← Book details Beelal Buk Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 13

Sashe 4

Beelal Buk Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hahahaha ai dole ne a sha man amarya ko da taƙi" Imran ya faɗa.

*ƘAUYEN MAZARI*

~FATIMA~

Cikin bacci ta fara jiyo ana kiran sallar asuba, dan haka a hankali ta buɗe idanunta tana yamutsa fuska alamar mai bacci. Hannu ta kai gefenta domin taɓo Beelal sai ta ji baya nan, hakan ya sanya ta ɗauka ko ya gangara gefe guda ne da yake har lokacin akwai sauran duhu haske bai riga da ya fara fitowa ba.

Hannu ta kai inda take ajiye fitilar ta touchlight ta ɗauko, kunnawa ta yi ta haska amma abin mamaki haske na gauraye ɗakib sai ta ga wayam babu Beelal a inda yake kwance, bata kawo komai a ranta ba hakan ya sanya ta yi zaton ko fitsari ya fita duk da ta yi mamakin fitarsa fitsarin ba tare da ya tasheta ta raka shi ba ko kuma ya karɓi fitila ba.

Sai kawai ta danganta hakan da kawaici da sanin ya kamata irin na Beelal ta tabbata wataƙila dan ya ga tana bacci ya ƙi tashin ta ya gwammace ya fita fitsarin a duhu. Sai lokacin ta shiga karanto addu'ar tashi daga bacci (Alhamdulillahil lazi ahyana ba'adama amatana wa ilaihin nushur) Sannan ta miƙe ta fito daga ɗakin ganin shimfiɗar Idrisu ba ya kwance sai ta yi mamaki kar dai tashi ya yi dan zuwa ya yi jam'i a masallaci mutumin da ko kaɗan ibada bata dame shi ba shi dama jam'i ma ba zuwa yake ba a gida yake sallarsa shi ma ba a kan lokacin ba. Hamdala ta shiga yi tana ganin dama kwana biyun nan da ya yi da dawo wa ya canja mata gabaɗaya ba kamar yadda ta saba ganinshi ba, ashe dai canjin har na ibada. Addu'a ta shiga yi a kan Allah ya ƙara shiryar da shi ya gane gaskiya ya daina zaluntarsu ita da Beelal. Tun tana tsaye tana jiran fitowar Beelal daga bayi har dai ta fara haska fitilar daga inda take tana haska bayin tana karkaɗa fitilar tare da kiran sunan Beelal ɗin dan yanzu ta fara danganta shiga bayin nasa da kashi, dan tana ganin jimawar tashi ta zarce fitsari.

"Beelal ka kula ka fito mana mu yi sallar kar lokaci ya ƙure, kuma ma ka je ka shiga bayi babu fitila ai da ka tashe ni na baka fitilar" Ta faɗa da ɗan ƙarfi yadda zai ji. Jin shiru sai kawai ta ɗan ji gabanta ya faɗi amma bata kawo komai a ranta ba. Takalmi ta sanya ta nufi bayin cikin ɗaurewar kai dan ta san dai Beelal ko gyaran murya da ya mata, amma kuma shirun da ta ji sai ta fara tunani ko dai zamewa ya yi a bayin ya faɗi, wannan tunanin sai ya sanya gabanta mummunan bugawa a nan take sai ta ƙara sauri dan zuwa ta ga mai ke wakana. Addu'ar shiga bayi ta ( Allahumma inni a'uzu bika minal kubisi wal kaba'isi) Da mugun sauri ta afka bayin abin da ya ƙara sanya gabanta faɗuwa ganin bayin wayam babu alamar wani bil adama a ciki. Idanu ta zaro tana ƙwala kiran sunan Beelal ɗin tare da ƙara haske bayin wai ko idanunta ne basu gani dai dai ba amma sai ta ƙara gani babu ma wata alamar an shiga bayin, dan ko ɗigon ruwa ma babu.

"To ko dai Beelal da Babansa suka tafi masallacin?" Wani ɓangare na zuciyarta ya jefa mata tambayar.

"To kuma indai tare suka tafi masallaci to a ina suka yi alwala, tun da dai babu alamar ruwa ma ya taɓa bayin sannan ga butoci nan a cike kamar yadda na ajiye" Ta sake baiwa kanta amsa.

"Amma kuma Baban Beelal ba ya son ko kaɗan Beelal ya raɓe shi to ta yaya zai tafi da shi masallaci?"

"Kika sani ko ya canja ra'ayi, tun da dao kin ga tun da ya dawo ya sakar da fuska ba kamar da ba, kuma kika sani ko a masallacin za su yi alwalar" Wata zuciyar ta raya mata hakan. Wata ajiyar zuciya ta sauke jin wannan tunanin sai ta É—an ji hankalinta ya kwanta.

A haka ta daure ta yi tsarki ta gabatar da alwala duk da ba wai hankalinta ya kwanta bane dan ta san Idrisu ko kaɗan ba ya ƙaunar Beelal in dai ba ra'a yi ya canja ba duk da cewa wanda ya ce ba ya yi da kai to kuwa ba ya yi da kai ɗin ne har abada, duk wanda ya ce ba ya ƙaunarka to ba ya ƙaunarka ɗin ko da ya dawo daga baya ya ce yana sonka to tabbas ba lallai ya kasance so na gaskiya ba so na haƙiƙa ba. Shi yasa ma manzo S.A.W ya ce idan za ka so mutum to kada ka zurfafa son sa domin wata rana zai iya zama maƙiyinka idan za ka ƙi mutum kar ka zurfafa ƙinsa domin shi ma zai iya zama masoyinka. Allah haɗamu da ma su son mu da gaskiya amin.

