← Book details Beelal Buk Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 13

Sashe 11

Beelal Buk Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Imran na ƙarasawa inda Idrisu yake suka bar wajen suka koma ƙasan wata bishiya kusa sa wata mota suka zauna suka cinye abincin suka sayi pure water suka sha abinsu.

"Gaskiya abokina ba ƙaramar dibara ka mana ba da ka taho mana wannan annakasun" Cewar Imran yana cilla ledar pure watern da ya gama sha, sama ya bugata da ƙafarsa ta yi gefe guda.

"Ai nake faÉ—a maka sai da na yi dogon tunani kafin na yanke hukuncin" Idrisu ya faÉ—a yana wani washe baki jin abokinsa ya yabe shi da abin da ya yi.

"Aikuwa dai ka ceto mu daga yunwa da rashin kuÉ—i, ji fa yanzu ba ko asinmu amma mun ci mun sha har da kuÉ—in kashewa gashi za mu raba, dan ma dai na ga kamar har yanzu bai saki jikinsa ba yana É—ari-É—ari da abin da za mu samu ma ya fi haka"

"Rabu da shi zai ware ne, yanzu dan farko ne amma idan ya ga dole uwar naƙi dole ya rage dantse ya samo mana ko dan ya ci shi ma, dan idan bai samo da yawa ba yana ji yana gani za mu cinye ɗan wanda ya samo ɗin" Idrisu ya faɗa yana dariyar ƙeta.

"Kana lokacinka nawan" Cewar Imran yana miƙawa Idrisu hannu suka tafa.

Beelal kuwa ganin sun karɓe abincin da kuɗin sai ya rasa ma ya zai yi dan yunwa yake ji kamar me gashi kuma la'asar ta yi sosai, haka ya shiga can ciki yana bin wurin sana'ar mutane yana tsayawa wani wajen a koreshi, wani wajen a tambayeshi mai zai siya, idan ya ce sadaka yake nema sai a hantareshi a ce barar ce kuma ba za kake yi da bakinka ba sai ka tsayawa mutane zoƙoƙo. Hakan ne ya sanya Beelal ɗin ya cigaba da tafiya sai dai yana bara saboda ya ga ba a bashi sadaka saboda ba ya bara dan haka babu yadda ya iya ba dan ransa ya so ba haka ya shiga faɗin.

"A taimakawa almajiri da sadaka, almajiri yana bara" Amma duk lokacin da zai ambaci sadaka sai ya ji wata ƙwalla ta kawo idanunsa saboda ya san dai ragas yake Allah bai masa nakasar da zai ke yin bara ba.

Cikin iko da hikima ta ubangiji sai kawai yake ta samun sadaka, dan sai ya ga jama'a ma kamar shi kaÉ—ai suke baiwa sadakar saboda idan ya ce

"A taimakawa almajiri da sadaka, almajiri yana bara"

Sai kuma ya ƙara da cewa.

"Duk wanda ya bayar domin Allah, Allah zai mayar masa fiye da abin da ya bada" Wannan hikimar d ya sanya a cikin barar tasa ita ce ta sanya mutane ko basu da niyyar bashi sadakar sai su bashi, shi kuma wannan hikimar maganar ya koya ne a wajen Mamarsa, saboda idan suna da ishashshen abin da za su ci, kuma sai almajiri ya yi bara to tana kiran almajirin ne ta bashi ko da a cikin wanda za ta ci ne, idan Beelal É—in ya ce

"Mama ya kika bayar da abincin da za ki ci kika bar É—an kaÉ—an?" Sai ta ce masa

"Beela ai duk wanda ya bayar domin Allah to Allah zai mayar masa fiye da abin da ya bada, ka ga kenan idan na bai wa almajiri sai Allah mu ma ya ƙara kawo mana ta wata hanyar da bamu yi zato ba" Wannan abin da take faɗa masa ne yasa yake saka hikimar maganar tata cikin barar tashi sai gashi kuma hakan ya sanya yana samun sadaka, lallai abin da uwa za ta koya wa ƴaƴanta ba iya lokacin zai musu amfani ba har da bayan wasu lokutan ma dan yanzu gashi Beelal ya yi amfani da abin da ya koya daga mahaifiyarsa ya samu hanyar samun bara cikin sauƙi.Tabbas tarbiya ba ƙaramin makami bane mai kyau da uwa take bai wa ƴaƴanta wanda wannan makamin zai amfane su duniya da lahira, mahaifya ta gari idan ta bai wa ƴaƴanta tarbiya mai kyau haƙiƙa tana jifan tsuntsu ne da dutse biyu, tarbiyar za ta amfane su duniya ne da kuma lahira.

Sai da ya ji an fara kiran sallar magriba ya fara tuƙo keken yana fitowa daga cikin jama'a, yana ta kallon yadda mata inyamurai ke ɗakko ƙaton baho ko daro a kansu cike da kaya, tabbas ya jinjina musu dan ya san hausawan mu ba za su yi haka ba. Yana fitowa ya hangi wurin da ya ga su Imran suna tsaye amma basa wurin hakan ya sanya ya rinƙa kutsa mutane ya samu ya fito ya samu gefe guda, cikin abincin da ya samu, ya sanya hannu ya fara ci, sai da ya ɗan ci amma ba sosai ba dan yana tsoron kar ya ci ya ƙoshi su gane ya ci su masa wani abun.

