← Book details Dubai Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 19

Sashe 11

Dubai Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana gama fadin haka ta miqe ta fice a guje Habeey ta miqa hannu zata riqota amma tariga ta fice daidai lkcn da Mom ta danno ta shigo da sauri ja tayi ta tsaya turus tare da murje idanunta ta matsa ta qara haska fuskar Habeey da wayar hanunta ta tabbatar itace.
Ja tayi da baya da sauri Taheer ya matsa yace “kinga ikon Allah ko Mom jiya da dare wajen qarfe uku saura ta tashi...." Daukeshi tayi da wani kidimammen mari ta danna masa zagi tace “ina ruwana Taheer Ina ruwana da farkawar wannan shegiyar yarinyar nifa bari kaji Taheer na tsani Habeey kuma bazan taba sonta ba har abada wai garin yayama ta farka ita da akace zatayi shekara a kwance?"

Tsoro da mamakin yanayin tashin hankalin da Mom ta shiga ya bayyana a fuskar kowa shikam Taheer tuni idanunsa suka rine sukayi jawur da bala'i yace “to ba saiki hana Allah ikonsa ba tunda kina baqin ciki ta tash..."
Wata uwar shaqa tayi masa data firgita Dad da yake shigowa dama Abba tace “na rantse da Allah indai ni Safinah nice na dauki cikinka watanni tara na tsugunna na haifeka saika saki Habeey saki uku kamar yanda ka saki Saudat yar qanwata da nasha nono na saki uwarta takama"
Bazai saki ba taji an furta a bayanta ta juya da sauri kawai sai taga Granny ta matso tace “sakeshi butulu marar mutunci"

Sakinshi tayi tana haqi Granny ta dubi dai tace “duk ranar da Safinah ta qara furta danta ya saki jikata Habbatullah bazan hanashi ba domin uwarsa ce tanada matsayi a gurinsa amma kuma nima zan murda nawa kambun domin nima uwarkace Aliyu nasan bazakaqi yimin biyayya ba domin dama Safinah zabina ce, wajibine Habeey bazata bar qarqashin igiyar auren Taheer ba harsai ka fara rattabawa Safinah saki uku tukunna kaga zawarcin zaifi ma'ana uwa nayi ya nayi"
Juyawa tayi ta kalli Taheer tace “kaikuma na dawo gareka ka tattare matarka da duk abinda kasan zata buqata ka dawomin da ita gdana dama baayi mata gyaran amarci ba itama a gyarata idan ta qarajin sauqi ta tare a gidanka ba gdan ubanka ba inda zaa hanaku rawar gaban hantsi bance ka saurara Mata ba domin zabinka ce kuma horonka ce Taheer kayi komai ba komai takace har abada so nake nan da shekara biyu naga gdanka ya cika da yara kaji Lelen Granny"................

_Sorry sisters yau kunjini Shiru kuyi manerge da wannan zuwa tomorrow muga abinda zai wakana tunda Granny tabawa jarumin mu damar yayi komai ba komai_
# *UMMUH HAIRAN*
[8/9, 4:09 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: Littafina na kudine ki biya kafin ki karanta bazance Allah ya isa ba amma nasan zai isarmin tunda shi isasshene just 200 VIP 600 ta account number 0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB ko kati MTN ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment dinki ta wannan number dake sama.

*17* Qwanqwasa qofar da akayi yasashi tashi a gajiye ya shiga bathroom ya sakarwa kansa ruwa ya tsaftace jikinsa ya fito ya sanya kayansa ya juya ya kalleta tanata binsa da kallo har ya iso gareta ya dagota a hankali ya rinqa taimaka mata tasa kayanta ya hade mata magungunan ta ya kamata a hankali tana daga qafarta a kasalce har suka fito Dad shidai baiso tafiyar ba yaso su zauna a kusa dashi amma Bai Isa yaja da hukuncin tsohuwar tasa ba.
Ita kuwa Mom tana sama ta zubawa Taheer da Habeey idanu tana qare musu kallo Koda bata qaunar Habeey tasan duk fam dinsu babu mace me kyawun halittarta wai a hakama don ta rame babu rabinta, numfashi ta sauke ta saki labulen tace “wlh indai ina raye sai ka rabu da yarinyar nan Taheer kyau! Kyau shine yake rudarka zan samo maka wacce tafita kyau da..." Saikuma tayi shiru saboda tasan intai mgnr nasaba yanzu ta zagi kanta ne kakan Habeey shine ya saki nono ya bawa ubanta saboda haka kininsu gudane.

Dafe kanta tayi tace “ko Zahrah ce tunda bansonta bansonta" tanajin tashin motarsu ta figi mayafi ta fice fuuuu ta shiga mota tabar gdan ta nufi gdan Ummah anan suka hadu da Zahrah suka dunguma suka nufi dajin falgore gurin wani bokan Hajiya Ummah.
Bai barsu sun masa bayani ba yace “nasan komai watsattsu nasan abinda ya kawoku danki yayi aure ya auri yar uwarsa wadda baki qauna to shakka babu wannan aure babu rabuwa an daurashi kenan yar qanwarki saidai ta rungumi sorry akwai so akwai qauna sannan akwai rabo"

Wasu hawaye ne masu dumi suka zubowa Mom tace “wlh ko million nawa ne zan kashe indai yarinyar nan zata lalace nifa kawai qaunarta ne banayi" dariya ya kece da ita yace “shashasha ai kinyi sakaci da kika bari danki ya aureta bazasu taba rabuwa ba kuma indai zai kusanceta to duk wani shirinki rusasshene abu daya da zakiyi kici nasara shine ki lalata gaban danki a wajenta ta yanda bazai taba kusantarta ba hakan zaisa su tsani junansu sunajin haushin juna zai fara tunanin mafita idan har ya gane cewa ita kadaice baya iya yin komai a gurinta kodai ya qara aure ko kuma ya fantsama bariki dole dayan biyu zata faru"

