← Book details Darasi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 7

Sashe 7

Darasi Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Sai da Sakinay ta ɗan dunguri Falmata sannan ta dawo cikin hayyacinta,tana harar bayan Sakinat don gani take Sakinat bata dace da wannan gidan ba ita ce ta dace dashi,don haka ko ta halin ƙaƙa sai ta zauna itama a wannan gidan kuma ta fitar da ƙawarta Sakinat.

Tunda Falmata tazo gidan babu abinda take sai zuga Sakinat akan cewa wai tsabar baya sonta har yanzu yaƙi ya kaita gidanta ya barta a gidan iyayensa,wani lokacin kuma ta ce kinga gidansu kamar aljannar duniya ko ina gwanin sha'awa,duk yadda akayi komai shi yake a gidan kuma yana jin maganar mahaifiyarsa.

Da ya ke Sakinat sokuwa ce sai maganganun Falmata suka fara tasiri aranta har ta fara ganin ayanzu za ta iya fito na fito da Ammi don tun ba yau ba tana ganin irin abubuwan da Ammar ya ke wa Ammi,yana matuƙar girmama maganarta don har yafi jin maganar mahaifiyarsa da ta mahaifinsa.

Acikin satin Ammi babu irin rashin kunyar da ba ta gani ba awajen Sakinat kuma ta lura Falmata ce ke ƙara zugata,don haka duk sai ta watsar da su ta cigaba da sabgoginta,don dama Khalisat tana boarding Ammar kuwa ya yi tafiya zuwa ƙasar England wani aiki.

Ƙwanan Falmata biyar ta haɗa kayanta don tafiya gida,ta tambayi Sakinat ina ne ɗakin Hajiya,babu musu Sakinat ta nuna mata ta ƙwanƙwasa alokacin Ammi tana azkhar.
Ammi ta buɗe mata ta shigo tana gaida Ammi,ta amsa tana mamakin ganinta bata gama mamakin ba ta jiyo Falmata tana ce wa.

"Da man gida zan tafi shine na ce bari inyi miki sallama sannan in faɗa miki wata magana don nasan baki sani ba,lulluɓin biri aka yi muku.

Da mamaki Ammi ta ke kallonta tana mamakin hali irin na Falmata na munafurci,wato don taga ƙawarta ba ta nan shikkenan sai kuma ta yi gulmarta.

"Hajiya Sakinat fa kafin ta auri ɗanku sai da aka cire mata ciki har sau biyu,kuma wallahi har yanzu bata daina bin maza ba".

da sauri Ammi ta ɗaga mata hannu sannan ta ce cikin tsawa"get out in my room".

da sauri Falmata ta fito har tana haɗa hanya tana da na sanin zuwa wajen Ammi don yadda kasan zaki haka ta juye mata.

Akan hanya suka haɗu da Sakinat sannan ta rakata har bakin gate,tana mamakin sauyin Falmata lokaci ɗaya.

Ammar yana dawowa Ammi ta sakashi a gaba da ya tafi da Sakinat sabon gidansa na Abuja,babu yadda ya iya haka ya tafi da ita ransa baiso ba.

Wannan tafiya itace ta zamewa Ammi wannan mummunan tabo a rayuwarta don tun daga ranar Ammar bai sake zuwa wajen mahaifiyarsa ba,don tun bayan komawarsu da Sakinat ta ga Ammar ba ya ko kallonta ballan tana ta saka ya yi mata magana.

Da kanta ta nemi Falmata suka haɗa kai aka raba tsakanin ɗa da uwa Ammar da Ammi.

*Cigaban Labari*

*Fahima*
-------------------

A yanzu Amma ta matsamin wai acikin mane ma na wai in fito da mutum ɗaya don ita ta gaji da kallona babu aure,abin har mamaki ya ke bani don har yanzu ko shekara sha biyar ba amman ake min zancen aure.

A cikin masu sona aƙwai wani Alhaji Tasi'u mai nera,shine wanda Amma tafi don yana matuƙar jiƙata da kuɗi.

