← Book details Hajar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 2 OF 6

Chapter 45 is available on 👉 Arewa book...

Hajar Part 1 Complete Hausa Novel · about 15 min read

Arewa book suna rigaku samun update da wuri, follow my account to stay connected @ feenerhfeeche02
💛 HAJAR 💛
by Feenerh feeche

{45..}
Da sauri Nurain ya lumshe idonsa tsabar yadda hasken ya kashe masa su, Hajar da tsoro ya sandarar da ita ta kasa wani cikakken motsi, sosai ta razana don ba tayi tunanin akwai mutum a wajen ba, Nurain ya ajiye cup din Coffeen ya kaucewa hasken yace "kee mene haka kuma are you mad...?", da sauri ta janye hasken daga kansa, furiously ya tashi ya kunna bulbs haske ya gauraye palourn, wani irin shan kunu Hajar tayi ta shige kitchen da sigar ko in kula, sarai tasan haske masa ido tayi amma she don't care tinda dai ba intentionally ta aikata hakan ba, wani tuƙuƙi ne ma ya mamaye mata zuciya da taga fuskar tasa, plate ta ɗauka ta zuba dubulan da Alkaki sai chin chin, cup ta ɗauka ta buɗe tap din sink ta cika da ruwa, daga haka ta fita daga kitchen din, direct stairs ta dosa, Nurain ya miƙe daga hannun kujerar da ya zauna ya zuba both hands dinsa a pocket fuskarsa a murtuke yace "hey you stay there", tamke fuskarta tayi ta cigaba da tafiya a hankali sbd kar cup din da ta ciko da ruwa yayi tambal tambal ya zube, yayi blocking front dinta yana binta da wani kallon tsana yace "wnn shine karo na ƙarshe da zaki sake fitowa palourn nan idan ina zaune, daga ƙarfe shida na yamma bana son ko silhouette naki ya gifta ta palourn nan, ko me za kiyi ki yisa kafin wnn time din that is weekdays knn, a weekend kuma you just have 3 hours daga shida na safe zuwa tara, daga nan kuma sai gobe, am i clear...?", ta juya lulu eyes ɗinta ta yamutsa fuska sbd yadda tayi perceiving pure men scent dinsa, ta taɓe baki tace "sorry you can't tell me what to do...", yace "ko, toh ki jini da kyau as far as you are living in my house you must follow my rules, bad attitudes din kike ji dashi toh ki tattarasa ki ajiye gefe, ba dai a nan ba saiki bari lokacin da kika gaji da zama kika sallami kanki ki ɗauki abinki ki ƙara gaba, this is my last warning...", da haka ya barta tsaye ya ɗauki Laptop dinsa da cup of coffeen zai haura sama, wata nannayar ajiyar zuciya Hajar ta sauke, har wani huci take masifar ta motsa, idonta ya kawo ruwa, tana ganin yayi rabin stairs din tace "ji mana malam, karka tsaya wahalar da kanka, ka damƙa min shaida kaga idan ban ƙara gaban ba", ya juyo ya wurga mata wani mugun kallo yace "save the time that you are free to roam in my house..." da haka ya juya ya haura stairs, har wajen 50seconds tana tsaye inda ya barta, gyaɗa kai tayi ta numfasa tace "lallai wnn mutumin bai sanni ba, sanin da yayi min na taɓin gishiri ne, mu zuba ni da kai wanda ya fasa bai haifu ba", ɗakinta ta wuce abinta, akan mirror ta ajiye plate da cup din da ta shigo dasu, ta zauna akan stool dake gaban mirror din tana kallon kanta, kwafa tayi ta girgiza kai ta ja plate din gabanta ta fara cin tarkacen da ta ɗeba, tana gama cin iya yadda zai mata ta sha ruwa, tayi kwanciyarta kan carpet kamar yadda tayi jiya, ta lulluɓe da duvet don wani azabar sanyi ɗakin yake mata sbd Ac gashi bata san ta inda zata kashe ba. Nurain ya gama abinda zai yi jikin Laptop kafin ya kashe ya mayar da ita bag, ya fita da cup din daya gama shan Coffee zuwa Kitchen yana dawowa kuma ya kwanta, da Asuba bayan ya shiga toilet ya dauro alwala ya fita daga room din nasa, a