← Book details Darasi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 7

Sashe 2

Darasi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Don Allah Amir Ka tausayamin Ka turomin number Umma,na kasance cikin bakin ciki, kwakwalwata tana gab da tarwatsewa kunnuwa na suna yimin kuwwar muryar Umma na,ina San inji Muryar Umma na",sai wasu hawaye masu zafi suka zubo masa.

Kashe wayar Amir ya yi hawaye yana fitowa a idanuwansa ya saka handcachiep dinsa ya goge hawayen da ya zubo masa,ya Danna message ya Nemo number Umma yana kuka ya turawa Ammar number.

Tunda Amir ya kashe wayar Ammar ya tashi tsaye a office dinsa ya buga tebur idanuwansa sukayi jawur sosai kamar garwashi,allurar Soja ta tashi,gashin jikinsa ya Fara mimmik'ewa,ya Rasa abinda yasa duk wata mace in dai ba Sakinat ba,Baya taba ganinta da gashi ciki kuwa harda Mahaifiyarsa wato Umma,wacce take matukar sonshi da k'aunarsa itace ta dauki nauyin karatunsa tun kafin ya Zama wani Abu ta shige mishi a gaba ya zamo abinda ya Zama tun bayan rasuwar Mahaifinsa,yana cikin wannan tunanin Yaji k'arar shigowar sako,da sauri ya dauka yana sharce wata uwar zufar da ta zubo masa,hannunsa yana kakkarwa ya dauka ya duba number Umma ya kirawo Hannunsa sai k'erma ya ke.

Wayar tana hannun Khalisat wato kanwar Ammar,tana Assignment an Kira yafi sau 3 taki dagawa sai tsaki take tana cewa"gaskiya ko waye wannan ya iya nacin jaraba",ta Fadi hakan cikin yaran Fillo wato fulatanci,sai da wayar ta kusa tsinkewa sannan ta d'aga cikin dakusasshiyar murya tace"waye"?.

"Common ki kawai wa Umma stupid!".

Da sauri jikinta ya Fara kakkarwa don tabbas ta gane muryar yayanta,hawaye suka Fara zubo mata da sauri ta haye step,tana kwalawa Umma Kira wacce alokacin ta ke sallar duha,wato sallar walaha, Khalisat cikin kuka ta ce Umma ya Yaya Ammar a waya"!.

Lokaci daya Umma taji kanta ya Shiga sarawa sosai,zuciyarta taji tana bugawa ta saka hannunta ta danne saitin zuciyarta daya tsananta buga mata.

Khalisat tasan za'ayi haka Amman sai ta goge hawayenta ta ce"Umma ki daga wayar nan kiji me zaice Miki,ki ajje fushinki a gefe ki janyo danki a jikinki don Allah".

Hannun Umma yana k'erma ta saka hannunta ta amshi wayar,sai dai ta kasa saka wayar a kunnenta.

Yaron da ta keso ta ke k'aunarsa Amman yau an wayi gari ya wofantar da ita,ya guje ta tamkar wata mujiya,idan Bata manta ba yau tsahon shekara 5 rabon da ta saka Ammar a idaniyarta balle har ya bugo mata waya.

Duk abinda a keyi Ammar yana Ji,kuma yana jiyo kukan Amminsa,hankalinsa ya tashi jijiyoyin kansa suka tashi sosai ya dafe kansa yana kuka.

Da sauri Khalisat ta saka wayar a handsfree don Umma taji muryar d'anta sosai,ai kuwa tana saka muryar taji Ammar yana cewa.

"Ammina"!

Sai kuka yaci k'arfin Ammar wani amai ya taho masa,ya ajje wayar ya ringa kwarara amai kamar me yaron ciki,ta cen bangaren Umma tana Jin Ammar ya Fara amai,hankalinta ya tashi ta Fara Kiran sunansa tana cewa"Ammar don Allah Kada Ka saka kanka cikin wani Hali Nima Ka sakani,don Allah kayi magana inji Muryar Ka".

Itama anan kukan yaci k'arfinta ta yarda wayar tana matsanancin Kuka,Khalisat ma hawayen ta ke tana sharewa Umma hawayen sannan tana bubbuga bayan Umman kamar k'aramar yarinya.

Kiran wayar Ammar Khalisat ta ringa yi Amman Bai daga ba,k'arshe ma taji an kashe wayar,hankalinta ya tashi ta Rasa Yadda zatayi gashi,ga Umma ciwon zuciyarta ya tashi da k'er ta Samu ta balli maganinta ta Bata ta Samu bacci,gashi kuma Yaya Ammar shima yana cikin wani Hali.

Kifa kanta tayi tana kuka me tsuma zuciya,tana kuka tana cewa"Anty Sakinat Baki kyauta mana ba kin rabamu da sanyin idaniyarmu,kin raba D'a da uwa,kin raba soyayya me k'arfi,Why me yasa kika yi mana haka?Meye ribarki?".

Nan dai Khalisat ta ringa surutai marasa Kan gado,daga Baya ta tashi ta yi alwala ta Fara sallar Nafila tana kuka tana rokon Allah subhanahu wata'ala ya kawo musu sauki da haske cikin wannan lamarin.

************
"Wallahi Fahima Kada ki sake ki dauki tallannan ki zubarmin da kudi,kika yarda kika zubarmin da kudina ranar saina ci ubanki a Gidanan".

"Na gode"

Na ji muryar Baba ya fito daga ban d'aki ya cigaba da cewa"Fahima Kada ki Dade kina zuwa idan kiga babu ciniki ki dawo".

Cikin sassanyar Murya ta na ce"Insha Allah Baba bazan dad'e ba".

Na dauki tallan na tafi ina tunanin Hali irin na Amma,ita dai zata Samu kud'i babu ruwanta da matsala,ko da hakan yana barazanar lalacewar rayuwar y'ayanta.

Yauma banyi wani cinkin kirki ba na taho gida saboda ƴan garuwar da muke siyarwa duk sun tafi gida don haka yanzu babu ciniki,gaba yana dukan 3 na taho gida don nasan yau Amma Bala'in ta akan babanmu zai ƙare.

Tun daga soro na kejin hayaniyar atika mai kayan gonjo da amma ana ta hira ana shewa,sam ban son matar Ƙwata2 saboda Atika duk wani rashin mutunci itace ta ke koyawa amma shi,ko kallon Atika banyi ba nayi hanyar ɗakinmu tare da yiwa Amma sannu da gida,ko amsamin bata yiba sai kallon kayan tallan kaina ta ke tana hararata,jikina ya hau rawa don idan nayi sa'a ne ma zai tsaya a zagi don nasan har duka sai ta yi.

"Ke zo nan don ƙaniyarki".
da sauri naje har ina haɗa hanya don tsoron Amma na ke ji kamar mala'ikan mutuwa.

"Yanzu ita Atikan itace abin wulaƙantawa a wajenki?idan Adama ƙanwar ubanki ce zakiyi mata haka?tsugunna ki gaisheta kafin inci ubanki la'ada waje don bazan zuba miki ido kina rashin mutuncin da kika dama ba.

"Hmm Amma dama kin ƙeleta yaran yanzu ai sai a hankali ballantana ma idan suka ga sun fara tashen balaga sai kaga abubuwa kala2".

"haba Atika ba tashen balaga ba Allah yasa tashen tsuntsaye ne wallahi ni babu ruwana dukan kawo wuƙa zanyi mata, daman ga haushin ubansu ina fama dashi ayi namiji kamar mai zuciyar karya baya ajje komai sai yawon ƙasan bishiya daga wannan ta tafi ya koma wancan inuwa."

zuciya ta ce naji tana ta tafarfasa kamar zata ƙone don naƙi jinin a zagar min uba abin yana taɓa min zuciyata sosai.

Ina cikin wannan tunanin sai kuwa naji Atika tana cewa"ni wallahi Amma dama birni kika bayar da wannan yarinyar aka kaita aiki da mun huta da ganinta tsogai2 tana yawo a gari.

Saurin ɗago kaina nayi jin maganarta wai a kaini aiki?

*ummu maher ce*
*DARASI!!*

Free page 3

Rabiatu Bashir
(ummu maher)miss green.

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajarsu ta online zasu biya 2k*

03

.. . . . . ."Wallahi Amma ni babu wani gidan aiki da za'a kaini ina jin fa yadda ake bada labarin duk yaron da aka kaishi aiki yanke kanshi ƴan birni suke su cinye namanshi har da romanshi".

