← Book details Beelal Buk Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 13

Sashe 2

Beelal Buk Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Shegen ina yinka nawan wallahi ai kai fa kan ka na ja ba kamar nawan ba amma in jika, gaskiya ka mana babban kamun da za mu daɗe muna mora tabbas wannan duk inda ya shiga zai samo sadaka, baka ma ganin yadda tsofaffi wanda ma basu da nakasa suke samo sadaka irin waɗan da ke zuwa neman kuɗi daga arewa da sunan bara, ka ga tsohuwa ta takarkare tana zabga waƙar bara ƴar jagora tana mata amshi kuma fa ita ba gurguwa ba, ba makauniya ba babu wani ɓangare na jikinta da yake a nakashe amma kuma sai ta maida hakan hanyar samun kuɗi, kuma wallahi sosai suke samun kuɗi, ka gansu idan suka tashi tafiya gida arewa sun koma da maƙudan kuɗin da ba lallai ne wanda suka zo nan ɗin da sunan neman kuɗi ba su samu ko da rabin hakan ne"

Imran ya kai ƙarshen maganar yana kallon Idrisu.

" Kai ai sai yanzu nake jin mugun daÉ—i da na taho da yaron nan, dan na san tsuntsunmu zai kama tarko"

"Sosai ma kuwa"

"Kai gurgun mage ƙaraso ka zo nan" Idrisu ya faɗa yana kallon Beelal da ya takure daga wajen ƙofa ya ƙi shigowa cikin shagon.

Haka ya janyo ƙafarsa ya ƙaraso wurinsu, ga ɗakin ban da warim sigari baka jin komai.

"Kai idan za ka saki jikinka ka saki jiki, dan nan fa shi ne garin da za ka cigaba da rayuwa a cikinsa, idan kuma ba haka ba za mu ladabtar da kai ta ƙarfi da yaji" Imran ya faɗa yana yiwa Beelal wani kallo na tsana da tsangwama.
Beelal dai kansa a sunkuye yana durƙushe a gabansu.

"Ka ɗago ka bamu amsa mu ba ma son wannan munfurcin sadda kan irin na uwaka" Idrisu ya faɗa cikin ɓacin rai.

"Zan yi Bab...

"Ba?" Cewar Idrisu yana kallon Beelal da mamaki, dan ya san dai É—azun nan ya gargaÉ—esa a kan kiransa da suna Baba .

"Gaskiya da sake abokina ya ma za a yi wannan abin yake kiranka da Baba son ya ja ake kallon mu ai wannan abin kunya ne wallahi" Cewar Imran

"Ni ban san ya zan ke kiranka ba, ba zan iya faÉ—ar sunanka ba" Cewar Beelal yana hawaye ganin duk sun tsare shi da ido.

"To haɗi garemu dan ka kirani da sunana ni fa na faɗa maka na janye dukkan alaƙa d dangantakar tsakani na da kai" Cewar Idrisu.

"Kawai yake ce maka Alhaji, ko da wani ya ji ya kiraka da hakan zai É—auka taimakonsa yake kuma wannan suna ne mai É—aga daraja kawai yake kiranka da haka" Imran ya faÉ—a yana kallon Idrisu.

"Amma na ji daÉ—i da ka samo min wannan suna to kuwa ba ni kaÉ—ai zai ke faÉ—awa ba kai ma haka zai ke kiranka" Cewar Idrisu yana murmushi.

"Kai tanƙwashen kifi faɗi mu ji, dan yadda ƙafa da hannun nan naka suka sha kwana sai suka min kama da kifi tanƙwashe" Imran ya ce yana kallon Beelal.

"Alhaji" Cewar Beelal ƙwalla na taruwa a cikin idanunsa.

Hahahahaha gabaɗaya suka ƙyalƙyale da wata irin dariya kamar mahaukata sabon kamu.

MMN AFRAH 09030283375

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

*BEELAL*

💦💦💦💦💦💦

NA

MAMAN AFRAH

Book 2

*FCW*💛

Page3️⃣➡️4️⃣

"Yanzu ka san me za a yi abokina?" Imran ya faÉ—a yana kallon Idrisu.

"Sai ka faÉ—a"

"Ka san akwai keken guragu a cikin wancan rufeffen shagon na wannan gurgun da suke zaune a cikin shagon da ya mutu, sauran ma suka fasa hayar shagon to tun da ba wai so ake ba shi za mu É—akko shi wannan sai yake hawa"

"Kamar ya yake hawa, bayan yana tafiya gani nake duk inda zai je kafin ya je a keken ya je a ƙafa, kuma ma so kake ka sauƙaƙa masa tafiyar ya zama yana yin barar yana samowa a ɓagas ba zai san zafin nema ba kenan? Ai gwara dai yake yawo da ƙafafunsa duk da dai ba wata tafiyar kirki yake ba sai ka je wuri sau goma ka dawo ka tarar da shi yana hanya bai je ba"

"Haba ka gane mana ba wai dan ya samu hutu za a bashi keken ba ka san yanzu idan aka ganshi zaune a keken kuma hannu da ƙafa a lanƙwashe za a ɗauka gurgu ne a haka sai ya fi samun sadaka, a kan a ce da ƙafarsa aka ganshi"

"Shege Baaba wallahi kwanyarka na ja amma a wajen son samu fa" Idrisu ya faÉ—a yana baiwa Imran hannu suka kashe.