A haka ta gabatar da salla tare da yin addu'o in ta kamar yadda ta saba, bayan ta gama sai ta shiga gabatar da azkar ɗin safiya, tana yi amma kuma tana jiran jin shigowar su Beelal, a haka har gari ya yi haske tangararai amma babu wanda ya shigo, so take ta tashi ta fita amma kuma bata so ta yi laifi a wajen Idrisu haka ya sanya ta ƙara daurewa. Zuwa can ta ji haƙurinta ya ƙare ba za ta iya cigaba da zama ba tare da ta ga Beelal ba dan haka cikin sauri ta fito daga ɗakin gabanta na dukan uku-uku dan ta san dai matsawar masallaci suka je da Idrisu kuma suka tsaya a masallacin ko kuma a wani wajen to tabbas ba za ta fita b a wajen Idrisu duk da yana mata ɗan faram-faram sai ya mata masifa amma haka ta daure dan ta san dai duk abin da zai mata nafila ne a kan halin da take jin zuciyarta tana ciki yanzu.

Tana fitowa ta ga ƙofar gidan a buɗe, haka ta shiga duba sawun amma abin mamaki sai take ta ganin sawun Idrisu babu na Beelal, sannan tun da ta fito daga gidan sai ta ga sawun Idrisu bai bi hanyar da masallaci yake ba, a hankali take bin sawun cikin faɗuwar gaba dan tabbas sai yanzu take jin hankalinta bai kwanta da kasancewar Beelal a wajen Idrisu tana bin sawun duk da tana haɗuwa da mutane jifi-jifi har da masu tambayarta ko lafiya. Amma bata da ƙwarin gwiwar amsa musu tambayarsu sai dai kawai ta gyaɗa musu kai, ganin sawun Idrisu ya nufi hanyar fita gari a take wata mummunar faɗuwar gaba ta ziyarci zuciyarta duk da ta kasa gane menene hakan ke nufi.

Mmn Afrah 09030283375

❤️❤️❤️❤️❤️❤️

*BEELAL*

💦💦💦💦💦💦

NA

MAMAN AFARAH

*FCW*💛

Book 2

page7️⃣➡️8️⃣

Idanu Fatima ta zaro cikin tashin hankali, tun da dai ta san ita ma da ta tashi da asuba bata ga Beelal ko Idrisu ba, to kenan tun kan asuba suka fito, ko kuma ma ya aka yi bata ganin sawun Beelal sai na Idrisu kawai, wannan tambayoyin take jefawa kan ta hankali tashe, dan ita dai ta san waye ɗanta babu yadda za a yi Beelal ya fita ko da nan da ƙofar gida ne bai faɗa mata ba, ko da, da rana ne bare kuma dare bare ma Beelal ba ya yawo dama gidan su Hameeda ne yake zuwa amma tun da iyayenta suka mutu su kuma wanda take hannunsu wato Yayan mahaifinta da matarsa sun tsani Beelal ɗin ya raɓi Hameedar ma ban da ma uwar wahalar da suke bata kamar baiwa, bare ma yanzu ta kwana biyu bata ga Hameedar ba gashi ko gidan ta je matar gidan ta ringa ci mata fuska, kuma ba za ta bari ta ga Hameedar ba hakan ya sanya ta daina zuwa.

Wani uban birki ta ja ta tsaya ganin sawun Idrisu dai ya nufi hanyar barin gari ko lanƙwasa babu gashi kuma ta ma rasa wane irin tunani za ta yi ta ina za ta fara. Hawaye ne suka shiga zarya a fuskarta wani irin jiri ta ji ya fara juyawa da ita hannu ta miƙa ta dafe wani maina da ke kusa da inda take tsaye.

"Wai ni ke Fatima me kike dubawa a ƙasa ne ko kuɗi kika jefar ne, tun daɗewa kowa zai wuce ana tambayarki lafiya amma sai ki ɗagawa mutane kai kamar wata ƙadangaruwa, kuma lafiyar ce ta sanya yanzu kike zubar da hawaye har kina neman faɗuwa sai da kika riƙe maina" Cewar wani matashi da yake mata magana cikin muryar ƴan shaye-shaye sai wani tangaɗi yake idanun nan jajawur.

" Wayyo Allah na Beelal nake nema wallahi ban ganshi ba da na tashi"
Wani uban tsaki ya ja sannan ya ce

"To kuma menene dan baki ga wannan mai ƙafa a lanƙwashen ba, ke ba ma kya ganin irin baƙin jinin da yaron nan ya jawo miki a garin nan tun da kika haifeshi amma har wani ruwan hawaye kike dan baki ganshi ba ai na zata mur...

"Ba wai na faɗa maka bane dan ka ci mini mutunci, kamar yadda kowacce uwa take so da ƙaunar ɗanta to haka ni ma nake matuƙar ƙaunar nawa ɗan in ma ban fi wata uwar ƙaunar ɗana ba, kuma wani baƙin jini a wajen mutane bai dameni ba dan jahilci ne yake damunsu suna mantawa da cewa Allah shi ke halittar mutane shi ke yin kowa yadda ya so shi ke barin kowa a yadda ya so babu wani mahaluƙi da zai ja da ikon ubangiji ko ya canja halittar ubangiji ko da kuwa ta kiyashi ce bare kuma ta ɗan adam, dan haka ina ƙaunar Beelal ko da kuwa gabaɗaya mutanen duniya za su tsane ni su ƙyamace ni, ni na san ubangijina yana so na, kuma yana sane da ni, sannan soyayar ubangiji a gareni ne yasa ya bani Beelal bayan ya hana miliyoyin mutane haihuwa ni kuma ya bani dan haka ina daɗa gode masa a bisa ni'imarsa gareni" Ta ɗora da cewa
Chapter 4 · 0% Book details