← Book details Bahagon Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 4 OF 4

Part din din mu aka fara kaini ko zama banyi su gwago suka ce akaimu wurin uwar mijina.

Bahagon Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 454 min read

Mutane suna biye damu inda har zuwa dakin sai dai yan uwana sun tsaya a part dina basu biyo mu ba sai gwago da mahaifiyar Samira da mama da su samira da amina su bakwai dai suka rufa min baya.
Ta idar da sallah ke nan aka ce mata ga amarya an kawo mata tace sun koyi sallah mahaifiyar Samira ne tace yanzu dai muke so a bamu wurin muyi mun kawo amarya masauki ta ne.
Dariya tadan yi tana mikewa daga inda take tare dafadin aiko na gode da wanan zumuntan da kuka nuna min iso inda nake rufe da fuskana ta rugumay ni tana kokarin zaunar dani saman kujera.
Sai na zamay na zube kasa tace a a taso ki hau kujera mana kai na girgiza mata tace Allah yai maki albarka tasa hannu tana bude rufin fuskana.
Naji tace tubarkallah masha Allahu tare da zubamin idanunta akaina ina duke da fuskana kasa ban yarda na dago kaina ba munyi ido biyu da ita.
Gaba sai faduwa yakeyi ta juya wurin sauran yan uwanta dake shake a dakin tace tubar kallah kunga baba na ya iya zaben mata Allah yasa yadda fuskan ki yake dakyau har da halin ki mai kyau ne inji wata daga cikin matan dake dakin tace.
Mahaifiyar Samira ta amshe dace insha Allah yadda take dakyau haka ma zuciyar ta yake farar belbelace wanan mai farin nama.
Sai suka sa guda dakin ya amsa da shewan su nan dai su gwago suka mike suna fadin a basu wuri suyi sallah.
Nima daga inda nake zaune a kasa rufe da fiska nace sallah sai wata daga cikin kan nen shi tazo tace may kike fada amaryan mu kasa kasa nace sallah zanyi.
Baaba wai amaryan mu zatayi sallah tace kaita daki don Allah suyi sai sukace wani abu sai amaryan Abbati baaba dako jikoki bata yarda su shiga mata bayi yau gashi tace amarya ta shiga nan na fahinci yawan tsabtan da tijuwar ashe a gunta ya gado tsabtan shi.
Ni da samira Amina da yaya Samira muka shiga dakin sai lokacin na bude rufin kaina ina jin Samira na fadin ikon Allah wai dakin tsohowa ke nan garin dadi na nisa.
Bayan munyi sallah an wadda tamu da abinci da sha zuwa takwasa akace in fito a kaini part dina mun fito tare da rakiyan matan da hajiya baaba tace su rakani wurina.
Nan muka shiga suka bude dakin dake rufe wanda nasan shike zamana a gidan muka shiga .
Nan suka fice suka barmu sai nida yan uwana a dakin wanda sai lokacin na bude rufin fuskana don in sha iska tare da bin dakin da kallo.
Nan kowa ya sake yana diban abin da yake so da aka wadata mu dashi a part din nawa sai hira ake kwasa sai jefi nake saka baki don zulmin da ya ke damuna a raina.
Yaya Saadune suka shigo wurin mu dasu yaya Sani nan akai ta bakwanci dasu suna biyewa gwago da take jan su.
Wurina ya nufa yana fadin amarya yaya dai na duk kinyi wani laushi dake ajiyan zuciya na sauke tare da kakaro murmushi a fuskana.
Nan muka zauna dashi yana kara yimun nasiha a kan sabon wurin da na shigo yake fafin in kwantar da hankali na in fahinci yanayin su.
In zauna lafiya da kowa a yadda ya fahinci family kamar Sulaiman bai shaku da su ba sosai don duk wanda yazi sai yaji suna mai korafin bai zuwa gida.
Yace kin ga yanzu sai kiyi amfani da wanan daman ki sakashi a hanya ta yadda zai mami yan uwanshi kan sashi kuna zuwa gida lokaci lokaci.
Ki kuma sa ya danga masu alheri yadda ya kamata ke ma dai kin san sauran ba sai na gaya maki ba.
Dagowa nayi idona yana zubar da hawaye nace na gode yaya insha Allahu zanyi kokari inyi yadda ka koya min din.
Nan su yaya Sani suka shigo suma mun dauki lokaci dasu muna hira a wurin sanan sukai muna sallama suka fice.
Amina ta dawo wuri na tana kara haska min rayuwa abinda ya dace in daga yi da yadda zanyi in sa sabo a tsakanimu daidai sauran su.
Naji dadin shawaran ta duk da dama nasan wasu a dan zamana da anty danayi sai dai karin da tayi min na wasu da nake ganin kamar ba masu amfani bane a lokaci.
Sai dare sosai muka samu muka kwanta inda suka ce da safe zasu fita zuwa cikin gari don su bada labarin garin bauchi idan sun koma gida.
Washe gari akai haddaden walima a gidan aka watse lafiya nan mutanen mu suka shiga zaga gari ya rage saura ni da gwago da mama a dakin.
Sulaiman ne ya shigo don ganin fitan su da yayi yana saye da babban riga da yar ciki na farin voile sai dan dinkin da akaimai ba mai yawa ba can.
Ganin su gwago yasa shi jin kunya zai koma gwago tace mukan bari mu fice wurin hajiya mu barku ku gaisa yana fadin su zauna amma sai suka fice.
Acan suka samu su hajiya na al,ajabin kayan garan da muks kawo masu sukace kuko wanan dawai niya haka babu iyaka don roban guguru har bakwai da ruban nama biyu na ragon da aka soya sai zabin da ya sha gyara da hadi biyu alkaki roba biyu kwan zabbi an cika roba biyu sai jarkan man shanu da na nono da sauran tarkace masu muhinmanci.
Bai iya tsayawa ba a dakin don kunya yace barin in fita na dauka ai ke kadai ne a dakin na shigo yana magana yana min wani irin shuumin kallo har sai da gabana ya fadi.
Bai iya tsaya ba juya zuwa wurin baaba nan ya samu suna kallon kayan da aka baza a kofan dakin hajiya baaba ana kallo.
Lumshe ido yayi dayaji baaba da yan uwanshi na ta yabon karanmacin da muka nuna masu da kawo wanan kayan haka a matsayin gara.
Nima kuma a nawa bangare sai yabo sulaiman din da yan uwanshi ke sha wurin yan kawo ni don irin karamcin da aka gwada masu a gidan.
Washe gari suka kama hanya sai dai an bar gwago da mahaifiyar Samira su zasuyi min rakiya Abuja sauran aka tafi dasu mun dade da Amina muna tataunawa.
Gidan ya rage daga ni sai su mummy kamar yadda naji samira na kiran mahaifiyar nata.
Babu kowa a dakin nawa ya shigo ina tsaye gaban mirrow dakin ina kokarin tubke kaina da ya sha kitso ya zubo min a fuska.
Kamshi turaren shi ne ya fara sanar min da shigowan shi dakin nawa sai kuma na gashi ta cikin mirrow tsaye ya soka hannayen shi a cikin aljihun wandon shi tare da kare min kallo don bai taba ganina haka ba hijjabi ajikina ko gyale duk sai na daburce na rasa natsuwana a lokaci guda.
Daidai baya na yazo ya tsaya daidai inda nake a hankali ya ciro hannun shi daga aljihun da suke ya sauke su saman kun kuruna ban san lokacin da na lumshe idanuwa na ba.
A hankali ya dora kanshi saman bayana ban daina abinda nakeyi ba amma na kasa yi masa magana a lokacin saboda kunyan shi da nake ji.
Wai nice yau gani ga uncle a karkashin inuwa daya a matsayin ma aurata nauyi da kunya sun hanani juyowa gare shi in fuskance shi.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , ,

🧕🏿5️⃣5️⃣🧕🏿


NOVEL DIN NAN ONLINE NOVEL NE NA KUDI IDAN KIN SAN DARAJAN ALLAH DA MAZON SA KADA KI FITAR MIN DA NOVEL DINA YAR UWA.


Fuska biyu ga mulsumi abune mai muni ga alumma a hada dashi da Allah bai san darajan shi don zuciyar ta tayi tsauri shedan ya rinjaye shi amma kuma yana musulmi babu Allah a zuciyar shi.
Kafiri ma yana tsoron Allah balle ke mai sallah biyar a rana ina zaki da hakkin wani a kan ki naki ma ya ishe ki kaya gobe kiyama.
Bai damuwa don nasan da kayana zaki dauka ranan dauka akai babu mai taya ka sai halin ka muje zuwa yar makawa yanzu ta fara novel yar matashiya ce a cikin ku.
Ana cewa novel ba dadi ba ma ana kuma gashi ya zama kamar dole a karanta harda sato maku akeyi don kawai son duniya.
A hankali ya sa hannuwanshi ya juyo ni ta yadda zamu iua fuskantan juna dashi irin tsabar soyayyan da nagani a cikin kwayan idon sulaiman din ban taba ganin shi a cikin kwayan idon wani na miji ba.
Haka yasa ni sunkuyar da kaina kasa da sauri gabana ya na bugawa uku uku don firgice sai ji nayi idanuwa sun ciko min da hawaye ban san sun zobo ba.
Sai gani nayi yasa hannun shi yana sharewa a hankali jikin shi babu idan inda bai rawa a lokacin don wani irin sha,awa dake fisgan shi a lokacin.
Sannu a hankali yake goge min hawayen sai naji sun zubu gaba daya kuka ne yaci karfe na ji nayi ya rugumoni zuwa jikin shi.
Cikin sautin kuka nayi karfin halin bude baki na ina cewa dashi Uncle, , , Uncle sulaiman don Allah , , , don Allah ka rike ni amana karka ci amanata don Allah ka soni tsakani da Allah ka so ni saboda Allah badon wani abu ba.
Sassauta rikon dayai min yayi don yaji maganan ya doki kwakwalwan shi a lokaci guda.
Sai kuma naji ya riko ni fiye da na farko kamar zai hadiye ni, shima magana ya soma cikin sanyin murya kamar haka.
Safiya ki kwantar da hankalin ki mu fahinci juna mu zauna lafiya wallahi Safiya bazan taba hada son ki da wani ko wata ba.
Ina son kine tsakani da Allah, ina son ki sani ni ban soki dan wani abu ba ko wata manufa nawa, ina mai tabbatar maki ba zan ci amanar ki ba a rayuwana don banga ribar da zan samu ba ga yin haka.
So dan Allah ki saki jikin ki dani mu zauna lafiya cikin amincin Allah, ina tare da ke komai wuya komai dadi.
Don ba zan taba hada darajan girman ki ba da wata mace a fadin duniysn nan mahaifiya ta ce kadai zan iya hada son ta da naki don ita kadai ne mafi daraja a gare ni a duniyan nan yanzu bayan ke.
Don haka ku biyu ne kada yanzu zaku iya juya ni yadda kuke so a rayuwan ku.
Ni nace ina son ki duk yadda kike ba zan taba kowa dake ba mudin na samay ki yadda nake so muyi zaman mu lafiya mu karasa rayuwan mu a tare cikin salama.
Ya kare da fadin okey ?
Ajiyan zuciya na sauke amma ban iya dago kai in kalle shi ba har wanan lokacin sai kawai naji yayi amfani da hannun shi na dama ya dago min habana.
Kafin ince zan mayar naji ya hada fuskan shi da nawa yana kokarin neman baki na da na sa idanuwan shi a lumshe suke lokacin.
A tsorace nake an ma na kasa hanashi abin da yake min din sai ji nake yi tsikar jikina yana tashi sai kuma naji hannun shi na hagu na kaiwa da komawa a godan baya na.
Tankar yana lalashi na harshe shi naji ya zura a tsakiyar bakina tare da maida hankalin shi wurin shafar wasu sassan jikina musanman godon baya na zuwa mazauna na.
A lokaci guda kuma naji yana yana sumbatar tsakankanin wuyana da kaina haka yasani dole na shiga magana cikin inda inda ina fadin.
Uncle, , , , , uncle yi hakkuri don Allah shiko wani irin zaki yaji muryan nawa yai masa kawai sai naji ya sunkuceni har wanan lokacin bai zare bakin shi a nawa ba bai sauke ni ba sai a tsakiyar makeken gado dake dakin.
Ya kwantar dani haka ya bani daman tokara hannuna saman kirjin shi da hanayena guda biyu don gudun kar jikin mu ya hade wuri guda.
Amma sai ji nayi ya kama hannuwa nawa ya ware su sosai sai ya dafe su da nasa saman godon dole jikin mu ya hade sosai son ran shi.
Kirjin sa na saman nawa ya shiga lasar kunne na yana rada min wasu kalma na soyayya masu dauke da sunayen mu.
Rintse idanuwa nayi suratan da yake yi na sunayen mu wanda suke daidai da sambatu sam ba zan iya amsa ko daya ba.
Hakan kuma na kasa aiwatar da komai a bangare ns duk yadda yaso haka yake yi dani don tuni ya gama tafiya da hankalina da irin siddabarun sa wanda ya gama sanin sirin mallakar mace dashi don ya lura idan ba hakan yabi dani ba, ba zai sameni cikin sauki ba.
Sai da ya gaji don kan sa ya sarara min tare da sauke ajiyan zuciya tare da mirginawa gefe daya yana sauke numfashi a hankali.
Da sauri na jawo zanin dake gefena na saya jikina dashi ji nayi yayi murmushi kawai ya juya min baya.
Da haka muka kwanta sai can naji ya mike ya shiga ban daki da alamar wanka yake yi don dadewan da yayi a ciki.
Haka ya bani daman mikewa da sauri na gyara kaina kafin ya fito naji ya turo kofan ya fito da sauri nima na mike na fada ban dakin don tsarkake jikina.
Ko da nafito baya dakin zama nayi a bakin gadona ina sauke murmushin da ban san na maye ba wata kila na yau muradina ya cika ne ko kuma na na samu mai sona tsakani da Allah ne.
Haka na kwanta ban sake bi takan shi ba sai can cikin dare sosai na jishi a baya bai hanani barci na ba amma dai nauyin shi a kusa dani shiya hanani sakat.
Washe gari ya rigani tashi bai dakin sai dana gama komai na fito don in gaida su mummy sai na samu dakin nasu ba kowa har kayan su.
Na juya zan koma sai gashi ya fito daga dakin da nake tunanen nasa ne ban yarda mun hada ido dashi ba na dan sunkuya ina mashi ina kwana.
Murmushi naji yayi yace an tashi lafiya yaya bakunta nima murmushin na dan kakaro a fuska na kadan.
Au su gwago kike nema naji yace abinda yasa na dago kai na kalle shi kenan da sauri alaman eh yace sun kama kan su ai tun jiya da yamma don sun ga mai masukin nasu bata su take yi ba.
Suna part din hajiya acan suka kwana don haka muje mu karya sai muje gaishesu daga nan sai ki masu bayanin abinda yasa kika watsar dasu a garin mutane bayan ke kika kawo su garin.
Nace kai uncle na watsar dasu kuma fa kace ya fara tafiya yana cewa kin kula da kina da baki ne a gidan tunda kika dafe kan angon ki.
Binshi nayi a baya zuwa dinning inda naga ya nufa tare da zama yana kokarin jawo plate a gaban shi.
Da sauri na karasa wurin ina karban plate din tare da jawo wormer din abincin ina budewa nace amma dai a bari in fara aiki na kar kuma ace min na shagala dayin haka don naga ango na zaune.
Murmushi shima naji yayi bai hanani zuba abincin da nake zuba mai har na cika plate din da shi na juya na zauna ina jawo plate zan zuba ma kaina naji yace wanan da kika zuba dani da waye ?
Dole na dauki spoon din na saka a plate din da kyat na diba sau daya nakai a bakina don kunya ganiin bazan ci ba yasa shi diba ya miko min yana fadin bude bakin ki dole na bude badon na so ba.
A haka muka koshi muka mike zuwa part din hajiya baaba bayan na kawar da kayan zuwa kitchen muka nufin wurin su baaba din.
Shike gaba ina bayan shi muka shiga da sallaman mu don tun bamu shiga ba muke jin hayaniyar mutane a part din nata.
Sallaman shi yasa duk suka juyo gare mu zama yayi saman daya daga cikin kujerun falon ni kuma sai na zube kasa daidai inda ya aje kafan shi.
Sai naji wata daga cikin wa yanda ke falon tace da alaman amaryan tamu tana da kunya don naga ko ranan da aka kawo ta bata zauna akan kujeran ba.
Murmushi naji yayi tare da fadin kun tashi lafiya sai kuma naga ya dan zamo saman kujerar yana hajiya barka da Safiya yaya gajiyan jama a ?
A lokacin nima na samu daman gaida ita da kwana ta amsa min fuska sake tana cewa yaya bakunta ?
Komawa yayi saman kujerar ya zauna da kyau tare da tambayan ta ina bakin ta suke tace suna ciki sai wacce tai maganan farko taci gaba da magana tana fadin kada kiji kunyan mu munan duk yan gida ne.
Yace Well, Safiya meet my sisters wanan itace Aisha wanan kuma khadija, and that is my cousin sister jamila and nuriya duk anan wurin hajiya mu suka tashi.
Na dago kai ina bin su da kallo araina ina cewa ashe yana da yan uwa mata haka ya lakewa anty kawai kamar wanda baida kowa.
Mikewa yayi yana cewa bari mu gaida bakin mu kafin in fita don ina son zuwa gidan su kawu kafin mu wuce.
Hajiya ne tace dani bishi mana ku shiga suna ciki a dakin muka samay su kwance suna jin sallaman mu suka mike zaune.
Ni na fara shiga shi ya biyo ni a baya sai da na zauna na fara gaida mummy sannan na juya wurin gwago dake gyara daurin dan kwalin ta nace gwago yaya bukun ta.
Tace bari kedai ai har tunanen komawa gida nakeyi wallahi wanan uban nisan da muka kwaso nayi dariya nace gashi kuma gobe zaki kara kwansan nisan .
Tace yar nan kin faye zari da har idon ki ya kyala har wata kasan dauko miji.
Dariya yayi mata yace gwago ai tafiya yanzu kika fara don yanzu aka fara yi wata rana har waje zamu fita dake garin masu jan kune.
Zaro ido tayi waje tana cewa rufa min asiri dan nan nan ma ya isa haka ai an gode ta kalle mu tace to yanzu dai Allah ya hada wanan aure don Allah a yaki zuciya yi nayi bari na bari sai a zauna lafiya Allah ya kawar da idon makiya a tsakanin ku.
Mummy ne ta amsa da karfi da amin ya Allah tana mai daga hannuwa sama alaman addua ya karbu.
Nan dai aka dan taba hira ya mike yana fadin zai fita ya juya gare ni yana fadin zaki iya komawa part din mu yanzu don babu kowa a cikin sa.
Sai mummy tace bari ta taso zata samay ni a can tare muka fito ya tsaya magana da yan uwan shi nikuma na wuce part din mu.
Bayan na dan gyara wuri sai ga mummy ta shigo da gwago nan na dawo falo na zauna wurin su tare da kuna tv dake falon.
Kwantawa nayi saman doguwar kujeran dake falon tare da lumshe idanuwa na a han kali ina mai ci gaba da tunanen makomar rayuwa na.
Ban san lokacin da barci ya dauke ni ba sune zaune suna hiran su jefi jefi wanda hiran akan inna ne da halinta.
Shigowan sisters din shi ne yasa na farka naji suna cewa ayya barci takeyi ne sai na bude idona tare da tashi zaune ina masu sannu da zuwa.
Wuri suka samu suka zauna suna fadin mun zo muyi maki sallama ne don yau zamu koma gidajen mu sai dai Aisha ce don ita a abuja suke zama da mijin ta.
Murmushi nayi ina mikewa nace har zaku koma ke nan suka may kuma zamu yi nace ai kunyi kokari an gode nace ina zuwa daki na shiga na bude akwati na hado masu kayan shafa da kayan buki na fito masu da leda hudu a hannu na.
Mika masu nayi mamaki sukayi suka kayan naki kika kwaso muna kuma nace ai don amfani aka sayo su godiya suka yi man, nayi tare da sallama na raka su har kofa.
Bayan tafiyan su na dawo na zauna inda su gwago suke muna hira jefi jefi dasu Uncle ya dawo gidan da sallaman shi ya shigo falon.
Su gwago suna mai sannu da zuwa suna kokarin mikewa su bar falon yake ce dasu don Allah ku zauna abinku yaya kuma zaku tashi amma sai basu tsaya ba sukace dama mun shigo ne don tana ita kadai zamu wurin hajiya mu taya ta hira.
Suka fice ni kuma da nake zaune ina kallon draman su sai lokacin nayi mai sannu da dawowa.
Zama yayi kusa dani batare da ya amsa ba sai dai ni kuma ban yarda mun hada ido dashi ba ji nayi ya kamo yan yatsun hannu dake saman jikina ya rike.
Ya dago hannun nawa yakai masu sumbata tare da kura min idanuwan shi a kaina, ji nayi kamar in nutse a lokacin don kunyan shi da nake ji.
Jawo ni naji yayi zuwa jikin shi yana kokarin runguma a jikin shi nayi karfin halin ce mashi uncle baka gudun wani yashigo ya samay mu a haka ?
Cikin karfin hali ya iya fadin wazai shigo nan ko mm a sun shigo ba matana suka sama ina runguma ba da banda aure sun ga na rungumi watane.
Nace amma, , , katse ni yayi da fadin amma may ke kuwa zamu shirya dake don naga kina neman hanani abinda Allah ya halasta min.
Murmushi nayi nace ban dai son wani ya samay mune a hakan yace and so what inda an samay mu su gwago da suka san kan su baki ga sun fita ba.
Dole haka na kyaleshi yaci gaba da murzana yadda yake so ina runtse idanuwa na don kanshi ya kyale dama jan magana yakeso.
ya sumbaci kuncina tare dan dagowa daidai kunena yana magana kamar maiyin rada kina kunyan azo a same mu ne ina taba mata na.
Nace kai da baka jin kuyan ai sai kayi tayi amma ni ina gaban sarakuwa ina zan biye maka ace min jarababban amarya.
Ya fidda karamar dariya yana matsa min hannaye na yace af nine banda kunya barin nuna maki banda kuyan yanzu.
Na dan shagwabe mashi murya ina cewa Uncle kabari Allah kuwa zamuyi rigima dakai yanzu.
Dariya na kara bashi ya sake jawo ni jikin shi gaba daya yana fadin bari mu fara rigimar tun yanzu.
Zillewa nayi ya sake ni yana dariya dakin shi ya shiga ban ji fitowan shi ba har na mike nima zan shiga daki sai gashi ya fito.
Yana fadin ki fa shirya jirgin bakwai zamu bi zuwa Abuja gobe don haka ki fada ma su gwago su zauna da shiri don kar a girshesu.
Ina mamakin shi gashi dai yana son yan uwa don shi da kanshi ya kawo shawaran abar mutum biyu da zasu rakani Abuja yace kuma da gwago cikin wanda za a bari da da mama zasu tsaya sai kuma aka tsaida shawaran mummy ta tsaya su yaya Saadu zasu biyo tanan sai su dauke ta.
Amma kuma na fahinci yan uwanshi kamar basu jin dadin shi kamar yadda Faiza ta taba gaya min amma dai koma may ne yanzu tun da Allah ya jefani cikin su da sannu zan fahinci komai.
Washe gari dukan mu muna zaune gaban hajiya baaba tana muna nasiha sai lokacin take ce ga yar kanin ta nan zahar ta karbo muna zamu zauna da ita .
Koshi ashe baisan da maganan ba sai naga yayi saurin dagowa yana duban mahaifiyar tashi don kawar da komai da sauri nace mun gode baaba Allah ya taya mu riko.
Tace keda kika fishi hankali baki ki alherin da nai maku ba amma shi har yanzu ban san abinda yasa baka mantuwa ba a ranka ana son musulmi da yawan yafiya ko yaushe.
Murmushi yayi yana mike wa tare da sosa kan shi yace hajiya mu zamu tafi ai muna fatan alheri.
Addua ta shiga kwararowa tana bin mu da fatan alheri har muka fice part din su gwago kan har an shiga motar da zata kaimu airport.
Sai da muka sauka ne naga ashe da Aishan shi zamu tafi zata koma itama gidan mijin ta tare muka shiga jirge gwago kan sai kama mummy take yi.
Mun bar yarinyar zata biyo driver da zai zo da motar da sauran kayan mu don suma sammako zasu yi don su isa da wuri.

Mun isa lafiya motaci biyu suka zo daukan mu zuwa gidan shi harda Aisha duka muka tafi gidan nasa.
Mun samu an kara gyara gidan anyi abinda ban san gidan dashi ba ya kara wani kyau da daukan ido na juyo na kalleshi da mamaki ya gyada min kai kawai yana lumshe idanuwan shi.
Gwago da mummy sun kasa boye farin cikin su na ganin gida sai yaba kyawon gidan suke yi har muka zauna nan mai aikin shi ya fara gabatar muna da abinci.
Mun ci mun sha a tare dasu mummy da Aisha don shi ana sauke mu ya shiga ya canza kaya ya fito bayan ya nuna muna dakuna ya fita.
Tare da Aisha da mummy muka gyara dakin da ke zaman nawa tana da sakewa sosai don tana jana da hira sai dai nine ban sake jiki da ita ba.
Take fada min yaran ta uku yanzu duka mata ta barsu nan Abuja ne a wurin kishiyar ta nace Anty Aisha kina da kishiya ne?
Tayi murmushi tace mu uku ne ai dayar tana can bauchi don a can take aiki ita kuma dayar da suke nan dama anan ya aure ta.
Sauke ajiyan zuciya nayi batare da na kara magana ba sai naji tayi dariya tace kwantar da hankalin ki yaya na mai son yawan tara iyali bane.
Idan kika dubi yanayin shi rayuwan shi kaf na turawa ne don dan kaida ne shi sai kinyi da gaske kafin ki fahince shi amma idan kin fahince shi zaku zauna lafiya.
Ina son ki jajirce wurin hakkuri da kawar da idon ki a alamuran shi bai faye son mamuwar mutane ba don Allah Safiya ki taimaka muna ya ja mu a jiki dan yazo kice kadai hope din mu.
Murmushi nayi kawai nace a fili Allah yasa tace yayana yana da saurin fushi amma kuma yana hucewa a dan lokaci musasnman idan kai mashi laifi ka bashi hakkuri.
Tace ina fada maki halin shi ne don ki kiyayye don naga kamar ba wani sanin juna kukayi sosai ba.
A raina nace ashe akwai aiki kuwa ashe ganin kitse saman ruwa nake mashi ke nan sai naji tace idan kin ga ya tashi bai son magana kada ki damu kanki kidan nisance shi sai ya nemo ki don kada ku samu matsala tace bani wayan ki in saka maki layi na don mu ringa waya dake.
Na mika mata tasa layin ta ta kira ya shiga tayi adding dina a contact din ta isowan driver da kayan mune yasa mu fitowa daga dakin muna taron su.
Nan dai Aishan ta taimaka min muka kawar da kayan komai mukai mai mazauni munyi sallah la,asar mijinta yazo ya dauke ta tana mai ce min baya sati zata shigo ta duba mu.
Bayan tafiyan ta na sauke ajiyan zuciya naga yanzu may abin yi nan na fara shawaran ko girki zan dora muna amma sai na samu har mai aiki ya gama ko yana shirin wuce wa gida.
Wuein su mummy na koma na zauna nan muka fara hira dasu mummy ke cewa dani taji abinda kaunar mijina le fada min dazu don haka take son fada min .
Inyi amfani da baiwar da Allah yai min na mace wurin canza mashi halayen da suka ce yana da musali idan yai fushin ba kaucewa zan yi ba kokari zanyi in jawo shi a jiki ta hanyan yin kwalliya da girki mai dadi da nasan yana so.
In kuma tabbatar da na hada da addua da yaiwata sadaka din ganin haske ga alamarina in kuma yi kokari in koya mashi bin yan uwan shi ya saba dasu amma indinga boye sirina dana mijina tsakani na dasu .
Do ba komai nai ya kamata su sani ba tace kinga wanan yarinya da aka hadoki da ita to itace ido da kunnuwar uwar mijin ku.
Don haka koda zaki sake mata ba irin sosai din nan ba kada ki dingayin abu a gabanta do shine zai sa ta dinga kwasa tana fadi a gida.
Ga kayan kwalliya ga sutura Allah ya wadataki dasu don ha ki daure da yaiwata kwalliya ajikin kina lamshi da saurar su zurfin karatu ba shiba ba indan akwai kudi babu abinda mutum ba zai iya ba sai ki dan more ma wanda kika samu a baya.
Sai dai mijin nan naki naga mai wayayyen kai ne mai yuwa ya barki ki koma makaranta ki kara ilimi.
Nan dai muke sai biyar da wani abu ya dawo gidan lokacin naci kwalliya da wani English wear a jikina ina tsaye ina magana da zarah a falo yashigo gidan.
Sannu da zuwa mukai mashi nida Zarah bai amsa ba sai kallon zarah da yayi bat ta bar wurin kai tsaye yanufo inda nake tsaye.
Kai tsaye ya hada bakin sa da nawa ya manna min ragowar lemon plus din dake cikin bakin shi na rufe bakina da sweet din ina ce mai thanks.
Yace kin ga irin gaisuwar da nake so daga gare ki daga yau sai ki saba dashi murshi na sauke mai laushi.
Ya koma saman kujera ya zauna na wuce na dauko mai ruwa mai sanyi na kawo mai tare da kokarin zubawa a kofi ya dagakatar dani da amsan goran ya kwankwade ruwan roban gaba daya.
Yana sauke numfashi nace bakaci komai ba tun karyan safe ko?
Ido ya lumshe min na koma kitchen na hado mai kayan bukin da muka zo dashi na da alkaki da goran juice ya karba yana min godiya.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/15/20, 7:51 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , ,


🧕🏿5️⃣6️⃣🧕🏿


NOVEL DINA NA KUDINE KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA NA SAUKE HAKKINA A KAN KU MAI FITARWA KUMA UBANGIJI YA BI MIN HAKKINA AKANTA KO WACECE.


Bazan gaji da jan Allah ya isa ba a kanki mara tsoron Allah don ki gyara masu kike daukan nauyi a kan ki don baki san nauyin Allah ya isa ba zaki fadi ranan da nadama zata riske ki ko zata riskeka yadda baka/ki fasa fitar min ba nima ban gajiya da bin hakkina a kan ku dabara ta saura gyaraka/ki mara zuciya da gudun goben ta
Duk da gajiyan dayake tare da shi bai hanashi mike wa yana ce min sorry na barki ba bayanin komai a gidan.
Kamoni yayi ya mikar yana fadin muje kiga tsarin gidan naki ko ban musa ba na bishi yana rike dani yake nuna min ko ina na gidan.
Sai naga ashe kallon tsoro nakewa gidan dama duk ban san komao ba a tsorace nake kallon gidan ashe yace da fatan komai yayi maki yadda kike so.
Murmushin da yake so nayi masa daidai lokacin da muke komawa falon don zama yace yanzu may kike son a karo maki a gidan koda na nauin kayan kitchen ne nace komai yayi a yanzu daga baya idan ina so zanma magana.
Hannu na ya kamo ya danka min mamullaiyan da alama na gidan ne sai wani wanda ban fahinci ko na maye ba.
Kallon mamaki nake mai sai naji yace makulin motar ki ce tana waje aje sai ki shirya koyon mota yanzu sauran kuma na sauran dakunan gidan ne don ni ba zaunin gida ba ne koda bukatan shiga ya taso maki.
Ban iya magana sai mikewa da nayi na durkusa a gaban shi gwiwoyi na biyu na saman carpet din falon hannaye na biyu na dora a kan cinyan shi na fara zanbga mashi godiya.
Yace No no stop it safiya do you know how much i care for you?
Na gyada mashi kai hawaye na zuba min a idona bayana naji ya fara shafawa a hankali tare da share min hawayen dake zuba min a fuska da hannunshi na dama.
Cikin raunin murya na craking nace uncle dole in yi kuka ka nuna min kaunar da ban taba zaton samu ba a rayuwa na.
Sai naji ya sunkuya ya rungumoni zuwa jikin shi ya na zaunar danu saman kujera yake fadin you deserve morethan this a wurina kin dawo min da farin cikin da na cire tsanmanin zan sake samu a rayuwa na.
Yan zuma haka in bakiyi hankali ba ina dap da in baki kaina gaba daya ji nayi kamar dariya zai kubce min a hankali na zare jikina daga nasa na zauna kusa dashi.
Gaba daya rikewa bayi wai yau nice a cikin wanan rayuwan da na dade ina mafalkin samu wanda sai dai inga anayi a tv ko wani gida gani yau na tsinci kaina ciki tsundon.
Sai nake ganin abin kamar yar koyau na koma don ban saba da irin wanan rayuwan ba tun daga farko ji nayi yana tsiyaya lemon dake gaban mu a cup ya dan kurba sai ya miko min sauran gaba daya na zuke.
Naji muryan shi yana fadin baki ce min komai ba batun kara karatun ki ko da yake idan son samuna ne ki zauna gida as a house wife zai fi min dadi naki jinin mace mai yawan fita a rayuwa na sha fada maki hakan a baya.
Zan maki kokarin da duk wani abin da zaki bukata na rayuwa idan kin yi laakari da irin halin da muke ciki na rayuwa rayuwan ma har nawa take a gare mu yanzu ?
Na dago idanu na dan kalle shi kadan sai naga ya zuba min idanun shi yana yana sauraren amsan da zan bashi.
Haka yasa nayi saurin sauke idanuna kasa ina wasa da yan yatsun mu dake hade a hankali na iya furta mashi uncle na hakkura da karatu.
Kin hakkura fa kika ce da karatun na kada mashi kai alaman eh yanisa yace saboda may ke fa kika ce min kina sha, awan karatu a baya .
Na nisa nace yanzu na fasa a hankali.
But why , ?
Ko dan abinda na fada yanzu ne kika fasa cika burin ki ?
Nace a hankali eh to duk mai hankali yayi tunane haka din ne don may kuma nake bukata ga karatu yanzu banda in zauna dakina in nemi ladan aure.
Don maganan ka gaskiya ne har wani rayuwa zai ba ni shawa yanzu kuma bayan wanan da nake ciki indan nayi duba da dafin mutuwan da ke a jiki na karatun ma karshen inyi ban mora ba gara kawai in zauna in rugumi kaddarata da hannu biyu yafi.
Yace hakan yayi maki don ban son daga baya ki koka dani ko kadan duk da zanyi iya kokari na wajen kare maki hakkin ki dana bukatun ki.
Na na insha Allah yayi min zan zauna in kula da gida da bukatun ka na lura kaima hakan yafi maka don dai kaga ina sha, awan karatun ne ka mara min baya akai.
Guntun Murmushi naji yayi mai alaman da magana na dago kai na kalle shi sai yace hakan na dakyau don kin fara cinye jerabawan da nake gwadawa akan ki.
Saboda haka nayi maki alkawarin zaki rika amsan albashi kamar yadda nake ba sauran maikatana duk wata.
Katse shi nayi da fadin a a Uncle gaskiya ni hakan ya, , , , ji nayi yarufe min bakina da hannun shi tare da fadin Shhhh, , , , .
A hankali yace min shine magana na don may ake aiki ba saboda neman kudi da tallafa ma kaiba don haka shawaran da na yanke ke nan a kan rashin karatun ki.
Duk kuma lokacin da naga kin samo sallon batani da irin takon ku na mata sai in canza raayina zuwa wani nauin don kin san mace bata da wuyan bata namiji da halin ta don gashi kwana nawa da auren mu har kin koya min rasgin zama gurin aiki gashi yanzu sai da na dawo gida don ki.
Mikewa nayi tsaye ina kokarin gudu cike da jin kunyan shi amma sai ya kamoni zuwa jikin shi yana fadin.
Where do you think you are going ?
Yana sakin dariya yana kokarin janyoni jikin shi ina fadi kada mummy tafito fa ta samay mu haka yace may zai kawo mummy nan part dina.
Da kyat na samu ya sake ni koshi don an fara kiran sallah ne a lokacin don haka muka watse zuwa sallah.
Da dare har dakin da su gwago ke ciki ya samay su akan yana son su fito muci abinci tare dasu basu so ba amma haka suka fito yana jan su da fira har suka sake jiki da shi suna cin abincin.
Bayan mun gama na kwashe kayan ya zauna dasu suna mashi hira anan yake fahintar yaya Saadu company da yake aiki dasu yanzu sun durkushe.
Ni dai daki na koma na fada wanka don naga sabon angon nawa ba na wasa bane wurin son tsabta da lalubar mace bayan na shirya waya na dauko muna magana da Amina don wani ruwa da ta bani ina son tai min bayani akan shi.
Nan muka tsaya tana min hira bayan komawan su gida yadda suka kwasa wirin rabon kudin da aka basu tukwaici acan.
Kofa naji an turo ko ban duba ba nasan cewa shine ya turo kofan dakin ya shigo yana tsaye da jallabiya baka mara hannu.
Ya rike cup yana shan abu a ciki sai dai bani iya cewa ga abinda yake sha a cup din kai tsaye ya nufo ni sai da ya zuke abinda yake shan ya tambaye ni da kin sha maganin ki kuwa ?
Kai na girgiza mashi alamar a a zama yayi yana fadin dauko tare da fadin kina wasa da shan magani ko safiya baki san in kin kiyi kwana daya baki sha ba zai iya tambayan ki ba.
Mikewa nayi na bude wardrobe dina na dauko kwalin maganin ina barewa sai yace miko min in gani ya karba ya dan duba sai ya miko min tare da fadin akwai wanda na anso a italy zan baki ki gwada sai dai yana da matukar karfi sosai idan kin sha zai sa ki cin abinci sosai amma yana aiki sosai a jiki.
Kofa na nufa don in dauko ruwan da zan hade maganin dashi sai naji yace dani no barshi in munje daki kya hade.
Kallon shi nayi da sauri yace yes dakina zamu yau ko kin fison kullun dan kwali ya jawo hula har a saka muna ido a gidan.
Don ni gaskiya ba yanzu nake son gwago ta koma ba so nake ta dan zauna damu na dan wani lokacin kafin a maida ta in son samu ne har da mummy din don matar na da dadin zama.
Murmushi nayi nace uncle ai sai kasa a zage mu daga kawo amarya sai su samu wuri su zauna.
Ina fadi kamar zanyi kuka yace common wa zai san ma suna gidan nan balle a fadi haka ko baki son zaman su ne sun takura maki keda angon ki.
Wani kallo nayi mai na ba haka bane sai naji ya sukkuce ni bai tsaya dani ko ina ba sai tsakiyar gadon dakin shi.
Da kyat ya barni na sha maganin nawa duk rokon da nake mai baijini ba sai da yayi abinda yake son yi ya samu natsuwa.
Washe gari su yaya Saadu suka iso Abujan don daukan mummy su tafi amma sai Uncle ya dinga masu delay da tafiyan sai da suka share kwana hudu tare da mu.
Ranan da zasu tafine yaya ke gaya min Uncle ya dauke shi aiki a company shi tare da bashi wuri zama da iyalin shi kuma yaya sani zai zo don shima an sama mashi aiki anan.
Nayi murna kwarai ko banza nima na samu dan uwa a kusa dani yanzu abokin shawara ga matar shi Samira akwai shiri sosai a tsakanin mu da ita.
A ranan na biyar suka kama hanya nan suka barni cike da kewan su don dan zaman da mukayi ba karamin jin dadin hakan nayi ba.
Gidan ya rage daga ni sai gwago wace da kyat a rana ta fito falo sau biyu ko yaushe ta daki daga sallah sai lazimi tana kallo.
Sai in dare yayi ya dawo gida zai dan je gunta su dan taba hira wani lokaci har da ni sai Zarah da har yanzu bata gama sake jiki dani ba sai dai akwaita da son kallo ko yau a cikin kallo take ita.
Na tambaye ta karatu fa take ce min ta gama secondry bana jiran jerabawa take yi yanzu ina kula dashi da duk yazo ya samay mu da ita zaune sai in ga ya daure fuskan shi har yarinyar ta dan shiga tsarguwa da taga lokacin dawowan shi gida yayi zata shige daki bata kara fitowa kuma.
Ranan ina tambayan shi may sa yake mata haka sai cewa yayi dani cikin tsawa gada ki kara yi min maganan wanan yarinyar don ba zamana takeyi ba a gidan nan .
Da sauri nace Uncle in ba zaman ka takeyi ba zamanwa take a gidan ina kai hajiya taba ita muzo da ita don debe kewa bai yi magana ba sai mikewan da yayi ya fice dakin ya koma dakin karatun shi ya zauna.
Nikan abin ya daure min kai sai na ja baki na nayi shiru har naje gun gwago na zauna muna hira hankali na yana gurin shi don haka nace ma gwago ina zuwa.
Kitchen na shiga na hado mai snack da drinks na nufi dakin da yake da sallama na tura kofa ban tsanmani ya amsa min ba sai dai dan juyowa da yayi ya mayar da kanshi ga abinda yake yi cikin laptop din shi.
Sannu da aiki uncle sai da ya sauke ajiyan ziciya ya iya amsa min da yauwa sannu madam nace ga abin motsa baki nan na kawo maka kadan jika makoshin ka.
Na aje na juya zan fice daga dakin sai naji ya riko min hannu yana cewa ba tare da ya bar abinda yake yi ba bazaki karasa ladan ki ba kin kawo min abin sha baki zuba min ba zaki wuce.
Dawowa nayi na tsaya ba tare danayi magana na fara zuba mashi acin cup din dake saman tire din, mika mashi nayi tare da dan rusunawa.
Sai lokacin naga ya dauke kan shi saman sytem din yana fadin thanks nace aiki nane hakan ya zuke yana lumshe idanuwan shi.
Ya mayar da cup din cikin tire din yana maida kan shi saman laptop din jiki a sanyaye na fita daga dakin yana aiki yana cin dabun naman daya ji curry da kayan kamshi ya lumshe idanuwan shi.
Ban koma ta kan shiba na tsaya kitchen da falo na gyara ina gap da karasawa naga fitowan shi daga dakin har yanzu fuskan shi babu walwala a cikin sa.
Da gefen ido ya kallo ni ya shige part din shi tare da rufo kofan da karfi araina nace ga maganan Aisha ya fito take maganan mummy ya fado min a rai.
Idan yayi fushi ke ki kwantar da fushin ki ki bishi sai zama yayi dadi amma kin hau namiji ya hau wazai kwantar ma wani da fishin shi wata kila ma fushin da dalili yake yin sa.
Dakin gwago na leka na gaishe ta nake gaya mata lokacin sallah ya gabato tace ai har na dauro alwala wanan gida naku ba ajin kiran sallah.
Dariya nayi mata nace baga agogo nan ya sayo maki ba don ya dinga kira maki sallah kina ji tace kaiya ban faye amincewa da wanan abin nasaran ba ai.
Nace yanzu dai da kinji ya kira sallah sai ki mike lokaci ne yayi baya karya sai idan batir din da yake aiki dashi ne ya kare tace bakaji ba.
Ina dariya nace gwago kafin ya kare fa sai nan da kusan wata biyu tace wata biyu ni ina, ina yar nan ai kisa a dauke mu mutanen banza nifa har na fara yiwa maigidan ki tunin gida don naga so kuke sai kinyi ciki ina gidan nan kulle kamar kurkuku.
Fita nayi na barta ina dariya kada in makara da dauro alwala a lokacin naga gittawan shi zai fita zuwa sallah don ko yaushe sallah jam,i bai wuce shi.
Bayan isha,i na gama komai har abincin shi yana saman table na koma daki na shirya tsaba a cikin wani dogon riga baki mai hanuwa shara shara yaji kwalliya har kasa da kananan duwatsu an dan buda kasan shi kadan.
Ban fito ba sai da na ji motsin shi a falo ya na sauraren News hakan ya sani fitowa daga daki ture kusan kala uku na shafe jikina dasu yan saudiya.
Kamshi ya hade da sanyin da AC falon yake saukarwa ya bada wani inrin yanayi a falon tun fitowa ya dago ya kalleni ya kauda kai yaci gaba da kallon TV dake gaban shi.
Har na karaso gaban shi cikin daurewa na karaso gaban shi na dan duka daga bayan shi tare da sagala hannu na daga bayan shi nace sannu da hutawa Uncle.
Dan murmushi ya sake da bai sauka ciki ba yace barka da gida madam din Uncle zagayo dani yayi zuwa gaban shi ya zaunar dani saman kujerar daga gefen shi yana mai ci gaba dakallon shi sai dai har wanan lokacin bai sake min yatsun hannu na da yake wasa dasu ba.
Cikin daurewa nace Uncle abinci fa yace dauko min nan zan ci na mike cikin wani tako da ban san na iya irin sa ba na nufi dining din kwaso kayan da na jera akai.
Sai lokacin ya sauke wani iri ajiyan zuciya har ina jin shi don na kusa kawowa wurin shi a raina nace su zuciya manya.
Ashe akwai aiki a gabana dan wanan magana yake ta jawa rai haka anya kuwa zan iya sai da na gama jerawa nace bissimillah na samu wuri a kasa na zauna tare da jan plate zan fara zuba mai.
Ganin kayan tare a gaban shi kashi kashi yasa yace min may ye haka yau John ya girka muna?
Banyi magana ba sai ci gaba da bude warmer din nayi inda na fara ziba mai tuwon shikafa da miyar shawaka da yaji agusi da manja sai nama manyan yanka da nayi amfani dashi wurin hadawa da dan man gyada kadan.
Kamshi me ya kaure falon alokacin da na bude ferfesun kifin dana hada wanda nayi amfani da kayan yajin mu na gargajiya sai ruwa dana zuba da maggi.
Gani nayi ya sauko kasa abin wanke hannu na jawo tare da dauko ruwanda na tanada don wanke hannun nashi.
A hankali ya miko hannuwa fuskanshi akan tv ina zuba mai ruwan ya na wankewa a hankali na jaye ruwan gefe guda sai ya kallo ni yace ke ba zaki ci ba nace munci da gwago da Zarah tun dazun dana gama.
Naga ya kara hade rai yayi bissimilla ya fara ci har ya kare bai yi magana ba ni dai ina zaune na saka ma tv ido nima kamar mai saurare abinda ake fadi nan ko zuciya ta tambaya kanta take yi mai ya kawo wanan matsalar haka wai ?
Naji yace amma ba John yayi abincin nan ba eh kawai na bashi amsa dashi na fara hada kayan ina kwashewa na barshi dana ferfesun yana sha a hankali yana kallon tv.
Bayan ya gama na kwashe na dauko kamshi na bude falon dashi yadda ba za a ji karnin kifin ba idan an shigo falon.
Zama yayi a kasan tare da jingina bayan shi da kujerar daya sauka a kai tare da mike kafafuwan shi a kasa yana kadasu a hankali zaman naji shiru yayi yawa don haka na mike zan leka gwago a dakin ta.
Yace jimana sai na dawo na zauna cikin basarwa yace gwago tayi min maganan zuwa gida yau da safe don haka nake son ku fita ai mata tsaraba zuwa gobe.
Allah ya kaimu nace sai na juya na wuce bina yayi da kallo komay ya tuna a ranshi sai yaga bai kyauta min ba sauke ajiyan zuciya yayi may ye laifina a cikin wanan magana daga tambaya kawai ya dora min laifin dabashi ba.
Nasan nayi laifi na kuma dauka ina binshi don yayi hakkuri ya kasa cire laifin da bani nayi shi ba akaina.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/15/20, 10:51 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , , ,


🧕🏿5️⃣7️⃣🧕🏿

NOVEL DINA NA KUDI NE IDAN KIN FITAR UBANGIJI YABI MIN HAKKINA A KAN KI/KA.


YAR UWA MAINE RIBAN KARANTA KAYAN ALLAH YA ISA KARATU FA IYAKAR SHI DUNIYA.
Karfe goma saura har lokacin ina zaune dakina na kasa zuwa dakin uncle don ban san da wani fuska zai karbe ni har nayi kamar in share shi saidai na mike na fara shirin zuwa wurin shi.
Komai na falon an an kashe alaman dai ya shige tuni dakin shi sai wutan da zai sadani da nashi part din ne kawai a kunne.
Ahankali na kwankwasa kofar tare da turawa sai najita a bude nasa kai na shiga dakin can na hango shi tsaye bakin window dake kallon wajen gidan yana tsaye ya rike labule da alama iskan dake busawa a lokacin yake shaka don yana mai dadi.
Shigowana baisa ya juyo gareni ba har na karasa inda yake tsaye batare da jin kunya ba na rungumay shi ta baya tare da zagaye hannaye na saman ruwan cikin shi.
Ajiyan zuciya naji ya sauke a sanyayye nace uncle may kake yi anan tsaye kai kadai batare da ya juyo ya kallene ba ya bani amsa da yanayin yana min dadi ne madam.
Sake shi nayi nima nakoma gefen shi na tsaya ina kallon waje sai naga motoci suna wulgaiya jefi jefi ga iska mai dadi na hurowa ta tagan dakin.
Gwaron numfashi na sauke amma a fili na kasa fadin komai sai tsayawa danayi ina kallon wajen kamar yadda shima yake kallo.
Shi ya kawar da shirun da cewa na dauka kinyi barci ne dana jiki shiru ai ajiyan zuciya na sauke nace uncle ina zan iya barci bayan miji yana fushi dani karo na farko a rayuwan mu tare.
Murmushi yayi tare da sanya hannuwanshi saman kirjin shi yace bada ke nake fushi ba sai dai maganan ki ce ta jawo min fushi na.
A marairai ce nace kayi hakkuri uncle ban san maganan zai bata maka rai ba haka da banyi ba ni gani nayi yarinyar tana zaman kane a gidan kuma bata samu sakin fuska a wurin ka ba.
Naji na gode amma ke bakuwa kike a cikin mu shiyasa zan daga maki kafa ga maganan yanzu amma indai akan zancen wanan zurian ne bani son daga yau ki kara yi min shi a gidan nan.
Ki barni da yan uwana ki zauna matsayin ki na matana a cikin su bani son ki zure masu har su samu kafar shige min haka.
Murmushi nayi na kwantar da kaina saman kafadan shi nace uncle yadda kake so haka za a yi har kullun a shirye nake da in maka biyayya a rayuwana.
Amma Uncle ina son ka zama mai yafiya ga duk wanda ya zulunce ka saboda kayi koyi da sunnan mai,akin Allah sallalahu Alaihim wassalam.
Yau uncle in har akwai abinda sukai ma rayuwan ka sai ince ya zama maka taki ayanzu don hassada ga mai rabo taki ne.
Uncle har kullun sai dai inci gaba da yima addua da fatan alheri a garemu uncle ba zan boye maka ba bantaba ganin mutum adali irin ka ba uncle.
Sai dai kuma cikar kamalan mutum baya kammals sai ya cika sharudun Allah a kan shi yanke zumuta dasu don sun taba yi ma rayuwanka illar killa can baya ba shine mafita ba a gare ka.
Kamata yayi uncle kai ka saka masu da alherin ka barsu da halin su Allah shine mai hisabi arayuwan biyan sa.
Amma uncle akan may zaka rike gawarshin wuta a hannuwan ka su kona ma aikin na alheri har ka gamu da fushin ubangiji ka ta sanadin su.
Uncle kafan Allah yana fushi da may yanke zumunci sannan na fahinci baaba tayi hakane don kawar da wani abu a gare ka.
Sannan Uncle ba, , , , ji nayi ya dora dan yatsanshi saman bakina yace ya isa haka naji na gode zanyi iya kokarina inga na fitar da abin a zuciyata.
Ina alfahiri da kasancewar ki matana a yanzu don samu mace ta gari yana haifar da alheri acikin zuri,a dawamamiya.
Ya rugumay ni zuwa bakin gadon shi sai lokacin da ya sauke ajiyan zuciya yace may kika tanadarwa tafiyan gwago ne ?
Ban bata lokaci ba nace gwago mai za a tanadar mata dayafi jarin kuli da takeyi ba dare ba rana duk shi ya hanata zama hankalin ta na can wurin masu zuwa sarin mangyadan ta.
Kai naji yace yanzu kina nufin gwago har yanzu tana irin aikin wahalan nan na kuli nace da hannunta ko take komai wallahi.
Nisawa naji yayi yana kaiwa kwance nace Uncle kuna waya da anty kuwa ?
Yayi dan guntun murmushi tare da fadin ina jiran sai ta huce da kanta zata nemomu don yanzun ta hau sosai .
Nisawa nayi nace a kullun idan na tuna irin alherin dake tsakanina da ita ban jin dadi a raina da haka ta kasance a tsakanin mu.
Baiyi magana ba sai kamomi dayayi zuwa jikin shi muka kwanta anan labarin ya canza sallon shi.
Washe gari bayan ya gama karyawa ne alokacin gwago na da mako biyar a wurin mu kamar yadda yace kudi ya dora min saman cinya na yana fadin ku shiga kasuwa da gwago asaya mata duk abinda take so don Allah kada kibi son ranta a sai mata duk abinda ya dace da ita.
Dago fuska nayi ina kallon shi ganin yadda ya daure fuska yasa na kasa fadin abinda nayi niyar fada mai din.
Sai dai da ganin fuskana kasan so nake ince mai hidamar da yakeyi a kaina sunyi yawa haka gani nayi ya gyada min kai tare da fadin karki ce min komai indai ba so kike ki bata min rai ba.
Ajiyan zuciya na sauke tare da fadin Uncle ni may zance sai dai inci gaba da maka fatan alheri Allah ya saka da alherin sa.
Sai dai ba zan iya boye maka ba ban taba ganin mutum irin ka ba a rayuwa na har tsoro nake ji kada yan uwanka su fara zargina akan haka.
Murmushi nan nashi ya sakar min inda ya fara tafiya yana fadin yau ba zan samu rakiyan bane ?
Na mike da sauri ina fadin ban isa ba ai a tare muka fito ina rike da yar briefcase din shi har zuwa bakin motar shi inda iya nan nake tsaya dama.
Sai da yayi kissing din goshina ya fara tuki yana cewa ku fita da wuri don idan yamma yayi tafiyan ba dadin fita garin.
Na dawo ciki cike da murna a nan falo na samu Zarah ta fito ban tsaya ta kanta ba na nufi dakin gwago tabi bayana da kallo.
Zaune na samu gwago ta kura ma tv ido ga tasbaha a hannun ta tana ja tayi kyau ta kara kiba da haske sosai nace kai gwago wanan irin kyau haka karfa ki koma inji zawarori sun fara zuwa wurin ki.
Dakuwa ta nuno min tana fadin wani shegen bazawari zai zo wurina yanzu ai sunyi nacin su sun barni nan so sukeyi su dan cinye abinda muka dan gada su barmu muna leke a gidan wasu.
Don gaskiya gwago batayi tsufan da za a ce bata da aure don kunsan yadda aure yake a kauye irin auren nan na wuri atara zuria da wuri.
Sai da na zauna kusa da ita sannan na fito mata da kudin na aje a gabanta tabini da kallo sai kuma ta juya ta kalli kudin dake gaban ta tare da zaro ido.
Dariya nayi nace gwago kidin ki ne yace zamu shiga dake gari a sayo maki duk abinda kike so kuma ya ce don Allah a saya maki abinda naga zaki bukata indan kin koma gida.
Zaro ido ta karayi tare da fadin yar nan duk wanan uban kudin duka nawa ne haka gaskiya sunyiwa ki raba uku ki maida mashi da kashi biyu kice na gode.
Sauran na samu na kara jari ai sun isheni sayen buhun gyada goma nan gaba kin ga jari ya tasa ke nan nan gaba.
Da sauri nace a a gwago Allah ne ya kawo muna hutu a karkashin shi Allah ya duba wahalan mu na can baya lokacin da sai kin dauko abinci a gidan ki kin kawo muna muci da sauran abin amfani.
Don haka ma kin madaiji abinda ya fada wai na kaso maki su duka idan mun fita da sauri naji tace waneni wanan kudi yai yawa da kashewa yar nan.
Haka dai na lalabata ta shirya driver ya fita damu mu uku da zara muka fita gwago batayi niyar a sai mata abin kwarai ba so tayi ta dunkule kudinta ta koma gida dasu.
Amma naki yarda sai da na sai mata abinda naga zasuyi mata amfani idan ta koma da tsaraban da zata kai ma mutanen gida.
A gajiye muka dawo gidan sai dan abin motsa baki da muka sawo muka zauna nan mukaci muka kora da drinks zarah ta mike ta shiga dakin ta tare da abinda na sayo mata a fitar namu.
Bayan mun huta na dora girki na dawo wurin gwago na dubata tare da dan taba hira na koma ban sake dawowa wurin ta ba saida dare bayan na gama komai kafin ya dawo don ranan yayi dare bai dawo da wuri ba na fara hada mata kayan ina mata bayanin komai da wanda na sayo masu mama Jummai zata kai masu tsara da yaran su.
Sulaiman ya dawo gidan da alamun a gajiya ya dawo don tun bai shigo gidan ba ya rage sassauta tie di wuyan shi tare da balle rabin anineyan gaban rigan shi.
Sannu da zuwa muke mai daga ni har gwago yana amsawa da kyat yana kaiwa zaune yace gwago ana nan anashiri ko tace kaidai dan Albarka sannu da kokari wanan irin abin arziki haka mai yawa baka gajiya da dawainiya damu ?
Yace kai gwago ai albarka ku muke nema ko yaushe don abinda muke nema yayi albarka tace haka nane ubangiji ya kara rufa asiri Allah ya kara daukaka da nisan kwana .
Ya amsa cikin jin dadi da amin gwago abinda muke nema ke nan gare ku addua da fatan alheri ya juya inda nake tsaye ina saurare su bayan na gama hada mata kayan.
Yace madam yaya gida yana mikewa tsaye yake fadin haka nace Alhamdullahi yaya gajiya aiki yace not bad nabi bayan shi muka fita tare har zuwa dakin shi dauke da briefcase din sa dana karba.
Muna shiga dakin ya zube saman gado gaba dayan shi na aje na juyo ina kallon shi bayan na aje jakkan a ma ajiyar shi takowa nayi zuwa wurin na duka a hankali na fara cire mai takalman dake kafan shi tare da safa sai naji ya sauke ajiyan zuci bandaki na shiga na hada mai ruwan wanka.
Na fito still yana kwance a yadda na barshi ga ruwa can ya hadu uncle na fada mashi ina kokarin fita dakin don na dora ruwa a kattle.
A lalace naji muryan shi yace madam na juyo da ina kallon shi yace da wanan yarinyar kuka fita sayayya dazun ?
Nace eh zarah ko ?
Sai naji yayi gajeriyar murmushi yace I know it dama mikewa yayi zaune bai bi ta kaina ba ya fara kokarin cire kayan shi.
Ya barni tsaye ina jimamay tambayan shi gare ganin baita kaina yasa na fita dakin naje yin tsabgan gabana.
Bayan ya fito yaci abinci bai dade ba ya koma dakin shi tun bayan gama kallon news da yayi tare da cin abinci.
Nima sai banyi nawa ba na gama na samay shi a dakin amma yana waya a lokacin ga yadda na fahinta kafin in shigo fada yakeyi a waya amma ina shigowa sai ya rage sautin fadan shi tare da fadin na fada maku bazan dauki wanan halin ba.
Wuce shi nayi na dauki flask din na tafi daga dakin har na dawo waya yake na aje na samu wuri na zauna a bakin gado wayan ya kashe yana mai sauke numfashi tare da wurga wayan saman gado ya shiga ban daki nikan kwaciya nayi kafin ya fito.
Banji fitowan shi ba sai muryan shi da naji yana fadi daga bayana don may kika dauki yarinyar na kuka je sayayya da ita?
Na juyo da sauri yana goge jikin shi da towel nace uncle naga zamu barta gida ita kadai ne yace a harzuke ku barta mana sai may?
Ai dama bari nayi kisan halin su da kanki basai nayi warning dinki ba yanzu kin ji abinda tayi ta buga waya tana cewa wai kudi nake sakar maki kamar may don ko gwago da zata tafi wai ba karamin kudi na bayar ba akatafi kasuwa mata sayayya.
Ban san lokacin da na mike zaune ba yace yes dama na sani kadan daga cikin aikin su ne wanan.
A mairaraice nace uncle wani abu yafaru ne ?
Ya faru mana daidai lokacin da yake hawa saman gadon yace waya tayi gida wai take fada masu a hankali nace Zarah din yace dama may ya kawo ta ?
Shiru nayi a raina nace wai rufin kofa da barawo ke nan ashe idon su hajiya ce Zarah ban sani ba ashe da munafuka muke zaune a gida aiko nawa ya ya samay ni.
Tunanen may kike yi dama baki san ma,anan zuwa da ita da uwarta ta matsa ma hajiya sai munyi da ita ba.
Aisha ta fada min komai tun can hannatu ta fada min komai amma tunda naga ke kina da raayin zama da ita yasa na kyale sai tayi maki.
Da wanan bakin cikin na kwana a raina na Zarah da safe da na tashi bayan nayi sallah naje muka gaisa da gwago ban tsaya ba kitchen na shiga don dora breakfast.
Sai na samu har Jonh ya shigo yana yayanka kifin da zaiyi ferfesu dashi don shine mai muna abinci ni kuma kazantar cin abincin shi nakeyi shiko uncle bai damu ba cin abinsa yake yi.
Na gaisawa mukayi da shi tare da fada mai ya barshi zanyi baiso ba amma ban bashi fuskan tsayawa ba ya fita daga kitchen din.
Bai dade da fita ba sai ga zarah tashigo muryan ta naji daga bayana tana fadin anty ina kwana ?
Dan juyowa nayi ina amsa mata tace dani may zan kama maki anty ?
Nayi mamakin jin tambayan don bata fitowa haka da safe sai idan mun gama tace barci ne ya dauke ta bata san gari ya wayewa ba.
Yau kuma ko tafito ganin wani abin ne ta sake fada ban sani ba sai nace da ita ki barshi kawai ba wani aiki mai yawa zanyi ba ai.
Tayi dan jimmm sai naga ta nufi wurin dankali nace ki barshi yau ba zan soya dankali ba ai nan naci gaba da aiki na share ta.
Ta dan jima atsaye sai ta juya ta fita daga kitchen din na gaba na ba kowa nasa wanka nayi kafin ya fito na shirya cikin wasu atamfan Super mai launin makuba na fito zuwa wurin shi.
A tare muka fito dashi daya gama shiri tana falo wanan lokacin ganin mu yasa ta zamo daga saman kujera duk ta daburce da ganin ta bata da gaskiya ko kadan ta na gaishe shi a daure ya amsa mata.
Bayan kwana biyu gwago ta koma gida tare da abin arziki mai yawa da ta samu wurin maigida don har injin din tatsar mai ashe ya saya mata duk bamu sani ba sai da ta koma nakejin labari.
Naso bayan tafiyan gwago in daure ma zarah amma sai nayi shawara na fasa nuna mata nayi ban san komai ba gaba na da yawa ai.
Sai dai na bar yin komai a gaban ta yanzu na kuma rage bata fuskan da nakeyi sosai so nake ita da kanta tabar gidan batare da wani abu ya fito daga gare mu ba.
Wata na biyu cur a gidan uncle na canza acikin dan kankanin lokaci saboda abin more rayuwan da nake samu a gidan shi.
Don babu abinda ya rage ni dashi na fannin rayuwa duk wanda ya ganni sai yayi maganan canzawa na ni kaina nasan ina daga cikin matan da suka dace da gidan miji.
Banda tunanen komai a raina in ma ina da bai wuce na ciwon dake jikin mu ba kuma Alhamdullahi muna samun kula yadda ya dace sosai dama abinda ciwon ke bukata kenan.
Haka zai sawo abubuwan kara jini ya sakani a gaba sai munci tare magani kuma idan yana gari a tare muke sha kullum kafin mu kwanta don ka,idar shan shi ke nan.
Yaya Saadu yazo sau biyu a lokacin don ba a gama gyaran gidan da zai zauna ba sai yake zuwa yana komawa.
Ranan ina daki kwance dakina da yamma daidai lokacin dawowan uncle gida ta kusa sai ga zarah ta shigo da sallaman ta dakin tayi sallama na amsa mata ta shigo ba kasafai take shigo min daki ba sai idan da wani dalili.
Anty kin yi baki tace min na dago daga kwancen da nake ina fadin baki tace eh suna falo zaune suna jiran ki.
Dama bani zama babu kwaliya a gida tsab nake banda wani kushe a jikina kara dan gyarawa nayi dakyau na fito don ganin ko su waye suka zo.
Mata na hango zaune su hudu a falo sai dai ban sheda ko su waye ba daga nesa sai da na karso wurin ina fadin sannu ku da zuwa gaba daya suka juyo sai da gabana ya fadi.
Fon ganin bakin nawa don ba kowa bane anty Uwa ce da yaranta uku gaba daya a gidan namu, , ,


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/17/20, 10:17 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , , ,


