← Book details Dakarun Musulunci Part 5 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 4 OF 7

PART LAST CHAPTER ✍️✍️🙏

Dakarun Musulunci Part 5 Complete Hausa Novel · about 50 min read

NA ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI👮👮
TYPING:-UMAR FAROUQ ZANGO✍️✍️
POSTING:- Najibullahi Muhammad 🥷🥷

KARSHEN LITTAFIN 👇👇👇

Tsayawarsu ke wuya sai aka zubawa Huzaifa da lafirat da Luhaira abinci a kwano guda koda fara cin abincin sai ke da wuya sai Huzaifa yayi shiru ya kasa ci gaba da cin abincin, yayin da ya fada cikin kogin tunani, koda lafirat ta dago kai ta lura da halin da ya shiga sai ta dan girgiza kafadarsa, koda ta girgiza kafadar tasa sai yayi ajiyar zuciya, cikin damuwa ta dubeshi tace, ya kai gwarzona shin wanne irin tunani kake haka wanda har ya hanaka ci gaba da cin abincin.
Koda jin wannan tambaya sai ya sake yin ajiyar zuciya a karo na biyu sannan yace, ki sani yake lafirat cewa ni yanzu gaba daya babu abinda ke min dadi, babu abinda nake tunani face halin da jamaar birninmu suke ciki sannan kuma ga tunanin halin da sarki da kuma dan uwana ukashat yake ciki, tabbas mahaifinki ya cutar damu matuka sosai, yayi mana babbar illa mai wuyar gyarawa.
Koda jin haka sai tayi ajiyar zuciya tace, tabbas abinda ka fada hakane, amma kada ka manta da cewa a kullum ubangiji yana bayan gaskiya, kuma komai daren dadewa gaskiya itace take yin nasara kuma mai gaskiya shine yake yin nasara matukar yayi hakuri kuma ya jure duk wata musiba da wata jarrabawa data fado masa.
Yayin da shi kuma ramin karya kurarrene, kuma mulki da Zalunci baya dorewa, wata rana sai an wayi gari babu mulkin kuma babu mai mulkin, haka zalika kuma karyar itace zata kaishi kasa kuma ta zamo abokiyar gabarsa.
Koda jin haka sai Huzaifa yayi ajiyar numfashi yace, tabbas zancenki gaskiya ne. Sai ta kuma kallonsa cikin damuwa tace, ni Yanzu gaba daya nasan cewa mutanen ku ba lallai su yarda dani ba kasancewar ni yar babban makiyinku ne. Amma kuma basu san cewa ma tsani mahaifin nawa ba kamar yadda na tsani mutuwata, tabbas ina cikin fargaba domin kuwa gabana tsinine bayana kuma siyaki.
Koda jin haka sai Luhaira ta ce to ai nice babbar abar tausayi tunda ke kin san asalinki da mahaifarki, to ni fa ban san kowa ba sai haidaman da suke hidima a cikin gidan gonar sarki.
Kuma ban san komai ba na alamuran rayuwa, wai shin mai wannan kalmar take nufi da kikace gabanki tsini bayanki kuma siyaki.
Koda jin wannan tambaya sai ta doka mata harara tace ai dama ke jahilace rainon gidan gona shi yasa bazaki san abinda ake nufi da hakan ba.
Koda fadar hakan sai lafirat ta mike tsaye ta barsu a gurin. Tabbas kishi ne yasa ta fadar hakan, kuma shima Huzaifa ya lura da hakan, sai dai kuma abinda ta fadawa Luhaira bai masa dadi ba, haka itama Luhaira kalmar ta yi mata zafi.
Haka dai aka gama cin abinci sannan aka kwashe kaya aka kimtsa sannan aka ci gaba da tafiya a wannan karon ma babu wani mai yin magana ko surutu, saboda gaba daya kowa ka ganshi hanlinshi ya dugunzuma kawai so ake aje birnin Darul Husuf domin a ga halin da birnin ke ciki, kuma aga lafiyar sarki.

* * * * * *

Al'amrin sarki shaaran da gimbiya Sazirat da tawagarsu kuwa, tunda suka fito daga birnin Darul Husuf suka nausa cikin daji basa tsayawa sai idan sunji yunwa ko kuma idan dare yayi, kai koda daren yayi indai ansamu hasken Farin wata to fa basa tsawaya. Haka suka ci gaba da tafiya ba sassauci su kwana nan su tashi can har sai da suka karaso kofar birnin shumbul.
Tun daga nesa sarki shaaran yaga wasu alamomi wanda bai saba ganinsu ba a cikin birnin yayinda yayi tafiya ko kuma yaje yaki ya dawo.
Kawai sai ya kalli Sazirat yace shin baki ga wasu bakin lamura ba daga cikin birnin mu ba?
Koda jin wannan tambaya sai Sazirat ta daga kanta sama ta kalli cikin birnin sannan tace, na lura da cewar kamar tutar dake kan tsakiyar ginin kurkukun birnin babu ita. Tabbas akwai wani babban alamari da ya faru a bayan baka nan.
Koda jin haka sai sarki shaaran ya bayar da umarni a tsaya da tafiyar.
Sannan sai ya sauka daga kan dokin sa shi da Sazirat suka ci gaba da tafiya a kafa har suka kusanci kofar birnin shumbul sosai amma kuma sai ya zamana cewa sun buya a cikin duhuwar ciyayin gurin ta ta yadda babu mai iya ganinsu.
Sannan sai sarki shaaran ya fiddo da mudubin tsafinsa ya shafeshi da hannunsa na hagu, yana mai karanta wasu dalasiman tsafi, take kuwa duk abinda ya faru a cikin birnin ya bayyana a cikin mudubin tsafin, tun daga lokacin da aka kai Huzaifa gaban wakilin sarki a matsayin tsohuwar mata, har zuwa lokacin da suka sami nasarar shawo kan tsoho Humzalu, da kuma shiga gidan kurkuku da nasara da suka samu a gidan gonar sa har hurusul Marwas ya dauko Luhaira. Kawo izuwa fitowarsu daga cikin birnin.
Koda gama ganin wannan alamari sai nan da nan sarki shaaran ya kamu da bakin ciki mai tsanani, bai san saadda ya mike tsaye da gudu ba ya durfafi masu gadin kofar birnin ya hausu da sara da suka. Da kyar Sazirat ta dakatar da shi sannan ta dubeshi cikin takaici tana cewa, ya kai abbana saboda me zaka huce haushinka akan dakarunmu.
Cikin fushi sarki shaaran ya dubi Sazirat yace, ai kwada ki barni na karar da wadannan marasa amfanin, tunda har zasu iya barin abokin gabarmu ya shiga cikin birninmu yayi mana barna ba tare da sun iya dakatar da shi ba.
Koda jin haka sai Sazirat ta kamashi ta jashi gefe daya, suka bar bakin kofar birnin suka yi tafiya mai nisa har aka daina hangosu.
Sannan suka samu guri suka zauna, tsawon yan dakiku dayansu bai ce komai ba.
Daga can sai sarki Shaaran ya dubi Sazirat yace, yake yata Yanzu menene abinyi, tunda kinga dai yanzu makiya sun sami nasarar shiga birnina kuma har cikin kurkukuna da gidan gonata sun sami nasarar kubutar da dakarunsu da kuma yarinyar da nake ta kwadayin na aureta.
Koda jin wannan tambaya sai Sazirat ta sake fadawa cikin kogin tunani, daga can sai ta dago kai ta kalli sarki shaaran tace, ina da wata dabara ko shawara guda daya.
Cikin sauri sarki shaaran yace fadamana ita muji kafin nima na fadi abinda nayi tunani da kuma hukuncin da na yake a raina.
Koda jin haka sai Sazirat ta sake ajiyar numfashi tace, ni a ganina kada mu shiga cikin birnin nan yanzu, mu koma da baya cikin daji mu sami nutsuwa daga nan sai mu aika da gorin gayya izuwa kasashen wannan nahiya tamu musamman wadanda sukayi imani da tsafi, mu nemi taimakon dakarunsu, kuma muyi musu romon baka muce duk kasar da ta bamu Aron dakarunta kuma mukayi nasara a wannan yaki to duk zamu hada kai mu yaki duk wata kasa da take irin addinin mutanen birnin Darul Husuf, kuma kowanne sarki zai samu kaso mai tsoka a cikin birnin zama a iya bashi mulkin rabin birnin.
Ina ganin idan mukayi hakan zamu samu damar tara dakaru masu tsananin yawa sannan kuma mu hada da namu na cikin gida ka ga babu ta yadda sarki uwaisul karni da jamaarsa zasu sami nasara akanmu.
Koda jin wannan shawara sai Farin ciki ya lullube sarki shaaran ya buhse da dariya, sannan yace, tabbas tunanina da naki sunzo daya, nima irin abinda na yanke kenan tabbas idan har muka sami wannan nasara to birnin Darul Husuf nakine.
Koda gama fadin hakan sai ya rungume Sazirat cikin tsananin Farin ciki, nan ya kuma tarawa da ita sukayi lalatar su.
Suka tashi suka koma can inda suka baro sauran dakarun da suka taho da su daga birnin Darul Husuf bayan sunci birnin da yaki kuma sun bar jiran gari a hannun mahaifiyar ukashat wato gimbiya muzaira.

