← Book details Dakarun Musulunci Part 5 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 2 OF 7

PART C ✍️ ♥️

Dakarun Musulunci Part 5 Complete Hausa Novel · about 14 min read

NA ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI
TYPING :-UMAR FAROUQ ZANGO ✍️
POSTING:- Najibullahi Muhammad

Cikin alamun tsananin mamaki ukashat ya dubi sarki yace, ya kai Abbana ina dalilin tsayuwarmu anan?
Ai kamata yayi mu karasa cikin gari da sauri ko don't mu sami jam'in sallar magriba a masallaci.
Saadda sarki uwaisul karni yaji wanann tambaya sai yayi murmunshi sannan ya dubi ukashat yace, hakika kai yaro ne har yanzu ba ka san tuggun yaki ba da sharrin abokan gaba.
Ina son ka sani cewa duk ranar da ka baro gida to idan ka dawo kada ka shiga gari kai tsaye muddin ka san cewa kana da abokin gaba.
Anan zamuyi sallar magriba sannan mu tura kwararren dan leken asiri yaje ya gano mana irin yanayin da birnin mu keciki.
Babu mamaki a bayan ba ma nan anzo an cimu da yaki bamu sani ba, kun ga ke nan za'a iya dana mana tarko muna shiga cikin garin a kamamu ko a hallaka mu.
Lokacin da sarki uwaisul karni yazo nan a jawabinsa sai jikin kowa yayi sanyi aka yi tsit! Har izuwa tsawon yan dakiku sannan ukashat ya sake dubansa yace, ya kai abbana, to wai shin yanzu ta yaya dan leken asirin da zaka tura zai iya gano wani abu idan har an shirya mana wank tuggu?
Koda jin wannan batu sai sarki uwaisul karni ya sake yin murmushi a karo na biyu yace, ya kai dana, ka kyale mai abu da abinsa, sai yau da gobe ta fi karfin wasa.
Akwai abubuwa da dama wadanda zan lura da su, idan har na ga sauyin su na san cewa an kulle kofa da barawo a cikin birnina.
Idan dan leken asirin da zan tura yaje ya dawo akwai tambayoyin da zan yi masa na musamman.
Daga irin amsoshin da zai bani ne zan gane komai.
Yanzu sai mu yi alwala don gabatar da sallah.
Nan take kuwa kowa ya sauka daga kan dokinsa aka gangara bakin wata korama aka yi alwala.
Da lokacin sallah yayi sai sarki uwaisul karni yayi limanci aka gabatar da farilla.
Bayan an idar da sallar kuma anyi adduoi na neman tsari daga dukkan mugun abu da abokan gaba an shafa sai sarki uwaisul karni ya tura wani hadiminsa mai suna SHABBARU.
Ya dubeshi yace, maza ka tafi izuwa dafda kofar birninmu a cikin sanda da labiya kuma ka tabbatar da cewa ba'a ganka ba ko a kamaka sai ka sami wuri ka buya a cikin duhuwa ka zuba ido izuwa kofar birnin har izuwa Tsawon kamar rabin saa, sannan ka dawo nan wajen mu.
Lallai ka lura da duk abubuwan da ke gudana a kofar birnin kada ka mance da komai.
Koda jin wannan batu sai shabbaru ya risina yace, an gama.
Nan take shabbaru ya mike tsaye ya fice daga cikin tantin sarki uwaisul karni ya koma cikin nasa tantin yayi sauyin tufafi ya sa wadamsj korayen tufafi wadanda suka saje da yanayin ciyawa cikin dajin.
Ba tare da ya dauki wani makami ba kawai sai ya fice daga cikin tantin ya falfala da gudu izuwa cikin duhun daji.
Duk da cewar gari ya gauraye da matukar duhu ko tafi hannu mutum baya iya gani amma ko kadan shabbaru bai damu ba sai dada kutsawa yake yi ta cikin koramai, kwazazzabai da duwarwatsu tamkar da rana yake tafiyar ba da daddare ba.
