← Book details Dakarun Musulunci Part 5 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 6 OF 7

PART D ✍️ ♥️

Dakarun Musulunci Part 5 Complete Hausa Novel · about 22 min read

NA ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI👮
TYPING:- UMAR FAROUQ ZANGO✍️✍️
POSTING:- NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥷🥷

SANARWA!! Bayan gaisuwa d fatan Alheri GA mutanen wannan gida, Ina so na sanar da ku cewa yakamata ku sauya akan abinda ya shaf cigaban wannan gida..
*COMMENTS
* LIKES
* SHARE
wadannan abubuwan guda uku suna da matukar muhimmanci wajen Karawa MARUBUCI karfin gwiwa. Abin mamaki shi ne, duk lokacin da aka dakatar da posting na tsawon kowa 1 week ne, sai kaga mutane sama da 200 suna maka magana akan dalilin dayasa aka dakatar. Amma Kuma idan ana typing da posting din littafin, Bai wuce mutum 10 ko 20 ba suke comments da likes, Daman haka ake nuna son Abu? Daman idan aka baka abinda kake so baka iya yin godiya sai dai kayi shiru?
A Gaskiya muddin kuna son cigaban wannan gida to yakamata bayan Karanta wannan sakon to ku ware lokacin comments da likes.
Muna fatan Allah ya taimakemu ✍️ ✍️ ✍️ 🙏

* * * * * *

Al'amarin su Huzaifat kuwa, tun da suka baro gidan gonar sarki shaaran dauke da Luhaira bisa aljani hurusul marwas sai suka ci gaba da tafiya a cikin daji ba sassauci suna kept kwazazzabai, koramai da duwatsu da bishiyoyi har izuwa tsawon saa uku basu ya da zango ba kuma basu hadu da komai ba.
Suna cikin wannan tafiya ne suka iso cikin wani daji mai yawan sarkakiya, duhuwowi da dogayen biahiyoyi masu wadansu irin siffofi na ban tsoro.
Koda Huzaifat ya ga sun shigo wannan daji sai ya bayar da da wata adduar ta neman tsari daga sharrin aljanu da dukkan mugun abu aka yi ta karantawa.
A dai dai wannan lokaci ne magriba ta riskesu din haka sai aka ya da zango a cikin wannan daji aka kafa tantuna aka shiga kokarin yin alwala.
Duk wannan tsawon lokaci da aka shafe ana tafiya Luhaira nata farka ba daga barcin da take ba don haka ma aljani hurusul marwas na sauka kasa sai Husain ya dauketa daga kansa ya kaita cikin tantinsa ya Kwantar da ita bisa shimfida yayi juyi kuma ta ci gaba fa barcinta.
Sai da su Huzaifat suka idar da sallar isha, aka fara hada hadar cin abincin dare, sannan Luhaira ta farka daga barcin.
Koda ta bude idanunta ta tsinci kanta a cikin tanti kuma a dokar daji cikin dare sai ta kwalla ihu da karfi cikin tsananin razana.
A wannan lokaci Huzaifat yana zaune tare da sauran dakaru suna tulawar karatu alkurani.
Koda ya jiyo ihunta daga cikin tantinsa sai ya mike tsaye zumbur a firgice ya ruga izuwa cikin tantin domin a zaton sa macijine ya shiga cikin tantin ya sareta ko kuma wani mugun kwaro ne ya cijeta.
Da shigar sa cikin tantin sai ya iske Luhaira tsaye jikinta na karkarwa.
Koda tayi arba da shi sai ta koma can baya jikin karshen tantin ta dubeshi a firgice tace, wanene kai, kuma Yaya akayi kuka daukoni daga gidan gonar sarki kuka kawo ni nan?
Shin baku san matsayina bane? To nice amaryar sarki shaaran ta nan gaba. Ina mai shawartarku daku gaggauta mayar dani inda kuka daukoni in ba haka na kuwa gaba dayanku kun sayi ajalinku da kudinku.
Lokacin da tazo nan a zancenta sai ta ga Huzaifat ya duneta cikin nutsuwa ba da tsoron komai ba yayi murmunshi sannan ya budi baki yace, an gaya miki cewa kowa ne yaje tsoron sarki shaaran?