corridor ya tsaya yana kallon ƙofar ɗakinta, after looking at the for few seconds kawai ya sauka downstairs, bayan ya dawo daga masallaci ya zauna yayi recitation of the holy book, sai wajen 8 na safe ya rufe karatun, daman already yau Monday yake son komawa work, bathroom ya shiga bayan yayi wanka ya fito da towel a hannunsa yana goge cikakkiyar sumarsa, 9 ya gama shirinsa tsaf ya ɗauki briefcase da ya saka Laptop dinsa ya sauko ƙasa bayan ya rufe part din nasa, bai ga dai alamar ta sakko ba har ya shiga kitchen, ya haɗa tea ya dawo palour yana sha, tsaki yayi don ya saba yin full breakfast kafin ya fita aiki, daga karshe dai ya gama shanye tean ya kai cup din kitchen, daga haka ya fita compound bayan ya rufe main door ya zuba keys din a pocket, da sauri Inuwa dake zaune kan white plastic chair a bakin gate ya taso, ya russuna da kyau ya gaida Nurain, a takaice ya amsa yace "akwai wanda suka zo jiya ne bayan fita ta..?", Inuwa yace "Eh alhj anyi baƙi sunxo nan da kayan abinci..", Nurain ya gyaɗa kai bai ce komai ba ya buɗe motarsa da Inuwa ya gogeta tass ya wanke wheels ɗin kuma, bayan ya gama warming ya ja motar ya bar parking space din ya fita daga gidan dan already mai gadi ya buɗe gate, after a ride of 20mins ya isa hospital, yayi parking motar, kallon yawarsa dake kan dashboard yayi kafin yasa hannu ya ɗauka ya zurata a pocket, ya fito walking majestically ya nufi hanyar office dinsa, securities da sauran ma'aikata suka ringa gaishesa da welcoming dinsa, briefly yake amsa gaisuwar yana tafiya, yana ƙarasawa office din ya buɗe ya shiga, secretaryn sa Haleema da ya turawa saƙo ta email cewa zai shigo on Monday, shiyasa tin ranar friday tasa aka kyara office din, Haleema ta tashi with respect tace "good morning sir", da sakakkiyar fuska ya amsa mata yace "morning, ykk..", tace "alhmdllh sir an dawo lfy..?", yace "fine alhmdllh" da haka ya shige cikin office din, ƙarewa office din kallo yayi kafin ya ajiye briefcase din hannunsa kan huge table dake office din, after surveying the huge office ya zauna kan kujera yana sauke ajiyar zuciya, ya kalli glass nameplate dake gaban table din mai ɗauke da sunansa (Dr Uthman). wayarsa ya ciro ya kunna, saida ta gama booting uban messages da suke pending suka gama shigowa, call log ya shiga yayi dialing numbern Khaleel, tana fara ringing Khaleel yayi picking, Khaleel yace "ba dai ka dawo ba boss..", Nurain yace "gani ma a office", Khaleel ya katse kiran, after like 5minutes ya shigo office din, Khaleel ya zauna kan ɗaya daga biyun kujeru da suke gaban table din, bayan sunyi exchanging greetings Khaleel yace "An dawo lfy..?", Nurain yace "alhmdllh, Dr Marwan ya shigo..?", Khaleel yace "yeah amma ya shiga surgery not too long ago", Nurain yace "Ohk", Khaleel ya ciro wayarsa da tayi ringing daga pocket din labcoat dinsa, few seconds ya katse kiran ya tashi yace "i have to go now ana kirana a E.R". Khaleel na fita office din Nurain ya kira Haleema ta landline, tayi picking tace "yess sir", yace "Patients zasu iya fara shigowa", tace "Okay sir". Nurain ya fara attending first patient da ya shigo, yana yiwa patient din ƴan tambayoyi aka buɗe ƙofa aka shigo, kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kansa ya cigaba da attending patient dinsa, jingina Ruqayyah tayi jikin ƙofar tana mayar da numfashi, ta lumshe idonta tana sauke ajiyar zuciya sai kuma ta buɗe idanun, kamar a yanzu ta fara ganinsa haka ta zuba masa na mujiya, kawai kallonsa take babu ƙiftawa ta jingina