Kashi dai karfafa ne gashi da tsayi da saje ya kewaye masa fuska a ido kamar kamili idan ka gashi amma duka halinsa ba na saye.
Bahagon Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 476 min read
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , ,
🧕🏿1️⃣7️⃣🧕🏿
YAR UWA WANAN NOVEL DIN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, ,
Gani ina gida ya sa ya juya ya fita nasan ba komai ya dawo yi gidan ba abincin da na dauko tun na safe gidan maman biyu shina yini ci a cikina.
Mugun bai dawo gida ba sai da magariba ya shigo da leda biyu a hannun shi na dauka wani abu ya sayo ashe wai garin kwaki ne.
Dayan ledan kuma kayan break fast din safe da zai karya dashi ne ya sayo ce na dauki garin ni ya sayowa na aje mai kayan tea din shi da safe zai karya dashi.
Na dauka nakai saman fridge na aje ashe yana kula dani ban sha ba yace ke garin bazaki sha bane a dakile nace na koshi a harzuke yace kin koshi may kika ci ?.
Nace komai atakaice.
Kamar zaiyi magana sai ya fasa ya sai ya mike zuwa dakina yana bincike baiga komai ba a dakin ya fito yana kutawa.
Yace idan ma baki sha ba ke kika sani ni dai hakkina zaki bani ba ruwa na da rashin cin ki wanan ke ya shafa.
Banko dago kai na kalle shi ba na kurama tv da ta shigo ya samu ina kallon super story.
Tashi nayi zuwa sallah inshai don lokaci yayi ban fito ba ina gurin da na sallama sallah zaune sai gashi ya shigo daga shi sai gajeren wandon boxes a jikin shi.
Kallo daya nai mashi na kawar da kaina don bani son ganin shi a irin siffan nan yace ke bake nake jira bane.
Nai dabur dabur na rasa abinda zanyi gashi ya tsure ni da idanuwan shi jajaye kamar garwashi wuta.
Yace a dake ki samay ni a dakina ina jiran ki gabana ne ya fadi badai wanan dakin matataran karuwan shi da mashayan giya yau zai ce na samay shi ciki.
Dan jin nayi na dan wanj lokaci tunane ya hana zuciya na shakat a lokacin ta shi nayi na bude kaya na na ciro turaren jiki duk na mulke jikina dashi hijjab dina na sallah na cire na nike a saman gado na canza zanin jikina.
Ina tsaye ina kara kintsawa sai gashi ya dawo kamar maye yaso kurwa yace yana zazzare ido wai ashe bake nake jiraba ne.
Tare da tsura min ido kamar zai cinye ni danya nace gani zuwa ina gyarawa ne yaja tsuki ya fice daga dakin nace kaji dashi dai kazami ko wanka baiyi idan za a kwanta dashi.
Na shiga dakin da sallama na yana kwace dadaya saman gadon dakin ga abin taba nan ko ina sakin birjit warwatse a kasa sai kwalaben dake wani gafe a ajiye.
Ina shiga ya kalle ni sama da kasa yace mallama dallah zo konji ina da abin yi tun dazu kin shanya ni ina jiran ki.
Dan matsawa ni bakin gadon zan zauna sai ko naji ya sa hannuwan shi masu kama da na karfe ya hankado ni saman gadon sai na kai kwance.
Tun takwas da wani abu nake dakin bani na fito ba sai daya da wani abu na dare ya koro ni koshi nasan giya zai hada dashi.
Ina fita ruwan zafi na samu nai wanka tare da gassa jikina dashi san nan na samu barci sai dai barcin sama sama nake yin sa.
Da safe na tashi duk jikina yana min ciwo amma don rashi imani sai da yasa na dafa mai ruwa tea ya zauna yasha ya sha ya koshi bai ko kalli gefen da nake ba.
Nima sai harkan gaba make yi ban kula abinda yake sha ba a lokacin har ya gama ya fice na sauke ajiyan zuciya.
Golden morn na hada na karya dashi na mayar maboya na boye sauran inda bai gani na sama yan kitso sun zo min don haka nake busy da jamma, a wata mata ce ta gwada min inda ake sayar da wake da bread a area namu.
Shi na sayo na ci abanicin rana na sai shan ruwa ya biyu bayan har na gama ma mutun biyar kitso bai dawo gida ba na lissafe in kudina na na soke na gyara wurin kamar banyi ba.
Bai ma dawo gidan ba sai dare koda zai shigo a buge ya shigo gidan ranan ko matsin haukan shi baiyi ba.
Washe gari sai karfe goma saura ya tashi sai ya hauni da fada wai yaya akayi ban tashe shi ba har yakai rana.
Badon na gudu ba da ya dake ni son ranshi da naga yana da niyar bugu na bude gida na gudu sai da ya fita na dawo gidan.
Na samu yai baja naja da kaya na yana neman kudi a ciki bai samu komai ba sai dari biyar da na aje canji ya gani ya dauke .
Nagyara kayana tare da mayar da komai inda yake ma dafa abinci naci na koshi na dan kwanta falo in huta sai barci masu kitso suka tayar dani kai biyu na kama ranan kawai.
********* ********* *********
Ina sauri in shirya in tafi gidan su gaida gwago na dake fama da kafa kwana biyu bata ko iya tashi.
Tsaida ni yayi wai sai na dafa mashi ruwan zafi a gurguje na dafa mashi don an dauke wuta na zube mai ya kewa ya na fito kada ya hana ni in yi laifi gun ta.
Yau basu sana a duk yan matan gidan su nan kowa da abinda take yi sai dai masu hira da maza cikin su sunfi yawa.
Na shiga duk suka bini da idoban kula su ba na shiga dakin gwago din na bada baya naji sun kwashe da dariya.
Na shiga naga gwagon nai mata sannu da jiki tana amsa min da kyat inda ciwo har da hali kamar bata son ansa min.
Muka dan zauna tsawon wani lokaci a dakin shiru itace ta kawar da shirun da fadin shi yana gida ne ko ya fita aiki ?
Nace yana gida na barshi zai fita yanzu kaita kada min can ta sake cewa ke har yanzu babu ko batar wata sai aukin akawo maki ki juye a masai.
Shiru nayi ina wasa da yatsun kafana ta sake cewa idan har kin san wani abu kike yin don karki samu ciki idan na gane ki bazaki sha da dadi ba gare ni.
Teema tashigo dakin wanan yarinyar da muka taba haduwa da ita a gidan farin zuwa na tana gani na sai ta washe baki tana min dariya.
Duk naje gidan mukan dan kebe da ita muyi hira wani lokaci takan ziyarce ni ko taje nai mata kitso a sace.
Yau ma mun samu mun killance take cewa dani ashe kin zo nace eh kwana biyu ban ganki ba tace kin san mutanen namu sai a hankali.
Kwana ki hajiya taji natafi wurin ki taita sababi dani ta kar na sake zuwa gidan ku idan na koma duk abinda tai min nina ja wa kaina.
Nace o o zuwan kuma da kike yi an maishe shi tsegumi tace ai basa so na je ba don suna ganin zan fada maki abubuwa gamay da mijin ki.
Tsaki nayi nace in dai wanan mijin nawa ne mai zaki fada mi wanda ban sani ba tai saurin jiyowa gareni tace akwai shi amarya kedai baki sani ba kawai.
Wata sabuwar fuska naga ta fito daga wani daki tana wani shan kamshi tana wani yamutse fuska ta dube mu a wulkance tafita daga gidan.
Da ganin ta goggace takwarai yar barikin gaske ce don basai an fada maka ba tafiya ma tana wani girgiza jiki goggagan karuwa da ita.
Sai naga teema tayi dariya tace dani kinga ta nan nace da ita eh sai kuma tace bari dai zanzo har gida in fada maki magana baiyi a nan an saka muna ido da yawa.
Ban damu da naji komay zata fada min ba muka dauki wani zancen zuwa can naji gaba na yana faduwa da farko na zo da suna yini ne a gidan sai kuma naji bazan iya ba.
Nace zan koma gida na leka gwago tana barci don haka na tafi ban sallamay ta ba Sadiya kawai na sama a gidan
mukai sallama na tafi.
Na murda kofan gidan najishi a bude nai mamaki da har lokacin bai fita ba zuwa aiki ba na tura kofa a sannu na shiga gidan.
Gaba daya baka jin komai sai nishin su a falon basu masan na shigo ba sai ihun da suka ji na kurma don gigicewa.
Da sauri ya tashi yana fadin ke ke ke may ye haka maynene zaki tara muna mutane akai kamar kin ga wani mugun abu.
Ban tsaya saurare shi ba sai na shiga kitchen na dauko yuka na nufo su dashi suna kokarin shigewa daki na nufosu da yuka gadan gadan nai kan yarinyar da yuka sai ya tare ni.
Nai cikin su gaba daya suka shige dakin sai da ya kimtsa yafito yaso ya jibge ni nai tsaye nace wallahi yau idan ka dake ni akan wata mace a gida nan sai nayi karan ka wajen yan sanda.
Fadin da nayi bai yarda ba sai da taji nace dama maman biyu tace ko harara na ka sake yi na fada mata ai karan ka.
Jin na ambaci maman biyu yasa ya dakata dako har yana nade belt zai shirin jibgana dashi yaga banza.
Amma duk da haka sai da ya tureni na fadi gefe na shiga bakina ni kaina naji mamakin kaina da na dake nai masu yankar kauna a gidan.
Ta fita tana wani taunan chewagun sai lokacin ma na gane ashe wanan yarinyar mai sallon da na gani gidan su ne wurin gwago.
Ta kalle ni a wullakance tace kin dauki bashi in dai wanan ne a tare kika samay mu tare kuma zaki barmu.
Ta wuce gaba yaba binta baya suka fice a gidan nasa hannu a kai nace ba shiga uku nikan nawa ya samay ni.
Dama abinda teema tai niyar fadamin kenan ta fasa naji dai tsna cewa ki tafi gida yanzu kada ki wuni a nan .
Naso na tambaye ta sai na share kuma don ban gane manufanta ba don tace magana baiyi a gidan sai dai tazo.
Wanan karon na turza na kafa mashi cin mutunci banji tsoron shi ba yace ke ki rufe min baki Liliya ta fiki komai ke inba kaddaraba may zai kaini aure ki.
Nace kamar yadda ka zamu min mijin kaddara a rayuwana in badon darajan iyayye ba mai zanyi da dan giya mazinaci a rayuw, , , ,
Marin da ya kwashe ni dashi yahanani karasa abinda zan fadi ya samay ni ya mamara awurin yakuma ce.
Auren Liliya zaiyi ko da ita taki shiyasa uwarshi ta aura mashi ni don ya manta da Liliya.
Nace auren ku bai damay ni ba zina daine bazan yarda ashigo har cikin gida ai min ba yace tunda gidan ki ne sai ki hanani abinda nake so yi.
Ranan dai munyi shi ba dadi yafice yabar min gidan bai kwana a gida ba washe gari na shirya zuwa gidan maman biyu.
Na samayta a gida bata fita aiki ranan na bata labarin tace ni wanan mijin naki na rasa wani iri dan iska ne safiya ai mashaya giya wasun su basu damu da mata ba.
Nace anty shi fa tatirin dan iska ne na gaske tace aiko ba irin ki ya kamata ya aura ba daidai dashi ya kamata ya samu yar iska irin shi su saje.
Amma ke ai cutar ki zai ta yi a banza don baki saba da abin yan bariki ba ni fa ina jin tsoron kar ya kwaso maki karuwa su halaka ki.
Nace nima anty abinda nakewa gudu kenan wallahi yau wanan tazo gobe ma wata zai kwaso duk a mutum daya.
Tace Allah dai ya kyauta ban dawo gida ba sai yamma lis koda na dawo gidan yana nan kamar yadda na samay shi alamu sun nuna bai dawo ba har lokacin.
Na kule gidan na shige dakina bayan na gama abinda nakeyi ne na kwanta can cikin dare naji dawowan shi na fito na bude kofan ya shiga ciki.
Fuska a daure babu walwala nima haka na daure fuska na ina budewa na wuce zuwa ciki abina na kwanta.
Da safe kafin na fito yayi sakkon barin gidan duk da yake weekend ne a lokacin amma sai da ya fita gidan .
Can yan iska irin shi fada ya hada su sukai mashi dukan tsiya akan Liliyan Allah ya rama min ya dawo gida jina jina dashi.
Nan ya zube min a falo yana kwala min kira na fito da sauri yace taimaka min da ruwan zafi na gasa kafa na.
Nai kamar kada insa sai na tuna da hadisin da kecewa Aljanan ku na karkashin kafan majajen ku.
Da taimakona ya samu ya gagasa jikin shi da kyan ya samu barci koshi sama sama da safe jikin yai masa tsami sosai.
Kwana biyu bai iya ko dagawa nan yan iska suka shiga shigowa gida maza da matan su wai sun zo gaida shi.
Naga mutane iri iri a gidan wurin dubiya sai na kara tsunke ma alamarin shi a raina nasan ba karamin dan duniya bane ashe nake zaune dashi .
Harda maza masu kitso mata masu dan buje iya cinya da sauran su inaji harda shugaban yan giyan lagos yazo gaida shi wasu in sun zo su bani alheri in sun tarar dani a falon wurin shi don boyewa yake cewa nayi kada su ganni wai yana jin kunya ace nice matar shi.
Gashi ina jinya shi amma sai zagina yake ba kakautawa ranan sai ga mahaifiyar shi tazo ankawo ta ta gaida shi nan na dan ji abinda ya faru da kyau wurin ta.
Sun sha sun bugu ne sai wani yazo yaja liliya sai ya hana su kuma suka tarar mashi sukai mai dukan tsiya sai da aka kwace su.
Abinda yasa bai je asibiti ba yan sanda zasu cisu kudi sosai ne shine akai rufa rufa yake jinya a gida.
Bayan su gwago sun tafi daki na shige naki fitowa yai kira kamar may naki fitowa waje da ya matsa min sai na leko nace kira karuwan ka tai jinyar ka mana .
Ita da kaje fada don ta da ya dauka baza iya ba sai yaga na koma daki na rufo kofana nabarshi zaune a falon.
Zagi kan na sha shi a wurin shi amma baisa na fito ba sai da safe na fito yana zaune yana gyan gyadi saman kujera yana jin motsina ya bude idon shi da sukai ja yace don Allah taimaka min nai brushe kafan nan ya matsamin da ciwo.
Nace karuwan da kai fada a kanta bazata tai maka ma bane ai ita ya kamata tai jinyar ka ba ni ba.
Ya marairaice yana cewa don Allah taimaka min asibiti zan koma a duba min kafar kamar zan share shi sai dai na taimaka mashi yai wanka.
Ranan harda sallah akayi amma saidai a zaune ya ban kudi wai a sayo abin karyawa na safe na hada yace na taimaka mashi yaci sai wani cika nake da batsewa.
Yadawa asibiti da rana sai ga yar iskan ta shigo muna gida da kawayen ta nan suka zube falo ana ta tafka iskanci da iya shege a folon namu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , ,
🧕🏿1️⃣8️⃣🧕🏿
YAR UWA NOVEL NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KAR KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , ,
Satin shi guda cur a gidan yana zaune yana jin ya Lilliya takar itake jinyan shi kusan ma a gidan take kwana nai magana ya zundumi ubana tun lokacin ban sake kallon su ba.
Idan dai gari ya waye zan masa ina kwana da yaya jikin idan tana kusa zai amsa min da kyat kamar baya son gaisuwan nawa.
Sai in bata kusa zan samu ya dan amsa min har yasani wani abin in mashi ranan maman biyu tazo duba shi ta samu Lillya mane dashi.
Ya dan ji nauyin hakan amma abin su na yan duniya sai bai nuna a fili ba ya basar ta kasa yin shiru tace wanan fa da take manne dakai haka.
Matar kace ko mai, sai yadan yunkura yana cewa No kawatace take dubani.
Kallon mamaki taimai tace amma kasan hakan ba daidai bane agidan ka wata karuwa zata shigo ga matar ka na sunna da sunan wai tana duban ka ai duk abinda zakuyi ku tsaya iya waje ku yi shi.
Lilliya ta dago kai tai mata wani kallon banza tace ke wacece da zaki zage ni da sunan karuwa ai karuwancin ma isa ne ko.
Tace OK yanzu zaki san ni ko wacece ya dago da sauri yana ce mata will you keep quite.
Take ta har zugo mashi maman biyu batai mata magana ba ta mike zuwa kofa ta sa mashi key ta rike ke din a hannun ta.
Waya ta dauko tai kira dashi aka amsa mata sai lokacin suka kulla da ita Lilliya ta dago tana cewa may zaki yi in bariki ne nafiki iya wa tace bissimillah ina son yau inga iya barikin naki.
Taso taja da ita jacket din dake jikin ta tacire sai uniform din ta ya baiyyana dakatar da abinda tai niyar yi mata tayi tana cewa haka kawai zaki zageni.
Karyan bariki kike yau zan gwada maki akwai wa yanda suka fiki suka riga ki shiga bariki da lasisi.
Mari takai mata naji dadin hakan daga inda nake tsaye a rakube jikin kujera.
Taso turzawa amma karfi ba guda ba take ta murde ta kafin tai wani abu aka fara dukan kofan ta je ta bude sai ga kartan sojojin tsaye a kofa ko wani a cikin shirin shi.
Hakkuri ta fara badawa harda shi munafukin yana cewa madam don Allah ayi hakkuri rashin sanin ke wacece yasa tai maki haka.
Arest her tace da su take ko suka kamata saura shi tace shima a tafi dashi fuskata babu burbushin rahama take maganan.
An fice har dashi a gidan wani dadi ya kamani sai hawaye bata ko tsaya ta kaina ba ta fice gidan itama ta bisu.
Daga inda nake tsaye a cikin fargaba da tsoro na mara masu baya ina tsaye motocin su suka wuce dasu.
Ko ba koma yau maman biyu ta daukan min fansan wullakacin da ake min a gidan don ya gama zagine ke nan a kanta ta shigo gidan ta samay ni daki ina kuka nasan abinda ya kara harzuka ta kenan.
Ina zaune takure a cikin damuwa sai gashi ya dawo duk ya jirkita azotana da yadawo zai hauni da duka da zagi yadda ya saba ne.
Sai gashi naga sabanin hakanan ya dawo ya bukaci ruwa masu zafi zai gasa jikin shi dashi sai kuma dan abinda zaici.
Yana zaune bayan ya fito wanka ga abinci a gaban shi yace Safiya ina daki na amsa masa na fito kujera ya nuna min da hannu alaman wai na zauna.
Sannu a hankali na kai zaune saman kujeran ina fuskantar shi tare da sauraren abinda zai fada min a lokacin.
Yace kin dai ga yanda wanan matar suka yi a gidan nan ko na dago kaina a hankali ns dubeshi ya tsare ni da idawan shi.
Na sake dukar da kaina kasa ba tare da na amsa mashi ba yace yanzu dai ba wanan ba abinda nake so dake shine.
Kiwa ita madam din nan magana a sake Lilliya don ba karamin tsaro sukai mata ba yau kawai duk ta jemay saboda tsaro da horo irin nasu na sojoji.
Ban san cewa girman ta da kimarta yakai haka ba sai yau din nan da na gani ke kaidace zakiyi magana a saki Liliya da sauri inba haka ba abin zai jawo min matsala sosai gani zaune gida banda lafiya.
Banyi magana ba naji yana cewa umurni na baki ba son jin raayin nake so ba ki mata magana a sake ta.
Na nisa nace shike nan kiran yace eh shike nan nake so ki fada mata a sake ta.
Na mike ina ce mai ai da kai kai mata magana zai fi don zata fi jin maganan ka sama da nawa do ni ban san ta inda zan dauko mata zancen ba.
Rashin mutunci tai mata ta dauki mataki ta dauka irina ne da kuke wa son ranku a gidan ku taka ni iya son ranku a zauna lafiya.
Ni banga laifin maman biyu ba da ta dauki mataki ga marasa mutunci irin ku wayan da basu san darajan aure ba.
Ke ya isa ya dakatar dani ta hanyan daga min hannu shi yace umurni fa na baki in kina son kanki da lafiya gidan nan kiyi abinda na umurce ki da shi.
Fuskan shi babu alaman sauki gare shi don haka na juya na tafi kawai ba tare da nai wani magana ba.
Da safe nai sammakon zuwa gidan maman biyu nayi sa a tana gida kasa na zube ina mata godiya ga hawaye na zuba a idona.
Ta ce assha safiya tashi tashi don Allah may ye hakan ai dole a tausaya maki don kinyi karanta da irin wanan rayuwan.
Dudu fa baki kai ashirin ba amma kike fuskantar wanan bahangon mijin naki mai rayuwan kazan ta.
A gaskiya dani wata ce a cikin zurian ku da sai ince a raba wanan auren don baida alaman nadama ko gaba duk kaga namiji yakai haka alamarin akwai ban tsoro cikin sa.
Nace yanzu ma shi ya turo ni akan nazo na baki hakkluri a sake ta wai idan ba haka ba zan gane kurena gare shi.
Tace da sauri kinji ba na fada maki ai baida nadama ko kadan ai dana sani abarshi can shima amma sai na tausayama luluran da yake ciki.
Gaskiya naso yin wani abu akan zaman nan naku amma sai ina ganin kamar ciki ne dake .
Nai saurin dagowa ina duban ta a gidimay nace ciki kuma anty tace tabbas indan ba hasashe nake yi ba kina da shigan ciki.
Gabana yai mugun faduwa tace yaushe ne rabon dakiyi jini a tare dake ?
Nai shiru ina nazari can nace gaskiya wata uku kenan tun da nayi ina gida ba sake yi ba.
Tace shit,
Zargina ya tabbata gaskiya akanki na dade dama ina zargin hakan amma zan sa aimaki test a gani.
Yanzu ki ci abinci zanyi waya a sake ta don ba imani ke ga irin su ba tare suke da yan daba sai dai da yake zamu kafa hujja akan in wani abu ya samay ki nan da shekara biyar itace.
Naga tasa akawo mata abinyin test ta auna fitsari na ya nuna positive alaman ina dauke da cikin wata ukun.
Nai bakin ciki da jin wanan labari kwarai da gaske munyi sallama zan tafi take cewa in kwantar da hankalina killa sanadiyar cikin nan in samu sauki a gurin shi don wasu maza nason yara.
Ta dan bani shawarwari masu mana ta cika ni da abin arziki na bar wurinta zuwa gida zuviya ciki da bakin cikin labarin cikin dake jikina.
Yana zaune ya kura ma tv ido na shigo bako kin dawo sai cewa yayi yaya kin samay ta a gida ?
Nace eh na samu dama zata sa a sake ta saboda kai koda banje ba din tace abin da tayi matane ya bata mata rai ai.
Bai yi magana ba kuma naji ta yadauki waya kowa yake sanar ma zancen sakin nata oho nadai ji ya dade yana waya din.
Nikan abinda ya damay ni ya damay ni zancen cikin dake jiki nakewa bakin da nadama ina tausayawa rayuwan da abin cikin cikin nawa zai taso ya ga ubanshi nayi a duniya.
A haka ma ba tarbiya yaya za a ce aiwa yara tarbiyan rayu kirikiri bani shiga mutane duk da bariki ana cewa ba ruwan wani da wani .
Ina ganin barikin dane bana yanzu ba don wata mace da tazo kitso ya dawo ya shigo murtun compound din tace .
Na dis yeye man you marry , .
Dis man too dey follow women .
Murmushi nayi mata kawai ban bata amsa ba sai wata da take zaune ne tayi mata magana da cewa hakana fa ba kyau.
Sai tayi shiru damuwa ya isheni da fargaban halin da zan shiga nan gaba a garin mutane .
Sai wuraren sha dayan rana aka sako lilliya daga hannun sojoji bayan tasha dan banzan wahala.
Haka ya daure ya fara fita tun wanan ranan baya zama gida yana wurinta acan kafar ta karasa warkewa a hanya.
********* ********* *********
Yau na tashi jikin ba dadi ga damuwa dana sawa raina ga kuma halin maigidan ba sauki akan komai.
Kwace nake a falo saman dogon kujera nayi da daya da kafana ko zan ji dadi jikina misalin karfe biyar na yamma.
Can na fara barci naji dawowan shi gidan yana gauran kofan shigowa gidan gabana ne ya fadi don ganin shi a murtuke da fuska.
Innalillah wa,inna ilaihi rajiun Allahuma Ajirni min musibati waakhimi min kharir minha na anbato a raina.
Ya shigo yana ta faman kalle kalle har ya kai zaune saman kujera tsoro ya kamani don ban an damay ya shigo ba.
Na dago cike da natsuwa da girmamawa na furta sannu da dawowa bai amsa min ba sai taba da ya ciro cikin aljihun shi yana kokarin kunawa warin taban ya gauraye falon lokaci guda.
Na mike da sauri zan bar falon sai lokacin yai magana yace ke mayye haka kuma ?
Ina kokarin tare aman da yazo min a baki nace zan zan zan sai na mike da gudu na fada dakina direct makewayi na shiga nai ta shega amai aciki.
Bina yayi da kallon mamaki bai yarda dani ba, ya mike ya bini yana tsaye nake ta aman sai da nagama na mike zan fito naganshi a tsaye ya rike kugun shi.
Gabana ya sake faduwa yana min wani irin kallo na tuhuma mai kama da bai yarda dani ba yace ke mai ke samun ki ke amai haka.
Na amsa dakyat da cewa ban da lafiyane .
May ke damun ki koma may nene ke kika sani don ni banda lokacin ki ya juya har ya fara tafiya ya juyo yana ce mun ki sani ban son kazanta a gidana.
Na yamutsa fuska nace kona bata ma aini ke gyarawa ba wani ba ya juyo yace may kika ce ne ?
Nace bada kai nake ba ai yace shgiya naga randa bakin nan naki zai mutu da bakar magana dibi yadda kika murje kikai wani bulbul dake duk abincina kike cinyewa ga banza.
Yafice na sauke ajiyan zuciya na zauna nadan huta na fito kai tsaye kitchen na fada don girka abinci don nasan a gida zai kai dare tunda ya dawo da wuri.
Na gama aiki da kyat na shiga na watsa ruwa don lokacin sallah ya gabato ina zaune ina lazimi naji ya kwala min kira.
Na taso dagani sai yar doguwar rigan da anty ta bani ranan da naje gurin ta tace ta gani ne dataje sayayya ta sayo min shi.
Na fito abincin da na aje mai yana bude na sauke idanuwana akan abincin dake gaban shi din.
Ya watso min harara yana cewa wani irin abinci kika dafa haka nace shi kadai ya saura muna a gidan shiyasa na dafa taliya ne nai jelop din shi.
A fusace yace what, what are you saying ?
Kina nufin har abincin da na sayo yakare komay ?
Na girgiza kai nace yaushe rabon da ka sayo abinci a gidan nan wanda ka sayo din ai shi na dafa lokacin da bakada lafiya masu jiyan ka suka cinye.
Ya dakatar dani da hannu yana fadin ya isa haka maganan ya isheni sai ki zauna ki cinye dama haka kike so ai.
Ya dauke makulin motar shi dake saman tabur yabar gidan yana faman huci.
Sai da muka share kwana uku cur ban da lafiya kuma ba a girka komai a gidan.
Ina kwance daki ina fama da kai na nidai kamar kar maman biyu ta ambaci cikin nan wahala ya soma zuwa min.
Sai kawai gashi ya shigo min daki misalin goma na dare don rashin imani irin nashi sai ji nayi ya afka min .
Na soma kuka ya gama ya daga yana cewa may ye haka tsiyan azo wurin ki kenan walahi ki damu mutum da munafukin kukan ki.
Na dago ina cewa azo min haka kamar wata karya ni kadai nasan abinda nake ji a jiki na yanzu haka ji nake kamar baya na zai tsage san nan ban ci komai ba tun safe ga yunwa na damuna.
Yakai kofa ya juyo yana cewa ai sai ki samu abinda kikaci ko kije asibiti adubaki nace da nawa zan tafi asibitin yace ke kika sani.
Washe gari ma da ciwon na tashi don da dare banyi barci ba ciwon mara ya hanani shakat a rayuwa na.
Ban fito ba har ya gama shirin shi zai fita komay ya gani sai ya leka dakin nawa.
Ina kwance ina faman murde murde a saman gado ni kadai a dakin ya leko yadan dade tsaye akaina sai ya karaso bakin gadon yana cewa.
Wai ke may ke damuwan ki ne haka kike faman murde mude a gado ke kadai a dakin ?
Da kyat na bude bakina nace cikina ke ciwo sai kaina dake sarawa kamar zai balle min nake ji.
Ya fita da zai dawo sai gashi da magani da maltina da peak milk mai sanyi a leda da kayan abinci ya sayo.
Ya samay ni a falo na yi laga laga dani ya miko min maganin da maltina yana cewa ga magani ki sha.
Nai mamaki ganin magani harda maltina ya sayo min babu kunya babu alamanta ya zauna yana cemin tashi ki sha.
Da taimakon shi na hadiye maganin sannan ya hada min maltina da madara yace in shanye kafin ya fito.
Bayan kaman minti shirin sai gashi ya fito ya dubeni yace yanzu ya fada maki ko yana nan ?
Nayi ajiyan zuciya nace ya fada min nace na gode yace na taimaka maki ne don nima kin taimaka min da banda lafiya don haka arama ma kura aniyan ta.
Na ciza baki na yunkura ina cewa aiko kura ta gode in don Allah akai mata.
Ya harare ni yace gunma ki wartsake don ba zan dauki nadewa a gado ba tunda kun hanani hurda da yan mata na yanzu.
Na saurin kallon shi ina cewa wa ya isa ya hanaka da abinka muka ganka mu mun isa wanan sai Allah daya hallice ka ai.
Sai kawai naji ya kyalkyale da dariya sai nai saurin dago kai na kalle shi cike da mamaki yau shike dariya haka kamar ba shi ba.
Yace ashe kun san da haka da baki wahalan hada baki da matar sojs tashigo abin da bai shafe ta ba.
Ya fice ban sake jin duriyan shi ba sai dare sai gashi ya dawo min a cikin maye yana ta tsuki burutsun shi a gidan.
Ina daki ya samay ni a haka na dan dago ina kallon shi naga ya nufo ni gadan gadan sai na fashe mai da kuka don na san halin fitinar shi sarai ba imani ne dashi ba.
Yace a cikin maye ke ke may nene haka ?
Na yun kura na tashi da kyat ina cewa don Allah yaya kayi hakkuri wallahi ban iyawa banda lafiya ne.
Na gaya maki zan maki wani abune kawai kawai yana inda inda ya kasa fadin abinda zai fada din ya juya yana suruntun abinda banji ba ya fice dakin.
Na lumshe idanuwa na a hankali ina sauke ajiyan zuciya ganin ya fita natashi na rufe kofan dakin nawa.

🧕🏿1️⃣9️⃣🧕🏿
YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDINE IDAN BAKI BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE.
Kwanaki goma sha uku da aukuwan wanan lamari yana zaune a falo ya harde kafa yana shan ruwan kwalba da sigari yana sha yana yamutsan fuska kamar an sashi dole ya sha.
Na fito daga daki rike da cup a hannu na ban san yana zaune wurin ba sai ganin shi nayi yana korawa.
Da sauri na wulkita zan juya dakin da nafito ganin haka yasa shi mike a ida yake zaune din ya nuna ni da hannu.
Ke ban san sau nawa zan fada maki cewa idan ina zaune kika gani ki daina gudu kamar wata mara gaskiya dake.
Nikan ban masan yana yi ba don na dafe bakina da hannu daya kar amai danake ji ya fito mun a falon.
Ganin yanayin da nake ya dakatar dashi ga fadan da yakeyi din ya kafa min idanu yana kallona a cikin zargi.
Yace Safiya ciki gare ki ne ko may ban sani ba don tun ga kwanaki naga kina wanan aman na tsiya.
Nikan ban ma san yanayi ba ina tsugune na dafe kaina sai kakarin amai da nakeyi a ban dakin .
Hakkali a tashe ya sake magana da cewa kefa nake tambaya na dago da kyat ina cewa cikin yanayin ciwo warin taban nan ne ke wahal dani.
Ya ja tsuki ya juya yabar wurin dakin shi ya shige da bacin rai bai fito ba haka nima ban fito ba na kara dunkulewa cikin dakina.
Kwana biyu baya gidan ban san ina ya shiga ba ga komai ya kare min don haka na shirya zuwa gidan maman biyu.
Yanayi na kawai ta kalla tasan ban jin dadin jikina yace wai ko kunje asibiti kaina girgizamata kawai alaman a a.
Safiya kamata yayi ki fito ki sanar dashi zancen cikin nan amma ba wai ki boye ba don ba zai yuyu kibar ciwo a jikin ki ba don ciki ciwone.
Nace to Anti shidin ne almarin shi har yanzu ba canji kin ga tun kwanaki ya gane bana jin dadin jikina amma don rashi imani yau kwana biyu kenan baya gidan kuma ban san ida ya shiga ba.
Idan ma yana nan ba wai kyaleni zai ba don banda lafiya haka zai afka min kamar dabba don rashi imani irin nasa.
Tace ke Safiya kar in sake jin kalman dabban nan a bakin ki, karki manta shifa mijin ki ne na sunna.
Nace anty ai ba fadina bane, Annabi nefa ya siffanta duk mai irin wanan dabian da daba, sannan sai kinga irin wahalan da yake bani abin har da mugun ta yake hadawa.
Wai in mun hana shi bin mata banza waje ni zanji a jikina tunda nace ina iyawa.
Sai na soma mata kuka tai saurin cewa may ye haka kuma safiya ko so kike ki tada min hankali ?
Ina kuka nace wallahi anty ba haka bane wallahi ni kadai nasan abinda nake ji ajikina yanzu haka idan indan ina tafiya jire nake gani marana kuma kamar zai tsage min biyu nake jinsa sanan na kasa sa komai a baki na komai naci sai ya dawo min.
Tace ya zama dole ki dada masa idan bai dauki wani mataki ba ki zo kifada min kina jina ko don ba a zama a duhu haka kina jina ko.
Nace naji zandan kwanta kozan samu barci yanzu haka jiri nake gani tace inshiga daga ciki don kar a dameni nan falo na kasa barci.
Na samu nayi barci sosai sai wajen uku na rana na farka daga barcin naji dadin jikina matuka don naji kaina yabar sarawa.
Nai sallah naci abinci sannan na fara shirin komawa gida ta harhado min komai da zan bukata zakace ko uwatace ko wata yar uwana ta jini abinda take min.
Kusan karfe hudu da rabi na dawo gidan na danji saukin jikina ko banza nadan samu warwarewan zuciya na dana dan samu idan da na tsiyaye.
Har na dawo na dan gyara gida tunda na samu karfin jikina bayan nai sallah ishai ina kwace saman carpet ina kallo ya dawo gidan.
Kai tsaye dakin shi ya wuce bai fito ba yan yai wanka ya fito saye da guntun wando da singlet sai taba a hannun shi.
Bai same ni a falo ba yayi zaton ina dakin girki ne sai da ya saurara sannan yajiyo kakarin amai daga daki na ina cikin ban daki.
Ya mike da sauri zai bini sai gani na fito ina tafiya kamar wacce tayi makwanni cikin ciwo ya dinga sata kallona har na dawo inda na tashi saman carpet na kara kwantawa.
Na daure na dago kai a hankali nace dazun ka dawo ina gaisheka baka amsa min ba ido kawai ya tsura min baiyi magana ba.
Sai cewa yayi tashi muje chemist a duba min ke ban yarda wanan uban amai da kike min haka ba cikin gida in an yi magana kice babu komai.
Ban mussaba na yunkura na tashi daki na shiga na dauko hijjab dina na fito ya kulle gidan muka wuce chemist din da yace.
Sai daya bata lokaci sosai yana dudubani don har fitsari yasa nayi ya auna ni ga dan karen tambayoyi da yake min har na gaji da amsawa daga karshe dai ya bashi tabbacin ina da ciki wata hudu da kwanaki.
Ya bani magunguna da zanyi amfani dasu don taimaka min wurin rage aman da nakeyi don acewa mai chemist din yawan kakarin da nakeyi yasa cikina kullewa .
Amma ba ciwo bane mai tsanani don haka mu kwantar da hankali mu tunda ya fara magana yake gum baiyi magana ba sai mur din da yasha.
Hakan da yayi yasa nasan akwai magana fan a zuciyar shi dama kuma abinda nake gudu ke nan ban yi saurin fada mashi ba.
Ya sallami mai shagon muka kamo hanyan gida har lokacin yana gum da bakin shi sai da muka shiga gida na yi hanyan daki na sai kawai naji ya shakoni ta baya.
Idanuwa suka firfito waje kamar zan shude yace a hasale uban wa yai maki cikin da kike dauke dashi nace .
A lokacin da yasan bakin cikin da nake ciki nafi bukatan ya kashe ni in huta da wanna rayuwan wahala da na samu kaina a cikin sa.
Jin kaifin shakan yai yawa nace uban da yake matseni duk dare yai min dole ka taba kwana dani a cikin yarda nane a gidan nan.
Ya kara shako ni yana fadin yar iska sai ki san yadda zakiyi da cikin nan inba haka ba na lahira sai ya fiki jin dadi.
Nace cikin karfin hali amma kadai san ba yar iska ka samay ni ba ko bantaba kwana da wani namiji ba bayan kai a rayuwa na da zakai min wanan tambayan yan iska.
Yace good sai ki san yarda zakiyi da cikin nan a gidan nan don ni ban shirya haihuwa ba yanzu
yara su hanani shakat a rayuwa na.
Ras naji gabana ya fadi nace wata sabuwa kenan kuma inji yan caca wani sabon fitina kuma zai kawo min yanzu.
Hakana mukai ta jidali a gidab dagani sai shi daga karshe dai ya kaini kara wurin ma haifiyar shi akan lalelale sai na zubar da cikin nan in ina son a zauna lafiya.
Babu kunya ta kirani nazo gidan ta ta tare ni da maganan cikin har tana cewa nafison in cika gida da yara miji baida wadata.
Nace Allah daya bani shi zai dubeni da abinda ke cikin cikin nawa don haka na san zunubin da ke ga wanda yai kashin kai ni ba zan zubar ba.
Tace tunda haka kiks zaba duk abinda yai maki ke kika jiyo baruwa na karma kice kin sanni.
Ranan ban kwana ba sai da yai min dan karen dukan tsiya har ya barni kwace da kyat na lalaba naja jikina zuwa dakina.
Washe gari jikin yai min tsami na lalaba nai wanka na lalubo sauran magani na hade na koma na dun kule.
Waya naji yana yi da wani likita akan zubar da cikin koda ya leko dakina na lafe kamar mai barci sai ya fice gidan.
Ina nan ina sake zuci sai sallaman maman biyu naji gidan don tun ranan da suka samu matsala akan lilliya bata dawo gidan ba.
Yau tazo taji yadda mukayi dashi ne akan zancen cikin na tare da murna na abinka da wanda ta rigaka kwana sai ya rigaka tashi.
A take ta gane yanayin da nake ciki na bugun da yai min a daren jiya kan naki yarda a zubar da cikin cikin sauki.
Tace dani kunyi halin naku ko, ?
Kin sha dukan ko badai duk akan cikin bane wannan dukan haka ?
Idana sun ciko da hawayen na dama nace anty cewa yayi wai a zubar da cikin shi bai shirya haihuwa yanzu ba.
Tace a cikin mama what ?
Na hade wasu yawun bakin ciki nace har da maman shi abinda tace dani kenan wai idan ban zubar ba duk abinda ya samay ni ba ruwan ta.
Kai ta dafe tai shiru na wani lokaci can tace wai wa yan nan mutane kuwa musulmai ne kuwa ?
Na murmusa nace wai musulmai ne kuwa anty babu dai tauhidi a zukatan su ne kawai.
Ta mike ta fice gidan kai tsaye ashe wurin aikin su ta tafi don ta bincika tasan komai akan shi.
Can ta samay shi tace su hadu gidan shi yanzu sanin halin shi da tayi yasa baiyi gardama ba ta riga shi isa gidan ya samu tana jiran shi.
Yana shigowa tace zauna shagon mata don ka zama shagon mata baka da aiki sai dukan mace macen ma karamar alhaki irin wannan.
Dadin may kake ji cikin dukan da kake mata ne wai, kai bama wanan ba cikin dake jikin ta waye mata shi ?
Ya dago ya kalle ta don jin abinda ta fada tace eh ina son inji ko ba naka bane don musan abin yi.
Yace kin gane madam nasan ciki nawa ne to amma ni gaskiya ban shirya, , , ,
Sai yai shuru tace, go on, baka shirya may ba dama ka auro tane kawai don ka more rayuwan ka da ita ko may ?
Tace tirr da hali irin naka tirr da rayuwan kafiran farko kai acikin su ma kana kasa da fir,auna.
Ashe kai ba abin farin ciki ne ya samay ka ba maimakon ka godewa Allah da baiwan da yai maka sai kawai kai halin ku na yan duniya.
Ba a haihuwa kai aka haife ka, dama kenan ka auro tane don kawai kaji dadin rayuwa da ita ko may tun wuri ka gyara halin ka tun duniya nayi dakai.
Tai mashi kaca kaca yana saurare ta kamar wani salihi can dashi ni nasan jin ta kawai yake yi badon nasihan ta shige shi ba.
Ta nisa tace dashi haba dai kamar wanda baida tausayi katuna fa kaima kana da kanai kuma haihuwa zakayi indan anyiwa taka haka yaya zakaji.
Sannan ina son ka sani idan wani abu ya samay ta, ko cikin dake jiki ta sai nasa an daure kowa naka a duk inda suke a garin nan sai antona man su.
Kuma ka tabbatar da kana bata abincin daya dace mace mai ciki taci dan lafiyan jikin ta dana baby dake cikin ta.
Duk ta baibaye shi ta ko ina baida halin motsawa ta mike tana gyara gyalen jikin ta, ta wuce ko kallona batayi ba ina kuka da mahaifina da ya jefani wanan halin.
Ya dinga sintiri a cikin falo yaje ya dawo har na wani lokaci ya dawo inda nake rakube yace ke ki fada min may ye hadin ki da wanan matar.
Nai shiru ya kara daka min tsawa yace ba zaki fada min ba, nace yar uwan mahaifiyata ce na fada maka tun farko sai ya ja tsuki ya fice gidan.
Tun wanan lokacin bai ce min ban ce mai zaman doya da manja muke yi dashi a gidan sai ya kwashe kwanaki bai gidan sai yaga dama zai dawo bai dadewa kuma ya fice.
Nima haka ya fiye min dadi don ba matsi ba tsagwama ba warin taba da giya sai in yini falo gidan hankalina kwance.
Abinci dai da maman biyu tasa mai doka ina samu sai dai bamai dadi ba amma ina ci in koshi ko ba dadi yafi babu.
Ranan ina zaune a falo ina kallo sai gashi da liliya yana gaba tana binshi a baya da katon akwatin ta, suna kokarin shigowa dashi.
Wai ashe auren bariki sukayi, yan giya yan uwan su suka daura masu aure acan mashaya su.
Ko kallona basuyi ba suna kokarin shigewa da kayan nata, ina zaune ina kallon ikon Allah, suka shige dakin shi da kayan can sai gata ta fito ta bude munafukin gyalen da ta rufe fuskan ta dashi tace.
Ke wa kike da suna ina son fada maki ban son ganin ki a falon nan indan maigidan na gida in ba kiran ki akayi ba.
Nace ke kuma a suwa dan wake a hotel, tace ni a su matar gidan, inda ance min karuwa yanzu na zama matar gidan sai
a nemi wani suna a canza min.
Ya wuce a kiraki da kilaki ko mai dadiro don sunan da ya dace dake kena don kin fi cancan ta dashi.
Shine ya fito yana cewa baby na fada maki bani son kina shiga tsabgan yarinyar nan, da ita da babu duk daya a gare ni tana zaman cikin ta ne da tace taji ta gani dashi.
Kema kin san wanan ba ajina bace kawai dai matsala aka samu aka aura min ita amma wanan abar ai da gidan aiki ya kamata ta a danganta ta.
Nace andai ji kunya wallahi tunda dadiro aka fake aiko anci baya wallahi ya balla min harara da jajayen idon shi.
Yaja ta suka shige ina jin suna dariya dariyen su a dakin ga kida na tashi ina daga dakina bakin ciki ya cika ni.
Haka dai muke zaune a gidan ba ruwan shi dani ina kallo zasu sayo abu su zauna a falo su baje suci inya rage a zubar ga abin shara.
Ko ta dafa da kanta a gidan kanshi yana tashi gidan haka zanta juye da cikina su gama su cinye su hana min ina kallon su ko kallo ban ishe su ba.
Ranan suna zaune suna ta shakiyancin su a falo na samay shi a falon suna gani na, ta wani shige mai jiki .
Shi kuma sai ya daure fuska murtuk nace dashi yaya abincin da ka saya min ya kare tun kwana biyu da ya wuce.
Sai cewa yayi kije gidan ku a baki don ni ba dole bane sai na baki tunda baki jin magana na.
Ita kuma ta dago kai ta wani harareni tace ke bana fada maki kada ki kara kula min miji in yana nan ba shine don maita irin naki kikai mai magana yanzu wai manyar ina ce halan.
Nace ke tsohuwar kilaki rufe min bakin ki da ke nakeyi balle ki samun baki ga zance na.
Tsawa ya daka min yace duk ranan da na sake jin kin kira min mata da kilaki sai na halaka ki a gidan nan.
Kallon mamaki nabi shi dashi ina cewa ai akwai Allah yana sane da komai da ka ke yi shi zai saka min.
Ban karasa ba ya buge min baki gau da mari sai da wani wuta ya gittamin gaba na.

🧕🏿2️⃣1️⃣🧕🏿
YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , , ,
Tun muna jiyo maganan su sannu sannu har suka fara daga murya mudai har barci ya kwashe mu bamu san lokacin da suka kwanta ba.
Shiko yaya saadu gida ya tafi ya samu mahaifiyar da yanzu jikin sai a hankali sun kammala cinikin dare habiba na kirga kudi da sukai ciniki.
Dinban habiba yaya yace munafukan banza da wofi kizo ki zauna da yar uwar ki kikace baki da lafiya ne.
Yanzu may kike yi anan zatai magana ya dago kamar zai make ta yana cewa duk dai abinda kawa wani kasani sai an rama mashi.
Mahaifiyar su tace kai kada kazo fa kace zaka samin yara gaba da hitina kan safiya.
Idanuwan shi sukai jawur ya kalleta yace mummy halinda yariyan nan ke ciki ba wanda ya ja mata sai ke saboda son kai,
Kin san danki yafi karfin ki kema da kika haifeshi baki iya shi rayuwan mu ba daya ba da tashin arewa amma kika rufe ido kika nace sai anyi.
Mummy ansan mukadari ne ba wanda ya isa ya goge shi amma kuma sai ki saka ido a kanshi aike kika haifi abin ki.
Ajiyan zuciya tayi wani bakin ciki ya tokare mata zuciya, tace Saadu, nayi kuskure da na dauka Safiya idan ta auri yayan ku zata gyara rayuwansa na jefa rayuwan yarinya cikin kunci da wahala.
Ni kaina nasan ba aiwa yarinyan nan adalci ba amma ba yadda na iya dashi sai ya ce zai dauki mata akan magana na.
Gashi mahaifinta dan uwa na gari ya dauki amana ya damka a hannu na don ba da halin zuwa gidan su gun mahaifanta takai kara uba yace bai yafe mata ba.
Yaya saadu ya katse ta da cewa safiya tana cikin kunci da bakin ciki wanda duk wanda ya ganta yana da imani dole ya tausaya mata ace ana horon mutum yunwa saboda Allah fa.
Sannan mummy keda kanki kika bashi goyon bayan a fitar da cikin da jikinta keda kanki mummy mu mai yasa baki fitar da cikin mu ba da kika samu.
Wani kallo ta watso mai bai damu ba ganina acikin kunci da bakin ciki yafi komai bata mashi rai yace yanzu gashi tace zubar da cikin zatayi ta huta da wahala.
A razane tace zata zubar kuma da cikin yace eh to ba abinda kuka zaba kenan ba dama itama yanzu shiyafi mata sauki zubar da cikin.
Mummy zan inya hana wani abu mummuna da zai faru nan gaba kema kiyi abinda abin da ya dace akan zaman nan nasu amatsayinki na uwa gare shi.
Don sai karuwan nan ta bar gidan nan wallahi ko ta halin yaya, ya juya zai fita daga dakin a hasale tace saureren nan Saadu kaji.
Ban son kana shiga harkan gidan dan uwanka haka nan kabarshi shike da gidab shi da su.
Ya zamana na karshe kada ka sake zuwa mai gida katayar mashi da hankalin iyalin shi.
Ya juyo ya kalle ta yayi dariyan takaici yace mummy da kun hana ni na yarda nabar zuwa don biyyaya a gare ku.
Amma yanzu na fahince ku bakin ku daya ne akan yar uwata muddin Safiya tana gidan shi bazan taba fasa zuwa gidan nan ba.
A wane dalili zan nisanta kaina da yar uwana saboda karuwa ko may, zanyi haka wanan karon ba zan sake dauke kafana a gidan ba indai safiya tana ciki.
Muddin ina raye ina numfashi ba zan sake bari a kuntatawa rayuwan safiya ba, danki yana danne mata hakkin ta batada matsayi da yancin a gidan shi amma duk baiyi laifi ba
Mummy kin dauki yariya karama kamar safiya kin aura ma mutun irin Ahmed, ya dauko karuwa mata karuwa a gida ya hada tada ita sun taru suna kuntata mata kice wai baki sani ba.
Duk kece sillan lalacewa rayuwan rayuwan mu haka mummy yarinya na zaman ukuba a hannun danki kice wai kada a taimaka mata, duk kece mai kawo matsala a tsakanin mu mama.
Yana gama fadi ya juya ya fita yabar gwago cikin kunan rai ta bishi da kallo har ya kule tace Saadu kao baka san uwa da soyayyan dan ta ba.
Inda zaka bincika kaga yadda nake cikin damuwa da bacin rai akan yaran nan da baka furta hakan ba inda kasan nauyin da maihaifin yarinyar nan ya danka min banda yadda na iya ne.
Baka san nauyi da rikon amana kedashiba da matukar wahala duk abin nan ina sane dasu amma son dana ya rufe mun ido.
Shiko dan waje ya koma yana jigina jikin shi ga mota yana tunane ya dinga kuna wiwi yana zuka yana wa kwakwalwan sa caji tare da neman mafita akan matsalar mu.
Ya nisa yana cewa a ranshi hakika Safiya ke yar uwata ce ta jini kuma mata ga dan uwa na zan tabbatarb kin kasance cikin farin ciki zan fuskaci duk wanda ya nemi ya kawo maki kunci a rayuwan ki.
Burin mahaifinki akan hadin auren ki shine da dan uwana yaga an hada zuria mai dorewa a tsakanin shi da yar uwar shi amma dan uwana yana son yaga rushewan wanan alakan saboda rayuwan duniyanci daya dauka.
Ya Allah ka tabbatar da farinciki da kwanciyan hankali a rayuwan ku kar zumunta ya baci a sanadin auren ku.
Iya sani na mummy bata da gidan zuwa a arewa wanda ya wuce gidan mahaifin Safiya don ko sako ne ta gareshi take turawa a sayo mata abu a aiko dashi nan.
Haka dai ya kwana yana yawan tunane barkatai da samo fita ga matsalar mu .
********* ********* *********
Fitanan sune ya farka damu daga barcin safe da muka samu mukeyi a gidan nida Sadiya.
Fada suke yi sosai shida ita hakan yasa mu fitowa da sauri dakin mu danbe suke yi a tsakanin su.
Suna ta faman fashe fashen kayan falon da suke fadawa da gani har sadiya ba mai iya raba su don sun fimu karfi.
Sun dauki lokaci suna abu guda saida sadiya takira yaya saadu yazo ya raba su ta kwashe kayan ta tana mai zagin kaskanci irin na yan duniya.
Wani magana da ta fada sai da yaya saadu ya kadu bayan tafiyanta ne sadiya ta taimaka min don mu gyara gidan mu mai da komai inda yake.
Kuka nake ban iya aiwatar da komai ba a lokacin sai gasu sun shigo gidan da shida dan uwanshi.
Sun zauna suna fuskantar juna yaya saadu yace dashi matan bariki dama haka suke su raba ka da ta kwarai su kuma daga karshe su guje maka.
Kamayi arziki bata kai ga kore maka mata ba ta tafi ya dago ya kalli dan uwan nashi ai ba tafiya tayi ba barazana ne kawai.
Yaya Saadu yace yar bariki ne zata iya dawo ma rayuwana in yau ta ga dama ko gobe sai dai ka sani.
Yarinyar na Safiya yar uwan muce jinin mu ne ita kamar yar cikin mummy take a wurin mu infact dai kasan wanan auren naku anyi shine don kara zumunci.
A ganina bai kamata ace abinda iyayye sukai maka gata akan saba shikake wullakantawa.
Na tabbatar da mahaifin yarinyar nan na kusa ko yasan halin da yarsa take ciki da tuni ya raban auren ku da ita.
Ya kamata ace Safiya ta samu kulawan ka fiya da komai a gidan ka bata isa ta hanaka barikin kaba amma kabata kullawa yadda ya dace don kauce ma shiga hakki.
Nasan da mahaifinta yasan halin da yarsa ke ciki a gidan ka da duk wanan abin bakai ga yinsa ba.
Don basu san halinka na boye ba mummy ta rufe massu kokai waye ta aura maka karamar yarinya da yaci ace yanzun tana karatu ne.
Please Ahmed ka gyara rayuwan ka duk wani abinda kasan yana kawo nakasan rayuwan ka nesance shi.
Ba abinda ya zamo ma dan adam dole a rayuwa mussamman abinda zai nesantakan da ubangijin ka yazama dole ka yakeshi a ranka.
Musamma giya da mata ba alheri bane ga rayuwan dan adam ba dole bane ba kuma inda yazama ma dole sai kayi shi.
Don Allah bros ka rabu da wanan rayuwan ka rugumi matarka ka rike yarinyan nan amana zaka ga yadda rayuwan ka zai canza duk wanda ya samu mace kamar safiya yayi saa a rayuwa shi ga tsabata ga hakkuri da biyyaya.
Ya sa hannu ya dafe kanshi kamar maganan yana shiga zuciyar shi can ya lumshe idanuwan shi yana hango kyakkyawan fuskan na da suran da Allah yaimin da natsuwa da hakkuri.
Yace kai baka ko gudun ka dauko maku cuta ka manna wa yar mutane matar nan fa baka san iya mutanen da take hurda dasu ba har wata kasa take zuwa.
Yaji zuciyar shi da jikin shi yai sanyi saboda maganan da dan uwanshi ke fadi gaskiya ne ko abokan shi sun sha fada mashi hakan.
Gaba daya jikin shi yaji yai sanyi amma kuma yasan abu mai wuyane ya iya rabuwa da lilliya ko ya rabu da kowa bai iya rabuwa da ita wasan dadi.
Ya kalli yaya Saadu yace na gode daka tunarta dani wasu abubuwan da na manta dasu a rayuwa.
Yaya saadu bai tafi ba sai da ya tabbatar da ya daidata komai a tsakanin mu yabar gidan .
Abinda bai sani ba shine na kudiri aniyar kwatar kaina daga gare su bazan kara yarda da irin cin fuskan da yake min ba agaban matan bazan shi da yake kwasowa.
Kwana biyu kamar komai ya lafa sai dai a raina nasan kwanton bauna yayi kawai na kwana biyu.
Yana kawo min abinci kai da kai kuma idan zai fita zai sallamay ni kuma idan ya dawo nakan taso daga dakina ko nabar abinda nake yi nazo na gaida shi da dawowa.
Wata rana zai fita na tambaye shi zuwa wurin maman biyu indubata kamar ba zai barni in tafi ba sai dai kuma yace kada in dade.
Na gama shiryawa na rufe gidan na kama hanyan gidan ta nayi saa ta dawo wai ashe bata garin duk wanan dadewan da tayi.
Take tambaya na ko nazo bata nan ne sai nake fada mata irin kullen da yasani da dauko Lilliya da yayi ya kawo gidan.
Da irin horon da na sha a wurin su har yaya Saadu yazo ya kwace ni a hannun su daidai lokacin da nake ganuwan shan wahalan su.
Ta nisa tare dacewa safiya wanan mijin naki bariki ta aure shi rashin sani yasa mahaifinki ya nace da ki zauna dashi hakana.
Amma wanan da kike gani tuban mazuru yai maku kawai may yuyuwa ya canza mata gidana suna haduwa baki sani ba.
Nace inma gida ya canza mata baida may ni ba don ban gani ba abinda sukeyi bisa ga yadda suka zauna min gida ana iya shege a gabana.
Nifa anty yanzu cikin nan ne kawai matsalata badon ciki ba da duk abinda baba zai mun sai dai yai min ba zan zauna ba.
Sai dai nakan tuna furucin baba sai jikina yai sanyi da yake cewa indan aurena ya mutu in tabbatar da zaman ummina ma ya kare a gidan shi.
In badon wanan ba aida tuni na gudu na koma ga iyayyena ko don maganar kine wallahi don da dan uwanshi kemai magana ya rabu da Lilliya cewa yayi.
Wai abinda yasa ba zai rabuda itama ba sun jima tare ni tun baida komai suke tare tabar maza da yawa take zaman shi shi kadai.
Wai cewa yayi har musulunta tayi saboda shi saida sukai alkawari da ita cewa bazai wullakantataba kuma ba zai taba rabuwa da ita ba shi dalilin da yake duba.
Sai dan uwan ke tamabayan shi yana ganin Lilliya ta musulunts ne matar da ko shiga irin na musulmai batayi kuma ita bata daina hurda da wasu mazan banza ba har yanzu.
Kai amma mijin nan naki wani irin soko ne wallahi indan ka gan shi a fuska kamar mutumin kwairai inji anty.
Tace yanzu shi baiji kunyan fadar wanan dalilin nashi na bazan ba shi watau baiyi tunanen harcin da iyayyen ki sukai mashi ba sai na wata matar banza can.
Nace ai haka dan uwan ya fada mai idan yana son zaman lafiya da kwanciya hakali sai ya rabu da matan bariki.
Sai cewa yai mai wai bayajin zai iya rabuwa da lilliya ko ya rabu da kowa don baida matsala da ita tana binshi shi sau da kafa tana mashi komai ko wanan akasi aka samu suka sami matsala.
Kanin yace mai aiko ya zama dole ya rabu da ita don farin cikin gidan shi nace kin san may ya cewa kanin ?
Wai mau zai sa kanin na shiga mai harkan shi wai ai lilliya ma tarsa ce don haka zai zauna da wacce ya ga dama a cikin mu ya saki wacce yake son saki ko kuma ya zauna da mu dukkan mu.
Sai cewa yayi dan uwan ya rabu dashi kar ya caja mashi kwakwalwa don yana bukatan hutu tare dashi.
Na kinga kenan bazai iya rabuwa da ita ba ni ko yana iya rabuwa da ni inya so.
Haka dai dan uwan ya lalaba shi har suka samu suka rabu lafiya dashi ya wuce in ba haka ba ranan nasan ba karamin tashin hankali za a yi ba a tsakanin su.
Tace kin ga ni yanzu so nake ki kwantar da hankalin ki ga komai ki kula da kanki sosai don ki haihu lafiya.
A hankali na daga mata kai alaman na gane ta kawo kudi masu yawa ta bani da zan koma tare da kwantar min da hankali.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , ,
🧕🏿2️⃣0️⃣🧕🏿
YAR UWAN NOVEL DIN NAN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , , , ,
Abin yai min yawa a tare da ni ga yunwa ga ciwo ga ciki sai yar dadiron gida da tazo ta kakace gidan da zama .
Ga miji dani da babu duk daya a gare shi bai san cina ba bai san sha na ba ko ciwo gashi har wanan lokacin maman biyu bata zo gidan mu ni kuma ban fita ba.
Don da zaran nafita da ya dawo fada mai take yi ya samay ni yaita jibgana sai ya ga dama ya yabar ni.
Suna zaune falo sun sayo kaji gassasu suna ci ga kayan shaye shaye nan mai sanyi agaban su wasu ansha wasu ba a taba ba.
Kayan abincin da maman biyu ta bani duk sun kare banda komai da zanyi dabara dan kitson da nakeyi ya hanani wai ana cika masa gida.
Jin motsin su a falo da dariye dariyen su yasa ni fitowa na samay shi, da farko da nai magana tankar bai jini ba.
Sai da na kara cewa yaya wurin ka fa nazo tun jiya ban ci komai ba a gidan nan sai ya dago ya dubeni wani irin yai karfin halin daga Lilliya daga jikin shi.
Ido ya zubamin na sake cewa tun jiya da safe banci komai ba a gidan nan, Lilliya ce ta sake kwanta mai a jiki tana wani iri da idanuwanta.
Yai karfin halin sake daga ta daga jikin nashi again yace baki ci abinci ba mai kike jira da baki dafa ba.
Nace wanda ka saya min ya kare sai ya juya ida take zaune yana kallonta ya zuba mata ido yana kallon ta.
Yace baby kin san ba a horo da yunwa a bari ta dinga dafa abinci tunda akwai shi kuma ke ba damuwa da dafawa kikayi ba.
Ta wani ya mutsa fuska tace abata badon halin ta ba don albarkacin wanan baby dake jikin ta.
Tsayawa nayi ina masu kallon mamaki abincin ma da zanci wai sai ya nemi yardan karuwasa idan ta yarda a bani indafa.
Ganin ban wuce ba yasa yace bakiji ba abinda tace kinci albarkacin cikin jikin ki tace eh don kuwa babyn dear na ne kinga kuwa bazamu barshi da yunwa ba.
Kije mana ya daka min tsawa yana harara na wai na wuce mana tunda an bani na kalle shi nace haba yaya kaji tsaro Allah.
Yanzu cikin daren nan karfe goma ya wuce wani abinci kake son na dafa inci a wannan lokacin.
Ya zuba min ido yana kallona da idanuwan shi da sukai ja amma ya kasa fadin koma sai bina da kallo da yake yi.
Sai a lokacin Lilliya da ke jin mu ta dago jajayen idanuwanta da suka rine tace wannan abinda muke ci kike so komay
Kasan mai ciki da gwada zai yiyu kamshin shi taji tafito daga dakin ta, idan har shi ko kika biyu wallahi kwalelen ki idai wannan ne.
Kofan da aka turo ne yasani juyawa bani ba harsu din suna diban kofan don suga mai shigowa lokacin.
Bakowa bane illa yaya saadu ya shigo gidan fuskan shi a daure da alaman har yanzu yana cikin zafi da maigidan.
Tunda yai sallama ya shigo gidan jikin shi ya bashi cewa akwai wani tsiyan da aka shukawa a gidan.
A hankali murya a sanyaye na gaida shi da zuwa sabanin yadda na saba gaida shi abaya idan ya zo.
Tambaya na yake a gagauce yana yi yana kallon inda suke zaune a ciken hasala maynene matsalan safiya may sukai maki nace , ?
Ganin shi yasa kuka da banyi niyar yiba yazo min a lokaci guda .
Durkusawa nayi a gaban su ina tsananin kuka kamar na fita yacina Yaya Ahmed ya daga zaune ya zuba min idonsa da suke jawur , ya kasa fadin komai, .
Kumshin naman kazan daya rage guda daya basu taba ledan shi ba shi ya dauka ya miko min yana fadin.
Indai wanan ne kikewa kuka don ba a baki ba gashin nan kije kicke baby bari zan saya maki wani kafin mu kwanta.
Ban karba ba kuka kawai nake yi ya sake cewa karbi mana kibani wuri da kukan nan naki hakanan.
Yaya Saadune yace safiya in nama kikewa ki karba gashinan ya baki sai na dan tsagaita kukan da nake yi nace yaya tun jiya ban ci komai ba a gidan nan .
Na fada mashi yace wai wanan ta bani indafa yanzu yaya yaushe zan dafa har inci da daren nan .
Na juya ina fuskatan shi nace yaya ina cikin wani babban matsala da tashin hankali da ban taba tunane ko tsanmanin zan shige shi ba.
Yaya Saadu ka mai dani gida inyakani baba zai yi kan naki zama gidan dan yar uwanshi sai dai ya yankani a kan hakan ko dabba aka daure a gida ana bata abinci taci balle mutum.
Yaya saadu kai kadai nake jin saukim rayuwa a wurin ka sai kuma maman biyu da tai min tsaye, .
Ita ma bakin ciki da takaici ya sa ta dauke kafanta da zuwa dubana bani da kowa dake zuwa dibani sai kai da kazo yau din nan.
Ya tausaya min sosai yace kinyi hakkuri safiya tun jiya na dawo motana ne keda matsala sai na tsaya gyara da na dowa nike tambayan mummy ke sai take fada min wai kina nan da ciki kuma kuna samun matsala.
Ya juya wurin dan uwanshi yana cewa yanzu kai rayuwar daka zabawa kanka ke ga ka dauko karuwa har cikin gidan kana sunna kana fifita ta sama ga matar ka.
Yaushe zaka girma kasan ana mutuwa ayi hissabi wai har ace kace matar ka ta zubar da cikin da kuka samu wai har ka tsaya kana mata wullakanci akan hakan.
Wanan matar banzan daka dauko ka kawo mata gida fa a matsayin may take ita in ma har zakuyi abin ku , ku tsaya can kuyi inda bata ji balle ta gani.
Yanzu bakajin nauyi da kunya kana ciyar da matar banza abinda kake so ka kasa ciyar da matarka ta sunna ga ciki ga bakin cikin ka da yunwa yaya kake son tayi.
Tsawa ya daka mai yace ya isheka Saadu ya isa haka gidan ka ko gidana ka sani matar da kake kira da matar banza matatace.
Mata mata fakace yai masu wani kallo yana tafa hannun shi yace dakyau wanan ce matar kake nufi ko may .
Tun wuri idon ka ya bude akan wanan ya nuna Lilliya yace wan yan kaddangarun bariki masu ma mutum shigo shigo ba zurfi.
Yanzu ka dubi wanan yarinya wata take dashi garin nan bayan mu bata da kowa Allah ne gatan ta kaine gatan ta amma ga ciki jikin ta kuma ga horo da yunwa.
Nice na katse su nace yaya bansan yaya zanyi da matsala ta ba ya zama wajibi na zubar da cikin nan dake jiki na.
Gaba daya suka dubo ni nace shine kwanciyan hakalina a yanzu ina ni kadai ban san yaya zanyi da kaina ba ina ga mun zama mu biyu nan gaba.
Na san idan na zubar ina da daman yin wasu abubuwa , ban kai ga fadin abinda zan fada ma sai naji yaya Ahmed yace duk kika taba cikin nan a yanzu bakin auren ki.
Nai mai wani irin kallo na juya ina fuskantar shi nace tsaron mutuwar aure na shine zai hana ni fitarwa ba, indai zubarwa zai kawo min kwaciyan hankali..
Matsala ta guda shine baba don nasan bazai barni in zauna mai gida ba don ya rantse kan haka.
Tausayina ya kama shi baisan lokacin da idanuwan shi suka kawo hawaye ba ya kalli wan nashi da yake hassale shima yana sauraren mu .
Wani kallon yake min ga alaman yunwa a tare dani da rashin kwaciyan hankali, kai bashi ba ma duk wanda ya ganni sai ya tausaya min saboda nayi kankanta da shiga irin rayuwan nan.
Shi kanshi lokaci na farko da yadan tausaya min kenan a gidan don wanan shine lokaci na farko a rayuwan shi da yaji ya tausaya min ya sake kallona ina cikin kun ci da tashin hankali.
Shiko yaya Saadu wani irin radadi da bacin rai ya dinga ji a zuciyar ji yake kamar ya samay su yai ta dukan su a lokacin.
Do yana tausaya min ya son abani kulawa yadda ya dace amma wan nashi yaki ya saurare shi.
Ganina da tayi cikin wanan halin kuncin fa ciwo ga yunwa da bakin ciki ya fi komai bata mashi rai.
Ya kasa jure gani na cikin wanan halin ya fita waje ya barmu a yadda ya samay mu shiko gogan harara ya watsa min yace.
Ban san abinda yasa kike son hadani da dan uwa na ba a dalilin ki bamu shiri yanzu da shi.
Sai liliya tace munafunci mana munafuka wai harda cewa zata zubar da cikin jikin ta da da akace ki zubar uban wa ya hanaki zubarwa.
Ke kilaki rufe ma mutane baki don ba a kasa dake ba a zancen nan kibar masu magana suyi.
Nan cacan baki ya kaure tsakanin mu don bazan in mata bane ko banza tafini karfi ga tsayi ga komai turwa kawai nakeyi ina maida mata martani ganin shi zaune.
Shiko gogan taba ya jawo ya dinga kunnawa yana zukewa yana fesar da hayaki sama kwakwalwan shi ta dinga caji yana neman mafita.
Yaya Saadune ya dawo ya samay mu a haka da kayan abinci niki niki ya jani zuwa dakina ya bani magana da kalamai masu kwatar da hankali.
Yace safiya na fahinci matsalar ku muddin bai daina hurda da matan bariki ba zaku samu zaman lafiya ba.
Nai maki alkawri zan kula dake da abincikin cikin ki har ki haihu bazan taba batin ki kwana da yunwa ko kishin ruwa ba.
Safiya ban san abin ya kai maku haka dashi ba har yana horon ki da yunwa ga kuma karuwa ya dauko maki a gida.
Nan dai ya sani gaba har saida yaga na ci abincin da ya sayo min din saidai na kasa cin abin kwarai a lokacin don ciki na ya kulle sosai.
Ya rasa abinda zai yi ya fice ya daho ruwan zafi tea ya hada min mai zafi shina samu na dan sha a lokacin sai kuma na fara shega amai.
Yana ta faman yi min sannu waya ya dauka ya kira habiba da safiya suzo su kwana dani .
Shedaniyar ko bata san yana kulle da ita ba jira yake yaga hankalina ya kwanta ya koma kansu.
Sai cewa tayi amma wanan abin da kake mata baiyi ba wallahi kune ke kara shagwabata takeyin abinda taga dama.
Sadiya kawai tazo habiba tace wai kanta ke ciwo itama ta tausaya ma halin da nake ciki sosai tace bakida lafiya har haka amma bamu sani ba kuma gashi yaya suna zuwa gidan mu shida lilliya.
Suna nan zaune inda suke yaya saadu ya fito yabar ni da sadiya ta taimaka min ya dawo wurinsu falo.
Lilliya tasa halin shi sosai bai daukan raini tun farko ya tsane ta sosai don baison taraiyan ta da dan uwanshi .
Ahmed har yaushe zaka zauna macen banza tana dinga juya ka a gidan ka tana yiwa mutane iko haka, na tausaya wa rayuwanka da ka kare a gidin wanan matar da duniya ta gama yayinta.
Tasan halin sa sarai tana son magana tana gudun jibga yace idan matar nan bata bar gidan nan ba sai na sa andaure min ita a garin nan.
Fada yake yana zare idanu halinshi ba dama dai tai magana tasha na jiki a gurin shi da daren nan mikewa tayi ta shige daki.
Nan ya zauna yana suna magana nasiha nasiha fada fada dashi karshe dai yace wai yayi kuskure zai gyara .
Amma zancen Lilliya tabar gida bai taso ba shi kanshi ba fa dadin ta yake ji ba don ta gama isarsa dan kwanakin da sukayi tare amma kamar jaraba bai iya rabuwa da ita.
Shi kuma yaua ya kafe akan lalai sai tabar gidan tunda ba auren kwarai sukayi da ita ba.
Lalai kuwa Safiya ba zata zauna da wanan yar duniya a gidan nan ba kaji na fada maka tun wuri kasan abinyi.
Yasan yaya saadu ya fishi zama dan duniya sai ya dafe kai ya rasa abinyi do maganan shi ta girgiza shi ainun .
Muna daki muna jin badakalar da suke kwasa tsakanin su jikina yai sanyi don kirikiri ya fifita da ni yadda yake maganan aibanci gamay dani.
Jiki na yai sanyi sosai tsananin tausayin kaina ya kama ni na tuna yadda nake cikin yan uwana yau gashi an kawo ni dani da tutu duk daya.
Hawaye ne ya wanke min fuska itama sadiya dake jin fadan da sukeyi kuka takeyi karshe dai shigewa yayi yabar kanin nashi a falon yana fada.
Dakin ya shigo wurin mu ya kalle ni tausayina ya kama shi yasan duk mahaifiyar suce ta jefa ni wanan halin .
Don tasan halin data sarai amma ta nace sai yayi aure a zurian ta wai ko zai daina abinda yake yi wanan yarinyar haka ina zata iya shirya wanda ya haura talantin da wani abu can.
Yace Safiya ni zan tafi dare yayi nai maki alkawrin da sannu zan dinga warware ko wace irin matsala a rayuwan ku muddin ina raye.
Ko ina gari ko bana nan tankar kauna na da muka fito ciki guda nake jin ki mijin ki yayi nisa sosai da bariki sai addua lamarin sa.
Yai muna sai da safe yana ma sadiya tuni da ta tabbatar da naci abinci da safe na sha magani na.
Bayan tafiyan shi munajin suna hayaniya a dakin su nan sadiya ke kara fada min ko wacece lilliya da halayen yayan nasu da abin da yasa uwarsu ta auro mashi ni din.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , ,
🧕🏿2️⃣2️⃣🧕🏿
YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN SU PLEASE, , , , ,
A can gida sani Allah sani annabi aka samu ummi ta dawo dakin ta amma har ta dawo tana nan akan bakan ta na bata zama gidan da bata da yancin kanta balle diya.
Inda ba a san darajan mace ba da yara ake masu mulkin kama karya a gidan baka da wani tacewa sai yadda akayi dakai.
Yan uwanta kuma suka mara mata baya sai da baba ya koma yana karamin murya da sani Allah sani Annabi mahaifinta ya kara tursasamata ta dawo gidan.
Sai dai dawowan a tsatsaye ta dawo masu gidan bata shayin kowa da anmata abu yanzu ne zata maida martani akai.
Hakan ya dan saman mata sauki a gidan gashi tun bayan ni da nai aure ba wanda ta kara aure a gidan mu nima din danayi sunan nayi ne kawai.
Yanzun dai suke fitar da mazajen auren don haka kowa shirin aurar da yar shi yake yi a gidan in ka debe ummi na daga cikin wacce ke kumsan bakin cikin yarta.
********* ********* *********
Zaune nake a kasa saman dan center carpet din falon abinci a gaba na sai kira,an dana kunna ina saurare ina bi a hankali.
Nayi wani irin fari duk wanda ya ganni sai yai maganan farin dana kara cikin jikina ya turo sosai don ya girma yanzu.
Banji shigowan shi falon ba sai ganin shi nayi a tsakiyan falon yana ce min wanan wani irin abune kin ruda gida haka da karan karatu idan bi kike baki rage karan yadda zaki ji mai shigowa gidan.
Ban kula shi ba sai dai ina mamaki a raina shida yake sake kida ya kure karan kamar gidan zai tashi don kara baac mai komai ba sai ni yau da na saka kira,a gidan yake fada
Ban saure shi ba ya dauki remote ya rage karan ya juya ya shige dakin shi kai tsaye.
Kiran sallah magariba akayi don haka na mike zuwa daki na don yin sallah har na idar banji motsin shi ya fito daga dakin ba.
Don haka na mike na leka dakin kwance yake yana sharar barci ko kaya bai cire ba yadda ya saba yi indan yadawo gidan.
Muryana ya dinga ji a tsakiyar barcin shi ina tada ya tashi yau sallah bai saurare ni ba ya gyara kwanciya yaci gaba da barcin shi.
Saida yaga dama ya tashi don kanshi yai abinda zai yi ya dan fita nasan giyan shi ya je ya dirka sai dai bai bugu ba ya dawo da ledodi da yasayo abin breakfast din mu.
Na kashe wutan daki na kwanta ina jin motsin shi a falon barci ya daukeni motsin shi da naji a dakina ne ya tayar dani daga barcin da na fara yi.
Yace na kasa barcine shiyasa nazo taya ki hira namiji baida ta ido ko kadan nida yace ban iya komai ba yake fadawa wanan maganan haka.
Nidai na matsa mai ya hawo ya kwanta daf dani naji ya fara shafana a hankali.
Idona na lumshe ina maijin tsanar shi a raina don ban iya mantawa da cin fuskan da sukai min gidan shida lilliya.
Ya juyo gareni yana cewa may ye azuciyar ki may yake yawo a kwakwalwar ki gamay dani.
Nace kai dan uwa na ne na jini kuma mijin da mahaifina ya zaba min dole komai yai zafi ina tare da kai duk rintsi komai wuya komai dadi ina tare da kai a gidan nan amatsayin matar ka kar kayi tunanen daukan fansa a gare ni don kai dan uwana ne kuma mijina.
Wani iri yaji har acikin zuciyar shi don yasan ya cuta min ta ko ina harda ma inda ban sani ba sai dai kawai ayi hakkuri da juna.
Nisawa yayi tare da gyara kwanciyar shi yace to ki daiyi hakkuri da komai.
Nace hakkuri kan na yi amma yaya bazan sake irin hakkurin da nayi a baya ba amma zama kan yamin dole a gidan ka.
Shiru yayi ya kasa barci yana ta juye juye ya tsinci kansa a wani yaniyi tabbas ya san ya zulunce ni tako ina duk kokarin da nakeyi baisan may yasa ba ya gani ba.
Yarinya ba inda ta gaza dashi tsabta da girki da kula da kayan gida da kokartawa da bashi hakkin shi duk ta yanda yazo mata amma shi ya kasa daina barikin shi a zauna lafiya.
Ga saadu kanin shine na baya amma har ya fishi hangen nesa ya hanngo mai abinda bai taba tunanen hangowa ba a rayuwan shi.
Ya tashi ya yai zaune yana maici gaba da tunanen abubuwan rayuwa a ran shi.
Har barci ya fara dauka na naji matsin shi yai yawa na haska hasken tocina don in ga may yake yi a lokaci tare da cewa ba kayi barci bane ?
Yace yau na kasa barci ne ban san abinda ke damuna ba haka nace Allah ya kyauta ko may nene amma da zaka koma dakin ka ka barni zaifi min in samu barci.
Ban dauki lokaci barci mai nauyi ya dauke ni ya lumshe idon shi yana mai kare min kallo na dunkule a wuri daya ina barcina hankali kwance.
Sai wuraren asuba ya samu barci ya dauke shi bai wani dade kwarai yana barcin ba ya dinga jin murya na ina tadashi yai sallah.
Bai saure ni ba sai barcin shi yake yi nan na barshi a kwance na wuce nai wanka tare da dauro alwala har na fito bai falka ba.
Nata da sallah na harna idar sai nasari yake kwasa a cikin barci duk ya wani rudamin daki dashi.
Na idar ina addua na sake ta dashi da yaga kamar damun shi nakeyi sai ya dauki filo ya danne kanshi dashi.
Har na gama anbinda nakeyi yana nan a kwace min dirin a daki yana barci matsa mai nayi sai ya tashi.
Nan ya mike a harzuke ya hauni da masifa meye damuwan ki da rashin tashina kibarni lokacin da duk na tashi zan iya yin sallah na.
Ban samu barci da wuriba jiya da kyat na samu barcin ya dauke ni yanzu kuma kinzo zaki matsamin ki kyale ni nai barci na karki sake tasheni.
Nan nima nace a harzuke zan tashe ka dole in tashe ka ko sau nawa zaka koma barci muddin bakayi sallah ba sai na ta dakai.
Haka kawai ana sallah kana kwance kana barci katashi in kayi sallah sai ka koma ka kwanta yafi, magana da nakeyi na damay shi.
Ya mike a hasale zai koma dakin shi ya kwanta yana fama dani na daure nace yanzu kai bakajin, kunya ko tsaron Allah kaine fa yakamata ace ka data dani nayi sallah amatsayi na kaunan ka ko matan ka.
Amma ana sallah asuba kai kullun kana kwance kana barci a daidai lokacin da Allah yake sauke rahamarsa ga bayin sa.
Yana kuma yi ma bayin sa gaffara yana raba alheri ga masu rabon samu ya sa imani azuciyar masu imani, amma kai sai dai ka kwanta kawai kana barci ko yaushe.
Bai kula ni ba ya shige dakin shi ya kyaleni ina wa,azina koda ya shiga ya koma barcin shi bai damu da surutun da nai mashi ba.
Sai wajajen takwas saura ya falka yai wanka tare da yin sallah ya fito da shirin zuwa aiki a falo ya samay ni zaune.
Ina ganinya fito na mike zuwa hado mai abin karyawan shi dama na gama yana aje.
Na tsugun na gaban shi na aje tare da mashi ina kwana ya amsa min adakile, ban daga ba daga wurin ba nace dashi.
Yaya don Allah ka daure da yin ibada bai kamata ba magidanci da kai kana wasa da addinin ka, may yasa kuna diyan musulmai kuke sakaci da ibada.
Hannu ya daga min ya dakatar dani daga maganan da nakeyi yayi da hannuwa don haka naja bakina nai shiru tare da komawa gefe na zauna.
Yagama ya fice abinshi lokacin naji gidan kamar an debe min kaya da nauyi akaina na mike na shiga gyaran gida dakyat na samu na gama .
********* ********* *********
Kwana biyu banda matsalan komai da shi a gidan sai dai ba sakin fuska akaina wanan bai damay ni ba indai hat zaibar zuciya ta ta samu saida.
Ranan na samay shi zancen zuwa asibiti a duba ni don ina fama da ciwon mara idan dare yayi bana barci da dadi.
Ya kawo kudin zuwa ya bani yace na shirya ya sauke ni indan zai fita nako shirya da wuri na zauna jiran shi.
Sai da ya gama abinda yake yi ya fito muka kama hanya a can wani unguwa ya kaini wani asibiti mai kyau na kudi .
Yace idan zan dawo ga yadda zanyi ga yadda zanyi nace na gane na yanki kati nabi sahun masu ganin likita a wurin.
Can layi ya kawo kaina aka ce nai fitsari aka kuma debi jina na dan aunawa an gama na koma na zauna sai da layi ya sake kawo kaina na shiga.
Ba matsalan komai ba likita yai min yan tambayoyi irin na likita karshe sai ya rubuta min magani sai kuma yadan dubeni yace dani idan ba damuwa yana son nazo da mijina yana son ganin shi gobe.
Banji komai a raina ba nace zan fada mai ya bani wani dan note yace dashi zai zo idan zaizo din na karba nai mashi godiya na fice.
Na dawo gida a gajiye na samu bai dawo ba na kwanta na dan huta don na sayo abinda zanci a hanya da zan dawo.
Ban tashi ba sai wajajen karfe uku na tashi a gagauce nai sallah najira akai la,asar na hada nayi sai na mike na dora girki dare.
Har na gama bai dawo ba lokacin da ya saba dawowa kafin magariba na shige sallah na gama ina sauraren dawowan shi, naji shiru nan na fara tunanen ko ina ya tsaya.
Shiru bai shigo ba har nagaji na kashe kayan kallo na kwanta sai wuraren sha dayan dare naji ya shigo gidan a cikin maye.
Inna lillilahi nayi a raina ina jinshi yana ta hauragiyan shi shi kadai a falon na tashi na kargamay kofan dakina don ma kada ya shigo min dakina.
Haka na kwana ga ciwo ga bacin rai nasan mairaba shi da wanan halin sai Allah duk wani wa a zi da sauransu bai shigan shi don yayi nisa.
Gari ya waye ban fito da wuri ba sai wuraren takwas na fito ina yan aikace aikace na duk da nayi nauyi ban iya dukawa sosai yanzu.
Ya fito yana wani murzan idanu kamar wanda barci bai isheshi ba, ashe shi din ne kuwa don ya na cikin sauran maye har yanzu, .
Dan juyowa nayi na kalleshi na mayar dakaina naci gaba da abinda nakeyi nace mai ina kwana a takaice ba tare da na fuskace shi ba.
Shima yai mamakin a yadda na gaida shi don ba haka nake gaida shiba din yadai amsa min ne kawai don yasan wai fushi nakeyi ke nan.
Ya zauna yana tambaya na abin karyanwanshi na ba shi amsa dacewa dashi ban yi ba har zai yi magana sai kuma ya tuna bai sayowa ba daren jiya da zai dawo gida don a buge yake lokacin kuma masu kaya sun kwashe.
Zama ya dan yi na wani lokaci yai shiru sai can ya furzo iska daga bakin shi yana mikewa yake tambayana jiya kin samu ganin likitan ?
A takaice nace mai eh nagan shi yama bani takarda wai yana son ganin ka asibitin sai ya dago da sauri yana kallona yace.
May zanmai ba ya dubaki ba shine kuma zai ce sai na je ya ganni ni ban iya lalurar su na likitoci don Allah.
Nace to kasani ko wani abin ne yake neman ka din kamaf tai magana sai kuma ya fasa ya karbi takardan dake hannuna yana cewa idan na fita zan biya nagan shi.
Tun wanan lokacin bai kara min magana ba nice ma dana tambaye shi yake cewa yaje yace ya dinga sai min kayan karin jini ne.
Da alama yanzu ya koma ruwa sosai don sai dare yake dawowa indan kuma bai zuwa aiki ya zauna min falo yaita bakin rai a falo yana jin fada.
Zai sha abinda yaga dama a wurin da nai magana yanzu zaiyi cikina da cin mutunci da tonan asiri sai ya gaji ya kyale don kan sa.
Wata rana na tafi gaida mahaifiyar shi gwago na mun gaisa dadi dadi da ita sai kowa yai shiru zuwa can tace dani yanzu komai yai daidai tsakanin ku ko an daina jin korafin ki.
Nai mamaki dajin wanan magana nata datai min nace da ita dama ai ba korafi bane fahinta ne akan addini don akwai karancin illimin addini a kan shi.
Nan ta haye tace wai ita nake fadawa magana akan dan ta nihar yaushe aka haife ni da zan ce zan koya masu addini.
Nidai nai shiru ina sauraren ta har ta gama dama da wuya nazo gidan bamu samu matsala akan dan ta ba bata kaunar a fadi magana gamay dashi ko kadan .
Ban dade ba nai sallama dasu na juyo zuwa gida da kafa na tako nan na hadu da wata yar unguwar mu a hanya muka jera da ita muna tafe muna zuba bayeraba na amma kano aka haife ta ta iya hausa sosao don haka in taga bahaushe take matukar jin dadi a ranta.
Tafe muke muna hira tana tambaya na yaji da kuka take so nake cewa da ita ina dashi ai tazo zan bata taji dadi tana ta min godiya.
Tun daga nesa na hango motar shi nasan cewa yana gida sai dai nayi mamakin may yake yi a gida wanan lokacin haka mun dan tsaya da wata makwabciyar mu suna magana da Mujida har take ce min yanzu na yi nauyi nabar kitso ko ?
Nai dariya nake cewa da ita na daina ma don maigidan ne ya hana nai mai kitso a gida .
Ta rike baki tana mamakin halin maza tace shi bai ganin baiwa ne daga Allah na hanyan samu yai maki zai hanaki samu nan dai muka wasan ce muka wuce ita kuma ta kama gaban ta.
Mun zo kofan gidan na tura kofan yana bude sai nace ta jira ni a kofa na dauko mata don kada na shiga da ita kuma ya zama min fitina wurin shi .
Sai ta tsaya a waje tana jirana tana ce min karfa ki shiga mai gida ya rike ki ki manta dani a waje.
Kunsan yare idan yana jin hausa iya yin gare su shi sai ya nuna yafi bahaushen iya hausan ma ga kuma mutane suna kallon mu tana jin dadi.
Nidai na wuce ta ina dariyan abinda naji ta fada zuciyana cike da mamakin abinda ya dawo yi gida da ranan nan haka.
Don dama da sunan zan wuni gida gwago na tafi sai yamma zan dawo ta ban samu fuskaba do haka nai shawara indawo gida kawai in nemi abinda naci don har na fara jin yunwa ko.
ZAINABU IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , ,
🧕🏿2️⃣4️⃣🧕🏿
YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , , , , , , ,
Mun isa garin mu garin mu an shiga sallah magariba kafan mutane ya dauke sosai mota ya tsaya dani kofan gidan gwagon ummi na.
A nan aka sauke min kayana kaf sai faman tabayana takeyi lafiya kuwa nakai ma driver ruwa nan dai na fada mata tsaye muka wuce gidan mu.
Nan aka karasa sauke min kayana nai sallama da drever na shiga gida tunda yaran gidan suka kyala ido suka ganni suka ce ga Safiya nan da nan na cikin daki suka firfito waje suna min sannu da zuwa.
Dakin Ummina na nufa yayin da aka shigo min da kayan da nazo dashi ciki yar jakar kayana da tsaraban da nazo masu dashi.
