← Book details Darasi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 7

Sashe 6

Darasi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sakinar ƴar asalin maiduguri ce a cen aka haifeta ita kaɗai ce awajen mahaifinta tun tana ƙarama mahaifiyarta ta rasu,bayan mahaifiyarta ta rasu ne suka koma garin adamawa anan kuma riƙonta ya koma gun yayar mahaifinta.

Yayar mahaifinta ita ce ta kai Sakinat wajen aiki da kanta don ta ce tunda taƙi talla dole ne ta yi aiki,gidan farko da aka kaita yaron gidan ya yi mata fyaɗe daga nan kuma suka jo ne da yaron gidan don kullum Sakinat tana ɗakinsa,duk sanda
Za suyi mu'amala sai ya bata wata ƙwaya ta hana ɗaukar juna biyu,sakinat kuwa bata san ko na me ye ba don ba tada ilimin da za ta gane.
Kwatsa rannan mahaifiyar yaron ta gansu ta yiwa Sakinat korar kare,daga nan ta koma gidan yayar mahaifinta mai suna Abuwalle.

Abuwalle mace ce mai shegen son kuɗi da son duniya don haka babu daɗewa ta samo wa Sakinat aiki a gidansu Ammar.
Tun ranar da Sakinat ta fara aiki a gisansu Khalisat Ammar ya dawo daga tafiya daga ƙasar germany,Tun da Sakinat taga Ammar hankalinta ya tashi don kyaunsa da nutsuwarsa ba ƙaramin dagula mata lissafi ya yi ba.

Ta rasa yadda za ta yi da rayuwarta don ko kallo bata ishe sa,ko mopping ta ke idan ta hangosa ɓuya take saboda matuƙar ta gansa to fa zuciyarta ta yi ta bugawa kenan,har sai ya bar wajen da kusan awanni sannan za ta samu damar fitowa don cigaba da aiki.

Ammi ba macece mai takura ba saboda ba ta ɗaya daga cikin matan da ke wahalar da ƴan aikinsu ba,saboda macece mai mutunci da kuma karamci.

Ana cikin haka ne Sakinat ta fara wani irin ciwo,idan ciwon na ta ya tashi har aman jini ta ke,babu shiri Ammi da Alhaji Muhammad Lamiɗo wato mahaifin su Ammar suka kai Sakinat asibiti.

Tashin farko bayan likita ya gama gwaji ya ce ai Sakinat tana da ciwon zuciya,adinga yi mata duk abinda ta keso saboda idan ba haka ba ciwon ba zai warke ba.

Hankalinsu ya tashi sosai bayan sun dawo gida shima Ammar ya dawo ganin da Sakinat suke tare ya yi gaba zuwa cikin babban farlon gidansu,yana zama sai ga su Ammi sun shigo.

Suka saka Sakinat a gaba da tambayar abinda ya ke damunta kai tsaye ta ce ita Ammar ta ke so. . . ..

Kuyi haƙuri wani busy ne shiga ne👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻.

*Miss green ce*
*✨DARASI!!!✨*
(Topic)
*` _``a love&```_ destiny story*

By
Ummu Maher(Miss green)🍀💚

*Littafin na kuɗi ne ban yarda ki karanta mun baki biyani ba,Gamai buƙata n cigaban labarin zai biya ₦300 normal* group...Vip group
₦500... Special₦1k....zaku iya Turo da katin MTN ta wannan number 07068606171
ko kuma ku tura ta wannan account number 2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith Bank.

*Free page*
16/17

. . .Wani Mugun kallo Ammar ya wurgawa Sakinat da ke lafe a jikin Ammi,sannan ya kalleta cikin wata muguwar tsawa yace"i hate u!i said i hate u!"shin ana soyayya dole ne,me zanyi dake kucaka ƙazama mara class,ni kuma in rasa wacce zan aura sai ke? Stupid girl kawai mssttttt".

Ya buga wani uban tsaki ya haye upstair don gani ya ke idan ya cigaba da kallon wannan mumu girl ɗin komai zai iya faruwa dashi,ƙarshe power ɗinsa na soldier ya motsa ya shiga jibgarta.

A hankaki Alhaji Muhammad Lamiɗo ya zauna ya kalli Sakinat ya ce"tashi ki koma ɗaki ki kwanta kinji Allah ya yi miki albarka".

da sauri Sakinat ta tashi kamar daman ta matsu ta tashi ɗin,Ammi tabi bayanta da kallo ta ce"Alhaji yanzu ya ya ka ke ganin za ayi"?.

"Insha Allah komai zaizo da sauƙi amman kafin nan zanyi shawara zuwa ko gobe fatanmu Allah ya tabbatar mana da alkhairi.

***

Ammar yana ɗakin motsa jikinsa yaji a jikinsa kamar ana kallonsa,da sauri ya juyo,Sakinat ce tsaye a kansa ta lu-la duniyat tunani,wata uwar tsawa ya buga mata ita kuwa tana cen kogin tunaninsa yadda gashin ƙirjinsa ya ƙwanta luf luf gwanin sha'awa ruwan gumin jikinsa ya jiƙa duk beauty ɗin skin ɗinsa abinka da ƙyaƙƙyawa sai ya yi wani ƙyau mai ɗaukar hankali.
Wani banzan kallo ya yi mata a karo na biyu sannan ya tashi ya yi tafiyarsa.
Sakinat ta bisa dana mujiya kamar za ta haɗiyesa tsabar so da ƙaunarsa.

"Ammar!"Alhaji muhammad ya faƊi sunansa cikin babbar murya ya ce"me sunan manya Ɗazu misalin Ƙarfe uku da rabi na rana an Ɗaura aurenka da wannan Yarinyar Sakinat abisa yardar waliyyanka da waliyanta don har garinsu na je muka taho da babanta".

Kansa a sunkuye tun da Alhaji ya fara magana baice komai ba,don iyayensu sun yi matuƙar ƙoƙari wajen basu tarbiyayya,idanuwansa sunyi jawur sosai jijiyoyin kansa sun tashi ruɗu ruɗu,ba Ammar ba hatta Khalisat sai da taji wani iri har a cikin zuciyarta.

Tunda Ammar ya Tashi daga wajen mahaifansa kai tsaye motarsa ya hau ya fita,wayarsa ya ɗauka ya kirawo Aliyu ringing na farko ya ɗaga yana tsokanarsa da ango don ɗazu yaji komai na game da auran da Dad ɗinsa ya yi masa.

Banza Ammar ya yiwa Aliyu ya cigaba da shaƙiyancinsa har ya yi shiru sannan Ammar ya ce idan har ka gama ka sameni a hill&vally.

Waje ne kyakkyawan waje wanda ya tsaru,an ƙawata shi da followers da bishi yu kala kala,ga sanyi da ni ima ta ubangiji,mutane da dama suna zuwa wajenne saboda shaƙatawa,ko kuma hutawa saboda zuciyarka ta samu reliep.

Yana zaune yana ta kallon ruwan da ya ke ta zubowa ta cikin ƙasa,shima wajen an ƙawata shi sosai gwanin ban sha'awa.

Tunani kawai ya ke yi a game da makomar aurensa shi da wannan mummunar yarinyar,sam ba irin kalar Sakinat ya ke buƙata a matsayin matar aurensa ba,gaba ki ɗaya ma dai ya tsani yarinyar sosai,har bai san adadin tsanar da ya yi mata ba.

Yana zaune kiran Amir ya shigo wayarsa ya ɗaga a hankali kamar ba soja mazan fama ba,nasiha mai ratsa jiki Amir ya dinga yi mai a game da auren da mahaifinsa ya yi masa,kada ya bijirewa mahaifansa ya yi abin da suke so wataran zai tsinci haƘurin a gaba.

Tnx kawai ya cewa Amir sannan ya kashe wayarsa saboda tsabar haushi,don shi haryanzu bai yarda zai tsinci wani alkhairi a gurin wannan fush girl ɗinnan ba.
Ammi ma ta rasa mai yasa tunda Mijin na ta ya yi mata albishir da ɗaura auren Sakinat da ɗanta ta tsinci kanta a mai mummunan faɗuwar gaba ta rasa me ya ke yi mata daɗi,ba wai auran ta tsana ba a ah kawai zuciyarta ce bata aminta dashi ba,musamman yadda taga Ammar gaba ki ɗaya ya canza alokaci ɗaya,ta tsani abinda zai ɓata ran Ammar tana yi masa wani irin mugun so da tausayinsa a matsayinta na mahaifiyarsa,Allah kaɗai yasan irin zaman da zasuyi shi da yarinyar,amman koma dai menene tana roƙon Allah ya kawo sauƙinsa cikin ruwan sanyi.
Sannan tana yi masa fatan samun zaman lfy . . ..