Ledar ya ƙulle ya rataye ta a jikin hannun keken nasa, masallacin da ke kusa wanda ya ji ana kiran sallah ya nufa yana zuwa ya ajiye keken a gefe guda, aikuwa sai da ya faki idanun mutane ya tashi tsaye daga kan keken gudun kar a ganshi da ƙafarsa a ce ya hau keken guragu mutane ba a iya musu duk da ma dai akwai nakasa a jikinsa amma ba wacce zai hau keken guragu ba. Wajen famfuna ya nufa ya yi alwala ya shiga masallacin sai da ya yi sallar la'asar dan bai yi sallah ba amma Idrisu bai damu da ya ce ya yi sallah ba ko abincin da zai sanya a cikinsa, ko dan shi ma Idrisun sallar ba damunsu ta yi ba. Ya idar da sallar kenan sai aka tada sallar magriba dan dama wa'azi aka gama a masallacin shi ne kuma za a yi sallah.

Bayan an idar da sallar ya yi addu'arsa sai ya fito ya ƙarasa wajen keken, idanun mutanen dai ya faka ya hau keken ya baro cikin masallacin, yana fitowa kwa ya hango Idrisu da Imran sai sintiri suke a wajen suna nemansa, hangoshi da suka yi, ya fito daga masallacin cikin hanzari suka nufo shi suna wani zare

"Kai gurgun mage ina ka tafi ka sa sai duba ka muke a wajen nan?" Idrisu ya jefa masa tambayar yana kallon ledar da Beelal É—in ya rataye a jikin keken wacce abinci ne da yawa a ciki.

"Masallaci na shiga na yi sallah, ko la'asar ban yi ba"

"To sallau, wato kai ga mai sallah to mu nan ko azahar bamu yi ba" Imran ya faÉ—a yana kallonsa.

Shiru ya yi shi dai Beelal bai ce komai ba dan shi in banda larura ma babu yadda za a yi ya haÉ—a salloli amma su gasu manya da su wai ko azahar basu yi ba kuma gashi yanzu har an yi magariba, kuma ko alamar yin niyya babu a tare da su.

"Kawo kuÉ—in" Cewar Idrisu.

Hannu ya sanya a aljihun nasa ya fito da duka kuÉ—in dan a farar leda ma ya sanya sannan ya sa a a ljihun. Su duka baki suka washe ganin har da Æ´an É—ari biyu guda biyu a ciki sauran kuma canjuna ne, lissafawa É—ari takwas ne da naira ashirin. Hannu Imran ya sanya a cire ledar abincin ya ce.

"Miƙo hannunka mu san maka abincin"

Hannu Beelal ya haɗe duka biyun Imran ya zuba masa abincin, Idrisu naira ashirin ɗin ta saman kuɗin ya miƙa wa Beelal ya ce.

"Karɓi wannan in ka tafi hanya ko za ka siyi wani abu ka ƙara" Abincin hannun nasa ya cinye ya karɓi ashirin ɗin.

"Ai dai ka ga inda muka biyo a tahowa, waccen hanyar inda da wancan motar yashin take tsaye, ka bi nan ka koma shagon namu, mu akwai inda za mu je" Cewar Imran yana kallon Beelal.

"To" Kawai Beelal ya ce ya juya kan keken nasa ya tafi, su ma suka kama gabansu. Wata mai soya dankalin hausa ya bai wa ashirin É—in ita ma da ta tausaya masa ganinshi a kan keken gurragu kuma ga in'inna kawai sai ta cika masa farar leda.

"Duk na ashirin É—in ne wannan" Ya faÉ—a da mamaki.

"A'a sadaka na baka sauran" Mai dankalin ta faɗa tana murmushi dan sai ta ji ya birgeta ganinshi mai nakasa kuma mabuƙaci amma kuma har yana buƙatar halal ɗinsa kawai.

"Allah karɓa, ai na ɗauka ko baki lissafa dai dai bane"

"Ina sane" Ta faɗa tana zubawa wani fa ya sayi dankalin a baƙar leda.

Haka ya kama hanyar da suka biyo da su Imran yake tafiya da yake ma unguwar duk jama'a ne sai ya zama ko ina ma akwai mutane ga haske tarr kamar safiya, cikin ikon Allah sai gashi ya gane shagon, a buɗe ya ga ƙofar lokacin da ya zo, keken ya ajiye yana jin bayasa duk ya ƙage ga mazaunansa duk ciwo suke saboda zaman kan ƙarfen keken. Daga bakin ƙofa ya tsaya yana yin sallama hannunsa riƙe da ledar dankalinsa. Amimulla da ke ciki jin muryar Beelal sai ya tashi da sauri ya fito aikuwa yana fitowa ya ga Beelal ɗin ne wani tausayin yaron ne ya ji ya kama shi hakan ya sanya ya amsa masa sallamar tare da miƙa hannu ya kamo Beelal ɗin ganin shi kaɗai ne babu iyeyen gidan nasa wato su Imran

09030283375
❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BEELAL*
💦💦💦💦💦💦💦
*BOOK 2*

FCW

Book 1 free
Book 2 paid 300

Mai buƙata zai biya ta asusun Fa'iza abubakar unity bank
0020281885
Shaidar biya ta 09030283375

Last free page 1️⃣7️⃣➡️1️⃣8️⃣

*HAMEEDA*

Gabaɗaya ta yi narai-narai da ido za ta yi kuka, sai dai tuna furucin Musty a kan yankan da yace zai mata sai ta fasa sakin kukan, hannu biyu ta sanya ta dafe pant ɗinta, shi kuma ya shiga kiciniyar rabata dashi, amma duk yadda ya so ya cire pant ɗin abin ya faskara dan dama da ya haɗe hannayen nata ya riƙe ƙafafunta da take haurawa tana bangajarsa da su hakan ya sanya shi sakin hannayen nata ya maida hankali wajen cire mata wandon.
Chapter 11 · 0% Book details