🧕🏿5️⃣8️⃣🧕🏿


NOVEL DIN NAN NA KUDI NE IDAN KIN FITAR UBANGIJI YABI MIN HAKKINA A KAN KI/KA DON WALLAHI BAN YAFE BA, , , ,


Ganin bakin nawa take naji gaba na yayi wani irin bugawa don tsoro da fargaban ganin su haka a gida na may ya kawa su kuma nake tambayan kai na.
Muryan anty uwa ne ya dawo dani daga duniyan tunanen da na lula da farko naji tana fadin a, a tau, amaryan ce wanan masu gari tana bin zanin jikina da kallon tun daga sama har kasa na binshi da kallo sukeyi.
Allah ya rufa min asiri yau da safe bai fita gidan da wuri ba don haka na sha kwalliya tun da safe da atamfan brocade a jikina.
Dinkin shi mai kyau tun daga Dubai ya sayo min shi hakana din kakken shi murmushi na kakaro a fuska na ina cewa dasu sannuku da zuwa tare da sakin fuska sai da na zauna nake cewa ina wuni Anty Uwa kamar yadda naji anty na na lagos na kiranta dashi.
Waya na dauka ina latsawa mai aikin mu na kira ina fadin make something special for our visitor's.
Na gama na dago tareda cewa sannun ku da zuwa duk naga sun kura min ido sai bin gidan suke yi da kallo sauran yaran nata itako sai faman tabe baki take yi.
Mun gaisa sai dan shiru ya biyo fallon anty uwa din ne ta kawar da shirun da falon yayi a lokacin.
Ji nayi tace dani maigidan ya fitane ko yana ciki nace ya fita yana gun aiki sai zuwa yamma zai dawo gidan.
Dakatar, ni , wata daga cikin diyan nata, tayi da fadin ai dama bashi muka zo gani ba gun ki dai ke snacher muka zo,
Murmushi nayi don jin sunan da suka kirani da shi wanda su ya dace a kira da sunan tun farko amma sai gashi suna lakakamin sunan don basu da kunya.
Uwar ne ta dakatar da ita da fadin dakata lawisa sai ta juyo gare ni tana fadin ke wama kike da suna what ever dai ba mun zo bane nan don dogon surutu sai don mu zo mu ga idon yar kauye kamar ki da har ta iya kwacen maza haka son ranta.
Tun wuri ki san da sanin Nafisa zata shigo gidan don haka ki zauna da shirin taron ta ke wanan gidan ma ai sam bai dace da irin ki ba yar kauye ga gida har gida amma wai yar kauye gaja ce irin ki a gidan ba ilimi ba komai.
John ya shigo da tire shake da drinks da sauran abin taba baki ya girke a gaban su don basu da kunya sai suka zari guda guda suna balla bakin su tare da kafa kai.
Duk da uwar taji kunyan abinda sukayi sai dai banda ita Nafisa din fada ta fara yi musu akan su natsu mana suyi abinda ya kawo su.
Ina zaune na kafa masu ina kallon abinda ke wakana nasa yatsan hannu na guda na tallaba haba na dashi tare da kura masu ido.
Bayan sun dan natsu ne uwar taci gaba da fadin yanzu ke har kin san ki yaudari matar da ta tsamo ki a cikin talauci da wahala ki tsallakata bayan ta gama maki komai kin gudu kin barta don halin dan adam butulu saboda kina hangen nesa.
Yanzu ke baki ji kunyan asirce ta da kikayi tun farko ba bai maki ba kuma kika asirce mata kanin miji da bakar asirin ki don kawai kin samu labarin yar waje na yake nema yanzu.
To ai baki sani ba idan asiri kike takama dashi nafiki idan kuma barikanci da iya duniyan ci kika ce kin iya duk na dama ki na shanye.
Gidan nan sai Nafisa ta shigo shi ko yau ko gobe ki zauna a cikin shiri don da ta shigo waje kika yi ke.
Don gidan nan ba gidan zaman ki ba bai dace da mace yar kauye kazama irin ki ba don haka ki sani, , , , , , ,
Madam yaya gida ya fada ba tare da ya kallo mu ba driver shi na binsa baya da jakkan shi na ai har ya nufi hanyan dakin shi sai kuma ya juyo yana cewa sorry baki kikayi ne ?
Murmushi nayi tare da fadin anty Uwa ne fa da yaranta da, , , ji nayi ya katse ni karasa magana na da tambayan da ya daure min kai.
Uwa waye uwa ya fada yana maimaita sunan cikin daure fuska dan gyara zama tayi tana fadin Sulaiman baka gane ni bane ?
Uwa sister din yaya Lawal soja dake Lagos minjin maimuna wai kana nufin ka manta dani uwa na gidan malam garba teacher.
Katse ta yayi da fadin kenan ke sister din lawal ne ko kece ke zaune a nan garin da sauri tace eh nice ai , yace anzo diba madam ne ?
Wani kunyan ne ya kamata ba ita ba har diyan nata sai da sukaji nauyi don yanzu suka gama cika baki akan shi gashi kuma ya shigo ya nuna baida halaka da su asalima bai san su ba.
Yana batun wucewa na bude baki da sauri ina fadin Uncle bakin ka ne fa , don wurin ka suka zo da mamaki yake kallon fuska na kuma ya dan kallon su sai ya dawo ya zauna.
Na mike zan nasu wuri ya ce No zauna idan sunzo wurina ai kamar wurin ki suka zo so ki zauna ba wani abu bane ya juya wurinta yana cewa lafiya ko hajiya ?
Duk sun natsu ta kasa magana sai mai bi ma Nafisan ce ta fara mikewa tana fadin sai da na fada maku kada muzo gashi munzo an wullakanta mu a banza.
Karamar tace wai kana nufin ba ka masan Anty Nafisa ba ko may ta juta wirin uwar tace mummy duk wanan abin da akeyi dama bai san ku ba ne ?
Mikewa yayi yana fadin tunda baku ma san abinda ya kawo ku ba zaku iya fice min daga gida don Allah bana son a shigo ana damuwar mu.
Waima yaba su daman shigo min gidane ya fadi tare da mikewa yana fita hanyan waje suma da sauri suka mike zasu tafi nace to Anty uwa na gode da ziyaran da kuka kawo min sai gani na biyu kuma.
Ban san ko ina gidan ko kun fitar dani don yarki yar birni zata shigo niko yar kauye ne bankai matsayi zama da su ba.
Sai dai zaku ya tafiya da drinks din nace ma yaran tare da nuna masu tire din da suke ciki nace don naku ne ku aka kawo ma kushi daga haka na juya na fara tafiya komawa ciki nan na barsu tsaye da takaici.
Suna jin yadda yake ma maigadi fada duk wanda yazo kada ya sake barin shi ya shigo mai gida kai tsaye batare da an bashi umurnin ya bude mai ya shiga ba.
Ko ba komai naji dadin yadda uncle yayi masu a raina don da bai dawo ba Allah kadai ya san irin cin fuskan da zasu yi min su tafi sunci bulus.
Da ya shigo nan falo ya zauna yana huce har yana fadin zai kori maigadi da sun shigo sunyi wani abu fa may zaice shi.
Na dai samu ya sausauta ta hanyar kawo mai ruwa da bashi baki yayi hakkuri ya kurbi ruwan ya dago kai yana fadin kin san ida Allah bai dawo dani yanzu ba iya abinda zasu yi maki.
Zan kira in fada ma mijin ta kada ta kara zo min gida may ye hadina da ita da dan uwanta nake da zumunta ba itaba.
Ya dafe kai da hannu guda tare da lumshe idanuwan shi don takaicin da ke damun shi lokacin ranan haka ya karasa shi babu wani walwala a tare da shi.
Washe gari da muka tashi yana kule dasu a ranshi ya baci da su sosai sai zuwa sha daya saura ya fito falo ya zauna.
Na fito da kayan yake farce a hannuna ina son gyarawa sai naji yace da zaki iya dakin fara gyara min nace Uncle ke nan may zai hana in iya aikin lada.
A hankali na sauko kasa inda na fara da yanke mai na kafafuwan shi gyara nake mai yana waya sai ajiyan zuciya yake sauke wai.
Har na gama gyara mai kafafun shi yana a kan wayan naji yayi sallama da wanda yake wayan daidai zan tashi in koma saman kujera in fara yanke mai na hannuwan shi.
Ya kare wayan daidai na dago hannunwan shi zan fara gyarawa yake ce abokina na Canada yana gaida ke ina sa ran zamu tafi nan da wani dan lokaci.
Da sauri na kallo shi nace uncle dani fa kace ya dan subbanci kuncina yace ke fa madam nace Allah ya nuna muna lokaci lafiya Amin yace.
Ya soma magana kamar mai rada bakinshi a daidai kunne na naga alaman kina farin ciki da tafiyan nan ko ?
Nace ai dole uncle don ban taba fita daga cikin kasan nan zuwa wata kasa ba sai wanan karon.
Ya fiddo da karamar dariya yana matsa hannun dake cikin hannun shi yace tafiya ai yanzu kika fara shi don tare zamu dinga fita duk inda zan tafi sai dai idan kinyi ciki ya tsufa zan dan baki hutu a lokacin.
Da shagwaban murya nace uncle ka bari don Allah ni fa ban shirya haihuwa yanzu ba da sauri ya kalle yace baki da tausayi ne ?
Yanzu duk su Aisha suna da yara wanda ada hakan baya damu sai yazo da nayi aure naji nima ina son na shigo gida in samu mai min daddy oyoyo .
Shiru nayi ina tunane don nima yanzu haihuwa ne tashin hankalina don wanan ne karo na biyu da yake nuna min yana son haihuwa sosai.
Don haka ba abinda zan iya farauta mashi rai da shi a wanan lokaci sai daukan ciki da ya kwallafa rai gare shi.
Na nisa ta yadda yake iya jina yace da sauri naga kamar ke abin bai damay ki ba ko nace ba hakana bane Uncle.
Haihuwar dai naga baizo inda ake neman shi ba sai wurin da ba a maraba dashi ina tuna haihuwa na na baya ne kawai.
Da sauri yace kin taba haihuwa ne a hankali na gyada mashi kai alaman eh naji mamaki da baka san na taba haihuwa ba uncle.
Yace ban samu wanda ya fada min ba cikin masu bani labarin ki a hankali na fara bashi labarin haihuwa nawa fuskan shi kawai zaka kalla kaga alaman tausayawa a cikin ta.
Shafo fuskana naji yayi gami da lumshe idanuwan shi yana sauke ajiyan zuciya yace haka abin yake ya samu yai sakaci da samun shi.
Abin da nake gani ya taba yarinyar don baku amsan treatment a lokacin har yakai abin ya shafi yarinyar a ciki nace uncle sai bayan haihuwar ta nasan cewa ina da cutar a jikina.
Koshi sai da yaya Saadu yaga zan halaka ne yasa a kaini asibiti a dubani shine aka san ina dauke da cutan a lokacin don kowa bai kawo haka ba a ranshi.
Yace ni kin ga tun da na samira ya baiyana na tafi akaimin awo sai aka samu nima na dauka sai dai nata yafi karfi akan nawa ne.
Sun dai cuce mu nace dashi yace sun cuci kan su dan zunubi akan su yake Allah ya gani bata zina muka samay shi ba shine saukin mu ga Allah.
Ciwo kuma kaffara ne ga bayin sa kin ga mun samu riba biyu ga abin koma ukku zance idan ba ta sanadin hakan ba ai wata kila ba zamu hadu ba.
So ki fitar da zancen cewa sun cuta muna don ni tu lokacin na bar ma Allah sanin sa akai kin ga ta ida ya saka min dashi kuma.
Na gama yanke mai akaifar na tatara na zuba a inda muke zubawa kafin mu binne wani akaifa da suma da nake tarawa idan sun cika sai na fita baya can in tona rami in rufe su.
Koda na dawo saman kujera two setter na koma na kwanta nayi rigingine ina lallon fankan dake kadawa a hankali falon.
Shima dai shiru yayi nasan akwai abinda yake tunane a zuciyar shi wanda kila bai wuce zancen haihuwan da yaji na taba yi ne koma may ye ai bai nuna min komai ba a fili.
Sai naji ya jefo min tambaya a bazata dacewa na dauka idan mace ta taba haihuwa ai ana ganewa ne ?
Murmushi nayi na dago tare da cewa uncle may kake son ka gane uncle a kai sai ya murmusa kawai yace forget.
Nace tau ni dai tun haihuwana yarinyar bata ma sha nono ba don haka har ta koma banda ruwa bata sha wani abuba a duniyan nan.
Yace kai labarin akwai ban tausayi wallahi abinda mutane da yawa ke fuskanta ke nan yanzu har bakin ciki ya kashe mutum yanzo idan da za a fadi halin da mutane da yawa ke ciki akan lalurar nan sai ka tausaya masu.
Nisawa nayi daga inda nake kwance nace Allah ya sauwa yace amin wayan da aka bugo ne ya dakatar muna da hiran namu nan dai na mike na shiga kitchen ban fito ba don yau yana gida na tsaya hada mashi abinci da zamuci.
A kitchen din ya samay ya byo bayana lokacin ina motsa miya sai jin hannayen shi na ji saman jikina ya rugumay ni ta baya yana fadin.
Na ga dai baki aminta da aikin John a gidan nan ba yanzu na nisa tare da fadin Uncle da raina da lafiya na zan kwanta kato na yi min girki ina ci.
Juyo dani yayi daidai na gama motsa miyan ya juyo dani muna fuskantar juna yace idan aikin namiji ne baki so sai a canza muna da mace dama dauko shi nayi a maaikatar su .
Don banda mace a gida ne nace a bani na miji yafi yanzu kuma tunda kin zo da magana sai a bamu mace don gaskiya bazan lamunci kina shiga kitchen wanan jikin naki da nake huta gajiya na a cikin sa ba yana daukan zafi.
Kunya maganar ta bani na yi saurin dukar da kaina daga kallon shi yace ai gaskiyana fada nafison ki huta ko yaushe sai idan yara sun zo kuma ki ji da namu lalurar duka.
A hankali na dago nace uncle kana ganin hakan ban cutawa shi john din ba dakai naga sabo ya shiga tsakanin ku kama a gaskiya yana jin dadin aiki dakai din.
Kada nazo na shiga rayuwan shi in nayi mai haka kamar na toshe mai wurin samun shi ne ai murmushi yayi tare da dan buga mi baya na yace .
John zai zauna sai ki sama mai abinyi a gidan kada yayi ta karban kudin banza ko macen kuma za a kawo maki ita goben nan in Allah ya kaimu hakan yayi maki ko.
Nace yayi uncle na gode sai dai macen ta kasance musulma uncle don Allah yace kuma dai za a duba ba matsala da haka har na kare na kwashe na koma nayi wanka na shirya na fito muka zauna cin abinci .
Ban yi fushi da zarah ba ina dan kula ta muna zama muyi hira sai dai bata gane komai a gidan yadda take so.
Ranan yaya Saadu ya shigo da marance bayan na cika mai ciki da abinci nan suka zauna da shi suna fira ganin sun dauko hiran aiki yasa na dan basu wuri na samu zarah a dakin ta kwance.
Tana ganina ta mike zaune nace ai na dauka barci kike yi ne tace a a kwantawa dai nayi naga yau yaya yana gida bai fita bane shiyasa ban fito ba.
Wuri na samu na zauna kusa da ita ina cewa don yana gida shine baki fita ta dan murmusa tace ban san abinda nayi wa yaya ba baya kallona a yar uwanshi kamar kice yar uwar tawa yanzu don kice kawai may kula ni a gidan.
Nace a a zarah kin fi ni sanin waye uncle fa dan a tare kuka taso wuri daya dashi yakamata ace kin san ko waye uncle yanzu.
Murmushi tayi kawai mai kama da yake tace nima ina ganin dai gida zan koma nace tun yanzu Zarah mai mukayi maki kuma ?
Tace babu komai anty gani dai nayi kamar zaman nawa yana takura maku ne nace ko daya wallahi kece dai kika kasa sakin jikin ki damu.
Nan dai na zauna mukai ta hira da ita sai da uncle ya kirani nabar dakin nata yaya Saadu ne zai tafi shine kiran da yake min din.
Nan yaya din ke fada min zai koma gobe dawowan da zai yi tare da iyalin shi zai dawo garin naji dadi sosai yake ce min yaya waya gida dazun da yana hanya.
Naji dadin haka yace baba ya fada min abin arzikin da maigidan ki yayi masu da sauri na juya na kalli uncle din .
Yace tau bai fada maki bane bana baba da ummi zasu sauke farali a kasa mai tsarki har da Sani don ya kula dasu.
Bansan lokacin da na juya wurin uncle din ba ina murna yaya yace ai na rigaki yin godiya ko ya fice yana yi min dariya.
Ranan ban san ma irin godiyan da zan ma uncle din ba mun dai kwana muna farantawa juna rai kawai don banda abin bashi bayan wanan din.
Kwana biyu dayin haka na samu uncle a daki yana shirin fita nake cewa ina son zuwa gidan Anty Aisha.
Kamar ba zai yi magana ba sai can yace nafa fada maki ban son yawo a rayuwana nafin inganki a gida kullun.
Nace don Allah uncle kayi hakkuri ba dadewa zamuyi ba koshi don munyi waya da itane tace yaran ta biyu ba lafiya.
Yace sai ki shirya in sauke ku in zan fita nima in duba yaran daga can naji dadin hakan don dama tana min korafin bai taba zuwa gidan ta ba.
Mun isa gidan akai muna iso mun samu maigidan ta dakishiryata zasu fita a lokacin nan dai muka gaisa dasu.
Mijin nata yana ta faman kamay kamay da gani baida gaskiya nan suka fice suka barmu da ita munga yaran basu da lafiya har lokacin.
Yake tambaya ko an kaisu asibiti tace baban nasu ya sawo masu magani dai tace baida kudin kaisu asibiti sai naga ya tabe baki kawai.
Yana bin gidan da kallo bai dade ba yace shi zai tafi zai dawo karfe hudu ya dauke mu naji dadi sosai da zai fita ya kira Aishan suka fita tare.
Ta dawo tana murna tana fadin yau maganan hajiya ya tabbata yau yaya ne a gidana Safiya ?
Murmushi nayi nace albarkacin yaran ki ne ya kawo shi tace a a albarkavin ki dai gashi har da zama gidana yau safiya abinda kullun gidan nan ake min gori dashi.
Nan dai ta shiga bani labari don ta tura zarah tai muna girki haka yasa ta samun daman sakewa tana bani labarin halin da take ciki a gidan.
Na fahinci abubuwa da dama a gare ta sai da bance komai ba banda hakkuri da na bata ta fitar da kudi masu yawa tana nuna min wai uncle ne ya bata su takai yara asibiti.
Nace kin ga ko sai ki kai su don asan halin da suke ciki tace ai gobe in sha Allahu zan kai su anan dai muka wuni tana cikin farin ciki damu.
Ya dawo ya kwashe muka tafi tana ta mashi godiya mun dauki hanya ne naji ya nisa tare da fadin mai kika fahinta a zaman Aisha a gidan nan ?
Nace bari mu sauka uncle akwai magana ai sai ya dan kalli zarah dake baya zaune yayi tsaki har muka kai gida ba wanda yayi magana a cikin mu.
Sai da mukai sallah ishai muka dawo falo nan na dauko mai maganan Aisha din yace tun farko sai da na fada masu ba mutumin kirki bane suka ji.
Alokacin yana sakar masu kudi sun dauka mutumin kwarai ne niko tun tasowan mu dashi nasan dan karya ne sosai.
Nace uncle yanzu tunda har akwai haihuwa har uku a tsakanin su baza a bi ta wanan ba taimaka mata ko masu su duka ya kamata kayi.
Ta hanyar sama masu sanaa da zasu dogara dashi da yaran su don na fahinci tana cikin wani hali a gida don baka ga part din kishiyar taba tsan wallahi amma ita ga nata kamar na wata tsohuwa can.
Tsaki yayi yace ko an bata wanan mugun mijin ai ba zai bar mata ba nace uncle adai tamaka mata din yafi don gorin da suke mata a kan ka.
Yace gori fa ?
Shi har yana da bakin da zai min gori akai wanda kulun yana office dina da bukatar shi nace kagani shike morar ka itako bata kosan anyi ba.
Yace zai kira Aishan idan yaranta suji sauki ansan abinda za ayi mata din nace uncle mun gode wallahi.
Kallo na yayi yace wai ke a ina kika koyo wanan godiyar taki ce haka tun bakiga may zanyi ba kina zabga min godiya haka.
Nace koma may zakayi indai ka gyara mata wurin zamanta ka bata abinda kudi zai dinga shigo mata ai ka gama mata komai.
Yace ai ido nasaka masu daga su har hajiyan don naga gidun su nace uncle kayi kuskure wallahi idan basu dadi a wurin ka ba duniya wurin wa zasu ji.
Nan dai nayi ta kawo mashi musalai iri iri yana saurare na bai yi magana nasan dai ya gamsu da bayani na ne da nakeyi.
Yace wai ke indan da kin yi karatu mai zurfi zan iya dake kuwa Safiya ?
Nace uncle don may ba zaka iya dani ba ai fahinta daban fannin aure daban don haka karkaji komai a kaina .


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/18/20, 10:16 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , ,


🧕🏿5️⃣9️⃣🧕🏿


NOVEL DIN NAN NA KUDI NE IDAN KIN FITAR UBANGIJI YABI MIN HAKKINA A KAN KI/KA DON BAN YAFE BA, , , ,


Kamar yadda yaya Saadu ya fada haka ne ya faru don yayo kaura daga kalaba zuwa abuja da iyalin shi inda suka zo da yar uwan Samira da mijinta ya rasu zata dan kwana biyu a wurin su.
Sai bayan kwana biyu suka zo gidan mu don bamu da wani nisa sosai dasu dasu ban san da zuwan su ranan ba sai ganin su nayi kawai a gidan.
Sun shigo ina daki Zarah ce tazo tana fada min zuwan su cewa tayi nayi baki suna falo azatona ko anty uwace suka sake dawowa gidan.
Amma kuma sai nayi tunanen mai zai kawo su kuma in ba rashin zuciya ba yadda aka kwasa dasu din nan ya nuna shi sam bai san su ba.
Wanda kuma nasan yayi hakane don ya kakabe su daga gidan namu gaba daya da zuwa don zuwan nasu babu alheri a cikin sa.
Fitowa nayi sai mukayi arba da sister kamar yadda suke kiran safiya karama dashi.
Nace Lah bakin kalaba ne a gidan namu baku tsaya munzo taron ku ba har kun tula min nauyi na aka ?
Samira tace a, a mun huttar dake aikin san ke amarya ce ba a matsamaki yanzu na samu wuri na zauna ina mikawa sister hannu tazo wuri na sai yarinyar ta make hannun ta bata zuwa.
Gaisawa mukayi ina tambayan su mutanen gida da sauran yan uwanta tare da fadin ai na dauka zaku zo min da mummy ne wallahi.
Tace mun so mu zo da ita kodan azumi dake tafe takine sai da gabaya zata biyo mu in dan ta shirya.
Nace kai mummy ho har wanu shiri zata yi kuma makin ta biyo ku kawai kuzo tare samira ne tace wai Safiya kin ko ga yadda kika canza gaba daya.
Nace kai samira dashi kuma zaki tare ni tace wallahi safiya kin canza gaba daya komai naki ya canza kamar ba Safiyan yaya saadu ba.
Dariya muka ka kwashe dashi gaba dayan mu falon nace aikin Uncle tace aina gani wallahi gaskiya aure ya karbe ki sosai wallahi.
Nayi murmushi dadi har cikin rai na nace bakomai bane Samira sai kwanciyan hankalin da na samu yanzu.
Nura na kira sabuwar mai aikina yar kabilar yarbawa ce ita ta shigo nake cewa ta kawo ma bakina abin sha ta kuma hada abinci dasu don da mu zasu wuni.
Samira ne ta dakatar da ita da cewa wallahi a koshe muke don bamu dade da karyawa ba muka fito gidan.
Gaba daya Samira sai yabawa da yadda aure ya sake ni take yi nan take fada min ai jiya yayan ki yayi waya gida ashe ita yar uwar ki ta haihu ne kuma mijin yaki aurar ta ?
Nace wallahi ai yanzu takai wata biyu da haihuwa kyale dan iska so yake sai anbiyu mai ta bayan gida akan zancen zaimai da hankali ayi.
Tace ai naji yayan ki na fadin karshen mako zai tafi abinda ya hana Sani zuwa kenan cikin satin nan yace ya jirashi sai ya zo.
Nace kai mutane sai sannu baison ta yayi mata ciki dan iska kawai tace ai haka yayan ku ya fada shima yace dole ya aure ta don bai baro garin nan sai an daura auren su.
Nace haka yagi wallahi don idan anyi mai sakwa sakwa tsarewa zai yi ya barta da yaron tana wallaha ita kadai.
Tace ga uwar su wata kala ita kuma naji sani ya bugo ma yayan ku waya yana fada mashi rashin mutuncin da tayi ma mama ranan.
Nace kai inna ai sai a hankali ta tare da fadin akan makkan da su baba zasu tafi ne wai mama na maula gashi an biya wa mahaifiyar ki anbarta nan.
Wanan matar ai halin ta sai ita Samira ni ban taba ganin mace irin ta ba wallahi diyan ta tun suna bayan ta har sun gaji sun gane ta yanzu.
Tace wai itama ko yadda minjin nan naki ya rike Sani bata ko jin kunya ta rage wani abin amma sam bata san wanan nace wa inna aima yanzu ta rage wani abu don baba ya fita bayan ta yanzu.
Nan dai muke ta hira har muka shiga hiran gidan su yaya Saadu take fada min kwanaki sun tafi gaida gwago sun samu jikin yaya Ahmed yayi mai tsanani yana kwance yana jiya a gida.
Allah ya bashi lafiya nace da ita don dan uwana ne ko banja Allah ya isa ba Allah zai isar min da cin amanan zumuci da suka.
Murmushi nayi ina tambayan wai su habiba fa ko sun yi aure ne yanzu tace ke dai bari sadiya ce kadai a gida wai ita habiban ta tare gidan wani saurayin ta.
Sadiyan ce ta bugo waya kwanaki tana fada ma yayan yace zai zo har muka taho kuma bai je ba ko ta dawo gida ban sani ba.
Sadiya din ai da tace wai zata biyo mu ta dawo nan shine yaki yarda yace ta zauna ta kula da uwa don yanzu ba wani karfi ne gare ta ba.
Nifa Safiya ba wani shiri nake yi da mutanen nan ba tun zuwan da nayi na farko uwar da habiba ke cewa wai ya auro masu kwatakwalin ghana.
Na lah kece wai kwatakwalin ghana tace wallahi ko ai nace masu ni uwana da ubana yan katsina ne aiki dai ya kaimu kalaba baba kuma yayi ritaya bai koma gida damu ba amma har yanzu muna zuwa garin mu.
Dariya nayi kawai ina tunanen rayuwan da ya wuce baya irin cin fuskan da gwago da habiba suke min sai sadiya ce mai kula ni a garin da ban san kowa ba.
Su kuma sauran mazan biyu yanzu duk sun kama gaban su kowa ya watse dama haihuwan bariki ke nan.
Mun dade muna hira sai da muka mike zuwa sallah muka dawo muka zauna cin abinci tare muka gyara gidan dasu kafin su wuce sai yamma yaya Saadu yazo ya kwashe su.
Kafin su tafi mun dan tsaya da yaya saadu munyi magana akan matsalar saadatu dashi in da nace kafin ya wuce gida ya biyo ta wurin tukun.
Mukai sallama suka tafi lokacin shima mai gidan ya dawo wurin aiki ya samay su a gidan mintsila naji yakai min gefe na na dafe wurin da sauri ina kallon shi.
Yace yau don kin ga yan uwanki shine ko hugging ban dan samu ba nace afuwan yallabai kasan dan uwa aikwai dadi wallahi.
Ya riko min hannu muka shiga ciki yana fadin tafiyan mu fa yana matsowa don haka nake son muje ai maki pasphot din ki.
Naji dadi nace uncle ashe da gaske kakeyi batun tafiyan dani zaka tafi kai ya gyada min tare da fadin kin dauka wasa nake yi baza mu dawo ba sai mun tsaya umura daga don watan azumi da zai kama.
Don ni ban azumi a kasan nan a can saudiya nake azumina don haka nake son mu samu lokaci muyi list din mutanen da za a taimakawa.
Nisawa nayi alokacin da muka iso wurin kujerun falon tare da zaunawa sama har lokacin bai sake min hannu ba.
Nace uncle, , in uncle dama akan maganan su Aisha ne har yanzu naji shiru akan zancen shine nake maka tuni na fada tare da dukar da kaina kasa.
Tallabo habana yayi yana fadin ban manta ba ai akwai abinda nake shiryawa a kan su su ukun duka har ma da sauran yan nasu.
Sai dai da farko tunda kin matsa sai ku shiga da ita Niima house decoretion ku zabi abinda ya dace da ita sai a gyara mata part din nata ni inda mijin zai yarda sai in bata gidan da zata zauna da ga ita sai yaranta kawai.
Dadin maganan shi naji kamar yan uwa na za aiwa hakan sai nakai mashi runguma tare da bashi kiss gefen fuskan shi.
Murmushi ya sauke yace ashe kin iya nokewa kawai kikeyi yanzu da nayi maganan masoyiyar ki aikin bani ba tare da na nema ba.
Nan dai muka zauna har lokacin sallah yayi muka mike zuwa sallah ina maijin dadi sosai a raina bayan na idar da sallah ne na jawo wayana dake jone a caji ina kiran Aisha din.
Ta dauka tana fadin matar yaya dazun fa nake maganan ki a raina nace na zama yar halas ke na kin ki ambato tayi dariya kawai.
Nace kin samay tace a a matar yaya sai kin fada nan dai na kora mata albishir din dayayi mata akan gyaran wurin ta da kuma zancen mijin ta ko zai yarda a bata wurin zama ta zauna daga ita sai yaran ta kawai.
Tace cikin sauke ajiyan zuciya wallahi da yaya yaimin haka da ya kyauta min wallahi ni ko bai yarda ba komawa zan yi idan ya bani wurin zama.
Nace ki dai lalabashi ko zai yarda da hakan tace wallahi ba wanda yasan halin da nake ciki a gidan nan ne da yaya ba zai fadi haka.
Daga maigidan har abokiyar zaman nawa hakkuri kawai nakeyi a zaman mu don dai kada in koma gida ne aimun dariya da kuma yara da suke samun karatu a nan.
Nan dai mukayi ta hira tana fada min irin kuntatawan da suke fuskanta ita da yaran ta a gidan wurin kishiyar ta da mijin ta.
Shigowan shi dakin nawa ne ya katse muna hiran mu sai da ya zauna bayan mun gama wayan naji yana tambayana ke da wakuke wayane haka tun dazun.
Nace anty Aishan kace yace ok nan dai nake fada mai halin da take fuskanta a gidan har na gama baiyi magana ba dama kuma ni ban tsanmaci yayi din ba yana dai iya bani lokaci wurin saurare na.
Da safe Aisha tayi sakkon samun shi gida kafin ya fita nan dai na basu wuri suka kebe da dan uwan nata karshe dai da ya fita na shigo na samu tana share hawaye.
Ruwa na koma na dauko mata na kawo mata ina fadin tasha ko zataji sanyi take ce ai bata ko karya ba ta fito Nura na kira nace ta hada masu breakfast a daning.
Sai da taci ta koshi har yaran nace Anty Aisha kiyi hakkuri don Allah komai na duniya mai wucewa ne ga bawa.
Tace matan yaya ban san abinda yasa yaya ya kasa fahinta na ba har yanzu maganan shi guda koda yaushe akan miji nima inda nasan haka tun farko aida ban aure shi ba.
Hakkuri nake ta ba ta tare da fadin ki shirya driver zai dawo ya kaimu mu duba kayan yanzu na juya wurin yaranta ina tambayar su ko sun koshi.
Kada kai sukayi alaman sun koshi din nace to ku tashi kutafi wurin anty Zarah tana dakin ta kuyi mata fira sai lokacin take cewa zarah na gidan nan ne ?
Nace tana nan dakin ta bata fito bane sai bayan fitan yaran ne na samu magana da ita inda mukayi magana na fahinta nake kara bata hakkuri tabar bari yaran suna jin damuwan ta da mijin nata ko yaushe.
A karshe dai driver yazo na muka fita gidan bayan na rufe ko ina na gidan Nura kawai muka bari a gidan tana aikinta.
Mun tafi wurin mun kuma duba suna da kaya sosai a wurin mun zabi mai kyau cikin mafi tsada da daraja har labulen da za a saka mun zaba bayan mun gama muka kirashi mukai mai bayani.
Yace mu bashi shugaban wurin suyi magana dashi nan na bashi matar sukai magana ta fada mai kudin kayan sun tasan ma milayan daya da dari biyar yace ta bashi account din su.
Mun dawo gida a gajiye don dan zakayawan da mukayi a wurin akarshe falo muka zube duk mun kwaso gaji a tare damu sai Nura ce ta kawo muna ruwa da abinsha muka dan sha ga abinci ta gama mukaci muka tafi sallah.
Aisha ganin abin takeyi kamar a mafalki sai maganan takeyi duk zaman da mukayi daki na bude mata don ta shiga da yaranta su huta a ciki inda nima na wuce nawa dakin don yin sallah.
Bayan na idar da sallah na zauna ina tunanen ratuwan Uncle da yan uwanshi na rasa gane may ye matsalan shi da su haka.
Gashi ni yana iya yiwa yan uwa na dama wasu lalura ba tare da jin kyashin komai ba a ranshi amma nasa kafin yayi sai ya ja masu rai zaiyi.
Koma may watarana tunda ina cikin su zan ji ko may ye matsala da inda abin nasu ya samo asalin faruwa.
Ita ko Aisha tana shiga dakin dana bude masu wanda yake gyare komai akwai a cikin sa gashi kuma kullun a gyare yake duk da ba kowa a dakunan.
Wayan ta tadauko a cikin jakkan ta ida ta kira mahaifiyar ta bayan sun gaisa take cewa hajiya maganan ki ya fara tabbata gaskiya.
Yau yaya yasa mun fita da matar shi muje in zabi kayan dakin da nake so a wani shago nan dai take fada mata duk yadda akayi a wurin da kuma fadan da yayi mata kafin ya fita.
Murmushi mahaifiyar tayi tace kamar yadda nake fada maku wanan yarinyar zata zamay muna alheri a cikin mu sannu a hankali zamu samu ta canza muna shi amma fa sai kin bita a sannu komai zai daidaita.
A hankali tace kwarai hajiya aina ga alaman hakan tun yanzu gashi yaya har da zuwa gida na yayi ta dalilin ta nan dai take fada mata son canza mata wurin zaman da yake son yi ma,ana ya raba masu gida da kishiyar ta.
Wanan maganan mahaifiyar taji dadin din shi sosai inda tace Allah yasa Aisha su kuma Allah ya saka masu da alherin sa.
Ki barshi da mijin naki ai kar tasan kar shi da shi, shi yasan ta inda zai fito mashi da maganan a tsakanin su har ya yarda da maganan a saukake.
Bayan la,asar muka fito nan falo muka zauna muna hira sai gashi ya dawo gidan yaranta dake waje suna wasa ya shigo dasu rike a hannun shi.
Sannu da zuwa mukeyi mashi amma hankalinshi na ga hiran da yaran suke yi mashi sai dai da kai yake iya amsa muna gaisuwan da muke yi mashi.
Ina zaune rakube ina kallon yadda yakewa yaran tausayi ya bani don nasan yadda yake tsananin son haihuwa a wanan lokacin.
Ido na zuba masu sosai daga inda nake zaune tashin hankali na da uncle yanzu shine haihu wata shidda kenan cur a gidan shi ba bu wani labari ciki a gare ni shiko yanzu ba abinda zai farauta mashi rai kamar ya ganni da ciki.
Nace oh safiya wai haihuwa bai zuwa a inda ake neman sa ne ga gidan Ahmed da bai son haihuwan a can Allah ya bani gashi a gidan uncle wanda yasan daraja da kimar haihuwa shiru kake ji.
Jin yana magana dani yasani dawowa cikin hayaci inda yake fadin may yasa baku sayo wa boy abinda yake so kuka sayawa amira ?
Murmushi nayi tare da sauke ajiyan zuciya nace uncle rabuda boy din nan rikici yake ji dai shifa yace a saya masu wanan din da yake ma fushi tun dazu bayan an sayo kuma wai shi bai so a canza mai.
Ya rugumo yaron zuwa jikin shi yana fadin kyalesu zamu fita in sayo maka wanda kake so yanzu barin in ci abinci sai mu fita dakai bada su Amira ba.
Abinci na gabatar mashi da kaina ya zauna tare da yaran sukaci suna ta zuba mai surutu har suka gama suka fice gidan shida yaran.
Aisha ta kalle ni tace ashe yaya yana so yara haka wallahi ban taba sanin yana kula yara ba ke kuma gaki shiru har yanzu babu labari kodai kina planning ne safiya.
Ajiyan zuciya na sauke nace nawa na aje da zanyi planning anty wallahi nima nasan haihuwa yake so Allah dai ne bai kawo ba har yanzu.
Take cewa ki dinga shan miyan kuka tun da safe haka ma idan zaki kwanta barci in Allah ya nufa zaki iya samu da wuri ki haihu.
Nace aiki na gode kice in samo kuka ke nan in dinga sha don nasan idan hakkurin uncle ya kure zai kai ga yi min magana nima kuma ina son in ga na haihu wallahi na kare ina lumshe idanuwa na.
Sai dare ya dawo da yaran idan kafin ya dawo ya kira wayana in fada mata ta shirya gashi nan zuwa zai maida ta gida na fada mata tare da hada mata tsaraba ya iso bai ko shigo ba muka fita .
Inda muka samay shi da yaran a mota nan mukayi sallama suka wuce gidan Aishan dashi koda ya je gidan bai shiga sai cewa yayi ta sallamo mashi maigidan nata.
Tana shiga shiko ya hau ya zugo a wurin kishiyar ta tana sa kafa tana fadin gidan uban wa kuka tafi har dare haka uban wa zai dafa maki abincin dare a gidan.
Sai dai ku kwana da yunwa ke da yaranki don ba zan bata kudina wurin sayen wani abu don ku ci.
Shi mai kudin gidan naku da baida moriya kije ya baki abinda zakuci da diyan naki kishiryarta na zaune gefe da diyan ta suna shan cornflake tace ta aje jaka a gida mana to ban dafa ba in an dawo acine.
Wani kallo tayi masu tace kaje yana waje yana sallama da kai yace wa cikin zaro idanuwan shi tace yaya Sulaiman da sauri ya zura sillifas din shi a kafa ya fice a hanya ya hadu da yaron gidan yana shigo da manyan kwalayen da ya sayo masu tsaraba wanda dagani har Aishan bamu san ya saye ba.
Kishiyar kuma baki ya mutu ganin kwalayen da ake shigowa dasu gidan ana dire su kofan Aisha din wani irin kishi ne ya kamata a lokacin.
Ya fita sun gana dashi ban san yadda sukayi ba dai da mijin Aishan can ya dawo ciki bayan sun dauki lokaci da uncle a waje yana cewa boy yau uncle ya kaiku shopping ne haka ?
Yana ta faman washe baki namiji dama baida kunya nan yabar kishiryar zaune tana kallon mamaki shine har da yiwa yara wasa a lokacin.
Uncle bai dawo ba sai tara da rabi ya shigo da ledan kajin da ya sayo wanka ya shiga sai bayan ya fito wankan ya fito falo yana fadin in bude mai kajin su zai iyaci kawai yau.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/21/20, 6:24 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , ,


🧕🏿6️⃣0️⃣🧕🏿


NOVEL DINA NA KUDI NE IDAN KIN FITAR MIN KO KA FITAR MIN BAN YAFE MAKU BA UBANGIJI YABIN HAKKINA AKAN KU DA DUK WANDA YA KARANTA BAI BIYA BA.


Satii biyu ya rage mu daga zuwa kasar Canada wanda yai dai dai da kwanan kin azumi baifi kwana goma ba tsaka ni.
Zaune yake a saman gadon ya mai da hankali ga laptop din shi daya tasa a gaban shi ya mai da hankalin shi gaba daya akan abinda yake yi din.
Dakin na shigo dauke da abinda ya sa in dafa mashi na nauin samun lafiyan maza na shigo dakin dakin da sallama na.
Har na isa saman dan katamin table din dake dakin na aje tire din da ke dauke a hannu na da kayan shaye shaye irin na maza mai kara masu lafiya karfi.
Bayan ma aje na samu wuri na zauna a kusa dashi ina fadin uncle ga yanan na gama hada maka idon shi na akan laptop din shi nima dai ba wai shi nake kallo ba ko da na zauna hankalina yana ga wani takarda da na gani saman gadon shi a lokacin.
Amma wanan kamar wurin da muka sayo ma Anty Aisha kaya mana, nake cewa dashi cikin dan, kallon fuskan shi dake duke saman laptop din.
Bai ce komai ba sai ci gaba da abinda yake yi yana murmushi nagama kallon takardan na aje inda na ganshi tunfarko tare da mikewa zan bar dakin .
Da sauri ya dan riko min hannaye na yana fadin ki dan dakata min in gama please komawa nayi na zauna tare da dan kai kafaduna saman gadon nayi rigingine.
Bai dade ba naji ya sauke ajiyan zuciya ya juyo yana dubana tare da kokarin rufe laptop din da yake aiki a cikin sa .
May zaki yi yanzu idan kin fita, yace dani, sai tambayan nashi ya bani mamaki sai dai ban kai karshen tunane ba naji yace dani zuba min ruwan maganin na.
Na dago a hankali zuwa gaban dan table din na fara tsiyaya mai ruwan ganyen maganin da ya sa na dafa mai.
Muryan shi naji tana cewa yanzu yaya zamuyi da mutane ga tafiya a gaban mu kafin azumi wanda ba zamu dawo ba sai bayan sallah insha Allah kin ga ban gida za ai azumi da sallah ke nan.
Juyowa nayi gare shi dauke da cup ina mika mai nace hakane Uncle a yadda kace za ai tafiyan ya amshi ruwan maganin dake tiriri a cup ya dan kurba yaji da saura zafi.
Ya dago ya kalle ni nace da sauran zafi ko kai ya gyada min amsa nayi nadan kada spoon a ciki ina dan motsawa a hankali yana zaune ya mayar da hannuwan sa baya ya tokare a saman gado.
Ya kura min ida baya ko kiftawa na dago kai ina cewa dashi sai dan ban san abinda kake shirin yi wa mutane ba kan azumin da sallah.
Yace in banda abinki yanzu ai wanan a cikin aikin ki yake ni dai kawai idan kin tsara sai ki sanar dani komai ake ciki da can madam maimuna ce take tsara min komai indan lokaci yayi.
Na ce a raina akwai aiki gaba na ashe don ban san komai a yadda take shirin ta amma dai ba matsala zan yi iya kokarina yadda ya dace.
Mika mashi cup din ruwan maganin nayi ya karba ya kafa kai bai cire ba sai da ya kurbe duk ruwan maganin a lokaci guda.
Ya kare yana ya mutsa fuska da alama bai da dadin sha ya dauki ruwa kadan mara sanyi ya dan kora a cikin shi.
Gauron numfashi na sauke ina fadin wai wanan maganin may ye haka kake sha kwanan nan yace ba matsalan ki ba ne yanzu.
Mikewa yayi tsaye yana fadin ke nake saurare yanzu don bani son a makara zan baki list din last year don ki san mutanen da ake aikawa .
Wurin wani dan drower dake dakin ya nufa yana tono list din ya juyo yana fadin sai dai ta wajen baba can gida ban san wa yanda kike so aiwa sadakan acan.
At list mutane hamsi maza nake son a raba ma abinci da mata hamsin suma a basu abin azumi dana sallah haka nakeyi duk shekara daga riban da nake samu na wurin masana,antan taya na.
Duk bayanin da yake min bai dago kai ya kalle ni ba sai da yake miko min takardan ne ya kare da fadin ki duba idan an samu kari sai a kara dasu.
Ni zan fita dama maganin nan ya tsayar dani yau akwai aiki a gaba ina son in kammala komai a yanda nake so shi a cikin satin nan.
Namike tare da daukar mai jakkan aikin shi yana gaba ina binshi baya har muka isa haraban aje motocin gidan bai dauki driver ba shida kan sa ya tuka motar ya fita.
Nayi ajiyan zuciya na juya zuwa cikin gidan zuciyana fam da tunanen nauyin da ya dora min akai yau a gidan.
Dakina na wuce sai da na kara yin wanka na gyara jikina na dawo na zauna na fara tunane gashi yana jaddada min kada nayi mashi delay a tsarin ni yanzu ta ina zan fara ne.
Anty Aisha ne ta fado min a rai da sauri na jawo wayana ina kiranta har kiran ya katse na sake danna kiran sai nayi sa a ta dauka.
Mungaisa tare da tambayanta yara da gida ta amsa da suna lafiya kafin ta fadi wani abu nace Anty Aisha ki taimake ni don Allah banda wani mafita yanzu sai gare ki.
Tana dariya tace niko matar yaya mai zan taimaka maki dashine haka a rayuwana nace bari kedai yayan kine ya dora min nauyin rabon kayan azumi da na sallah bana.
Dariya naji ta kwashe dashi tare da fadin Allah mun gode da ka nuna muna wanan ranan don wanan magana kika tayar min da hankalina da farko.
Ai wanan abin farin ciki a gare ki don dama matar yaya na can lagos ne take yo mashi sayayyan sai abinda muka gani zata bamu.
Nace to yanzu yaya zamuyi don kawai mu kawar da zancen anty da take son daukowa nan dai tayi min bayanin abinda suka samu last time sai na kwatanta na gani idan nabi list din zasu samu abinda yafi haka.
Godiya nayi mata ba tare da na tsaya sauraranta ba tace wai ko kin san kokarin da yayana yayi min na maganan canza gida nan take kora min bayanin abinda ya kasance tsakanin shi da maigidan ta.
Tace yanzu tunda aka fara zancen ba zaman lafiya tsakanin shi da kishiryar ta kullun fitina suke kwasa a tsakanin su ita yanzu ta matsu ta tashi ta bar mata gidan ta koma gidan ta.
Nace kin ga haka yafi aiyafi ance kazantar daba kagani ba sunanta tsabata shi takewa bakin ciki yanzu true colour din ta zai fita a tsakanin su.
Kin ga sai yasan halin ta na gaskiya shi take ma gudu dama tace gata ragguwa ko jikin ta bata iya gyarawa balle na diyanta.
Mun dai dauki lokaci muna magana akan gidan mijin nata a karshe mukayi sallama nan ta barni ina tunane ai ita tasan tana da kishiya ke nan ni yanzu ban san idan na dosa don wanan nauyin da ya dora min zai iya saka wani sabon tsana tsakanina da anty kuma.
Kamar yadda yace duk cikin kwana kin nan abinda muke fita ke nan yi daga sayan kayan masrufi zuwa tufafi da kayan tea da sauran su .
Ga kuma shirin komawan Aisha sabon gidan ta a wani sati da muke yi a makon nan muka shiga bauchi inda na samu taro na mutunci a wurin yan uwan Uncle da mahaifiyar shi don yanzu Aisha ta gama shigar dani a gare su ko.
Saida mukayi sallah muka shiga wurin hsjiya baaba don mu gaida ita tana zaune cikin kamala duk muka zube kasa a gaban ta .
Da fara,ata take muna sannu da zuwa da yaya hanya daga nan kuma suka fara dan hira da danta a cikin hiran ne yake mata bayanin tafiyan da zamuyi.
Wanda yasa muka zo kawo masu abin sallah dana azumi kafin mu wuce din tayi farin ciki da jin haka tace babana kokai fa abinda nake fada ma ke nan da dadewa cewa samun mace ta gari zai iya canza maka rayuwanka.
Yanzu gashi tun ba a je ko ina ba abubuwa suna canzawa sannu a hankali a wajen ka wanda wanan kokari ba kowane ya kawo shi ba sai ke mai sunan gwago na.
Na dago kai na dan kalle ta cikin mutunci da nuna alkunya gare ta tace eh a dalilin ki na samu farin ciki da hadin kan diya na da yan uwan uban su suka watsa min kawunan su a baya saboda son zuciya.
Yau gashi babana dake zaman yaya kuma uba a gare su ya dawo ya rugumi yan uwan shi da hannu bibiyu abinda na dade ina fatsn gani a gare su.
Yau ko wacen su tana farin ciki a dakin auren ta ta sanadin ki kin saka ya sauya masu rayuwan su na kunci don dan abinda suka gada a wurin mahaifisu dama yan uwa sun ciyen shi kaf gare su basu barsu da komai a hannun su ba.
Fatana gare ku yanzu shine Allah ya baku zuria masu albarka nima in ga jikokina ta wurin babana in runguma in goya kamar yadda ko wace uwa ke burin gani a rayuwan ta.
Kaina na dukar kasa don kunyan abinda ta fada a karshe sun dauko maganan da ya shafi gida don haka na zamay jiki zuwa inda kaunar shi take wacce baaba ke riko a gidan a wurinta nake jin ashe ya gyara ma sauran sisters din shi dakunan su a nan garin kamar yadda ya gyarawa Aisha nata.
Naji dadin jin wanan labarin da ta bani nan muka zauna ina fahintar wani abu a cikin hiran ta sai da zai fita ne hajiyan ta kirani na fito muka tafi.
Muna shiga part din mu na kai mashi runguma ya juyo yana kallona da mamaki nace Uncle naji abin alherin da kayiwa su anty suwaiba unangiji ya saka da alheri ya kara budi.
Murmushi yayi ya kamoni zuwa jikin shi tare da subbatan goshina sai ya soma magana kamar mai rada bakin shi a daidai kunne na yace ba wanan godiyan nake so ba kin dai ji abinda baaba tai muna addua a kai.
Kunya ne ya kamani na kara shigewa cikin jikin shi sosai ina dariya don kunya ina fadin insha Allah soon.
Ya jawo ni ya kara matseni sosai yana fadin da kyau bari ma yanzu mu fara gwada sa,ar mu mu gani ko zamu dace dariya ya bani da haka muka kwanta barci don muna da gajiya dama.
Washe gari muka tashi da aikin rabon kaya wa yan uwa da abokan arziki don motar kaya ta isa da daddare sosai ne.
Saboda hakan ne muka bari sai da safe banga zarah ba tun jiyan da muka iso tana gidan iyayyen ta tunda muka zo.
Saida muka share kwana uku muna abu guda ana hudu ne muka dawo abuja sai dai uncle ya hanani zuwa gida in kai wa mutanen gida abinda ya saya masu da kaina a cewar shi sai mun dawo zamu tafi gaida su.
Yaya Sani aka kira nayi mashi bayanin komai da wayan da zai ba na hada dashi da kayan suka tafi nan muka fara shirin tafiya wanda ni ta fanni na ba wani shirin da nayi don a shirye din nake dama.
Ina murnan tafiya sai ga shi yana fada min gidan anty zamu sauka indan mun tashi daga nan abinda ya sani cikin damuwa ke nan kuma.
Shiko naga ko a jikin shi bai damu ba kamar ba wani abinda ya faru tsakanin mu tun farko da ita sai ni ya bari da tarin damuwa a zuciyana.
Ana gobe zamu tafi ne dadare muna zaune falo yake cewa dani wai may ke damun ki ne kwanan nan naga kin shiga damuwa ?
Gwauro numfashi na sauke tare da kakaro murmushin dole a fuska na nace babu komai may kaga ?
Ya tsuramin ido kafin yace dani tun fa ranan da mukayi magana dake na sheda maki lagos zamu fara tsaya muyi kwana biyu naga kin ta da hankalin ki a gidan nan.
Ajiyan zuciya nayi wanda ya baiyana a fili nace uncle bawai nadamu bane kawai dai ina tunanen yadda zan hada fuskana da ita ne bayan abinda ya faru a tsakanin mu din.
Murmushi yayi ya kamo ni zuwa jikin shi yace kin san ko muna waya da ita a yan kwanakin nan kuma ni bata nuna min komai akan abinda ya faru din.
A raina nace kaika ai ba zata gwada ma komai ba nice dai matsala dama a tsakanin ku ji nayi yace dani kin dai san ba zan taba barin ta muzanta baki ba kina a maysayin mata ko ?
Nace amma uncle abinne da nauyi wallahi yadda anty ta rike ni ace haka ya kasance a tsakanin mu aikasan da nauyi wallahi.
Yace koma dai may ne yanzu sai ki bari idan mun je ayita ta kare yafi wanan boye boye da kike yi mata kamar mara gaskiya a tsakanin ku.
In ke kina da laifi ai itama tafiki laifi a wanan magana don ko dani dake itace ta hada mu don may daga baya zata kawo wani zance kuma.
Haka dai yayi ta karfafa min gwaiwa har na danji raina ya dan sake koma may nene gara dai ayita ta kare ma nace a zuciyata.
Washe gari yan uwa da abokan arziki sukayi ta zuwa sallaman mu yaya don sai da yamma ne zamu tashi.
Yaya saadu da anty Aisha kusan anan suka wuni damu shiga na alfarma nay duk da ba wasu kaya na kwasa ba ga tafiyan.
Mun sauka lagos da karfe shida da wani abu hotel muka wuce bamu tafi gidan ba a ranan anan hotel din muka tsaya.
Washe gari ma da yafita bai dawo banan ya barni ina ta barci abina hankali kwance sai bayan karfe biyu ya dawo yai wanka ya ci abinci yake fada min in shirya muje mugaida anty din da mijin ta.
Kayan da Anty Aisha ta zabar min don in sa idan zamu gidan na saka wani lace ne da suka sayo dubai lokacin da suka tafi sayayyan auren mu da ita shine na saka.
Sai sarkan gwalal da zaikai kimanin kudin nigeria milayan daya da dan kai wanda shi yafi tsada a cikin kayan da suka sayo da wasu takalma masu dan hill da duwatsu masu kyan sin shiga da lace din sune a kafana da jakkan su.
Na gama tsab ban san yana zaune yana kallona ba sai da na gama shiri na na dago zan yi mashi magana na samu ya kafa min idanuwan shi a kaina.
Murmushi nayi ina isowa wurin shi da sauri yace ashe matar tawa ta iya shiga ne haka ban sani ba.
Yace ai wanan shiga zaki sa yau madam ta rude tace koba safiyan ta bane da ta ke dauka yar kauye bata dace dani ba.
Ya miko min hannu a haka muka fito zuwa lifter muka sauka kasa inda muka shiga mota muka kama hanya.
Ko a hanyama sai faman zolayata yake yi wai zan hana shi tuki da kamshin turaren da na sa a jikina yace turaren yana da dadi shi nake son ki dinga amfani dashi ko yaushe.
Mun isa gidan musalin karfe hudu na marance lokacin na tabbatar da daddy yana gida don motar shi da nagani a waje abinda ya sani sauke ajiyan zuciya ke nan don nasan ko maue zai zo muna da sauki tunda yana gida.
A tare muka fito zuwa cikin gidan inda ya danna bell din shiga cikin gidan ba ajima ba na jiyo tafiyan mutum xuwa bude muna kofan nace ko yaushe suka fara rufe kofa haka kuma.
Zuciyana sai duka yake uku uku fargaba da tsoro suka mamaye min zuciya a lokaci daya sai dai hakan bai hanani yin addua a bakina ba.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/22/20, 5:53 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , ,


🧕🏿6️⃣1️⃣🧕🏿


NOVEL DIN NAN NA KUDI NE DON ALLAH KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA BA YAR UWA DON ALLAH ZAI SAKA MIN A KAN KI, , , ,


A hankali kofan ya bude shike gaba ina daga bayan shi cikin fargaban ko wa zai bude kofan a lokacin gabana sai danka yake uku uku.
Muryan Faiza ce naji tana fadin a yaya sannu da zuwa ya amsa mata kamar yadda yake amsa muna a can baya idan muna gaida shi a gidan idan ya shigo.
Fara takawa yayi don shiga gidan na bishi a baya wanda sai lokacin Faiza ta ganni taa sake dan ihu da karfi sai kuma taja bakin ta har da rikewa tace ashe tare kuke cikin washe baki tana nuna farin ciki da gani na a lokacin.
Gaba dayan su har daddy suna falo zaune a lokacin da twins din ta Fati ce kawai bata cikin su jin muryan shi da twins sukayi yasa suka mike gaba dayan su suka nufashi da murnan su.
Suna gani na kuma sai suka barshi suka nufoni tare da fadin anty safiya oyo,yo duk suka fada min a jikina nima rungumo yaran nayi zuwa jikina cikin shaukin junan mu da andade ba a hadu ba.
Daddy ke fadin kar ku karya mummy naku mana wurin murna lokacin shi har ya kai inda suke zaune yana kokarin zama.
Dayar tace anty safiya shine kika gudu kika barmu muna ta kewan ki kin dawo ke nan inji dayar take tambayana cikin kallon fuska na.
Nace na dawo yan biyu ba gani kin ganni ba ba na fadi ina kara rungumay su a jikina cikin jin dadin ganin su da nayi yau.
Mummy ga anty Safiya ta zo suke cewa uwar tasu data mayar da hankalinta ga uncle suna gaisa wa dashi bayan ya zauna.
Tace da yaran naga safiya kuda kuke kewanta sai ku tare ta nidai ba wurina tazo ba sai in wurin ku tazo hakan yasa na karasa gurin ina fadin haba anty kiyi hakkuri mana.
Dariya daddy yayi yace kin ji tun ba a kai ko ina ba ma ta baki hakkuri na karaso ina durkusawa a gaban su tare da gaishe su.
Daddy ya amsa min cikin daddin rai da sakin fuska yace yau yar gidan antyn ta ne gidan namu nayi dariya ina noke kaina a tsakiyan kafafuwa na don kunya.
Na dago kaina cikin kunya ina gaida ita ta amsa min ba wani walwala a fuskan ta da cewa lafiya lau yaya gida.
Uncle ya maiyar da bayan shi a makariyan kujeran da yake zaune yana fadin yau dai ga kaunar ki nan na kawo maki don damuna da take yawan yi akan ki.
Murmushi tayi tace aikuwa ga Safiya na gani a gabana yau ga kuma uncle nidai kaina na duke sai da daddy yace tashi mana ki zauna saman kujera Safiya nace a kunyace daddy nan ma yayi mun ai.
Na kara dukar da kaina kasa nace daddy nan ma yayi min a lokacin ne faiza ta iso wurin dauke da tire da abin sha a sama.
Ta dire a gaban mu tana cewa yau ga amarya a gidan mu anty ta ce ga fa amarya da akai muna rowan buki a gidan tazo
Daddy yace aure yayi kyau dukkan su sai wani sheki suke yi da annuri tace sulaiman ba amma itakan ai auren ma rama ya sakata yi.
Murmushi uncle yayi don yasan gatse tayi min kawai da wata manufa ta fadi maganan ta ya mika hannu ya dauki goran ruwan yana ballewa tare da kafa bakin shi akai bayan ya goge bakin goran da hannun shi.
Ga ruwan nan tace dani cikin rashin fuska a gare ta na dan dago kaina nace da ita na koshi sai dai anjima tace yayi sai ta juya ga uncle din sukaci gaba da magana dash.
Nan su yan biyu suka shiga hira dani ina dan basu amsa a hankali tana kallona ta gefen ido tana mamaki a ranta yadda na juye kamar bani bace a lokaci guda.
Kayan dake jikina kawai ma abin kallo da yadda na tsara kwalliya kamar wata balarabiya dani babu inda nake da mukusa a jikina.
Ya gyara zama tare da fuskantar anty din bayan ya kai duban shi gare ni yaga yadda nake zaune a takure gashi kuma matar gidan sai basar dani takeyi a wurin.
Dan uwan nashi ya fuskanta tare da fadin mu zamu koma yaya dama na kawota ne ta gaishe ku kafin mu tafi da sauri daddy din yace tun yanzu zaku tafi ba a ko gaisa ba.
Ido da ido ya kalli anty din yace matar gidan ce naga bata maraba da zuwan mata na gida so ba zan juri ganin wanan a tsakanin su ba.
Saboda may daddy yace idan bata mara ba daku ai mu da twins muna maraba daku don wurin mu kuka zo.
Yace na dauka abin da ya faru a tsakanin su ya wuce don da nasan har yanzu madam tana rike da ita a zuciyar ta ba zan kawo ta gidan nan ba.
A yadda yayi maganan ya nuna ranshi ys baci ga abinda tayi muna ya juya inda nake zaune yana fadin tare da mikewa tsaya yace tashi mu tafi.
Dago kai nayi ina kallon shi tare da dan marairaicewa nace Uncle kayi hakkuri ka bari a bata hakkuri ta yafe min.
Tare suke hada baki wurin fadin ta yafe maki da kikai mata may zaki ce ta yafe maki inji daddy ya fadi yana mai kura mata ido.
Yadda sukai mata yasa taji nauyi da kunya ta fara kamay kamay tana fadin yanzu may nace ina wanan maganan an wuce shi ko.
Uncle yace cikin girgiza kai madan bayi expecting din haka daga wajen ki ba don kece ki ka nuna mun Safiya a gidan nan duk abinda mukayi mun yi biyayya ne bisa umurnin ki.
Banji dadin yadda haka ya kasance a tsakanin ku ba a sanadiya na na dauka kin fahinci ni kowaye zuwa yanzu ni mutum ne da ban magana biyu a rayuwana.
Don , , , , daddy ne ya katse uncle da fadin ya isa haka please sulaiman dauki matar ka katafi Allah ya tsare Allah ya baku zaman lafiya.
Sulaiman don Allah kuyi hakkuri da kai da Safiya in Allah ya yarda haka ba zai sake faruwa ba ta fadi tana duban sulaiman din.
Daddy ya rausaya kai yana nuna ma uncle kujera ya zauna lokacin ne su twins ke cewa in tashi in zo inga gadon da daddy ya sake masu a dakin su.
Dole na tashi na bisu dakin nasu nan suka samu daman sakewa inda daddy yai mutaukar nuna mata bacin rai ga yadda ta tare ni.
Har yake cewa bata san Allah ne ya rufa mata asiri da anty uwa da Uncle ya yarda da auren diyar anty Uwa da kashinta ya bushe.
Karshe tace amma anan zaka barta sai dare ka dawo daukanta don karkace ban kula maka mata don naga tun yanzu ka nuna min matarka kake so dani.
Dariya suka kwashe yace ba dole ba ai safiya ta yi don yarinyar ce data san kanta wurin komai na rayuwa ya fadi hakane don ta san bada wasa yakeyi mata ba.
Ta mike tana fadin barin rafi wurin Safiyan in barku kar kuma nayi wani laifi ga mai gidan again nan ta mike ta barsu da dan uwan nashi.
Muna daki da yaranta sai gata ta shigo dakin kallon da take min yasa na dukar da kai cikin fargaban abinda zata fada min din.
Sai da ta samu wuri tavzauna take ce min Safiya kin san baki kyauta min ba don kin yaudare da sauri na dago ina kallon ta don jin kalman yaudarar da ta kiramin din.
Tace kin san kun shirya komai da Sulaiman kika boye min hakan sai jin zance buki kawai nayi gun mutane amma ke baki sanar min ba.
Nace anty bansan da auren nan ba ba fada maki tun farko daga zuwa tambaya aka daura muna aure dashi.
Nakiraki kuma in maki bayani baki saurare ni ba a lokacin kin dauki zafi dani, duk yadda na so ki fahince ni kin ki saurararona a lokacin.
Tace ai dole a daura maki aure daga zuwa tambaya tunda kuna matse ku samay shi kada ya kubce maku a hannu.
Naji wani zafi a raina nace haka ne anty don masu son su samay shi a lokacin muna da yawa da yake Allah yayi nice matar ai an daura dani ba shiri.
Kallo na tayi kamar zata yi magana sai kuma tayi shiru kawai ta murmusa a ranta tace eh lalai kin zama matan manya a yanzu safiya .
Amma a fili sai tace dani yaya zaman ku da yan uwan sulaiman din yake yanzu na gyara zama nace da ita lafiya kalau muke satin da ya wuce ma muna bauchi din mun tafi sallaman su kuma ya kai masu kayan azumi da na sallah.
Da sauri ta kallo ni tace what har sulaiman yayi rabon kayan azumi da sallah banda labari wa ya saka ya dauko mashi kayan da ya raba bana.
Nace yan uwanshi yaba nauyin yin hakan don sune sukayi rabon da muka je acan shiru tayi na dan lokaci sai tace zan ganshi inji yadda akayi hakan ya faru.
Nan dai muka zauna wanda duk hiran namu bugun cikina take yi amma sai in nuna mata ban san komai ba a kai har ya turo yan biyu kirana wai zamu tafi.
Tare muka fito da ita daga dakin take cewa dani kin dai san namiji ba ai mashi farar daya don haka duk abinda kike samu sai ki turo ai maki tanadin shi yafi.
Nace to anty insha Allah zan dinga turowa sai dai na fahinci uncle ba irin mazan dake ba mace kudi bane haka na amma yana kashe min kudi ga duk abinda nake so.
Tace may ye baki dashi yanzu dole ne kisan yadda zaki juyashi ya dinga sakar maki kudi kina turowa nan ana maki tanadin su.
Ina gyara gyale nace insha Allahu anty duk abinda nake samu zan dinga turowa gare ki da zaran na samu tace koke fa haka yasa muka fito muna dariya sau mazan suka dauka mun shirya a tsakanin mu ne.
Daddy ne ya nuna ma uncle din mu yace gani ba dama nace ma ai sun fi kusa kaga kamar ba yanzu muka shirya su ba.
Nan dai muka samay su tana kara jaddada min karfa ki manta da sakona nace in sha Allahu anty.
Gaban daddy nazo na durkusa gaban daddy tare da sunkuyar da kaina ina fadin daddy zamu tafi yace ubangiji ya kaiku lafiya ku dawo lafiya safiya ayi ta hakkuri shi zaman aure dan hakkuri ne.
Har waje suka rakomu muka wuce suna daga muna hannu sai da muka bar area din na sauke ajiyan zuciya a fili.
Uncle yace dani yanzu dai hankalin ki ya kwanta kun shirya da anty ki ko nace ai hakan yafi don da ba haka ba bazan taba samun kwanciyar hankali ba a raina.
Amma cikin zuciyana kuma tunanen anty din nake yi ashe dai duk rayuwan mutun sai mutane sun gane halin shi na banza mutum dai dan tara yake bai cika goma ba wallahi.
Nan dai muka isa masaukin mu kowa da abinda yake sakawa a zuciyar shi a lokacin bayan munyi sallah mukaci abinci bamu dade ba muka shiga barci.
Tashin asuba zamuyi don hakane muka kwanta da wuri shiya tadamu mukayi wanka karfe biyar a airport yayi muna mun gama komai kafin shidda muna cikin jirgin da zai daga.
Na dauka zuwa Canada wasa ne ashe ba karamin tafiya bane nan na jinjina ma uncle da bai jin wutan tafiye tafiyen da yake yawan yi ko yaushe sai da muka kwana washe gari muka sauka canada din.
Inda abokin shi yazo ta tare mu wani dan gida madaidaici ya kaimu nikan ban boye kauyancina sai kallon abin mamaki nakeyi a garin. .
Wanka mukayi da sallah sai abincin da mukaci nan muka kwanta ranan duk kwakwan uncle sai da ya barni shima barci yake yi sosai.
Sai wani lokaci muka tashi ko shi zuwan wanan abokin nashi da iyalinshi yasa mu tashi barci don sun kawo muna abinci irin namu na bakaken fata.
Matar shi tana gani na tashiga yaba tana fadin lalai Uncle bakayi ruwan idon banza ba wirin zaben mace haka maikyau ga tsari ga hankali.
Mijin yace na gaya maki ai mutumin nawa ruwan idon shi da dalili ya tsaya yin shi nan dai sukayi muna fatan alheri basu wani dade ba sukayi muna sallama suka tafi.
Kwana biyu uncle baya fita ko ina muna gida acewan shi yanzu ne yake more amatcin shi dariya nayi nace wani amarci ya saura amarya wata shidda a dakin ta kuma.
Yace ai wuyan aiki ba a fara ba don ni so nake kafin mu bar nan din sai kin samo ma hajiya baaba dan jikan da tace tana son dauka nawa.
Daya fara fita ko saida na raina kaina naji dama ya barni a gida ne yafi don ko yaya muna dan hira da zara ko Nuratu mai aikin mu.
Amma nan haka zan wuni sai kallo sai ko kwanciya ban tsinana komai a rayuwa tunda safe in yafita sai dare sosai yake dawowa gidan.
Haka kuma idan gari ya waye zai sa kafa ya fice gidan sai kuma dare kwana zai dawo duk suna wurin harkan kasuwancin su.
A kasan muka fara azumi duk da ba musulmi a kasan sai jefi jefi wani lokaci zai dawo gida da wuri tunda azumi ya fara.
Mukan dan fita idan ya dawo da wuri yadan nuna min garin mu dan yi sayayya mu dawo gida bai kara fita sai kuma gobe.
Ranan ya dawo gida da wuri ya shigo da sallaman shi da gani a gajiye ya shigo gidan don yanayin shi kawai zai nuna hakan.
Kwance nake saman carpet ban ko iya daga kai in mashi sannu da dawo ba a lokacin don tun cikin dare nake jin jiki kuma ga azumi a bakina.
Ya cire takalmanshi akofa kamar yadda mukeyi acan tare da rataye rigar sanyin da ya dora saman kayan jikin shi.
Ya tako har inda nake tare da sunkuyowa gaba yana fadin madam yau lafiya kike kuwa da kyat na iya dago kai na dan dube shi da idanuwa na da sukayi min ja saboda wahala.
Na mayar dakai na kasa ina wani irin numfashin wahala nace da kyat uncle sannu da dawowa.
Kasa yakai zaune a inda nake don ya tabbatar da ba lafiya nake ba a lokacin zama yayi saman carpet din tare da dan tallabo kaina yana fadin may ke damun ki ne haka ?
Na runtse idanuwa tare da cije baki na nace uncle banda lafiya ne tun da dare nake jin zazzabi yana damuna sai kuma amai ya biyo baya bayan fitar ka gidan.
Dan taba jikina ya shiga yi yazo daidai wuyana yaji yadda jikina yayi zafi ya gashe sosai a lokacin yace shine baki kirani ba ana wasa da ciwo ne komai karantar shi akace maki.
Ya ce ki tashi muje asibiti yanzu a duba ki ansan abinda za a baki na cije baki nace uncle bari in ansha ruwa mu tafi don yanzu ina dauke da azumi.
Ya katse ni da cewa wani azumi kina haraswa haka sai ya mike tea mai zafi ya shiga ya hado min ya dawo inda nake yana min sannu ya mikar dani ya matsa min sai da na sha ina runtse idanuwa don ba dadin tea din nakeji ba.
Ina sha yana min sannu da fadin dan kara dai ko kadan ne na cije baki na kara amsar cup din ina kurbawa da gudu na mike zuwa bandaki sai da na amaye shi kaf na samu saida a raina.
Yana tsaye a bayana yana min sannu na dago cikin cije baki ina maida numfashina dakyat ya rungumoni muka dawo falo daki ya shiga ya dauko min hajjab dina na sa.
Sai faman cije baki nake yi haka ya kamani zuwa waje inda muka shiga motar da yake amfani dashi a kasar wani asibiti mukaje.
Nan ya yaki kati inda babu dadewa suka shiga yimin gwaje gwajen su na likitoci tare da yan tambayoyi.
A karshe da result ya fito likitan yayi mashi albishir ina dauke da juna biyu na wata biyu a jikina hakan ya nuna tun a gida nageria nike dauke da cikin a jikina bamu sani ba.
Tun fitowan mu yake faman washe baki shi yana jin wani irin dadi a ranshi yana yi yana dan kamoni tare da fadin Allah ya karba adduan mu dana hajiya baaba.
Ni dai ban iya ce mashi komai ba har muka shigo gida har na haye kujera na kara lafewa kafin ya shigo yakkule ko ina na gidan haka yasa na fahinci bai kara fita ko ina ke nan ranan.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/23/20, 5:39 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , ,


🧕🏿6️⃣2️⃣🧕🏿


NOVEL DIN NAN NA KUDI NE DON ALLAH KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA BA YAR UWA IDAN KUMA KIN FITAR MIN DASHI UBANGIJI ZAI SAKA MIN A KANKI KAN NOVEL.

