← Book details Daurin Goro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 18

Sashe 8

Daurin Goro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Masha Allah, toh ke sai kiyi hakuri, dama aure a hannun Iyayen maza yake."

"Alhaji Bismillah."

Matsowa Daddy ya sake yi ya zura hannu a aljihun sa ya ciro kudi, alama yayi wa da driver sa ya fito da sauran kayan dake booth ɗin, ganin haka yasa Inno fashewa da kuka ta yi saurin fadawa gidan mai gari. Bisa ga shaidu da wakilan kowanne bangare aka shiga gabatar da daurin auren da ya zamo tsanin farko na duk wata rayuwa da Aminatu zata taka a gaba.

***
Cikin dare ta kasa bacci, babu abinda take sai juyi, bata san yadda zatayi ba, idan har auren nan na nufin katanga da cikar burin ta, zata iya komai akai, duk da babu wanda yasan abinda ya faru sai mutane uku kachal a duniyar nan, amma ba zata bari damar ta ta karshe ta kwace mata ba, wanda auren nan yana nufin rugujewar komai. Har akayi asubah tana bitar abu daya, bata jira gari ya gama haske ba, ta tashi Aminatu ta bata kunu, ta ballo mata magungunan ta ta bata sannan ta dauki yar karamar purse din ta da mayafin ta, ta fice daga gidan. Tafiya me nisan gaske tsakanin kauyen nasu da wanda ke makwabtaka dasu, sanda ta isa gari yayi haske sosai, mutum daya jallin jal data san sirrin ta, sirrin da yake shirin zama tarihi idan har ta aminta da wannan auren, wajen ta tazo, dan samun mafita. Da sallama ta shiga gidan duk matan gidan suka kalle ta cike da mamakin wannan zuwan nata da sassafe haka, gaishe su tayi a tsaitsaye bata damu da irin kallon da suke mata ba ta fada dakin wadda tazo wajen ta.

"Akwai matsala kenan." Ta fada tana kallon ta har ta ƙaraso ciki.

"Ita ce ta taso ni, ina cikin matsala wallahi harira, bansan ya zanyi ba."

"Lallai ai naga alama, me ya faru hala? Ko dai wani abun ya samu yar mutane ne?"

"Kusan haka." Ta cire mayafin ta ta zauna gefen gadon, sannan ta shiga bata labarin komai. Ajiyar zuciya Harira ta sauke bayan ta gama sauraron ta

"Kema dai Inno kinyi sakaci, bayan kinsan dalilinmu da kudurinmu a nan gaba, amma kikayi sakaci da yarinyar mutane har wannan abin ya faru da ita, kina ganin zasu yarda ne su kyale mu duk ranar da gaskiya ya fito? Bayan irin rikon da sukayi wa namu d'an."

"Duk nayi dana sani wallahi, zuciya ce ta d'ebe ni, amma yanzu na gano kuskure na, ki taymaka nidai da shawarar yadda za'a yi da auren nan, idan yaran nan ya dauke ta suka bar kauyen nan kina ganin zai sake dawowa da ita ne?"

"Gaskiya dai, gashi kince an riga an daura auren."

"An daura wallahi."

"Toh mafita daya ce gaskiya idan zaki iya..."

"Zanyi koma menene idan akan d'ana ne."

Murmushi harira tayi ta matso kusa da ita.

***
Kamar kayan wanki haka suka fito dashi, a kwana biyun da yayi duk yai baki ya rame sosai kamar ba shi ba, kauda kai Daddy yayi daga kallon sa, sun riga sun fito a shirye zasu tafi, Dada kawai za'a bari itama dan tace babu inda zata ne, gashi ba zai iya musu da ita ba. Su Ja'afar kuwa tuni suka tsufa a can sai dai Daddy ya ja musu kunne akan maganar, baya son kowa yaji har sai ya dawo da kansa zai sanar musu. Atm card ya ciro ya wurga masa, sai mukullayen gidan.

"Gashi nan, tun da kalar rayuwar daka zaba ma kanka kenan."

Da sauri ya kalli daddyn, sanin hakan me yake nufi ne yasa ya hau rokon sa

"Daddy dan Allah ka tsaya ka saurare ni, wallahi ban aikata abinda ake zargi na dashi ba."

Da wani mugun kallo ya dube shi

"Ni sa'an ka ne Farouk? Ko ka fara shaye-shayen ne dai da gaske?"

"Wallahi ban taba shan komai ba, ka saurare ni kadai nayi maka bayani, wallahi bani da laifin komai."

"You must be a fool, nace baka da hankali sam, idan har kana ganin zan tsaya sauraran ka bayan da kanka ba wani ya matsa bakin ka ba ka amsa laifin ka a gaban kowa, sannan yanzu kazo min da wani banzan zancen ka, toh kayi karya wallahi."

Riko ƙafafuwan sa yayi da sauri yana sake sakin kuka

"Wallahi ban aikata ba, bansan me ya hau kaina ba na amsa, dan Aallah Daddy kar kuyi min haka."

Buge hannun sa yayi ya janye ƙafarsa yana matsawa.

"Idan ka gama haukan naka zamu wuce."

"Daddy ka taimaka min, maganar karatuna fa dan Allah, wallahi ban aikata abinda kake tunani ba, taimakon ta kawai nayi, wanda na dauke ta tamkar Amal."

