← Book details Daurin Goro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 18

Sashe 14

Daurin Goro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga masa kai nayi ba tare da na gane abinda yake nufi ba, matsawa nayi baya kadan na sake kwanciya ina kokarin kama cikina da naji ya murda.

"Kince abibci?"

"Umm umm."

"Ok Ina zuwa."

Ya tashi tsam ya nufi Kitchen din, chan sai gashi da abinci a tray da ruwa, zama yayi a kasa ya tankwashe kafarsa ya nuna min kusa dashi

"Oya..."

Da sauri na sauko dama abinda nake jira kenan, tare muka shiga ci yana bani labarin makarantar da yaje, nan danan na ware na shiga yi masa hira nima, ni na kwashe kayan na mayar na dawo na zauna ina duban wayar sa dake saman kujera..

"Dan kira min Amal dan Allah na bata labari."

Girgiza min kai yayi yana cewa

"Karki fada mata, ki bari kawai sai dai tazo ta ganki da uniform."

"Tohm shikenan." Nace ina murmushi. Mik'ewa yayi ya nufi kofar fita yana cewa

"Kije ki kwanta kinji, gobe da safe zamu fita."

"Toh." Nace ina mik'ewa dá sauri nayi daki.

***Da safe shine ya tashe ni, ya taimaka min na shirya muka fito, dakin Dadah muka wuce yana rike da hannu na, tana ganin mu ta riko ni tana sani a jikin ta, kallon shi naga tanayi cike da tsantsar tausayi. Girgiza kai kawai yayi yace "Zamu wuce Dadah, ayi mana addu'a." Hannu ta ɗora a kaina ta yi min addu'a, sannan ta rike hannun shi shima ta haɗa waje daya da nawa..

"Dan Allah Farouk karka yi wasa da abin da mukayi magana akai jiya, zan iya cewa kwana nayi ban runtsa ba ina tunanin komai."

"In Sha Allah." Ya amsa mata

Sakin hannun tayi tace muje Allah yayi mana albarka. Haka muka fito yana rike da hannun nawa har mota, wannan karon bayan shima ya shiga tare dani maimakon gaba, driver yaja muka dau hanya. Har muka isa makarantar be daina amsa waya ba, bansan da wa suke maganar ba amma tabbas maganar me matukar muhimmanci ce, lokaci zuwa lokaci yakan kalle ni ya sakar min murmushi. Sai daya ga mun doshi cikin makarantar sannan ya ajiye wayar, waje muka samu muka zauna har aka fara zuwa, ina ta kallon komai kamar almara, dandazon daliban dake kaiwa da komowa a cikin makarantar su suka fi jan hankali na, uniform dinsu ma kawai abin kallo ne, cikin tsafta da tsantsar nutsuwa. Sai wajajen goma da rabi sannan wani mutum yayi mana umarni da muka shigo, shiga mukayi muka zauna ya ɗan fita ya barmu. Kallo na ya Farouk yayi yace

"Idan suka tambaye ki sunanki, kice Aminatu Farouk MD kinji?"

Kafin nayi magana mutumin ya sake shigowa, zama yayi ya umarci ya Farouk ya ɗan jira a waje, fita yayi ya rufo mana kofar, kujerar kusa dashi yace na dawo, ya shiga yi min tambayoyi, da yawa ban san amsar ba, musamman bangaren turanci da lissafi, duk da na kan fuskanci wani abun saboda dan zaman da nayi da Ya Farouk da karatun da yake min dukka da turancin yake min su, sai dai ba komai ne nake ganewa ba duba da yanayi da makarantar da nake yi a dah. Tashi yayi ya leka ya sake kirawo shi.

"Mr Farouk, mun mata interview sai dai fa she's left far behind, ya zata iya catching kuwa? I doubt so."

Folding hannun sa yayi yana duban ya Farouk, murmushi yayi ya ce

"Sir munyi duk maganar nan da principal, zamu biya kudin extra lesson da za'a dinga mata har Allah yasa tayi picking, and bani da doubt zata kamosu, tana son karatu sosai so ina da hope akan ta."

"Ok Good, if that's the case, sai muyi komai yanzu, next week Monday ta zama full student, ina ga hakan zaifi."

"Hakan ma yayi, thank you very much."

"It's our pleasure."

Tashi yayi yace ya mu biyo bayan sa, muka bishi wasu offices, duk wasu formalities bamu bar school din ba sai da muka gama su, a ranar aka bani komai har da uniform, murna da farin cikin da nakeyi ba'a magana, haka muka dawo gida ina rungume da komai kamar wani ne zai raba ni dasu.