Ni bani sanin cewa na sake masu amma su suna ganin wai na zama wata yar birni dani take inna wani kishi ya tarsu a zuciyar ta na yadda na canza.
Lafiya kalau suka tare ni sabanin ummina da ta shiga zargin zuwana gani da juna biyu a jikina kuma.
Mama tazao muka gaisa take tambaya na kowa nace duk suna lafiya take cewa ashe da sai dai muji haihuwan ki kawai don bamu ma san kina da ciki ba.
Murmushi nai mata kawai muka gaisa ta fita daga dakin ta koma ta aiko min da abinci daga wurin mama din.
Ban iya cin komai ba sai kunu da na nema don ummina bata rasa kunu a dakin ta.
Baba ya shigo gida daga masallaci yara suka tare shi da cewa safiya tazo baba cikin mamaki yake tambaya da cewa Safiya ?
Ya nufi daki Ummi yana tambayana nazo lafiya nace Alhamdullahi sai da ya tambayi kowa har Ahmed din da kan nesa.
Sai kuma ya dakatar yana tabmbaya na da lafiya dai na ganki ke kadai ina mijin naki yake ne?
Ban ji tsoro shi ba nace dashi yana gida baba ni kadai nazo, kamar zaiyi magana sai ya juya ya fice dakin na mu.
Yan gidan mu suna baibaiye dani har wani lokaci sannan suka dauke kafan su.
Nasan ba komai yasa sukai min haka sai tsaraban da nazo masu dashi wancan zuwa da ni tare da yaya sani.
Har lokacin da suka barni dakin ummina na min kallon zargi sai dai batai min magana ba sai da na dan kimtsa na samu wuri na kwanta don a gajiye nake sosai.
Ban falka ba sai cikin dare na falka da tunane a raina barkatai na yadda zamu kwashe da mahaifina gashi daga zuwa ba abinda ya fara tambayana sai Ahmed din da mahaifiyar shi.
Na dade a haka ina tunane sai zuwa asuba wani barcin ya dauke ni kuma har na makara da sallah sai da ummi na ta ta tadani.
Nayi sallah na fito na gaida iyayyena na koma daki don baba bai shigowa gida sai hantsi ya fito yake dawowa daga masallaci.
Ummi na samu tayi zaune tana tunane ita kadai a dakin na samu wuri na zauna sai tace min yar nan lafiya kika zo gida a haka yadda kike nan ?
Kuma ba a samu wani ya biyo ki ba kika biyo hanya ke kadai haka gari ba kusa ba ?
Kafinta gama maganan ta hawaye ne ya cika min ido na cikin kuka nace mata ummi saki na yayi yau kwana hudu kenan yace na bar mashi gidan shi .
Salati ta saka tare da dafe gaban ta tace yasake ki ka ce fa za tai magana sai kuma naga ta mike kawai ta fita dakin.
Na bita da kallon tausayi har ta bace min ashe dakin mama ta tafi ta kirata sai gasu sun dawo dakin cikin rudewa.
Mama a rude take tambayana Safiya may ke faruwa ne wai ni dama tun jiya da kika zo nake zargin wani abu.
Ban boye masu komai ba duk yadda mukayi na kwashe na fada masu da abinda gwagona tai min duk ban boye masu ba.
Salati mama ta saka itako ummi na sai kuka takeyi ba tsagai tawa mama ne ta samu bakin cewa amma in haka Asiya tai muna taci amanan zumunci wallahi sai Allah ya saka maki.
Inna da yarta ta fadawa taji ummi na kuka kuma mama na dakin mu ta kasa gidin zama taje ta dawo a tsakar gida don taji may akeyi.
Mama ne ta kirata sai ko gata tazo nan suke fada mata abinda ya faru dani ummi dai bats samu bakin magana ba sai inna ne tace adai binkita aji gaskiyan maganan.
Tunda naji ta fadi haka nasan zata iya zuga baba a kan maganan don ta wuce nan kadan ne daga cikin sherin ta.
Shigowan baba gidan yasa suka fito daga dakin mu dakin Inna yake ta bishi dakin ko may ta fada mashi sai gashi ya fito yana cewa ina Safiyan take.
Nan ya fado dakin mu ya samay mu da ummi na a dakin yace ki fada min gaskiya may ke faruwa dake ?
Yadda na fada masu mama haka na mayar mashi da maganan tiryan tiryan yana saurare na har na gama fada mashi komai.
Yace cikin tsawa ke safiya badai gidan nan ba ai na fada maki tun farko kada ki dawo min gida.
Sai lokacin ummi tai magana tace idan bata dawo ba duniya kake son ta shiga ya koreta akan karuwa tabar mai gida ina yake son ta tafi garin mutane kai bakai tunanen haka ba baka gode ma Allah da ya kawo muna ita gida lafiya ba.
Ke Rabi kifita a idona tun muna sheda juna nida ke ke tsaya kiji bazaki zauna min a gida ba muddin kika kashe auren nan kiji na fada maki.
Ya tashi ya fita yana fada yaya sani ne yashigo gidan yace yaji ance nazo jiya da dare sai kuma ya samu labarin abinda ke faruwa.
Nan yace ai dama nasan haka zai faru ko ta koma da idona fa na samu ya dauko karuwa a gidan kuma yaiwa safiya dan banzan duka.
Amma baba ya hana aiyi magana to ai ga irints nan yanzu cikin kuka nace yaya Sani wanan ba wacce ka sani bane nan na shiga basu labarin abinda suke mun yaya sani yace kai ina wallahi bai yuyuwa gaskiya.
Dole baba ya canza maganan shi na komawa n ki gidan nan sai dai in yasa yaci kudin sune yake kamay kamay.
Daganan Inna ta kirashi dakin da yazo, to to ita kuma Inna zata fara abinta kenan baije ba saida ta sake daga murya ta kirashi ya tafi.
Fada tai mai sosai akan ya canza hali yafita batuna da uwana don ba ysn goyo muke ba yace ni Inna baruwa na da harkanku na kishi, ni kaunata nake tausayawa.
Fita yayi ya tara kan yan uwan baba suka hada mai mitin din kashi akan ya fada masu gaskiya in ya karbe kudi wurin gwagona ne yasa bai iya raba aure na da Ahmed.
Nan baba ya kara yin fushi ranshi ya baci sosai ya kumbura sosai yahau yace diyar su ko diyar shi da zasu tsure shi akaina.
Yamike yana fadin yau yau din nan zan bar shi gidan shi in koma gidan mijina ko mu bashi gidan shi nida uwata.
Allah ya taimake ni yazo gida sai ga su yaya sani sun shigo yace infito da kaya na inbar mashi gidan shi in kuma ban komawa gidan mijina mu fita mai gida dani da ummi.
Fitina ya tashi si yaya sani suka ce mu zauna kada muje ko ina ya shigo har dakin mu zai doke ni mama da ummi suka taso mai sukace idan ka dake ta da tsoho ciki haka wani abu ya samay ta sai an daure ka a garin nan.
Sai jikin shi yai sanyi ya dauki kayana dake gefe yafita dasu waje gidan ya watsar yaya Nura ya kwaso ya dawo dashi ciki yace haba baba wai kodai Safiya ba diya cikin ka bane ?
Yaringa fa tun tasowan ta bata da gata a cikin gidan nan kamar kowa kun tsane ta ita da uwar ta may yasa baba kake mata haka kai kayi su İnna suyi ?
Sai jikin shi yai sanyi yabi yaranda da kallon mamaki Yaya Sani ya karasa kwaso min kayan ya shigo dasu gida.
Ya rasa abinda zai yi ya fice yana fadin sai sun bar min gida yau ita da uwar ta kowa yai mata tsaye a garin nan.
Nan ne gidan ubanta basu zuwa ko ina inji yaya sani haka kawai ka bayar da yarinya ana mata wullakancin da aka ga dama amma kamar bakai ka haifeta ba.
Sai ga yan uwan shi sun shigo maza da mata nan suka taru sukai mai tas a kan mu suka ce sai sunyi karan shi ga hukuma idan ya kore mu ni da ummi gidan nan ai ba kaina aka fara aure ya mutu ba.
Nan ya fice gidab yana banbami kowa na mai tirda halin shi itako ummi ta hada kaya wai zata bargidan aka taru har gwagon ta da ta shigo akace ina zata tabar yar ta da tsohon ciki haka ?
İna waje tsugune a ina kuka mama ta fito tace a hasale tashi ki shiga ciki kin zauna waje kina kuka ba inda zaki tafi.
İnna sai wani kallon banza take min ita da diyan ta don ba haka suka so ba sun so baba ya kora mu ne yadda yai niya.
Muna sauraren dawo wan baba muji may zaice sai muka ga ya dawo bai ce komai ba ashe maigari ya samu labari ne yai mashi tas gwagon ummina ta kai karan shi wurin shi.
Sai dai bana fitowa waje in kuma gari ya waye na gaida shi da kwana baya amsa min sai ya kawar da kanshi yaki kulani wanan abin ya matukar tayar min da hankali a gida.
İnna ta shiga sake maganganu a gidan wai sai bakin ciki na ya kashe masu miji inda basuyi hankali ba.
Sai yarta ta karbe da cewa wallahi sai dai ta kashe uwarta ba mahaifin mu ba ita da ta hana ta zaman aure, ai da har wani jin kai ake muna an auri dan birni za a tafi birni.
Ban saurare su ba don ina sharan kofan mune mama ce tace sai ko makiyin Allah bai fadin haka ga Rabi.
Don kowa yasan yadda ta nuna kin ta ga auren nan abu dai ne in an fi karfin ka baka da yadda zakayi sai hakkuri amma zancen ta wa mutane hawan kai karya ne.
Nan dai fada ya kaure a tsakanin su koma sai da suka dauki lokaci suna yi suka dakatar don kan su.
********* ********* *********
Tunda hakan ya faru na samu dan sa ida a gidan sai dai ba wani dadi ga zaman gidan yayana nan a yadda yake baya komai ya lafa ne na kwaso kaya dake gidan gwagon ummi.
Wanda maman biyu ta hada min kan kudi na taimin kari ta saro min kaya dasu wai na juya kar nai zaman banza haka na.
Sai lokacin su inna yan sin banza suka dan sake min fuska don ana son banza nadai basu wanda na yo tsara a kyauta sauran kuma na shiga lodawa kanne na suna fita min da su.
Kafin wani lokaci mutuwan aure na ya ba gari mu kowa ya sani ana tir da halun baba kowa sai cewa yake yaci kudin su ne in ba kudin su yaci ba may ya kawo haka gare shi.
Ana dukan yar ka a wullakanta ta har tazo ma gidan da rauni kace wai sai ta koma gidan mijin nan da zama.
Wurin yanne na maza nake samun gata sosai don zasu sayo min abin kwalama da yan abubuwa idan sun fita.
İtako ummi har lokacin ba dadi tsakanin ta da baba zaman dai akeyi amma kullun sai masifa a tsakanin su.
Gashi shiru tunda na zo baba baiji wani labari daga wurin su gwago ba ita bata zo ba dan ta bai zo ba sai jikin baba ya fara sanyi .
Gashi yai masu aike yafi a kirga amma sun ki bashi amsa balle ya san abinda yake ciki din yana a kan bakan shi sai na koma gidan dole.
Ranan kwatsam sai ga yaya Saadu ya dira gari wai sun shigo arewa ne yace zai karaso ya dubani.
Yana zaune dakin mama naje gaishe shi da zuwa sai ga baba yazo shima anyi sa a yana gida bai fita ba bsyan sun gaisa sai ya dube ni yace ke kuma ashe haka abin yakai.
Baba sai dai kai hakkuri don maman mu da dan uwana basu rike amana ba ba gwama ma da auren na ya mutu tun baika ga kasheta ba a rasata.
Akai tsit ana sauraren shi ya shiga lissafo masu irin rayuwan da nayi a can harda wanda ban fada ba na yunwa da irin zagin da yake min na cin fuska.
Yace baba wallahi Ahmed da wuya ya sauya halin shi don yayi nisa da duniya yaudaran ku dai mummy mu tayi bata fada maku halinshi ba na gaskiya.
Amma baba yarinyar nan tasha matukar wuya a han shi yai amai ta kwashe ya shawo giya yazo yai mats dukan tsiya a gidan sai ya barta kwance.
Ya kwaso mata tana zaune suna cin abu ya hana mata ga ciki a jikin ta, kai abin ma baya faduwa wallahi sai dai Allah ya saka mata ka wai za a ce.
Jikin baba ne yai sanyi ga bayanin da yake masu nauyi da kunya suka rufe shi don har su yaya Sani suna a tsaye wurin suna sauraren baiyanin shi.
Zai tafi ya kawo kudi yaba baba yaba su mama da yaran gida ni kuma ya rubuta lanba ya bani ya bani karamar wayan shi yace inda wani abu a kirashi insha Allah zai taimaka ya kawo kyautan kudi masu yawa ya bani.
Yace idan aiki ya sake kawo shi arewa zai dawo ya duba mu lokacin yasan na haihu yace kiyi hakkuri Safiya tun yazu Allah ya fara saka maki ai don ya fara ganun abinshi.
Nai murmushi nace yaya banda abinda zance sai godiya gare ka don ka fitar dani zargi a gurin baba.
Don ni na kasa mai bayani yadda kai masu saboda ina jin kunya fadi amma yanzu sunji nagode maka da Allah ya kawo ka zo kai masu bayani.
Ya tafi yabar zukata da magana da kiyastawa na abubuwan da ya fada baba kan nauyi da kunya sun hana shi shakat a rayuwan shi.
Mahaifina ya dan sasauta min don tun da yaya Saadu yazo yana amsa min gaisuwa indan na gaida shi sabanin da da yake kyale ni.
Ranan wata jumma,a ya dawo daga kasuwa ya shigo da leda a hannun shi ashe rogo ke ciki mai zafi da zogala ya sayo min.
İnna zata karbi ledan yace a a barshi kayan safiya ne sai ya kwala min kira ina daga dakin mu najib sai na fito.
Ya miko min ledan dake hannun nasa yace karbi jeki ki gyara ki ci inna na tsaye har lokacin tana son tasan may a cikin ledan.
Na duka na karba a cikin ladabi nai mashi godiya sai naji inna na cewa wata sabuwa ke nan kuma.
Ban dai kula ta ba na wuce dakin mu sai da nashiga na bude naga ashe rogo ne daffafa da zogale.
Jikina rawa na shiga gyarawa sai da na gyara na kasa naba kowa na gidan mu ba wanda ban ba na zauna na dan ciyen sauran na kora da ruwa.
Tun wanan ranan idan zai dawo gida yakan dan riko min dan abin kwadai irin cimar kauye na gyara naci duk da ina ba kowa isan na gyara amma sai da hakan ya zama tsegumi a wurin İnna.
Don da ta tayar da fitina ta kaca kaca taiwa baba ranan kan haka yace shi yana sayo min ne don ya ga ina cikin lalura na ciki.
Gashi kuma ban da miji kusa yasa yake sawo min amma duk da haka bata yarda ba tana ta faman fada.
Sai mama ne ta dakatar da ita tace haba haba wanan abin da kikeyi bai kawo kallo ba wallahi abinda ba ita kadai take zama taci ba kowa sai ta ba gidan nan.
Shine kuma har ya zama abin fitina haka yarinyar nan koke kike dashi ai kina mata basai malam yayi ba.
Nan ta juya kan mama da fitinar ta tana ce mata munafuka ai da ita ake kulla komai da akeyi a gidan.
Bata kare fadan taba sai ga Yaya Sani ya shigo min da kade a leda yana kwala min kira na fito in karba.
Mama tace ta kin gani yanzu kuma may zaki ce duk wanda ke da imani dole ne ya tausayawa safiya halin da take ciki a gidan nan.
Tace ai bani na aike ta da ba ana yi muna rawan kai an tafi birni ba diyan mu suna nan sai da dubu ya cika za a zo a zauna muna gida dan kudin da za a yo muna cefane a kwashi ana sayo mata gaye dashi.
Mama tace dubu bai cika ba don iyayyen kirki duk basu rushe gidan yar su sai dai su gina shi don haka ki natsu kisan may kike fadi idan da yar ki ne haka ya cika da ita yaya zaki yi.
Tai wani iri shewa tace can dai gasu gada diyana basu ciki wallahi tace amma kin zuga na wasu sun shiga ai.
Tace muka dai zuga tare karki debe kan ki ciki wayai ruwa yai tsaki cikin wanan hadin , tunda kin sai tun ba a yi auren ba watsetse ne shi.
Mama tace sanin haka danayi yasa ai nake tausaya ma yarinyar don kar abin yai min yawa.
Kuma sa bakin da nayi ayi bawai na sheri bane don a hada zumun ta ne nayi badon wani abuba kedai kika yi don sheri kije kitayi ai.
Ummi tana jin su tace wanda duk ya cuci wani dai Allah yana ganin sa shine Alkalin mu daku.
Baba ne ya sake shigowa gidan ya iske suna rigiman har lokacin ya ce wanan wani irin rigima haka kuke yi.
Kun ishi mutane da hayaniya haka yaci gaba da fadin dame kuke son muji da tashin hankalin ku koda halin da yariya ke ciki.
Yanzu ba lokacin hayaniya bane abinda ya faru ba za a canza shi ba ku barmu muji da abinda zuka tanmu ke ciki mana.
Yarinyar nan tana bukatan kwanciyan hakali amma kun tsaya kuna tonon asiri irin haka yarinyar nan fa ba ita ta saka kan ta ba.
ZAİNAB İDRİS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , ,
🧕🏿2️⃣2️⃣🧕🏿
YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , , , ,
Na tura kofan na shiga da sallama yana kwance saman dogon kujera daga shi sai kajeren wanda ga taba rike a hannushi yana zukawa.
Daidai lokacin da Lilliya ta fito daga dakin tana waya gaisuwar da nai niyar yimai ban samu yi ba na shige kitchen abina kai tsaye ina tsuki.
Shiko yana ganin na gani na sai ya dan zabura alaman rashin gaskiya a tare da shi.
Ina fitowa da ledan da na hadawa Mujida kayan miyan da tarokeni ci ta gama wayan ta juya gare shi tana cewa.
Ahmed kayi gagawan yi ma wana yarinyar waigi kaina, kai mata magana ka tsawata mata don bazan lamunci batacin ta gare ni ba.
Wai kaima kamar ka, ke zama da wanan karamar yarinyar mara kunya banza zata shigo tasamu mutane tana masu tsuki kamar wacce ta samu dabbobi, karamar mara kunya kawai.
Har zan wuce banyi niyar kula suba jin tace dani mara kunya sai na juyo gare ta na fasa fita daga gidan.
Nai mata wani irin kallo sama da kasa a wullakance nace kar ki dauki alhakin dabba kici mai mutunci, don ko dabban ma ya fiki mutunci da daraja a idon jama a.
Don da dabba yana da baki aikai mai sallama da zai amsa sallaman kai tsaye kin ko kaga ashe sunfiki darajja kenan daidai nan mujida ta shigo gidan ta tsaya tana sauraren mu.
Nace ke dani yanzu waye mara kunya da zaki zo har cikin gidana duk da na kyale ki ki nemi ki kirani wai mara kunya ni yar kice ko may ?
Mujida ne ta katse ni da cewa towai ita din waye nace ban san ko ita din waye ba na dai dawo na same ta a cikin gida na tana shige da fice min a gida ai yanzu dai muka shigo dake gidan ko ?
Na tambayi mujida ta amsa min da eh wallahi nima naji shiru baki fito ba shine naji muryan ki na leko.
To ta tare ni da suratai tana fada dani amasifance ni kuma bansan da watake yi ba ma, a gidan sai dai ko idan mahaukaciya ce ita din don in ba hauka ba ba yadda za ayi ta shigo min gida ki tube haka zindir don daga ita sai breziya da gajeren wando a jikinta.
Mujida ta kalli Lilliya ta sake kallo na taga ban da inda nake da hadi da ita na kinga ina da hadi da ita ne mujida ?
Sai Mujida tace kai dis one na ashawo,
Wanan ai karuwan titi ne ta shigo maki gida taci maki miji ne , "na so dem dey do ehhuu ashawo ta shiga mata ihu da sowa akai tana batun tara mata mutane.
Lokacin ya zabura zaune kamar zai yi magana Mujida ta juya gare shi tace Oga barin fada maka gaskiya zama da irin wa yan nan shedanun yana jawowa mutum babban asara a rayuwa.
Ka gansu nan guba ne irin su don a take sun nakasa wa mutum rayuwa ko ta jama hasara babba.
Da mamaki suka tsaya suna kallon mujida don bata da alaman tsoro ko kadan irin matan nan ne da suka san kan lagos ciki da bai dinta.
Fada ba nata ba ta saye zancen haka, wai ko ina Safiya take haduwa da irin goggagun mata haka yan duniya dasu oho.
Itako Lilliya zuciyar ta ji take yi kamar zai fashe don bakin ci, kalaman da muke fada mata sun mata muni sosai.
Shiko maigidan da mamaki a fuskan shi ya ke kallon mu yana son yai magana sai dai bai iya cacan bakin mata ne dai kawai.
Zan sake yin magana sai ya daga min hannu da cewa dakata, min don Allah, shin munyi dake cewa gidan kine ke kadai.
Yadda gidan nan yake gidan mijin ki, na fada maki itama gidan mijin ta ne, tana da daman shigowa duk lokacin da take so.
Sai Lilliya ta karbe da ai wanan cin mutumtuci ne kamar wanan zan zauna gida daya da ita tana min rashin kuya don bata da tarbiya, wanan yar kauyen da ita may ta sani banda jarabar maza iri naka har da zuwa mata ciki don kwakwa.
Wanan ga kankanta ga jahilci Mujida ta cabe da cewa yi muna shiru munafuka masu yawon kwantan mijin mutane kawai ashawon banza ai gara da ita an sheda daurin auren ta kefa a bariki ne aka dauro naku.
Na ce kin taba ganin karuwa tayi aure ne ai sai zaman banza dai, sai na hada da cewa karuwan titi anzo za a samu wurin fake wa.
A hasale ya dani ki iya bakin ki Safiya kiyi hankali dani wanan dakike gani, ni a wurina tafiki tunda tasan mutinci da daraja a idota.
Don kana dan bariki irin ta ba muje ne ya tadda mutafi kai da ita duk ruwan bariki na cinku kaga dole kasan ta fini, tafini iya shan giya da karuwanci ba.
Fayau fayau ya kwashe ni da mari biyu masu kyau a fuska na yace ba nace ki iya bakin ki ba wanan da kike gani tashigo gidan nan ke nan bata sake fita ko ina.
Na dade a duke tare da dafe kumci na inda ya mare ni , inajin mujida na ta mai ruwan balai akai ta hadu su ta zage tas yace shi ba zai mata komai ba ni dai dana jawo ta gidan zaiyi wa.
Don haka in zaki zauna ki zauna in ba zaki iya zama da ita ba ga hanya nan ki fice min gida na fada maki sai lokacin na samu baki magana.
Nace zan fice amma sai ka bani shedan ficewa karna je gida ace zaa sake dawowa dani gidan ka kuma don da in dawo gidan nan gwama muta.
Yace abu mai sauki kenan wai takarda kike nufi komay nace dashi eh a hasale.
Mujida dajin haka ta fara fadin a, aa kada kayi mata haka mana, ga ciki ajikinta ga kurciya kace zaka saketa don wanan ashawon matar ta nuna Lilliya a wullakance.
Wallahi na fada ma wanan da kake gani poison ne sai ta halaka ka, har dukiya ka da komai naka, daga karshe ta gudu ta barka da wahala.
Indan taga sakin yafi mata sauki ai a shirye nake da yin sakin kalman sun ban mamaki wai a kan karuwa yake maganan sakina.
To ko na zauna may zan tsinta ga mutumin da ya furta hakan banda tarin takaici da bakin ciki da sune na ke gani a koda yaushe na dago kai na kalli Lilliya wace ke tsaye tana wani muzurai da ido don jin abin da ke wakana tsakanin mu.
Bata da wani abinda za a so daga gare ta haka take kamar kato yai shirin mata da ita, sai farin na mai data shafa ke aiki jikin ta kawai.
Muryan Lilliya ne ke fadin dama ai karanbani ne da kwadayi ya shigo da ita ba komai ba may zaka deba a jikin wanan yarinya nema wai.
Na ce ai shi yasan abinda yake diba gare ni kullun in ba kaddaraba may zai shigo dani cikin fasikai irin ku.
Ta tafa hannu da min tsowa miji dai ya dawo hannun na dama nawane ba naki ba, dama matsala aka samu ya aure ki dan wani dalili yanzu ya dawo hannuna kenan .
Lilliya ya ambaci sunan ta cikin tsawa ta bar maganan da take yi din yace kyale ta ni ma nagaji da wannan yarinyar mara tarbiya haka.
Nace dashi kayya amma kai kan anyi hasarare baka ko jin kunyan kiran wanan a matsayi matar ka.
Wallahi kaban mamaki wai da hankalin ka da ilimim ka namiji kamar ka, zaka kar awanan matar titin fuska a kone yasha mai, ga kai kamar iccen kwakwa,
Abu haka a tsaye kamar kato, mace ba addini ba al,ada ba dabia na kwarai, mutum irin ka maijin duniya da hayaki bai kamata ya buge a wannan abin banzan ba .
Dama wata mai surar kwarai ce sai kai min gadara a dajin kai a kanta dan wanan dai kake cewa wai tafini tafini iya shedana ko.
Wallahi na tausaya maka yaya kayi hasara namijin duniya kamar ka ya kare a dadiro da wannan abu da bata cikin tsarin mata.
Ai gara dani da kankantana da rashin ilimina ko ba komai ina da addinina kuma a gaban iyayyena ka dauko ni ba bariki na biyo ba
In dai wanan matar ne gatanan ga ka ba zan zauna ku kashe ni da bakin hali irin na kuba kai da ita , da yarinta na tsohuwar banza ta zo ta zauna min gida tsofai tsofai da ita wai kuna dadiro dadiron na kuma na iya shege ne.
Banji tsoron su ba haka na tsaya gaban su nai masu tasa yana tsaye kamar wani soko a buge yake har lokacin.
Ya kalle mu nida mujida rai bace yace ku fice ku bani gidana, sannan ki tatara yau yau ki bar min gida na ki bar garin nan ki koma gida uban ki na sake ki saki daya.
Mujida zatai magana ya daka mata tsawa yace na fada maku kubar min gidana haka na.
Nasan halin shi sarai don haka na dakatar da mujida nai mata godiya tare da bata abinda ta bukata gareni, ta fice tana tausaya min.
Dakina na shiga wurin da nake boye kudi na daga na kwashi kudina da takarduna na fito ba tare da na sake waigen su ba yana zaune yayi tagumi kamar wanda abin ya dama.
Koda na fita waje tsayawa nayi ina tunanen inda zan nufa araina ko inje gidan gwago na don kartace ban fada mata ba na wuce.
Sai kuma nace banzan tafi ba gidan anty zan nufa maman biyu sai na tare taxi na tafi, ina tafe ina tunane idanuwa na suka yi jawur ina jin zuciyana yana min zafi da wani irin kuna da zugi.
Ina tuno irin cin mutuncin da nai ta fuskanta a gida duk hakkurina sai da haka ta kasan ce dani yanzu in naje gida a haka ko wani iri hukunci zan fuskan ta gun mahaifina kuma.
Wasu hawaye suka zubo min ina jin tsanar shi ya kara shiga min rai na har na kai gidan maman biyu ina tunane a zuciya na.
Na samu ta dawo aiki kenan tana zaune yaran ta sun zagaye ta suna mata hira sai gani na shigo.
A yadda ta ganni ta fahinci ba lafiya yaran suka rugumay ni suna min oyoyo da ganina tace oya ku shiga ku cire uniform a huta .
Duk suka shige suka barmu da ita sai a lokacin ta dago kai ta dibeni take cewa Safiya nayi mamakin ganin ki yanzu da yamman nan .
Dukar da kai nayi bance da ita komai ba nace anty yuwa nake ji murmushi tayi tace yunwan ne kike ji yasa ki kuka don ga alaman kuka nan tare da ke.
Ban samu cewa komai ba takira yar aikin ta tace ta kawo min abinci da zai isheni wai yunwa nake ji kin san abu gamai ciki.
An kawo abinci sai dai ban iya ci ba tana lura dani tana waya sai ta katse waya tace a, a Safiya bakici abincin ba mana ko baiyi maki dadin ci bane.
Maimakon in yi magana sai ga hawaye yana zubo min a idona nace a hankali anty gida zan tafi yau.
Ta dago da sauri tace wani gidan dai kike magana zuwa nace garin mu.
Tace kina ko da hankali kuwa yau din nan kina haka kice zaki tafi arewa may zaki tafi yi arewa kina cikin wanan condition din.
A hankali nace da ita ya sake ni ne zan koma garin mu ne.
Ya may kika ce ta fada a razane .
Na sake cewa anty ya sake ni akan wanan karuwan tashi yaban saki ya zabi zama da ita sama da ni ne.
Innalillahi take maimaitawa da karfi a bakin ta tace Safiya da gaskiya kike ko wasa wai?
Nan na fara bata labarin abinda ya faru a gidan tun fitana har dawowa na gidan da nazo na samay a cikin gidan.
Tace yanzu abin nashi har yakai can ya sake ki da tsohon ciki a jikin ki babu ko tausayi hakan .
Anya wanan mijin naki ko yana da imani ya bata maki kurciyan ki ga banza ya cuci rayuwan ki.
Kin ga hakkuri zaki duk abinda ya samu bawa mukkadari na daga ubangiji bai cuciki ba kanshi ya cuta da yardan ubangiji zai girbi abin sa.
Amma uwarshi ta sani kuwa na girgiza mata kai alaman aa na hada da cewa ban tafi can ba nan nayo.
Tace ya kamata muje mu sanar da ita karta ce baki fada mata ba don mutum abin tsoro ne yanzu balle tana gani itace makusanciyar ki a garin nan.
Nan dai ta yanke shawaran mu tafi mu sanar da ita ko banza dai gwago nace ita din .
Mun tafi mun samay ta tana cika tana batsewa dakyat take karba muna gaisuwan da muke mata, bayan mun zauna ne tace kun kai ga yadda kuke so kedashi.
Yanzu may kika zo yin mun sai da kuka bata abu zaki taso ki zo min may kike son na aiwatar yanzu din.
Gidan shi ne shike da iko da abinshi ki kyale shi mana yayi yadda yake son da gida shi kema ba kawo ki akayi ba acikin gidan.
Anty ne ta katse ta da cewa kai kai wanan magana taki baiyi ba a saki yarinya sai kuma ki bita da wanan irin maganan .
Yanzu in yarki ce ta samu wanan matsalar abinda zaki ce da ita kenan, karuwa fa zaman dadiro a cikin gidan ta haba hajiya kiyi tunane mana.
Tace haka zan fada mana to waya ja wanan matsalar haka karamar yarinya da ita ta iya kishin tsiya.
Yanzu ai sai ki koma gida kuje kuyi ta zaman gida ai kin san abinda kika baro gidan naku ba wani abu ya canza ba.
Tsam anty ta mike tace dani tashi muje Safiya akwai Allah duk wanda ya cuci wani a cikin ku Allah yana ganin sa ai.
Haka na muka fice gidan muka barta nan tana ta faman fada abin dai zabar kunya don bai ma faduwa .
Gidan mama biyu nai kwana biyu ta rakani gidan na dauko abinda nake so cikin kayana washe gari na kama hanyan arewa acikin motar da akai min shata sai gida.
Asubanci mukayi amma sai dare muka kai garin mu lokacin da mota ya tsaya kofan gidan mu an shiga sallah isha,i .

🧕🏿2️⃣5️⃣🧕🏿
YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDINE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , , ,
Cikin wata daya da nayi a gidan mu cikina ya karasa shiga wata na tara duk da nace ma ummi da mama bansan ko wata nawa cikin yake ba.
Amma su daya ke manya ne sun gane na shiga watan tara nan aka shiga min jikile jike ana bani.
Don samun saukin haihuwa wai idan haihuwa yazo vazan wahala ba sosai indan ina shan abin karya zaki.
Watarana da dadare ina cikin barci na farka da matsanacin ciwon mara da ban taba jin irin sa ba, wai ashe nakuda ya kamani .
Cikin barci na dinga tada ummi na daga barci ina fadi wayyo ummi bayana marata ciwo kamar zai fashe min nake jin shi.
Ummi ta tashi a rude take tambayana ya nake ji na fada mata, fita tayi daga dakin taje ta tada mama sai gasu sun dawo a tare da mama din dakin.
Nan suka fara bani abinda ya dace da akewa mai na kuda da fada min yadda zanyi abin yazo min da sauki.
Abu wasa wasa har wuraren karfe sha biyu na rana ba labarin haihuwa gashi ina dan banzan wahala.
Don haka suka yanke shawaran su kaini asibiti don ina wahala sosai na gala baita matuka na wahala a gida.
Mun isa asibiti aka duba ni suka ce haihuwa ne sai dai bazan iya da kaina ba don haka za ai min theater ne.
Bani dake wahala ba harda su mama da suka kawoni sai da hankalin su yai matukar tashi, aka rubuta masu abinda za a sayo kafin theater din.
Baba ya fara fadi tashin neman kudi don ya sayo maganin da sauran kayan aikin don baida kudin a hannunshi.
A cikin karfin hali na daure nace baba akwai kudi a hannuna a tambayi ummi na agida ta duba zata gansu.
Allah da ikon shi anshiga dani dakin theater sai Allah ya kawo min saukin haihuwa na nisa sai abin cikin cikin nawa ya fito.
Ashe abin da matsala ne shiya sa na wahala diya ce mace sai dai tazo da wani irin halitta na daban likitoci suka taru akan mu suna dibata.
Daga karshe dai hakana dai aka sallamay mu muka koma gida da ita cikin yanayin da tazo.
Sai dai mama ta hana abawa kowa yar ya gani tana dunkule a raggan zani duk wanda yaga abinda yarinyar keyi dole ya tausaya mata.
Karamar yarinya da bata dauki alhakin kowa ba a kanta tana bautar Allah cikin wani yanayi na ban tausayi.
Amma ita inna har kiran mutane take su zo su aga abinda na haifa mutane ko sai suka fara tururuwan zuwa ganin halittan yar.
Kwana daya da haihuwa Baba ya shigo gida da dadare yake ce min yaya za a yi a samu su gwago can lagos a fada masu zancen haihuwan nawa.
Na lumshe ido nace baba aida a kyale su kawai, yace aa baki da hankaline yarsu ce fa suna da hakkin a fada masu ai.
Sai nace sai dai yaya saadu don shi kawai nake da nomban shi wayan shi cikin su bayan shi ban da lanban kowa cikin su.
Ko shi da yazo ne yaban wayan da zo dashi shine har na samu namban shi din, da ban da layin kowa a cikin su.
Yaya sani ne yakirashi sai baba ya karba yana fadama mashi zancen haihuwan yayi murna sosai dajin na haihu lafiya da Allah ya saukeni lafiya ba tare da anmin aiki ba.
Sun gama da baba yace a bani wayan yai min barka na karba cikin jin kuya nake karba mai yace da ya kashe zai kira mummy da Ahmed ya fada masu na sauka lafiya.
Hakan ko akayi nan ya kirsu ya sheda masu zancen haihuwan nawa sai dai ba wanda yai farin ciki da jin haihuwan daga cikin su.
Shima gogan daya kira shi cewa yayi and so what idan ta haihu may kake son nayi mata yanzu kuma ?
Ashe lokacin suna tare da Liliya ne ya kirashi don haka baida halin nuna farin ciki da haihuwan nawa.
Nan dai dan uwan yai mashi tas yakuma ce indan baiyi hankali ba sai ya hada shi da hukuma akan wanan case din.
A haifa ma ya kace min and so what kai wani irin jahilin mutum ne wai kana koda inmani kuwa kai ?
A cikin fushi ya nufi gidan su yana fada ma mahaifiyar su yadda sukayi da saadu din wai ya kira shi da jahili.
Tace ai gaskiya ya fada maka dole ne ai a fada muna san nan ai wani abu daga nan wurin mu kuma ya zama dole mu tafi yace wa ?
Cikin hasala shi ba inda zan tafi indai ke zaki tafi ban hanaki ba amma nikan ba inda zan tafi tun wuri .
Don nasan a jirace suke damu yanzu kuma sun samu kafar samun mu ke nan don haka ni ba inda zan tafi final.
Saadu yazo yasa uwar a gaba son su hada abinda zasu sai mu na kayan suna suzo muna dashi, mahaifiyar nasu tace bata da kudi yanzu a dai tambayi Ahmed din.
Gogan da aka tambaye shi dubu goma kawai suka samu a wurin shi wai baida kudi duk karuwai sun cinye kudin shi da giya dole yaya saadin ne ya fitar da kudi ya sai muna abinda za a zo dashi din.
Sun saka ranan tafiya saura kwana biyu suna munyi waya dashi nai mashi kwatancen gidan maman biyu don yaje ya fada mata.
Ya ko je tayi murna dajin na haihu din ta karbi lanba na a wirin shi ta bashi abinda zai kawo min sai dai bai gwadawa mahaifiyar ta suba.
Da dare ina zaune a dakin mama don anan nake jegona sai naji wayana na tsuwa alaman kira ya shigo min .
Na dauka da sallama muryan wace najine ko a barci na falka ina sheda shi maman biyu ce ta kirani, na dan kwala ihu do jin muryan ta, tace dani.
Ai nayi fushi dake nace anty ba hakana bane wallahi kullun kina a raina ban san yadda zanyi in kiraki bane.
Don lanban da kika bani ya bata nan dai muka taba hira da ita take tambayana yadda muka kwasa da mahaifin mu da nazo gida ?
Ta fada mata komai harda zuwan yaya Saadu wurin mu da yadda ya wanke ni a gaban su baba da sauran yan uwana.
A karshe mukai sallama da ita tace zan ga sako wurin yaya saadu idan ya zo nai mata godiya na kashe wayan.
Idan na kalli yarinyar tausayi take ban don yadda take wahala matuka taita murde murde da hannu idanuwa warwaje tana wani irin numfashi a wahalce kace ko zaka je kadawo kasamu bata da rai.
Mama ce ke kwana wahalce da ita har safe sai a kama mata tadan kwanta da rana ta runtsa barcin ba wani barci ba take tashi.
Da aka ga wahalan yai ma yarinya yawa aka koma asibiti da ita likita ya tambaye ni idan na taba mugun faduwa da ciki.
Nace a a yace duka fa kowani buguwa mai karfi sai nai shiru mama tace mijin da ta aura yake dukan ta da ciki likita yace wanan abun ne ya taba yarinyan tun a cikin ciki yasa tazo kamar jujartata.
Hawaye na fara yi ina tausayin yarinyar da kaina, magani aka rubuta muna muka dawo gida rai baci tun a mota mama ke ta zabga fada tana cewa mutane ba imani haka ?.
Yanzu gashi ke ke wahala shi yana can yana barikin shi hankali kwance abinshi.
Mun iso gida mama tana kuka tana ma mutanen gida mu bayani komai da likita ya fadi.
Allah ya isa yaya sani suke ta ja baba baki ya mutu da har ya fara cewa in gwago tazo sai in hakkuri in koma dakina.
Wai kada yarinya ta tashi ba uba tare da ita maganin da likita ya bayar a bata shi ake bata kai da kai sai numfashin ya fara ragewa ya dan fara komawa nomal.
Su yaya Saadu sun taso kamar yadda suka shirya ba isoba sai da safe don tafiyan dare sukayi.
Tun da ya shigo yagga yadda yarinyar take hankalin shi yai matukar tashi sosai gwago tun taron da yan gidam mu sukai mata ta shiga tsarguwa.
Mama na kuka take fada masu abinda likita yace a gamay da yarinyar yaya yace komai akace ya faru ne ba a kyauta ba gaskiya amma ayi hakkuri.
Suka bayar da abinda suka zo dashi wanda ni nasan yaya saadu ne yayi shi don nidai duk zama na gidan bai taba yin min sutura ba.
An karba da godiya sai gwago tace adai yi hakkuri dashi mama tace ba a dai kyauta ba gaskiya malam ya bada yarinyar don zumunci ya dore gashi abin kuma baiyi dadi ba.
Baba sun zauna da gwago ya nuna mata bacin ran shi sosai ga irin rikon da dan ta yai min acan har da nata laifin ma, sai ta kama kukan munafunci wai yara zasu bata masu zumuncin su.
Baba yace basu bata muna zumunta don ba su suka hada mu ba balle su yanke muna zumuncin mu.
Nan ta danji sauki har ta fara aibanta ni wai ban da kirki banda tatali banda sanin ya kamata ko ita rashin kunya nake mata..
Sai da yaya saadu ya bari ta gama ya kawo matsalnta duk ya fada ma baba da yadda tabar tarbiyan su ya lalace komai ya fadi.
Sun dade suna magana baba ya san yi mata nasiha har da alkwarin wai zai mayar dani dakina yace dasu.
Ana gobe sunane sun zo washe gari da safe yarinyar ta koma Allah ya gani banji bacin rai da rashin ta ba don a halin da tazo da ta rayu wani gwamma ta koma yafi.
Nan dai aka kawar da ita yan uwana sun tausaya min sosai nidai abu ga kurciya ga bacin rai banji komai ba a lokacin.
Sai gwago ta kebe da yaya saadu da mama wai a rage abinda suka zo dashi tunda yarinya ta koma nan yaya saadu yai cikin ta.
Yace indon dubu goman da Ahmed ya bayar kike jin zafi ga dubu goma ki mayar mai da abinshi ban iya abin kunyan da kike shirin yi.
Mama tace wai ko Rakiya kan ki daya kuwa may yasa abin duniya yake rufe maki ido haka ita yarinyar da tai wahalan haihuwa fa ?
Nan dai suka yi shi baran baran sai da rayuka suka baci masu, washe gari suka daga suka koma inda suka fito.
Bayan wucewar sune mama ke mayar da yadda suka kwashe da gwago kan kayan nace mama aida kun mayar masu da abinsu ma.
Don ni bani son komai da ya fito daga wurin Ahmed sai mama tace ai ai a she shi dubu goma kawai ya basu su kara.
Duk kanin ne yai sauran kayan da kuka gani uwar bata sako komai ba ni bansan inda Rakiya zata kai son kudin ta ba wallahi.
Nan nake basu labari ai ko zuwa nayi gaida ita bata bani abinci sayarwan ta sai ansaya mun zan ci.
Kowa yai tir da irin hali nata na son kudi da rashin taimakawa uwan uwa kullun tazo sai kukan babu takeyi.
Maman biyu ta bugo min waya da dare tana min barka da taro ya watse lafiya ?
Murmushi nace anty ai yarinyar ta koma jiya nan dai nake fada mata yadda akayi da abinda likita ya fada akan ta.
Tace kin ma huta wallahi Allah ta baki lafiya yasa ita kuma ta huta nace amin nan dai mukai hira tana tambayana yadda aka kwashe da gwago tazo nake fada mata komai karshe nai mata godiyan sakon da ta aiko min mukai sallama da ita.
Tun da akai sati na dan watsake ina yin komai sannu a hankali ina mai da jiki na ina harkokina na yau da kullun sai dai ban fita ko ina ina gida koda yaushe.
Dan dama dama naka dan dauki lokaci in fita ziyaran yan uwa ban dadewa in dawo gida don ko na fita sai na tsargi kaina don ban son a dauko min maganan zama lagos.
Sana a nake gadan gadan kanena ke fita mun dashi don haka hankali na yadan kwanta har nakan manta da rayuwan gidan Ahmed din da nayi a baya.
Zan tura kudina wa maman biyu da kudi sai ta sayo kaya ta turo min dashi ta motar haya a kawo min.
Haka nake har na dan samu nawa sai kuma kyashi da hassada ya shiga zukatan Inna da wasu yaran gidan namu zaka ji ana sake magana akan sanaa nawa a tsakar gida koda yaushe.
********* ********** *********
Hai huwana da wata uku na dan fara ciwon kai sakuma yawan zazzabi da yake biyowa akai akai.
Ranan ina kwance yaya saadu ya bugo min waya na mike da kyat na dauki wayan tare da sallama yanayin murya na da yaji yasa yace baki da lafiya ne Safiya.
A hankali na bashi amsa da wallahi yaya kwanan nan duk kai da zazzabi ke yawan damu na na rasa gane kan jikin nawa.
Yace subbahanallahi kin kuwa je asibiti nace ban je asobiti ba ina dai shan magani a gida ne yana min sauki in na sha magani ai.
