Chapter 47.... Arewabooks @ feenerhfeeche02
Hajar Part 1 Complete Hausa Novel · about 25 min read
💛 HAJAR 💛
Feenerh feeche ce
{47..}
Da mamaki Nurain ya ringa kallonta dan bai taɓa tunanin da ita akay surgeryn ba Nurse Amina ba, Ruqayyah ta sauke idonta ƙasa a hankali tace "the surgery was a success, alhmdllh..", baice mata ƙala ba ya juya ya fita daga surgery room din ya barta tsaye, tabi bayansa da kallo hawayen da suka taru idonta suka fara bin kuncinta, fita tayi daga room din bayan ta gama matsewa, ta cire surgeon gown kafin ta wuce Nurse station, bag dinta ta buɗe ta ɗauki black Abaya ta ɗora saman uniform dinta, daga haka ta saƙala jakarta a shoulder ta yiwa colleagues dinta sallama ta bar hospital din, tana fita titi ta tari napep ta gaya masa unguwar da zai kaita, shiga napep din tayi bayan sun gama ciniki, tafiyar minti ashirin ce ta kaisu unguwar, ya shiga da ita har layin da ta masa kwatance, sauka tayi daga napep din ta buɗe handbag dinta ta ciro kuɗinsa ta basa, ya miƙa mata chanjinta yaja machine dinsa, wani gida mai brown paint da black gate ta dosa ta fara knocking, almajirin gidan ne ya buɗe mata, bayan ta shiga ya gaisheta ta amsa a takaice kafin ta nufi entrance din gidan, ta buɗe ƙofa ta shiga palour da sallama, ƙarewa palourn dake tashi da ƙamshin turaren wuta gauraye da na freshner kallo take sai kace wani baƙonta, ta sake yin wata sallamar kafin ta zauna kan kujera, ƙofar wani room dake palourn aka buɗe, Kulsoom ta fito da 2months old babyn ta goye a baya tana jijjigasa, ganin Ruqayyah tace "Ruqayyatu kece kika ta sallama sai kace wata baƙuwa..", Ruqayyah ta cire ƙaramin hijab dinta tayi resting da kujera tace "ina wuni sister..", Kulsoom ta ƙaraso cikin palourn tana jijjiga babyn dake ƙishi ƙishin kuka tace "mun yini lfy...", Ruqayyah tace "alhmdllh..", Kulsoom na kallon fuskar ƴar uwarta ta da ta lura tayi duhu tace "kin kwaso rana..", Ruqayyah tayi ajiyar zuciya tace "kawosa naga kamar kuka zaiyi..", Kulsoom ta kwanto babyn ta miƙa mata tace "rigimamme ne wllh.." da haka ta wuce kitchen, Ruqayyah ta ringa kallon Babyn kafin ta lakuce masa hanci tace "shine kake wa sister na kukan banza ko, tubarkallah ga ka dai narkeke sai kace ba watanka biyu ba bare ace yunwa kake ji", ta ringa patting soft cheeks dinsa, deeply in her mind taji dama babyn ta ne, da anyi aurenta da Dearest da tini itama ta kusa haifar baby, Kulsoom ta fito kitchen da tray a hannunta, ajiye trayn tayi kan Centre table tace "toh ga ruwa kisha kafin na gama girki na ga kinyi wani wujiga wujiga...", Ruqayyah tace "na gaji ne, kuma gashi na shiga surgery yau na 3hours", Kulsoom dai ta gyaɗa kai tace "Okay", a ƙasan ranta tasan bayan gajiya akwai damuwa a tattare da Ruqayyah, Ruqayyah ta zuba ruwa tasha tana jin yadda sanyin ruwan ya sanyaya mata maƙoshi, bayan kamar 15mins Kulsoom ta tashi ta shiga kitchen, babu jimawa ta fito da plate da bowl a hannunta, Ruqayyah ta ringa kallon abincin tana jin appetite dinta na dawowa, lafiyayyen dambun shinkafa ne wanda yaji attaruhu da albasa da gyaɗa yana bayar da wani ƙayataccen aroma, sai kuma coleslaw a bowl, Ruqayyah ta janyo abincin tana ci a hankali, kallonta Kulsoom ta ringa yi tana feeding babyn ta, saida taga ta ture plate din alamar ta ƙoshi tace "kin gama....?", Ruqayyah tayi gyatsa tace "alhmdllh, godiya dubu..", Kulsoom na shafa kan babyn ta looking at Ruqayyah tace "now tell me, me yake damunki sister...?", Ruqayyah ta zaro ido tace "Ni.. me kika gani..?", Kulsoom ta saka serious face tace "haba Ruqayyah nifa ƴar uwarki ce na sanki ciki da bai, wllh there most be something troubling