Akan wane dalili zan ji tsoron mutum dan uwana wanda bai kasance ubangiji ba?
Koda jin wannan batu sai jikin Luhaira yayi sanyi ta cika da tsananin mamaki domin ita a iya tasowarta daga kuruciyarta har izuwa girmanta ba ta taba ji wani mahaluki da ya ambaci sunan sarki shaaran ba haka karara sai Huzaifat, kuma kowa yana tsoron sa yana yi masa biyayya an daukeshi tamkar wani ubangiji domin babu abin da ake bautawa a cikin wanann gidan gona sai shi.
A zatonta sarki shaaran ubangijine abin bautawa, amma sai gashi yanzu taji ana kaskantar da shi an fifita wani ubangiji sama da shi.
Cikin alamun tsananin mamaki da tsoro Luhaira ta kurawa Huzaifat idanu cikin nutsuwa tace, ya kai wannan saurayi maabocin kyawu da kwarjini, wai shin wanene kai kuma anya kuwa kai mutumin kasarmune shumbul?
Koda jin wannan tambaya sai Huzaifat ya sake bushewa da dariya yace, sunana yarima Huzaifat, daga sarki uwaisul karni na birnin darul husuf.
Luhaira ta gyada kai cikin dadin mamaki tace, ni kam ban tana jin sunanka ba bare sunan mahaifinka dana kasarku.
Ban san ko ina ba face gidan gonar da aka haifeni a ciki, kuma ban san kowa ba face hafiman da suke yi min aiki sai sunan mai girma shaaran ana gaya min cewar shi ne mijin da zan aura nan da zuwa karshen wanna shekara.
A iya sanina ban taba fita ba daga cikin harabar wannan gidan gona kuma kullum sai naji ana kirana da sunan mai tsarki Matar mai sarki sha'aran.
Koda jin wannan batu sai Huzaifat yayi hailala ya fubi Luhaira ya daka mata tsawa yace, kada ki kuskura ki kara yin irin wannan furuci domin sabone mai girman gaske, domin babu wani mahaluki da ya cancanci a ki rashi da mai tsarki face Allah da mazaonsa Annabi Muhammad S A W.
Sarki da shi ne ya halicci komai da kowa, kuma ya aiko manzonsa Annabi Muhammad a garemu domin ya sanar da mi shi da yadda zamu baiya masa.
Sarki sha'aran ba komai bane face azzalumin sarki daga irin sarakunan da suke mulkar biranen duniya.
Ya ke wannan maabocoyar kyawu ta ban alajabi, shin kin san iyayenki ko kuwa kin san yadda akayi kika taso a cikin gidan gonar azzalumi sarki sha'aran?
Koda jin wannan tambaya sai nan take idanun Luhaira suka ciko da kwallah har hawaye ya subuto mata sannan tace, ai ni ban taba sanin wacece ni ba kk asalina.
Ni dai kawai na taso na tsinci kaina a cikin kasaitaccen gida mai dauke da komai na nin dadin duniya a cikin wannan gida na gona tare da hadimai maza da mata wadanda adadinsu ya kai dubu masu yi min hidima iri iri.
Hatta wanka, cin abinci da sanya tufafi ban taba yi ba da kaina.
Ba san bakincikiba bare wani abu da ya dameni a cikin zuciyata har sai da na cika shekara goma sha takwas sannan wata rana a boye kuma a sirrance na yi hirar kusan rabin sa'a da wani hadimina wanda ya kasance saurayi kamarka maabocin kyawu mai suna shukairu.
Shukairu ne ya sanar dani cewa dukkan dan Adam yana da iyaye, uwa da uba, kuma shine ya gaya mini cewa babu wanda ya san iyayena ko asalina domin tin ina kankanuwa aka kawoni cikin wannan gida aka ci gaba da rainona har na girma a matsayin Matar da maigirma shaaran zai aura.
Koda Luhaira tazo nan a labarinta sai idanunta suka ciko da kwallah ta ci gaba da cewa, daga wannan lokaci na ci gaba da hira a boye da shukairu ba tare da kowa ya sani ba har muka shaku ainun.
