanin shirmen da ta masa ɗaxu, sai a lokacin ya sake gasgata tabbas akwai tsantsar yarinta a lamarinta, murya ƙasan maƙoshi yace "Silly girl", kitchen ya shiga ya ɗauki plate with spoon da ruwa da lemo ya ɗora kan basket din hannunsa, da haka ya fito ya haura upstairs. washe gari da safe Hajar ce take sakkowa a hankali daga stairs, takaici duk ya isheta na rashin waya don wayar ce ke ɗebe mata kewa, gashi so take ta kira Umma taji ya jikin Mu'azzam, Still tayi ta ƙurawa hannun kujera idanu tana kallon wayarsa dake kai, ta ƙarewa palourn kallo tana murza slim fingers dinta, a hankali ta matsa ta ɗauki wayar tana kallonta, tinda take bata taɓa ganin waya mai kyanta ba, waya gaba ɗaya glass, juya wayar take a hannunta tana neman ta inda ake kunnata, da sauri ta dubi ƙofa jin an murɗa handle, tini idonta ya faɗa cikin kaifafan nasa, wani irin harbawa zuciyarta tayi, hannunta ya kalla a takaice, tana ganin haka tayi sauri zata ajiye wayar, ai kam garin sauri ta ajiye ba daidai ba, ji kake tass wayar ta faɗi akan tiles, durƙusawa tayi ta ɗauka, tana ganin yadda screen din yayi kwatsa kwatsa tayi sauri ta ajiye a ƙasa ta miƙe tana zaro ido, Nurain ya ƙaraso ya duƙa ya ɗauki wayar, da wayar a hannunsa ya miƙe yana kallon yadda screen din yayi kwatsa kwatsa, har wani numfashi ya ajiye tsabar yadda ransa ya mugun ɓaci, ya ɗago idonsa ya kalleta, tinda take dashi bata taɓa jin tsoronsa irin na yau ba, ƙafarta ta fara karkarwa ta juya da mugun gudu zata haura sama, Nurain yayi wurgi da wayar kan kujera, fixgo hannunta yayi ya juyo da ita, habawa ai tsabar firgita kawai ta tafi luu sai kace wacca aka hankaɗa ta zube a ƙasa......✍️

Plxx share as widely as possible 🙏
💛 HAJAR 💛

{53..}
Tsayawa yayi kawai yana kallonta, taja jiki ta koma can bayan kujera ta rakuɓe ta haɗe kanta da guiwa, tsabar yadda zuciyarsa take tafarfasa kasa cewa komai yayi, kuma baiyi yunƙurin taɓa ta ba, a lokacin idan yace zai taɓa ta to tsaf zai karya ta, Hajar kam ta tsorata iya tsorata har wani karrr jikinta yake, a yadda taga reaction din fuskarsa sai take tunanin yau ba ɗalle mata lips zaiyi ba tsaf zai rabata dasu, ɗago kanta tayi taga har lokacin yana tsaye a kanta, tayi sauri ta ɗora kanta kan knee tana sake takure jikinta, ajiyar zuciya yayi ya figi hannunta ya miƙar da ita tsaya, ƴar ƙara tayi tana zaro ido sai kuma ta fara yarfe hannu, gashi dai ta tsorata kuma tayi nadama amma kuma girman kai bazai barta tace sorry ba, shi kuma a ynxu sorryn ne zaisa ya yafe mata tinda ya lura ba tada shirin faɗa, figarta yayi zuwa cikin palourn, yana riƙe da hannunta ya tura Centre table da ƙafarsa zuwa daf fa kujera 2sitter, zaunar da ita yayi kan Centre table din shi kuma ya zauna kan kujerar suna fuskantar juna, ta haɗe legs dinta waje guda tana kallon ƙafarsa dake sanye cikin soft room slippers, gashi ya saka legs din nata a tsakiyar nasa, ƙoƙarin zamowa ƙasa tayi tana turo baki, da sauri ya mayar da ita ta zauna, zuciyarta na tsananta bugu ta ɗago idonta tana kallonsa, ya haɗe gira ya ɗauki wayarsa dake kan kujerar ya ɗora mata kan laps yace "biyani..", ta ringa kallon wayar ba tace komai ba, yace "uhmm am talking to you young lady, nace ki biyani..", ta juya lulu eyes dinta ta wani ci mur sai kace ita aka yiwa ɓarnar tace "nawa ce wayar taka ba sai na biyaka din ba..", ganin yadda tayi mganar ba tare da wata nadama ba yasa yaji ta matuƙar basa haushi, wai maimakon tace yayi haƙuri shine har tanada kwarin guiwar da zata tambayi nawa wayar, shi yasan ba tada kuɗin da zata biyasa a yanxu dai, kawai ya faɗi hakan ne to test her yaga irin girman kanta, ɗalle bakin yayi yace "wa ya gaya miki da kuɗi zaki biyani nonsense..", da sauri ta kai hannu ta shafa bakinta, ai kam ta dangwalo jini, tace "kai ka kai ka kai toh idan ba da kuɗi ba da mai ka sayi wayar da zaka dakar min baki haka..?, kuma naga ai ba ina sane na fasa ba.." tana gama faɗin haka ta yunƙura zata bar wajen, ya zaunar da ita da sauri, ƙafafuwansa da ya rutsa nata yasa ya matseta snn ya rutsa hannayenta da hannu ɗaya, kokawa ta fara yi dashi tana gunguni ita lallai sai ya saketa, dan kanta ta haƙura ganin bazata iya kwacewa ba, yace "har yanzu ba kiyi nadama ba young lady..", hijab dinta ya tattaro ya kawosa zuwa laps dinta, zaro ido tayi tana mutsu mutsu tace "malam meye haka... ni ka sake..", ya kalleta ba tare da yace komai ba, hijab din ya zare daga kanta ya sauka a wuyanta, nan da nan ƴan hanjin Hajar suka juya, idonta kamar zai faɗo tana turo baki tace "ka sake ni malam...", kwafa yayi ya cije lower lips dinsa painlessly yana kallon yadda take zabga masa harara, ba tay aune ba ya cire hular kanta, ta fasa ƙara a gigice ta kai masa cixo a hannu, gwaɓe bakinta yayi yace "karki kuskura..", tini idonta ya kawo ruwa jikinta na tsananta rawa, hijab din ya cire gaba ɗaya daga jikinta, wata gagarumar ƙara ta fasa har saida ya runtse idonsa sbd yadda ear drum dinsa yayi beating, he can feel yadda jikinta ke rawa, sbd kayan bacci ne ajikinta shiyasa ta razana sosai, ya ɗalle lips din yace "karki sake min ihu a nan, are you mad, by now kin fahimci da mai zaki biyani wayana..", wani numfashi ta sauke tamkar zata shiɗe ta fara girgiza kai, tama kasa yin magana tsabar yadda take shivering, bata sake firgita ba saida taji ya ɗaga ƴar rigarta sama, ta muskuta baya tana ƙoƙarin fixge kanta, janyota yayi da ƙarfi har kusancinsu yafi na da, bakinta na rawa sai kace an jona mata shocking tace "wayyoh Allahna na shiga uku na lalace... nifa ba ƴar iska bace..", sosai tayi mugun basa dariya amma ya shanye yace "nima ba ɗan iska bane amma saina fanshe wayana..", wnn furucin da yayi ba karamin ɗaga mata hankali yayi ba, hannunsa ya zura cikin rigarta, idonta yayi wani farrr sai kace wacca zata suma kafin ta kwallara ƙara da iya volume dinta tace "Allahumma ajirni fi musibati... na shiga ukuna..", ya ɗago kansa yana kallon yadda hawaye ya wanke fuskarta tass, gashi kuma tayi jajir sai kace jan ƙosai, a gigice tace "yi haƙuri don Allah, dan girman Allah kayi haƙuri", idonta a runtse bama ta kallonsa, yayi ajiyar zuciya kafin ya ciro hannun daga rigarta yace "maimaita..", lips dinta na rawa tace "kayi haƙuri dan Allah..", ya gyaɗa kai yace "ni sa'an kine da zaki ringa min rashin kunya..?", ta girgiza kai har lokacin bata buɗe idonta ba tace "A'a wllh kai ba sa'ana bane ka girmeni..", yace "good.. zaki sake min rashin kunya..?", nan ma ta girgiza kai tace "A'a wllh har abada bazan sake ba.. kayi haƙuri don Allah..", yana sakinta tayi baya luuu zata fada kan glass din center table din, fixgota yayi yace "open your eyes..", a daburce ta buɗe idon, samm taƙi yarda ta haɗa ido dashi, ta yayibi hijab dinta da ya wurgar kan carpet ta lulluɓe jikinta, a miliyan ta haura sama har tana zabga tuntuɓe, yabi bayanta da kallo yace "Silly girl..", wayarsa da ta faɗi nan kan carpet ya sunkuya ya ɗauka, ya ringa jujjuyata a hannunsa kafin ya tashi ya haura sama da ita.

★Ƙarfe Shida da rabi Ruqayyah ta fito wanka, bayan ta gama shafe shafenta ta buɗe wardrobe ta ɗauki doguwar rigar atamfa ta saka a jikinta, palour ta fita ta shiga kitchen ta haɗa thick tea ta fito, bread ta ɗauka a kan dining ta shafa masa strawberry jam sbd rashin appetite da ta tashi dashi, slowly take cin abincin tana turawa da kyar, da kyar taci slice biyu na bread din shima jam din ne ya taimaka mata taci, ta shanye tea din shima daman ba mai yawa ta haɗa ba, room dinta ta koma ta bude bedside drawer ta ɓalli 2tablets of paracetamol ta sha da bottle water dake kan mirror, daga nan ta saka hijab din da ta fito dashi ta ɗauki handbag dinta ta fita, ta shiga room din Momy ta tarar bata nan, she knows tana part din Daddy kawai ta juya ta fita compound, bayan ta bar layin gidansu ta samu wani pos ta cire cash sbd na jikinta ba zasu isheta ba, ta tsari napep ta shiga, bayan tafiyar 20mins ya ajiyeta a motor park, Ruqayyah bata shiga ko wace mota ba sai wacca taga ta kusa cika, tana shiga motar ta tashi cause itace ta cike wajen mutum ɗaya daya rage, ƙarfe takwas suka isa Zaria, wayarta ce ta fara ringing, ta cirota daga handbag ganin mai kiran tayi sauri ta ɗaga, from the other side Momy tace "kina ina Ruqayyah, na duba room dinki bakya nan..", Ruqayyah ta haɗiyi yawu tana neman ƙaryar da zata rangaɗa, jin shiru Momy tace "ba kya jina ne..?", Ruqayyah tace "Momy gidansu Meema naje..", Momy tace "da safiyar Allah kika je musu gida..", Ruqayyah ta sauke ajiyar zuciya bayan sun gama waya da Momy, bayan tafiyar almost 2hrs suka iso garin Kaduna, ta biya kuɗin motarta snn ta fito daga motor park din, napep ta tare, ya tambayeta ina zata tace "Malali..", yace "Malali wacce..?", Ruqayyah tace "Malalin har nawa ce ni Ruqayyah..", ya gaya mata, taɓe baki tayi tace "toh muje dai wataqila na gane idan mun shiga garii", da kyar Ruqayyah ta iya gane gidan bayan sun gama gallafiri tsakanin unguwanni, mai napep kam ya cajeta kudi da yawa, ta fello haƙƙinsa ta basa ita dai tinda ta gane gidan ai mgana ta ƙare, almost 3yrs fa rabonta da zuwa wata kaduna, wani gida mai bakin gate wanda yake da manyan bishiyar dogon yaro a gabansa ta isa, tayi knocking door, few seconds mai gadi ya buɗe mata, shiga compound din tayi ta wuce main building din gidan, sai a lokacin taji fargata tazo mata, ta dake ta shiga da sallama. yaran da suke zaune palourn su uku suka ɗaga kai a tare suna kallonta, kamar yadda bata ganesu ba suma haka basu santa ba, babban cikin kawai ta gane tace "Mujaheed..", yayi yaƙe ya gaisheta duk da dai bai santa ba, sauran ma suka gaidata, kan kujera Ruqayyah ta zauna tana raba idanu, courage dinta ma duk ya fara narkewa, Ruqayyah ta kira ƴar macen, yarinyar ta taso ta tsaya gefenta, Ruqayyah tace "ya sunanki..?", yarinyar tace "Hanan..", Ruqayyah tace "ina Mamamki..?", Hanan tace "tana gidan mu, ni jiya aka kawoni nan wajen Mammah..", Ruqayyah ta gyaɗa kai bata kai ga cewa komai ba aka buɗe wata ƙofa, wata dattijuwa ce ta fito da tray a hannunta an ɗora masa cups uku tana mita "wnn wane irin rikici ne, na gama ɗawainiya da iyayenku kuma yanzu na ɗora da taku, dan bala'i duk sati sai a kawomin ƴaƴa wai weekend, iyayen ku nacan suna tiƙar bacci ni an barni da tashin sassafe da guntuwar hamma..", sai kuma tayi shiru ganin Ruqayyah tana ƙanƙance ido, Ruqayyah ta zamo ƙasa tace "Mammah ina kwana..", Mammah ta ajiye trayn da ta haɗowa jikokin nata shayi tana kallon Ruqayyah da kyau, Mammah ta riƙe haɓa tace "Ruqayyatu hala dai ɓatan kai ki kayi ko..?", Ruqayyah tayi murmushin yaƙe tace "A'a Mammah zuwa nayi na gaisheku..", Mammah tace "toh sannu da zuwa daga kanon kike..?", Ruqayyah ta gyaɗa kai tana murza fingers, kitchen Mammah ta koma ta fito da plate din dankali da kwai ta ajiyewa jikokin nata da har sun afka kan shayin da ta ajiye musu, daga nan ta zauna suka gaisa da Ruqayyah da kyau tana tambayarta Daddyn ta. ƙarfe biyu da rabi Mammah ta shiga ɗakin da aka sauki Ruqayyah tace "kinci abincin..?", Ruqayyah tace "Eh naci..", Mammah tace "toh kixo ku gaisa da mijin naki, ni tsautsayi ne ma ya sani na kai kishiya har ɗaka..", Ruqayyah dai tayi murmushi ta tashi tabi bayan Mammah, ɗakin Kawu wanda yake ƙanin mahaifin Daddy Mammah ta kai Ruqayyah, kana ganin dattijon kasan sun haɗa dangantaka da Daddy don kamar shi ya haifi Daddy sbd resambulance, da ladabi Ruqayyah ta gaida Kawu, ya amsa yana tsokanarta a matsayinta na jikarsa, Ruqayyah ta duƙar da kai tana wasa da ƙafarta, a hankali ta shigar da ainahin abinda ya kawota Kaduna, Kawu ya gyaɗa kai bayan sauraronta yace "toh ko so kike ki zama tsohuwar guzuma babu aure ƴar nan.. naga tsohon naki gata zai miki..", Ruqayyah ta fara sharar hawaye tace "Kawu wllh wnda zai auramin ne banaso..", Kawu ya jinjina kai yana kallonta da kyau yace "ja'ira daman ba zuwan Allah da ma'aiki kikay ba, ashe takakkiyarki ce ta kawoki". kafin magrib Ruqayyah ta iso kano, a galabaice tazo duk tayi wani wiƙi wiƙi, daman ba wata lfy ta samu ba kuma shine ta tarki uwar tafiya.