you, ji fa yadda kika rame kuma kinyi duhu ai ba haka hasken ki yake ba..", Ruqayyah bata san lokacin da hawaye ya fara zuba cheeks dinta ba, Kulsoom ba tace komai ba kawai kallonta take, Ruqayyah ta share hawayen tace "tin lokacin da na dawo Daddy ya yankamin warning cewa na fito da miji shi aurar dani zaiyi idan kuma banyi hakan ba zai aura min Dauda, Dauda fa wnn mai bacogalar ƙafar, da kyar da maƙyarƙyata na shawo kan Momy ta shigemin a wajen Daddy bayan na shirga mata ƙarya nace ai mun sasanta da Dr, idan ya dawo daga tafiya za a ɗaura mna aure, da haka na samu abubuwa suka lafamin a wajen Daddy, sister wllh na gama sakankancewa ina tutiya da irin son da Dr yake min kawai jira nake ya dawo na basa haƙuri, and now he is back almost 2weeks da dawowarsa, nayi kiran a waya na tura text message amma duk a banza, babu kalar haƙurin da ban rubuta a message na tura masa ba amma he didn't respond to any of it, ke na ƙarƙare miki mgana jiya har office dinsa naje ina basa haƙuri amma yaƙi saurarata, daga ƙarshe ya kiramin security, yau kam he kick me out of the surgery team..", Ruqayyah ta fashe da kuka tace "wllh Allah ina sonsa, i can't live without him Allah kuwa..", Kulsoom ta jinjina kai ta kwantar da Babyn da ta gama feeding tace "gsky kinyi babban kuskure da kika yiwa Momy ƙarya Ruqayyah..", Ruqayyah tace "toh ya zanyi sister dole ce tasa na mata ƙaryar nan, da banyi haka ba da tini an wuce wajen an auramin Dauda bacogala..", Kulsoom tace "ke kika fusata Daddy shiyasa ya kafe sai ya aurar dake, Ruqayyah yau inda ace baki aikata abinda kika yi ba wllh kinji dai har na rantse babu abinda zai sa Daddy ya miki auren dole, zai dauka cewa Allah ne bai kawo lokacin aurenki ba, amma akazo akay komai da komai ranar ɗaurin aure kika kwashi ƙafa kika gudu...", Ruqayyah ta kastseta da faɗin "wllh ba guduwa nayi ba..", Kulsoom ta haɗe gira tace "let me land malama, idan ba guduwar ki kay ba toh uban me ki kai, yanzu dai ina baki shawara kije ki gayawa Momy cewa ƙarya kika shirga mata snn kuma ki haƙura da wani Dr, yo Allah na tuba mazan yanzu har wasu abin so ne, an gaya miki in this era ana yiwa namiji makahon so ne, namiji ya soka ma yaka ƙare da wulaƙancin sa ballantana wanda ya fito ra'ayil aini ya nuna baya sonka, idan Dr ya soki a baya toh yanzu ba hakan bane, ai kin masa narkakken wulaƙanci ba ƙarya duk abinda ya miki ke kika siya da kuɗinki, so wake up malama ki san inda yake miki ciwo, kin zauna kina wani ɓare baki kina kuka shaɓa shaɓe akan wani namiji.... ehen ki ajiyesa a gefe ko shine autan maza", tinda ta fara magana Ruqayyah ta saki baki hanci kunne tana kallonta tamkar wata psycho, idonta har wani wulƙilewa yayi tsabar yadda take kallon Kulsoom cike da ruɗin abinda ta gaya mata, Dearest din zata ajiye a gefe, da kyar ta iya cewa "wai doctorn zan ajiye a gefe..?", Kulsoom tace "yhap shi din mna tinda kinyi loosing opportunity tin farko...", Ruqayyah ba ta sake cewa komai ba ta fara haɗa kayanta, ta saka wayarta a jaka, hijab dinta ta sanya kafin ta miƙe ta fara zura Abaya, Kulsoom ta bita da ido, Ruqayyah na gama saka Abayar ta ɗauki handbag dinta tace "sai anjima", Kulsoom ta taɓe baki tace "mu jima da yawa..", ficewa Ruqayyah tayi daga gidan fuskarta a haɗe, da badan Kulsoom ƴar uwarta bace da babu abinda zai hanata danƙara mata baƙar magana, kuma taci sa'a elder sister dinta ce yau da ace itace gaba da Kulsoom to babu abinda zai dakatar da ita daga kwalla mata marii, wai ta ajiye Dearest a gefe wato ta rabu da shi, never ever babu abinda zai sa ta rabu da shi sai mutuwa, tana isa bakin titi ta tari napep zuwa gida.