Kwatsam wata rana sai tsautsayi yasa shukairu ya taba jikina a lokacin da na fadi kasa ya kawo mini dauki.
A dalilin haka ne maigirma sha'aran yasa aka tsire masa idan uwansa biyu kuma aka yanke masa hannaye.
Daga wannan rana ban sake ganin shukairu ba dai dai duk saadda na tuni irin wannan hukunci da aka yi masa sai na yi ta kuka kamar bazan daina ba.
Koda Luhaira tazo nan a zancenta sai kuwa ta fashe da kuka.
Bisa mamaki sai tagga Huzaifat idanuna sun kama zubar da hawaye.
Al'amarin da ya bata mamaki ke nan har tayi shiru ga barin nata kukan ta dubeshi tace, ya kai wannan dan sarki kai kuwa menene dalilin zubar wannan hawatue naka?
Shin tausayin ajima ne ya kamarka ko kuwa tausayi nane?
Saadda Huzaifat yaji wanann tambaya sai ya sa hannu ya share hawayensa sannan ya dubi Luhaira cikin nutsuwa yace, shin shukairu bai baki labarin cewar yana da mahaifi wanda ake kira da humzalu ba?
Cikin mamaki Luhaira tayi farat tace, tabbas ya bani labarinka mahaifinsa kuma sunan da ma fadi yanzu shi ya ambata kuma na fuskanci cewar yana son mahaifinsa fiye da komai a doron kasa.
Kai kuwa yaya akayi ka san Mahaifin shukairu alhakin ka gaya mini cewa kai ba haifaffen birnin shumbul bane?
Koda jin wanann tambaya sai Huzaifat yayi murmunshi yace ai kema na san usulunki kuma na san ko suwaye iyayenki da yadda akayi aka kawo ki gidan gonar sarki shaaran tun kina yar karama.
Ke na takaice miki labari ma babu abinda ya kawo ni birnin shumbul daga birninmu na darul husuf face domin na kubutar da rayuwar wadansu dakarunsu daga cikin kurkukun sarki sha'aran sannan na dauko ki daga gidan gonar sarki sha'aran na mayar dake mahaifarki inda iyayenki na jini suke.
Koda jin wannan batu sai Luhaira ta kwallah ihu mai tsananin kara ta dubi Huzaifat cikin alamun rashin yarda tana mai kara ja da baya tace, ta yaya zan yarda da kai na gamsu cewar duk abinda ka gaya mini yanzu gaskiyane?
Huzaifat yayi murmushi yace ai ita gaskiyane guda Dayace, kuma shi ramin karya kurarrene.
Idan har satoki nayi daga gidan gonar sarki sha'aran saboda kawai son zuciyata ko don son biyan wata bukata tawa sai asirina ya tonu kin gane hakan.
Idan kuna gaskiyane kina da haifa da usuli duk ranar da kika hadu dasu sai kin ji a jikinki cewar lallai nakine.
Koda gama fadin hakan sai Huzaifat ya juya ya fice da ga cikin tantin ya bar Luhaira a tsaye cikin tsananin damuwa, rudewa famj da wasi wasi.
Abinda ya far fado mata a rai shine, yanzu kuwa shin gaskiyane inda da iyaye, kuma ina da usuli?
Idan har hakan ne lallai sarki sha'aran satonj yayi daga wajen iyayena saboda kyawuna domin ya mallakeni kawai.
To tayaya wannan matashi saurayin yasan duk wannan lamarin , haka dai taci gaba da wannan tunani har izuwa tsawon wani lokaci daga can kuma sai ta fito, tadubi Huzaifa tace ya kai wannan saurayi shin bazaka taimakeni da abinci ba ina Nin Yunwa.
Sai Huzaifa ya mika mata naman wata dabba koda ta kai bakinta sai ta furzar ta kasa ci, sai ta dubeshi tace, bazan iya cin wannan naman ba.
Sai yace to shine da mu idan zaki ci kici idan kuma bazaki iya ba to I kwana haka. Haka ta tashi ta koma cikin tantin tana tunani har dare ya raba, barci ya saceta bata sani ba.