Idan yayi dan gudu na Tsawon yan dakiku a cikin duhuwar ciyawa sai ya tsaya cak! Yayi lambo yana mai kasa kunnuwansa ko zai ji alamar ana biye da shi ko kuma zai ji motsin labewar wasu.
A haka dai yaci gaba da tafiya har ya iso dag da kofar birnin Darul Husuf bai gamu da kowa ba kuma bai ji motsin komai ba.
Da isowarsa dag da birnin sai ya kwanta a cikin duhun ciyawa tamkar lambon maciji ya zubo ido izuwa ga kofar birnin.
Shabbaru bai kawar da idanunsa ba daga kan kofar birnin sai da rabin saa ta cika, sannan ya juyo da baya da gudu ya dawo wajen da su sarki uwaisul karni suka ya da zango.
Da isowarsa yayi inkiya dakaru suka bashi hanya ya shiga cikin sansanin kuma ya wuce kai tsaye izuwa tantin sarki uwaisul karni.
Sarki uwaisul karni na zaune bisa kan sallama rike da casbaha yana lazimi sai yaji muryar shabbaru yana mai yi masa sallama, sarki uwaisul karni ya amsa masa sallamar gami da bashi izinin shigowa.
Shabbaru ya shigo cikin tantin ya durkusa a gabansa bisa gwiwowinsa yana mai sunkui da kansa kas cikin biyayya.
Sai da sarki uwaisul karni ya karasa lazimin da yake yi sannan ya dago kai ya dubi shabbaru yace, shin lokacin da ka je kayi lambo kana kallon kofar birninmu ka jiyo sautin zikirin da aka saba yi a masallaci kullum a irin wannan rana ta yau,v wato jumaa?
Shabbaru ya gyada kai yace, ya shugabana ai nafi rabin saa a kwance cikin ciyawa kuma dag da kofar birnin amma kunnuwana basu ji sautin wani zikiri ba.
Sarki uwaisul karni yayi murmushi gami da ajiyar zuciya yace, shin ka hango hayakin wutar nan da aka saba kunnawa a bayan gidana wacce malamanmu ke jin dumi da ita a duk saadda suka zauna taron karawa juna ilimi bayan sallar magriba?
Shabbaru ya gyada kai yace, ko kadan ban hango wannan hayaki ba.
Koda jin wannan batu sai idanun sarki uwaisul karni suka zazzaro, ya sake duban shabbaru cikin alamun tsananin tashin hankali ya ce, shin ka ga an fito da abinci a cikin kwanon gidan sarauta an kawowa masu gadin kofar gari?
Shabbaru yace, a'a har na baro wajen ban ga ma an bude kofar gari ba.
Koda jin wannan amsa sai nan take idanun sarki uwaisul karni suka ciko da kwalla har hawaye ya zubo masa yayi Salati gami da hailala yace, shikenan abinda nake gudu ya afku.
Tabbas an zub da jinin muminai a cikin birnina kuma an karbe garin daga hannun jamaarmu.
Koda gama fadin hakan sai sarki uwaisul karni ya mike tsaye zumbur a dimauce ya fice daga cikin tantinsa yana mai kwalawa ukashat kira tare da sauran manyan mayakansa.
Nan take kuwa suka rugo da dugu izuwa bakin tantin sarki uwaisul karni, sukayi masa kawanya.
Koda kowa yaga hawaye na zuba a idanun sarki uwaisul karni sai hankali ya tashi.
Ukashat ya matso dag da shi yace, ya abbana shin abin da kake zargine ya tabba?
Sarki uwaisul karni ya girgiza kai yana mai nuna alamun cewa Hakane.
Ai kuwa sai aka barke da hailala, kowa ya kamu da tsananin bakinciki domin da yawa sun san cewa zasu iya komawa su tarar da cewa an kashe makusantansu ko aminansu.
Tsawo yan dakiku ana ta alhini an rasa wanda zaice kala.
Kawai sai ukashat ya zare takobinsa cikin tsananin fishi ya dubi sarki uwaisul karni yace, ya kai abbana ka bani izini na jagoranci dakarunmu da ke nan muje mu yaki abokan gabarmu da ke cikin birninmu domin mu karbi birninmu da karfin tsiya!!!