"Tunanin me ki ke yi Zulaihat"?.
da sauri Ammi ta cire tagumin da ta yi ta yiwa mijin na ta murmushi don kada ya fuskanci halin da ta ke ciki.

Murmushi ya yi sannan ya ce"Zulaiha na sanki tun kafin ki kai shekarun haka shekararki 14 aka auramin ke alokacin ni kuma ina da kusan talatin kuma ina matsayin soja a wannan lokacin,ki kayi haƙuri ki ka zauna dani a halin da na ke ciki na yaron soja don kowa yasan halin zuciyar soja awannan lokacin harma da yanzu,to me yasa ki ka kasa haƙuri akan wannan auren dana ɗaurawa ɗanki?aƙwai abubuwa da yawa dana duba kafin in haɗa wannan aure ba da ka na yi saba,wannan yarinyar ba tada gata sai Allah akan ɗanmu ta kamu da ciwon zuciya fa?idan ƴarki ce zaki so hakan ya faru da ita?to kinga ba zaki so ba."

Tun daga nan Ammi bata sake haɗe ranta ba kullum cikin yiwa ɗanta nasiha ta ke,tare da addu'ah.

Tafiya ce ta kamasi zuwa bauchi garin aminin Alhaji Muhammad,da ammi za aje amman kuma sai ta ce ta fasa tana da buki,da Khalisat da Sakinat aka yi tafiyar sai Alhaji don shi uban gayyar Ammar yana Abuja.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.

Aranar bayan sun tafi kan hanya sukayi hatsari aka nufi dasu asibitin da ke kusa,shi dai Alhaji abin sai addu a,Sakinat da Khalisat kuwa ɗan kukkurjewa ne kawai.

Aka kirawo su Ammi a waya cikin tashin hankali tazo,yadda taga mijinta abin sai addu'a,ta kirawo Ammar tana kuka ta ce yazo ta faɗa masa halin da suke ciki,kai tsaye daga Abuja ya taho hankalinsa a tashe.

Da ƙer Alhaji ya fara magana yana yiwa Ammar nasiha akan Sakinat,kuka kawai Ammar ya ke na ganin halin da mahaifinsa ya ke.

*Miss green ce*
*✨🌈DARASI!!!🌈✨*
(Topic)
*` _``a love&```_ destiny story*

By
Ummu Maher(Miss green)🍀💚

*Littafin na kuɗi ne ban yarda ki karanta mun baki biyani ba,Gamai buƙata n cigaban labarin zai biya ₦300 normal* group...Vip group
₦500... Special₦1k....zaku iya Turo da katin MTN ta wannan number 07068606171
ko kuma ku tura ta wannan account number 2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith Bank.

*Free page*

18/19

Maganar ƙarshe da mahaifin Ammar ya faɗa shine"Ammar kada ka wulaƙanta wannan yarinyar kada ka juya mata baya,don kaga bani da rai,kada ka taɓa rabuwa da ita ma'ana ka saketa matuƙar ka saketa to ka saka a ranka babu ni babu kai."

wannan maganar ita ce ta ƙarshe da ya faɗa ya fara wani irin tari mai sarƙe maƙoshi daga nan rai ya yi halinsa,babu irin kukan da Ammar bai yi ba na rashin mahaifinsa ga abu goma da ashirin wai kada ya yarda ya saki Sakinat,shi ya rasa me yasa ma ƙwata2 ko kallonta ba yasan ya yi,yadda kasan wata mujiya haka take a wajen Ammar amman ya zamar masa dole ya fara sakin jiki da ita ko don nasihar mahaifinsa.

Bayan wata biyu rannan Sakinat tana zaune suna hira da Ammi,aka yi sallama da gudu Sakinat ta rungume Falmata ƙawarta ta yarinya ta,sosai taji daɗin zuwan Falmata don tunda ta yi aure ko dangin mahaifiyarta basu zo ba,don basu san ma ta yi auren ba.

Kalle2 Falmata ta shiga yi sosai irin kallon tsaf ɗinnan,Ammi sai kallonta take tana mamakin hali irin na wannan baiwar Allah.
Chapter 6 · 0% Book details