Ina kwance na saman kujera na dunkule a ciki naji ya sauke min kiss a goshina yana fadin Alhamdullahi kinga Allah ya amsa muna adduan mu yanzu ni na gama aikina saura naki.
Da sauri na bude idanuwa na dake lumshe na sauke su gareshi acikin sanyayyar murya nace dashi.
Uncle kada ka zamo mara tausayi mana kana nufin yanzu aikin nawa ne ni kadai kai ka gama naka ke nan ?
Ya mike ya samu wuri ya zauna yana fadin eh to ai gaskiya na fada don nayi yadda duk wani kosashen namiji ya kamata yayi dasa ciki a jikin mace.
Kin ga yanzu ke kuma sai kiji da amai da daukan nauyin ciki amma kada ki damu zandan rika taya daukan shi ta hanyan rage maki jin nauyin shi a jikin ki.
Sai idan haihuwan yazo kuma ai tare zamuyi labour dake ba inda zan fita ranan hararan shi nayi sai muka kwashe da dariya kuma.
Nace ashe kai har wahala kayi wurin dasa vikin a jikina yace ba kadan ba ai nayi kokari sosai wallahi yanzu jina nake wasai don na fara sauke nauyi na.
Murmushi nayi mai ina gyara kwanciya ban san lokacin da barci mai nauyi ya dauke ni ina dan tunane daga inda nake kwance.
Ban falka daga barcin ba shikuma bai tadani ba sai karfe takwas na dare lokavin yana zaune yana buda baki a falon kusa dani.
Jin motsin da nayi yasa shi dago idanuwan shi ya dube ni ganin shi nayi zaune yana yana buda baki da sauri na mike ina fadin anyi sallah ne Uncle ?
Yayi murmushi yana fadin kin falka yays jikin nace da sauki tare da sauko da kafafuwana kasan kujera da nake sama.
Yun kurawa nayi don in tashi zuwa sallah sai na gaza tashi wani irin jiri ya dauke ni da sauri ya mike ya taso zuwa inda nake yana fadin yi a hankali fa.
Kin san ba ke saya kike ba yanzu dole kibi sannu don Allah zama yayi saman kujeran tare da riko min hanaye na ya mayar dani ya kwantar yana fadin sannu bari ya dan sake ki sai ki tashi.
Na dan dade kwance a wurin sai da naji jirin ya sake ni na mike na shiga dakin kwanan mu wanka nayi don nauyin da jikina yayi a lokacin ko zai sake.
Na fito na tada sallah bayan na idar na dade a wurin zaune ina mika godiyana ga Allah tare da fatan Allah ya bani mai albarka.
Ina nike abin sallah nawa sai gashi ya shigo dakin dauke da abinci a hannun shi wanda noddle ne ya dafa a lokacin yake shan ruwa dashi kallo daya nayiwa abincin naji wani amai yazo min a bakina.
Da sauri na juya tare da boye fuskana ga ganin abincin dake gaba na tashi na shiga ban daki banyi komai ba na fito.
Yana zaune bakin gado yake fadin abincin bai maki bane kuma na cewa ban dai jin cin shi ne a raina kawai.
To may zaki ci ya tambaye ni nace zan dai ci fruits in na samu falo ya koma ya debo min fruits mai yawa zai juya sai gani na fito falon na karbi plate din a hannun shi da sauri na koma saman kujera na zauna.
A hankali nake taunan apple dana fara dauka naji yayi min dadi a baki na muna hira ina cin abina sai gashi na cin fruits din sosai.
Naji yace a lissafi na cikin nan tun kan mu tafi bauchi gaida hajiya kika samay shi idanuwa na na lumshe kawai tare da daukan dan annibi in jefa a bakina.
Tun wanan lokacin na ke samun wani kula na mussanman daga wurin uncle din nawa ciki kuma na bunkasa acikin koshin lafiya da samun kulawa a jikina.
Don ban damu da cin abinci ba saidai bani wasa da cin diyan itatuwa dama gashi akwaishi kasan da muke kamar banza.
Tun Uncle na fadan rashin cin abinci ya gaji ya kyale ni tunda yaga diyan iccen kawai zanci ya zauna lafiya a cikina abincin da raina ke so babu shi a kasan.
Alhdullahi uncle ya gama abinda ya kawo shi kasan kai ya kammala sunyi nasaran shiga da kayan su daga nageria sun kuma juya su sun zama kudi sun saro abinda suke so a can sun tura nigeria din.
Saura sati daya mu bar kasan zuwa kasa mai tsarki ya dauke ni mukaje shopping din kayan baby acewar shi yana da wuya ya samu dawowa kasan kafin in haihu.
Mun dawo a gajiye gida ba abinda nake so kamar indan watsa ruwa lokacin sai in dan kwanta kuma don in huta saboda naci gaba da azumi da na samu sauki.
Bayan na fito daga wanka falo na dawo inda yake zaune yana wani lissafi a cikin laptop din shi a lokacin.
Kujera na samu na zauna ina kokarin kwanta a lokacin sai ga kiran Faiza ya shigo min na dauka da sauri muka shiga gaisawa da ita din.
Yana zaune yana jin hiran mu take fada min wai ashe haka mukayi ma anty bana na hana uncle ya bata rabon kaya wa yan uwa sai ni na raba.
Nan dai take fada min irin zagin da nake sha gun anty yana jin mu sai murmushi yake yi kawai yana ci gaba da aikin shi mukayi sallama na dago ina sauke ajiyan zuciya.
Tare da fadin nikan na shigesu ga anty wai sai yaushe ne wanan abin zai kare a tsakanin mu ne wai ?
Bata tare da ya kalli inda nake yana aikin shi yace sai ranan da zaki bar mata mijin ki ta aura ma wacce take son ta aura min din.
Nace zan dai bita a hankali in gani ko zamu kawo karshen matsalan amma zancen in bar mata mijina ai ko a mafalki bata raya haka gare ni yanzu.
Ina wurin kwance har lokacin shan ruwa yayi na mike jiki a sabule na har hada muna komai anan mukayi buda baki shine yake bamu sallah kullun dani da shi.
Mun idar muka zauna cin abinci kowa yayi shiru sai cin diyan icce na nakeyi hankali kwance naji yace dani zanso kafin mu bar kasan nan mu koma asibiti su baki don kin san asibitin irin ta masu lalurar mune zallah a wurin.
Da sauri na dago kai na dan kalle shi nace uncle kana nufin duk mutanen da na gani a wurin suna da cutar dake karya garkuwan jiki a tare dasu.
Yace ai kin san kasan nan mafiyawan su kasan baki ne don haka kowa ke abinda ya ga dama a kasan shiyasa har suka kai ga bude asibiti irin haka.
A hankali na shiga tunane a raina don zama da uncle yasa yanzu har sai in manta cewa muna dauke da matsala a jikin.
Tuno abinda zan haifa nayi ko in haifi mai lafiya ko kuma kasin hakan Allah kadai ya sani banyi aune ba naji idona yana fitar da hawaye tausayin kan mu da abinda zamu haifa din ya kamani a lokaci guda.
Dago kai yayi ya dan kalle ko ban fada ba yasan abinda nakewa kuka a lokacin don yasan tunane na idan ya nufa.
Ji nayi yace dani kiyi hakkuri madam ni kaina wanan tunanen kanzo min a rai har a baya nikan raya ba zan yi aure ba balle har in haihu in mutu in bar yara a cikin maraicin iyayyen su.
Amma da na natsu sai naga ai Allah mai kashewa kima shine mai rayawa ga masu lafiya suna mutuwa subar marasa lafiyan abin daga hannun Allah yake don haka sai na barwa ubangiji sanin sa.
Haduwa ta dake kuma sai kika kara mantar dani daga damuwan da nake ciki a baya don haka yanzu na ragumi kaddaran da ubangiji ya jarabi rayuwan mu dashi a duniya.
Ga komai na rayuwa ubangiji ya hore ma rayuwan mu dashi amma sai dai muna rayuwan ne cikin BAHAGON RAYUWA.
Domin bamu san yadda abin zai kasance damu ba a karshe sai dai muyi fatan gamawa da duniya lafiya don wanan rayuwan yishi kawai ake a bahagon yanayi.
Nado kai a hankali muka kalli juna sai naji so da kaunar shi da tausayin mu ya dira min a zuciyana.
Nace Uncle mu namu kaddaran ke nan yazo muna a haka sai muyi fatan samun mai lafiya mutaima mu bashi tarbiya mai inganci koda bayan mu bazai samu matsalan rayuwa ba.
Naji ya riko min hannuwana da na sake fruit din da nake sha a hankali yana dan murzawa yace Safiya har kullun addua na shine mu samu zurian da zamu bari a duniya ko bayan mu zamu samu masu muna addua da tunamu a matsayin iyayye a gare su.
Addua na yanzu shine Allah ya sauke ki lafiya ina mai tabbatar maki bayan haihuwan ki zaku samu kullan yadda ya dace a gare ni.
Don a lokacin zan tabbatar maku dani din zsn zamay muna jigon rayuwa da ko bayan raina zakuyi alfari da samu na a tare daku.
Nayi murmushi tare da fadin insha Allahu a tare zamu raka da junan mu har diyan da zamu haifa din yace tau Allah ya bamu rai da lafiya din nace amin da sauri don yadda ya karasa maganan shi akwai tarin damuwa a zuciyar shi sosai.
Nayi ajiyan zuciya tare da kokarin hada kayan da mukaci abinci ina gyara wurin ina gamawa na shiga wanka don a gajiye nake lokacin.
Bayan shima ya fito wankan ne ina zaune bakin gado na mayar da hankalina sosoi a wayana ina duban sakon nin dana samu ranan.
Yafito daga wankan yake cewa dani ya kamata dai tunda anji sauki kuma sai in samu tukwaici haka horon yayi yawa mana madam ya iso gare ni yana kokarin taba min , , , .
Da sauri na manna mashi cizo daidai kunnen shi cikin rashin damuwa sai dai kokuwan da muka fara yana sai ya rama a lokacin na shiga rokon shi sai kirjina yake hari wai anan zai rama cizon shi na fara tsala mai ihu bai sa ya sake ni ba.
Sai dariya da yake kwasa yana fadin sai ya rama cizon shi anan din saman kirji dole na kyaleshi yayi abinda yake so din.
Washe gari muka tafi asibitin kamar yadda yace munga likita yakuma dora mu a maganin da zanyi amfani dashi da kuma yadda zan kare lafiyana dana jariri har reno da komai sai da yayi muna bayani yadda ya dace.
Yaje ya sayo maganin masu inganci da amfani wanda bazamu samu a gida nigeria ba sai a nan din ko wata kasa da taci gaba sosai a duniya.
Mun hada komai na ranan thursday muka tashi da dare zuwa saudiya inda zamu yadda zango a wata kasa kafin mu isa can din.
Sai dai duk wani sayaya da mukayi a canada ya tura gida Nigeria za a tafi muna dashi a cikin sabin kayan da zasu tura can.
Mun sauka a birnin madina direct inda already an sama muna masauki inda zamu zauna wanka kawai mukayi muka isa masallacin fiyayyen halita muka mika gaisuwan mu gare shi bamu dawo masaukin mu ba sai da mukayi sallah ishai acan muna ta rokon Allah saukin alamura.
Kwanan mu takwas a madina muka wuce birnin makka mukayi umurah sai mu muka shiga zama ko yaushe a massalaci barci ne kawai ke kaimu masaukin mu.
Ban taba sanin haka uncle keda yawan ibada ba sai wanan tafiyan namu don duk da yasan ina cikin lalura hakan bai sa mun dan huta ba sai dai ko yaushe yana kara min karfin gwiwa da fadin in dai jajirce in matsa mu samu wanan falalan.
Cikin ikon Allah Allah ya bani lafiya sosai dana samu kwarin yin abinda ya kaimu kasan mai tsarki ranan da aka sha ruwa washegari muka fara shirin komawa gida .
Ban samu zuwa sayayya ba shida wani abokin shi da matar shi suka tafi sun ko sayo muna kaya masu kyau koni naje da kaina iyakar abinda zan sayowa kaina ke nan.
Jirgin mu ya sauka lafiya a Abuja inda su yaya saadu suka zo taron mu da dawo kallo daya mutum zai min ya fahinci na samu sauyin rayuwana.
Na murje na zama wata katuwa na kara girma da cika ta ko wani sassan jikina haskena na asali ya fito sosai a jikina.
Rigar dake jikina ya biye cikin jikina sai may kaifin tunane ne zai gane hakan gare ni da sauri amma wanda bai san ciki ba sai yace na samu lafiya ne kawai.
Na dan jirkita don zaman jirgin da nayi don haka hutu kawai nake bukata a lokacin don tafiyan dare mukayi muka iso da safe.
Don haka muna shiga gida sallah na gabatar sai na samu wuri na kwanta sai barci da zazzabi mai karfi ya rufe ni ga samira da su Aisha duk gidan amma ban samu zama dasu ba a ranan.
Sunzo sun fahinci banda lafiya haka yasa jikin su yayi sanyi sai kuma aka shiga yi min sannu ina dunkule a cikin bargo shi yashi ya bani magani na sai barci ya dauke ni.
Ni dai har suka watse gidan ban sani sai mummy maman samira da yarta aka barmin so zauna dani a gidan sai da nayi kwana biyu sannan na samu zazzabin ya sauka min.
Na fito falo da yamma na zauna don jikin nawa ya dan kara sake min sosai ya shigo gidan anan ya samay mu zaune muna dan hira jefi jefi dasu.
Zama yayi a kusa dani yana gaida mummy da gida sai ya juya inda nake yana fadin jiki ya jikin madam ?
A hankali irin mutum ya tashi ciwo yadda yake ji nace mai naji sauki tare da lumshe idanuwana a hankali.
Mummy dake gefena zaune ta nisa tare da fadin amma sai ina ganin kamar wanan madam din ta samu karuwa ne don tun ranan da kuka dawo nake ganin haka a gareta.
Uncle yayi saurin dago kai ya kalleni na dukar da kaina kasa yace mummy na magana dake fa.
Nace aiba dani take magana ba dariya yayi ya gyara zaman shi yana fuskantar mummy din sai dai ina ga in jikin bai bari ba zuwa gobe sai mu koma asibiti.
Da sauri nace mashi ai naji sauki ba gashi na fito ba yace kin ci abinci nace kai nake jira ka aika a sayo min fruit in sha.
Mummy tayi saurin cewa bana fada maka ba wanan ciwon nata da walaki a cikin sa mutum yace baicin komai sai diyan icce kawai yake dura ma cikin shi.
Ya dan kalle ni yayi murmushi yace mummy ko acan shine kawai abincin ta duk abinda taci sai ta amaye shi shi kadai take ci a zauna lafiya.
Mummy ta sake cewa ai duk wanda yasan ciki ya kalli Safiya yasan tana da ciki ubangiji ya raba ku lafiya yaba rayayye mai albarka ya amsa da amin da sauri.
Mikewa yayi yana fadin barin in sa a sayo maki yanzu ki samu kisha ko jikin zai kara sakewa yace mummy dai ta gano abinda kike boye masu.
Murmushi nayi kawai idan yaso wasa sai ya juye kamar ba shi ba a gidan amma indan yan kai na saman kan shi zaifi sati daya yana dunkulan baki rai bai magana da kowa bayan gaisuwa.
Ni yanzu na saba da halin shi don haka duk irin yadda ya juya nasan yadda zan bi dashi a zauna lafiya masan mun dawo gida yanzu halin zai tashi mai.
Don a can ko yayi fushin bai jimawa yana yi zai sake mu koma daidai amma da zaran naga ya fara daure fuska nima sai in kama kaina dashi.
Washe gari ne mukayi baki daga bauchi inda yan uwanshi ne mata zallah hajiya baaba taba mota wai su zo su dubani su kuma ga sauksn mu.
Basu fada muna suna tafe ba sai ganin su mukayi Allah ya taimake ni mummy na gidan kafin wani lokaci tayi masu abinci mafi sauki don har Nura ta tafiko yamma yayi.
Dole na mike haka na ba dadi jikin nawa muka shiga hidimar baki a gidan ya dawo ya samay su don sun fita da yaya Saadu a lokacin .
Yayi murnan ganin su sai dai tunda suka gaisa ya shige dakin shi bai sake fitowa ba sai da naji shi shiru ne na leka shi dakin nashi.
Na samu ya fito wanka yana saye da jallabiya a jikin shi haka yasa na gane zai fita sallah ne a lokacin yana gani na yace ashe baki gare ki haka gidan ?
Murmushi nayi don jin abinda ya fadi nace wallahi aisun yi kokari da suka zo dubamu don basu taba zuwa ba sai wanan karon.
Gashi kuma naji suna fadin wai gobe zasu koma baaba tace dasu lalai su dawo a gobe din yace kai haba ai ta bari su dan kwana biyu dai.
Nace to sai kayi masu magana ai suma zasu so hakan wallahi don akwai gajiya a jikim su.
Tare muka fito ya wuce massalaci nikuma na koma daki na don inyi shirin alwala sai da na bi ta wurin su naga basu bukatan komai na wuce bayan sun dan jani da wasa irin ta kannen miji da akeyi.
Naji dadin kansan cewar mummy a gidan don tana da matukar kokari sosai bata jin nauyin jikin ta ko kadan kamar ba ita ta haifi Samira ba, don samira bata kaita kiza kiza ba.
Bayan na idar da sallah nan dai na dan kai kwance don yanayin jikin nawa da bai gama sake ni a lokacin wanda nasan gajiyan aikin da mukayi ya dan tambaye ni da zaman jirgi.
Yar uwa riban da kike samu wurin fitar da novel dina sai ki shirya dake da masu karatun novel din sata don taki ta samay ki a rayuwa muje zuwa in dai kin ce wasa da kallaman Allah kike yi .


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/25/20, 10:38 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , , , ,


🧕🏿6️⃣4️⃣🧕🏿

NOVEL DINA NA KUDI NE IDAN KIN FITAR ALLAH ZAI FITAR MIN DA HAKKINA AKAN KI IDAN KUMA KIN KARANTA KI SAN HAKKINA NA KAN KI.

Yar uwa na fadi zan sake fada ban yafe ba idan kin fitar min da novel waje Allah yabi min hakkina akan ki don bayan yafe ba.
Idan kin karanta min novel baki biya ba ubangiji ya kwato min hakkina a gunki cikin gagawa.
Bakin mu sun tafi cikin dadin rai muka rabu dasu lafiya suna ta farin alherin da dan uwan su yai masu da zasu tafi koni nayi mamaki don a yanda uncle yake bakacewa yana da tarin arziki irin haka a rayuwan shi.
Kyaunta yamun dadi har cikin raina don yadda ya dauko yiwa yan uwa alheri ba karamin alheri bane agare ni don na fita zargi daga bakuna su.
Yadda nake jin suna zagin anty kan ta kakace komai da karshe akaina zagin zai dawo sai gashi ya sauya gaba daya wanda suke ganin wai nice na sauya shi hakan.
Ko yan uwana bai bari ba don kullun aiken shi na hanya zuwa wirin yan uwana da iyayyena sai dai inji sun bugo waya suna min godiya abinda ya aika masu din.
Gashi dana fara mai godiya zai daga min hannu alaman ya isa haka na sai da yayi dana gode mai bani fasawa.
Ba abinda ke mun dadi kamar yadda mahaifan mu ke sa mashi albarka har nima abin ya shafe ni don da hajiya baaba da babana ida sun fara mai addua idan ina kusa sai na lumshe idona don jin dadi.
Sai dai halin shi na fushi yanzu ya rage don baya wuce kwana daya yana fushi dani ko don cikin dake jikina ne yake raga min ban sani ba.
Don Uncle akwaishi da saurin fushi abinda baka dauka abin fada ba yanzu zakaji ya juye ya koma fada gare shi.
Sanin halin shi da nayi yanzu na gane bai son kana magana yana yi sai in ja bakina inyi shiru sai ya gaji ya kyale don kan shi.
Abin da kan yawan hada mu shine fita a dade duk da ba fita nake yi ba don bai bari na mami kowa a garin ba sai yan uwa tsiraru da muke dasu ko nafita sayen wani abu da zaran ya kira nace ban koma gida ba ya ishe shi jidali har wani lokaci.
Ya hana mummy komawa gidan yaya Saadu wai ta zauna dani har in kara jin karfin jikina don acewar shi ban gama warwarewa ba har yanzu.
Ina jin dadin zaman mummy don mace mai dadin zama ga sa mutum hanyan daya dace yabi na alheri ga kuma bata jin kiuya ko kadan aiki ba sha mata kai ga tsabata gidan nan ko yaushe kwal yake don tsabtan ta.
Hakan yasa ya yanke sharan bata albashi duk wata da farko taki karba wai ai an zama daya don yaya saadu yana kokari dasu.
Sai uncle yake cewa ta karba ai duk wanda ke karkashin shi haka yake masu shine dalilin karban kudin ta duk wata.
Yaya Saadu da matar shi samira sunzo kan hakan da yake yi sai cewa yayi shi in son samune ma mummy ta zauna damu tunda ba komai take yi ba acan.
Idan tana son zuwa ganin yaranta ba zai hana ba taje tayi kwanakin da zatayi ta dawo don shi hankalin shi ya kwanta da ita don ko na haihu dole ne ya nemo wanda zai kula da baby din.
Yaya Saadu yai mata magana kuma ta amince mashi din da hakan tunda dama zaman hakkuri takeyi can yara kowa ya kama gaban shi.
Muna waya da anty don dawowan nan namu na tura mata kudi wanda yake bani duk wata na hada dari biyar na tura mata don dai a zuna lafiya ni da ita don kawai na fitar da komai a ranta mu zauna lafiya.
Ranan nasha yabo a gunta take cewa in dan hada da dabara ina rika amsan kudi idan sun taro sai ta san abinda zatayi min dasu nace anty na gode.
Wanan yasa ko yaushe yanzu muna waya akai akai da ita ba kamar baya ba can da ta share ni din haka yasa han kalina ya kwanta yanzu don da ina cikin damuwa idan na tuna halin da muke ciki da ita na rashin shi.
Yau tun safe uncle bai fito ba yana dakin shi bayan na gama karyawa na nufi dakin shi don in duba shi sai na samu yana rufe yana barci haka yasa nayi zaton hutu yake yi kawai.
A hankali na jawo mai kofa na rufe sai naji muryan shi yana kirana don haka na tura kofan na koma ciki karasawa nayi bakin gadon da yake.
Murya ta alaman rashin lafiya yake magana da cewa don Allah hado min tea ki kawo min nan zan sha magani da sauri na duka ina fadin Uncle baka da lafiya ne?
Kai ya gyada min alaman eh sai nakai hannuna saman laulausar kan shi dako yaushe bai rabuwa da gashi irin na fulani yayi kwance lup a saman kan shi.
Zafi naji jikin nashi yayi nace subbahanallahi Uncle kuma kake kwance jiki ba dadi haka a gida gyara kwanciya yayi yace jeki hado min tea din don Allah.
Fita nayi da sauri nan dai na hada mai komai na dauka zuwa dakin har lokacin da na dawo dakin yana kwance a yadda na barshi na fita.
Bayan na aje ne na dan taba shi ina fadin ga tea din na hado maka Uncle ya dan yi mika tare da bude idanuwan shi ya sauke a kaina.
Ina tsaye akan shi cikin damuwa na kura mashi ido sai da ya dan jima ya mike zaune tare don son yunkurawa ya tafi ban daki nasan kewaya yake son yi amma ya kasa.
Tsoro naji sosai a lokacin nace in taimaka maka ne ka tashi ya dago kai yadan kallene sai ya girgiza kan shi yace hada min ruwa dai a ban dakin .
Na shiga na hada mai na dawo wurin shi har lokacin yana zaune a yadda na barshi hannunwan shi na rike sai ya dafa ni ya tashi tsaye da taimoko na ya je ban dakin ganin ya shiga ya fara tubewa na barshi na fito.
Wayana na dauko na kira yaya Saadu nake fada mai yau Uncle ba lafiya da sauri yace gashi nan zuwa yanzu ya dan jima ciki ya fito bai ko tsaya share jikin shi ya dawo saman gadon dana gyara bayan tashin shi.
Kurban tea din yayi bai sha wani abu ya koma ya kwanta tare da dan yin nishi nace maganin fa yace barin dan huta zan sha ai.
Ina tsaye a kan shi ina kura mai ido idanuwan shi a lumshe ina tunanen lokacin da yaya Ahmed yayi jinya ina gidan shi yadda yayi tayi mun a lokacin da yadda hankalina ya tashi gani ni kadai a gida dagani sai shi haka nayi ta jiyar shi har ya samu lafiya.
Nace kilama lokacin duk yana dauke da cutan yake jiya hakana ni ban sani ba saboda kurciya da nake dashi.
Wayana yai kara ne yasa nasan yaya Saadu ya iso ke nan da sauri na juya na fita zuwa wurin shi yana tsaye falo ko zama baiyi ba.
Ina fitowa ya tare ni yana fadin yana ina nace yana dakin shi bai tsaya ta kaina ba ya nufi dakin nashi da sauri ina biye dashi a baya nima da sauri nake mara mai baya hankali na yayi kololuwar tashi da yadda yake kwance sharaf.
Muna isa kofan ya shiga da sallaman shi uncle yana kwance a yadda na barshi ciki jin muryan yaya daji yasa shi dan dagowa kadan yana amsa sallaman da kyat.
Yaya ya karasa gun shi yana fadin yallabai yau jikin ba dadi ne haka yadan dago yana dan yake yace Saadu ta taso da kaine kuma ?
Yace wallahi fa na kirata mu gaisa sai take fada min jikin naka yau bakajin dadin sa sosai ya dan kara gyarawa yace wallahi ai duk kwanan nan karfin hali nake bana jin dadi.
Nabishi da ido da mamaki cike a fuskana sai naji yaya Saadu na tambayan shi ko zasu tafi asibiti ne sai yace kasan matsalan ciwon mu da zaran mutum yayi dan ganganci yanzu ciwon zai bugar dashi ne.
Akwai wani yaro dake zuwa nan gida ya kara min ruwa shima yana da irin matsalan tare dashi yana kokarin jawo wayan shi dake karshin filon da yake kwance akai.
Yace amma kafin yaron yazo barin in hade magani da zai saukar min da zazzabin don baa shan maganin sai aci abinci sosai.
Cikin marairai ce murya nace dashi a kawo ma wani abu kaci ne yanzu kai girgiza min ya bude baki da kyat yana cewa tea dana sha is ok for me.
Drower ya nuna min da hannu yace jawo wancan zaki ga wani dogon roba fari ki dauko min na isa wurin da sauri na tare da jawo drower din na dauko mai maganin.
Yaya ya karba naje dauko mai goran ruwa mara sanyi ko da na shigo na samu yana kiran mai kara mai ruwa din a wayan shi.
Jefi jefi yake jefo ma yaya magana wanda nasan don ya kwantar muna da hankali yake yin haka amma ta yanayin maganan zaka gane yana jin jiki karfin hali ne kawai irin na maza.
Doctor ya iso idan ya kira wayan shi yaya saadune ya fita don ya shigo da likitan dakin shi bayan fitan yaya ne ya kalle ni sai yaga ina hawaye a lokacin.
May kike ma kuka madam baki son in mutu in barki ne kai na gyada mai tare da fadin don Allah uncle kabar wanan magana haka insha Allah bazaka mutu yanzu ba sai ka tsufa damu .
Murmushin karfin hali yayi yace kaiyya ko daina wanan tunanen daga ni har ke ko yaushe mutuwa ai zata riskan mu koda ciwo ko babu ciwo don haka addua kawai ya kamata ki muna shine mafita.
Shigowan su yaya Saadu ne dakin da likita wanda yanayin shi ya nuna kamar kabila ne shi yake cewa yaya ga kaunar ka nan kuka takeyi wai bata son in mutu in barta.
Murmushi yaya yayi wanda nasan na karfin hali ne shima yace ki kwantar da hankalin ki Safiya in sha Allahu zai ji sauki.
Jikin dai ne nashi ya dan motsa mai kin san sha anin yau da kullun dole haka ya kasance ga bawa ko yaya ne don haka ki koma dakin ki kiba likita wuri yayi aikin shi.
Dagawa nayi jiki a sabule zan fita a dakin Uncle ya kirani yake cewa don Allah kada ki bugawa kowa waya banda lafiya har Aisha .
Kai na gyada mai na fice daga dakin raina ba dadi don duk na tsarace da ciwon nashi wanda dan lokacin kadan duk ya ramay kamar ya dade yana jinya akwance.
Ina fito sai ga mummy ganin yanayi yasa take tambayana ko lafiya taga Saadu yazo gidan ya shiga dakin maigida kuma.
Nace yau baya jin dadin jikin shi ne shine yaya saadu ya dauko mai likita da sauri tace subbahanallahi da sauki dai ko ?
Ta tambaya cikin son karin bayani nace jikin da sauki mummy nan muka zauna tana kwantar min da hankali har likitan ya fito dashi da yaya.
Yaya yace in je yana kirana sai dai kafin in isa dakin ya samu barci a lokacin nan dai na zauna wurin shi ina kallon yadda ruwan da ake kara mai yake shiga jikin shi.
Yaya Saadu bai dawo wurin shi ba haka yasa na dauka ko ya wuce office din sune ashe yaje ya sawo wani magani ne da fruit da dai wasu abubuwa.
Da ido yaya saadu yayi min magana na biyo shi muka fito daga dakin a falo muka tsaya ya juyo yana fuskanta na tare da cewa ki kwantar da hankalin ki.
Insha Allahu zai samu lafiya zazzabi ne mai karfi yadan bugeshi kin san mijikin baya hutu sai irin haka ya kasance dashi.
Kamata yayi ace ya ware wasu ranaku da zai rika zama gida ya huta don jikin nashi bai maison wahala bane ko kadan don Allah ki san yadda zaki kawo mai wanan shawara nima zanyi nawa kokari inga na fahintar dashi.
Nace na gode yaya yace shi zai tafi don suna da aiki akwai kayan da zasu shigo masu daga waje zai je yaga komai ya kammala a wurin.
Na sake mai godiya yace ba komai wanan ai duk ya shafe mu har zai tafi sai ya juyo yana fadin don Allah kada a tasheshi idan ba shi ya falka da kansa ba.
Mummy tafito jin muryan yaya tana fadin zaka tafi ke nan yace eh zai koma wurin aiki sai dai an jima zai dawo ya duba jikin nashi.
Bayan mun dayi magana da mummy na koma dakin wanda har lokacin ya sharar barci sai dai dan hannushi da ya dan karkace mai na gyara mashi a hankali hakan bai sa ya falka ba daga barcin da ya samu din.
Zaune nake na kura mai ido daga saman kujeran da nake zaune zuciya sai faman sake sake take min a kan shi ban sani ba har barci ya dauke ni a wurin mai nauyi nima.
Ban san tsawon lokacin da na dauka ina barcin ba shi ya fara falkawa ya hangoni zaune nake barci tausayi na bashi.
Don yasan wai gadin shi nake a haka barci ya dauke ni a gurin ya dade kwance yana kallon yadda nake barci a wahalce daga zaune.
Ga ruwan dake makale a hannun shi saura kiris ya kare a ledan jin kamar motsi yasa na zabura shi na gani a zaune yana cire roban ruwan a hannun shi.
Da sauri na mike na isa wurin shi ina fadin ka tashi yaya jikin na ka ina kokarin taimaka mai da ledan ta hanyar rataye ledan da allura sama.
Sai da ya dan dade zaune ba tare da yayi magana ba sai ya mike zuwa ban daki ya dan jima ya fito tare da dauro alwala zai yi sallah.
Nace dashi lokacin sallah yayi ne yace kina barci ina zaki san lokaci yayi anya haka ake jinya mai jinya barci mai ciwo barci ni dake wazai dubi wani a haka.
Murmushi nayi ina shimfida mai abin sallah tare da cewa wallahi ban san lokacin da barci ya daukd ni ba a haka zaune bai magana ba sai murmushi ganin ya tada sallah na nufi dakina don nima in gabatar da nawa sallah.
Na dade zaune bayan na idar ina kai kuka na ga Allah yabamu lafiya ni da mijina a wuri san nan na mike na fito abinci na fara hada mai nakai mashi.
Har lokacin yana zaune yadan kara jikin shi da bangon dakin kamar yana tunane na shigo dauke da abincin na zauna bayan na aje mai a gaban shi.
Ya dago kai yana kallona tare da da fadin zan ko iya cin abincin nan da dai fruit kika hado min watakila zan iya dan sha.
Nace uncle kayi ko two spoon ko three zaifi ka zauna bakaci komai duk yinin yau hakan zai iya jawo ma wani matsala kuma don Allah kadan daure kaci ko kadan ne.
Baiki ba na zuba mai ganin baya son ci yasa na karbi cibin a hannun shi ne debo nakai mai a bakin shi.
Murmushi yayi ya bude bakin ya karbi abincin yaci nima na debo nakai bakina don dai ya danci Alhamdullahi na samu yaci yakai cibi hudu yace ya koshi.
Mike nayi na kwashe kayan sai ya riko ni yana fadin ke ba zakici ba kin san fa kin finu lalura sosai kada kije ki haifa muna baby ba kosasshe ba.
Murmushi nayi nace nima fruit din zan sha idan na gyara hakan yasa shi ya kyale ni na fita da kayan nakai kitchen nan na tsaya na hada muna fruits salad.
Nan mummy tazo ta samay ni ina gap da gamawa take tambaya na yaya mai jikin nace da sauki mummy har ya danci abinci yanzu.
Tace a da sauki ke nan in dai ana cin abinci ai zai zo da sauki ciwon da ba a ci ba a sha ai yafi wahala ga mai jinya.
Nace muje ki duba shi mana mummy tace a bana shiga dakin mijin ki ba nace haba muje dai ai ba a kwance yake ba.
Ina gama mummy na bayana na shigo dauke da bowl din dana hada salad din daga kofa mummy ta tsaya take gaida shi ya amsa da mummy ne shigo mana.
Bata dai shigo har cikin dakin ba ta tsaya daga kofa tana mashi yaya jiki ya amsa da mummy naji sauki sosai tace Alaji ka dan dinga hutawa mana haba ga kunan kullun cikin aiki ba hutu.
Murmushi yayi yace mummy ai aikin nawa mai sauki ne da wanda ke yini a cikin rana ko yaushe jikin dai ne dama ba lafiya gare shi ba.
Tayi mashi sannu ta fita daga dakin ya mata godiya tana fita na zauna a kusa dashi tare da fara zuba mai yana zaune ya kura min ido kawai har nagama na miko mai.
Yakarba tare da fadin thanks gefe na koma na zauna tare da tsura mai ido da ido yayi min alaman in diba mana sai na kada mai kai tare da fadin ban jin sha.
Yau din baki shan fruits din nace na koshi ne sai naga ya debo ya mika min ba yadda na iya dole na bude baki ya zuba min amma sai naji yau abincin nawa ya koma min kamar madaci.
Da kyat na iya hade wanda ya rage min abaki na sai na samu kaina da tura kaina cikin kafafuna na dunkule a waje daya ina kuka.
Ji na ya kamoni zuwa jikin shi tare da dan bubuga min baya a hankali ba hana ni kukan ba sai da nayi may isa ta ya mika min ruwa in sha.
Ban ki na karba na dan kurba na aje kofin shidai yana zaune ya kukara min ido muryan shi naji ya katse min tunanen dana fara yi a lokacin wai may kike ma kuka ne haka.
Na bude baki nace Uncle bani son in rasaka cikin wanan halin da nake ciki kaine uwa da uba a gare mu idan na rasaka yaya rayuwa zata koma ?
Sai na fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciyan mai sauraron ta kamoni yayi zuwa jikin shi ya lalashi na wayan shine yayi kara a lokacin hakan ya dakatar damu da maganan da mukeyi.
Ji nayi bayan ya amsa wayan yana fada min ga yaya Saadu nan yadawo duba jikina yana falo.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/28/20, 11:45 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , , , ,

🧕🏿6️⃣6️⃣🧕🏿


Barci mai dadi ne ya dauke ni bayan sallah azahar inda na sallamay sallah a wurin na kwanta saman ties sai barci.
Muryan mummy nake ji sama sama a cikin barcin nawa take fada min ga dan uwan ki nan yazo da kyat na bude idanawa na ganta tsaye akaina.
A cikin idon barci nake magana da ita nace mummy kina magana ne tace eh dan uwanki ne yazo daga gida.
Da sauri na mike zaune don nasan da zuwan yaya sani din a lokacin na dan jama zaune bayan mummy ta fita daga dakin .
Na fito yana zaune yana cin abincin da mummy ta gabatar a gare shi cikin jin dadi da ganin shi ina murmushi nace yaya sani kaine a garin yau?
Shima murmushi yake da gani na yace wallahi nine Safiya ai tun jiya naso zuwa to nakai su babane da ummi wurin alluran mahajta shiyasa na bari yau na taso.
Nace Allah sarki kuna kuna shirin tafiya zaku taka kasa mai tsarki abinku yace wallahi kin ga ikon Allah ke nan Safiya.
Ai maganan baba kullun yanzu akan mijin ki yake yana yawan cewa bai san itin adduan da zaiwa bawan Allah nan a rayuwan shi ga gida kuma ga makka kusan lokaci guda.
Nace haka abin Allah yake sai yazo ma ta inda baka zata ba a rayuwan ka na fadi ina zama kusa dashi.
Yace wai naso ummi taga yadda Safiyan ta ta koma kamar wata irin hajiyan birnin nan wallahi safiya haka kika koma yanzu.
Dariya nayi mai nace kai yaya sani ho yau kuma yar kaunar taka kake zolaya haka ?
Yace wallahi ba zolaya bane kin koma din ne yace ashe maigidan ya fita waje sai yanzu nake ji a wurin mummy da nazo gashi kuma shiyace in shigo a cikin satin nan.
Nace ai ina ganin yaya Saadu ne zaka hani don yabar sakon ka a gunshi koda yake ba,ayi dani ba amma kamar sakon na babane.
Yace kuma dai baba bai sani ba da bai bari nazo ba don sai da yaja min kunne tace kada in yarda yace zai yimin wani dawainiya gidan zumu ba kasuwa bane.
Murmushi nayi Allah ne kadai zai saka mashi da alherin sa ai amma Uncle yana dauwainiya dayawa wallahi bamu kadi harda yan uwanshi haka yake fama dasu suma.
Yace haka aike so indan ka samu yan uwanka ma su su san ka samu ba kazo masu inuwar giginya ba hange daga nesa.
Fitowar Mummy daga daki ne ya katse muna magana inda take tambayan shi Rukkaiya yace tana can gidan mijin ta ai yanzu.
Nace banko tambaye ka labarin mutanen gida ba mun zauna muna zuba hira yace cikin dariya kowa lafiya lau yake wallai.
Nan itama ta zauna mukai ta hiran gida dashi yana bamu labarin kasawar shanun baba da yadda abin yazo mai amma baba ya rabe wa mutane naman duka yace shima ai a alheri ya samu ya saya.
Sai da akai kiran sallah laasar yafita sallah muma muka kama gaban mu daga can ya fice gidan ya nufi gurin yaya Saadu.
Na idar da sallah ke nan waya na yayi kara na dauka hajiya baaba ce ke kirana da ladabi na amsa wayan kamar tana gaba na a lokacin.
Mun gaisa da ita take tambaya muna dai lafiya nace mata lafiya muke tace ashe shi yayi tafiya ne kuma nace hajiya bai fada maku bane ?
Tace ina zai fada muna don yasan in ya fada bazan barshi ya tafi cikin yadda tsufa din nan nace ai lafiya nake hajiya tace to aidaiyi ta hakkuri kin dai san yanayin mijin naki yanzu ba wani don haka zama tare sai da hakkuri nace nagode hajiya.
Tace yaya wurin su Aisha nace ta kwana biyu bata shigo ba amma dai lafiya take dai tunda naji shiru munyi sallama har zata kashe wayan naji ta tambaye ni.
Yanzu ke kadai ne a wanan katon gidan naku dariya nayi nace hajiya ai akwai mutane agidan yan aiki suna tare dani ban yarda na fada mata mummy na gurina don ban san yadda zata fasara abinba.
Tace hakan yayi ni dai ba zaku ganin ba sai idan Allah ya sauke ki lafiya zan zo inga jika na tunda nasan ba a nan zaki haihu muna ba.
Nace haka dai ummina tace bazata zo gida na ba sai na haihu tace ai shine mutunci ina dadi kullun kana yawo gidan dan ka.
Tasan mutuncin kanta ne tunda ta fadi hakan nace indai ummi ne hajiya nasan ba zuwan zata yi cewa zatayi ga iyayye na da yawa su zasu zo tace wanan shine daidai.
Kada kiga laifin ta dariya nayi nace amma ai hajiya mu bamuki ko yaushe mu ganku ba in zamu samu.
Ina jin dariyan ta tace bakuma zaku samu ba mudai fatan mu ku zauna lafiya shine adduan mu kullun akan ku.
Mun gama wayan naji dadin yadda hajiya ke jana a jiki tana nuna min kauna kamar yar cikin ta ko yaushe.
Wayan na jona charji zan fita daga dakin sai ya koma yin kuka na juya na dauka anty ce ke kirana saida gaba na ya fadi dam.
Na dauka da sallama muka gaisa tace kwana biyu najiki shiru nace barin in kiraki nace wallahi anty banjin dadi ne shiyasa ban kiraki ba kwana biyu.
Tayi min yaya na kara ji nace naji sauki ta dora da fadin kodai abin arziki ya samu ne kin ga ai magana na nafita yanzu sai mu tara kudi da tushe.
Zuwa haihuwan ki mun san abin da muka tanada ba sai dai kawai aga muna bushashan mu ba da kudi amma kin tsaya kina noke noke.
Ke barin fada maki duk wata mace da kike ganin tana heleke da haka ta tara ga gumin mijin ta amma ke naga tsoro yayi maki yawa baki karban kudi yadda ya dace ki tatse shi.
Murmushi nayi nace anty matsalan shi baya bada kudi ne sai dai yayiwa mutum hidima tace aike zaki koya mashi bayarwan .
Yanzu dai kin ga kin samu ciki kila don haka sai ki mayar da hankali kafin haihuwar ki musan abinda muka samu a wurin shi.
Ni dai murmushi nake mata kawai nace anty zanyi yadda kikace din idan ya dawo tace ina ya tafi nace yaje Spain ne.
Allah dawo dashi lafiya tace tana kara jaddada min in yi kokari ina yagan wani abu a wushin nace mata to anty tana fadin nan da yan watanin ai mun tara maiyawa yanzu haka daddy su twins ba karamin karba nake a wurin shi ba kin gani na.
Kokari nake yanzu in fara sanaa in bar wanan aikin nagaji dashi wallahi kullun mutum baida hutu a rayuwan shi yana hanya aiki.
Nayi mata godiya muka kashe wayan fitan da banyi ba ke nan na zauna ina tunanen maganan mu da ita yadda zan mu kwashe a karshe.
Don dai ni ban fada mata ina da ciki har ya tsufa a jikina ita da ke maganan nan da wasu watanen masu zuwa can.
Nidai buri na shine in samu mu rabu lafiya da ita don haka na yanke shawaran tura mata wasu kudi da ya bar min a gida don kawar da maganan.
Bayan sallah magariba su yaya saadu da yaya sani suka shigo gidan na fito falo wurin su nan muka zauna muna gaisuwa dasu.
Yaya Saadu sai sheri yake min wai na tsufa sosai na wani kara girma kamar bani ba kodai biyu na kwaso masu ne ?
Dariya na kece dashi nace aida sai Samira ta dawo gidan nan don ba zamu iya mu kadai da mummy ba.
Yace kina wasa mummy sarai ta iya rike so akwaita da kokari fa nace ai na gani wallahi itace ra fito daga daki tana masu sannu da zuwa.
Ta tambaye shi mutanen gidan shi yace suna lafiya yaji suna fadin gobe anan zasu wuni ai nace nikan ai saidai kuyi hakkuri dani yaya .
Don Allah ya hada ni da miji mai kule yace ai shi yafi Safiya mace mai yawan yawo ai bata da dadi sai da aiyi hakkuri kawai.
Mummy tace banda samira don ko dazun ta kirani wai suna kasuwa yayi saurin kare ta da fadin sun je sayayya ne fa mummy .
Don ni banda lokaci shiyasa nake bata kudi ita taje tace kudai zama yan bariki ai kaida matar taka dariya yayi yana kare matar shi wai ai bata da yawo.
Yaya sani ya kawar da hiran yace Safiya ki ji mijin ki wai ashe shanaye yake son sai wa baba .
Ido na zaro waje yaya Saadu yace yasan shanun baba ya kasa ne ko nace eh da yaya sani ya bugo waya muna tare anan yaji amma bai mun magana ba tun lokacin.
Yaya yace ai ya fadi don yace wai kada a fada maki nima next week nake son mushi wirin su muyi sallama don zuwa wani satin sama zasu fara tashi.
Mummy tace nasan dai kafin su daya suna samun kin haihu nace mummy tun yanzu tace laila da wuya in ba hakana zai faru ba kan.
Nace wai idan na haihu ummi bata kasan sai yaya sani ya tare ni da cewa ba aikwai mutane a gida ba sai wayanda ke nan suyi buki mana.
Shiru nayi dan tuna katobar dana so yi a gaban shi nace ai fa akwai mutane kan dayawa a gida zan dai ga yan gida kan.
Munyi hira dasu inda yaya Sani yace zai bi yaya saadu gidan shi ya kwana washegari samako yake son yi kada a nemay su baya nan.
Nace wai Alhaji sani ke nan yace bari ke dai Safiya har fa mutane sun fara kirana da Alhaji wasu ma gani suke da farko kamar karya ne ba zan tafi ba.
Nace wai ina yaya Nura yace yana nan wallahi ai yaso ya bata rai sai da mama ta fita bayan shi ya shiga hankalin shi.
Nace ya sani ko idan zamu tafi badi in Allah yakai ran mu muje tare yaya saadune yace dayake shi baida aiki sai kai yan uwan ki makka ba.
Dariya mm ayi tare da fadin yaya Allah ne ya kawo mu lokacin hutu mummy tace don haka sai a huta kuwa ai lokacin abu ayishi.
Mun dan jima muna hira mukayi sallama suka tafi mummy ta hada min abinci wai inci ban son ci amma dole tasani gaba dole na ci shi.
Daki daya muke kwana da mummy a dakina don haka muke kawa wani lokaci mu dan hira da ita sai mun gaji mu kwanta.
Washe gari su samira suka zo gidan nan muka wuni da ita da yar uwar ta anan nake jin wai yar uwar nata ta samu miji aure a inda suke.
A cikin hiran mu ne nake fada ma Samira abinda ke faruwa tsakanina da anty zancen in tura mata kudi tace.
Amma dai wanan matar ta fadi kasa wallahi ita duk kudin ta sai tayi zari haka mummy tasa muna baki a maganan mu tace hakan da Safiya keyi yayi kyau su dai rabu lafiya da ita ba shike nan ba.
Kudin may mutuncin da tayi mata yafi kudi ai tunda halin ta ke nan ba sai ai mata yadda take so ba a rabu lafiya rashin yin zai haifar da wani rikici a tsakanin su ne kuma.
Tunda yanzu mutane ba tsoron Allah ne da su ba kun sani ko har yanzu suna ga bakan su na son mijin ta ya auri yar wanan dayar matan.
Nace mummy in dai ma auren zasu yi su barni da lafiya suje suyi tayi kowa ya tsaya a matsayin shi mummy tayi saurin cewa dani.
Umm umm yar nan kada ki soma fadin haka kishiya idan ba dace ba babu wanda ke son ayi mashi sai dai in ya kama dole shine ba mafita.
Ai da zaran ya kara aure yanzu duk wanan mutuncin da kikaga yana maki sai ya ragu namiji ai ki barshi kawai.
Idanuwa na na lumshe ina tunanen maganan ta idan uncle yayi min kishi ni ai na shiga uku ko a gidan mu ba balle gun bakin jama,a.
Samira ne ke fadin jifa kishirya Aishan ku sai da mijin ya bata saki kwanan don ta ishe shi akan zancen gida da motar da aka sai wa Aisha din ji da muka je take fada muna.
Nace ai kaji matsalar duk da ba mijin nasu ya saya masu ba amma bata bari an zauna kalau ba kuma ?
Tace wai har nan gidan Aisha ta biyo shi da masifa anan ya dankara ma yar iska saki sai gata kuma ta zube tana kuka a gidan.
Mummy tace shine ai matsalar matan yanzu dan abu ba abu ba su mayar dashi fitina su hana kan su shaka da abokan zaman su.
Nace ai wanan zaman namu mummy sai mu, mace ta samu gidan aure amma kishi sai ya rufe muna ido mukasa koyi da halin iyayyen mu na baya.
Kuma mafi yawan mata haka muke yanzu da bakin kishi bamu natsuwa muyi kishin hankali sai na hauka wanda idan mutum yaji sai ya rena masu hankali.
Mun wuni cikin dadin rai dasu Samira a gidan sai yamma lis yaya yazo ya dauke suka tafi daga gidan.
A gaskiya ina jin dadin zama da mummy don ba karamin debe min kewa take a gidan ba bata bari taga na shiga damuwa ko kadan.
Mahajjata sun tashi lafiya har sun sauka kasa mai tsarki inda suka bugo min waya na samu layin da zan dinga kiran su a can .
Yaya sani ne ke rike da wayan a hannun shi don haka idan zan kira ummina ko baba sai nakirashi yake mika masu waya muyi maganan da zanyi dasu wanda duk wayan namu gaisuwa ne.
Har yanzu uncle yana gurin tafiya bai dawo ba a wani dare ya bugo muna hira yake fada min ba zai samu dawowa ba daga can zai wuce saudiya ya sauke fari a can.
Nace Uncle kayi min wayo ke nan ka tafi saudiya au na manta fa ki shirya gobe kema zaki biyo jirgin safe ki samay ni anan.
Kai daddy kana son a koroni tun filin jirgin Nageria ke nan a yadda nake nan na tun kare su ai sai suce ban da hankali yace.
Ki fada masu ke fa matar uncle ne ai zasu bari ki wuce kawai nace uncle abin ya koma yar haka ne kuma tsakanin kai dai kawai ka yarda kayi min wayo yace to na yarda madam ai min afuwan ko nace ayi ma Uncle.
Munyi hiran sosai dashi kwana biyu aka hau arfat nan mahajata na jirgin yawo suka fara shirin dawowa gida acikin su harda uncle.
Sallah da kwana biyar na tashi da matsanacin ciwon mara cikin dare mummy ta rude duk da tasan cewa haihuwa ne yaya saadu ta kira baizo gidan ba sai tare da likitan uncle da wata nurse.
Don haka agida Allah ya saukeni lafiya da taimakon Allah da tasu na likitoci na samu na haihu karfe biyar na asuba.
Nurse din ce ta taimaka min har wankan yaro da komai da itace tayi nan a gaban mummy bayan yan aune aunen da sukayi min sukace kada aba yaron nono wai ina da matsalan kaikayi a jikina wanda ni san suyi hakane don kawai batar da sawu.
Likitan ya kara dacewa mummy ba kowa za a bari yasan yaron bai shan nono ba don yawan surutun mutane amma zan dan iya bashi lokaci lokaci kafin yayi wayo.
Don sun diba zan iya shayarwa na dan wani lokaci yaya yace tunda akwai abinda zai sha kawai kada ma na bashi nonon ita mummy tace hakan ma yafi.
Tace ta fahinta yaya Saadu ma ya gara gargadin ta kada ta bari kowa yasan zancen mummy tace ai ko samira baza taji ba don bama zata bari aga yaron ba.
Nan ya kwashe su ya mayar gida don lokacin har gari ya haska ko an fara fitowa shaanin yau da kullun.
Mummy ne ta miko min yaron bayan sun wuce na kalli yadda ya kwaso uban shi da kama wai jinin uban shi yafi kadfin nawa a cewar ta.
Murmushi nace mummy ke nan daga inda nake zaune ba tare da na karbe shi ba nake kwararo mai addua.
Barcin gajiya ne ya dauke mu a gidan dagani har mummy din sai tara na safe su yaya saadu suka shigo da su samira gidan.
Shigowan su ne yasa muka tashi basu jima ba sai ga Aisha ta iso kowa sai yaba kyau yaron yake yi don ya gado kyau ta ko ina daga iyayyen shi.
Aisha sai cewa tayi dasu yaron yafi kama dan ya dauko fuskan yan gidan su ne ni dai sai murmushi nake masu karshe ma barci nayi na barsu nan.
Ganin na sake komawa barci mummy tace su dawo falo su bar ni in huta yaya Saadune ya shigo dauke da madaran da za a ba yaron da ruwan zamzam .
Nan dai yadan bata lokaci yana buga ma mutanen su matar oga ta haihu yau na tashi mummy tace na danje na gasa kaina a bayi.
Naje na taba ruwa na dawo dai dai lokacin da Uncle ya sake buga waya akace dashi na falka daga barcin.
Wayan yaya saadu ya miko min yace madam barkan mu da arziki ashe an sauka bayana dariya nayi nace Allah ya sauke ni uncle Allah ya rufa min asiri baka garin na haihu baki alaikum.
Yace kudai kunyi min wayau naso ace nine zanyi karban haihuwan ai naga kalar rakin ki har video zan yi maki a lokacin.
Murmushi nayi nace wanan dai ya wuce ka yayi saurin cewa saura wani uncle rufa min asiri nace dashi da sauri tare da kashe wayan


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/29/20, 11:42 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , ,

🧕🏿6️⃣7️⃣🧕🏿


Ranan duk da gajiya ban samu hutawa da amsan wayan daga yan uwa da abokan arziki ba masu bugowa su na min barka da arziki.
Sai da dare samira suka bar gidan amma yar uwarta ta zauna a wurina zata taya mummy aikin jego nima naji dadin zaman nata.
Nafito bayi don yin tsarki dare saboda zan kwata a lokacin ina tsaye ina shiryawa wayana yayi kara mummy ke fadin wa kuma yakiraki yanzu kina shirin kwanciya ?
Daukan wayan nayi amma sai gabana ya fadi mummy tana ganin yadda na firgita da ganin mai kira na din a lokacin.
Waye mummy ta tambaya cikin son ji nace mata anty lagos ne bata san ina da ciki ba nassan taji zancen haihuwan ne take kirana anty tace dauka mana sai ki fada mata kin dauka ta sani ne ai.
Kiran ya katse sai ni na kirata kira biyu gana uku ta dauka nace mata anty ina bayi ne da kika kira tace yanzu nake jin wai kin haihu sulaiman yakira yana fada min.
Nace eh anty kin kyauta tace min lalai Safiya yanzu nasan yadda kika dauke ni har kiyi ciki ban sani ba sai dai inji haihuwa kawai daga sama.
Ko shekaran jiya fa kin kira ni mun gaisa dake amma baki fada min cikin ki ya tsufa ba haka sai dai inji haihuwa kawai.
Nace anty kiyi hakkuri na bansan yadda zan fada maki bane da baki na na dauka ai ya fada makine da dadewa.
Ya fada min may shine zai fada min ko ke to bari kiji kada kiyi tsamanin kiyi min kan ki kikayiwa sai ta kashe wayan kit.
Wayan nabi da kallon mamaki a hannuwan kamar ita ke gabana sai kuma na sake wani murmushi kawai.
Don nasan inda maganan ta ya dosa alokacin bai wuce zancen kudi ba ne don ko gabanin sallah na tura mata da kudi ta account din da ta turo min.
Mummy takatse da tambayan cewa may take nufi da kinyi wa kanki ko da ban san ta ba nadai san a yanzu babu abinda zata gwada maki na rayuwan duniya.
Tana miko min tea mai kauri take fadin haka nace mummy anty tayi abinda bazan iya mantawa da ita ba rayuwana .
Ta katseni da fadin don kaiwa mutun alheri ba saboda Allah kayi sai kuma mutum ya zama bawan ka saboda Allah haka Allah yace ayi taimako duniya?
Tea din na karba na shaye sai ga zufa na karyowa a jikina na aje cup din ina shirin kwanciya yaron mummy ta miko min tana fadin taba yaron ga tunda yazo duniya baiji dumin uwar shi ba.
Karban yaron nayi na rugumay shi a jikina kamar wani babba da yasan may ake nufi da haka sai naji ya sauke ajiyan zuciya a hankali a jikina.
A hankali hawaye ke zubuwa daga idanuwa na wanda ban san ina yin su ba alokacin tausayin kan mu dana yaron ne ya kamani a lokaci guda.
Mummy tace a a yaya haka kuma daga karban yaro ki kama hawaye haka don Allah kibar irin wanan dabiar mana ta mika hannu ta karbi yaron daga hannu na.
Har lokacin ban daina kuka ba wiwi badai ce min komai ba da kukan ya isheta sai kuma ta koma lalashi na tana fadin.
Haba Safiya ke da zakiwa Allah godiya sai kuma ki gode mai da kuka kamar baki gode mai da kyautar da yayi maki ba.
Tadai samu nayi shiru tare da nadewa saman godo ni kadai nasan abinda ke damun zuciyana a lokacin wanda ita mummy ba ta sani ba.
A haka barci mai nauyi ya dauke ni sai da asuba naji motsin mummy ta tashi zuwa ban dakin ta wanda acan take kewayawa bata shiga nawa har wankan yaron acan take yi mashi.
Yau da yake ikilima yar ta na gidan sai ta dan jima bata dawo ba haka yasa na samu daman komawa batcin dake idona.
Sai wani lokaci naji tana ta dani wai in tashi inyi wanka tun rana bai yiba sosai haka na tashi na shiga na gasa jikina a ban dakin.
Na fito na shirya cikin wasu super masu launi ja da fari dinkin shi mai daukan ido don an tsara shi dakyau da fasahan teloli na zamani.
Wayan Uncle ne ya shigo a lokacin da na gama saka sutura a jikina mun gaisa yake tambayana babu matsakan komai a tare dani ko ?
Nace lafiya kalau muke Uncle sai dai kewan ka daya cika muna zuciya baka gidan gidan babu dadi yace muyi hakkuri zamu ganshi nan da sati uku mai zuwa.
Nace haba uncle har sati uku baka zo kaga kyautan da ubagiji yayi maka ba yace karki damu ina nan ina gode ma Allah ki san a gaban shi nake ma yanzu don ina dawfin bankwana ne yanzu haka ina fitowa daga cikin kaaba ne.
Allah ya tsare nayi mashi yake tambayana mummy nace tana dakin ta da baby suna karyawa ya sake tambaya idan muna da matsala in fadawa yaya saadu nace uncle bamu da matsakan komai a tare damu.
Mukayi sallama naci gaba da shirina zuciyata cike da kewar miji na da bai kusa damu a lokaxin da muke bukatan shi a tare damu din.
Goma da rabi ma,iakatan wurin su yaya saadu suka shigo min barka bisa jagorancin yaya saadu din sun kai su goma duk kan su sun sha corth a jikin su bakake.
Wanda nake gani haka yanayin shigar wurin aikin nasu yake a falo suka girshe ni zaune dasu mummy ba hijjab a jikina kafin a dauko min hajjib duk sun kare min kallon da yaba hallitana a zukatan su.
Yaron mummy ta dauko masu nan suka shiga yaba kyawon yaron wasu na fadin wai ni ya biyo wasu kuma suna fadin ogan su yaron ya biyo.
Basu dade ba suka aje muna kyatutukan da suka zo muna dashi sukayi muna sallama suka tafi yaya saadu ne yadan tsaya fada muna samira na tafe ta tsaya gyaran gida ne yanzu zai koma ya dauko ta.
Basu zo tare ba sai gata wai wani driver yasa ya dauko ta shi ya shiga kasuwa muna zaune sai hira ake faman zubawa irin na mata idan an hadu.
Sai ga matan maikatan su Uncle sun shi su da yawa muka zauna ana gaisawa wanda duk basu sanni ba sai a wanan lokacin.
Wata daga cikin su ce ke tambayan waye mai haihuwan sai samira ta nuna na turancin yan Nigeari suka fara yi suna cewa ayyah.
Very young Lady nan hira ya kaure a tsakanin su suma dai yaba kyawon jaririn suke ta faman yi zasu tafi suka aje muna kyautan da suka zo muna dashi.
Sun fice muna masu godiya naji Samira tace shegu muna fukai kawai ina ruwansu da kurciyan ki dama sun zata ke tsohuwace ko may ?
Na da sauri nace kai Samira daga abin arziki sai zagi haka kuma tace ke baki san komai ba ina wanan maidan jan gyale wai ita mijin ki take mutuwar so kamar ta mutu.
Nace wa uncle tace shifa wallahi kyale wahalaliya wai kuma a wurin dan uwan ki take kamun kafa wai ya shawo mata kan shi.
Dariya nayi nace ashe aiki ja yagan ta kuwa sai kuma ita bakar nan mai kama da zubin arnan daji itace ta lakewa yayan ki sai da na kirata ranan naci mata mutunci sosai.
Dariya ta bamu dukan mu mummy tace ashe kina da aiki wanan zamanin idan kince zaki dinga kiran yan mata a wayan miji kina zagin su.
Don haka zasu samu damar shige mai su nuna ai su na kwarai ne sai tafiya yayi nisa su fitar da halin su na boye.
Nace ni yanzu mata sun baci mummy tace bari ke dai mace fa yanzu ba abin kunya bane ta tunkari na miji da kalman son shi takeyi .
Nace ni mummy ba abinda keci mun rai da matan yanzu sai kiga mace na tafi taga mota tafe ta kasa kawar da idon ta ga mai motar.
Har ba da matan aure dabi an su ne yanzu bin namiji da kallo cikin mota ba birnin ba ba kauye ba.
Samira tace ai sai kiyi ai wanan yanzu ya zama ruwan dare a ko ina mata da sunji rurin mota basu da kwanciyan hankali sai mai motar ya wuce su.
Yaya Saadu ne ya shigo gidan yana neman Nura akace tana kitchen kiranta ikilima tayi sai gata da saurin ta ta fito yake ce mata tazo ta duba kayan kitchen abinda babu ta fadi a sawo zata koma kitchen din yace mata a a tafito suje waje suka fice tare dashi samira ta tashi ta bisu wajen.
Dariya muka kwashe mata dashi tace kuka ga abin dariya tsaron kaya yafi cigiyan shi ai nace ke dai baayi niyya ba mai zaki iya hanawa samira.
Mummy tace rabu da mahaukaciya sun dade a waje sai gasu suna shigowa da kayan abinci cikin gidan katon katon komai an sawo.
Zai fita nace haba dan uwa zauna na mana kaci abinci nasan wanan zirga zirgan da kakeyi baka tsaya kaci wani abu ba.
Mummy tace ga matar shi sai kishin hauka takeyi bata san ta tambayi lafiyan mijin ta ba.
Tace ai nasan ko nayi mai tayi bai zama yaci yana wanan zirga zigan haka mummy tace haka ake son aminin kwarai yayi maka tsaye da gidan ka idan bukatan haka ya taso bai kusa.
Abincin yaci yana ci muna hira yake fada min sunyi waya da baba yaya sani ya fada mashi kila jirgi na biyu zasu biyu don da shi suka tashi.
Mummy tace kafin su dawo ai mu mun sha bukin mu sai dai suji labari a bakin mu .
Wai yaushe shi maigidan zai dawo take tambayan yaya saadun yace basu yi waya ba don ko yabar saudiya Dubai zai tafi daga can sai dai ranan da muka gane shi.
Banji dadi ba a raina har hakan ya baiyana a fuskana yaya saadu ne yake mun sheri dan murmushi nayi kawai ban iya bashi amsa ba.
Jego ya karbe ni sai dai ina makin yadda nono na basuyi min ambaliyan ruwa ba sai na fahinci kila maganin da likita ya bani ne ya kawo hakan.
Suna saura kwana ukku muna daki da dare mu uku muna shirin kwanciya ikilima tana muna hira a dakin mu mukaji bell din gidan na kuka alaman ana sallama ke nan.
Mummy ce ta fita zuwa duba ko waye goye da yaron a bayan ta don takan goyashi kafin mu kwata don tace idan yaro yasha baya kafin ya kwanta yafi dadewa yana barci da dare.
Shiru bata dawo dakin ba yasa ikilima fita ta dubo ta sai gata ta dawo tana fadin Safiya maigidan ki ne fa ya dawo.
Gadunan dasu yaya saadu a falo ana shigo da kaya cikin gida wani iri naji gaba na ya amsa min mummy ta dawo ta sauke yaron dake bayan ta tare da kiran ikilima suka fita.
Ya shigo dakin a daidai lokacin da nake aje kofin tea saman dan drower dake gefe na dago kai nayi ina kallon shi.
Yaja yayi tsaye daga kofan dakin yana kare muna kallon cikin shaawa daga nesa tasowa nayi zuwa gare shi .
Take ya ware min hannuwan shi na shige ciki ya mayar da hanayen shi ya rungumay ni tare da matse ni cikin jikin shi.
Ajiyan zuciya kowan mu ke saukewa a lokacin babu abin da nake tunawa sai haihuwan wahalan danayi na farko babu muji babu aike shi.
Allah mai yin yadda yaso ga bayin shi na furta a raina yanzu gani gidan akwai gidan mutunci inda akasan daraja na da kimana ana tarairariyana kamar kwai.
Sake juna mukayi tare da jana zuwa wurin gadon da yaron yake kwance yana barci acikin net din jarirai .
Hannu na ya sake ya duka ya dauko yaron dake ta barcin shi hankali kwance ya rugumay shi a jikin shi.
A hankali bayan yagama mai adduan da yake mai a duka bangarorin jikin shi ya dago yana kallona inda nake zaune a bakin gado na zuba masu ido.
Sannu madam yace tare da sake min murmushi mai ma,anoni da yawa a zuciyar shi nima murmushi nayi mai kamar yadda yake min.
Yace wanan katon baby haka yaya kika iya haihuwan shi a gida nace da taimakon Allah da na nurse Lidia na haife shi uncle.
Zama yayi da yaron a hannun shi yana mai kura mai ido babu ko kiftawa nace uncle shine baka fada muna zaka dawo yau ba mu sani a shirya ma abinci.
Yace aini akoshe nake ganin ku ya kosar dani da komai yanzu ya sake dago kai yace sannu safiya ubangiji ya raya muna wanan yaron yasa mashi albarka a rayuwan shi kin min komai tunda kin haifar min baba na a yau.
Nace sunan Abba ke nan zaici yace ba dole ba Safiya ina matukar son mahaifina shima yana sona amma mutuwa ta raba mu alokacin da muke jin dadin junan mu.
Allah ya gafarta masu na furta yace amin yau ki dawo min da tsohona dana rasa wanda har yau cikin yan uwana babu wanda ya taba min kara yace zai saka sunan shi.
Nace ai gashi Allah ya baka yanzu ka huce haushin hakan yace wallahi na dade ina jiran wanan ranan a raina har da na cire tsaman sumun shi a rayuwa na.
Sai gashi a lokacin da ban taba zato ba ubangiji ya dawo min dashi a rayuwa safiya zan so yaron nan kamar yadda nima mahaifina yaso ni a rayuwan shi ki taimake ni ki tayani sin shi don Allah.
Nace har ma zan fika ni da yake babana kuma sukina ina kewar rashin shi a lokacin da muke bukatan shi a tare damu a lokacin da ya kamata ya kasance dakai yaji dadin haihuwan ka.
Mummy ne ta leko dakin tana fadin Alhaji ga abinci can an hada maka yace mummy sannu da kokari ina jin labarin kokarin da kikewa babana sosai a wurin safiya.
Murmushi mummy tayi tace masha Allah tsohon gida ne ya dawo ashe?
Ya na aje yaron yake cewa baba na ya dawo mummy ku tayani farin cikin samun wanan daman da ubangij yayi min .
Ya aje yaron yana kallona yace zan je in watsa ruwa sai da safe idan Allah ya kai mu don naga kuna shirin barci ne yanzu.
Nace barin taso in hada ma ruwan wanka don ban hada heater ba yace na hutar dake yi zaman ki sai da safe ma hadu ai mummy sun kawar da komai yadda ya dace.
Yana fita mummy ta shigo dakin tana cewa kin ga kyautar ubangiji watau sunan tsoho yaro ci ubangiji ya raya muna shi nace amin mummy.
Nace da alama akwai shakuwa mai tsanani tsakanin shi da mahaifin shi tace ai da ganin yadda yake yi akan yaron kin sani kema.
Yanzu aiki ya samay ki yadda yake ji da yaron nan sai ki taimaka ku bashi kulawa yadda ya dace in kina cire wanan filancin da kike yi yanzu sai ki cire don haka zai iya kawo matsaka a tsakanin ku.
Murmushi nayi ina gyara kwanciya na nace mummy ai naga alama nasan akwai aiki a gabana sosai haka ta kashe wutan dakin muka kwanta asuba ta gari yan uwa.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/31/20, 11:07 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , ,


🧕🏿6️⃣8️⃣🧕🏿


Washegari tunda ya shigo ya duba mu da safe ban sake ganin shi ba sai dare ya dawo gidan a lokacin na samu kebewa dashi da yaron dauke a hannu na na shiga wurin shi.
Na samu ya fito wanka yana shirin fitowa falo don cin abinci sai gani na shigo dakin nashi yana goge jiki amma idon shi yana a kan mu har na karaso bakin gado.
Inda na aje yaron saman gado na nufe shi tare da kokarin karban da dan towel dake hannun shi na fara goge mashi kan shi a hankali.
Murmushi naji ya dan sake tare da rike min hannu ya fara fadin duk da gajiyan da kike ciki zaki koma wahal da kanki ga waban kuma ?
Nace gajiya ai yabi jiki yace haba in shirya baki wani baban nawa ko hajiya baaba ke nan da sauri nace kai Uncle sai ana zaune kalau ka dauko maganan da zai firgita mutum.
To be frank ba wasa a magana na sai ki fara shiryawa nan da kwanaki funda naga baki gaji ba kin ga sai mu tara zurian mu hankali kwance ko yaya kikace hararan wasa nayi mai tare da kawar da zancen da ki sa gabana faduwa idan naji.
Nace daddy nazo ne in fada ma ma,aikatan ku sun zo sun kawo muna abin arziki da baka nan yace yana dan duba yaron Saadu ya fada min sun zo sai dai nayi mashi fada may yasa ya bari suka shigo min gida.
Nace uncle ai danka ne ya jawo su da ba a haife shi ba aibasu zo gidan ka ba yace ai sun dade suna son zuwa basu ga fuskan haka bane.
Kila ma sun gama kalle min ke ban sani ba nace ko sun kalle ni nan zasu barni tunda ba kayan su baca ni ina da kishi sosai fa yace min .
Nace ai naga alama amma ai har da budurwan ka akazo ko itace baka son ta gani don yar kauye ce ni da sauri ya kallo ni don jin abinda na fada mai.
Bayi magana ya juya zuwan wurin kayan shi ya dauko wani light brown din jallabiya yana sawa a jikin shi sai da ya gama dakan shi ya dauko yaron dake kwance saman godon shi ya gyara shi da kyau a kafadan shi yana fadin in kin gama fadin maganan ki muje inci abinci.
Tashi nayi nabi bayan su har lokacin bai kara yin magana ba sai da zai zauna cin abincin ya miko min yaro wuce wa nayi wurin su mummy nakai mata yaron.
Ban dawo wurin shi ba sai da ya neme ni na dawo na samu har ya gama cin abincin nace mai na kewa yane bayi,
Tambayana yayi may kuka shirya na maganan suna ne don nasan gobe gidan nan zai cika da baki masu zuwa suna duk da nace su huta aiyi buki acan bauchin .
Amma hajiya tace min dole sai wasu sun zo nan idan sun koma zasuyi bukin su nisawa nayi tare da fadin ni ba wasu mutane nake dasu nan din ba karfin mutanan duk baki ne da zasu zo daga bangaren mu.
Yace ok na dai sa a gyara masu gidajen da zasu sauka a ciki don nan din ba zai ishe mu ba sai abinci naso inji shirin da kukayi akai don zan bada aiki a hotel ne ai muna nace da Aisha da mummy ya kamata kayi maganan don Aishan nan bata wuce ba.
Yace may take yi har yanzu anan nace dashi aiki sukeyi a kitchen shiru yayi sai can yace yimin magana da mummy din da ita Aishan.
Zuwa nayi na kisu sai gasu sun fito daga dakin zuwa gare shi bayan su zaune yayi ma mummy yaya gida ta amsa da Alhamdullahi .
Yake tambayan ta abinda ake shiri akan suna tare da mata bayanin yadda ya tsara abin gaba dayan su sukace hakan yayi dama har Aisha na tunanen yadda zasuyi dahuwa a nan gida .
Yace da sauri a ina zakuyi wanan aiki tace wai da anan mana yaya murmushi yayi kawai tare da kada kafan shi sunci gaba da tsara yadda abin zai kasance da yar uwanshi sai mummy da take a bangare ne.
Nikan mikewa nayi na shige na barsu a wurin don na fara jin barci na damuna sai da na falko ne naga har mummy tashigo ta kashe muna wutan dakin ko na gyara kwanciya na da kyau.
Washe gari zuwa karfe ukun rana baki sun fara isowa duk na matsu inga masu zuwa daga bangare na alokacin sai hudu na yamma suka shigo garin inda yaya Saadu yaje ya taro su a hanya.
Shigowan su yayi daidai da fitowa na daga bayi don tsarkake kaina da nake yawan yi lokaci lokaci saboda in samu walwala a jikina.
Samira naji tana masu oyoyo yasa nasan sun iso ke nan don haka na fito taron su falo da shafiu kanina na fara arba da sauri yayo wuri rungumay shi nayi cikin murna da jin dadin ganin shi.
Don Allah ya hada jina da yaron sosai duk da bashi ke bin mun amma shine abokin shawara na a dakin mu mama na gani na sake shi na rungumay ta.
Abin mamaki shi har da Inna yau a gidan aure na da kannen ummi na da suka zo mutum hudu da gwago nan dai gida ya cika alokaci guda.
Zama sukayi aka fara gaisuwa tare da gabatar masu da abinci da na sha wanda har uncle ya fara odan su a gidan don bakin mu da suka zo.
Yan bauchima sun iso mota biyu suka zo dashi bus cike da mutane gidan sai ya koma min kamar ba gidan mu ba duk girman gidan inda ka duba jama, a ne tako ina.
Inna ta koma can hanya coridor din shiga part din uncle tayi zaune tana raba ido tana kallon ikon Allah tana anyanawa a ranta.
Wai yau gidan Safiya ne haka safiyan da taso agida ita da uwarta ko na sabulu wuya yake masu gaskiya nake ganin kowa na rawan kafa da ita yanzu ashe sun san abinda suka gani ne.
Tasa hannu ta shafo ties din kasan da ta zauna tana kallo wanda aka malalashi kamar ruwa da kifaye suna yawo acikin sa.
Mummy ne ta katse ta da cewa aa Rakiya nan kika zo kika zauna hanyan dakin surukin ki kuma tashi mana ki shiga dakin diyar taki tana can ciki ai.
Tace ummm, ummm aiko nan ma yayi min tace a a taso dai ki shiga wurin ta sauran jamma, an da kuka zo ai suna can tare da ita.
Janta tayi har zuwa daki inda nake tsakiyan su mamana suna min bayani kan abinda suka shirya akazo min dashi wanda ummi tabar kudi da zata tafi sai su kuma su kara tasu a wurin dawai niyar.
Nayi mamakin abunda suka zo min dashi don ba karamin kashe kudi akayi ba kamar lokacin aure wanan karon ma haka suka hado mi gara mai yawa akazo dashi.
Sai hango inna nayi can daga kofa ta rakube wuri guda tana bin dakin da kallo har tana dagen kai wurin kallon dakin nawa.
Nace a a inna karaso mana shigo daga ciki ki zauna na mike ina fadin kinci abinci kuwa na juya wurin khadija kauna ta ina cewa khadiza debo ma inna abinci don Allah tana fadin anbata abinci ai taci.
Nace jeki debo mata nama ki kawo masu ta karaso ciki ta samu wuri ta zauna nace a mika mata jaririn dake goye a bayan gwago dake zaune a kasa.
Aka kawo mata nama cike a plate ta karba tana washe baki ina kallon ta ta fakaici idon mutane ta juye a wani tsohon jakka dake rataye a kafadan ta.
Murmushi nayi don bata ganni ba mama ma tashigo nan suka zauna nace su shiga bayi suyi alwala a dakina suka fito na mike da kaina na dauko masu abin sallah.
Karshe wasu waje suka koma suka zauna saman fararen kujeron roban da aka baza a wurin sai ci ake da sha ga ma aikata wuri su Nura sai raba abinci sukewa mutane.
Fitowa nayi zuwa wurin yan bauchi muna gaisawa dasu gungu gungu tare da masu ban gajiyan tafiya.
Dare yayi yaya Saadu yashigo gidan yana fadin yan bauchi su fito akaisu masaukin da zasu sauka suka fara fito fogayen mota wurin aikin su Uncle suna waje ciki suka shiga aka tafi dasu.
Suka dawo aka kwashi yan garin mu aka tafi dasu zuwa wirin da suma akai masu masaukin su gidan ya rage daga mummy sai gwago da yayan samira da muke zaune sai Rukaiya da na hana wucewa da Khadija na.
Hira mukai tayi da rukaiya a daki tana bani labarin auren ta da Ado mai mai da yadda zaman ta da kishiyoyin ta yake yanzu a gida.
Rukaiya tace dani na shigo dakin dada sai kika ga Inna ta biyo mu nace wallahi ai nayi mamakin zuwan su duka su biyu tace.
Ita fa akace ta zauna gida da yara taki wai sai tazo yaya Sani kuma dama yaja mata kunne sosai kafin ya tafi.
Nace kai Inna ho har yanzu dai tana nan da halin tace ai dole ta rage yanzu da kika ganta nan bata dako lafiya tafiyan karfin hali ne kawai tayi inji khadija na dake gyara ma yaro jiki a hannun ta ya gama shan madara zata kai ma gwago ta goya shi.
Washe gari kafin wani lokaci aka fara shaanin buki baki da yan gari sun fara cika gida don haka kowa ya koma busy cikin mu maigidan tunda ya shigo da safe yace zai tafi unguwa bai dawo gidan ba.
Kowa yasan sunan yaro Abdulrahaman nan yan bauchi suka fara kiran Abbamu ya dawo yaro yaci sunan tsoho ke nan.
Anci ansha an raba kyaututuka masu ma,ana dake dauke da photo jariri da sunan shi a jikin kyauntan sai ga wasu mata sun shigo wai mata yan kasuwa ne suka zu taya mu murna har da yan wurin aikin su uncle wasu sun turo matan su wasu kuma ma,aikatan su mata ne masu aure suka zo.
Alhamdullahi har dare babu wanin hayaniyar da akayi sai faman ci da sha mata keyi koma anyi ba mai yawa bane abinda ba a rasawa ne kawai na taron mata.
Na shiga na fita walima mukayi inda wata malama da tazo daga bauchi tayi mu nasiha akan "ya"ya da hankin uwa akan dan ta.
Nashiga na fita daga suturun da Uncle ya waddatani dasu don fitan buki wanda daga Dubai wanda duk wanda nasa sai an kalle ni daga ni har yaron.
Ban da abin cewa sai hamdala ga ubangiji subbahanahu wata,ala da ya wadatani daga cikin ni,imomin shi nake rayuwa kamar banda wani tabo na tashin hankali a jikina.
Har kishiyar Aisha da abokan aikin ta sunzo mata karan suna da makwabtan Samira da suke zamar arziki dasu suma sunzo mata kara.
Sadiya kaunan su yaya saadu yasa tazo daga lagos don halartan sunan kawai naji mamakin ganin ta kwarai da gaske don yaya bai fada min cewa zata zo ba sai ganin ta nayi kawai da safe da suka shigo.
Mun rage daga mu sai bakin mu suma da dare aka maidasu masauki don a gajiye kowa yake yana son hutu.
Khadija ne dakin da samira suna nade min kayan da nayi amfani dashi da rana ni kuma ina zaune bakin gado rike da wayana a hannu.
Ina kokarin neman layin anty mu gaisa Uncle ne ya shigo dakin suka shiga gaida shi da gajiya dago kai nayi ina kallon shi yana wasa da khadija na.
Yace ke budurwan kauye kin boye kawai abinki a kauye baki ko tuna mutane ta turo baki gaba tana cewa ai mu yanzu garin mu ba a kiran shi kauye don mun waye.
Yace amma dai zaki dan zauna kwana biyu nan ko don ki kara wayewa dakyau dariya tayi nayi saurin cewa a a kan tace nima bance zan zauna ba ai.
Nace dama shafiu ne da ko wata nawa zaiyi ban damuwa amma wanan wataran zaka dawo ka samu tamin dan karen duka a gidan nan.
Tace kai anty Safiya ai dane muna kanana ko tun da muka girma ai muka bar fada dariya su samira suka kwashe dashi.
Yace au ashe da gaske da kina dukan min mata tace wallahi yaya sherin anty Safiya ne itace dai mai dukan mu din.
Nace ke khadija ni yaushe nake dukan ku ina kafa kafa kada inna ta cuta maku a lokacin tace ai kin yi kokari wallahi.
Nan Samira ke fadin munafuka sai gata tazo tana simi simi da ita Uncle yace tazo ne ita ma khadija tayi saurin fadin tazo gulma bata da ko lafiya.
Shirin fita dakin sukayi su sai ya dakatar dasu da fadi No ku zauna abinku ni fita zanyi nazo duba madam dina ne.
Samira tace gako madam nan ta sauke gajiya yaron ya tambaya khadija tayi saurin fadi yana gurin gwago ai kun samu maigadi yau gwago bata bari kowa ya dauke shi ba yau ita da mummy.
Yace amma sun kyauta min ina can ina tunanen wanan taron dana gani za ai ta jagulamin yaro da kuma na tuna mummy na nan sai ban damu sosai ba.
Khadija tace oho ita anty nawa fa dariya kawai yayi ya fita dakin har ya kai kofa ya juyo yace khadija ba fa dake za a koma ba kinji na fada maki.
Samira ce tace bayan ya fita daga dakin ashe uncle yana magana haka mai tsawo nace yan maganan dai ke kusa yau.
Washegari baki basu shigo da wuri ba don gajiyan da suka tara sun fita zuwa kasuwa masu shiga gari ma sun shiga ziyaran yan uwa sai iyayyena da suka ce gidan yaya Saadu zasu tafi suga gida.
Dare anan sukaci abincin dare aka kwashe su zuwa masauki sai washe gari zasuyi asubancin komawa gida.
Zaune muke daki suna ta faman saka kaya a leda wanda yaya Saadu ya shigo dashi gidan da za a bawa baki sallama matsayin kyautar bukin su.
Na kalli Rukaiya nace yanzu haka kike zaune a gidan baki sanaan komai Rukaiya ga yaro ta dago kai tace to yaya zanyi Safiya.
Ni dai zaman yafi min zama gida wurin inna don yanzu sai ta ganin zatai fitinan ta ranan da ya samu ya kawa muci randa bai samu ba muyi hakkuri hakana.
Nace yanzun dai zan baki wasu dan kudi sai ki dinga juyawa shima zan baki kikai mai amma don Allah ki bashi don zaman magidanci ba sana,a ba dadi wallahi.
Don ina tuna lokacin da muke kanana baba baida wani sana,a irin wahalan da iyayyen mu mata suka dinga yi a gida.
Tace bari kedai lokacin ai ba a magana amma yanzu ga baba nan kamar ba ayi ba ya gyagije ya zama kamar yaro dashi.
Nace wanan leda ta saka mai turmi uku takai wa kishiyoyin ta komai ta saka ma nan na shiga lissafa masu duk muka cire ma wa yanda suka zo sai mahaifiyar Amina don Amina nada tsohon ciki bata samu zuwa ba.
Kudi na mike na dauko na bata nace ta cire dubu hamsim taba mijin nata dubu hamsim Khadija ne ta katse ni da fadin itafa ba a cire mata leda ba.
Nace ba kinji uncle yace ba tare dake zasu koma ba nasan kuma da gaske yake yi tunda kikaji ya fada.
Tace ita dai a cire mata nace zabi wanda kike so ba shike nan ba Rukaiya na ta min godiya nace tadai samu sana,a da zatayi dasu nasan zasu isheki ai.
Washe gari ko wani mota ya basu na shan ruwa hanya kusanna lokaci daya suka tashi sai gidan ya koma saura mu kadai a ciki.
Sai yan wirin aikin su Nura dake ta faman gyaran gida don tsabatace wuri uncle badai tsabta ba kan don bai son kazanta ko kada shi.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/2/20, 11:42 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , ,