★Bayan sallar la'asar Hajar ta buɗe ƙofar ɗakinta a hankali, saida ta gama ƙarewa corridor kallo taga babu kowa snn ta fito, walking slowly ta sauka downstairs, zuciyarta ta ringa bugawa cause ba ta son encounter dashi, luckily for her ta tarar babu kowa a palourn, da sauri ta shige kitchen ta dafa Noodles sharp sharp ta fito, tana rufe ƙofar saiga footsteps ana sakkowa ƙasa, ta ɗaga kai ta kalli stairs din, suna yin ido huɗu tayi sauri ta juya masa baya tana turo baki, runtse idonta tayi ta wawaki handle ta murɗa ta koma kitchen din ta rufe ƙofar, jingina tayi da ƙofar tana mayar da numfashi, kawai abinda ya mata yau da safe ke mata yawo a brain, idan ta tuna sai taji tamkar ƙasa ta tsage ta shige, bayan kamar minti goma ta buɗe ƙofar ta leƙa, ajiyar zuciya tayi ta fito ta haura sama bayan hancinta ya cika da ƙamshinsa da ya bari a palourn. washe gari Nurain ya fito daga room dinsa ya gama shirinsa na fita aiki, har zai sauka sai kuma ya duba tsadadden agogon dake wrist dinsa, ƙarfe tara da minti biyu, ƙofar room dinta ya buɗe ya shiga, Hajar dake zaune gefen bed ta ɗago ta kallesa, tin ɗazu ta tashi tayi wanka ta shirya, so take ta fita amma kuma ta kasa, tana ganin shine ta tashi da mugun gudu ta shige bathroom ta garƙama lock, Nurain ya haɗe thick eyebrows dinsa ya ringa kallon ƙofar bathroom din kafin ya juya ya fita, yana zuwa hospital din patient huɗu yayi attending suka shiga meeting, akan Seminar da nan da 3weeks zata zo akay meeting din, shi dai baiso ba kwata kwata, don har dashi acikin wadanda zasu, duk yadda yaso ya noƙe kar yaje amma haka Dr Mansoor yace ai shine zaiyi representing thoracic surgeon, bbu yadda Nurain ya iya hka ya fito meeting din under probability don yace sai yayi tunani tukun, baima koma office dinsa ba kawai ya bar hospital din, saida ya biya aiken da Abba ya masa na amso passports snn ya wuce gidansu, da yamma ya shiga wajen Abba ya kai masa saƙon tinda ya dawo a lokacin, da sallama ya shiga great room din, yana zama saiga Abba nan ya fito daga bedroom, bayan sun gaisa Nurain ya ajiye envelope din da ya shigo da ita yace "gashi Abba..", Abba ya buɗe envelope din ya fara ciro passports din, Nurain na kallon passports din yace "harda Noor ne..?", Abba yace "yeah..", Nurain ya gyaɗa kai yace "amma exams din fa..?", Abba yace "kafin nan ta gama ai, tace nan da 2weeks zata gama exams din..", Nurain yace "alright.. bari na wuce mosque..", Abba yace "Ohk" da haka ya tashi ya shiga bedroom to perform ablution. da misalin karfe takwas da rabi na dare Nurain na tsaye jikin motarsa yana jiran Noor, hannu na dukan cinya Noor ta fito compound din ta isa bakin motar tana kallonsa tace "Mami ta hana na zuba maka abincin wai kaci a gida..", kasa cewa komai yayi ya tsaya yana kallonta, Noor da taga reaction dinsa weird tace "Yaya wai Anty Hajar din bata iya girki bane..?", yace "just cut it good night...", motarsa ya shiga ya bar gidan with speed, yana zuwa gida yayi refreshing kansa ya sakko downstairs, cup of Café latte ya haɗama kansa, da cup din a hannunsa ya fita balcony ya zauna kan kujera dake wajen, slowly yake sipping coffee, kira yaga yana shigowa ta jikin smart watch dake hannunsa, daman yau duk dashi yayi amfani wajen calls, airpods ya ciro daga pocket dinsa ya saka one ear, Calmly yace "yeah sister..", from the other side Sakeena tace "brother tataccen mai kirki how are you..?", yayi murmushi don ya fahimci ba'a take masa yace "am fine alhmdllh..", tace "toh Yayi.. ya Hajar..?", yayi sipping coffee yace "kin bar mijinki shi kaɗai ni zaki hanani bacci nan haka..", tace "Yah c^mon bani amsana...", yace "ohh she's fyn..", tace "good..", dariya yayi yace "are you alone..?", tace "yess yess", ya sake yin wata dariyar yace "toh don kar kije kiyi ihu ki razana mutane...", tace "toh nidae ka gayamin mene..?", yace "hmm wai daman Umrahn babu ke za a..?", Sakeena ta miƙe daga kan kujerar da take kwance tace "bangane bani ba, harda ni mna..", Nurain ya gyara airpod din kunnesa ya ɗauki cup of coffeen sa ya shiga ciki, Sakeena tace "tafiyar tazo ne..?", yace "A'a ban sani ba fa, nida babu ni to what concern me da lokacin tafiya..", tace "Auho ai na dauka tafiyar ne yaxo..", dariya ya sake yi don ya hango ydda reaction dinta zai kasance yace "madam where is your passport..?", ta juyo hannu kamar yana kallonta tace "yana nan saina lalubo sa..", yace "hmm toh a nemo lfy", ɗaga kansa yayi yana kallon Hajar da take sakkowa, bata lura dashi ba saida ta gama sakkowa tass, tayi sauri ta sunkuyar da kanta sai kuma ta juya ta koma saman da sauri, Nurain yace "i will call you tomorrow insha Allah sister" ya cire airpod din kunnesa yana kallon stairs, ajiyar zuciya yayi ya nufi stairs din.....✍️
Join my WhatsApp group 👇
💛 HAJAR 💛

{55..}
★Washe gari Monday Nurain na zaune office dinsa yana duba patient, yana gama duba patient dake office din kira ya shigo ta wayar landline, picking yayi yace "yess", Secretaryn sa Haleema tace "sir A Nurse tana son ganinka..", yace "i thought it is something important, next patient ya shigo.." bai jira cewarta ba ya katse kiran, Haleema ta ajiye landline din tana kallon Ruqayyah da tayi tsuru tsuru a gabanta, duk ta rame kamar ba Nurse Ruqayyah ƴar gayu ba, yanzu gayun ma baya amsarta ko tayi, Haleema tace "A Nurse ki ɗan jira a waje yace Patients yake dubawa..", Calmly Ruqayyah ta gyaɗa kai tace "Okay", tinda dai yace ta jira ai mgana ta ƙare, knn zai saurareta idan ya gama duba patient din, fita tayi daga office din ta zauna kan silver chair dake waje, tanata zaune a wajen har patient din da suke bin layi suka ƙare daman su 20ne, wayarta dake cikin scrub pocket ce tayi ringing, ta ciro wayar tana kallon mai kiran kafin tayi picking ta kara a kunne tace "ina ji Jiddah..", Nurse Jiddah tace "haba Ruqayyah ina kika tafi haka, station din fa babu kowa, Amina ta riga tayi miki handing over fa, gashi can ma ward din da kike kula dashi lokacin yiwa diabetic patient din nan insulin ya cika, ya kamata kixo ki masa yaci abinci dan Allah...", Ruqayyah ta lumshe idonta dan kanta ne ya sara tace "Jiddah dan Allah kije ki masa allurar ni na ɗan fita ne bana nan, zan jima kafin na dawo in yaso nayi night duty...", Nurse Jiddah ta taɓe baki tace "Au haka kika fita bayan ga jakarki nan da Abayarki ina gani, ko dai haka kika fita ƙindu ƙindu with Scrub...", Ruqayyah tace "to dai bana cikin department din ina can Pediatric department..", Nurse Jiddah tace "Ohk, toh gsky this is the last tsakani ga Allah, ke kaɗai kike raɓarɓashe albashinki..", Ruqayyah tace "thank you..", Nurse Jiddah dai ta kashe wayar tana tsaki, Ruqayyah ta mayar da wayar pocket, ta ɗaga kai tana kallon ƙofar office din, tashi tayi kafin ta buɗe aka rigata ta ciki, Nurain ne ya fito riƙe da briefcase dinsa don ya gama gida zai wuce, Ruqayyah ta dubi hannunsa ganin briefcase tace "are you leaving...?", ko kallonta beyi ba ya wuce zai bar wajen, ta bisa da sauri ta riƙe hannunsa hawaye har ya ciko idonta, wani mugun kallo ya watsawa hannun nata with stern voice yace "hands off..", ta cikasa sai kuma ta sha gabansa tana kallonsa, tace "Do you know how much i love You..?, do you know how long i waited to see you...?, why do you not listen to me...?, i don't want to part from you again, so you must listen to me dearest.." tana gama faɗin hakan ta fashe da kuka tana dukansa a chest painlessly, kukan da ta fashe dashi ne ya janyo attention din few mutanen dake wajen, har lokacin bata dena rusa masa kuka ba, janta yayi zuwa office dinsa, Haleema da ta gama shiryawa itama zata tafi ta bisu da ido, Nurain ya ajiye briefcase din kan table ya shafa hair dinsa kafin ya zura both hands dinsa a pocket, juyowa yayi yana kallon Ruqayyah da take kuka bil haƙƙi, ya sauke ajiyar zuciya yace "damn it.. what are you doing Ruqayyah..", ta zuba masa jajayen idanunta da muryar kuka tace "ai ka ƙi ka haƙura sai haƙuri nake baka Dearest..", ya girgiza kai yace "we already sort it out Ruqayyah, am not keeping any grudge against you, ki dena bani haƙuri ni babu abinda kika min, in ma akwai toh na haƙura..", tana shessheƙa tace "ka haƙura toh me yasa kake avoiding dina, ka dena picking calls dina, idan nazo office dinka ba a barina na shigo..", ya dubi ceiling feeling confuse yace "Ruqayyah..", bata amsa ba amma ta zuba masa idanu, yace "Allah ma ya gani am done with you, I don't have any feeling for you now and forever, please let me be, bana so na miki abinda baza kiji daɗi ba so stay far away from me, kawai abinda ya wuce ya riga ya wuce, abu ɗaya na sani yanxu akanki shine kina cikin team members dina bayan haka babu komai... kiyi abinda zai fisshe ki A Nurse.." yana gama faɗin haka ya ɗauki briefcase dinsa ya bar office din with speed, like one living statue haka Ruqayyah ta daskare a tsaye, tamkar an dagargaza zuciyarta haka take ji, Haleema ce ta shigo tana kallonta tace "amm zan rufe office din..", Ruqayyah ta ja ƙafa ta fito, da ido Haleema ta bita tana girgiza kai tace "sai ki haƙura dai tinda tin farko kin yiwa kanki sagegeduwa..", Ruqayyah ta juyo ta kalleta dan ramm taji abinda ta faɗa, sai kuma ta juya ta cigaba da tafiya. Ruqayyah bata zauna a asibitin ba haka nan ta shirya ta tafi gida, Ruqayyah na zuwa gida ta gamu da tashin hankalin da ya shalleke tunaninta domin kwa saƙonta ya isa ga Daddy, daman tin kwanaki biyu da zuwan Ruqayyah kadunan Kawu ya kira Daddy yace yana son ganinsa, Daddy yace masa zaizo insha Allah ranar Litinin, toh yau Monday da wuri Daddy ya shirya ya tafi Kadunan don yaji kiran da ƙanin mahaifin nasa ke masa, ba ƙaramin fusata Daddy yayi ba, Kawu kawai mgana ya masa ba wata mai zafi ko ɗumi ba, shi takaicin Daddy wai har Ruqayyah ce zata kaisa ƙara wajen Kawu, knn ja dashi zatay, tinda ya ɗauko hanyar kano bayan ya bar Kaduna nan ya kira Momy a waya, tashin hankalin da ta shiga ba kaɗan bane, itama taji haushin abinda Ruqayyah tayi. Momy na zaune palour ta dafe kanta tace "Ruwayyah ki haɗa kayanki ki wuce gidan Safiya..", Ruqayyah ta ƙarasa palourn zuciyarta na bugawa tace "Momy sbd me dan Allah..?", Momy tace "kinje Kaduna wajen Kawu ko bakije ba..?", Ruqayyah ta sunkuyar da kanta tamkar munafuka, Momy ta daka mata wata tsawa tace "tambayarki nake malama", Ruqayyah ta koma ta manne da bango ta sunkuyar da kanta tace "naje..", Momy tace "innalillah wa'inna ilayhirraji'un, kin kyautawa kanki, ki wuce kiyi abinda nace..", Momy ta tashi ta shiga room dinta ta kira ƙanwarta Haj Safiyya ta sanar da ita Ruqayyah zata zo, bayan ta gama wayar ta fito ta shiga room din Ruqayyah, zaune ta tarar da ita kan bedside ta zabga tagumi, Momy tace "kin haɗa kayan Ruqayyah..?", Ruqayyah tayi firgigit bayan ta fito daga duniyar tunani tace "A'a", Momy ta gyaɗa kai tace "toh kar kiyi sauri ki zauna har ya dawo gidan ya sameki, wllh babu ruwana, dalla malama tashi ki shirya..", Ruqayyah na sharar kwalla ta gama haɗa kayanta set biyu a ƙaramar jaka, duk Momy na tsaye tana kallonta, da jakar a hannunta Momy ta iza ƙeyarta har palour, ganin batada niyyar fita Momy ta turata waje tace "maza ki tafi.." da hka tayi banging door, Momy na sane tace Ruqayyah ta bar gidan, tasan ran Daddy ya ɓaci matuƙa, gwara idan ya ɗanyi sanyi ta dawo koma wane hukuncin zai mata ita ta janyo amma dai banda lokacin da ransa yake tafasa.

★Bayan Hajar ta idar da sallar la'asar ta sakko downstairs, kitchen ta shiga ta ɗakko abincin da ta dafa tin ɗazu, har zata haura sama da warmer din sai kuma ta fasa ta zauna nan palour, tana fara cin abincin saiga ƙarar bell, ta ajiye spoon din hannunta tana kallon door, saida aka sake danna bell din snn ta tashi still tana kallon ƙofar, toh Allah yasa dai a buɗe take tinda dai tasan kullum a rufe take, da wnn tunanin ta isa kusa da ƙofar ta murɗa handle, zaro ido tayi jin a buɗe take, tana buɗewa tayi arba da Hafsah, Hajar ta gwalo ido don bata taɓa tsammani ba, cike da murna tayi hugging dinta tana welcoming dinta, Hafsah dai kawai binta take da kallo ganin yadda ta canza, ta kusa linka ainahin farinta har wani pink pink take, a palour suka zauna Hajar tace "yasu Humairah da Anty..?", Hafsah tace "suna nan lfy wllh.." sai kuma ta riƙe haɓa tace "kinyi luf luf abinki, wnn luƙui luƙui haka..", Hajar ta galla mata harara tace "ke nan din ya miki kama da wajen da mutum zai wani luf.." tashi tayi ta shiga kitchen ta kawo mata ruwa da lemo, Hafsah tace "ke kullum wayarki a kashe..", Hajar ta taɓe baki tace "hmm ta lalace..", Hafsah ta ringa kallon palourn tace "shi bai sayar miki wata ba..", Hajar ta yamutsa fuska tace "shi din wa.. Hafsah knn..", Hafsah ta ɗauki lemon ta zuba a cup tasha, after like 40mins Hafsah tace "toh na gaisheki Hajar, tafiya zanyi bazan kai magrib ba, unguwar nan napep wahala yake, kinga ma waccan karon da nazo ban samu napep ba..." sai kuma tayi shiru tana murmushi tace "kinsan kwa wane ya mayar dani gida a ranar..", Hajar tace "sai kin faɗa..", Hafsah tace "wnn mutumin da muka hadu dashi a Supermarket, Ahmad din nan..", Hajar tace "ohhh Allah sarki..", Hafsah ta sauka daga napep bayan tazo gida, handbag dinta ta bude ta basa kuɗinsa, kallon motar dake parke a gefen titi ta ringa yi, ta dai amshi canjinta ta zaga wajen slapp zata shiga gida, buɗe motar yayi ya fito yana kallonta, ya rufe motar yabi bayanta Calmly yace "Assalamu alaikum..", no doubt zamm ta ɗauki muryar, amma she was shocked, a hankali ta juya tana ƙirƙirar murmushi tace "Wslm..", ya shafa kwantaccen beard dinsa yace "how are you doing..?", tana ɗaga kanta taga Abdallah yana tsallakowa daga other side din titi, zuciyarta ta buga da ƙarfi, ɗauke kanta tayi tace "lfy alhmdllh ngd..", yace "masha Allah daman i am passing by nace bari mu gaisa da friend dita tinda bata picking call a gaisa..", daidai nan Abdallah ya tsallako, jimm yayi yana kallonta sai kuma ya wuce cikin gida, Hafsah tayi murmushi tace "toh ngd sai anjima", ta juya ta shige gida da sauri, Ahmad ya bita da kallo bayan wani lokaci ya shiga motarsa ya bar unguwar, Hafsah na shiga gida ta tarar da Anty zaune a palour, Abdallah ma na palourn zaune kan 1sitter yana cin abinci, ta kalli position din da yake sau ɗaya sai kuma ta dubi Anty tace "Anty na dawo..", Anty tace "toh sannu da zuwa ya Hajar din..?", Hafsah tace "wllh sumul take Anty, tayi kyau abinta..", Anty tace "masha Allah..", Hafsah ta dubi jakarta jin wayarta na ringing, tashi tayi ta shiga room dinsu tana satan kallon Abdallah da ya bita da kallo, Anty ta ɗauki wayarta dake gefenta ta kira Umma, bayan sun gaisa Anty tace "ya jikin Mu'azzam..?", Umma tace "jiki alhmdllh ai yaji sauƙi sosai..", Anty tace "toh an gode Allah, ai Hafsah na tura taje ta duban ƴar tawa kafin naje da kaina..", Umma ta numfasa tace "ba wata matsala ko Jamilah..?", Anty tace "lfy lou wllh Adda, kinsan ƴar tawa haƙuri wala, idan da gaske ba zaman lfyar da tini ta taho fa, amma tinda kika ga shiru toh lafiya ce gsky..", Umma tace "nima nayi tunanin hka..", Anty tace "yanzu idan an kwan biyu sai naje da kaina..", Umma tace "toh shknn ngd Jamilah..", Anty tace "ba komai Adda, sai anjima.." da haka sukay sallama.