* * * * * *

A can kofar birnin Darul Husuf kuwa, bayan gari ya waye sai sarki uwaisul karni ya tattara gaba daya dakarunsa guri daya, sannan ya dubesu cikin kwarin gwiwa yace, yaku dirkokin birnina hakika an samu maci amana a cikin birnina wanda aka hada kai dashi aka zubar da jini a cikin birninmu. Dole mu dage da addua kuma mu jajurce wajen ganin mun kwato birninmu daga hannun makiya, don haka na bayar da umarni kowa ya gyara damararsa domin kuwa gobe ne zamu je izuwa cikin birnin don kwatar birninmu a hannun makiya Allah.
Babu gudu kuma babu ka da baya koda kuwa za'a karar damu gaba daya.
Koda jin haka sai aka shiga kwalla kabbara, sannan aka shiga shirye shiryen fara yaki.
Kashe gari kuwa da safe kowa ya shiriya akayi sahu sahu ana jiran fitowar sarki uwaisul karni, ganin ya dade bai fitoba ne wakilin sarkin yakin Darul Husuf ya tafi izuwa ga tantin sarki uwaisul karni, yana zuwa yayi sallama ya shiga ciki ai kuwa da shigar sa sai yaga sarki uwaisul karni ya kalli gabas yayi sujjada yana tayiwa Allah kirari akan ya basu nasara akan abokan gaba.
Bayan wasu yan dakiku sai sarki uwaisul karni ya dago daga sujjadar sannan ya kara daga hannu nanma yayi addua sannan ya shafa.
Sai ya juyo ya kalli wakilin sarkin yaki, sai wakilin sarkin yakin yace ya shugabana dakarunmu duk sun shirya kai kadai ake jira.
Koda jin haka sai sarki uwaisul karni ya dubeshi yace, kaje ka shaidawa dakarunmu cewar ganinan fitowa na tsaya nema mana nasara ne a wajen ubangiji, sannan ka isar musu da sakona cewar suka kasance masu addua, duk rintsi kada sun manta da neman taimakon ubangiji.
Koda jin haka sai nan da nan wakilin sarkin yaki ya juya ya tafi izuwa ga rundunar tasu kuma ya sanar da su sakon da sarki ya fada masa.
Ai kuwa bai dade da fada musu wannan sako ba, sai ga sarki uwaisul karni ya fito daga cikin tantinsa ya nufo inda dakarun suke.
Nan da nan gurin ya kaure da kabbara ai kuwa babu wani jira sarki uwaisul karni ya hau dokinsa ya zabureshi da gudu yana mai kwalla kabbara aikuwa sai suma dakarun suka rufa masa baya kamar kaza da yayanta.
Suna zuwa tun daga nesa suka fara yiwa masu gadin kofar birnin ruwan kibiyoyi, ba sassauci suna zuwa baki kofar birnin suka banke kofar birnin suka shiga da karfin tsiya.
Nan da nan garin ya hautsine da yaki, aka fara cinikin rayuwaka, cikin izinin ubangiji kuwa dakarun musulunci suka fara samun nasara a hankali sarki uwaisul karni suna kutsawa har suka dan gana ga fadar birnin, kafin kace wani abu tuni an karar da dakarun dake gadin gimbiya muzaira.
Kawai sai sarki uwaisul karni ya sauko daga kan dokinsa ya nufi inda muzaira take nan da nan cikinta ya duri ruwa idonta ya zazzaro alamun rashin gaskiya suka bayyana akan fuskarta. Kawai sai ta sulale kasa aumammiya, sai sarki uwaisul karni yace, akaita kurkuku.
Sannan ya dubi wani ba fade yace, ina sauran hakimaina waziri da kuma malaman wannan gar, kawai sai yace ai duk makiya sun kaisu kurkuku sun kulle.
Koda jin haka ai sarki uwaisul karni yayi umarni da aje a fito da su.
Daga nan sarki yayiwa jamaar gari bayanin duk abinda ya faru da su, aikuwa sai wasu suka hau jimami wasu kuma suka hau hailala.
Daga can kuma bayan an kawo su waziri da hikamai da kuma sauran malaman garin sai sarki ya kuma yin jawabin wani mafarki da yayi.
Yace a cikin mafarkin nasa an nuna masa cewa dan sa yarima Huzaifa ya sami nasarar ceto dakarun da sarki shaaran ya kulle a kurkuku kuma ya sami nasarar dauko Luhaira yar gidan likita abi sharhaz.
Koda jin wannan labari sai mutane suka hau kabbara da murana, sarki ya daga hannunsa kowa yayi shiru sannan kuma yace, an nuna min cewa makiya sunan suna yin mugun tanadi akanmu don haka daga yau na umarci duk wani badakare ya kasance cikin shirin yaki domin bako wanne lokaci zasu iya kawo mana harin sumame, haka zalika na umarci dukkan malaman mu da mutanen dake cikin wannan birnin su dukufa da addua domin Allah ya karemu daga sharrin abokan gaba.
Nan dai sarki ya sallami kowa yace gobe za'a kuma haduwa a fada.
Nan dai kowa ya tafi yama fadin albarkacin bakinsa, kashe gari da safe kuwa fadar birnin Darul Husuf ta cika makil, ko inaka duba ba abinda mutum zai hanga face kawunan jamaa ko ina, bayan kowa ya gama hallara sai daga can sarki uwaisul karni ya fito, cikin kashin lafiya, koda jamaar gari suka rude da kabbara har sai da sarki ya zauna akan karagar sa daga can sai sari ya tashi yayiwa jamaa sallama sanna ya fara da cewa, ya ku jamaar birnin Darul Husuf mai albarka, ku sani cewa lokaci yayi da zamu farka daga barci mu tashi tsaye mu zage damtse d addua, domin kuwa abokan gabarmu suna nan suna yi mana mugun tanadi na zuwa su yakemu, duk da irin nasarar da muka samu a kansu a can filin yaki, da kuma nasarar da Huzaifa ya samu na shiga birnin su tare da ceto rayuwar dakarun mu a cikin kurkukun birninsu da kuma dauko Luhaira yar likita abu sharhaz, sanin wannan nasarori da muka samu akansu dole ne su fusata kuma suyi babban shiri na ganin sun dauki fansar abinda muka yi musu. Duk da cewa suma sun shigo namu birnin sun kashe mana jamaarmu, amma kuma cikin nasarar ubangiji gashi birninmu ya kuma dawowa hannunmu.
Wannan ba karamar nasara bace daga ubangijin mu, don haka dolene mu gode masa bisa wannan nasara kuma mu sake rokonsa akan samun nasara a akan abokan gabarmu anan gaba.
Domin kuwa naci alwashin cewa wannan yaki da zamu sake yi da mutanen birnin shumbul shine yaki na karshe tsakanin mu, Kodai mu karar dasu mu mulki birninsu ko kuma su karar da mu su mulki birninmu, abinda nake so da ku shine ku dage da addua sannan kuma ina mai jan hankali ga dakarun mu su mai da hankali wajen ganin munyi shiri mai kyau don tabbatar da nasarar mu a filin daga. Haka kuma kuma malaman mu na umarceku da ku Shiga halwa ta tsawon a kalla kwana uku domin kara roko nasara akan abokan gabarmu.
Da wannan nake muku Sallama sai mun sake haduwa nan da kwana uku wanda shine lokacin da zamu koma bayan gari domin tarbar abokan gaba.
Koda gama wannan jawabi sai sarki ya tashi ya shiga gida, shigarsa gida ke da wuya bai zame ko ina ba sai turakar gimbiya shulaifa wato mahaifiyar Huzaifa.
Koda shiga sai ya tarar da ita cikin damuwa zulumi da fargaba, idanunta sunyi jajawur alamun ta dade tana kuka.
Lokacin da sarki ya shiga cikin turakar tare da yi mata sallama sai ta mike tsaye ta tareshi tare da amsa sallamar tasa. Koda sarki uwaisul karni ya ga halin da take ciki, sai ya kama kafadunta yace yake matata ina dalilin shiga wannan yayi naki.
Koda jin wannan tambaya sai shulaifa ta dubeshi a lokacin da hawaye ya subuto mata tace, ya kai mijina hakika na shiga fargaba da tashin hankali a lokacin da ka tafi wannan yaki kai da su Huzaifa, har na dinga wasu irin munanan mafarkai na tashin hankali, ko da yaushe bani da nutsuwa kuma bana iya cin abinci.
Lokacin da sarki shaaran ya shigo birnin nan na gama saddakarwa cewa na tasaka kai da da na Huzaifa, ta tabbata cewa zan zama bazawarar kuyanga ko baiwa mara da.
Lokacin da na samu labarin shigowarku cikin birnin nan bayan tafiyar su sarki shaaran ina gidan kurkuku nayi Farin ciki tare da yi muku Fatan nasara, yanzu kuma gashi kana cewa nan da kwana uku zaku sake fita wani yakin, wanda kai kanka baka da tabbacin cewa zaka rayu.
Baya ga haka ga Huzaifa bai dawoba ba musan halin da yake ciki ba.
Koda jin wannan batu daga bakin shulaifa sai sari uwaisul karni ya dubeta cikin murmushi sannan yace, ki kwantar da hankalinki da izinn ubangiji zamuyi nasara a wannan yaki, haka kuma ina mai yi miki albishir da cewa danki Huzaifa yana nan cikin kashin lafiya, don ya sami nasarar abinda ya je aiwatarwa a birnin shumbul, ya ceto rayuwar dakarun mu da sarki shaaran ya kama, haka kuma ya sami nasarar dauko Luhaira yar likita abu sharhaz dake tsare a can gidan gonar sarki shaaran tare da taimakon wani aljani.
Don haka ki kwantar da hankalinki Insha Allahu mune zamu sami nasara a wannan yaki.
Haka kuma abinda baki sani ba shine, dan Huzaifa wato yarima ukashat ya dawo bangare mu domin ya gane gaskiya kuma ya nemi afuwarmu baki daya.
Koda jin wannna batu sai ta fashe da kukan Farin ciki tare da yiwa Allah godiya, nan da sarki uwaisul karni ya ci gaba da kwantar mata da hankali har ya samu ta saki ranta daga nan yayi mata sallama ya tafi izuwa turakarsa.