🧕🏿6️⃣9️⃣🧕🏿


Ban fasa ja maki Allah ya isa ke ko kai mai fitar min da novel waje ubangiji yayi min bakar isa akan ko waye don gangancin yayi yawa baki da tsoron Allah ko baka da tsoron Allah na roki Allah yabi min hakkina akan wanda ya fitar da wanda ya karanta bai biya ba cikin gagawa.
Allah nasan kana amsa min rokona don akan hakkina na nake magana bana wani ba ubangiji na kara kai kuka na gare ka kahana ma mai shi farin cikin da yake nema don shiga hakkina da yake yi.
Ranan da bakin mu suka tafi munyi barcin gajiya sosai a gidan sai yamma kowan mu ya ya tashi naji dadin barin khadija da akayi min don zata debe min kewa sosai a gidan.
Yaya Saadu na samu ya tsaya min akan ta tsaya din don su mama sun kafe sai da ita zasu koma don baba zaiyi fada idan ya dawo.
Sai yaya yace ace shiya ce ta tsaya din haka yasa sukai shiru suka kyale ta badon sun so ba tun dai inna da tasan zaman na ta na iya zama wani alheri a gare mu.
Samira bata shigo ba sai bayan kwana biyu da suna tazo gidan nan muka baje muna duba kyaututukan da muka samu ga bukin.
Itace da dago tana fadin yanzu ai zaki fara shiga mutane musanman matan yan wurin aikin mijin ki da sukazo maki kara kin san dole suma idan ya samay su kije masu.
Nace nasan zamu kwasa da uncle ta wanan fanin don ba ko wani zai bari naje ba tace ana dai son mutum da zumunci ba ko yaushe ki zauna sai dai azo maki ba.
Muna cikin hiran ta jefo min tambaya tace anty ki dai bata zo ba bata turo maki sako ba ko nace antyn nan nawa fushi take yi dani har yanzu samira.
Ai dole tayi fushi dake tunda baki bar masu miji sun aura ba nace ba haka na bane akwai dai kila abinda nayi mata wanda ni ban sani ba.
Samira tayi saurin cewa ga abinda kikai mata nan kuwa Allah ya kyauta nace da ita tare da fadin ni ban son komai ya fito daga wuri na don irin halarcin da tayi min a rayuwa na ba zan iya matawa da ita ba.
Ikon Allah yanzu kayan da khadija na take sakawa sai naga sun zama min na yan kyau wanda a da ni bani ko saka irin su don ban ma samay su ba.
Haka yasa na bude wardrove dina na fitar mata da duk kayan da nasan ban amfani dasu yanzu don samun ci gaban rayuwa da na samu a tare dani .
Wanda Allah yayi min gatan da ban taba zaton zan samay shi a rayuwa na sai gashi cikin hukucin Allah ya wadatani da abinda ko a mafalki ban taba mafalkin haka ba agare ni.
Yau da nayi wanka na tunkari dakin Uncle dauke da Abbati a hannu na wanda yasha kayan sanyin da mummy ta saka mai cikin kayan da muka da uncle a kasan Spain.
Kayan sun matukar karban jikin yaron don ko wa yaga kayan zai yaba da kyawon su a jikin yaron ya hade da kyau halittan da Allah yayiwa yaron.
Sallama nayi tun daga kofan dakin uana ciki kwance ya amsa min na shigo tare da kura mai ido ina mamakin ganin shi kwance har wanan lokacin.
Sai da na samu wuri na zauna na fara gaida shi da kwana ya karba min cikin dan dagowa yana kokarin mikewa zaune nace Uncle yau ba aiki ne , ?
Murmushi yayi yana kai hannun shi ga yaron haka yasa na mika mai yaron dake hannu din gaba daya ya karbe shi ya rungumay a jikin shi tare da fadin.
Bawan Allah ka yafe muna Abbana ba laifin mu bane hana maka abincin ka da mukayi son lafiyan ka ne ya kawo haka gare ka.
Wani irin abu ne naji ya ziyarci zuciyana lokaci guda tausayi da damuwa nace tamu kaddaran ratuwan ke ne ubangiji ya bamu ikon ciye jerabawan mu.
Amin ya fada cikin lumshe idanuwan shi yana sauke ziciya yace duk abinda nake yi tunanen yaron nan yana cikin raina wallahi.
Uncle sai hakkuri ai tunda ma yana shan madara da sauki sosai wallahi yace yana sha sosai ko nace yana sha cikin sanyin murya.
Yace ai mu godewa Allah da ya nufe mu da rike zurian mu da hannun mu sai muyi fatan Allah ya raya munashi nace amin Uncle.
Dakata yace dani nayi saurin dago kai ina kallon shi yace ni wanan Uncle da ake kiramin ya isheni fa yanzu Allah ya bani da kamar kowa don haka akirani da sunan baban dana.
Dariya ya bani nace ai su yan biyu suka sakani kiran ka uncle da sauri yace dama ina son in tambaye ki wai ko madam ta kiraki tunda kika haihu ?
Nace eh ranan da na haihu ta kirani da yamma tana fada dani wai ban fada mata cewa ina da ciki ba sai haihuwa kawai taji a wurin daddy.
Bata ji ba fatace maki nace abinda ta fada min ke nam yace tun muna Spain na kira su na she da mata zancen cikin ki.
Wai may matar nan take nufi ne haka shiru nayi mashi ya sake cewa ko bayan maganan mu akwai abinda ya farune a tsakanin ku na kada kai tare da fadin wallahi ni matsalan komai bai taba shiga tsakani na da ita ba.
Doka tasa min in dinga tura mata kudi zata san abinda zatayi min dashi nan gaba kuma ina tura mata da kudin duk karshen wata idan kaba salary dina.
May ne ?
Ya tambaya cikin dan zaburowa daga inda yake kishingide da yaron saman kirjin shi yana dan shafan bayan yaron a hankali.
Nace a hankali ina tura mata kudin kamar yadda ta bukata yace Safiya ashe baki da wayo haka ban sani ba ?
Yanzu ko shafiu ku ko khadija suna iya yin wanan wautan da kikayi to bari kiji ni ina baki kudin nan ne don ki tare lalurar ki wanda ba sai kin fada min ba.
Na dauka gida kike tura masu suna amfani dashi ashe ke baki san ciwon kan ki ba ban sani ba to bari kiji.
Inda maimuna ko ba da ita tunda Allah ya kadara aure a tsakanin mu har da rabo ita bata isa ta hana ba ko ta sa ayi wanan abu ne nufin Allah.
Allah dai ya nufa ta dalilin ta zamu hadu idan kuma yaso zai iya hada mu ta wani dalilin bata gurin ta ba.
Daga yau na yanke duk wani hurdan dake tsakanin ki da ita har ma da kowa nata idan kina yi don ban son rainin hankali.
May ta mayar dani ne wai taga ta biyo ta hanyana bataci galaba na ba shine yanzu ta dawo gare ki .
Zan kira mijin ta yayi mata iyaka dake tun wuri ta shiga hankalin ta dani kafin rayuka su baci kada tace ko ban san abinda takeyi bane a baya na sani sarai albarkacin mijin ta da yaranta take ci gare ni.
Mun kwasa da ita akanki sosai amma ke baki sani ba don ba dole bane sai kin san yadda mukayi a kanki da ita shine ta biyo ta baya wurin ki tana min yankan baya ko ?
Ta nuna min cewa ke ba komai bane na nuna mata cewa ke wani abune mai muhinmanci a gare ni yadda take daukan ki kin wuce nan a gare ne.
Don so tayi shawaran komai dole sai da ita zanyi ban isa in ma dan uwana wani abuba ko ke ba ta hanyan ta ba.
Ranan ta jini sosai don rufe ido nayi naci mata mutunci ta yadda bata zata zan iya masu ba.
Na nuna mata kina da mahinmanci a gare ni fiye da kowa nawa a yanzu da taga hakan ta bai cin ma ruwa ba sai ta juyo tanan din dake.
To zanyi maganin ta tasan nafi karfin ta da mijin ta taci albarkacin shi wallahi da yau nasa ta dawo maki da kudin da duk ta karba daga gare ki.
Zan kara maki kashedi a kanta kada naji kada na gani na yanke duk wani alaka da ke tsakanin ki da ita daga yau din nan kinji na fada maki ko ?
A sanyaye na amsa mashi da eh ya koma ya kwanta tare da lumshe idanuwan shi ya fita batuna ranshi na bace da maganan da mukayi akan anty din.
Na dade zaune na kasa ko motsawa daga inda nake shi kuma ya fita batuna sai can na yunkura na mike na fita dakin na barshi da yaron .
Daki na koma na samu khadija kwance tana kallon tv dake aiki tana kallon wani series na yan Chaina kin dawo tace min na amsa mata rai babu dadi da eh kawai na bata amsa dashi.
Samun wuri nayi na kwanta ba tare da nakara magana ba nasan itama ta fahinci akwai matsala ne sai ta kyale ni taci gaba da kallon ta.
A idan nake har barci ya dauke ni ban sani ba ina cikin barci ne naji yana kokarin ta dani daga barcin yana dan jijigan yaron dake dan kuka a hannun shi.
Mikewa nayi zaune ina kokarin amsan yaron a hannun shi yace abashi abinci ina ganin yunwa yake ji ya fada.
Madara khadija ce ta mike da sauri ta hada ma yaron madara ta karbe shi a hannu na ta fara bashi ya karba da sauri yake jan feeder.
Uban ya dan dade tsaye yana kallin yadda yaron ke jan feeder da sauri murmushi yayi ya nufi kofan dakin yana cewa Khadija ashe kin iya reno ne haka ?
Dariya tayi kawai bata samu bashi amsa ba hankalinta na ga yaron da take ba abinci saida ya fita dakin na samun bakin magana.
Nace dama bai sha ba da akai mai wanka yayi barci shine na kai shi wurin baban shi su gaisa nasan ya tashi ya damay shi da kuka ne ya kawo shi.
Hira muka dan fara yi da ita kadan kadan har na dan sake na fitar da damuwa da nake ciki tana mi labarin yadda zaman gidan mu yake yanzu.
Nace yanzu da baki koma ba wazai dubi su wasila dake gida tace ai gwago ta fada ma su mama Jummai su koma wuri su da zama kafin ummi ta dawo.
Amma kuma nasan ko basu koma can din ba ai mama zata kula dasu a gidan don mama na kokari sosai wallahi duk da gorin da inna take mata akan abinda take yi din.
Yunwan da na fara ji yasa muka fito falo in ci abinci khadija na goye da yaron a bayan ta lokacin su gwago suka fito daga dakin da suke suka samay mu a falon.
Mummy ne ke fadin ai na dauka kuna barci ne danaji shiru nace barcin baiyi nisa ba muka tashi sallaman akayi kofan shigowa muka amsa.
Aisha ne tare da wata makwabciyar ta suka shigo gidan nan aka shiga gaisuwa ta kalle ni tace wai madam wanan irin kiba da kike narkawa fa ?
Dariya ne nace ina kiba anan duk na zube yanzu ma haka wallahi banjin dadin jiki na karfin halin kawai nake yi wallahi.
Mummy ne tace akasarin mata idan sun haihu dama sai sunyi zazzabi wanda ake kira dahuwan kassa don wahalan haihuwa da sukayi .
Kin san mace a wurin haihuwa duk sassanta jiki ta sai ya motsa to wanan motsawan shike haifarwa mata da irin wanan zazzabi daga baya.
Kayan da na ware zan bata cikin wanda muka samu daga yan uwa da abikan arxiki nabawa samira nata na Aishan ne dama ya rage shi nace khadija ta dauko mata a daki.
Basu dade suka tafi tun tafiyan su na kwanta zazzabi wasa wasa sai da ya kwantar dani dole washegari sai da muka tafi asibiti wuri likitan shi.
Magani ya rubuta min da allura akai min yayi muna bayani cewa dole dama sai nayi ciwo saboda jinin da na zubar a wurin haihuwa saukin abin ma don ina samun kulawa yadda ya dace ne.
Sai dai in matsa da cin abubuwan da zasu kara min jini a jiki don kada na jirkita da yawa kamar yadda masu irin lalurar ke shan wahala yayin da suka haihu don jinin da ya rage a jikin su.
Duk da allurai da maganin da aka bamu sai da na wahala sosai don ba karamin jin jiki nayi ba har na ramay sosai.
Wanan raman da nayi shiya daga hankalin Uncle sosai har ya koma wurin likita yace mai babu komai zan samu lafiya haka abin yake wani lokaci.
Ai nawa matsalan yana da dama don kafin ciwon ya bugeni sosai an daukar mai matakin daya dace gashi kuma ina kula da shan magani.
Na dan fara jin saukin jikina wanda ya koma nake jin shi kamar ba jikina ba ya shigo dakin yana min sannu cikin nuna kulawan shi a gare .
Zaune nake lokacin da ya shigo dakin yake tambaya na ko ina jin wani abu yanzu a jikin nawa ?
Nadan lumshe idona a hankali na nace mashi banjin komai uncle sai dai jikin nawa ne ban jin karfin shi ko kadan.
Kina ko shan maganin kin akai akai nace ina sha na yaune ban sha ba don ban karya ba tukun yace may kike jira baki ci abinci ba har tara da rabi na safe yanzu.
Nace bakomai a hankali bakin nawa ne dai banjin dadin shi dan sunkuyowa yayi gare ni yana fadin may kike son kici sai a dafa maki.
Kunu da kosai nace mai sai naga ya daga yana murmushi yace khadija taje ta fada ma mummy asa Nura tayi min .
Tana fita yace bari ya dauko min fruits in sha kafin a gama kada yunwa yai min yawa a ciki nace uncle banjin cin komai wallahi bakin nawa ba dadi nake jin shi.
Ido ya dan tsura min sai yake kai zaune bakin gadon cikin kwantar da murya yace dani ki daure ki ci diyan icce zasu taimaka maki wurin gyaran dandanon bakin ki kai na gyada mai alaman to.
Ya mike ya fita yasa aka wanke fruits shida kanshi ya shigo min dasu dakin ina zaune a yadda ya barni lemo mai bawa ya fara bani don zai wanke min bakin nawa yace.
A haka dai har na dan ji sauki saboda kulan da nake samu ta ko wani bangare har naji sauki na murmure kamar bani ba.
Ranan ina zaune kwatsan sai ga Faiza gidana tazo nayi mamakin ganin ta kwari da gaske tace wai anan abuja ta kwana ta fito lagos zata gida bauchi ne.
Nan da nan nasa a cika mata gaban ta da abinci da abin sha muna hira tana cin abincin dake gaban ta labari take bani na anty yadda take zagina wai yanzu na guje ta don ina ganin na samu gidan miji.
Ai tasan asiri nayiwa Uncle ya aure iyayyena makwadaita ne sun ga kudi idon su ya rufe wai idan ummi na ta kira ta tana ganin kiran sai taki dauka.
Dariya nayi nace anty ke nan yanzu kuma nice na koma abin zagi a wurin ta tace tun yaushe ai na fada maki halinta tun farko shiya kike ganin ina fada maki .
Yanzu haka Fati tabar wirin ta uwarta ta dauke ta ta mayar da ita can yobe garin su don yawan matsalan da suke samu akan fati din.
Ranan dai a nan ta kwana sai dai ban yarda na fadi komai ba akan anty din don yanzu mutum abin tsoro ne washe gari ta wuce bayan na cika ta da abin arziki .
Kwana biyu sai ga yaya saadu yazo yana ce min zai tafi lagos an bugo mai waya jikin gwago da na Ahmed wai ya tsanan ta don haka zai tafi ya dubo ta.
Kudi na dauko nace ya kaiwa gwago ya gayar min da ita idan yaje yaso yaki karba amma na matsa mai sai da ya karba don sako ne na bashi.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/3/20, 8:54 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , , ,


🧕🏿7️⃣0️⃣🧕


Tu wuce wanan yaya saadu ban tuna da zancen gwago ba sai da yake da kwana biyu da tafiya ya bugo min waya ya hada mu da gwago wai mu gaisa da ita.
Ba yadda na iya shiru ya dan biyu bayan wayan can na ce salamu alaikum ta amsa da fadin Safiya nace naam gwago kuna lafiya yaya jikin naki.
Ta cikin wani murya mai rauni ta amsa da jiki da sauki safiya yaya wajen ku kuna lafiya ko nace lafiya muke gwago tace naga sakon ki wurin dan uwan ki na gode Safiya.
Nace babu komai gwago Allah dai ya baki lafiya tace amin sai ta kama kuka tana son yin magana amma kuka ya rinjayi maganan da take son yi din.
Nikan sai na kashe waya don kada ta kashe min jijiya bayan na kashe ne yaya Saadu ya kirani ya ce kinji gwagon ki ko ga Ahmed yana gaida ke jikin nashi ne ba dadi sosai nace ka gaida shi Allah ya bashi lafiya.
Ya san ban amsan wayan shi ke nan yasa ya kyale ni bai hada ni dashi din ba ya tambaye ni yaya Abbati nace yana wurin gwago ta goya shi.
Bayan mun gama wayan khadija dake zaune gefe na da mummy suka ce wai amma kina da karfin hali wallahi.
Mummy tace ai gara da tayi masu haka na ta barsu da aniyar su ko yanzu Allah ya gwada masu abin su ai.
Ni dai murmushi nayi kawai ban ce komai ba sai dogon tunanen da nashiga tun lokacin kuma na watsar da zancen su a zuciya na gaba daya.
Haka rayuwa ke ci gaba ga duk mai rai da lafiya cikin hukuncin ubangiji har gashi nayi arbain da haihuwa yaro kuma yana cikin koshin lafiyan shi.
Yayi mulmul dashi bazaka ce bai shan nono ba idan ka ganshi don iri kulawan da yake samu na abinci da magunguna da zai bashi lafiya da kuzari.
Tun da nayi arbain nake ta shirin zuwa gida kunsan maza da jan fitina amma sai uncle yace ba zan tafi ba sai munje bauchi mun kai ma baaba yaron ta gan shi.
Naso tayar da hankali mummy da gwago suka sani gaba sukace ko murai kada na nuna mashi komai yadda yake so in bishi da hakana muje mukai ma mahaifiyar shi jikanta ta gani.
Haka yasa na daure ban nuna mashi komai ba da yake tsanmanin zan ce ban yarda ba da hakan daya tsara muna don yasan yadda nake dokin zuwa gida .
Wanda tun aure na dashi banje garin mu ba ina binshi a yadda yake sona dashi din don kawai a zauna lafiya.
Dole akalan tafiyan yacan za ta zuwa bauchi din mummy da gwago zamu barsu gida sai mun dawo da khadija kawai zamu tafi.
Mun shirya tsaba inda ranan jumma, a zamu bi jirgin safe mu tafi kamar yadda ya tsara don har da buki zamuyi na diyan wani kawon shi haka yasa na dauki kaya na alfarma don tafiya dasu.
Inda motacin shi na shiga biyu sun kama hanya da tsaraban mu da kayan mu zasu samay mu acan kamar yadda ya tsara din.
Mun sauka lafiya inda su Nafiu suka zo daukan mu zuwa gida da motaci biyu mun isa mun samu yan uwan shi mata suna gidan kaf din su sun zo tariyan mu har da Aisha da ta tafi sati daya daya wuce bukin kannen mijin ta.
Mun sauka inda suka fito waje taron mu yaron yana hannun khadija har muka isa gidan nan suka karbe shi kowa na nuna kulawan shi akan yaron sai fadi suke Abban mu Abban mu.
Suka nufi cikin gida da yaron su kuma suka tsaya muna gaisawa tun a waje part din hajiya baaba muka nufa gaba dayan mu don mika gaisuwa a gare ta.
Koda muka shiga mun samu ta karbin yaron tana fadin Allahu akbar yau jinin babana a hannu na haka ina kallo da raina da lafiya na.
Muka shigo da sallaman mu muna gaida ita ta juyo gare mu cikin farin ciki tana muna sannu da zuwa tare da fadin ai yanzu kin zama uwar mijina kuma wanan irin mijin da kika haifo min haka?
Murmushi nayi ina kai gwiwana kasa dukka guda biyu tare da fara gaida ita cikin girmamawa .
Amsawa take yi yayin da hankalin ta ke yaron tana fadin wanan duk gida ya kwaso wallahi ana fada ban yarda ba sai yanzu dana gani da ido na.
Uncle ya ce hajiya mun samay ku lafiya tace sannu kai dai dan Albarka ai duk na rude da ganin wanan mijin nawa da Allah ya nuna min zuwan shi da raina da lafiya na.
Sai da ta jagula yaron anty Suwaiba ta karbe shi sannan ta dawo da hankalinta gare mu sai lokacin taga khadija da muke tare tace a a da bakuwa kuke ashe ?
Da ganin wanan yar uwar Safiya ce don kama ya nuna kanshi basai antambaya ba wanan kamar uncle ne ce kaunar ta dake wurin ta ne ai tunda ta haihu suka zo suna take nan tare da mu.
Gaisawa sukayi da khadijan tare da tambayanta yaya hanya ta amsa cikin ladabi da lafiya lau hajiya.
Juyawa tayi tana fadin ku kawo masu abinci mana kun tsaya kuna shiriri ta haka suka ce hajiya baki ce a dauko masu bane ai.
Yau ga tsiya tace dasu abincin ma sai nace ku kawo masu zaku dauko masu uncle ne yace hajiya bar abincin nan yanzu a dai kai muna can part din mu zamu fi jin dadin ci acan.
Nan aka shiga kwasan abincin zuwa part din mu dashi shi kuma suka ci gaba da gaisawa da mahaifiyar tashi.
Nan na juya wurin Aisha nace mutanen bauchi ke nan ina yaran suke tace suna can gida na barsu banzo dasu ba yau.
Hiran mu muke yayin da hajiya da dan ta suna can zaune a inda muka barsu suna magana a tsakanin su.
Karshe ma sai su Aishan suka jamu zuwa cikin uwar daka nan muka shige daki guda daga cikin dakunan part din nan dai muka fara hira tana cewa ai ta godewa Allah da muka iso yau gobe ne bukin gidan su sai muje mata karan buki da sauran yan uwa.
Kiran da hajiya tayi ma suwaiba sai gata ta dawo tana fadin wai mu fito zuwa part din mu uncle yana son ya huta haka muka fito muka nufi can har lokacin yaron na wurin hajiya tana bashi madaran da khadija ta hada mashi.
Mun shiga part din komai neat kamar muna cikin shi ko yaushe yasha gyara sai kyali yake yi nan na aje handa ban dina Aisha ta biyo mu da dan troley din da muka riko.
Abincin da aka aje muna muka fara zama ci inda masa ne wanda yasha mai sai kyali yake fari tas a cikin kula sai miyar kassan rago da akayi da ganye alaihu sai kamshi ke tashi ga ferfesun kaji dayaji kayan kamshi yana tashi shima a kulan shi.
Nan dai muka taru muka fara cin abincin sai santi kowan mu keyi kan dadin masan dake gaban mu uncle ne kawai bai magana sai murmushi yake muna kawai.
Mun ci munyi kat ko dinban ferfesuf din bamuyi ba ni da uncle sai khadija ne ta dan sha kadan ta ture don ta koshi da masan da taci .
Yaron ne aka shigo dashi yana kyallara ihu kamar wanda wani abu ya sama karban shi nayi ina fadin yanzu haka fitsari yayi yake damun shi haka yake yi idan ya bata pemppers din jikin shi.
Tube shi nayi gaba daya na cire mai tufafin dake jikin shi don in sauya mashi wani na shan iska nagama shirya shi na kara mai madaran tare da bashi grive water yasha sai gyatsa na bawa khadija shi ta goya.
Kwantawa nayi don in huta don tafiyan safe da mukayi barci ne taf a idona lokacin shima uncle ya kwanta bai fita hanin kowa ba a lokacin don yace yana son dan hutawa ne .
Koda na farka khadija na kwance sunyi barci da Abba a jikin ta haka yasa na dan mike a hankali kada na tayar dasu daga barcin dakin .
Na samay shi yana barci ga sanyin AC ya karade dakin zuwa nayi wurin shi na dan taba mai huska a hankali sai ya bude ido nace lokacin zuwa masallaci yayi kada ka makara.
Salati yadan yi tare da juyawa yana fadin badon kin shigo ba da na makara don naji dadin barcin nan sosai wuce wa nayi bathroom na hada mai ruwan wanka na dawo ina fada mashi ruwa ya hadu.
Ok kawai yace na juya zan fita daga dakin yace ai na dauka za a bani goron jumma a ne kuma sai zaki fita .
Na juyo da dariya na nace kai uncle har a garin mutane ba a bakun ta na fice ina dariya don nasan in nayi sake bai da wasa wirin wanan harkan.
Wanka nayi nima na sauya kaya a lokacin sai gashi ya shigo cikin wani farin yadi mai laushi da taushi yana daukan ido da hular shi a hannu yana gyara karata da kyau.
Wayan shi ne tayi kara ya dauka su musa driver ne suka iso suke sanar dashi zuwan su tare da tambayan ina za a nufa da kayan.
Yace su shigo dashi part din shi nan ya juya zuwa wurin su yana fadin daga can zai wuce masallaci ne nayi mai a dawo lafiya.
Lokacin khadija ta falka bayan fitan shi ne tace sai yanzu masu motar suka iso garin kai amma akwai nisa ashe haka ?
Kodon da jirgin mukazo mu sai naga kamar ba nisa wallahi nace kema kin san ai da nisa mana zaki hada tafiyan mota da jirgine.
Shigo da kayan yasa na fito falon ina gwadaasu inda zasu zube muna kayan don ba karamin tsara muka lafto masu ba wanda zamu raba har uncle na fada wai kayan sunyi yawa haka.
Sallah na dawo na tayar don lokaci ya gabato ina son inyi nafila kafin jumma a din sai da na idar na juya wurin khadija dake kwance har lokacin nace hajiya sallah fa.
Ta nuna min yaron dake saman hannun ta kwance wai kada ta tashi yaron ya motsa na watsa mata harara nace yanzu don kada ya tashi ne bazaki je kiyi sallah ba.
Tana mikewa yaton na wani irin zabura ya fara dan shure shuren kafa yana dan kuka sama sama nace ashe aiki ya ganku kuda kuka koya mashi hakan ?
Nikan ba wanda zai hanani barci yanzu kuka yake sosai dole nabar adduan da nakeyi na kamashi ina lalashin shi.
Dan shiru yayi dole na goya shi a karo na farko tunda na haife kasan cewa su mummy da gwago ke faman dawainiya dashi a gida.
Ni iyaka na dashi in dan dauke shi inyayi koka kuma in mikawa mummy shi su karata can amma kasancewa yau basu kusa dole reno ya dawo kaina.
Khadija na fitowa bayi wanda nake ganin wanka ta tsaya yi ta kalle mu ta tuntsure da dariya tace ai na fada maki bai yarda wallahi ya saba da dumin mutum a jikin shi.
Idan bayaji mutum a tare dashi ba bai yarda yayi barci nace ai duk ku kuka shagwabashi dake dasu mummy yanzu gashi yazo nan yana wahalda mutane.
Sallah ta tayar muryan Aisha naji tana fadin ina matar gidan nan take ni zan tafi nawa masauki yanzi yaya gobe din in sa rain zuwan ku ne cika muna taron buki.
Allah ya kaimu nace da ita har zaki tafi ke nan gashi ko da ina son zaki tayani fitar da tsaraba wa mutane.
Sai naga ta kalle ni ta tuntsire da dariya tace yau Allah ya kamaki mummy bata kusa ai dole baban mu ya samu baya ya hau.
Dan tsaki naja nace ai uwar shi ta idar da sallah ta karbe shi su da suka saba mashi da jiki nace muje falo ki ga kayan da muka zo dashi din don yanzu su musa suka iso dasu suna can sun tafi masallaci da uncle.
Falon muka fito ta kalli kayan tare da fadin dan kari duk wanan uban tsaraba haka safiya nace to kin san mun dade bamu zo ba ai.
Nan muka fara aikin in duka yaron yace baison dukawa sai ga khadija ta fito daga daki tana zuwa ta karbe shi saman cheast din ta ta dora shi tana lalashin shi.
Nan naji dadin aikin da muke inda muka kwashe sauran zuwa wani daki tace ko da daga baya zaki tuna wani ba a bashi ba kin ga sai a diba anan.
Sai bayan mun gama ne ta wuce har waje muka fito rakiyan ta da motar ta tazo don haka a ciki muka saka mata nata tsaraban nan muka tsaya take fada min kishiyar ta lami tazo tana nan sun hada kai da uwar gidan ta suna kulla mata muna funchi.
Nace rabu dasu Allah ya fiso duk abinda zasuyi basuyi kamar Allah ba ai tace wallahi da da yaya baya kulamu an samu abin fada yanzu kuma da yake muna ance ina muka fito
Mun dauki lokaci muna magana tsaye a waje nace taje ta kama yaranta dake gida tace wallahi nasan suna can yamzu wuri wuri suna nema na mukayi sallama badon mun gama gulman mu ba ta wuce tana jaddamin batun zuwa na gidan su gobe.
Ciki muka koma muka kwaso ma hajiya tsaraban ta zuwa part din ta su kuma su anty suwaiba duk wanda zai tafi na bashi nashi tsaraban.
Sai dare su uncle suka dawo gidan lokacin muna falon hajiya baaba muna hira don gidan an watse sai mu da tsirarun mutane wa yanda ke gidan wurin ta muka rage a gidan.
Yashi alokacin ya cire babban rigar dake jikin shi ya rage daga shi sai yar ciki a jikin shi tafiyan shi kawai ya isa ka gane a gajiye yake a lokacin.
Sannu da zuwa mukayi mashi ya isa gaban mahaifiyar shi yana gaida ita inda ya juyo gare ni yana fadin .
Madam yaya bakunta nayi dan murmushi nace ai mun sauke shi yanzu mun zama yan gari ko dariya yayi yace yana zama na gaji wallahi.
Hajiya ta tambaye shi ina ya shiga haka shiru shiru yace yarima ya jani muka dinga zuwa ziyara tsufin abokan mu har yamma yayi muna haka.
Tace ai hakan na dakyau ba karamin lada kuka samu ba wallahi ai ziyara nada kyau mutane ne basu gane ba.
Ban iya magana ba don hajiya na wurin ina jin kunyanta don haka ma sai na kawar da kaina gare su muna hira da su khadija mikewa nayi.
Abinci na mike na dauko mai tare da aje mai komi da zai bukata a wurin shegewa mukayi can wurin yaran hajiya don mu basu wuri su tatauna da mahaifiyar shi.
Muna shiga tace mashi babana harda wani uban tsaraba haka mai yawa kuka zo wa mutane dashi bayan kullun dawainiyar ka bai karewa gare mu.
Yace hajiya ban ko san ta hada tsaraban nan ba sai gani nayi ana sakawa a mota tace yanzu duk itace da wanan dawainiyar haka , ?
Shiyasa ake son samun mace tagari wacce zata dinga kare wa mutum mutuncin shi dana yan uwan shi wanan yarinyar gata dai karama amma kuma tana da wayau wallahi tasan darajan mutane sosai.
Sai bayan goma na dare muka fito zuwa shiyan mu bayan mun yi shirin kwanciya ne nake fada mai zancen zuwa gidan su Aisha buki da muke son yi gobe.
Yace mantawa nayi Aisha na garin nan dana dage tafiyan mu sai wani lokaci don nasan yawo zata jaki ku dinga yi a nan niko kin san ban bukatan hakan ko.
Shiru nayi don idan na tanka zai samu hanyan da zai hana fitan gobe wanda ba zaimin dadi ba har Aishan bayan nayi mata alkawari.
Jin nayi shiru ne ya kyale baici gaba da maganan ba sai ji nayi ya jawo ni zuwa jikin shi nace a raina nan kafi auki dama.
Yana fafin kima ganin khadija zata iya kwana da yaron nan kuwa nace ita tace ai a barshi tunda ba nono yake sha ba.
Yace tana da kokari wallahi shine hikimar da nayi ai wirin cewa a barta don nasan zata temaka maki ta hanyoyi da dama.
Washe gari tun tashin mu gyaran part din mu mukayi muka fita zuwa gaida hajiya din mun dan jima wurin ta har da karyawa mukayi kafin mu dawo mu fara shirin zuwa gidan Aisha wurin buki inda yan uwa zasu taro sai mu dunguma mu tafi gaba dayan mu gidan bukin da abinda za a kai mata don da autar dakin su maigida cikin bukin.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/5/20, 11:23 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , ,

🧕🏿7️⃣1️⃣🧕


Uncle ya shigo dakin da muke wanda shine kamar mallakina a gidan shi na bauchi sai faman shiri baby khadija keyi acikin wani riga da wandon maza duk da kayan yara maza ba a faye samun wani sauyi a cikin su ba iya ka dai wando da rigace kawai kayan adon su.
Amma shi wanan din da uncle ya sawo yazo muna dashi yana da matukar kyau sosai don gaskiya ya hadu sosai.
Ina zaune gafenta ina waya da ummin mu da suka dawo bamu samu ganin su ba tana bani labarin taba inna tsaraba ta dawo mata dashi wai bata so saboda anyi rikici da ita anka yara tsakanin su.
Nace yanzu ummi ya kamata ace kin fahinci waye inna ita kullun gari ya waye tana neman wanda zata sauke masifan ta ne akan shi.
Ban karasa maganan ba iya abinda yajike nan shigowan shi sai na kara da fadin ta kyale ta kawai ta aje kayan indan ta sako daga fushin ai zata dawo ta karba ne.
Maganan da yakewa khadija dakewa yaro shiri tana fashi wasa yace zaki koya mai kiuya yazo bai san kowa ba sai ku ko?
Katse wayan nayi da ummin nace uncle fita zakayi ne yace eh daga can yana son ya samu halartan daurin auren gidan su miji Aisha din da zaayi.
Nake cewa zamu tafi dasu anty suwaiba idan sun zo yace yaji kawai nasan fitar ya zama mai dole ne kawai ya barni kudi ya fida yana miko min wraper din yan diri biyar biyar har biyu tare da fadin a watse lafiya.
Godiya nayi mai ya miko ma khadija dake zaune itama sai dai ban diba a lokacin balle in san ko nawa ne ya bata.
Yadan dauki Abba yana mai wasa tare da fadin kayan nan sun matukar karban ka babana nace anbinda khadija take fadi ke nan.
Ya aje yaron ya fara tafiya ya juyo yana ce min sai kuyi amfani da dayan motar don ni zan fita da dayan ne.
Makuli ya miko min tare da tambaya ko ya bar muna driver ne nace ai zan iya ja kada ya zauna a takure a cikin mata.
Murmushi yayi yasa kai ya fita mukai mashi adawo lafiya yace amin fitan shi khadija tahau murnan kudin da ta samu awurin shi ta shiga kirgawa cikin murna.
Nice na kawar mata da murnan da jefo mata maganan su ummi dake ci min rai tace ba dai ummi ta karbi kayan ba nace eh ra karba tunda har daki ta kai mata.
Tace ai shike nan mana inna fa sune basu san halinta ba har yanzu gurin ta shine kada ta ga wani yafi ko ta wullakanta mutum kan abinda bai kai ya kawo ba.
Muna cikin maganan su anty suwaiba ta shigo nan muka shiga gaida ita take fadi bamu shirya ba don mu samu waliman da za a yi .
Aisha tace ta bugo min waya ban dauka ba sai na tuna wayan na guda yana dakin uncle na barshi acan tunda safe ban dauko ba .
Nace ai wayan yana dakin uncle na barshi yana caji a can tace tana tambaya ko anbarki zuwa gidan nasu nace mata mun rabudake jiya akan zaku zo din ai.
Nace tasan halin dan uwanta shiyasa take ganin kamar ba zamu zo din ba tace ita fa so take muje mu cika mata daki lami tasan tana da yan uwa da yawa.
Aiko zata ga gaiyya yau don kowa zai tafi yar dariya nayi kawai nace ana dai zuba kishi a gidan su Aisha kan.
Tace ai yanzu haka ne ako ina kedai sai idan baka da kishiyace ka huta da wanan kwamacalan rayuwan.
Ba birni ba ba kauye ba duk abin daya ne wallahi nace lokacin muke da kishin fili akeyi bana boye ba irin na iyayyen mu da ya wuce.
Fita tayi da Abba a hannun ta tana jadda muna muyi mu shirya don Allah idan sauran sun iso sai su samay mu a can.
Nace yanzu anty gamunan fitowa wani buje da riga na saka dan dubai wanda tsayawa fadin shi bata lokaci ne sai gyalen su mai kyau ga taushi da sanshi yana lefewa ajikin mutum.
Takalma da jakka da suka dace da kayan jikina takalman mai tsones da hill sai daukan ido yake yi don kyau da har handbag din shi sai sarka da awarwaro dana zuba a jikina masu tsadan gaske.
Turare na shafe jikina da gyale na dashi itama khadija shigan ta na yan matan zamani ta yi don shigan yayi mata kyau sosai a jikinta.
Mun rufe part din na kai wa baaba makulin koda uncle zai shigo bamu nan khadija na rataye da dan jakkan da muka zuba kayan Abba a cikin sa maikyau dashi.
Muna shigowa kallo ya koma kan mu a falon na baaba inda yan uwa duk sun hadu bamu jima ba muka fito don tafiya don mutum uku ne basu iso ba a lokacin.
Hajiya baaba tace mutafi zasu samay mu acan haka yasa muka mike tafiya gidan su Aisha din gaba dayan mu dake falon.
Mun fito alokacin sauran sun iso aka tsaya don motacin su anty suwaiba dake wurin zamu tafi dasu a zaton su da tasu zamuyi amfani dukkan mu.
Nan nace da suwa zamu tafi a motar mu motar suka kalla gaba dayan su suna fadin au da taku motar zaku tafi ashe nace eh kawai.
Yan matan suka ce a tamu zasu tafi don haka na bude na shiga suma suka biyo mu a jera mota hudu muka nufi unguwar su Aisha din inda a tsohon uguwar su gidan yake.
Suke gaba muna bin su a baya har muka kai gidan dake can unguwan su tsoho wurin a cike yake da jamma, a maza da mata saman kujeru roba kungiya kungiya.
Duk sai kallo ya dawo gare mu a wurin wuri muka samu muka tsaya inda ba mutane da yawa mun fito muka kulle motocin mu.
A lokaci daya muke shiga gidan wanda da alama gidan yawa ne mai part aciki lungu lungu har muka isa wani wanda yafi yawa anan dakunan su Aisha din yake.
Kafin mu iso labari ya iso mata na mun iso duk mutanen sai kokarin kallon mu suke suna aiki Aishan ne ta ratso mutane tana muna sannu da zuwa inda bata bari mun shiga daki ba sai da takai mu wurin uwar mijin su a gidan.
Nan muka shiga dakin dattijuwar ta tare mu ba yabo ba fallasa a fuskan ta tare da tambayan hajiya baaba muke tana gaida su.
Har mun juya zamu tafi take cewa ance har da matar Sulaimana a ciki ko itace wanan yar farar ko tana nuna ni cikin su.
Aisha ne ta bata amsa da eh tace ai naga alama mukan muka fita zuwa dakin ta anan muka ga lami a kofar su suna hada zobo na buki.
Tunda ta dago ta kalle mu tayi muna sannu da zuwa ta dukar da kai kasa tare da ci gaba da abinda takeyi bata sake dogo kai ba har muka shishiga dakin Aisha din.
Wanda a falo muka zube mutanen dake cikin dakin kafin mu shigo suka firfito daga dakin a kujaran dake fuskantar waje na zauna don haka ina iya hango wanda ke waje suna gittaiya a inda nake zaune din.
Aisha tazo muna gaisawa da ita tama rasa da wanda zata gaisa a cikin mu a lokacin don mu goma sha biyar muka zo gida cika taron buki.
Nan ta juyo kaina tare da dafani tace madam kin kuru da kika zo da wanan mijin naki mai rowan matar shi wa mutane sai nayi masa yajin wata uku gidan shi ban leka ba.
Dariya nayi ina kamota nace aida kin ga nazo bikon ki har wata uku bakizo inda muke ba da zama bai ganin ba.
Tashi tayi tana dariya ta fita daga dakin mu kuma akaci gaba da hira irin na mata idan an hadu wanda gulman Lami aka dauko da uwargidan Aisha din.
Ido na zuba masu ina sauraren kalamin kowacen su a lokacin don har yanzu ba sabawa nayi dasu sosai ba shigowan Aishan daki anty suwaiba ke ce mata ashe lami tazo ne ?
Tace gashi ko jiya ina fadi cewa ta shigo tun shekaran jiya da kawayen ta suna nan sai feleke suke muna a gidan.
Ido na kurawa Lami din a inda nake zaune don ina iya hango su daga zaunen da nake din kafin wani lokaci ancika muna gaban mu da abinci kala kala na nau,in bukin da sukayi.
Nan aka baje ana ta faman ci ana raha kamar yadda mata suka saba idan aje buki sai anty suwaiba ne ta farga bani cin komai a wurin take tambayana.
Murmushi nayi ina fadin a koshe nake sai dai idan anjima din kila zanci maryam ta ce kin san fa su ba abinci suke ci mai yawa ba yan kaidan cin abinci ne kada suyi kiba.
Dariya nayi kawai tare da cewa kai anty maryam zolaya ne kuma haka Lami ne ta shigo dakin tana gaida mu sai raba ido take a kan mu tana raba ido da alama wani gulma sukayi a wajen tazo gani don hankalina na gare su da suke maganan a waje.
Nan dai ta juya tafita tabar dakin don ta gama ganin abinda tazo gani din a cikin mu naga ta koma tana magana da sauran abokan hiran nata.
Munkai awa daya da rabi aka fito don yin walima bamu fito da wuri ba don har an fara waliman munka fito wuri ta tanadar muna daga can baya inda matan da muka samu a wurin idanuwan su ya dawo a kan mu kamar ba walima akeyi ba.
Mun zauna muna sauraren walima hankali na wurin matar dake muna waazi akan aure inda wasu matan ke gulma suna dan leken mu lokaci lokaci.
Zuwan mu wurin ya hana Lami da kawayen ta shakat a lokacin don ji take kamar ta bada umurni a kore mu a gidan bukin don duk wani ahurin da ta shirya ma bukin don taso ta gwada ma kishiyoyin nata ta zarta su ne.
Amma sai taga cewa Aisha yanzu ta mata zara a ko wani fage duk da bata aiki itace mai aiki da uwar gidan su .
Bata san cewa uncle yanzu yanawa yan uwanshi ihisani ba duk wata da dan abinda ya ware ake basu suna samun na kashewa.
An tashi walima lafiya an raba snack's da drinks a wurin da aka mika min da sauri yaran da mukazo tare dasu suka karba daga hannun mai rabawan.
Ciki muka koma inda wanan karon ban zauna a falo ba kuryan Aisha na shige nida maryam muka baje saman godon ta daya sha gyara nan wasu suka shigo sai firan yadawo kuryan dakin.
Muna ciki ne mijin ya shigo gaida mu har kurya inda nake yana fadin hajiya safiya ashe kun samu shigowa yana ta min godiya don ya dauka bukin ya kawo mu muma.
Yana fita yake tambayan abba nace yana nan falo wurin yan mata nan ya fice maryam tace dan iska mai ladanin shegu ai dole yazo gaida ke ya samu gurin tatsa yanzu yadda yake so.
Dariya nayi mata nace kaji min mata tatsar may yake yi kuma tace da ba gori suke hadewa suyiwa Aishan ba yanzu daya ga akwai ci shine babu kunya yake wani ashe kunzo ne ?
Aisha da ta shigo taji tana zagan mata miji tace wa ake zagi tace mijin ki mana da baida kunya nake zagi.
Tace wanan shigowan dayayi gaida ku yanzu sau yaja fitina a gidan nan gun matan shi da mahaifiyar shi in ba ai hankali ba.
Nace gaisawan kawai kuma muna gidan akai sallah mun yi sallah a dakin ta sai bayan mun idar aka shigo muna da abinci .
Jeloup yaji hadi sai tuwo da miyar taushe nace aban tuwon shi zan ci sai gashi an zubo min da yawa a plate nace wai anty kubara ina zan kai wanan abincin haka maryam tace abarshi muci tare.
Mun zaune akace mu fito wurin wanke amare nan kowa ta gyara muka fita dakin Abba ke ta kuka wanda nasan zafi ne ke damun shi.
Muna dakin sai da mukayi mashi wanka khadija ta saka mai wasu kaya muka fito inda ake wasan a fitar da amare a tsakiyan fili ana ta zuba masu kudi suna rawa a hankali.
Anty suwaiba tace muje muyi wa amaren liki take muna kwantancen kaunan su Ado din mijin Aisha din muka saka Aisha gaba muna binta a baya haka muka ratso tsakiyar filin nan kallo ya dawo gare mu .
Mun zuba mata kudi sosai inda yan matan bukin ta ke kwashewa suna zubawa a wani jakka.
Nan wuri ya dauki sowa da fitowan mu sai gulma mata keyi ni dai na fito na zauna a ida muka tashi don a tsawale nake gurin.
Abba khadija ta miko min tana fadin tana zuwa na karbi yaron da duk wahala ya jirkitar dashi a lokacin maryam ta dawo tana zama nake ce mata mu koma ciki in kwantar da yaron ta suri jakkan ta muka shiga ciki.
Mun dan jima zaune sai fa su anty suwaiba sun shigo na dan make murya nace anty gida tace yanzu nima maganan da nakeyi ke nan nasan baaba tana can tana fadan rashin dawowan mu akan lokaci.
Haka yasa muka mike don haramar komawa gida inda sai da aka nemo muna yan mata muna doso gida naga motan uncle a waje alaman yana gida ke nan.
A falon gidan da ban daka ana amfani dashi ba naga takalman maza wurin zube ba iyaka haka yasa nasan da mutane yake lokacin.
Muna shiga ina gaida baaba tambayan mukulin mu nayi ta miko min tana fadin mijin ki yazo yana fada wai may kuka tsaya yi tun da safe gidan mutane nace dama nasan sai yayi fada don mun dade.
Nan na fita zuwa part din mu na barsu nan muna shiga na shiga cire tufafin dake jikina don wanka nake son yi sai dai ban shiga ba na tsaya tube Abba da har yanzu fita yake yi fanka na dan sake mai da ac sai yayi shiru ina fitowa na kashe fanka na bar mai ac din.
Zaune nake kafin magariba yayi nasa wani dogon riga na shan iska a jikina sai gashi ya turo kofan khadija na kwance da Abba saman kirjin ta tana dan buga bayan shi a hankali.
Kallo daya nayi mai na hango fitina a kwayan idon shi gaishe shi muke da kyat ya amsa ma khadija yace sai yanzu kuka dawo ?
Zan yi magana ya tare nan ya haufada har yagaji ya fita sai bayan ya fitane khadija ke fadin ashe haka yake da fada ?
Nace kadan ma kika gani don ya ganki ne baiyi fada sosai ba kuma bai son abashi hakkuri shiyasa kikaji na kyale shi ai.
Mun idar da sallah muna zaune muna hiran bukin ne maryam ta shigo muna da ledojin bukin a hannun ta na juya gun khadija ina tambayan zataci ne tace a koshe take gaskiya nace maryam kije dashi ku kara ko kin barshi nan ba ci za muyi ba.
Tana fita sai gashi an shigo muna da abinci na karba na aje saman dining table din dake part din nace mun gode kafin ya shigo na gyara wurin ya shigo har yanzu fadan nan a fuskan shi.
Don haka ban wani zure mashi ba don sanin hali da nayi raban dai haka muka kwanta yana hasale dani a ranshi washe gari na fahinci Abba baijin dadin jikin shi ne don da dare koka yayi tayi sai da khadija ta tadani na bashi magani ya sha nakoma dashi dakin uncle muka kwata dashi can.
Ranan kan nasha fada sai da nakai ga yin magana nace uncle a cikin taro mukaje fa kana ganin zan dawo na barsu can ne ni kadai na dawo gida ?
Ya dauki yaron yafita dashi sun dauki lokaci basu dawo ba sai can gashi da magani a leda yace a bashi yasha idan ya falka daga barci.
Tunda naje gaida baaba da safe ban koma part din ba ina cikin barci naji muryan ta a wurin mu tazo duba jikin Abban tace uban shi yana ta fada wai kun kwaso mai zazzabi a gidan buki.
Murmushi nayi nace haka yace min har yana fadin wai zamu koma abuja idan banyi hankali ba.
Murmushi tayi tace kyale shi kinji haka dai ya fada nace mai ya taba ganin yaron da aka haifa bayi ciwo ba ai da shima baijin dadi hakan don ranan da zai yi ba za ayi mai kyau ba.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/6/20, 10:18 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , ,


🧕🏿7️⃣2️⃣🧕


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU KU, , ,


Duk da bakunta muka zo amma bai hana uncle sheri ni ba a gaban kowa akan bukin gidan yar uwar shi da muka tafi har khadija ta fahinci bamu cikin dadin rai dashi.
Sai dai yazo ya duba dan shi yadan yiwa khadija magana ya fice dakin batare da ya kalli inda nake ba a rana ta uku yashigo duba Abba da ke kwance saman gado yana ta wasa irin na yara.
Nikuma ina wa khadija kalaba a kan ta ya shigo ina kwana khadija tayi mai ya tambaye kin tashi lafiya ta amsa mai da lafiya kalau.
Yadan yiwa yaron wasa ya juya ya fita ajiyan zuciya na sauke bayan fitan shi daga dakin har tana iya jiyo ni lokacin.
Muryanta ne ya katse ni ga dan tunanen da na fara a lokacin tana cewa wai anty mijin ki fushi yake dashi haka ne ?
Tun dan maganan fitan nan yakewa fushi haka naga ko abincin da ake aje mai baya ci haka yake fita ya bar shi anan nace a gun hajiya yake zuwa yaci ai.
Ashe haka yake da fushi anty ?
Na sake sauke numfashi nace matsalar shi ke nan wallahi khadija ni abin na damu na ko an bashi hakkuri kamar zugashi mutum ke yi.
Tap ai irin su ko wuyar zama gare su may acikin wanan dan maganan don Allah da zai rike haka kuma fa bukin yar uwar shi ai muka je.
Nace wallahi haka yake khadija sai kiga magana bai kai abin fushi ba amma sai ya saka a ranshi har ka gaji da fushin.
To kema ba sai ki koya ba idan ya hau ki hau sai ai tayi nace ban taba gwada hakan ba ina dai iya kokarina naga ya sauko daga fushin nasa ne.
Aiko ki na da aiki to wallahi bari kiji abinci ma yanzu idan an kawo mayarwa zance ayi mun koshi kuma ba zamu sake fita ko falon hajiya ba indan yayi magana in baki iya bashi amsa ni zan nashi ne.
Yaya zai kawo mu garin mutane kuma yasan din shi muka zo zai kama wullakanta ki haka a gaban kowa.
Itama mahaifiyar tashi bazatayi mai magana ba wanan abu yaki ci yaki cinyewa kamar cin kwan mahaukaciya.
Barshi haka muka saba da kan shi zai sauko ai tace wallahi sai mun gwada maza fa sai da harbi yanzu idan yana takama dashi ne aikema kina takama da kimar ki ta mata don Allah ki kwantar wa kanki yanci .
Idan ya hau kifishi hawa aga wa zai wahala ko dakin shi kada ko koma zuwa idan nashi ya nemoki ba.
Ni wai auren Ahmed ya mai dake haka ko may ko dama haka kike han sani ba don wayau na baikai in gane bane.
Nifa yanzu ko a kidan mu na koyi abubuwan zaman aure da dama wallahi zan iya zama cikin mata uku in tashi tsaf dasu.
Dariya ta bani har nakai mata dan gwara a kai tare da fadin na raba ki mata uku wasane kin kuwa san kishin yanzu khadija.
Tace tsab kuwa wallahi na miji idan baka wana shi sai ka koma shata, lalaganshi a gaban kowa yana iya muzanta ka ji fa jiya gaban su anty suwaiba ya disga ki.
Nace ai shi bahagon mutum ne ga dadin zama ga wuyan zama dadin shi kawai idan yana cikin dadin rai da kai idan kuma ya hau abin ba dadi duk nakan tsawala ne wallahi.
Kowa ya mashi darasi aike ma mutunce kamar kowa kina da inda kike da ranan ki bawai kudine zai ba mutum abinda yake so ba ko yaushe.
Ni ba don kudin shi na aure shi ba don rifin asirin kaina da samun inda zan fake ne tace sai kuma akace bazaka san darahan na tare da kai ba nace kai khadija ummi ke nan .
Tace ban son abin haushi ne wallahi shi daga ma kin rufa mai asiri ya tsufa ko kwai baka aje ba ka samu mata yarinya ke idan lafiyan ki kalau yadda kike nan ba sai kin darje kin samu miji ba na zaba.
Ji yadda kika koma kamar wata matar gwauna can dake kin yi wani kiba kinyi jajir duk inda kika shiga abin kallo ne ga mutane baki da inda za a raina ki in ba wurin ilimi ba.
Dangwara na kara kai mata nace badai ina da na zuwa lahira ba ashe ko ina da ilimi don may yafi kana da karatun ka na Allah dadi.
Nifa abin da yasa kika ga ban wani damuwa da karatun ba khadija na ga dai har guda nawa duniyan take a yanzu dai ban rasa komai ba nasan kuma idan karatun zan yi shi zaita hada mu fada kishin shi.
Don haka ne kawai na rungumi aure na na zauna dakina tunda ban rasa ci da sha ba da sutura tace ai shine na gani tunda a lokacin kowa gani yake mutuwa zaki yi amma yanzu gashi har ana mantawa ma da akwai wani matsala a tare daku.
Shi wanan ma bai ishe shi ba har sai yayi wani fushi kana cikin irin hali haka na ubangiji.
Sai naji maganan ta na shiga dama mun je gaida baaba da safe tun lokacin bamu kar fita daga part din ba akwai drink's da su kayan tea a wurin mu da dabun nama shi muka yini ci don ko da aka kawo abincin rana sai nace a mayar abawa mutane mun gode a koshe muke mu.
Ga na dare ma haka nace a maida kar ya baci mun koshi ina gama sallah ishai muka rufe dakin mu anan dakina wirin khadija na kwanta.
Ya dawo sai mahaifiyar tashi ke fadin yau ko matar ka lafiya suke daga ita har kaunar ta dake zuwa wurin yaran nan hira ba wanda ya leko mu tun safe.
Abinci ma ankai masu suka ce a dawo dashi sun koshi ban san may sukaci ba ka bincika min su don Allah.
Koda ya shigo part din mukan har munyi nisa da barci a lokacin a zaton shi ina dakin shi kwace don wutan ko ina a kunne yake.
Ya kashe wutan ya ya shige yana waigen kofan dakin mu don yasan yanzu khadija tayi barci ko ba daman ganin yaron shi.
Yana shiga dakin duhu ya ziyarci idon shi da kyat ya nemi makunnin wuta ya kuna haske ya gauraye dakin lokaci guda yakai duban shi saman gado don a cike ya shigo ya sauke min fada rashin kashe wutan falo da ban yi ba na kwanta abin namu kuma ya karu.
Har ya na shirin shi yana yi yana kallon kofan daki har ya gama ya kwanta ban shigo dakin ba har ya kwanta yana faman juye juye saman gado don bai saba kwana shi kadai ba sai tare dani.
Yau kuma ya rasa dalilin kaurace mai gaba daya danayi ga hajiya tace tun safe bamu ci abincin gidan da masu aikinta ke girkawa ba a gidan gaba daya.
Nikan ina dakina mun baje a gado sai sharar barcin mu mukeyi duk da hankalina kafin inyi barci yana gun shi.
Da safe ma da muka tashi ban shiga wurin shi ba har ya shirya zai fita komay ya gani sai gashi dakin namu.
Kwace nake kishingide sai Abba dake wasa kusa da cheast dina saman gado yana gwalanniya iri ta yara yana faman har ba kafafuwan shi sama dayan yatsan shi na rike a hannun na .
Khadija na gefe saman gadon tana kallo a wayan ta jin sallaman shi yasa ta dan dago tana kallon shi tare da fadin yaya ina kwana ta mayar da kanta ga kallo kafin ma ya amsa.
Ina kwana nima nace mai daga inda nake kwance rigingine ban tashi ba kamar ba zai amsa min ba sai naji ya amsa a wani irin yanayi.
Ban kawar da idona gare shi ba yadan yiwa Abba din wasa sai ya juya kamar zai wuce sai kuma ya juyo yana cewa dani jimana.
Sai ya fara tafiya zuwa falo anan na samay shi tsaye kamar mai nazari nace gani fuska a daure babu fara a gare ni.
Ba a kawo abin karyawa bane daga wurin hajiya nace an kawo yace ina yake nace an koma dashi don babu maici idan an aje a nan din.
Kamar yaya ba maici ku baku ci ne nace akoshe muke mu wani kallo ya watso min naji tsoron kallin amma na dake na bar tsoron a raina.
Kina nufin baku iyacin abincin gidan nan ne komay ?
Akan may bamu iya ci agidan mu akwai irin sane kawai de banjin cin komai ne ai idan zaci ba bakuwar hajiya nake ba sai naje can in diba kai kuma naga ba a nan kake ci ba shiyasa.
Hannu ya daga min alaman dakatar dani yana fadin ya isa haka ban tambaye ki dogon shirhi ba na fahince ki yanzu.
Akan may fa ?
Na tambaya cikin dakewa kamar zaiyi magana sai kuma ya sakai ya fita daga dakin na juya na koma daki na nima.
Ya isa wirin hajiya ta ga yana cika yana batsewa kamar zai fashe tace dashi ina son ka da hakkuri kada ka dauko yar mutane uwar duniya kazo nan kana cuta mata akan dan abu kadan.
Hajiya kyale wanan yarinyar rainin wayo take son kawo min idan ma ta kawo ma raini ba mijin ta kake ba ?
Ka tsaya ku fahinci juna da ita yanzu haka ba wani matsala bane amma kai ka dauke shi babba haka kada fa ka koya ma wanan yariyar halin da ba nata ba.
Don ba zai maka dadi gaba ba gashi kun fara tara zuria da ita kowa na murnan haka ni banga wani matsalan da take dashi ba.
Bai iya magana ba sai faman tura abincin da yake yi a bakin shi murya ta daga ta kira yarinya guda tazo tace jeki part din su kikira min matar shi yanzu.
Yarinyar ta fita zuwa part din taci gaba da mashi nasiha a kusan tare muka shigo falon na hajiya da yar aiken.
Ina saye da hijjabin sallah na ajikina na shigo da sallama na sai da na kara gaida ita na samu wuri na zauna a kasa gefen kujera.
Dan shiru ya biyo a falon sai faman shan ferfesu take ba tare da ya daga idon shi ba balle ma yasan na shigo falon a lokacin.
Safiya ta kira sunana da sauri nadan dago kaina dake kasa na kalle ta tare da fadin naam hajiya.
Tace may ke faruwa ne tsakanin ku da mijin ki kunzo min lafiya yanzu kuma sai na fahinci akwai abinda ke wakana a tsakanin ku dukkan ku ku biyu don ba haka kuka zo min ba nan.
Shiru nayi ban dago kaina ba sai da ta kara maimaita maganan ta tace kada ki boye min idan wani abu ke faruwa ni uwa ce ga dukkan ku.
Kai na kara saddawa kasa nayi shiru sai tayi murmushi tace bai fada min kinyi mai wani abuba sai dai na fahinci kwana biyun nan da yana zuwa nan cin abinci.
Kuma ke idan an aika maku sai kice a dawo min dashi ko an barshi acan babu mai ci yaya zaku zo min bakunta gidana kuma ku tsiru min wani hali na daban ?
Haba safiya ki fada min idan wani abu ke faruwa na sani tun baku koma haka a dunkule ba kin ga sai in zama uwar banza gare ku.
Sai lokacin na dan dago kaina nace ba haka na bane hajiya ba komai wallahi ta katse ni da fadin akwai komay idan babu may kuke ci keda yar uwar ki data rako ki kuma ?
Hajiya nima ban san may nayi mai ba tun ranan da muka je gun bukin gidan su Aisha yake wanan fushin dani kuma ya daina zama yaci abincin a can ko nayi mai magana baya amsa min sai dai yayi ta fushi.
Wanda ni ban san dalilin yin hakan da yake min ba na bashi hakuri da fada mai tare da yan uwa muka tafi ba zan dawo na barsu can ba tunda tare muka tafi dasu.
Tana cewa kwarai kuwa shi kuma yana fadin karya kike yi ai kin san bana son yawo amma kika tafi kika zauna sai da kika kwaso ma yaron nan zazzabi da ya wahala.
Sokike ki, , , , , ,
Ya isa haka baba ya isa nace maka ko yace hajiya could you belief wai har tana iya fushi akan na dauki mataki akan abinda tayi min.
Kai baba karage wanan zuciyar naka ina ce ka daina jin ku shiru danayi ashe kai har yanzu halin naka nan maka ?
Bukin yar uwakar fa taje tare da yan uwan ka kuma ashe kai wanan ba abin farin ciki bane gare ka yau ga iyalin ka cikin yan uwan ka anayi dasu.
Ciwo koma da yaro yayi ai canjin ruwa ne yara dawa haka na faruwa dasu idan anje sabon wuri da basu saba da yanayin shi ba.
Kaiwa yarinyar nan adalci mana haba yanzu cikin wanan magana may ye na zafi haka a cikin shi don Allah kai ka hau ita ta hau kaga abin bai yi kyau gani ba wallahi.
Shi fa mutum mai hakkuri ba a son a kure shi idan yake an kure shi abin bai kyau yanzu gashi kace wai tana fushi da kai ?
Ta gaji ne da baka hakkuri ta kyale ka hakana tunda kai ba a iyaka ina da labarin zaman ku sarai a kunne na yarinyar tsoron ka take ji kada ka kaita makura ta koma ma kamar sauran mataku na bariki.
Ke kuma ba a gajiya da hakkuri tun dai ga miji zaman takewan aure da hakkuri ake cin riban shi ba zaki biye mai ba har ku kai ga sabon Allah don haka na kashe wanan magana.
Tashi ki koma dakin ki wanan magana kuma ya mutu a nan kada in kara jin irin shi don Allah na dago tare da fadin baaba na gode.
Na mike na fita tace ku samu abinda kukaci ke da yar uwar ki kada ku zauna da yun wa haka ba a bakun ta da yunwa ko ai fushi da abinci.
Ina sa takalmina a kofa naji tana fashi fada sosai irin na da mahaifi ni dai na wuce part din don ko fada ta yi mai kan shi da yanzu sai yiwa wasu fadan haka kuma ahi din yake yin haka a gidan shi.
Ko da na koma Khadija tana nan tana kallon ta a waya shigowa na yasa ta dago kan ta tana fadin may akayi anty ?
Nace kila kara na yakai gun baaba ban sani ba ta dai yi muna magana ne akan abinda ke faruwa tace ai yanzu kiga ya gyara nace kila ba.
Wai kina ma da hakkuri nace in ban yi hakkuri ba khadija may kike son inyi a nan ai hakkuri ya zama min dole tunda haka halin sa yake cikin ma wai ya rage ke nan fa.
Falo muka dawo muna kallo har anty suwaiba tazo a gurguje ta leko mu tana fadin sauri takeyi ta kawo ma hajiyan su sako ne.
Na dan rakata zuwa part din baaba din na dawo ban dade da zama ba sai gashi ya dawo gidan sannu da zuwa muka mai cikin rashin sakewa tare da mu.
Kallon khadija yayi yace khadija har dake ake fushin da ni ko ?
Tace a a yaya wane ni shiga tsakanin miji da mata ai kun fi kusa ni ba ruwana da maganan ku yana zama yace ban yarda dake ba.
Idan ita bataci abinci ba ke may ke hana ki cin abinci tace kasan ni ba damuwa nayi da cin abinci ba dama.
Yace ban sani ba don ban je gidan ki ba koda yake naga alaman kamar yan bauchi zasu sake samun karuwa don naji ance kin yi saurayi a nan ko.
Maganan da yake yi ne yasa nasan ya sauko daga fushin da ba dalili da yake yi din na mike na barsu nan suna ba,a da ita dining naje na hada mai abincin ranan da aka kawo muna part din mu.
Ga abinci can uncle na fada yace cikin sakin fuska kamar ba shi ba barin dan shiga in fito kafin in zauna ci.
Ya juya ya shige tana jin karan rufe kofan shi ta juyo tana kallo na tace aina fada maki irin su sai da saiti wallahi nace ai naga alama.
Ya dan jima ya fito daga dakin ya sauya kayan jikin shi don zafin da ake a gare direct dining ya nufa don haka na tashi naje don zuba mai abincin har lokacin ba wani walwala a fuska.
Har na zuba mai na juya zan wuce yace yaya haka ku kunci abuncin ne halan ?
Nace mun ci tun dazu yace ta ki zauna na gama kin san ban son a bani abinci a wuce dole na dawo na zauna ina dakilan wayana can naji yace ki shirya da dare zamu tafi gidan su babffa mu gaida su.
Allah ya kai mu na bashi amsa har ya gama ina kokari kawar da kayan ne naji yace naso zuwa Abuja gobe in dawo jibi amma sai abin da hali yayi goben.
Allah ya kaimu na bashi amsa tare da cewa wani abune zaka je naga saura yan kwanaki mu koma can din ai.
Zan tafi duba wasu kayane da suka iso Saadu ya bugo min waya wai kayan basu cika ba kuma ba irin wanda mukayi oda aka kawo muna ba.
Goben dai zaka tafi ke nan na sake tambayashi ya mike saman kujera daga zaune ya balance da kafafuwan shi yace ai dole in je in gani da ido na kada su cuce mu kafin a bude don ban son abinda zai kashe muna kasuwan mu.
Allah ya kaimu nace dashi tare da ci gaba da abinda nake a wayana wanda hankalina yana a kai.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/7/20, 8:07 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA , , ,