★Bayan tafiyar Hafsah Hajar ta koma room dinta, two hijab sai kayan baccin da ta saka ta ɗauka ta shiga bathroom dasu ta wanke, bayan ta gama wankewa ta fito dasu a cikin bucket ta sauka ƙasa don ta shanya, ta main door ta fita daga building din, can backyard taje ta shanya snn ta dawo ciki, tana dawowa daman an kira sallar magrib don haka tayi sallarta, can wajen ƙarfe tara harta yada pillow zata kwanta ta tina da kayan shanyarta, tashi tayi ta leƙa window taga garin akwai hadari, hijab ta saka ta fito daga room dinta Walking like a chameleon ta sauka, tsaye tayi a palourn tana kallon Tv da ta gani a kunne, ga kuma Lap top kan hannun kujera itama a kunne, ta taɓe baki ta nufi ƙofa, zagawa tayi can backyard din ta kwaso kayanta, tana tafiya tana kallon gidan in it's night view, fitilu ko ina sai kace rana, tsaye tayi daidai window din kitchen tana kallon ciki, lokaci guda ta matsa gaban windown tana kallonsa, he is in his pajamas making coffee, ta ringa bin duk abinda yake da kallo tana taɓe baki, a gabanta ya gama haɗa coffeen ya tsiyaye a cup ya fita bayan ya kashe coffee makern, ta zagayo ta buɗe ƙofa ta shiga, Nurain ya juya yana kallonta, ɗauke kanta tayi ta nufi stairs abinda, ya haɗe thick eyebrows dinsa ya cigaba da abinda yake jikin Laptop. washe gari Hajar na idar da sallar asuba ta fito, har lokacin gari baiyi haske ba, tana shiga kitchen ta buɗe cupboard ta ciro coffee powder, har wani nishadi take yau zata sha abinda take marmari, switch din coffee maker ta kunna, No milk no sugar da tsurar cocoa powder tayi amfani, tana gamawa ta tsiyaye a cup, harda wani ɗan karkaɗa cup din wai ya huce da zafi, tana sha ta yamutsa fuska bayan ta guntsesa a baki, wani mugun ɗaci ne ya kaure mata a baki, da sauri ta tofar da na bakinta acikin sink, ta kunna pampo ta kuskure bakinta, kallon cup din worst coffeen da ta haɗa tayi tace "chaɓɗi jamm nida maɗaci..", tini ta sakar masa ruwan pampo ta wanke cup din ta fita daga kitchen din tana gyatsine. ƙarfe bakwai da rabi Nurain ya sakko downstairs, yana zaune a palour yana shan sahibin nasa, ya duba time ta faskeken agogon dake manne a palourn, tashi yayi ya fita compound zai sanar da Inuwa ya wanke masa wheels din motarsa kafin ya fita. tinda Hajar ta hango cup din daga sama tayi sauri ta sakko, ehen ai kam sai tasha kuwa, ta isa inda cup din yake ta ɗauka, tini ta kwankwaɗe tass ta ajiye kofin a inda yake, saidai tana ɗaga kanta sukay ido hudu dashi, yayi folding hands dinsa yana kallonta babu ko ƙiftawa, ɗauke kanta tayi ta sha kunu irin ai nawa ne din nan, ta juya zata bar wajen kawai taji saukar muryarsa mai zurfi a kunnenta "Ke.. dan kinga jiya ban miki mgana ba shine ma yau kika aikata ko..?", ta juyo tana ɗage gira babu ko nadama a fuskarta tace "Au akan wnn maɗacin...", ya tsuke ido irin what, ta juya lulu eyes dinta tace "toh wllh sai nasha wani yace ka ringa ajiyewa", ta galla masa harara ta wuce zata hau stairs, bai bata damar hakan ba dan tini yayi blocking front dinta, ta ɗaga kai tana kallon how huge he is, gata wata dwarft a gabansa, Calmly yace "yeah no problem tinda kinada abin biya young lady..", da sauri ta ɗaga kai ta kallesa, lokaci guda brain dinta tayi booting on, ta zaro lulu eyes dinta kafin ta ja da baya tana girgiza kai, a karo na farko da ta taɓa ganin murmushinsa amma kuma sai ya mata kama dana mugunta yace "sai kin biya..", da gudu ta koma cikin palourn tana ƙoƙarin zagayesa ta haura sama nan ma ya hana hakan, ganin zai cafkota ta tsala wani uban ihu ta ruga corridorn shiga guest room, sosai zuciyarta ta buga ganinsa a corridorn ya biyota, ai kam ta murɗa ƙofar guest room din ta shige da sauri tayi banging door, saidai fa unfortunately for her taga babu key ajikin ƙofar, ta jingina da jikin ƙofar ta danne with all her strength, sai kace wanda ya tura wani bicycle haka ya tura ƙofar ya buɗe, wani uban ihu ta tsala ta koma can ƙarshen ɗakin tana zaro ido tamkar ɓera a buta, ya mayar da ƙofar ya rufe ya tsaya yana kallonta yace "ke da kike da abin biyan bashi young lady mene kuma na tsorata, ohh c^mon ki biya ko na fanshe abina..", ta shiga yarfe hannu tace "na shiga uku".....✍️
********************** **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
************************* **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > [email protected]

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

WhatsApp Number: 08138873799


Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafinmu ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** **************************
💛 HAJAR 💛

{56..}
Ko one step bai ƙara ba daga inda yake tsaye jikin ƙofa yace "mene kuma na shiga uku.. zaki biyani ko sai na fanshe..?", bakinta na rawa sai kace an jona mata shoking tace "zan biyaka..", yace "with what..?", tace "shi shayin naka dashi zan biya ka", yayi nodding kansa yace "alright muje ki bani", ta gyaɗa kai da sauri, har zufa ta jiƙa mata goshi gashin wajen ya sake kwanciya da santsi akan ydda yake na asali, ganin bata motsa ba sai muzurai take yace "kona fanshe ne..?", ta yarfe hannu ta girgiza kai tace "A'a dan Allah..", ya matsa daga bakin ƙofa yace "toh zo ki wuce..", ta gyaɗa masa kai kafin ta fara tafiya a hankali, tana zuwa bakin ƙofar tace "dan Allah karka taɓani..", yayi folding hands dinsa yace "wuce nace..", sum sum ta fita daga ɗakin yana biye da ita. tana zuwa palour ta fakaici kallonsa ta gefen ido, taga dai biye yake da ita kuma babu distance sosai a tsakaninsu, speed ta ƙara, ai kam yana ganin haka yasan akwai abinda take target, da mugun gudu ta ɗiba zata haura sama, tini ya fixgota ai kam ta tsala ihu ta fara kiciniyar kwace kanta, ya tsuke piercing eyes dinsa yace "Ke..! you think am joking ba..", ta girgiza kai tace "toh ba nace zan biyaka ba ai haɗa maka zanyii", tayi wani farr da dogayen eye lashes dinta, sakinta yayi ya ɗaure fuska ya nuna mata kitchen yace "ai nan za kiyi malama..", Kitchen din ta shiga tana turo baki, tsaye yayi a bakin ƙofa yana kallonta, haka nan ta buɗe cupboard ta ciro Cocoa powder ta matsa gaban coffee maker, kawai kallonta yake hannunsa zube a pocket, ƙasa ƙasa Hajar take ƙunƙuni tana jiran shirmen da ta haɗa ya kammala, wata glass kitchen Ware ta buɗe ta ɗakko Mug ta tsiyaye a ciki, shi dai kawai kallonta yake without blinking, juyowa tayi da Cup din a hannunta ta miƙa masa tace "gashi na biyaka", kallon cup din yayi sai kuma ya dubeta, ko kallonsa ba tayi taci mur, ganin bai amshi cup din ba ta kallesa, ganin kallon da yake mata ta ajiye cup din kan cabinet tace "gashi nan ka ɗauka", yace "shanye na bar miki..", ta gwalo idanu ta girgiza kai tace "A'a bana sha..", chab haka kurum ta ɓata bakinta, na ɗazu data haɗa saida ta kuskure bakinta da mouth rinks, ciro hannunsa yayi daga pocket walking towards her yace "ɗauka ki shanye", ta murguɗa masa baki tace "A'a wai ana dole ne, nifa bazan sha ba..", da baya ta koma ta manne da jikin cabinet, ya matsa daf da ita har ya mata rumfa, zaro ido tayi jin ƙamshinsa har throat dinta, tayi ƙoƙarin zillewa amma ya hana hakan ta hanyar saka hannayensa a sides dinta ya dafa cabinet din data manne da ita, wani mugun yawu ta haɗiya tana shaƙar scent dinsa tace "wai meye haka ne, bana biyaka shayin ba..", looking at her pink lips yace "shine nace ki shanye na bar miki..", ta kau da kanta tana turo baki tace "ni bazan sha ba..", yayi slight smirk yace "really..", ta gyaɗa kai irin yess, zaro ido tayi ganin abinda yake shirin yi ta tsala ihu tace "ni bana son irin haka wllh..", without care yace "for the last time i said drink it..", da sauri ta wafto mug din ta kafa a baki, a hankali ta kurɓa sbd akwai zafi, ta yamutsa fuska tana kakari bayan ta haɗiye da kyar, yana kallon reaction din fuskarta yace "good..", Mug din zata mayar ta ajiye yace "shanyewa fa za kiyi young Lady..", wani daram zuciyarta ta buga har tana jin bugun har maƙoshi, tini idonta ya ciko da hawaye, ta sake kafa kai ta kwalkwala bayan ta ɗauke numfashinta, yana kallonta saida ta shanye tass, ya sunkuya yana kallon empty cup din da har lokacin yake riƙe a hannunta tana mayar da numfashi tamkar wacca tayi gudun shekara, ta ɗaga idanunta da suka cika da hawaye ta kallesa, ido huɗu sukay tayi sauri ta sunkuyar da kanta, ajiye kofin tayi bata bari sun sake haɗa ido ba, ta sulale ƙasa ta raɓa ta wuce, bai dakatar da ita ba ya juyo yana kallonta thick eyebrows dinsa a haɗe, Hajar ta buɗe ƙofar kitchen din sai kuma ta fashe da kuka tace "Allah sai ya sakamin da ka bani maɗaci nasha.." with speed ta fita tana kuka sosai ta haura sama, murya ƙasan throat yace "Silly girl..", fitowa yayi daga kitchen din, ya kalli agogo ganin har takwas da rabi ta gota ya haura sama, ɓangarensa ya shiga ya wuce bathroom, bayan yayi wanka ya fito yana goge sumarsa da hand towel, yana gama shiryawa ya fito ya sauka downstairs, compound ya fita zuwa parking space, ya tarar har Inuwa ya gama wanke wheels din motar, buɗe motar yayi ya shiga ya fara warming dinta, yana jiran ta gama warming yace "hmm silly girl..", driving ya fara yi slowly ya fita daga gidan mai gadi na ɗaga masa hannu, yana isa hospital E.R ya wuce cause Haleema ta sanar masa akwai patient da zai duba a can din, Nurse Jidda ce a gefensa tana masa bayani, ya amshi stethoscope dake hannunta yayi listening bugun zuciyar patient din da yake unconscious, yana gama examining patient din ya fita bayan yace ɗaya daga cikin familynsa ya samesa a office, Calmly Nurain ya yiwa relative din patient din bayanin komai, snn ya masa tambayoyi akan tin yaushe patient din yake rashin lafiyar, a take Nurain ya sanar masa cewa surgery yake buƙata in not less than 48hrs in ba haka ba his life is in risk, godiya ya yiwa Nurain kafin ya tashi ya fita, daga haka Nurain ya fara attending patient dinsa, After 40mins Khaleel ya shigo da lab coat ajikinsa, he wasn't himself cikin damuwa yace "Dr Boss kaxo ka duba patient din nan he is gasping..", da sauri Nurain ya tashi ya fita, Khaleel yabi bayansa, E.R ya wuce da sauri, bayan ya samu patient din ya daidai snn ya fito, ya dubi Khaleel yace "get ready for surgery...", Khaleel yace "Yeah..", Nurain yace "A Nurse su shirya patient din zuwa surgery room..", Khaleel yace "tom". Nurain na tsaye gaban wash hand sink dake surgery room yana wanke hannunsa, har ya saka surgeon gown, Dr Marwan da zaiyi first assistance already ya gama wanke hannu ya shiga room din, Khaleel ne ya shigo a ƙarshe yana kallon Nurain da yake ta durje hannu da liquid soap yace "Ammm A Nurse fa ba tazo ba amma ga Nurse Jiddah...", Nurain ya ɗaga kai yana kallon Nurse din dake cikin surgery room din tana jera instrument acikin tray, ta saka nose mask a fuskarta, shi yasha ma Ruqayyahn ce ashe ba ita bace, keenly yace "Ohk.." ya cigaba da wanke hannunsa, yana gamawa ya shiga surgery room din ya saka nose mask da hand gloves, gaban surgery bed din ya isa ya tsaya a position dinsa na haed of the surgery.

★Umma na zaune tsakar gida a kan kujera tana tsince waken Alala, Sabrah ta fito daga ɗaki sanye da uniform da jakarta goye a baya, Umma tace "Auta kin gama shan kunun..?", Sabrah ta gyaɗa kai tace "Eh Umma nasha..", Umma tace "yawwa toh shiga ki gaida Baba saiki fito ki tafi karki makara kinji yarinyar kirki..", Sabrah ta shiga ɗakin Baba bayan ta gaishesa ya bata kuɗin makaranta ta fito, ta yiwa Umma sallama snn ta tafi, Umma tabi bayanta da kallo tana murmushi dan zamm yayarta. Sa'adatu ce ta fito ɗakin Maama da brush da toothpaste a hannunta, vest ce a jikinta sai zani, tayi wata wawuyar hamma babu ko rufe baki ta ɗaga hannu tayi miƙa, armpits din nan ba a cewa komai don kamar a kitsa, fatarta har wani shuni shuni take don taji chemical din allura, daman kana ganinta kasan sallah wala don batayi ba kuma batada niyyar yi, tukwanen ruwa ta buɗe ta zuba a buta ta tsugunna ta fara brush, tana gama brush din ta wanke fuskarta da ta cika da kwantsa, ta tashi ta shiga ɗaki, Maama dake zaune ɗakin tace "Sa'adatun Maama ba kiyi wanka ba fa haka zaki tafi kina tsami..", Sa'adatu tace "wllh bazan iya wanka a wnn kwaraɓaɓɓen banɗakin ba sai naje can zanyi..", Maama tace "toh shknn.. ina kwa ƴan albarkar ƙawayen naki..?", Sa'adatu ta ciro Uniform daga cikin Ghana most go wanda sukaci uban squeezing, tana bige uniform din wani bashi ya tashi tace "Mabruk da zeen suna nan sumul, kin manta rashin mutuncin da Baba ya musu da kuma abinda shegiyar gidan nan nunar rana ta musu..", Maama tace "ai kam yanxu zasu iya zuwa su gaisheni ranar da malam baya nan..", Sa'adatu ta taɓe baki tace "hmm wllh sunfi ƙarfin zuwa nan gidan, amma sbd yadda suke sona suka zo aka musu wulaƙanci, nidae bazan sake cewa suxo ba saidai ke kije ki gaishesu, in gaya miki babbar Hajiya mai gidan da muke zama ma ta dawo daga ƙasar waje, ashe gidan nata ne su Mabaruka da Zeenatu yaranta ne..", Maama tace "Aaaa sai naje ai..", Sa'adatu ta gama saka yamutsattsun kayan ta kwama jaka kamar gaske, alhalin jakar babu littafi ko ɗaya kayan sawa ne aciki, Nabilah dai ta taɓe baki don tana jin abinda suke cewa, Sa'adatu tace "toh Maama saina dawo.." da haka ta fita daga ɗakin, tin daga sama har ƙasa Umma ta dubeta kafin ta cigaba da tsintar wakenta, Sa'adatu ta ɗaga murya tana yamutsa fuska tace "Baba na tafi makarantar..", ko second ɗaya bata ƙara ba ta nufi soro ta cire higab din jikinta ta sauya da wani wanda ta fitar daga cikin jaka ta fita, Baba ya fito daga ɗakinsa yana kallon Umma yace "ina Sa'adatun..?", Umma ta nuna soro tace "ta fita..", Baba ya fita daga gidan, Maama ta fito daga ɗakinta tana baza zani ta kalli Umma tace "Munafuka Algunguma meye kuma nace masa ta fita ai cewa za kiyi ta tafi makaranta ba ta fita ba..", Umma ta ajiye farantin da take tsince wake tace "A'a baiwar Allah ya ina mgana da mai gidana zaki sako min baki.. nifa banason shisshigi da kwala kai a faranti, ko kinga ina shiga sabgarki ne...?", Maama ta ƙanƙance mici micin idanunta tace "Eh lallai Faɗima.. ni kike mayarwa da martani..?, Nii..?", Umma ta taɓe baki ta ɗauki farantin wakenta zata wuce ta wanke, Maama ta buga cinya tace "ahayye Eh lallai fa, yau ni naga muggun abu, wato ƴarki tayi aure gidan masu hannu da shuni shine kike fiffiƙalemin Faɗima..", da mamaki Umma ta juyo tana kallonta jin abinda ta faɗa, toh me ya kawo wnn magnar kuma, Maama ta cigaba da faɗin "toh ai saiki bari ƴar taki ta sha kafin ki fara fiffiƙalewa, dan da yardar Allah sai an gille mata kai an kawo miki gunduguilar a kwali..", Umma tayi murmushin ƙarfin hali tace "ki gani a ƙoƙon shanki, insha Allah babu abinda zai samu ƴata sai alkhairy da albarka..", Maama ta fito a fusace ta ɗauki taɓarya ta nufi Umma tace "ki sake cewa tak kiga idan ban jirga miki ita ba, shegiya ragowa.. dangin ubanki ma na Yola kasa zama sukay dake sbd baƙin hali..", Mu'azzam ne ya fito daga ɗakinsu idanunsa sunyi jajir, wajen mahaifiyarsa ya isa yace "Umma dan Allah koma ɗaki...", Umma tayi still tana kallon Maama ta kasa cewa komai, Mu'azzam ya sake cewa "dan Allah Umma", Umma ta kallesa sau ɗaya snn ta wuce ta shiga ɗakinta yabi bayanta, ganinta yayi zaune gefen gado hawaye na zuba idonta, ya isa gaban gadon ya durƙusa gabanta yace "Umma kiyi haƙuri dan Allah..", Umma ta share hawayen tace "Ibrahim idan tura ta kai bango ɗan Adam baya iya jurewa... kana ganin taɓarya ta ɗauka zata bugamin, me na mata ne a duniyar nan, ƙiyayyar bata tsaya iya kaina ba harku ta shafa, Hajara ma da ta bar gidan kullum sai an saka mata baki..", Mu'azzam yayi ajiyar zuciya yace "Umma insha Allah ba zaki ƙara wata biyar a gidan nan ba, akwai kuɗin da nake tarawa insha Allah zan siya miki gida ki koma can da zama..", Umma dai kawai kallonsa take kafin ta girgiza kai tace "ka gina gidan da zaka zauna dai Ibrahim..", ya girgiza kai yace "Umma saina gina miki gida snn zan iya gina nawa..", Umma tayi murmushi tana nuna masa kofin dake rufe kan mirror tace "ga kunun ka can..", ya tashi ya ɗauki Cup din yace "nagode Umma..", Umma tace "sai wani satin za a duba ɗaurin ko..?", ya kalli hannusa mai ɗaurin karaya yace "Eh" da haka ya fita a ɗakin da cup din kunun sa.