da jikin ƙofar, Nurain yayi prescribing patient din with drugs da cewar zai dawo nan da 2weeks follow up, Ruqayyah ta matsa gefe ta bawa patient din hanya ya fita, tamkar wacca kawai ya fashewa acikin haka ta isa gaban table din nasa kanta a ƙasa tana wasa with her fingers, tinda ya mata kallo ɗayan nan bai sake ba, kwata kwata bai nuna yasan ma da shigowarta ba, ya cigaba da rubutu jikin record book, muryarta na rawa kanta a ƙasa tace "Dearest...", next patient ce ta shigo ƴar dattijuwa, ganin haka yasa Ruqayyah ta bata space, sai a lokacin Nurain ya ɗago yayi attending patient dinsa, a haka dai saida yayi attending 5 Patients kuma har lokacin Ruqayyah na tsaye bata fita ba, na biyar din patient na fita, da sauri Ruqayyah taje ta rufe ƙofa, Nurain ya kira landline yace "i need security now", kasaƙe Ruqayyah tayi tana kallonsa sai kuma ta haɗa hannayenta waje ɗaya tace "plxx talk to me, dan Allah kayi haƙuri ka saurareni Dearest...", rubuce rubucen sa ya cigaba da yi, Security man ya buɗe ƙofa ya shigo with respect yace "sir you call", ba tare da ya ɗago kansa ba yace "get her out of my office", security man yace "yess", ya kalli Ruqayyah da Mamaki ya gama daskarar da ita yace "Muje hajiya..", wani kwallo mai uban tauri Ruqayyah ta haɗiya lokaci guda ta fita daga office din with speed hawaye na zuba idonta. Nurse station ta wuce, tana zuwa ta zauna kan kujera ta hade kanta da table din station din ta fashe da kuka, Nurse Jidda da ita kaɗai ce a station din duk sauran sun shiga ward ta ajiye kidney dish din hannunta tace "Ruqayyah lfy...?", Kuka kawai Ruqayyah take taƙi tace komai, da damuwa Jiddah tace "subhanallah dan Allah ki gayamin mene ya faru..?", Ruqayyah ta ɗago kanta tana kallon Jiddah da jajayen idanunta tace "Jiddah ni yanxu ya zanyi, Dr yaƙi saurarata...", Jiddah ta jinjina kai ba tace komai ba, ita ganin ƙarfin halin Ruqayyah take, yo ko itace Dr ai bazata saurareta ba, Ruqayyah ta goge cheeks dinta tace "wai fa security ya kira yace yayi waje dani sai kace wata ɓarauniya..", ta sake fashewa da kuka, Jidda tace "bari na duba patient a ward A" da haka ta saka kidney dish din da ta ajiye a cikin tray ta ɗauka tabar station din.

★Sai goma da rabi Hajar ta farka daga baccin da ta koma bayan ta idar da sallar asuba, bathroom ta shiga tayi brush ta wanke bakinta da mouth wash, tayi wanka, saida ta wanke bathroom din snn ta fito, tsaye tayi bakin mirror tana kallon uban kayan shafe shafen da Hafsah ta jera mata jiya, wani body lotion ta ɗauka tana duba sunansa sbd da shower gel dinsa tayi wanka, ta zauna kan stool ta fara rubbing lotion din, ta ringa kallon gashin kanta da duk kitson ya fara warwarewa da kansa, bai ɗauketa wani minti 20 ba ta gama tsefe ƙananan kitson kanta tass, daga ta kama jelar zugeta kawai take cause gashinta mai laushi da santsi ne na fulani, combing hair din tayi ta shafa masa oil shima da ta gani, tayi parking dinsa a ƙeya ta tufke jelar, daga haka ta tashi daga gaban mirrorn, ta buɗe huge wardrobe tana taɓe baki, ita dama a box Hafsah ta bar mata kayanta, wata doguwar riga ta atamfa ta saka, ta zumbula hijab ta fita a ɗakin ta sauka ƙasa da cup da plate din jiya da taci kayan gara, kayan garar ta sake ɗiba taci a kitchen din tasha ruwanta a famfo kafin ta fito ta koma room dinta, tanata zaune a ɗakin saidai tayi game a wayarta inta gaji ta ajiye har akay sallar Azahar, tana idar da sallah taji wata yunwa ta bijiro mata, kayan garar dai ta kuma ɗurawa cikinta, samm taƙi yin