← Book details Gwarzon Namiji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 11

Sashe 7

Gwarzon Namiji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Nace Bari mijina ya dawo ya koran mun ke aidai nan gida na ne ko dole ki fice daga rayuwa ta da mijina"

"😂😂😂anya kuwa matar ne? To in kin kasa gane me ye dalilin zamana a gidan ki ,ina zaune ne ina cike gaf din da kika bari na gurbin mata da miji ,sannan ina so ki sani nan Afrika ne ba qasar waje ba ,munada lasisin cin duriiiihhhh ahhhh"
Ta qare magana tana lashe leɓenta na qasa kamar kwartuwa

"Ya Allah ,zuby Ni kike ma haka? Ni kike ma gadara and You think kina da capacity? Idan bacin bana son Major ke me kike dashi da zakiyi tunanin iya sarrafa mun miji a gado and beside kina iqirarin kedin kwartuwansa ce ? Ya Salam,kodayake nasan makircin diya mace so bazan biye maki ba wlh mijina kintsatse ne ya dauko ki dai don ki koya mun darasin da na girme maki ,so watch me in action"

"Allah srki kinajin har a jikinki kina da wani abu da zaki burge nagartaccen mutum kamar Adeel ? Shahararren mai kudi mai baiwa gomnati bashi ,Nigeria na Alfahari dashi ,jibeki fa me kike dashi"

"Ke ke na gaji ,na gaji da sauraron rubbish ɗinki ,kinsan menene minti biyar tak na baki ki tattara komatsanki ki bar mun cikin gidana"

"Dallah yi mun shiru"

"Zubaida ki tattara kayanki ki fita ko kuma zan nuna maki asalin kalan hauka na"

"Oh shut up she-goat 😏"

Nunata da yatsa tayi
"Ok kar kice ban gargadeki ba,plz kar kice ban maki warning ba" tana fadin hakan ta juya fuuu ta fice a dakin.

Girgiza kai tayi gamida jan tsaki "hmmm Yusrah kenan yaro man kaza😊"

Oum Aphnan
09965990265
[6/28, 4:50 PM] Chuchu👻: After Isha
Major Adeel yana zaune a falonsa na qasa yana shan chocolate coffee din da zuby ta hado masa ,kadan kadan yake sipping yana kallon news

Zuby saman kansa ta tsaya ta fara marmatsa masa kafada a hankula ,cike da gwanancewa na karuwai da suka goge wajen tunkado sha'awar da namiji ,ya dauki cup din coffee din yakai baki yaji tana masa tafiyar tsutsa a bayan wuyarsa ,dayan hannunta tana masa wasa da gashin kansa .
Wani yarrrr dummmm yaji kunnensa ya dauka ya dode na wuccin gadi da sauri ya hadiye wanda ya guntsara ya dire cup din akan table din gabansa Saida ya gyara muryarsa kana ya kira sunanta " Zuby"

Maimakon ta amsa sai kama lilin kunnuwarsa tayi tana shafawa ,muryarta can qasan maqoshi tace "humm"

Da qyar yake qoqarin saita kansa saboda yanda take masa susan kunne da er qaramar yatsan hannunta
"Amma kinsan dai Ni me aure ne ko,kuma a gidan aure na nike kuma Matana ta na nan ko?kina nan ne saboda manufa ta"

"Amma ai dai kasan qwalama da muradin zuciya plz karka haramta mun abinda nike qawa kaima fa na gani sarai a qwarar idonka abun nan kake so...and beside me yusran take dashi wanda banda gomansa kalleni fa"

"Kawai dai kina nan ne saboda manufa ta so concentrate on that"

"But why😢me yasa?"