★Hajar ta gyara É—akinta fes bayan ta gama cin Noodles da ta dafa, ta rufe É—akin ta sauka downstairs zata kai plate da cup din da tayi amfani dasu kitchen, gaban sink ta tsaya tana kallon liquid soap dake wajen, ta kunna pampo ta matsa liquid soap din a plate ta tashi foam, sponge ta dauka ta fara wanke utensils din da ta É“ata, tass ta wankesu ta kife a inda ta É—auka, duk da kitchen din babu datti amma saida ta sake gyarasa, tayi drying hannunta da towel kafin ta fita daga kitchen din, room dinta ta koma tayi zugum sai kace wata prisoner, can dai ta gaji da zaman daÆ™in ta tashi ta fita, ta kitchen tabi ta fita daga gidan zuwa backyard, through out the day anan tayi zamanta kamar dai jiya sai idan za tayi sallah ne take komawa ciki, bayan ta idar da sallar la'asar ta birkito kayan da ta saka set biyu sai nities da hijab biyu, toilet ta shiga da kayan ta zazzaga detergent a bucket ta shiga wankesu duk da cewa ba suyi wani datti ba, tana gama wankewa ta É—auraye toilet din ta fito da kayan cikin bucket, can backyard din ta wuce ta shanya kayan jikin flowers, tana cikin shanyar saiga mai gadi da watering can a hannunsa zai bawa flowers ruwan yamma, dan russunawa yayi ya gaisheta ta amsa kafin ta É—auki bucket din tabar wajen dan ta gama shanyar, tana shiga palour taji kamar ana buÉ—e main door din gidan, ta ringa kallon Æ™ofar har aka buÉ—eta, Nurain ne ya shigo Farooq biye dashi, suna yin ido huÉ—u tayi sauri ta É—auke kanta ta wuce zata haura sama taji ance "Amarya..", dakatawa tayi amma bata juya ba, Nurain ya wurgawa Farooq wani kallo kafin ya wuce ya haye sama, Farooq ya É—aga shoulder ya Æ™arasa cikin palourn, a hankali Hajar tace "ina yini..", Farooq yayi murmushi yace "lfy lou amarya.. how are you..", tace "am fine thank you.." da haka ta nufi stairs ta haura sama, Farooq ya zaune kan kujera ya ciro wayarsa daga pocket yana latsawa, after 20mins yana zaune palourn ya daga kai yana kallon stairs, contact ya shiga yayi dialing numbern Nurain har ta gama ringing bai É—auka ba, babu jimawa saiga shi nan yana sakkowa, Farooq ya ringa kallonsa har ya Æ™araso palourn yace "muje..", Farooq bai motsa ba yace "daga É—akko paper saika tsaya wanka kuma..", Nurain ya nufi door yace "c^mon let go..", Farooq na fitowa Nurain ya rufe Æ™ofar da mukulli, shidai Farooq yana so yace wani abun amma dai ya fasa, a tare suka nufi gate, Inuwa dake zaune nan bakin gate din yayi saurin miÆ™ewa har suka Æ™araso, russunawa yayi ya gaidasu duka, shidai bai san lokacin da suka shigo ba sbd a lokacin ya tafi can backyard, Nurain yace "ba wanda yazo..?", Inuwa yace "Eh Alhj..", Nurain yace "Okay, zan sake fita sai na dawo..", Inuwa yace "Allah ya tsare..", Nurain yace "Ameen" ya buÉ—e Æ™ofa suka fita gidan da Farooq, motarsa da ya parker nan waje ya bude ya shiga, Farooq ya shiga front seat, tada Motar Nurain yayi ya fara driving out of the street, suna hawa main road Farooq yace "Allah yasa dai ba rufe yar mutane kake a gida ba..", banza Nurain yayi dashi kamar baiji ba, Farooq ya sake cewa "kaga idan ma rufeta kake to ka dena dan naji Mami tayi complain akan hakan a asibiti..", still Nurain bai tanka masa ba kawai driving dinsa yake, Farooq ya gyara zama yace "if i were you banza zanyi da rayuwa wllh, tini zan saki jikina with my cutie wifey, the girl is so cute...", Nurain ya Æ™ara speed din motar kafin ya juyo ya dubi Farooq yace "really, tinda she is cute idan kana sonta sai in saketa kawai ka aureta punk...", Farooq ya haÉ—e gira yace "you're not serious...", Nurain yace "am jet serious..", da wani irin expression Farooq ya ringa kallonsa ya kasa cewa komai, Nurain ya juyo sukay ido huÉ—u, ganin reaction din fuskarsa Nurain