Yace No kije asibiti a duba lafiyan ki asan may ke damuwan ki yafi sauki da shan maganin nan da kike yi nace naji yaya zan tafi.
Mukai sallama yace dama ya bugo ne yaji lafiyana tunda suka koma bai samu kirana ba sai yau nayi hakkuri nace nagode kwara muka sallama yana kara jaddada min akan in tafi asibiti fa nace zan tafi ai.
Kwana biyu na ji sauki nikan na manta da zuwa asibitin da mukayi dashi naci gaba da harkokina kawai.
Kamar naji sauki da jikin zai tashi mun sai yakaini kwace kasa nai ta faman jiya a gida ina zuwa chemist ina karbo magani na dan ji sauki.
Ban san yaya akayi yaya saadu ya samu lanban yaya Sani ba ya buga mai yana cewa ya kirani wayana a kashe.
Sai yaya sani yake ce mai ai banda lafiya ne kwana biyu kila na kashe wayan ne .
Yace subbahanal lahi kon ka kaita asibiti andubata yace dashi a a ina ganin bataje asibiti ba yace da yaya sani don Allah akaini a dubani.
Shi zai turo da kudin zuwa asibitin haka ko akayi amma da yaya sani yai magana gida akace mai dahuwan kassa nakeyi tunda banyi ba da na haihu sai yanzu nakeyi.
Sunyi waya dashi yaya sani ke fada mai abinda akace ya matsa wa yaya sani aka ya kaini asibiti fa yanzu ba a wasa da ciwo gida.
Har na dan ji sauki kwana biyu kuma sai jikin nawa dawo fiye da farko dole muka kwasa sai asibiti.

🧕🏿2️⃣6️⃣🧕🏿
YAR UWA NOVEL DIN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLESASE, , , , , , , , , ,
Mun yanki kati muka bi layin ganin likita a tare da sauran jamma a da muka samu a wurin.
Sannu sannu har layi ya kawo gare mu muka shiga wurin likitan bayan yan tambayoyi sai ya tura mu wurin yin test.
A can ma mun dan bata lokacin mu a wurin don mutane da sukai yawa masu son ai masu test din.
Mundan jira suka bamu sakamakon mu koma wurin likita dashi muna zaune a gaban likita dani da baban mu da yaya sani.
Munyi zaune shiru ya gama rubutun da zai yi ya dago kai yace baba wanan yar kace ?
Baba ya gyara zama yace kwarai kuwa yata ce wanan kuma wan ta, sai likitan ya sake tambaya tana da aure ?
Baba ya dan kara gyara zaman shi yace eh to ta dai taba auren yanzu wata hudu kenan da mijin ya sakota da ciki ta dawo gida wata uku kenan da ta haihu goyon ta koma.
Sai likitan ya girgiza kanshi alaman tausayawa gare ni ya sake tambayan baba yanzu ina mijin nata yake muna son ganin shi, shi mijin nata.
Baba yace ayya ai ba nan yake ba can Lagos yake da zama da iyayyen shi shiru likitan yayi yasa biro da yake rubutu a bakin shi kamar mai nazari.
Ya dago yace baba indan ba damuwa su fita waje muyi magana dakai sai baba yace ai ba damuwa likita duk diyana ne indan kaga wani matsala ne kafadi muji.
Sai likitan yai shiru can kuma ya dan dago kai ya kalli baba din yace a gaskiya ba yar ka tana dauke da cutan tsida mai karya garkuwan jikin dan adam.
Baba yace ban fahince kaba hawanjini komay kace likitan ya girgiza kai yace gwaji ya nuna muna tana dauke da cuta mai karya garkuwa jikin dan adam watau HIV.
Ban san lokacin da na yanka ihu ba baba yace ke may ye haka kuma daga bayani ki yanka muna ihu tashin hankali.
Likita yace tana da right din yin haka don ba karamin masifa bane ya samay ta.
Baba tace likita may kace yace ina nufin ciwon da ya samay ta yana da wuyan sha ani sai ya fara yiwa baba bayani yace.
Sai da ya kawo wiri aure ya ce mace na dauka ta mijin ta idan mijin ba mai tsayawa ga matar sa bane yana neman mata a waje shine dalili daya na tambaye ku mijin nata yana ina?
Da sai mu ga gwada shi mugani shike da ciwon ko ita anan zamu fahinci wanda ya sawa wani ciwon a cikin su.
Baba ya miki yace ke tashi muje kin ji ai ba nan kawai bane asibiti akwai wasu guraren zuwa bayan nan.
Da kyat na miki don duk illahirin jikina yai sanyi baba na ta faman fada niko tunane nake yi ko shiyasa yaya saadu ya matsa in je asibiti.
Yasan dan uwan shi nada ciwon ne yasa ya damu da zancen azo dani asibiti a duna dai aga may ke damuna ne.
Mun shiga gida ana fadin kun dawo baba ya na fada kaji min dan iskan likita kawai ka rasa abin dafa mata sai mugun ciwon da kowa ke guda.
Nan da nan aka firfito waje don saure inna ce tace may akace yana damun tane wai ?
Yace bar mugun liki wai wai Safiya na dauke da wani ciwo ko tsida ko may tace badai kanjamau ba yace wai shi .
Nan da nan Inna ta dafe gaban ta munshiga uku mun lalace a gidan nan muke zaune da mai kanjamau sai ya dakata fadan yana kallon inna din da ta rikice.
Yace ke kuma may nene duk kin bi kin wani rude dake ?
Tace malam kanjamau fa akace irin ciwon da ya kashe dan gidan malam sahabi kwana ki har akaki taba gawan sa.
Nan jikin baba ya fara sanyi yace don Allah ki bari ke ma kin yarda ke nan tana da wanan ciwon ?
Tace bani yarda tunda mijin ta karuwai ne abokan hurdan shi ko yaushe cikin su yake yana like a gidin su yaya bazan yarda da maganan likita ba.
Ummi na tasaka kuka mai tsuma zuciya mai sauren ta tana cewa na shiga uku na lalace yau ni Rabi may zan gani a rayauwa.
Tayi dakin ta tana kuka cikin dakin ta samay ni nima kukan nakeyi in cewa ummi yaya Ahmed ya cuci rayuwa na.
Ummina na mutuwa zanyi in barki in barki da yan uwana da kowa naki ni safiya na shiga uku.
Yar nan Ahmed bai cuce ki ba malam ya cuce ki shida ya bashike duk da yasan halin yaron ya kuma amince da ya hadaku.
Kuka muke yi nida ummi da kanne na adakin baji ba gani sai baba ya tsaya daga kofa yana cewa wai baku barin kukan nan ba a fa sheda cewa shine abinda ke damun ki ba kun aza ma mutane kuka haka a gida.
Dole mukai shiru irin yadda yake ta faman fada sai dai ummi bata tsagaita nata kukan ba da take yi gwanin van tausayi ance uwa uwace bakowa ke karba sunan ba.
Baba ta samu an tsagaita kukan ya kwantar masu da hankali dan kwana biyu ga damuwa ga ciwo naci na baba ya ki kwantar da hankali ya fahinci komai.
Wanan karon an jijigani sosai Yaya sani sukai waya da yaya saadu yana tambayan shi yaya jikin nawa ?
Ya fada mashi ina jin jiki anje asibiti ga abinda likita ya fada innalillahi yake maimaitawa yace dama ina tuhumar haka ya faru .
Don shima Ahmed din tun fitan Safiya baida cikakan lafiya tare dashi yace a kaiwa baba waya su yi magana.
Bayan ankai sun gaisa da baba yake cewa baba naji ance kun kai Safiya asibiti likita ya fadi abinda ke damun ta kun karyata.
Baba yace gaskiya ne haka akayi wani likitane mai mugun nufi ya zarga mata wanan sherin don kazafi irin na likitoci.
Yaya Saadu yace baba ka saurare ni kaji yace ina jinka yace don Allah don Allah kukai yarinyar nan asibiti ta karbi magani in ba so kuke mu rasata ba gaba daya.
Abinda likita ya fada ba karya bane haka ne don na dade ina zargin haka shi ya da ita don mijin ta ma nemin mata ne ga shan giya idan ya sha baya laakari da irin matan da yake hurda dasu.
Baba kukai ta asibiti a san abinda ake ciki su dora ta ga maganin da ya dace tasha tin bai mata nisa ba.
Baba yai mashi godiya sama sama sukai sallama ya dukar dakai yana kukan nadama ya cuce ni ya cuci mahaifiya ta dashi kan shi.
Tun wanan lokacin ya koma kamar baida lafiya a gidan washe gari ma bai tafi wurin bidan kudin shi ba.
Ina daki mun bana fitowa don da na fito yanzu kowa zai kama kan shi babu mai zama dani balle idan na taba abu wani ya taba.
Daga ni sai yan dakimu nake hurda kawai a gidan suma kamar ana kyanaman su din kamar ni.
Abinda yasa na fara ganewa yadda mama ta dauke kafanta ga sha,ani na agidan ba ruwanta dani yanzu.
Ba may son ace yana hurda dani kamar zan lika masu cutan a jikin su koda yaushe ina daki ga jikin ba dadi min.
Shi baba har lokacin bai yarda ba saidai nadama ya shige shi sosai na yadda yaba da ni ga dan gwago duk da yasan bana kwarai bane shi.
Ya dinga tuna irin badakalar da suka kwasa da ummi a gidan kan aure na , ashe tafishi gaskiya da ta nuna rashin yardan ta da aure.
Ashe mafalkin da tace tayi dani mara dadi nada na saba da abinda zai faru da nine gaskiya idan haka ne gwago taci amanan zumunci.
Ga ciwo ga saki ga haihuwa ba yar tazo a wani irin yanayi takoma ni ina zan kai alhakin wanan yarinyar a kaina.
Sai hawayen nadama da dana sani suka fara zubo mai yana fadin Safiya ni na cuce ki da kaina da na tursasa maki auren wanan yaro akan ki.
Kwana biyu baba yayi cikin wani irin yana yi ga ummi na kullun tana faman kuka a daki gwagon ma haka.
Kwana bakwai da faruwan wanan maganan sai ga yaya saadu ya dira garin da dare mun dai ji zuwan shi amma bai shigo ba don dare yayi lokacin.
Da safe ya shigo gidan ba wani taron arzikin da ya samu gun mutanen gidan mu sai a wurina da ummi na da bata gwada mashi komai ba.
Don ni nasan irin taimakon dayai wa rayuwa na a likacin da nake bukatan taimako ba kowa a kusa dani.
Ya gaisa dasu ya shigo har dakin mu ina kwance na mike da kyat da kwance da nake ina mashi sannu da zuwa.
Yace dani sannu Safiya ashe kuma haka abin ya kasance ban iya bashi amsa ba sai hawayen da ke zuba min a idon .
Ummina ma kukan takeyi yana share hawaye yace dani bari kuka Allah na sane dake safiya kowani mai rai da irin tashi jerabawan.
Allah yasa mu iya cinye jerabawan mu ummi tace dashi amin mun gode da kulawan ka gare mu yace nazo ne mu kaiki babban asibiti ki karbi magani da ya dace.
In Allah ya yarda zaki samu lafiya in dai kina shan magani Allah da yai cuta shi keda maganin sa.
Sai ga baba ya shigo dakin namu ya kalle ni yace sannu safiya yaya jikin na amsa dakyat da da sauki baba.
Daga inda yake tsaye hawaye ya fara zuba mishi yace haka Allah ya nufa dake zumunci nai wa suka ci amanan ki.
Yaya yace ayi hakkuri baba in Allah yaso zata samu lafiya indai tana shan magani ai yanzu an samu maganin cutar.
Yanzu baba asibitin birni zamu da ita inda zamu ji mafanin da ya dace a bata tana amfani da shi.
Ikon Allah kana ganin zata samu lafiya idan ana shan maganin yace kwarai kuwa don ai mutane da yawa na dashi amma saboda suna amfani da maganin ba a ganewa.
Yace a shirya ta sai in san da suwa zamu tafi mota na nan da nazo dashi dashi zamu tafi.
Abin mamaki da baba ya fita ya lalubo mama don tafiyan sai cewa tayi gaskiya bazata samu zuwa ba adaije da wani.
Muna jin ta daga dakin mu ina kuka ummi na kuka tace oh Allah mutum da ranshi ya koma abin gudu.
Yaya saadu yace babu komai mama insha Allahu zata samu lafiya tace baka san halin mutanen gidan nan ba.
Tun yanzu sin tsane mu sun tsagwamay ta kyama da tsoron mu suke ji wai zamu saka masu cuta mu halakasu.
Yace babu komai mama a dai bari ta fara sha maganin a gani suda kansu zasu daina ai sai dai ta kiyayye rezan da take amfani dashi kada ta bari jinin ta ya fita wani ya taba.
Da wanan masullan kitson naku na mata idan an kiyayye hakan ba abin da zai faru da kowa duk fadan mutane ne kawai amma banda haka ana mua mullar komai da mutum kamar kowa.
Tace kayya yarinya dai ai ta nakasa yanzu ba zancen aure a gare ta ke nan har abada ko samun zuria a gare ta.
Yace aa mama duk dai wanan a barshi har Allah ya bata lafiya yace mama ki shirya mu tafi dake kawai ina jin rikicin wanda zai tafi akeyi a waje da baba.
Mama ki rungumi yar ki kar ki yarda ki biyewa mutane ki kyamace ta sai kowa ya ji dadin kayamatar ta a gidan.
Ummi ta share hawaye tace babu komai ai idan na kyamace ta wa zai duba min ita ya riga da ya cuce ta yariyar nan ta bisa bakin ta da cewa baida tarbiya .
Amma malam ya rufe ido yaci muna mutunci a gidan nan har yana ikirarin korana a gidan.
Yazu da haka ya cika da ita wake wahala dani da ita a daki kawai ke wahala ba wanda ya damu da mu a gidan nan har da wa yanda ke zuga shi kan zancen.
Baba ne ya shigo rai a bace yace duk sun ce bazasu tafi ba sai ummi tace ni zan kai ta da kaina barin tashi na shirya.
Suka fita shida yaya saadu suka bar mu ummi na shirin tafiya sai ga gwagon ta ta shigo gidan nan ta samu ummi na shiri take fada mata abin dake faruwa a gidan.
Gwagon tace baki zuwa zauna ki fake yaran ki ni aiki may nake da sai kin je da kan ki kamar baki da kowa duniya.
Ta juya zuwa gida din ta shirya tai sallama da yan uwan ta bata dauki lokaci ba ta dawo dama yaya yana waje suna jiran a fito dani.
Ummi na da gwago suka tallaboni zuwa wajen mota duk yan gidan mu sun zubo muna ido wasu na ce muna sannu wasu kuma sai kallon tsoro suke min.
Mama ne take tambaya dawa zamu tafi gwago tace da ita za ai tafiyan sukai mata Allah ya bada lafiya.
Aka kamani na shiga mota na zauna da kyat gwago ta shiga suna tsatsaye suna kallon mu yaya sani yai magana da cewa
A a bada mama za a tafi bane gwago tace ai sun gama nasu ranan wuya sai naka ai sai kawai yace ina zuwa barin zo dani za a tafi.
Ya shiga gida da sauri sai gashi ya fito da shirin shi uwarshi na kwala mashi kira yace sai ta dawo zan raka safiya asibiti ne.
Nan tashiga da fada wai sai yaje an halaka shi ya mai she ta baya amma una baiji ba mota ya daga yaya saadu yaja babana yana gaba mu muna baya muka tafi.
Mun bar ummi da jin bakar magana a gidan mussanman inna da ke ta zage zage dan ta daya bi.
Har saida ummi ta gaji ta bata amsa tace ai itama ba saye tayi ba kuma ba qurin yawon banza ta kwaso shi ba.
Yanzu kuce haka amma lokacin da kuke zuga baba a kan auren baku nuna bacin rai ba sai yanzu da ta baci kowa ya zamau jikin shi ya na nuna mata kyama.
Allah da ya jarebeta dashi bai manta da ita ba yana sane da halin da take ciki kuma kowan ku bai wuce nan ba ai.
Sai mama tace Rabi bai kamata ki fadi haka ba kuwa yaya zamu kyamace ta ai mun san ba ita ta dorawa kanta ba.
Sun dai cuce ta kuma sai Allah ya saka mata don Rakiya da danta ba suyi ba wallahi abaku yarinya da lafiyan ta ku illanta yar mutane ko waiwaye babu.
Yadda sukai wa yarinyan nan sai ubangiji ya saka mata ummi tace ai ba Rakiya kawai da duk wanda ke da hannu a ciki ubangiji ba zai barshi ba da yarda Allah.
Mama ta shiga damuwa da maganan ummi ummi ta shiga daki tana kuka tabi ta tana bata hakkuri ummi tace wallahi ba zan taba yafe wa ba yaya.
Kiyi hakkuri Rabi komai da kika gani ya faru da bawa Allah na sane dashi ummi tace amna yaya ya dace yadda kuke kyamatar yarinyar nan abin har mu ya shafa.
Wanan maganan na ummi shi ya kawo laushi ga mama har ta tsawaci yayan ta a daki kan su daina guduna haka bai da kyau su kyale inna dama haka take son gani fa kowa a gida burin tane taga an koma baya.

🧕🏿2️⃣7️⃣🧕🏿
YAR UWA NOVEL DIN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , , , , , , , ,
Yaya Saadu yana tuki yana min sannu yana jin wani tukuki a zuciyar shi gamay dani, yana ji kamar ya rabani da wanan ciwon gaba daya a jikina.
Tausayi nake bashi jina yake tankar yar uwar shi da suka fito ciki daya ba komai ya yasa yake ji dani ba sai irin girmama shi da nakeyi.
Wanda ko wayanda suka fito ciki daya basuyi mai yadda nake mai ya lumshe idon shi tare da nisawa.
Yace a ranshi Safiya nai maki alkawari zan dinga kula dake muddin ina raye insha Allahu zan baki kulawa daya dace.
Baba ne ke magana dashi amma baiji shi ba sai da baba ya sake maimaita maganan shi yaji shi.
Saadu kayi hakkuri kasa imani da addua a a ranka nima abinda nayi nayi nadamar shi ban wa yarinyar nan adalci ba.
Wallahi ban san abinda dan uwanka da mahaifiyar ku kuntatawan da suke wa yarinyar nan yakai yakai haka ba.
Ya nisa yace baba abinda ya faru ba wanda ya isa ya goge shi sai dai tabbas tun farko anyi kuskuren aura mata shi don sanin ko waye Ahmed din sam bai dace da kamilar yarinya irin Safiya ba don sani ko shi waye da akayi.
Yace yanzun haka karuwan da ya saki Safiya a kan ta ta gudu ta barshi bayan ta gama yashe shi kaf bata barshi da komai ba.
Shima yanzun haka din ya fara jinya don ciwon nasa ya fi na Safiyan nisa sai yanzu ne wai mummy take data sani dashi.
Bayan a lokacin da yake miyagun halayensa ta kasa tankwara shi ta dauki son duniya ta dora a kan shi.
Itama karuwan naji ance takai kwance a inda take tana bukatan taimako.
Ina zaune a bayan mota ina jin su na lumshe idona don bakin ciki sun cuce ni sun illanta min rayuwa na.
Mun isa garin muka nufi asibitin direct nan ya bar mu cikin mota suka fita dashi da yaya sani zuwa ganin likita.
Gwago ta ga mai ruwa ta kirashi ta saye muna tabani nasha baba na kallon yadda nake shan ruwan da kyat yana min sannu Safiya.
Gwago ne tace Allah ya isar maki yar nan ya saka maki da gagawa sim cuce ki sun illanta rayuwanki ga banza.
Baba yana jin ta hawaye yake na nadama yana gogewa yace gwago banyi wanan hadin da wata manufa ba a rayuwa na.
Sai don zumunci ya kara karfi a ysakanin mu iyayyen mu duk abu guda suke ta uwa ta uba shine da tazo da wanan zancen naga dacewan shi nayi.
Yaya Saadune suka dawo dauke da keken da ake sa maralafiya yace a kamani asa sama yaya sani ya ciciboni ina wai ya dora a keken.
Wani daki ne muka nufa ashe likita ke ciki ya dan yi min tambayoyi su yaya da baba ke amsa mai yai rubutu ya bayar yace zasu dan kwantar dani inda masu irin case dina suke in sha magani na kwana biyu a gani.
Aduniya ban san irin godiyan da zan ma bawan Allah nan ba sai dai ince Allah ya biya shi da alherin sa.
Nan take ya sayo magani da ruwan da za a kara min da abubuwan gina jiki kuma yace ba zai tafi ba sai yaga yadda jikin nawa ya kasance.
Baba kuka yake yana mashi godiya yace baba komai nai wa Safiya kaina nai wa don yar uwata ce ta jini.
Na samu kulawan da ya dace dani ashe ciwo in ba a dace da magani ba sai ai ta wahala dashi.
Don yanzu na rage yawa jin abinda nake ji a jiki na so sai sannu a hankali nake jin sauki yana shiga na.
Kwana biyar suka sallamay mu daga asibitin, har lokacin muna asibitin da yaya Saadu da yaya sani.
Sun bani magani amin register zan dunga zuwa ansan magani a wurin su tare da fada min mata kan da zan bi don kare kaina da sauran alumma da nake zama da su.
Aka bamu sallama na dawo gida da dan karfin jiki na sai da yaya ya sawo min abubuwan bukata na rayuwa yai muna sallama ana ta yi mashi godiya ya kama hanya.
Yan gidan mu na dan ga dan canji a wurin su yaran mama sun rage tsanar da suke min amma dai suna kyamana don in na taba abu sai an wake ko a yar a bayan idona.
Kauna tace ta fada min haka sai dai nai murmushi kawai na ware kayan amfanina a gidan ban amfani da kayan kowa har da na su ummi na don na nema masu mafita.
Da sannu ina warware wa na fara harkan kasuwanci na da mutane da farko suna kyamar saye daga baya kuma suka fara saya.
********* ********* *********
Yaya Saadu daya bar wurin mu gida ya koma direct tun da ya iso jikin su ya basu cewa bai cikin dadin rai.
Sai da ya huta yai wanka yadan taba abinci kadan ya tashi ya fice gidan yaya Ahmed ya nufa.
Ba kalman dake mai yawo arai sai da ya shigo dakin ummi ina kwance na dago nace dashi yaya ya Ahmed ya cuce ni
Ya illanta min rayuwa ya kashe ni da yarinta na ya mai dani abin tsoro a cikin yan uwana da gari sai ya runtse idanuwan shi.
Yai sallama yana ciki kwance ya taso da kyat ya bude kofan gida yaya saadu ya shigo ciki yana mai wani irin kallo.
Zama yayi yai shiru ba tare da yai magana ba shima wuri ya samu ya zauna yana kallon shi don yasan magana ya kawa shi .
Don tun da na bar gidan ba sake zuwa gidan ba sai yau da yazo ya tunkare shi akan magana na.
Ya dan dago ya gyara zaman shi dakyau baiyi magana ba saida ya dan furzo da iska daga bakin shi ya numfasa yace.
Kana da labarin Safiya bata da lafiya har ciwon yai tsanani sai da naje na kaita asibiti, yace dashi ban sani ba, banda labarin ta tun tafiyan ta inbada ta haihu kazo kafada muna ba, sai yace dashi
Ahmed ka cuci Safiya ka illanta rayuwan karaman yarinya a banza saboda son kai irin nata ka zuba mata kanjamau tana ta wahala a rayuwan ta.
Ahmed din yai mai wani kallo na tambaya sai yace dashi na illanta ta kamar yaya ?
Yace kasan Safiya tana dauke da HIV kuma kaika saka mata shi don dai kai kafi kowa sanin kamilar yarinya ce ita.
Ahmed din yace tasan dai inda ta samo abinta don dai ni banda komai normal nake kowa ya sani.
Saadu yai saurin cewa normal kake kamar yaya aiko makaho ya lalaba yasan may kake ciki.
Sai yace dashi sheri zakai min ko may ?
Babu sheri anan .
Don mummy da mahaifin safiya sunyi kuskuren aure maka kamilar yarinya kamar safiya don sun san halinka na boye suka aure maka ita hakana.
In ma shi mahaifin nata bai sani ba ita mummy mu ta sani saidai ta boye masu ne.
Ahmed ba yadda ban yi da kai ba ns baka shawara ka gyara rayuwan ka ka nisan ta kanka da fasikanci.
Ba abinda ya zama ma dan adam dole may kake nema gun mace kai da Allah ya hore ma mace yarinya karama a gida.
Sai da na fada ma wanan matar da ka aje a gida ba alheri bace gare ka amma kaki ji yanzu gata ta sa ka cuci yar mutane.
Ya dafe kai gami da lumshe idanu yana tunane a ran shi yana hango irin wahalan da nake yi da ciwon a ranshi.
Ya hango surana da muryana da irin karfin halin da nake dashi wurin turzawa sai kuma muryana idan ina son abu da tsabta na.
A take ya ji jikin shi ya mace wani na dama da tsoro ya shige shi amma sai ya dake yace wa kanin nashi.
Wai may ya damay ka da nine rayuwan ka ko nawa kuje can kai da ita ku nemi inda ta kwaso cutan ta.
Please ka rabu dani don Allah da zancen wata safiya can kwakwalwata yana son hutu dan Allah kazo min da wani zancen ka na bazanza.
Yace okay haka kace ya mike ya fita zuciyar shi kamar wuta yake jin shi ba abinda yake tunawa sai halin da ya barni ciki.
Gidan su ya koma inda ya samu mahaifiyarsu da zancen, tun shigowan shi ta sha jinin jikin ta don tasan da abinda ke damun shi.
Sai daya zauna take cewa dashi ina kafito ne aikai ma abin kari baka nan ka fita.
Ya nisa yace da ita daga wurin Ahmed nake mummy kin san Ahmed ya cuci yarinyar nan safiya a rayuwan ta .
Tace may ya faru kuma da Safiya din zancen wai har yanzu bai kare ba a gare ka kana bin dan uwanka da maganan ta rayukan ku na baci ga banza kasan fa yace bai mai da ita.
Mummy yazu wake batun komawan ta bayan ya illanta ma yarinyar mutane rayuwa har abada.
Wani kallo taimai nason jin ba a sin maganan shi yace Safiya fa HIV ne gare ta kuma ba kowa ya samata ba shine.
Innallilahi ta furta da karfi tace H may yanzu kana nufin har shi Ahmed din yana dashi komay ?
Yace ai yasan yana dashi mugu shiyasa ya sake masu ya don kar asirin shi ya tonu.
Hannu ta fara tafawa tana salalami tana cewa wai ta shiga uku ta lalace Ahmed na da kanjamau ko may ?
Yace mummy Ahmed kawai kike ji mawa ita diyan mutane da kuka cuta fa ita ba abin tausayawa bane ?
Sai ta kama inda inda tana cewa ai dukkan su abin tausayawa ne itama ai dole a tausaya mata.
Yace mummy dake da mahaifin yarinyar nan kuna da kamisho cikin ciwon yarinyar nan.
Amma shi mahaifin da yasan kun cuce ta ai kuka yake kuma yana nadaman abinda kuka kulla sai dai ko kadan bai kufulece kiba.
Amma ke gaki yanzu dan ki kawai kika sani kika damu da damuwar shi ita ko ko oho ?
Idan zaki kirashi ki masa magana yaje ya duba diyar mutane tun wuri ki masa.
Ahmed din bai shigo ba saida yamma ya shigo rai a bace shi aladole an bata mashi rai.
Nan ya zauna da uwar ta dauko mai zancen da cewa abinda naji da gaske ne ko karya ne yazo ya fada min.
Nan ya shiga fada wai Saadu na binshi da mugun nufi har yana lakaka mashi mugun ciwo.
Tai ajiya zuciya tace yanzu naji magana amma yazo ya tayar min da hankali ga banza ya hanani sukuni a rayuwana duk yinin yau ko ruwa ban sha ba.
Mummy kazafi yake min ta san ida ta dauko cutan ta can ni bani da masaniya akan haka.
Uwar ta hau ta yarda da maganan shi nan ta shika fadin mugun zance akaina da mahaifana yana tayata fadi.
Sun yanke yiwa yaya Saadu kaca kaca kan maganan da yake so ya dora wa dan uwan nashi wai yana son ya bata mashi suna ga banza.
Ya shigo sunyi kaca kaca dashi a gaban mahaifiyar tasu tana tayashi zagin shi yace dasu OK haka kukace .
Time will soon come da gaskiya zata bayyana kan ta indai ana boyon komai ba a boyon ciwo ai muje zuwa ni daku.
Macucin banza da wofi kawai kawai ka cuci yar mutane kazo kana wani kamay kamay azzalumi banza da wofi sai Allah ya tona maka asiri ai.
Yace dai naji kuje can ku nemi wanda yasa mata cuta idan ma kaine ka fito fili kafadi yafi don naga zakewan ka yayi yawa akan ta dama.
Wani irin shock ya kama shi ta juyo yana duban dan uwan da mamaki sai kuma yai murmushi yace ni ba dan akuya bane irin ka.
Ina dai kokarin sauke hakkin da kai ka kasa saukewa ne akan ta amma baku ganewa sai lokacin ku gane gaskiya inyayi.
Ya fice ya basu wuri bai kara shigowa gidan ba har ya tafi bai koma wurin aikin shi ba sai da yaje gidan maman biyu ya sanar da ita halin da nake ciki.
Da taji hankalin ta ya tashi sosai ya kwantar mata da hankali da cewa ya kaini asibiti yanzu ina samun sauki an daiyi arziki cutan baiyi nisa sosai ba aka tare shi.
Ranan haka ta wuni a cikin bacin rai tana ta tsine ma Ahmed din da uwar shi ta ma kasa kirana don in ta kirani ma may zata fada min banda karin tashin hankali.
Sai dai ta kasa daurewa bayan kwana biyu ina zaune daki da ummi wayana yai kara na dauka na ga itace take kirana.
Na dauka tare da fadin Anty kwana biyu kina a raina ban samu kiran ki ba banda lafiya ne.
Asanyaye tace safiya naji komai yayan ki yazo nan ya fada min halin da kike ciki Allah ubangiji ya isar maki.
Sai na kama kuka tace bari kuka haka Allah ya kaddara da rayuwanki Allah ya nufe ki da rayuwan BAHAGGON AURE.
Komai da bawa ya gani yana cikin littafin sa rubuttace ne ga ubangiji dama sai dai muyi fatan Allah ya baki lafiya.
Nace amin anty tace ki kwantar da hankalin ki ki sha magani kada kiyi wasa da sha magani sosai don kada cutar yayi galaba a kanki.
Nan nake jin yadda yaya Saadu suka kwashe da yaya Ahmed din da uwar su tace min barsu ai Allah ba azalumin kowa bane.
Da sannu gaskiya zatai halinta in sun ce su mahainta ne ciwo ai ba a boyon sa shi zai baiyana kasa agani watarana.
Ta dade tana lalashina ina kuka tace ina ummi nace gata a kusa dani tace inba ummi waya su gaisa.
Nabata wayan suka gaisa tai mata jajen akan abinda ke faruwa tare da kwantar mata da hankalin ta takumace duk lokacin da muke da damuwa mu tutube ta zata taimaka muna.
Nai sallama da ita har take tambaya na sana, a ta nace yana nan ina yi tace to karki daina shine zai tallafa maki kina samun dan kudin sayen abinda zai gina maki jiki kiji ko nace na gode kuka ne yaci karfina na kasa magana na kashe wayan ina tunane a raina.
Bayan mun gama wayan na dade ina kuka ina tunane a raina karshe na hakkura na kyale na barwa Allah komai shi zai mun mafita da yardan ubangiji.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , , , , ,
🧕🏿2️⃣9️⃣🧕🏿

Wurin motar muka nufa gaba dayan mu saadatu na kwace a ciki sheme kamar bata numfashi kuka muka saka a lokaci daya.
Dayan dan sanda ke fadi ba kuka zakuyi ba ayi niya akaita asibiti tun lokaci bai kure ba a take baba da yaya sani suka fada motar da inna.
Suka nufi asibiti da ita har lokacin mu ba mu san may ya samay taba asuban fari baba ya dawo gida rai a bace.
Da mukaji shigowan shi lokacin mun tashi muka firfito waje mama ne ke cewa malam lafiya may ya faru da Saaden ne ?
Cikin takaici yake fadin fyade akai mata wai kuma bata san ko su waye ba tadai ce sunkan zo cin kasuwa su sai sana ar ta.
Kowa ya dafe kirji da firgici a cikin mu ta sake tambayan shi da ta farfado dai ko yace a takaice da ta falka yanzu sai dai bata san inda take ba.
Nan ya shige ya barmu a cikin tashin hankali ba kwanta ba da mukai sallah cikin kayan abinci na na diba na hada masu abin karyawa.
Na gama da wuri muka isa asibitin tana kwance sharkaf kamar bata da rai Inna na zaune a gefen ta cikin tashin hankali.
Munyi mata sannu da yaya mai jikin tace da sauki na bata abinda nazo dashi nace su mama suna nan tafe.
Maganin da likita ya rubuta ake neman kudin saye baba yace baida shi inna kuma tace dama dan abinda ke gare ta ne nan ta juya dashi sukai sana a.
Na bude post dina na kirga kudin na bayar sai lokacin aka sawo magani da ruwan da za a karamata.
Anyi mata allurai da sauran abinda ya dace a taimaka mata dashi bayan kamar awa daya ta farfado da kuwan wayyo inna zasu kashe ni.
Tana fisge fisge nan dai muka taru muka taushe ta nurse tazo ta kara ba ta allura sai aka samu tayi barci.
Ranan dai asibiti muka wuni ba dadi kafin wani lokaci labari yabi gari mutane sai shigowa suke yi dubata.
Suna asbitin kafin a sallamota sai ga yan gidan mijin da zata aura wai a basu kayan su yace ya fasa dama itace ta biyu zata shiga.
Wani sabon tashin hankali kuma nan suka shiga hayaniya da su mama tace aiko baku da imani kwa tsaya har a sallameta dai ko koma may ye sai ayi shi hankali kwance.
Nan dai aka samu suka tafi suna bakaken magana wai dama ai shi yaji yagani a kanta ina ba haka ba me zaiyi da ita ma.
Andai samu an lalaba su suka tafi baba ya shigo gidan ake mayar mashi ranshi ya baci yace ai sai su bari inda ta dawo ita data karbi kayan su sai ta mayar masu da abinsu.
Inna na can labari ya samay ta nan ta sa hannu akai tana kuka wai so suke su tozarta ta in bashi ba ai wanan abindaya faru da yar ta kaddara ne kwai.
Ji fa inna na kalleta a raina nace ashe tasan akwai kaddara shine ni taki yarda da nawa kaddaran da yazo min.
Na yar tane abin yarda ke nan mu dai hakkuri muka bata kawai muka bar dakin muka koma waje muka zauna.
Washe gari aka sallamo su suka dawo gida an basu wata uku su koma ai mata awon ciki dana HIV nan hankalin inna ya sake tashi sosai tana kuka tana fasin Alah ya tsine ma wa yanda sukaiwa yarta fyade.
Da yamma bayan sun dawo gida tana cikin jimamay maganan likita sai ga ya gidan mijin na saade sun dawo wai sun samu labarin an sallamata ta dawo gida shine suka zo karban kayan su.
Nan suka hau da inna tace baza ta bayar ba aiba ita tace ta fasa ba don haka bata yarda shi mijin yace bai yi ba sai dai in sherin yan uwan shine.
Suka tafi basu gane komai ba nan suka barta ta na halakatai a tsakar gida wai basu da imani yarinya na fama da abinda ya samay ta zasu zo masu da wani fitina kuma.
Mu dai muna daki muna sauraren ta sai baba ne ya shigo yace da ita don may bazata basu kayan su ba tun da sunce sun fasa.
Nan ta shiga kamay kamay Ummi tace dani wasu kaya kayan da ta sayar wasu kuma yarinya ta sa ajikin ta.
Nace ashe akwai cakwakiya don naga mutanen basu da alaman mutunci tare dasu.
Ummi tace na dai kallo kawai ai mun yi imani da mukai mata jajen abinda ya faru in wasu ne aiko kallo bata ushesu ba.
Da itace ba abin da zai sa ta kalle mu dama haka Allah yake ai yanzu in tana da imani tayi ai ta daina aibanta kin da takeyi a gidan.
Murmushin takaici nayi nace badai inna ba ai laifi tudu ne katake naka ka hango na wani watarama kiji tayi min fade in halin ta ya tashi.
Ummi tace dako tajini don yanzu nima Allah ya bani abin fada mata ai kowa ya ji da nasa abin fade.
Kwana biyu Saade bata ko iya fito tsakar gida koda yaushe tana daki ranan mukaji Inna na mata fada wai ta fito ta kunkumay acikin daki.
Mai ciwo ma ta fito tana walawa sai ita zata tsiri zaman daki muna jin ta ummi tace anzo wurin .
Sai ko ummi tai wuf tafita waje tace may zaki fada min bayan Allah ya nuna maki bakin halin ki tun a nan duniya.
Ai ni gara tawa ansan gidan miji ta kwaso shi ke ko fa daba a ko san suwaye sukai mata kaca kaca ba a gari.
Baba yana jin sun fara ya fito tare da daka masu tsawa yace ke Rakiya yaushe ne zaki hankali yanzu duk wanan isharan da Allah ya gwada maki bai isheki ba sai kin tsaya jan magana.
Sai cewa Inna tayi Allah ne ya nufe ta da ganin haka a rayuwan ta kuma ba zai zama abin fade ba ai.
Yace ita ko itace ta saya da kudin ta ko ke in kina da kunya har zaki kawo irin wanan magana haka wanan abin bai isheki ba.
Ko tafiya nake na koma ana gwada ni a gari banda sukuni a cikin mutane gida kuma babu dadi.
Wanan karon bazan lamunce ki ba duk kika haddasa min fitina a gida zan dauki mata mumuna akan ki ne.
Jin abin daya ambata yasa tai sanyi don ta zaburo wa ummina sosai kamar zata cinye ta danya ya kara da fadin .
Ke wata irin mace ce wata ukun da aka bamu mu koma baiti ba har kin shiga goranta ma wata halin da take ciki ki bari a san makomar yar taki tukun san nan ki samu abin fadi.
Dama Inna bata son zancen komawa asibitin nan don ko yaushe tsinewa likitan takeyi akan yace su koma a sake auna ta.
Nan ta shiga cewa insha Allahu babu abinda zai faru da ita sai alheri na gane kaima so kake wani sheri ya faru da ita a gidan nan su zama daya da yar ka.
Tai ta sababi ba wanda ya sake kulata har tayi ta gaji ta koma dakin ta tana mai zuba mugun addua ga masu fyaden da masu zagin yar ta.
********* ********** *********
Ranan ina waki tufafin mu da rana naji anyi sallama muryan dai ta wace na sani ne amma kuma may zai kawo ta nan.
Naji tana tambayan ina nan da sauri na dauraye hannuwa na fito daga inda nake wanki mama biyu ne tare da yan tagwayen ta.
Sun girma sun kara wanj irin kyau dasu da uwar su baki daya ban san lokacin da nai cikin suba da murna na sai fadi take alhamdullah.
Naji dasin yadda na samay ki alamu ya nuna min kina ahan maganin ki ke nan mun shiga dakin mu na rasa ina zan sakata.
Na fara gabatar ma mutanen gidan mu da ita suka shiga gaisawa da ita suna tambayaan ta yara da maigida nan na fito na aika a sayo masu fanta kwalba da ruwa mai sanyi.
Tace no ki barshi ashe garin naku yana da nisa haka ne yanzu zamu wuce dama nayi alkwarin zanzo na duba ki ne tunda ke kin yada mu.
A kunyace nace ban yada kuba anty yanayi dai ne yazo da hakan mun dan taba hira tamike tace zasu wuce don dare yayi yau zasu koma dama buki tazo yi arewa shine tace bari tazo ta gane ni.
Ina ta rawan jiki na rasa may zan basu tace huta abinki bashi ya kawo ni ba tunda nagan ki alhamdullahi.
Ta kawo kudi tace in bawa ummi na ga tsaraba mai yawa da ta kawo muna a cikin buhu ta fito tsakar gida taba su inna dubu ashirin su raba.
Takawo wani tace aba baba in ya dawo nafita na rakata bakin motar ta anan take cewa dani idan na samu lokaci indan leko wuein su ina kuka ta rungumay ni tana share min hawaye.
Nan dai suka tafi suka barni cike da kewar au gani nike abun kamar a mafalki wai anty ce a garin mu yau.
Mun koma naji inna na fadin tunda nike ban taba rike ko dubu biyar ba na kaina a rayuwana yau ga bakuwar arziki ta zo mun dashi.
Ban tsaya ba na shiga dakin mu na bude tsaraban da ta kawo min turmin zani guda uku da sauran tarkace ne a ciki nai murna sosai tare da yin hamdala.
Mun dade muna hiran ta ina fadawa ummi irin taimakon da tai tayi min acan lokacin da nake cikin bukatan aimin din.
Ummi tace Allah ya saka mata da alheri daga waje naji mama na fadin mukan ai Safiya kin jawo muna arziki har gida wannan abin arzikin da may yai kama.
Baba ya dawo gida ummi ta bashi kudi da akace a bashi din ya shiga murna da saka mata albarka.
Yana ta godiya yace haka Allah ke ikon sa yau na tashi tun shekaran jiya banda ko kobo a aljihun nan yazu ga kyauta na samu daga sama.
Kwana biyu ana facali a gidan mu kafin su kare nidai ina kallon su kawai ba kunya ba tsoron Allah a tare dasu.
Haka rayuwan yake gudana dan dama yanzu bakin Inna ya mutu ko tayi ma sai a bayan mu don da ta fadi ummi take mayar mata.
Sai dai indan wani abin can na kishi ya hadasu daban amma dai ba gori ba don yar ta na gida kamar mujiya da ta fita sai a kama nuna ta.
Wasu ma harda kari wurin bada labari zancen nata suke karawa don maganan yai dadin fada shiyasa Saaden bata son fita ko ina koda yaushe tana gida zaune.
Yaya Saadu yazo diba mu bayan kamar wata shida da tafiyan maman biyu shima yazo muna da abin arziki kamar yadda ya saba kawo muna idan zai zo.
Sai dai wanan karon da wata yazo yarece dai amma yace matar sa ce da ya aura ya kawo muna ita taga gida.
Baba yace ikon Allah kayi aure bamu sani ba a gurina matar tashi ta sauka don bata jin hausa munyi dan hira da ita kwanan su biyu damu sukai muna sallama suka koma.
Kafin ya tafi yake min maganan aure wani iri naji don bayi zaton zai min wanan maganan ba ya kula da kaduwan da nayi sai yace.
Safiya ki daure ki samu wani mai irin matsalar ki ki aura hakkuri zaki yi bawai don kina so ba sai dai don kare mutuncin ki.
Nai shiru na dago kaina idona na zubar da hawaye nace ni yanzu yaya ina zan samu miji a haka yadda nake kowa fa garin nan ya san zance na ba inda inna bata kaini ba .
Yace ai kinji abinda na fada mai irin matsalar ki zaki aura acan gurin ansan maganin zasu iya hada ki da wani mai wanan lalurar idan hakakin ki ya kwanta sai ki daure ki aure shi.
Hakkuri zaki yi da almarin kaddarane kuma yadda kikai tawakkali yana dakyau sosai haka ake son musulumi dayi.
Shima Ahmed yana can ciwon yakai shi kwance sosai sai da nazo ne na kaishi asibiti da yana gida kwance yana karyan wai sammu ne.
Nai dariya nace shida yace baida shi yaya akayi haka kuma yace kyale su don Allah wai saida muka je asibiti ya baiyana yanzu ne mummy ke fadin an cuce ki.
Da wani ido zata kalli baba dashi bayan duk wahalan da kika yi bata zo ta dubaki ba har yau yanzu dai suna can na barta dashi ban san yadda zasu karata ba nidai na kaishi asibiti yadan samu sauki yanzu yana nan gida.
Allah ya sauwa ka nace yace ko zaki hakkura ki koma mai kiyi hakkuri ku zauna hakana.
Nai saurin cewa Allah ya sauwa ka yaya ida bakai ka fada min haka ba yau da sai an raba mu amma kaine ban cewa komai.
Yai dariya yace Allah da zaki hakkura ki koma yanzu ai yayi nadaman abinda yai maki ya koma yana daya sani ita ma Lilliya naji ance an kwashe ta zuwa garin su okene.
Nace yaya don Allah mu bar hiran su kazo zamu rabu da dadin rai kuma kana son ka bata tsarin nace ai zan shigo lagos indan anyi daidai kana nan sai na karasa wurin ku naga mazaunin ku.
Yace yaushe kenan nace idan baba ya barni sabin wata nake son zuwa nake fada mai zuwan maman biyu da tace in dai je in mata kwana biyu yace idan zaki zo sai ki sanar dani tunda ga waya.
Nan suka kama hanya suka tafi ya barmu cike da kewar shi yaya Saadu mutum ne wanda yasan kan sa yasan hakkin zumunci.
Yanzu fa zuwa yayi ya kawo muna matar da ya aura wai taga garin su da yan uwan shi don tasan yana da asali.
Rayuwa yaci gaba muna a gidan dadi ba dadi haka muke hakkuri mu zauna a cikin sa anyi bukin yar wurin mama salin alin mun sha buki inna na kallo ita da tasha alwashin yar ta zatayi aure.
Sai gashi Allah yai nashi ikon a kan ta ba maganan aure gare ta sai in Allah ya kawo mijin nasan dai ba a karkaran mu ba kan don ba inda zancen ta bai kaiba har da makwabtan garin mu.
Dole muka koma fita tare da ita tun uwar na fada har ta gaji ta saka muna ido don yanzu haka muka koma kamar aminai da ita.
Sai dai ban yarda tasan sirina don su ba abin yarda bane ga mutane sherin su yawa gareshi don ta gado uwar ta da hassada sosai.
Idan wata ya zagayo sai in tafi amsan magani acan wani ya leke min wai shi sona yake yi har da zuwa gidan mu.
Ranan da ya fara zuwa kin fita nayi sai da yaya sani ya shigo na fita bayan wuce wanshi nace da yaya sani ni ban yarda da shi bane.
Don da ganin shi manemin mata ne sosai don tsarin shi ya tabbatar da hakan yana magana yana wani iri.
Niko yanzu ba zan yarda na koma wa wala ba bayan na fito gare shi yace ki dai kwantar da hankalin ki ki bishi sannu mu gani.
Ni dai a raina nasan abinda na yanke shawara a kai so nake baba ya yarde min in tafi wurin maman biyu sai ranan da suka gane ni.
Amma ban fadawa ko ummi na ba na bar zancen a raina don naga ko ita tayi aman na da zuwan mutumin wuri na su ala dole na samu mai sona da halin da nake ciki in dai yi aure ko yaya ne su nasu kawai kenan garesu.
Basu tunanen hali na gari ko wani irin rayuwa zan je kuma na tarar ga ciwo ga taulalin miji a kaina.
Shi yasa na yanke wa kaina shawaran barin gari salin alin batare da kowa yasan manufana ba a gidan.
Don in sun sani ba zasu yarda in yi nesa da suba ko kadan shiyasa na bar abin a raina ni kadai.
Sai in lokaci yayi su san manufana idan kuma basu gane ba a tafi a hakana duk inda nake sarin kaya a birni tare da kanina nake zuwa don ya iya ya saba dasu don ko na tafi bazai sha wani wahala ba ya iya.
Harkan kasuwan ci na tare dashi muke yi yasan kan komai da yadda muke aje uwar kudi mu fidda riba daban duk ya iya.

🧕🏿2️⃣8️⃣🧕🏿
YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE..........
Matsala na yanzu Inna ce tabi gari tana bada labari a kaina wasu har zuwa suke yi ganina a gidan mu.
A cikin gida kuma ita da yaran ta ne suka tsan gwamay ni a gidan ko zama nayi a wurin sai sun share ko su goge zasu zauna.
Idan na taba ubu bazasu taba ba koda sunyi niyar taba abin sai su fasa.
Ga sake habaici a tsakar gida wai an kwaso cuta an zo za a lakaka masu sudai an cuci rayuwan su wallahi.
In naji su na kan yi murmushi kai a fili amma cikin raina nakan ji zafi da dacin zuciya ya kama ni.
Wani lokaci kuma idan sunyi man nakan shige daki inyi ta kuka sai ummi na tai min nasiha nakan yin shiru ko inji dan dama da sanyi.
Har aikin da kan taya ummi sai suka tsani cin abinta idan na dan taba wani abu daga ciki ko ta gama ta basu sai kaji ana kiran almajiri a juye mashi.
Da na gane hakan sai inyi zamana kawai a daki bana fitowa taya ta aikin ita ummi ta fahinci manufa na sai tace min ki zaman ki a daki yafi maki har kiji sauki.
Ranan ina daki kwance ina karatu akai sallama ina jin bakuwar suna gaisawa da mutanen gidan mu.
Sai take tambayan Safiya tana nan kuwa aka nuna mata dakin mu ta nufi can suka bita da kallon mamaki yar gayu da ita zata zo wuri.
Jin ta ambaci suna na yasa ni saurin tashi ina da sauri ina daga labulen dakin mu don in ga ko wacece take nema na din .
Bakowa bace sai Amina kawa na da mukayi karatu tare da sauri na sake labule na nufo ta muka rungumay nuna da ita sai yan gidan mu sukai tsaye cirko cirko suna kallon mu.
Na san ba komai bane suke ma mamaki sai yadda ta rugumay ni ne su gashi suna gudu na agidan suna gwada min kyama a fili.
Muka shiga dakin mu nan na aika ka sayo mata pure wata mai sanyi tana cewa a a nace ta dai bari a sayo mata bayan yaron ya fice sayen ruwan ne.
Tace dani ashe kuma haka abin ya kasan ce dake alamarin yazo da matsala haka Allah ya nufa Safiya kiyi hakkuri nima da na shigo jiya mama na ke fadamin abindake faruwa.
Safiya jiya da naji maganan nan ban iya barci ba amma kuma danaga masu shi yanzu ba a gane su a fuska sai na barwa Allah alamari .
Gaskiya naji dadi yadda nazo na samay ki baki gala baita ba gaki har jikin ki na dawo naji dadin haka kwarai da gaske.
Nan na fara bata labarin abinda ya faru tun farko sai cewa take subbahanallahi amma wanan mutum baida tausayi baida imani ko kadan.
Tana share hawaye tana fadin Safiya Allah ya duba maki alamarin ki ya tausaya maki wanan BAHAGGON rayuwan da kika taso a cikin shi.
Nace da ita amin don yanzu idona ya kyan kyashe da kukan nayi nayi nagaji sai dai na kasa daurewa ganin tana kukan nima kukan nake yi.
Sai ummi ne take bamu hakkuri tana cewa haka Allah ya nufa ba yadda banki auren nan ba amma mahaifinta da matan shi suka nace da sai tayi.
Yanzu da wahala ya cika da ita duk sun watse din sa muna ido da ni da ita a daki sun koma suna kyamatar ta a gidan.
Safiya tace ai wanan jahilci ne ba a gudun mutum sai dai ayi taka tsantsan wurin yana yin zaman takewa.
Amma in ana gudun mutum tunane sai ya shiga maishi sai ciwon ya samu galaban samun wurin yin barna da kyau.
Mun dade da ita a gidan nan ta wuni wurina nai mata dahuwa taci zata tafi na rakata bakin kofan gidan mu.
Zan shigo gida na hadu da Inna ta yafa zata fita ta wuce na shiga gida ashe tabi bayan Aminan ne ta tsaida ita.
Tace keko yar nan baki san may ke faruwa da Safiya bane nagan ki wurin ta har da cin girkin da tai maki.
Amina tai murmushi tace kwarai kuwa na sani shine ma ya kawo ni wurin ta ai don in mata jajen abinda ya faru da ita.
Inna tace baki gudun ki dauki wanan cutar kema a wurin ta don ance saurin yadduwa ne dashi.
Amina ta girgiza kai tace ba haka bane gaskiya a samun sa ta hanyar saduwa kamar yadda ita Safiya ta samu daga mijinta.
Sai kuma ta wurin amfani da zera ko masilar kitso ko allura idan jinin maishi ya shiga jikin ka to kaima kana iya samun wanan cutar bayan haka zaku iya hurda ko wani iri da mai wanan cutar kamar kowa.
Inna tai mata wani irin kallon rashin gamsuwa da maganan ta tace ni dai na fada maki gaskiya don naga kamar baki sani bane.
Ashe kin san komai idan iye iyen ki ya kai ki kika dauko ma kanki cuta ke kika sani ninayi nan.
Amina tace da ita dakata inna sai ta juyo ta tsaya tace da ita wanan abinda kuke yi ya kamata ku dai na wanan halin da kuke nunawa safiya.
Inna ki sani idan yarki ce ta shiga irin wanan halin yaya zakiyi sai ta tofar da miyau tace bakin ki ya sari dutse Allah yai ma diyana tsari.
Tace kin gani itama fa ba da son ranta ta samay shi ba kin sani ya kamata ku jawo ta a jiki kuna kwantar mata da hankali ba ku dinga aibanta ta kuna hattaran ta ba haka.
Don Allah Inna ku daina wanan abin da keyi sai ta tare ta dacewa mugun halin uwarta ce ya bisu ai kadan ma suka gani ai.
Allah ya kyauta Amina tace da ita ta wuce tana bakaken magana Amina dai tabita da kallo tare da girgiza kanta kawai ta wuce.
Inna ta dawo ido mirsisi tana zage zage a fakaice sai kuma ta shige daki suna magana da diyan ta kus kus kus.
********* *********
*********
Ina zaune a dakin ummi tun safe da na fito van sake leko waje ba ina dai jin hayaniyar mutanen gidan mu daga waje suna harkokin su na yau da kullum.
Ba abinda nakeyi sai tunane abu biyu ne ya tsaya min a raina na farko in na tuna muamula na da mutane yadda ya ja baya yanzu.
Sai na biyu yaya rayuwa ta zata kasance a haka zan zauna dakin uwa ta in kare rayuwa na ba wani abin ci gaba da zanyi wa rayuwana.
Na lumshe idanuwa na cike da takaici take naji hawaye na zubo min ashe ummi ta shigo dakin ban sani ba tana tsaye a kaina nadan wani lokaci.
Muryan tane yasani bude idanuwa tana tsaye a kaina tana kallo na cikin bacin rai da ya baiyyana a fuskan ta.
Ta lumshe idanuwan ta cikin takaici ta juya tana neman abinda tazo dauka a dakin lokacin muryan ta yayi rauni ta fara magana ba tare da ta dubeni ba.
Watau so kike kuma ki jawa kanki sabon matsala a rayuwa baki san ciwon kan ki ba ana fada maki ko yaushe kiyi hakkuri kibar wa Allah almarin ki.
Amma sai ki zauna a daki ki ta kuka kina tunane ke kadai ana fada maki gaskiya baki dauka to maye amfanin zama na a gidan kina kara min bakin ciki ?
Ki rungumi kaddaran da ubangiji ya jarabe mu dashi sai Allah ya tausaya maki yai maki mafita ta inda baki zata ba.
Kuka nake yi sosai nace ummi ba hakana bane in na tuna da irin zaluncin da sukai min ne sai na kasa hakkuri a raina.
Tace sai kin fitar dasu a ranki ki rungumi kaddara ki mai da alamarin ki ga ubangiji kamar yadda kowa ke fada maki a kullun duk masoyin ki abinda kawai zai fada maki kenan a yanzu.
Don kaddara ya riga fata gare ki ki dinga fita kina mu amula yadda kowa keyi a gidan gida na ubanki ne babu mai koran ki cikin sa koshi bau isa ya kore ki ba tunda shi ya jefa ki a wanan halin.
Da sannu zasu janye manufarsu a gare ki kowa a dawo daidai dama zaman gashi nan dai ne anayi har duniyan ma nawa take ga dan adam.
Ba abin mamaki bane ki mara lafiya ki rayu mai lafiyan ya mace ga Allah duk wanan sau nawa yana faruwa ga dan adam.
Don haka har kulun nake godewa Allah da ba wurin wani hanya mara kyau kika kwaso wanan cutan ba .
Har kulun ina godewa Allah daya bani yayan da suke da hankali da hangen nesa Allah ya kara shirya min ku sak na amsa mata da Amin.
Naji dadin wanan nasihan sosai na ummi kiran da a kai mata a waje ne yasata fita dakin lokacin na sauke ajiyan zuciya na mike tsaye.
Washe gari tun da safe da nai sallah ban kwanta ba na fito na share tsakar gidan mu tas baba da ya dawo massalaci ya gani ina wanke wanke yake min sannu.
Ya zuba min ido cike da tausayi ya wuce dakin shi yana tunanen a ran shi yana daya sani ya barni na auri zabi na gashi yanzu yaron ya zama wani abu a gari lokaci guda ya samu wurin aiki mai kyau yayi aure shi anan garin.
Haka naci gaba da rayuwa zaune a gida in lokacin karban magani yayi in shiga mota in je in karbo idan zan dawo na dan riko ma yaran gidan mu tsaraba.
Sai kaji suna cewa yaushe ne zan tafi birni in sayo masu abu kaza dana taba sayo masu acan.
Yanzu hankalina ya kwanta ina samun walwala sannu a hankali har nakan fita zuwa gidan gwago da yan uwan mahaifiya ta da kawaye na don sun gaji sun daina gudana.
Masu son kaya har gida sukan biyo ni don saya ko ba da sautu a sayo masu wani abin idan suna so.
Haka sai mu a mula na ya dawo daidai da mu tane ina hurda da kowa babu tsangwama ko hattaran da suke min da farko.
Na tayar da sana a ta zanga zanga dashi nake samun ina juya rayuwan mu harda na kanne a gidan don haka muka koma bamu da wata damuwa a tare damu.
Sai dai har yanzu wanan muguwar akidar ta inna nan a ranta da wasu diyanta abin yana damu na sosai yadda suke nuna min tsana a hili tundai babban yar ta da ake shirin yiwa aure.
Don da dan abu ya hada mu da ita yanzu zatai min gori da ciwon dake jiki na zata tsaya tai muna tas a tsakar gida babu kunya ko jin tausayi na ga halin da na tsinci kaina a ciki.
Yau kasuwan garin mu yaran gidan mu masu sana a suna ta sha anin sana an su da zasu fita dashi cin kasuwan.
Maganan yara ya taso sai rikici ya hada su da yaran dakin mu dana Inna da diyan dakin mu subbahanallahi ranan naji tonon asiri da ban taba ji ba a wurin inna kamar dai ta dade tana shirya muna ne.
Abin da yafi kona min rai shine irin zagin da take min da cewa naje na debo cuta don mugunta ina son in yada ma gida kowa ya samu.
Haihuwana ya zame masu bakar haihuwa a gidan da barnan suna ko fita sukayi sai ai ta nuna su basuci ba basu shaba
Wai tun auro ummi gidan ya juye masu da tsiya basu kara gane gidan nasu ba.
Tai ta fadan maganganun har tayi ta gaji karshe ta juya ga ummimu nan sukai tayi tace itama ai ba sayen shi tayi ba aure ne yaci ta .
Inna tace oho dai da ana muna sallo wai itace mai karatun boko a gidan nan anyi aure a birni, to yanzu ina bokon yake ?
Wai ina zaune a gida haka zan tabbata ina kallo yan uwanta na aure ni ko ba halin yin aure a rayuwan na.
Ummi tace Allah ya fi mu sanin daidai don yana sane da komai da kowa a rayuwa sai da baba ya shigo gidan san nan suka daina.
Watau a gaskiya tunda inna ke fada min bakar magana akan ciwon nan bai taba kona min rai irin na yau da tai min ba ni dai ina zaune ina kallon ta ina aiki na banko tanka mata ba har taci ta sude ita kadai.
Sai dai ance ko shiru magana ne don haka shirun da nayi sai yaci mata rai kuma wai na mayar da ita mahaukaciyan tsakar gida don nasan abinda na jajibo gidan.
Mama ne tai magana da cewa haba dai ya kamata ki tauayawa yarinyar nan kin dai yi fadan nan bata tankaki ba baki bari hakana.
Ta koma kan mama kuma wai ai ta san mama bakin ciki take da mijin da yarta tasamu don yafi na yar ta shiyasa take kyashi yar nata.
Mama tai dariya tace kuma dai an ba a san maci tuwo ba sai miya ya kare .
Tace ai tun yanzu Allah ya baiyyana an sani in bashiba da ita ake zancen da zata saye ya zama nata nan dai baba ya kara shigowa ya raba su fadan.
Yaran suka fita da sanaa su gidan ya koma shiru ina kwance a dakin ummi na sai ga kanina ya dawo daga kasuwa tare da sakon dana bashi ya sayo min idan zai dawo gida.
Ina waje ina aikin miyan danyen kifi ne sai ganyen zogale na gyara ban hada ba yar wurin mama da ta dawo talla nace ta hada muna nabata kayan hadin ta gyara muna ta raba taba kowa nasa.
Na gama na shiga daki na dibarwa kowa miyan na aika masu dashi sai Inna tace a dawo min dashi.
Yaya Sani yana gida lokacin yace mata saboda may za a mayar mata ya ansa hannun yaron da na aika dashi yana ma uwar nasiha.
Shiru shiru kowa ya dawo sai yar wurin ta babban da ake shirin yiwa aure ne bata shigo ba .
Ina jin mama na tambayan ta har yanzu Saadatu bata shigo bane tace kila ta tsaya amsan kudin ta ne.
Har magariba shiru bata dawo ba nan hankalin uwar ya tashi ta yafa ta fita bata gane ta ba.
Can sai gata ta dawo tana fadin ban san ida yarinyar nan ta shiga ba na duba har layin da suke aje sana ar su ban ganta ba.
Shiru shiru an baza yara ko ina ba a gane taba nace wa ummi na bari na fita in duba ko Allah zai sa a dace.
Tace dani ki zamawa agun uwar su indai wanan matar ce barta inda kika ganta nace wa ummi aini ba don ta zani ba.
Don yar uwata ne da baba don naga hankalin shi ya tashi sosai tace sai na dawo .
Har goma da wani abu na dare muna yawon bidan ta babu labarin ta hankalin gidan mu duk ya tashi.
Muna tsaye kofan gida cirko cirko da wasu yan uguwan mu cikin zulumin ina ta shiga baban mu hankalin shi duk ya tashi na bada shawaran aje gun yan sanda a sanar dasu.
Baba da yaya sani suka nufi wurin yan sanda da daren nan suka sanar dasu abin da ake ciki har daya da wani abu na dare dole muka hakkura muka shiga gida hankali tashe.
A cikin gidan ma ba kwantawa mukayi don babu mai hankalin kwanciya sai yara kanana kawai sukai barci.
Dole baba ya hakkura suka shigo gida bayan duk an bincika gidan yan uwa da abokan arziki ba a samay ta nan ba.
Wani irin ihu da kururuwa Inna tasa da daren nan tabamu tausayi muka koma bata hakkuri amma ina bata ko sauraren mu.
Can wuraren biyu da rabi na dare mota ya tsaya kofan gidan mu da sauri baba ya bude dakin shi shi da su yaya sani suka fita don ganin ko nan ne motar ta tsaya.
Kafin sukai ma har an fara dokan kofan gidan namu da sauri baba ya bude tare da tabayan ko waye ?
Suka ce yan sandane ya bude kofan suka fice nan muka fara bude kofunan dakunan mu muna fitowa don jin may ke faruwa yan sanda gidan na mu da dare haka.
Sun ja baba gefe suna mashi bayani muna tsaye cirko cirko cikin jimay abinda ke shirin faruwa Inna baba ya kira inda suka karasa bakin motan muna biye dasu a bayan su.
Wani irin ihu Inna ta saka duk sai da muka firgice mun zaci ko gawan Saadatu inna tagani a motan.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , , , , ,
🧕🏿3️⃣0️⃣🧕🏿
YAR UWA NOVEL DON NAN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , , ,
Idan nace zaman danakeyi gidan mu akwai dadi nayi karya zama dai nake yi na wacce ta rasa gatan ta da madafa saidai dadin .
Abin ban dogara da sai abin gida ba ina tsaye ina nemawa kaina mafita ga rayuwa shiya sa abin yazo min a cikin sauke,
Don ban kallon abin wani sai ma su su kalla a wuri na a nema in bayar akuma yi min gori daga karshe.
Gidan da sai an nema aci ai kin san gida ne na mawuyacin rayuwa ga bawa don ranan da bai suma ba kowa tashi fisshe shi da yaran ta.
Duk da yake mahaifi mu mutum ne mai zafin nemawa kansa bai dogara ga sana a daya ba buga nan buga can yake yi har a samu ubangiji ya rufa asiri.
Yau ma mun wayi gari baba ya wuni bai samu kudin da za ai muna girki ba har kwana biyu ga kuma Inna bakin halin nata ya motsa sosai.
Don da yar ta ta fara a daki ta nemi kudin a gunta ta rasa dan sana, an mai da takeyi jarin yana kokarin karye mata sai inna tace ta basu su sayo abinci da zasu ci tace bata da kudi.
Nan take ta fada tun tana yi a daki har ta fito waje da jidalin a bakin ta ganin ta shiga daki yasa na fito don dora muna girkin abinda zamuci a dakin mu.
Ba wani abin tsone ido nayi ba dafaduka ne na taliyan da make sayar wa na dauki biyu in dafa muna adan kau da miyau sai da dare nake son in muna tiwon masara.
Tunda ta kyala ido ta ganin a bakin murhu ta fara irin maganan ta da cewa gida ya koma muna wurin gwada tsara muda diya.
Mun koma kamar kishiyoyi a gida da mu da ku ai gara ma ke Saadatu ba a debe tsamanin aure a gare ki ba do baki da cuta amma wata kan ai haka zamu zauna muna nuna hali da mu da ita.
Tafito ba komai takeyi ba amma taje ta dawo a tsakar gida tana dauke dauke a tsakar gida kamar mai sabon hauka.
Da ummi taji abin yayi yawa sai gata ta fito waje da sauri na dago don jin motsinta nace da ita don Allah ummi kada kice zaki tanka mata.
Tai tsaye tai shiru sai taka koma daki ko ba a fada ba maganganun na Inna sun bata wa ummi rai sosai.
Yar ta Saadatu ne tafito daga dakin su tace da ita wai ke inna akan naki taba kudin mutane ne kike wanan magana har kina hadawa da Safiya may tai maki yanzu ?
Mafarin kija fitina ku kama fada da tononasiri da ummi a gidan nan ke baki taba fadan gaskiya sai ayita akare kece baki da gaskiya kulun.
Nan kuma ta juya akan Saade din tunda bata samu wace zatayi da itaba tace ke gara can shanyayya kawai an hada dake an shanye keda dan uwanki.
Nidai nagama aikina na shige dakin mu na raba na aikawa kowa gidan da nasa, muka zauna nida kanne mukaci namu.
Bayan mun gama cine nace wa ummi da take zaune tayi shiru a dakin namu tana kallon mu.
Ummi gaskiya barin gidan nan zanyi na dan kwana biyu, da sauri tace dani ina zaki tafi inda yafi maki nan din ?
Nace ba wani wuri zan tafi ba gun maman biyu zani in dan kwana biyu a can kin gama zata tace ban yada ita ba ai.
Tace dani kina ganin magafinki zai barki ki tafi kada ma ki soma wanan magana rayuka su zo su baci ga banza tsakanin mu da shi.
Nace ummi don Allah kiyi hakkuri kibar ki barni in gwada sa ata na gani ko zai yarda in tafi wallahi idan ban gusa naba inna wuri ba wata raba ana abinda ba daidai ba a gidan nan.
Ummi tace ai saidai kada akara amma kan Allah dai ya sauwaka kawai za a ce ma zancen nace amin.
Ummi na dauka nabar zancen ne niko iya gaskiya na kenan na fada bayan kamar kwana biyu na samu baba a kofan shi zaune bayan ya gama cin abincin dare nake fada maishi kudirina nason yin tafiya zuwa wirin maman biyu.
Sai da ya kurkure baki ya watar da ruwan da ya gunda a baki yace dani anyya Safiya ba zaki hakkuri ki zauna nan ba ki barwa Allah alamarin sa yafi.
Gyara tsuguni nayi da kyau nace dashi baba ai ba zama zanje nayi ba zuwa zanyi na ganta kwana biyu sai na dawo gida.
Yace safiya bawai naki tafiyan ki bane ai wanan matar tana da mutunci da zaa gunta amma kinsan halin da kike ciki yanzu
Yan uwan ki ma da kuka fito ciki guda dasu suna nuna maki kyama balle wata can da girma da arziki ne ya hada ku kawai.
Nace baba ba haka na bane ita ta bukaci da naje gun ta, na dan kwana biyu sai in dawo don kawai nai mata alkwari ne zan zo nake son zuwa ai.
Yace Allah ya kaiki lafiya nace amin baba na gode baba yace ba koma har na mikr tsaye naji yace dake dawa zaku tafi sai na danyi shiru sai kuma nace ni kadai zan tafi baba.
Yace tau Allah ya kyauta agaida su Inna na kofar ta bata san maganan may mukeyi da baba haka hankain ta yana gurin mu .
No juya na nufi daki naji tana cewa a yanazu kuma mai cuta a jiki tafi ko wani da gidan nan samun ido , nidai wuce wa niyi ban kula taba sai magana take tana dariya.
Tun ranan da mukai magana da baba na fara shirin tafiya zuwa lagos gun mama biyu sai da na shirya tsaba na fitar da zancen tafiyan gun mutanen gidan mu.
Aiko a take inna ta kasa boye jan halinta tace zaki koma a dora daga inda aka tsaya ne na hadi wasu yawin bakin ciki nace niba wurin gwagona zan tafi ba.
Naji tana son daukan zancen da zafi daga zan tafi lagos gobe mata take ta kasa boye min bakin cikin ta a fili ta nuna hassada akan tafiyan ban tsaya kula taba washe gari na dauki hayan zuwa garin lagos.
********* ********* *********
Ban isa ba sai dare sosai na iso garin lokacin ya fara yin shiru don haka ban sha wahalan zuwa unguwar su maman biyun ba da ba don dare ne abin hawa sun rage zirga zirga a hanya lokacin .
Nazo na samu sun rufe gida sun kuma canza mai gadi kusan ma,aikatan gida duk an canza su an kawo wasu.
Don haka basu gane ni ba araina nace kodai ba gidan bane nazo sai mai gadin ne ke tambayana wurin wa nazo nace dashi madam Hauwa sai naga ya juya zuwa ciki na dan lokaci ya dawo yana tanbayan daga ina nake na fada mai sai gasu tare sun fito da ita.
Tana farin ciki da murnan gani na muka kwasa zuwa cikin gida tare farin ciki gani na duk ya cika mata zuciya.
A raina nace ikon Allah gidan mu suna kyama na wasu kuma bare na farin ciki da zuwana cikin su haka duniya ta gada.
Naga halarci agun mutanen gidan na samu kaunata tazo da kuma yar uwar mijin ta suna zaune da ita sai kuma gani na zo.
Amma duk da haka basu nuna min rashin jin dadin zuwa na ba sai ma taro na arziki da na samu a guri su.
An cika min gaba da abinci ban iya ci sosai ba don nisan tafiyan da na kwaso sai dai ina kallon abincin ina tuna su ummi da kanne na ko yanzu wani hali suke ciki oho ?
Da zan bar gida na mikawa ummi na waya na kwashe nombobi na akan idan na zo ja samu yar karamar waya in saye don wanan ta ji jiki sosai.
Ban dade zaune ba sai gata ta fito daga dakin ta dake sama take cewa dani Safiya taso akaiki dakin da zaki zauna don ki huta naga kin gaji da yawa.
Na mike tare da daukan hand bag dina muka nufi dakin daki ne babba wanda ya kumshi gado da mirro da ban daki da tv da AC acikin sa.
Bata dade ba tafita na sauke ajiyan zuciya tare da bin dakin da kallo ina mamaki ban bata lokaci ba na fada bandakin na watso ruwa tare da dauro alwala nafito na rama sallolin da ake bina .
Daga nan na kwanta ban dade ba abu ga wanda ya gaji barci ya kwashe bani na falka sai da asuba don na saba tashi a wanan lokacin.
Na shiga ban dakin na dauro alwala nafito nai sallah ban kwanta ba na dade zaune ina addua kamar yadda na saba yi duk safe sai da gari ya haska na fito daga dakin bayan na gyara na samu mai aiki tana ta gyaran wuri sai na so taya ta amma sai ta hana.
Nan dai na taya ta aiki mikayi tare sai tabar min ta tafi hada abin karyawa muna gab da gama aikin anty tafito daga dakin ta tana cewa.
Dama nayi tuna nen hakan dake Safiya may yasa ba zaki huta ki natsu ba sai ki fito ki kama aiki.
Murmushi nayi nace da ita ai wanan duk ba aiki bane a gida duk nike wa ummina aikin da ya dace inyi na.
Murmushi tayi tace yanzu dai ki dan huta tukun kafin na san abinyi a kan ki nafi son naga kin huta kin kwantar da hankali kafin mu san abinyi a kanki.
Bayan mun yi wanka ne an fito karyawa take gabatar min da yar uwar mijin ta dake zama dasu sai kaunan ta da ke zaune dasu wai tana karatu naga tana min wani kallo na rainin wayo.
Ni dai ban kulata ba muka ci abinci inda duk hiran da ni maman biyu keyin shi akan yanayin garin mu da ta gani ina bata labarin garin namu da abubuwan da muke shukawa a karlaran mu din.
Mun gama na mike don kwashe kayan tace in barshi mai aiki ta kwashe nace haba anty kamar dai ba mata ba na kwashe naje na wanke ban dawo inda suke ba na shige don yin sallah walha.
Dana gama na dan mike don har yanzu akwai gajiya tare dani sai barci ashe ta leko dakin ta samu ina barci a inda na idar da sallah na.
Ta juya ta koma tare da jawo min kofan ban farka ba sai sha biyu da wani abu na gyara jikina na fito nan falo na same su da kauna tana mata fada ko da ban sani ba nasan a kaina don naji tana fadin.
Na dai gaya maki karki yarda ki sawa yarinyar na ido a gidan nan don ba wurin ki tazo ba indan ma tayi wani abinda ba daidaiba just ki fada min.
Don ban son abinda ya faru da dake da faiza ya kara faruwa akanta don duka daya na dauke ku don ko ita din ma ni na kawo ta nan din.
A take sai naji kuka yazo min a hankali na juya zuwa dakina da na fito din ba zan iya rike kukan ba a lokaci kuma gashi ban son suji na ji maganan su.
Sai dai a raina nasa duk yadda kaunan nata take zan iya hade bacin ran da zan gani a gurin ta don mu rabu lafiya ni da nazo cin arziki ina ni ina fada da masu gida.
Ina daki dunkule ban fito ba suma basu nemay ni ba ashrle ta fita ne gida sai shidda na yamma ta dawo gidan nan ta zube a falo inda ta samay su suna kallo.
Nan na fito cikin su tare da gaida su na samu wuri na zauna ta dago kai tana cewa Safiya kin tashi ai na leka ki har sau biyu na samu kina barci.
Nace wallahi anty sai yanzu na fito nima ban san barci ya kwashe ni ba sai tace tare da nuna kaunan mijita dake zaune ban gabatar maki da wa yan nan ba bayan tafiyan ki ne suma suka zo anan suke zaune tare damu yanzu.
Wanan ita ce faiza kaunar maigidan ne auren ta ya mutu ne tadawo nan da zama wirin mu.
Sai wanan yar uwatace itace autar mu itama anan take zaune yanzu tare dani da fatan zaku zauna a cikin aminci har kowa ta samu miji tayi auren ta.
Tace kuma wanan itace safiyan da kuke ji ina fadin zata iya zuwa ko wani lokaci yar uwata ce itama zata zauna damu anan na dan wani lokaci da fatan zaku rike juna da amana.
Sai naga Fatin ta dago ta kalle ta don jin ta kirani da yar uwa nima ban san dalilin anty na fada masu haka ba.
Faizan ne tai murmushi tace kai anty lallai kina ji da wanan safiyan ai kin fada muna zuwan ta tuntuni kuma insha Allahu zaki samay mu yadda kike so a cikin amana.
Sai ta juyo gare ni tana cewa ki saki jikin ki kuma ki ja kowa ajiki saboda yanzu mun zama daya da junar mu ga gidan gidan Jamma a ne.
Wa yanda ma bamu san inda suka fito ba suna zuwa suci arziki su tafi ni dai abu daya ne ko kadan bana kaunar rashin gaskiya duk abinda zamuyi mu yi shi a cikin gaskiya da amana.
Murmushi maman biyu tayi tace indai Safiya ce to kar kiji komai a kanta, saboda komai daidai gwagwado Allah ya wadatar da ita da natsuwa da sanin ya kama ta daidai misali.
Ta nisa tace tare da cewa ai shekenan Allah ya zaunar da mu lafiya da junan mu tace aini naji dadin zuwan ta kwara don in kun watse nakan ji gidan ya koma min shiru wallahi.
Ita dai fatin tana ta charting din ta ba dago kai ta kalle mu ba balle tasan may muke fadi ma.
Na ce a raina wanan da gani zamu kwasa da ita sai dai duk abinda zata zo min da shi zan yi kokarin kawar da kaina akanta.
Muryan maman biyu ya katse min tunane na take tambaya na ko nayi waya da mutanen gida da nazo nace da ita banda waya a hannu na don wayan da zanzo na barwa su ummi shi acan don su samay ni.
Tace a a ke ko ana haka ai ya kamata ki kirasu su san kin iso lafiya yafi ke fati je daki ki dauko min wanan wayan dake saman mirro na ki kawo.
Kamar bataji yar nata ba sai da ta kara maimaita maganan nata ne ta mike zuwa dauko wayan a dakin ta.
Ta bita da kallo tare da firgiza kan ta tace kai Faiza akwai matsala wallahi sai kun ta hakkuri da ita don Allah.
Faiza tace aini yanzu nasan halin ta ba abinda zata yi ya dakay ni kuma sai dai ita Safiya da bata saba da halin ta ba.
Ta kawo wayan tana mikawa yar nata ba tare da ta kalli kowa a wurin ba ta karba tana ce min ina sim din ki yake na tashi zuwa daukowa.
Ashe bayan na tashi yar take mata fada sai tai hushi tabar falon gaba daya ta koma daki.
Koda na fito ban gane ta ba na mika wa anty sim din na samu harta cire nata dake ciki tana cewa ki fara amfani da wanan har in sayo maki naki wayan .
Ta saka min sim din tace karbi ki kirasu su san kin sauka lafiya ko hankalinsu ya kwanta idan sun jiki.
Faiza tace lalai kan do irin haka hakali baya kwanci sai kaji mutum balle lagos garin ne mai tare da hatsari sosai.
Na karba kira biyu sai kaunata dake bi mun ta dauki wayan nan dai muka gaisa nace tabawa ummi wayan muka gaisa na fada masu na iso lafiya nace ga anty.
Ta karbi wayan sun gaisa sosai ummi tai mata godiya tare da cewa don Allah don ma aikin Allah ki rike min ita amana don gidan nan ba dadi shiya sa ta zabi zuwa wirin ki ta zauna.
Tace ummi kada kiji komai zaman Safiya a guri na tankar a gida take daku saboda Allah kadai yasan abinda ke zuciya ta kuma shi ya san yadda nake jin Safiya a raina.
Ummi tai mata godiya ta bani wayan ina tambayanta sauran mutanen gidan mu tace duk suna lafiya.
Lokacin sallah da ya gabayo ne yasamu watsewa inda na kula da kowa dakin ta daban ashe a gidan sai dai duk kan mu ukun a kasa muke sai masu gidan ne ke sama da yaran su.
Yanzu yar uwa kin kwamace in barki da Allah da kike fitar min da novel waje kiba rabawa group group ki tuna duniya ba matabbata bane.
Akwai ranan hisabi tsakanin mu dake ban san kin shigo da fuska biyu bane amma idan baki iya rikon amana ki magana na baki kudin ki don bazan taba yafe kaki ba ko wace ce ke ubangiji yai gagawan isar min a gare ki idan kika kara fitar min da novel ga wanda bai biya ba.
Allah yai min sakayya a gare ki ko wacece ke.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , ,
🧕🏿3️⃣1️⃣🧕🏿
YAR UWA NOVEL NAN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU DON BA ZAN YAFE MAKI BA IDAN KUMA KIKA FITAR MIN DA NOVEL UBANGIJI YABI MIN HAKKINA A KAN KI, , ,
Washegari misalin karfe goma na safe ina zaune a daki sai ga dayan yan biyu ta ta shigo dakina tace dani mumm is calling you.
Ban bata lokaci ba na mike nabi bayan ta zuwa amsa kiran sama naga ta nufa don haka nabi baya yarinyan nata can .
Wanan ne karo na farko dana taba haurawa wa sama dakunan gidan koda muka hau sai naga saman ashe babba ne da dakunoni kamar kasan.
Ina mamakin girman gidan yarinyar ta tura kofa ta shiga nima na mara mata baya tare da sallama na shiga.
Na samu tana tsaye tana gyara rigar uniform din ta a jikin ta ta dauko abaya ta dagwara a sama fara gaida ita nayi nace anty ina kwana ta juyo tana fuskanta na fuskanta dauke da murmushi tace Safiya an tashi lafiya.
Nace Alhamdullahi ta sake tambayana da kin ko yi break fast don yau banda time din fita ina shirin zuwa office ne.
Nai murmushi nace yanzu zanyi anty tai saaurin ce aa kada kiyi wasa da karyawa keda kike shan magani zaki tsaya biye muna kada ki bari tara yayi baki karya ba a kullum.
Kai na gyada mata kawai alaman to tace dama na ce akira min ke na kara fada maki don fita zanyi don Allah a kada kishiga shirgin su faiza ki zauna da kowa da zuciya daya.
Fati ba kirki ne da ita ba don bata da kunya koma kisan hiran da zaki yi dasu don inda halima ina son ki kama bakin ki akansu maana sirin ki kibar wa cikin ki shiya sama ban hada kowa a daki daya ba nabawa kowa nata dakin daban.
Tace da fatan zaki fahince ni na ce a sanyaye da eh anty nagode ta sake cewa idan kina son wani abu ki tambayi mai aiki ko Faiza su baki nace to ta juya saman gadon ta tace kwashi wayan nan kayan ki fara amfani dasu kafin na dinka maki naki.
Na fara mata godiya sai ta dago min hannu alaman in bari duk da haka sai da na gode mata din.
Daki na koma batare da na hadu da kowa a falon ba har na shige na aje kayan yadda na dauko su da zata fita saida ta leka kowan mu sannan ta fice gidan.
Na gyara dakin sai lokacin na bude kayan don in kaisu a wardrabe din kayana kaya ne masu kyau har kala biyar sai dogon riga daya cikon na shidda kenan.
Na gwargwada sai naga size dina ne ma nasan ta dade dayin su ba yanzu da ta kara jikin girma ba dai.
Nai murna a raina ranan doguwar rigar na sa don yaba kyauta kenan maishi ya ji dadi indan ya ganka da abinda ya baka a jiki.
Shiru yai yawa a daki na fito waje anan na samu yaran zaune suna kallo su kadai suna gani na suka nufoni nan muka zauna ina biye ma shirmay su suna bani labari wai uncle yace zai zo ya kaisu birch zan bisu ko muje tare eh kawai nace dasu.
Ganin kan su ya tsufa da kitson dake kansu yasa nai shawaran sance masu nai masu wani mai kyau na hannu don dai indai kitsone Allah ya hore min iyawa ko wani iri.
Faiza ce ta fito ta samu muna kitson karshe dagani daga barci ta tashi tace wai ashe kuna nan na saba ba in fito ba kowa a falon dole nima na koyi zaman daki ta kai zaune tana yaba kitson da mukeyi tare da cewa ashe kin iya kitso ne haka ?
Na dai yi mata murmushi a raina nace ai kitson ne ya jawo min wanan alherin da nake ciki don lokacin da ta fara kawo su har sau biyu tana zuwa amma bana karban kudin su sai ince su din ai yara nane.
Haka yasa uwar ta daina kawo min kudi a lokacin sai dai wani abin da tafiya yai tafiya kuma ta fahinci halin da nake ciki ta shiga taimaka min.
Jefi jefi muke hira da ita na gama tare da daura masu ribon don shuku biyu nai mako waccen su sai take cewa nima gobe zan sance kaina ki mun ghana wiving don shi nake so nace da ita Allah ya kaimu kawai.
Fati ne ta fito daga dakin ta ko kallo inda muke bamu ishe ta ba zata wuce mu nace mata anty Fati ina kwana cikinciki ta amsa min gaisuwan ita ko Faiza ta ja wani tsaki tare da kawar da kanta.
Dining ta wuce ta bubude kulolin dake wurin ta wani tabe baki tace duk ma an jagule abincin ambar jagwalgwale.
Ba wanda ya kulata sai kuma naga ta zauna tana diba nan ta zauna taci ba tare da kula mu ba sai dai tana yi tana satan kallon mu a fakaice.
Ni dai ina mamakin ta a raina dayar yan biyun ta nufeta take cewa ta dubi kitson da Anty tai masu korar yarinyan tayi daga wurin ta ta wuto tana yi tana waigen ta kamar zatai kuka ganin haka yasa nace zo nan kada ki kuka kyale anty.
Ke naji ta fada kamar wacce ta samu diyarta don haka ban dauka da ni takeyi ba sai da ta sake fadin ke Safiya bakiji bane san nan na dago kai ina kallon ta.
Tace ban faye son ana shiga harkata ba don haka ki kiyayye yar kice ko yar yar uwata koda yake ma kalan dagi ce ke don naji anty na fadin wai kema kauna tace ko a ina ta samay ki oho ?
Ko da yake kila ta wurin mamanta kika fito ban sani ba nan na fahinci ba uwarsu daya ba ashe kila uba suka hada.
Ni dai ban ce da ita komai ba sai Faiza ce tace mata amma dai kin san ba girmuwanta kikayi ba da zaki fada mata haka.
Koda yake baki da laifi don ita ta fara kiran ki wai da anty shiyasa kan ki ya fasu haka kike jin kanki wata babba can.
Ya ishe ki gida dai ne baki iya korana don nima gidan yar uwata ce dariya naji tayi tace yar uwa ko muna yar uwa ai da yar uwan kwarai ce da kin so abinda take so ke yanzu baki ji kuyar korar wanan yarinyar a gurin ki.
Nan dai sukai ta cacan baki wanda nake gani ba yau suka fara irin haka a tsakanin su ba da naji abin yai yawa nace da ita ta kyale ta don Allah maganan ya kare ai mutum guda bai fada.
Sai kuma ta juya kaina tace wai ai dama taga zubina na munafukai ne don haka sai dai hassada ya kashe mu don ita ta wuce ajin muko.
A raina nace wata sabuwa kenan kuma nayi gudun gara na fada ma zago in na gudo gidan mu don inna ga wata kuma na samu a nan yan kuwa zamana nan mai dorewa ne kuwa.
Maigidan bata dawo ba sai hudu na marance daya bayan daya muke shiga muna gaida ita da dawowa koshi ban san ta dawo ba sai da Faiza ta fada min sannan na tafi.
Dama yaran na wuri na sun rigani isa don sai da na tsaya nai sallah na fita zuwa gaida ita din da dawowa.
Zaune take kasa yayin da diyan nata suke saman jikin ta ta mimike kafa suna zuba mata surutu saman jikin ta na gaida ita ta dago har kullun fuskan ta a cikin murmushi tace dani safiya yaya muka wuni nace lafiya kalau anty kin dawo lafiya ta amsa a sake da lafiya.
Sai na juya tace kin ga Safiya debo min abinci na nan don ban iya saukowa kasan nan yanzu na gaji yau da yawa.
Na juya zuwa dauko mata abincin ashe baya wucewa na sai yar tace mummy kin san may yau da baki nan mummy fati tana ta fada su Anty tana ta zagin su .
Sai dayar tace sai da wanan anty tai kuka ita gwagon mu batai kuka ba tana bata amsa sukayi ta fada sosai.
Na shigo dauke da ture tace dani ashe kunsha kitso ne haka sannu da kokari murmushi kawai nayi na aje mata tana cewa yauwa sannu yar gidan anty na gode.
Na juya na fita dakin har nakai kofa tace don Allah yimin magana da Faiza idan kin fita nace to anty.
Ina fita na nufi dakin faizan tana zaune tana waya na isar mata da sakon anty na fito daga dakin.
Sai da ta gama ta fita daki na koma na kira ummi na don jin lafiyan su da sauran mutanen gida .
Nan take fada min bayan wuce wana ai anyi fada da baba da inna har don bata san inda naje ba sai daga baya da taji take zage zage wai naje yawon dandi zanbarbada wa maza cuta.