girki sbd gani take knn ma rayuwa mai tsayi zata yi, palour ta fito ta ringa kallon ƙofa kafin ta matsa kusa da ita ta kama handle ta murɗa, a rufe taji ƙofar, ta koma kitchen ta buɗe ƙofar da zata sadaka da backyard din gidan, luckily ta jita a buɗe, ta ringa kallon backyard din tana ɗan zagawa, ta zauna kan wani dakali da ta gani wanda shine chamber na ruwa, sosai zaman wajen yayi mata daɗi don ji tayi kamar an cirota daga maƙabarta, ba tasan iya awannin da ta ɗauka zaune a wajen ba tana tunani iri iri, motsin zubar ruwa ta jiyo daga front din gidan, tashi tayi ta ringa bin inda motsin yake, mai gadi ne ya kunna famfon compound din yana alwala, ɗan russunawa yayi ganinta ya kashe famfon yace "ina wuni Hajiya..", Hajar ta mayar masa da gaisuwar don ta ganesa ranar da suka dawo gidan shi suka tarar, Inuwa ya duƙar da kai yace "wani abin za a amso miki hajiya...?", Hajar ta girgiza kai ta juya ta koma backyard din, ciki ta koma don yin sallah, tana idar da sallah wayarta ta fara ringing, ta ringa kallon screen ɗin wayar ganin number ke kiranta kuma bata san numbern ba har kiran ya katse wani ya sake shigowa, picking tayi ta kara a kunne ba tace komai ba, wani murmushi tayi bayan ta ɗau murya tace "Noor...", Noor tayi dariya tace "ta ya akay kika gane...?", Hajar tayi ƴar dariya tace "your voice mna", Noor tace "toh ykk ya gida...", Hajar tace "lfy lou and you..?", Noor tace "am great wllh..", Hajar tace "good, toh yaushe zaki zo..?", zaro ido Noor tayi tace "not soon..", Hajar ta marairaice murya tace "kefa kika ce zaki zo..", Noor tace "yeah zan zo amma ba yanzu ba..", Hajar tace "toh shknn sai kinxo", sun ɗan jima suna hira da Noor kafin daga karshe Noor tayi mata sallama, Hajar ta tashi ta naɗe darduman da tayi sallah, sai kace wata ƴar kurkuku haka take jin rayuwar gidan, daga ƙarshe dai ta fara gyara ɗakinta wanda babu wani datti ta masa turaren wuta wai dan duk ta ɗan ware, taje kitchen ta ciko plate da kayan garar da ta mayar abinci, da kyar ta iya hawa stairs bayan ta fito daga kitchen sbd ƙullewar da cikinta yayi, ta samu dai ta shiga ɗakinta ta zaune gefen gado ta danne cikin da yake kan murɗa mata, bayan wani lokaci cikin na murɗawa sai ta fara yin ƙalas, maiƙon Alkaki yazo ya tsaya mata a wuya har tana jin kamar za tayi amai.

★ƙarfe biyu da ƴan mintina Nurain ya fito daga office dinsa holding his briefcase, saida yayi attending kaf patient da suka zo shiyasa ya kai wnn time din, acikin doctors da suke aiki a hospital din shine me wnn halin, indai kaga kazo ganinsa bai duba ka ba toh akwai babban dalili amma duk yawan patient yana squeezing ya duba su, Ruqayyah dake zaune bakin office din over three hours tana jiran fitowarsa ta tashi da sauri tabi bayansa, tana zuwa gaf dashi tace "Dr..", dakatawa yayi da tafiyar ya jiyo yana kallonta ba tare da yace komai ba, kallon da yayi nata sai taji gaba ɗaya ɗan guntun courage dinta ya narke gami da tsiyayewa ta guiwarta, ta kasa cewa komai amma lips dinta sai ɓari suke, shi kam da yasan ma itace wllh bazai dakata ba, shi Allah ya masa wani hali na bagarar da lamari indai ya bar abu topa shknn, don yanzu idan nace muku ya manta muryarta ne shiyasa ma har ya juyo data kirasa kar kuyi mamaki, ya haɗe thick eyebrows dinsa ya juya ya cigaba da tafiyarsa, Ruqayyah tayi ajiyar zuciya ta lumshe idanunta da suke mata zugi tsabar kukan da ta sha, da sauri ta kuma binsa sai kace mayya tace "dan girman Allah Dearest kayi haƙuri, make time for us so that we can discuss