Sashe 19
Canjin Rayuwa Part 4 Complete Hausa Novel · about 6 min read
6⃣2⃣Masallacinsu kam yana cika tantsam har ta harabar makarantar. Ganin haka sai Ismail ya kawo ma manyan malamai dasu Malam Aminu shawarar cewa, me zai hana su kafa asusun marayu don taimakon marayun dake unguwarsu da maqotan Unguwar. Suka amince. Shida Mahmud suka soma bada tasu gudunmuwar har yace ga ta yayarsa da kuma matarsa. Shi kuwa Mahmud harda ta dansa mus'ab ya saka. Daganan sai Ismail yace yanason kowa ya saka tashi sadakar a ranar na duk abinda Allah ya hore masa. Ranar dai yayi wa'azi ne akan falalar dake cikin taimakon marayu da tsabar ladar da hakan ke dashi. Kafin wani lokaci mutane sukayi ta zuba kudi, wadanda kuwa basuda shi sukayi alwashin kawowa gobe. Kafin sati daya saida takaisu ga bude asusu a Banki. Sbd, wadanda suke kallon wa'azin a TV kuma suna son su bada tasu sadakar. Wannan al'amari ya haskaka Ismail, amma dukda haka bai kasance daga cikin malaman da in daukaka tazo musu, zakaga sunayin girman kai ba. Yana bin duk malamin daya san zai samu qaruwa dashi, ko da kuwa ya girmi malamin. Hakanan ko qaramin yaro ya nuna masa kurensa a harkar karatu yana kar6a. Sannan ko yau yayi tafsir, bayan ya tashi wani yace masa, jiya fa kaza ba daidai bane, in ya dawo gobe zaiyi bayani cewa jiya nace kaza, ba daidai bane, wani dan uwa yayi min gyara. Haka nan shi yayi imani cewa, daukaka ta Allah ce, ba wai iliminsa ne ya kaishi ba. Daukaka daban, ilimi da hikimar wa'azi daban. Ismail ya zama cikin uzurin da sai yayi kwanaki baije gidansu Mimi ba. Ita kuwa Mimi sai take zargin ko don yaga ya soma zama wani abu shine zaija baya dasu. Yau kwana uku tanason ganinsa don taji wacece matarsa din daya bada sadaka harda ita. Amma baizo ba, saidai su ganshi a TV in yana tafsir ko lacca, wadda aketa faman gayyatarsa. Yana yiwa maza ko mata, wata lacca da aka nuna yayi wa mata mai taken Ramadan lacca. Tasha mamakin yadda yake fadawa mata su riqe mazajensu, da hanyoyin kula da miji. Ya kuma kwadaita musu irin romon ladan da zasu samu a gurin mahaliccinsu. Sai taga duk ta zama wata sokuwa, domin ita kanta da take macen bata san abubuwan dashi ya sani ba, na game da yadda ita kanta mace zata kula da kanta. Ta jima tana Mamaki, kuma ta sake yarda Ismail ya dara kallon da takeyi masa.6⃣3⃣Shikam Ismail yakan kira yaya Amina su gaisa, yaji lafiyar Mimi a gurinta, kuma tana sanar da Mimin, domin bashida lokacin kansa. Ba su suka ga Ismail ba, sai azumi yana ashirin, misalin qarfe uku, lokacin Ummi tana daga citta zata kai niqan geron kunun tsamiya, ta gai dashi. Ya amsa tare da cewa, ina mamanki? Mimi qin dago kai tayi. Ummi tace, tana ciki. Yaya ce ta fito tana fadin dan gyangyadi ne ya soma dauka ta, sai kuma naji muryarka sama-sama. Yace, nine kun ganni sai yau. Ya saci kallon Mimi, cikin zolaya yace, 'yar amanata ma na lura fushi takeyi dani. Ko kallo ban isheta ba. Mimi ta dago ta dubeshi, ya dan rame, hakan sai ya qara masa kyau. Shaddar jikinsa mai tsada ce sosai, mai ruwan siminti, hular kansa ta dace sosai. Ta maida kanta taci gaba da firar dankalin da dama shi takeyi tun kafin ya shigo. Ta kammala ta kwashe 6awon sannan ta kai kicin ta wanke hannunta, duk yana kallonta, suna 'yar hira da yaya. Ta zo ta shige dakinta. Ya bita tare da cema yaya, bari inyi lallashi. Can saman