Shikuma baba ya kasa kyale ta nan dai abin ya kaisu har da duka abin da bai taba yi wa wata mace ba a gidan nan.
Nace ni kuwa ummi may na tsare ma inna ne a gidan tafi dason in zauna in wulkanta tana min gori ko yaushe a gida ?
Yanzu dai ai ya dauki mataki a kanta don da wuya ta sake maganan ki kuma ai a gidan nan yadda suka kwasa dashi abin ba dadi wallahi.
Nan dai muka sha hiran mu kan matsalan gidan namu da ita karshe nai mata sallama na tashi don gyaran daki sam bani barin dakin da kazanta ko kadan.
********* ********* *********
Faiza na shiga dakin anty tace ta samu wuri ta zauna sai da ta kai zaune tace da ita yanzu yaran nan ke fada min abinda ya faru da bana nan.
Shi nake son ki fada min komai nan ta fara fadi yaran na tuna mata wani abin har ta kai karshen zancen ta.
Tace wanan yarinyar sai na fito mata ta bayan gida zamu zauna lafiya bata kara furta wani abin ba sai faiza da ta mike ta fice daga dakin tana masu yan biyu wasa.
Hankalina yanzu akwace yake babu abinda ke damuna araina Fati ce kawai matsalata ban kuma kulata bayan gaisuwa da yama kamar na dole a tsakanin mu babu abinda ke hada mu da ita.
Nayi wani haske na kara kyau sakamakon mayuyukan da Anty ta sayo min in dinga amfani dasu a maimakon vesiline da nake shafawa da.
Wanda ko vaseline din ban damu da shafawa da don oilyskine din da nake dashi sai dai ina da dry face amma haka nake barinsa ba gyara.
Nan ko anty ta maysa min son ita yar son kwaliyane taki jinin taga mace bata gyara fuska ba ko jikin ta tun ban iya ba dole na kowa duk kowa da ba inda nake zuwa daga gida sai gida.
Duk wanan halin da nake ciki nakan tuna da halin da rayuwa na yake ciki zamana kenan ba karatu ba aure tare da ni.
Duk da anty na iya bakin kokarin ta wajen ko dayaushe takan muna nasiha da gargadin mai kyau da nagarta .
Babu irin wanda batai muna badon komai ba ba sai don jin tsoron Allah takance ku kama kan ku daga duk wani nauin shiga tarkon shedan
Takance duk kanku amma kuke a wurina don haka ba zan yi sakaci da tarbiyan ku ba don baku gaban iyayyen ku.
Ta kuwa sa a don duk kan mu babu wanda baya daukan nasihan ta dan dama Fati wani lokaci sukan kwasa wajen saka tufafi sai taso tace zata saka irin na kabilu nan sukan kwasa da yar nata.
Bayan ita bata da wani matsala da kowan mu gashi yanzu zuwa na zatafi hankalin ta kwace don tasan yaran ta zasu samu kulawan da ya dace ko bata gida.
Don ni dama haka nake dayara kona waye sai kaga atake yaro ya lake min a jiki bai damu da uwarsa ba koda na zauna gida akwai yar makwaciyar mu data lake mun duk safe da an mata wanka zata zo gidan mu sai da yamma indan dare yayi zan maida ita gida.
Amma naiyyanar ciwon dake jikina sai uwar ta hana yarinyar zuwa wanda nasan aikin Inna ne don dama tana jin haushin hurdana da matar.
Dadine gashinan sai abinda mutum bai so a gidan anty mijin ta kuma baya kasan tun zuwa na wai yaje US wani aikin suna sojoji amma kwanan nan naji antyn tana maganan dawowan shi kasan.
Don haka muke yi yadda muka ga dama a gidan babu mai takura muna amma naji Faiza na fadin yanzu yaya zai dawo gidan zai koma ba dadi don in yana nan babu wali a gare mu.
Ni dai dama ba sanin shi nayi ba don haka ban damu ba don koda yana nan ba ruwa na sai in fake ma daki inda har yana gida baiko ganin giccina a gidan nace a raina.
Muna zaune falo da anty take cewa wani sati maigidan zai dawo kuma tana ganin shida sulaiman zasu dawo.
Faiza tai saurin cewa harda shi zai dawo anty tace ba dole ba yana zuwa ya zauna a kasar mutane gashi arzikin shi sai kara habbaka yake yi yanzu ai gara dai ya dawo gida asan abin yi kan case din shi.
Kamar yadda anty ta fada hakane satin da muka shiga bamu da hutu a gidan don shirye shiryen taron maigidan da kanin sa da zasu dawo kasan.
Kusan aikin nice a gaba don banda kasala akan aiki duk yadda yake kuwa kafin wani lokaci mun hada komai yadda ya kamata muyi.
Sai a wanan lokacin naga Fati na rawan kafa don har takan dan saka hannun ta ga aikin da mukeyi ayi tare da ita.
Tai ta faman murna tace ance harda Uncle sulaiman zai dawo ashe gidan namu zai cika ke nan kwanan nan.
Da yake ba hira muka saba yi da ita ba babu wanda ke kulata har tayi ta gama sukiburutsun ta ta bar wurin.
Don ba sabawa tayi da irin haka ba don haka bata da jimirin dade wa tare damu a falon ranan da zasu dawo kuwa tun safe muke murzan aiki sai yamma muka gama kowa yaje yai wanka kafin shigowan shi.
Tun da nai wanka na jawo dogon rigata na saka a jikina na koma nabi gado na haye don dama a gajiye nake don mun sha aiki sosai.
Ban fito ba ina jin ana ta hayaniya a gidan nasan matafiyan namu sun iso kenan zuwa dare anty ta leko daki na tana cewa najiki shiru ga bakin mu sun iso gida lafiya har sunci abinci baki fito ba ke .
Nai murmushi nace sun iso lafiya anty tace kalau suka iso nace da safe indan sun huta mu gaisa dasu ai wani kallo tai min.
Tace amma Safiya baki ko kyau ta min ba in kin ce sai gobe mutum ya kwaso gajiya na mike zubur nace tuba nake anty ta dan harare ni tace ke kika sani ai.
Tace ai har uncle din yara ya tafi abishi don shi dama bai son yawan magana na fita da zumbulelen hijabina yana shirin tashi sai gani shi kadai na gani a wurin sai anty da yaran ta har kasa na kai ina cewa daddy barka da dawowa.
Ya juyo da sauri tare da amsawa yana kallo na yace Safiyar taki ke nan ashe ma karamar yarinya ce haka yace mun samay ku lafiya nace lafiya kalau.
To yaya hakkurin abinda ya faru aita hakkuri haka duniya yake dama ba komai ne ke zuwa wa mutun daidai ba a sanyayye nace nagode a huta gajiya don har idona ya kawo kwalla ko.
Na juya zan tafi naji anty tace dani Safiya a rage kayan nan daga wurin nan na juyo na fara kwasan kayan ida ba wani cin abincin sukayi ba sosai dan tabawa sukayi suka barshi duk uban wahalan da mukaci na aikin yin shi.
Na saka na fridge a cikin sauran kuma na adana su inda ya dace a jiye su san nan na koma dakina na rufo Asuba ta gari indan tunane ya barni nai barci yadda ya kamata
Yar uwa ina zaki da hakki a kan ki na mutane ance ba a yafe ba baki barin turawa kina daukan nauyi a kan ki,
Karatun nan fa ba dole bane kiba kanki lafiya mana da daukan nauyi don neman suna kike turawa ko don kina ganin haka ba komai bane.
To nace Allah yai min gagawan isa ga mai fitar min da novel waje .

🧕🏿3️⃣2️⃣🧕🏿

Washegari muka hade a falo duk kan mu sai anty dake wurin mijin ta Fati sai faman murna take yi uncle Sulaiman ya dawo,
Hararan gefen ido Faiza tabita dashi tace wai kina ta murnan dawowan Sulaiman wanan dan bakin rai jiya kin ga ya dubemu ne ma.
Kai wallahi turai ya karbeshi kin ko ga yadda ya kara girma yai wani fresh dashi kamar bashi ba don Allah.
Faiza ta watsa mata dan harara tace yanzu ai kanki ake ji shi baki ko isheshi kallo ba, ta bata rai tana fadin oho dai ko bai san ina yi ba wata rana zai sani ai.
Mako uku cur da dawon su amma sau biyu naga daddy a gidan haka wanda Fati ke maganan shi ko yaushe ban taba ganin shi ba kuma sunce yakan shigo gidan wani lokaci amma Allah bai taba sawa mun hadu da shi ba.
Yau ya shigo gidan anty tai mai tayin abinci yace bai jin cin komai a lokacin kai ta girgiza tace wai kai har yanzu kana nufin baka fitar da zancan Samira a rayuwan ka bane ?
Yai murmushi yace kai samiran may can ai ni yanzu in ba lokaci ba ban faye kawo ta a raina ba sai dai ai kin san yazama dole ba zan taba mantawa da ita bane.
Anty ta nisa tacd dashi Allah ya sauwaka amma don Allah ka rage yawan tunane ka koma alamarin ka kamar kowa ita fa har naji ance tayi wani aure ko.
Yace nima haka naji gun wani dan uwan su can.
Ta dade tana dan kallon shi sanan ta gyara zama tace na cewa dashi ya kamata ka manta da komai hakana ka samu wata wace kake zuwa wurin ta ku shirya.
Sai yaneme ya katse zancen sai ta hana shi samun damar yin hakan tace kyale ni har in gama tukun yanzu sulaiman da hankalinka da ilimin ka da komai kaifa ka iya sa wani agaba kai mai fada idan kaga zai kauce irin haka.
To yaya za a ce kai da kan ka ke irin haka kuma.
Kar fa ka manta Allah yana sane da komai na bawan sa shekara biyar kenan ka kasa cire hafsat a ranka sau kace ba musulmi ba ?
Haba sulaiman shi fa musulmi da tawali,u aka san shi saboda hadisi ne ingantacce daya tabatar muna da hakan imanin dayan ku baya kammala har sai yayi imani da kaddara mai kyau da kuma akasin hakan.
To what come over you ?
Sulaiman
Da zaka manta da duk wanan a ranka ?
Gaba da daya lamannin shi suka sauya a lokaci guda ciwon da dade yana cin zurciulyar shi ya dawo mashi sabo fil, wanan dalilin ne yasa dama yake gudun gida don kowa na shakkun fada mai zancen aure.
Ko ita kanta anty sai daga baya taji dama bata dauko mai zancen ba don kawai ganin yadda ya sauya alokaci guda.
Ta kalle shi a sanyayye tace sulaiman ban dauko wanan maganar ba don in tayar maka da hankali amma kayi hakkuri kayi tunane akai.
Kar kaga na dauko ma maganan da kowa yake gudun fada maka nayi hakane amatsayi na wacce muka shaku dakai don zaman ka a haka yana damun kowa.
Ya mike don bai son maganan yai nisa yace zan fita sai na dawo sai dai ba lalle ne in dawo kusa ba don ina son in leka bauchi kwanan nan.
Ba damuwa haka na da kyau ai aje gida adubasu yafi amma kayi tunane aka magana na don Allah shi yafi.
Ya sauke ajiyan zuciya tare da karfin halin fidda murmushi a fuskan shi yace zan diba madam ni zan tafi tace aiko danafi kowa jin dadi wallahi.
Ta sake cewa yau dai kaki taba abincin gidan na mu ya dan yi murmushi yace mata yau bana jin yunwa ne shiyasa.
Ya fice a sanyayye tabishi da kallo tausaya mashi daidai lokacin Fati tashigo get din gidan bai ko kalli inda take tana gaidashi ba yaja motar shi zuwa wurin da ake masa aiki.
Ta shi go da yar fara an ta a fuskan ta tana cewa ashe uncle yazo gidan sai dai kuma bai dade ba ya wuce kuma ?
Anty ta kalle ta fuska daure tace ke Fati ki saurare ni dakyau kiji may zan fada maki naga kina wani rawan kai tun zuwan Sulaima.
To ki kama kan ki don sulaiman ba ajinki bane ya wauce sanin ki ki tsaya a matsayin ki idan kina son mu rabu lafiya dake ke ina ma kika ga haka zai yuyu dube ki ki dubeshi ina zaki hada kan ki dashi.
Kuma ni ina auren dan uwan shi ina kika taba ganin an yi hakan sai ta turi baki gaba tana cewa damay yafini kuma ni ba mace bane halan ?
Ta shige tana kumkumi ta bita da harara har ta bace mata dagani tana sauke ajiyan zuciya ina fitowa daga daki na.
Nace anty ashe kina zaune nan ban sani ba dana fito na taya ki hira ai tun dazu.
Ta kara sauke ajiyan zuciya tace ai bani kadai bane nida uncle din yara ne yanzu ya fita daga nan .
Nace ayya aiko da na ganshi kullun muna samun sabani sai ya tafi nake fitowa har yau ban sanshi ba .
Tace aikuwa da kinga shi yaro mai taken zamani don Sulaiman abin son a san shine bari rana da ya shigo zan kiraki ku gaisa don yace zai tafi gida ya duba su ya dade rabon shi da gida.
Nace Allah sarki dan uwanki ne anty ?
Tace a a dan uwan mai gidan ne iyayyen su guda sai dai tasu tazo daya da manjor ne kawai sai muke dasawa da shi sosai.
Bai iya boye min komai nasa nima haka shiyasa nake son shi da komai nasa don shawaran shi baya wuce ni shima.
Nan muka zauna tana ta bani labari da irin arzikin da yan gidan su daddy ke dashi da sauran su har Faiza tafito ta samay mu anan itama ta zauna.
Fati bata fito ba sai da yamma lis ta fito tana jan kamshi Faiza ne tace yau may ke faruwa da yar mulki ne naga tun dazun take fushi a gidan ?
Anty ta ja tsaki tace rabu da mara wayau kawai bata san abinda take yi bane shiya sa sai gata ta fito a fusace tana fada wai waya shiga dakin ta da batanan ya dauko mata hand dryer din ta.
Faiza tace itace don Safiya ta karbi nawa kuma bata bude kofa ba lokacin shiya sa na dauko naki din.
Nan ko ta shiga fada ta inda take shiga ba nan take fita ba sai da anty ta dakatar da ita da cewa.
Ke Fati kin ishe ni wallahi haba ke kika saye shi ko ni da zaki saka mutane a gaba kina masu fada haifan su kikayi komay ?
Don haka ki shirya kayan ki gida zan maida ke nagaji wallahi duk naji abinda kikewa Safiya tun zuwan ta garin nan ido kawai nasa maki inga gudun ki.
Tun farko ina sai da na hada ku nai maku nasiha amma kika shure magana kina yadda ran ki yaso dasu a gidan nan.
Wai halan kikai Faiza matsayi ne agidan da zaki dinga hura ma mutane hanci yadda kike so ya zama dole in mai dake gida don ban iya zama da wanan iskacin naki haka .
Jin anty na ambato gida yasa ta sausauta maganan ta ita ko faiza kai ya fasu jin ance tafi kowa matsayi a cikin mu sai wani budawa take yi.
Nan dai anty ta kafe akan lallai ta shirya ta maida ta gida sai na shiga ba anty hakkuri tana ta faman fada da ita.
Ds kyat na samu ta hakkura da zance sai dai tace wallahi ta shiga hankali ta don ta gaji da ita a gidan
Tun wanan lokacin ta shiga hankalin ta da kowa dama ba mai shiga tsabgan ta cikin mu don haka bamu damu da ita ba.
Da anty zata dawo ranan sai ta sayo min nawa in huta da aron nasu da nakeyi tare da yan sayayyen kayan makeup dina.
Zama na a gidan yasa yanzu zaka ga komai a gidan tsab don kai aiki iyakan ta girki nice ke tsabatace gida kafin duk su tashi na gama komai har in kama mata yin girkin kuma.
Wanan abinda nakeyi shiya na kara shiga ran anty sosai tana tausaya ma halin da nake ciki takan kaini amsan magani secretly ba tare da kowa ya sani ba a gidan.
Kuma ban taba jin wani ko ganin an kyan kyankyamayni ba a gidan zama suke dani ba wani nuna rashin yarda dani gashi bata rage ni da komai ba na fannin rayuwa kuma.
Sati uku da maganan mu ina daki kwance yan biyu ta tashigo da gudu tace wai inji mummy su inzo .
Na dauki dan kwalina dake saman gado nai rolling din kaina dashi tare da dan gyara fuskana kartai min kwankwami rashin gyara.
Na fito su biyu na samu a fali sai dai may shi ya hada baya ban iya ganin fuskan shi a lokacin.
Gasu yan biyu sun na wasa da hannuwan shi sai dai mai shi fari ne soll da ganin shi yan biyu tana ta jan yatsun hannun shi na iso wurin tace yauwa Safiya ga uncle yau a gidan.
Sai ya juyo da sauri yana kallon wace akace ma safiya din don bai taba jin sunan a gidan ba sai yanzu.
Juyo wan shi mukai ido biyu dashi sai da gabana ya fadi don ban taba ganin namiji hadade irin shi ba nan dai na gaisheshi ciki kunya kunya.
Ya amsa min da lafiya lau kawai ya juya yaci gaba da wasa da yaran dake damun shi nace anty gani.
Tace shike nan dama kiran ki nayi ku gaisa da uncle din yara da baki sani ba sai nai murmushi na juya na barsu wurin daya fahinci na wuce.
Sai yace ita kuma wanan din wacece ita anan gidan take itama da zama ?
Tace budurwan da nai maka kamay ke nan yace kai haba madam kikan fara maganan ki don ki koreni ko.
Tace daga maganan mace zan koreka wai ko sai mun kaika mararaba mun ma wanka ne zaka daina tsaron mata.
Yace kai don Allah bari wanan ma ta gama secondry ne tace tun yau she ta kare Allah da gaske nake yi inda kana ciki sai in kama ma kawai musha buki.
Take ya daure fuskan shi alaman ba wasa a tare da shi tace kai ke nan da an maganan aure sai ka bata rai may kake nufi ne wai ?
Bai bata amsa ba sai ci gaba da yayi da hira da yaran dake gaban shi sai da ta kawo mai zancen aikin da akeyi mai ta samu ya sake fuskan shi.
Ni ko tunda na juya na wuce ina ta mamakin haduwan wanan mutumin da anty tace dan uwan daddy ne mijin ta kuma wai may kudi naji anty na cewa.
Na gaji da tunane na watsar da zancen na kama sha anin gabana daya damay ni kwai sai ga fati ta shigo dakina abinda ban taba gani ba tun zuwa na gidan.
Tana shigowa ta fada saman gadon dakin nawa da yasha gyara sai kamshi ke tashi a dakin tako ina na dakin.
Safiya kin san kowa yau ina cikin farin ciki ga uncle can a falo yazo tun dazun yazo yana falo na dade dakina ina leken shi ta fada saman gadon tana wani irin dariya.
Nikan kallon mamaki kawai nake binta dashi don abin ya daure mun kai sosai tace wai kin san wani abune safiya na gyara zama tare da cewa aa.
Tace wallahi anty tana kawo min kubsawa don sam bata son zance da guy din nan ni kuwa duk yadda zanyi in ga yaso ni sai nayi kin san abinka da yan uba.
Sai nai saurin kallon ta don jin kalamin ta gamay da anty duk wanan halarcin da take mata amma wai tana kiranta da yan uba.
Ta kara lumshe ido tana ce min guy din ya hadu ne sai ma in kin ganshi wallahi yanzu tashi zan yi in dake kawai in je mu gaisa dashi ko bata so ni ban damu in dai bukatana zai biya.
Nace haka za a yi kije ku gaisa ko ki samu shiga ai ba a bori da sanyin gwiwa tace ai shi na gani wallahi.
Ta mike tana wani juye juye tace yaya kika gani na hadu ko da gyara nace cikin daga kai komai tsab wallahi.
Ta fice daga dakin na bita da kallon mamaki nace oho zamani ina zaki damu mata cusa kai ga maza haka ?
Acan falo tun da anty taga ta tun karo wurin su tace kin ga Fati kira min safiya ta hada ma uncle fruit salad wai abinda yake so ke nan.
Tace anty bagani ba zan iya hada mashi ai tace don Allah ki raba ni da shirmay ki ranan da ta hada masu bacewa kikayi ke baki iyaba.
Sai tace ai naga yadda ta hada din kin ga kira min Safiya nace don Allah ban son shirmay ki hakan nan.
Ta wuce tana mai jin haushi yar uwar nata data kwabsa mata a gaban shi sai gata dakina tana cika tana batsewa tace tana kiran ki .
Niko ina cewa yaya anyi nasara dai ko kin samu magana dashi tace ina yar bakin cikin zata bari ai komawa zanyi ko bata so.
Nace antyn ne yar bakin ciki tace to in ba bakin ciki ba ko zama bata bari nayi ba ta koreni da karfi da yaji ban san abinda take nufi da hakan ba.
Mikewa nayi zuwa amsa kiran anty na je da sallama na ce anty ance kina kirana tace eh kin ga don Allah wanan gwauron zaki hada ma fruit salad wai yake son sha yau.
Ban tsaya ba na juya zuwa kitchen din ya dan kalle ni ta witsiyar ido a ranshi yace ba laifi yarinyan sai dai akwai shamaki a tsakanin mu.
Ban dauki wani lokaci ba wurin hadawa don akwai komai na bukata kankara na jefa yadda zai yi saurin yin sanyi bayan na hada din.
Na nufo dashi nan na tsikayi Fati zaune tare da su tana wani kwarkwasa yar nata nata hararan ta bata damu ba nazo gaban shi na aje yace dani thanks kawai na juya zan wuce..
Anty tace dan tsaya ki zuba mashi nima ki zubo min karya shanye ba sha ba nan na juya na sake dukawa gaban shi ina diban mata kamshin turaren madina dana shafa ya dokan hancin shi sai lumshe ido yake yi cikin sytle.
Na diba na bata na dago muka hada ido da Fati sai naga tana harara na ni dai na wuce abina ban kara juyowa ba.
Sai gata dakin ban bari tayi magana ba nace kai amma Fati kunyi balain dacewa da wanan mutumin gaskiya.
Da da fushi ta shigo amma jin abinda nace yasa ta washe baki tana fadin gaski Safiya nace kwarai kuwa kiyi kokari anty tafahinci ki .
Tace haka za ayi ai don haka sai na zauna ki fada min ta inda zamu bullo mata nace niwa aini yar kauye ce ban san komai ba wallahi..
Da yamma muna falo gaba dayan mu Faiza ke cewa wai ni yaushe Yaya sulaiman ya wuce dazu ne ?
Kafin anty ta bada amsa Fati tai carab tace ai kedai yau ya dade gidan nan sai anty ta balla mata harara tace ke aka tambaya ko kin san wucewar shine.
Wai ke may yasa baki da hankali ne Fati sai tai wani turo baki kamar karamar yarinya nace anty kin sani ko za ayi yar gida ne.
Tai saurin cewa haba Safiya don Allah kibar wanan zance ki kyale ta da shirmay ta can so take mukai ga yadda ba a so.
Ita ke haukan ta nan shi yana da wace zai aura ko ina ma zai kai ki haka kazama dake sai tai fushi ta daga wurin Faiza tace da gaske anty ya samu mata.
Tace insha Allahu muna fatan hakan amma sai komai ya kankama zamu je ayi magana don ba yar kasan nan bace yace.
Nan ta hau murna don jin dan uwan nata ya samu wace zai aura ashe maganan ya fada kunnen Fati dake wuce wa.
Sai da na dawo daki ta samay ni da maganan nace tayi kokarin cusa kan ta dai in Allah yayi ai ba wanda ya isa ya hana ta sauke ajiyan zuciya tace shiyasa nake son ki wallahi don fadin gaskiya.
Ni dai na samu ta fita na rufe kofa na asuba ta gari sai kuma in Allah ya kaimu lafiya muji da wace zata zo min kuma a gidan.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , , , , ,
🧕🏿3️⃣3️⃣🧕🏿
YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDINE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BAN YAFE BA IDAN KON FITAR MIN DA NOVEL UBANGIJI YA SAKA MIN A KANKI CIKIN GAGAWA.
Wanan abin yasa yanzun muke shiri da Fati don ko yaushe tana dakina muna hira abu daya kullun na yadda zata shawo kan shine a gidan.
Zata shigo ta fadi nidai ina ta mata dariya indan ta gaji ta fice ta koma dakin ta, sai dai abu daya ne wanda ban yarda da shi ba.
Irin yadda take kushe maganan anty ko take sukan ta da munana kalamai marasa dadin saurare.
Don haka sai na dakatar da ita nace idan zamuyi hiran mu mubar saka sunan kowa mudai nemi mafita akan yadda zamu fito mazancen ta da sulaiman din.
Taso tai hushi alokacin amma sai tai tunanen ba ida take kai maganan ta ba tare da wani yaji ba sai gurina, sai gashi ta dawo da kanta.
Ina kwance daki sai gata ta fado min daki tana dariyan jin dadi nace halan mutumin ya shigo ne.
Tai wani far da idanuwa tace dani bai shigo ba tukun amma naji mijin anty na waya dashi wai su hadu karfe hudu nan gidan.
Nan dai mukai shawaran abinda ya dace tayi tabar dakin tana ta murna nikan fitan ta dakin na kwanta abina don ina fashin yin sallah a lokacin ban son shiga mutane.
Kamar yadda Fati ta fada hakan ne yazo gidan bayan hudu ya dan gwauta kadan yana falo da anty daya sama a falon ita da yaran ta.
Tun shigowan shi take faman sake murmushi a fuskanta kamar yadda ta saba indan sun hadu.
Ya zauna suna gaisawa da ita yace komao lafiya ko ta amsa mai da lafiya kalau muke, tace yaya aiki kuma?, ya lumshe idon shi yana cire hular kan shi .
Yace aiki muna kai wallahi yai ajiyam zuciya yace yanzu ma mijin ki ne ya kirani koda yake dama yau ina da niyar shigowa gidan naku.
Sai ga mijinki ya kirani kuma tace ka kwana biyu baka shigo nan din bane ya sake cewa wallahi yau nake da niyar shigowa don ina son in baki wani aiki ne.
Ta nisa tare dacewa tau fa, ina jinka rankaya dade,
See you nine ranka ya dade kuma ni dai kisa a hada min wanan abin don yau dashi zan tafi don ina son shi sosai wallahi.
Mikewa tayi don yaran sun shige don bude tsaraban da ya shigo masu dashi da zaizo don haka babu yaro kusa sai anty taje kirana da kanta.
Tana wucewa Fati ta fito acikin wani irin kwaliya tana kashe ido wai tana mai sannu da zuwa takai zaune a dayan kujeran falon.
Niko ina daki na kwanta wuri daya na dunkule wani iri kamar maijin sanyi idan ka ga yadda na kwanta.
Tabani, tayi tana kiran sunana a hankali, inda na bude ido na sauke a fauskanta ina mai kallonta cikin magagin barci sai naji ta tambaye ni dacewa lafiya kike kuwa kike ta barci haka ?
Na murza idona tare da cemata anty barci ne kawai ya dauke ni tun dazun tace to tashi don Allah aiki zan saka ki don wanan bakin batauren ya shigo wai fruit salad yake son aimashi.
Na sake murza idona nace to anty barin tashi yanzu zan fito ta mike don barin dakin nawa har takai kofa nace ina mike wa Fati na nan ne muyi tare.
Tace Fati ko mashiririciya may zata iya wanan don Allah fito ki hada mashi tunda har yai magana kada ya tafi ba a hada mai ba kuma.
Hankalin shi naga wayan shi baiko san tana zaune a wurin ba ita kuma sai wani gyare gyare take yi daga zaune kamar wacce ake tsunkulan ta.
Anty ne ta iso gurin tun da ta ganta ta daure fuskan ta har tazo ta zauna ba walwala a fuskan ta.
Ta zauna tare da cewa ke kuma may kike anan din kije safiya na jiranki ki kama mata aiki.
Ta juya inda yake tana murmushi tace ina jinka sakon may kake magana akai ne wai ?
Ok dama account dinki nake so inyi amfani dashi in tura ma wani kudi miliyan hamsin mun sai injin ne a gurin sa .
Sai bayan sati biyu zaa fitar da kudin kinga kenan kema zaki iya samun wani abu daga yin hakan .
Tace sulaima ba matsala gayin hakan dagowa yayi yana mata dariya yace idan da matsala ai ba zan saki a ciki ba kedai ki bayar zaki gane abinda nake nufi.
Sai ya fara mata bayani a takwaice yace ashe ke matsoraciya ne kina tsoron kada a yaudare ki ko da irin haka yawancin mutane suke dagawa ina son inga account dinki yana motsine.
Nan ta shiga dariya don ta gane mafusa arlallan business yake son sakata ciki itama nan ta shiga yi mashi godiya daga mata hannu yayi yace haba madam ya idan ban maku ba suwa zan taimakawa ?
Yace sai dai gida da fili danake son saya a Abuja ta saki baki tana kallon shi don jin irin bayani da yake mata na gida da filin da yake so.
Ta sake cewa yanzu sulaiman ga gida ga fili kake shirin saya haka yace ai wanan ba komai bane sai tai wani irin shewa.
Tace iyyye tun yanzu ashe bari mu fara shirin buki ashe,
Dariya ya fara mata yace ba a sayen gida sai za ai aure ki rufa min asiri tun dawowan mu kudin nan nake son in sai gida da fili dasu, don ina yin wani aiki acan Abujan kuma dai ina ganin anan zan zauna don nafi son zama arewa da nan din.
Tace kayi dabara wallahi shawaran da nake ba daddy su kenan ko yaushe amma naga shi ra, ayin shi baison zama arewa sam.
Yace arewan ne babu dadin zama saboda mutane yan sa ido ga abin da bai shafe su ba sai suyi tama zargin banza ba gaira ba dalili kai kana neman nakan ka amma mutane idon su na kanka.
Mijin anty ne yashigo sai suka can za firan suka fara gaisawa dashi a daidai lokacin da na fito dauke da tiren a hannu na da na shiryo mashi.
Daddy din na fara gyarwa sai shi sai daddyn yace Safiya kike ko kina gidan nan ban gani ki sai nike tsamanin ko kin koma ne ban sani ba.
Murmushi nayi kawai sai anty ne ke cewa ita wanan ai in ka ganta waje su yan biyu ne suka fitar da ita dole zaman daki baya isan ta ko yaushe tana ciki kumshe.
Na gama jerawa zan wuce sai naji tace yauwa daddy shine nace ma mutumi na ko zai fada neman Safiya ne ya tsaya yana min kwana kwana.
Don Allah ba sai yar gida gida ba kawai ga mata har gida ya samu ba niba har mijin nata wani irin kallo yai mata nidai na wuce na barsu nan.
Ina ganin sun dade a wurin sai dai ban san maganan da sukeyi ba dagani dai maganan tana da muhinmanci a gare su.
Sai can naji fitan mazan daga gidan wanda ban debe tsamani sallah suka fita yi don lokaci da yayi yan biyu ne tazo take ce min mummy su na kiran su.
Ban tsaya ba na jawo dankwali na dora a kaina muka fito tare da yarinyar da tazo kirana din .
Tana zaune tana hada wasu takardu dake saman table din gaban ta tace kinga bai ko sami tafiya dashi ba yadda yace anan suka shanye abinsu shida major.
Ina kwasan kayan nake jin yadda anty ke ta faman yabon sulaiman din har take ce min wallahi safiya idan na samu nai wanan hadin a tsakanin ku kowa naki ya huta indai Sulaiman ne don bai da matse na tare dashi balle matar shi mutum ne mai sakin aljihun shi sosai wallahi.
Nidai abinda na saba nai mata watau murmushi sai dai a raina nace kardai anty ta zamo cikin masu rufe ido ayi cuta da ita kan abin duniya.
Ni dake da lalura har take zancen hadani da wani wanda baida matsala irin nawa ni yanzu aiko mai irin matsalata banda lokacin shi balle mai lafiya in cuta mai.
Na kwashe kayan zuwa kitchen da zan fito ma ban dawo wurin ta ba sai nai hanyan dakin na don zancen ta ba abin saurare bane a wurina.
********* ********* *********
A can gida kuwa ummi da kanina shafiu sun rike sanaar da na bar masu dakyau don takar ina gari ne don yaron bai da wasa ko kadan.
Saadatu inna ta kwaso ciki tun ba a gane ba har mutanen gidan mu suka gane ana ta kumbiya kumbiyar zubarwa sai dai Saadatun taki ba Inna hadin kai a zubar da cikin tace tsoro take ji.
A wani dare basu san baba yana waje yana alwala ba rikici kan azubar da cikin ya hada ta da inna a dakin su tun bai sauraren su har takai baba ya saka kunne ga maganan su.
Nan yaji abinda ya tayar mashi da hankali ya koma dakin shi sai kuka koda gari ya waye bai fito ba har wani lokaci.
Mama ne ta shiga dakin shi don taga may ya samay shi ta samay shi a cikin wani hali take hankalin ta ya tashi.
Zata tara mashi jamma a yace taje dai ta kira mai inna da su ummi da yaya Sani su zo.
Kowa ya taru suna jiran suji may zai fada masu sai can yace ma mama yanzu har da ke ashe za a hada kai a cuta min gidan nan.
Abu na faruwa haka amma an rasa wanda zai iya fada min sai da Allah ya sanar dani jiya da dare nan ya kwashe abin da yaji tsakanin inna da Saadatu yake fada masu.
Nan Inna ta kama fadan karya wai baidai ji da kyau ba mama ne tace haba Rakiya ko makaho ya lalube saadatu ai yasan halin da take ciki.
Don baki samu bane shiyasa muka kawo ido muka saka maku kawai amma batu duk ya gama bin gari ai.
Shiru wurin yayi sai yaya Sani ne ya kawar da shirun da cewa Inna kin kai ga yadda kike so ba abin da baki fada akan matsalan Safiya agidan nan.
Yanzu gashi ke Allah ya nuna maki nashi isharan sai ku san yadda zakuyi da ciki ai maza basu son ta da aure amma suna son ta da lalata.
Baba yai magana karo na biyu yace ba mai zubar da cikin nan a gidan nan don bani kunya biyu abarshi ta haifi abinta kuma duk wanda yace zai yi yunkurin zubar da cikin nan sharia ce zata raba mu dashi.
Nan ko inna ta aza hannu akai wai dama ta sani baba bai kaunar ta da diyan ta ai yafi son yaga sun lalace a gidan.
Yace yadai ji amma ba mai zubar mai da ciki a gidan shi sai inna tace zata kaita wurin yan uwanta a wani kauye a zubar can.
Amma ba yace bai yarda ba da kuyan lahira ya kwmmace yai na lahira don zunubin shi bai kona shiba na yar shi ba zai kona shi ba.
Haka dai aka watse baram baram a wurin inna ta shige dakin ta tana kuka diyan ta ma suka bita kukan sukeyi suma.
Gidan dai ya koma masu ba dadi na kira ummi da safe don inji lafiyan su take fada min halin da ake ciki nan ko na tausaya masu sosai.
Ummi tace min abinta ne Allah ya mayar mata ta gani ko tafiyan nan ba abinda bata fada ba wai karuwanci kika je yi acan.
Yanzu gashi taga abinta har a kuryan dakin ta ta koma mujiya a gidan don ko fitowa bata son yi tsakar gida.
Abin su na kishi a yadda ummi ke magana sam bata tausaya ma inna da Saadatun ba sai nine nace ummi wanan abin fa ba inna kadai ya shafa ba har daku dake da diya a gidan.
Don suna gidan mu ne zai lalace ga banza sai ai muna bugun dan kadanya gaba dayan mu ba wai za a ware ta ita kadai bane a zaga.
Sai naji tayi lau shi tace abin tane ai da ban haushi wallahi nace hakkuri za a yi a rungumi kaddara tun da baba yace ba a taba cikin.
Nan dai na bata shawara nakuma ga ta dauka san nan mukai sallama na kashe wayan cike da jimay abunda naji din.
Banyi niyan kiran saadatun a yanzu ba sai hankali ya kwanta zan kirata in kwantar mata da hankali don nasan bayin ta bane sherin uwar ta ne Allah yake nuna mata abin ta tun a duniya.
Sai dai kwana biyu na shiga damuwa sosai har anty ta fahinci haka ranan ta kirani dakin ta dama nasan kira dakin ta magana ne na muhinmanci.
Nan ta shiga tsoratani da nasihohi iri iri na ban tsoro don ita tana zaton halin da nake ciki ne nasa damuwa akan shi.
Nan dai nace mata anty bashine ke damuna ba yar uwata ce ta shiga wani hali abin yake damuna arai.
Ba abin da zan iya boye mata yanzu sai na kwashe komai dake faruwa na fada mata sai da ta bari na gama fada mata komai sai tace dani.
Lallai Safiya kina da imani a zuciyar ki in bashi ba matar da take son taga bayanki zaki dauki damuwar ta ki saka a ranki karfa ki jawa kan ki wani sabon lalura gaki yarinya karama dake.
Addua zakiyi mata kawai shiya fi nace anty ban taba jin tsanar diyan Inna araina ba don itace maisa suke min abinda sukeyi din tace ai shi nace kiwa yar uwar ki addua Allah ya rabata lafiya don aikin gama ya gama ko.
Nai mata godiya zan fita tacevin dakata ledan dake gefen ta ta miko min nasa hannu biyu na karba ina godiya tace bani zaki godewa Sulaiman ne ya saya maku.
Yaji ina maganan saya maki waya yace in bari zai kawo maku waya yau ina office sai gashi dasu guda uku shi na zaba maki wanan farin ga sauran nan zan ba su faiza nasu ita da fati .
Nan shiga mashi godiya da addua ita ko sai dariya ta min tace ai wanan karamin aikin shine wallahi .
Ranan haka muka kwana da murna tare da mu kowa yana farin cikin rike babban waya a cikin mu wanda kudin shi zai iya kai dari da hamsi.
Ranan ina kwace falo saman doguwar kujera kasalance sanyi da iskan dake fitowa daga naoran sanyayya falon na barazanan saukar min da barcin marance.
Sai ga Fati ta fito falon daga dakin ta take cewa dani wai dama dakina zata ashe ina nan zama tayi gap da kaina tace .
Dama wani abu nake son kin min Safiya sai na dago ina kallon ta don jin may take so na dashi.
Ta dan nisa take cewa ba wani abu bane nake so sai ki dauko min lamban mutumi na a wayan anty idan kin samu hali don bata yarda in dauki wayan ta sam.
Ke naga kuna dasawa da ita don jiya naga ta baki wai ki tura abubuwa a cikin wayan ki.
Ban kai ga bata amsa ba sai muka ji sallaman shi a kofan falo ya karasa shigowa yana rike da brief case din shi tare da su yan biyu a bayan shi ga katuwan leda da ya riko a dayan hannun shi wanda nasan tsaraban su yan biyu ne a ciki.
Daga inda nake kwance mukayi arba dashi ban riga na kai ga tashi zaune ba.
Har suka karaso inda nake yaran suka fado min suna cewa yau uncle ya kaisu yawo birch sun ga ruwa da kifi .
Na yun kura na tashi zaune ina kamo dan kwalin kaina da ya zamay min don a kwance nake.
Ita ko Fati duk ta rude da ganin shi zuciyar ta ya rinka saka mata tunane daban daban ba gaira ba dalili na samu na kai zaune ina mashi sannu da zuwa.
Bai dago ya kalle ni ba sai dai a ranshi yana nasawa tabbas yarinyar kyakyawa ce mai cike da kwarjini da kamala ya fadi a zuciyar shi.
Sai naji Fati cikin rudewa tana cewa gashi ko anty ta fita har yanzu bata dawo ba kamar bai son magana naji ya bata amsa da tana tafe sunyi waya da ita ai.
Mikewa nayi zuwa kicthen na hado mai abin sha da ruwa na kawo mashi sai ga anty ta dawo har fati ta zauna tana mashi zuba a gaban shi.
Nan mukai mata sannu da dawowa nikan na bar wurin sai yaran suka biyu ni suna bani labarin fitan su da uncle din.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , ,
🧕🏿3️⃣4️⃣🧕🏿
YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU DON BA A YAFE BA, , , ,
Anty ce ta shigo gida da karfe shidda na yammaci duk muna a falo zaune sannu da zuwa muke faman yima ta tana amsawa a gajiye takai saman kujara ta zauna tare da fadi wassh Allah yau na gaji sosai ga shi kuma gobe zan bi hanya da safe.
Gaba dayan mu maida mata hankali mukayi don jin ina zata tafi kuma da safe da tace din, mike kafa tayi saman dan stole din da ke gaban ta tana gyara zama take fadin .
Gobe tafiya zamuyi da uncle Sulaiman zuwa abuja zamu tafi muga wurin da yake son saya ya matsa sai baban su yan biyu yaje yaga wurin dani kafin ya saya.
Faiza ne tace ai hakan nada kyau mutum ya dinga sa ba gabatan shi gaba kafin yaya abu sai anty tace wanan ai halin Sulaiman ne.
Har sukaci suka sude ban saka masu baki ba ina daga kwance ina sauraren hiran tasu anan na dan fahinci wani abu a tsakanin su.
Tun da asuba ta shirya wai ashe ta jirgi zasuyi tafiyan bakwai yai masu a airport jirgin su bai dade ba ya daga zuwa abuja.
Muna gida zaune ni da faiza ita kuma fati tun tafiyan su ta fita daga sunan baza ta dade ba sai gashi har hudu na yamma yanzu.
Hudu ya gwauta sai gata hurjanjan ta shigo gidan bata ko kalle mu ba ta shige dakin ta Faiza ta kalle ta ta tabe baki.
Nidai na mayar da hankali ga tv don karamin aikin faiza ne yanzu ta dauko topic din fati aduniya taki jinin Fati da komai nata.
Itama fatin na kula da haka bata kaunar Faiza don takance min munafukace wai don haka zama a taka tsantsan ya kamani a cikin su sai bani yarda daya yayi da daya a bayan shi.
Ban jima ba a wurin na mike na shige daki da yan biyu don bada su aka tafi ba na zata kwana zasuyi sai gashi sun dawo da yamma .
Tana da gajiya don haka bata zauna da mu ba tayi dakin ta don sauke gajiya a jikinta lokacin ne fati ra samu daman shigowa dakina.
Ni sai da naji tsoro lokacin dana ganta tace ke matsoraciya nice na sauke ajiyan zuciya .
Nace may ke faruwa ne Fati na ganki da daren nan haka, ta dai ce uhumm kawai ba tare da tai magana ba takai zaune a wurin .
Tace aike dai baki sani ba yau naje wurin wani mai magani ne a wani kauye wani irin kallo nai mata na dafe kirjina nace maigani kuma ?
May kika tafi nema gun mai magani ko baki da lafiya ne ban sani ba sai naga ta girgiza kai tana cewa haba dai kamar ba mace kike ba .
Zuwa nayi a samo min kan madam din gida da kuma mutumin nawa gaba nane ya fadi ras taci gaba da yi min bayanin abinda ya kaita .
Ban iya karasa sauraren ta ba sakamakon fadawa tunanen danayi mai zurfi a raina nace tabas inda akwai abinda na tsana shine inga mace tana biyan bokaye da malamai a rayuwanta.
Balle fati da ko aure batayi ba ta fada wanan akidar sanan babu kunya babu tsoron Allah ko nauyi bata ji har tana fada min inda ta tafi da yadda akayi.
Wanan abin ba karamin tashin hankali bane musanman ma da tace takai har da anty gun mai magani to aima yar uwar nata may can.
Ida babu kuya babu tsoron Allah take fada muna yadda suka kwashe da boka a take na suma jin hawaye masu dumi na bin kuncina bata farga da hankan ba sai daga baya.
Maganan da tai min ne ya dawo dani hayaci na kallona take yi da wani irin mamaki baiyyane a fuskan ta ta ce dani Safiya may ke faruwa ne naga kina kuka daga ina baki labari.
Girgiza kai nayi cikin takaici nace Fati waya baki wanan shawaran na zuwa wurin boka at dis age da kike har kin san hanya bin bokaye.
Abin haushi da takaici kuma kirasa wacce zaki kai sai yar uwar haihuwar ki wace ta zamay maki uwa da uba ga komai naki.
May kike nema wanda wanan boyar Allah batai maki ba a rayuwan ki muma da ba uba daya muke ba may ta rage mu dashi a rayuwan mu.
Kafin in fadi wani abu sai ta katseni da cewa bafa wani abu nake so gare ta ba kawai yardan ta nake so ga bukata na akan sulaiman kawai.
Na girgiza kai har wanan lokacin fuskana yana dauke da guntun hawaye wani irin kallo nake binta da shi mai nuna tsanan abinda ta fada min.
