← Book details Gwarzon Namiji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 11

Sashe 9

Gwarzon Namiji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Me kike mun a daki?"
Ya tambaye ta a firgice
Yusrah kam ko a jikinta sai ma qara yalwatar murmushinta da tayi zuwa qaramin dariya maras sauti "Good morning"

Ko kallonta baiyi ba ya sake dan hangade duvet din yana qare ma kansa kallo
"Ya na ganni tsirara 🥹"?

"Circumstance"

"Baki bani amsar tambaya ta ba ,ina kayana nace?!"

"While laifine don ka ganka tsirara bayan kana tare da matarka?" Ta bashi amsa tana karkada masa ido cikin gari da kisisina.

"Wait wait ,karkice mun kin mun fyade"?

Murmushi tayi mai tsananin qayatarwa "Tabbas munyi komai da komai....ahhhh dama haka kake? You Are a bad guy... Wallahi ka iya tattalin mace a gado ,hummmmm ahhhhh Allah nagode maka da na samu ingarman miji kamar ka..." Ta qare maganar ta tana kai hannunta gefen hannunsa tana shafa masa daga kafadunsa zuwa qasa .

Qif qif da ido yayi yana kallonta tana wani irin karairaya tana lashe leɓenta na qasa tana jan numfashi ciki ciki.

"Ke ke kice mun wasa kike mun,wannan ma ai ba'a ne!"

"Akan me zan maka wasa ? Da gaske ka iya 😂" ta fashe da dariya lokaci daya kuma ta gintse fuska ta dirka daga kan gadon ta wuce tana jujjuya masa en madaidaitan mazauna ta da suka saje da ɗan slim jikinta ,ta bude qofa ta fice a dakin ta barshi a nan yana bin bayanta da kallo yanajin kamar ya cafko qugunta mai dauke da er farar short din nan yayi wasa dasu .saidai inaaa qwalelensa.

"Auccchhhh " ya kaima katifar da yake kai naushi yana ayyana abubuwa a ransa.

Oum Aphnan
09065990265
Littafin kudine dai ,You can get yours by sending your payment via this account details
9065990265
Opay
Mohammed Hassana

Ko
7782217014
Fcmb
Mohammed Hassana
[7/6, 7:25 PM] Chuchu👻: Yusrah tana zuwa dakinta wanka tayi tai brush ta dauro Alwala ,ta shimfida praying mat din ta ta gabatar da sallan farilla ,tadan tsaya tayi addu'ointa da ta saba ,saidai haka nan ta tsinkayi leɓenta na masu addu'an zaman lafiya ita da mijinta ,tare da fatan sanya ma zuciyarta ruwan sanyi ta daina masa rashin kunya kuma tayi masa biyayya gwargwadon Iyawanta.
Cikin hawaye ta ninke darduman ta wuce kicin ta soma hada masu break fast .
Doya mai yawa ta fere tasa a wuta tana simmering dinshi in a low flame ta qara pintch of salt da sugar For taste ,kana ta dakko kayan miya tumatur ,red pepper da bell pepper ta gyarasu ta zuba a blender ta niqasu ta bude fridge ta dauko kankana wanda bai nuna sosai ba da kwashe ciki ta fidda seeds din ta zubar ta nike kankanan ta cakuda da kayan miyan ta zuba a cikin tukunya ta zuba tafasasshen naman rago da left over din soyayyen kazan da take dashi.

Kafin ta gama haɗa wannan stew din doyanta yayi laushi ta tsane ta soya shi da isashen kwai ,ta zuba a mazubi mai kyau ta rufe da foil ppr ,ta dawo ta sa wani tukunyar ta daura dahuwar white rice da yarfin peas a ciki .
Cikin qanqanin lokaci ta gama komai ta gyara ta haɗa masa lafiyayyen shayi irin na larabawa harda su cloves da na'a na'a tasa a qaton Flask din gida wasu kuma duk ta diba ta zuzzuba a jakan abinci .
7.15am komai nata ya daidaita ta dauko kayan abincin ta wuce dashi zuwa wajen compound dinsu ta damqa ma driver dinsa tace ya saka masa a mota .
Sauran tea da fried yam din ta dauko zuwa dinning ta ajiye condensed milk dinta da evaporated milk sai milo da raguwar cake dinta na fridge ta jere a wajen ta kunna ma dinning din turare mai sanyin kamshi ta fito falon tana mopping karafaren wargajejen falon .
A nutse ta gama shima tabi labilen tana turare su da kamshi zuwa kujerun ta dawo da qaramin towel din hannunta tana karkade kayan kallonta zuwa manyan aljifan maajiyar TVn .all of a sudden ta zaro wasu folders wanda taga kamar da safe ya fita dasu ,debosu tayi da nufin ta kai masa daki .sai washarrrr suka zube a qasa
"Subhanallh" abunda ta furta kenan ta duka tana tattarewa
"Ya salam!!"

Hoton Nutsatsiyar mace ta gani ta nade jikinta cikin abaya mai ruwan jinin kare ,fuskarta fal fara'a sai qyalqyali take cikin gwala-gwalai .