🧕🏿7️⃣3️⃣🧕

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU


Kamar yadda ya fada haka tafiya ta kamashi don an sake bugo mai waya da dare akan kayan da aka shigo masu dashi dole ya shirya da safe ya bar garin.
Sai mu ya bari a bauchin koshi don zai dawo buki ne yasa ya tafi ya barmu sai gidan ya koma muna ba dadi muna part din mu ni da khadija sai yan mata da suke dan shigowa wurin khadija jefi jefi.
Tashi nayi nacewa khadija ta zo mu shi wuri hajiya mu gaida ta na lura bata so zuwa ba don tana kallon wani india film ne.
Amma bata iya mussa min dole ta tashi muka shiga don Abba yana can gurin yan matan sun dauke shi da suka shigo dazun.
Tana zaune a falon ta kamar kullun tare da wasu mata da suka shigo wurin ta amma matan na shirin wuce wa don naji suna sallama da ita har daya ta mike tsaye daga cikin su.
Shigowan mu matan suka mayar da hankali sun su a gare mu, gaida hajiyan mukayi bamu tsaya wurin su ba sai muka nufi hanya shiga dakunan hajiya din.
Muryan hajiya naji tana fadin maman Abba zo ku gaisa da sarakunan ki matan baffanin ku ne suka shigo dubani.
Sai dayan ke fadin ko matar baba ne don kin san ai bamu santa ba tace dasu eh itace kin san sun zo don kawo muna yaro mu gani.
Haka mukaji ta haihu kwanaki da su suwaiba suka tafi suna can abujan, dawowa nayi na duka ina gaida su don cewa da baaba tayi sarakunnena su yasa na duka masu.
Masha Allahu suke fada yarinya ce ashe ikon Allah matar mutum ance kabarin sa har can akace ya auro ta ko baaba dai dariya tayi na mike ina jin suna magana a kaina ban tsaya sauraren su ba.
Dakin yan matan suna barbaje a dakin nasu na zauna a gefen gadon su suka shiga cewa ashe tare kuke da anty khadija tace eh.
Hira suke yi in dan jefa baki a hiran nasu amma hankali yana ga waya na da muke charting da samira tana zolayana wai naji dadin bauchi naki dawowa gashi ance uncle ya shigo abuja yau.
Nace da ita bauchi zama daram ai tace kina fara shi ai da mun biyo ki nan muma dariya ta bani har ina darawa ni kadai da wayan .
Yar wurin anty suwaiba da tafita duba girkin da sukeyi ta dawo tana fadin mummy hajiya tana magana dake.
Haka yasa na mike ina rubutawa samira yanzu idan kin gani ai baki gane ni saboda dadin da sarakuwa na ke bani kullun.
Na tura mata daidai ina isa falin hajiya nayi saurin kashe wayan na karasa ina fadin hajiya gani tace kunyi waya ko yace ya isa ?
Eh baaba ya sauka tunda safe ina ji aiki ne yasha mai kai be kara kira ba tun bayan isar nasu ta sake fadin yace yau yake so ya dawo in da hali nace haka ya fada baaba.
Nakai zaune a saman dan Center Capet din falon tace su dai maza basu mayar da tafiya a bakin komai ba ni gashi kullun ina waken zuwa duba masaukin ku acan amma ban tsayar da lokaci ba har kuka kai ga zuwa.
Nace ai shi uncle tafiya ko acan muke haka yake yawan yin shi idan ya kama mashi tace ai hakan na dakyau don bidan na kai ne.
Ni dai abinda zan fada maki shi ne ki kara hakkuri hakan danaji yasa na mayar da hankalina gare ta taci gaba da fadin ko can da maza sai a hankali balle mazan wanan zamanin da muke ciki.
Ko wani gida kika gani ta kalar tasu matsalan daban don haka idan ya na fushin shi ki bar biye mai kuna zama daya shi wanan fushi da zan iya raba babana dashi da na rabashi dashi tun yana yaro .
Don haka ya tashi shi yanzun ma ai ya rage sosai wallahi sai ma ince shigowan ki yasa ya daina abubuwa da dama ni ban san halin wanda ya dauko haka ba wallahi.
Murmushi nayi nace baaba ai yanzu na saba da halin shi ni abinshi bai kan damay tun farko Anty Aisha ta sanar dani halin shi shiyasa abin yazo min da sauki.
Abinci da suka gama suka kawo suna fada mata ga abinci nan an gama hajiya shiya dakatar da mu ga hiran tamu nan take fadin.
Ai ku zubo mutaru muci anan don zumunci wanan halin na hajiya yana matukar burge ni sosai don sam bata da matsala irin na wasu uwayen miji da nake gani.
Birbiscon gero sukayi da miyar taushe sai man shanu da za a zuba ga mai so da dan miyan dage dage ga wanda baison ci da miyar taushen.
Fitowa sukayi daga dakunan su nan aka shiga zuzuba abincin kowa yaja nashi plate din khadija ce ke tambaya na wai wanan wani irin abinci ne haka ?
Dariya muka soma yi mata nan hajiya ke mata bayanin akan abinci sai faman juya cibi take a cikin sa nan hajiya tace taci taji yana da dadi sosai.
Muna ci hajiyan hankalin ta yana wurin mu a ranta take cewa Allah ka shirya tsakanin yaran nan su zauna lafiya ban son fitina sam a tsakanin su.
Don yarinyar na da tarbiya sosai gashi sanadin ta abubuwa sun sauya ga rayuwan baba na sosai wallahi ba zan so ace yana yawan samun matsala ga auren shi ba.
Mun kare lokacin sallah yayi nace zamu tafi muyi sallah tace mu shiga daki muyi hijjabai na nan saman kujeran dakin nata don haka sallah ma anan mukayi .
Bamu koma shiyan mu don na tsaya na taya yan matan aikin abincin dare duk da hajiyan ta hana nace ko a gida hajiya ai nakan yi girki sosai .
Tace kin ko kyauta ma kanki wallahi yo may nene auren dama ai girki yana cikin ginshikin aure sosai amma matan yanzu basu gane hakan.
Sai su dauka wai wayewa ne daukan yar aikin da suke yi basu san wani daman su bane suke ragewa har ga Allah.
Kwanan uncle biyu ya dawo ranan da ake ta shiri zuwa kamun amare da za a yi don bai nan nima kuma fitan yanzu bai a raina don na saba da rashin fita tunda shike jawo muna matsala tsakani na dashi.
Sai ban mai da kai da mutafi ba misakin sha biyun rana ya shigo bauchi da gajiya don haka tunda yayi wanka ya kwanta wai yana son ya huta ne.
Khadija sun fita tare da yan matan gidan zuwa gidan bukin haka yasa na dauki Abba muka samay shi a dakin shi.
Barcin nima nayi a lokacin sallah azahar ya tayar damu sai kuma cin abinci misalin karfe hudu sai ga anty suwaiba ta shigo lokacin muna falon mu zaune da shi.
Sun gaisa tayi mai yaya hanya ya amsa mata da lafiya sai da suka gama gaisuwa ne tajuyo tana cewa dani Safiya yaya haka kuma naga baki shirya ba kun san kuma karfe hudu ne akasa program din.
Nace anty ku tafi kawai ba zan samu zuwa ba yace mata ina zaku kuma tace gidan su kawu wurin kamun amare zamu tafi yace oky, .
Bai sake magana ba sai ita ke fadin amma ko banji dadin rashin zuwan ki ba wallahi gaku cikin gari kin san fa mune zamu wakilci baaba fa.
Anty kiyi hakkuri ba zan samu fita ba don kin ga ma yau ya dawo tace oky yayi ta juya tana fadin to mukan sai in mun dawo zamu fita don sauran sunce mu hadu a can.
Dama don ke nazo don mu tafi tare daku din ashe ma baki samun zuwa din a dawo lafiya nayi mata ko kallon mu bai sake yi ba tunda ya kawar da kai.
Sai bayan fitar ta yake fadin saka lalle din ne har sai anje yin wani program can don sun bidia kawai irin na mata shiru nayi ban yi magana ba ya mike yana fadin bari in leka hajiya tunda na shigo ban fita ba.
Itako anty suwaiba tana shiga tana fada sai hajiya tace kada kiga laifin yar mutane kin san fitan ku na satin da ya wuce sai da suka samu fitina a tsakanin su.
Bar mashi matar shi a inda yake son ganin ta don Allah kin dai san halin shi ko tace amma baaba ai suma suna son idan nasu ya tashi a tafi ko ?
Bata san yana shigowa ba saiji tayi yana fadi daga bayan ta nace baza ta fita ba ku baku iya zama gidajen mazan ku kullun kuke nan hanyar gidan buki ?
Banzo nan da ita don yawon buki ba don haka kada na kara jin wanan magana ya fadi yana hararanta yana zama tace amma dai yaya zaka bari ranan buki ko ?
Ta tambaya tana kallon fuskan shi don son jin amsa kafin yayi magana hajiya ta amsa mata da cewa a a ranan buki kan zata tafi mana tunda suna gari.
Kallin mahaifiyar tasu yayi sai bai ce komai ba tunda ta yanke hukunci yake cewa shike nan ai amma ku rage wanan yawan zuwa bukin naku.
Ku wai mazajen ku basu kishin ku ne wai?
Dariya tayi tace kai yaya kowa fa ba irin ka bane mai kishi wai ko don matar ka tana da kyaune haka yasa baka son a ganta ?
See you yace don na hana ta fita shine wani abu baaba tace shifa raayin shine haka kin manta lokacin da kuke yan mata yadda kuke kwasa dashi ne ?
Safiyan ma tana da hakkuri wallahi tace tunda sukai aure fa bata je gida ba har yanzu ido hajiya ta fitar waje tace kai baba na kada ka raba yarinya da iyayyen ta don Allah.
Yace haba baaba may zata je tayi kullun ba suna waya ba tana jin lafiyan su kadai samu mai hakkuri ne tace amma wanan samiran taka ta farko ai shashani ce sarkin yawo.
Tsaki yaja yace don Allah ku bar dauko min maganan wanan macuciyar ban ma son in tunata a rayuwa na wallahi.
Mikewa suwaiba tayi tana fadin ni zan tafi kada a fara badani ba hararan ta yayi kawai ya kawar da kai ta fice tana mashi dariya hajiya na mata sai sun dawo.
Babana zumunci yana da dadi ba yawo bane haka don mutum ya ziyarci bukin yan uwan shi ka rage wanan tsananin da ke wa yarinyar nan don Allah ka bata freedon din kanta itama ta shiga yan uwanta matsin yayi yawa wallahi.
Murmushi yayi ya kawar da zancen yana fadin ai hajiya gara dana daure nayi tafiyan nan don mutane yanzu basu da gaskiya ashe laifin wanda muka tura odo kayan ne yayi muna wanan sheri.
Nan ya fara mata bayani komai da ya faru tace yanzu yaya zakuyi da kayan da kuka ce basu da kyau ?
Yace dole zamu karyar dasu a farashi mai sauki shi kuma mun sallamay shi don ba zan zauna da mahainci ba.
Nikan ina can part din mu damuwa da kadaici ya ishe ni a lokaci ga khadija dake debe min kewa ta fita yau don haka dagani sai Abbati ke part din namu.
Haka yasa na dauko waya muna hira da ummi na haka ya dan rage min zaman kadaicin da nake yi ni kadai babu abokin hira.
Idan banda wanan matsala na uncle da sai in ce banda matsala ko da muwa a wanan auren nawa don zai bani ci da sha da sutura mai kyau amma ba fita ko ina sai dai idan mutum yaji marmarin ganina yazo gidan.
Don na fahinci har da yan uwa na idan banyi da gaske ba uncle zai rabani da su ne don basu zaman zuwa wurina kullun ni ban zuwa gurin su.
Saukin abin ma yanzu da yaya Saadu ke kusa dani yana debe min kewan yan gidan mu sai ko yaya sani da kan shigo jefi jefi idan yazo yin wani abin.
Tun da ya fita gun hajiya bai dawo ba don yayi baki daga cab suka fice da mutanen bai dawo ba sai bayan sallah ishai ya shigo lokacin khadija bata dade da shigowa gidan ba.
Muna zaune tana min hiran event din da akayi sai gashi ya turo kofan dakin da sallaman shi sannu da zuwa mukai mashi.
Ya dan je nakin mirrow ya tsaya tare da jingina jikin shi akan mirrow din yana fadin naga alama khadija garin nan ya amshe ki fa ?
Dariya tayi tace kai wane ni yaya nida na matsu mu koma mu tafi gida inga ummi na da sauran yan uwa .
Yace ba yanzu ko mun koma sai na tafi Egypt na dawo zaku tafi gida da sauri na dago kai na dube shi ban kuma kawar da idanuwa na akan shi ba
Ya gane may nake nufi don ba haka mukayi da shi da gida zan tafi sai yace mu dakatar da zuwa gida sai idan mun koma daga bauchi zamu tafi.
Yes yace haka na tsara tsara yanzu don nima ina son in tafi in duba su idan ban samu zuwa tare da kuba tafiyan zai min nauyi ne daga baya.
Haushi bai bari nayi magana ba alokacin don khadija kuma dake wurin sai kawar da kaina da nayi daga duban shi kawai.
Sun dan taba hira da khadija sama sama ya fita ban bishi ba yana fita nace mutumin nan ban san abinda yake nufi ba a kaina khadija ?
Kiyi hakkuri kibishi yadda yake nidai da mun koma zan tafi don bazan tsaya jiran ku ba don babu ranan tafiyan ku gwago ma nasan ba zata tsaya yadda ta matsu din nan.
Ta yunkura tana tashi daga inda take zaune tace nasan ko ya dawo cewa zaiyi zai tafi Etopiar kuma dariya ta bani nace a a Niger zai tafi tace a ba ya zama sarkin yawo ba shi.
Nace ni kuma wanan bahagon rayuwan na sake fadawa idan ka fita wanan ka fada wancan idan bakai hakkuri ba sai ace kai mace sai aga laifin ka amma saboda Allah don kana aure sai ka watsar da iyayyen ka ai ba komai kudi ke sayawa mutum ba a duniya.
Sai da na gama abinda nakeyi na fito don duba shi waya yake yi don haka na juya na koma don shi wayan shi ba mai karewa bane da wuri.
Fita nayi zuwa wurin hajiya nayi mata sai da safe a lokacin take cewa ga abin bukina da suwaiba ta bayar a bani don ba ta tsaya ba sauri take yi da ta shigo.
Na karba cikin ladabi na juya na koma part din namu, daki na shiga na shirya tare da gyara Abba don yau khadija na san a gajiye take sosai a ranan don haka na dauki yaron na tafi dashi.
Koda na tura kofan ya fito daga wanka yana tsaye yana goge jikin shi jin shigowan mu yasa ya maida hankalin shi gare mu.
Yaron na shimfede saman godo na juya na fita naje dauko abincin shi duk da bai faye falkwa da dare ba sosai amma ban kwanciya sai da abincin shi a kusa dani.
Na dawo dakin da sallamata na shigo na samu wuri na aje a gefen da zamu kwanta fita nayi na rufo kofunan part din namu tare da kashe wutan ko ina na dawo dakin.
Zama nayi a bakin godan dakin tare da zuba tagumi a lokaci daya tare da dukar da kaina kasa may ke faruwa ne koma naji ya jefo min tambaya.
Na dago nace yanzu uncle don Allah bazaka bari naje gida naga iyayye na ba sai ka tsiru da wani zancen tafiya kuma bayan ba haka muka yi da kai ba kuma ?
Ke dakata may kike so dani ne wai so kike ki na aje abinda ke gaba na don na dadada maki ranki komay , ?
Da mamaki nake kallon shi don kaina ya daure sosai ga maganan shi yace nace bazaki ba sai na dawo Egypt period.
Ya juya ya dauki laptop din shi ya haye gado batare da ya kara bi ta kaina ba har ya fara latse latse sai kuma ya juya gare ni yana fadin .
Kuma bari kiji idan har zaki tayar min da hankali akan maganan nan gaba daya sai in ce bazaki tafi ba inga yadda zakiyi ?
Da mamaki na sake dago kaina kamar zanyi magana sai kuma na fasa naja bakina na rufe a raina nace ashe maza duka haka suke.
Nadan saci kallon shi aikin shi yakeyi bai kulani ba na gyara na haye gadon tare da rungumay dana muka kwanta tare da bashi baya.
Ban jima ba da kwanciya barci ya dauke ni don ban yarda na saka zancen shi a raina ba tunda naji ya fada ya tabbata ke nan ba zan tafi din ba sai ya dawo.
Sai dai na san cewa gwago da khadija bazasu iya kara lokaci haka ba suna jira na don kullun maganan su ta zuwa gida ne tun da nayi arbain.
Juya yayi yakalle mu ina kwance ina yadda na kwanta na kankamay yaron ga jikina kamar za a sace min shi a jikina shima yaron sai kwasar barcin shi yake yi hankali a kwance.
Rufe laptop din yayi tare da kashe wutan dakin ya hawo gadon ya kwanta rigingine tare da harde hanaye shi wuri daya yana tunane.
Don shi gani yake na canza mai yanzu bani bin umurnin shi ina son in tsiro da wasu halaiyan da bai sanni da shi ba a baya.
Ya rasa ko may ya canza ni haka lokaci guda ya zama mai dole yayi wa wanan halin da na tsiro mai waige tun da wuri.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/9/20, 9:20 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , ,

🧕🏿7️⃣4️⃣🧕

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUN KU

Gari ya waye mun tashi lafiya ban yi mamakin rashin taya ni da baiyi ba rana don in da sabo na saba idan yana fushi bai kallon inda nake nima kuma a yadda nake ji haka yafi mim sauki ai.
Kafin ya fito bayi na koma dakina tunda nayi sallah ina wurin zaune ina azzakar din safiya da neman cikawa da imani tare da rokon Allah abubuwan bukata ga bawa.
Na gama na tashi ina nade abin sallah lokacin khadija ta motsa inda take kwance don tana fashi sallah haka yasa bata tashi ba daga barci .
Fita nayi falo na gyara ko ina saura da kuna wanka na shiga don in gyara jikina na fito na zauna na shirya kaina ina gab da zan gama shiri naji kukan Abba daga falo nasan uncle ne ya dauko shi ya tashi daga barci yana jin yunwan safe.
Ya shigo dakin dashi na karbe shi don ihun da yake tsalawa sosai a lokacin ya fadin fuska a dake ki bashi abinci yaci ya falka yana kuka haka.
Karban yaron nayi daga hannun shi tare da fadin ina kwana uncle ya amsa min a dake ya fita na bishi da kallo ina fadin ikon Allah a raina.
Wanka na fara yiwa yaron sai da na shirya shi khadija lokacin ta mike tana hada mashi abinci tace amma anty dole ki samu yarinya da zata zauna dake ko , ?
Nace ba gaki nan ba na bata amsa a takaice.
Dariya tayi tace in na zauna ummin mu fa dawa zata zauna nace ke din zaki tabbata a dakin ummi ba zakiyi aure ba khadija ?
Dariya tayi tace ko zanyi ba yanzu ba ni sai nayi karatu ina zama saman gado da yaron tana miko min feeder shi nace kin yi sa a yanzu baba ya sauko sosai idan kin ce zakiyi karatu na san a yanzu zai iya barin ki.
Don darasin da ya samu a kaina amma in bashi ba ai da kema nasan abinda ya faru damu zai faru dake asamu wani dan uwa a laka maki.
Tab wallahi ni ba zan yarda da wanan abinda sukai maki ba ai fuskana yana ga yaron nake cewa baidai kama ba khadija.
Tace ai yanzu ba shi ba ma yarinya auren dole kullun yana fadi bai son ma ku hadu idan ya tuna da abinda yayi maki shi da su inna sai yaji ranshi na baci.
Murmushi nayi nace baba ke nan ai ubangiji yakawo muna saukin abinda da yanzu kila an manta dani ko ina nan ina wulakanta wurin yan uwa.
Shiyasa kika ga duk abinda mutumin nan yayi min khadija nake shanyewa don tuna inda rayuwana ya fito cikin kaskanci .
Matsalan shi dai shi ne wanan saurin fushi da rikon magana amma don don fitan da yake min na cewa kada na fita ni dama can ba ma,abociyar son fita bane ke kin sani yanzu ne ma ai har nake shiga mutane da ummin mu da yan uwan ta kawai muka bude ido kin ga abin ya zo min da sauki ai.
Sallaman yan matan hajiya da suka shigo muna da abin karya ne a falon muka amsa kusan a lokaci daya da khadija bayan ta aje ta leko muna ina kwana.
Nace ki cewa baaba mijin tane ya tashi da fitina ban samu shigowa da wuri ba yarinyar ta dauke shi tana fadin yau mijin hajiya ka dagawa mutane hankali ko ?
Nace wallahi idan ya tashi shi ba abinda yake nema sai abinci kamar an fada mai shi kawai ake zaman ci daukan shi tayi ta dan mai wasa nace ta ajeshi yayi kashi zan canza mai permpas din jikin shi ta fita tana mashi sheri.
Khadija ce ta shiga dashi bayi ta wanke mai jiki ta fito dashi tana saka mai wani fita nayi na barsu na je hada muna abinci ida naga sinasir sukayi da ferfesu sai tea da dankali nace a raina wanan uban abinci haka duk na karin safe.
Nasan sinasir din don uncle sukayi shi don yana son cin sa sosai ni kuma ban iya ba don haka ne ban mashi a gida amma zan koya a wurin su da birabisco din da naga sunyi ranan na gero.
Da sallama a bakina na shiga dakin shi yana saka tufafin shi a lokacin ya dan juyo ya kalle ni yana amsa sallamana.
Nace an kawo abin karyawa ne nazo fada ma oky naji yace dani yaci gaba da abinda yake yi zanin gadon na juya na yaye don canza wani don wanan yayi dauda.
Ya gama ya fice ya barni a dakin sai da na gama na fito yana zaune a gurin cin abincin yana waya cikin fada fada gurin na nufa na fara zuba mai.
Yana kallon yadda nake zuba mai yana wayan sai da yakai munzalin yadda yake so yace dani barshi haka na.
Na rufe na juya na tafi ya bini da kallo bai daiyi magana ba ina shiga na samu ta fito wanka tana zaune tana shafa mai a jikin ta.
Nace yau halin mutumun nawa ya tashi bari ya gama ci sai muje muci namu abincin tace ikon Allah haka kike fama anty ?
Murmushi nayi ina kaiwa zaune nace to yaya zanyi khadija haka kuma Allah ya jerabi ni da gani ni yanzu ma kamar kada in haihun ga sai naga fushin ya karu mai sosai wallahi.
Dariya tayi tace ko da abba yake kishi kin mayar da hankalin ki ga yaro kin daina bashi kulawan da kike bashi a baya ?
Hali ne dai kawai dama haka akace yake wai ma ya rage ne yanzu da fa da kowa bai hurda cikin yan uwan shi kowa mai laifine a gare shi.
Dariya tayi tace barin je in samay shi ai mu gaisa tun bai fita ba karasa shiri tayi a gurguje ta fita wurin shi falo inda yake kwantawa nayi kafin ta dawo.
Tare da lumshe idanuwa ina tunane duk maza halin su daya sai dai halin zamantakewar ne ya banbanta wani ya dara wani.
Mu mata a biye muke dasu komai kyautatawan mace sai namiji ya kaita iyaka da zata sauya halin ta a gare shi ko yaya ne khadija naga ta dan dade sai can gata ta shigo.
Tana fadin ya fita har na kwashe kayan kai uncle oho ya fasan abinda yake maki sarai anty haka dai halin shi yake in ba shi yace abuba ba zai yarda ayi ba.
Yanzun yake ce min wai kina fushi dashi don yace ba zaki gida idan mun koma ba to haka yace hakan kuma ya tsara abinsa tace ni dai hakkuri na bashi nace aiko baki yi fushi ba don banji kin sake maganan ba.
Can wurin baaba da ya shiga gaida ita take mai yaya gajiyan tafiya ya amsa mata ba a sake ba ta fahinci yana cikin yanayin nasa ke nan.
Take tambayan shi anyi wani abune ya zauna yana hura iska tare da fadin yarinyar nan tana son ta fito da wasu hali da ban santa da shi ba yanzu.
Ba dama ince mata ga abinda nake so sai ta kawo nata korafin akai wallahi zanyi maganin ta ne a gidan nan.
Babana may kuma ya faru a tsakanin ku ne wai haka dama kake zama da yar mutane da wanan halin nan dai ya koro mata yadda mukayi.
Murmushi tayi mai tace yanzu may ye laifin yarinyar nan a cikin zancen nan daka fada kace bata zuwa ta kara cema wani abune kuma ?
Ko taki kula kane akan maganan kai dai ne ke tsiru da wasu abu yanzu ko kana cikin mazan da dazaran mace ta haihu sai su fara kyamkyamin ta ne.
Ya dago da sauri ya kalle ta tace in ba haka bane may ya kawo wanan yawan fitina haka ko acan ma haka kake mata ne ?
Yace ina na zauna gida balle ta ganni ina wurin bidan na kaina babana ka gyara halin ka wallahi yarinyar nan tana da dadin zama ga ladabi da biyayya gare ta to may kuma ake so ga mace.
Tun ina ji har gashi na gani da idona bata da wani matsala wallahi yace ai ban ce tana da matsala ba nima ban dai son abinda take min ne kawai ina fadi tana musayawa ita wacece da ba zata abinda nake so ba wai ?
Nan dai ta kara mai magana tare da nuna mashi bacin ran ta sosai akan halin da yake yi wanda ta nusar dashi da fada mai kada fa ya manta halin rayuwan da muke ciki dani dashi.
Idan bai bi a sannu bai a sannu na har na gaji da hakkuri na gudu fa yasan dai ba kimai kudi ke samuwa zai iya samun wata mace amma ba mai irin hakkuri na ba.
Wanan maganganun na baaba sun tsaya mashi a rai sosai don da zancen ta ya wuni yana mai yawo a zuciyar shi.
Ni dai naga ya dawo gida bayan la,asar ya shigo da dan sakin fuska alikacin muna falon mu zaune muna hira har da yan mata hajiya dake shirin fita gidan buki da khadija.
Mun gaida shi ya shiga dakin shi bai zauna falon ba don ganin su a part din da yayi muryan shi ya daga ya kirani na amsa na tashi zuwa gare shi.
Tsaye yake yana rage kayan jikin shi na shigo dakin daga inda yake tsaye yake magana yana fadin hada min ruwa in dan watsa ma jikina.
Ban yi magana ba na kama hanyan ban dakin kamo hannu na naji yayi na juyo ina kallon shi batare da sakin fuska ba sai naga yayi murmushi yana fadin.
Wai fushin zuwa gidan ne haka har yanzu akeyi nace fushi akan may zanyi fushi uncle idan ma kace ban zuwa gaba daya ai ba zanyi fushi ba.
Tunda nasan kana da dalilin fadin haka kawai dai idan mun koma sai gwago da khadija su wuce don ba zasu zauna har zuwa lokacin da kake son mu tafi.
Haba dai yace nace a matse suke da gida don dai kawai ba yarda zasu yi ne ina kokarin kwance hannu na daga rikon da yai mun din.
Bina yayi da kallo sai kuma na bashi tausayi sosai yaji bai kyauta min haka kawai ya hana zukatan mu samun sanyi a wani dan lokaci da ya kamata ace mun samu shakuwa sosai a tsakanin mu na zaman da mukeyi a nan din.
Har na fito daga bayin yana tsaye a idan na barshi jingine da wardrove din dakin uncle na hada ruwan, nace mai ya nisa tare da fadin nagode.
Na juyo ina kallon shi ya wani lumshe idanuwan shi ni dai na fita na barshi a wurin yana kallo na har nakai kofa yace zo nan safiya.
Na juyo gare shi ina dan kallon shi ya bude hanayen shi yana jiran in iso gare shi din nace daga inda nake ba wanka zaka shiga ba uncle ?
Idan wanka zan shiga bazaki zo ba don ina da kazanta a jikina komay ?
Dariya maganan shi ta bani har na dan murmusa kadan yace to ko ke fa duk na rasa gane kan ki kwanan har kin sa na fara zargin yan uwana ko su ke zuga ki ga abinda kike min din.
Da sauri na karaso inda yake ina fadin wallahi haram kada ka zarge su da komai idan basuce in soka ba in ma biyaya kasan dai ba zasu taba cewa in guji dan uwan su suba.
Zama lafiya kawai ke tsakanina dasu har kakai ga fahintar haka a gare mu ya rugumoni zuwa jikin shi yana fadin to ke din ce yanzu naga kina son yi min gardama ga abinda na fada.
Uncle may na fada ga maganan tunda kace ga yadda kake so ayi murmushi yayi ya rungumini kawai ban son kina min gardaman ga abinda nace.
Insha Allahu nace tare da kokarin jaye jikina daga nashi na juya kawai ban kara cewa komai ba tsayawa yayi yana bina da kallo har na fice daga dakin.
Falo na dawo na samu har sun gama shiryawa suna jira inzo in karbi Abba su fita nace ku dai kula da kan ku don Allah idan kun fita.
Insha Allahu suke cewa kusan a lokaci daya nayi masu a dawo lafiya tare da daukan yaro na nasa saman jikina.
Sai da ya gama shirin shi ya fito ina kwance saman dogon kujera da yaron da yayi barci a jikina nima barcin ne keson daukana a lokacin.
Badai barcin marace zakiyi ba kin san baida kyau nace shidai nake ji tare da dan dagowa kadan daga yadda nake kwancen.
Wurin cin abinci ya nufa yana bude kayan abincin sai wayan shi yayi kara daga cikin aljihun shi ya ciro ya duba ya dan ja tsuki tare da daukan wayan ya kara a kunnen shi.
Naji ya amsa tare da fadin ba ida zan tafi yanzu na gaji sosai yau ina son in dan huta gidana da iyalina a raina nace kamar wanda yasan damuwan iyalin nasa.
Muna zaune a falon daga ni sai shi sai dan mu dake barci a gefe na sai karan na,uran sanyi dake ta aiki a falon ya gama waya yaci abinci ya dawo saman kujerun falon ya zauna.
Khadija fa yake tambaya na nace ta fita da yan matan hajiya zuwa gidan buki rai naga ya bata baidai yi magana ba nima ban yi ba na share shi kawai.
Kwance yake yana fadin mummy tace wai kada ki manta da sakon ta ko may ye sakon nace ai nayiwa anty suwaiba magana masan bauchi take so azo masu dashi idan zamu koma.
Yace masa kuma ba ko kirdamo ba nayiwa mutanen gidan gona na magana su sama muna kindarmo da zai wadace mu idan mun koma.
Nace amma ko naji dadi tundai da nazo nan na koyi shan shi da shinkafa yana min dadi sosai wallahi yace au ashe kina so ke nan ?
Ai kullun sai na tsiyayo a falon hajiya don akwaishi koda yaushe mutum ke so dama ita hajiya tana son shi sosai awurin ta ma muka koyi shan sa.
Sallama akayi muryan namiji ne daga kofan shigowa falon ya amsa mai da fadin mustapha shigo mana na fara dan kamay kamay jikina don nasan ba abu mai wuya bane hakan ya hada mu.
Yace ki zauna abin ki baki san mustapha ba ko kanin yayana ne mijin anty ki ai bakon ke fadin bamu taba haduwa ba da ita ko kin sanni ya juyo yana tambaya na.
Kai na girgiza mai alaman ban san shi ba mike wa nayi ina fadin bari na leka baaba na dawo nan na fice na barsu sai yaron dake barci.
Ita kadai a wurin ta sai tv dake ta faman aiki tana zaune tana waya na shigo ganin tana waya yasa na mayar da hankalina ga tv dake aiki a falon.
Hankalina naga tv naji ta ce dani maryam tace a fada maki wai gobe zata zo damai gyaran jiki a gyara maki kan ki da kumshi dariya nayi nace wai data barshi ai don na kaina bai dade ba ma tace sunyi magana don itama ina gani za ai matane.
Allah ya kaimu nace tace ai ku yara gyara jiki gareku baya baci balle wanan miji nake dake da saka ido dole ki mayar da hankali ga gyara don shi dan korafi ne.
Nasan shi sarai da son gyara ga mace don yaran nan shike basu kudi suje kitso suna kanana kin ga ko yanzu a kan ki zai koma ke matar shi.
Dariya nayi tace nasan halin shi sarai wurin tsabta indai babana nace wallahi ko baaba haka ma yake ko acan ina da matar dake zuwa har gida tayi min kitso ko wanke kai tace bakaji ba baida wasa wirin tsabata shi.
Alhamdullahi duk abin da nake jiye mashi ya samu a wurin ki tunda ba wanda ya taba jin kan ku ai kin ga an zauna kalau ba korafi.
Sai dai abinda nake so dake shine ki kara hakkuri nasan kina da da baki da shi da yanzu anji kan ku da wanan fushin nashi nayi mai magana kan zuwa gida da kike son yi shikuma yana son hanawa.
Da sauri na dago kai na dan kalle ta ina mamaki a raina ina taji wanan zancen don dai ni ban fadawa wani ba ko kuma wurin khadija yan matan hajiya sukaji suka kwarmata mata.
Kai khadija bata fadi na sani to a ina taji nake tambayan kai kamar tasan abinda nake tunane naji tace nan yazo da safe yake fada min na nuna mashi kuskuren shi.
Nan dai ta shiga yimi fada nima tana kara lurar dani zaman takewan zama tare da yadda hakkuri ke jawa mutum riban aure a rayuwa.
Shi ya shigo yana fadin Abba ya tashi yana dauke da yaron a kafadan shi ya miko min shi tashi nayi na fita don abincin shi nacan part din mu don haka na koma can.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/9/20, 9:21 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , ,

🧕🏿7️⃣5️⃣🧕

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU KU

NOVEL DINA NA KUDI NE IDAN KI FITAR MIN HAKKIN AMANA YA BI IDAN KIN KARANTA BAKI BIYA INA BINKI BASHI HAR BAYAN RANKI, , , ,

Nabiku bashi masu karantawa ta sace har bayan ran ku don online novel ne na kudi kun sani kuke take sani saboda son zuciya idan baki biya ba don girman Allah kada ki karanta min novel don Allah Allah kuma ba wasa bane.
Kamar yadda maryam tace sai ga mai gyaran jiki da yaranta tun da safe a gidan namu suka sallama tare da fadin itace tace suzo suyiwa anty safiya gyaran jiki.
Allah ya taimake ni nagama dan abinda nake yi na koma daki na fada ma uncle Allah ba da saa yace min ya koma ya kwanta.
Da yake su hudu ne nan wasu suka fara sance min kaina dake da kitson da nazo dashi wasu kuma suka kama kafana suka shiga wanke min shi mai min dilka tanayi.
Kafin wani lokaci sai gashi ya fito da shirin shi yace zai shiga wurin baaba acan zai karya haka yake kamar mai gudun baki har nakan yi maki yadda yan uwana ke zuwa ya sake dasu.
Kafin wani lokaci sun gama sance kan ka shaga wake wa ni kaina yau nasan na hadu da gamo na wurin gyaran jiki haki ne turare na duk anbini an shafe jikina da komai nidai iyakata ido suce yi kaza in yi shine nawa.
Kafin wani lokaci munyi nisa ga komai sun gyara ni tas mun kusa gamawa sai ga maryam din ta iso tana min dariya nace ke baki fada min in shirya da wuri tace nasan ba zaki jure wanan abin ba idan na fada maki.
Gaisawa sukayi nan suka juya a kan ta wanda suka gama aikin su suka shiga gyarata ita ma ko ban duba madubi ba yau na san an hadani iya haduwa nan take fada min cewa ai yan sundan ne su aikin su ke nan gyara.
Nace wanan ai in da Abuja suke dana samu wirin gyara matar tace min ai akwai yar uwarta dake yi acan zata ban nombanta idan mun gama.
Kafin wani lokaci sun gama maryam zata sallamay su nace ta bari in sallamay su na shiga na dauko kudi duba ashirin na basu a mu biyu suna ta godiya suka wuce tare da bani wasu turaruka wai idan zanyi wanka in dinga digawa a ruwa.
Maryam ta koma part din hajiyan su ta barni na shiga wanka in gyara jikina washe gari ina cikin wasu material yellow nayi mai dinkin bubu tare da daura dan kwalin shi akaina.
Sai ga diyan baaba sun shigo gidan alokacin ina wurin ta muna hiran masu gyaran jikin da suka zo jiya mun gaisa dasu suke fadin yawwa safiya da anty suwaiba ta iso sai mu tafi tunda kun shirya nace ina da sauri ?
Maryam tace gidan buki mana nace sai kun dawo may kike nufi baki zuwa ko may nan suka hau bakin su sai ga Aisha ta shigo itama ta hau bakin ta tace wallahi ni na dauka shirin ke nan kikayi ai.
Nace ba zan samu zuwa ba kun ga ma ranan da naje sai da Abba yayi zazzabi zasuyi magana hajiya ce ta katse su tace kun fa san halin mijin ta wacan ma zuwan gidan ku da tayi ba karamin tashin hankali sukayi da shi ba.
Sai ga anty suwaiba tashigo ta samu ana maganan tace gaskiya hajiya don ko ni ranan dana biyo daukan ta muje wurin kamu a gaban shi amma wallahi kemay may yaya ya hanata zuwa.
Nace bama zan tafi ba ban iya jidalin shi ke Aisha aikin san halin shi ba sai na fada maki ba don kin san komai na karasa fadi ina kauda kai gefe.
A sanyaye tace nafa sani gaskiya yaya baida dadi halin shi sai ke Safiya hajiya tace bani waya na ku kira min shi ai mantawa nayi har ya fita ban fada mai ba.
Nace hajiya da kin barshi don Allah ni ba zan tafi ba amma bata bi ta kaina ba sai da ta kirashi tace matar ka zasu gidan buki da yan uwan ka nakuma ce ta tafi amma tace bata zuwa don sanin halin ka datayi.
Yace tunda kince ta tafi ta tafi mana tace gata kai mata magana tamiko wayan na karba tare da karawa a kunne na inajin shi yace wai bazaki tafi ba kikace nace eh banjin fitanan ne.
Yace to ki shirya ku tafi yanzu zan turo maki da mota don ina nan gidan gonane zanyi magana yace nace ku tafi ko ?
Ya kashe wayan shi wallahi hajiya dakun barshi Uncle bahagon mutum ne yanzu sai na dawo zai samu wani laifin yace nayi mai ni na gaji da halin shi wallahi.
Nan dai suke ta magana ba yadda na iya dole na mike zuwa part din mu don in shirya tare da maryam muka tafi bayan tafiyana hajiya tace.
Abinda nake fada mai ke nan kada yakai yarinyar nan makura ta daina jin tsoron shi Aisha tace ai in dai yayane yafi danan tana dai iya halin shi ne kawai.
A daki kuma shiri nake yi muna maganan da Aisha take cewa kin gani ba idan mutum bai sani ba sai yace kece ke juyashi ke amma fadi ai don da akaga yana muna abu yanzu cewa ake kece ke sakashi yi.
Wai duk yan uwanki sun mamaye shi sai abinda kikace yake yi Aisha ce ke fada ma hajiya karya ne kema ba dadin sa kike ji ai.
Di dai hajiyan bata da daukan irin maganan ne kin ga shegiyar yarinyar nan da aka tura maku kwanaki yar isakan yarinya ce sosai wallahi duk ita tazo da wanan zancen.
Nace zarah ko tace ita mana nayi bakin cikin da hajiya ta yarda tabi ku a lokacin wai mako tazo gaida ke da kuka zo ?
Nace ban ganta ba wallahi nima na dauka ko bata garin ne ai tace tana nan yar iska in kinji abinda take fada ai abin bakyau wallahi akan ku.
Har na gama shiri muna hira akan zarah da iyayyen ta wasu kaya ta gani ta yaba nace idan kina so ki dauka ban taba saka su ba ma.
Tace cikin murna ashe abinda ake fada kan ki gaskiya ne nan ta barni ina shirya Abba ta fita don khadija sun fita da yan matan gida da wuri yau.
Tsaba na shirya na dauko yaron da jakkana dana abincin shi na rufo kofan part din mu zuwa part din hajiya ko da nazo maryam har ta shirya cikin kayan dana bata ta kwabe wanda tasa.
Ina shiga suka dauki ihu suna fadin dole ma yau mu fasa taro don dole kallo ya dawo wurin mu murmushi nayi ina aje kayan dake hannu na na mika wa hajiya key din idan uncle ya dawo.
Bamu jima ba muka kwasa sai gidan bukin kofan a cike yake da jamma a yan buki har ta cikin haraban gidan inda muke kokarin shiga.
Matane ko ina zazaune saman kujerun roba ana nuna hali tun da muka tun karo wurin kallon su ya dawo kan mu wata tobashiyan su ce ta tare mu tana fadin matar sulaiman di ne nan ?
Gaskiya yake daga hanci ashe yasan zarin da yayi mun gaisa da ita tana mi ba ina dariya dago kan da zanyi in kalli wurin sai a idon anty dake min wani kallo tun daga nisa.
Gabana yaba da wani irin kara a lokaci daya nace innalillahi Aisha ga anty can tace wata anty suna kokarin kallo suga wacece nake magana.
Anty suwaiba tace ko maimuna kike magana wai nace ita jikina sai rawa yakeyi da ganin ta Aisha ne tace kin ga tsaya safiya maimuna may can ai itama yanzu tasan kin fi karfin ta tako ina wallahi ki dake kamar ba abinda yafaru ku gaisa kawai idan ta jaki da mutunci ayi .
In kuma ta nuna maki wani abu akasin haka gamu wurin ai sai na dake sai da muka dan gaisa da mutane muka karasa wurin da suke zaune da wasu mata ashe su anty uwace.
Mun karaso aka fara gaisawa yan biyun ta suna gani na sukayo kaina da murna suka rungumay ni nima na rungumay su muna murnan ganin juna.
Sai can na dan juyo ina fadin anty sannun ku da zuwa tace ai dukan mu ke da sannu da zuwan don duk baki muke anan .
Anty uwa sai kallon na takeyi tana batsarwa kasa da sama tana tabe baki nace da ita anty ina wunin ku tace lafiya kawai ta juya kai ga kallo na.
Sai yanzu na fahinci inda muka zo watau family house din su daddy ne mijin anty gidan su hajiya baaba kenan famnin mahaifan ta gidan kawunan su uncle ke nan.
Mun gaisa dasu muka wuce zuwa cikin gidan don gaisawa da mutanen gida mun bar maryam a wurin tana magana da wata basu ankara ba gulma ya ci su a wurin basu kula da ita ba.
Suna hada baki wurin fadin duniya maimuna yar aikin kine ta koma haka inji anty uwa ke magana sai anty din tace bari ke dai ai ni na suma zaune wallahi .
Uwa din ta sake cewa kin ga kayan jikin ta da sarkan ta kuwa tace ai shi nayi wa mutuwar zaune ana inji anty ta basu amsa .
Anty uwa tace da bamu san asalin ta ba sai mu dauka ai yar wani da wata ce nan ko ba diyar kowa ba wallahi.
Maryam ta kasa hakkuri tace shi fini da uba ai in fiki da miji yanzu haka abin yake ba yar kowa ba gata Allah ya kaita gaba ta basu amsa sai duk suka yake don basu san tana kusa ba.
Suka mayar da abin wasa don dama tobasai suke tace yayan mu ya iya kiwo ke nan ashe ta fadi tana wucewa suka bita da harara.
Nan sukaci gaba da zagina har uncle din sai da yasha zagi ranan wurin su anty dai kasa magana tayi tace ni abin ma mamaki yake bani wallahi.
Mun shiga ciki mu dakin tsohuwar gidan ana gaisawa sai ina akasaka take faman yi damu nan aka kawo muna abinci da sha su yan biyu su manne da mu.
Sai faman daukan Abba suke suna tambaya na wai yana tafiya nace ko zama bai fara ba ai maryam ta shigo nan dai take fada muna abinda suke fadi a gamay dani.
Murmushj nayi kawai nace dama nasan abinda zasu fada ke nan bayan mu bayan mun gama cin abincin ne ni dai ban taba komai ba a wurin muka fito waje don mu sha iska.
Kujeru aka kawo muna muka zauna dukkan mu ahankali nake fahintar komai a wurin ina kallon su yan biyu suka kai mata abba ta dauke shi tana mai wasa.
Kamar babu wani abu a tsakanin mu take nunawa a lokacin sai wani washe baki suke yi karshe dai muka hade wuri daya dasu don rana da yacin ma inda suke zaune.
Nan suka kare min kallo tsab ba yawan magana nake dashi ba ko banza balle yanzu da nake jina kamar a bakin kura na zauna.
Naga Faiza nake tambayan ta fati tace tanan garin amma bata shigo wurin bukin ba sai da anty uwa ta tashi don an kirata na samu tayi min kallon mutunci.
Kamar mai jin tsoron ta dai nan muka zauna muna hira kamar ba abinda ya faru a tsakanin mun dan taba hira har zuwa karfe uku da wani abu nace zan tafi gida tace ba zaki zauna har a wanke amare ba.
Nace zan kai Abba ya huta ne gida anty don bai da jimirin dauka da yawa murmshi tayi kawai nace yaushe zaku koma anty tace daddy bai yi magana ba amma tana ganin basu kai ranan tuesday.
Nace zan shigo in gaida ke su yan biyu suka lake min wai sai sun bimu zata hana wata yar uwar daddy tace ta barsu mana su bine ai za a dawo dasu.
Ko da nace zan wuce su Aisha basu hana ba don duk sun san kwanan wasan tare da maryam da Aisha muka dawo gida muka bar sauran a can.
Tunda muka shigo yaran suka ga uncle suka koma wurin shi mu kuma aka zube falon baaba sai hiran abinda ya faru ake yi a wurin.
Baaba sai murmushin manya take yi kawai tana sauraren mu sai can tace kuma maganan kuke so ai kusan dole tayi bakin ciki tunda ba haka taso ba .
Har ga Allah banjin dadin aibanta anty da suke tayi don dai ni kan batayi min komai ba sai alheri a tsakanin mu.
Duk abinda tayi min ban dauke shi komai ba a raina uncle dai ne da yayi min iyaka a tsakanin mu nan dai na mike zuwa part din mu don in sauya kayan jikina.
Sai da dare ya mayar da su yan biyu gida wurin mahaifan su, su sundage wai anan zasu kwana wuri nace suje gobe zan zo in dauke su.
Sai da ya dawo ne muna shirin kwanciya yace danu ashe yau kin hadu da anty ki nace wallahi uncle baka fada min sun zo ba ai.
Na manta ne ya bani amsa a takaice sai na kyale shi don nasan baison maganan ne yasa nayi shiru sai can naji yace yaya akayi ta bari twins suka biyo ki ?
Nace wata mata tayi mata magana don bata so su biyu ni ba ai yace naga alama ni yanzu sama sama muke da ita.
Mijin ta dai ne bata da yadda zata rabamu dole ta saka ido itama uwar da take mara wa baya naji ance kwanaki sunyi rikici a tsakanin su ai.
Nace tare muka gansu zaune yace zaman dai ne amma sunyi ba dadi har mijin ya tashi sakin ta wai su uwa sun sama mashi wata bazawara a abuja shine taji dama ko akwai kudi ne a tsakanin su ban dai saurari maganan ba sosai.
Nace kuma suna fada haka a tsakanin su ba aminan juna bane na gani yace ke ma ba uwar dakin ki bace kuka samu sabani da ita.
Washe gari da yamma sai ga daddy ya kwaso su sun zo gaida hajiya baaba lokacin duk muna falon ta zaune mun masu taro na arziki sosai daddy ke fadi a a Safiya jiya su yan biyu ke fada min sun ganki har da baby ki wai.
Dariya nayi na durkusa har kasa na gaidashi a lokacin yake min barka ya karbi yaron hannun khadija anty dai sai kamay kamay take yi kawai a wajen.
Tana fadin gashi nan safiya ya biyu sak sai daddy da hajiya ke fadin ai wanan yaron duk gida ya kwaso wallahi ba inda ya raga sulaiman ko kadan.
Yace ni ban ga inda ya biyu safiya ba ai da anganshi anga wanda ya dauko gidan su sak tace don dai kai baka kallon safiya ne killa shi yasa.
Hajiya ta dan yi dariya tace ba abinda ya debo na uwar shi kowa ya gane shi yana fadin gida ya biyo sai dai ke ce ke ganin kamar shi da uwar.
Fita nayi daga falon dasu yan biyu sai zuwa part din mu sai da na fice ne hajiya ta dauko maganan abinda ke faruwa a tsakanin mu din .
Nasiha tayi wa anty din sosai sai da jikin ta yayi sanyi ta kara da fadin ku sasanta dake da yar uwar ki wanan duniya har nawa yake gamay tunane ?
Nan dai anty tace da hajiyan babu komai komai ya wuce ita dama bata dauki abinda zafi ba safiyan dai na ta dauki magana da zafi har waya ta daina bugo min yanzu hajiya bata ji nauyin fada mata cewa uncle ne ya hana in buga mata waya don bai iya jure wulakancin da take min din.
Tayi wani iri tare da dukar dakai tace hajiya wallahi yarinyar nan makira ce ban san may ta fadawa sulaiman ya dauka haka dazafi ba.
Daddy ne ya katse ta da fadin a a maman twins safiya bata tatanci wannan shedan da a gare ki ke dai sai dai in akwai wani abin a lokacin uncle ya shigo falon don daddy ya buga mai waya gasu gidan shi.
Tace kin gan shi nan hajiya yanzun ko wayana ya daina dauka sai ya ga dama safiya ta shiga ysakani na dashi ban san may ta fada mai nayi ba.
Safiya bata shiga tsakanina dake ba don ba ita ta hadani daku ba kawai dai ba zan yarda bane da wulkanta min mata da kike yi koda kuwa ciki daya kuka fito da ita.
A iya sani na har zagina mutane ke yi akan ki yau ko ashe duk abinda na ji na gani ina so ashe in akwai amana takamata kiso abin nan.
So nikuma shiyasa nace duk ranan da na sake ganin ta buga maki waya sai na bata mata rai sosai don ba zan juri gani irin yadda kike mata gaskiya.
Tunda ya fara magana kallon shi suke yi dama daddy ba gwanin surutu bane sosai don haka kai kawai yake kadawa yana saurare.
Sai da uncle ya gama magana yace dashi duk sherin uwace na fada mata tun farko ta fita hanya uwa ba son zaman lafiya suke yi ba su taki yarda yanzun da yafita a tsakanin su ai tayi hankali.
Sun kai wani lokaci a falon hajiya tana sulhunta su sai daga karshe anty ta mike zuwa part din mu inda ta samay mu da su yan biyu muna ta zuba game abin mu hankali kwance.
Mun dan zauna kowa bai sake da dan uwa ba sai da zasu tafine take cewa ashe mijin ki ya hana ki hurda dani ne ban sani ba ?
Nayi dan murmshi nace akan may anty tace nasan abinda kika fada mashi ne tunda ya iya cewa hakan sai dai ina son ki tuna koda shi ko ba dashi ba zan iya rayuwa a duniya.
Nace na sani anty amma kiyi hakkuri tace wa yaran ta su tashi su tafi yaran basu so wucewa ba dole suka mike suka wuce nayi masu rakiya tare da basu tsaraban da na saka masu a leda suka wuce na sallami daddy ya amsa min cikin dadin rai.
Tare da dan yi min nasiha akan duniya bayan wucewan sune khadija tace wai anty may wanan matar ke nufi dake ne haka ?


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/11/20, 7:20 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , ,


🧕🏿7️⃣6️⃣🧕

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU KU


Washegari da rana uncle ke fadin gobe zamu koma Abuja maganan tafiyan yazo min a bazata don ban shirya komai ba namu.
Dole haka yasa mu shiri da tanadar duk wani abinda muke bukata a bauchi wanda muke so sai dai ba a cikin dadin rai muke shirin ba don rashin sanar damu da wuri da bai yi ba.
Sai dare na samu shigo gun hajiya baaba tana gani na tace ashe gobe zaku koma nace haka yace muna hajiya nima banda masaniya akan tafiyan.
Babana bai kyauta ba aika fadawa mutane su shirya ko amma haka da rana tsaka kace tafiya zakuyi nace baaba yadda yake so haka yake muna tace sai dai hakkuri shi kuma nasa halin ke nan gadara ga wanda yafi.
Abinda da ta tanadar muna ta nuna min inda nayi godiya tare da nuna mata farin ciki na akan hakan.
Tafiyan safe zamuyi don haka sauran kayan mu hajiyace zata turo min dasu ban samu koyin sallama da yan uwanshi badon ba lokaci.
Washe gari gare goma muna cikin garin Abuja a gajiya don akwai barci a idanun mu mun samu su mummy da gwago lafiya inda suke ta cewa bauchi ya karbe mu sosai.
Ni dai sai murmushi nake masu Uncle bai dade a gidan ba ya fita zuwa wurin aiki muma barcin mukayi don mu huta ranan Samira ta zo ganin mu da yi muna sannu da dawowa.
Motar kayan mu sai washe gari zasu taso don a hada muna kayan mu da kyau koshi sai da hajiya baaba ta roka muna saboda masan da nace mummy tace muzo mata dashi.
Mun dade da Samira a dakina muna hira sai dare yaya yazo ya dauke su suka tafi washe gari motar suka iso wajajen uku na rana da kayan mu ciki.
Sai da na kawar da komai yadda ya dace na dawo falo bayan nayi sallah laasar na zauna tare da mummy da gwago da suka fito falon.
Mummy ke fadin gwago sai kuma shirin gida yanzu ko kafin in magana khadija ta cabe zancen da cewa cabdi gida kan ai ba yanzu ba.
Don dai mai tafiyan yace wai sai yadawo kasan waje zamu tafi gwogo tace wane ni nan ashe ko zan barku anan don yanzu haka munyi suna fada min wai ragona ya kasa shekaran jiya.
Nidai ban yi magana ba tana ta fadin ita gida tayi bata kara lokaci sai mummy ce tace da gwogo din kada kuyi haka don Allah don baku san tsarin shi ba.
Ni dai abinda nake so ku saka mashi ido akan zance musanman ke gwago da kin yi magana zai iya sa ya zaci wani abu don Allah ku sa mai ido kubi sannu.
Tace shine kuma amma gaskiya badon nauyi ba da nayi gaba ni daga baya basai su su iso ba idan ya shirya masu tafiyan.
Nidai jinsu kawai nake yi da khadija ta matsa nace a zafafe aiko yanzu zaki iya tafiya khadija ba sai kin jira zuwa wani lokaci ba.
Sanin baka nayi mata yasa taja bakin ta tayi shiru bata kara magana ba a gaba sai kumbure kumburen da take faman yi ita kadai.
Gwago ma da yake kakace sai cewa tayi kun dai rike mu ke nan ke da mijin ki ai na gane nufin ku damu sai dan ku ya iya tafiya kila zaku bari muje gida.
Dariyan dole tasani nace wai gwago may zaki je gida kiyi ne don Allah baya kina nan hankalin ki kwance.
Da sauri tace ina ne hankali na akwance garin naku da haka ganin kowa kullun gaka gida a kumshe kamar kayan wanki.
Acan din yawo kike zuwa ne ba ko yaushe kina cikin soyan gyada da fitar da mai ba nasan duk wanan aikin ke a ranki.
Mummy tace ashe ki gane gwago dai ta juya wurin khadija da ta cika fam tace ta wuri kyale su kinji dole sai yadda sukayi damu yanzu mmutum ko hanyar fita unguwar nan bai sani ba balle ya guda.
Dariya duk muka kwashe dashi nan dai akai ta hira har lokacin sallah magariba yayi muka watse kowa ya nufi wurin sallah.
Yau kwanan mu biyu da dawowa bauchi kowa ya sake a gidan ba zancen zuwa gidan da suke min matsi a kan shi kuma.
Suna zaune falo na fito cikin wani dogo riga green color har kasa sai shape din da aka fitar ma rigan aka dan buda kasan shi sosai cup ne a hannu na na ciko da kindarmo dana dan zuba shikafa a cikin sa kadan ina sha.
Mummy dake zaune tana ba Abba abincin shi tana magana da khadija da ta mimike kafa saman kujera kafin in kai zaune nace ta kwashe kayan da ke saman sauran kujerran don Allah ta kawar dasu.
Tace yanzu nake magana ai don nasan gidan yan tsabta nazo ko tsinke ba a gani a gidan ku zama nayi ina ce mata yanzu wake son kazanta khadija.
Ai ba dadi ne aganka a waje fes azo gidan ka asamay ka ciki kazanta kin ga hakan ai ba dadi a riskeka ta yadda baka so ba.
Ta kawar da komai ta dawo zata zauna sai ga driver shi ya shigo da wasu kwalaye gidan yana gaishe mu da gida mummy ne ke tambayan shi tare kuke da ya bata amsa da eh sai naga sun shiga mikewa suna shigewa dakunan su.
Sai ni da khadija aka bari a wurin muna masu dariya ya shigo yana waya muna mashi sannu da dawowa yana amsa muna da kai kawai.
Dakin shi ya nufa ta kalle ni tace kamar kin san yana zuwa yanzu kika ce in kwashe kayan saman kujerun nan anty khadija nasan zai iya dawowa ko wani lokaci shiyasa ban yarda ya riske mu a hakan ai.
Fitowa yayi daga dakin bayan ya rage kayan jikin shi ya sauya wasu nan yazo falo inda muke zaune ya zauna khadija zata tashi yace No zauna abinki ba komai zanyi ba ai.
Ba ta dai zauna ba ta mike ta shige wurin su gwago tana dariya ya juyo gare ni tare da dan furzar da iska daga bakin shi yace ina son kiyi min list din abinda kike bukata na tafiyan ku.
Da wanda za a saiwa gwago da khadija ko kuma dai ki kira samira ku fita tare kiyo masu sayyaya don banda lokaci gobe ina son zuwa lagos in dawo gobe din kuma.
Don jibi nake son muyi tafiyan nan nakaiku gida kafin in dawo kin dan sha gida kadan, wani irin dadi naji ya ziyarci zuciyana a lokacin wanda ban san lokacin da nayi mai godiya ba.
Daga gwago har khadija duba dari dari ya basu su sayi abinda suke bukata na kasan su da zasu tafi dashi gida.
Sai kuma yace ke kuma ban san irin tsaraban da kike son ki tafi dashi ga dai wanan sai ki shiga kasuwa ki gani zan sa a kawo maki shadda da a tamfofi so ba sai kin saye su ba su.
Har kasa nakai ina mashi godiya tare da nuna farin cikina a gare shi waya aka bugo mai ya mike ya fita waje haka yaba ni daman mikewa zuwa masu bayani a dakin su.
A dakin su na shiga da sallama na nan na samay su suna hira ana dariya na zauna tare da fito da kudin ina mika wa kowa nasa sai kallo na suke yi da mamaki a fuskan su.
Nace Uncle yace na baku wai gobe a shiga kasuwa a sayo wa kowan ku abinda take so na tafiya shiru dakin yayi na dan wani lokaci.
Sai mummy ne tace Allah ya umfana ya saka da alheri yayiwa dukiya yawalta nace amin mummy gwago ta bude baki da kyat tace ni na rasa abinda zance wallahi.
Shi baya gajiya da dawainiya ne kullun kazo da alherin da za a bika dashi haka ba kadan ba kuma ?
Haihuwa ne tayi ranan ta inji mummy hakurin yar ku ne yaja maku haka da Safiya bata da hakkuri a rayuwa da ba acin ma hakan ba.
Biyayyan aure ba abinda baisa miji yayi ma mace da yan uwan ta sai aga kaman wani asiri take wa mijin yake sakar mata hannu haka.
Nan ko mutane basu san iya hakkuri da diya mace ke hadewa a dakin auren ta ba sai idan dadi yazo ne zakaji ana fadin ta mallakeshi ne musanman dangin miji.
Sun fi jin zafin macen da mijin ta ke yawan kyautata mata da yan uwanta koda yana ma nashi yan uwan sai suga ai yafi kyautatawa matarshi da yan uwanta.
Gwago tace haka abin yake a ko wani gida wallahi mu dai bamu da abin da zamu ce wa wanan yaron sai dai muyi mashi fatan alheri da gamawa da duniya lafiya.
Duk muka ce amin dakin nan khadija ta shiga rawan kai tana lissafo abubuwan da take bukata na rayuwan ta.
Gwago tace ke arr wawiyar banza baki lissafin kayan daki ba sai shirmay kike faman lissafa muna kawai ko kwabo bazaki taba ba cikin kudin nan.
Uwarki za a kaiwa su gida idan mun koma lafiya take ta turo baki gaba tana magaba kasa kasa.
Rankwashe gwago takai mata akai nace gwago rabu da ita don Allah kudin tane fa yaba ta ne don bukatunta mana.
Tace kaiyya yaro mankaza yanzu har dake kike bata shawara ta kashe kudin nan ga banza ba zata kai ma uwar ta tasai mata abin kwarai ba.
Nace haba gwago ayi fatan a samu wadata mana kafin auren anci gaba ai gaba gaba muke fata a rayuwan mu shiru tayi nace khadija barin buga ma Samira waya ta shigo gobe sai mu fita kasuwan.
Khadija ta fara murna ji zan barta tasai abinda ranta ke so gwago tace miko min kudin nan baza ki kashe su duka ba mara hankali kawai.
Tace anty wai may yasa kika bani nawane a gaban gwago yanzu zata sakani gaba da tsegumi wallahi bayan itama an bata nata ta kulle a lalitan ta.
Gwago zata taso tabar dakin da gudu tana dariya ta juya gare ni tana fadin Allah dai ya shirya ku mummy tace ai idan zaki kara mata da naki indai yaran yanzu ne tas zata kashe su wallahi.
Ban zauna ba nabi yar uwana muka zuwa daki nan muka zauna muna hiran da ita har na kira samira tace zata shigo goben mu fita.
Washe gari Uncle yayi asubancin barin gida kamar yadda yace bayan yaja min kune akan kada mu dade idan mun fita ya kama hanyan airport.
Sai misalin sha biyun rana samira ta shigo gidan bamu jima ba muka tafi bayan mungama zolayan gwago ta kawo kudin ta a kaso mata.
Tace Allah ya tsari kakanta kande da tashi fatalwa ai idan mun anshi kudin nan a hannun ta kashe ta mukayi.
Bamu dawo gida ba sai da muka cika bayan hilux din da muka shiga kasuwa dashi fan na hado tsaraba mai himilin yawa muka dawo gida karfe biyar da wani abu na yamma.
Mun shigo a gajiye mummy tana muna sannu da zuwa gwago dake daki tafito tana daura dankwali a kanta tana fadin .
Yau kan akuyan daure ta samu saki naso ace mijin nan naki yana gari inga karshen yawon ku sai da aka fara shigo muna da kayan ne ta kama fadin dan kari.
Ban tsaya ba na shige daki wanka nayi na rage kayan jikina n tare da jero sallah da ake bina na fito falon.
Sannu a hankali muke bude kayan da ba ayi packeding din su ba muna gyawa dani da samira da mummy muka hade komai gwago na kallon mu.
Sai dare uncle ya iso gida don tafiyan yini yayi ranan tunda ya shige bai fito ba sai washe gari nan yake fadawa gwago washe gari zamu tafi in Allah ya kaimu.
Murna wurin gwago ba a cewa komai do haka ban samu kaina ba ranan sai faman shirin tafiya nake yi sai yamma na samu kaina na huta.
Kayan da uncle yaga na dauka yasa shi yin magana wai yaushe ne zaki dawo wanan uban kayan da kika dauka haka ?
Nace ko kwana nawa ka bani ai shi zanyi bakari cikin sa murmushi ya gyara zama yana fadin kwana hudu yayi maki ko da kallon fuska na don son jin amsan da zan bashi a lokacin.
Nace na gode Uncle ya ce ki kwanta don sammako nike son muyi don inje in dawo gobe din don jibi zamu daga zuwa Egypt.
Mun raya daren mu cikin dadin rai inda nayi asubancin tashi tare da tayar da su gwago muka shiga shirin tafiya kafin shida duk mun shirya ko .
Ban san da yaya Saadu za ai tafiyan ba sai da yazo da safe yake fada muna ai dashi zamu tafi inda mummy zata je fatakwal kafin mu dawo ta duba yaran ta nacan amma ba ranan zata tafi ba gidan yaya Saadu zata dan zauna tukun.
An gama saka kaya a motocin da zamuyi tafiya dashi mu uku baya su biyu da yaya Saadu a gaba sai dayan motan driver da wani mutum ke ciki da kayan mu wanda ban san mutumin ba ko gaisuwan kirki bamuyi dashi uncle ya tsare ni da ido.
Ban son yawan gaisawa da mazan da ban sani ba duk da wurin shi suke zuwa amma da naga bai so sai nima nake share su kawai.
Don ko zuwa da ma aikatan su sukayi da na haihu ba karamin fada yayi ba daya dawo wai na zauna wasu kattan baza suna kallo na dama suma abinda ya kawo su ke na don su ganni saboda sun ga bai gari.
Wanan abin tun yana bata min rai har nagaji na bari don halin shi kishin maza irin na haukan nan har ba a san abin fadi ba.
Shida yaya saadu ke fira sai jefi jefi nake saka masu baki daga inda muke zaune a bayan motan don gudun zurewa ya kuma samu abinda yace nayi mai abinda ba dadi don ba freedom yadda ya dace.
Tunda zamu taso na buga ma ummi na waya cewa zamu taso don haka ayiwa su uncle abinci kafin mu iso don yau zasu juyo su.
Mun sauka mi salin kare biyu saura na rana don ba karamin gudu yaya yake yi ba shiyasa muka sauka da wuri wani iri nake ji a raina yau zanga yan uwana da iyayyena dana dade ban gani da sauran abokan arzikin mu.
Tunda aka ce gamu mun iso yan uwana sukayo waje da gudu don taron mu abin gwanin ban shaawa kaina sukayo ni da khadija.
Da murna muka rungumay juna kowa yazo kokari yake ya rungumay ni kamar bani bace safiyan da suke gudu da karna shafa masu cutan dake jikina a baya.
Sai gashi yau sanadin auren mai kudi da samun gata an manta da komai da ya faru a baya an koma kamar ba a yi ba muryan shi naji a bayan mu yana fadin.
Watau yar uwarku kawai kuka sani baku san kowa ba ko nan suka shiga mashi sannu da zuwa wasu suna fadin ashe da mijin ki kuka zo yaya saadu yace ai kauyawa ne wa yan nan.
Nan muka shiga gida suka dinga kwaso kayan da yaya saadu ke dora masu yana masu sheri irin na tobasai uncle sai murmushi yake yi kawai .