* * * * * *

A can bangaren su Huzaifa kuwa bayan sun kammala cin abincin sai Huzaifa ya bayar da umarni a kwashe kaya a ci gaba da tafiya, haka suka ci gaba da tafiya ba sassautawa sai idan lokacin cin abinci ko kuma loakcin sallah ya riskesu ko kuma idan dare yayi kuma babu hasken farin wata, su kwana nan su tashi can har tsawon kwana uku.
A kwana ukun ne suka fara shigo wannan daji inda kwafsa yaki tsakanin su da mutanen birnin shumbul, anan aka yada zango sai da fair ya waye sannan aka ci gaba da tafiya.

A can bangaren su sarki shaaran kuwa, bayan sunya da zango a cikin dajin da ke bakin kofar birnin shumbul sai suka kafa tantuna anan suke wana kuma anan suke tashi, kuma sai ya zamana cewa suna masu baiwa kansu horon yaki a wannan guri, har tsawon kwana hudu a kwana na hudun ne dakarun agaji suka fara zuwan wannan sansani na su sarki shaaran, aikuwa rana da suka fara zuwa sarki shaaran yayi Farin ciki sosai haka zalika ya samu kwarin gwiwa tare da cikakken yakinin cewa shine zaiyi nasara wannan yaki.
Haka dai yaci gaba da baiwa wadannan dakaru horon yaki ba dare ba rana, haka kuma kullum sai dakarun agaji sunzo daga kasahse daban daban dake nahiyar gaba daya.
Kafin cikar kwana bakwai sai da sarki shaaran ya tara dakaru sama da guda dubu dari hudu. A rana da kwana bakwai ta cika ne ya tara gaba daya dakarun sannan ya sanar musu da cewa a gobene zasu tunkari birnin Darul Husuf domin yakin karshe tsakaninsa da mutane wannan birnin.
Sannan yayi sanarwar cewa duk mutumin da ya ya ko masa kan yarsa Lafirat yayi masa alkawarin babbar kyauta, haka zalika wanda duk ya ya ko kan Huzaifa da kuma kan ukashat shima akwai kyauta ta musamman, wanda duk kuma ya sato Luhaira daga cikin gidan sarautar birnin Darul Husuf ya kawo masa ita to tabbas daga ranar zai bashi babban matsayi a cikin fadarsa.
Koda jin wadannan alkwura da sarki shaaran yayi sai kowa ya cika da buri da kwadayin ganin ya samu wannan dama duk da sun san cewa ba abune wanda zai faru cikin sauki ba.
Kashe gari tun da dukun safiya dakaru suka tashi suka fara shiri masu wasa makami na yi masu gyaran sirdi nayi kowa da irin abinda yake gyarawa dan shirya wa tafiyar.
Sai da rana ta fito gari yayi haske sosai sannan kowa ya gama shiryawa akayi sahu sahu ana jiran sarki shaaran da gimbiya Sazirat.
Su kuwa naso fito ba sai da rana ta take sosai sannan suka fito cikin shigar bakin sulke na yaki, wohoho duk wanda ya ga wannan shiga da sarki shaaran yayi da yarsa gimbiya Sazirat sai ya firgita kuma sai yayi tunanin su kadai ma zasu iya yakar duk biranen nahiyar su cisu da yaki saboda shigar ta fito da kwarjinin su da kirar su ta sadaukai musamman ma shi sarki shaaran.
Ba tare da jiran komai ba kuwa sarki shaaran da Sazirat suka hau dawakansu, suna hawa dawakannasu sai dawakan suka daga kafafunsu na gaba tare da yin haniniya a dai dai lokacin da sarki shaaran ya kwarara uban ihu tare da zare takobinsa ya nuna hanyar da za su bi dan komawa izuwa birnin Darul Husuf.
Ai kuwa dokin yana dire kafafunsa a kasa sai sarki shaaran ya zabureshi da gudu izuwa cikin daji aikuwa sai wadannan dakaru suka rufa masa baya suna masu ihu da kururuwa kai kace mutanen duniya zasu je yaka.

A can bangaren sarki uwaisul karni kuwa yana kwance yana cikin barci a cikin turakarsa kawai sai yayi wani mummunan mafarki.
A cikin mafarkin annuna masa cewa amfani gonaki na wannan birni sun kone haka kuma jini sai kwarara yake a cikin wadananna gonakai.
Koda gama wannan mafarki sai sarki uwaisul karni ya farka yana mai yin hailala, kawai sai ya sakko daga kan gadonsa ya fito daga ciki dakin nasa, kawai sai ya kira wani hafiminsa yace masa, yaje gidan babban liman maza maza ya kirashi, kuma sannan ya biya ta gidan sauran malaman garin su taru a fada da anyi sallar asubahi.
Ai kuwa ana idar da sallar asbahi sai fada ta cika makil da jamaar gari tare da manyan malaman fada da kuma hakimai da sauran fadawa.
Nana sarki ya tashi yayi sallama sannan akayi addua bayan anshafa ne sarki yayi jawabin mafarkin da yayi jiya da daddare koda jin bayanin wannan mafarki sai wani babban malami wanda ya kasance dattijo kuma masanin fassarar mafarki ya tashi ya fassarawa sarki wannan mafarki nasa inda yake cewa hakika abinda mafarkina ke nuni da shi shine makiya na dab da shigowa cikin birnin nan namu mai albarka, koda jin wannan fassara daga bakin wannan makami sai mutanen dake fadar suka rude da hayaniya da salati.
Koda jin haka sai sarki ya daga hannunsa sama kowa ya sake yin shiru, kawai sai sarki uwaisul karni yace, daga yanzu zuwa rana ta fito kowanne badakare ya je ya shirya a hadu kofara fada haka zalika ya umarci duk mutanen gari da su zauna a gida kada wanda ya kuma fitowa waje har sai suna dawo daga wannan yaki da zasuyi ya umarci malaman garin cewar gaba dayan su su hallara a masallaci su dukafa da addua haka suma mutanen gari sauran dakaru kuma dasu za'a fita wannna yaki.
Koda gama wannan jawabi sai sarki uwaisul karni ya juya ya shiga gida domin shirin yaki, sa da aka shafe sama da sa'a hudu ana shirin fita yaki sannan kowa ya kammala dakaru sukyi sahu sahu a bakin kofar fada ana jiran fitowar sarki, jima kadan sai ga sarki uwaisul karni yvta fito cikin shigar Kayan yaki na fararen sulke, tabbas shigar da yayi sai da ta kara masa kwarjini sosai.
Aikuwa yana zuwa ba wani jira ya kama dokinsa ya hau sannan ya zaburesi da gudu izuwa kofar birnin.
Anan aka kafa tantuna aka zauna ana jiran isowar abokan gaba.
Alamarin su sarki shaaran kuwa suma haka abin y kasance sun kwana nan su tashi can har tsawon kwana takwas, a kwana na tara ne suka iso bakin kofar birnin Darul Husuf, kasancewar a lokacin duhu ya fara bisa dole suma suka ya da zango kuma suka kafa tantuna suna jiran gari ya waye domin a gwabaza wannan yaki.

Kashe gari kuwa tunda fukin safiya dakarun kowanne bangare suka hau sahu sahu, kowacce runduna ta na jira shugabanta ya fito, domin a bayarda umarni.
Can sai ga sarki uwaisul karni da sarki shaaran sun fito gaban jamaarsu, kawai sai aka ga wani daga cikin dakarun sarki shaaran ya sukwano dokinsa izuwa sansanin su sarki uwaisul karni.
Har wani badakare ya zare takobinsa da nufin yata tareshi kawai sai sarki uwaisul karni ya dakatar da shi.
Da zuwa sai wannan badakare ya sauka daga kan dokinsa, ya zo Har gaban sarki uwaisul karni ya mika masa wata wasika, sai sarki ya karbi wasikar, sannan ya fara karantawa kamar haka.
*sako daga sarki mai cikakken ikon zuwa ga abokin gaba ta, ina mai yin umarni a gareka da ka janye dakarunka daga wannan filin yaki, domin kuwa babu ta yadda za'ayi kuyi nasara a wannan yaki domin kuwa sarki yawa yafi sarkin karfi, sannan kuma ina so kazo har gabana ka fadi bisa gwiwarka ka nuna cewa kayi mana mubayaa, wannan shine kadai abinda zai sa na yafe maka zunubin da kuka aikata min, idan kuma ba haka ba to ina mai yi maka rantsuwa da girman kujerata sai na mayar da kasarka birnin nakasassu.*

Koda gama wannan jawabi sai ran sarki uwaisul karni ya baci, sai yasa aka rubuta martanin wasikar kamar haka.
*karyar ka ta sha karya kai gafalallen sarki ka tuba ka karbi addinin Allah sannan kuma ka koma ga Allah ka nemi afuwarsa gareka, sannan kuma kayi alkawarin cewa bazaka kara zubar da jini ko zalunci a bayan kasa ba, idan har kayi haka tabbas zan Barka da ranka idan kuma baka tuba ba to tabbas a yau daina shafe tarihinka a doron kasa*