yayi murmushi, Farooq ya fara latsa wayarsa bai sake cewa komai ba har suka je inda zasu, 40mins suka É—auka a wajen kafin suka gama abinda za suyi suka fito, bayan sun shiga Mota Farooq yace "dude you have to make this thing serious, container nawa ce zata sauka..?", Nurain yace "three.. next month", Farooq yace "Ohk..", Nurain yace "lokacin da nake India naje China nayi order dinsu, you know shipping zasu jima basu zo ba..", suna zuwa wani junction Farooq yace "drop me here..", Nurain yace "bari nayi dropping dinka gida mna..", Farooq yace "i have another appointment..", Nurain yace "Ohk", Farooq ya buÉ—e motar ya sauka. Nurain na zaune main palourn gidansu bayan ya dawo daga masallaci sallar isha'i, Noor ta shigo palourn da Laptop dinta a hannu, ta zauna a gefensa tace "Yaya please duba min..", keenly yace "Ohk..", kunna Laptop din tayi ta shiga slide din, duba mata ya fara yi inda akwai gyara sai ya nuna mata ta goge ta gyara, resting yayi jikin kujera ya lumshe idonsa, Noor ta gama typing mistake din da ya gyara mata tace "Ya am done..", yace "get me something to eat first..", tace "tom" ta tashi ta shiga kitchen, abincin da aka dafa na dinner ta zubo masa, ta haÉ—o da ruwa da lemo ta kawo masa a tray, saida ya gama cin abincin snn suka cigaba, Mami ce ta shigo, tayi still tana kallonsa kafin ta dubi wall clock dake palourn da ya nuna 9:20 dot, Mami ta kalli Plate din abincin da ya gama ci, tini taji wani iri a ranta, sau uku knn, Mami ta Æ™araso kusa dasu tace "Nurain me yasa kake dare ne baka tafi gida ba, i thought ka tafi ma since..", ya shafa kansa a hankali yace "ina dubawa Noor project dinta ne...", Noor tayi saurin cewa "we will continue tomorrow then Yaya, thank you..", Nurain ya miÆ™e yace "Mami saida safe..", without looking at him Mami tace "Ohh Allah ya tashe mu lfy..", Noor tace "Yaya ka gaida Hajar Please..", ya gyaÉ—a kai kawai da haka ya fita, Mami na kallon Noor tace "wane yaci abinci..?", Noor tace "Yaya ne", Mami ta wuce part din Abba dan daman nan ta fito shiga, Noor ta kwala kiran mai aiki, Laure ta fito daga kitchen tace "gani hajiya Æ™arama..", Noor tace "Please gyara nan wajen", Laure ta dauke trayn ta shiga kitchen. Æ™arfe tara da minti arba'in a gida ta yiwa Nurain cause gudunsa ya falfala a mota, kuma yana shiga gidan daman Kitchen ya wuce, yaufa gaba É—aya bai sha coffee ba shiyasa yake jinsa moody, kuma bazai iya bacci bai sha ba, ya buÉ—e Cupboard ya É—akko Coffee powder yana sake duba expire date, coffeen da ya sha da safe was the worst coffee ever da ya taÉ“a sha, shine yake duba expire date wai ko powdern tayi expire shiyasa yaji na safe da ya hada rotten, still dai wani sabon pack din ya buÉ—e cause bai yarda ba kar yaje daga powdern ne, da sauri ya dubi window ganin kamar mutum ya gifta, ya Æ™urawa windown ido yana mamakin abinda ya gani, Æ™ofar kitchen wacca ta fita ta backyard aka buÉ—e, rumgume da kayanta da ta wanke ta shigo, ta É—an firgita ganinsa a kitchen din sai kuma ta haÉ—e rai ta wuce, ta buÉ—e Æ™ofar shiga cikin gidan ta shiga palour, Nurain ya ringa kallon Æ™ofar backyard din, jinjina kansa yayi ya fita kitchen din, ya haura sama ya shiga part dinsa, drawer da ya ajiye kaff spare keys din gidan ya buÉ—e ya É—auki guda É—aya kafin ya fito ya koma kitchen din, ya gama making coffee ya juye a cup, ya matsa gaban Æ™ofar backyard din ya zura key din ya kulle, saida ya tabbatar ta rufe gamm snn ya cire key din, ya É—auki Cup of Coffee dinsa ya bar kitchen din bayan ya kashe lights....âœï¸
yan Arewa ku rungumi sorry yau 😅ðŸŒ
💛 HAJAR 💛
by Feenerh feeche
{48..}