Shiru tayi cikin tashin hankali ga qoshi ga kwanan yunwa da sauri Ummah tace “boka ya qara auren dai zaifi ai itama a barikin ya tsinto mana ita harma da haihuwar yar kafin fatiha idan ya Kuma lalacewa aimu muka lalace" dariya boka yayi yace “baku da zabi kuje kawai ku dawo washe garin ranar data tare a gidansa daganan wasan zai fara"
Zazzage masa kudi sukayi suka tafi zuciyoyinsu cike da zulumi,
Kwanaki sunata tafiya Abba yana qara narkar da kudi akan lafiyar yar tasa tanata samun sauqi yanzu tana miqewa tayiwa kanta komai lfy ta samu, shaquwarta da Saudat tana qara qarfi tana shigewa jikinta din da Saudat takeyi yasa ta saki jiki da ita a cikin kwanakin ne Saudat tazo Mata da zance Dr Shattima yanasonta ya tagani ta aureshi ko yaya, shawara sosai ta bata ta kuwa amince ta bashi dama cikin watanni biyun da Habeey tayi a gdan Granny akasa bikin Saudat hidima akeyi sosai cikin lkcn Habeey ta matsawa Taheer itafa yakaita gurin Addanta.

Yana sane ya shirya musu tafiyar da dare Granny taso hanawa amma ya kafe har yana cewa da ita kwana biyar ya rage tabashi matarsa abinda baiyi a baya ba yanzu bazaiyi ba.
Da haka ya siye zuciyar Granny ta bashi matarsa suka dauki hanya, tunda suka taho yake tafiya slow saboda dama target dinsa ne suyi dare aikuwa tara suka shiga garin gombe ya juyo ya kalleta yayi mata murmushi yace “a tsarina fah bana zuwa baqunta da dare saidai kiyi hqr da safe ma qarasa idan mun huta"......
# *UMMUH HAIRAN*
[8/9, 4:09 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: *HABEEYTAH*
*_DUBAI PART 2_*

*16*

Wani ihu yayi ya rungume Granny yace “na gde kakata yanzu kuwa zanfi sakewa wlh a gidanki" wani mugun kallo Mom ta watsa masa amma babu damar mgn haka ta juya sumsum ta fice zuciyarta kamar zata tarwatse.
A fusace ta shiga part din nata ta fada kujera tana huci ta dauki wayarta ta kira Ummah ta miqe ta shiga daki tana cewa “yanzu haka tsinnane bokan zaiyi mana yarinyar nan memakon ta dawwama a kwance bayan aiwatar da aikin daya bani nayi kawai sai na samu labarin tashinta daga gamawa ta to wlh bazai yuwu ba ki koma Yaya Ummah inma kudin ne yayi kadan zan qara masa nifa rayuwar yarinyar ce kawai banaso a doron qasa"

Iska Ummah ta furzar tace “kambu yanzu rashin mutuncin da boka yayi mana kenan aikuwa bamuga ta zama ba dole mu tashi tsaye ki bari anjima zan kiraki" aje wayar sukayi taci gaba da zagaye tsakanin corner da corner ta dakin tsanar Habeey na qara nunkuwa a ranta wannan karon dole ta hada harda Granny cikin shirinta domin ta lura itama ruguza mata shiri zata keyi.
A bangaren Habeey kuwa Taheer baiyi sakaci da damar da Granny ta bashi ba kafin gari ya qarasa wayewa ya hadawa matarsa kayanta tsaf ya zuba mata a mota dakansa ya shiga kitchen Abba da Granny da Dad suna zaune a parlour yazo ya wuccesu lkcn likitan da yake taimakawa Abba wajen kula da Habeey din yazo yayi Mata ragowar alluranta.

Zama yayi da cup din kunun alkama a hannunsa da yaji madara sai plantain daya soya mata kasancewar likitan yace kartaci abi me tauri, a hankali ya matsa ta janyeta daga jikin Granny ya dagata ya kwantar da ita a jikinsa ya dauki cokali ya debo kunun saida yaji yayi daidai yanda zata iya sha sannan ya fara bata.
Daqyar ta karba itakam a qasan zuciyarta batayi murna da kasancewar aure tsakaninsu ba don dai batada wani qarfin yiwa kanta wani Abu ne amma taciwa kanta alwashin sai tabawa Mom mamaki zata nuna Mata ita cikakkiyar yar bariki ce indai Taheer ne wataran saita kirashi yace wacece.

Shigowar Bushirah ne yasata qara narkewa a jikinsa ya dauki plantain din ya tauna a bakinsa ya dago kanta yayi ya dora bakinsa saman nata yana tsotsa tare da tura harshensa har ya samu ta bude masa ya cafki harshenta tare da sauke ajiyar zuciya ya juye mata plantain din a bakinta ta janye bakinta a hankali daga nasa fitinannen har yanayinsa ya fara canzawa suka hada ido da Abba yayi saurin sunkuyar da kansa.
Girgiza kai Abba yayi ya miqe yace “abincinka iya matarka kayishi mu bari muje mu nema a cikin gda" shidai kunya bata bashi damar mgn ba ya lumshe idonsa Bushirah tace “amma Yaya badai anan zakuci gaba da zama ba ko?" Kada Mata kai kawai yayi yana shafa bayan Habeey yanajin abinda yakeji na qaruwa, Dad ne ya miqe yabi bayan Abba Granny tace “idan kun gama shiryawa sai ku taho ka shiryata da wuri zan tafi da Safnah Saboda kwafi sauri"
Chapter 11 · 0% Book details