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/11/20, 8:20 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , , ,


🧕🏿7️⃣7️⃣🧕


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU


NOVEL DINA NA KUDI UBANGIJI YABI MIN HAKKINA AKAN WACCE KE FITARWA DAGA GROUP DINA ALLAH NA KAI KUKA NA GARE KA KA BI MIN HAKKIN CIN AMANA AKAN KO WACECE, , ,

Ya ubangiji Allah kayi gagawan daukan min fasa akan muna fuka ko munafukin dake fitar min da hakkina waje.
Ya Allah kayi gagawan amsan min hakkina akan wanda duk yafitar da novel din nan waje ko wacece annaminiya mai fuska biyu ko a lahira Allah ya baiyana ta gaban jama, a wacce bata da amana kawai.
Sai dai dadin abin na fada tun farko na kudi ne kuma online novel ne kika yar da kika shigo group din Alhamdullahi ina jin dadi idan na tuna hakan.
Mun shiga cikin gida su mama da ummi sai taron mu suke yi da fadin maraba da mutanen Abuja suna kokarin amsan Abba dake hannun yara.
Idon kowa na a kaina har muka karaso cikin inda kofan dakin ummi yake muka nufa ciki muka shiga da farin ciki a zukatan mu.
Daga mu har mahaifiyar tamu da akewa lakani da uwar mata don mata mun fi yawa a cikin yaranta.
Kayan da nazo dashi ake ta faman shigowa da su gidan ana jibge su dakin ummi na kofa kuma suna ajewa a kofan dakin.
Mun tasa ummin mu a gaba da kallon yaushe tabo aga juna sai muryan yaya saadu mukaji yana fadin a kawo wa baki ruwa mana.
Da sauri ummi ta tashi ta hado ruwa sanyi a cikin plate taba yaro ya kaiwa mazan dake waje da sauri nace ku rage kayan nan da kuka tara nan ashiga dasu ciki da sauri yaran suka fara kwasan kayan suna shigewa dasu.
Uncle ne da yaya Saadu suka shigo gidan da sallaman su nan su mama da ummi suka shiga kankantawa don suruki ya shigo a lokacin.
Sai lokacin na lura tun shigowan mu ban ga inna ba a gidan ina tambaya kafin mama ta bani amsa yaran dake wurin su ke fadin tana daki bata da lafiya.
Subbahanallah nace tare da kara tambayan su bata da lafiya may yasamay ta ?
Ina fita daga dakin dake cike da yan uwana da abokan arziki da suka shigo taro na da zuwa jin murya na inna tayi dan tambayan yanta sai gata ta fito waje tana yamusan fuskan ta alaman akwai yani guri dake matsa .
Gaishe ta nayi tare da tambayan yaya gida tana tambayan uncle nace tare muka shigo dashi gaya can dakin ummi.
Yaran dake cikin dakin khadija ta koro zuwa waje nan dai suka samu gaisawa da su ummi da mama sai gwago dake ciki zaune dasu.
Sun yi wa ummi yaya hanya Allah yasa makasudiya ce ummi ta amsa da amin tana dada godiya yana fadin bako mai ai mama.
Muryan baba ne ya shigo gidan da farin ciki dakin dan ganin su sannu da zuwa yake ta faman yi masu suna amsawa cikin alkunyan daga inda yake yake tambayan ina yaron yake jin muryan baban mu da nayi yadawo gida yasa na juyo na bar wurin inna din da nake tsaye.
Yana tambayana na amsa mashi daga inda nake tafe a bayan shi da fadin baba mun samay ku lafiya na durkusa har kasa ina gaida shi.
Yace tashi tashi yar albarka ashe yau kuna yafe garin namu ne sai da safe Rabi ke fadin kin ce yau zaku zo.
Murmushi nayi kai na kasa nake fadin baba an dawo lafiya Allah ya karba ibadun da akayi yace amin amin yana karban yaron da shafiu ya fito dashi wurin abokan su yaya sani a waje.
Yace ikon Allah yaron ke nan yayi wayau haka tubarkallah masha Allahu abu ko yayi kyau wallahi sosai yake fadi ni dai murmushi nayi daga inda nake tsugunne ina gaida baba ya juya zuwa sashen shi dauke da yaron a hannun shi.
Dakin na koma inda na samu ummi tasa khadija ta baza masu uncle da yaya kayan abinci suna ci a falon nata sai kuma wanda ta bayar akaiwa driver da muka zo dasu waje.
Dakin na shigo yaya saadu ke fadin Safiya ki debi abincin ki ci mana ga gwago nan tana cika cikin ta itama nace ai zanci ba yanzu ba yaya .
Sun gama sun tashi zuwa dakin baba don su gaisa nan yaya Saadu ya barshi dakin tare damu inda yace ummi ina ganin na fita ke nan don zamu kama hanya da wuri muke son barin garin nan.
Daga inda nake zaune a gefen shi ya juyo yana kallo na tare da fadin ina ganin sati biyu ko uku zanyi acan so zaki yi kwana goma zan turo Saadu ya zo ya dauke ku kafin in dawo daga Egypt din .
Wani dadi naji har cikin raina kamar na sani kwana hudun da yace zanyi kawai na dai dauko kaya daya fi na kwana hudu kamar mai shirin yin wata daya.
Ya kirgo kudi ya ba ummi masu yawa ya kara kirgowa ya ba gwago tare da khadija sai kuma su shafiu dake dakin suma ya basu already ya bani tun kafin mu zo.
Nan ya fita sun dan jima da baba ya fito bayan yayi mashi alheri yaba su mama nasu tare da sauran yaran gida bamu samu yaya sani a gida ba ko da muka zo.
Mun fita rakasu ne na hango shi can ya tsallaka wurin datawan unguwan mu da matasa yana masu alheri abinda ya sauka a gare shi.
Sai dai na lura bada motar zasu tafi ba saboda ganin sun shiga hilux din da takawo muna kaya da zamu zo haka yasa na gane bada ita zamu koma ba sai wanan mutumin kamar security yake a gare mu ashe ma a nan zuwa dashi ke nan da mukayi
Ya dawo na dan dade gaban mota muna magana dashi mutane sun kura muna ido a zaton su wani hiran dadi mukeyi a lokaci.
Amma a zahiri warning dina yake yi da baison yawo ya barni gida ne in dan jima don ganin yadda yan gidan namu suke kewan gani na.
Wanan abin yake fada min wanda bai sani ba sai yayi zaton wani hira mai dadi mukeyi a lokacin kasancewar duk fuskokin mu yana dauke da murmushi ne a lokacin.
Nan mukayi sallama suka ja mota suka tafi yau gida yayi bakin abuja cike dakin ummi yake da yaran gidan mu suna min hira shafiu ko yana makale da Abba bai bari kowa ya dauke shi cikin yaran.
Sai da suka rage a dakin ya rage sai mu da yan dakin kade a lokacin nake cewa ummi wai may ke damuwan inna ne haka ta zube a lokaci daya ?
Shafiu yayi saurin cewa injin bakije dakin ta ba anty da sauri na kalle shi nace may ye a dakin nata da ba a shiga ?
Yace ance ciwon tari ke damun ta don haka baba yayi muna kashe a kanta da kuma taba kayan da tayi amfani dashi don gudun daukar cutar gare mu.
Wani irin ras gaba na yaba da a lokaci daya nace ummi da gaskiya abinda ke damun inna ke nan shine ba afada min ba ko a waya.
Hankali na ne bai kai da in fada maki ba ai hakan bai hanata rashin mutuncin da ta saba yi ba a gidan shiyasa malam ya kafa doka akanta har yaranta.
Nan dai suke muna hira yadda abin yake mata da dalilin daya baba har ya kafa mata doka mai tsanani a gidan kamar yadda likita yace a kiyayye don gudun daukan cutar.
Gwago ce da zata gida muka fito sai lokacin na ke magana da baba don aba driver da wanan mutumin da ya bar min zamu zauna dasu don kaini wurare inda zasu zauna.
Baba yace a gyara masu dakin yaya Sani don dama shi driver ya saba zuwa tun kafin muyi aure da uncle ya zama dan gida yanzu.
Nasa shafiu ya gyara dakin tare da kai masu abubuwan bukata a dakin don bukatun yau da kullun.
Da yamma yaya Sani ya dawo garin nan ya samu mun zo da murnan shi ya shigo dakin ummi yana taron mu ya samay ni zaune Abba na kuka ina lalashin shi .
Yace ummi ashe yau baki ne haka a gidan namu khadija ce ta leko daga kuryan daki tace yaya sani oyoyo yace ho yar birni an dawo tana fitowa yace kai kai kai.
Ummi ki ko ga yadda yarki ta koma wata big girl haka wai ma tsaya naga alaman fa kin cinye masu kayan abincin gidan su fa khadija.
Nace wane ita tadai ci iya cin ta ta dawo ta bar muna saura yaya ka dawo lafiya mun zo bamu samay ka gashi har da mutumin ka muka zo yau din.
Yace haka naji tun a waje nazo na iske su Adam nata washe baki yau a jike suke dumus suke labarta min sai kuma naga musa drivern ku a waje.
Nace nan ya barsu wai zasu kula damu a nan kasan mutumin naka bashi da yarda don wai kada in ta yawo mutane suna gani na.
Dariya sukayi har ummi tace ai shine maganin matan yanzu da basu mai da fita a bakin komai ba sai kiga mace ko bada sanin mijin taba ta saba gyale akai ta fita.
Yaya Sani ne yace ummi ai har mata kauye yanzu sun koyi wanan dabian kwana ki nan rikice ya barke tsakanin isah da matar shi wai taje buki bata fada mai ba sai dawowa tayi gida ya samu ta
Ummi tace kaga abinda ke sauri halaka mace a yanzu don ace da mijin ka ya dawo gida daga tafiya ya samu mace bata gida.
Gara ya dawo ya samu gawan ta a gidan yafi sauki amma kin ga matan yanzu basu damu da wanan abubuwan ba sam.
Khadija dake shiri fita waje tace cabdi yanzu kan ai sai Allah ya gyara kawai dama akwai irin su anty masu tsoron miji kin ga yadda take tsoron mijin ta kuwa ummi .
Ummi tayi saurin katse ta da cewa masha Allahu ai gara da naji wanan shedan da kikayi wa yar uwar ki din don yanzu na gamsu da irin tarbiyan da na dora ku a kai.
Kallon ummi tayi kawai ta girgiza kai irin watau ummi din bata san komai ba ke nan yaro yayi sallama yashigo da abinci yana fadin inji Saadatu tace ya kawo wa baki.
Karban abincin nayi ina ma yaron godiya na ce shafiu ya bashi dari biyu a cikin jakkana dake kusa dashi.
Yaron yana godiya ya fita nace ya gaida ita ummi tace Allah sarki wace ke fama da kanta kuma har da kokarin kawo abinci haka.
Yaya Sani yace ummi ai shine zumuncin ko yayane kaima dan uwanka shima yasan ka damu shi ba kullun sai dai aita baka ba kana karbewa.
Hakane inji ummi tace naga tana cikin yanayi ne kawai mijin nan nasu yana ta kan shi yanzu ba wani sana a mai karfi yake yi ba.
Bude abincin nayi inda naga tuwon masara da miyar busassan kubewa da kifi bussashe ba wasu manya ba miyan yana kamshin dadawa da kayan yaji.
Zama nayi muna hira da yaya naci abincin sosai don na dade banci irin shi ba sai mamaki suke yadda nake kai loman tuwon a bakina ina yaba dadin da tuwon yayi.
Yaya sani ya fita ina shan miyar ummi tace da alama miyan yayi maki dadi sosai ko ?
Nace wallahi ummi naji dadin miyar sosai don na dade ban ci miyar kubewa busassa ba tun bari na gida fa ummi.
Sai bayan da na wanke hannu na dawo na zauna nake tambayan ummi may ye matsalan mijin saadatu ne wai ?
Tace masu bashi kayan ne da farko suka daina yanzu wai don ya auri Saadatu din ashe dama wani dan uwan matar shi ne yake bashi kayan yana sayarwa.
Kai na girgiza kawai ba tare da na furta komai ba sai dai cikin zuciyana ina tunanen may ya kamata nayi akan maganan ne ?
Ranan mun kai wani lokaci muna hira da ummi na inda take goye da Abba a bayanta acewar ta wai zai dade yana barci idan ya kwanta ga ruwan zafi daya sha a jikin shi ya gasu sosai a wurin mama da tayi mashi wanka.
Khadija kan tun da ta shigo ta kwanta tana sauke gajiya a gida wanda ta dade tana kewan gida a ranta don zamanta na abuja a matse take ba fita ko ina.
Washe gari ban tashi da wuri ba don dadewan da mukayi da ummina muna hiran yaushe rabo tare da ita daren jiya din.
Shogowan dan gidan da Ainau ke aure yar wurin anty da kwanon kosai da koko na daka wanda yasha kayan kamshi yana tashi a cikin shi yace wai ance ya kawo wa bakuwa da tazo daga Abuja.
Fitowa nayi don in ba yaron wani abu don naji ummi na sallaman shi tana fadin kace mata an gode kaji na fito ciki ina fadin ga wanan a bashi kace ina gaida ita na gode kwarai.
Wanan abin da yan uwana suka yi min naji dadin shi sosai a raina hakan na nuna yaran gidan mu akwai hadin kai sosai wurin son junan mu.
Ban fito ba sai da nayi wanka na shirya cikin wani dogon riga mai taushi na fita zuwa gaida mutanen gidan mu.
Dakin mama na fara zuwa tana ciki sun baje da yaranta suna karyawa na shigo dakin da sallamana a dakin na samu Abba a bayan mama tana goye dashi yana barci.
Na dan dade dakin muna hira dasu sai na tashi zuwa dakin inna inda na samay ta zaune a falon dakin ta tana zaune ita kadai yaran dakin ta duka suna kofan ummi na suna karyawa a lokacin.
Na shigo da sallama na nace inna ashe baki ji dadi bane haka ta gyara rufin zanin da ta rufa a jikin ta tace wallahi ke dai safiya.
Ciwo wasa wasa gashi sai gaba yake min nace inna kuna na asibiti kuwa tace tau safiya waye zaiyi jimirin kaini asibiti ko wani lokaci.
Tausayi tabani sosai nace to inna sai a zauna da ciwo haka a gida ai gara dai a tafi asibiti a gani zaifi hawayen da yazo matane ta shere a fuskanta
Tace safiya yan uwan ki kowa gudu na yake yi a gidan nan har malam din kanshi guduna yakeyi yanzu wakike gani zai kulani a hakan bayan duk suna tsoron zuwa kusa dani don cutar da nake dauke dashi.
Koma asibitin nace zan tafi ba wasu kudi issasu a hannuna da zasu kaini ance maganin tsada gare shi wai.
Ba komai inna bari yaya sani ya shigo sai muji yadda za a yi amma ai ba a zauna haka da ciwo a gida ba kullun yana kara maki illa a jiki haka ?
Abin mamaki sai ga inna tana cewa da bakin ta ubangiji Allah yai maki albarka safiya na gode kwarai wallahi Allah ya kara arziki , .
Mikewa nayi nace bakomai ina har na kai kofa nace ki ko karya tayi murmushi kawai tare da fadin abinda akace inci ne ba samun shi nakeyi ba akai akai.
Fita nayi daga dakin inda ban koma dakin mu ba baba bai gida ya tafi zanen suna tun da safe ya fita gidan don haka na leka waje na kira yaya sani yana zuwa nace mashi.
Haba yaya sani kasa halin da inna take ciki shine kuma ka kyale ta haka a daki ko karyawa batayi har yanzu ace mara lafiya bai karya ba har wanan lokacin.
Humm yace safiya jiya da mijin ki yazo ai ya basu kudi ina takai nata nace babu ruwan ka yaya ladan haihuwa zaka nema a wurin ta ai.
Ba zakayi fatan kaga ka rama mata abinda tayi maka ba kana yaro yanzu har zaka tsaya yaya duban wai tana da kudi tayi amfani dasu .
Ka sani ko tana da abinda zatayi da kudin data samu jiya don Allah yaya ku daina wanan hali kune fa manya a gidan nan da zamuyi koyi da halin ku na gari.
Yace wani yanzu ai mun baki girman safiya kece antyn mu kaf a gidan nan mun biki mun bi Allah don shi ya baki girman dariya ya bani har yasa na kasa karasa maganan da nake mashi don banbadancin da yake zuba min a lokacin.
Nace ni dai yanzu muje in baka kudi ka sayo mata abinda ya dace zan maka list din komai ta fara karyawa kafin mu je asibiti da ita.
Yace amfa je asibitin ita ce taki yarda ai mata alluran wata uku da sukace zasu yi mata wai karya da kazafi ake mata akan ciwon.
Nace inma da tace karya ne yanzu batace ba don munyi maganan da ita daga dakin ta nake yanzu ma yace tunda ke ce ai yanzu ta yarda.
Mun je dakin na kirga kudi na bashi anan muka aje magana zai dauko wanda zai mata alluran da aka rubuta mata tayi din da magani sai yazo zamuji ko nawa za a kashe sai a fara mata alluran ranan.
Kunun da Ainau ta kawo min na zauna nasha ina wurin zaune na dauko waya na kira uncle yace ya kirani bai samay ni ba gashi zasu tafi airport yanzu Allah ya tsare nayi mashi muka kashe wayan bayan ya tambayi Abba dasu khadija nace suna lafiya.
Tsaraban kayan abincin da nazo dashi na fara raba sai kuma na shiga rabawa yan gidan mu tsaraban da nazo ma kowa a gidan mata sun samu turamay zannuwa da sabulai da man shafa ida maza shadda na raba masu da turare da takalmomi matan sun fi maza samun tsaraba sosai dana kawo masu.
Yaya sani ne ya shigo da malamin asibiti muka shiga dakin inna dashi inda yayi bayanin a gaban ta da abubuwan da zata daina ci da wanda zataci har tsawon wata uku .
A gabanta na biya kudin komai da za a yi mata kukan da ta fara ne yasa na bar daki na koma dakin ummi jiki a sanyayye ida yan gidan mu kaf suke dakin na ummi khadija tana masu hiran abuja da bauchi.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/12/20, 7:42 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , , , ,

🧕🏿7️⃣8️⃣🧕


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU


Muna tsaye kofan inna muna kallon yadda likitan yake mata allura zabban tausayi har ya gaba ya fito yana cire safan hannu da takunkumin da ya rufe hancin shi dashi inda ya jefa a wani leda zai fita dashi.
Nan yake fadi a gaban kowa yace a kikyayi zama kusa da ita a daina amfani da duk wani abin amfanin ta don ciwo ne mai saukin dauka ga mutum idan da hali a raba makwanci da ita.
Kuka inna ta saka mai ban tausayi tana fadin ni rakiya yau naga ta kaina na zama abin gudu har ga diyan da na haifa a duniya.
Daga kofa inda nake nake fadin cikin murya mai rauni inna kiyi hakkuri ciwo ba mutuwa bane zaki samu lafiya in Allah ya yarda adai kiyaye abin daya fada kawai.
Yaya sani yace yau bagaki ba safiya may ye ba ayiba a lokacin ciwo ki a gidan nan wanda ba kowa ya sa ai maki ba sai ke inna ina fada maki ki bari amma kamar zugaki nakeyi a gidan nan.
Har kika fara gaba dani ummi gata da ranta ita tayi min fada akan in bi maganan ki in bar fushi dake komai Safiya ta taba a gidan nan damun bi ta naki inna kona shi zamuyi a lokacin.
Likita yace ai wanan ciwon yafi kanjamau saurin kisa yanzu baga safiya ta gyagije ba kamar ba a yi ba da ta fake magani .
Ai ba a gudun mai kanjamau kamar may irin cutar nan don saurin dauke gare shi sosai ga wa yanda ke kusantan ka sai kawai mukaji inna ta saka wani irin kuka mai kama da ihu a lokaci guda duk muka rudu ga kowa na tsoron shiga dakin wurin ta don kada ya kamu da ciwon.
Nayi kundunbala na fada dakin ina bata hakkuri sai fadin take safiya dole inyi kuka cutar nan kila kasheni zaiyi safiya.
Ina naje dana dauko wanan mumunan cutar a jikina yaya sani shima ya shigo daka ciki muna bata hakkuri likitan yace idan zamu shiga wurinta mu dinga saka takukumi a hancin mu dau saukin shakan nufashin ta.
Mun fito muka sallami likitan na bashi duk wani abin bukata har zuwa lokacin da alluran zai kare.
Shigowan Saadatu ke nan gidan da goyon ta wanda yayi wayo sosai yaron ganin mu a kofan dakin inna yasa hankalin ta ya tashi bamu ko gaisa ba take tambayan mi may ke faruwa ne ta gamu cirkocirko haka tsaye ?
Bakomai na fada ina karban dan dake goye a bayan ta amma sai yaron yaki zuwa wurina don kiuya irin na yara da yake dashi.
Dakin ta shiga ta ga uwar a zaune a tsakiyan falon ta tace inna yaya jikin naki tace da sauki nan dai ta dan tsaye, tsaye jim sai ta fito waje.
Lokacin na koma bangare ummi na ina batun aika yaro yakai ma mahaifiyar Amina sokon a gidan su sai da nagama bada sokon na juyo gareta ina Saadutu an shigo ashe ?
Gaisawa mukayi tare da tambayan lafiyan su sai godiyan abincin da ta aiko min dashi daren jiya din da tayi shima nayi mata godiya akan shi.
Tace kai don Allah nasan ai bazakici ba na dai aiko ne kawai kada dan uwanka yazo gari baka aika mai da komai na sannu da zuwa ba.
Kika ce wai ba zanci ba toga ummi nan tambaya kiji sai da naci fiye da rabi nakuma shanye miyar tas wallahi taji sadi don fuskanta yanuna hakan.
Tace ikon Allah har abokiyar zama na fadin wai zan dai kawo ne amma ku yan birni ai ko kallon wanan abincin bakuyi ai haka dai na daure na kawo maki shi.
Nace aini banki ba kullun kina kawo min irin wanan din don ina son shi sosai wallahi samu dai ne ban yi a can.
Ikon Allah na katse ta da fadin yaya Adamu maigidan ki yake dariya tayi tace mutumin ki yana nan lafiya wallahi sai dai yanayin garin da muke ciki yanzu kawai amma ya daina halin nan yanzu lafiya lau muke dashi sai abinda ba a rasa ba.
Tace ai yaji dadin kudin da kika aiko mai kwanaki har ya fara sana a sai wa yanda suke sana,an tare ashe suna bishi kudi nan sukayi karan shi karshe har da na wurina muka hada aka bashi yanzu yana zaune bai komai kuma.
Na tausaya mashi nace mutum magidanci ya zauna ba sana,a haka ai abin baiyi ba wallahi tace ai yace yana nan zuwa ya gaida ke da zuwa.
Nan Ainau ta shigo gidan itama da goyon ta muka hade mu uku duk sun girmay ni amma samun wuri da kuma maganin da nake sha wanda ya hurani na danyi kiba ba sosai ba.
Anan muka wuni tare da su inda na dauko masu tsaraban su na basu sai farin ciki sukeyi da murna ga abinda na basu din.
Sai yamma suka tafi gida inda nace masu idan na huta zan shigo gidajen nasu mu gaisa na dan raka su na dawo na dibi ruwa zan watsa ma jiki sai ga shafiu ya shigo da Abba a hannun shi yana fadin wai ga Adamu nan mijin Saadatu yazo gaida ni ya shiga ya gaida inna da sauri na mayar da rigan dana cire a jikina kafin ya shigo dakin ummi din mu gaisa dashi.
Da sallama ya shigo ina saman kujera na mike ina ce mashi ga wurin zama nan ya zauna yace a a zai zauna kasa na hana shi dole ya hau kujeran ya zauna.
Ni kuma na koma daga kofan kuryan dakin ummi na fara gaida shi yace kunzo lafiya nace Alhamdullahi yace to barka da arziki ashe an sauka murmushi nayi yace bamu ba da komai ba sai kuma ga sako na gani nagode nagode kwarai Allah ya kara rufa asiri.
Nace kai haba bakomai wallahi kasuwa dai yana tafiya yanzu ko na tambaya kamar banji komai ba a kan shi yace tau Alhamdullahi zamu ce hajiya don ba a cewa komai sai hamdala.
Amma gaskiya yanzu komai ya tsaya ne cak wallahi kudin da kika turo min kwanaki na fara dauko mai jerka biyar dashi tunda wa yanda muka fara sana, a dasu sukaga na dan samu suna bina kudi sai sukayi karana dole na hada kan kudi na biyasu abinsu shine yanzu nake zaune ina zaman ba sana a .
Kin san ance wanda ya amshi kudi hannu mace yana tare da gori komai daren dadewa to abinda ya cini ke nan dama yan uwan matane suke bani yanzu kuma wanan abin daya gitta har na auri saadatu sai suka karbe dukiyan su a hannu na suga yadda zanyi watau.
Dariya nayi nace baduk mata suke haka ba ai wasu dai ne haka suke shiyasa nima banyi maganan komai da Saadatu ba har tazo ta wuce ta dai fada min kamar yadda ka fada min yanzu din yanzu a misali idan na baka dubu dari biyu zasu isheka ka fara sana,a mai dan kauri dasu.
Hajiya dari biyu ai ba karamin kudi bane yanzu nace to zan baka sai ka fara mu gani ya katseni da cewa har zuwa yaushe zan maida maki kudin ina mikewa nace a a baka nayi halal malak kaja jari dasu ba rance na baka ba ni kyautan su na baka.
Zamowa yayi saman kujeran da yake zaune da farko ya hada hannayen shi biyu a wuri daya ya fara zabga addua da fatan alheri a gare ni.
Nace ba sai ka fadawa kowa ba Adamu nidai bukatana a gareka shine ka rike min yar uwata amana don Allah ka kula dasu dukan su ukun matan kane.
Godiya ya kara min yana kokarin tura kudin da ya karba a hannu na cikin aljihun rigan shi tare da yi min sallama har yake kofa ya juyo yana fadin gobe gobe in Allah ya kaimu zanyi asubancin zuwa birni wurin saro man in sayo.
Nan dai ya fice cike da farin ciki nikan yana fita daga dakin na mike don duk zafi nake ji a jikina ina son in dan watsa ruwa inji sayi.
Kafin wani lokaci gari kowa yasan na zo wasu idan sunga mota a wajen gidan mu ne suke tambayawa a fada masu.
Wasu kuma idan na aika masu da tsaraba suke sanin na zo garin ban fara fita ba sai da na kwana uku yan uwa da abokan arziki suna zuwa gaida ni suna kuma aiko min da abinci da dan abin marmari don kulawa.
Har da makwata dana ba tsara ba sun shigo taro na da gani dan da na haifa wasu dai gulma ne ke kawo su ganina kawai suga yadda ake fadin na koma yanzu.
Gidan mummy mahaifiyar Amina kawana na fara zuwa inda musa driver ne ya kaini gidan shi da security din mu na dade gidan muna hira da mummy inda nace ai zan shiga wurin Amina kafin in koma in Allah ya yarda.
Ina fitowa na wuce gidan su mama jummai na gaida su suma duk inda naje sai na jima a gidan daga wurin su na dawo gida.
Duk abinda nasan inna naso wanda akace tace na sa yaya sani ya sayo mata inda nayiwa yaranta nasiha su kula da uwar su don Allah.
Wanda ba kowa ta jawo hakan ba ga yaran gidan mu sai inna din don batayi zoton abin zai shafe ta ba haka.
Washe gari gidan Ainau na fara zuwa tun da safe muka fita sai karfe daya na bargidan na wuce gidan saadatu .
Gidane may irin dakunan nan ajere suke guda hudu sai baranda ba wani siri da mutum zai iya yi ba a ido yan uwa ba.
Yaran gidan sun kai bakwai saadatu ne ke da daya a cikin su na samu wata mata da daure gaba tana tuka tuwo a tsakar gidan inda suke girki.
Yin sallamana yasa sauran fitowa daga dakunan su mai tuka tuwon tunda tayi muna sannu da zuwa ta mayar da kai ga aikin ta bata kara juyowa gare mu ba.
Tare da su khadija muke muka shiga dakin saadatu din daki daya ne single da gado da mirrow sai drower gadon dake gefe an dagwara mai roses guda guda da ledan kasa malale a dakin .
Kujara mai zaman mutum uku damai zaman mutum daya sune a dakin zama mukayi aka fara gaisuwa a tsakanin mu saiga wanan matar da tafita tare mu dauke da kwanon sha cike da ruwa ta kawo muna.
Tana fadin safiya ko ai yanzu bata gane ni tunda an dade ruwan na karba na sha nace wallahi kan ban gane ki ba yar uwa tayi dariya tace mune senior ku don muna gaban ku da shekara uku sai dai ni ban gama ba nayi aure lokacin mai yawo dasu Aisha sani na kusa da gidan ku.
Nan dai suka shiga min bayani ita da Saadatu saida na gane ta nace ankoyi haka tace gamu mun hade da yar uwarki muna auren miji daya yanzu.
Allah sarki nace kuna lafiya yaya yara yaron ta karba a hannun kauna na yar wurin mama da muka zo da ita tace tubarkallah yaro yayi wayo sosai.
Mun dayi hira ta fita dakin mukaci gaba da hiran mu na abinda ya shafemu na gida maigirkin taba dan tuwo kasan kwano a kawo muna mukace a maida mata a koshe muke mu.
Sai lokacin ta shigo tana fadin bazakuci abincin mu ba nace gidan Ainau muke sunci taliya acan ni kuma na koshi yanzu ganye kawai nake son in samu inci.
Ta juya ta wuce saade tace ganye kike so nace eh tace barin nemo yaro ya sayo maki sai khadija tace baga maimu na ba abata taje ta sayo bakin kasuwa mana.
Dubu daya na zaro a jakkana na bata tace na nawa nace ta sayo na duka ido suka zaro mun a lokaci daya suna fadin har ganyen dubu daya haba dai.
Na dari biyu dai ko daya nace kuba zaku ci ba ne sukace zamu ci yar uwar zaman saade ne ta shigo dakin tana fadin ko zaki sha fura ne a sayo maki nace ganye dai nake son ci ga kudi na bada a sayo min tace wa zai sayo sai khadija tace maimu zata sayo.
Ta sake tambayan da kuli zance ko soya min za ayi nace da kuli dai za a gyara min tace to ki sayo na dari biyu di sai kayan hadi sai saade tace kuje kiyi mata bayanin abinda zata sayo.
Suka fice dakin nan dai mukaci gaba da hiran mu sai ga maimu ta dawo ba, a jima ba aka gyaro ganyen sallah muka farayi muka zauna gaba dayan mu muna hada hannu muke ci a katon tire dukkan mu.
Khadija ce take fadin amma anty saade kunfi zaman lafiya da wanan matar data gyara muna ganyen nan tace ba ruwanta ai bata da fitina amma ita dayan haka take kamar innar mu wurin fitina.
Kullun sai tayi fada da wani cikin mu kan diya ko kan girki sanan tana muna kurin yan uwanta na da kudi a cikin mu har gori tayi min da muka taba fada.
Wai yar uwar tawa da nake kuri tana birni bata ko san dani ba a duniya sai ta kashe take bamu dariya nayi nace badai kina da mai kashewa ta baki din ba ai yafi babu.
Tace ina ma kika sani dana dawo wurin sunan yaron nan da naje cewa tayi kuma wai naje nayo maula ne gurin ki ai ba shiri a tsakanin mu da ya dakin ku.
Nace fita batun ta don Allah irin matan nan ne da sai su zuga ka har ka aikata abinda baka tashi yi ba tace ai na gane ta yanzu ban biye mata.
Khadija na bawa makulin mota don bamu fito da su malam musa ba mu kadai muka fito yau, nace ta je ta dauko min kayan dake bayan seat a farar leda.
Ta fita sai gata ta shigo da ledan nan nanuwa saade turamay zani da sabulu nace tabawa kishiyoyin nata.
Tace duka safiya nace kada ki damu girman ki nake ja maki a hakan ai fita tayi sai nabi dakin da kallo don in san abinda zan mata a dakin nata don ace inna batai mata komai ga auren nata wai bata son auren.
Ta dawo sai gasu tare sun shigo dasu sukayi godiya suka fita khadija ke fadin dama Atikan kawai kiba wallahi nace ai ba ayin hakana kuko.
Nace saade yanzu kina ganin dakin nan yana daukan fridge da kayan kallo kuwa tace aiko bai yi zan sa afita da kuje daya sai in samu wuri nace to yayi sai ki gwada mu gani mikewa nayi nace barin shiga dakin senior dina mu gaisa na suri jakkana na fita daga dakin.
Ina jin khadija na fadi zataje tayi mata dumus ke nan tunda kinga ta dauki jakkan hannunt ban tsaya bana fice daga dakin.
Tana gani ta kama washe baki tana sannu da zuwa dakin nata gwanin ban tausayi wallahi kai mata muna cikin wani hali a rayuwan auren mu har na tuna da dakunan su ummi na da.
Sai a kai mace da kayan mutunci gidan su amma sai a kashe kayan da miji ba zai damu da ya sayawa matar wasu ba tunda a tare ake amfani dasu sai dai ita mace ne zata kama kulla kulla har ta samu ta dan saye nima nasan da ina gidan Ahmed da har yanzu da dan gadon katakon dake daki na zan ta rayuwa.
Mun dan zauna ina tambayan ta wa yanda mukai karatu a tare tana bani labarin su hannu na tura a jakka na na kirga dubu ashirin na aza mata a gadon ta nace ayi hakkuri akwai abubuwa da yawa amma wata rana zakiji sakona da yardan Allah.
Na fice tun bata fara yi min godiya ba na shiga dakin dayar mai kurin arzikin gidan itama babu komai a dakin sai wani tsohon gadon na katako da wasu rubabun kujeru manya a dakin dubu biyar na bata na fito bayan mun gaisa da ita.
Ina shiga nace ku taso mu tafi saade sai na sake dawowa maimu da hindutu ne ke rige rigen karban jakkar hannu na khadija tace naga alama mai kamar dai dake za a koma Abuja nan ko ?
Nace maimu da hindatu kan ai tashina tashin su tunda ke kin gudo ban yarda in rasa abokin hira a gida ni kadai sai mummy.
Nan suka shiga masu sheri suko yaran sai murna sukeyi zasu tafi abuja khadija na fadin kuje kuyi zaman kurkuku ai ba shiga ba fita sai zaman gida.
Na bude mota muka shiga na tayar ina masu horn duk suka daga muna hannu muka tafi sai gida tun dawowan mu na dan leka inna wacce yanzu maganin ya fara bata reaction tana yawan galabaicewa sosai na samay ta zaune yaya Sani ya sawo mata lemo mai bawa tana sha.
Na gaida ita na fito na shiga wuri mama itama na gaida ita na koma dakin ummina ina fadin wai kamar nayi wani abu yau duk na gaji ummi na sai dariya take yi cikin jin dadi da kulawa.
Mun dan taba hira wanda kusan hiran na kishiyoyin Saadatu ne sai nace maimu dake lake dani ta kira min yaya sani a waje idan yana nan tashi maimu ummi tace ashe kin samu yan rakiya Abuja ne yanzu maimu ke fada min da su za a tafi wai ?
Nace haka nake so ummi shima yayi mi maganan hakan don yaso khadija ta zauna damu amma taki kanta na rawa.
Ummi tace bar ta kawai mara hankali ba komai ya hata zama ba sai wanan sauryin nata mara mutunci da take son dauko muna wahala taki zama.
Nace nima dai ummi yaron bai kwanta min a raiba wallahi don ba yan mutunci bane ta rasa wanda zatayi soyayya dashi duk garin nan sai zurian su inna.
Gaskiya nima hadin bai min dadi ba gaskiya ummi ai ta samu wasu a bauchi da muka tafi ban dai sani ba ko har yanzu a kan shi take.
Ummi tace kinga ko bata fada ba don karnaji nayi mata fada tana tsaye daga kofan kuryan ummi tana sauraren mu ta turo baki gaba.
Ummi tace tsayin may zaki zo ki muna a kai in kina tsayawa kima kan ki fada tun wuri gara ki tsaya ga masu son ki na kwarai don dai ni ba yarda zanyi da wanan zaben naki ba.
Juyawa tayi ciki da fushi tana magana kasa kasa nace ji wawiya don Allah ana fada maki gaskiya har kina ganin laifin mutane akai.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/13/20, 7:47 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , ,


🧕🏿7️⃣9️⃣🧕


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

Shigowan yaya sani ya katse muna maganan da muke akan khadija din don ko ba komai baza mu so yaji muna sukan dan uwan mahaifiyar shi ba a fili.
Ya shigo yana fadin yanzu maimu da hindu suka tare ni a hanya suna fadin wai dasu zaki tafi idan zaki koma ?
Nace a sanyaye haka nake so indan zan samu baba ya yarde min don gidan yana min girma ba kowa a kusa dani.
Yace ai ba wani matsala bane idan mijin ki zai yarda da hakan sai dai kin san wasu baza basu son haka sam a rayuwan su.
Nace shi ya bani shawaran hakan ma sai dai bai san da zancen maimu ba hindu dai mukayi magana a kanta da zan zo saboda ita khadija taki zama can.
Yace khadija kan ai tafi son nan tana gudun kada a kwace mata guy din ta sanusi sai dai kuma ni naga sanusi baida alkibila don da batan yar gidan hakimi ya koma nema.
But khadija ta fito daga daki tace yaya sani may kace yace au ashe kina ciki takara tambayan shi yace mata bai sani ba tace uhumm ummm ai naji abinda ka fada dama shafiu ya fara fada min yace kinji shine kike kara tambayana kuma.
Nace yaya sani kaga muyi maganan abinda yasa na kira ka don Allah bar wanan zancen nata na shirmay ko a gidan shi kike da ke kadai zaki zauna balle bakuyi aure ba yana saurayi zai zauna dake ke kadai.
Yaya sani ni kaga shawara na kiraka muyi don Allah yace to anty ina jin ki da sauri nace kai yaya sani nine kuma antyn naka kuma ?
Bakiji abinda na fada maki ranan ba ne Safiya yanzu ai kin zama antyn mu gidan nan don ko maishi a yanzu shine babba don shawaran komai shike kawowa kin ga ko dole ne mu girmamaki ai.
Ummi tace kai kaidai sani baka rabuwa da barkwanci wallahi yace ummi wallahi gaskiyan ke na ai anty ina jin ki.
Dariya ya bamu sosai gaba dayan mu dakin sai da muka dara mai nace dama shawara nakiraka muyi akan Saade da Ainau.
Yace bakaji magana na yafito ba ummi yanzu ni da ke nan ai ban taba shawara akan su ba ko yanzu ita gata tazo da shawara kuma nasan wanda zai amfane su ne.
Murmushi nayi wanan karon ban dara ba don abin na yaya sani ya wuce sani na yanzu ya juyo yana fadin ina jinki anty safiya ?
Nace yau naje dakunan su ziyara naga halin da kowacen su take ciki to ina dan son inyi wani abu akai ne a halin da suke ciki din na farko dai shin gyara masu daki zamuyi ko abin sana,a zamu ba ko wacen su ta kama sana,a kanta.
Yana fadin a a ummi ma tana fadin ummu ummm kudai yi shawara don ko kun basu kudi mazajen su zasu karbe kudin nan ne.
Yaya sani yace abinda zan fadi ke nan ummi kika rigani fadi yanzu wallahi nace to yanzu idan na saiya wa kowacen su freezer yayi da kayan kallo a daki don debe masu kewa da kira masu kasuwan sana, an su hakan zaiyi yaya ?
Kwarai kuwa ummi ta fada da sauri shiko yaya sani kai ya fara girgiza yana fadin Allahu akbar lalai safiya samun mai irin zuciyar ki yanzu sai antona wallahi.
Yanzu har kin manta da irin wullakancin da suka dinga maki a baya a gidan nan da sauri ummi ta tare shi da fadin ummm umm sani idan ana tuna baya ba, a zumunci yanzu.
Don Allah ku bar tuna wanan magana ya wuce sai dai zumunci tsakanin ta da yan uwanta irin haka ai Allah bai maja fada ka tsaya kuma ranawa.
Sai ga hawaye a idon yaya sani din ya fito har yana sharewa da bayan hannun shi nace haba yaya sani may ye haka kuma ashe ba godiya yakamata kayi wa Allah ba da ta buda muna ta hanyar dabu zata ba yanzu.
Wa ya dauka zan rayu har na kai wanan lokacin da Allah ya kawo mu har ya bani daman taimakawa yan uwana da iyayyena.
Yace wallahi ummi jiya ni kadai a daki sai da nayi ta kuka in na tuna irin abinda inna tayiwa safiya a gidan nan sai in kama jin kunyan kaina duk da bani nayi abin ba amma uwatace fa tayi dole inji kuyan kaina.
Yanzu badon zuwan safiya da ta bata kulawa ba ai mu nan duk ido muka sa mata a gidan don bamu da hankalin fahintar haka gare ta.
Ummi tace sani abar tuna baya don Allah don tuna bayan baida amfani sai yasa mutum ya sare yaji bai iya aikata wa dan uwanshi alheri.
Nan dai muka tsayar da magana nace gobe sai ku shiga birni kaida su malam musa ku sayo masu abinda ya dace a saya masu ko wace zan bada duba dari dari a kashe mata sauran canji a basu abinsu idan ya rage dama kudin da yake bani ne duk wata.
Ban yin komai dasu ba don idan nazo gida inyi amfani dasu yadda ya dace kaga su sunci nasu rabon ke nan yanzu.
Wani irin dadi ummi taji har cikin ranta nan ta shiga samin albarka yata sani na fadin amin ummi ya mike zuwa dakin inna wai zai dubata nasan kuma zancen zai kyankyasa mata taji.
Don har zuciyar shi yake magana don bazance ga wani rana da yaya sani ya taba kuntata min ko ummi na a gidan mu tun tasowa na ahaka yake damu kamar dan ummi da ta haifa.
Shiya mahaifiyar shi ke fadin wai ummi ce uwar dakin shi tabi boka tabi malam ta mallake mata da ta hana shi hurda da ita da yan uwanshi sai mu.
A can dakin inna nan yaya sani yasa ta gaba yana fadin inna kin gani kin ga kunyan da kika ja muna agidan kirikiri kin san kina cin zalun din wanan boyar Allah a lokacin.
Amma kika rufe ido kuka dinga cusguna mata a gidan nan ita da diyar ta da mama ta gane hakan ba daidai bane sai ta zamay jiki ta barki ke kadai kina masu cin fuska yadda kike so.
Yanzu gashi dama irin haka ne akarshe irin mutanen da akaci zalum din shi suna hadiyewa suna hakkuri suna shayewa Allah bai bari su tabe banza.
Yau gashi ina ciwon safiya baika yadda ke ake gudun ki ba a gidan wanda har diyan cikin ki suna gudun su shigo dakin nan wurin ki.
Wanda ita alokacin ba a gujeta ba haka kamar naki ni nasan duk wanan abin ishara ne kawai Allah ke nuna maki abinki da zaki roki yarinyar nan safiya tun wuri ta yafe maki da zaifi sauki wallahi inna ga wanan halin da kike ciki.
Da kyat inna ta iya dago kai ta kalleshi tana share hawayen dake fuskanta tace sani na dade yin wanan tunanen a raina nasan na zulunci yarinyar nan sosai a rayuwana.
Ba kowane sillar auren ta da yaron wurin gwagon kuba sai ni jin dani yaran basu da tarbiya, ni na je nabata gwogon ku shawara mai zai hana ta nemawa danta safiya tunda gashi ta kusa gama boko.
Nayi hakane don inga rayuwan safiya ya tarwatse ban tuna da cewa ba ayiwa Allah wayo ba sai yanzu na fahinci hakan.
Da farko har ina murna naga bayan su ita da uwar ta a gidan nan sai kuma gashi ubangiji ya kawo mata miji ta sanadin ciwon da ta dauko wurin dan uwar ku.
Sai yan, , , , , katse ta yayi inna mai sukai maki haka mai zafi har kika bisu da wanan mugun nufi haka a rayuwan su.
Kishi ne kawai sani kishi tun ranan da malam ya auro uwar safiya a gidan nan na dauki karar tsana na dora a kan Rabi ba don komai ba sai don ganin tafini kurciya da kyau .
Wanda zai sa malam ya dauke hankalin shi a gare mu da diyan mu gashi kuma ta dage ta saka diyan ta a makarantan boko wanda ku diyan mu talla yafi muhinmaci a wurin mu duk bakuyi karatu ba sai nata diya.
Kuka ne yaci karfin yaya sani yake fadi wallahi inna kin cuci kan ki kin cuce ba komai ki bibiyar mu ba sai alhakin wa yan nan bayin Allah dake kan ki.
Mikewa yayi yabar dakin cikin bacin rai ya fita daga gidan can ya koma waje ya samu wuri yana kuka har yagaji sai da abokin shi shamsu yazo ya bashi hakkuri ya samu yayi shiru.
Washe gari kamar yadda mukayi magana da yaya sani hakan ne ya kasance don yaya sani sun kama hanyar birni shida su malam musa da shamsu abokin shi suka tafi sayayya.
Sai laasar suka dawo gidan mun fito mun ga kayan ba a sauke su ba mukace a wuce masu dashi gidan su .
Sai tambaya su mutane ke yi kayan waye haka yaya sani din ke fadin nasu Ainau ne da Saadatu safiya ta bada kudi a sawo masu a birni.
Murna ya cika yan gidan mu sai shewa suke da murna nan yaya sani suka wuce da kayan zuwa gidajen su saadatu din.
Ranan ba a kwana ba saida su suka zo gidan Ainau da sarakuwar ta ita kuma saadatu da kishiryata da suke shiri suka zo godiya.
Kullun ina waye da uncle sai dare yake kirana ko da safe haka yasa na samu daman fita wurin yan uwa duk inda nake so yau zan shiga birni wurin Amina ida can zan kwana wurin ta.
Da khadija zamu tafi don tana son zuwa sayen abu acan sai sha biyu muka bar gida inda muka kama hanya da su malam musa driver da yaya sani zamu tafi.
Mun isa lafiya sun sauke mu suka shiga gari wai zasu diba masauki inda zasu sauka mun shiga wanda yake orin ginan quaters din nan ne mai daki biyu da falo sai ban daki da kitchen.
Muna zaue a falon ta ida take ina aka saka damu a gidan tasan da zuwan mu don mummy ta bugo mata tun ranan dana je wurinta nace ranan monday zan tafi wurin Amina din.
Zzaune muke ta cika muna gaba da abinci sai hira mukeyi da ita ga jaririn da ta haifa nan bayan haihuwana har ya dan yi wayo shima.
Bayan mun yi sallah mun huta khadija ta fita zuwa kasuwa sayo abinda ta shigo saye ni kuma Amina ta jani zuwa gidan kawayen ta tana nuna masu ni.
Yaya sani ne yakirani a waya wai gasu sun dawo yasa muka bar gidan kawarta na uku da muka shiga muka dawo gida.
Nan ta basu abinci sukaci muka dan taba hira dashi mijin ta ya dawo nan suka fita waje suka hade dasu malam musa sai hira.
Sai yamma khadija ta dawo da kaya niki niki data sayo tana cewa ai na fada maki anty garin ku yafi nan tsada wallahi.
Amina ce ta tare da fadin ke ko khadija ina zaki hada tsadan birni da na nan ai ba daya suke ba, zama tayi tana cewa garin nan akwai zafi Anty Amina mun fiku sanyi a gida.
Nace ba yanzu kika shigo ba ai dole kiji zafi Amina tace tadai saba zama a cikin AC can abuja amma ai kusan sanyin mu dayane da gida .
Magariba akayi muka tafi zuwa sallah tunda nayi sallah nake zaune a daki ban fito ba don naga mijin ta na gida a loikaci khadija na kwance saman gado tana sauraren waka a waya ta ni kuma ina kasa zaune saman sallaya da casbi a hannu na ina ja.
Amina ta shigo dakin ta zauna tana cewa Abba yayi barci ne ashe kallon inda yaron yake kwance tare da khadija nayi naga yana barci.
Tace ku fito muci abinci mana kun zauna a daki nace gani nayi kada mu takura ma maigidan ne yasa muka zauna a daki tace ai ya fita sai goma ko sha daya yake dawowa gida.
Kasa boye mamaki na nayi nace Amina sai sha daya yake dawowa fa kika ce tace watarana har yakan wuce sha daya wurin hira.
Addua na nayi tare daa aje tasbahan cikin handbag dina nace Amina ke kuma kika kyale shi a hakan kinaa kallon shi.
Kin san fa irin abinda ya ci ni ke nan a baya da yaya Ahmed ke irin wanan rayuwa bani da wayon da yancin da zan hana shi fitan dare har yazo ya zama min ja iba daga baya.
Don Allah kiyi kokari kisan yadda zaki hana mijin ki fitan dare duk wani hiran da zaiyi yayi shi agida tare dake da yaran ki.
Yawon namiji kada ya wuce takwas na dare zuwa tara indan yakai goma abin yakan baci ne sai dai idan da uzuri ki daga mai kafa akan haka.
Tace niko ban dauke shi komai ba wallahi nace Amina shine komai kuwa don nasan illan yin haka a baya kokari zakiyi cikin hikima da basiran ki irin tamu na mata zaki hanashi wanan yawon daren ba a cikin haukan kishi ba.
Amma ai duk wani magidanci na gari marancen farko ya kasance yana a cikin gidan sa sai dai idan wani uzuri ya fitar dashi waje.
Tace kin ga yanzu kaina ya kawo wuta wallahi don idan za a fita din sai anyi kwaliya an fesa tura da sauran su ake fitan.
Nace ba zugaki nake yi Amina amma ke da sauran mata yan uwa na yakama mu gyara ko da neman matan mijin ki keyi to ya zama may tsaba yake yi.
Da yawa mu mata muke bada gudunmawar haka ga mazajen mu don bamu tsayawa muyi masu abindaya dace mu jawo hankalin su gare mu.
Sai kiga mace da kayan da wuni dashi a jikin ta dashi kuma zata tari miji dashi daa dare ba wani kamshi a gidan kamar mai taron wanda yayi tafiya ya dawo.
Ko wani canza na,uin girki zuwa kalar da yake so a koyaushe ki canza nauin abincin ki ki gyara kanki da yaran ki gidan ki ya kasance a gyara har shimfidan ki zuwa bandaki da tsakar gida da sauran su.
Ajiyan zuciya ta sauke tace wallahi ni wanan duk bai damay ni ba, a dade da nake wanan shirin na gyara gida inyi komai da kika fadi yanzu.
Amma yanzu tunda na fara aje yara na tatara nabar komai wahalaan aiki dana yara sun isheni a gida safiya ga zuwa wurin aiki kuma.
Amina nace cikin wani irin murya yasa ta natsu ta daina maganan da takeyi tace safiya .
Nace don Allah ki mai da hankali ga mijin ki yanzu ba ai ma maza hakan ke da kan ki kike shirin rusa gidan ki tayaya bazaki ja mijin ki a jiki ba.
Har zaki ba wasu matan waje kafan ashe maki miji daga hannun ki wallahi ki mayar da hankalin ki kishiga karatun na natsu ga maza.
Mazan yanzu ma kayi masu ba tsira kake yi ba balle kaba su lasisin fita bariki suyi don Allah mu mayar da hankali mata shike sa matan waje suke shigo su raina ta gida don yin sakaci tundaga farko musanman mace da take ita kadai bata da kishi idan kinayi sai kikara akan wanda kike yi din.
Kamar yadda tace hakan ne kuwa sai sha daya da rabi naji dawowan mijin nata lokacin munyi sallama da ita ina kwance barci bai dauke ni ba.
Godiya nayiwa Allah da ya fitar dani cikin wanan rayuwa ina tuna lokacin da nake gidan Ahmed da yake dawowa cikin dare a buge ko da karuwa .
Sai dai dayake nan arewa ne fitsaran su baikai na mazau na kudu ba da basu da nauyin kowa a ransu abinda suka ga dama sukeyi sai wanda ke da tsoron Allah a zuciyar shine Allah ke tsarewa.
Amma nan arewa a cikin tako suke alamarin na yadda kafin a gane halin na miji sai ta dade yana cutar da mutane wani kuma ba yadda za a gane halin sa sai Allah.
Da ire iren wanan tunanen barci ya dauke ni bamu falka ba sai asuba don abba tunda ya tashi kafin mu kwanta na bashi madara yasha ya koma barci bai kara falkawa da dare sai dana tashi zan yi alwala don yanzu ya fara wayau ya tashi yana ta kuka.
Saida khadija ta kamashi ta goya ta hada mai madara yasha ya koma barci ina zaune take cewa yanzu fa ya fara gane ki anty.
Don daga tadhin ki yasa kuka wai don may kika tashi nace bari zaiyi ai idan mun koma don dan tafiyan da mukayi bauchine gashi kuma bamu zauna ba mun taho nan.
Hmmm aini idan na tuna badakal ku da uncle a bauchi abin dariya yake bani nace in dai uncle ne ai kadan ma kika gani don ban biye mashi ne kawai.
Yanzu baki ga dana nuna mashi ban damu ba dayace ban zuwa gida ban san abinda ya gani ba kuma yazo ya barni inzo da yaso ne fa da na zo mu koma tare dashi.
Tace hakan yana yuyuwa kuwa anty dz fa duk wanan ziyarar bakiyi shi kai koma a garin ba inda zaki ai.
Uncle ai halin shi sai shi wallahi wanda bai san halin shi ba sai yayi ta wahala da daki nakan shiga inta kuka daban gane haka yake ba.
Amma anty maganan da kika fada ma anty Amina daren jiya naga jikin ta yayi sanyi nace tayi sake ne tun farko ta saba mashi da hakan da tun farko ta koya mashi zama gida ba zai yi hajan ba koda zaiyi ba hakan da yawa ba dai.
Mazan mu na hausawa na da saukin kai idan mace ta san yadda zata bi dasu sai dai abinda basu so mace ta nuna masu kamar tana commading din su sai suce ka raina su.
Tun da mukayi sallah muke hira duniya dani da khadija anan na samu daman yi mata magana akan ta rabu da Sanusi dan uwar inna.
Na nuna mata illar abinda take shirin yi din dayin hakan nasan dai magana na batai wani tasiri a zuciyar ta ba sai dai a sanu zata gane abinda muke nufi gare ta.
Nayi mamakin ganin sai da rana ta take Amina ta tashi ida na fahinci ba wani dogon addini suke yi ba da ita da mijin nata don ta fito tana fadin wai sun makara ne.
Nace Amina ya kamata fa yanzu ki daina wasu abubuwa domin ke din uwace a yanzu kina kwaciya barci har asuba ta wuce bakuyi sallah ba ta yaya kike ganin zaki koya ma diyan ki ibada da hakan.
Shifa yaro anbinda kake yi yake koyi dashi mai kyau ko mara kyau don shi gani yake komai daidai kake yi.
Tace wai ni Safiya wanan mijin naki halan ustzune naga duk halaiyar ki sun kara canzawa yanzu ba a yanda na sanki ba duk da dama can babu ruwan ki baki kaimu rawan kai ba.
Dariya nayi kawai mun karya ban wani jin dadin zama a gidan ba don haka kamar yadda muka bar gida sha biyu haka muka baro gidan Amina zuwa gida bayan na masu alheri muka dawo gida.
Saboda gaba daya naga Aminan ta canza tabar halaiyan ta dana san ta dashi a baya sai wani nuna waye taki wanda bai dace da diyan musulmai ba da matan hausawa.
Abinda nake son mata su gane shine bawai sai mun nuna wayewa a fili za a san mun waye ba dabiun ki na diyar bahaushe musulma a ko ina ya rinjayi zuciyar ki.
Ako ina kika samu kan ki kada kiga kina zaman bariki ki watsar da tarbiyan da kika samu ki manta da rayuwan ki a yanzu yafi muhinmanci ga Allah.
Ki dinga fita yadda kika ga dama batare da kin rufe jikin ki ba wai ke zaman bariki kina daukan hakan a wayewa gare ki.
Kamata yayi yar musulma bahausa ta nuna a ko ina ta mai cikaken tarbiyane a duk inda ta riski rayuwan ta wanan rayuwan duniyan ba komai bane a gare mu.
Wataran kana gani anayi ba dakai ba lokacin ka makara ga gyaran dabi,un ka don yara sun taso sun dauki rayuwan da suka samu kanayi suna kanana.
Badon kan mu zamu daina wasu abubuwan ba sai don tunanen makomar yayan mu na yanzu da wanan tunanen na canzawan Amina a raina har muka iso gida a lokacin.
KUYI HAKKURI DA MAGANA NA YAN UWA MUNA CIKIN WANI HALI NA SAKACI DA ADDININ MU YANZU DON MUNA GANIN KAMAR WAYEWA NE.
MUN MANTA YAYAN MU NA TASOWA SUNA KOYI DA DABIUN MU MU CUSA ADDINI GA ZUKATAN YAYAN MU YAN UWA.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/14/20, 10:25 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , ,

🧕🏿8️⃣0️⃣🧕

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

Mun dawo gida mun samu jikin inna ba dadi ranan basu kwana da ita da dadi ba don maganin da ake mata allura a fara aiki a jikin ta sai ya jikin ta sakewa.
Dakin inna muka wuce don har baba yana gida ranan bai fita wurin sana,a shi ba don yanayin jikin inna din mun samu ta samu barci mun dade a wurin ta muka fito daga dakin.
Yan uwanta ma da suka zo a waje suka zauna suna tsoron shiga dakin inda take don gudun daukan ciwon da akace masu anayi.
Sai da na fito muka gaisa da su ban tsaya ba na wuce daki bamu dade da dawowa ba naji shigowan Saadatu gidan ashe dama tana nan ta fitane zuwa sayo masu abu.
Ina daki zaune da ummi na muna hira naji muryan ta tana cewa ashe bakin birni sun dawo nace eh anty Saa kin shigo ashe tace dama ina nan na dan fitane dazun .
Mun gaisa na jajanta mata akan jikin na inna ta samu wuri ta zauna a dakin ummi din tace ashe kin je wurin Amina ne birni nace eh munje ziyara wurin Amina.
Mun dade a dakin muna hira da ita tana bani labari har ta fara sana,a da fridge din ta kayan kallo kuma tun ranan aka hada mata su yanzu bata da wani damuwa ko zaman kadaici
Kiranta akayi waje ta fita na mike ina son in yi wanka dama sai ga mama ta shigo gaida mu da dawo nan na tsaya muka gaisa tana fadin ai babaku bai san zaku kwana ba ya dawo yana fada jiya.
Nace Amina tana da muhinmanci a wurina shiya naje na kwana mata daya yanzu saura kuma in tafi kauyen su ummi inyo ziyara in dawo in fara shirin tafiya don mun kusa cika kwanakin da aka bamu.
Tace au har can zaki tafi ashe nace ba dole inje in duba ma ummi yan tsofinta ba kada ta hake ni daga inda ummi take zaune tace ai ba a saki zuwa dole ba.
Dariya mukayi mata mama ne ke fadin ba a sata zuwa dole ba amma idan ta koma bata je ya isa ai mata gori ai tazo taki zuwa duba su.
Ummi dai dariya tayi da jin dadin zai tafi in duba yan uwan ta kuma nace kwana biyu zanyi a can fitan mama dakin yasa na mike na shiga bayi na watsa ruwa a jikina.
Na fito na samu shafiu ya dawo yana cika yana batsewa a falon ummi nake tambayan shi may ke faruwa shafiu yace bakomai cikin fushi.
Nace kuma ga yanayin ka ya nuna fushi kakeyi mana shafiu may akayi maka waya taba min kai nazo kusa dashi na zauna.
Ya wani turo baki a shagwabe yana fadin wai da su maimu zaki tafi indan kin tashi bayan na fada maki zan biki.
Murmushi nayi tare da dafa shi nace shafiu aikai namiji ne kuma in na tafi dakai wazai taimakawa ummi ga sana,an ta ?
Yace namiji bai zuwa gidan yayan shine akace nace kana zuwa shafiu idan anyi hutu sai yaya sani yakawo min kai hakan yayi maka ?
Dan shiru yayi kafin yace indai zaki sa ya kaini yayi mun don wallahi ina son zuwa wurin ki hutu anty nace zakazo shafiu.
Yanzun dai ka shirya zamu wurin su kawu dole gobe mukai masu ziyara kafin in koma yace ni sai kauye za a dani kun tafi birni bakuje dani ba ?
Wai shafiu yaushe ka zama haka ban sani ba bann saka da yawan hayayya ba fa ada ?
Ya mike yana fadin komai sai ace waini namijine namiji akace ba a yi dashi wallahi nima zan bar gidan nan ne.
Barci nayi ranan ban ko fito tsakar gida ba din ina son in dan huta ina jin ummi suna faman rikici da Abba a falon ta amma na kasa tasowa inzo inji may ya samay shi.
Har yaron yayi shiru ban sani ba don barcin dana koma a lokacin shigowan yaya Nura wuri na yasani tashi zaune.
Falo naa fito wurin shi mmun gaisa nace yaya Nura yaya akayi ne yace wallahi Safiya garin ne yayi zafi yanzu sam babu aiki tunda dama ya kama mutane sun mayar da kudin su gona.
Nace yanzu may ye shawara yaya ya shafa kan shi yana dan murmushi yace zuwa nayi wurin ki ki dan taimaka min da wani abu in dinga juyawa.
Shiru nayi ina nazari a raina sai nace yanzu dai ba wasu kudi nake dasu anan ba yaya gashi zan shi kauye wurin kawun ne na sai dai indan mun koma idan zaka iya shigowa Abuja sai musan abinda za ayi a can din .
Zaiyi magana na rigashi fadin barin in baka dubu ashirin duk da nasan zasuyi ma kadan amma kayi hakkuri dasu jibi zan koma ba dadewa zamuyi ba dama sai kazo mu san abinda za a yi don yaya Saadu na can.
Bva zai rasa wurin da zasu saka ba yafi wanan aikin da kakeyi a nan zaifi ma sauki nake gani idan zaka iya idan kuma kafi son zaman nan zan sama maka abin juyawa yace sai nayi shawara da mama ummi dake kofa tace shine daidai.
Na shiga daki na fito mai da dubu ashirin din na kawo mashi ya mike yana godiya ya fita daga dakin sai lokacin ummi tayi magana.
Kin san dai Nura ba kamar Sani yake ba karki saka shi a cikin harkan mijin ki ya yaudare shi bake kadai abin zai shafar mu nan zai iya shafan mu.
Nace har yanzu yaya Nura bai daina halinsa bane ummi tace ina zai daina tunda bajin maganan iyayye yake yi ba.
Shi haka rayuwan shi take a tsatsaye yake har yanzu baya ganin kowa da mutun ci a idon shi ko gidan nan ya shigo bai iya gaida mutane yanzu ma mamakin ganin shi a wurin ki ai.
Murmushi nayi nace amma duk abinda yake ummi ai bai kawo gare ki damu ko iya wanda ya shiga harkan shi yake tsayawa.
Ina dai ja maki kunne kisan abinyi tun wuri nace ummi ki bari a gwada shi ko sau daya ne kin ga ai mama bata jin dadin ganin da yaya sani kawai muke mu,amula a gidan nan ranta baya dadi nunawa kawai ne batayi.
Ba fa gwadawa a fili amma nima nasan abin yana damun ta nace ba a dukiyar uncle zan sakashi ba ai ummi nima nasan abinda nakeyi.
Washe gari muka isa garin kakan nina mun samu taro na mutantawa a wurin su irin taron da mutanen kauye kiwa wanda suke mutuntawa aikai muna a gidan.
Su yaya sani basu kwana ba suka dawo bayan sunci abi mukai sallama dasu suka tafi naji dadin kasan cewa a cikin yan uwan ummi danayi saboda yadda suke nuna muna don dukkan mu yaran ummi mukaje garin.
Mun so zuwa da ummi amma baba yahana ta zuwa don haka muka zo bada ita ba sai yamma mazan suka dawo daga gona wurin aiyukan su don da aiki noma da kiwo suke dogara su.
Sai da suka huta muka bisu daya baya daya muna gaida su a part din su najin dadin ganin mu a yadda sukaga munzo mu duka.
Mun fi dadewa a wurin kakan mu wanda tsofa ya kama yanzu har dan rankafa abu ga dogon mutum wanda ya manyanta don ko diyan shi ba yara bane balle shi tsawo rai daine daya samu yakai hakan.
Washe gari da muka tashi jumma a ne don haka kowa na gida basu zuwa gona duk ranan jumma, a ranan suke samu su dan huta a gida don yin sallah jumma a din.
Tsaraban da muka kawo masu ake ta rabawa a kofan kakan mu mace duk da ita ta haifi ummi mu ba wanda ta haife ta ta rasu tun ummi bata girma ba.
Amma ta rike su kamar ita ta haifesu yadda ta rike su a gidan nan suka fara shigowa godiya a gare mu duk mazan shaddan da ya bani na kawo masu dama na aje masu nasu.
Mun je wurin kakan mu gaida shi sai jan mu da hira yake yi yana bamu labarin rayuwa shi na baya yana kuma fada muna dan tarihin ummin da tasowan wata har auren ta a kauyen da tayi ta koma wurin gwago a garin mu.
Abba ke rikici a gaban shi yayi murmushi yace miko min shi nan khadija ta mika mashi yaron ya dauke shi tare da kara shi saman kafadan shi daidai saitin kunnen yaron ya dora bakin shi a hankali yana karato adduan daba mu san may yake fadi ba a lokacin.
Kara juya shi yayi bangaren hago ya kara maimaita abinda yayi mashi a bangaren dama ya gaba sai ya dan hura mai fuska take yaron ya zauke numfashi a hankali yake rage sautin kukan da yake yana ajiyan zuciya shikuma yana dan jijigashi a hankali saman kafadan shi har yai shiru ya lafe sai ajiyan zuciya yake sakewa a hankali.
Mudai mana kallon abinda yakewa yaron yace idan kunga yana kuka haka daukan yaro akeyi aimai kallaman shada sau uku a ko wani kunne da bissimilah zaku fara kowani sai kuga yaro ya yi shuru koda kuwa shedanune suka shafi yaro yana yawan kuka akai akai.
Nace aiko mun karu tsoho ya nisa tare da tambayana jiki na nace da sauki sosai yanzu gaskiya don ina shan magani kuma ina cin abinda zai gina min jikina ko yaushe.
Yace kin dai daina amfani da fitsarin rakumin ko don banga kin kara aikowa in sama maki ba nace gaskiya malam tunda na shanye wanda ka bani da farko ban kara amfani da shi ba kuma naji dadin shi sosai wallahi.
Yace tsiyan ku ke nan yaran yanzu baku tsaya ma magani har kuga aikin shi da kyau sai ku camza wani .
Nace tsoho ba inda zan samu ne a can kaga muna da nisa sosai yace kinzo a saa ai yau jumma a za a soke rakumi ayi tom tom din shi zan sama maki wasu abubuwan amfani da dama a ciki sai kije kiyi amfani dasu can idan kinji dasin su keda kan ki zaki aiko a kara maki wani.
Godiya nayi mashi tare da dan bashi kudin da na riko mashi duk da ina ganin basu da yawa amma shi sai washe baki yake yana saka min albarka.
Tashi mukayi daga wurin shi wanka mukayi muka shirya muka zagaya gaida dangin da suke a cikin gari
Bamu dawo ba sai yamma lis agajiye kowan mu yake abincin da suka aje muna na rana muka samu ba wani ci mukayi ba dama na bada sakon a saya min ganye da kwai da man shanu mai yawa da zan koma dashi Abuja.
Ganye nace khadija ta dan gyara min naci har dare dashi na kwanta a cikina don banji wani yunwa ba kuma.
Washe gari sai shirya muna tsaraba suke yi kin san kauye da kara wanan ya kawo wanan ya kawo sai gashi mun tashi da tsaraba mai yawa a gidan.
Sha buyu rana driver dasu yaya sani sun iso daukan mu bamu jima ba mukayi sallama dasu muka kama hanyan gida biyu da wani abu muna a cikin gidan iyayyena.
Kwana biyu yarage muna a garin sai shirya muna ummi da mama keyi nan ma dai tsaraban ake ta kawo min don duk wanda na ba tsaraba dana zo sai da ya dan samu abin da ya bani da zan koma sai dana ragewa su ummi wani abin.
Ana gobe zan koma ne da safe sai ga maimu da kuka ta samay ni wai baba yace ba zan tafi da kowa cikin su ba.
Hakkuri na bata nace zanyiwa baba magana da yamma da yadawa gida naje gaida shi yana zaune yana cin abinci mama na gefe shi na shiga wurin shi.
Gaisawa mukayi nayi mai yaya kasuwa ya amsa min cikin fara a na samu wuri na tsugun na yace kuna ta shirin komawa gobe ko nace eh baba.
Shine ma nazo fadama zan tafi da maimu da hindatu suyi min hutu idan hutu ya kare sai a dawo dasu.
Dan jimm yayi sai yace Safiya maigidan ki bazai ga rashin hankali mu ba kuwa nace ko daya baba babu ruwan shi ai shi bamai zama gida bane ko yaushe.
Sai yayi kwana nawa ma bai gansu a gidan ba idan ba ya kama ba yace nasan halin yaran nan basu jin magana kada kina zaman ki da mijin ki lafiya su je su tayar maki da hankali can.
Nace baba babu komai wallahi ai khadija ma baiso ta dawo ba itace ma ta matsa zata dawo din yace dayake tasawa kanta shiriritan son wanan yaron ba.
Niko da raina da lafiya na wanan abin ba zai yuyu ba muddin ina raye shirmay ta dai takeyi kawai.
Mun dan taba hira dashi yana ta min nasiha akan zaman aure da zaman takewa a cikin mutanen da ban saba dasu ba har magariba ya gabato muna wurin.
Haka ya mike yaje yayi alwala ni kuma na koma cikin gida ina shiga mama ta biyo ni dakin tana fadin kai Safiya ke kika iya da halin mahaifin ku.
Nace mama nasan halin baba don haka ban fito mai kai tsaye da daukan su zanyi ba sai na laba ga hutu ba sai ya gansu ba kuma ko yayi magana nasan abinda zan fada mashi gaba.
Yaran da sukaji za a tafi dasu suka fara murna mace kada su dauki wani kaya mai yawa kada baba ya gane tafiya zasu yi kayan sallah ku kawai zaku dauka.
Tun da safe ana ta fita muna da kaya waje duk sai naji raina ba dadi a lokacin ina kuryan dakin ummi ina shiri ta shigo dakin nace ummi amna dai ya kamata kizo kiga gida na idan na koma gaskiya.
Tace ba iyayyen ki sunje sun gani ba zuwan may zanyi kuma ni nace haba ummi kamar wace bata da gata ai dai dake da baba ku dan leka watarana ko ?
Tace ba dai yanzu ba sai maigidana zaiyi aure ko nace haba ummi khadija dake zaune gefe na tace kyale ta ninan zan rakota har Abuja idan kin koma.
Gwago dasu mama jimmai sun shigo sallama na dasu Saadatu har da mijin ta da kishiryar tan nan na fito tsab dani na shiga wurin baba na rusun na tare dasu maimu nace baba zamu tafi asa muna albarka.
Yace kullun cikin sa maku muke safiya nan yayi wa su maimu fada sosai na su natsu har su dawo lafiya na shiga wirin inna mukayi sallama nayi mata Allah ya sauwaka.
Na fito kofan gidan namu ya cika da jamma a ina tayiwa mutane ban kwana na shiga mota Adamu ya zo mukayi magana dashi ba wanda yaji may nake fada mashi.
Sai dariyan da yayi yana daga muna hannu nan muka barsu tsatsaye suna bin motar da kallo idona na lumshi ina jin wani iri a zuciya na gida a kwai dadi wallahi indai kazo da zuwan bakunta nace a raina.
Suka yaran sai farin ciki sukeyi yau zasu birni duk sun sallami abokai da yan uwa sai washe baki sukeyi cikin murna.
Sai karfe biyu da rabi muka shigo garin Abuja inda muka wuce gidan mu direct daga shigowan mu kanne na da suke ta surutu sai suka koma kallon gari.
Mun iso gidan duk zuciya ba dadi har lokacin a hankali na furta Alhamdullahi a fili tare da yunkurawa ina shirin fita daga motan ji nayi sunce anty mun iso ne eh kawai na iya ce masu.
Security din ne ya fito ya bude muna mota tare da fadin sannu madam sannu ismail na iya fada mai nace nagode.
Fita nayi daga motan tare da amsan Abba dake jikin maimu yana barci saida na karbeshi suka fito daga motan tare da daukar min jakkan hannu na muka nufi kofan shiga gidan.
A rufe gidan yake na dan danna bell ajima kadan sai aka bude Nura ce ta fito tana ganin mu tace ah wellcome madam.
Thanks nace mata ta matsa muka shiga tare da kanne na dake bina a baya tsakiyan falon na nufa na shimfede yaron saman kujerun falon da suka sha gyara.
Na juya naje kuna Ac da fanka a lokaci guda take falin ya fara canza yanayin shi daga zafi zuwa sanyi.
Har yanzu su maimu basu zauna ba nace dasu ku zauna mana gaku kamar masu tsoro da sauri suka zauna a takure saman kujeran duk sun matse juna.
Zama nayi ina kokarin dauko key din daki na a cikin jakka na can kasa naji key din na fito dashi daidai lokacin da Nura ta kawo muna ruwa da juices din kwali gaban mu da kofuna ta aje.
Goran ruwan na dauka na fara tsiyaya a cup tare da masu nuni da su dauki ruwa su sha mana suma da sauri kowa ta dauki cup din zasu zuba ruwa nace bazaku sha lemon bane muna sha maimu tace min da sauri.
Bayan na shanye ruwan na aje cup din na mayar da jikina ga makarin kujeran tare da lumshe idanuwa a hankali na danyi tunane sai kuma nayi ajiyan zuciya.
Wayana yayi kara daga cikin jakka na na jawo jakkan ina duba wayan yaya Saadune yake kira na alokacin na dauka tare da fadin hello yaya .
Yace Safiya yaya hanyan na amsa da Alhamdullahi yaya.
Yace kuna ina yanzu ?
Gamu gida yaya na bashi amsa a takaice.
Yace ashe kun iso ke nan , ?
Eh yaya
Yace OK sannun ku da zuwa gani nan tafe yanzu mu gaisa
Sai kazo yaya kawai nace na kashe wayan ina kara mayar da kaina yadda yake da farko.
Mikewa nayi na bude dakina yayin da su malam musa ke ta shigo muna da kaya cikin gida shi da wanan security din Nura ta tarawa daidai kofan kitchen din mu.
Dakin na shiga sai duhu na kunna wutan dakin tare da jefa jakkana saman gado kaya na fara cirewa a jikina na shiga wanka na dan dade ban fito ba.
Sai can na fito na sauya kayan jikina na samu Abba ya tashi daga barcin da yake yi tv na kunna kafin in zauna na kalli dining naga Nura ta jera muna abinci a wurin.
Makulin da nafito dashi daga daki na bude wani daki a kusa da na mummy nace da su maimu ku taso kuga dakin ku ko.
Da sauri suka taso zuwa inda na kira su wanda sai kayi dan tafiya zuwa wurin nace nan yayi maku ko yanzu dai gaku a cikin gidana.
Fushi ya kare maimu da baba dakin muka shiga dukan mu sai baza ido sukeyi kamar matsorata a raina nace rayuwan kauye baiyi ba gaskiya.
Ji yadda yara ke wani iri kamar wa yanda basu yarda dani ba ko wani saman gadon dakin na zauna nace suma su zauna Abba nake kokarin cire ma kayan jikin shi a lokacin.
Nace kunga ga bayi nan don Allah banda kazanta don shi zai hadani ku ba komai ba a kullun a wake bayin nan sau uku ko sau hudu a rana.
Taso muje in gwada maku yadda zakuyi amfani dashi nan dai na nuna masu komai nace su kwaso kayan su sushigo dashi dakin a tare muka fito ina ce masu suyi wanka muci abinci.
Sun gama sun fito shima Abba wanka nayi mai muka fito muka ci abinci muna kan ci yaya saadu suka iso gidan shi da samira.
Ina ganin su nace chewgun ke nan kina lake ko yaushe masu miji ke nan ina kuma kuka baro min diyata ?
Tana wurin uwarta tace ganin yaran yaya ce ina kuma kika kwaso wayan nan yan kauyen haka hararan shi nayi nace ina kaga yan kauye kuma anan ?
Tace ke ko kin so dawowa ji yadda kika koma kin je kin cinye ma tsofi abinci kin ki dawowa.
Na lumshe idona nace bari samira wallahi gida akwai dadi kamar karna dawo nake ke ji sai naga gidan nan yayi mi wani irin girma wallahi ba hayaniya ba motsin kowa.
Kajiki da wani zance har yaushe kika bar nan din da zakice wai wani gida dadi ai da ki zauna gida in baki dawo kin samu munyiwa uncle din ki aure ba.
Samira ke da kanki ke fada min haka lallai wata shigowan kishirya ki ya tsaya don wanan watan zamu kawo maki wanan karfen kafan da ta leke wa yayana.
Don Allah Safiya ki daina zancen wanan gajan matar da ta tashi aiki don wulkanci ta rasa wanda zata lekewa sai mijina yar iska.
Yace ai shike nan tunda kin san takon ta kuma da tayi maki tsiya bani go ahead kawai safiya na shigo da hafsat kai tsaye


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/15/20, 7:06 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , , ,


🧕🏿8️⃣1️⃣🧕

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU


Bayan tafiyan su samira da basu dade ba na shige daki nayi laasar na fito muka fara gyara kaya da Nura su maimu suna taya mu.
Kafin wani lokaci muyi ma komai muhalin shi mu aje a inda ya dace kuma na nuna masu wanda zasu ci inda suna bukatan ci din.
Falo na dawo inda kanne na suke suna kallon na zauna sai dai ni ba kallon nake yiba waya nake amsawa daga mutanen gidan mu suna tambaya na mun sauka lafiya .
Abincin dare suka ci ina zaune a kasa idan na sallamay sallah ishai wayana yayi kara uncle ne ya kirana a lokacin na dauka da sallama tare da karawa a kunne na.
Uncle ina wuni na fara fadi ya sauke a jiyan zuciya kadan yace madam kun dawo ko kuna can har yanzu nace uncle gani daki na muna ta kewan ka, gidan ya koma ba dadi da baka nan.
Murmushi yayi tare da fadin I miss you to my wife ina Abba dasu mummy nace ga Abban nan hannun maimu mummy kuma bata dawo ba.
Maimu ya maimaita sunan da na fada nace eh tare da su nazo ita da hindatu sin zo muna hutun kwana biyu ne .
Yace bana ce ki samu yarinya kizo da ita ba idan zaki dawo don ki samu abokiyar hira a gida nace ko yanzu ga su suna debe min kewa a gidan.
Bai kara yin magana sai cewan da yayi kara ma Abba waya inji muryan shi sai na manna ma yaron waya a kunnen shi nan ya fara yin gwalanci kamar ya san abinda ake nufi mika ma maimu wayan nayi tace ina wuni yaya yace a a ke yar kauye ashe kun shigo gari sai yarinyar tace eh.
Amshe wayan nayi ina fadin kin yarda ke nan ke yar kauye ce ko na kara ma hindatu tace cikin muryan ta mai sanyi ina wuni yaya ya amsa mata tare da tambayan da wa nake magana tace hindu ce.
Sun jima yana masu tambayoyi wani su bashi amsa daidai wani kuma su fada mashi ba daidai ba
Mukai sallama dashi yana fada min kada in rufe gida yanzu zaa kawo min sako in kar ba godiya nayi mai tare da tambayan shi yaushe zai dawo ?
Yace kin damu in dawo ne ko wani abin kike so madam nace babu komai sai dai kewan ka da mukeyi na rashinka a kusa damu.
Kararawa kofa yayi kara ni da kaina na tashi na bude gidan malam musa driver ne da ledoji da kwalaye ya shigo dasu ya koma ya dauko sauran sai leda daya miko min hannu da hannu na karba .
Bayan na karba na fahinci maye a cikin ledan don jin zafi danayi daga cikin ledan yana tashi da kamshi.
Yayi muna sallama nace ya tsaya ina zuwa yace a a hajiya nima maigida ya saya min nawa na gode wallahi sai da safen ku yana dan dukar da kai kasa alaman girmamawa gare ni .
Yana fita na koma wurin kayan daya shigo dasu ina duba inda naga kayan tea ne mayan gwangoni madara biyu sai na milo da nescafe da ovoltin sai katon din sugar na kwali.
Dayan kuma fruit ne a ciki iri iri masu kyau fresh one murmushi nayi don akwai wanan abin daduk aka sayo muna a gidan.
Ledan da kamshi ke tashi a cikin sa wanda tun ban bude ba na fahinci may ye a cikin wanan ledan kaji ne gassasu guda uku kosassu sun gasu dakyau irin gasuwan resturant din nan da albasa da kabeji da sauran tarkace wanda yakan sawo muci a gidan.
Yaran dake satan kallo nace hindatu ta dauko plate a kitchen guda uku kowa ya dauki kazan daya yaci maimu tace anty duka nace eh duka maimu.
Ban koma ta kansu ba ina faman dakilan wayana suna ci suna dan magana kasa kasa danaji maganan yayi yawa na dago ina cewa dasu wai may kuke fadi ne kasa kasa.
Wai cewa tayi kada mu cinye duka mu rage gobe muci saura nace akan may zaku rage idan kuna iya ci duka kuci mana.
Basu iya cinyewa dukka ba duk zalaman su anan suka barshi nace suje su saka a fridge ban ci nawa sai fruit din naci kawai bamu dade ba nace suje su kwanta su huta.
Sai da na tabbatar sunyi barci na dauki Abba zuws dakina na kashe wutan falon komai daya kamata in kashe na kashe na shiga na kwanta asuba ta gari.
Da safe muna tashi bayan munyi sallah nace suje suyi wanka kuma kullun da sunyi sallah haka zasu dinga yi suka shige daki don yin wankan dana ce suyi.
Abba nayiwa wanka na shirya shi na dauke shi nakai masu dakin shi na dawo nayi nawa wankan na shirya.
Nura ta iso ta fara aikin hada muna breakfast din safe a lokacin na shiga kitchen din nace kada tayi wani mai yawa don ba a ci sosai.
Bayan mun karya ne muka zauna su kallo ya dauke masu hankali waya na na dauko na kira samira muka dan taba hira da ita nace idan ta samu lokaci ta shigo don Allah ina son tayiwa su maimu sayayya kayan sawa don ni ba dama in fita uncle bai gari.
Tace zata shigo zuwa rana asan abinyi din akai nan muka kashe wayan nima kallon na kama yi don shine aikina kawai tunda ba fita nakeyi ko wani abuba.
Sai idan uncle yana gari ne watarana nakan shiga in muna abincin garagajiya don yana so ita kuma Nura bata iya ba sosai.
Hajiya baaba na kira don mu gaisa tace na dawo ko ina gida har yanzu nace hajiya mun dawo jiya muna Abuja yanzu.
Tace yaya muka baro su nace suna lafiya suna gaida ku baaba tace to yanzun dai kinje gida hankali ya kwanta ko ?
Don Allah safiya ki bi mijiki a yadda yake so ku zauna lafiya don Allah yanzu tunda kin san halin shi kibishi a yadda yake ban son yawan fitin da kuke wayan yi ko yaushe din nan.
Insha Allahu baaba zanyi yadda kikace din tace nasan komai safiya nasan kina hakuri sosai dashi shima din halin shine kawai haka bawai yana yi cikin son ranshi bane.
Godiya nayi mata na kashe wayan ina tunanen maganan da mukayi da hajiya din shigowan samira gidan ya kawar min da tunanen da nakeyi.
Samira ta shigo na bata kudi nace taje dasu don kada a samu akasi tace bata zuwa da kauyawa ko ina nace watarana kina ganin su nan sai sun fiki wayewa.
Tana masu sheri suka fita taja motan yaya tabar gidan tare dasu haka yasa na samu kwaciya nayi barci sosai dani da Abba kadai a gidan.
Zuwa rana suka dawo da kayan da ta sawo masu din kayan sunyi kyau sosai na bata atamfofi a cikin kayana da zata kai masu dinki.
Nace ina son yaran nan suyi clean ne samira su din rabin jikina ne da komai nawa watarana sune wa yanda zasu tallafa min a lokacin da nawa kadfin ya kare.
Tace gaskiya ne Safiya da har ina ganin wautar ki na dauko su sai yanzu na gane hikimar yin hakan da kikayi akan su.
Zasu taimaka maki kwarai a rayuwa ki don naka sai naka haka abin yake wallahi Allah ya taya ki rokon su nace amin samira.
Sannu a hankali nake koya masu komai kuma suna ganewa sosai don sun sauya kamar basu ba don da gani sun saurari fadan da akai masu da zasu zo.
Sai da uncle ya kara sati biyu ranan alhamis ya dawo da dare ni dai ina barci naji wayana yana ruri na dauka muryan shi naji yana fadin bude min gida don Allah.
Da sauri na mike tare da daukan key na fita daga dakin na bude gida da sauri yana tsaye yadan jigina jikin shi a bango suith din shi na sagale a kafadan shi.
Mirmushi na sake a fuskana tare da fadin sannu da zuwa uncle hannuwan shi ya bude da sauri na shige ciki .
Yana rike dani muka shiga gidan bai nufi dakin shi ba sai da ya tafi yaga Abba dake barci na wuce na bude mai daki tare da kunna naurorin dakin na hada mai ruwan wanka.
Kayan shi ake shigowa dasu gidan daya dawo dasu sun gama na rufe gida tare da yi masu sai da safe.
Ya dauko yaron ya nufi dakin shi dashi a kafadan shi nan na gama komai nabi bayan su nima tari naji yana yi sai muryan shi daya dan shake bai fita sosai.
Uncle baka jin dadi ne dan murmushi yayi yana kara gyara ma yaron shi kwanciya da kyau ya juyo gareni yana fadin .
Mura ne ya kamani kin san yanayin sanyi da ake yi yanzu acan ya fara kokarin cire kayan jikin shi na juya na fita zuwa kitchen inda na hada mashi shayi da cita da kanunfari na kowo mai dakin har lokacin bai fito daga wanka ba.
Bakin gado na zauna ina jiran shi koda ya fito yana goge ruwan dake jikin shi tari ya kama yi a lokacin tashi nayi na fara tsiyaya mashi ruwan tea din dana hada mashi a kofi.
Ya gama yasa kaya a jikin shi ya nufo inda nake jiran shi da cup din tea din da nake dan motsawa a hankali cup din na miko mai bayan naga ya zauna a saman gadon.
Karba yayi yana tari sosai hankali na ya daga sosai ya dan kurba kusan sau biyu yace na kwana biyu ina tarin nan tun acan.
Sannu nayi mai nace yi kokari ka shanye tea din zai taimaka maka ka samu barci da sauki don wanan tarin dake damun ka.
Ido ya dan lumshe kadan yace yaya kibaro mutanen gida nace duk suna lafiya suna gaida ku sun ce kuma ai masu godiya sosai.
Da akai may yana miko min kofin daya shanye tea din na aje a saman dan drower dake gefe na hawayayi saman godon ya dan dukule a wuri daya kamar mai jin sanyi.
Hankali ya tashi ga yanayi da naga yake ciki sai dai yana kokarin kwantar min da hakali da fadin ai murna ne kawai ke damun shi a lokacin.
Ki kwanta yace dani haka na kwanta a sanyayye tare da tausayin kan mu ga halin da muke ciki na rashin lafiya a jikin mu .
Ni yanzu in uncle ya mutu ya barni yaya zanyi da rayuwana jamma, a da sauri na kawar da wanan tunanen a raina tare da kai hannu na na dan shafa Abba dake barci a gefe na.
Ina sauke ajiyan zuciya hannu na guda nakai a saman goshin uncle wanda idon shi ke a lumshe a lokacin.
A haka barci ya dauke mu dama karfe uku na dare yayi ko haka yasa mu makara da safe ba laifi ya samu barci kamar yadda nace mashi din zai samu.
Washe gari ban fito daga dakin uncle da wuri ba don makaran da mukayi yan matana har sun fito sun zauna falo kin san dan kauye bai barcin safe shi.
Sai raba ido suke suga inda zan fito a gidan har Nura ta shigo ta fara aikin ta sacen na fito ganin inda na fito ina sabale da Abba daya tashi daga barci nayi mai wanka acan.
Da sauri suka taso suna gaida ni da kwana na amsa masu cikin dadin rai ina fada masu baban Abba ya dawo jiya da dare .
Sun nuna farin cikin su a hakan daki na shiga tare da kiran su muje dakin nawa a lokacin a saman gado na aje Abba na juya dauko mashi kaya in saka mashi.
Hindatu ta dauke shi tana mashi wasa maimu tace anty na zata kin fita ne da ban ganki ba nace aini maimu ban faye fita unguwa ba sai idan ya kama.
Mun gama muka fito falo bayan na shirya suna zaune suna jirana a dakin sai da nagama tsab muka fito lokacin had Nura ta hada abinci a table na dan duba nake fada mata dawowan uncle tea din jiya na kara hada mai tare da bude fridge na dauko hadin tsoho na zuba a cup na nufi dakin shi.
Na samu ya tashi yana zaune yana duban wasu takardu a hannun shi nace uncle ina kwana yaya jiki da gajiyan hanya.
Na aje kayan kafin ya amsa na juyo na dan kai mai kiss a saman goshin shi yace da sauki madam yaya gida yaya bakin ki kuma ?
Suna lafiya na bashi amsa ina zama kusa dashi nace yaya jikin naka don yanzu na kulla a raina duk fushin shi ko shirun shi zanyi kokari inaga na kara kawo kusanci a tsakanin mu.
Ko zan samu in rage mai yawan saurin fushi a rayuwan shi wanda ni kadai ne a yanzu zan iya kawar mashi da hakan.
Na fada masu ka dawo suna can suna murna na barsu suna karyawa a falo yanzun haka.
Yace akwai kaya cikin kayan da na dawo dashi ki duba ban samu wani lokacin tsaya yi maku tsaraba sosai ba don yanayin jiki na.
Uncle aimu kullun cikin tsara ba muke ina kai hannu na saman cup din maganin tsoho daya bamu musha.
Dauka nayi na kurba na kara kurbawa sosai sai na mika mashi don kawar da zargin wani abu a ranshi duban cup din yayi yace wanan kuma may nene haka ?
Magani ne kasha uncle yana da kyau sosai wallahi tsoho ne danaje ya sama muna don yanayin jkkin mu sai dai ban fada mai ko may ye ba don kada yaji kazantar sha.
Amsa yayi ya kurbe duk ya aje cup din tea din na mika mai yasha nace irin na jiya ne na hada ma naga ka samu saukin tarin jiya da dare.
Kwana kikayi ke nan gadina ashe naji ya fada nace ba dole ba baban mu ya dawo gida ba lafiya ina naga kwanciyan hakalina.
Murshi yayi ya karba ya fara dan spping din tea din a hankali yana lumshe ido har ya shanye ya dan yi gyaran murya nasan cittan ne ke aikin shi a lokacin.
Tashi muje in gaisa da bakin nawa yace min bayan tea din ya dan fada mai wurin na dan gyara kafin mu fito na kwaso kayan da na kai mashi tea din zuwa kitchen.
Suna zaune sai wasa suke ma abba yana dariya suka ji muryan shi a bayan su yana cewa wasu kauyawa ne haka a gidan namu ?
Juyowa sukayi suna gaishe shi ban fito kitchen din ba sai dana dauraye kayan dana shiga dasu din don rage ma Nura aiki.
Na fito na samu yana hira dasu cikin natsuwa yana tambayan su aji nawa kuke yanzu aji uku maimu ta fadi yace kaji ba kauya ba haka zaki ce ba .
Sai hindatu tace primary three yace a a ashe hundatun dai ta waye tafi maimuna jin turan ci ke nan nace ko go and come back ba wanda ya sani cikin su.
Anty munaji fa ana koya muna maimu tace nace makarantan da sai an kora ku kuke zuwa yaushe kuka tafi har ku iya wani abu.
Shigowan yaya saadu ne ya katse muna hiran ya shigo yanayi mai sannu da zuwa sun dan gaisa yace da cashiar suke haka yasa uncle fita.
Don bai yarda a shigo mashi gida kamar yadda sauran maza suke amincewa da kowa ya shiga masu gida kai tsaye.
Haka a kidojin shi suke kamar mutumin da shi yawan tsare iyali da sa ido akan mace ga komai da takeyi fitan su falon mukaci gaba da hiran makaranta da yan kanne na .
Yaya Saadune ya dawo yana fadin ashe maigida baijin dadin jikin shi ne ko da ya dawo yanzun naji yace likitan shi yazo ya duba shi.
Nace yace sanyi ke damun shi mura ya kamashi yace yadai boye maki amma ai ke ma kinga ya ramay sosai ciwo yayi sosai acan fa.
Wani iri naji a raina sosai a lokacin nace nima nayi zargin haka yaya yadda naga ya ramay sosai wallahi.
Yace kafin in gama tunane yace ki bani takardu a saman gado daya aje tashi nayi zuwa kwaso mashi takardun a dakin shi.
Bayan na dauko na kai mashi na koma dakin don hada sauran takarcen daya dawo dasu daga tafiyan nan naga takardan asibiti a ciki na dauka na duba abinda na dan fahinta ciwon nashi ne ya tashi mai acan har ya kwanta asibiti.
Shine kuma uncle zai boye min hakan idan wani abu ya faru dashi fa fiye da funanen shi sai banji dadin yin hakan da yayi min ba ai ba a boye ciwo ga masoyi nace wa kaina.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/21/20, 9:58 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , , , ,


🧕🏿8️⃣2️⃣🧕


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

NOVEL DINA NA KUDI NE IDAN KIN KARANTA BAKI BIYA BA NA BARKI DA ALLAH KE/KAI MAI FITAR WA HAKIN AMANA YA HAUKAN KU DON BAN YAFE BA.