Tsaki Daddy yaja, ya gaji da jin wannan shirmen nasa, bashi da lokacin da zai kara batawa ya saurare shi, duk wata hujja tasa bata da amfani tun da be kawo ta a lokacin da ya kamata ba, ko a gaban alkali ne to Tabbas ya tabbata mai laifi tun da har yayi saurin amsawa. Duban shi yayi, baya so ya karya masa zuciya, saboda haka ya nuna shi da hannun sa

"Kai yanzu ai na gama da kai, ba zan iya tsayawa sauraren shirmen ka ba. Maganar karatu kuwa in kana so zaka iya neman admission ka soma karatun anan, kar dai ka manta akwai responsibilities na matar ka kanka, so you have to be very careful."

Hannu ya watsa baya ya juya cikin takun kasaita ya fada mota, Amal ce suka fito da Dada tana kuka sosai akan dole ba zata tafi ba, da sauri ya rarrafa gaban Dadan yana sakin kuka me tsuma rai.

"Dada kiyi min rai dan Allah, Daddy ya dau zafi sosai yaki saurarata."

Dago shi tayi ta bude kofar falon ta tura shi ciki ta rufe, motar ta nufa rike da hannun Amal, daddy na ganin haka ya fito.

"Ka barta ta zauna tare dani har zuwa lokacin da za'ayi resuming makarantar su, sai azo a tafi da ita dan Allah."

"Duk yadda kika ce haka za'a yi, mu zamu wuce."

"Allah ya kiyaye hanya, ka kara nazari akan hukuncin da ka yanke wa Babana, duk abinda ka shirya sai ka sanar min a waya."

"Shikenan in Sha Allah."

Matsawa baya sukayi motocin suka fice daya bayan daya, ajiyar zuciya ta sauke ta kama hannun Amal suka juya ciki.

Kaiwa kawai yake da komowa a tsakiyar falon, yana jin an bude yayi wajen ta da sauri ya fada jikinta yana sakin kuka. Bata hana shi ba, tasan zuciyar sa a cunkushe take kukan kadai zai rage masa radadin da yake ji. Ya dau lokaci sosai yana kokawa da zuciyar sa, yana jin kamar ya hadiye ta ya huta da radadi da zafin da take masa, a hankali ta fara sanyi sakamakon addu'ar da yaji Dadan na tofa masa, da sauri shima ya kama yana karanto innalillah wa inna ilaihi raji'un. Sosai hakan yayi masa tasiri kwarai, zamewa yayi ya zauna akan tiles yana sauke kansa kasa.

"Babana..."

"Tashi ka shiga kayi wanka ka gyara jikin ka, dukkan tsanani yana tare da sauki, kuma komai zai warware cikin ruwan sanyi. Ka cigaba da addu'a."

Be musa ba, illa mik'ewa da yayi yana nufar dakin sa cikin tafiyar da tafi kama da wanda ya kwanta jinya me tsawo.

***Ina kwance yau ma kamar ko yaushe tun barowar mu asibiti bana iya aiwatar da komai sai abinda Inno tace, komai yimin ake abinci ma sai ta bani a baki, shigowa tayi tana tura kyauren dakin namu, gefen da muke ajiye kayan mu ni dasu Karime ta nufa, ta jawo ledar kayana ta fito dasu, set uku ne an wanke su sai hijabi daya da mayafi yellow, wata ledar sabuwa da alamun ita ta shigo da ita ta bude ta zuba kayan, takalmi na guda daya samfurin sukwal ta jawo shima ta saka min, sai dan kunne da sarka duk suma na sallah ta ne, ina kallon ta har tapp gama tana jan tsaki.

"Tashi kije ki watsa ruwa maza."

Mik'ewa nayi na amsa da toh na nufi bayin dake tsakar gidan mu, su Hanne na gani da su Karime sun cin kwalliya sun sa sababbin kayan su na sallah, kamar na tsaya yi musu magana sai kuma na fasa na shiga wankan. Mintuna kadan na fito na sake wucesu na shige ciki, da hannu Inno ta nuna min kayan dake ajiye a gefen tabarmar dakin. Dauka nayi na saka na koma na zauna ina tunanin inda zamu ake ta wannan shirin. Fita tayi ta barni a nan, ina ta jiyo hayaniyar yaran gidan sama sama, da gudu naji karime ta shigo gidan tana kiran Inno

"Ga motar chan tazo Inno."

"Naji me bakin aku."

Ta katse ta tana hararar ta, mamaki ne ya kamani, yau Inno ce ke cewa karime me bakin aku, lallai ba karamin bacin rai take ciki ba. Shigowar ta dakin ne yasa nayi saurin kallon ta

"Tashi maza ku kama hanya, saura inji ko in gani, ba dadewa zakiyi ba zaki dawo."

Da sauri nace

"Ina zani Inna?"

"Ban sani ba, tashi nace ki wuce suna jiran ki."

Tashi nayi jiki a sanyaye na fito tsakar gidan, Yalwati da Babar su Hanne na gani a tsaye duk sun sha lullubi, kamoni sukayi muka nufi kofar fita daga gidan. Motar dake ajiye a waje aka bude mana muka shiga, sai a lokacin naga Hanne da Karime a gaba, ajiyar zuciya nayi na ɗan ji sauki tun da bani kadai bace. Ina ji aka tashi motar muka dau hanya. Wannan tafiyar tana daya daga cikin shafukan rayuwa ta da bazan taba mantawa ba.

Rano 😍  ©®HafsatRano

*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo

                    (7)
Chapter 8 · 0% Book details