Bayan su Huzaifa sun gama hira sai ya shiga cikin tantin, a lokacin iska na kadawa sosai a cikin dajin, yana shiga sai ya kura mata idanu, koda yaga irin tsananin kyawun da Allah ya bata, ya kwatantata da gimbiya Lafirat da kuma Sazirat sai ya ga banbancin tamkar fari da baki ne.
Nan da nan sai yayi sauri ya dauko wani mayafi mai kauri ya lullubeta da shi dan kada shedan ya rinjayi zuciyar sa, Ya fita ya kyaleta ita kadai.
Kashe gari tunda dukukun safiya iskar da taje kadawa mai karfi da sanyi ta tasheta, sai tunanin jiya ya fado mata. Kawai sai tace tabbas idan har Hakane sarki shaaran ya ya cutar dani da ya boyeni a cikin waje daya Tsawon shekar da shekaru.
Tana cikin wannan hali ne tama dube dube a cikin sansanin ai ta hago Huzaifa a can gefe daya yana gyara kwari da bakansa.
Kai tsaye Luhaira ta tunkareshi. Da zuwamta dag da shi sai ta dubeshi tace dashi, saboda me zaku barni da Yunwa alhalin na saba cin abincin safe da wuri?
Ko kallona Huzaifa bai yi ba ce, ai mu ba bayinki bane da zamu je mu kai miki abinci mu zauna muna jiran ki tashi daga barci. Duk wanda kika ga yana cin abinci yanzu guzurinsa ne ke kuma baki da guzurin nima bani da shi.
Yanzu haka da kika ga ina gyara kwari da bakana cikin daji nan zan shiga na farautar sai ki zo muje kiyi domin ya kamata ki koya tun yanzu.
Koda jin wannan batu sai murmushi ya kunucewa Luhaira taji wani dadi a rantsa bisa jin cewar za'a tafi farauta da ita.
Ita dai ta sha jin hirar farauta a bakin hadimanta har ana bata labarin irin na manyan jarumai masu kama manyan dabbobi a daji ko suyi gumurzu dasu amma ba ta tana ganin alamarin ba da idanunta.
Luhaira ta dubi Huzaifa cikin murmushi mai tashi wanda ya kara matso tasananin kyanta tace, ina fata zaka koya mini yadda ake amfani da kwari da baka kuma zaka koya mini yadda ake yaki da takobi?
Maimakon Huzaifa ya baiwa Luhaira amsar wannan tambaya da ta yi masa sai ya kasa sakamakon bugawar da karfin gaske kuma ba komai ne ya haddasa hakan ba face take yaji kiniyar son Luhaira ta sokeshi a kirji.
Kawai sai ya kauda kai ga bari kallona ya mike tsaye ya nufi cikine daji da sauri, itama sai ta bishi da gudu don kada yayi mata nisa.
Huzaifa da Luhaira suka ci gaba da nausawa cikin daji, duk inda ya kurda sai itana ta shiga. Abinki da wadda bata saba shiga daji na sai ta dinka faduwa a duk saadda take taka cikin kwazazzbai. Da zarar tanadi sai ka ji tayi dan ihu amma sai Huzaifa ya juyo ya dubeta ya dauke kai kawai ba ya kokarin taimakonta.

Alhamdulillahi nan zan dakata sai Allah ya kaimu sati mai zuwa Insha Allahu za'a jini da ci gaban wannan Littafi.

Bayan haka ina so nayi amfani da wannan dama na sanar da yan uwa kuma abokai aminai na wannan gida cewar mahaifin daya daga cikin dan uwan mu kuma abokin wato Safyanu wanda aka sani da Abban yara shine mahaifinsa bashi da lafiya yanzu haka an kwantar dashi a nan asibitin Nassarawa muna rokon yan uwa da kusa shi a cikin adduar ku.
Muna fatan Allah ya bashi lafiya yasa tazama kaffara. Wadanda suka rigamu gidan gaskiya Allah ya jikansu da rahama, wadanda kuma suke tare da mu Allah ya bamu ikon kyautata musu kuma ya rabamu da su lafiya.
Ina yiwa kowa Fatan alkhairi. Wassalamu alaikum warahamatullahi wa barakatuhu.