about it, i will tell you all what happened...", har suka fito harabar hospital din tana biye dashi tana masa magiya, ganin ba sauraronta zaiyi ba ta tsaya a ƙofar department din gudun kar ta dizga kanta a public, Nurain yana isa parking space ya shiga motarsa, keys ya zura a ignition ya kunna motar, har lokacin girarsa a haɗe take don ba ƙaramin fama masa zuciya waccar psycho din tayi ba, he dislike the sight of her, direct gidansu ya dosa don bazai koma gidansa yaga wani abun da zai sake ɓata masa rai ba, bayan yayi parking motarsa ya shiga ciki. Mami na zaune a main palourn da wasu close friends dinta guda biyu, ya ƙarasa shiga palourn ya gaishesu duka da ladabi, Mami dai tayi mamakin ganinsa a wnn lokacin it seems like daga wajen aiki yake shine ya zarto nan a maimakon gidansa, shidai yana gama gaidasu ya wuce upstairs, Mami ta bisa da kallo, Haj Sadeeya tace "Aaa aha ashe duk munyi furfura don Allah kalli yadda yaron nan ya koma Nurainin Mami, kinga ma ban tambayesa iyalin ba don ina Canada kika gayamin zancen aurensa...", Mami tayi yaƙe tace "matarsa na nan lfy baifi kwana goma da yin auren ba..", Haj Sadeeya tace "kwana goma kuma nifa mganar almost one year nake miki..", Haj Fati tace "ni dai nasan wancan an fasa yinsa, bayan nan ma Nurain din ya koma India, toh dai wnn na kwana goman ne bansan dashi ba.." ta fadi hakan tana kallon Mami, Mami ta kallesu duka tace "wllh auren ne yazo unexpected, nima kaina saida aka ɗaurasa na sani, prof ne ya haɗasa da ƴar abokinsa, shima yaron ba sani yayi ba don lokacin ma bai dawo ƙasar ba..", Haj Sadeeya tace "duk ba labari da fasa wancan din da kuma sabon, toh in banda abinki Mami aiko baza mu zo ba ai kya gaya mana", Mami tayi ajiyar zuciya tace "duk kuyi haƙuri abin ne yazo unexpected shiyasa, ba a nitse nake ba wllh". uku da minti goma Nurain ya sakko har yayi wanka ya sauya kayan jikinsa, yana kallon Mami yace "Noory fa..", Mami tace "bata dawo schl ba..", yace "Okay" yana kallon hanyar kitchen kafin ya wuce can din, kitchen din ya shiga bayan few minutes ya fito da plate din Abinci, dining ya wuce ya zauna ya fara cin abincin, saida ya cinye tass don yunwa yake ji ba kaɗan ba tin tea da yasha da safe bai sake cin komai ba banda water, Nurain bai baro gidansu ba sai ƙarfe takwas na dare, a hakan ma sbd Mami ne dan ya lura da irin kallon da take masa ga dukkan alamu tana so ta fadi wani abun ne amma bata fada ba, yana zuwa gida daman a palourn ƙasa yayi branching, yayi powering TV kafin ya zauna kan exclusive sofa dake palourn, almost 30mins da zamansa aka buɗe ƙofar kitchen, da sauri ya kalli direction din, a hankali ta fito daga kitchen din da cup ta ciko da ruwa, ta juya ta rufe ƙofar, ƙishi ruwa ne yasata fitowa tin ɗazu, shine da tazo kitchen ɗiba ciwon cikin ya murɗa mata ta durƙushe a ƙasan kitchen din tana murƙususu har saida taji dama dama snn ta iya tashi ta ɗebi ruwan ta samu ta fito, wani irin haɗe rai Nurain yayi, wato bata ji warning din da ya mata ba knn, how dare her zata ringa masa taurin kai, who born her with her bad attitudes, dole tayi abinda yace indai tana son cigaba da zama a gidan, furiously ya tashi yace "ke ba kiji warning din da na miki ba knn..", hannunta ɗaya riƙe da cup dayan kuma ta dafe cikinta, da kyar ta iya cewa "daman nace maka naji ne.., na riga na gaya maka you can't tell me what to do malam" tana gama fadin haka ta nufi stairs, bata ankara ba taji an fixgota baya ta bige da hannun kujera.....✍️
Chapter 2 · 0% Book details