Washe gari tinda Hajar ta idar da sallar asuba bata koma bacci ba sbd da wuri ta kwanta jiya, tana kwance kan carpet ta rufa da duvet da wayarta ta buɗe Alqur'anin tana karantawa, sai ƙarfe bakwai da rabi ta ajiye karatun, linke duvet din tayi ta maida kan bed, shima pillow da ta tada kai ta mayar dashi gado, bathroom ta shiga dan yin wanka, minti ashirin ta ɗauka tana wankan kafin ta fito ɗaure da towel da yazo mata har guiwa, sai ƙamshin tsadadden showel gel da tayi wanka ne ke tashi a ɗakin, gaban mirror ta tsaya kafin taja stool ta zauna, body lotion ta janyo ta fara rubbing a jikinta, a hankali take shafa man tunani iri iri na amsawa a brain dinta, da sauri ta dubi ƙofa jin alamar za a shigo, ido huɗu sukay da Nurain, yana riƙe da handle din ƙofar, Hajar ta zaro ido kafin ta fasa ƙara ta fara kare jikinta, ya ɗauke kansa fuskarsa a murtuke, da wani irin zafin nama ta tashi daga kan stool din ta wafci hijab dinta ta saka, ƙarasa shigowa ɗakin yayi ya ajiye pen da jotter din hannunsa, da haka ya doshi ƙofa zai fita, Hajar da jikinta yake mugun rawa sbd tinda take babu wani namiji da ya taɓa ganinta a haka, har ruwa idonta ya kawo, da kyar tace "malam ka dena shigo min haka nan without notice...", fita yayi daga ɗakin, ta bisa da sauri ta tsaya bakin ƙofa tace "kai da Allah da ka shigo min babu sallama...", tana kallonsa ya shiga part dinsa, ta juya ta koma ɗakinta zuciyarta na tafasa, wani irin yamutsa fuska tayi sbd kawai ƙamshinsa da ya bari ne ke tashi a ɗakin, ƙamshin da sam baya mata daɗi, ta ɗauki freshner ta hau feshe room din amma duk da haka pure men scent dinsa bai disashe ba, Shafa man da bata ƙarasa ba knn ta buɗe wardrobe ta ɗauki kaya ta saka, har ta gama shiryawa zuciyarta ba ta dena tafasa ba, knn yaga bati, a fili tace "shi ya isa yaga bati, wllh Allah ban yafe ba..", gaban mirror ta koma ta ringa kallon jotter da pen din da ya ajiye, ta taɓe baki kafin ta ɗauki biron, rubutun da bai wuce 5lines tayi ba ta yage papern tayi folding dinta, da papern a hannunta ta sauka downstairs, ta wurga takardar kan Centre table tace "wnn kaɗai nake buƙata a wajen ka malam..", kitchen ta shiga dan samawa kanta abinda zata ci, ta buɗe fridge tana kallon fresh vegetables dake ciki, ta rufe fridge din kafin ta buɗe freezer wacca take cike da nama da chicken ga kuma fish duk frozen, shawara ta yanke akan cewa anjima za tayi stew saita ajiye a fridge ta ringa amfani da abarta na ƴan kwanaki, ruwan shayi ta tafasa ta soya kwai guda biyu da haka tabar kitchen din, bata haura sama ba ta zauna nan palour, Centre table da Tv stand da kujerun duk sunyi ƙura, tin ranar da Hafsah ta gyara palourn rabonsa da ganin tsintsiya, taɓe baki Hajar tayi tace "uhmm tinda ba ubana ne ya zuba ba babu abinda ya shalleni..", ta ɗauki kofin shayinta ta fara sha tana gutsirar kwai, tana gama cin abincin ta tashi ta shiga kitchen, ta wanke kwanukan da ta ɓata ta mayar dasu position dinsu, tin kafin ta gama wanke wanken ma take kallon ƙofar backyard, Alla alla take ta gama ta fita can ta ɗan sarara, bakin door din ta isa ta murɗa handle, sake murɗa handle din tayi da ɗan ƙarfi jin ƙofar taƙi buɗewa, lokaci guda ta saki handle din ta kafawa ƙofar ido, shiknn a kulle take, sosai ranta ya ɓaci dan zaman backyard din nan sosai yake rage mata kaɗaici, ranta duk ba daɗi ta bar kitchen din, main door ta ringa attempting buɗewa itama dai a rufe. tinda aka kawota gidan duk wnn ranar tafi mata zafi, baccin rana ma kasawa tayi, babban abinda yafi tsaya mata a rai bai wuce na safe da ya shigo mata ba, bayan tayi sallar la'asar ta kira Umma, gaisawa sukay Umma ta tambayeta ya take, Hajar dai tace lfy amma dai a ƙasan ranta ba haka bane, har Sabra ta tambaya tana cewa yaushe za a kawo mata ita, Umma tace mata ba yanzu ba, da haka suka kashe wayar.