[12/14, 6:53 PM] INSTRUCTOR⚓: **DAKARUN MUSULUNCI**
LITTAFI NA BIYAR 5
PART E ✍️ ♥️

NA ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI🪖
Typing :- UMAR FAROUQ ZANGO✍️
Posting:- NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥷🥷

Comments da likes da share...

Haka suka dai suka ci gaba da yawo a cikin dajin Huzaifa na neman dabbar dajin da zai harba ko tsuntsu amma bai gani ba har ya zamana cewa duk su biyun sun gaji ainun kuma gashi rana ta kara takewa yunwa taishesu.
Bisa dole suka sami wuri duka zauna suna hutawa da nufin koma da baya izuwa sansaninsu bayan sun huta din domin aci gaba da tafiya.
Suna cikin wannan hali ne kwatsam! Suka hango wata katuwar kura a gabansu ta dira akan wani katon dutse wanda tazararsu da shi ba ta wuce taku goma ba.
Kallo daya suka yiwa kurar suka gane cewar Lallai a cikin tsananin yunwa take domin sai haki take tana zazzago harshenta waje.
Koda kurar ta dago kai tayi arba da su, su ma sukayi arba da ita sai Luhaira ta kurma uban ihu, saboda tsananin tsoro bata san saadda takama bayan huta ba ta rukunkumeshi, shi kuwa sai ya mike tsaye a hankali yana mai kurawa kurar idanu, itama kurar ta kura masa idanu tana gurnani shi kuma yana ta karanta wata addua a bakinsa don kada kofinta ya kamashi.
Huzaifa yana so ya daki idon kurar ya zare takobinsa amma sai ya ga itama kurar tana yunkurin ta shammaceshi tada ka tsalle ta diro kansu.
Nan dai aka ci gaba da kallan kallo tsakanin kurar da Huzaifa har tsawon yan daki. Daga can sai kurar ta dako tsalle a sama cikin shammace domin ta turmushesu a tare shi da Luhaira ta tafi can gefe daya kurar ta fado kansa shi kadai suka kacame da kokowa.
Su fada nan, su fada can, suka rinka dudufniya a kasa, kurar na kokarin kafa masa hakoranta a jikinsa shi kuma sai ya rinka gabza mata naushi a fuskar ta yana kawar da kanta.
A lokacin ne kurar ta rinka yakusar jikinsa da faratan hannayenta da kafafunta.
Nan fa duk su biyun shi da kurar suka fara gane kurensu domin ya hada nata jini da majiya a bakinta, idanunta da hancinta, ita kuna ta kakkarce masa sassan jikinsa jini na ta zuba.
Duk wannan abu dake faruwa Luhaira na zaune a kas gefe daya tana kallonsu kuma tana ta faman rusa ihu da kuka amma ta kasa tashi ta gudu saboda tsananin tsoro da firgitar da tayi.
Sai da aka shafe sama da saa daya ana wannan bakin gumurzu tsakanin Huzaifa da wannan kura, ya zaman cewa duk su biyun sun galabaita ainun amma saboda naci gami da Taurin zuciya kowannensu na kokarin hallaka dayan.
Koda kurar taga tayi iya kokarinta akan ta turmushe Huzaifa ta cinyeshi domin ta kawar da muguwar yunwar data addabeta sai ta sakeshi ta juyo izuwa kan Luhaira ta dako wawan tsalle a sama da nufin ta dira amanta ta turmusheta gashi a wannan lokaci Huzaifa ya galabaita ainun ya kasa mikewa da sauri ya ceci rayuwar Kuna Luhaira.
Koda Luhaira ta ga kurar nan ta dako tsalle zata dira akanta sai ta sulale kasa sumammiya saboda tsananin tsoro.
Ai kuwa sai Huzaifa gani yayi wata irin katuwar kibiya ta taho da gudu ta soki kirjin kurar ta bullo ta gadon bayanta.
Take kurar ta fado kasa Tim! Matacciya ko motsawa batayi ba.
Koda Huzaifa ya daga kansa sama ya dubi saitin da kibiyar tafito dai ya kame saboda tsanin mamaki wanda ya gani rine da kwari ya tunkaro inda yake.
Ba wani ya gani ba face gimbiya lafirat yar sarki shaaran ta kura masa idanu tana murmushi.