Yusra ji tayi kamar an sassara mata gwuiwa dakyar taja jiki zuwa gaban kujeranta ta zauna yaraf hannunta na kakkarwa riqe da hoton matar Adeel

Kafeta da ido tayi bakinta na rawa na wanda kuka yake son cin qarfinsa
"Kiyi haquri ki yafe mun...ban da nufin sanadiyyar barinki duniya balle har in maye gurbin gidanki ,ke nutsattsiyar macece da duk wani namiji zai fatan samunki matsayin matar sa ,daga sanda naji adduoinki akan mijinki naji kin sauya mun rayuwa ,naji kin burgeni naji sonki yana ratsa bargon jikina, naji ina ma kina raye inje in sameki mu zama qawaye ko kya bani shawarar zaman duniya ?!!! Amma kuma a yanzu da na ganki gani sai naji na tafka kuskuren da bazan taba gyara shi ba ,dole ne in amsa hukunci a wajen mijinki ,banga azaban komai ba ,kuma tabbas na cancanci hukuncin da ya fi hakan ma ,amma plz ki yafe Ni kuma inaso ki sani mijinki yana sonki kuma nasan bazai taɓa qaunata ba har abadan...amma nayi maki alkawari zan cigaba da kula maki dashi har iyakan numfashi na na qarshe wannan fansan ranki ne da soyayyar ku ...😭😭😭" Kasa cigaba da maganar tayi saboda yanda kukanta yaci qarfinta wani irin kuka mai shesheqa da kururuwa takeyi kamar wacce ta rasa komai nata na rayuwa.

Adeel dake tsaye kamar drawing yana jin duk abinda Yusrah ke cewa ,yana ganin zata dago yayi gaggawar ja da baya da baya har ya isa qofa ya bude a hankali ya fice zuwa office.

Oum Aphnan
[7/6, 8:26 PM] Chuchu👻: Yusrah zama da Major Adeel ta fahimci mutum ne mai son gida ,sannan yana son yaci abinci a gida musamman na gargajiya ,kuma ta karanci duk inda 6pm yayi to yana hanyar gida .don haka tun 4.30 ta tashi ta sake gyara gidan ta sauya ma gadajen gidan sabbin zanin gado ta wuce kicin dinta na second floor ta samu dogon stool ta zauna ta shiga youtube ta yi searching vegetable couscous sbd tasan dai bazata iya masa dambu ba . Tana kallo tana girkin ta har ta haɗa kyakkyawar couscous yaji hanta da veges ta yi masa kunun aya mai dadi ta maida a fridge ta haɗa masa shayi mai kyau daje ta jeresu a dinning ta saka turare mai fidda ruwa. Tana jin qarar shigowar motocin sa ta haye saman dakinta da sauri sam bata son su hada ido dashi kunyarsa yanzu take ji . Wani sanyin niimtaccen dadi yake ziyartar kofofin hancinsa tunda ya shiga gidan ,cike da zaquwa ya je yayi wanka ya wuce dinning dukda Yusrah ba gwana bace a girki amma iya dan training din muguntar da zuby ta bata da dan zama da qawaye yasa ta ɗan koya ba tare da wahala ba ,sannan wani abun jin dadi abincin yayi dadi tamkar qwararriya,yaji dadin abincin da takai masa office sannan yaji dadin ganin na dinning na jiransa .
Saida yaci sosai shi kansa ya manta when last ya nutsu yaci abinci haka in baiyi qarya ba tun kafin matarsa ta rasu .

A daki kuwa yusra bayan tayi wankanta ta sauya zuwa kayan barci qarfe tara ta feshe jikinta da turare ta haye kan gado tana cigaba da kallon yanda ake tuwon samo ta youtube.

Adeel knock daya yayi bai jira izininta ba ya tura kai cikin dakin .
"Hi"
Murmushi tayi masa mai fadi ta kife fuskar wayanta akan gadon saboda kar yaga me take gani
"Me kike kallo?"

"Ina koyon yanda ake tuwon semo ne,gobe zan ma shi shine nake ta bita"

"Hhh shine ya saki nishadi har hakan?"

Rausayar da qwarorin idonta tayi ,ta na ɗan sosa kai cikin jin kunya.

"Ohh kalan naki salon yaudarar kenan? Shiyasa kika kashe mun mata? Saboda kizo ki zambaceni? Kin kashe ta ke kuma don ki samu ki maye gurbin ta!"
Cikin mamaki ta nuna kanta da yatsa
"Wai Ni?"

"Aah bake ba Ni"

"Haba Adeel ya kamata zuwa yanzu ka dauki qaddara ko matarka ta kwanta lafiya a kabarin ta kayi hakuri kaji duk kuskurene kuma an aikata ba kuma zai gyaru ba"

"Baki isa ba ,yanda banyi farinciki ba haka kema"

Cikin sarewa ta mike tsaye "Haba Adeel ya kake so inyi da rayuwata ne...in nayi masifa kace nayi and now i am trying to fix it..."

"Fix what? Shedaniya makira algunguma?!"

Dafe kai tayi cikin ɓacin rai kawai a harzuqe ta dago "Adeel kasan menene kawai ka kashe Ni! Aidai kana da bindiga ko? Ka dauki matakin da ya dace ka kashe Ni ko ka fanshe haushin na kashe maka mata,meye amfanin ka barni a raye kana ganin ajalin matarka?! Kashe Ni kawai ka huta zaka iya kuma ba wanda zai tuhumeka doka ta baka dama"

"Ke Ni zaki isheni da barazana? In na kasheki kina nufin kinci banza kenan? To baki isa ba sai kin fada mun me yasa kika kashe mun mata"

"Kai kanaji ko? Na gaji kawai na gaji sake Ni inyi gaba na yarda talaucin ya kashe mu Allah da ya bamu a da in ka qwace in da rabonmu zai qara mana wani...don haka sakeni inyi gaba "

"Bazan sake ki din ba anan zaki mutu"

"Kai mahaukaci ne🤧" ta juya bagazan² zata fice .da sauri ya bi bayanta
"Waye mahaukacin?"
"Nace kai!........" Daidai nan ta wangale kofa kuma a take ta hadiye miyan bakinta ganin wanda ke bakin qofar .yanda ta ɗauke wuta shima haka Adeel da ya biyo bayanta ya ɗauke wuta cikin mugun razana.
Chapter 9 · 0% Book details