Gadonta ta harde qafafun ta. Ya shigo da sallama,a ciki ta amsa. Ya tsaya a gaban gadon, "yau fushi kkyi dani? To, kiyi haquri. Ya ranqwafo tare da sa hannuwansa duka biyu ya dafa gadon. Kinji. Sam ta kasa fada masa cewa, rashin ganinsa ne ya bata haushi. Sai ta kauda kai. Yace, kullum ina fada ma yaya ta gaisheki, sannan ina fada mata uzururruka na, ko bata fada miki? Ta turo baki, ni fa rashin zuwanka bai dameni ba. Cewa din dakai ni matarka ce. Ya zauna, na fada a ina? Cikin salon shagwa6arta ta nuna TV, "anan mana, daka bada sadaka, harma kace, da na yaya. Yayi murmushi, yana son salon shagwa6arta. Yace amma nace matata khadija? Ni fa nufina wadda zan aura. Ta ware idanunta ta kalleshi, zakayi aure ne? Yace eh mana insha Allah. Ta ta6a baki tare da cewa, Hu'um! Zuciyarta fal da takaici. Ta dubeshi, "to ni yaushe zamu rabu? Tayi tambayar cikin daurewar fuska yace, kinsan dai ko ba lokacin azumi ba, laifi ne mace ta nemi a sake ta, babban laifi ne ko!? Ta sake turo baki, ai shi ma alqawari cikashi abu ne mai kyau ko? Yayi murmushi, "haka ne, amma banda haramtaccen alqawari. Ina nufin kayi alqawarin laifi. Misali mutum ne yayi alqawarin aikata wani laifi da Allah baya so, to ba'ason ya cika. Tace, jiya fa naji kana cewa saki halasne, a cikin tafsirinka. Yace, sai kuma nace me? Allah baya sonshi, dukda halas ne. Na lura in kinyi ilimi nan gaba za'ayi fama dake kema.6⃣4⃣Yasa hannu cikin aljihu ya ciro kudi 'yan dari biyar-biyar. Yace zan sallameku sbd batun sallah dake gabatowa. Tace, ai yaya zaka bawa kudi. Ni ina zuwa kasuwa? Yace, nima bance kije kasuwa ba ai. Tace, to naga zaka bani kudi ne. Yace na fasa baki ki shirya gobe muje tare. Tace, kana son sole sai wanda ya sanni ya ganni kai kam. To shikenan, ki rubuta min abinda kk so. Ya miqe ya shiga dakin yaya ya qirga dubu goma ya bata, yace ta saima yara kayan sallah. Tayi godiya tare da cewa, kaima da kk fama da kanka. Kaima fa dalibi ne har ynxu. Yace wani bawan Allah ne ya sameni nayi masa bayanin yadda zai fidda zakkarsa, shine da ya cire ya bani. Yaya tace, Allah ya taimaka. Ai ranar da kayi wa'azin zakkarnan, dole zukatan mutane su raunana, indai da sauran imani, su fito da zakkar su ba da. Yace kinsan kudi shiga zuci ne dasu. Sai su dinga ganin kamar in sun bada zakka kudin zai qare. Ba su san in sun cire haqqin Allah daga cikin dukiyarsu ba, Allah zaisa musu albarka, qila ma tafi ta da. Tace, rannan ma munji ka bada sadaka harda mu. Allah ya saka da alheri. Yace, Amin. Tare da miqewa. Ya koma dakin Mimi, "bani in kin rubuta. Ta miqa masa 'yar guntuwar takarda. Ya amsa, ya bude. Sai yaga ta rubuta cewa, duk abinda ya sauwaqa. Ya kalleta, zuciyarsa dajin dadin hakan da tayi. Yace nasan ba zan iya sai miki abinda kk so ba, amma zanyi iyakacin qoqarina. Ya juya ya fita. Kwana uku bayan nan, Ismail yazo Gidan da safe, misalin qarfe takwas, Mimi tana varcin safe. Ya gaisa da yaya sannan ya shiga dakinta. Bai mata dogon kallo ba, ya aje ledar hannunsa ya duba durowar gefen gadonta ya dauko takarda da biro ya rubuta cewa, ga kayan nan, in kin farka ya ke mai yin kyau a varci. Ya dora takardar a tafin hannunta. Sannan ya fice, yayi sallama da yaya ya wuce.
[25/09 9:28 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa
[25/09 9:28 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa