← Book details Dubai Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 19

Sashe 7

Dubai Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana fadin haka ta sake fadawa jikin Aunty Zahrah tace “shikenan Taheer ya tabbata ba nawaba dama yasha fadamin shi na Habeeytah ne gara nabarshi tun kafin lkc ya sanya nabarshi ta qarfi yanzu gashi ta qarfin zan barshi aunty naga samu naga rashi ya sakeni saki uku minti uku da daura aurens dashi ya turomin text massage a baya na qudurce bazan fadawa kowa ba amma yanzu dole lkc yasa na fada harma an maye masa gurbina da yar uwata Habbatullah...."
Jijjigata Aunty Zahrah tayi tace “keni kin cikani da shirme wace Habbatullah?" Bushirah dake shigowa tayi murmushin jin dadi tace “uwar wannan yarinyar" ta nuna Safnah dake kwance a kafadarta tana baccinta taci gaba da cewa “dama qarya fure take bata yaya rabon gsky ta bayyana mu qara dangi ne yar uwarmu ta dawo garemu yasa har hakan ta faru ni na tabbata Koda ace auren nan ya dade to bazaa zauna lfy ba saboda zuciyarsa tana gurin uwar yarsa" ta juya ta kalli Mom tace “kema yau kaifin harshena bazai tsallakeki ba Mom an dade anayi Ina sanya ido to yau dai gsky ta bayyana Habeey da kike qi har kike shirka saboda ki rabata da danki itama jininki ce dake da Abba Sahabi abokan wasane da babansa da babaki uwa daya uba daya yanzu kije a zuqe jinin Abba Sahabi daga jikinki kinga shikenan kin huta mudai munason yar'uwarmu sannan aure Allah baiyi hadin naki ba nasa ya qullah Yaya Taheer ya angwance da amaryarsa Habibatullah dan baqin ciki saidai ya mutu Safnah zata tashi cikin gatanta ta zama yar gata haihuwar dangi duk wanda ya zagi uwarta kansa ya zaga ka zagi ubanta ka gingimo dutsin dala dabara ta rage take Mom nidai shawara na baki kiyi maza kije a zuqe miki digon jinin Dad da Abba Sahabi a cikin jininki"................
# *UMMUH HAIRAN*
[8/9, 4:08 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: *HABEEYTAH*
*_DUBAI PART 2_*

*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
    *UMMUH HAIRAN*

_Please ki biya kafin ki karanta,daganan zuwa 10/8/2020 VIP 400 single 150, account 0255526235_
_Fauziyya Tasi'u Umar GTB idan katine ta wannan number 09013718241 hoton katin Zaki tura ko lambobinsa ta wannan number dake sama idan ta account ne Zaki tura evidance of payment dinki ta number dake sama._

*10*

Dafe qirji Mom tayi tace “Nashiga uku ni Safinah Bushirah me kike cewa ne wlh qwanyata ta tafi hutu bana gane komai" tabe baki Bushirah tayi ta dauki Pampers din baby Safnah ta fice tana cewa “kanku dai akeji aure Allah yayi alqawarin Habibah ce matar Yaya Taheer sai ku hadiyi zuciya ku mutu ku huta"
Binta sukayi da kallo har ta fice kalma daya ta kasa fitowa daga bakinsu Mom ta zube a gurin dabar tare da Dora hannunta aka ta zunduma ihun days firgita kowa suka sake yowa dakin da sauri, zare idanu takeyi tana kallon kowa ta cafki hannun Kubrah tace “me...meye yake faruwa Kubrah don Allah fadamin me ake Shirin yimin ne"

Dariya tabawa Kubrah tace “mom kema da abin haushi kike to meyene kuma alqawarin Allah ne ya cika Taheer mijin Habbatullah kinqi Allah yaso ya qulla abinsa yabarki da kunya amma Mom ai kina da wani dan ki hadashi da wannan yarinyar mana, dama ai gadon ari sai fanna"
Miqewa Aunty Zahrah tayi tana sharar hawaye tace “ashe dama wulaqancin da kuka shirya yimin da yayanki kenan Yaya Safinah kuka matsa saida muka baro England mukazo 9ja, tur wlh kin bani kunya ashe isar taki ta banzace baki isa da danki da mijinki ba Yaya kinbani kunya nayi nadamar zama qanwarki tunda kin kasa cikawa tilon yata burinta data rayu dashi tun quruciya har kawo girma"

Fincikar Hannun Saudat tayi tace “duk Dan daya hana uwarsa bacci to yasa a ransa shima bazaiyi ba zan dauki mataki farin ciki dai Taheer bazaiyishi bs kamar yanda ya hanamin yata ta warwasa"
Riqeta Mom tayi tace “kada muyi haka dake Zahrah ki muje dakina mubi komai a sannu fadan ya canza salo halan ke baki fahimci ma abinda suke cewa ba, to bari nayi miki bayani wannan karuwar yarinyar da nake fada miki Lele ya mutu akansa ta tsaface zuciyarsa ba kowa bace face yar Hajar matar Alh Sahabi ma'ana babbar yarsa da muka kashe maqudan kudade dan batar da babinta cikin rayuwar zuri'ar Maje Bauchi"

Wani mugun tsoro ne ya kama Zahrah ta zame qasa cikin tashin hankali tace “nashiga ukuna Yaya ai ban fahimci abinda yake faruwa ba dama ashe bata mutu ba Mal yacemin zai batar da ita a duniya zata lalace sannan daga baya a yawon barikinta ta dauko abin kunya ta jajubo cutar qanjamau ta mutu ashe duk qarya yayimin"
Rufe mata baki tayi lkcn da Dad yake shigowa ya bisu da kallo Mom tayi saurin miqewa tace “dama yanzu nake shirin kiranka Dad kaji abinda yaron nan yayi mana minti uku da daura aurensa da yar'uwarsa Saudat ya rattaba mata saki uku?"

Kallon inda Saudat take nade yayi yace “haka Allah ya tsara muma godewa Allah da abin ya tsaya iyanan da baiyi hakan ba da abin ya rikice mana ashe yarinyar nan Habbatullah yayar Saudat ce ubansu daya kinga kuwa ai da anyi abin kunya duk da kasancewar aure ya halatta tsakanin Saudat da Taheer tunda a baya ba auren Habbatullah yayi ba Amma ai ana barin halak ko don kunya musamman da yake Taheer ba Saudat yakeso ba Habbatullah yakeso"
Girgiza kai Mom tayi tace “Lallai kam da anyi abin kunya to Allah yasa hakan shi yafi alkhairi yanzu Ina suke ance kun dora auren ko?"

Jinjina kai yayi yace “Granny dinsu ta tursasa aka daura auren tace Koda dayansu zai mutu saidai su mutu matsayin ma'aurata" wani mashi ne ya sake sukar maqoshin Mom amma sai tace “hakanma yayi yanzu ina suke?" Cikin jin dadin yarda Mom ta Basu hadinkai governor Waziri yace “a halin da ake ciki ita Habbatullah jin cewa Taheer ya zama mijin qanwarta yasata yanke jiki ta fadi qanwar matacciya a fadar likitoci sunce zata iya daukar watanni goma a wannan halin na doguwar suma shikuwa Lale ya samu heart attack yanzu haka yana samun kulawa daga likitocin asibitin Sahabi dake gombe amma akwai yuwuwar zaa tafi dasu England acan zasufi samun kulawa"

Cikin tashin hankali Mom tace “taheer din yanzu Kuma mutuwa zaiyi don Allah Dad ayi duk abinda ya dace" miqewa yayi yace “insha Allahu zasu tashi suyi rayuwa me tsayi sai sun Haifa mana halattatun jikoki, Ina Safnah yau banganta ba"
Tabe baki tayi tace “tana gurin iyayenta" sai yanzu ya tuna da yayan nasa mata duka matsayin matan wasu suke, yace “Subhanallahi meye ya hanasu tafiya gidajen mazajensu bayan an gama komai"
Itadai bata bashi amsa ba ya juya ya fice yayi niyyar tasosu yakai kowacce gdan mijinta Amma sai yaga har shabiyu na dare kuma Basu gama bidi'arsu ba.