Cikin tsananin Farin ciki Huzaifa ya mike tsaye da sauri ya tareta ya budi baki da nufin yayi mata magana.
Koda taga yawan raunikan da ke jikinsa sai ta dimauce, bata san saadda ta kama kafadunsa ba ta zaunar dashi a kasa ta sa hannunta ta yage rigar jikinsa wacce dama tuni ta gama yayyagewa ta yi kaca kaca da jini.
Cikin hanzari lafirat ta dauko battar ruwan Shanta ta wanke duk jinin dake jikin Huzaifa sannan ta dauko garin magani ta fara shafa masa a jikin raunikan nasa.
A dai dai wannan lokaci ne Luhaira ta farfado daga sumun da tayi.
Koda ta bude idanunta taga Huzaifa zaune tare da lafrirat tana taba jikinsa tana shafa masa magani sai kawai taji kishi ya turnuketa, a sannane taji wani irin bau ya shigeta wanda ba ta san ko menene ba, kawai sai ta kurawa Huzaifa da lafirat idanu ba tare da su lura da cewar ta farfadoba.
A wannan lokaci ne Huzaifa yayi gyaran murya yace, yaje jarumar jarumai, yanzu ina kika nufa ne, kuma me kika sani dangane da abin da ya faru a filin yaki?
Koda jin wannan tambaya sai lafirat tayi murmushi tace, ai ni bani da wajen zuwa face farautar ka domin a halin yanzu bani da kowa cikin duniya sai kaitunda na rabi da ubana da yar uwata kuma na tsanesu kamar yadda na tasani mutuwa ta.
N hakura da kasaita ta haihuwa wato birnin shumbul, bani da sauran buri a duniya face na koma birninku na Darul Husuf inda zan karasa sauran rayuwata na bude sabon shafin rayuwa na yi aure na sami tawa zuriyar.
Bayan lafirat ta gama wannan jawabi sai ta kwashe labarin duk abinda ya faru a filin yaji ta zaiyane masa sannan tace, dama saboda na gamu da kai shi yasa na biyo wannan hanyar ta birninmu amma ko kadan bani da shaawar komawa cikin birnin shumbul har abada.
Lokacin da lafirat tazo nan a jawabin ta sai Huzaifa ya cika da tsananin Farin ciki bisa jin nasarar da suka samu a filin yaki.
Nan take shima ya ba ta labarin irin bakin gumurzu da sukayi a kurkuku kafin su fito da Dakarun musulunci daga kurkuku da kuma yadda aljani hurusul Marwas ya sha bakar wahala wajen kokarin dauko Luhaira a cikin gidan gonar sarki inda ya fafata kazamin yaki da wadansu mugayen zakwakuran aljanu guda dubu daya da dari daya da kyar ya samu ya hallakasu bayan ya kusan rasa tasa rayuwar.
Koda gimbiya lafirat taji wannan labarin sai ta kamu da tsananin Farin ciki bisa jin yadda aka tarwatsa mugun nufin mahaifinta akan dakarun musulunci da ya kama yatsare da kuma kyakkyawa Luhaira wacce yaci burin aurenta bayan ya kawar da birnin Darul Husuf.
Lafirat na cikin wannan Farin ciki sai kuma fuskarta ta juye izuwa tasananin damuwa ta sunkuyar da kai kas tayi shiru batace komai ba.
Alamarin da ya dugunzuma hankalin Huzaifa kenan ta dubeta cikin alamun tsananin damuwa yace, yake lafirat menene ya faru na ga kuma fuskarki ta sauya yanzu take cikin yanayin damuwa?
Koda taji wannan tambaya sai lafirat tayi ajiyar zuciya tace, wani labari mara dadi na samu a bakin wadan su fatake wadanda na hadu dasu a hanya a lokacin da na biyo hanyar zuwa birnin shumbul.
Naji wadannan fatale suna cewa sarki shaaran ya samu nasarar shiga har cikin birninku na Darul Husuf yaci shi da yaki.
Koda jin wadannan bayi sai Huzaifa ya mike tsaye zumbur a dimauce yace, kai karya ne abin ba zai taba yi yuwa ba ke nan domin na sam.cewa katangar birninmu tana da wani asiri na musamman tun zamanin iyaye da kakanninmu wanda babu wani kafiri sa ya isa ya shiga cikin birnin.