Koda jin wannan furuci na ukashat, sai hawaye ya zubowa sarki uwaisul karni ya dubeshi cikin alamun tausayawa yace, ai kuna zuwa za ku fada cikin taron abokan gaba.
Babban abin bakin cikin ma shine da dan gari akanci gari.
Tabbas koda mun bi wata hanyar daban akwai mutumin daya JAL wanda zai iya wargatsa mana dukkan shirin mu ya tina mana asiri tunda yafi kowa sanin sirrin da dukkan dakaruna na yaki.
Kodajin haka sai ukashat ya dubi sarki uwaisul karni cikin alamun tsananin damuwa yace, ya kai Abbana wanene wannan mutum wanda yafi kowa sanin sirrin kuma ya zamana cewa shine zai tona mana asirinmu da dukkan shirin mu?
Na rantse da girman Allah duk saadda nayi arba da shi sai na cisge kansa da kaifin takobina domin bai cika musulmi na kwarai ba.
Koda ukashat ya zo nan a jawabinsa sai hawaye ya sake zubowa sarki uwaisul karni yayiwa ukashat wani irin kallo mai nuna tsantsar tausayawa sannan ya juya da sauri ya koma cikin tantinsa.
Al'amarin da yai matukar baiwa kowa mamaki kr nan domin ba a san dalilin da ya sa sarki uwaisul karni ya saka gayawa ukashat ko wane ne wannan munafuki mutum ba kuma gashi bai tsaya an gama tantance matakin da ya kamata dauka ba a yanzu akan wannan gagarumar matsala.
Cikin sanyin jiki yarima ukashat ya bi sarki uwaisul karni cikin tantinsa.
Da shigar sa ciki sai ya iske sarki uwaisul karni zaune bisa wata kujera mai tudu ya hada kai da gwiwa yana kukan bakin ciki irin na manya har ma ana jin shesshekar kukan nasa a fili.
Al'amarin da ya firgita ukashat kenan, kuma ya dugunzuma hankalinsa ainun fiye da ko yaushe, saboda bai taba ganin ranar da sarki uwaisul karni yayi kuka ba haja sai yanzu.
Cikin sauri ukashat ya karasa gaban sarki uwaisul karni ya durkusa bisa gwowinsa sannan ya kama hannunsa da hannayensa biyu suka kurawa juna idanu a lokacin da kowanne nai ke zubar da hawaye yace, ya kai abbana wai shin wane ne wannan maci amanr naka wanda har ka kasa bayyana min shi?
Ka sani cewa bani da wani makiyi a doron kasa sama da wanda ya sa bawayenka mai albarka ya zuba.
Ka gaggauta sanar da ni mi wane ne domin na tafi izuwa cikin birnin darul husuf yanzu na yanko kansa na ajiyeshi a gabanka.
Lokacin da ukashat yazo nan a zancensa sai sarki uwaisul karni ya rungumeshi kuma ya fashe da natsanaicin kuka na bakin ciki kuma ya kasa cewa komai.
Al'amarin da ya kara dagawa yarima ukashat hankali kenan, ajima ya fashe da matsanaicin kukan, sai daga can ya janye jikinsa daga cikin sarki uwaisul karni sannan ya dubeshi yace, ya kai dana hakika ba wani bane wanda ya ci amanar mu ya hada kai da makiyanmu ba face mahaifiyar ka.
Cikin tsananin mamaki da razana ukashat ya dago kai ya dubi sarki uwaisul karni. A lokacin wani zazzafan hawaye ya kara zubowa sarki uwaisul karni, sannan yace tabbas mahaifiyar ka taci amanata, kuma wannan ba komai bane face kin bin umarnin mahaifiyata, tabbas yau na kara tabbatar da cewa duk wanda ya ketare maganar manya to tabbas ba zaiga da kyauba.
Sarki uwaisul karni ya ci gaba da cewa a rayuwata idan akwai wani kuskure da nayi wanda nake nadamarsa to tabbas zai zama shine shine sabawa umarnin mahaifiyata akan auren mahaifiyar ka.
Ka saurara da kyau kaji labarin da zan baka watakila kaima ka samu wani darasi daga tarihin rayuwata kuma ya aa daga aikata irin kuskuren da na aikata.