★Da misalin takwas na dare Nurain na zaune palourn Mami yayi resting da jikin kujera, Mami dake shan fruit salad ta dubesa tace "ai da zuwa kayi ka kwanta since you are exhausted..", ya buɗe idonsa dake a lumshe yace "yeah.. zuwa eight thirty zan wuce..", Mami tace "Okay.. wai hour nawa surgeryn ya ɗiba..?", ya sauke numfashi yace "5hours..", Mami ta gyaɗa kai tace "Ohk..", Noor ce ta shigo da plate a hannunta ta ajiye kan carpet tace "Yaya gashi..", plate din ya ɗauka ya buɗe, Mami ta leƙa ganin abinda ke ciki tace "wnn abar tana riƙe ciki ne, ko da yake ga protein a gefe..", Nurain ya ɗauki fork ya fara ci a hankali, yace "Mami i thought harda Sakeena a tafiyar naku..", Mami tace "yeah harda ita ai..", Nurain yace "opp amma babu passport dinta a wanda na amso..", Mami tace "Are you sure..", ya gyaɗa kai yace "sure", Mami tayi jim kafin tace "ohh zan tambayi Abba may be ya canza ne..", bayan Nurain ya gama cin abincin ya tashi ya wuce kitchen da plate din, wajen Mami ya shiga ya mata sallama ya fito, yana fita compound yaga wani gagarumin hadari ya haɗo, motarsa ya shiga ya kunna, agogon dashboard ya duba yaga nine dot, with his speed driving zai iya isa gida kafin nine twenty, yana kan hanya aka fara yayyafi, har dai ya isa gida ba a tsuge da ruwa ba, parking yayi a parking space ya fito yana amsa sannu da zuwan da Inuwa yake watso masa, balcony ya wuce yana murɗa door handle akai wata walƙiya mai shegen haske sai kuma wata tsawa mai burga ƴan hanji, tini ruwa ya tsuge kamar da bakin kwarya, a lokaci guda ji kake ɗiff wutar gidan ta ɗauke. Hajar ta fito daga wanka knn tana shirin buɗe wardrobe taji tsawar har ƙoƙon kanta, zuciyarta ta bugu da ƙarfi, bata gama daidaita ba wani mugun duhu ya kaure room din ko tafin hannunta bata gani, a hankali ta sulale ƙasa ta takure waje ɗaya, kawai saita tuna shekaran jiya da yace mata akwai Aljanu da dodo a toilet, wnn tunanin yasa ta sake firgita matuƙa, gashi batada waya ballanta ta kunna taga haske. Nurain ya tsuke piercing eyes dinsa dan wnn abu ne da bai taɓa faruwa ba, toh ai ko nepa aka ɗauke Solar da kanta take canzawa ba tare da an canza ba, wayarsa ya ciro daga pocket ya kunna torch, inda wutar gidan take ya wuce, yafi 20mins trying to figure out what is happening amma ya kasa cause it's out of his field, kwata kwata ya rasa mene ya jawo hakan, bayan ya gaji da taɓe taɓensa ya bar wajen ya wuce cikin gida, da fitilar wayarsa ya haska har ya haura upstairs ya shiga ɓangarensa, ba ƙaramin ɓaci ransa yayi ba gashi kuma ya gaji so yake ya kwanta ya huta, bathroom ya wuce yayi refreshing kansa ya fito yayi wrapping kansa da bathrope, after ya saka Pajamas dinsa kawai ya haye gado ya kwanta, yana lumshe idonsa yaji ta faɗo masa, zaune ya tashi ya zura room slippers ya fito daga bedroom din zuwa palour kafin ya fita long corridor din, after few seconds staring at the door ya buɗe ya shiga, kan bed ya fara haskawa yaga wayam, ya haska kan carpet nan ma yaga wayam, shiga ɗakin yayi sosai yana haska ko ina, shessheƙar kuka ya jiyo daga wajen wardrobe a ta gefen gado, wajen ya isa yana haskawa ya ganta ta haɗe kanta da guiwa ta dunƙule waje ɗaya, ɗauke kansa yayi ganin hasken fatarta, towel ne kawai a jikinta, Hajar ta ɗaga jajayen idanunta da suka kumbura tana kallonsa, ba tasan lokacin da ta miƙe ta faɗa jikinsa ba ta fashe masa da kuka, he just loose his stamina all of a sudden, ji yayi ƙafafuwansa kamar bazasu ɗaukesa ba, ita kam Hajar ƙanƙamesa tayi tana rusa kuka har kanta na sarawa, shoulder dinta ya taɓa yayi saurin ɗauke hannunsa daga wajen ya dafa bayanta, Calmly yace "Ke cikani..", ta girgiza kai ba tace komai ba, yana jin yadda zuciyarta ke bugawa, shi dai kawai yana dafe da bayanta trying to control himself......✍️
💛 HAJAR 💛

{57..}
A hankali ta zame jikinta a nasa kanta a ƙasa, sai kuma ta fara dube duben abinda zata yafa a jikinta tinda har lokacin towel ne a jikin nata, Nurain kam tinda ya ɗauke kansa bai sake kallonta ba, a hankali ta zaga ta bayansa ta wafci hijab dinta ta saka ta koma gefe tana zazzare ido, kawai gani tayi ya nufi ƙofa zai fita, afujajan tabi bayansa ta fashe da kuka tace "dan Allah karka barni a duhu..", ya juyo yana kallonta yace "toh ya kike so na miki..? dole ki zauna a darkness tinda baki jin tsoron yiwa elders dinki rashin kunya.." da haka ya murɗa door handle zai fita, tini Hajar tabi bayansa tana rusa kuka tace "na shiga uku wllh bana son duhu..", kallonta kawai yake wondering ydda kuka baya mata whala, duk wnn rashin kunyar ta ta abu kaɗan saita ɓare baki, komawa yayi cikin room din ya ajiye mata wayar akan mirror snn ya fita, Hajar ta sauke ajiyar zuciya tana turo baki sai kuma ta goge idonta, ta cire hijab ta ƙarasa shiryawa ta saka kayan bacci, riga ce wacca ta tsaya mata a knee, ta ɗakko pillow da duvet ta kwanta kan carpet, kasa bacci tayi don tsoro ma take ji a hakan duk da fitilar da ya bar mata, ga wani ruwan sama da ake ketawa shi kanshi sake firgita ta yake bare idan anyi tsawa, ta duƙunƙune a duvet idonta a runtse, har 11 idonta biyu kuma babu alamar bacci a tare da ita, a hankali Nurain ya buɗe ƙofar ya shigo, kallo ɗaya ya mata ganin idonta a rufe ya wuce ya ɗauki wayarsa ya nufi ƙofa, firgigit Hajar ta buɗe idonta ta miƙe tsaye, da sauri tabi bayansa ta fashe da kuka, still yayi bai juyo ba dan bai san idonta biyu ba, slight hiss yayi yace "ke wai kinada hankali ma kuwa, abin kuka baya miki kaɗan... c^mon wuce ki kwanta am leaving with my phone...", wani sabon kukan ta fashe dashi harda shessheƙa, Nurain ya maida duk attention dinsa kanta yana kallonta cike da mamaki, yarinyar nan kanta ɗaya kuwa, ya haska fuskarta wai yaga na ƙarya ne ko akwai hawaye, taɓe baki yayi ganin hawayen ma sai kace an buɗe famfo, da sauri ta juya masa baya tana ƙunƙuni wai ya haske mata ido, murya ƙasa ƙasa tace "ni ka dena haske ni..", ba tayi zaton ya jita ba kawai taji yace "ohh really... stay in the darkness" da haka ya fice daga ɗakin ya fita corridor, da gudu ta bisa still tana kuka amma kuma a hankali, bai juyo ya kalleta ba ya cigaba da tafiya yana jinta a bayansa har ya isa ƙofar ɓangarensa, yayi sliding door kafin ya juyo ya dubeta yace "yaya dai kike bina young lady...", ita dai ba tace masa uffan ba kanta na ƙasa tana jan fingers dinta tana shessheƙa a hankali, from head to toe ya dubeta da ƴar ɓingilar rigar baccinta iya guiwa, ko ina ta baro hijab din, Calmly yace "don't follow me...", kafin ya shiga ma ita ta rigasa shiga da mugun speed, buɗe baki yayi ya haɗe thick eyebrows dinsa strictly yace "hey get out before i smash you...", ta sunkuyar da kanta without saying anything, ja da baya tayi ta shiga palourn nasa sosai tana turo baki, ya sauke ajiyar zuciya ya isa kan three sitter ya zauna, sai a lokacin ta ɗaga kai ta kallesa sai kuma tabi palourn da kallo, duk da ba haske sosai amma tasan tsadadde ne huge and luxury, Nurain ya duba wayar yaga batteryn ta is running down, ajiyewa yayi kan hannun kujera yayi folding hands dinsa, after few seconds yayi slight hiss ya cire slippers din ƙafarsa ya kwanta kan kujerar, ba sai kuma yaga yadda za tay idan charge din ya ƙare ba, ya lumshe idonsa, nan inda take ta sulale ta zauna kan tiles ta jingina da bango, wani irin sanyi ne ya ringa shigarta, ga sanyin tiles ga kuma na gari da ake ruwa, tanata zaune a haka harta fara gyangyaɗi, takure kanta tayi ta kwanta a ƙasa, cikin bacci taji ana tapping dinta, a zabure ta miƙe tana zaro ido, ya mata nuni da kujera two sitter yace "hey koma can ki kwanta...", har ta turo baki zata lafta masa rashin kunya sai kuma ta fasa, tashi tayi ta tafi inda ya nuna matan ta kwanta, ko seconds 40 bata ƙara ba baccin ya sake ɗauketa, Nurain ya sauke ajiyar zuciya ya koma kan three sitter ya kwanta kafin ya janyo wayar ya kashe fitilar kar yaje ya rasa wcca zai haska da asuba tinda charge din ya kusa ƙarewa. ƙarfe biyar da minti uku Nurain ya farka, tashi yayi zaune yana karanto addu'ar da ma'aiki ya koyar damu, yayi stretching kansa ya lalubi wayar a inda ya ajiyeta ya kunna torch, slippers dinsa ya zura ya tashi ya shiga bedroom ya wuce toilet ya ɗora alwala, bayan ya fito ya saka wata light brown jallabiya ya fita palour, kallon Hajar dake dunƙule kan kujera yayi kafin ya ajiye wayar kan Centre table ya fita zuwa masallaci, koda ya dawo daga mosque a palourn downstairs yayi kwanciyarsa. Hajar ta buɗe idonta a hankali sai kuma ta miƙe zaune tana ƙarewa inda take kallo, kallon wayar dake kan Centre table tayi, ta ɗauki wayar sum sum sum ta nufi ƙofa ta fita, direct room dinta ta wuce, bayan tayi alwala tayi sallah, kan prayer mat din ta kwanta ta duƙunƙune da hijab ɗin da tayi sallah. shida da rabi ya shigo ɗakin, kallo ɗaya ya mata ya ɗauke wayarsa da ya gani gefenta ya fita, wayar harta mutu da kanta, ɓangarensa ya shiga ya ɗakko key din mota ya fito, downstairs ya sauka ya fita zuwa compound ya isa parking space, motarsa ya buɗe ya kunnata yayi plugging wayar a charge, a kunne yabar motar ya koma ciki ya shiga kitchen ya haɗa coffee, saida wayar ta ɗanyi chargi ya kira Engineer din da ya haɗa wutar gidan. kafin ƙarfe goma Engineer din har yaxo yayi fixing komai wutar gidan ta dawo. sai ƙarfe biyu na rana Nurain ya fita, hospital ya fara zuwa ya duba patient din da ya yiwa surgery jiya, alhmdllh patient din har ya farka kuma he is healing.