"Ki yi kawai abunda na baki umurni banason musu"

"Haba now ya zakayi mun haka Major bayan kasa na dandani romon ka ,ka bari muyi ko sau daya ne ,kana sane waccan yarinyar mai kama da kifin Hausa bata da komai da zata iya gansar dakai Ni naji bance dole sai ka aure Ni ba amma let us be friend"

"Bazai yiwu ba na dauke ki ne ina biyanki don ki sauya mata rayuwa kiyi abunda nace and go ... plz "

Bude baki tayi zata sake magana ,hannunta nakan haɓarsa tana dan shafa masa gemu ,saidai suka ga yusra a kansu .ko kallon sashen zuby batayi ba tai masa qerere akai cikin wata ɓingilar riga ga kan nonuwarta sun caccarko ta cikin rigar ,kallo daya ya mata yayi saurin sunkuyar da qawarar idonsa amma cikin idonsa sai gizo shape din nonuwanta suke masa so yace ya sake dagowa ya kalla amma where is his steeze?

"Adeel Ahmed?"!
Ta kira sunanshi a gaba daya ,wani dararas yaji qirjinsa ya buga ,when last aka kirashi da wannan sunan?

"Adeel ina magana?"

"Ehen?"

"Inaso ka koran mun watan nan abar yanzu yanzun nan"

Kafin ya mata wani magana zuby ta kwatseta "Dallah tattare mana plates din nan da ya ɓata da cups din nan zuwa kitchen bansan yaushe zaki natsu ki dawo hayyacinki ba"

"Ke qaramar karuwa jira sai na dawo ta kanki yanzu da mijina nike yi tukun jahila kilaki!"

Tassss! Taji ta yanke ta da gigitaccen mari ,da sauri Yusrah ta dafe kunci ta fasa ihu ,Adeel kam da sauri ya rimtse ido ya toshe kunne yana dan murmushi .

"Sai yaushe zaki koya dabian iya magana? Ehyeh?"

Dago jajayen idonta tayi suka kalli juna "kika mareni?"

Banza tayi mata tana girgiza hannunta rike da qugu

"Adeel ,zama za kayi kana kallon wannan karuwar tana humuliating dina a gabanka?" Maimakon ya bata amsa sai ya sake daukan cup din coffee ya kurba a hankali fuskarsa fal murmushi da annuri

"Ƴan mata ,ina da urgent meeting a office a daren nan so bye" ya tashi tsam ya fara tafiya yana zuwa gaban yusra ya tsaya gamida yin qasa da murya "Nasan ke jarumace bari in bar maku gidan ku dambatu kinji ! Ki mata dukan mamaki" yana fadin hakan yayi saɗaf saɗaf ya fice yana guntse dariya kamar tsohon munafuki😂

Hangame baki Yusrah tayi hannunta still dafe da kuncinta.
Tana kallo har ya fice,dangas dangas zuby tazo ta gabanta tasa qirjinta ta wani kai mata bangaji ,tayi taga taga zata kifa.

"Zo kiyi dambe dani qaramar mara kunya"

Ta wuce fuuu tana taku da qarfin izzah ta bar ta yashe cikin rashin madafa a falon

Oum Aphnan
09065990265
[6/29, 7:28 AM] Chuchu👻: Washegari
Yusrah kwance take tana barci akan gadon ta sai juyi take tana jin dadin barcin ta tun bayan sallah asuba ,bata da niyyar tashi ma .
Zuby ne ta shiga dakin a hankali hannunta rike da cup din ruwa ,tana zuwa tsakiyar kanta ta fara tsiyaya mata ruwan sanyin nan a fuska.a gigice yusra ta bude ido cikin haki da tashin hankali take tambayar waye ... Waye...

"Dallah tashi ki bamu waje malalaciya ,kina matar aure har qarfe takwas da rabi baki tashi barci ba"

"Shine zaki tsiyaya mun ruwan qanqara a fuska ? Kinyi hauka ne? "

"Zaki tashi ki taho muje kichen ko sai nayi qasa qasa dake ?" Kafeta da ido tayi tana mamakin ta amma ita ko dage ido ta kalleta ma batayi ba.

Na baki minti biyar ki fito kar ki bari in dawo in tardake a gadon nan malalaciya,ta sheko mata sauran ruwan cup din hannunta wani gigif Yusrah tayi gamida jan ajiyar rai itakuwa zuby ,ta wuce fakam fakam ta fice ta banko mata kofa gararam!