"Wallahi nake faɗa maka ko kaɗan ni ma kawai jin maganar na yi ta sauka a kwanya ta ba tare da dogon nazari ko tunani ba na ce bari dai na faɗa maka tun da dai na san ai ni da kai bata ɓaci"

"Ai tuni ma an gama yanzu je ka fito masa da keken ya hau ya fara fita tun yanzu ka san da zafi-zafi a kan daki ƙarfe"

"Kai Idrisu wutar cikin naka ta yi yawa yanzu daga zuwanku kake cewa ya tafi bara ko hutawa baku yi ba kuma bai samu komai ya ci ba, kuma ma na ɗauka sai an ɗan nuna masa wajejen zuwa tun da ba inda ya sani kar ya je ya ɓata a shiga tara" Imran ya faɗa yana kallon Idrisu.

"Kai ka jika da wani zance, to me ma za a bashi ya ci ai sai ya nemo mu ma za mu ci, kuma da kake cewa daga zuwanmu, zai fara fita to ma wai shin mai za a fasa mutuwa ko hisabi? Kuma zancen ɓata a shiga tara ai ko uku ba za mu shiga ba dan ya ɓata Allah raka taki gona gaba ta kaini gobarar titi na huta da yiwa gyatumarsa bayanin dalilin da ya sa na tafi da duk da dama ba wai tsoronta nake ba, shi idan ya ɓata sai na nuna ba ni ne na tafi da shi ba"

"Ni fa ba wai rasa shi ne tarar da za mu shiga ba, to in dai zai ke samo mana kuma a rasa shi dole mu shiga tara tun da haryar samu ta toshe mana"

" Kuma fa haka ne, amma yanzu idan ya hau keken mu za muke tafiya yana bin mu a baya sai mu kai shi inda za a fi samun sadaka muna daga gefe a tsaye kamar ba tare muje d shi ba idan muka ga ya tara mana abin da muke so sai mu dawo" Idris ya faɗa yana dariya. Shi dai Beelal yana nan durƙushe bai ce komai ba kansa sunkuye a ƙasa yana sauraren duk abin da suke cewa.

"Bari na ɗakko masa keken" Imran ya faɗa yana miƙewa tsaye.

"Zan yi a hakan ba sai da keken ba" Beelal ya faÉ—a cikin in'innarsa.

"Kai dalla rufewa mutane baki, kai har wani zaɓi ne da kai, wato kai ma duk a yadda kaken nan a nakashe ta ko ina har kana ƙyamatar hawa keken guragu dan kar a kiraka gurgu ko?" Idrisu ya faɗa yana hararar Beelal da kansa ke sunkuye.

"Ba haka bane Alhaji, ni da a ce ma bani da nakasa ba na jin zan ƙyamaci kowane irin halittar Allah kawai dai tun da Allah ya mini ni'imar samun ƙafa ina tafiya bai kamata in hau keken guragu ba, in ɓata ni'imar da Allah ya mini ta ƙafafu bayan ni ba gurgu bane saboda kawai in samu abin duniya sai na butulcewa baiwa da ni'imar da Allah ya mini" Ya faɗa cikin in'innarsa yana ɗago kansa a karo na farko ya sanya idanunsa cikin idanun Imran.

Wani uban haushi ne ya turnuƙe Imran cikin zafin nama ya ɗaga hannu ya kaiwa fuskar Beelal wani gigitaccen mari, Beelal ma cikin sauri ya duƙar da kansa ƙasa, Imran ya mari iska, ganin iska ya mara bai samu fuskar Beelal ba daga Imran har Idrisu suka tsaya kallon -kallo da mamaki.

"Kai har ni ka ɗaukewa kai na mari iska" Cewar Imran cikin ɓacin rai.

"Ni ma mamakin da ya kasa barin raina kenan" Idrisu ya faÉ—a cikin mamaki.

"Ai ban yi laifin da za a mare ni ba" Beelal ya faÉ—a cikin in'innarsa.

"Lallai ma yaron nan, kai da kake a ƙarƙashinmu sai yadda muka yi da kai kana garin da baka da kowa baka da uwa ba uba babu dangin iya bare na Baba amma har kana da ƙarfin gwiwar butulcewa umarni ko tsallake abin da muka yi niyyar yi?" Imran ya faɗa yana wani zare idanu.

"Bani da kowa amma ina da Allah, shi ke tare da bayinsa daɗi ko wuya, shi ne wanda baya gajiya da buƙatun bayinsa, shi ne yake bayarwa ya ƙara kuma yana tare da duk wanda bai manta da shi ba" Beelal ya faɗa hawaye na kwaranyo masa saboda gabaɗaya abin da yake faɗa daga ƙwalƙwalwarsa yake tahowa domin gabaɗaya kalaman Mamarsa ne wanda take faɗa mas suke zama daram a ƙwalƙwakwarsa.

"Lallai gurgun mage ka ga makwancinmu wato har kai ma kana iya musayar yawu damu, a haka bakinka babu daÉ—i kana magana da in'inna har kana rufe idanu saboda in'innar amma a hakan kake faÉ—ar ra'ayinka"

Cewar Idrisu da mamaki fal a fuskarsa. Shi dai Beelal bai ƙara cewa komai ba.

"Rabu da shi abokina da mu yake zancen, keke ne dai ko ba ya so sai ya hau dan shi da gurgun ni ban ga maraba ba" Imran ya faÉ—a yana fitowa daga shagon domin É—akko keken a É—aya rufaffen shagon.

"Dan Allah Alhaji ka yi haƙuri ka ce kar ya ɗakko keken nan, ya kamata ɗan adam ya zama mai godiya ga ubangajinsa a duk yadda Allah ya haliccesa, Allah ya bani ƙafafu bai kamata nake yawo a keken da duk wanda ya ganni zai yi zaton bani da ƙafa ni gurgu ne, kuma in har a ƙafartawa ma nake iya rabona kawai zan samu a barar babu wanda zai haɗa min da rabon wani...
Chapter 2 · 0% Book details