Wasa wasa sai da uncle ya share sati daya a gida yana jinyan jikin shi wanda yawan jigilan da yake yi ya jawo mashi hakan.
Dani da yan kanne na dana dauko daga gida muke jiyan shi ida ya hana mu fadawa ko wani dan uwa nawa da shi.
Muna cikin sulilin rashin lafiyan uncle duk da yaji sauki zuwa yanzu ya dan samu sauki sosai sai dai bai fita har yanzu.
Labarin sakin anty ya zo muna inda ake fada mashi faruwa abin yau kwana biyu ke nan waya yakeyi ina sauraren shi hankalina yayi matukar tashi dajin abinda ya furta din a waya.
Take na fara maimaita innalillahi wa inna alaihim rajjiun a fili har ya gama wayan ya dago kai nace da sauri uncle anty na daddy ya saka.
A hankali ya sauke ajiyan zuciya yana fadin innalillahi shi ma cikin tashin hankali yake maganan nace may yayi zafi haka uncle ?
Tace wai kudine ya hadasu fada ya shigo da kudin aikin su gidan washe gari zai fita dasu sai ta taba yayi yayi ta fito mai dasu taki shine ya kawo masu sabani.
Nakai zaune don tsaye nake dama akan shi na dauko mai waya a daki sai na tsaya bayan kujera daga bayan shi.
Nace haba anty wai may takeyi da kudine haka don Allah kudi dai tana samun su mijin ta kuma tana samu a gare shi.
May zai sa ta daukan ma daddy kudin shi kuma har abin yakai ga jawo masu sabani haka ina magana ina girgiza kaina a hankali cikin damuwa.
Nisawa uncle yayi tare da fadin nima tunanen da nakeyi yanzu kenan a raina don son kudin maimuna yayi yawa wallahi.
Wanan labarin mutuwar auren anty ne ya kashe min jiki yinin ranan haka na wuni a lalace ina son kiranta ban san amsan da zan samu a gare ra ba.
Washe gari mummy ta dawo daga wurin yaran ta da taje gani mun yi murnan dawowan ta sosai a ranan gidan ya koma muna happy house don kowa na nan.
Nan su maimu suka koma hira da mummy dawuya su fito falo wurin mu suna wurin ta koda yaushe.
Har uncle ya fara fita aiki bai kara magana kan su anty ba kuma gashi ina son in tamabaye shi halin da ake ciki da zancen na su.
Ranan na kira hajiya baaba ina gaida ita bayan mun gaisa mun dan taba hira da ita take cewa dani sai kuka ji labari ba dadi rabuwan maimuna da mijin ta.
Nace wallahi hajiya tace manya sun zauna akan zancen ya nuna masu sam ba zai sake zama da ita ba kuma yanzun haka aure zai yi.
Don su uwa sun hada shi da wata nan abujan har anje tsayar da magana akai mutumiyar adamawa ce wacce ya samu din.
Inna lillahi nake iya maimaitawa a bakina nace hajiya yanzu shike nan su rabu da anty din tana ina yanzu hajiya ki bashi hakkuri mana da kan ki tunda daddy yana jin maganan ki sosai.
Murmushi naji tayi tace kaiyya safiya ai labarin ba dadin jine wallahi tun da abin har da zargi a ciki sosai.
Munyi sallama ina tunanen maganan hajiya din da mukayi data ce har da zargi ni dai iya sanina shine anty tana da yawan ibada kuma banga wani alama na wanan halin a gare ta ba tunda muna fita tare wani lokaci.
Da dare da uncle ya dawo nake fada mai munyi waya da baaba har nake fada mai yadda mukayi akan maganan anty din da ita.
Yace koma may ye ai zalaman ta zai iya sawa suyi mata hakan tunda ita ta yarda dasu a marairaice nace uncle kasa baki ga maganan nan don Allah.
Yaran nan nake tausayi wallahi yace yanzu ke duk abinda sukayi maki baki tsane ta ba saboda su fa ta gujeki har abada take fushi dake.
Nace uncle ba a duban wanan domin tayi min a rayuna yadda ba zan taba mantawa da ita ba a rayuwana.
Yace yanzu yaya kike son in yi ke nan nace uncle baki ya kamata kasa a zancen anty uwa yar sherin matace sosai wallahi komai suna iya yi din su kuntatawa mutum don ba tsoraan Allah garesu ba.
Shiru yayi na dan wani lokaci tare da ci gaba da cin abincin dake gaban shi har ya gama idona yana kan shi don son jin may zaice akan maganan.
Bayan kwana uku da mukai waya da hajiya ne sai ga anty taje gidan nata duk cikin son a shawo kan daddy din take fada mata ai munyi waya nima abinda na fada mata ke nan.
Tace zatayi wani abu akan zance zata kira daddy din su zauna dashi koda tafita tunane takeyi ashe safiya har yanzu bata fita zance na ba har zata iya bada hakkuri akan magana na.
Haka yasa ta shirya washe gari sai gata ta iso abuja a lokacin mu kadai ke gida uncle yana wurin aikin shi.
Ina daki hindatu ta shigo tana ce min anty wai kinyi bakuwa tana falo nace wacece tazo tace nima ban santa ba anty na dan gyara na fito taba da baya don haka ban gane ta ba.
Nace daga bayanta sannu da zuwa ta nata bin gidan da kallo ko ina a lokacin ta juyo da sauri tana amsa wa ganin itace da sauri na karasa wurin ta ina fadin lah anty sannu da zuwa.
Yanzu kike tafe ashe duk na rude da ganin ta nayi kamar zan zauna sai kuma na nufi kitchen na hado mata abin sha.
Bayan na aje na zauna ina gaishe ta ta amsa min cikin sanyin rai ba kamar yadda take amsawa mutum da izza ba.
Nan dai nace anty kisha ruwan mana tace bari Safiya ashe kin ji abinda ya faru tsakani na da baban su yan biyu da yan uwan shi.
A sanyaye nace da ita naji anty abin baiyi dadi ba wallahi hankalina a tashe yake akan maganan tun ranan dana samu labarin.
Amma anty uwa basu kyauta maki ba anty duk irin yadda kike dasu kike kyautata masu haka zasuyi maki sakaiya dashi kuma.
Safiya bari wanan zance yanzun ai duniya ta koya min darasi sosai wallahi wai har uwa ke cewa daddy maza nake bi idan bai jan shi kuma ya yarda.
Could you believe that safiya wai uwa ke fadan haka kuma aka yarda ita ba a ce mata haka ba sai itace zata fadi haka a kaina a yarda.
Nace anty kiyi hakkuri don Allah tace ina sulaiman yana gari ko na kirashi bai dauki waya ba har sau biyu da abin ya faru.
Wayana na dauka na kirashi ina fada mashi zuwan ta yace tana ina nace gata zaune a gida wuri na yace yana zuwa ta kura min ido tana kallon yadda nake wayan cikin ladabi kamar yana gabana a lokacin.
Na sauke ajiyan zuciya nace anty wai yana zuwa ki sha wani abu don Allah ki rage wanan tunanen haka bakyau komai zai zo da sauki da yardan Allah tace safiya kina ganin hakan zai yuyu yadda daddy ya hau din nan ?
Nace anty babu abin da ya gagari ubagiji ai idan ke ce da gaskiya Allah bai basu ikon samun galaba akan ki dayardan ubangiji.
Tayi ajiyan zuciya ta dan tsiyaya ruwan ta kurba tasha mukaci gaba da maganan ya dan dauki lokaci sai gashi ya shigo gidan .
Yace madam ashe kina tafe tace ba dole ba na yanke shawars inzo wirin ku ne ku taimaka min ga abinda daddy ke shirin yi min.
Yace saki nawa ke tsakanin ku ina jin haka sai na mike uncle yace ina zaki kuma ana magana kin kuma tashi.
A marairaice nace dashi zan baku wuri ne da yace ai wanan maganan ta shafe ki tunda ta shefi anty ki ki dawo ki zauna ya fadi cikin daure fuskan shi.
Da sauri na dawo na zauna tace saki biyu ne don da cen da dadewa ya taba sakina sai kuma yanzun da ya kara daya.
Nan dai yake mata tambayoyi tana bashi amsa duk muna sauraron su yace ke ma kina da laifi wallahi.
May yasa dayace ki bashi kudi shi baki mayar mashi ba tun abin baiyi maku nisa haka ba tace sjerin shedan ne kawai ya kawo haka.
Yace ga tanan tun lokacin da muka ji zancen take bina akan in sa baki tace ban son shiga tsakanin miji da mata ne ban kula mata ba da tun tuni nayi magana akai.
Juyawa tayi ta dan kalle ni sai ta sadda kanta kasa tace nasan nayi kuskure babba a kanki safiya sherin shedan ne dana hajiya uwa da take zugani a kan ki.
To yanzu bari in kirashi inji ta bakin ki uncle yace yana lalubo wayan shi a cikin aljihu yake fadin wani yasan kin zo nan ne da zaki zo tace ba wanda na fadawa zanzo nan din.
Neman layin shi yayi kira biyu a na uku ya dauka yana fadin kadawo kenan tunda naga nomban Nigeria yace two weeks kenan da dawowa na ai na yi rashin lafiya ne dashi na dawo shiyasa baka jini ba.
Yayi mai jajen jikin yace ai bansan cewa kana kasan ba wallahi yace yana na sai dai wani magana nakeji mara dadi yana faru ?
Dariya yayi kamar a fili yake kusa damu yace may kaji kuma yace maganan ku da madam gaskiya brother banji dadin hakan ba sosai .
Daddy yace to yaya za a daurowa ne abin maimuna ta ishe ni dan uwa uncle yace dakata yaya aure ba a cewa haka abune da akeyi da fatan har mutuwa amma ba daga dan magana kadan ace rabuwa ba.
Yace na sani Sulaiman amma yanzu banjin zan iya mayar da ita gida na doni aure zanyi very soon taje ita ma ta samu wani a a dan uwa hakkuri dai zaka yi zan cen maganan auren nan don Allah kabar shi.
Sai daddy yayi murmushi wanda har muke iya jin shi yace ai magana har yai nisa yace to ni nace ka fasa tace har yanzu baka san wace zaka auro wa kan ka ba ne da bakayi ba.
Don nayi bincike a kanta bada da record mai kyau sam wallahi yace uwa fa ta sama min ita kuma ta yarda da natsuwan ta anty ta daga hannu alaman kinji ko nima da baki nayi magana irin ta kuramay nace ah tare da rike habana da mamaki.
Uncle yace kasan ba zan cuce ka ba don Allah ka janye maganan nan kayi hakuri madam ta koma dakin ta kuyi hakkuri da juna please ?
Yace to shike nan don kasa baki ne amma ka ganta ka ja mata kunne idan zata ji maganan ka don yanzu ban daukan iri halayen nan nata.
Yace insha Allahu nan dai ya gaya mashi irin halaiyan su hajiya uwa da abinda suke aikatawa a gari yace shine take son rabaka da matar ka ta hada ka da balai ko ?
Sun dan jima suna magana uncle ya kashe wayan bayan sunyi sallama da junan su ya juya wurinta yana fadin uwa yar iskan matace na sani ba yau ba shiya kika ga sam ban dauki maganan ta ko kadan da muhin manci ba don nasan kowaye uwa.
Tana share hawaye tace ni kaina nakan yi mamakin yadda tazo daga baya ta shige min jiki duk da yana fada akan in rabu da ita amma banji ba.
Ya mike yana fsdin shi zai koma sai gobe ne zaki tafi ko tace wai da yau nace zan koma yace yau kan ai dare yayi yaushe zaki isa bauchi a wanan lokacin ki bari gobe sai ki koma.
Ya fita nace ta taso ta shiga daki wani dakin na bude yana a gyara dama don baki irin haka muka gyara shi nan na sauke ta na fita na kawo mata abin bukata a dakin .
Sallah tayi na kawo mata wani dogon riga da nake ganin zai mata nace ta canza kayan jikin ta na juya zan fita daga dakin tace safiya sai na juyo da sauri.
Ganin taba da magana yasani dawo wa inda take na samu bakin gado na zauna ina sauraren abinda zata fadi a lokacin.
Tace nasan nayi maki ba daidai ba a cikin zaman mu amma duk da haka ke kina bina da alheri har yanzu banta dana sanin rabuwa dake a rayuwana ba sai yanzu da na shiga wanan halin.
Uwa ta cuce ni safiya ta cuci rayuwana wanda nasan ba banza ta barni ba a yanzu da nake tuna irin yaudara na da taitayi ita da diya ta da sunan zasu taimaka min.
Ashe ha,inta na sukeyi ban sani ba ni na dauka so ne ance ka samu dangin miji ka rike mutum guda a ciki shine na riketa ashe ita bada zuciya daya take zaune dani ba.
Ni dai hakkuri nake bata kawai don ban ma san may zance da ita ba a wanan lokacin sai bata hakkuri nake kawai dakin su mummy na shiga don in duba su.
Yaran suna kallo nace mummy kuna ciki ne tace eh ai dazun zan fito naga kuna da bakuwa bakuwa kukayi ne a gidan nace eh mummy anty ce tazo.
Wata anty ta tambaya cikin son sani ko wanake nufi nace anty na da nayi zama a wurinta lagos itace tazo dazun .
Allah sarki ashe da rabin zan santa bata taba zuwa ba nake gani ai nace ko yanzu ma ba zuwan lafiya tayi ba na zauna ina bata labarin abinda ke faruwa.
Sai dana gama fada mata tace ikon Allah haka abin Allah yake fa gashi tun ba a je ko ina ba Allah ya fitar maki da hakkin ki baki da Alhakin ta ke nan.
Ai wanan zamanin ana abu wallahi da karfi da yaji akeson tubbuke ka a gidan auren ka don kawai wani ta shiga ko idan shi yashiga alhaki zai barshi ya zauna ne shi ?
Mata kyashi da hassada yayi muna yawa yanzu sai kiga ko da yan uwa na jini da nine yanzu suna kyashin junan tun dai idan an ga daya ya dara daya sai hassada yazo ya shiga tsakani.
Ke dai fita batun yan duniya ki rungumi mijin ki tunda bai raga ki da komai ba na bukata kuyi zaman ku lafiya ba fita kike yi balle ki ga wani abun a kan shi.
Shine amfanin zama guri daya yau idan baka kula mutane ka huta ma rayuwan ka sai zuciyar ka ta zauna lafiya da kowa ba abinda ya damay ka.
Amma kinga yawan kwashe kwashen na babu abinda bai haifarwa shi nake guje wa mutumiyar ki ai kullun ina kan bakina da ita samira bata san ciwo kan ta ba wallahi.
Nace mummy may tayi kuma tace waya san iyaka yar nan gashi yanzu yar uwanta ke fadin dawowan nan danayi tace wai sabbin abaikai tayi ko yaushe idan su basu zo ba ta taje wirin su.
Kinga ai irin haka mutum ke gudu wa rayuwanshi don ba a gane mugu a goshi tunda ba zuciyar mutane ake gani ba wanan abin na yarinyar nan yana damu na wallahi.
Nace ni mummy sai yanzu nake ganun fa,idar barina in fita da uncle bai yawan yi koma wani wuri zan tafi in ba wurin Aisha ko samira zan tafi sai dai mu fita tare sai kuma idan wani abu zan fita in sawo mai muhinmanci a gare ni.
Mun dauki lokaci muna hira da ita nafito daga dakin don magariba ya kawo jiki a lokacin don haka na fito don zuwa sallah.
Ko da uncle ya dawo da dare tafito sun dan taba hira dashi ta koma daki ni dai sai haba haba nakeyi da ita a gidan in samu mu rabu lafiya ina mai kara bata hakkuri.
Washe gari ta wuce da safe tana matukar bani tausayi tace don Allah in kara yiwa uncle magana akan zancen nace insha Allahu anty zanyi bayan tafiyan ta muka zauna nan da mummy a falo muna hira.
Duk jikina yayi sanyi wai yau anty ne take kumsan bakin cikin da na miji a kanta matar da suke gwanin ban sha,awa agidan su ita da mijin ta da yayan ta a gida har damu da mu kaje cin arziki a gidan.
Yau sai gashi wai sun samu sabanin mai muni a tsakanin su dole mata mu rika taka tsamtsam da maje komai dadewan mu a gidan miji.
Haka rayuwa ke guda yau dadi gobe madaci ga bawa watarana kuma a dara uncle yayi kokari ya mayar da anty dakin ta tare da basu hakkuri daga ita har daddy din.
Haka yasa anty uwa da kawar ta suga shiga tashin hankali don komai sunyi na shirin buki a lokaci da bincike da komai suka gano uncle ne yayi sanadin komawan anty gidan daddy din.
Haka yasa suka niko gari zuwa gidan namu uncle ya shawo kan daddy ya yarda a tsayar da zancen auren su da sahura.
Muna zaune a falo duk da safiya ne amma hakan baisa sun shigo sun samay muda shirin mu a gidan bamu da wani makusa sai kanshi ke tashi yana kwance saman dogon kujera don ranan babu aiki.
Abba yana saman jikin shi yana mai wasa sai ni dasu maimu dake zaune muna mashi hiran shirmay su don yace zai saka su islamiya shine suke biya inda suke.
Sallaman su mukaji daga sama shigowa falon gidan kai tsaye da mamaki nake kallon su don shi yana kwance a lokacin.
Baiga fuskokin su ba sai dai yana kokarin mikewa zaune a lokacin gane su da yayi yasa ya daure fuskan shi yana cewa uwa kune tafe ?
Tace eh gamu mun shigo yau ziyara sannu ku dazuwa kawai nace dasu ban kara bita kan su ba kuma ban bar wurin ba sai cewa dani dasu hindu su shige ciki.
Ban kuma mike zuwa dauko masu abinsha ba na zauna tare da harde hannuwana wuri guda jikina yana gugan na shi a yanayin zaman da muka dashi.
Bayan su gaisa dashi anty uwa ta dan dube ni tace don Allah bamu wuri magana mukazo yi dashi kallon ta nayi na cewa ni tare da nuna kai na ?
Tace eh magana ya kawo mu wirin shi mukazo kafin ince wani abu don yau nayi niyar mata rashin mutunci sosai sai naji uncle yace da ita.
A, a bakizo ganina bakan duk abinda zaki fada min idan baki iya fada a gaban matana ai ba alheri ya kawo ki ba ke nan.
So idan kinyi niyar gani na ba idan zata tafi don gidan ta kika shigo kinga ko baki da right din cewa ta baki wuri ki fadi maganan ki kai tsaye kawai naji.
Don ni mata itace abokiyar rayuwa abokiyar shawarana gaba daya don ko kin fada a bayan ta ma fada mata zanyi tsab.
Nisawa tayi tace dama bawani abu ya kawo mu ba sai zancen yayana da kawana sahura gata har an saka lokacin aure yanzu kuma yace wai ya fasa komawar wanan macuciyar matar tashi da ta shiga ta fi, , , ,
Dakata uwa don Allah ban son sha shanci kin sani ke har zaki iya dauko kafa kizo min gida da wanan zancen naku na banza .
Yanzu don baku da kunya kuke kokari shiga tsakanin mijin da matan da suka shafe sheru goma sha wani abu da aure kina kokarin cusa mashi wata bare can.
To bari kiji ban cikin wanan magana naki na hauka kuma aure yaya ba zai taba kara aure ba muddin maimuna na gidan nan.
Tashi tayi da fushi tana fadin don munzo wurin ka neman taimakon bawai yana nufin munzo roko ko maula ba balle kayi kokarin fada min magana haka ?
Dole yasa ka ga mun zo wurin ka don kawai ka dafa muna ba wai wani abu ba yace oho gani mahaukacin daure kun kwaso kafan ku kunzo a hada kai ayi cuta to ban iya ba ku bace min da ga tun raina bai baci ba na kira maki yan sanda yanzu.
Sai da ta watsa min hara nima na mayar mata daga inda nake zaune ta fita fuuuuu sauran suna biye da ita a baya.
Yaci gaba da fada a falon yana fadin wanan matar tana da hankali kuwa ko abin nata ya zama hauka ne wai ?
Naji dadi sosai har cikin raina yadda uncle bai raga masu ba ya kore su ya kira wayan daddy yana fada mashi abinda ke faruwa a gidan.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/21/20, 9:58 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , , , ,


🧕🏿8️⃣3️⃣🧕

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU


Haka rayuwan mu yaci gaba da tafiya a gidan muna samun kula yadda ya dace daga wurin uncle har yasa yan kanne na wani school mai tsada a nan cikin Abuja.
Sa su makaranta yasa yanzu ina fita in kai su in kuma je hudu in dauko su in sun shirya nakaisu islamiya ranan da ban iya fita kuma sai driver ya dauko su daga school din.
Yau haka na kwana ba lafiya a jikina sai karfin halin da nakeyi ban son asan halin da nake ciki a gidan sai dai jikin ya matsa min har ban iya boyewa mutane halin da nake ciki.
Wanda ya saukar min da zazzabi zuwa rana mai karfi har yakaini da rufuwa da bargo da kyat barci ya dauke ni cikin zafin jiki nake barcin a wahale a lokacin.
Jina shiru ban fito ba tun safe da na sauke yara makaranta yasa mummy lekowa dakina ta duba ni ganina kwance na rufe da bargo har kaina yasa ta shigo tana fadin .
Safiya yau lafiya kike kuwa abinda ya falko dani daga barcin dana dan samu ke nan na bude idona dakyat nace.
Mummy ban jin dadin jikina ne yau tun dare zazzabi ya rufeni sai da nasha magani ya lafa yanzun kuma ya kara dawowa.
Ina gyara kwanci nace karfe nawa yanzu mummy tace uku da rabi ya wuce dan yunkurawa nayi ina son in dauko waya amma na kasa.
Sai mummy ta gane abinda nake son yi tazo da sauri ta dauko min wayan ta mika min neman layin uncle nayi don in fada mai a dauko min su maimu daga school .
Jin murya na yasa shi fadin may ya samay ki safiya ?
Banda lafiya na iya fadi kawai sai naji ya kashe wayan da sauri na gyara kwanciya nayi don ko sallah ban iya yiba a lokacin.
Ba afi wasu mintina ba sai gashi gidan yacewa malam musa yaje ya dauko yaran daga school ya dawo yanzu ya juya ya fita daga gidan kamar yadda ya umurce shi dayi din.
Ciki ya shigo bayan ya sallami malam musa din dakina ya nufo don yafi tsamanin ina can din a lokaci ya turo kofan da sauri.
A kwance ya hangoni kwance na dunkule a wuri daya ina makarkyatan dari duk jikina rawa yake a lokacin .
Bargon dana rufe jikina ya kwarai tare da dan taba jikina a hankali zafi yaji radau a jikin nawa jin hannun shi a jikin nawa yasa na bude ido na hanshi zaune a kusa dani yace .
Safiya baki da lafiya ne har haka baki fada min ba kuma baki kirani ba take ya daga waya ya kira likitan shi yace yana wani wuri amma gashi nan zuwa yanzu.
Yana dakin har likitan ya shigo gida fita yayi sai gasu sun shigo tare da likita dakina ya ce madam sannu yaya jikin ?
Nace da sauki ina takurewa a wuri daya yace yaya nake ji ne ?
Nan na fada mai yau kwana hudu da amai amai ya fara min sai kuma daren jiya ya saukar min da zazzabi .
Yayi min yan tambayo na bashi amsa uncle na zaune ya kafeni da idanuwan shi sai yace bari ya fara saukar min da zazzabin gobe zai dawo akwai awon da zai min.
Wani irin ras ras naji gabana ya bada don ambatan awon da yace na dauka akan maysalan ciwon mu zai mun awo din na yaba allura har biyu tare da magani.
Suka fita da uncle daidai lokacin yan makaranta suka dawo dakina suka shigo don tun a hanya malam musa ya fada masu banda lafiya shiyasa banzo daukan su ba.
Don su fison in tafi dauko su don duk abinda suka gani na marmari a hanya sukan ce min insaya masu ko kuma in tambaye su asai maku abu kaza ne ?
Gaishe ni sukeyi kowa tana kokarin ganin fuskana kamar an fada masu a fuska na ciwo dake damu na yake min.
Dan samun saukin da nayi na rarafa naje ban daki na dauro alwala nazo na tayar da sallah don har da azahar banyi ba ina kwance.
Ina sallah naji shigowan uncle dakin bai fita ba don ina sallah zama yayi har lokacin da na idar da sallah din ya miko min maganin da likita ya rubuta mai ashe shine ya fita sawowa.
Nan ya tsaya sai da na shaye maganin na koma na kwanta fita yayi ya samu Nura mai aiki yace ta hado min tea takai min dakina.
Ina kwance sai ga Nura ta shigo dakin dauke da dan karamin tire a hannun ta da kayan tea ta kawo min tana min sannu.
Ban tashi ba sai ga uncle ya shigo dakin na lura sallah yayi yana fadin kinsha tea din kuwa yana kai idon shi inda kayan suke aje kai kawai na girgiza mai alaman ban sha ba.
Zama yayi ya hada min tea din yana tashi kisha cikin commad yayi maganan shi bawai alaman lalashi ba dole na tashi na sha tea din rabin kofi na koma na kwanta ya mike yana fadin zai dan fita ba dadewa zaiyi ba zai dawo.
Har yakai kofa wani irin amai ya taso min da sauri na yunkura zuwa ban daki kafin in isa na sake amai mai karfi a tsakiyan daki na.
Wani irin kallo ya bini dashi tare da yi min sannu cikin tausayawa a gare ni na karasa zuwa ban daki amai nayi sosai duk da ba komai a cikina.
Fita yayi ya fadawa mummy nayi amai na bata dakina dashi da sauri ta taso da Abba goye a bayan ta ta nufi dakin nawa.
Mummy ta gashe ni ta sauke yaron ta fara gyaran wurin dana bata din da amai sai sannu nake mata ina fadin ai da ta barshi zan gyara wurin ko ta turo su maimu su gyara don suna gida yau ba islamiya.
Tace haba wanan ai ba komai bane aikina ne barin yi ta gama gyara wurin ta dawo tadan zauna sai ga maimu tashi tana saye da wandon tie baki iya gwiwa da yellow din dan riga sannu take min cikin tausayawa.
Nace jeki kitchen ki dauko min lemo guda biyu ki wade min su ki kawo min da sauri ta fita ta dan dauki lokaci ta kawo min na yunkura na tashi dakyat na iya shaye guda na koma na kwanta don sam banjin dadin jiki na.
Ban dade da kwanciya sai barci yau ni dake hana wasu barcin bayan laasar sai gashi ni ina yi fita mummy tayi da yara don kada su ta dani tare da jawo min kofan dakin.
Uncle ya dawo gida kafin magariba ya wuce dakina kai tsaye ya tura kofan ya samu ina barci ga lemon da aka wade min a gefe na aje yadan dade tsaye kaina ban san ya shigo ba.
Ya dan taba ni kadan sai na bude idona yace tashi magariba ya gabato da kyat na samu na tashi zaune yayi min sannu da kara tambaya ko na sake yin aman bayan fitar shi nace banyi Allah ya sauwa yayi min.
Bayan fitan shi daga dakin na daure na tashi na shiga bayi wanka nayi da ruwa masu dumi sosai na dan gasa jikina tare da dauro alwala na fito.
Sai da na zauna na dan huta na mike na gabatar da sallah a inda na idar na sake dunkulewa a cikin hijabi na banyi barci ba ina jiran inyi ishai a wurin mummy ne tashigo duba na.
Ta samu nayi sallah ta yi min yaya jikin nace da sauki mummy murya can kasa kasa na amsa mata tace har yanzu bai fada maki ba ?
Nace na rage jin sanyi yanzu kaina ke ciwo kamar ya tsage nake jin shi sannu tayi min ta dan jima zaune a wuri duk da ba hira muke yi ba a lokacin sallah ya tayar da ita tana idar wa suka dawo tare dasu hindatu suka zauna a dakin.
Uncle ya dawo dauke da ledoji a hannun shi dakin ya nufa dasu su Mommy na ganin shi suka shiga gayar dashi hindatu da maimu suna rige rigen amsan ledojin dake hannun shi din.
Mika masu yayi tare da fadin su aje karamin su tafi da babban suci ya juya wurin mommy data mike tsaye ko tana shirin fita dakin .
Yana tambayan ta bata kara amai ba ko mummy tace bata sakeyi ba sai dai kanta tace yana mata ciwo sosai kamar zai tsage.
Yace kuma again ban san may yasa zata boye min bata da lafiya haka ba har saida abin yayi nisa sosai yanzu ai ba a wasa da ciwo.
Tace kila bata dauka sosai bane haka ko irin dan zazzabin da kan zo ya wuce ma mutum ne shaaa .
Fitan mummy ya dan kwanto yana tambayana yadda nake ji nace da sauki yace kan fa ya lafa yanzu nace eh kawai badon ya lafa min ba din.
Ya ce in tashi inci wani abu ga nama na da fresh milk in sha kai na girgiza alaman a a yace to a hado maki tea ki sake sha nacs uncle ko nasha ba zai zauna min ba ne .
Ya mike yana bakuma zaki kwanta da yunwa ba kin sani dole ne kici wani abu sai cewa nayi koko zan sha ka fada wa mommy.
Koko kuma a ina za a samay shu yanzu da daren nan nace muna da abindama shi a fridge mommy ta san inda yake na bashi amsa.
Uhmmm yace kawai ya mike tsaye ya nufi wurin mommy din ya fada mata abinda nace ta tashi da sauri ta shiga kitchen din don Nura ta tafi gida ko dare yayi.
Ta damo min kunun ta kawo min shi na dan samu na sha ya zauna min a cikina har na samu barci ya dauke ni sosai ban farko ba sai cikin dare fitsari ya tayar dani.
Nan dakina naga uncle kwace a kusa dani yana barci jin motsina bayan na fito banda yasa shi falkawa yace yaya ne kuma ?
Nace ban daki na fito da sauri yace haras wan ne kuma nacs fitsari nayi yaya jikin yanzu nace da sauki cikin gundura da magana na haye gadon na kwanta a bayan shi.
Haka barci ya kara daukan mu sallah asuba ya fita yi don jin jikina yadda ya gashe kuma ina rawan sanyi yasa shi fita bai tayar dani ba.
Har yaje massalaci ya dawo ina kwance sai kaduwa jikina keyi ina wani irin sam bato hakorana suna kadawa da yan uwan su na kasa.
Hawowa yayi saman gadon tare da dan tallabo ni yana fadin tashi muje asibiti hakana .
Kasa tashi nayi dakyat ya samu na tashi nace kuma zanyi sallah kina iyawa yace dani kai kawai na gyada mai na shiga ban dakin ya biyoni ciki har nayi alwala na gama na fito ya miko min hijjab dina.
Da kyat na sallamay bai saya jiran komai ba ya dagani muka fita daga dakin da kanshi ya toka motar muka fice a gidan bayan ya buga ma mommy zamu tafi asibiti tace jikin ne har yanzu ?
Eh kawai yace ya fice bamu dawo gida ba sai da suka bani gado suka kwantar dani likitan shi ne a kaina sai wasu dakan dan shigo sun debi fitsarina da jini zasu auna su gani.
Alluran da akai min yasa ni barci sosai fita yayi ya kira yaya Saadu ya fada mai anbani gado ya kashe ya kira Aisha tace gata nan zuwa da ta sauke yara makaranta.
Gida ya kira mommy ya fada mata don hankalin ta ya kwanta shigowan yaya Saadune da samira na dan falka ban dade ba na koma barcin don karfin alluran da akai min din.
Zuwan su samira yasa shi komawa gida don anan suka barsu a tare dani sai barci nakeyi hankali kwance ga ruwa daure a hannu na .
Aisha ta zo nan suka hade wurin suna dan hira mummy da zai dawo bayan yara sun tafi makarantane yazo da ita don ance sai sha biyu result zai fito na test din da akayi.
Bai shigo dakin ba amso result din yayi suka hade da likita bayan ya karba yafita sai ya dawo dakin da nake kwance din sun gaisa dashi ya nufi wurin gadon yana tambaya ban falka ba har yanzu ?
Samira tace na dan falka dazu ban dade ba kuma na koma barci ya dade tsaye a kaina ya juya ya fita sai suka hade da likitan.
Hannu likitan ya mika mai yana fadin congratulation sir madam.cikine gare ta har five week shine ya jawo mata ciwo haka kuma kasan yanayin jikin nata gashi kuma bata dade da haihuwa ba strees yayi mata yawa ne.
Wani irin lumshe ido uncle yayi tare da dan rike hannun likitan yana fadin ya gode kamar shi ya bani cikin.
Takardan magani ya mika mai yace asamo wanan maganin idan ta tashi zata samu sauki sai tasha don jikin nata ya samu dan karfi don yanayin ta.
Bai dawo dakin ba don mata sunyi yawa a ciki yake gani wurin sayen magani ya tafi daga can ya wuce office ya duba wasu bakin da yayi sai bayan la,asar sosai ya shigo asibitin.
Lokacin ina zaune ina tauna Apple din da nace yaya Saadu yazo min dashi idan zai zo gaishe sukayi ya amsa a duduke ba tare da ya kalle su ba.
Bakin gadon ya karaso yana tambayana yaya jiki da sauki kawai na iya bashi amsa ya kalle ni duk na ramay na fada a lokaci guda kamar na dade ina ciwo .
Fita suka fariyi a dakin kamar wa yan da ya kora bansan may sa suke shakkan shi idan yana wuri har samira bata sakewa takan ce dani mijin nan naki kamar ustazu yake baya kallon mutane ko kana gaida shi sai ya dinga yi kamar yana tsoron mata.
Muryan shi naji yana ce min cin fruits din ya tashi ko da sauri na kalle shi sai kuma na sadda kaina nayi kasa .
Sai kuma na dago nace dashi ciwo yasani ci idan bashi na dan ci ba banjin dadin baki na yace aifa yanzu banda sauran wasa da saye fruits .
Haba uncle daga ciwo kuma sai in buge da shan fruits ko yaushe murmishi yayi yana gyara zama da kyau yace yanzu yaya kike ji naji sauki na fadi a hankali kamar banson magana.
Ga magani likita ya rubuta yace a sayo dazun sai kin ci wani abu zaki sha don haka barin fita in kira Aisha ta zuba maki kici sai ki sha ido na lumshe a hankali tare da fadin bazan ci abinci ba zan dai sha koko da mummy ta damo min.
Yace ok kisha din sai ki sha maganin ya mike ya fita ya kira Aisha tazo ta zuba min ya dawo ya zauna inda ya tashi yana zaune har na gama sha ya bare maganin ya bani na hadiye na koma na kwanta.
Kwana daya nayi aka sallamay muka koma gida ba laifi don na samu lafiya sosai sai dai jikin nawa ba karfi har lokacin su Maimu da hindatu keyi wa Abba wasa ina zaune na kura masu ido kawai banjin dadin hayaniyar nasu amma kuma ban iya tsawata masu su bari.
Mummy ne ta fito tana masu fada daga dakin ta lokacin uncle ya shigo gidan zama yayi nan falo inda muke mommy ta gaida da dawowa.
Bayan ya tambayeni jikin yana yi ma abba dan wasa ya leke mai wai ya dauke shi yace tafi wurin uwar ka maimu zan dan watsa ruwane a jikina.
Ya mike ya shiga dakin shi ya jima a ciki na tashi na bishi dakin nashi don ban iya jure hayaniyan da yaran ke yi haka kawai nake jin haushi komai ba gaira ba dalili.
Shiga nayi na kwanta saman gado har ya fito ya samay ni a nan nan kika dawo kuma nace haniyan yaran nake jin shi har cikin raina wallahi.
Sai da ya gama shirin shi yasa jallabiya ya fesa turare a jikin shi haka yasa nasan bazai fita ba ke nan yau kuma don baya fita hakana.
Takowa yayi inda nake din yazo ya zauna safiya naji ya kira sunana a hankali na dan bude idona da suke lumshe na sauke akan shi tare da dan kakaro murmushi a fuskana kadan.
Kin san kina dauke da ciki a jikin ki na wata daya da kwanaki da sauri na daga daga kwanciyan da nake ina fadin na shiga uku.
Kin sha uku akan may safiya ban taba zaton jin wanan furucin daga bakin ki ba domin ko abin farin cikine ya samay mu bana shiga uku ba.
Uncle abi fari ciki fa kace yaro na yana da wata bakwai uncle zakace wai abin farin ciki ya samay mu ?
Kallon da yake min ne yasani natsuwa na farga da katobaran da nake shirin yi a gaban shi a yadda na san shi da son haihuwa yanzu.
Yana yawan fada min shi haihuwa yake so yayi yanzu yana son ganin yara sun cika mai gida kamar sauran gidajen yan uwan shi da abokai.
Sai gashi ina shirin yin baranbarama da albishir din da yake min na dan cikin da ke jikina wanda ashe shiyani zazzabin nan da nake yi duk dare.
A hankali na koma na kwanta tare da lumshe idona ina mai jin zafi a raina da samun wanan cikin na jikina a wanan lokacin da ban tsamace shi ba.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/21/20, 9:58 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , , , ,

🧕🏿8️⃣4️⃣🧕

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU


Fita yayi daga dakin batare da ya kara magana komai ba nima komawa nayi na kwanta ina jin zuciya na yana min zafi maikon in ji farin ciki a raina.
Ba don komai ba sai irin surutun da mutane zasu dinga yi ga haihuwa na a kai akai da nake yi kowa zai fassara min shi da wata manufa ta daban.
Na dade a wurin kwance ban motsa ba shi kuma bai shigo dakin ba har wanan lokacin barci ne ya dauke ni wanda na dade ina yi sai a zahar na tashi don sallah.
Ko da na fito nasamu bai gidan sun fita da yaran zuwa shan ice cream dakina na nufa ban iya yin wani abuba a dakin sai kwanciya da nayi.
Ina nan kwance sai ga hindatu ta shigo da Abba dauke a hannun ta maimu na bayan ta dauke da ledan tsara da ya sayo masu.
Suna zuwa suka fada min a jiki gaba dayan su na dan lumshe idanuwa a hankali ina jin su a jikina kun dawo nace dasu anty kin ga abubuwan da baba Abba ya sayo muna yakai mu mun ga biri da zaki abubuwa da yawa muka gani inji hindu.
Murmushi nayi nace su bude kayan in gani ba komai bane sai tarkacen kayan lashe lashe na yara dasu yought din robobi nace sai kuje wurin mummy kuyi ta sha ai.
Na samu na iza su suna fita na sauke ajiyan zuciya har wani lokaci banji motsin uncle da banyi ba yasa banji dadin haka ba a raina nasan idan na biye mashi fushin nan nashi ne zai wakana a tsakanin mu kwana biyu.
Haka yasa na dan mike jiki ba kwari na nufi dakin shi don bai falo a lokacin dakin shi na nufa na tura da sallama yana ciki zaune ya tasa laptop din shi a gaba yana aiki dashi.
Jin sallama na da yayi ya dago kai ya dan dube ni kadan ya mayar da kan shi ga abinda yake yi a hankali na karaso inda yake zaune nace.
Uncle sannu da aiki kun dawo yau kasha kiriniya da rawan kai wurin su maimu ya ce na kaisu shan iskane da Abba don kin san farin cikin yara shine nawa a yanzu.
Nasan magana ya fada min a fakaice cikin dakewa nace Allah ya raya muna su ta farkin addinin musulunci yace amin kawai ba tare da ya dube ni ba.
Gyara zama nayi da dakyau a kusa dashi na dan dora kaina saman jikin shi ajiyan zuciya naji ya sauke a raina nace su zuciya manya.
An fara sauka ke nan don naji ya sauke ajiyan zuciya karo na farko shiru ba wanda yayi magana a cikin mu har na wani lokaci sai aiki yake yi wanda nake gani sako yake turawa a lokacin.
Gajiya nayi da kwanci haka na na sai na dan juya ina kokarin jawo filo in kwanta sama muryan shi naji yana fadin kin ci abinci kuwa nasha koko nace mashi.
Koko ba abinci bane kin dai ji likita yace ki dinga cin abinda zai gina maki jiki ko yaushe uncle zan ci nace a takaice.
Rufe laptop din yayi ya mike ya fita sai gashi dauke da abinci yazo ya aje a gabana yana fadin oya tashi ga abinci ki ci na kai duban ga abincin .
Sakwara ne da miyan gaye yaji agushi sai manja da tayi amfani dashi da nama manyan yanka da ta saka sai kamshi ke tashi a gabana.
Take naji warin abincin ya nashe ni har amai na son taso min a lokacin amma don dai kawai in farauta mashi rai haka na daure nayi loma biyar da kyat har nayi kusan rabin plate din dake gaba sai dai ban kai ko ina na ba koda ya dawo mayar da kayan abincin ya samay a bayi ina haraswa sosai.
Na galabaita abinda yasani barcin yamma ke nan ranan sai magariba na falka jina na shiru da mommy tayi ta tambaya lafiya nake kuwa ?
Murmushi yayi yace mummy jikin nata yanzu sai a hankali ai don lalurar juna biyu sai a hankali.
Murmushin jin dadi mommy tayi tana fadin masha Allah nikan nayi tunanen haka yadda naga ta koma kwanan amma naji dadi jin haka wallahi .
Maganan mummy wanda yasa shi jin dadi har cikin ranshi yace mummy na gode kwarai don Allah a tayani kulla da ita a gidan idan ban nan.
Kada kaji komai suriki wanan ai farin cikin mu ne mu duka Allah dai ya raba lafiya ya bamu masu albarka rayulayyu masu tarbiya yace amin mummy.
Dana tashi don sallah magariba da yayi na dawo dakina na yi ban fito ba har ishai sai da mayi wanka na fito falon bai shigo gida ba har lokacin.
Mommy tazo ta samay ni a falon zaune wuri ta samu tana fadin ayya safiya ashe abin arziki muka samu da sauri na kalleta tace mun zamu samu karuwa .
Murmushi nayi na sadda kaina kasa don kunya tace wanan abin yayi dadi wallahi da sauri nace haba mummy.
Dudu fa Abba yanzu wata na bakwai yake shiga ko fafiya bai fara ba kuma ace na samu wani ciki a jikina.
To may ye naji ta katsani yo mai shege ma ta goya balle ke naki da ubansu zaki wani ce bai yi ba ai indan ma wata uku uku zakiyi kina haihuwa ba wani matsa bane a hankan yanzu.
Don ko uban su na da halin kula abin shi yanzu ai gara mutum yayi ya gama da wuri wanan haihu mai wahala na yanzu.
Shiru nayi ina nazarin maganan ta sai kuma na tuna a garin mu matar da tai ciki da goyo har waka ake mata da shagube bata da sauran shakat a rayuwan ta kuma.
Ummi tayi haka lokacin goyon hindatu ta samu cikin autar mu har girkin ta inna tace basu ci a gidan wai tayi kazanta tayi abin kunya don bakar jaraba.
Ta shiga wani hali a lokacin sosai a gidan mu duk da banda wayo amma na fahinci halin da mahaifiya na take ciki a lokacin.
Dole kula da hindatu ya dawo kaina sai inda na fita zuwa makaran ta hindatu ke raban ummi a lokacin inna na bin ta da gori tsakar gida.
Muryan mummy ya katse ni tana fadin ai yanzu mata sun waye da ne can ake daukan shi wani abu amma yanzu ai ya zama isa ga mace goyo da ciki ikon Allah.
Ni dai murmushi yake nayi kawai taci gaba da fadin balle ke da ba nono ma diyan ki ke sha ba ai gara kiyi abinki da wuri ki gama ki gyagiji ko taso tare da su.
Dariya ta bani don jin wai in taso tare dasu da tace sai dai banyi magana ba hira take min uncle ya dawo daga wurin sallah.
Muka gaida shi da dawowa daki ya wuce nasan ruwa zai watsa mu kuma mukaci gaba da sha anin mu a falon har lokacin da ya fito mommy ta shige ta bar mu da su maimu dake kallon katun da Abba dake kiriniya ya koyon mikewa tsaye suna ihu su kuma idan ya mike din.
Zama yayi har lokacin fuskan shi babu annuri a ciki sai dai bai daure sosai ba zama yayi yana kallon yaran yana murmushi.
Juyowa yayi gare ni yana fadin maimuna na gaida ke takira wayan ki a kashe sai ta kirani nace ayyah suna lafiya tun da na dawo asibiti ban koma ta wayan nan ba ai zankira mu gaisa idan na tashi.
Abinci ya mike yaje yaci anan ya barni kwance sai da ya gama ya dawo dauke da fruits a plate ya aje a gaba hindatu na bayan shi dauke da cup din koko mai zafi yana tururi.
Kallon shi nayi na yamotsa fuska yace kina nufin haka zaki kwanta da yunwa a cikin ki dauki cup din nan kisha kokon tunda shi kike so in kin gama ga fruits nan ki sha.
Ya koma ya zauna yana facing dina dole na dauka na dan kurba ina yamotsa fuskana ba halin magana ya tsureni da idanuwan shi da kyat na shaye dan cup din kunun ina sauke numfashi.
Gyatsan haraswa nake yi har na samu ya fada min ban fito ba na koma nakai kance alokacin komai ban so don jikina gaba daya ba dadin shi nake jiba.
Ashe barci ya dauke ni har yayi kallon news yaran suka shige sai lokacin daya gama naji yana tayar dani inje in kwanta yace ya rufo min dakina don haka muka wuce dakin shi gaba dayan mu.
Ba laifi na samu na dan warware don kulawan da nake samu gurin uncle da mummy sosai suke bani kulawa yan kaina ma ba a barsu a baya ba suna nasu kokarin dani sosai a gidan har gyaran wuri suke taya mummy da yan sauran aiyukan daba su fi karfin su ba.
Anty tazo daga lagos gani na da yaran ta har da funke mai aikin ta don ita kadai ke gidan yanzu su fati da faiza kowa ya koma gidan su da zama.
Naji dadin wanan zuwan na anty da dare muna dakina da ita tace ashe cikine yake wahalal dake haka amma wanan cikin yazo maki da wahala don kamar bakiyi haka ba cikin Abba ko ?
Idona ya kawo hawaye nace anty sam banyi tsamanin samun ciki yanzu ba duka duka fa Abba wata bakwai yake da haihuwa na takwas yanzu yake bidan shiga.
To shine may safiya ga mijin ki shi yana ta farin ciki da samun cikin shi ke fada min kin samu ciki mai wahala wanan karon cikin yana wahal dake sosai.
Ni gaskiya anty ban son daukan ciki yanzu gaskiya da sauri tace saboda da may nace kinga wata da muke zuwa amsan magani da ita tayi irin haka.
Sai jinta yayi week kamar zata mutu wallahi da kyat ta sha har an debi tsamani a gare ta sai likita ya fada mata masu irin lalurar mu bai dace suna saurin haihuwa ba da wuri haka saboda jinin su dake ragewa suna iya shiga wani hali kan haka.
Shi kuma uncle ya kasa fahinta na gaba daya yama ki bari muyi maganan dashi na fahinta tace toke yanzu yaya kikeso bayan cikin ya riga da ya samu dole zaki kula da kanki sosai yanzu.
Shiru nayi ban fada mata nufina na son in zubar ba don naga tana goyon bayan uncle tace kada ki hada kan ki da waccan don kila ita bata samun kulan da kike samu.
Mun dade muna hira ta tafi ta kwanta nima na shige kwana daya sukayi muna suka juya lagos don dama ganina kawai suka zo yi.
Yau na tashi da son gyara jikina don yanzu shagon matar nan yar uwar wacce tayi min gyara a bauchi na karbi lambata can nake zuwa tayi min gyaran da nake so.
Tare da kanne na na tafi har da mummy amma tace kitso kawai take so nan samira tazo ta samay mu tunda nace mata gamu wurin gyaran jiki tace gata nan zuwa itama ayi da ita.
Angama ma mummy kitso ganin yaran zasu damay yasa sakina ta kaisu gidan ta su zauna ta dawo mukaci gaba da hira.
Nan nake fada mata ina son zubar da cikin jiki na ido ta zaro min tace saboda may madam niko a gani na da kibar abinki kwana nawa kin haife abinki safiya.
Wata mata da ta girmay muna tana jin mu tace mai zai sa ki zubar yar uwa idona yayi kwalkwal ya kawo ruwa nace yanzu fa dana watan shi bakwai da haihuwa hajiya.
Shine suke son in bar cikin kuma inyi yaya da su su biyun don Allah tace ashe ba a yaye shi ba ma lalai wata bakwai kan akwai wahala wallahi.
Yakai wata nawa cikin jikin naki nace yanzu wata biyu da kwanaki bai cika uku ba cif tace ai mai sauki ne barin rubuta maki su kwaya sai ki saya ki sha mu gani idan bai fita ba sai ki hada da alluran shi.
In haka yaki fitar dashi sai kin je an cire maki ke nan ta bude jakkata ta ciro takarda da biro ta rubuta min nayi mata godiya na karba har mukayi musayan lamba da ita a wurin.
Ban je gida ba sai dana biya na sayi maganin a wani babban chemist dake hanyan mu na kwaso mummy da yaran gidan su samira muka dawo gida.
Kai aka wanke min sukayi min kitso sai dai ba kanana ba sai gyaran jiki da sukayi min don jina nake na koma wata irin gaja dani rashin gyaran da ban samu kwana biyu inyi.
Jin jikina nake yau kamar ba nawa ba sai dare Uncle ya dawo don suje site din su dake sulaje yau a can store din su yake babba inda suke tara kaya indan an kawo masu.
Idan yaje can ya dawo yakan gaji sosai don aikin wahala akeyi a wurin har shi yakan taba aikin aje a dawo basu da hutu ranan.
Ko da yadawo ya gaji sosai wanka yayi yaci abinci ya kwanta nima ban dade ba na samay shi a dakin har ya kwanta ko sai dai bayi barci ba.
Na shigo na rufe kofa ido ya tsura min daga inda yake kwance har na iso gare shi yace yau wanan gyara haka sai ya mayar min dake wata irin yar yarinya under age.
Murmushi nayi na karasa hawa godan na kwanta nace under age haka kamar kumama dani yace to be serious yau kin koma yarinya sosai murmushi nayi kawai ina gyara kwanciya na.
Ranan bai barni ba sai da ya dan lalube ni muka gama muka sake wanka na kwanta zuwa asuba sai zazzabi ya rufe ni kuma da kyat na tashi nayi sallah na kara kwantawa.
Har ya gama shirin shi ban sani ba sai da zai fitane yake tayar dani zai fita indan jikin ya matsa ki kirani mu koma asibiti tau kawai na iya ce mai na koma na kwanta.
Yafita ya sauke yara makaranta ban fito ba sai kusan shabiyu koshi na fito in samu dan ruwan liptop ne in sha.
Anan falo na zube na umarci Nura ta hado min ruwan liptop jin muryana yasa mummy fitowa tana min yaya jikin , ?
Fuska a yamutse nace mummy da sauki take cewa ko jigilar gyaran jikin da nayi jiya ne ya saukar min da zazzabi ciwon ne kawai ya dawo mummy.
Litop din ya taimaka min naji bakina ya koma min dan daidai har na sha lemu anebi wanka na naje nayi dakina koda na fito wayana yana ruri a lokacin.
Na dauka da dan sauri kada ya katse uncle ne yake kirana a lokacin ina dauka nace uncle yaya aiki shiku bai tsaya bani amsa ba sai tambayana yayi da yaya jikin naki ?
Nace da sauki uncle kin ci abinci ya tambaya nace mai naci alhalin banci din ba bani mummy yacd nace mommy tana dakin ta nima dakina nake kwance.
Ok sai ki sha magani kafin in dawo Allah ya sauka nace dashi amin ya kashe wayan na wurga wayan saman godo naci gaba da shirina.
Bayan yadawo gida da yaran ya samu naji sauki sosai zaune ma nake da Aisha data kwaso yara tabiyo tanan dubani da jiki mun da ita kafin ta wuce gidan ta.
A gida yayi magariba duk banda wani matsala komai zuwa tara kaina ta fara ciwo kamar zai tsage min haka yasa dole ya fita ya samu min magani nasha.
Zazzabi sosai nayi da dare dole da safe muka nufi asibiti ban so zuwa ba amma ba yanda zanyi dole naje aka dubani muka dawo gida.
A hanya ya matsa min may nake so ya saya min nace ban son komai sai masa mai zafi idan zan samu dariya yayi yace aiki ko ya samay ni ni madam wani irin ciki kika dauko wanan karon kuma ?
Haka mukayi ta yawo gidajen abincin hausawa ana muna kwantace sai da kyat muka samu masa yayo min take away leda biyu muka juyu gida ina ji a mota yana ma hajitan shi waya ta sa a turo muna da masa bana ya samu dan gargajiya a gidan shi.
Dariya tayi tace insha Allahu goben zata sa ai min za a samu wanda zai kawo min in Allah ya yarda tace ya bani waya idan ina kusa muka gaisa tayi min yaya jiki har muka iso ina magana dasu.
Ban tsaya falo ba dakina na nufa na aje jaka da maganin da aka bamu asibitin irin ta masu lalurar mun ta masu ciki sai na saka a jakkana.
Ruwa na watsa ma jikina don in ji dadi nafito nayi sallah sai na dawo falo na zauna masan naci shi sosai kusan na kusa cinye take away din.
Na sha ruwa nan muka zauna hira da mummy shiya dawo gida da yaran yau ma ya zauna kusa dani yana wasa da Abba kamshin turare shi ya haddasa min wani irin ciwon kai.
Gudu nayi na shige daki na kwanta sai kuma amai yazo min nan na amaye dan masan danaci koda zai saura a cikina sai kadan.
Shine ya shigo yana tambayana a harasawan ya dawo ne kuma yanzu kai yace har ya juya yace kin sha maganin ki kuwa nace ban kai gasha da na bari idan zan kwantane tunda sunce yana da karfi.
Ina kika a je maganin yace min tare da kafe ni da idanuwan shi bako kiftawa nace gayan nan cikin hand bag dina ina fadi ina mikewa zaune don nasan shan maganin zanyi.
Sai damay yana cikin tona jakkan ya jawo wanan maganin da na sawo a chemist wanda matar nan ta banj na zubar da ciki.
Jin shi shiru danayi yasani juyowa inga may yake yi a lokacin maganin na ganshi rike dashi a hannun shi yana karanta wa.
Take naji gabana ya fadi a wurin juyowa yayi yana tambaya na wanan maganin may Safiya ?
Magani na ne nace mashi yace ai nasan maganin ki ne na may ye na tambaya ?
Kaina na dukar kasa ban ce dashi uffan ba Safiya naji yace na dago kaina yace cutana zaki yi komay ?
Shiru nayi na kasa magana sai naga ya fita da maganin a hannun shi take fuskan shi ya juye ya koma wani irin zaki a gabana.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/21/20, 9:58 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , , , ,

🧕🏿8️⃣5️⃣🧕

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU


NOVEL DINA NA KUDI NE DON ALLAH DON ALLAH IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA DON DON SHIGA HAKKIN WANKI DON GIRMAN ALLAH

Ke kuma mai fitar min da da novel nasan basai anje lahira ba ubangiji yazai daukan min fasan akan ki don kin nuna baki da imani da tsoron Allah a fili.
Mai imani bai wanan halin ko yaya yana nuna tsoron Allah ba zance dake komai ba amma zaki ga ni a rabon ki shi amana bibiya yake ta inda baki zata ba.
Jin dakin shiru bakajin komai sau karan nauran wutan dake aiki a dakin sai ko ni da nake sauke numfashin wallah har wani zufa nake yi don tsoro da fargaba alokaci daya.
Da kyat na yunkura na mike na sauke kafafuwa na daga saman gadona cikin karfin hali na nufi dakin shi don babu kowa a falo gidan yayi wani tsit a lokacin.
Ganin kofan shi a bude ya tabbatar min yana gidan har wanan lokacin bai fita ba ke nan da far gaba na tura kofan a hankali na shiga dakin.
Ya tsaye bakin window dakin dake kallon haraban gidan ya harde hannaye shi duka biyu a saman kirjin shi kamar bai san na shigo dakin ba ya nuna min.
A hankali jikina a sanyaye na karasa inda yake tsaye har na iso gab dashi na sa hannu na da nufin in rungumay shi ta baya ya juyo a zafafe cikin zafin rai ya kwashe da wasu irin lafiyayun maru guda biyu masu kyau.
Sai da na kai kasa ban sani ba ya nuna ni da dan yatsan hannun shi yana fadin ashe baki da mutunci baki da tausayi ban sani ba Safiya.
Ashe ke mutumiyar banzace nake zaune da ke ban sani ashe baki da tsoron Allah a rayuwan ki ban taba zaton haka ba a gare ki ban taba ba Safiya.
Ashe daukan da nake maki ba hakana kika dauke ni ba ke may nayi maki da kike son ki cuce ni haka da zafi may na rage ki dashi wanda na kasa baki kike son saka min da wanan abin da kike shirin yi min.
Ni dai ina duke na rike kumci na sai hawayen da ba kuka nake fitar wa wani nabin wani iri rike da kumatuna da yasha mahaukatan maru gare shi.
Kuma cikin maganan da yake fadi wani ma ban fahintar shi a lokacin wanda nake ji kuma ta yaya zan fara bashi amsan su don suyi min yawa a lokacin.
Naji yace uban wa ya baki wanan magani a ina kika samo shi yau naji na tsane ki nayi dana sanin auren ki dana nayi safiya tunda baki so na da karuwa banga dalilin zama dake ba a rayuwa na.
Dago kai nayi na kalle shi karo na farko bayan marin da yayi min da hawaye na shabe shabe a fuskana.
Mikewa nayi daga inda nake tsam ina shirin fita dakin wani tsawa ya daka min yace dakata baki bani amsa na ba tukun .
Uban wa ya baki wanan maganin nace tare da nuno min maganin a hannu shi dan kuturun yazo min nima a lokacin ban bashi amsa ba kawai na fice a dakin ba tare dana kara juyowa gare shi ba.
Daki na koma na haye gado na dunkule a wuri daya take wani irin kuka yazo min a lokaci daya mummy ne ta shigo dakin don taga fitowana daga dakin shi ita da Nura suna magana a falo.
Hajiya lafiya may ke faruwa ko jikin naki ne ya matsa maki haka take tambayana a jere lokaci daya sai kuka nake ban iya magana ba.
Banko kofar dakin da yayi da karfi shiya dakatar da mommy dake tsaye a kaina tana jera min tambayoyin ta a lokacin.
Ganin mommy bai hanashi fadin abin da yazo fada min ba yace ni zaki mayar mutumin banza ina magana ki wani fitowa ki barni yau sai kin fada min wanda ya baki maganin nan ko ki fice ki bar min gida na don ba zan zauna da macen da zata haince ni ba.
Da sauri mommy tace subbahanallahi Alhaji mai yayi zafi haka tsakanin ku har kake fadin wanan maganan haka ?
Kallon mommy yayi cikin bacin rai kamar zai mata magana kuma ya fasa nasan zuciya ce ta kawo mashi maiyi a banza balle yau ga dalili.
Ya juya gareni yace ke har kin isa baki san halina bane wallahi da bakiyi min hakan ba ban cutan na tare da ni shi kuma Allah bai yarda ya cuce ni.
Don Allah Alhaji kayi hakkuri ku bi abin sannu niko ina saman gado na dunkule sai kuka nake yi ya juya wirin mommy yana fadin mummy ashe duk ciwon da yarinyar nan keyi ita taja wa kan ta.
Da sauri mommy ta mayar da han kalin ta gare shi tace ita taja wankanta garin yaya haka ya faru kuma hajiya ?.
Gata nan shi nake tambayan ta tana son raina min wayau yanzu bayan Allah ya tona mata asiri wai mummy kin san zubar da ciki take kokarin yi yanzu na kamata.
Innalillahi safiya baki da hankali ne may yayi zafi haka cikin da kowa ke farin ciki da samun shi zaki ce kuma zaki fitar haba haka baiyi kyau ba wallahi.
Ni dai kukana nake ban saurare su ba don Allah Alhaji kayi hakkuri tunda ta gane kuren ta ai mata afuwan kurciyane ya kai ta ga hakan da batayi ba idan ta sani.
Kurciya ina kurciyan yake anan tunda har tasan ta zubar da ciki ta cuce ni ga abinda nake so don tana munafuka wawiya.
Zagin yayi min yawa uncle na iya furtawa da karfi a cikin kuka ya watsa min harara yana fadin ok har ma kina da bakin magana zagi yayi maki yawa ko ?
Alhaji kayi hakkuri don Allah ka bar zancen nan haka na tunda ta gane kuren ta yace sai fa ta fada min a inda ta samo wanan maganin zan barta mommy yace.
Zuwan yaya Saadu da ya kira ne ya katse shi ya fita falo wirin shi ya samay shi nan yake fada mashi abinda ke faruwa a tsakanin cikin bacin rai.
Mommy ce ta fito dakina a lokacin goye da Abba bayan ta da yake barci ta karaso inda suke tana gaisawa da yaya Saadu daya shigo.
Yaya saadu yace mummy abinda safiya take shirin yi ke nan ashe shiya tare da fadin ina mommy zata san mugun nufita tunda batason kowa ya sani nima Allah ne ya nuna min tun batayi min sawalwalin cikin ba.
Ka fada mata idan bata fada min wanda ya bata wanan maganin ba sai ta barmin gida na yau don ban zama da mace da bata sona da karuwa .
Yi hakkuri yallabai ina Safiyan take yana tambayan mommy tace tana nan dakin ta yace mommy ai min magana da ita don Allah.
Nan mommy ta juya ta shiga wurin ta fada min ga yaya Saadu yana magana dani azuciyar ta kuma sai addua take Allah dai yasa ba samira bace don rawan kan samira na da yawa.
Sai can na fito saye da hijjabin sallah na har kasa ina yiwa yaya saadu sannu da zuwa cikin miryan na da ya dishe saboda kuka da ciwo da fargaba.
Ina zama Uncle yana bina da harara yaya saadu ne yace safiya yaya haka kuma ya faru cikin lalama yake min magana wanda shi uncle din bai so haka ba a gare shi so yayi ya balbala ni da bala,i a lokacin.
Sai kuma yaji yana min magana may kama da lalashi yace may ya kawo haka safiya haihuwan ne baki so ko tsoro kike ji ne ?
Haushine ya kama uncle yace kaga malam ba lalashinta na kiraka kayi ba ta fada muna inda ta samo maganin nan in ba haka ba bata zama min gida.
Na dago cikin zafin rai nace samay idan na bar maka gidan ina dai da gidan ubana ko sai kuma idan ginan da kai muna zaka sa a rushe ka mayar muna da namu.
Tashi yayi kamar kububuwa yayo kaina yaya saadu ya tare shi yana fadin bari mubi a hankali yallabai abin bai kai haka ai zata fadi nasan halin safiya.
Yace amma kana jin har ta samu bakin fada min bakar magana ko da mamaki yake kallona ni kuma cikin zafin rai da hasala nace.
Dole in fada maka kana ta magana in bar maka gida, gida kan tunda ba anan aka haife ni ba ai nasan ba gidan ubana bane sai in bari din sai may.
Safiya ashe haka kike inji yaya saadu nace yaya abin yayi min yawa ne wallahi daga magana sai ya wanke ni da mari kawai.
Mari kinyi laife mai muni ne safiya dole ya mare ki ko nine abinda zanyi sai yafi wanan da yayi maki ai don may ba zaki tsaya kuyi magana ta fahinta ba kin tsaya garda yace ki fada mashi inda kika samo magani kin tsaya kina ja.
Wai may ma zai sa ki zubar da cikin ne safiya may cikin ya tare maki da kike son zubarwa ne da baki iya hakkuri ki haife shi.
Yaya maganin nan ya dade a cikin jakkata wallahi ba yanzu na saye shi ba da yake nufi ni kuma ba wanda ya bani dama na san shi tuntuni sai na sayo da nake ganin kamar ciki ke gare ni a baya.
Ba yanzun na saye shi ba yaya karya take wallahi yanzu ta sayo shi take sha don cikin ya bare to bari kiji ni ba dan rayuwa kawai na kawo ki gidana ba.
Don raya sunnan ma,aiki na kawo ki mu hayayafa mu cika sunna mai karfi ba a haihuwa ke aka haife ki yana fadi kamar zai buge yaya saadu ya rufe da duka.
Ranan iyakan bacin ranshi na gani a gidan ni kuma naki fadin inda na samu maganin na tsaya kai da fata maganin ya dade min a cikin jakkana kuma ba wanda ya bani maganin saye kawai nayi don na san shi.
Naki fadi ne don kada naja wa matar mutane jiddali daga taimako nasan kuma idan na fadi gaskiya abin zai iya shafan samira duk da bata da laifi aciki amma muna tare aka bani.
Har magariba ya gwauta muna wurin zaune yaya Saadu da mommy sai bashi hakuri suke yi suna fadin nayi kuskure sosai na bashi hakkuri.
Nace ni ban sha ba koda yake fadin nasha ban sha maganin ba aida cikin ya fita inda nasha din yace cikin dai yafi karfin ki ne yaki fita.
Nace ban dai so zubar dashi ba da babu abinda zai hana na zubar din yace yaya Saadu kana dai jin abinda take fadi.
Tayi laifi ban isa ta bani hakkuri akan abinda tayi min din nace ni ban san nayi laifi ba tunda ban sha komai ba.
Yaya Saadu ya tursasa akan in bashi hakkuri a gaban nace nayi kuskure ka yafe min daki ya wuce zuciyar shi nayi mai kuna sai tuna maganan hajiya baaba yake yi da tace mai ya rage matsamin don zan iya bijere mai daga baya.
Yanzu ko gashi ya ga na fara din wai safiya ce yake fadi take fadi har tana ikirarin na rushe gidan da nayiwa mahaifanta na mayar masu da kangon su.
Kwafa yayi yace dani kike wasa yarinya zan nuna maki kuren ki a gidan nan zaki san kin taba ni don sai kin gane kuren ki.
Yana alwala yana maganan zuci a falo kuma yaya saadune yayi min fada sosai akan yadda nayi ban kyauta ba nayi laifi kawai in bashi hakkuri.
Nace yaya kanaji fa yana fadin ban kwana mashi gida yau akan maganan ga zai ta fadin haka in ba dama ya gaji dani bane yana son mafita akaina.
A daidai lokaxin ya fito daga dakin shi ya kallemu kamar harara yana fadin Saadu muje muyi sallah rabu da ita mommy jekiyi sallah lokaci ya kure ko.
Yaya Saadu ya kalleni yana mikewa yace safiya yaushe kika kuma haka ne wai duk kin bi kin tada hankalin mutane a lokaci daya haka.
Don Allah ki kara bashi hakkuri idan na wuce don ba lalai ne in dawo tanan ba yayiwa mommy saida safe ya fice daga gidan, itama mommy tashi tayi zuwa sallah inda na dan dade zaune ina tuna irin karfin halin dana rufe idona nayi masu.
Mikewa nayi zuwa sallah nima ban fito don ishai yayi nan na zauna abina sai su hindatu ne suka shigo dakin suna min hira wanda ba fahintar su ma nakeyi ba.
Fitar maimu sai gata ta dawo tana fada min anty baban Abba ya dawo yana falo zaune nace ku tafi ku gaida shi yau banjin dadin jikinane.
Yaran suka fita zuwa wurin su suna gaida shi da dawowa ya amsa masu fuska a sake kamar yadda ya saba yi dasu kullun.
Nan suka dan zauna suna mashi hira suke fada mai antyn mu tace yau jikin ta yana damun ta bata iya fitowa Allah ya sauwaka yace ai na bata magani dazun.
Mommy ce ta kirasu suka shige ciki wurin ta ya gama abinda yake yi ya shige dakin shi batare da ko waigowa kofana ba.
Nima nasan da hakan shiyasa nayi zama na a daki ban fita don yasan nima ina jan zancen na gama har na kwanta a lokacin naja bargo na rufe kaina a ciki.
Da safe Samira ne tazo gidan dubani da kuma tambayana yadda akayi haka ya faru har na bari uncle yaga inda na aje maganin.
Nace kedai bari Samira baban Abba yakai dan halas wai mutumin da bai taba, taba min jakka ba shine wai da yake Allah yayi asirina zai tono sai gashi yaje daukan maganin da muka karbo asibiti a cikin jakka ta.
Na manta shaf wallahi da wanan maganin ai da na yunkura na tashi komai ciwon da nake ji na rufawa kaina asiri.
Tace ke dai bari aini da yayan ki ya fara min maganan baki ga yadda na tsure ba ina gudun suna na yafito a maganan tawa ta samay ni, in shiga uku gashi muna alkunya da mutum da ina zan saka kaina.
Dariya nayi mata nace ni zan fara ne in fadi gaskiya da fa har gidan matan nan yana iya zuwa yai mata cin mutum ci shiyasa na kafe dacewa dama nasan maganin na dade da sayan shi.
Zai kuma iya hani zuwa gyaran jiki shiyasa nayi mai borin kunya na labe ga zancen gida don yabar maganan.
Kuma nasan abinda yasa yayi sanyi ke nan a yadda ya dauki niyar ci mun mutunci ido rufe tace kai safiya sai kika lauye bawan Allah da jijiyoyin shi.
Nace ke kuwa kin san yadda uncle ya hau har fa maru biyu ya bani masu kyau rabona da duka tun gidan yaya Ahmed fa samira.
Tace ni banga dalilin ki sin zubar da cikin nan ba safiya baki rasa ci ba baki rasa shaba a gidan nan wanda zai gina maki jiki.
Don may zaki nace sai kin halaka dan cikin ki kika sani ko gwauna ko shugaban kasa kika samo muna zakiyi muna sawalwalin tsiya haka.
Nace samira ai yanzu na yi nadama sosai yadda naga uncle ya kwalafa rai ga haihuwan nan haka yasa jikina yayi sanyi wallahi.
Tace yanzu dubara ya saura gare ki ai sai ki san yadda zaki bashi hakkuri ya sauko maki don nasan yanzu ya hau sosai dake a gidan nan.
Nace ya hau kan zan jira sai ya sauka don yanzu yi mashi magana wani jidalin zan kara jawowa kaina barshi mu tafi haka har ya sauko da kan shi dai.
Tace kina ganin haka zaifi safiya nace ni na san halin uncle Samira barshi dai muje a hakan tace to shike nan ai mai daki shiyasan inda ruwa ke yoyo.
Tace sai da na fada maki tun farko safiya kada ki yunkurin zubar da cikin nan don dan halas sai an haife shi tunda an samu.
Wasa wasa mun share wurin sati biyu yanzun ba mai kula wani sai dai zan mai ina kwana ya amsa min a dake ba sakin fuska ko kadan.
Tun ina dari dari har abin yazo ya daina damuna tunda ban rasa ci da sha ba ba kuma korana yayi a gidan shi ba.
Sai dai wani lokaci abin yakan damay ni amma yaya zanyi tunda yaki tsayawa mu fahinci juna har in bashi hakuri ga kuskure na.
Allah ya gani tsoro nake ji don abin da ya samu kawata shine ya tsaya min a raina sosai saboda irin haka tayi tasha da kyat.