★Ruqayyah na kwance kan gado tunani fal zuciyarta, bude ƙofar ɗakin akay, Meema wacca take matsayin cousin dinta kuma age mate dinta ce ta shigo, Ruqayyah ta ɗaga kai ta dubeta, ƙarasa shigowa Meema tayi ta ajiye cup da plate dake hannunta a kan bedside tana kallon Ruqayyah tace "ga breakfast..", Ruqayyah ta tashi ta dafe kanta da ya sara, Meema ta ɗauki cup mai ɗauke da tea ta miƙa mata tace "ki daure kici abinci sai kisha drugs dinki..", amsar cup din Ruqayyah tayi ta fara shan shayin, sosai ya mata daɗi har taji appetite dinta ya dawo, da kanta ta ɗauki plate din dankali da kwai ta fara ci tana dangwalar ketchup, baifi rabi taci ba ta ajiye ta cigaba da sipping tea, Meema dake zaune gefenta tana latsa waya tace "yauwa kinga yanzu ai kyaji kwarin jikinki sister..", gyaɗa mata kai kawai Ruqayyah tayi, bayan tasha drugs dinta ta koma ta kwanta, kuka ta fara yi a hankali, tin Meema bata ankara ba har ta gane, with care ta ɗora hannu akan goshinta tana tambayarta is she okay, Ruqayyah ta girgiza kai da kyar tace "not at All.. zuciyata zata fashe Meema..", Meema tace "please tell me what happened..?", Ruqayyah ta tashi zaune ta jingina da allon gadon tana sauke silent tears tace "Meema bazan taɓa dawowa daidai ba indai Dearest bai dawo gareni ba..", da mamaki Meema ke kallonta tace "waye kuma Dearest...?", Ruqayyah tace "Dr..", Meema ta ƙanƙance ido tace "wai Dr Uthman wanda aka fasa aurenku..?", Ruqayyah ta gyaɗa kai hawaye na zuba idanunta, Meema was very shocked, kan uba anya Ruqayyah kalau take, Meema ta mayar da hankalinta sosai kan Ruqayyah tace "sister ba ke kika gudu sbd ba kya son auren ba..", Ruqayyah ta girgiza kai tace "wllh tllh ba guduwa nayi ba, wai wane mashahurin maƙaryacin ne ya laƙaba min wnn sharrin yake yamaɗiɗi dani wai bana son aure na gudu, nifa bance bana son auren ba wllh Allah..", Meema tayi ajiyar zuciya tace "what are you trying to say sister..?", Ruqayyah tayi shiru ba tace komai ba, Meema na kallonta da kyau tace "toh a fahimta ta yanxu dai so kike ki auri Dr ko..?", Ruqayyah ta gyaɗa kai tace "amma ya zanyi sister, na rasa inda zan dosa, Dr yaƙi ya kulani, Daddy yace zai auramin Dauda bacogala, har gidan sister Kulsoom naje itama wai tace na haƙura da Dr, kiji fa wai na haƙura.. anya kwa ta san mene ne so..", Meema tace "me sister Kulsoom din tace miki..?", Ruqayyah ta share hawayen idonta ta shiga gaya mata ydda sukay da Kulsoom lokacin da taje gidanta, Meema ta jinjina kai tace "gaskiya ta gaya miki wllh, kuma nima na goyi da bayanta, babu ta yadda za ai Dr ya dawo gareki Ruqayyah, karfa ki manta ranar aurenku kika tsallake kika barsa, yanzu dan yace baya sonki ni banga laifinsa ba wllh, ke kika jawa kanki, zan ƙara akan abinda Kulsoom ta gaya miki kawai kiyi haƙuri ki rungumi sorry, Allah ya baki wanda ya fisa...", katseta Ruqayyah tayi da faɗin "yaushe kika fara shan wiwi da Sholisho..?", Meema tace "what..?", Ruqayyah ta daka wani uban tsaki tana zabga mata harara tace "ki bari duk ranar da kika haƙura da justice sai ki gayamin haka..", ta sauka daga kan gadon ta shiga bathroom, Meema ta taɓe baki tace "kece za kiyi ta zama a ƙoshin wahala..", Ruqayyah ta fito wanka ta shirya cikin uniform dinta, gwara dai ta fita aiki duk da yau ma ba tayi niyyar zuwa ba, handbag dinta ta ɗauka ta fita ɗakin, Haj Safiyya ta tarar da Meema a palour suna breakfast, Ruqayyah ta durƙusa ta gaidata da ladabi, Haj Safiyya tace "lfy lou Ruqayyatu, ya jikin naki..?", Ruqayyah tace "da sauƙi..", Haj Safiyya tace "ba dai fita za kiyi ba..", Ruqayyah tace "wajen aiki zan tafi..", Haj Safiyya tace "toh za dai ki iya zuwa ko..?", Ruqayyah ta gyaɗa kai tace "Eh" da haka ta tashi ta nufi door, Meema ta bita da kallo. Ruqayyah na zuwa hospital ta fara aikinta, dan Nurse Jiddah ta gaya mata daf ake da bata query, tana tsaye gaban bed tana shirya post Anesthetic bed, forcep dake hannunta ta ajiye cikin tray tana jin wani jiri na ƙoƙarin ɗebeta, duk dai dagewa take tana so tayi aikin, luu tayi baya zata faɗa kan suction machine tayi saurin dafe bed, wani Nurse namiji da yake ward din ya iso inda take yace "are you okay...?", ta girgiza kai tace "partially", yace "alright ki wuce station i will handle it..", tace "thank you in 10mins za a kawo patient din daga surgery..", yace "alright..", Ruqayyah ta wuce station ta kwanta a room dinsu na female Nurses dake asibitin.

★Washe gari da yamma Nurain ya isa gidansu, yana shiga main palour ya tarar da Sakeena a zaune, daman yaga motarta a compound, ƙarasa shiga palourn yayi ya zauna opposite to her yana kallonta, tace "brka da shigowa brother, ya sister na..?", yace "she's great alhmdllh...", ta gyaɗa kai tace "good to yaushe zaka kawo min ita..?", ya ɗage thick eyebrows dinsa yace "sooner or later", Sakeena ta gyara zama tana kallonsa tace "brother serious talk how is the girl..? ba wani matsala ko..?", ya sauke ajiyar zuciya yace "i can't say all is well amma dai kinsan she is not my choice and not my type, alfarma kawai nake mata na zauna da ita snn kuma sbd Abba..", babu wani kwana kwana ya fadi hakan don yadda suka saba da Sakeena baya iya ɓoye mata komai kuma baya mata ƙarya, Sakeena tayi jim don tinda yace mata haka tasan hakan ne, shi kam wayarsa ya ciro yana dannawa, ɗaxu ne suke mgana da Mami shine Mami tace ta tmbayesa tinda tasan ydda suke dashi, dan Mami tana suspecting kamar auren is not stable, Sakeena tace "brother..", still yana latsa wayarsa yace "Na'am", shiru tayi ba tace komai ba, ya ɗago ya kalleta ganin kallonsa take ya waro ido yace "yess..", ta mayar da attention dinta kacokan kansa tace "why are you saying that... the words choice and type bai kamata ka ambace su ba, gwara ma dai favor din, brother idan fa baka saki jiki da ita ba babu ta yadda za ai ku saba, kaga ita maca ce zata ringa shakkarka ko kuma taƙi sakin jikinta da kai as her husband, kaga dai ba tada wani aibu physically and she is beautiful masha Allah, halinta kawai zaka karanta shknn fa kuma am very sure she must be a good girl with that innocent face..", wani murmushi yayi jin abinda ta faɗa, wai she must be a good girl with that innocent face, chab lallai ba tasan wace ce yarinyar nan ba, Calmly yace "Ohh yeah really..", Sakeena ta haɗe gira tace "bafa joke nake a nan ba..", yace "yeah nima ai ba wasa nake ba, wollah alfarma na yiwa yarinyar nan kuma sbd Abba nake zaune da ita, ni a yanzu ma aka bani pen da paper tsaf xan yankar mata ticket... ammafa sai Abba ya yarda.. kinga da zaki temakamin ki masa mgana ya yarda na saketa da na baki tukuici.." yana gama faɗin haka ya tashi ya nufi stairs yace "i have something to do..", Sakeena ta bisa da kallo tace "hey come back here am not done with you..", ya juyo yana kallonta sai kuma yayi murmushi yace "saidai ki canza topic bansan maganar wollah", Sakeena was shocked tace "ita kwa zamu cigaba..", bai ce mata uffan ba ya wuce zai hau stairs sai kuma ya fasa ya dawo palourn yana kallonta yace "where is our Mami..?", ta juya hannu alamar ban sani ba, ɓangaren Mami ya shiga, after like 10mins ya fito ya haura sama, babu jimawa Mami ta fito, tana kallon Sakeena tace "nan kika zauna daughter..?", Sakeena tace "dana fito wajen Abba shine na zauna nan kawai..", Mami tace "Ohk" lokacin da ta zauna, Sakeena ta buɗe wayarta ta shiga message ta haskawa Mami credit alert daya shigo 30mins back tace "from Abba", Mami tace "keda partner din naki za a bari knn..?", Sakeena tace "yeah, nasan damuwar Abba grandkids dinsa kuma fa da can wajen paternal grandma dinsu zan kaisu, nayi shirina mu keta haxo, amma yace nan da 5 months insha Allah sai mu tafi da Nurain with his wife..", Mami ta gyaɗa kai tace "Ohk", Sakeena tace "Mami i talk to him fa, in my view ba wani matsala insha Allah..", Mami tace "are you sure..?", Sakeena ta ƙirƙiri fake smile tace "Sure", Mami tayi ajiyar zuciya tace "toh alhmdllh, bana san wata tangarɗa ta faru a auren ne..", Sakeena ta sake yin wani fake murmushin tace "ba abinda zai faru sai alkhairy insha Allah". kafin magrib Sakeena ta tafi, as usual Nurain bai bar gidan ba saida ya yiwa Maminsa sallama. washe gari da safe Nurain na zaune palourn downstairs yana shan coffee, Hajar ce ke sakkowa daga kan stairs, saura step biyu ta kai ƙasa sai kuma ta dakata tana kallon palourn, Nurain ya sauke cup of coffee da ya kai baki ya dubi stairs din, da sauri ta sauke idonta ƙasa sai kuma ta juya a hankali zata koma sama, lower lip dinsa ya cixa painlessly, daga throat maganar ta fito bayan ya runtse idonsa ya buɗasu a hankali yace "Hajar..", cak Hajar ta tsaya amma bata juyo ba tana riƙe da railer, a hankali ta juyo ta kalli palourn sukay ido huɗu, ta juyar da kanta tana wasa da hannunta dake riƙe da railer, Nurain ya tashi daga kan sofa walking towards the stairs yace "let's work together", ta zuba masa lulu eyes dinta tace "work together as in how..?", yace "young lady nasan ba kya san zama anan ko..? i mean ba kya son auren..", gyaɗa masa kai tayi tace "sosai ma kuwa" ta haɗe girarta mai kyau tamkar wcca aka zana mata ita, ya jinjina kai yace "same here, as i said let work together, kina jina yanzu ki kawomin jotter da pen dana baki..", tsuro tayi tana kallonsa lokaci guda kwanyarta ta amsa, biro da takarda, da sauri ta juya ta haura sama, babu jimawa ta dawo da jotter with pen riƙe a hannunta, yana zaune kan exclusive sofa ta dawo, tunani yake is he doing the right thing, ajiye masa pen da jottern tayi ta koma gefe ta harɗe hannayenta, ya ɗaga kai ya dubeta yace "then listen, abinda nake shirin yi yanxu shine zanyi ending komai dake tsakaninmu, zan rubuta miki saki, ni da ke kowa yayi rayuwarsa munyi freeing juna, kin fahimta..", tinda ya fara magana take kallonsa, da sauri ta gyaɗa kai tace "da kwa ka kyauta idan ka sauwaƙe mana", yayi ajiyar zuciya yace "but idan na rubuta duk abinda ya biyo baya kece za kiyi bearing consequences din...", without thinking twice tace "na amince..", daman abinda take so knn, wani nishadin daɗi ne ya tsarga mata zuciya, Nurain ya dauki biron da jottern ya ɗora kan Centre table, buɗe jottern yayi ya ɗora pen ya fara rubutu.....✍️

Masu comments a ringa yi kullum Please ku sani ba doc ne a ajiye ba, sai nayi typing nake posting, snn kuma am occupied kawai dai ina squeezing inayi ne, plxx be patient... more love 🥰
💛 HAJAR 💛