Lafirat ta gyada kai tace, ai bisa labarin da naji daga bakin fataken sun ce mutanen ku ne suka cire tsafin da ke jikin katangar birnin taku da hannunsa amma mahaifina ne ya yaudaresu yace yaci birnin shumbul da yaki kuma saboda murna ba zai shigo cikin birnin ba har sai ancike wadannan layu wadanda aka binne a karakshin katangar.
Ai kuwa ana cire layin ne shi da dakarunsa suka afka cikin birnin suka hau mutane da sara da suka.
Ance ankashe sama da mutane dubu dari uku da hamsin kuma gaba daya malaman garin da manyan fadawan sarki an kullesu a kurkuku.
Koda lafirat tazonan a labarinta sai Huzaifa ya murna uban ihu Kuma ya fashe da kukan bakin ciki yace, Lallai mahaifinki ya cutar da duk wannan nasara da nasamu ta karbo dakarunmu da dauko Luhaira sun zama a banza.
Ya zama wajibi yanzu mu garzaya mu tafi neman su sarki a duk inda suke domin mu san hanyar da zamu bi mu karbo birninmu.
Koda bama fadin hakan Sai Luhaira ta mike tsaye ta karaso gabansu ta dubi irin kibiyoyin da ke cikin kuttun da lafirat ta rataya a bayanta sai taga iri daya ne da kibiyar da ta soke wannan kurar da ta yi yunkurin kasheta, take ta gane cewar lafirat ce ta ceci rayuwata saboda haka sai dubeta tayi mata godiya sannan ta kama hannun Huzaifa akaron farko a rayuwarta ta jashi izuwa gefe ta dubeshi tace, ya kai wannan babban jarumi, kayi sani cewa ni yanzu na aminta da kai kuma nayi imani da duk abubuwan da kafada mini, amma taya ya kake tsammanin cewar zan ci gaba da da aminta da kai a cikin wannan hali kana tare da yar abokin makiyinmu wanda ya jefa rayuia cikin duhu ya rabani da komai da kowa nawa?
Menene ne tabbacinka cewar itama ba zata yaudareka ba, ta cutar da kai kamar yadda mahaifinta ya yaudari mutanen birninku ya cutar da su.
Ka tuna fa cewa karewa bata tayi gudu ba danta yayi rarrafe.
Lokacin da Luhaira tazo nan a zancenta sai hankalin Huzaifa ya dugunzuma ta rasa irin matakin da ya kamata ya dauka domin ya kasa tantancewa a tsakanin lafirat da Luhaira wacce ya kamata ya rike hannu biyu kuna yayi amfani da maganganunta?
Kawai sai ya dubesu duk su biyun yace, ku zo mu koma izuwa masaukinku domin mu yi shirin tafiya izuwa birnin Darul Husuf.
Ba tare da gardama kuwa Luhaira da Lafirat suka bi Huzaifa a baya da sauri suka nufi sansanin nasu inda suka ya da zango.
Da zuwansu sai Huzaifa ya bayar da umarni a kwashe kaya domin a ci gaba da tafiya.
Koda Humzalu da aljani hurusul Marwas suka ga Huzaifa ya dawo da gimbiya lafirat sai suma hankalinsu ya dugunzuma, haka ma sauran dakarun musulunci.
Yayin da Huzaifa ya fahimci halin da kowa ke ciki sai ya dubesu gaba daya yayi murmushi sannan yace, Yaku yan uwana kuyi sani cewa yanzu lafirat ba abar kyama bace a cikinmu domin kuwa yar uwarmu ce addinin musulunci.
Ta hakura da iyayenta, da danginta da kasarsu kuma ta zabi takoma cikinmu inda zata karasa sauran rayuwarta.
Ina mai tabbatar muku da cewa lafirat bayar da gagarumar gudunmawa a yakin da muka fafata da mutanensu kuma yanzu ma ta ceci rayuwarmu ni da Luhaira a cikin dajin daga sharrin wata muguwar kura tafin da muke yin farauta.
Bugu da jari kuma tazo ta sanar da ni halin da birninmu yake ciki na Darul Husuf wanda shine dalilin da yasa yanzu na ce mu gagauta shirin tafiya.