★Nurain na zaune bisa executive kujera dake office dinsa bayan ya gama attending last patient, Æ™ofar office din aka buÉ—e aka shigo, ya ajiye plastic heart like da yake wasa da ita ya É—aga kai ya dubi wanda ya shigo, lokaci guda ya haÉ—e thick eyebrows dinsa, da sauri Haleema ta shigo office din itama gaba É—aya a ruÉ—e take, ta kalli Ruqayyah tace "Maam please get out..", ko kallonta Ruqayyah ba tayi ba ta isa gaban table tana kallon Nurain tace "i can stand any humiliation as far as zaka saurareni Dearest....", Nurain ya maida dubansa ga Haleema yace "amm me na gaya miki ne...?", with due respect Haleema tace "don't let her in..", Calmly as if speaking to himself yace "bayan nan..?", Haleema tace "call security..", ya gyaÉ—a kai yace "good.." kafin ya É—auki heart din da ya ajiye ya cigaba da wasa da ita, Haleema ta fita daga office din da sauri, Ruqayyah ta zauna kan É—aya daga kujeru biyu dake gaban table din, kallonsa ta ringa yi babu ko Æ™iftawa, kifa kanta tayi da table din ta fashe da kuka tana girgiza kai tace "na haÉ—aka da Allah, na haÉ—aka da manzon Allah, please talk to me Dearest, ko scolding dina kayi that will be better amma...", ta kasa cigaba da maganar tana kuka sosaii, a hankali yayi baya da kujerarsa ya tashi salum alum ya nufi door ya buÉ—e ya fita, Ruqayyah ta É—ago kanta ta bisa da kallo da jajayen idanunta, Office din Dr Marwan ya wuce, Dr Marwan na kallonsa yace "is there any problem Dr..?", Nurain yace "not at all, how is the patient..?", Dr Marwan yace "alhmdllh he is recovering gradually..", Nurain ya gyaÉ—a kai yace "how about his vital..?", Dr Marwan yace "great, Khaleel ya duba not too long ago", Nurain bai sake cewa komai ba yayi resting jikin kujerar, after few minutes of silence Dr Marwan yace "naji ana maganar Seminar wacca za aje Abuja nan da 1month, all thoracic surgeon must be there..", Nurain yace "am not going..", Dr Marwan yace "why..?", Nurain ya É—aga shoulder yace "kawai.." da haka ya dubi wrist watch dinsa, tashi yayi ya yiwa Dr Marwan sallama, yana fita daga department din ya ciro wayarsa yayi dialing numbern Haleema, tana picking yace ta kawo masa briefcase dinsa yana parking lot, da haka ya kashe kiran ya cigaba da tafiya zuwa inda ya parker motarsa, buÉ—e motar yayi ya shiga, babu jimawa saiga Haleema da briefcase din tasa, ya amsa ba yabo ba fallasa yace "thank you..", tace "am so sorry sir about what happened, i tried to stopped her...", ya É—aga mata hannu yace "it's okay..", tace "thank you sir", murmushi kawai ya mata ya sauke handbrake yaja motar yabar harabar hospital din, driving kawai yake saman titi amma bai san inda ya nufa ba, lokaci guda yayi murmushi yace "ironlady..", yana zuwa wani roundabout ya juya kan motar, yana zuwa gidan ya danna horn, mai gadi ya buÉ—e masa gate ya shigar da motar, fitowa yayi daga motar bayan ya gama parking, ta baya yabi inda direct nan ne zai kaika part din Hajiya, da sallama ya shiga palourn Hajiya, Hajiya na zaune kan darduma Æ´ar dattijuwar mai aikinta tana yanka mata papaya, Hajiya ta kalli Nurain ta saman kantamemen glasses dinta tace "ywwa ga likita ma Allah jefomin daga sama, Usuman cikina ne ya É—aure kwana biyu ban kewaya ba, toh duk ya dameni ji nake kamar anyi min jeren marmaroni a kyuiÉ“i ko isasshen bacci bana samu, dana gaji da azaba shine nasa Umaru ya kwaso min gwanda kwallo uku, na sha kwallo guda da safe yanzu ma gashi ana yankan wata zan shanye, da daddare in Allah ya kaimu a yanke min gudar da ta rage itama na shanye, ai idan nayi hakan na huta da jarabar basir din nan, ba kaga da yaya na shanye wacca aka yankan da safe ba, cikina har baya kamar zanyi amai amma kuma ai lfy nake nema, yanzu haka har na fara tararrbin yadda