Koda aka wannan badakaren ya kaiwa sarki shaaran martanin wannan wasika tasa sai ran sarki shaaran ya baci, aikuwa nan take ya bayar da umarni da a afkawa su sarki uwaisul karni.
Aikuwa sai gaba dayan dakurun sarki shaaran suka zare makamansu suka zaburi dawakansu izuwa kan su sarki uwaisul karni suna masu kururuwa da ihu, kafafuwam dokin su na karyar kasa nan da nan kura ta turnuke sama kasa ta dinga girgiza kamar zata tsage.
Koda sarki uwaisul karni yaga dakarun sarki shaaran sun durfafosu cikin mugun nufi sai shima ya bawa dakarunsa umarni da atare su tun kafin su karaso, aikuwa sai suma suka zaburi dawakansu suna masu zare takubba tare da kabbara, suma suka kai dauki kan dakarun sarki shaaran, aikuwa ana haduwa a tsakiya sai aka gwamutse kirazan dawakai suka fara bangazara na yan uwansu Nanfa aka fara cinkin rayuka.
Komai kallon kurallar mutum bai isa ya banbance bangaren da ke samun nasara ba. Domin kuwa kare jini biri jini akeyi, nanfa maza je suka fara kwamarzuwa babu sassauci ana kaiwa juna sara da suka cikin zafin nama juraya da jarumata.
Duk inda sarki uwaisul karni yasa gabansa sai dai kaga dakaru na zubewa a kasa kamar sassabe a gona, hakama a bangaren sarki shaaran wato dai sai yiwa dakarunsu suke sarki ya hana dawa tsaiwa.
Koda ganin irin barnar da kowa ke yiwa kowa sai sarki uwaisul karni da sarki suka tarwatsa dakarun dake gabansu suka zaburi dawakansu suka nufi kan juna cikin mugun nufi da zakuwa.
Ai kuwa suna haduwa suka fara kaiwa junan su sara da suka cikin tsananin zafin nama juriya da bakinta da jarumta cikin salo da kwarewa irin ta manyan mayakan da suka ga jiya suka ga yau.
Haka dai aka ci gaba da wannan yaki, to amma kasancewar dakarun sarki shaaran sunfi dakarun sarki uwaisul karni yawa sai ya zamana cewa an fara cin karfin dakarun birnin Darul Husuf, haka dai aka ci gaba da dauki ba dadi har tsawon sa'a hudu, koda ganin cewa wankin hula zai kaisu dare sai dakarun sarki shaaran suka fara amfani da karfin tsafi domin su karar da dakarun sarki uwaisul karni, koda ganin haka sai dakarun sarki uwaisul suka fara karanta wata addua ta musamman ai kuwa duk tsafin nasu sai ya tashi a banza, haka dai aka ci gaba da yaki har ya zamana cewa an karar da kaso biyu cikin uku na dakarun birnin Darul Husuf, su kuma dakarun sarki shaaran an karar da kaso daya cikin ukunsu.
Koda fahimatar hakan sai sarki uwaisul karni ya dan ka da baya kadan ya tsaya yana mai gyara tsayuwa koda ganin haka sai shima sarki shaaran yayi koyi dashi.
Sannan sai sarki shaaran ya dubi sarki uwaisul karni cikin murmushi mugunta yacena fada maka wannan yaki na mune kuma dolene muyi nasara akanku kana da dama har yanzu lokaci bai kura maka ba, indai har zakayi abinda nace maka tunda farko to zan yafe maka.
Koda jin haka sai sarki uwaisul karni ya dubeshi cikin fushi yake cewa, kai Munafukin Allah kayo sani cewa har abada babu sulhu tsakanin da makiya addinin Allah ni dasu sai kaifin takobi kawai.
Kuma idan har na mutu ina da yakinin cewa nayi shahada kuma zaa tashe mu a wata rayawar daban a ranar alkiyama don ayiwa kowa hisabi bisa abinda ya a doron duniya, wadanda sukayi imani kuma suka aikata aiki na kwarai zasu samu babban rabo, wadanda kuma suka bijire suka aikata zalunci irin ka to zasu sansani azaba mai radadi.
Sai ka fadamin menene ribarka anan, kodajin haka sai sarki shaaran ya bushe da dariya sannan yace, ai ku kukayi imani da wannan zancen mu kam sam zamuyi imani dashi ba, kaicho kaji rashin rabo. Hakika wanda yayi nisa baya jin kira.
Ana cikin wannan haline sai su sarki uwaisul karni suka jiyo takun sawayen dawakai daga cikin daji, ba kowa bane face Huzaifa tare da dakarun musulunci wanda sarki shaaran ya rufe a gidan kurkuku.
Ai kuwa tuna kafin su karaso filin yaki suka zare makamansu ai kuwa sai filin ya kuma hargitsewa da zazzafa kuma mummunan yaki, ana cikin haka kuma sai ga dakarun ukashat nan suma sun nufo filin yakin aikuwa sai musulmai suka kara samun sabon kwarin gwiwa, nan da nan aka sa dakarun sarki shaaran a tsakiya.
Sarki uwaisul karni ya tari sarki shaaran, ukashat ya tari sarkin yakin birnin shumbul, Huzaifa kuma sai ya tari mai bakaken kaya, Lafirat ta tari yar uwarta Sazirat, uwar mayu da hirama suma suka afka cikin wannan yaki.
Kowa na kaiwa kowa mummunan hari cikin mugun nufi. Haka dai akayi ta dauki ba dadi har tsawon wata sa'a ukun a sannane aka fara cin karfin dakarun sarki shaaran koda suka ga an kusa karar da su sai suka fara guduwa daga filin yakin koda ganin haka sai sarki shaaran ya dinga yin tsafi duk wanda zai gudu sai ya kama da wuta ya kone kurmus.
A lokacin da sarki uwaisul karni yayiwa sarki shaaran munanan sara har guda uku daya a gadon bayansa daya kuma a kan dantsensa na dama sai kuma cinyarsa ta hagu, gurin ya bude sai jinine ke zuba.
Shi kuma sarki uwaisul karni ya sami raunika har guda biyu daya a cinyarsa ta dama daya kuma dantsensa na hagu aman ranuni baiyi zurfi sosai ba.
Ana cikin haka ne sarki uwaisul karni ya shammaci sarki shaaran ya dan kara masa sara a kasan cibiyarsa, kawai sai ji akayi sarki shaaran ya kwarara uban ihu sannan ya durkushe bisa gwiwowinsa, ana cikin Hakane itama Lafirat ta shammaci Sazirat ta dan kara mata naushi a cikin tana durkusawa tayi mata mugun duka a gadon baya, aikuwa sai ta kife kasa tana mai aman jini cikin galabaita gashi duk sunyi wa junan su munanan rauni ka alamun karfi yazo daya.
Kawai sai Lafirat ta taka kafafunta tana mai tafiya da kyar tazo kan Sazirat a lokacin da hawaye ya zubo mata tace, yake yar uwata kiyi sani cewa bani da wani sauran da uwa na jini a wannan duniya sai ke, ina mai baki shawara daki tuba ki koma ga ubangiji musulunci, ki karbi addinin gaskiya.
Koda jin haka sai Sazirat ta takarkare ta bushe da dariya tace, kiyi hakuri yake yar uwata bakin alkalami ya riga ya bushe, nikam da nayiwa iyayena da kakannina butulci gwara na mutum a cikin addinina.
Koda jin haka sai Lafirat ta sa takobinta ta sare kan yar uwarta Sazirat.
Hakama a bangaren su Huzaifa ta ukashat kowa ya kashe abokin gwaminsa.
Ya zamana cewa saura sarki shaaran kawai a kwance ya kasa tashi, a haka sarki shaaran ya ci gaba da kakarin mutuwa har rantsa ya fita idanunsa suka kakkafe harshensa ya zazzago kasa. Tur Allah wadai da irin wannan mummunar mutuwa.
Daga nan aka dunguma aka koma cikin birnin Darul Husuf. Ukashat ya dubi Huzaifa ya bashi hakuri abisa abinda ya faru tsakaninsu a baya ya nemi yafiyarsa cikin Farin ciki da murna suka rungume juna, sannan yarima Huzaifa yace da ukashat ga babbar kyauta nayi maka kawai sai ya nun amsa gimbiya Luhaira.
Ana cikin haka sai gimbiya Lafirat ta zai gaban sarki uwaisul karni tace itama tanadi a shigar da ita cikin addinin musulunci, nan da nan kuwa sarki ya biya mata kalmar shahada ta maimaita.
Yarima Huzaifa yace yanzune kika zamo cikakkiyar yar iwarmu musulma, sarki yasa zakaje ka fito da mahaifiyar ukashat daga gidan kurkuku koda aka zo da ita gaban sarki taga nasara da suka samu sai kawai ta hadiyi zuciya ta mutu nan take.
Kashe gari da safe mutanen gari da malaman fada da haikamai da fadawa gaba daya aka hallara a fadaaka daura auren yarima Huzaifa da gimbiya Lafirat, sannan na yarima ukashat da gimbiya Luhaira, aka shagalin biki.
Ita kuwa uwar mayu da hirama sai suka zama sune manyan dakarun birnin Darul Husuf, Maana sune a bakin kofar birnin, sannan zakaje har birnin shumbul aka kafa tutar musulunci dama nahiyar baki daya.