Nan dai Huzaifa ya zaiyane musu duk labarin da Lafirat ta zo musu da shi.
Koda jamaa suka ji wannan batu sai hankalin kowa ya dugunzuma, wasu suka fara kuka da bakin ciki, wasu kuma suka kama yiwa yan uwansu adduar Allah ya jikansu domin sunji a jikin su cewar mutuwa ta dauke su.
Haka dai aka shirya aka kwashe kaya gaba daya aka ci gaba da tafiya cikin sanyin jiki, rashin kuzari da alhini.
Ana fara tafiyar ne Luhaira ta kama yin hamma sakamakon yunwar da take ji. Shi kuwa Huzaifa saboda yana cikin tsananin bakin ciki da har zuciyar sa ji yake tana tafarfasa kamar zata kone ya ma daina jin yunwar, yayin da lafirat da lura da halin da Luhaira take ciki sai ta matso da dokinta kusa da na Luhaira sannan ta bude jakarta tafiddo gasasshen nama n wani tsunsu ta miko mata.
Ciki matukar murna gami da godiya ta karba. Har ta yagi naman zata kai bakinta sai ta tuna cewar Huzaifa ma bai ci komai ba kawai sai ta raba naman duka kaso biyu tamikawa Huzaifa.
Huzaifa ya kau da kai yace, bazan iya cin komai ba har sai na sadu sarki naga lafiyarsa.
Koda jin haka sai itama Luhaira tafama cin naman ta daureshi taje fashi cikin jakarta da ke bisa kan dokinta. Ashe lafirat ta lura da ita, nan take itama taji kishi ya turnuketa tace, a cikin zuciyar ta.
Yanzu kenan itama wannan yarinyar tana kaunar yarima kamar yadda nake sonsa har ma ta kai cewa ba zata iya cin abinci ba saboda shima bai ci ba?
Ni kuwa zan zuba ido na ga iyakar adalcin Huzaifa.
Ni dai nasan cewa dani ya fara yin soyayya to yanzu zai rabu da ni ne ya kama Luhaira ko kuwa ni zai kama ya rabi da ita?
Tana cikin wannan Hakane taga aljani hurusul Marwas ya saki fuka fukinsa ya sauko kas kasa dag da Huzaifa ya dubshi yace ya shugabana kayi sani cewa idan kai zaka iya jure yunwa ta Tsawon lokaci to wadannan yan matan biyu bazasu iya ba. Saboda na lura duka su biyun suna cikin yunwa amma kuma saboda kaki cin komai suma sunki yadda suci komai.
Koda jin haka sai Huzaifa ya dube su duka su biyun ya danyi jim daga can kuma sai ya bada umarnin a tsaya aci abincin kowa da kowa.

Alhamdulillahi anan zan dakata sai kuma Allah yakaimu sati maizuwa inda zakujini da karshen wannan Littafi wanda Insha Allahu nake sa ran cewa a rana itayau zamu kawo karahensa gaba daya.
A madadin mutanen wannan gida mai albarka muna mara yiwa Safyanu Abban yara gaisuwar mahaifinsa bisa rashin lafiyarsa duk da cewar mun hadu da shi a ranar laraba ya shigo unguwar mu wajen yayarsa mun hadu da shi kuma ya fada min cewa ai an sallamesu a asbitin sun koma gida.
Don haka a madadin sa ina yiwa mutanen wannan gida godiya bisa addu'o'i da kuka dinga masa muna godiya ubangiji Allah ya bar zumunci kuma Allah ya kara hada kawunan mu.
Allah kuma ya kara masa lafiya da sauran mutanen da ke kwance a gida ko asibiti.
Ni UMAR FAROUQ ZANGO nake muku Fatan alkhairi sai Allah ya hadamu a sati mai zuwa inda zamu karkare wannan Littafi kuma Insha Allahu kawai tambayoyin da zasu biyo baya, idan mun kammala shi wannan Littafi ina muku Fatan alkhairi.
[12/14, 6:53 PM] INSTRUCTOR⚓: **DAKARUN MUSULUNCI**
LITTAFI NA BIYAR 5
Chapter 6 · 0% Book details