{58..}
A hankali yake rubutun, Hajar na tsaye ta ƙurawa hannunsa idanu, Alla Alla take ya gama ya miƙo mata, shknn tinda safiya ce sai ta fara haɗa kayanta da wuri, Allah ya rabata da wnn jarababben auren ta ruwan sanyi, Nurain ya dakata da rubutun ya ƙurawa papern ido, ya sauke numfashi lokaci guda ya ɗaga takardar ya fara yayyagata, Hajar ta zaro ido ganin abinda yake tace "meye haka kuma..?", bai ce mata uffan ba ya cigaba da yaga papern, saida ya mata gutsi gutsi ya watsar da ita nan kan Centre table din, with speed ya tashi ya haura sama, Hajar tabi bayansa da kallo wasu hawayen baƙin ciki suka ciko mata idanu, bata san lokacin da ta fashe da kuka ba, ita taga samu kuma taga rashi, shknn ya yaga shedar da zata nuna cewa babu aure a tsakaninsu, to wace shaida ma ai bata saku ba ma tinda ba taga me ya rubuta ba, jar uba knn dai auren yana nan daram ko girgiza bai yi ba, zubewa tayi a ƙasa ta shiga rafsa uban kuka sai kace wacca akaiwa mugun duka, saida taci kukanta ta ƙoshi sai kuma taja jiki ta matsa kusa da Centre table din tana kallon pieces din takardar, shessheƙa take a hankali ta fara ƙoƙarin arranging din papern wai ko zata gane mai ya rubuta, saidai fa abin yafi ƙarfin ƙwaƙwalwarta don kwata kwata ta kasa gane farko ma bare aje ga tsakiya ballantana ƙarshen rubutun, har alphabets din ma bata iya ganewa sbd yadda yayi rubutun sai kace prescription, takaici yasa ta tattare pieces din takardar ta shiga kitchen ta kunna gas ta barbarɗa takardar ta ƙoneta, fitowa tayi daga kitchen din tana cika tana batsewa, still ta tsaya a bakin ƙofa sakamakon amsawar da brain dinta tayi, gsky tayi ragon azanci, da ba saita ajiye pieces din in yaso ta nunata a matsayin shaida, sai tace itace ta yaga amma ba a cikin hayyacinta ba, da sauri ta koma kitchen din ta matsa gaban gas, ta ringa kallon tokar papern tana jin haushin kanta, tamkar wacca kwai ya fashewa haka ta fito ta haura sama, tsaye tayi tana kallon huge sliding door din shiga ɓangarensa, ta koma ta jingina da bango still tana kallon ƙofar, after like 10mins saiga shi nan ya fito, he changed into sweat pant and white shirt irin dai shigar da yake ta zaman gida, har wani coiled black hair dinsa yake sbd yadda yaji oil yana shining, kallo ɗaya ya mata ya dauke kai ya rufe ƙofarsa, ya zura hannunsa a pocket ya wuce zai sauka downstairs, da sauri tace "kace fa zaka rubutan takardar kuma fa baka bani ba...", cak ya tsaya kafin ya juya yana kallonta, ganin yadda idonta ya haura ya taɓe baki don yasan tabbas halin nata tayi, ya ɗage gira yace "wace takarda kike magana akai..?", ta haɗe rai ta buɗe baki da nufin lafto masa rashin kunya sai kuma ta fasa, ta sauke idanunta ƙasa tana jan slim fingers dinta tace "wacca kace na kawo maka jotter da pen zaka raba tsakaninmu..", yace "ohhh that i was only joking..", zaro ido tayi ta sha kunu tace "bangane ba.. meye kuma joking daman ana wasa da saki ne..?", ya ɗaga shoulder yace "wait ni cewa nayi zan sakeki ma, toh what's the point idan nace zan wani sakeki, all i know ni nasan banida wata mata bare na rubuta mata saki..", wata shegiyar harara ta galla masa tana yamutsa fuska tace "ai kwa dai kaji kunya.. sangameme da kai kana yin magana biyu, saura ƙiris ka zama maƙaryaci, toh wllh daka rubuta da kar ka rubuta nidae na saku kuma a yau ba sai gobe ba zan bar gidan nan, koda yake ma ai ka rubuta ka yaga kuma..." gumm tayi ganinsa gaf da ita, ba tayi aune ba sai jin wata mummunar gwabza tayi a bakinta, har taste din blood saida taji a bakin, habawa sai kace an fesawa wuta petrol haka ta hasala, ta murguɗa baki tace "toh ƙarya nayi ba magana biyun kayi...", bai bari ta ƙarasa ba ya sake buge bakin da ɗan ƙarfi, har cikin kwakwalwar kanta taji zafi, ta rutse ido tana buɗewa sai zirr hawaye suka fara zarya, tsit bakin tsiwar ya mutu duk da irin hargowar rashin kunyar da ke taso mata, yana kallon cikin idonta yace "yeah you can leave ko an gaya miki zan dakatar dake ne, the door is open young lady you are free, tinda kinada evidence din da zaki nuna.." yana gama faɗin haka ya barta tsaye a wajen ya sauka ƙasa, Hajar ta goge hawayen da ya jiƙa mata cheeks tace "hmmm kamar yadda kere ke yawo kaza ma take yawo toh haka takardar sakina take a hannunka, ko bajima ko ba daɗe saika sakeni wllh tllh, kai asuwa da zaka zauna da aurena" sai kuma tayi shiru kafin tayi kwafa tana jin haushin kanta da ta faɗi hakan, ta buɗe ƙofar ɗakinta ta shiga tana cewa "kai ka isa ka aureni". Compound Nurain ya fita, Inuwa ya ajiye watering can da yake bawa flowers ruwa yabi bayansa zuwa parking space, shi dai yasan ranar Asabar boss din nasa baya fita da wuri, ya ɗan russuna yace "Alhaji barka da fitowa", sama sama Nurain ya amsa masa don Silly girl dinsa ta hayaƙasa kafin ya fito, buɗe black car ɗinsa yayi ya shiga yace "buɗen gate..", da rawar jiki Inuwa ya tafi buɗe gate, Nurain ya zura key a ignition ya tashi motar, resting yayi da kujera yana jiran ta gama warming, motar na gama warming ya fara driving yabar gidan, after a ride of about 30mins ya isa inda zashi, parking yayi gaban wani ƙaton warehouse, bayan ya kashe motar ya fito, wasu mutane biyu ne kan benci a gaban warehouse din, Nurain ya isa inda suke, da sauri ɗaya ya miƙe don ya gane Nurain, russunawa zaiyi Nurain ya miƙa masa hannu, ya ɗan russuna yace "barka da zuwa Alhj..", Nurain yace "yauwa mal Ɗayyab..", gaisawa sukay da ɗayan mutumin wnda abokin mal Ɗayyab ne, mal Ɗayyab yace "wajen za a duba Alhaji...?", Nurain yace "Eh", mal Ɗayyab yace "toh" da haka yaje ya buɗe ƙatuwar ƙofar warehouse din. Nurain baifi 20mins a wajen ba ya wuce bayan ya yiwa mal Ɗayyab alkairi da ya saba a duk sanda ya ziyarci warehouse din nasa. daga nan Mall Nurain ya wuce yayo Grocery shopping, yana parking motarsa bayan ya iso gida ya buɗe booth, da kansa ya ringa ɗiban ledojin abinda ya siyo yana shigar dasu ciki, bayan ya gama sigar da komai ya buɗe kitchen ya shiga, saida yayi refilling freezer da fridge duk da cewa kaɗan aka ɗiba, ya ajiye coffee powder da ya siyo itama a cupboard. throughout the day yana ɓangarensa bai sake fita ba, saidai lokacin sallah ya je mosque, bayan ya dawo daga sallar la'asar ya shiga kitchen, tsaye ya ganta a bakin gas tana zuba seasoning a jollof rice da take dafawa, yayi kamar baima san da ita a kitchen din ba ita ma hakan tayi, plate ya ɗauka ya buɗe fridge ya ɗauki bunch of grapes one Apple sai kuma pea itama guda ɗaya, ya koma gaban sink ya buɗe tap ya sake wanke fruits din duk da cewa a wanke suke, Hajar dai ta masa kallon wutsiyar ido tana taɓe baki, wnn tarkacen ne abinci chaɓ, ita tinda take dashi ma bata taɓa ganin yaci abinci ba sai shan coffeen tsiya ma malam, yana gama wanke fruits dinsa ya bar kitchen din... washe gari da ta kasance Sunday da misalin ƙarfe sha ɗaya na safe Hajar ta fito wanka ɗaure da towel, as usual ta gama rubbing lotion a fatarta da a yanxu take wani azabar glowing, don shower gel da man da take shafawa masu kyau ne da tsada, warware jelar gashinta da ta tufke tayi domin tajewa za tay don bata son ya danƙare mata, saida ta jiƙasa da hair butter snn ta sharce, riga da skirt na atampa ta fiddo ta saka, tayi ɗaurin ture kaga tsiya, tsaf ta feshe jikinta da turare snn ta saka takalmi ta fita daga ɗakin, ido huɗu sukay dashi shima ya fito daga ɓangarensa waya kare a kunnensa, kallon da ta ga ya watsa mata ne yasa ta dubi kanta, ta tabe baki ta wuce ta fara sauka daga stairs tana cewa "uhmm gani ba taɓawa ba asarar ido". Nurain ya gyara wayar dake kunnensa bayan Hajar ta ɓace masa daga gani, duk da irin turaren da yake jikinsa amma saida yaji ƙamshin nata, Sakeena jin brother din nata yayi shiru na almost 40sec tace "hey Nurain kana ji kuwa..?", yace "yeah", tace "Au ko bazaka kawomin ita bane iyee... tin jiya fa nake maka magiya tinda dai kai bakayi hankalin kawota wajen next mother ba har saida na roƙa saika kawomin ita..", yace "ohh God ki bari sai next week ni yanxu har na shirya fita zanyi fa..", tace "and where are you heading to..?", yace "zanje gida snn kuma inada wasu appointments", Sakeena tace "Alright first dai gida zaka fara zuwa right..?", yace "Eh", tace "ba saika biyo tanan ka kawomin ita ba..", yace "Okay..", tace "yawwa.." da haka tayi breaking call din, Nurain ya sauke ajiyar zuciya ya saka wayar a pocket, toh shi ta ina ma zai fara ɗaukar yarinyar na ya fita da ita, ba ma wnn ba me zaice mata ne. palourn downstairs ya sauka ya zauna kan kujera yana kallon ƙofar kitchen, babu jimawa sai gata nan ta fito da cup din black tea sai plate na indomie, da yake idonsa akan ƙofar yake aikam sukay ido huɗu, ita ta fara ɗauke nata ta wuce zata haye sama, a ranta saida tayi danasanin fitowa without hijab, don sosai ta tsargu da kallon da yake mata, kawai saukar muryarsa taji a kunnenta "idan kin gama ki ɗakko veil dinki ki sameni a nan..", still tayi a inda take ba tare da ta waiga ba, ta wani taɓe baki ta haye sama abinta, bayan ta gama cin abincin ta sauka da plate da cup din, har lokacin yana zaune palour yana latsa wayarsa, agogon wrist dinsa ya kalla lokaci guda ya miƙe yace "damn it", tana fitowa daga kitchen yace "3mins kije ki ɗakko veil dinki", tayi kamar ba taji abinda yace ba tayi wucewarta, har 3mins ta wuce babu alamar zata sakko, thick eyebrows dinsa ya haɗe ya haura saman, da ɗan karfi ya buga ƙofar ɗakin nata har saida tayi ƙara, Hajar dake zaune gefen gado ta miƙe zumbur tana zaro ido, saukar da idanunta tayi ƙasa don sosai ya mata kwarjini, with stern voice yace "are you mad... me nace kiyi..", ba ta bari sun haɗa ido ba tana jan fingers dinta tace "toh wai ina ruwanka dani da za kace na ɗauko mayafi na sameka a ƙasa.. meye hadina da kai.." ta ƙarashe tana turo baki, wata tsawa da ya daka mata har saida ta tafi da baya ta ƙume da bango tsabar gigicewa, ba tasan lokacin da ta buɗe wardrobe ba ta ɗakko mayafin da hannunta ya fara taɓawa, shivering jikinta ya fara hawaye ya cika idonta, murya ƙasan maƙoshi yace "Silly girl.. zo ki wuce", ko yafa mayafin ba tay ba haka ta nufi ƙofa da sauri ta fita bayan ta saka takalminta, tini idanunta suka cicciko da ruwa, yana biye da ita har suka sauka ƙasa, sai a lokacin ta warware mayafin ta yafa, color dinsa ya shiga da zanen flower dake jikin atampar da ta saka, main door ya buɗe yace "wuce", ba musu ta fita tana turo baki, rufe ƙofar yayi da key ya zura a pocket, kallon dressing din nata yayi yaga ba wani aibu kafin ya wuce gaba, bayansa tabi zuwa parking space, ya buɗe motar kafin ya buɗe front seat yace "get in..", ƙasa ƙasa ta nasa masa harara kuma ya lura da hakan snn ta shiga, ya rufe mata ƙofar ya zaga driver seat ya shiga motar, already Inuwa ya buɗe gate, suna isa bakin gate din Nurain ya tsaya yana kallon Inuwa yace "ba kowa a gidan a kula sosai..", Inuwa ya russuna yace "Allah ya tsare hanya..", Nurain yace "Ameen" da haka yaja motar suka bar gidan, suna fita daga street din gidan Hajar ta ɗaga kai ta ɗan kallesa, ko ina zai kaita oho, a hankali ta koma ta jingina da kujera ta lumshe idonta sbd kanta da ya fara juya mata, tinda suka hau main road ya take accelerator kawai falfala gudu yake, wani burki yaci bayan ya kaucewa wani tricycle ya cigaba da falfala gudu abinsa, tini Hajar ta buɗe idonta ba tasan lokacin da ta riƙe hannunsa dake kan gear ba tace "ni wllh raina guda ɗaya ne karka salwantar min da abuna... na shiga uku, wayyoh Ummana..", sai kuma ta fashe da kuka ta kifa kanta kan hannunta data damƙe nasa, ya ɗan kalleta kafin ya ɗauke kai yana kallon road yace "hands off", gam ta riƙe masa hannu taƙi cikawa kuma bata dena rusa masa kuka a motar ba, shi dai baice mata uffan ba ya cigaba da driving din da hannu ɗaya, slowing down yayi, a hankali Hajar ta ɗago tana shessheƙa, tayi sauri ta goge hawayen cheeks dinta ta koma ta zauna da kyau tana jan zuciya, a bakin gate din wani gida yayi parking, ya kalli dogon hannun rigarsa da ta jiƙa masa da hawaye, ya juya yana kallon side view din fuskarta, idonta har ya haura, girgiza kai yayi yace "sauka", buɗe motar tayi ta fita, shima ya buɗe ya fito ya ciro wayarsa daga pocket yayi dialing numbern Sakeena, tana picking yace "gani a gate fa..", tace "haba ku shigo mna.." katse wayar yayi ya nufi gate din shiga gidan, da car key yayi knocking, mai gadi ya buɗe ƙofar gate din, ya waiga yana kallonta sai kuma ya juya ya shiga gidan, da sauri tabi bayansa. ba ƙaramin farin ciki Sakeena tayi ba, sosai tayi welcoming Hajar, Hajar dai murmushin yaƙe kawai take, bayan sun gama gaiswa da few minutes Nurain ya ajiye little Ayman da tin zuwansa ya makale masa yace "i gotta go...", Sakeena tace "Ohk.. bazaka jira na gama abinci ba..", yace "yeah am full" da haka ya miƙe yana jan rigarsa, Sakeena tace "uhmm inka dawa kaci toh don favourite dinka ne...", yace "Ohk" da haka ya nufi door, tsugul Hajar ta miƙe tana gyara yafen mayafinta, Sakeena ta sakar mata murmushi tace "Ai ke kina nan..", wani daram Hajar taji ya buga a zuciyarta, kawai sai taji ba ta son ta zauna a nan din, ganin bata koma ta zauna ba Sakeena tayi murmushi tace "Okay see him off dear", kafin Hajar ta fito har Nurain ya isa gate, ai kam da gudu tabi bayansa, har ya buɗe mota zai shiga yaga fitowarta, dakatawa yayi yana kallonta har ta iso gaban motar ta tsaya, yace "ina kuma zaki ki koma cikin gida", ta maƙe shoulder tace "A'a ni bazan zauna ba..", ya tsuke ido irin what sai kuma yayi smirk ya shiga mota, da sauri ta zaga driver seat ta riƙe handle din ƙofa, zirrr hawaye suka fara sauka idonta, ajiyar zuciya yayi ya buɗe motar ya fito, from head to toe yake kallonta, yace "ke wai kinada hankali ma kuwa... me aka miki..?", sai kace wnda ya zigata kawai ta fashe da kukan gaba ɗaya, ya kalli street din yaga dai babu kowa, ya rage murya yace "karki taramin jama'a malama, wani abun akay miki kike ɓarewa mutane baki..?, ko an gaya miki inda za a cuce ki na kawoki, you see that woman she is my elder sister kuma ita tace na kawo mata ke, and i can't say no to her, ki wuce ciki malama no one is going to harm you..", kukan take a hankali tana jinsa, lokaci guda ta fara tafiya a hankali ƙafarta na harɗewa ta nufi gate din gidan, bayanta yabi tana daf da shiga gidan ya riƙo hannunta.......✍️
💛 HAJAR 💛

{59..}
A hankali ta juyo tana kallon hannunta da ya riƙe, ya saki hannun nata fuskarsa ba yabo ba fallasa yace "Please kar kije ki ringa yiwa mutane kuka, i told you no body will harm you.. kinji ba..?", ta haɗe gira tace "naji..", hannu ya zura a pocket dinsa ya ciro handkerchief ya miƙa mata yace "wipe those tears..", kallon handkerchief din tayi ta kai hannu zata amsa sai kuma ta fasa tace "no thank you" da haka ta juya zata shiga gidan, still tayi a bakin ƙofar ba ta shiga ba, ta juyo tana kallonsa sai kuma ta kai hannu ta amshe handkerchief din daga hannunsa tana turo baki, daga nan bata ƙara ko 1sec a wajen ba tayi wucewarta, kafin ta shiga ciki ta tsaya ta goge fuskarta da handkerchief din da pure designer scent dinsa ne kawai yake tashi a jiki, tass ta goge fuskarta perceiving the scent kafin ta shiga cikin gidan, a bakin ƙofar palour ta tarar da Sakeena, Sakeena ta sakar mata murmushi tace "kin raka san..?", Hajar ta gyaɗa kai tana kallon ƙasa, sosai Hajar taji daɗin spending wnn ranar a gidan Sakeena, ta lura dai ƴan uwansa sun san darajar mutane kuma sun iya karrama su, haka Noor ma take kula da ita lokacin da take gidansu, ga Mami ma wacca take ganin a wajenta suka gado wnn sassanyan halin mai kyau, shi kaɗai ne ya fita bare a cikinsu don ta canfa shi mugun hali garesa, Hajar ta ajiye plate din hannunta mai ɗauke da snacks a ƙasan carpet, Sakeena dake zaune palourn tare da ita tace "toh taso muje ciki kiyi sallar ko..", Hajar ta miƙe tana gyara yafen mayafinta, ɗaya daga cikin three bedrooms da take dashi ta kai Hajar ta nuna mata toilet, a hankali Hajar ta cire veil dinta ta wuce ta shiga toilet din, bayan tayi alwala ta fito tana ƙoƙarin ɗaura ɗan kwalinta Sakeena ta shigo hannunta riƙe da babban hijab da prayer mat, da kanta ta shimfiɗa mata darduman snn ta ajiye mata hijab din a gefen gado, Hajar tace "nagode", Sakeena tace "you're welcome" da haka ta juya ta nufi door, Hajar tayi ajiyar zuciya kafin ta dauki hijab din ta saka ta tayar da sallah. tana idarwa ta naɗe dardumar ta linke hijab din shima ta ajiye gefe guda snn ta saka mayafinta ta fita, palour ta koma ta zauna tana kallon damfareriyar Tv dake aiki a palourn, bata jima da zama ba akai knocking door, saida aka sake knocking snn ta kalli ƙofar kafin ta tashi ta buɗe, wata budurwa ce wacca bazata wuce 23yrs ba, tace "wajen Anty Sakeena nazo..", Hajar ba tace mata komai ba ta matsa mata hanya ta wuce, kan carpet ta samu ta zauna, Sakeena ce ta shigo palourn tana kallon Hajar dake zaune kan sofa tace "na barki ke ka ɗai ko..?", Hajar dai tayi murmushi ba tace komai ba, yarinyar dake zaune kan carpet tace "Anty ina wuni..", Sakeena tace "lfy lou Bilkisu.. bari na ɗakko comb da kibiya", Comb da kibiya Sakeena taje ta dakko ta kawowa mai kitson nata, ana gamawa Sakeena kitson tace "saura ke Hajar..", Hajar ta nuna kanta tace "Ni", Sakeena tace "daga gani baki son kitso ai naga kan naki ba a kitse yake ba", medium kitson Kalba akaiwa Hajar wnda aka tsagasa kamar fashin kwakwa jelar ta yarfo ta gefen kunnenta har ƙasan shoulder dinta. Da misalin takwas na dare kiran Nurain ya shigo wayar Sakeena, picking tayi tace "yess brother..", yace "gani a ƙofar gida can i come in...?", Sakeena ta kalli Hajar tace "Au nasha ai anan zaka bar min ita ta ɗan kwana biyu", cire wayar yayi daga kunnensa ya kalli screen din kafin ya mayar kunnen yace "Ohk.. good night.." har zai katse wayar tace "ka shigo we need to talk", tana katse kiran ta kalli Hajar tace "kije kiyi sallar isha'i kafin yazo ko..", Hajar tace "toh" ta tashi tana noƙe kai sbd kitson da akay mata don ta tsani kitso. babu jimawa Nurain ya shigo, Aymana da brother dinta da suke kallon catoon suka ruga wajen uncle din nasu, murmushi yayi ya riƙo hannayensu suka ƙarasa shiga palourn, ya zauna kan kujera ya damƙa musu ledar sweet da chocolate da ya siyo masu, Aymana dake da wayo tace "thank you Uncle..", Ayman ma ya kwaikwayi sister din tasa yace "shenkiyu Anchul", Sakeena tace "oya go to your room kuyi game a tab", da gudu suka ruga zuwa room din nasu da ledar chocolate dinsu a hannu. Nurain na kallon sister din tasa yace "Amm Madam...", Sakeena ta ɗauki remote control na TV ta rage volume ta maida nutsuwarta kansa tace "please karka min wani wala wala brother, ranar nan muna mgana a gida ka ringa mayar da ita not serious", Shafa kansa yayi ya sauke ajiyar zuciya yace "ya subhanallah... in dai wnn mganar ne ai mun gama, nafa gaya miki komai..", ta haɗe gira tace "ka gayamin komai as in how...?", ya gyara zamansa yace "listen sister you need not to worry, your brother here bashi da wani matsala ke kinfi kowa sani aii..", tayi tsaki tace "in banda kafiya ba, idan ka kafe akan abu ai babu me iya juya maka ra'ayi..", yace "Nah..?", tace "yess you", yace "Okay fine, nasan duk mtsalan dai akan wnn yarinyar ne kuma na gaya miki ni favor kawai na mata nake zaune da ita cause she's not my type and choice..", Sakeena tace "but Abba's choice right...", ya ɗaga shoulder baice komai ba, Sakeena tace "sai dai ka saki jiki da ita snn zaka gane wace ce kuma kaima tasan wane kai.. i think I told you" ta ƙarashe faɗin hakan ne lokacin da ta miƙe tsaye, kitchen ta shiga ba ta daɗe ba ta fito, ta ajiye trayn da ta fito dashi kan Centre table ta koma ta zauna a position dinta tace "gashi nan na ajiye maka abincin da kace sai ka dawo zaka ci", ya shafa kansa yace "am full..", ta galla masa harara tace "open it first kafin kace wani am full..", ƙaramar warmer din ya buɗe yaga miyar spinach ce da taji lafiyayyen smoked fish da pure palm oil, medium warmer din kuma pounded yam da zafinta don da magrib ta ruɗata, kallonta yayi yace "Please serve me..", zuba masa tayi, kaɗan yaci ya ture ya zuba ruwa a glass cup yasha, few minutes ya miƙe yana jan rigarsa yace "Good night, a miƙan gaisuwa wajen Abban kids", tace "Ohk, baya gari ma next tomorrow zai dawo insha Allah", yace "Ohk", ganin ya nufi ƙofa kai tsaye ta bisa da kallon mamaki kuma da gaske fita zaiyi tace "Nurain your wife", ya juyo yace "Ai kince na bar miki ita ta kwana..", Sakeena ta buɗe baki kafin tace "we are not from same planet... ka jira matarka ku wuce gida" tana kaiwa nan ta shiga ɗakin da Hajar take, zaune ta sameta kan carpet ta jingina da jikin gado, tin ɗazu da ta idar da sallah ta tashi zata fita tana gaf da palour taji muryarsa da scent dinsa shiyasa ta dawo ɗakin tayi zamanta, har compound Sakeena ta raka Hajar da ledar da ta haɗa mata sha tara ta arziƙi, ganin fitowarsu Nurain dake tsaye bakin gate ya fita, Hajar ta yiwa Sakeena godiya tana riƙe da ledar da ta bata ta fita, ta ringa kallon motarsa da already ya bude ya shiga, sauke kanta tayi ta ƙarasa ta buɗe front seat ta shiga ta rufe, ya ringa kallonta kamar a lokacin ya fara ganinta, kaifin idonsa akanta yasa ta juya ta ɗan kallesa, ido huɗu sukay tayi sauri ta ɗauke kanta tana kallo window ta turo baki, murya ƙasan maƙoshi yace "nuna min inda aka gutsira a jikinki..", da sauri ta juya ta zuba masa lulu eyes dinta ba tace komai ba, yana kallon cikin idonta yace "uhmmm answer me young lady..", haɗe gira tayi ta zare idonta daga cikin nasa ta kalli window, ajiyar zuciya yayi ya kunna motar, a ɗan firgice Hajar ta juya jin saukar numfashinsa a saitin fuskarta, ta sake shigewa cikin kujera ganin fuskarsa gaf da ta ta, yasa hannu ya janyo seat belt ya mata fastening, ya ɗan kalli slim pointed nose dinta kafin ya sakko da idanunsa zuwa pink lips dinta, slowly ya kai dubansa kan wuyanta that is fair ya hango jelar gashi biyu da ta leƙo ta sauka akan fatar wuyan, Hajar ta sake shigewa cikin kujera da cracking voice tace "stop staring at me..?", gaba ɗaya hancinta ya cika da ƙamshinsa and she can even feel his breathing, ya ɗago idonsa yace "is there anything to stare at...", ya koma ya zauna a seat dinsa ya ɗora hannunsa kan steering, after few seconds ya sauke handbrake ya fara driving, ita dai tinda ta kalli window ba ta sake gigin juyo da kanta ba, kawai irin kallon da ya mata ne ya tsaya mata a rai, ta ringa nanata gani ba taɓawa ba asarar ido a zuciyarta, saida suka hau babban titi ta fahimci dalilinsa na ɗaura mata belt, ai kam ta runtse idonta gamm ta jingina da kujera ko kyakkyawan motsi ba tay ba. suna isa gida yayi parking motar, sai a lokacin Hajar ta buɗe idonta, ƙoƙarin cire belt din ta fara amma ta kasa, ganin tana kiciniyar cirewa ya matso ya cire mata yana lura da yadda ta runtse idonta, da sauri ta buɗe motar ta fita ta nufi entrance, shima fitowa yayi ya rufe motar da haka yabi bayanta, ya ciro key ya buɗe ƙofar entrance, ba ta ko kalli inda yake ba ta shige ciki direct kuma ta haura sama da ledarta a hannu, bayanta yabi da kallo yana sauke ajiyar zuciya, ya sakawa ƙofar lock ta ciki kafin ya haura sama zuwa ɓangarensa.