Alhamdulillahi nan muka kawo karshen wannan Littafi na DAKARUN MUSULUNCI wanda Abdul aIzi sani Madakin gini ya rubuta ni kuma Umar Farouq Zango na kawo muku sharhinsa tun daga Littafi na daya har zuwa na biyar.
Fatan kun nishadantu da wannan Littafi. Nan gaba kadan kuma Insha Allahu zan saka littatfai guda biyu za'ayi kuria a kansu duk wanda mutane suka fi yawa to shi zamu saka.
Wanda mu UMAR FAROUQ ZANGO da NAJIBULLAH MUHAMMAD muke cewa sai mun hadu a wani sabon littafin muna yi muku Fatan alkhairi.
MUNGODE[12/14, 6:53 PM] INSTRUCTOR⚓: **DAKARUN MUSULUNCI**
LITTAFI NA BIYAR 5
PART A ✍️ ✍️ ✍️

NA ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI👮
TYPING:-UMAR FAROUQ ZANGO✍️✍️
POSTING:- NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥷🥷

ASLM, bayan tsokacin da dakatawar posting din Dakarun Musulunci insha Allah a yau zamuci gaba, Muna fatan Allah ya taimakemu 🙏🥰♥️♥️

Duk sa'adda Huzaifa ya sami nasarar saran jikin katon mutumin ko ya sokeshi da takobinsa sai yaji kamar dutse ya doka ko kwarzanewa jikinsa baya yi sai dai kaga tartsatsin wuta na tashi.
Wannan barandami na mutumin kuwa, duk abinda ya sama dashi sai ya rabe gida biyu walau dutse ko karfe.
Duk irin zafin naman Huzaifa da tsananin jarumtakarsa sai yaga duk sun zama na banza domin katon ya ninkashi a komai.
In ba don ma yana da mutukar kwarewa ba da iya yaki da tuni katon yayi masa kwaf daya.
Suna cikin wannan bakin gumurzu ne katon ya shammaci Huzaifa ya gabza masa naushi fuska.
Saboda karfin naushi sai da Huzaifa yayi sama ya gwaru da jikin bango a lokacin da wani gudan jini yayi fitar burgu daga cikin bakinsa ya fado kasa a mutukar galabaice takobinsa ma sai ta subuce daga hannunsa ta fado kasa.
Koda ganin abinda ya faru sai aljani huraisul Marwas ya fusata ainun ya bude fuka fukansa ya kawowa katon mutumin suka a kirji da wani mashinsa na yaki.
Kawai sai katon ya tare sukar da tafin hannunsa.
Take mashin ya narke ya kama diga kasa tamkar ya kwana dari a cikin wuta yana damuwa.
Cikin zafin nama katon ya kaiwa hurusul Marwas mangari da hannunsa guda, ai kuwa sai yayi Saar samunsa a fuka fukinsa na hagu.
Kamar an cilla tsakuwa haka hurusul Marwas ya fada can baya ya gwaru da bango ya fado kasa sumamme sakamakon karyewar fuka fukinsa.
Koda katon ya ga wannan nasara da ya samu sai ya bushe da dariya mugunta sannan ya juya izuwa kan yarima Huzaifa yaje kansa ya tsaya ya raba kafafunsa kuma ya sunkuyo da nufin ya kama kan Huzaifa ya murde masa wuya.
Ashe a dai dai wannan lokaci hunzalu na ta yiwa Allah kirari yana neman ya karfafeshi da karfin da zai iya taimakon su Huzaifa.
Ai kuwa nan take yaji wani gagrumin karfi ya shiga jikinsa, kawai sai gani yayi ya daka tsalle daga inda yake ya dira akan wannan garjejen kato.
Kafin katon ya kamo kan Huzaifa da hannayensa tuni hunzalu ya naushi gadon bayansa.
Saboda tsananin karfin naushi take gadon bayan katon ya burme, sai ga hannun hunzalu ya Faso ta cikin katon.
Yana zare hannunsa sai katon ya sulale kasa matacce, ji kake Tim! Tamkar giwa ce ta fadi.
Shi kansa hunzalu bai san saadda ya kame ba kamar gunki saboda tsananin mamaki bisa ganin wannan gagarumar jarumta da yayi. Kawai sai yaji tsoron Allah da kaunarsa sun karu ainun a cikin ransa, bai san saadda idanunsa suka ciko da kwallah ba suka fara zubar da hawayen murna.
Huzaifa da aljani hurusul Marwas kuwa, kasa motsawa sukayi saboda tsananin alajabi sai bayan yan dakiku sannan Huzaifa ya mike tsaye ya dubi hunzalu cikin murmushi yace, ya kai hunzalu kayi sani cewa wanda duk ya yi imani da Allah kuna ya dogara da shi bisa dukkan lamuransa to fa babu abinda zai gagareshi a doron kasa.
Tabbas imaninka da tsoronka ga Allah ne suka sa ka sami wannan gagarumin karfi har ka sami nasarar kashe wannan katon ka ceto rayuwarmu.
Ni da hurusul Marwas kuwa ajizanci ne irin na dan Adam yasa muka shaafa da ci gaba da neman taimakon Allah, a lokacin da muke yin yaki da wannan kato, shi yasa muka masa samun nasara a kansa.
Koda Huzaifa yazo nan a zancensa sai yaji ana ta kiran sunansa a bayansa.
Koda ya waiga da sauri sai yaga ashe ba wasu bane face dakarun garinsu wadanda ke cikin wannan daki a kulle, su duka sun zo bakin kofar dakin sun tsaitsaya wacce take a kulle da katon kwado kuma an yi tane da sandunan karfe mai kauri.
Nan take Huzaifa ya sunkuya ya dauki takobinsa ya tofa mata wata addua sannan ya dagata sama ya sare kwadon mukullin da aka rufe kofar da shi.
Take kwadon ya fadi kasa kofar ta bude, sai dakarun suka fito waje gaba dayansu cikin tsananin farinciki suna yiwa Allah godiya gami da yiwa Huzaifa jinjina.
Nan dai aka dunguma da nufin a fice daga cikin kurkukun gaba daya amma sai Huzaifa ya tsaya cak! Sakamakon aljani hurusul Marwas a kwance yana nishi ya kasa tashi.
Cikin kaduwa Huzaifa ya ruga gareshi ya durkusa a gabansa yace, ya kai dan uwanavv menene ya sameka ka kasa tashi kana ta nishi haka?
Hurusul Marwas ya budi baki da kyar yace, shi baka ganin yadda fuka fukina na hagu ya kumbura bane?
Ai na karye ne kuma ba zan iya koda motsawa ba daga nan face an gyara mini wannan karaya.
Koda Huzaifa ya dubi fuka fukin ya ga yadda ya karye kuma ya kumbura sumtum! Sai hankalinsa ya dugunzuma domin bai san yadda ake DOA aljanu ba yayin da suka karye.
Huzaifa ya dubi aljani hurusul Marwas yace, yanzu menene abinyi?
Kaga dai inda zamu taru mu duka nan ni da dakarun nan da muka ceto rayuwarsu ba za mu iya daukarka ba sannan kuma bamu san yadda ake gyara karaya ba irin taku ta aljanu.
Koda jin wannan batu sai aljani hurusul Marwas yayi murmushin karfin haki yace, ai batun gyaran karayarmu iri dayane da naku, kawai yanzu ku garzaya ku samo itatuwan bishiya masu kauri gami da danyar jijiyar bishiya kuzo ku gyara karayar da sauri kafin abokan gaba su zo su afka mana domin na san cewa nan da zuwa wani lokaci akilin sarki shaaran zai iya samun labarin halin da kurkuku ke ciki aboda tsegumi irin na yan uwana aljanu. Yanzu ma karfin addu'armu ne ya hana aljanun dake yaso munafunci zuwa kusa da nan bare su san halin da ake ciki.
Koda jin wannan batu sai Huzaifa ya umarci wasu daga cikin dakarun na musulunci da su ruga suje u samo manyan itatuwa da danyar jijiyar bishiya.
Nan da nan kuwa dakarun suka cika umarni. Lokacin da aka zo da abubuwa biyun sai aljani hurusul Marwas ya dubi yarima Huzaifa yace, ina mai baku shawara daku samo murtukekiyar sarkar karfe ku fara daure hannayena, kafafuna da wuyana kasa cikin dirkoki in ba haka ba kuwa gyaran karayar nan ba zai yiwu ba.
Koda jin wannan batu sai yarima Huzaifa yayi murmushi yace, hakika aikin mai shawara baya baci.
Aaje a samo irin sarkokin da ake daure fursunonin aljanu a gidan nan, sannan vkuma ina son muci gaba da yin adduoi gaba dayanmu domin Allah ya hana abokan gabarmu zuwa nan harmu kammala duk abinda muka zo yi.
Nan take kuwa akayi amfani da wannan umarni.
Bayan an samo wata murtukekiyar sarkar karfe an daure hanaye, kafafu da wuyan aljani hurusul Marwas a jikin wadan su manyan dirkokin gini, sai hurusul Marwas ya sake bayar da shawara a toshe bakinsa da tsummokara a daureshi tamau.
Wannan shawara ma ba ayi biris da ita ba,, koda aka fara gyara karayar fuka fukin nasa kuwa yaji wani irin mugun radadi da zugi sai ya yunkura cikin azabbaben karfi, ya kwarara uban ihu.
Da yake bakinsa a toshe yake sai ihun ya zamo kamar an busa bututun algaita, amma duk da haka sai da karar sautin ta cika birnin shumbul gaba daya ta firgita komai da kowa.
Motsawar da yayi kuwa, sai da gaba dayan ginin gidan kurkukun yayi girgiza kamar zai rushe.
Cikin hanzari Huzaifa da sauran jamaarsa suka daka tsalle suka dira akan hurusul Marwas suna kokarin danneshi.
Duk da haka sai suka kasa ladaftar da shi domin da zarar ya yunkura sakamakon zafin da yake ji na gyaran karayar sai kaga ya watsar da su kasa tamkar busassun ganyayen bishiya na zubowa kasa.