* * * * * *

A Lokacin da nake kamarka na kasance dan guda daya da Allah ya bawa mahaifina, na taso da ilimin addini da hikima gami da gagrumar jarumta, na kasance a wancan lokacin mai dakawa maza gumba a hannu, amma kuma sai ya zamana cewa yan mata basa gabana, Ma'ana bana soyayya kuma bani da wani shaawa akan soyayya da kuma aure, saboda ni burina kawai shine na kasance ko da yaushe cikin jihadi da daukaka Kalmar Allah da kuma tallata addinina zuwa sauran kasashen dake makwabtaka.
Ina cikin wannan hali ne iyayena suka fara min maganar aure, sai nace ai da sauran lokaci. Haka dai tun suna lallabani har ta kai cewa sun fara fusata, ganin hakan ne yasa na Fara tunanin macen da ya kamata ace na aura.
Wata rana naje cikin gari ina rangadi sai kwatsam na ci karo da wata kyakkyawar budurwa, koda muka hada idanu da ita take naji gabana ya fadi. Haka naci gaba da tafiya ian satar kallonta, daga can sai na lura ashe itama satar kallona take, koda na fuskanci hakan sai tsayar da dokina har suka zo zasu wuce ta gabana.
Sai na tsayar da su na musu sallama tare da gabatar da kaina a gareta, itama ta sai ta gabatar min da kanta lokacin da naji daga inda take sai nayi mamaki, ba daga ko ina take ba face ta fitone daga gidan likita abu sharhaz wato likitan gidanmu.
Nayi mamaki matuka saboda ni a sanina likata abu sharhaz bashi da da ko ya.
Lokacin da na gabatar mata da abinda ke cikin raina nayi tunanin ko zata ki amma bisa mamaki sai ta karbi tayin soyayya ta, ta karbeni hannu bibbiyu.
Lokacin da muka fara soyayya mun kasance ko da yaushe cikin shauki da son ganin juna, har ta kai cewa bama iya sa'a hudu ba tare da mun nemi juna ba.
Lokacin da shakuwarmu ta kara nisa sai na gabatar da abinda ke raina ga mahaifina, sai yayi farin ciki, ita kuma mahaifiyata sai abin ya faskara daga gareta.
Tace ita bata amince da wannan hadin ba saboda ita yarinyar bani take so ba mulkin da nake ciki take so.
A lokacin soyayya ta rufe min idanu bana ganin laifin muzaira ko kadan. Haka mahaifiyata taci gaba da nusar da nai akan auren muzaira amma ina na rigada nayi nisa a cikin gokin sonta.
Bayan anyi auren mu sai Allah ya dauki ran mahaifiyata, lokacin da takwanta rashin lafiya sai ta min wasiyya da na kara aure domin kuwa Matar da nake tare da ita ba sona take mulki na take so, idan har ka samu wata mace mai tsoron Allah mai cikakken imani to tabbas zata iya kareka daga sharrin wannan Matar taka.
Lokacin da na jewa matata da batun Karin aure ta nuna kishi da damuwa sosai, amma kuma daga baya ina mata nasiha sai ta daina, nayi tunanin hakan so ne daga gareta ashe ita akwai manufarta, wadda gashi yanzu ta nuna ta a fili.
Tabbas mahaisfiyarka babu irin son da ban nuna mata ba amma sai gashi yau tana neman rayuwata da mulkina.
Wannan shine babban kuskuren da na aikata a rayuwata. Koda sarki uwaisul karni ya zonan a zancensa, sai hawaye ya zubowa ukashat, yace yanzu duk akan neman duniya da kuma mulki ta hada duk wannan fitinar. Tabbas sharrin mace yafi ga haka, ya kai Abbana ban taba ganin mutum mai hankali, ilimi da hangen nesa ba kamar ka a wannan nahiya tamu gaba daya.
Lallai zan kasance mai bin dukkan umarninka ba zan saba maka kuma zan ci gaba yiwa mahaifiyata addua akan Allah ya shiryeta, ya sa ta gane gaskiya.