Sai ta hau cewa ni fa yarda da amincewa yasa na fada maki da ace nasan ke ba yar hannu bace ga wanan harkan ba abinda zai kaini fada maki .
Nisawa nayi nace wallahi zan fada maki gaskiya tun wuri ki daina wanan halin tun bai zama maki jiki ba ko.
Ta mike tana cewa yau hiran namu dake ba zai yi ba do bani son mutum mai kara min zuciya akan abin da na saka gabana.
Tamike tare da nuna ni da yatsa tace i hope wanan maganan ya tsaya iya ni dake kawai a gidan nan idan naji shi a waje zamu samu matsala dani dake sai ta fice.
Kallon mamaki na rakata da shi ta buga min kofan daki garau ta fita na sauke ajiyan zuciya ina mamaki halin matan yanzu har da macen da batai aure ba ta iya zuwa gurin boka don kawai a asirirce mata yar uwar ta ina ga in ta samu kishiya kuma ?
Tun wanan lokacin mukai sanyi ni da Fati Faiza tayi tayi tasan may ya hada mu bamu kaman da amma naki fada mata sai ce mata nake yi kila ta samu wata kawar ne a waje.
Yanzu anty bata faye zama a gida ba suna aiki sosai a wurin aikin su don haka sai kula da gidan ya dawo hannun mu.
Duk da dai sauran ba wani abu sukeyi ba sai ni da mai aiki zamu aiwatar da komai kafin masu gidab su dawo Faiza irin mutanen ne masu fuska biyu.
Amma bayan haka ta na da kirki sosai amma sai na fahinci akwaita da aikin ganin ido abinda bata sani komai da muke a gidan yana kunnen anty.
Ta san yadda kowa ke rayuwan shi a gidan ido kawai ta saka muna tana kallon kowa da halin sa ranan da rana anty tai muna dawowan bazata a gidan .
Ina daga ni sai mai aiki dake wankin kayan ta nikuma ina muna girki da zamuci ga yaran ta zaune suna kallo a falo na dafa masu indomie kafin an gama hada abincin gida.
Su ko faiza tana barci a dakin ta tayi dadaya a saman gadon ta Fati kuma ta fita yawan ta sai in yai mata dadi kafin yar ta dawo aiki take dawowa gida.
Tana shigowa ta samu yaran na cin abincin da na aje masu suke ci take tambayan su suka ce anty safiya ne ta dafa muna.
Jin motsi yasani fitowa ina yarfe ruwan da na daureye hannu a hankali naga itace ashe ta dawo nake mata sannu da zuwa.
Tace sannu da aiki safiya shiya yanzu sai in fita gidan nan hankalina kwace ba tare da fargaban wani abu ba ga yaran nan dako ban da kwanciya hankali idan na barsu a gida don kamar ban barsu da kowa bane saboda basu samun kulawa yadda ya dace..
Har na gama girki na kawo ma anty nata sai mai aiki ta shigo ta samay ta a zaune falo ta fara gaisheta da dawowa.
Tace yanzu na gane zuwan safiya gidan nan yai maki dadi don duk kin tatara aiki kin bar matayi daidai ina kawowa anty ruwan sha naji tana fadin haka sai nace a a anty tare, , , ,
Hannu ta daga mi alaman in shiru naja bakina naci gaba da jera mata abincin tana may ci gaba da fadan da takewa funke mai aikin ta.
Sai ga Fati ta dawo nan tabita da harara simi simi ta shigo tana kamay kamay fada tai mata sosai ranan har ni din bata bari ba.
Bayan kamar kwana hudu dayin haka kowa a cikin mu ya shiga taitayin shi don gudun laife gare ta daga ni sai Faiza dake charting a wayan ta.
Sai gata ta shigo gidan sun dawo unguwa da yaran zaune nake zugun nayi tagumi nayi zurfi acikin tunanen duniya.
Sai muryan ta naji daga sama a kaina tana fadin Safiya wallahi zamu bata dake a gidan nan matukar baki daina damun rayuwanki da tune tunen marasa tushe ba ke kadai ke gidan nan ne da kika kasa sake ranki cikin yan uwa kiyi walwala.
Na dago kai da sauri ina kallon ta a lokacin ya shigo da kaya niki niki da suka sayo ashe tare dashi suka fita unguwan .
Nisawa nayi ina mata sannu da zuwa sai dai bata amsa ba sai ci gaba da fadan da takeyi min kamar ba magana yake yi ba don hausa shi da baya fita da kyau yace.
Bata da lafiya ne ko may ke damun ta haka din ?
May kuwa uncle na rasa gane hankalin yarinyar nan tun da tazo gidan nan taki ta sake jikin ta kamar kowa sai zama tana yawan tunanen banza da wofi ita kadai.
Zaune yakai saman kujeran da fuskantar mu tare da aje kayan da suka shigo dashi din tace kamar wanan yarinyar da bata wuce 19 years ba zata saka ma kanta tune haka.
Jinayi yace keko may yasa kike haka din tunda antyn ki bata son yadda take ganin ki ba kamar kowa ba a gidan yana magana yana kallo na .
Yaci gaba da cewa don Allah ki kwantar da hankalin ki ki daina damun kanki koma may ye a ranki ki fitar dashi don tunane yana iya kawo maki illa a lafiyar ki.
Ya maida kallon shi ga anty yace bata dade da zuwa nan din bane ko may ko gida take tunane haka ?
Tsaki tayi tace wani irin dadewa kuma ai duk ta rigasu zuwa nan halintane hakana din kawai dason shiga damuwa.
Shi ya kawar da maganan da dauko maganan bude gidan shi da suke shirin yi yace sai in an gama tsarawa zai zo mata da yadda akayi ya mike yana shirin wucewa sai lokacin tace dashi ba zaka tsaya ta hada maka fruit din ba.
Yace no barshi kawai zan tafi don naga mai hadawan bata cikin hayacin ta mikewa nayi da sauri nace barin hada zan iya ai.
Ban dauki lokaci ba na hado mai nakawo yace dashi zai tafi don baida lokacin tsayawa yasha a nan din, har waje suka fita da anty sun dade sai gata ta dawo ciki.
Lokacin muna zaune da diyan ta da Faiza tace in bude ledan da suka shigo dashi gidan in fitar da kayan dake ciki.
Nan Faiza ta tayani fitarwa muka fitar da kayan wanda yawanci duk na twins din tane tufafi da kayan makulashen yara tace mu diba in kai saura dakin su.
Bata barni haka ba dana dawo na zauna sai da ta bini da nasiha kan in cire damuwa a raina Faiza ke cewa ta rasa may nake wa yawan tunane hakana.
Ba laifi nayi korin ganin na fitar da komai a raina sai dai ba abinda zan iya fitarwa kai tsaye bane yadda take nufi amma na dan rage yawan sa ma kaina damuwan da nakeyi din.
Mako biyu tsakani ranan muna zaune dukkan a falo sai ga ta ta sauko daga sama ta zauna take cewa Fati ta shirya mata kayan su yan biyu zata Abuja gobe tafiya ya kamata.
Sai ta juya gareni tana cewa ke ma Safiya ki shirya don dake zan tafi saboda yaran nan ba zasu barni ba inyi abinda ya kaimu da sauri Fati tace anty nima in shirya ina sin zuwa Abuja wallahi.
Tace da Safiya zan tafi ko ita don yara zan tafi da ita Sulaiman zai yi bukin bude company a can da gidan da ya saya a take fati ta shiga rokon ta wai taje da ita.
Tace karatun ki fa fati kina fa wasa da karatu gashi kun kusa rubuta jerabawan fita ke bakiyi ma kanki fada ne wai kamarki har yanzu a secondry school ?
Nan ta turo baki gaba tana fadin na dai gane kin fi son safiya damu a gidan nan komai sai kice safiya ita kadai.
Tace dole ne in ce safiya don tafiku hankali da tunanen abinda ya kamata ko ruwa kuna iya ba mutum ne in ba ya kama maku dole ba.
Faiza ma ta marairaice mata saida tace duk su shirya mu tafi tare sannan aka samu lafiya don da Fati ta hau sosai ga maganan.
Kowa ya shiga shirin tafiya don tace sako zamuyi mu tafi kala uku kawai na dauka koshi dogayen riguna ne kawai na zaba.
Tun da safe muka kama hanyan abuja a mota mukai tafiyan don mijin ta baya nan suna ruwa wurin aikin shi basu fitowa sai bayan watanni a ruwan shiyasa ma bai faye zama a gidan ba.
Gidan su na abuja muka sauka wanda shi mijin tane wai yake dashi don harda funke mukayi tafiyan bamu bar kowa a gida ba.
Gidane mai dauke da dakuna hudu da falo daya na maigidan inda ta zauna a ciki sai dayan wanda fati da Faiza zasu zauna ni da yara tace mu shiga guda sai mu bar ma funke na farin shigowa wanda dama saboda masu aiki akayi shi.
Ba wani hira don kowa na da gajiya tare dashi wanka kawai mukayi sai abincin da aka kawo muna daga wani gidan abinci ina jin Faiza da fati na ta santin abincin don dadin shi niko takura bai bari naci sosai ba don na lura dukkan su biyu kamar yanzu sun tsane ni a gidan don yawan nuna mani kulan da maigidan namu takeyi ko a gaban kowa.
Na riga kowa shigewa ashe sulaiman din yazo gidan bayan na shiga barci nan Fati ta kama rawan kai saida anty ta tura ta ciki ta basu wuri.
Washe gari tun da safe da ta fita bata dawo ba sai wurare karfe hudu ta dawo gidan nan ma bata huta ba don wasu suka zo suna tsarare dasu.
Har na kwanta sai ga anty dakin na mu hannuta rike da tasbaha tana ja shiyasa nake son ta don wayen wata da tsabgogin gabanta bai hanata yin ibadan ta sam.
Mikewa nayi zaune daga kwanciyan da nake ta kalle ni tace wai ko kin dauko kayan kwarai kuwa Safiya don taro ne na masu hannu da shuni za a yi.
Nace anty na dauko wanan riga ne da kika sayo muna ranan na fadi tare da kallon ta don jin may zata fada gamay da shi.
Cike da tsukana tace min Safiya ai da kin tona min asiri a cikin taro da sai in nuna ba tare dani kike ba a wurin kawai kisa mutane su raina min da wayo ?
Dariya nayi itama abin ya bata dariya don jin nace anty wanan riga mai balain kyau.
Tace kin ga ni yanzu ma fita nazo kirakani muyi dama nayi tunanen hakan ki shirya ina fitowa yanzu zamu fita da faiza ba zan je da wanan mai rawan kan tsiya ba ta bani kunya.
Ashe harta fada ma Faiza ko koda na fito faiza na falo zaune tana kallo hijjab da dogon riga nasa ta kalleni ta wani kwashe da dariya .
Sai kuma tace min mutumiyar na ciki tana fushi wai za a fita damu bada itaba kafin in magana sai ga ta tafito tana saka ma kofa key tare da kiran Funke tana cewa ta kula mata da yara da sukai barci tun da magariba.
Na muka fita tare da rufo kofan gidan mukai ma Funke sai mun dawo wata mota baka muka samu waje a kunne yana jiran fitowan mu.
Baya muka zauna inda sai wani kamshi da ban taba ji ba ya daki hancina ga sanyi AC mota suka hade suna bada wani irin yanayi a motar, ita ta zauna gaba tare da driver muka kama hanya fita daga gidan kallon titi nakeyi inda naji Faiza tace ina wuni yaya Sulaiman .
Sai lokacin na dawo daga tunanena nace dashi ina wuni ya amsa muna a tare lokaci guda anty ke ta hira sai eh ko aa yake ce mata.
Tafiya mukayi mai nisa sai gamu bakin wani shago maigirma anan muka firfito inda muka barshi a cikin motar zaune muka fara shiga mu da anty.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , ,
🧕🏿3️⃣5️⃣🧕🏿
YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA DON BA A YAFE MAKI BA HAKKIN KARANTAWA BA BIYA.
Tunda nake ban taba zuwa wuri irin wannan ba a rayuwa na sai dai ban nuna ba saboda natsuwan da Allah yai min.
Sune a gaba ina binsu baya a hankali anty tace mu diba mu gani sai ban tafiba nabi bayan anty din wasu jakka da ta kalma take dubawa bata san ina bayanta ba.
Sai nace kai anty wanan kayan zaiwa su yan biyu kyawo sosai ta juyo da sauri tana cemin har kin duba ne?
Jin nai shiru yasa ta juyowa tana fuskanta tana tare da cewa mai kika zaba ne nace ban dauki komai ba kai ta girgiza kawai taci gaba da daukan abinda take so.
Tafiya takeyi tana fadin sai ki zabar ma diyan naki kayan a tare mukaje wurin kayan yara na fara duba masu sai kuma na gaza itace tai ta zama musu kalloli masu kyau.
Batai min magana ba sai wucewa da tayi layin riguna ina biye da ita can ma zaban taitayi tare da atamfofi.
Ni dai har muka gama a shagon banga sulaiman din ba sai nai zaton ya ajemu ya tafi ne to wa zai mai damu gida daren nan haka.
Acan wurin biyan kudi muka hade dashi bai sai komai ba sai turare guda biyu ya dauka bazaka ce tare muke dashi ba yadda ya nuna a wurin.
Ni dai kafana ya gaji da tsayawa sai na fita daga shago na samu bayan wani mota na jigina jikina dashi.
Sun gama suka kwaso kaya niki niki suka fito zuwa motar na tako inda suke na samay su ta dago tana ceman yayi da ake sakayan a both din motan da muka zo dashi.
May yasa kika fito daga ciki nace na zata magana zasuyi ai shine na basu wuri tsaki taja kwai tana bude kofan motan muma muka nufu motar muna budewa.
Har muka iso gida ba wanda yai magana a tsakanin ni da Faiza sai da motar ta tsaya ne muka fito nan muka fara jidan kayan zuwa ciki dasu sai a lokacin naga ashe ba karamin sayaya mukayi ba .
Dakin anty muka nufa dan kai kayan can amma sai tace mu zube su a falo na ta zauna tare da jawo wani laida sai naga ashe nama ne gadade suka saya a wurin .
Tana fitar da kayan tana cin nama hankali kwance ta miko min wani laida shake da kaya tana cewa ungo naki matsoraciya kawai ta kuma mika min wani karamin laida da kayan sanyi da naman ciki faiza kuma ta dauki nata zuwa dakin su kowa ya shige muka kashe wuta muka watse wurin.
Da safe kowan mu ya makara don haka bamu fito da wuri ba ni dai ina kwance bayan nayi sallah sai na koma barci.
Banyi nisa da barcin ba sai ga anty ta shigo daki da hijjab din ta tayar dani tayi na mike zaune tare da gaisheta da kwana takalleni tace safiya kinyi sallah kuwa ?
A girmamay nace nayi sallah anty tun dazun sai tace madalla tashi mu fita gidan nan tun yan bakin nan basu tashi ba mu fita daga gidan nan maza ki tayar min da wa yan nan sarakunan barcin yanzu mu tafi.
Har muka gama muka fice daga gidan basu sani ba wurin gyaran gashi suka tafi don har dani anyi mawa ina ban so amma sai da anty tasa akaimin gyaran na koma kamar bani ba.
Ni kaina nasan gyaran ya fitar min da kyaun surar fuskana don ban taba gyara irin haka ba bamu dawo gida ba sai shabiyu da rabi muka shigo gidan.
Mun samu sun cika fam sai dai ba mai iya yin magana a cikin su dole kuma suke gyashe mu da dawowa .
Nan muka zube a falo tare da muna neman abinci ina yawan mamakin yadda sam anty bata kyaman mu,amula dani kamar yadda gidan mu suke gwada min.
Sai da muka gama ne sai Faiza ta kula da gyaran gashin da akai mun din tace wai dama anty wurin gyaran kai kuka tafi ba tare da muba.
Tace fuska gimtse eh idan kun shirya driver yana waje sai ya kai ku kuma bata da daman da zatai mata wani korafi ba.
Sai harare harare suke aikamin a fakaice bandai kula suba anty ta shige dakin ta sai lokacin Faiza ta samu yi min magana akan fitan mu nace nine nace zan bita da zata fita tace idan kun tashi zaku tafi.
Fitowan anty ne ya hana maganan yayi nisa sosai ta fito tana cewa da au baku tashi kun shirya bane ke kuma Safiya tashi zakiyi ki sallah sai mu fara hada kayan gift din nan tun ba ai yawa ba ki kira funke ta taimaka maki hadawa.
Su idan sun dawo sai su karasa a inda kuka tsaya din don takwas za a fara program din ban son a samu matsala a wurin mu ko kadan.
Mikewa nayi din zuwa sallah nake cewa da su idan sun wuce sai sun dawo ni zan shiga in sallah faiza ne kawai ta amsa min ciki ciki na shige abina.
Sallah nayi na fito anty bata falo don haka na bita dakin ta a inda na samay ta zaune a kasa inda ta idar da sallah tace yauwa Safiya kin ga dauko wancan buhun ki miko min.
Koma da yake ai shi uban gayyan yace ba zai gayyaci mutane dayawa ba a gurin sai nine ma na gayyato mai abokaina da mazan su sai abokan mai gidan da suke garin nan.
Nace haka nake ganin sa kamar baida rigima ai tace haka yake sai kuma wanan kaddara da samay shi ya kara sawa yana gudun mutane yanzu.
Kamar ince wani kaddarane anty sai naga ni may ya shafe ni kuma da zan je wani tambayan abinda bai shafe ni ba can.
Na miko mata inda na aje a gabanta sai tace ai ma mu tafi falo kwaso su duka ki fito min dasu tamike tana cewa ko dai in tai maka maki ne da kwasa.
Ida da sauri nace haba anty barshi kawai zan iya ai basu da wani yawa ta fice inda na fara kin kimo wa zuwa falon inda har ta zauna ko kasa saman center carpet.
Na dauko sauran na samu sufi na farkon nauyi haka dai na ta kwasowa zuwa falon har na gama.
Ba bata lokaci muka fara hadawa dani da funke tana directing din mu ina mamaki a raina wai bukin bude gida da company akewa wanan gift din kamar na wani buki can da ya shahara nace kai masu kudi na shagalin su.
Anty ne ke fadin ko basu yi ba a kara ne safiya naga abin bai wani cika ido ba sosai nace wai anty duk wanan za a ace bai cika ido ba tace kin ko san wa yanda muka gaiyata a wurin ne.
Jakka ne dan na tafiya sai towel da sabule da turare da man shafi da su drinks da snack muke zubawa ako wani bag.
Tsab muka shirya komai yadda ya dace sai tace funke tai ta kwasa zuwa mota inda driver da ya kai su faiza yadawo yana waje sai da aka gama kwasa ta ce in fito mu tafi inda za a kai.
Na gaji amma babu halin in nuna mata gajiya na don ban so ta fahinci hakan daga gare ni a tare muka fito inda yaran har sun fice waje ko.
Nan mu ka kama hanya sai wani unguwa mai nisa tsarin unguwar yafi na su anty haduwa sosai don ginane sai kace a kasan turai mutum yake ga ba yawan hayani ya a wurin ko wani gida a rufe yake.
Wani tsararen gida muka shiga da motan mu tace bude ido da kyau kiga gidan da sulaiman ya kera dan dawowan nan nasu kai kudi suna aiki wallahi.
Nai mamakin jin kalaman anty tace wallahi sulaiman mutum ne dake tsaya ga neman na kasa yaro ne wanda tun farko bai tsaya jiran sai ambashi ba haka ya taso da neman na kansa.
Gashi maraya ne bai tashi da mahaifin shi ba don tun yana matakin karatun shi na farko mahaifin shi ya rasu sanadiyan hatsarin mota.
Dan dukiyan da aka raba masu ne a wanan lokacin ya fara juyawa shine Allah yasa masa albarka har yakai haka yanzu sai dai ya taba aure duka duka watan su shida suka rabu da matar.
Motan mu ne ya tsaya a ciki gidan koma suna tsaye a waje da wasu abokan shi shi ya dakatar da labarin shi da take bani a motan .
Shi da kansa ne yazo ya bude mata motar muka firfito nan abokan shi suka shiga gaida ita wanda da gani sun san ta dama.
Ciki muka shiga nikan ba boyo dama bakauya nake nan ko nai ta zuba kauyan ci wurin kalle kallen gidan.
Nayi mamaki wai wanan dai sulaiman din ne mai wanan gidan haka dana gani mun shiga mun fita ko ina sai faman yaba mai anty keyi.
Niko duk na takura a wurin don ban saba hurda da maza irin hakaba don yawan kalon da suke min din yayi wa a gani na.
Nuna mata nayi na gaji sai tace inje in zauna a mamakeken falon in jira su a nan tare da twins din ta muka zauna a falon nan na ci gaba da ba ido abinci don in samu na karaswa.
Wayana ne yai tsuwa na dako da sauri inda naga ummi na ce ke kirana a lokacin nace Allah sarki ummi taji shiru yau shine ta kira ni don kaida ne a rana sai na kirasu kusan sau biyu ko uku inji lafiyan su.
Nan nake fada mata bamu lagos mun zo Abuja ne da anty wurin bukin bude company kanin mijin ta da za a yi yau tace shi gidan harda wani buki ake mai kuma ?
Dariya ummi ta bani ban san lokacin da na bude baki ina kwasan dariya ba a daidai nan suka fito daga daki shine agaba sauran na bin shi a baya.
Nan nai saurin gimtsewa kamar bani bace mai yin dariyan a farko muna ta magana da ummi inda suka zauna sai na kasa sakewa a wurin.
Karshe dai don in fitar da zargi sai nace wa anty ga ummina su gaisa da ita ta karbi wayan tana murmushi nan suka gaisa ina jin anty nace mata gata nan ina ta bata wahala bamu zauna ba yau tun safe ai Safiya tana da kokari wallahi naji dadin zama da ita sosai ummi.
Sun gama gaisawa ta bani wayan nai mata sallama tare da kashe wayan nawa nan na zauna a takure a cikin su inda anty ta umurce ni da in bude jaka guda suga yadda muka hada kayan ciki.
Mikewa nayi ina gyara gulyalena dake zamewa akaina na dauko jakka guda tare da bude masu sai naji sulaiman din yace kai basuyi kadan ba.
Ban san lokacin da na dago na dan kalle shi ba sai naji anty din tace gata nan ai nace a kara don nasan halinka tace wai ya isa hakana.
Yace No if possible don Allah a kara mana why not na mata a saka zanuwa a cikin sa na maza ku saka masu shadda a ciki kai hamza kaje ka dauko su a cikin dakin nan a zuba.
Daga haka suka fice aka barmu nan muka ci gaba da aikin kara kayan bamu dawo ba sai shida na yamma don mu shirya.
Mun dawo mun samu su Fati na gida itakan anty dakin ta shige tana cewa mu shirya bakwai zamu bar gidan.
A kusan tare suke tambaya na ina muka tafi haka nace mun je inda za ai event din ne don hada wurin sai ita Fati tai tsaki tace to mu wai may ya kawo mune tunda ba a yi damu.
Faiza ne tace a a zaki iya wanan jigilan da Safiya keyi haka ba gajiya tace wane ni kuwa sai fatin tace wai mun ga sulaiman a wurin nace a a bamu ganshi ba ai.
Tace ai gara ma da ban tafi ba don ni shi kadai nake son gani dama ban damu da wasu can ba.
Sai faizan ta harare ta tace hum,umm ashe kina da aiki indai wanan miskilin ne mai yi kamar yana jin warin mata tace wasu matan ba.
Ni dai ban zauna ba shiga nayi sai na samu kaina da dan kwantawa don a gajiye nake so sai yaran ne da suka shigo na tashi dole na fara shirya su.
Ina cikin shirya sune anty ta leko tace da ni aa kunanan da mutanen naki kuna ta fama yauwa safiya sannu da kokari kiyi ki gama sai kema ki shirya.
Tace karbi nan nasan ki da sin dogon riga shiyasa na sayo maki ban baki bane don wa yan nan yan sa idon kada su damay ni da korafin banza.
Na amsa hannu bibiyu ina godiya tace kin ga don Allah ni kuyi sauri bamu da lokaci ban so ma in kai yanzu ba a nan bamu tafi ba.
Nan tafita ta barni ina duba kyawon rigan data bani rigan yakai riga wurin haduwa sosai na ce a raina wai na ko gode ashe idan na koma gida inna sai bakin ciki ya kashe ta.
Tsab muka fito bani ba ba yaran ba ban bari anty ta jiramu ba don a gagauce na shirya simple makeup nayi a fuska na duk da hakan ba karamin kyau nayi ba sosai.
Duk sun fito nice karshen fito wa a tare da su yan biyu muka fito kowan mu in ka gan mu basai an fada ma cewa ga inda zamu ba a lokacin.
Nan ko su Fati aka sako min ido take kowan su ya daure fuskan su, don basu san da rigan da na saba na gani amma nai kamar ban gan su ba.
Nan dai babu tsatsayawa muka fice gidan har da funke gaba dayan mu ba a bar kowa a gidan ba mota biyu mukai tafiya dasu inda nida yara da fati muka shiga mota guda sai anty da faiza da funke a dayar motar.
Da kamar ba za tai min magana ba sai naji tace wai yaya kika ga shiga na ne Safiya na fito kuwa ?
Nace kai ai duk kin fimu haduwa wallahi kin ko ga yadda ki ke wani haskawa wurin nan ashe akwai wanda zai kai ki haduwa a wurin.
Taji dadi ta washe baki tace ina yinki safiya wancan yar bakin cikin cewa tayi wai in saka dayan rigan nan don ta san baikai wanan din haduwa don ta fini fitowa.
Nace ke kyale ta don Allah ita Faiza bata taba fadawa mutum gaskiya ai tace da sauri ashe kema kin gane ta yanzu ni shiya bani shiga harkanta .
Mun isa wurin ba kowa sai anty damu muka karasa duba aikin da akayi bayan wuce wan mu nan muka shige wani daki muka kara gyarawa kafin a fara.
Ni dai kwance nake sai su ke ta heleke su da gwale junan su kamar wasu kishiyoyi can nidai murmushi kawai nake ta masu sai anty ne ta shigo dakin take cewa ai an bude wurin yanzu za a fara don Allah tana son kowan mu ya natsu muyi abu a hankali kada mu bada ita.
Bamu fito ba sai da taro yai taro muka fito muna mara ma anty baya tare da wasu yan uwan su da suka zo daga bauchi sai yanzu na gansu.
Sulaiman din ya fito tare da abokan nan nashi na dazu wanda na fahinci sune dai abokan shi na shakiki na kusa.
Mun fito wurin ya dauki tafi don mc na bayani akan Sulaiman din da dalilin haduwan a nan wurin ni dai biye kawai nake dasu kamar ace in sheka in ruga da gudu.
Don yawan mutanen dake wurin naga anty ba abinda ya damay ta sai walwala take tana ta gaisawa da mutanen wurinta saka wasu matarial sai walkiya take yi a gurin.
Ana ta bayanai akan ki shi din wanene tare da manufar shi na bude company da yayi nan wuri ya dauki tafi rafrafraf .
Sulalewa nayi na fice daga dakin taron na fita waje wani iska mai sanyi ya dake ni na shaka sai naji ina son in dan kadaice ni kadai a wuri daya.
Wani dakali na hango a gefen don haka na nufi wurin na zauna ina kallon masu shige da ficen wurin.
Nace a raina idan mutum na cikin wayan nan har sai ya manta da halin da yake ciki ya shagala da rudin duniya dan dai ma ita anty mace ce mai kula da addinin ta.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , , ,
🧕🏿3️⃣6️⃣🧕🏿
YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDINE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA DAKE DAKE TURAWA MUTANA DA SU DAKE KANRATAWA DUK ALLAH ZAI KARBAN MIN HAKKINA A GUN KU, , , ,
Hankali na ya tafi ga kallon yadda wani miji da mata suka shigo ririke da junan su a wurin har zuwa cikin holl din dadin kallon su yasa ban dago kai inga ko waye a kusa dani ba yana waya.
Gama wayan shi yayi daidai da kare kallona don sun zo sun shige har ina ajiyan zuciya naga mai shi ya zauna a saman abinda nake zaune.
Sai na dago da sauri ina kallon shi yace dani sun baki shaawane daidai da yake zama sai a lokacin na gane shi, yinayi kamar banji abinda yake fadi ba don yadda yai maganan baiyi shi akan zan iya jiba.
Da sauri na matsa mai sai dai ban tashi ba don wurin nada girma ko mutum huda zasu iya zama akai ya sake cewa hayaniya yayi yawa a ciki ko ?
Kai kawai na kada mai alaman eh sai yake cewa dani yana kallon wayan dake hannun shi
Bana son yawan hayaniya don haka na fito waje na sa driver yazo ya dauke ni yanzu zan tafi .
Saurin kallon shi nayi sai naga shi bai ko kallon inda nake gashi dan zaman da yayi kusa danu duk a takure nake a wurin.
Yana yi yana kallon agogon hannun shi akai akai nasan lokaci yake diba na zuwan driver shi nace sai naji yace bakiji tsoron zama a nan ke kadai ?
Karamar dariya nayi sai wanda ya saurara zai iya jina tare da nuna alaman ina jin nauyin sa wanda hakan ya zamay nin jiki ga kowa indan muna magana.
Sai kuma naji ya sauke wani murmushi shi ma yace koda yake bai kamata na katse maki yanayin da kike ciki ba na son ki kadaita kan ki ga mutane,
Kin san ku mayya sai a hankali bai kamata na katse maki jin dadin din ki ba wa wanan lokacin yar gajeran murmushi na sauke har yanzu akwai alaman jin kunya a tare dani.
Shiru ya biyo baya na runtse idona ina dan fidda ajiyan , gabana yaci gaba da bugawa don gani nake kamar a mafalki na shiga tambayan kaina shin may ya fito dashi waje a wanan lokacin da aka hadu don shi a kumayace zai wuce ya barsu
Sauke ajiyan zuciya na yi don ina mamaki hali iri na uncle sulaiman da ga mutum shiru shiru mai kyakyawan halitta da kyakyawan hali.
Jin shi da nayi yana jan dan tsiki akai akai kuma yana yi yana kallon agogo har yanzu lokaci zuwa lokaci.
Dagani ba sai an tambaya ba don mutum zai fahinci a gajiye yake a lokacin gana haka sai kawai na miko mai goran ruwan faro dage gefena ajiye wanda na fito dashi.
Nai mamaki dana ga ya amsa yana min godiya tare da kafa kai bai sauke ba sai da ya zuke ruwan goran duka.
Ya wurgga da goran yana kara min godiya dai dai nan abokin shi hamza ya isa wurin yana fadin kai ana can ana neman ka kuyi photo ashe kana nan ka boye.
Sai lokacin ya farga dani a wurin nima sai tsarguwa nayi a yadda ya samay mu kamar masu wani hira.
Saurin gaida shi nayi don kada ya zargi komai a tsakanin mu sai ya dago yana ma sulaiman din wani kallo mai kama da zargi yaya haka kuma ?
Baka da hankali yai mashi alama tare da mikewa yana shirin barin wurin nidai gyara zama na yi ba tare da na kalle su ba sai naji hamza yace a a zaka tafi kabar ta kuma a nan kawai barin koma dama bamu gan ka bane shine na fito in dubaka.
Yama rasa abinda zaicewa hamza din sai sauran biyun sun fito suna cewa hamza yaya sai hamza din yace yeh na gangashi ashe yana nan ne.
Dukkan su suka karaso ida muke, naji dayan na cewa kai muna can muna neman ka harda madam ashe kai kana nan hamza ne yai masu nuni da hannu cewa su duba sugani.
Sai duk suka juyo inda nake zaune wani dariyan shakiyan ci gudan ya dauka yace i see mutafi kawai inda ka gama mutane na jiranka kuyi photo a ciki .
Basu tsaya ba suka wuce suna ce mai sai ka shigo kenan girgiza kai yayi tare dadan jan tsuki ya juya yana dubam ida na tare da cewa ba zaki shiga daki ciki ba ?
Nace nan di yafi mun dadin zama akwai isaka mai dadi a wurin, shigewa yayi ba tare ya sake juyu ba yabar ni zaune na sauke ajiyan zuciya tare da lumshe idona.
Na dan dade zaune a wurin babu abinda nakeyi sai tunanen abubuwan da nake gani sai ga funke an aikota ta kirani ban dauki lokaci ba na koma ciki tare da ita take ce min mu fara ba mutane abin gift din kamar yadda aka tsara fon uban gaiyyan kan shi yace ya gaji sai da aka nemo muna shi waje ,
Wai da wata yarinya tana fadi batare da ta kalle ni ba take naji gabana ya yanke ya fadi ya kuma ci gaba da bugu uku uku don kada anty ta gane nice muke waje ince mata may .
A tare muka je dakin da kayan suke sai da muka shiga ta fara bayani san nan na sauke ajiyan zuciya tana mun bayani gabana yaci gaba da fadu.
Munyi yadda ya dace haka mutane sukai ta watsewa don komawa gidajen su don dare yayi sai mu yan gida kawai aka bari nan wata doguwar mota ta kwaso mu zuwa gida gaba dayan mu a gidan anty aka sauka.
Sai mazan ne suka sauka gidan sulaima din haka wuri yayi kada dole nida yara muka koma dakin anty sukuma bakin suka sauka a dakin mu.
Ni dai bayan na tube har nayi barcin na falka anty tana gun bakin suna hira ko tashi nawa yan biyu ce ta falka da ni wai zata yi fitsari.
Na dawo kaita sai ga anty ta shigo dakin take cewa bumuyi barci bane idona da sauran barci nake cewa yan husna zatai fisari natashi.
Tace kin ganni sai yanzu muna can muna fira yaushe rabo a kasa na kwanta su suka hau gado sai da ta fito han daki ta ganni kasa take cewa haba dai Safiya ku kwanta mana saman gadon da yara nace kasa ma yai min don na sa bargo.
Tace kedai kin huta wallahi shiya sa nake ma Sulaiman gwadayin ya aure ki ai don rayuwan ki ke simple ne kamar nashi.
Ai yanzu dole in matsa mashi don an fara kawo mai mata wai ya aura ko da kuwa bai so haka za saka shi a gaba sai ya yarda.
Jin abinda ta fada yasani kallon ta da mamaki tace kina ganin wautana ko kan abinda nake kokarin hadawa da hankalina Safiya.
Sulaima mutum ne da ko wacce ke mafalkin auren shi kyakyawa mai kyauwon siffa da hali na gari ga wadatan zuci da Allah ya bashi dana Aljihu mai tattare da illimi addini da na zamani uwa uba dan karen tsoron Allah kamar yana ganin sa.
Abin da na fadi shu ya dakatar da ita da yabon da take fadi nasa don cewa nayi anty ni ina ni ina Sulaiman gashi dan masu arziki niko yar tallakawa.
Dama dai Fati dake mutuwan son shi kikai kokarin hadawa dashi don ita yar uwar kine gashi tana mutuwan sin shi sosai , , , ,
Ke dan Allah rabani da abin haushi koda sulaiman zai iya auren ta ba zan yarda in hada shi da fati ba don bata da tarbiyan da ya dace da mutum kamar sulaiman a tare da ita.
Balle aure ita dashi ya haramta gare su don dai sulaiman shima victim ne irin ki matsalan ku daya dashi.
Da sauri na dago kai na kalleta nace nace a razane HIV anty ?
Tace wallahi Safiya tana hawa gado take cewa matsalan ku daya dashi shima wata ya aura maishi suka munafunce shi basu fada mai ba sai bayan aure ya baiyyana mata koda akaje aka duba akaga shike gare ta har yai nisa da aka auna shi aka samu shima ya samu daga gare ta.
Wallahi safiya daya kiramu yana kuka kamar karamin yaro yake fada muna ranan mun shiga tashin hankali ba karami ba a gidan nan .
Allah yasa daddy yana nan shi ya shiga jirgi yaje can South African ya samay su inda ya samu ya shawo kan shi sai dai kafin yaje har ya saketa ko.
Daga baya daddy yayi yayi dashi ya maida ita amma yace ya gama auren ta karshe ma yace shi ba zai kara aure ba a rayunwan shi.
Daga baya muke jin wai ta gaji da bin shi ta auri wanda yasa mata cutan yanzu shine kika ga sam baya son ai mashi maganan aure kuma ya koma gudun mata.
Dama can ba damuwa yayi da matan ba sai abin yazo mashi da sauki dalili kenan kika ga ina son in hada ku don ko banza halin ku zai zo daya dashi.
Yanzu haka yan uwa basu san halin da yake ciki ba don ba afitar da zancen waje wani yaji ba.
Shine ita mahaukaciyar kika ga tana wanan haukan haka shi yasa ma kika ga bai son zuwa kasan nan don matsin da iyayyen shi ke mai akan ya kara aure.
Kafin taga bani labarin fuskana har yacika da hawaye fam taji ina kuka tace ke ko saurin karaya gare ki ai hakkuri za a yi haka wani rayuwa yakan zo wa ba ya zama BAHAGGON RAYUWA .
Amma in ai yi hakkuri aka rungumi kaddara sai Allah ya duba ma mutum Allah mai tausayin bayin sa ne akoda yaushe yana ma mutum mafita ta hanyar da bai zata ba.
Nasan labarin nan da kika ji ya sa kin tuna da naki matsalan ya dawo maki da shi sabo sai hakkuri abin ba dadi gaskiya.
Ta haye gado ta kanta tare da kashe wutan dakin ya koma duhu ta barni cike da tausayin kan mu da ma sairan uan uwa musulmai da suka tsinci kansu a wanan halin irin namu.
Tabbas Sulaiman idan ya zama mijina zan yi kokari inga na bashi kwanciyan hankalin da ya dace dashi naji zuciya na ya sami karbuwa dashi dari bisa dari bawai don kudin shi ba don ni basu gaba na yanzu don ina ganin kwana nawa ma yarage min a duniyan.
Saboda na sha zama inyi ta nacin rokon Allah da yai min mafita ga matsala ta in samu miji wanda zan masa biyayya kuma yasan ina yi.
In har abin ya tabbata zan fi ko wata mace sa a a rayuwana amma kuma ban taba tunanen samun haka ba.
Sai gashi kwatsam Allah na baiyyana min ansan addua na yana batun bani uncle Sulaiman a matsayin miji a gare ni.
Nasan anty da naci kan abinda take so wanan abinda take shirin hada min da wani irin godiya zan saka mata dashi don tsabar girman shi da daraja a a gare ni.
Sai dai kuma kash nace a raina anys kuwa shi uncle sulaiman din zai soni kuwa ga yadda yake baya kallon ko wata mace.
Kuma ma yasan cewa na taba aure har da haihuwa indan bai taba sani ba anya zai so bazawara kamata kuma yar talakalis.
Wanan sune tambayoyin dana rika yiwa kaina kawai sai jin hawaye masu dumi nayi sun soma bin kuncina a karo na farko da na furta Allah ya isa ga Ahmed kenan.
Don shi ya jefa rayuwa na a wanan hali dan ma taimakon Allah ya kawo min sanadin sanin anty a rayuwa na har take kokarin mantar dani halin da nake ciki yanzu.
Na sake fadi Allah ya isa aure na da Ahmed cikin sanyin jiki na gyara kwanciya na ina ci gaba da tuna ne wanda ban san iya wanda nayi ba a lokacin.
Washe gari mun tashi da baki a gidan don haka tunda nai sallah muka fada kitchen dani da funke don hada masu abin karyawa.
Koda anty ta tashi har mun gyara gida mun gama hada breakfast din na shiga wanka ina jin tana fadin yau na shiga uku wani irin barci ne nayi haka mai nauyi.
Na fito ina mata ina kwana tace safiya ai yau kan ban san irinbarcin da nayi ba ga baki gida ban shirya masu abin karyawa ba har wanan lokaci.
Nace anty fita falo kiga abinda muka shirya masu ko yayi na dai hada ban san ko zaki soshi na tace kai Safiya ubangiji Allah yai maki albarka yasa mu raka da junan mu.
Har kin hada abinci ina daki kwance ban sani ba shiyasa nake son kada ki kubcewa Sulaiman don shi kadai ya dace dake.
Shima kene kika dace dashi sai ku taru ku rufawa junan ku asiri a zauna lafiya.
Murmushi nayi nace kai anty dai kina dai son musa kafan wando guda da fati a gidan nan don ta mutu akan so uncle din sosai wallahi.
Wai ba zaki rabani da wata Fati can ba ana maganan mutanen kwarai kina kawo min fati ciki wanan kazama may ta iya banda rashin kunya ita kuma Faiza ragguwa ce ta karshe bata iya aiwata komai banda kallo da kwanciya ai dai za a yita ta kare ga yan uwan haihuwan shi ai sunzo
Sai da mukai wanka muka fito falon a lokacin har bakin suma sun fito ko take cewa kun gani sai yanzu na tashi ba sukace suma basu dade da tashi daga barci ba ai.
Dayan tace gashi har an hada abin karyawa ko tace aikin sarakuwan ku ne wallahi sai duk suka kalleta matar take cewa sarakuwan mu ta ina tace Sulaiman mana.
Nan suka shi murna da sa albarka ga abin nidai kunya duk ya rufe ni dago kan da zanyi sai ga fuskan fati tana tsaye kamar ruwa yaci ta.
Uncle ne sukai sallama da sauran mazan da suka kwana gidansa suka shigo da murnan su sai ya samu suna zuba abinci yace a a madam baku gaji ba har kun iya tashi kunyi wanan aiki haka.
Bata kai ga bashi amsa ba sai wata tace kaidai ai kayi dace wallahi ga yarinya da kirki ga kunya Allah dai yasa ayi damu.
Kallon mamaki yake aikwa anty sai tace Safiya na fada masu nufinka akan ta shine suke ta murna da abin.
Ajiyan zuciya yayi ya gyada kai yana cewa kai madam baki da dama wallahi sai matar tace wallahi mukan munyi murna don wallahi zaben yayu kun dace kwarai .
Gashi muna barci an hada muna abin karyawa irin haka may ake nema gun mace dama tasan darajan yan uwaka an kuma samu tunda anty ta yaba da hankali ta may za a jira banda musha buki.
Ni dai duk na kasa sukuni a wurin don haka na mike da sauri na shige daki cikin kunya duk suka bini da dariya banda shi da yake jin wani iri a zuciyar shi.
Don may anty take son ta yaudari yar mutane gata karama zata cuta ma rayuwan ta bayan tasan halin da yake ciki.
Idan wani ma bai sani ba yasa take fadin haka ai shi da ita sun san matsalar shi ta rasa wanda zata cuta sai wanan yarinyar dake kokari da ita haka a gidan.
Shi har naka bashi tausayi idan yazo bai taba samun Faiza ko fati na kau da kara a gidan ba komai ni zai samu ina yi ko yara ke son abu sai dai yaji sunce anty Safiya.
Har suka gama karya da yan uwa yana cikin wanan tunanen yace su tashi yakai su su zaga gari don washe gari zasu koma gida don haka yake son ya fita dasu.
Har sun fita ya juyo yace madam idan na gama dasu kila zan dawo don akwai maganan da nake son yi dake idan mun samu time.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , ,
🧕🏿3️⃣7️⃣🧕🏿
INA ROKON ALLAH DA YA SADA MU DA RAHAMOMIN DAKE CIKIN WANAN WATA MAI ALBARKA YAN UWA, YASA MUNA CIKIN YANTATTUN BAYIN SHI, , ,
Bayan komawa yan bauchine gida sai muka fara shirin tafi muma don sam ba mu san zamuyi wanan kwanakin haka ba a abujan.
Har lokacin Fati bata sake min fuska ba cikin ma bataji kan maganan sosai ba don dukkan su basu kusa dan haka basu ji maganan da akayi da kyau ba rana.
Mun fara shirin komawa lagos sai dai har lokacin bamuga Sulaiman din a cewan anty tafiya ya kama shi ya tafi gida.
Shiri sosai mukeyi dole a mota mukai tafiyan don kayan da muka loda na amfanin gida a Abujan dama wasu tarkace can.
Mun dawo da kwana biyu mun warwale gajiya a jikin mu yau anty ta fita aiki Fati tafita zuwa makaranta sai Ni da Faiza kawai a gida.
Na gaji da kwaciya dan haka na fito falo muyi hira da Funke sai na samu Faiza ta rigani fitowa tana gani na take cewa kema kin fito shiru yai yawa a gidan.
Nan na zauna muna hira har funke din sai dai matasalan Faiza shine son ayi da wani a bayan shi wanda ni kuma ban lamunci haka ba sam.