* * * * * *
A can gidan sarautar sarki shaaran kuwa, lokacin da wakilin sarki da sauran jamaar asa suka jiyo sautin ihun aljani hurusul Marwas dai suka rude kuma suka cika da tsananin mamaki domin basu taba jin wani sauti ba makamancinsa a cikin garin.
Nan take wani babban badakare ya dubi wakilin sarki yace, ya shugabana anya kuwa ba abokan gabarmu mune suka shigo cikin garin nan bamu sani ba suka fara yi mana yakin sunkuru?
Koda jin wannan tambaya sai wakilin sarki shaaran ya dakawa badakaren tsawa yace, hana wannan wacce irin maganar banza kakeyi ne haka?
Ta yaya abokan gaba zasu iya shigowa cikin garin nan ba tare da mun sani ba alhalin ka san cewa a ko ina kuma dare da rana aljannunmu masu gadin birnin nan suna sintiri suna kewaya garin?
Badakaren ya numfasa yace, ya shugabana ni fa alamarin mutanen nan maabota addinin musulunci yana bani tsoro saboda suna da matukar karfin sihiri.
Ka tuna cewar bamu taba jin irin wannan sauti ba a garin nan sai wannan karon, kuma mutum ba zai iya fitar da wannan sauti ba sai dai gawurtaccen jarumin aljani kamar irin aljanun da suje gadin kurkukun sarki da gidan gonarsa.
Ni dai ina mai bayar da shawara ka tura dakaru suje su gano halin da kurkukun yake cikin da kuma gidan gona don kada makiya su zo su shammacemu.
Saadda wakilin sarki yaji wannan batu sai ya gyada kai yace, hakika aikin mai shawara baya baci, amma ai na san cewa babu ta yadda za'ayi makiya su iya shigowa cikin garin nan ba tar da asirinsu ya tonu ba saboda irin kwararan matakan tsaron da sarki ya dauka.
Koda gama fadin hakan sai wakilin sarki ya dubi wannan badakaren yace dashi yayi sauri ya hau dokinsa ya tafi izuwa kurkuku ya gano halin da yake ciki, sannan kuma ya wuce izuwa can gidan gonar sarki can ma ya gan ko akwai wata matsala.
Nan take kuwa badakaren ya hau dokinsa ya zabureshi da gudu ya nufi hanyar da zata kaishi kurkukun.

* * * * * *
A can kurkuku kuwa, cikin gaggawa su Huzaifa suka gama gyaran karayar aljani hurusul Marwas sannan Huzaifa ya bayar da wata addua ta musamman yace kowa yayi ta biyata a cikin zuciyarta sannan ya umarci humzalu da yayi musu jagora izuwa gidan gonar sarki.
Nan take kuwa suka hau dawakansu su duka suka fice daga cikin gidan kurkukun suna ta karanta wannan assay addua da Huzaifa ya basu suna ta wuce gawarwakin dakarun dake tsaro gaba daya.
Sai a wannan lokacine ragowar dakarun kurkukun da ke can kofofin farko na shigowa suka ankara da abinda ke faruwa, suka ruga da gudu izuwa kan su yarima Huzaifa da nufin su kashe su.
Nanfa aka rugumtsume da sabon azabbaben yaki.
Da yake wannan karon su Huzaifa na tare da dakarun musulunci sai nan da nan suka sami nasarar yakin.
Koda tsirarun dakarun suka ga saura su yan kadan sai suka zubar da makamansu suka fara yunkurin guduwa.
Cikin daga murya Huzaifa ya bayar da umarnin kada a bari dayansu ya tsira ya gudu daga cikin kurkukun.
Aikuwa sai dakarun musulunci suka rinka kurewa dakarun kurkukun gudu suna rafkesu.
Nan da nan aka karar dasu gaba daya. Faruwar haka ke da wuya sai aka sake hawa dawakai da nufin a tafi izuwa gidan gonar sarki. Har an iso baki kofar fita daga kurkukun sai wani tunani ya fadowa Huzaifa kawai sai yaja linzamin dokinsa ya tsaya cak sannan ya dubi hunzalu da sauran dakaru na musulunci ya ce, ba zamu iya tafiya ba izuwa gidan gonar sarki a haka ba dole ne mu yi bad da kama muyi shiga irin ta dakarun sarki shaaran yadda ko akan hanya babu mai taremu.
Wasu daga cikinmu kuma dole ne su yi shiga ta bayi sannan ina son mutum hudu daga cikinku wadanda zasu iya kundunbala su tsaya a bakin kofar kurkukun nan a matsayin masu gadi a cikin shigar masu gadin domin jikina ya bani cewa a ko Yaushe wakilin sarki shaaran zai iya turo mutanensa domin su zo su ga halin da kurkukun nan ke ciki.
Yanzu su waye zasu iya yin wannan kundunbala mu barsu anan kofar kirkir koda dai sun mutu sun san cewa shahada sukayi?
Kafin Huzaifa ya rufe bakinsa tuni gaba daya dakarun sun budi baki cikin hadin murya kowa dacewa shi ya amince.
Koda jin haka sai Farin ciki ya kama Huzaifa ya dubesu yace, hakika duka imaninku ya inganta domin dukka musulmi na gari yana da burin shahada.
Koda gana fadin hakan sai nan da nan aka shiga shirye shiryen sauya tufafi.
Cikin kankanin lokaci kowa ya gama komtsawa. Aljani hurusul Marwas ne kadai bai yi shiga irin ta dakarun shaaran ba a matsayinsa na aljani.
Take aka bar mutum hudu a bakin kofar kurkukun suka yi tsayuwa irin wacce masu gadin kurkukun ke yi koda Yaushe.
A sannane Huzaifa da sauran dakarun suka tusa keyar dakarunsu da suka yi shigar bayi suka gaba, hunzalu ne akan gaba cikin shigar dakarun birnin yana yi musu jagora, Huzaifa na daga can bayan karshe.
Suna cikin wannan tafiya ne suka yi kicibus da wannan badakare wanda wakilin sarki shaaran ya turo shi kurkukun domin yaga halin da kurkukun ke ciki.
Koda ganinsa sai wani daga cikin dakarun musulunci ya yunkura zai zare wuka ya kasheshi, amma sai Huzaifa ya yi masa inkiyar ya kyaleshi.
Lokacin da badakaren ya karaso dag da su ya ga ashe hunzalu ne ke jagorantar wadannan bayi sai ya risina cikin girmamawa ya gaisheshi yace, ya shugabana daga ina kuke haka, kuma ina zaku kai da wadannan bayi haka?
Koda jin wannan tambaya sai hunzalu ya dubi badakaren yace, daga kurkuku muke kuma gidan gonar sarki zamu kai wadannan fursunoni domin su canji maaiakatan can kamar yadda aka sabayi kullum.
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama badakaren yace, haba ya shugabana ta yaya zaka debo fursunoni daga kurkuku ka kaisu can gidan gonar sarki alhalin kafin sarki ya taci yaki ya kafa doka mai tsauri cewar babu mahalukin da zai sake shiga ko fita daga cikin kurkuku da gidan gonarsa?
Yanzu haka ma wakilin sarki ne yace na zo na ga halin da kurkukun ke ciki sannan na wuce izuwa can gidan gonar tasa, can ma na ga lafiyar sa.
Saadda badakaren yazo nan a zancensa sai yaji hunzalu ya bushe da dariya.
Lokaci guda kuma ya turbine fuskarsa ya daka masa tsawa yace, ina hankalinka ya taci ne?
Shin kana zaton zan aikata abinda zai bata ran sarki ne alhalin na san cewa ko yaya nayi wani kuskure sawa zaiyi a kashe dana guda daya dake tare a inda ban sani ba?
Ka sani cewa ni ne mai kula da aiyukan gidan gonar sarki idan aikin gonar sarki ya tsaya ko aka sami wata matsala yana dawowa zai hukuntani.
Ka ga ni yanzu kana bata mini lokaci kuma kana batawa kanka lokaci gwara ka tafi izuwa Aiken da aka yi maka.
Koda gama fadin hakan sai hunzalu ya bangaje wannan badakaren ya wuce gaba ayarin su Huzaifa suka take masa baya.
Da yake duk u Huzaifa suna sanye ne hulunan karfe ne badakaren bai ga fuskar dayansu ba bare ya gane cewar ba dakarun kasar bane, amma sai ya tafi yana waigensu cikin alamun mamaki da rashin yarda.
A wannan lokaci aljani hurusul Marwas na can sama cikin gajimare yana bin su Huzaifa kuma yana karanta dduar da Huzaifa ya bayar dalilin da ya sa sauran aljanun dake shawagi a sararin saman garin suka kasa ganinsa ke nan kuma suka kasa ganin su Huzaifa.
Lokacin da su Huzaifa suka ci gaba da tafiya sai wani badakare dake kusa da Huzaifa ya dubeshi cikin girmamawa yace, ya shugabana me yasa ba ka barni na kashe wancan badakaren ba dazu?
Kayi sani cewa barinsa a da rai a garemu ba karamin ganganci bane domin ga dukkan alamu bai yarda da mu ba, kuma zai iya zuwa ya kai labarin mu ga wakilin sarki shaaran can fada a turo mana mayaka masu yawa su kawo mana hari.
Saadda Huzaifa yaji wannan batu sai yayi ajiyar zuciya sannan yace, tabbas abinda ka fada gaskiya ne, to amma kuma kashe shin shine abu mafi hadari a garemu domin idan wakilin sarki ya ga ya dade bai koma ba zai turo abu sawunsa kuma idan aka zo aka ga gawarsa za'a gane cewar mun shigo cikin garin sai abi sawunmu har can gidan gonar a tarfa mu.
Yanzu kuwa idan yaje kofar kurkukun yaga dakarunsu a tsaye babu alamar wata matsala zai juyo ne ya biyomu izuwa can gidan gonar sarki, kafin ya riskemu kuma tuni mu munje mun dauko luhaira.
Koda Huzaifa yazo nan a zancensa sai gaba daya dakarun suka gamsu da bayaninsa kuma suka cika da tsananin mamakin irin basirarsa da yadda akayi ya shirya wannan dabara.