Sukuti Yusrah tayi wasu irin silent hawaye suka fara silalo mata a fuska
Girrrrr ! Wayarta ya soma vibrating ,a sanyaye ta mika hannu don ganin mai kiranta da wannnan duku dukun safen. A sarari ta furta momy sai dai ko ki bazaka iya yi ba saboda yanda Muryar tata ya dushe.

"Hello auta ta yakk"

Shiru auta ta kasa magana sai hawaye wani na tunkude wani "auta Are You alryt?"

Da qyar ta hadiye kukan ta muryarta nadan rawa tace "Yes i am fine momy"

"Kinajin dadin zaman kuwa"

"Yes" ta bata amsa a takaice saboda kar ta fahimci halin da take ciki

"Tom ya Adeel din hope dai yana kula dake sosai"

"Sosai da sosai mom ,yana da kirki kuma yana sona "

"Uhm that's gud yanzu ina ne zakuje honey moon"

Dararas ! Gabanta ya fadi "momy muna dai ta tunani bamu riga mun yanke shawara ba"

"Kai har yanzu? You guys arent try at all!...ina Adeel din nasan yana kusa dake sa maganata a speaker"

Duddulo ido waje tayi
"No momy yana qasa yana haɗa mun abin karyawa ,yana da sona sosai"

"Break fast kuma? Ina masu aikinku kuma?"

"Momy yace sabon aure baya son mutane suna damunsa maybe sai mun dawo honey moon din sannan"

"Oh ohk i missed u my angel"

"Nima nayi kewarku sosai momma na " ta qare maganar tana sharce ruwan hawaye

"We cant wait to see You back to the office"

"Yes mom...I love U" ta fadi a hankali tayi ending call din ta tsaya tayi shiru hannunta rike da wayar "Nine wannan banzar zata watsa ma ruwa?

***
Adeel kam yau tunda ya tashi yake neman wasu documents amma ya rasa inda ya watsa in zai iya tunawa tun late wife dinsa nada rai ,kuma in baiyi kuskure ba ita yaba ta ajiye masa lokacin .
Wannan yasa ya tafi dakin mamaciyar ya fara fiddo takardunta yana bincika wa ,cike da farinciki yaga doc din da sauri ya fiddo shi a jikin jacket file din ,wani farar takarda ne yaga ya fado ,haka siddan yaji gabansa ya fadi especially ganin rubutun tsohuwar matarsa ,da sauri ya duqa ya dauka ya fara karantawa

"Dear my loving husband,Mijina abun alfaharina ina sonka a koda yaushe ,Ina matukar godiya da inganta mun rayuwata da kayi ,Nagode ma Allah da samun nagartaccen miji kamar kai ,thank You For making me mother to be,Allah ya qara haɓɓaka hanyoyin arzikinka ya barrantaka da haram ,ya baka zuriya dayyiba saliha idan akwai rabon aure a tare da kai a gaba Allah ya baka mata saliha wacce ma ta fini komai ,Allah ya jikan iyayenmu Allah ya barmu tare har Aljannah.....Nagode mijina Happy our weeding anniversary 😍"

Tun da ya fara karanta wasikar idonsa ya fara tsiyaya da hawaye ya kasa dauke damuwarsa ,tunda ta rasu bai taba mata kuka ba sai yau ,kamar tasan zata rasu take roka mun mace ta gari sai dai kuma kash na samu fankashaliya oh god 😭😭😭 Yusrah kin cuce mu kin cuci Innocent soul baiwar Allah mai riko da addini wacce bata dauki duniya ko arziki a bakin komai ba....

Oum Aphnan
09065990265
[6/29, 12:40 PM] Chuchu👻: Da yanganta da kauɗinta ta shigo dakin kamar an wirgota ,cak ta ja ta tsaya tana kallonsa cikin mamakin ganinsa yana hawaye
Cikin rashin kula ,amma dai da dan nuna yanayin zaman tare tace "meke faruwa kuma?"
Chapter 7 · 0% Book details