★Da safe Maimuna da Sa'adatu suna shirinsu na zuwa schl din gogi, Sa'adatu har ta saka uniform tana zaune ƙasan leda tana irga kuɗin da suke rage mata, kallon Maimuna dake shafa BSC cream a fuska tayi tace "wai ke Maimu me yasa kin fiya hauka da baragada ne, nace miki ki dena shafa irin wnn mayukan a fuskarki amma kinƙi ji, ba kya jin kunya a dubi hannunki da fuskarki aga uban banbanci...", Maimuna ta rufe robar man tace "ba kiga safa nake sakawa a ƙafa ba, hannun kuma na ƙunshesa a hijabi, wllh duk masifarka baka isa ka gane ainahin launi na ba", Sa'adatu ta taɓe baki bata ce komai ba, Maama ta shigo tana gyara ɗaurin ƙirji tace "Au baku gama shiryawa ba.. yakamata kuyi da jiki dan ga malam can tsakar gida yayi takkwaba nasan so yake yaga kun fita..", Sa'adatu ta tashi ta saka hijab dinta na uniform ta ɗauki jakarta, Maimuna na gama shiryawa suka fito tsakar gida tare, Sa'adatu ta ɗan haɗe rai ganin Baba kafin ta wurga masa wata shegiyar gaisuwa daga tsaye, kallonta kawai yake bai amsa ba, Maimuna ta gaishesa irin mai spring din nan wcca da ita gwara babu, itama bai amsa mata din ba, Baba yace "ina kuke zuwa idan kuka fita daga gidan nan da nufin makaranta..?", Sa'adatu tace "ina kwa zamu idan ba makaranta ba..." bata rufe baki ba Baba ya gaura mata mari, Maimuna ta kwalalo ido jikinta na rawa, Sa'adatu dake riƙe da kuncinta tace "daman ni nasan Baba ka tsaneni a gidan nan, kawai sai ka zabgan mari dan ka tambaye ni na baka amsa", Baba ya juya yana kallon ɗakinsu Naseer yace "Nasiru zo nan", daga cikin ɗakin Naseer ya amsa babu jimawa ya fito, tini marasa kunyar suka sha jinin jikinsu, Naseer ya ƙaraso kusa da Baba ya rage tsaho yace "gani Baba..", Baba yace "yaran nan kullum idan suka fita daga gidan nan da shirin zuwa makaranta toh ba ita suke zuwa ba, ranar Alhamis naje makarantar tasu wajen principal yake gayamin tin ranar da aka kaisu basu sake zuwa ba, wata bakwai knn basa zuwa makaranta", da wani irin takaici Naseer ya dubi ƙannen nasa, tsawa ya daka musu yace "ba zaku tsugunna ba kuka wani tsaya ƙerere", zubewa sukay a ƙasa ko wacce na zare idanu, Baba yace "su gaya maka inda suke zuwa, kuma daga yau na soke zuwa makarantar...", babu irin barazanar da Naseer bai musu ba amma ko wace shegiya taƙi faɗar inda take zuwa, Naseer na kallon Baba yace "Baba ka bari na naɗi halittar yaran nan tinda an bisu ta lallami da arziƙi sunƙi su bada haɗin kai..", Baba ya girgiza kai yace "A'a Nasiru idan icce ya bushe bazai tankwaru ba, duka na nawa kuma, da ace suna jin duka da babu wacca zata sake laifi a cikinsu, rabu dasu Allah ya shiryesu, kawai dai kar wacca ta sake fita a gidan nan...", sai kuma ya kallesu da wani irin takaici yace "ku tashi ku ban waje, Allah ya shiryeku..", bazar bazar suka miƙe suka shige ɗaki, Naseer ya bisu da kallo zuciyarsa na tafasa don ji yake kamar ya bisu ɗakin ya farfasa musu jiki. Maama dake tsaye jikin labule kaff ta ji abinda ya faru, hura hanci kawai take tana gyatsine, ta lura dai ƴaƴanta aka sakawa idanu a gidan nan, zanin data ɗaura a ƙirji ta kunce ta dawo dashi ƙugu, gaba ɗaya alherin nata sun zube sai kace slippers, wata Tshirt me warin dauɗa ta saka ta fita daga ɗakin tana hura hanci wnda ya kusan cika fuskar tsabar ydda yake kamar tukuba, ɗakin Baba ta afka babu ko sallama, Baba ya dakata da sargafe kayan da yake jikin raki ya juya yana kallonta, ta ƙarasa ciki still tana hura hanci tace "mal ka ringa jin tsoron Allah kuma ka ringa kwatanta adalci a tsakanin ƴaƴan da Allah ya baka..", Baba ya gyara tsayuwarsa yana kallonta da kyau, tace "kawai saika ringa bin diddiƙin yara kana musu bita da ƙulli duk dan ka gano laifinsu, meye na binsu kaga inda suke zuwa, tinda Hajara take zuwa makaranta ka taɓa bin bayanta ne sai su, sbd daman ka tsanesu kuma baka sonsu, toh rabbil izzati dai yana sama yana gani... haba dan Allah kuma hakan duk bai isheka ba saida kazo bainar nasi a tsakar gida ka titsiyesu kana musu terere, toh a gsky nagaji karka sake wulaƙanta min ƴaƴa..", Baba ya sauke ajiyar zuciya ya nuna ƙofa yace "fitar min daga ɗaki..", ta sake hura hanci tace "bazan fita ba saina gama amayar da abinda yake zuciyata, ita waccar shegiyar mai salalon tsiya ai harta gama karatun baka taɓa titsiyeta kace ina ta tafi ba sbd ita ƴar mowa ce, su kuma su Sa'adatu da suke borori har neman laifin da zaka liƙa musu kake, karfa ka manta kafin ayi ɗaran akay kwanɗi ehee saida ka samesu kafin ka samu ita Hajarar ƴar gaba da fatiha..", ba ƙaramin hasala Baba yayi ba, ƙirjinsa har zafi yake masa, da kakkausar murya yace "nace ki fitar min a ɗaki..", ta taɓe baki tace "nan nan kaje ka nannago uban kayan abinci munaji muna gani ka aikawa Hajara...", katseta yayi da faɗin "Rabi daga yau baki da dama ko hurumin shigo min ɗaki har abada kuwa, igiyar auren da ta rage a tsakaninmu itama na datseta kije na sakeki..", Maama ta kwalalo mici micin idanunta waje ta dafe ƙirji bakinta na rawa tace "Adamu ni ka saka...? Ni..?", ta fashe da matsanancin kuka, Baba yace "zan rufa miki asiri babu wanda zai san babu aure a tsakaninmu, idan kinga dama sai kije ki yiwa kanki terere a bainar nasin da kika faɗa, amma daga yau babu ni babu ke kuma na shata miki layi da shigowa ɗakina", kuka Maama take wiwi harda fyace majina tace "da girmana da gemu na saida tsufa ya fara kamani zakamin irin wnn sakin na wulaƙancin", a fusace Baba ya fita ya bar mata daƙin don ko ganinta baya son yi, bayan wani lokaci Maama ta fito daga ɗakin idonta sun suntuma sun sake ƙanƙancewa, Umma dake gaban rariya tana rege wake ta ɗaga kai ta kalleta, Maama tace "shegiya mayya uwarki kike kallo", Umma ta ɗauke kai tana taɓe baki, Maama ta shige ɗakinta tana cigaba da rusa kuka, ƴaƴanta sukay cirko cirko akanta suna tambayarta lfy, babu wnda ta tankawa, gaba ɗaya ta wani gigice ta susuce, abu ɗaya take ta maimaitawa wato "da girmana da gemu na".

★Da wuri Hajar ta farka da safe sbd jiya da wuri ta kwanta, ta shiga toilet ta tsala wankanta ta fito ɗaure da towel, gaban mirror ta tsaya tana kallon kitson kanta, ta warware jelolin da ta naɗe da zata shiga wanka, taja stool ta zaune tayi shafe shafenta, tana gamawa ta dakko kaya ta saka, kasa ɗaura ɗan kwalin kayan tayi sbd har wani zugi fatar kanta ke mata, wata hula mara nauyi mai santsi ta saka, daga haka ta feshe jikinta da turare mai sanyin ƙamshi wnda ke cikin kayan da Sakeena ta bata jiya, a hankali ta buɗe ƙofa ta fita, shima a lokacin ya buɗe ƙofar ɓangarensa, da sauri ta ɗauke kai ta wuce ta tsaya gaban stairs ba tare da ta fara sauka ba, juyowa tayi taga yana tunkaro stairs din, ba tare da ta kalli gabanta ba kawai ta saka ƙafarta zata fara sauka, ai kam ƙafar tayi gaba suu, kawai ji tayi an fixgota baya, yasa hannu ya tallafo ƙugunta ta baya yayinda ita kuma ta damƙe gaban rigarsa ta yiwa kanta support, wani juyin masa yayi da ita ya jinginar da ita da bango, har lokacin hannunsa ɗaya na riƙe da ƙugunta ɗayan kuma shoulder dinta, Hajar ta ajiye numfashi kafin ta buɗe idonta ta ringa kallon hannunta da har lokacin yake damƙe da rigarsa, da sauri ta sakesa ta haɗe rai, ɗago kanta tayi ta kallesa wnda hakan yasa ya dena ganin baƙin gashinta da hular kanta ta zame sbd santsinsa, kawai kallon eye balls dinta yake, ta sauke idonta tana jin ƙamshinsa har ƙwaƙwalwar kanta, a bazata ta sake ɗaga kai tana kallonsa jin yayi motsi da hannunsa dake ƙugunta, ta juya lulu eyes dinta tana kallonsa tace "please let go off me"......✍️
💛 HAJAR 💛