zan shanye wnn..", Nurain yayi still yana sauraronta kafin ya samu waje ya zauna yace "karki sake shan wata ta safen is Okay..", Hajiya tace "Allah ko idan na sake sha zan iya tsurewa knn...?", ta dubi mai aikin tace "ke Asabe maza fita da ita duk warinta ya cikan hanci, kije can ki shanye rabonki ce", mai aikin ta É—auki plate din papayan tayi waje da ita. Hajiya tace "na ganawa kaina azaba har yanxu gyatsar wnn aba nake, kai ina jin ma harna koma ga mahalicca na bazan sake shan gwanda ba duk ta gundureni", Nurain yace "ba kya jin komai daga wnn...?", tace "A'a Æ™alau nake Usuman, haka kurum nace maka wani waje na min ciwo ka samu hanyar da zaka fara zuba min allurai..", yace "toh shknn tinda lafiyar ki Æ™alau..", Hajiya tace "toh madallah ya gyatumar taka.." sai kuma ta tsuke baki tace "ji wani sakarci nida zan fara tambayarka matarka kuma na tafi wani wajen, Mami ai ba gida É—aya kuke kwana ba yanzu..", shi dai baice mata komai ba, bayan Æ´an mintina yace "bari na gaida Ummi.." da haka ya tashi ya buÉ—e wata Æ™ofa ya shiga, luckily ya tarar da Ummi na palour, ya gaisheta with respect, amsawa tayi tana tambayarsa aiki da iyali, shi dai ya shafa kansa ya amsa a takaice kafin ya mata sallama ya bar palourn ya koma na Hajiya, babu jimawa da zamansa saiga Abinci Ummi tasa an kawo masa, sosai Nurain yaji daÉ—in hakan, plate ya É—auka zai zuba abincin Hajiya tace "wai ci za kayi kai Usuman na matarka fa..?", yace "shima zanci", ya faÉ—i hakan ne dan ya huta da surutunta ta barsa lfy yaci abincin kar ya dawo masa ta hanci. tin É—aya da rabi sai uku da arba'in Nurain ya bar gidan, bai jira Farooq ba sbd baya dawowa aikin da wuri cause na Company ne. gidansu ya wuce, yana gama parking motarsa yaji ana kiran sallah, yayi amfani da tap dake compound yayi alwala ya wuce mosque, bayan ya dawo masallaci ya shiga ciki, part din Mami ya shiga ya gaisheta kafin ya fito ya haura room dinsa. bashi ya sakko ba sai biyar saura shima sbd Noor ne wacca ta takura masa akan project dinsa, saida sukay chapter biyu snn ranta yayi fari tinda saura É—aya ya rage su gama. Æ™arfe bakwai da arba'in Nurain ya shiga wajen Mami, attention dinta ta mayar kansa, Nurain yace "Mami saida safe ni zan wuce..", Mami ta dubi agogo ganin lokaci tace "yawwa toh Allah ya tashemu lfy, ka ringa tafiya gida da wuri ai yafi son..", ya shafa kansa yace "tom Mami", Compound ya fita ya shiga motarsa, ya ciro wayarsa yayi dialing numbern Noor, tana picking yace "yi sauri malama", tace "Yaya gani nan..", few minutes saiga tanan ta É“illo ta can baya da basket a hannunta, ta buÉ—e front seat ta ajiye basket din ta rufe door, Nurain ya gyara zama ya tada motar. saida ya tsaya wajen suya ya siyi kaza snn ya wuce gida, fitowa yayi daga motar yana amsa sannu da zuwan da mai gadi yake masa, ya buÉ—e front seat ya É—auki basket din kafin ya nufi main building din gidan, keys ya ciro daga pocket ya buÉ—e door ya shiga ya mayar ya rufe still da muÆ™ulli, ajiye basket din yayi nan palour kafin ya haura sama, wanka yayi ya saka Pajamas masu sweat pant masu shegen kyau, downstairs ya sakko da room slippers a Æ™afarsa, kamar ce masa akay ya kalli wajen, ya ringa kallon papern dake kan Centre table, haÉ—e gira yayi kafin ya É—auki papern ya buÉ—e a wulaÆ™ance, beautiful handwriting din dake jiki ya fara karantawa.... "malam wai an gaya maka inada wata buÆ™ata ne a wajenka in banda guda É—aya, kawai ka sauwaÆ™e mana shine buÆ™atata..", tsaki yayi ya cukuikuiye takardar ya wurgar da ita, wani irin Æ™auri ya fara perceiving, da sauri ya nufi kitchen, yana buÉ—ewa yaja da baya ya toshe hancinsa, gaba É—aya kitchen din ya gumame da hayaÆ™i da uban yaji, da hannu É—aya ya rufe hancinsa É—ayan kuma ya ringa