Ita kuwa Fahima ta yi mugun tsanarsa don mutumin mugun ɗan iska ne duk ranar da yazo sai ya nemi daya taɓa jikina ni kuma in ƙi yarda.

Kuma kamar maye gobe ma sai ya dawo,kuma a ƙalla ko da baiyi shekara hamsin ba to kaɗanne.

*miss green ce*
*DARASI!!*

Free page 20/21

Rabiatu Bashir
(ummu maher)miss green.

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajarsu ta online zasu biya 2k*

Sakinat ce a zaune tana waya da Falmata, kana ganin Sakinat kasan ranta a ɓace ya ke ta ce"Falmata yau watanmu biyar da zuwa wajen bokannan amman har yanzu banji wani chanji ba da zaisa in gane ina da ciki,abin yana damuna Falmata ni dai idan babu hali kawai mu chanja wani bokan kawai ina ganin zaifi ko"?.

shiru Falmata ta yi tana mamakin hali irinna Sakinat don duk bin bokaye irin na Falmata bata ka ma ƙafar Sakinat ba,ko da ya ke Sakinat ta yi mata zarra a fannin kuɗi dole ta fita fitowa gari.

"Eh aƙwai wani boka da na ke tunanin zai iya wannan aikin wanda matuƙar ya yi miki aiki to fa shikkenan,zaki ganki da ciki a jikinki ko da na aljanu ne kuwa".

da sauri Sakinat ta ce"haba Falmata ya zaki ce wai ko da na aljanu ne,idan na samu cikin aljanu ai an samu matsala lafiyayye na ke son haifa".

Ƴar dariya ce ta kusa kufcewa Falmata don tasan duk wannan yawon da suke yi ba lallai ne ta haihu ba,don tun tana budurwa ta gama zubarda abinda tun a waje".

Ƙalubale gareku ƴan mata ku daure ku riƙe mutuncinku domin shi mutunci madara ne,kuma daga inda namiji ya yi amfani da ke ko da ciki bai shiga ba to kin gama cutar kanki,gwara duk rintsi ki daure ki kaiwa oganki(mijinki)budurcinki na ƴa mace,wallahu a 'alam.

Nan dai Sakinat da Falmata suka shirya zuwa har Ghana wajen wani tsohon mushriki don Sakinat ta samu Haihuwa,washe gari da wuri suka ɗauki hanya don ma jirgi zasu shiga sai Accra(Ghana).

Sun sami layi sosai don haka suka jira har layinsu yazo,suna shiga Sakinat ta fara toshe hancinta don wani irin mugun warin da wannan mushrikin bokan ya ke,Falmata ta riƙe hannun Sakinat tana janta don ta daina rufe idon,don idan bokannan ya zuciya zai iya gamaw dasu duka ya shanye musu jini.
Tun kafin su faɗi abinda ya kawosu Bokan ya fara faɗa musu duk abinda suke so ayi musu,ya janyo wani glass yana nuna musu abinda ke ciki.

Wata yarinya suka hango kyakkyawar Bafulata na suka hango yarinyar ba za ta wuce 13zuwa14 ba,cikin tsoro Sakinat ta ce"boka wannan kuma wacece?menene haɗinmu da ita?"

cikin sauri bokannan ya buɗe mushen bakinsa ya ce"ita wannan yarinyar ita ce za ta kawo ƙarshen matsalarki."

Alhmdh.

Anan na kawo ƙarshen book 1,kuma na gama free page idan ka tashi biyan kuɗinka ka neme ni ta wannan number.

07068606171

Ga
Details

*Littafin na kuɗi ne ban yarda ki karanta mun baki biyani ba,Gamai buƙata n cigaban labarin zai biya ₦300 normal* group...Vip group
₦500... Special₦1k....zaku iya Turo da katin MTN ta wannan number 07068606171
ko kuma ku tura ta wannan account number 2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith Bank.

*Miss green ce*
Chapter 7 · 0% Book details