Ina so ka sani cewa a halin yanzu babu abinda na ke so sama da na sake saduwa da dan uwana Huzaifat domin na nemi gafararsa kamar yadda na nemi taka bisa abubuwan da na aikata.
Haka kuma begensa da tunaninsa sun addabi zuciyata fiye da yadda nake yin na mahaifiyata saboda na gane cewa bani da wani dan uwa kuma masoyi sama da shi a wanann doron kasa, don't haka kusa bana son naga ya sauka a jikinsa bare ya taba lafiyar sa.
Lalli ina bukatar na je duk inda yake a cikin gaggawa domin na ga halin da yake ciki kuna na kai masa dauki.
Ya kai Abbana ka yi min izini na kwashi dakaru mu tafi izuwa hanyar birnin shumbul domin kaiwa Huzaifat dauki.
Lokacin da ukashat yazo nan a zancensa sai hankalin sarki uwaisul karni ya kara dugunzuma ya dubeshi cikin firgici yace, ta yaya kake tsamamnjn zan iya barnka ka tafi inda dan uwanka ya tafi bayan bani da tabbacin cewar shima yana raye?
So kake na yi biyu babu kenan yazamana cewa babu kai babu shi?
Ka tuna fa cewar haryanzu hankalina ya rabu gida biyu.
Ina tunanin jakin da jamaata ke ciki a cikin birninmu kuma ina tunanin halin da dan uwanka ke ciki a can birnin shumbul.
Idan kaima ka tafi ka barni wane irin hali zan shiga kenan?
Saadda ukashat yaji wannan batu sai yayi murmunshi ga sarki uwaisul karni yace, Haba ya kai Abbana, shin ka manta ne cewar tun muna yara ka koya mana rashin tsoro akan tukarar makiya Allah?
Shun ka manta ne cewar ka koya mana mu yi imani sa cewar babu Mao kashe wa da rayawa sai Allah, kuma duk abinda muka ga ya samemu kaddarace daga Allah?
Saboda me yanzu kake tsoron 'ya'yanka su mutu alhalin ka tabbatar mana da cewar matsoraci bashi zama Gwanin har abada?
Ka tuna da irin labaran da ka bamu irin na jarumatakar da kayi a zamaninka da irin tsananin wahalar da kuka shafa kau da iyayenka da kakanninka kafin ku sami nasarar tsare addinin Allah a cikin birnin darul husuf daga sharrin kafiri har kuka zami gagarabadau a filin fama, sunayenku suka daukaka a nahiyar ku ma zami dodanni ga kafiri masu son rushe addinin karya.
Shin ba ka so ne muma 'yayanka mu sami irin wannann daukaka ko kuwa ba ka son mu dace da samun babban rabo na kadan yada addinin Allah a doron kasa?
Koda ukashat yazo nan a zancensa sai jikin sarki uwaisul karni yayi sanyi ya sake rungumeshi a kirjin sa yana mai cewa, na yarje maka ka tafi izuwa wannan babban aiki ya kai dana kuma zan kasance mai yi maka adduar samin nasara har Allah ya dawo mun da kai lafiya.
Koda jin haka sai farin ciki ya kullube ukashat ya kama yiwa sarki godiya. Ba tare da bata lokaci ba ukashat yayiwa sarki sallama sannan ya kwashi dakarun yaki mutum dubu dari biyu da hamsin ya tafi da su.
A cikin su har da habibullah, hirama da uwar mayu, manya dakarun yaki na birnin darul husuf.
*Wannan shine abinda ya faru ga su sarki uwaisul karni bayan sun baro sansanin yaki sun dawo gida sun tarar da cewa tuni abokan gaba sun kama birnin nasu na darul husuf*

Alhamdulillahi anan zan tsaya sai Allah ya kaimu sati mai zuwa idan da rai da nisan kwana zamu sake haduwa a cikin wannan littafi na DAKARUN MUSULUNCI dan jin yadda zata kaya...
[12/14, 6:53 PM] INSTRUCTOR⚓: **DAKARUN MUSULUNCI**
LITTAFI NA BIYAR 5
Chapter 2 · 0% Book details