***
Dukkanin satin a cikin shiri muka karasa shi, sosai akayi min provision na dukkan abinda zan bukata, wannan karon Dada da kanta take tsaye akan komai, da ita aka gama shirya min komai. Sai dai ina lura kamar su ɗin ma hada kayan su suke tayi waje daya,sai dai ban kawo komai ba, na dauka ko wani abun dai zasuyi kawai, ana gobe tafiya makaranta dana matsu ina ji kamar na jawo ranar Dada tasa mai aiki ta rakani gidanmu. Gaba daya Inno tayi laushi kamar ba ita ba, ta rame sosai babu alamun walwala a tattare da ita. Kasa shiru nayi har sai dana tambaye ta ko bata da lafiya ne, ta bini da ido kawai ba tare da tace komai ba. Da muka zo tafiya ta dauko wata leda ta bani wai na makaranta ne, na karba nayi godiya na bawa mai aikin ta rike min, zamu tafi ta sake kirana daki ta hau min nasihar da bazan ce ga musabbinta ba, duk yawanci akan kula da karatu na ne, nidai kawai amsawa nake cike da mamaki, ban taba tunanin Inno zata min kwatankwacin hakan, duk sai naji babu dadi bana so na barta, da muka zo tafiya kuwa har da sharar kwalla ta cike da tausayin Inno da abinda yake damunta da bansan ko menene ba.
Washegari da wurwuri na shirya tsaf cikin uniform d'ina sababbi kal, na zauna zaman jiran Ya Farouk, ina zaune shima ya fito, dan tsayawa yayi da baya yana kunshe dariyar sa, hatta jakar da komai na ajiye a gefe, zaman jiran sa kawai nake, karasawa yayi ya zauna yana dauke kansa. Ban gaishe shi ba, kawai na fara maganar tafiya, kin amsa min yayi ya wuce Kitchen ya hado tea ya fito.

"Jeki nemi abu kici." Yace yana zama cikin kujerun falon, ganin fuskar sa babu wasa yasa na tashi tsam nayi Kitchen din, tea din nima na hado na dauko bread na fito, kamar magani haka nake ci cike da daukin tafiya, yana ta kallo na ta gefen ido har zuwa sanda ya gama ya maida komai Kitchen yazo ya fice, sauri sauri nayi na karasa na sake gyara komai na zauna ina kallon kofa. Chan sai gashi ya dawo dauke da wasu ledoji, a saman kujerar ya watsa su ya wuce dakin Dadah, jim kadan suka fito a tare itama ta shirya alamar tare zamu tafi. Da fara'a ta na gaishe ta, daga nan muka rankaya waje muka shiga mota ina ta murna kamar bakina zai yage. Uffan be ce min ba, yana dai noticing duk motsina. Haka nan yaji ba dadi, ko ba komai akwai matukar shakuwa tsakanin mu, amma hakan shine mafita ga dukan mu. Sanda muka isa makarantar sai naji duk babu dadi, Ina labe a bayan Dadah har aka gama komai, tuni fuska ta ta chanja dana ji an kirawo wata an ce ta tafi dani, da sauri na kankame Dada ina sakin kuka, dariya suka saka baki dayan su, hakan ya kara tunzura ni, hannu na ta kama cikin harshen turanci tace "muje ko?" Kwace hannu na nayi na sake saka kuka ina kallon Ya Farouk, shi dinma ni yake kallo, hannu yasa ya kirawo ni, da sauri na tafi gareshi, maimakon yayi min magana sai yaja hannu na muka fita daga office din, chan baya wajen wasu shuke-shuke ya kaimu, yana zuwa ya cika hannu na yana ja da baya.

"AMINATU..." Ya kira sunana yana saka idon shi a cikin nawa, raw raw na sake yi da idon zan cigaba da kukan, da sauri ya furta

"Ohh Ya Salam! Baki son makarantar ne?" Girgiza masa kai nayi na cigaba da kuka na.

"Toh menene, kin fasa karatun ne?" Nan ma girgiza kai nayi

"Bude baki ki faɗa min kinji." Ya fada yana sake matso wa sosai kusa dani, cikin muryar kuka nace

"Ni ba tafiya zakuyi ku barni anan ba."

Dan murmushi yayi kadan, yasan kwanan zance, lallashi na ya hau yi cikin son gamsar dani muhimmancin hakan, tare da alƙawarin zuwa duba ni kowanne lokaci, da kyar na sa kaina na amince, sai dai ban bar kukan ba, haka ya sani a jikin sa yana shafa bayana a hankali, lamo nayi na kasa kwakkwaran motsi, ina jin shi yana kokarin raba jikina da nashi jin takun tafiya, Dadah ce ta iso wajen tana nazarin mu.

"Babana sallamar ta isa haka nan, karka manta fa muna komawa..." Kallon danayi mata ne yasa ta gimtse maganar tana yin gaba

"Kuyi sauri dai ina mota ni, Aminatu Allah ya bada abinda aka zo nema, banda kawayen banza."

Daga haka ta bar wajen dukkanninmu muka bi bayan ta da kallo babu ko kiftawa, a hankali ya kamo hannu na, ya ciro dan karamin akwati ja me masifar kyau daga aljihun sa, bude ta yayi dan karamin zoben azurfa ya bayyana, ya kama ring finger na ya zura min, yana kallon fuska ta. Babban harafin D cikin wata irin kwalliya shi ya karawa zoben kyau da kawa, kura ma hannun nawa ido nayi cikin tunani me tsawo da bansan me nake son tunawar ba. A hankali cikin wata iriyar magana ya furta...

"Alk'awari kaya ne Aminatu, ki rike Alk'awari, nima zan rike, kiyi karatu, kiyi karatu har sai kin ji kamar kwakwalwar ki xata fashe, a sannan zan tabbatar da buri na ya cika, ina so ki zama cikakkiyar lawyer saboda wani kudiri nawa."

Daga kai kawai nayi ina cigaba da kuka ganin da gasken tafiya zasuyi, gaba yayi kawai nabi bayan shi da sauri, haka muka jera har gaban motar, da wani irin sauri ya fada ba tare da ya sake kallon bangaren da nake ba, ina ji ina gani suka fice daga cikin makarantar.

Jan kafafuwa nayi na wuce ina jin kamar wani babban bangare na rayuwa ta ya bar ni.
Chapter 14 · 0% Book details