{60..}
Kallonsa take tana jira ya saketa, ta ɗan turo baki tana turesa da iya ƙarfinta amma ko gezau, zaro ido tayi jin ya janyota jikinsa sosai, zuciyarta ta buga da ƙarfi ta fasa masa ƙara da iya volume dinta, da sauri ya saketa ya toshe kunnensa, da gudu ta shige room dinta tayi banging door, ƙofar da ta rufe ya kalla yace "Silly girl..", ya zura both hands dinsa a pocket kafin ya sauka downstairs, kitchen ya shiga yayi making coffee ma kansa, riƙe da cup din coffee da saucer dinsa ya fito ya haura sama, a tsakiyar makeken bed dinsa ya zauna, ya janyo Laptop ya kunna, yana operating system din at same time yana sipping Coffee, he was just starting at the monitor while his mind was totally not there, wani thinking din yake daban, ya ajiye cup din kan bedside, ajiyar zuciya yayi yace "Silly girl..", ya kalli agogon da yayi tickling 8 dot, ya ɗauki wayarsa yayi dialing numbern mai masa wankin mota yace masa yazo ya ɗauki motar, yana gama wayar ya tashi ya shiga bathroom, tsaf ya gama shirinsa ya ɗauki briefcase dinsa ya sauka downstairs, compound ya fita ya wuce parking space, babu jimawa kira ya shigo wayarsa, mai wankin motar ne ke kira ya sanar masa cewa yazo, direct Nurain yace ya shigo, bayan me wankin motar ya tafi da black car dinsa ya shiga other car din tasa ya bar gidan, hospital ya wuce wajen tara saura, tini ya fara attending patient da suke Queue suna jiransa, ƙarfe sha biyu saura ya gama da patient din, zaune yake kan office chair dinsa yana kallon glass nameplate mai ɗauke da sunansa, yayi stretching kansa feeling a bit better don ya gaji da zaman, knocking door akay yace "yess", Dr Marwan ne ya shigo da file da big sealed envelope a hannunsa, ɗaya daga cikin kujeru biyu da suke gaban table ya samu ya zauna, exchanging greetings sukay, Dr Marwan ya ajiye file da envelope din kan table yace "here nayi recording komai, ga hoton thorac din nan shima..", Nurain ya gyaɗa kai yace "what about the heart..?", Dr Marwan yace "itama akwai hoton ta", Nurain yace "alright i will check it later..", Dr Marwan yace "Ohk.. this week ne zaku tafi symposium din ko..?", Nurain yace "yeah it's going to start next week monday toh i think before then zamu tafi...", Dr Marwan yace "Ohk Lagos ne ko Abuja..?", Nurain yace "Abuja ne", Dr Marwan yace "okay.. sai anjima" da haka ya fita daga office din. Da yamma Nurain na zaune palourn Mami, Noor ma na zaune itama da Apple Laptop dinta tana kallon wani Chinese movie tana cin croissant, Nurain yace "kun gama exams din ne Noory..?", Noor tayi pausing movie din tace "yeah..", yace "saura jiran result", tace "Eh", wayarta ce ta fara ringing, ɗaukar wayar tayi tana satar kallon Mami sai kuma ta miƙe a hankali ta bar palourn, Nurain na kallon Mami yace "Mami yaushe ne tafiyar naku..?", tace "ohh i think ranar Saturday haka naji Abba yace", Nurain ya gyaɗa kai bai ce komai ba, sai ƙarfe takwas ya yiwa Mamin tasa sallama kafin ya bar part din nata, ya fita babban compound din gidansu, Noor ce ta fito compound din itama da small carton box a hannunta tace "Yaya", ya dakata da tafiyar ya juya yana kallonta har ta ƙaraso tace "Ya ga wnn please ka kai ma Hajar" ta fada tana miƙa masa box din, amsar box din yayi yace "sure", tace "thank you... good night" da haka ta wuce cikin gida, Nurain na isa gida direct ɓangarensa ya wuce, bayan yayi wanka ya saka white pajamas masu sweat pant, yayi combing hair dinsa kafin ya zura room slippers ya fita paloun sa, ajiyar zuciya yayi ya ɗauki box din daya ajiye kan kujera ya fita ɗakin, murɗa ƙofar room dinta yayi ya shiga bayan yayi sallama ƙasan maƙoshi, Hajar dake zaune kan carpet ta rufe jikinta da duvet bayanta jingine da bed ta ɗago ta kalli ƙofa, da sauri ta ɗauke kanta, ya ajiye box din kan makekiyar chest of drawers dake room din, ganin ya fara tafiya towards her tayi sauri ta kwanta ta rufe har ka tana turo baki, ya duƙa kusa da ita muryar ƙasan maƙoshi yace "hey", wata shegiyar harara ta shiga bankawa daga cikin duvet sai kace wata psycho, tapping dinta yayi yace "hey..", tini ta yaye rufar ta miƙe zaune tace "ni ka dena taɓani babu kyau fa, it's not proper", ta matsa baya tana harararsa ƙasa ƙasa, yace "then who said ki ringa kwanciya a nan..?", tace "ra'ayi", yace "everyone thinks you are a good gal basu san cewa you are just a hyena with goat skin ba, you gat an innocent face but you are so harsh and rude...", ya nuna mata box din da ya ajiye yace "from Noor ɗaya daga cikin mutanen da kikay deceiving don nasan bata san bad attitude dinki ba..", Hajar ta ƙura masa idanu tana jin zafin kalamansa, da kyar ta iya cewa "are you done.. please off the light idan zaka fita", da haka ta koma ta kwanta ta rufa har ka tana jin raɗaɗin abinda ya gaya mata, hawaye ya ciko idanunta ta fara shessheƙa a hankali, yess tasha zagi sosai a wajen siblings dinta don shegiya ma suke kiranta, gashi dai shi ba zaginta yayi ba kawai mgana ce ya gaya mata amma sosai ta taɓa mata zuciya, har lokacin yana duƙe gefenta yana jinta, duvet din ya kwashe daga jikinta, tayi sauri ta tashi zaune ta haɗe kanta da guiwa, ya haɗe thick eyebrows dinsa strictly yace "shut up... me aka miki zaki ɓarewa mutane baki", chaɓ mgnarsa wofi don cigaba da tayi da kukanta a hankali, ɗago kanta yayi tana jin hakan ta fixge ta ja da baya, kanta a ƙasa tace "Please dan Allah na roƙeka kawai ka sakeni, ka bani takarda ta ko kuma ka furtan da baki nayi tafiyata..", kallonta kawai yake cike da mamaki kafin yace "amm young lady you are asking the wrong person, i think i told you ni banida wata mata bare na rubuta mata saki", ta ɗaga kanta ta ɗan kallesa sai kuma ta mayar tana kallon yatsun ƙafarta tace "Okay toh kawai just imagine ni matarka ce kace ka sakeni shknn..", duƙar da kansa yayi to cover the slight smile on his face kafin ya ɗago girarsa a haɗe yace "never... i will never imagine you as my wife and you will never be.." yana gama faɗin haka ya tashi ya nufi ƙofa saida ya kashe mata fitilar snn ya fita, Hajar ta gyaɗa kai ta koma ta kwanta. Ranar Friday ƙarfe 1 Nurain ya fita zuwa mosque kuma bai dawo gidan ba sai yamma, yana shiga palour yaji wani ƙamshin turaren wuta ya huda masa hanci, ya ringa ƙarewa palourn kallon deeply in his mind yana appreciating, ƙofar Kitchen aka buɗe sai gata nan ta fito tana kakkaɓe hannunta, turus tayi tana kallonsa dan yau three days knn rabonta dashi, ta yamutsa fuska ta haura sama walking slowly, ɓangarensa ya wuce direct ya shiga bedroom, farin yadin jikinsa mai kyau ya cire ya shiga wanka, bayan ya fito daga wankan ya shiga closet ya ɗakko black Shirt na polo with trouser, yana gama shiryawa ya ɗauki car key ya fita, har ya sauka downstairs sai kuma ya tsaya yana kallon stairs din, lokaci guda ya juya ya koma saman, ƙofar ɗakinta ya buɗe, zaune ya sameta kan tiles tana yanke farce with nail cutter, ta ɗaga kai ta masa kallo ɗaya sai kuma ta cigaba da abinda take, Calmly yace "ki ɗakko veil dinki zamu fita..", with weird expression ta kallesa ba tace komai ba, ta sunkuyar da kanta tana kankare farcen, yace "kinji me nace kuwa..", a hankali ta gyaɗa masa kai, yace "toh ai banga kin tashi ba", jimm tayi sai kuma ta tashi ta ajiye nail cutter din a kan mirror, well ironed hijab ta ciro daga wardrobe ta saka, fita yayi daga ɗakin tabi bayansa tana harararsa ƙasa ƙasa, tana biye dashi har zuwa parking space gaban motar da taga ya tsaya, ya buɗe lock ya shiga, tsaye tayi taƙi buɗe motar ta shiga, fitowa yayi yana kallonta yace "get in malama kina ɓatamin lokaci..", ta maƙe shoulder tana jan fingers dinta tace "nidae saidai mu hau Napep..", zaro ido yayi yace "what.. tricycle..?", ta gyaɗa kai ba tare da ta dubesa ba, yace "toh me yasa zan hau Napep bayan ga car dina..?", tace "toh shknn ka hau motar naka nidae napep zan hau", kawai kallonta yake, she's so childish, wataran idan ta maka abu sai ka dauka wata babbar macen ce, daga zarar ta kwaɓa maka wata shiriritar anan zaka gane yarinya ce shataf, haɗe gira yayi yace "kee!! shiga mota bana son shirme", harde hannu tayi ta juyar da kai tana ƙunƙuni, zagayowa yayi ya buɗe front seat, ba tay aune ba taji ya fixgi hannunta ya sakata a motar ya kulle, ya zaga driver seat ya shiga, hawayen da ya zubo cheek dinta tayi ƙoƙarin gogewa da bayan hannu don kar ya gani amma kuma saida ya ganin, har suka bar unguwar suka hau saman titi zuciyarta bugawa take da ƙarfi, sosai ya gane ƙin hawa motar da tayi yasan speed dinsa take tsoro, with minimum speed yake jansu don karta hargitse masa kafin su isa inda zasu, suna karya kwanar gidan Abba ya juya ya kalleta for the first time yace "Ke!!..", ta ɗan kallesa tace "Hajar", yana driving slowly har ya tsaya gaban makeken gate din gidansu yace "whatever... na kawoki nan don ki yiwa Mami sallama cause gobe zata bar gari, nayi hakan ne sbd yadda suka daukeki amma ni dai a wajena you don't worth it" yana gama faɗin haka ya danna horn, mai gadi ya zuge masa gate ya shiga yayi parking a compound, ya kashe motar yace "and behave yourself..", ya buɗe motar ya fita, fitowa tayi itama, shi yayi leading dinta har katafaren main palour wnda ba baƙonta bane, ya nuna mata kujera yace "sit" kafin ya wuce part din Maminsa, three minutes da zamanta a palourn taji footsteps ana sakkowa daga sama, ta ɗaga kai sukay ido huɗu da Noor, Noor ta ware ido tace "Ohh my God... is this you Hajar", murmushi Hajar tayi ta gyaɗa mata kai, Noor ta ƙarasa inda take tana welcoming dinta sosai, Noor ta zauna gefenta tace "yaushe kika zo..", Hajar tace "just now..", Noor tace "amma dai tare da yaya kike ko..?", Hajar ba ta kai ga amsa mata ba aka bude ƙofar part din Mami, Nurain ne with a repartee yana kallon Hajar yace "come in" ya juya ya koma ciki, Noor tace "muje can din", tare suka shiga ɓangaren Mamin, Hajar ta gaida Mami da ladabi, amsa mata Mami tayi with care ta tmbyeta lfyrta, Nurain dai kawai satar kallonta yake ganin yadda ta koma wata saliha sai kace gske. kafin Magrib hajjaju Hajiya ta iso gidan tare da Farooq da ya kawota, a main palour tayi branching don daman idan tazo gidan anan take fara zama, zuwan Hajiya yasa Mami ta fita main palour wajenta, Nurain ma ya tashi ya fita, Noor ta riƙe hannun Hajar tace "muje muma mu gaida Iron lady". Hajiya ta ringa kallon duk wanda ya gaisheta ta ƙasan kantamemen glasses dinta, sai kuma ta amsa a fixge alamar ƴan rigimar ne a kanta, Hajar na gaisheta itama ta ƙura mata ido sai kuma tace "Ahh ahha wai matar Usuman ce..", Noor tace "Eh itace", Hajiya tace "ywwa yanxu naga kiwo mai kyau.. da Usuman yaƙi sakin abinci a gidansa gaba ɗaya yarinya ta tsomare har ta fara fita hayyacinta, ynxu kam alhmdllh ai ta mayar da komaɗarta har ma ta ƙara", Hajiya ta kalli Mami tace "wnn tuwon naki na alkama nake son ci wllh", Mami tayi murmushi tace "toh Hajiya bari na duba garin" da haka ta tashi ta bar palourn ta shiga kitchen, Hajar dake zaune gefen Noor ta ɗaga kai ta kalli Farooq da yake kallonta, saukar da idanunta tayi tace "ina yini", da fara'a ya amsa yace "how are you doing..?", tace "fyn alhmdllh..", Nurain ya ɗago kansa daga latsa wayar da yake ya dubi Farooq, miƙewa yayi ya saka wayar a pocket yace "mu wuce mosque lokacin sallah yayi punk" bai jira cewarsa ba ya nufi door, Farooq ya tashi yabi bayansa, a tap din dake compound suka tsaya yin alwala, Farooq na tsaye bakin pampon yana jiran Nurain ya gama shima yayi yace "naga ma ai ba a kira sallahn ba", Nurain na wanke ƙafarsa yace "Eh mu zama ready kafin a kira..", Farooq yace "Ohk", Nurain na gama alwalar Farooq ma yayi, daga nan suka fita zuwa mosque wnda sai ynxu ma aka fara kiran sallah. Hajar na zaune kan darduma bayan ta idar da sallahr magrib a dakin Noor, cikinta ne ya ƙulle tana jin kamar cramps amma dai bata tabbatar ba, Noor ta shigo tana murmushi from ear to ear tace "kixo inji Hajiya", Hajar ta ɗan zaro lulu eyes dinta tace "Okay", ta tashi tabi bayan Noor suka wuce part din Hajiya, turus Hajar tayi a bakin ƙofa ganinsa a palourn Hajiyar shi da Farooq, Noor dai ta wuce ta zauna kan sofa ta cigaba da chatting dinta a phone, Hajiya dake zaune kan lallausan rug tace "ƙaraso ciki mana ƴar nan", a hankali Hajar ta wuce ta zauna kan Carpet, Hajiya tace "yauwa ko kefa ƴar nan", Hajiya ta juya tana kallon Farooq tace "mai gidannn..", Farooq yace "Amaryasss", Hajiya tace "ina dubulan da Alkaki da ka kwana biyu kana ci a wajena...", Farooq ya gyaɗa kai yace "yess wnn masu daɗin", tace "ƴar Albarkar yarinyar nan ce ta ciko min leda dasu, ai naji dadin kayan zaƙin nan don duk ranar da na cii saina shi mata albarka... mai gidann na gaya maka sam fa batada rowa wllh tllh..", Farooq yayi murmushi yana kallon Hajar yace "ni kam rowa tamin da naje..", Hajar ta ɗaga kai ta kallesa tace "Ai baka zauna ba kana zuwa ka tafi", yace "Okay dana zauna da za a ban..?", ta gyaɗa kai tace "Eh", Nurain da ke zaune sai kace an dasa sa ya kalli Farooq sai kuma ya kalli Hajar, haɗe gira yayi ya tashi sai kace wnda aka mintsila yana kallon Farooq yace "i gat something to tell you...", Farooq yace "Ohk then tell me", Nurain yace "privately.." sai kuma ya nufi ƙofa ya buɗe ya fita, few seconds Farooq ya tashi yabi bayansa, a main palour ya tarar dashi zaune kan sofa, ya ƙarasa ya zauna yana kallonsa yace "what is it that you want to tell me...?", Nurain yace "nothing let stay here..", Farooq ya tsuke ido baice komai ba kawai ya tashi zai bar palourn, Nurain yayi saurin dakatar dashi da fadin "lets go to my room i will tell you there", Farooq dai ya kallesa baice komai ba, Nurain yayi tapping shoulder din Farooq yace "c^mom punk". Bayan fitarsu Nurain Hajiya ta taɓe baki tace "yau naga jalala shifa wnn fel wayar bai fiya san jama'a ba, yazo ya zauna min a kujera yayi wani ƙwamm dashi ba uhmm ba umm ummm sai kace bebe, kuma wnda muke ƴar firar ma ya ɗauke mana shi.. Allah dai ya kyauta da wnn hali", sai kuma ta kalli Noor tace "jeki amsomin tuwo na", Noor tace "toh iron lady" ta tashi ta fita, Hajiya ta zura hannu a ƙatotuwar jakarta ta ɗakko kwalbar man zafi tace "temaka min ƴar nan..", Hajar ta amshi kwalbar ta buɗe, albarka Hajiya ta shiga ɓarkawa Hajar bayan ta gama mulke mata ƙafafuwa da man zafi, Hajiya tace "tararrabin hawa jirgin nan nake don bana son zama a kujera kumburan ƙafa yake...". Ƙarfe tara saura Nurain ya fito daga great room din Abba bayan ya yiwa Abba sallama da cewar gobe da safe zaizo ya ajiyesu a airport don jirgin 8 zasu bi, Hajar ta shiga part din Mami don mata sallama, da ladabi tace "Allah ya kaiku lfy ya dawo daku lfy..", Mami tace "Ameen daughter Allah yayi albarka", har compound Noor ta raka Hajar, Nurain ya gama maganar da yake da Garba snn yaxo ya buɗe motar ya shiga, sallama sukay da Noor ta buɗe motar ta shiga, ta kalli window ko kallon position dinsa ba tay ba, driving ya farayi suka bar unguwar, koda ya hau babban titi baiyi irin gudun da ya saba ba amma dai gudun yake. gani tay kawai ya samu gefen titi ya tsaya, ita dai ta cigaba da kallon window ba ta kallesa ba, after few seconds taga dai basu cigaba da tafiya ba sai ta ɗan juya ta kallesa, kallonta taga yana yi without blinking, ta haɗe rai ta juyar da kanta, yace "So daman kinada manners..", ta juyo ta galla masa harara ta ɗauke kanta, yace "and kin kware wajen yiwa maza magana ko"......✍️
💛 HAJAR 💛
Chapter 5 · 0% Book details