Alhamdulillahi nan zan da kata sai Allah ya kaimu sati mai zuwa zaku jini dauke da ci gaban wannan labari.
Sunana Umar Farouq Zango nake muku Fatan alkhairi sai mun hadu a ranar jumaa idan Allah ya kaimu.🙏🙏🙏🙏
[12/14, 6:53 PM] INSTRUCTOR⚓: **DAKARUN MUSULUNCI**
LITTAFI NA BIYAR 5
Part B ❤️ ♥️

NA ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI👮👮
Typing:- UMAR FAROUQ ZANGO.✍️
Posting:- Najibullahi Muhammad 🥷🥷

Haka dai suka ci gaba da tafiya har tsawon kusan rabin sa'a sannan suka iso kofar gidan gonar sarki.
Tun daga mesa gabansu ya fadi sakamakon hango irin tsananin tsaron da ke gidan gonar, wanda ya ninka na kurkukun sau goma.
Nan take zuciyoyinsu suka karaya suka tabbar da cewar babu yadda za'ayi su shiga cikin wannan gidan gona cikin irin Saar da nasarar da suka samu a can kurkuku kuma komai zai iya faruwa ko dai su rasa rayuwarsu ko kuma a dade ana gumurzu har wakilin sarki ya san da zuwan su azo ayi musu rubdugu.
Koda yarima Huzaifa ya gama aiyana wannan alamari sai hankalinsa ya dugunzuma ya rasa abinda ke masa dadi ya fara shawara da zuciyar sa.
Abin da ya fado masa a rai shine, idan har basu sami damar shiga cikin gidan gonar ba kai tsaye har su gano inda Luhaira take a cikin kankanin lokaci ba duk shirin su ya wargatse.
Har suka karasa daf da kofar gidan gonar Huzaifa bai sami wata mafita ba.
Da isowarsu sai dakarun dake tsaron kofar suka dakatar dasu.
Shugaban masu gadin ya dubi Hunzalu a fusace yace, menene ya kawoka nan tare da bayi kalilan da kuma dakaru masu yawa haka?
Koda jin wannan tambaya sai zuciyar sa ta buga da karfi, tsoro ya baibayeshi ya firgita ainun domin yana ganin cewa asirinsa ya tonu amma sai ya yi ta maza ya dakawa shugaban masu gadin tsawa yace, shin ka manta da wanda kake maganane?
Ka manta da cewar nine mai kula da dukkanin bayin dake aiki a cikin gidan gonar nan fiye da shekaru talatin baya har ma sai da dana yazo ya gajeni?
Koda jin wannan batu sai shugaban masu gadin ya bushe da dariyar mugunta, lokaci guda kuma ya turbune fuskarsa yace, ai duk maganar da kake yi alamarin ne na da wanda ya wuce.
Shin ka manta ne da cewar dan naka daya gajeka Yanzu haka baya kan aikinsa kuma an sare masa hannuwansa da kafafunsa kuma antsire idamunsa sakamakon laifin da ya aikata na kusantar amaryar da sarki zai aura.
Kai kanka yaushe rabonka da shiga cikin gidan gonar nan, a kallah ankai sati guda.
Kuma sarkine da kansa ya dakatar da kai don tabbatar da tsaro a gidan gonar gaba daya bisa barazanar abokan gaba.
Ina mai tabbatar maka da cewa idan ba sarki shaaran bane ya zo da kansa nan yace mu bude maka kofa ku shiga ba babu yadda za'ayi ku shiga cikin gidan nan.
Koda jin wannan batu sai hankali su yarima Huzaifa ya dugunzuma ainun suka rasa abin da ke musu dadi.
Shugaban masu gadin ya sake duban hunzalu ya daka masa tsawa yace, ya kai hunzalu ina mai shawartarka da ka gaggauta janye gidan gonar nan kafin cikar dakika dari ko Yanzu nan na umarci dakaruna dake kan ganuwa suyi musu ruwan kibau.
Yana gama fadin hakan sai ya juya ya koma can bakin kofar gidan gonar inda sauran yan uwansa masu gadi suke.
Nan take hunzalu ya karaso gaban yarima Huzaifa ya dubeshi cikin tsananin damuwa yace, ya shugabana yanzu menene abinyi?
Kawai sai Huzaifa yace, ku zo mu koma da baya izuwa can cikin duhuwar dajin can.
Ba tare da bata lokaciba suka bi wannan umarni suka shige izuwa cikin duhuwar ciyayi da bishiyoyi wadanda ke nesa kadan da kofar gidan gonar inda ba a iya hangosu.
Da shigar su wannan wuri sai suka sauko daga kan damakansu kowa ya zauna a kasa dirshan cikin alamun karayar zuciya aka yi tsit tamkar babu mai laka a jikinsu.
Tsawon yan dakiku dayansu baice uffan ba kowa yana tunani, a sannane hunzalu ya dubi yarima Huzaifa yace, ya shugabana yanzu kana da wata dabara ne wacce kake ganin zamu iya amfani da ita wajen samun nasarar dauko Luhaira kuma mu fito a raye ba tare da mun fuskanci wata matsala ba?
Lokacin da hunzalu ya zo nan a zancensa sai Huzaifa yayi ajiyar zuciya sannan yace, a rayuwata ban taba samun karayar zuciya ba irin ta yanzu bisa duk abinda nasa a gabana.
Ina da yakinin cewa Allah zai iya bamu nasarar shiga cikin wannan gidan gona bisa taimakonsa, to amma bani da tabbacin cewar da yawan mu bazamu rasa rayuwarmu ba.
Abu na biyu shine, duk a cikinmu babu wanda yasan ainahin dai dai gurin da Luhaira take bare da zarar mun shiga ciki mu wuce kai tsaye izuwa wajen dole sai mun bata lokaci mai yawa wajen gano wajen ko kuwa hunzalu ka san inda aka ajiye Luhaira?
Humzalu ya gyada kai yace,ai kullum ai an sauyawa Luhaira dakin kwana a cikin gidan gonar nan, kuma a kallah dakunan sun fi guda dari uku, sannan kowanne daki tsakaninsa da wank akwai tazara ta a kalla tafiyar rabin saa.
Koda jin wannan batu sai zuciyar yarima Huzaifa ta sake karaya fiye da ko yaushe yaji kamar ya fashe da kuka saboda takaici, kawai sai ya dubi gaba daya dakarun yace, ku tashi muyi kokarin barin garin nan ba zamu iya shiga cikin gidan gonar nan ba har mu iya dauko Luhaira.
Tunda dai Allah ya sa ni da su aljani hurusul Marwas mun sami nasarar ceto rayuwarku ai mun sami gagarumar nasara ta farko.
Koda gama fadin hakan sai kowa ya mike da nufin a hau dawakai abi wata barauniyar hanya wacce zata kutsa dasu izuwa cikin daji.
Kwatsam! Sai suka hango badakaren nan wanda wakilin sarki ya tura can kurkuku domin yaga abinda ke faruwa bisa doki a sukwane ya durfafi kofar gidan gonar. Koda ganin haka sai hankalin su Huzaifa ya sake dugunzuma ainun domin sun san cewa da zarar ya iso bakin kofar gidan gonar ya tambayi labarin su asirinsu ya tonu kenan.
Ba zato ba tsammani sai kuma suka sake hango aljani hurusul Marwas ya sauko daga sama ya sure shi da dokinsa gaba daya yayi sama da su kamar shawo ya suri dantsako kuna dai ya lullubesu da fuka fukansa ya luluka da su izuwa can kololuwar sama.
Kafin kiftawar ido ya bace bat! Bayan yan dakiku sai gashi ya sake bayyana tsulum! A gaban Huzaifa.
Kawai sai ya dubeshi yace, ya shugabana ka yi mini izini ni kadai zan shiga cikin gidan gonar nan na dauko Luhaira cikin ikon Allah batare da asirina ya tonu ba.
Kuma a cikin dakiku kadan zan hattama wannan aiki.
Koda jin wannan batu sai Huzaifa yayi murmushi sannan yace, Yanzu ina kakai wannan badakaren da dokinsa?
Hurusul Marwas najin wannan tambaya sai ya mai da masa da martanin musmushin sannan yace ai tuni nayi aikin namu na aljanu.
Cikin jikinsa na shiga na komar da shi izuwa can wajen wakilin sarki ya shaida masa cewar yaje kurkuku da gidan gona ya tabbatar da babu wata matsala.
Bayan wakilin sarki ya sallameshi ya koma cikin yan uwansa bayi kuma sai na shafeshi na sa masa barci mai nauyi saboda ina tsoro cewar bayan na fita daga jikinsa zai iya dawowa cikin hayyacinsa ya koma wajen wakilin sarki ya sanar da shi ainahin gaskiyar alamari.
Koda aljani hurusul Marwas yazo nan a jawabinsa sai murna ta kama yarima Huzaifa da su Humzalu kuma suka Sam cikakken kwanciyar hankali.
Cikin faraa Huzaifa ya dubi aljani hurusul Marwas yace, tabbas Yanzu ne na dada tabbatarda cewa ni da kai duk muna bukatar juna kuma idan dayanmu baya tare da dayan to babu yadda za'ayi ya sami nasarar cika aikin da yazo yi a kasarnan.
Ya kai hurusul Marwas nayi maka izini maza ka shiga cikin gidan gonar nan ka dauko mini Luhaira.
Hurusul Marwas ya risina yace, an gama ya shugabana.
Kafin ya budi baki yace wani abu tuni aljani hurusul Marwas ya bace bat daga gabansa.
Nan fa tunanin zuci yace fadowa Huzaifa ya tambayi zuciyar sa yana mai cewa, menene dalilin da yasa aljani hurusul Marwas ya kirani da matsayin shugabansa a wannan karon alhalin tun daga lokacin da muka hadu dashi abokina yake kirana dashi?
Amsar da Huzaifa ya kasa baiwa kansa kenan, amma sai ya kudure a cikin ramsa cewar idan suka sami nutsuwa dai ya yi masa wannan tambayar.
Huzaifa na cikin yin wannan tunani ne kawai yaga aljani hurusul Marwas ya sake baiyana tsulum! A gabansa goge da Luhaira gadon bayansa amma ko ina a jikin hurusul Marwas sara ne na takobi sai jinine ke kwarara daga jikinsa.
Da rub da ciki aljani hurusul Marwas ya kife kasa yana numfashi sama sama, ita kuwa Luhaira dake kwance a bayansa, barci take ta faman sharara bata ma san abinda ke faruwa ba.
A dimauce, cikin tsananin firgici yarima Huzaifa ya dauke Luhaira daga kan bayansa. Hurusul Marwas ya shimfide akan ciyawa gefe daya sannan suka taru akan aljani hurusul Marwas suna yi masa magani gami da tofa masa adduoi domin su ceto rayuwarsa.
Sai da lokaci mai dan tsawo ya shafe sannan numfashin aljani hurusu Marwas ya dawo dai dai har ya iya bude idanunsa.
Koda ya tsinci kansa a gabansu Huzaifa kuma yaga Luhaira kwance a cana gefe daya tana ta shara barcinta sai ya yi kabbara cikin tsananin Farin ciki kuma yayi godiya ga Allah, sannan ya mike zaune ya dubi Huzaifa yace, ya shugabana burina na farko ya cika tunda har bukatunka sun biya bisa abinda kazo nema a garin nan.
Ka kubutar da dakarunku wadanda aka tsare a kurkuku sannan kuma ka dauko Luhaira.
Koda jin wannan batu sai Huzaifa yayi murmushi a gareshi yace, a'a gyara maganar ka, ba nine na dauko Luhaira ba kaine, kuma in ba don kai na da babu yadda za'ayi na iya daukota.
Gama fadin hakan ke da wuya sai hankalin kowa ya koma kan Luhaira wacce ke kwance akan ciyawa.
Nan fa su duka suka dimauce bisa ganin irin tsananin kyawun da Allah ya bata domin inda za'a hada kyawun gimbiya Lafirta dana yar uwarta Sazirat a waje guda bazai kai rabin ma Luhaira ba.
A wannan lokaci wata doguwar riga ce fara kal mai shara shara a jikinta, don haka duk surar jikinta a fili take, musamman ma idan iska ta kada rigar.
Cikin gaggawa Huzaifa ya cire alkyabbar jikinsa ya lullubeta da ita sanna ya dubi aljani hurusul Marwas yace, ya kai dan uwana yanzu menene abinyi?
Koda jin wannan tambaya sai hurusul Marwas yayi murmushi yace, babu abinyi face muyi sauri mu bar garin nan mu durfafi birninku na Darul husuf domin muje mu ga halin da ake ciki, walau anci nasarar yakin da ake yi ko ba'a ci ba.
Koda jin wannan batu sai Huzaifa yaji gaba daya hankalinsa ya koma kan birnin Darul Husuf.
Nan take ya sake daukar Luhaira ya dorata a gadon bayan aljani Hurusul Marwas sannan shima ya kama dokinsa ya hau, suma su Humzalu sai suka yi koyi da shi.
Nan take aka ci gaba da tafiya ana karanta wannan addua wacce yarima Huzaifa ya bayar tun da farko.
*wannan shine abinda ya faru ga su Huzaifa, bayan sun sami nasarar debo fursunoninsu daga kurkukun sarki shaaran kuma sun dauko Luhaira daga gidan gonar sa bayan sun sha bakar wahala da bakin gumurzu*