YAR UWA BA SAI KIN RUBUTA BATSA BA NOVEL DIN KI ZAI SAMU KARBUWA, KE MAI GYARA TARBIYAR AL, UMMA CE BA MAI BATA WA BA.
KIN SAN YARA NAWA NOVEL DIN KI YA HALAKA DA WA YAN DA KIKA SAKA ZINA TA SANADIN NOVEL DIN KI NA BATSA.
KI WA KANKI FADA TUN LOKACI BAI DAINA YI DAKE BA ABIN KWARAI AKE YAYI BA NA BANZA BA, , , , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/21/20, 10:00 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RARYUWA, , , , , , , , , ,


🧕🏿8️⃣6️⃣🧕


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU


Yau ya kama jumma, a tunda safe ina shirya yan kanne da zasu makaranta don dole duk safe koni ko mummy daya ya tsaya wurin su don su shirya.
Idan ba haka sai su tsaya shiririta da gardaman banza har su makara don yanzu sun rage zagwadi son makarantar da sukeyi .
Tunda sukaji baba ya yarda da zaman su a guri don da farko kin yarda yayi lokacin da hutun su ya kare yaji shiru sai gashi ya bugo min waya wai baiga yaran shi ba.
Nace baba yaran ka suna nan lafiya makaranta ne ya boye su yace wani irin makaranta kuma nace ai mun saka su school a nan din dana boko dana muhamdiya.
Yace bam yarda da wanan tsari ba don ba haka mukayi dake ba nace baba na sani amma kayi hakkuri da hakan da nayi.
Fada yayi sosai a wayan ina sauraren shi saida ya gama nace baba nasan munyi kuskuren yin haka da mukayi.
Amma ba nayi bane don mu raina maka nayi ne don taimaka wa rayuwan mu baki daya saboda indan suna nan zasu samu karatu mai inganci da ci gaban rayuwa.
Kayi hakkuri baba don Allah kabar min su anan don zama su a nan din yana da matukar muhinman sosai yace.
Safiya ai wanan rashin hankalin ne ki dauki yara har biyu ki kai wa mutum gida wanan ya zama rashin hankali ai.
Baba shi ya yarda da zaman su don shi da kan sa ya kaisu makaranta mai tsada ta kudo anan din munyi kuskure ba zamu kara ba in Allah ya yarda.
Bayan ya gama saurare na ya kasha wayan ya nufi wurin su ummi da fada mama ya fara kira sai ummi suka fito yake fadin.
Ashe kun hada kai da yarinyar nan safiya ne ta yaudareni ta kwashe yaran nan, ta tafi dasu su zauna a wurin ta ne ?
Haba malam ai wanan abin kamar taimokan ne tayi inji mama ta katse shi ga maganan shi yace ke dakata min.
Taimakon may nace na gaza da "ya"ya ne ita a ina ta taso in ba nan din ba ummi tace amma ni wanan abin sai naga kamar taimakon kane yarinyar nan tayi banga abin fada ba don safiya ta dauki kannen ta ta kaisu gare ta.
Mijin ta baiyi fadan haka na sai kaine zakiyi haka dakan shi ya bata baki kan hakan yace ke nan da sanin ku aka yaudare ni ?
Yaudara kuma malam babu yau dara acikin hakan wata rana hakan zai maka dadi yaya Nura ne yashigo gida a lokacin yake tambayan may ke faruwa.
Ummi ke fada mai yace baba koni safiya zata dauka yanzu ai zuwa zanyi da gudu balle maimu da hindatu yara nacen cikin daulan duniya za ai masu bakin ciki kuma.
Kaifa mahaukacine sakaran banza kawai waye zai masu bakin ciki din niko uwar ka ya wuce yana a bakin ciki za ai masu mana mai kaya ya daure sai mai cira ke wassh Allah.
Uwarka nace ya nufe shi gadan gadan shiko ya fice gidan yana dariya wanan abin yasa su ummi saurin watse wa gaban shi yaci fadan shi yana fadin ai zai gamu dani ne.
Murmushi nayi da tuna wanan magana da ummi ta fada min ya faru a gidan mu sauri muke mu tafi sai Abba ya kama kuka ina jin mommy tana lalashin shi yaki shiru.
Uncle ne ya leko daga dakin shi yana fadin wai may yaron nan yake ma kuka haka ne ke kuma baki dubashi ba ?
Bai mai magana ba sai wucewa da nayi dakin kawai na samu mommy tana lalashin shi yaki shiru daukan shi nayi ina lalashi bai yi shiru ba.
Mummy ta tara hannun yaki zuwa wurin ta dole sai na goya shi don yayi shiru saboda mommy ta saba mai da goyo yau kuma bata jin dadin jikin ta ne.
Ya fito daukan ruwa ya samu su maimu zaune falo suna jirana yake fadin baku tafi bane har bakwai da minti goma yanzu suka ce anty muke jira ta fito Abba ne ke kuka yaki yin shiru.
Sai gani na fito dakin mommy da goyon shi da goran ruwa a hannun shi ya dago yana kallona goye da yaron a bayana.
May ya samay shine yau ya fadi yana kallo na cikin dakewa nace fitane kawai yake ji mommy bata jin dadi tun jiya miko min shi nan yace dani ina kokarin sance yaron a baya ma in mika mashi sai yaton yaki ya kara lafewa.
Ke mi ko min shi yace goyon nan zai iya maki illar koda dama ba son cikin kikeyi ba nace yake zaune a jikina idan ban so ka barshi kawai mutafi in kaisu in dawo.
Barshi in kaisu naji yace tare da fadin ku tashi kada ku makara sosai yaran suka mike sai maimu ke fadin anty kudin exam din fa uncle zai bada ?
Nace ku bari monday zanje in biya maku idan na kaiku yake cewa nawane kudin suka ce five hundred kowan mu fita yayi baiyi magana ba ya wuce suna biye dashi a baya.
Nan suka fice na sauke ajiyan zuciya yaushe rabon da yayi min magana haka sai yau sanadin Abba dake kuka a gidan ya jawo yayi min magana.
Da motana ya fita dasu bai jima ba ya dawo ina zaune goye da Abba a bayana ya shigo wurin mu yayo direct yana fadin .
Babana may ya hadaka da mommy yau kake fushi haka ban san ka da fushi na fa ya dan duka yana yiwa yaron wasa sai kuma yace.
Kin bashi abinci yaci ko yunwa yake ji kai na girgiza mai yace ki bashi a gani ko yunwa yake ji don yanzu dai madara ba isan shi zaiyi ba.
Mikewa nayi zuwa inda Nura tafara jera abincin na dibo mashi dankali kadan na dawo ina sance yaron sai ya karbe shi a bayana shi da kan shi yake bashi abincin yaron yana karba.
Yace don Allah ku bar barin shi da yunwa haka yaya madara kawai zai ishi yaro dan wata tara yanzu nace ya dai so cin abincin ne yanzu amma in an bashi sai yaga dama yake ci.
To na dai ce a dinga bashi in baici a barshi daga yau naji nace dashi ya gama sai kuma yace sai in kara goya shi yasa muna fitina a wurin yana jawo zanin da na sance goyon shi a bayana.
Wuf uncle ya dauki yaron yayi ciki dashi murmushi nayi bayan sun shige daki da yaron wanda nasan ya fara saukowa ne da kanshi da ina binshi ina bashi hakkuri da yanzu bai isa saukowa ba haka.
Ya fito cikin shirin fita yake cewa Abba na nace daki yana barci ki lakashi don kada ya tashi yana kuka ya fado ya fada ba wani sakin fuska gare shi.
Fita yayi daga gidan mukai mai a dawo lafiya bayan awa daya ne naje dakin leka yadon yana kwance yana barci abinshi hankali kwance har lokacin nan nabi dakin da kallo yayi kaca kaca sai na fara gyara bathroom na fito na gyara ko ina na goge na sa mai room fresh yaron ya tashi kafin in gama.
Na sauke shi na canza mai zanin gadon na jawo mai kofa sha biyu daidai na fito zuwa dauko su maimu ni da Abba ne muka fita na dauko su tare motan mu ya kunno kai kwanan gidan.
Bayan mun shiga ciki na rufe mota bai fito ba har na shiga gida sai can gashi ya shigo muna falo zaune muna cin marasa gasas da muka sayo a hanya hajiya tana hanya zata shigo yace dani.
Ras naji gabana ya fadi ban san lokacin da nace mai hajiya baaba ba yace ita yana wuce wa dakin shi bai tsaya falon ba nasan shirin jumma,a yadawo yayi lokacin.
Yana shiga idon shine ya sauka a dakin dana gyara mai shi tson ya sauke ajiyan zuciya ya aje waya ya nufi ban daki nan ma a gyare yake komai sai walkiya yakeyi a wurin yasha gyara.
Murmushi ya sauke a fuskan shi shi kadai a dakin yace mata halin su sai su watau tunda yau nayi mata magana shiyasa ta shigo tayi min gyara itama ta iya ke nan yanzu.
Daren jiya kamar ummi ta sani tasa ni gaba a waya tayi min tas sai da nayi kuka sosai tace lalai lalai in bashi hakuri don nice ban da gaskiya ko ina akaje kuwa da maganan mu.
Kuma akan may zance wai ya rushe gida ya mayar muna da namu yaushe na koyi rashin kuya haka ko nice nasa ya gina muna gidan.
Idan banyi hankali ba zata hadani da mahaifin mu kuma zata kira uncle ta bashi hakkuri da sauri nace ni ummi ba sai kin kirashi ba ni zan bashi hakkuri da kaina.
Sai washe gari kuma na tashi naga ya rigani ma saukowa ko shima mahaifiyar shine tayi mai magana oho ?
Yanzun kuma da yace zata shigo sai tunane na ya kai ga ko tasan da matsalan ne zata zo inko har uncle ya fada ma hajiya yabar ni cikin tsunbul.
Fitowa yayi cikin farin voil na maza wanda har zaka iya hango farar singlet din shi na shiki yana haskawa a inda ya bar mu ya samay zaune har lokacin muna wurin.
Ke maimu ku shiya kafin in gama mu je masallaci ku shirya Abba yace dasu ya nufi hanya waje dama yakan je da yaran idan ya bushi iska amma ya dade bai tafi dasu ba sai yau.
Namike na nufi dakin mommy nace ta ban kayan shi zasu je masallaci ne da baban shi nan na zauna dakin ta na shirya yaro tsab anan kuma nake fada mata yau sarakuwa na zata zo.
Tayi murna da jin haka sai dai tace dani zato za ta samay ki cikin wanan zaman doya da manja da kukeyi a tsakanin ku haka ?
Ni mommy yaya zanyi tunda in ya hau bai sauka sai yaga dama don kan shi tace ke ko keda yadda zakiyi don ke ce mace safiya nasha fada maki kada ki fushi haka dashi tunda ke ce baki da gaskiya.
Babu namijin da zai kama mace da wanan laifin ya iya kyale ta ni naga hakkurin shi kwarai da gaske wallahi.
Mommy har yanzu fa fushi yake yi dani kan maganan kuma sai kice kinga hakurin shi mommy ?
Tace kin san girman laifin da kika aikata kuwa yar nan ai sai baka son namijine kake gudun haihuwa dashi nace shima yasan ai bada wata manufa nayi ba mommy kawai dai lafiya na nake jawa .
Amma ni ba wai don ban son haihuwa dashi bane kawai dai haka Allah ya nufa sai ya faru a tsakanin mu yaki yarda ya saurari manufata kuma.
Maza fa a sannu ake binsu diyar nan don Allah ya riga ya basu girma a kan mu ki lalaba mijin ki ku zauna lafiya yadda kuke yafi.
Hindatune ta shigo daukan Abba a lokacin ban koma daki ba na nufi kitchen don shirya ma hajiya abinci sai dai ban san ko su nawa zasu zo ba kuma.
Kafin su dawo nayi nisa ga aiki sosai don da Nura muke aikin abinci nagama abinda zanyi na fito kara gyara gidan su maimu na taya ni.
Mun hada komai zuwa hudu hudu da rabi suka iso gidan yafita a lokacin dakin da aka gyara masu na kaisu ita da anty suwaiba sai yan matan ta biyu da tazo dasu.
Mun gaisa na tambaye su sauran yan uwa suka ce duk suna lafiya abinci na gabatar masu sai da sukai sallah suka zauna ci .
Ban koma wurin su ba na barsu su dan huta don sun kwaso hanya mai nisa dakina na koma na dan kwanta kadan don na gaji a lokacin.
Cikin yan matan da suka zo da su ne daya tazo ta kirani.
Na samu har sunci abinci ko na shigo dakin dayar yarinyar naa kwashe kayan abincin daga dakin tana kaiwa kitchen baaba yaya gajiyan hanya nace bayan na kai zaune kasa gefen gadon.
Garin nan naku akwai nisa yar nan shiyasa ban sa kaina zuwa ba tun farko ko yanzu don naji ance kinyi fama da jikine har kin kwanta asibiti koda yake ke da ke da mijin nake ba fadar ciwo kukeyi ba.
Ko sannu akace maku ai an rage maku ciwo a daidai lokacin uncle ya shigo dakin yana fadin sannu ku da zuwa naje dan nesa shiyasa ban shigo da wuri ba.
Bata fasa maganan da takeyi tace idan shi bai fada min ba aike kya gaya min tunda muna waya kusan ko yaushe dake.
Zaune yakai kasa shima don mika gaisuwa ga mahaifiyar ta shi cikin girmamawa ta amsa mashi tana ci gaba dayi muna fadan rashin fada mata matsalar mu da baya yi.
Yace aiyi hakkuri baaba ai ta dade da samun sauki dama ba wani matsala bane sosai ke damun ta a raina nace ka fadi hakan mana tunda cikin ba ajikin ka yake ba ai.
Allah ya sauwaka tace muka amsa da amin tace Safiya kije ku bude tsaraban nan kada su lalace a saka a fridge nace baaba har da dawainiya aka zo muna kuma ?
Kin jiki da magana ina dawainiyar yake anan ni mai gida na nayowa tsaraba dama ba ku ba yar uwar ku dai ta kawo maku tsaraba.
Ina mikewa nake fadin baaba ba a zo da maryam na dai tace maryam din nan tana fama da laulauyin ciki bata iya zuwa ai taso ta biyo mu hakana hanata nayi.
Nace Allah sarki ashe zamu sha suna idan rai ya kai mu lafiya tace a toh zaku sha kan don wanan cikin ma ya zo mata da matsala sosai wallahi ba kamar wanda take a baya ba.
Yace dama ai haka ciki yake ko wani da kalar tashi zuwan fita nayi daga dakin na nufi inda kayansu yake yan matan na zaune falo da su maimu suna hira.
Da dare na shirya bayan na idar da sallah na shiga dakin nasu suna ciki dukan su muka gaisa na samu wuri na zauna muna fita da anty suwaiba hajiya na lazimi saman carpet din sallah har lokacin.
Ya shigo cikin jallabiya baka sai kamshin turare yake yi yace ke kije ki kama yaron nan haka na yau mommy bata jin dadin jikin ta.
Mikewa nayi na bar dakin ba tare da nayi mashi magana ba zuwa kama Abba din dake ta kuka a dakin mummy baaba ne ta shafa ta juyo gare shi tana fadin kullun ina fada maka kabi yarinyar nan a sannu.
Ji yadda kake faman daure mata fuska babu walwala a tare da ita duk tabi ta fige ta koma wata iri jikina yayi da bayan shi a bango yana fadin ni bani na fige ta ba baba halinta ne ya fige ta.
Dan kallon shi tayi kamar harara tana fadin wani hali ke ga wanan yarinyar banda kai dake son takura mata a kullun hakan da kake wallahi tun tana tsoron ka na fada ma zata zo ta daina ne.
Wani matsi ai bai da kyau wallahi idan yayi yawa ya danbala mutum ko ya hinjira shi murmushi yayi yace yanzu kuma wani matsi nake mata.
Yarinyar da take gani ban isa da ita ina fadi tana fadi tace ba zan taba yarda da wanan magana duk da karya ba haki ka bane a baya.
Hajiya yanzun haka ciki ke gare ta na kamata tana yunkurin zubar wa nayi magana tason tayi min rashin kunya kuma.
Kira min ita suwaiba tace anty suwaiba ta tashi zuwa kira na muna kitchen muna hira a can ta samay ni .
A daki kuma ce mata yake hajiya ban san may take nufi da yunkuri zubar min ciki da take yi ba ka zauna kunyi magana ta fahinta da ita ka saurare korafin da yayin hakan da tayi niya ?
Lokacin na shigo dakin nuna min wuri tayi alaman in zauna nakai zaune jiki a sanyaye sai da taja dan lokaci tace min.
Safiya yanzu mijinki ke fada min wani magana da banji dadin jin shi ba sam na dukar da kaina kasa sai haaaye tace Safiya may zai sa kiyi yunkurin zubar da cikin jikin ki kuma ?
Har kin sa zargi ya shiga tsakanin ki da mijin ki yana zaton kin yi haka ne don baki son shi ko baki son haihuwa dashi ?
Da kyat na dago kaina ga nauyi ga kunya dake cina nace ba hakana bane baba yaki ya fahinci manufata ne a hankali na kora mata bayani na da dalilin daya sa nake yinkurin cire cikin da farko.
Tace banda abinki ai komai na Allah ne Allah daya baki shine kuma zai raba ki dashi lafiya ai kowa da irin tashi kaddaran rayuwa.
Sai kiga ke kin haife komai ba zai samu ba cikin hukuncin Allah wani kuma sai yasha bakar wahala haka abin yake ga Allah.
Kinyi kuskure babba don kisan kai kika so kiyi ba don Allah ya gyara kin fahinta daga baya ba kiba mijin ki hakkuri ban son irin yadda na samay ku din nan sam.
Ana maku kallon sha,awa daga waje a ciki kuma baku da jittuwa tsakanin ku abin bai yi kyau ba wallahi kuna zaton wani bai san halin da kuke ciki ba to kirana akayi aka fada min abinda kuke ciki a gidan.
Da sauri kowan mu ya kalle ta da mamaki tace eh ba dole bane in fada maku wanda ya kira amma dole tasani tasowa in zo don in tsawa ta maku.
Dan shiru ne ya biyo dakin cikin sanyi murya nace uncle nayi kuskure ka yafe min don Allah babu komai yace a takaice.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/22/20, 8:13 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , , ,


🧕🏿8️⃣7️⃣🧕

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU


Bayan baaba ta shirya mu ne abin ya danyi sauki sosai tsakanin mu kwanan baaba biyu tare da mu a gidan bata tafi ko ina ba suka shirya komawa bauchi.
Ko gidan Aisha da kyat na samu ta tafi bamu dade ba muka dawo sai sahad store da muka shiga ta dan duba abinda take bukata ita da anty suwaiba da yan matan ta.
Kudin da uncle ya basu shi suka sawo yan kayayankin fashion dashi a cikin saukin farashi washe gari zasu tafi don haka bamuyi barci da wuri ba a gidan.
Da safe kuma na tashi nayi sakkon dora masu abin karayawa kafin su wuce saida suka karya suka dauki hanya anan suka barmu cike da kewan su a gidan.
Sai gidan ya koma muna tsit bayan wucewan su zuwa azahar na shiga kitchen na hado masan da nayi warming da miyar kassa na dawo falo na zauna kasa saman carpet ina ci.
Mommy ta shigo falon masan takai ma kallo daga inda nake zauna ina ci a hankali ina kallon tv take fadin wai ni na rasa yaya mutanen nan ke masan su yafi na ko ina dadi ?
Nace da ita suna tsaya su gyara ne ko ke a gidan ki mommy idan zaki tsaya ki gyara kamar yadda sukeyi zai koma ki.
Mommy ko na zubu maki ne na dago kai ina tambayan ta don nasan gwanace wurin cin masa nawa mai dalili ne cin da nakeyi don saboda ciki nake cin masa yanzu.
Zama tayi tana jawo Abba zuwa jikin ta na fadin Abba bazakaci masan nan mai miya ba don ruda ma ciki zaiyi nace bazan bashi bani idan kuna so ku debo naku ku dumama kuci.
Zan jira yan matana suzo ne sai mu dumama muci don suma suna son masan nan sosai nagani tace dama magana nazo muyi dake yanzu gaki kuma kina cin abinci.
Mommy may nene nace cikin dago kaina ina fuskantar ta ta ce ba wani magana bane dama gani nayi tunda an kai karshen matsalar ku da maigidan ki .
May zai sa har yanzu baki zuwa gare shi kike baya baya dashi bayan kisan kece mai laifi kuma an shirya maganan nan a tsakanin ku kuma kon kasa bashi hakkin shi har yanzu.
Jikina ne yayi sanyi sosai da maganan mommy saboda ban dauka ta fahinci ban shiga turakar incle ba dama don tana rigamu shigewa dakin ta.
Maganan ta yasani dagowa na sake kallon ta da tace indan kina haka kina cutar da mijin ki ne da kan ki zamana a cikin ku kima baida wani amfani ke nan.
Nasiha sosai tayi min akan abinda nakeyi akarshe nace na gode mommy in Allah yaso zan gyara mommy tace ki kulla don Allah diya ta.
Nace mommy ba wai ina share shi bane dama ban san may zai mun bane idan na kusanci ida yake kin san shi bai iya fishi ya sauka maza ba.
Komai zai maki dole ki shanye don shine gaba dake kece a kasa don haka ki maza ki shirya tsakanin ku komai ya wuce a tsakanin ku.
Mommy in sha Allahu komai ya wuce zan shanye duk wani abinda zai min kan hakan koda bai hakkura da hakkurin da mahafiyar shi ta bamu ba zan shaye duk wullakancin da zai min.
Allah yayi maki albarka da kika fahinci haka komai zai wuce da zaran yaga kin bishi kin kara bashi hakkuri.
Banki ta mommy ba da na gama na gyara mai daki tsab na feshe da room fresh na wanke ban dakin na rufo mai na dawo part dina.
Sai yama ya dawo gida lokacin muna falo zaune dukkan mu har mommy muna hira su kuma suna cin abinci.
Ya shigo da alaman a gajiye yake na mike nabi bayan shi zuwa dakin bayan na kara gaida shi na wuce ban daki hada mai ruwan wanka na fito ina fada mai na hada mai ruwa ok kawai yace min yana duban wasu takarda a hannun shi.
Ban tsaya ba na fice a dakin na koma falo na zauna ya gama ya fito cikin kayan da yake zama dasu a gida da alaman ya rufe fita ke nan yau din.
Gurin cin abinci ya nufa ya ja kujera ya zauna isowa nayi gurin ina kokarin bude kukolin abincin da aka aje don shi a wurin.
Sai da ja zuba mai tuwon semo da miyar yauki Nura tayi muna na abincin dare ya wanke hannun domin fara ci .
Daya daga cikin kujerun na jawo na zauna nima a wurin abincin shi yake ci hankali kwance kamar bai san ina wurin zaune ba a lokacin .
Sai zuwa Abba ne wurin namu ya fara magana yana fadin babana kaci abincin kuwa banga cikin ka ya cika ba shiko yaron kokarin daukan goran ruwan dake gaban shi yake yi.
Yace zuba mai ruwa kila kishin ruwa yake ji baida bakin fada na zuba zan ba yaron ya karba daga hannuna yana kokarin bashi yaron na kawar da kai sai goran yake son dauka kawai.
Daukan yaron yayi zuwa jikin shi ya dibi abincin ya fara kai mashi a baki tare da balle goran ruwan dake gefen shi ya kafa mai a baki sosai ya zuki ruwan daga cikin goran ya cire bakin shi yana mai da numfashi sama sama .
Ina zaune gefe na harde hanayena ina kallon su hankali kance yadda suke yi ba karamin son yara uncle keyi ba dole ya yi min masifa kan barar da cikin da nake shirin yi din don ko banza ya kamata ace yana da yaran da suka kai biyar yanzu a shekarun shi.
Ban ankara ba ashe ya dago yana fadin kin kuwa fara bashi maganin da hajiya ta kawo mai nace cikin kada kai tun tana nan aka fara bashi sai dai bai son sha idan an bashi sai da dare idan zai kwanta ake bashi.
Ke maimu dauko mai biscuit din shi ko zai ci nace biscuit kuma uncle da daren nan zai iya saka shi kashi don ruda ciki yake yi.
Ba tare da ya kalle ni ba yace ke ke wankewa idan yayi ko ba za a bashi idan yana so shiru nayi kawai ina kallon su mommy har ta mike ta shige tun fitowanshi nasan kallo take a dakin ta.
Ganin ya gama na hada kayan zuwa kitchen sai hindatu ta taso tana tayani kwashe kayan a wurin anan yake mata ba a tana murmshi.
Yau bai dade a falon ba ya shige sai dana dauki lokaci na gama hada mai blact tea din shi na ganyen na,ana na samay shi a dakin.
Kamshi ke tashi a jikina sosai a lokacin yana zaune yana aiki a laptop din shi tsab na gyara komai kafin in kwanta a bayan shi.
Bai daina abinda yakeyi din ba har wani lokaci ya rufe tare da mikewa ya nufi bayi can ya fito ya zauna yana shan tea da na aje mai a bakin gado.
Sannu a hankali na dago daga inda nake nakai zaune ina fadin Uncle don Allah kayi hakkuri ga abinda ya faru a baya ba munafata ke nan ba ga abinda kake tuhuma na dashi.
Har tsawon wani lokaci bai mun magana ba nima ban sake magana ba ina zaune shiru a inda nake a bayan shi cikin fargaba.
Sai can naji yace yanzu may kike son in ce tunda ke baki son haihuwa dani ni kuma ina son haihuwa a rayuwana baki min adalci ba Safiya ban cancanci haka a gare ki.
Baka yarda dani ba ke nan uncle nace akan may zan yarda dake yanzu bayan ba wani ya fada min ba ni nagani da ido na a lokacin da baki zata ba.
Murmushi nayi nace to shi ke nan na dauki laifina tunda haka kake son ji a bakina ko nayi kuskure a yafe min daidai yana kaiwa kwance yace min .
Magana daya ne yanzu inga kin haife cikin nan lafiya shine kawai zai sa hankali ya kwanta dake nace har yanzu kana zargina kenan bai yi magana ba sai kashe muna wuta da yayi yana gyara kwanciyan shi da kyau.
Nima komawa nayi na kwanta tare da lumshe idanuwa ina tunanen wanan hali na uncle duk abinda ya kamata nayi dai nayi mai a yanzu.
Ban tsamanin jin hannun daya kai jikina ba a lokacin amma sai tunane na ya kwance a lokacin may yasa maza suke hakane a wurin wanan fannin basu jin kunyan yin haka ko wani lokaci suke da bukata.
Washe gari ban koma barci ba don yace yana da tafiya zuwa Niger state sayen wasu kaya don haka na wuce kitchen don hada mai abinci da wuri kafin Nura tazo aiki.
Ina tsaka ga aiki sai gashi ya biyo ni da wayana a hannun shi da na baro dakin yace yaya Saadu ne ke kirana a lokacin .
Nayi mamakin kiran yaya Saadu haka da safen nan na karba daidai lokacin daya kara kirana din na dana wayan ina fadin ina kwana yaya .
Yace lafiya Safiya kin ga na kiraki da safe haka ko wallahi waya aka bugo min daga gida da dare Allah ya karbi ran Ahmed jiya da daren.
Innalillahi wa inna alaihim rajiun ya rasu yaya yace wallahi safiya da dare jiya suka bugo min waya yana tsaye daga kofa yana saurare na.
Na dago kaina na kalle shi ya tsure ni da idanuwan shi cikin son jin abinda ke faru a lokaci a sanyayye nace wai yaya Ahmed ne ya rasu jiya da dare.
Waye haka na yace dani a sanyaye nace yayan yaya Saadu dana taba aura a lagas Allah yai mai rahama yace yana wucewa zuwa dakin shi.
Jikina yayi sanyi na bishi da kallo dakin mommy na nufa a lokacin don fada mata abinda ke faruwa damu duk ta rude dataji maganan.
Na dan dade muna maganan na koma kitchen na karasa aikina hakana a dadafe sai tunanen zaman da mukayi dashi a gidan shi nakeyi.
Nashiga dakin bayan na gama komai na samu yana tsaye yana shiri har yayi wanka a lokacin ga abin karyawavcan nace mashi sai kuma naja na zauna bakin gado har ya gama shiri ban yi magana.
Tare muka fito a dakin nashi a lokacin zama yayi yake cewa mommy bata fito bane har yanzu nace ina ga shiryawa take zata gidan su yaya Saadu tace .
Baiyi magana sai jawo plate dayayi a gaban shi ganin duk a sabule nake a lokacin sai lokacin na natsu na mike na fara zuba mai arish din a plate.
Sai da ya fara cin abincin yace zasu tafi can lagas din ke nan yau da sauri nace ban sani ba don bamuyi maganan haka dashi ba.
Wayan shi ne yayi kara yaya saadu dine yakirashi a lokacin yake fada mai rasuwan dan uwan nashi yace eh ai daka bugo mata muna tare Allah ya jikan shi yasa ya huta.
Zaka tafi lagas din ke nan yace eh da yau nake son mu shirya mutafi da iyalina mota zaku bi ko jirgi yace ina ganin mota zamu bi don mu uku ne.
Bari kubi jirgi zaifi ku isa da wuri zan fito yanzu zan biyo ta gurin ku kafin in wuce ni dai sauraren maganan su nake yi banyi magana ba.
Sai dai zuciya ta ba dadi a lokacin don mutuwa ko na wanda baka sani ba yana shiga ranka balle ga wanda ka sani din.
Har ya gama yana min sai ya dawo ban iya cewa dashi zan tafi gidan yaya Saadu in mai gaisuwa ba don kada ya fassara min magana da wata manufa kuma.
A dawo lafiya nake yi mashi har yakai kofa yace idan mommy ta shirya sai ku tafi tare ki sauke ta ki masu gaisuwa.
Na gode nace mashi ya fice gidan na sauke ajiyan zuciya mikewa nayi zuwa dakina ko kayan ban ita kwashe wa na soma shiri nima.
Sai da na sauke kannena a makaranta muka wuce gidan mun samay su har sun shirya da ganin yaya Saadu kasan yayi rashin dan uwa a lokacin .
Don ya fita hayacin shi sosai kan mutuwan da akai mashi din samira ke fada muna ai Uncle yazo yanzu ya wuce shine ma ya biya muna kudin jirgi zuwa lagos din.
Nayi ma yaya Saadu gaisu nace idan sun je ya mika min gaisuwa ga sauran yan uwa yace zasu ji safiya .
Yace Ahmed dai ya rasu bai samu rokon ki gafaran abinda yayi maki ba har ya mutu nace babu komai yaya na gafarta mai.
Allah dai yayi mai rahama yasa mutuwa hutu ne gare shi yace amin safiya muna gidan har suka shirya muka raka su zuwa airport muka sauke su a can muka dawo gida.
Ranan dai haka na wuni jiki ba dadi zuwa rana samira ta kirani tana fada min sun isa lafiya yanzu haka suna gidan ma ana batun kauda shi ne.
Wani iri naji a raina na kara mata gaisuwa tace ga sadiya mu gaisa sai da na gyara na fara amsa mata gaisuwan tana kuka sosai a lokacin ni dai hakkuri na basu nace ta gaida min da gwago ina mata gaisuwan rashin da akayi din.
Sai yamma ya dawo a daki na samay shi muka gaisa na hada mai ruwan wanka na fita bayan ya fito falo ne yana cin abincin dare nake mai godiyan abin da yayiwa su yaya Saadu din.
Yace halin shine yasa nai mashi hakan din don yana da rikon gaskiya da amana a tare dashi banda abinda zan saka mai dashi in ba haka din ba.
Shiru nayi shima bai kara magana ba ya gama ya mike yana tambaya na mommy nace suna daki basu fito ba yau.
Bamu dade ba muka shige ciki nikan kwanciya nayi don har lokacin jiki na ba karfe don mutuwan ya shige ni sosai ranan.
Sai dai ina kokarin ganin bai fahinci hakan ba don gudun zargina zai sa yace na damu aiko ban tsira ba sai jin muryan shi nayi yana fadin yau dai kamar kina cikin damuwa ko ?
Da sauri nace damuwa kuma uncle akan may kuma zan damu an maki mutuwa yau mana uban diyar ki ya rasu.
Naji zafin maganan nashi amma a fili cewa nayi mutuwa ko na wanda baka sani ba kana tausayawa mamaci ai balle wanda ka zauna dashi a baya .
Ko ba komai kuma ai dan uwana ne shi kaga dole inji mutuwar a raina wanda nima ba komai nake tunane ba sai tawa makomar a yanzu.
Naga alama yace yana gyara kwanci ba tare da ya kara magana ba muka kwanta hakana ba wani abu daya shiga a tsakanin mu ranan.
Da safe ne yaya Saadu ya kirani wai zamu gaisa da gwago na dan jim nayi na karbi wayan muryan ta na rawa cikin gurbatacen hausan ta da ya gauraye yanzu tace Safiya ke ce yaya gida yaya maigidan naki.
Nace muna lafiya gwago yaya akaji da hakkuri tace hakkuri ya zama dole Safiya Ahmed ya rasu yana fadin a rokar mashike ki yafe mashi don Allah.
Nace gwago ni na yafe mashi tun tuni ai dan uwana ne sai naji ta kama kuka dole na kashe wayan don ban iya jimirin sauraren kukan nata a lokacin.
Nima kukan na kama a wirin sai dai nayi saurin share hawaye na kafin kuka yayi min yawa don ta bani tausayi sosai sai dai shedan na rudina ina tuna irin cutar da sukai min a lokacin.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/24/20, 5:48 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA , , , , , , , , , ,

🧕🏿8️⃣8️⃣🧕

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

Haka rayuwa ke ci gaba da gudana a gidan uncle watarana mu tashi a farinciki har dare wata rana kuma haka kawai zai daure fuska gare ni ba gaira ba dalili yayi ta fushi dani ga laifin da ban san nayi ba.
Ga dai ci da sha da sutura wadatace a gidan amma banda kwanciya zuciya a
gurin uncle ga fargaban ciwon dake jikin mu yau kaji ance babu wani a cikin masu irin lalaurar mu gobe kaji ance wata ta rasu akan laluran nan.
Ga ciki yayin wani irin girma a jiki saikace cikin tagwaye na dauka wanda bai san halin da nake ciki ba sai ya dauka ai ina cikin daular duniya ne ina cin ta da tsunki ba abinda ke damu na.
Sai dai da zan zauna dake in fada maki ciki na zaki fahinci rayuwan da nake yi a yanzu wanda zan iya kira maki shi da BAHAGGON RAYUWA .
Daga bakin ciki na fito na fada rashin kwanciyan hankali a gidan uncle don kullu a fargaba nake dashi kada yace ga laifin da nayi mai a gidan.
Amma idan yana cikin dadin rai idan ka ganmu saika dauka ba wanda ya kaimu soyewa a duniya a yanda muke daga bakin rayuwa zuwa haske da mai kumshe da magana a zuciya🧕🏿🧕.
Cikin wai a hakan ina jin yan uwan shi na fadin wai ya rage a cikin halin shi na baya sai nakan tuna da maganan da Faiza ta fada lokacin muna gidan anty a lagos.
Dadi na guda shine akwai waddata kuma yana taimakawa yan uwa da nashi da duk wanda yake rabe damu kodan wanan abin dole in yi hakkuri tunda na saba da irin rayuwan shi yanzu.
Su baba da mama sun tafi lagos gaisuwa sun kara tula ma gwangon mu nayi a ka wanda ranan da ta gansu taji kunya sosai ba kadan ba.
Baba yace ai zumunci bai yake ba don Saadu bai yarda zumunci ya lalace ba a tsakanin mu idan ma ke da Amadu bakuje ba ai shi yatafi gurin mu kin ga ko dan shi mazo wanan gaisuwan tunda bai yar damu ba ya dauke mu da muhinmaci sosai a rayuwa.
Mama kuma ta saka gwago a gaba tace yanzu n saboda son kai kika zabi wanan rayuwan a tsakanin kina ganin kin kyautawa kanki ne a hakan da kukayi.
Kun cuci yar mutane badon Allah ya kawo mata mafita ba a rayuwa da anmanta da rayuwan wanan yarinyar a duniya.
Da yake Allah bai barin bawan shi haka ya tabe sai ubagiji yayi mata dubaiya ya saka mata da miji yau itace ke rike damu da yan uwan ta baki daya duk ko da bakin cikin da ta fuskanta da farko a cikin mu bai sa yanzu da ta samu ta watsar damu ba ta jawo mu ta rungumay mu a jikin ta.
Kuka gwago keyi sosai na nadama mama ta gagaya mata magana masu zafi tace kiyi kokarin ganin ta ki roketa gafara zai fi.
Cikin ikon Allah na haifi dana lafiya asibiti don uncle yana gari a lokacin don haka a asibiti na haihu lafiya.
Bai samu gani na ba sai da aka fito dani dakin hutu suka shigo dakin ina kwance shida yaya saadu da mommy dasu samira .
Tunda mommy ta mika mai yaron ya rungumay shi a jikin shi bai yarda ya mikawa wani ba ya dade yanawa yaron addua.
Ya dago kai yace yaya Saadu kaga baiwan da Allah ya karamin kaunaka taso ta min bakin ciki ga hakan da Allah ya azurtani a dan lokaci kankanni ?
Murmushi yaya Saadu yayi yace yallabai ai mata hakkuri ta tuba murmushi yayi kawai ya mikawa yaya Saadu yaron.
Sun dade a dakin ana muhawaran wa yaron yabiyo cikin ni da uncle mommy tace wanan duk fuska gidan su suke daukowa Abba zai koma watarana don da ubansu suke da kama sosai.
An sallamay mu mun koma gida bayan dan wani lokaci sai dai ciwon kai da jiri da ke damu na akai akai wanda ya hanani walawa mun koma asibiti washe gari ba abinda likitan mu ya bani sai cewa yayi hutu jikina yake bukata kawai.
Kaina yana rike da hannuna na dafe goshina da hannu daya yana tuka mota muka nufo gida magana yake min amma ban iya bashi amsa a lokacin.
Har muka shigo gida ban tsaya ba na shige daki na kwanta maganin da aka rubuta min ya sayo na sha na samu barci mutane na shigowa amma ban sani ba.
Sai bayan karfe hudu na falka daga barcin da nakeyi kewayawa nayi sai dai daga ban dakin sai da mommy ta kamoni na dawo daki.
Uncle ta kira take fada mai abinda ke faruwa dani yace gashinan zuwa gidan dole ya baro aikin ya nufo gidan da sauri a ranshi yana fadin kardai yar mutane ta mutum dama abinda take gudu ke nan gashi kuma yana shirin faruwa da ita.
Gudun da yakeyi ne yasa shi isowa gida da wuri dakina yayo derict ina mai da numfashi guda guda ina fadin mommy kaina kamar zai fashe min nake jin shi.
Turo kofa yayi da sauri ya shigo dakin yana fadin Safiya har yanzu kan bai bari ba na dago idona da suka kade sukai min ja sosai gaban shi ne ya fadi yadda dan lokavin gadan na sauya nayi wani irin baki sosai.
Gashi na ramay lokaci daya kamar bani ba rike min kan yayi yana addua yana yarfarwa gefe ya dago yana tambayan mommy ko naci abinci tace ban ci komai tashina ke nan na shiga bandaki acan na tashi faduwa sai da ta kamoni muka fito.
Mommy hada mata tea mai kauri sosai ki kawo madarar ruwa da tomotor da gwagwanin maltina in fara bata da sauri mommy ta juya ta dauko abindaya lissafa mata ta shigo dasu take a wurin ya hada ya bani na sha.
Ta kawo tea din nace mata na koshi ba zan iya sha ba suka matsa min nasha rabin cup din nayi getsa sai ga zufa na karyo min lokaci daya na koma na kwanta tare da lumshe idona.
Ya dade a wurin tsaye ganin na samu barci yasa su fita su barni dakin ni daya mommy na goye da jiririn abayanta kallon mommy yayi yace ina ganin jinin da ta dan rasa ne a jikin ta yake haifar mata da ciwon kan haka.
Mommy tace dama shine fargaban ta a kullun wallahi ko haihuwan Abba tayi ciwon kai sai dai bai kai haka din ba gaskiya.
Yaron dake goye a bayan mommy ne yayi kuka ta sauke shi tana dan jijiga shi ajiyan zuciya ya sauke yace ina ganin kamar a kira gida gwago tazo ko khadija su taimaka maki don abin yayi maki yawa ke kadai haka.
Tace don dai abin yazo da akasi ne amma ai bai da matsala don ga yan matan tana suna taimaka min da kula da Abba idan suna gida.
Naji dadin kamun kan da yayi min don shi ya lafa min da ciwon kan da nake ji a baya sosai dana falka cikin dare ni da kai na nemi a bani abinci inci.
Na dauka dare yayi a lokacin sosai ashe wajajen karfe tara na dare muke a lokacin don ganin su maimu da nayi basuyi barci ba na tambaya mummy ke fada min time.
Ganin na tashi ne sukazo kusa dani suka zauna hindu na goye da jariri maimu kuma ta goya Abba.
Ido na lumshe a hankali tare da tunanen yanzu duk yaran nan nawane gasu kamar tagwaye don ba wani tserayan kirki a tsakanin su tunda Abba ma bai wuce goyo ba.
Uncle ne ya shigo dagin ya ganmu shiru sun tasani a gaba ba mai magana cikin mu duk da yawan rakafi su yau sun natsu sanadin rashin lafiyan da suka ganni ciki.
Wuri ya samu ya zauna a kusa dani yana ce masu kune yan jiya naga kunyi cirko cirko a dakin mommy dake zuba min ruwa ina wanke hannu tace dashi ba dole ba.
Sunga yar uwarsu a wani hali da basu saba ganin ta ba yace mommy ina ganin ba zan tsaya ayi suna ba zan fita da ita waje taje can ta samu hutu na dan wani lokaci.
Tace Alhaji kadai yi hakkuri yaron ya karbi sunan shi a nan don kasan mutane akwai tsegumi in anyi suna sai ku tafi.
Mommy ban damu da abinda mutane zasu fada ba kan haka lafiyan ta nake jawa kawai shine muradina, ina gudun kar abinda take gudu ya faru da ita don ta riga da ta nasa hakan gashi yana shirin faruwa da ita kuma.
Haba dai Alhaji bai kamata kayi saurin saka wanan a zuciyar ka ba don Allah ne mai yin komai ga bawan shi dama dai tasan irin kalubalin da hakan ke haifarwa ne tun wuri.
Kaida ayi fatan ta samu lafiya kanfin suna zaifi abar wanan maganan yanzu mu koma na neman lafiyanta kawai.
Ajiyan zuciya ya sauke mai nuna gansuwa da maganar mommy shine amfanin zama kusa da maya din da akeso a hankali nace ya kara min adduan da yayi min dazun don naji dasin shi sosai daya min.
Yaran mommy ta kada kan su zuwa waje dakin ya rage dagani sai shi a lokacin rugumay ni yayi zuwa jikin shi tare da dan shafa min baya yana fadin Allah ya baki lafiya matana ina jin da da halin in karbe ciwon nan a jikin ki.
Murmushi nayi nace Uncle ai ciwo kaffara ne ga bawan shi da yardan Allah zan samu lafiya in koma daidai dama sun fada muna haihuwa akai akai yana haifar da irin matsalan a gare mu rashin daukan matakin da bayi bane bayan haihuwar Abba yasani saurin daukan ciki da wuri.
Yace da rabon wanan yaron kuma yazo a wanan lokacin yasa muka manta da yin plaining a ziciyar mu sai dai yanzu dole a dauki mataki tunda na hango illar yin hakan yanzu.
Kaina ya kama ya fara min adduan da yayi min da rana sai da ya gama yace ki kwanta ki huta kinji abinda likita ya fada muna hutu kike bukata da cin abinda zai gina maki jiki da sauri jinin da kika rasa ya dawo.
Allah ya baki lafiya yace yana kokarin kwantar dani kamar karamar yarinya bakin ba don zaman dama ya isheni na koma na kwanta .
Da safe da ya shigo yake fada ma mommy ya dage sunan sai sarin mai zuwa har na kara jin sauki zai dai yankawa yaro rago idan sunan yazo buki sai wani sati.
Shi ida hali ma bukin ba sai anyi ba don in samu in huta a dakina baison azo a damay ni da hayaniya da yawa don taron suna hayaniyane kawai ba komai ba.
Yadda ya fada hakane ya faru don samira da Aisha sun ta kiran mutane suna fada masu suna sai wani sati idan Allah ya kaimu za ayi.
Sannu a hankali nake jin sauki har na dan bar jin ciwon kan sai dai yawan jiwa dake damuna idan na mike shima yana ragewa a hankali.
Haka dai suna yazo lokacin na samu lafiya sai dai a tsatsaye nake har lokacin akai suna yaro ci sunan uncle din sulaiman.
Na dauka zai min kara ya sa sunan nawa mahaifin sai naji yace wa mommy sunan yaro sulaiman nayiwa kaina takwara don kada a manta baya.
Yan uwana da nashi sunzo akai buki suka koma gida don ba wani hayaniya tunda ba lafiya gare ni ba haka yasa ummi na zuwa ita da su mama da babanmu da mommy mahaifiyar Amina kawata da motan gidan su suka zo.
Suna da kwana uku suka shigo garin da yamma da taimakon yaya Sani wanda yayo masu jagora.
Ba mu san da zuwan su don haka suka shiri da yamma sai ganin su mukayi suna shigowa da sallaman su muna zaune falo a lokacin sisters dina suna min hira mummy kuma na bawa Abba abinci kafin yayi barci.
Matan suka shigo baba sai baba ya tsaya a kofan gida bai shigoba a lokacin munyi mamakin ganin su sosai da tafiya haka babu sanarwa.
Yaran najin ance da baba akazo yana waje nan suka fice da ihun su suna murnan ganin shi yace ho yan nema mutan abuja ke nan.
Watau kuna nan kun shige birni kun manta da kowa ko dariya sukayi gaba daya sun sauya a idon shi sosai yaga sun kara mai girma sosai ba kamar yadda suka bar gida ba.
Da murna muka tare su sai fadin lalai Safiya ba lafiya jiki duk ya zube haka a lokaci daya murmushi nayi ina fadin ai naji sauki mama yanzun gashi ina iya mikewa kai tsaye ban taba komai ba.
Waya na dauka bayan mun gama gabatar masu da abinsha na kira uncle da bai dade da fita ba a lokacin ganin kirana yasa gaban shi faduwa sosai ya dauka cikin murya na yanayin mai ciwo nace su ummi na sun zo uncle har da baba.
Nan Abuja suka zo ko ina nace nan suka zo uncle yanzu suka iso garin da sauri yace gani nan tafe na kashe wayan na dago kai na kalli mummyn su Amina nace.
Mommy yaya hanya yaya wajen su Amina da yaranta tace suna lafiya naji tana fadin ai zats zo idan an kwana biyu tace yaya jikin naki yanzu ?
Naji sauki sosai mommy yanzu tace amma dai kan kinji jiki wallahi duk kin zube haka kamar kin dade kina jinya.
Mama tace yanzun kin ji sauki ke nan a haka gaskiya hankalin yan uwan ki ya kasa kwance sun koma suna fada muna ba dadi wallahi.
Sai da uncle ya iso ya matsa ma baba su shigo da dan uwan mommy daya jawo mota da yaya sani matan suka mike suka bi mommy zuwa ciki.
Har kasa muka zube muna gaida baba sai yaya jikin yake mun tare da jajantawa sun dade suna magana da uncle bai yarda yasha ko ruwa a gidan ba munyi munyi dashi yaki shan komai .
Gab da magariba yaya Saadu ya iso suka fice tare baba na fadin gidan dan shi zai tafi sai gobe idan sun shigo.
Mukai mai sallama ya tafi Allah ya taimake ni nura bata tafi ba a lokacin ta dora girki da sauri saboda bakin da tagani a gidan sun zo.
Gaskiya ina jin dadin zama da ita don tasan ya kamata sosai koda nace mummy taje asan abinda za a ayi masu sai ta samu har ta kusa gamawa a lokacin .
Ranan ban san irin farin cikin da nake ciki ba yau ummi ce da kanta a gidan aure na wani abu sai ciwo wallahi da ban san ranan zuwa mommy gidana ba.
Muna dakina dasu tunda akayi sallah suka shigo dakin lokacin ina ciki na dan kwanta anan suka samay ni mommy ce tayo masu jagora zuwa dakin.
A nan aka kawo masu abinci mama sai bin su maimu sukeyi da kallo wai yaran sun girma sosai yanzu..
Ranan dai kwanan farin ciki mukayi ga iyayye na a gidan uncle ya rasa ina zai saka su ya kwaso wanan ya sayo wanan yace a ba baki su ci.
Da safe suka tashi da shirin haraman komawa don wai kwana daya zasuyi muna anan uncle ya dago da maki da na samay shi a daki ina fada mai shirin tafiya sukeyi.
Take ya kira yaya Saadu yace mai yayi magana da baba ba zancen tafiya yau gare su sai gobe ko jibi idan an duba masu motar su.
Dole badon baba ya so ba ya hakkuri suka kara kwana yaya Saadu yazo ya dauke su suka tafi gidan shi ya kaisu kuma gidan Aisha.
Uncle ya shigo ya samay ni da rana yana fada min cewa ummi fa ba zata koma ba dasu don zata kwana muna biyu ina son muyi tafiyan nan da ita.
Yaya Saadu nace yayi wa magana don nasan ko baba ya yarda ita tana iya kin yarda tace bata zama gidan suruki komawa zatayi gida.
Hakan ko akayi shima baba bai so yarda ba da farko sai da yaya saadu yayi mai magana akan yara yake son a tafi da ita ya yarda.
Ita ko da aikai mata magana kafewa tayi bazata zauna ba su mommy suka ke be da ita a idon mama suka ce kada tayi haka.
Ko wace uwa tana fatan haka a wanan zamani Allah yayi mata baiwa don may zata guje ma haka dole bataso ba ta yarda ta zauna tana kallon washe gari suka kama hanya zuwa gida.
Kwana biyar muka kara wani yammaci sai gashi ya shigo har dakina yace an gama komai a shirin tafiyan mu don haka ranan monday zamu tashi har da yara zamu tafi don zamu kwana biyu a can.
Ban dauka har mommy su samira zamu tafi ba don ganin dawainiyar yayi yawa sai gashi da yaba pasphot na ga har da ita a tafiyan.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/25/20, 5:46 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , ,


🧕🏿8️⃣9️⃣🧕

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU


Mun sauka lafiya gidane da mai kyau irin ginan kasashen waje akwai da kuna sama da kasa da katon falo a cikin gidan.
Komai akwai na rayuwa a gidan kwana daya mukayi a kaini asibiti kusan bayanin su daya da likitan da ya dubani a Nigeria sai dai su, sun bada maganin da zai yi saurin shawo min matsala ta.
Sannu a hankali jikina ya fara dawowa normal har na fara dan kumatu a fuskana komai mai gina jiki da yananyin garin suka taimakamin wurin saurin cike wa da samun lafiya.
Ga mama da mommy dake kula da yaran da ni kaina a can ma bai bar kanne na hakana ba sai da ya somo masu makaranta suna zuwa.
Bai faye zama a guri daya ba ko yaushe yana wurin neman halak din shi zama wuri daya ya ishi ummi sai dai babu yadda zatayi ne kawai yasa tayi shiru.
Daga ita har mommy sun canza jikin su yayi kyau sosai dan samun hutu da sukayi a can ga kula da muke samu daga wurin uncle .
Baifi yayi kwana hudu ba ko biyar ya kama idan yazo har Nigeria yake zuwa ya dawo ya samay mu a nan dadi da daula mun samay shi a wurin uncle sosai watan mu takwas cur muka dunkulo maka dawo gida cike da abin arziki a tare damu.
Tun baba na fada a dawo mai da matar shi har yasa ido ya daina tambaya yaushe zamu dawo ne wai.
Niko banki muyi ta zama dasu haka ba har abada don ummi na kula min da yara sosai tana kuma basu tarbiyan daya dace a basu.
Wani irin kiba nayi ga haske dana kara da wayewa a lokaci daya mun zo mun samu komai na gidan an sauya muna anyi gyare gyare an canza ma gidan fasali sosai.
Saukan dare mukayi duk da haka su yaya Saadu sun zo taron mu da wasu ma, aikatan su gaba daya sai naga gidan ya sauya min gaba daya kamar ba gidan da muka bari ba a baya.
Mun shiga gidan kowa na mamakin sauyawan gida don uncle bai taba fada min cewa ana gyaran gidan sai da muka dawo kawai na gani yayi surprise din mu ga hakan.
Gaba daya komai ya sake dole muka tsaya a falo kafin yazo ya fada muna inda part din kowa yake mu shiga bayan ya gama sallaman mutane yace muyi hakkuri ya barmu a falo dakin su mommy ya fara nuna masu sai na su maimu kowa ya tashi da zumudi zuwa dakin sai lokacin ya nuna min part dina dake wani bangare nashi ma a dayan bangaren yake.
Duniya tayi min dadi yanzu sosai har nakan manta cewa ina da cuta a jikina a baya saboda yadda nake jin jikina a lafiye.
Ummi sati daya ta kara a tare damu muka kaita gida kwana biyu kawai nayi wanan karon na juyo ban samu tsayawa ba don zamu bauchi muga baaba da yan uwa.
Yarana sun girma don ko karamin da mommy tasa mashi suna azahabi yana tafiya yanzu da kafan shi ko ina yayi saurin girma sosai don ba jikin Abba da mahaifin shi ya debo ba shima Abba din ya girma sosai dan har ya fara karatu a can .
Ranan da muka dawo gida da yamma yaya Saadu yazo gidan yake fada min an bugo mai waya jikin gwago ya tsanan ta sosai don haka gobe zai tafi.
Na jajanta mashi tare da fatan Allah ya bata lafiya yadan dade wurin uncle suna fira ya tafi don dare yayi a lokacin .
Yaran ke rikice a gaban mu akan remote din tv nace wa Abba ya bar ma Azahabi kallo na uncle yayi cikin tsawa yace ma yaron ya kawo mashi remote din ya kora su zuwa dakin mommy wai suje ai masu shirin barci su kwanta dare yayi.
Bayan sun wuce ne don suna matukar tsoron shi ta juyo gare ni dama nasan ba zai barni ba sai na samu rabona a gurin kan hukuncin da na yanke din ga yaran.
Yace yanzu kinga kinyi wa Abba adalci ke nan a hakan shine babba fa ama kika ce karami ya rike remote din yanzu ne kike son sulaiman din fiye da Abba.
Uncle ba hakana bane nace gani nayi shine ya fara dauka shiyasa nace ya bar mai kai ya girgiza min yace ina lura dake kin fison shi akan Abba din don kirikiri yanzu a gabana kuka zalunce shi.
Nace cikin dago kaina ina kallon shi Zalunci uncle akan may zamu zalunce shi kuma wai ke baki san hakan da kike yi ba zalunci ne maimakon ki karbe duk a hannun su sai kice yabarwa kanin shi.
Shiru nayi kada zancen yayi nisa a tsakanin mu ya mike yana fadin irin haka sai ya kawo raini a tsakanin su balle yana ganin ya cin mashi da girma yanzu uncle har wanan yasan wanj abu raini a yanzu.
Yace a haka ake tasowa dashi ki taimake ni ki hada kan yayan nan don Allah kada ko bayan mu su samu matsala idan kan su yana hade babu wanda zai iya shiga tsakanin ko gaba.
Nasan inda maganan shi ya nufa yadda ya taso da yan uwan shi ne baison hakan ya faru da diyan shi daki ya wuce ni kuma na mike na shiga dakin nasu don in ga kwanciyan su.
Na samu mommy har ta shirya su ana rikici wurin kwanciya nace su kwanta su rike junan su sai suyi barcin a tare ba tare da sun rungumi mommy ba da suke ma fada.
Kwana biyu muka shirya muka tafi bauchi ganin hajiya taji dadin wannan ziyaran don mun dade bamu zo gida ba irin haka.
Banzo da kanne na badon makaranta da suke zuwa nan na barsu da mommy Abuja da yaran kawai nazo garin.
Mun dan zaga wurin dagi da sauran yan uwa mun gai dasu muna bauchi kwana hudu da zuwa bauchi sai ga sakon daddy sun yi nutsu a cikin ruwa inda suke aiki.
A ranan uncle da wasu yan uwa suka wuce lagas sun barmu hankali a tashe a gida sai zuwa safe muka samu labarin rashin dadddy din da akayi.
Hankali ya tashi sosai dole uncle yace mu biyo jirgi mu dawo Abuja in gari ya waye mu nufi lagos din don har wasu sun tafi ko.
Yadda yace haka mukayi hankali a tashe muka iso gida nike fadawa mommy abinda ke faruwa hankalinta ya tashi matuka da jin labari mara dadi daya dawo damu ba shiri.
Mun isa Abuja washe gari har lokacin ba a kawo gawan shi gida ba suna abinsu na yan kaki da gawan .
Mun shigo anty suna falo zaune gani na yasa ta sake wani kuka mai tsuma rai nima rungumay ta nayi ina kukan rashin da mukayi na daddy mutumin arziki.
Sai yamma suka bada gawan su nan aka shirya masu bi harda mu don zamu dafa ma anty baya.
Mun kwasa mun koma bauchi da gawan a jirgi guda da yan uwa isar mu da gawan ya tayar da hankalin yan uwa da abokan arziki.
Zuwa safe aka kaishi gidan shi na gaskiya har rana ban samu ganin uncle ba mu zaune a dakin anty cikin tashin hankali don ni na zamay mata kamar yar uwarta na jini a wurin duk da ga yan uwan nata a kusa da ita.
Shigowan yan uwan daddy maza a cikin su har da uncle sukayi gaisiwa tare da addua ga mamacin nan sukai dan bayani akan gobe zasu koma lagos dan ana son ganin su acan akan komai na daddy din.
Suna fita nabi bayan shi dole ya dan tsaya min na iso kallo daya nayi mai naga a lokaci daya duk ya sauya min a idona uncle kako ci wani abu na iya fadi.
Kai ya girgiza min yace yanzun dai nake son in karya magani fa nace dashi da sauri yace ban sha ba safiya ji nayi ina son in kebe dashi don ya samu ya karya yasha maganin shi kada ai biyu babu.
Su hajiya baaba ma suna gidan don haka na karbi makulli a hannun ta na fito muka wuce gida a sai da na zuba mai abinci na dauko mai maganin mu na bashi.
Yana zaune ya dafe kan shi a hankali na iso gare shi na zauna a gefen shi kuka yake yi nace uncle kayi hakkuri kowa yayi rashi amma ansan kai da anty akafi yi ma wanan rashin .
Yace safiya daddy mutumin kirki ne ya tafi ya barni a lokacin da nafi bukatan shi a tare dani rugumay shi nayi don maganan kara mashi bakin ciki yakeyi.
Sai da naga ya natsu sosai naji yace kinyi waya da mommy yaran na lafiya nace lafiya suke sai dai Abba ne tace yau ya tashi da mura ta bashi maganin shi.
Gobe zamu tafi lagos kuma da madam zamu tafi ina ga gida zaki koma don yaran sai ke tsaya Abuja ya kamata ki huta yanzu jigilan yayi maki yawa hakana.
Nace uncle ai kai keda jigila ga rashi ga ba hutu a tare da kai yace yaya za a yi dole nine zan bi komai nashi yanzu har komai ya daidaita.
Hari aka kawo masu na bazata shine ya zama ajalinsu haka su goma sha bakwai suka rasu a lokacin .
Allah dai ya jikan daddy nace yace amin yanzu ban san plain din madam ba nasan dai a can lagos din zata zauna saboda aikin ta ko kuma ta dawo arewa da aikin ina ganin zaifi mata sauki kusa da gida.
Haka dai sukai ta jigilan akan alamuran daddy har komai ya kammala ya dawo gida bayan wasu watanni aka nenawa anty trasfer ta dawo Abuja da aiki tare da yaranta.
Jikin gwago ya kiya baba yace a dawo da ita gida ayi na gargajiya a gani gashi basu jittuwa da Samira duk kokarin da take mata gwago bata gani sai zagi kawai ke shiga tsakanin su.
Haka yasa hankalin yaya Saadu yafi kwantawa da akaita gida don yawan fitinan da ake samu da samira duk da kokarin samira din.
An kaita gida ba afi wata biyu ba Allah ya amshi ranta muka je gida gaisuwa nan na samu zance aure yaya Sani ya tashi sai gina yake tayi inda zai saka matan shi.
Don yace bai son zama ko kusa da gida don gudun samun matsala da inna duk da inna yanzun tayi laushi sosai da fitina har in nazo takan dauki su Abba tayi masu wanka da sauran su.
Uncle yazo da ma, aikatasu sai dai basu kwana ba suka juya ranan mu sai da mukai kwana biyu muka dawo gwago ba karamin dukiya ta bari ba wa yayan ta.
Yaya Saadu yace yabarwa kannen shi mata idan sun samu mazan aure ai masu aure dashi sadiya ta dawo da zama wurin yaya Saadu.
Tare da mama da inna muka sauke farali inna ta saka hakora uku a bakin ta inda mama ta saka biyu sunyi dani in saka nace uncle yace baya so sai suka kyale ni.
A wurin jefa inna ta tashi mutuwa da kyat muka cetota wanan abin ya kara tsorata inna duk inda na jefa kafana tana biye dani.
Mu dawo lafiya saida suka kwana biyu a wurin mu suka wuce gida don ta Abuja suka tafi sai da muka dawo muka je gida bukin yaya Sani da yar wurin mai unguwar mu.
Abubuwa da yawa suna faruwa inda girma kuma ke kara shiga uncle da nauyi na yan uwa da abokan arziki idan aka kwana biyu kuma ya debe mo zuwa waje mu huta.
Bayan shekara hudu na sake haihuwa yar budurwa taci sunan hajiya baaba muna kiranta da baaba din sai na dakatar da haihuwan jikin kan dan motsa muna wani lokaci wani lokaci kuma sai ka gan mu kamar ba mu ba.
Yanzu nasan cuta baya kashi sai kwana ya kare do ga daddy mai lafiya ya tafi ya barmu gwago na ta tafi ta barmu muna rayuwan mu a cikin salama.
Yarana suna nan duk lafiyayun su basu da wata matsala a tare da su sun girma sun zama kyawawa dasu gwanin ban sha awa.
Ina kula da yan uwana da yan uwan miji nice na zama jigo a gidan mu inda ake girmama ni kamar wata babba a cikin zurian mu komai za ayi sai da shawarana.
Yanzu inna taba kai bori ya hau sai bi da lalami a tsakanin har in wani yaron ta yayi wani abin tana kawo min kara in yi mashi fada.
Rayuwan mu sosai yaci gaba don uncle ya bunkasa sosai ni da anty mun dinke sosai dawowan ta Abuja mun zama kamar uwa daya da ita.
Uncle ya dawo daga dubai bamu san da zuwan shi ba sai ganin shi mukayi ya sagalo jaket din shi a kafada Azahabi ya fara ganin shi .
Lokacin ina zaune dasu a dining suna cin abincin safe daddy daya ce yasamu duban kofa da gudu yaran suka nufe shi ya rugumay su duka ukun a jikin shi sai da ya gama sun batan su ya dago yana kallo na ina tsaye na taso taron shi na harde hannaye na wuri guda.
Yace madam Family yaya kuke nadan lumshe idona tare da yowa inda suke nima na rugumay su kit naji maimu ta dauke mu hoto daga inda take tsaye.

Alhamdullahi nan na kawo karshen labari na bahaggon rayuwa wata rana baki wataran fari haka rayuwan bawa yake tafiya har lokacin da naba da labarina gare ku muna nan raye da yaran mu lafiya lau cutar jikin mu bai nakasa mu ba.
Muna rayuwan mu normal kamar kowa ana bin mu kuma don baiwan arzikin mijina da muke ci tankar babu wani cuta a tare damu babu mai kyaman mu a cikin alumma komai daidai mukeyi da yan uwa.
Nima mai rubuta labarin na kare da cewa cuta ba mutuwa bane sai kwanan bawa ya kare uban giji yasa mu cika da imani a tare da mu.
Wanda na batawa ya yafe min don Allah.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
Chapter 4 · 0% Book details