← Book details Beelal Buk Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 13

Sashe 12

Beelal Buk Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hakan ne ya bata damar riƙe pant ɗin nata gamgam taƙi sakawa, dan duk da ƙarancin shekarunta amma bata manta yadda Ummarta ke nuna mata kar ta yadda wani ya cire mata wando bare har ya taɓa mata wajen fitsarinta, da yake komai yana zama ne a ƙwalƙwalwar yaro shi yasa bata manta da hakan ba duk da cewar mahaifiyar tata bata duniya amma tarbiyar da ta bata tana nan zaune daram a ƙwalƙwalwarta, shi yasa ake son kar ka raina ƙanƙantar yaro ka ce wai sai ya ƙara girma zan koya masa abu kaza da kaza shi yaro abu yana zama a kwanyarsa fiye da yadda zai zauna a kwanyar babba. Dan abu a kwanyar yaro tamkar rubutu ne a kan dutse baya goguwa saɓanin abu a kwanyar babba da yake kamar rubutu ne a kan ruwa gogewa yake.

Ganin ƙaramar yarinya na son wasa fa damarsa da kuma lokacinsa sai ya sanya mugun ƙarfi ya fisgi wandon nata daga gefe guda cikin nasara kuwa sai pant ɗin ya yage daga kan ɗinki, amma dan ƙarfin hali irin na Hameeda sai ta ƙara riƙe saitin da ya yaga mata, cikin fusata ya sanya hannu ya hankaɗata ta faɗi reran a kan gadon, haka ya haye kan gadon jikinsa babu kaya sai ƙaramin wando dan ya sanya a ransa a yau sai ya biya buƙatarsa da yarinyar dan shi babu abin da ya fi masa sama da ya kusanci ƙananan yara ya lalata musu rayuwa babu ruwansa su yi rai ko su mutu.

"Mustapha, Mustapha,Mustapha" Musty ya jiyo muryar Mom tana ƙwala masa kira daga falo kamar ta ari baki, wani irin miƙewa ya yi tare da sakkowa daga kan gadon cikin ɗaga murya ya shiga amsawa a lokaci guda kuma yana ƙoƙarin maida kayansa. Hameeda zaune ta tashi a kan gadon tare da kama wurin da ya yaga mata wandon ta shiga ƙullewa ta ja rigar tana rarraba ido, yana gama maida kayansa hakan ya yi dai dai da kama handle ɗin ƙofar da Mom ta yi domin buɗewa jin ƙofar a rufe sai ta shiga nocking tana kiran sunan Musty.

Musty kuwa gabaɗaya hankalinsa a tashe yake bashi da wata nutsuwa ko ƙwayar zarra a yanzu gabaɗaya hankalinsa ya ɗugunzuma zuwa maɓoyar da zai sanya Hameeda a ciki, waige-waige ya shiga yi har dai ya samu wurin da ya ɓoyewa ta tare da zare mata ido ya mata gargaɗi a kan kar ta kuskura ko tari ta yi bare magana ko kuma ta yi yunƙurin fitowa. Sai da ya murje idanunsa suka yi ɗan ja sannan ya buɗe ƙofar yana wani yamutsa fuska irin ta mai bacci, Mom kuwa gadan -gadan ta nufi shigowa ɗakin sai matsawa ya yi ya bata hanya ta wuce ciki shi ma ya mara mata baya.

A jikin mudubi ta ɗan jingina da katakon ta zubawa Musty ido da ya ƙaraso yana sakin wata uwar hamma ta mai bacci amma baccin ƙarya, ya samu bakin gadon ya zauna yana fuskantar Mom ɗin.

"Wai yaushe ma ka dawo? Ina aiken da na maka? Kawai sai motarka na hango kuma ashe har kana nan kana bacci"

"Kaina ke mini ciwo Mom ina dawo wa ban samu ƙarasawa ɓangarenki ba na zo na kwanta dan in ɗan ji sauƙi shi ne bacci ya samu nasarar ɗibana" Cewar Musty cikin muryarsa ta baccin ƙaryar da ya ƙirƙira.

"Ayya sannu ni fa in ce ashe dai akwai abin da ke damunka shi yasa baka je ka faÉ—a min aiken ba"

"Eh, eh, eh" Cewar Musty da ke ƙoƙarin bai wa Mom amsar sai dai haɗa ido da hijabin Hameeda da ya yi wanda ke yashe a ƙasan ɗakin ya sanya gabansa mugun faɗuwa har hakan ya sa maganar da yake son yi ta zama inda-inda

shi bai san dalilin da yasa yarinyar bata ɗauke wannan ƙazamin hijabin nata ba, kuma shi ma da yake ba a nutse yake ba burinsa kawai ya ɓoyeta sai bai lura da hijabin ba, gashi tana neman ta jaza masa jaraba a kansa, dan idan Mom ta ga hijabin ai asirinsa ya gama tonuwa . Cikin sauri ya faki idon Mom ya sanya ƙafarsa ya tura hijabin ƙasan gadon ba tare da Mom ta lura da abin da ya yi ba.

"Eh me?" Ta tambaya tana kallonsa dan ta ga ya É—an ruÉ—e sai dai bata san dalilin hakan ba.

"A'a cewa na yi eh akwai abin da ke damuna, amma ai na karɓo miki saƙon naki"

"Ohk yana ina?"