* * * * * *

Al'markin su sarki shaaran kuwa, bayan ya gama sanar da mahaifiyar ukashat duk abinda ya faru da kuma hukuncin da zai dauka na gaba wato neman taimakon dakarun yaki daga sauran kasashen kafirai na nahiyar don aje a yiwa birnin Darul Husuf rubdugu a gama da shi farat daya, sai ta kyalkyale da dariyar Fatin ciki sannan kuma ta tashe da kukan bakin ciki tace, tabbas dana ukashat ya ci amanata a matsayina na mahaifiyarsa, kuma ya bani kunya.
Lallai da hannayena zan kashe shi, amma kuma nayi matukar Farin ciki daka sami nasarar cin wannan birni namu da yaki cikin BAZATO!
Shawarar da zan baka itace, ka gaggauta shirin tafiya izuwa kasashen makwabtaka domin nemo dakarun gudunmawa na yaki amma kafin ka tafi ka bar jiran gari nan a hannuna.
Nayi maka alkawarin cewar kafin ma a sake yin yakin karshe zan kama sarki Uwaisul Karni da duk mukarrabansa sai dai ka dawo ka iskesu a cikin kurkuku a tsare.
Koda jin wannan batu sai sarki shaaran da yarda Sazirat suka kalli junan su sannan suka kalli mahaifiyar ukashat cikin alamun rashin yadda da gamsuwa, kawai sai suka koma gefe daya sukayi dan kuskuks.
Sarki shaaran ya dawo wajena ya dubeta yace, yake matar babban maki yina, kiyi sani cewa na yi shawara da yata Sazirat kuma mun yanke hukuncin cewar zamu bar Miki jiran birnin Darul Husuf a hannunki, amm bisa sharadi guda.
Sharadin kuwa shine, idan har da gaske zaki iya kama sarki uwaisul karni shi da mukarrabansa har ki tsaresu a kurkuku to mu dawo mu iske kan danki ukashat a tsire a jikin ice akan ganuwar garin nan.
Idan kuwa muka dawo muka ga babu wannan kai na Danko, to mun san cewa yaudararmu kikayi don haka zamu shigo cikin birnin ne da karfin tsiya mu sake yakarku kuma mu kashe kowa da komai ko kaza guda daya bazamu barta da rai ba.
Koda jin wannan sharadi sai hankalin mahaifiyar ukashat ya dugunzuma ainun saboda ta san cewa bazata iya kashe danta ba ko kuma ta sa wani ya kashe shi komai tsanar da take yi masa a rayuwarta.
Nan take ta nuna cewa zata cika wannan umarni, amma tan bukatar a bar mata kamar dakaru dubu dari wadanda zasu karta ta sami ikon tafiyar d komai kamar yadda ya kamata, sarki shaaran yayi murmushi yace, shikenan na amince da hakan.
Nan take ya ware dakaru dubu dari aka barsua birnin Darul Husuf sannan sarki shaaran, Sazirat da sauran dakarunsu suka yi shiri suka hau dawakansu suka fice daga cikin birnin suka nausa cikin daji a guje suka durfafi hanyar da zata kaisu birninsu na shumbul.

* * * * * *
Bayan kamar rabin sa'a da bacewar sarki shaaran a cikin daji, sai tawagar su sarki uwaisul karni ta bullo daga wata hanya daban ta durfafi birnin Darul Husuf.
Sarki uwaisul karni ne akan gaba tare da yarima ukashat.
Su da dukkanin dakarun dake biye da su sun yi shigar yaki ne dauke da makamai.
A wanann lokaci rana bata fadi ba amma magriba ta kawo kai.
Kafin a isa inda za'a iya hango kofar birnin sai sarki uwaisul karni ya ja linzamin dokinsa ya tsaya cak! Kuma ya bayar da umarnin a tsaya a wajen a kafa tantuna.
Alamarin da ya baiwa kowa mamaki ke nan, saboda bai kamata a tsaya a daji ba dag da magriba tunda ana dag da shia gari.

Alhamdulillahi, anan zan dakata kuma sai Allah ya kuma ara mana rana irin ta yau zaku jini dauke da ci gaban wannan Littafi.
[12/14, 6:53 PM] INSTRUCTOR⚓: **DAKARUN MUSULUNCI**
LITTAFI NA BIYAR 5
Chapter 4 · 0% Book details