"Ai wallahi ƙaryarki kuwa ki zauna min a gida muna haɗa kafaɗa da ke a cikin gidannan dolen ki tafiya birni kije ki nemo mana kuɗi wallahi,kullum mu kenan cikin talauci ke ko kunya ma bakyaji kullum kina yawo da wannan koɗaɗɗan zanin".

Kuka ne ya kufcemin na fita waje zuwa gidan kaka ta wacce ta haifi mahaifiyata,ina zuwa gidan na tarar da ita a bakon murhun ƙasa zata ɗora sanwar dare,na fashe mata da kuka sosai harda majina.

"Ke ƴar nan lafiyarki kuwa kika shigo min gida kina sharce hanci kamar wata tatsitsiyar yarinya"?.

"ba Amma bace ita da Atika wai birni zasu kaini aikin wanke2 da shara,ni kuma wallahi ba zanje ba."

"yanzu Amma son kuɗin nata har ya kai ta kaiki birni aiki? ni wallahi spn kuɗin yarinyar yana bani mamaki,don kawai Allah ya jarabci mahaifinki shikkenan sai ta shiga yawon neman kuɗi kamar wata wacce ta fito a turu,"maza tashi ki share hawayenki insha Allah babu wanda zai kaiki aikatau kinji".

sai da daddare sannan na koma gida amman a wannan lokacin Nusaiba ta dawo daga tallan kayan miya,tsaye nayi ina kallon ikon jalla mai duka,na kirawo sunanta da Ƙarfi har sai da ta tsorata.

"Daga ina ki ke Nusaiba"?.

"Yaya daga talla na ke,ban siyar da wuri bane shine wani mutumi yanzu ya siye duka yace gobe idan na ɗakko in kawo mishi wani kango zai siye duka,kinga na huta da dukan Amma".

Ƙwalla ce mai zafi ta zubo daga ƙwarmin idanuna na ce"Nusaiba daga yau ba zaki sake talla a gidannan ba wallahi",ina faɗar hakan naja hannunta tana wai gawa ko zata ga Amma don dukkanmu tsoranta muke sosai.

Gidan Inna na kaita inda na baro yanzu, har ta ja ƙofarta za ta rufe sai ta ganmu ni da Nusaiba mamaki ya hanata magana amman fuskarta fal ta ke da mamakin ganinmu.

"Inna don Allah don Annabi ga Nusaiba nan ta dawo wajenki da zama,saboda zamanta wajen Amma babban hatsari ne babba",na fashe da kuka Inna tana rarrashi na.

Nan na ƙwashe duk abinda ya faru tun daga farkon tallan Nusaiba har kawo yanzu,shiru Inna tayi tana tunanin hali irin na ƴarta wato Amaturrahman.

A yanzu hankalina ya ƙwanta sosai don riƙon Nusaiba ya koma gun Inna har ta saka ta a makarantar islamiya da ta boko,sai dai fa har yanzu aƙwai sauran Rina a kaba don yanzu Amma ta ƙara ƙaimi wajen kaini aika tau daman ga haushin na kai Nusaiba gidan Inna wai tunda ni ce na kaita dole yanzu in dinga yin tallan Nusaiba na kayan miya,da yamma kuma tallan taliya da mai da yaji,babu yadda na iya dole ne inyi abinda Amma tace don ni a yanzu daɗi na ke ji da riƙon Nusaiba ya koma gun Inna.

*** *** ***

Jirgin ƙarfe 10 ya hayo daga Tunesia zuwa Abuja,kana ganin yadda ya ke tafiya kasan bashi da cikkakiyar lafiya ajikinsa,don Ammar fari ne daman ƙal mai matsaicin jiki don haka duk wanda ya sanshi zai tabbatar da tabbas ba lafiya ya ke,motoci ne sun kai biyar suka zo tararshi a Airport ɗin suka shiga daskarewa suna sarawa ogansu wato general Ammar.

Kai tsaye ɓangarensa ya nufa sakamakon da sashen Sakinat ya ke fara zuwa amman yau sashensa ya nufa,babu wanda ya faɗawa zuwanshi Nigeria hatta da aminansa basu san da maganar dawowarsa ba.
Chapter 2 · 0% Book details