"Yana falo a kan kujera, dama nufina idan na ji ɗan dama-dama sai na miƙa miki"

"Ayya sannu bari in ajiye maka wannan sai in ɗan barka ka huta in na fita na ɗauki saƙon nawa" Ta faɗa tana barin jikin mudubin tare da yin hanyar bayi da wasu robobi guda biyu a hannunta da sai yanzu Musty ya lura da su amma ya ta,allaƙa hakan da rashin nutsuwar da yake ciki da kuma ruɗu shi ya sa bai ga robobin ba.

A sukwane ya tashi daga bakin gadon da yake zaune, wanda shi ma bai san hakan ba sai dai ganinsa da ya yi tsaye cankarkar a kan ƙafafunsa yana zare ido kamar wanda ya yiwa sarƙi ƙarya dama ƴan magana sun ce marar gaskiya ko a ruwa gumi yake. Aikuwa cikin sauri ya sha gaban Mom yana ƙirƙirar dariyar yaƙe ya ce

"Mom mai za ki yi a bayina kuma?"

"Haba Mustapha kai da baka da lafiya ya za ka taso, kuma ma mai zan yi a bayi wurin da ba kicin ba shi ba ɗaki ba, wannan robobin da kake gani shampoo ne da conditioner wanda na maka odar ɗinsu kwanaki sai jiya suka ƙaraso to shi ne zan ajiye maka" Ta faɗa tana ɗaga masa robobin hannun nata.Kafin ya haɗa kalmomin da zai rinjayeta ta fasa shiga bayin ta kewaye shi ta nufi bayin gadan -gadan.

_FATIMA_

"Tambaya nake dama?"

"Tambaya kuma" Matar ta tambayi Fatima cikin mamaki.

"Eh tambaya nake, wani nake nema sunansa Idrisu" Ta faÉ—a tana kallon matar.

"Ikon Allah wato dai matar nan ke ba ma ki san wanda kike tambaya ba ko wani ne ya ce miki a nan wurin yake zama?"

"A'a ni ban sani ba, hasali ma daga arewa na taho nemansa mijina ne" Cewar Fatima cikin sanyin murya.

Tabbas ta ƴan magana ne da suka ce in da ranka kasha kallo, in ba ƙarfin hali ɓarawo da sallama ba ma za yi ki taho tun daga arewa ki zo neman mijinki, bayan in ban da rashin godiya irin na wasu matan mijinki ya barki ya taho nemo muku abinci, amma ki biyo shi, saboda son zuciya da kishi gani kike nan ɗin wani saɓon Allah yake aikatawa ko wani abun da ban wanda bashi ya zo yi ba, to yanzu ko zaki yi shekara kina zaga garin Lagos ai ba za ki ganshi ba" Cewar ɗaya daga cikin masu cin abinci a wurin.

"Ikon Allah wai mai yasa mutane suke da saurin yanke hukunci ba tare da sanin ainihin gundarin magana ba? Daga tambaya kai baka san mai ya baro da ni gida ba har na biyo shi amma ka saki baki kana ta faɗar maganganu mararsa kai da ƙafa, Allah na tuba idan ba dalilin Beelal ba ni mai ma zai sa na ɗakko hanya na biyo bayan Idrisu tun daga arewa zuwa kudu, to ma kishin mai zan yi? Mutumin da bai sauke nauyin haƙƙinmu a kansa bane har zan ɓata lokacina wajen yin wannan doguwar tafiya da bibiyar rayuwarsa, ai komai ya yi kansa kuma kowa ya aikata da kyau zai ga da kyau"

"Malama ki bar nan ki ƙara gaba ko kya samu wanda za su ɓata nasu lokacin a kanki, amma ba dai a nan ba" Matar nan ta faɗa wanda hakan ne ya katsewa Fatima zancen zucin da take. Cikin sanyin jiki ta juya ta bar wajen, tana jiyo muryarsu suna ta faɗar son ransu a kanta.

Haka ta dinga tafiya tana ta kalle-kalle tana fatan Allah sa ta yi gam da katar na haɗuwa da tilon ɗanta a hanya, amma haka ta karaɗe wajen gabaɗaya amma ko mai kama da Beelal bata gani ba sai dai ta sha ganin masu nakasa a hanya wanda hakan ke sanya ta ji raunin zuciyarta ya ƙaru sannan damuwar son ganin Beelal ɗin ta ninku a ranta.

Har ƙarfinta ya ƙare amma bata samu cimma burinta ba na ganin Beelal ko kuma Idrisu wanda zai sada ta da Beelal ɗin. Duk lokacin sallah ta kan siya pure water ta yi alwala ta gabatar da sallah, a haka har ta ƙaraso wata unguwa mai shiru kamar ba mutane kowa yana cikin gida sai mutane jifa-jifa da ke ɗan wucewa, lokacin ana kiran sallar magriba ƙarewa unguwar kallo ta tsaya yi kamar mai son gano wani abu, daga ƙarshe dai ta samu ƙofar wani gida wanda ke da benci a wurin ta yada zango a kan bencin.Shiru ta ɗan yi a ranta tana ƙiyasta ina ma za ta hango Beelal yanzu da bata san irin farincikin da za ta tsinci kanta a ciki ba, amma ina... Hakan bai samu ba a haka ta yi alwala da sauran pute water guda ɗaya da yake wurinta ta shimfiɗa ɗankwalinta ta gabatar da sallar ta yi addu'o inta a kan samun nasarar abin da ta zo nema wato ɗanta.

Tana nan zaune a wajen har aka kira sallar ishsha'i, ta yi sallar ishsha'in bayan ta kammala ta koma kan bencin ta zauna ta lula duniyar tunani.
Chapter 12 · 0% Book details