kore hayaÆ™in har ya samu ya shiga kitchen din, gaban cooking gas ya isa yana Æ™oÆ™arin kashe wutar amma da yake hayaÆ™i yayi yawa baya gani sosai hannunsa ya jogali tukunya, da sauri ya janye hannun ya riÆ™e da other din, hkan ce tasa yayi perceiving Æ™aurin har cikin lungs dinsa, tini ya fara tari at same time yana Æ™oÆ™arin kashe gas din. Hajar ta saki pillow din hannunta bayan brain dinta ta amsa, shaf ta manta da kayan miyar da ta É—ora akan wuta, bata tsaya bi takan wani hijab ba ta gyara hular kanta ta fito daga room din, da sauri ta ringa sauka stairs har tana tuntuÉ“e, tin daga palour ta fara tari ga uban hayaÆ™i da ya rufe mata vision, gadan gadan kitchen ta shiga daidai lokacin da Nurain ya kashe gas din, da sauri ta juya kamar zata sa gudu sbd fitowar da tayi ba shiri, Allah yaso ma kayan baccin riga da wando ne kuma rigar ta saukar mata, tana fita daga kitchen din shima ya fito yasa Æ™afa ya banke Æ™ofar, tana shirin hawa stairs taji an fixgo hannunta, figarta yayi zuwa dining area inda babu hayaÆ™in sosai, haÉ—e ta yayi da bango still bai sakar mata hannu ba fighting with his breathing, sosai ya shaÆ™i hayaÆ™in shiyasa numfashinsa har yanzu bai dawo normal ba, kiciniyar kwace hannunta ta fara yi tana turesa da iya Æ™arfinta, sake matseta yayi da bango ta kasa motsi, heavily yake breathing har zuwa lokacin da yaji dama dama, a hankali take mayar da numfashi ta É“alla masa harara tace "let go off me, ni ka sake ni..", ita babban tashin hankalinta kayan jikinta, muryarsa ma bata fita sosai yace "from today henceforth karna sake ganinki a kitchen, are you mad fire outbreak zaki ja min a gida, koda wasa na sake ganinki a kitchen saina sumar dake nonsense" yana kaiwa nan ya hankaÉ—eta saura Æ™iris ta faÉ—i. da sauri ya nufi stairs ya haura sama don bazai iya Æ™ara koda 1minute a wajen ba, Hajar tabi bayansa da kallo zuciyarta ta ringa Æ™una kamar zata kama da wuta, zama tayi kan stairs din hawa dining ta haÉ—e kai da guiwa, after 10mins ta tashi ta haura sama kamar wacca kwai ya fashewa a ciki. washe gari da safe Nurain ya sauko downstairs, ta main door ya fita ya zaga can backyard ya kashe gas cylinder, cikin gida ya dawo bayan ya kashe gas din, ya shiga kitchen to make a cup of coffee, wani tsaki yayi ganin tukunyar dake kan cooking gas, tayi wani baÆ™i Æ™irin ko kyan gani babu, cikin sink ya saka tukunyar ya sakar mata ruwa saida ta cika damm snn ya kashe pampon, ya jona coffee maker. A hankali Hajar ta Æ™arasa sakkowa daga stairs idonta Æ™ur akan keys din dake jikin Æ™ofa, ta isa bakin Æ™ofar a hankali ta zare keys din, tana juyawa sukay ido huÉ—u dashi ya fito daga kitchen da cup a hannunsa, ta haÉ—e gira tayi sauri ta kunshe keys din a hijab, garin haka ji kake tass muÆ™ulli sun faÉ—i a kan tiles, kallon keys din Nurain yayi snn ya kalleta, ta wani haÉ—e rai, yana kallon main door ita kuma ta samu opportunity ta sunkuya ta É—auki mukullin ta kwasa a guje sai sama, a hannun kujera ya dungurar da Coffee din yabi bayanta da sauri, tana Æ™oÆ™arin rufe Æ™ofa yasa Æ™afa ya banke Æ™ofar, zaro ido tayi tace "na shiga uku" ta ruga can edge of the room ta boye hannunta a baya, daga bakin Æ™ofar ya tsaya yace "give me the keys..", ta murguÉ—a masa baki tace "wllh bazan bayar ba, ni ba tinkiyarka bace da zaka ringa kulleni", Æ™ofar bathroom ta kalla sai kuma ta kallesa tana banka masa harara, lokaci guda ta tafi da gudu zata shige bathroom din, ganin haka ya taho da speed ya fixgota ya haÉ—eta da jikin wardrobe, dunÆ™ule keys din tayi a hannunta ta É“oye a baya, tini ta ringa shaÆ™ar scent dinsa da bata so, ta É—aga lulu eyes É—inta ta kallesa, shima kallon cikin idanunta yake da wani irin expression zuciyarsa na tafasa.......âœï¸