Kallon Mom Zahrah tayi tace “shikenan burinsu ya cika na yata ya wargatse haka kike nufi Yaya?" Dafata tayi tace “har yanzu akwai quruciya a jikinki Zahrah idan rawa ta canza dole kida canzawa yakeyi kuma Shirin zaune yafi na tsaye a yanzu nuna qiyayyarmu ga yarinyar nan baqin jini zaija mana musamman ke, sakin ranmu zamuyi mu nuna komai ya wucce in yaso sai mu koma gefe mu sake shiri, ai wlh tunda na rantse banasonta bazan taba sonta ba sufa maza basu da tunani saboda haka mu bisu da yanda sukeso sai muci galaba akansu"

Haka suka rinqa tattaunawa har Hajiya Ummah yayarsu saida suka taso suka fada mata abinda yake faruwa, tayi dariya tace “kuma tanan suka bullo? Hmmm ku bar yan iska zamu iya dasu badai a kwance take ba to kuwa a haka zata qare rayuwarta saidai suyita asarar kudinsu a banza amma bazata tashi ba"
Dubanta Zahrah tayi tace “amma Yaya Ummah sai naga kamar yayi tsauri jinya tanada cin zuciya da jiki mudai nemi wata mafitar wannan batayi ba" harararta Mom tayi tace “bantaba yin tsafi ba sai akan shegiyar yarinyar nan nifa wlh yanda nakejin tsanarta da zata mutu ma da zanfi kowa farin ciki, Yaya Ummah shi Kuma wannan gardamammen yaron ya zamuyi dashi?"

Shiru tayi tana tunani sannan ta dago tace “kada ki damu dashi a barshi ya samu lfy ya warke qalau ita kuma a qara dora Mata jinya kuma ki tubure kice saidai a bashi ita yaje yayi jinyar matarsa ta hakane kawai zai fara nadamar bijire miki saboda zaiso kusanci da iyalinsa babu dama zaiso shima yaga matarsa a cikin halin lfy daga haka zai fara tunanin mafita zai fara danasanin aurenta zaiji tsanarta zai fara tunanin qara aure to daganan ne zamuyi amfani da wannan damar mu sanyashi sakinta sai mu maye masa gurbi da Saudat kinga shikenan ciki lfy baka lfy idan ta warke saita dauki jaka ta koma bariki lkcn komai ya kankama tsakaninshi da Saudat qila ma ta haihu kinga aure ya haramta tsakaninsu indai ba mutuwa Saudat tayi ba"

Wani ihu Mom tayi tace “shiyasa nake sonki kanki naja Yaya Allah yabar mana ke" murmushi Zahrah tayi itadai har yanzu da sauran imani a ranta amma ya zatayi bata da wata hanyar ceton yarta saita amince da wannan gurguwar shawarar.
Miqewa tayi ta matsa ta taba jikin Saudat da tayi baccin wahala jikinta zum da zazzabi, gyara Mata bargo tayi ta kwanta a kusa da ita tana shafa kanta tana tausayawa tilon yar tata tasan zafin rashin masoyi tun akan Abba Sahabi lkcn daya gujewa aurenta yaje ya auri Hajar, tana tuna irin azabar data rinqaji a heart dinta tana tunz irin wahalar da gangar jikinta ta shiga a lkcn, hawaye ta share tace badan wata kusan tafi wata ba da bazan bari a cutar dake ba Habibah duk da kasancewar harda sanya hanuna a lalacewarki amma bayyanarki da abubuwan da suka faru sun sanyayamin jiki lkcn da Yaya Safinah ta shigemin gaba wajen bata rayuwarki sai ya kasance kuma da gudan jininta kuka lalace ita ta tsarawa boka tanaso kiyi cikin shege yanzu gashi ita zata goya yar da ta assasa zuwanta duniya tabbas akwai matsala gaba bamusan meye zai faru ba, Amma Kuma ni Yaya zanyi da tawa yar idan naqi basu hadin kai".............……
# *UMMUH HAIRAN*
Chapter 7 · 0% Book details