Take fadi wai dama tana son mu samu lokaci ne ta fada min Fati fa ta fara zargina akan ina shishiwa don in fi kowa gun anty dama haka muke da bin bokaye ai duk inda bakauye yake ya san inda bokan kwarai yake ko malam.
Murmushi nayi nace aiko ba boka da malam idan ka gyara alakarka da mutane sai a soka ita tasan wanan don haka take zargin kowa da wanan halin.
Duk hiran da ta dauko sai in kawar dashi don mafi munin sabo shine giba amma ita shine sana,anta yi da wani idan baya kusa.
Munyi gyaran gidan nida Funke kamar ba tafiya muka yi ba munn maida gidan tsab gwanin ban shaawa na koma daki na kwanta ban falka ba sai da maigidan ta dawo ta turo yaran su kirani.
Ckin barci naji suna tadani wai mummy su na kira na, mika kawai nayii na sauko muka fice dakin zuwa falo tana tsaye a tsakar falon da waya a hannun ta.
Wuri na samu naja na tsaya ina jiran ta gama sai na zo na fahinci sa mijinta take waya sai da ta gama ne ta kashe wayan ta maida hankali gare ni..
Anty sannu da dawo wa nai mata ta amsa tare daga mun hannu tace yawa safiya zozozo nan kin ji tana mika hannu wai in zo kusa da ita haka take yi idan abu ya dan ruda ta ko ya bata mata rai.
Banyi nawa wurin karasawa inda take ba ta riko hannu bibiyu tana cewa Safiya kiji min daddy da rigima wai bai fada min zai fito ruwa ba mu shirya mai sai yazu da suka fito wai yake sanar dani sun fito.
Jimun daddy da neman rigima fa safiya ni kaina ma ya kulle ban san may nake ciki ba wallahi yanzu in an gama masu clearing za a kawo shi gida.
Nace anty ba daddy yafi son tuwo ba tace shi ne ai safiya nace akwai komai hade tuwon kawai zan tuka bani minti ashirin yanzu sai inyi warming din biya don dama jiya na hada su.
Tace kai Safiya sai ta rungumoni zuwa jikin ta tana cewa yarinyar nan basan godiyan da zan maki ba amma dai bari komai nake dabban zan fitar maki in daddy ya dawo.
Haka take dason abin ban dariya sai dai kuma indan ta tashi daure fuska ba mai gane kanta kuma sai taga daman saukowa dan kanta da kanta.
Kafin daddy ya iso gida mun hada mai table lafiyayyen abincin irin wanda yake so namu na gargaji na shirya mai tuwon semo sai miyar kubewa danya sai stwee din cow tail dashi zai hada ya ci simple.
Sai abin sha suma na jera su yadda ya kamata da kunun samiya da yake son sha sai kamshi kayan yaji yake yi.
Wanka na shige ina ciki naji jiniyan su ta aiki ta shigo gidan haka yasani sanin ya dawo take gida ya rude da murna don shima daddy kamar matar shi yake bai da matsala ko kadan da kowa a gidan.
Matsala daya ne ba a ganin shi sosai kullon yana ruwa kasancewa shi na sojan ruwa indan ma yana tudu aikin gaban shi ya shamai kai.
Ban fito ba sai da na shirya mai kawai na shafa na zura rigana na fito tari yan shi na samu kowa a falo security din shi na ta shige da fice nace aifa bissimillahi a raina yanzu zamu fara ganin kattan sojoji a gidan ba da dare ba rana.
Can na hango shi yana ta yanka loman tuwo yana kaiwa baki na karasa da sauri ina fadin daddy sannu da zuwa ya dago yana kokarin hade loman tuwon da ya cusa a baki yace.
Yace yanzu nake tambayan ki naga kowa ban ganki ba na dauka kin koma gida ne sai anty dake gefen shi tace ai yau da ta wuce da bakaci wanan tuwon ba aiki ta tsaya yi sai ta shiga wanka kafin ka iso.
Nan dai na gaida shi nai mashi sannu da zuwa da yaya aiki da hanya ya amsa a takaice yana mai ci gaba da cin tuwon dake gaban shi alama ya nuna yana jun dadin kasancewan shi a gida.
Tunda suka shige bai kara fitowa ba daga shi har matar nasa su yan biyun su suna tare dani ranan a wurina suka kwana basu koma dakin su ba.
Duk da daddy ya dawo bai hana anty fita aiki ba da safe sai da daddy ya tashi yai breakfast shi kadai nace a raina mijin ma,aikaciya kenan.
Bai fita ko ina ba muke ta fama da dauwainiyar shi a gida har zuwa lokacin da ta dawo don bata dade a wurin aikin ba ranan.
Da yamma aka fitar da tsaraban da yazo dashi wanda tufafi ne sai kayan ciye ciye irin na kasa shen ketara yazo dasu wannan kan an zube su ne kowa ya ci ya sha iya shan shi da ci.
Daki na koma ina kallon tsaraban ina mamaki dan zuwa na gidan su na karu da abubuwa da dama na rayuwa.
Na tuna da iyayyena da yan uwana dake zaman ukuba saboda talauci kullun ana ganin laifin juna a tsakanin zama tausayin halin da gidan mu ke ciki ya kamani.
Na wani fitina nan har da talauci ke kawo shi ma in kowa na dashi ai ba mai kallon halin da dan uwa ke ciki kowa tashi ta isheshi ma.
Daddy ne ya tsure anty a daki yana tambayan ta game da hadin daya samu labari tana batun hadawa a tsakani na da sulaiman.
Kin fi kowa sanin halin da yaron nan yake ciki amma shine zaki dauki yar mutane ki hadata dashi don kwadayi komai yaushe kika fara wanan halin na marasa imani ban sani ba.
Idan yarinyar ta gane an cuce ta kina ganin ba zatayi kuka dake ba kai har ma da mu duk abin zai iya shafa nan gaba.
Haba dai daddy may zai sa da hankalina nayi irin haka ga yar mutane may tai min yarinyar nan ai in babu godiya to kuma babu fallasa.
Ta sauke ajiyan zuciya tana cewa dashi matsalar su daya da sulaiman domin ita ma Safiya postive ce da sauri yace may ne ?
Tace wallahi kamar yadda shima ya samu ta sanidan aure haka itama ta samu gun mijin da aka aura mata dan uwanta nan dai ta shiga bashi labarina yana fadin subbahanallah.
Yanzu wanan yarinyar mai hankali haka aka dauka akabawa mashayi ya cutawa rayuwanta subbahanallahi wallahi dai ana cuta a duniyan nan.
Yana kada kai yana fadin wallahi ta ban tausayi gaske nake ganin ta shiru shiru ashe da abinda ke damunta a rayuwan ta.
Ya kara nisa yace yanzu na fahunce ki idan kinyi hankan kin taimaka masu sosai don sulaiman idan a biye masa baiki ya zauna a haka ba ba aure.
Tace ai shi na gani don haka kamar yadda kowa bai san da halin da suke ciki ba sai muyi rufa rufa a daura kawai ta tare an wuce wurin Allah kadai yasan gawan fari tsakanin mu da su.
Nan dai suka kara tatauna yadda zasu fitowa zance don kada a samu matsala a wani bangaren a taru a rufawa juna asiri.
Mako shi kusan uku tun a abuja daya bar mu ya tafi bai zo gidan ba wai ashe tafiya ta kamashi ya ketara waje sai yanzu ya samu kan shi ya dawo nigeria din.
Ranan jumma daidai an sauko daga sallah sai gashi gidan ya shigo babu kowa a falon gidan sai nauran kallo da yake aiki shi kadai a falon.
Goran ruwa yaje da kansa ya dauko a fridge ya dawo ya zauna yana sha sai ga funke ta fito ta ganshi a zaune da sauri ta gaida shi don tana son zuwan shi don dan abinda yake bayarwa a bamu bayan tafiyan shi.
Ta juya bayan ta gaida shi zuwa kiran Anty a sama dakin ta sai gata da saurin ta tana fadin oyoyo da karamin mai gida.
Yace ai nayi fushi tun yaushe nake nan zaune sai ni da kaina na dauko ruwan da zansha gaskiya gidan nan yana bukatan kari don gidan yai maki girma ke kadai dole yaya ya kara wata.
Tai wani dafe kirji tana cewa waini dakaina kawa Allah ka huce ina ni ina amarya yanzu a gidan nan.
Nan fa nabar su Faiza ashe duk sun shige subar falin ba kowa a wurin wane ni in kyale ka haka koda yake zuwa bazata kai ma kai muna ai yaudin.
Yace kuma hakane fa to na dai huce tunda anfini gaskiya ya nisa yana gyara zama dakyau yace wallahi nima dai haka tafiyan ya kama ni gashi tun a abuja bamu hadu ba sai naga ban kyauta ba ko ban gajiya ban samu yi maki ba .
Tace kai haba dai ai nasan yadda harkan naku yake bawani lokacin kanku kuke dashi ba sosai mu dai tunda kana lafiya ai shike nan.
Ya sake mika hannu yana daukan ruwa gami da bude roban ruwan yace wallahi lafiya nake sai dai abinda ba a rasa ba dai.
Tace bari a kawo maka abinci shima captain tunda suka tafi masallaci bai dawo ba shida twins yace ashe suna can yau ya dauki rigima .
Tace wallahi rankai dade abincin fa your fovourite akayi yau fa a gidan don nasan kaima kaman dan uwanka ne kana son cin tuwo shi Safiya ta girka mashi.
Dam gaba shi yai mugun bugawa jin ta ambaci suna na take yawan mafalkin da yake akaina ya fado mashi a rai don bai ko son ya ganni don bai son zuciyar shi yana fada mashi karya a kaina.
Ban san da shi ba a wurin don anty ta kirani na fito da dan kwalina a hannu ina kokarin daurawa akaina sai ganin su nayi tare zaune suna kwasan dariya.
Gaba yai mugun faduwa dan ban san da zuwan shiba gidan kuma ban tsamani anty ta sani ba don baji tana magana ba.
Ban yar da mun hada ido ba sai gasheshi nayi da cewa sannu da zuwa uncle, ya amsa da yauwa mun samay ku lafiya.
Tuni har anty ta lura da yadda na daburce ko sai tace safiya ga bako mun samu yau girkin ki ko saura bai ragewa don maciya biyu sun hade a gidan jeki zubo mai abincin kafin daddy ya dawo.
Sai yace ai da a bari ya dawo muci tare don tunda ya fita da su yan biyu bai nisa da gida yanzu tunda an sauko tun dazun.
Na kalli anty tace barshi kin ji bai jin yunwane sai dan uwanshi ya dawo kin san haka suke kamar tasbaha wajen zumunci.
Ya kalleta yai murmushi yace in dai an matsa muna sai mu kawo wa mutum kishi ya yanzu don na gane tako yanzu baki son zancen kishiyan nan.
Dariya suka kwashe dashi tace mu ai yanzu ba batun mu akeyi ba kai dai ne gwaro zamuwa aure don zaman nan naka haka yana bata min rai wallahi.
Ya kwar da maganan da cewa kin ga ke ne mai sin cin naman Turkey yana mota na sayo maki ki tura a kwaso maki da sauran tsaraban ki har na fara tafiya zuwa dakina don jin topic din da suka dauko.
Sai naji tana cewa kai safiya don Allah dawo kin ji ki dauko min a saka a fridge tun bai lalace ba kace gobe akwai harka a gidan nan ke nan komai bazan ci ba sai shi gobe in Allah ya kaimu .
Juyowa nayi na dawo inda suke na dan tsaya dan nisa kadan dasu tace taya ni murna maigidana ya sayo muna naman Turkey wai yana a motan shi waje.
Dan murmushi nayi kadan yasa hannu a aljihu yana ciro key din motar shi yace anya kuwa zata iya kwaso kayan ita daya ?
Tace ai shine kuma fa kodai ba ka son ta wahala ne tun yanzu yace kai madam baki da dama wallahi aidai yanzu nasan takonki in kin yi wasa sai kiji ayyururi a gidan.
Tace gaba dai ba nan ba ai anyi tun 1900 dariya yayi yana miko min key din tace nifa da gaske nakeyi wallahi ba wasa ga magana na tace kira funke ta taya ki kwaso kayan don waya nan mashiriritan nan san sun kwanta ne.
Funke na kira muka fita tare a daidai lokacin da motan daddy yake shigowa ge din gidan tun mota bai tsaya ba su yan biyu suke kwala min kira.
Sun fito suka nufo mu suna cewa daddy ya kaisu shopping da zasu dawo mosque nace kaga yan gata daddy kenan daddy ya fito muna mashi sanu da zuwa ya amsa tare da cewa motar waye anan ?
Funke ne da sauri tace uncle ne yazo aisai yaran suka kwasa da gudu ciki suna fadin uncle oyoyyo nan suka barmu muna dariya shima daddy ya bisu ba tare da ya kara fadin komai ba.
Nace a raina ko yaro yasan mai kyautata mashi ke nan muka bude buth din da kyar don dagani har ita ba wanda ya iya saida security din kofan ya taimaka muna budewa.
Mun shigo da kayan da kyat muka koma kwasowa mun samay su na ta murnan ganin juna shi da daddy sun zauna kamar abokai sun rungumay junan su.
Mun gama kwasowa muka zube su nan a inda suke zaune anty sai cewa take a a a Sulaiman duk may ka kwaso muna haka ?
Yace well yanzu dai ai ki buda ki gani don ni yarana na yowa sayayya bake ba tace aina sanj indai sin kaine akwai ku dashi ba a magana.
Nace daddy a kawo abinci ne yanzu ?
Na fada tare da dan kallon shi yace haka ya kamata yar albarka ke kan ai mijin ki ya huta wallahi.
Jeki ki bamu yunwa nake ji sosai ganin wanan ya hana in nema tun da na shigo haka dai kuke so mutum kada ya huta ko yaushe sai aiki.
Mikewa sukayu zuwa table din suna kara tattaunawa akan kasuwan cin Sulaiman din wanda ya fara yanzu a logos da Abuja wanda yake kuma son karawa a wasu jahohin kasan nan.
Cewan da nayi wanan ya isa daddy ko a kara ne nace da daddy din sai suka maida kallon su ga abincin dana zuba masu daidai anty na kawowa wurin.
Dakyau safiya inji anty ai gwauna da kika tula masu abinci yau muga iyakar son cin tuwon su suma dariya suka sake a lokaci daya.
Daddy ne yace Safiya sannu da aiki kinji Allah dai ya saka maki da alheri anty tace ya nuna muna auren ta da oga koda yake ma na fasa bada kawar tawa ai don sai mu ja maka rai muma.
Daddy ya jawo plate din shi gaban shi yana cewa a a haka kuma zaki muna kinyi niyar yin abin arziki kuma zaki zuga yarinya Safiya karki dauki maganan ta ina bayan ki kinji .
Fuska na daure ba annuri na azuba masu ruwa na juya na wuce lokacin ya jawo plate ya fara cin abincin kamar bai son ci zuciyar shi ba dadi a lokacin.
Sai mamakin su yake yi kawai sunyi nisa da cin abincin shiru yai yawa daddy ne ya kawar da shirun da cewa wanan maganan yai min dadi danaji.
Don shawara ne may kyau madam ta kawo sai a lokacin yai magana yace tare da dakatar da cin abincin da yakeyi amma sai nake ganin wanan abin kun san bamai yuyuwa bane.
Daddy ya tare shi da cewa kana ganin zamu hada abinda bai dace bane a kan ka ko zamu cuce ka ko yarinyar ?.
Gaba daya ture plate din dake gaban shi yayi daddy yace kaci abincin kamana naga abincin yayi dadi ai .
Baiki ba yasa hannu ya mayar ga abincin daddy yaci gaba da magana yace ka kwantar da hankalin ka ka saurare ni.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGO, , , , , , ,
🧕🏿3️⃣9️⃣🧕🏿
INA MAKU FATAN ALHERI ACIKIN WANNAN TAKIN DA MUKA SHIGA UBANGIJI ALLAH YASA MU DACE DA RAHAMOMISA AMIN YA ALLAH YAR UWA, , , , , , ,
Har ya juya ya tafi motar shi ta fita get din gidan tana tsaye tana daga mashi hannu tana murmushi a fuskan ta ta sauke ajiyan zuciya ta juya zuwa cikin gida.
Still su Faiza na falon ta shiga tana fadin aaah lafiya baku ga lokacin sallah yayi bane kuna zaune kuna kallo .
Nan suka bata rai sai anty tace may nene haka wai ina kuma safiyan ta shiga kuma bata zuwa ta dauke kayan nan a nan tashiga da su .
Faiza ce tai karfin halin fadin baza a bude muga abinda aka sayo ba shi muke jira mu watse dama wani kallon banza anty tai mata har ya sata natsuwa .
Tace don Allah baku jin kunyan hakan da kuke yarinyar nan bata saka maku ido amma ku kokarin ganin kwakwaf dinta kike yi ko yaushe.
Dan malama taya ni kwashe kayan nan mukai mata ciki kafin mu watse haka nan cikin bacin rai suka taya ta daukan kayan zuwa daki na sun shiga ga dakin tas sai kamshi ke tashi na gyara gado kamar wadda keda mijin aure a dakin.
Ina bandaki koda suka shigo sai maganan anty naji tana cewa ga kayan ki nan mun shigo maki dashi kafin fito ta face daga dakin don haka na tsaya nayi alwala nai sallah.
Sai da na idar da sallah duk suna falo sun fito na dauko kayan zuwa wurin anty da su buda tashiga yi tana yabawa da kyan abubuwan tace wanan irin kyauta haka Safiya ?
Na dan marairaici nace wallahi anty ni har abin yaban tsoro don haka yau ta diban kayan duk abinda yai mashi dadi a rai.
Wani irin dariya ta kwashe dashi tace ina ruwan sabon shiga dake dashi yanzu duk kun zama kamar yan koyo Faiza ce ta dakatar da duban wani ruba da ta dauka tana dubawa don bata san ko may ye a ciki ba.
Tai saurin aje roban a hannun ta tana kallon anty gami da cewa ko dai da walaki ne wanan sayayyan haka nikan nayi mamaki haka kawai zikau mutum zai yi hidama haka.
Ashe zamu sha buki kenan ta fada a cikin gatse wa mu biyun duka sai anty tace inda rai da lafiya mun kusa cassawa.
Tsukin da Fati taje ne ya katse hiranda faiza da anty keyi kan kaya tamike but ta shige tana ambatan munafunci shi kadai na iya ji cikin maganan ta.
Bayan shigewan tane anty tace wawiya kawai mara hankali don rashin wayyo wai ke ke gwada ma namiji kina son shi baza ki jira ya furta maki ba da bakin shi.
Sai faiza tace wanan shi ne son maso wani anty ta karasa da koshin wahala ba tana daki tana hauka shi hankalin shi na inda yake so.
Ashe bata karasa shiga ba tana jin duk abinda suke fadi sai dai bata ga bakin su sai ni da banyi magana ba taji haushi na.
Wai dama mu yan kyauye mun iya shige da fice wurin kwantan maza an raba kayan bayan anty ta fitar min da masu amfani naci din ne kawai tace a raba.
Bayan na koma daki wayana dake cikin jakkata yai kara da sauri najawo jakar ina daukan wayan wani irin firgita nayi don ganin kudi a jakar nawa.
Har wayan ya katse ban samu dauka ba don kudin ya firgitani kara waya ya kara yi sai na dauka a firgice ina sauke ajiyan zuciya.
Ummi na ce muka gaisa da ita na tambayi mutanen gida take cewa kowa lafiya sai dai mahaifin ki ne baiji dadi ba kwanan nan.
A firgice nake tambayan abinda ya samay shi take cewa dai je asibiti an bashi magani amma bin sai gaba yake yi kuma.
Na dauki salati nace ummi zan zo ko gobe ko zuwa jibi in Allah ya yarda mukai sallama hankali na bai kwanta ba ga zancen kudi ga maganan baba da ya tsaya min a rai.
Don haka na kasa bari sai da safe na saka hijjab a firgice tare da daukan kudin da wasu kaya daga cikin na dazun na hari dakin anty din.
Nayi sa a tana dakin bata nufi dakin daddy ba lokacin tana gani na ta mayar da hankalinta gare ni tare da fadin Safiya lafiya kuwa.
Karasawa nayi bakin gadon ta na zube kasa sai ta mayar da hankalinta gare ni na fitar da kudin ina mika mata nace anty yanzu nagan su a cikin jakkata ba san da su ba kuma.
Murmushi tayi ta karbi kudin a hannuna tana dan juya kudin tare da yi murmushi tace wa zai saka maki in ba Sulaiman ba don yasan in ya baki ba karba zakiyi ba don ya fada min kin ki ki saki jiki ku fahinci juna .
Dukar da kai nayi kasa ina tunanen yaushe ya zuba min su ban sani ba to wai ma ni ina zan kai wanan kudin haka masu uban yawa.
Ita ce ta katse ni da cewa indan kina tambaba ne bari yanzu in kirshi muji sai ta shi ga lalavan wayan ta dake bayan ta, alokacin nake fada mata cewa mun yi waya da ummi yanzu take fada min jikin baba ba dadi .
Sun je asibiti wai amma abin bai ja baya ba na karasa fadin ina son inje gida anty don in ga halin da yake ciki.
Ashe har ya dauki wayan ban sani ba yaji may nake fadi yake cewa tare kuke da mutumiyar ke nan tace eh wallahi gata nan tazo min a firgice wai taga kudi a cikin jakkanta.
Murmushi yayi yace rabon ta ne ya shiga jakkan ta kila tace ai dama nasan aikin kane amma dai ka ruda min kauna ka sani.
Dariya yayi yace ina son ta saba da halina ne tun yanzu idan zan ba mutum abu bana bashi ya sani sai baya na.
Tace kabi mun kauna a sannu ko muce mun fasa kaje gaba ka samu daidai da kai yace tuba nake babban yaya kin san kaunar taki sai a hankali.
Nan take fada mai zancen mahaifina da nazo mata dashi ya kama fadin subbahanallahi yazu yaya ke nan tace wallahi fa daddy nake son ya shigo musan yaya za a yi don tace zata tafi.
Yace OK kuyi magana dashi muji yaya za a tsara mata tafiyan don ba abin da za a tsaya bane wasa saboda ba a san halin da yake ciki ba.
Nan dai su kai sallama ta kashe wayan tare da mayar da kallon ta a kaina tana fadin dama yakanyi ciwo haka ne na girgiza kai tare da fadin gaskiya bai taba yin haka ba sai wanan karon.
Turo kofan da akayi ne muka mayar da hankalin mu ga may shigowa daddy ne yace a a kuna meeting ne haka komay ?
Tace dashi uhumm wallahi mahaifin ta ne aka bugo waya yanzu baida lafiya shi ka gan mu haka.
Subbahanallahi shi ma ya ambata yana cewa tunda suka bugo jikin ya matsa mashi ke nan kwarai tace ai itama maganan da takeyi yanzu ke nan hankalin ta ya koma can.
Yace dolle ne amm yazu dai abari zuwa safe sai inga yadda ya dace ayi ta tafi har ya juya zai fita daga dakin sai ya juyo yace shi sulaiman din yasan da zancen ?
Koda yake ma baridai zan sam abin yi akai adai bari har Allah ya kaimu gobe din tukun na ya fice daga dakin ta dawo da hankalin ta gare ni.
Tace yanzu dai ki kwantar da hankalin ki sai da safe din in Allah ya kai mu jeki ki kwanta har da safe.
Haka na mike gwiwa na yayi sanyi nace sai da safe anty tace Allah ya tashe mu lafiya ki dai kwantar da hankalin ki kinji na fada maki.
Nace tau anty na gode na fice tare da rufo mata kofan dakin ta bini da kallon tausayawa gare ni ta sauke ajiyan zuciya.
Tun da na tun karo dakin na fahinci an shiga min dakin na karasa shiga aiko nan naga kayana a hargitse alaman an tone min kaya ana neman abu.
Bandai san may aka dauka ba na gyara kayan tare da hayewa gado ina ci gaba da tunane a raina dole ne baba yai ciwo abu yai mashi yawa a zuciya yanzu.
Ga nawa matsalan ga na Saadatu sanan kuma ga na gida mazan gidan mu duk ba wanda ya mayar da kan shi abin kwarai.
Dole abu yai mai yawa a zuciya tausayin halin da gidan mu ke ciki ya kamani na kalli kayan da sulaiman ya kashe min kudi a kan su nace a raina ai wanan da kudin ya bani na sai wa yan gidan mu abinci dashi zai kai su har tsawon wani lokaci suna ci.
A haka har barci ya dauke ni sai asuba na falka na yi sallah ina idarwa kuwa na kira ummi ina tambayan ta yaya suka kwana.
Tace gaskiya kan jiya ba ai barci dashi da dadi ba yanzu ma yaya Sani yashigo yana shirin su koma dashi asibiti.
Nace a bashi waya mu gaisa in ji may ake ciki yake fada min wallahi kan baba yana jin jiki yanzu asibitin zasu koma.
Babu kudi da asibitin birni zasu tafi dashi aje can a duba shi a san may yake damun shi nace yaya ko yanzu can zaku tafi.
A ari kudi ko nawa ne idan nazo zan biya yace ai an nema ba asamu aro ba sai nace yaba ummi wayan muyi magana da ita.
Ya bata wayan nake ce wa tabada kudin da zasu sarin kaya tace jiya suka saro kaya dasu nace a je wurin gwagon ta duk inda zasu samo kudi a samu kafin in zo.
A haka muka rabu sunje sun samu kudi kudin dan gidan mama ne kaunar ummi na sadakin shi aka ara nace ba matsala insha Allahu idan nazo zan biya.
Ban fito ba yadda na saba sai ga anty dakin a lokacin nayi kuka idona yai ja ta zauna a kusa dani tana cewa kuka kikayi ne Safiya.
Na dukar da kai ina zubar da hawaye nace anty jikin na baba ya matsa mai jiya wai basuyi barci ba dashi.
Subbahanallahi suko sai su zauna da mutum gida haka yana jin jiki ba zasu kaishi asibiti sai su zura mai ido.
A sanyayye nace da ita wai ba kudin da zasu kai shi asibitin ne suka ce ikon Allah toh Allah ya sauwaka.
Yanzu dai ina gani sulaiman zaki bi yau ku bi jirgi idan kun isa Abuja sai ya saka ki mota da za a kai ki gida yau zasu tafi da shi da daddy can.
Jin tace da daddy zamu tafi yasa hankalina kwanci don da zance mata ta bari in tafi a mota yafi don gudun zargi amma jin da daddy zamu tafi sai hankali na ya dan kwanta.
Yanzu dai ki tashi ki shirya zan fita inga abinda ya dace ayi kafin ki wuce ta fita nikuma na tashi na shiga shirin tafiya.
Su faiza basu san da zancen tafiyana ba sai da na fito don daddy yace ace na fito shine suke tambaya anty ke fada masu mahaifina ne baida lafiya.
Fati tace shine kawai zata bi daddy da uncle don mahaifinta baida lafiya sai dai inda wata manufa zata tafi.
Da sauri anty tace may kike nufi ko may kika mayar damu ne kina nufin mu din mutanen banza ne komay ?
Shiru tayi don maganan itama haka yazo mata nan yar nata tai mata tas sai da ta raina kan ta Faiza cewa tayi zata rakani.
Anty tace da ita kema kin san yayan ki ba zai yarda ba ki tafi kar ma ki dauko wa kan ki wani magana a na zaune kalau.
Haka muka shirya muka fito motan daddy muka shiga zuwa airport din inda anty tai muna rakiya ita da Faiza .
Acan muka samu sulaiman nan sukai shige da fice har aka kira mu tafiya ya tashi ban san lokacin da kuka yazo min ba.
Anty tace dani a a kukan may kuma safiya kamar wacce ta tafi ke nan ashe akwai aiki randa zaki tafi gidan mijin ki.
Daddy yana muna sheri haka na barsu don anty itama ta karaya da kukan da taga ina yi din har sai da jirgin mu ya daga suka koma gida.
A jirgin kujeran su daya da daddy inda na samu wata mace tana da yawan surutu don har muka kawo hira take min a inda take ce min wai tazo ganin mahaifan ta ne a lagos.
Abuja take zaune ita da mijin ta sai dai mijin nata bayerabe ne ita kuma uwarta bayeraba ubanta bauhaushe.
Yaran ta biyu yanzu take tambayana ni a lagos nake zaune nake bata amsa da a wurin anty nake zaune zanje gida ne mahaifina baida lafiya.
Ta tausaya min har ta karbi lambana tace inda mun sauka zata kirani taji lafiyan mahaifin nawa.
Mun sauka duk a tsorace nake don ban taba ko ganin jirgi ba balle in shiga sai gani yau a cikin sa kuma mun sauka lafiya da kudirin ubangiji.
Mota yazo ya dauke mu muka tafi gidan daddy bamu dade ba suka fice suka barni ina zaune tunane ya cika min zuciya zuwa .
Zuwa sha biyu da rabi sai gasu sun dawo gidan sai dai sulaiman ne kawai bai ko son kallo na sosai ya zauna a kujeran yana fuskantana.
Yace sorry ko yanzu dai ki fara isa ga mota nan za a kaiki har gida sai kudi da zan baki ki yi duk yadda ya dace ayi.
Naso mutafi tare amma hakan ba zai yuyu ba don wasu yan matsalolin da nake dashi ki tabbatar anyi masa abinda ya dace dashi don Allah kudi ba matsala bane duk yadda ake ciki sai ki buggo min.
Nace a hankali na gode sai dai akwai kudi a hannu na don wanda ka bani anty ta bani kuma ta kara min wasu.
Yace bana son gardama kin san abunda zaki sama a can ne ya mike yana cewa ki kula da kanki kuma ai mashi duk abinda ya dace don Allah in akwai wani matsala a bugo min in sani .
Ki fito mota na jiranki a waje ku tafi daddy yace in maki sallama aiki ya rike shi bazai samu zuwa kuyi sallama ba.
Ban san lokacin da nakai har kasa ina mashi godiya irin wanan harcin da yai min ba dan haduwan mu dashi haka.
Murmushi yayi yace haba haba ba komai ki dai kula da kanki sai yai gaba na tashi a sanyayye nabi bayan shi.
A waje naga wata mota da driver naji yana cewa driver indan dare yai mashi goben in ban gama ba zai iya kwana ya bude min na shiga ina mashi godiya.
Muka wuce yana daga muna hannu sai lokacin na sauke ajiyan zuciya ina mika godiyana ga Allah da wanan baiwan da yai min dan lokaci guda.
Motar mu ta halba saman titi ina ta kallon yanayin garin zuciya fam da tunane kala kala muka nausa ga tafiya.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , ,
🧕🏿3️⃣8️⃣🧕🏿
UBANGIJI ALLAH YA BA MU IKON BAUTA MASHI, BAUTA TSARKAKKEKE,
YA ALLAH KA KARBA MUNA IBADUN MU, , , ,
Tsura ma dan uwan nashi ido yayi yana sauraren bayanin shi daddy yaci gaba da cewa kamar dai yadda aure ya cika kan wanan cutar haka itama aure ne sanadin samun wanan cutan a gare ta a halin yanzu.
Innalillahi yake iya fadi acikin ranshi da fili yace wai kuna nufin wannan yarinyar ta taba aure har an cuta mata irin haka.
Yace cikin garin nan na Lagos tana zauna da miji ta sai dai auren anyi zaman ne a cikin ukuba sai kuma ga wannan cutar ya baiyyana mata.
Ya ce Ya Allah kaza ma gatan mu yanzu wanan abin da mai yai kama mutum yasan cewa yana da cuta a tare dashi amma don ha inci sai yaki fadi har sai ya lika ma dan uwansa abu ya baci adawo ana dodofar tsiya.
Sun dauki lokaci suna magana daya kafin ya mike yace zai tafi har a lokacin ranshi bai mashi dadi sam don abin yadawo mashi sabo a rayuwan shi.
Yai masu sallama anty tana tabayan shi yaushe zai bullo kuma tasa aimai girki sai yace yana dan aiki idan ya rarage zai shigo.
Daddy ya mike suka fice daga gidan tare dashi sun shiga gari tare don duban wasu aiyuka da ya bayar aimashi tun wancen lokacin.
Washegari anty da zancen nama turkey ta dole shi aka dafa mata nai miyan shi nan aka taru a falo kowa na kwasan dafuwa.
Sai da anty ta bari sunyi nisa da cin abincin ne take cewa damu aduniyan nan babu abinda nake kamar wanan namar .
Nan kowa ya shiga fadan albarkacin bakin sa akan naman bandani dana ce ban taba cin shi ba a rayuwana dariya suke min sosai saka su daddy sun shigo gidan shi da Sulaima a bayan shi.
Daddy ne ke muna kallon mamaki ganin irin dariyan da sukeyi din yake tambayan maiyai maku dadi haka irin wanan dariya.
Fatine ta iya bashi amsa da cewa wai Safiya ne ke fadin ita bata taba cin naman turkey ba shine tabamu dariya sai daddyn ya mayar da kallon shi inda nake yana zama a kusa da matar shi yace.
Kauna na kada ki damu da dariyan su watarana sai kin ci abinda duk kan su basu taba ci ba don haka kema zaki rama nan ba da dadewa ba insha Allahu.
Yanzun dai tashi kin ji ki debo muna muma mu dandana muji santin da sukeyi akai don da gani yayi dadi tunda naga Fati yau haka baje baje.
Na mike zuwa hada masu abinci daddy ya kalle matan shi da dariya ya cika yace kar kuyi mamaki zama kauye don nan da wani lokaci ta fiku bude ido .
Dariya ya ci karfinta tace ai bamu haka da Safiya yadda take juya naman a kyamace ne yaban dariya.
Sulaiman ya katse ta da cewa ai cin nama ra ayi ne idan bata so sai a saya mata wani mana taci kuma kuna kallo.
Sai gani na dawo ina ce ma daddy na hada abincin dama na hada tun basu dawo ba anty tace dani to ke kin ji uncle yace tunda mun bata maki rai zai fita dake ki zabi naman da kike son ci a sayo maki muna kallo.
Na da yi mata murmushi nace ni fa anty kin san nama bai damay ni bane kawai ba wai wanan ba.
Kowa wurin yai mamakin jin abinda uncle ya fada do cewa yayi idan baki son nama sai a sayo maki wani abin don haka dana gama zamu fita.
Da sauri na dan kalle shi sai naga ba wasa ga maganan shi sai Fati ne tace Safiya muje mu shirya dama nima ina son fita kin ga sai mu tafi tare.
Anty tace waya kasa dake a ciki babu inda zaki sarkin son yawon tsiya kawai daga jin za ayi fita sai ki ara ki yafa har kina wani muje ki shirya kedin a shirye kike.
Faiza ne tace don Allah anty ki bari mu fita muma mu lakaci arziki ta sake cewa na fada maku ba mai bin su ko ina nice nace amma da twins zamu anty?
Ke kan ana kau da wasu kina jan wasu ai gara zuwa da wa yan nanbda zuwa da wa yancan yan sa maganan.
Shine yace da ita dana ai sune gaba wa yan nan din dai da kika hana su sun hanu babu wacce zamu fita da ita sai dai suga mun dawo.
Nai mamakin jin ashe yana magana mai tsayi irin haka don ban taba jin yayi magana mai tsawo ba duk sani na dashi.
Amma yau tun shigowan su na fahinci akwai canji a tare dashi sosai kodan ganin daddy tare dashi ne oho ?
Daki na shiga ba wani dogon shiga nayi ba dogon riga ne kawai sai dankwalin shi dana yane kaina dashi.
Zama nayi ina tunane ni kadai a daki na yadda zamu fita dagani sai shi sai ga su yan biyu sun shigo da murnan su wai in fito in ji uncle mu tafi.
Sai da na dan bata lokaci na fito anty bata falon sai su Fati ba wani magana mai dadi sai harara da suka raka ni dashi.
Ina tambayan su anty sai Faiza ne ta bani amsa da cewa tashige ciki nace in ta fito ki gaya mata mun tafi tace a sayo dawisu idan anje sai musan ke yar gaban goshin tane.
Nasan magana tasa min ban kulata ba na fice kawai abin yana sosa min zuciya fati ko tsaki naji taja tana bakar magana .
A mota na samay su shida su yan biyu zaune a baya hakan ya nuna min ke nan a gaba nibzan zauna kenan.
Kafin ma in karaso ya bude min gaban mota haka na daure na shiga duk a takure dani muka fice a gidan.
Tafiya muke babu mai magana sai su yan biyu dake ta hiran su a bayan motan basu ko kula mu ba fuskan shi na kallon titi niko na mayar da fuskana gefen da nake zaune ina kallon yadda garin a kullun yake da da girma da bunkasa duk da an dauke headquater anan.
Naji yace Safiya kin san abin da madam ke shirin shiryawa a tsakanin mu ko ?
Na kalli yaran dake bayan motan naga hankalin su baya wurin mu nace a hankali nadai ji tana fadi amma bamu yi magana da ita ba tukun.
Yayi ajiyan zuciya sanan ya nisa yace ya kamata in san raayin ki kiyi hakkuri muyi magana anan don bamu da wani lokaci na sake haduwa irin haka.
Shiru na dan yi kafin in sauke ajiyan zuciya ince dashi to uncle , uncle ina anty ta fada maka matsalan da nake ciki, din haka ni naga kawai ayi hakkuri ba abu bane da zai yuyu a tsakanin mu.
Saboda gaskiya sai na kasa magana karshe dai nace uncle mudai yi hakkuri kawai ya dakatar dani da fadin saboda may zamuyi hakkuri da maganan bayan abune wanda zai yuyu.
Ko bata fada maki cewa nima a halin da nake ciki ke nan ba sai na dan kalle shi kadan yace yes nima victim ne amma sai wanda ya sani zai sanda hakan.
Idana na kallon kasa look safiya ba wai abune da zamu tsaya muna yi wa juna kwana kwana ba da maganan.
Ina son ki sani wanan abinda mutanen nan suke kokarin hadawa a tsakanin mu gani sukayi mun dace da junane.
Ina son ki sani koda wanan matsalar ko babu shi akan mu wallahi ni son ki nakeyi tsakani da Allah ina mai tabbatar maki ba zan iya hakkura dake ba a yanzu.
Ya nisa ya sake cewa wallahi ina son ki sani ban taba haduwa da macen da hankalina ya kwanta da dabiun ta ba irin ki.
Gashi dan haduwan na dake da madam ta fara min maganan nan maganar sai bibiyata takeyi na rasa sukuni a tare dani.
Sai kuma naga yayi murmushi yace sorry bazan iya ci gaba da fada maki ba amma na gaya maki gaskiyan zuciya na don ba wani lokaci nake son a dauka ba ga zancen.
Nayi shiru ina sauraren shi sai da naji abunda ya fadi a karshe nai saurin dago fuskana sai wanan lokacin muka hada ido dashi.
Take gabana ya fadi don kwarjinin sa da na ga ya fito fili a idona nace da wuri uncle yace dani yes I mean it, idan kina shakkun hakan gara ki daina ko kuma kina iya bani baki ki gani.
Nayi shiru na rasa may zance dashi yadda naga ya zare min a lokaci guda to ni may zance dashi eh ko a a .
Har ga Allah uncle ya samu karbuwa ga zuciyana don ina son shi har cikin zuciyana saboda me ne sulaiman dai namijine wanda duk wata mace ke burin mallakan shi a matsayin mijin aure mutunci addini kamala da natsuwa da gaskiya irin na nuna shi din daban ne da sauran mazan dana sani akwashi.
Amma kuma nauyi da kunya ban taba ganin wanda nake jin nauyin shi da kunya ba irin shi don haka bazan iya nuna mashi kai tsaye na amince da bukatan shi ba.
Bai kara yi min magana ba har muka isa wani shopping mall anan ya tsaya yace mu fita kowa ya dauki abinda yake so.
Kunya bai bari na dauki komai ba sai wani turare dana dauka ganin kuya bai bari na dauki wani abu sai naga ya shiga daukan duk abinda yaga ya dace yana kadawa kwado sai da basket din ya cika sosai har yana zuba ya bari.
Mukaje gurin biya ya biya akai muna packeg din su a ledojin shagon muka fito.
Bai tsaya ba sai wurin wani shagon sai da nama kala kala nan ya shiga shi kadai sai gashi ya fito da ledoji shake a hannun shi yaja mota muka tafi.
Ba magana haka muke tafiyan sai ya koma hira da yaran har muka kawo gida sun fita na bude mota har na saka kafa na daya a waje naji yace dani ina sauraren ki nan da two weeks.
Ban ce dashi komai ba sai da na fito daga motan ne nace mun gode bai bari mun dauki komai ba ya kira security daya ya taya shi shiga da kayan ciki.
Lokacin yamma yayi sosai suna falo zaune muka shigo duk idanuwan su a kan mu anty farin ciki ya kasa boyuwa a fuskanta.
Suko nasan ba komai ya zaunar dasu ba sai gulma basuyi mamaki da irin kayan da muka shigo dashi ba don sanin waye sulaiman din da sukayi.
Bai tsaya ba baya ya aje sai yace da anty zai koma sai dai da safe idan ya shigo karyawa mikewa tayi ta bishi baya suka fita gidan tare.
Sai lokacin Faiza tace yau kan kun sha dadi wallahi naso ace anty ta bari mun bi ku muma mu lakato arziki don ba a barmu mu dawo haka ba.
Wai safiya kodai wani abu na shirin faruwa ne keda uncle nace may ko ke shirin faruwa rabona ne kawai ya koka a wurin shi dariyan ku akaina yazama min sanadin samun alheri yau a gurin sa.
Tace indai yai wari maji amma ai banza baya haka da sauri fati tace balle ma may zai yi wari a nan wanda ke gogayya da mata hamshakai ne zai tsaya a nan.
Nace ako hakan in Allah ya nufa sai ki ga ya faru anan din inda ba komai tai saurin cewa ki iya lafazin bakin ki ramin kura ba wurin wasan yaro bane koda kuwa an rika masa.
Dariya na wuce dakina ina yi ga leda a gaban su babu halin budawa su gani kada anty taci masu mutunci akai dole suka zauna zaman jiran ta ta dawo.
A can waje kuma sun tsaya wuri motan shi ne yayin da ya dafa mota da hannun shi daya suna magana da anty din tace to yaya ina fatan dai kun dan fahinci juna wanan fitan da kukayi tare.
Yai murmushi cikin jin kuya yace mata wanan kaunar taki kunya yai mata yawa taki sakin jiki mu fahinci juna kamar mai tsoron kar na sayar da ita.
Tayi saurin fadin may Safiyan tayi maka kuma yace yace kiyi hakkuri zakiyi mamaki amma wallahi nidai yarinyar tayi min so sai ta tsaya min a rai.
Amma naga kamar ba za iya shawo kanta ba don tana da kunya sosai ga kurciya a tare da ita kuma.
Anty zatayi magana ya hanata yace don Allah madam ki taimaka min ki shawo kanta wallahi son safiya nake yi da zuciya daya ina son ga na taimaka wa rayuwanta .
Auren ta nake soyi na bada dadewa ba sai dai ban san yaya zaku dauki maganan ba yanzu.
Ga baki daya maganan shi ya gama kashe mata jiki da mamaki don bata taba tunanen zai afaka haka da sauri a sona ba shiru kawai tayi ma rasa may zatace dashi.
Ganin tayi shiru yace madam kina mamakina ne ko tace ina jin ka dadi ne ya kashe ni wallahi wai yau kaine kake maganan aure haka a gabana babu kunya sanan wace kake so din gata yar gida ce.
Sulaiman gaskiya ka gama kasheni da jin dadi don haka ka kwatar da hankali ka da yardan Allah kamar ka auri safiya ka gama.
Bari ma ka gani yanzu da na shiga zan tun kare ta da maganan har sai ta bani baki ayi don yarinyar na jin magana na sosai.
Don haka ka barni da ita kawai zan san yadda nayi da ita kar abin ya dauki lokaci mai tsawo iyayyen ta kuma zan san yadda na lurar dasu akan zancen.
Yaji dadi har ya kasa boyewa ya rika fadin na gode madam thanks alot Allah ya bar min ke kin zama babban yayada gaske.
Tace au dama ke nan ta karyace yace ai da madam kike yanzu ko zamu zama sarakai dake tace aban tukwaici na yace ai tukwaicin ki shine daga ke ba wata a gidan nan .
Na biyun bazan fada maki ba sai abin ya yuyu zaki sani sai suka sa dariya a tare a haka ya tafi tana shamatar shi yana cewa yaji.

🧕🏿4️⃣0️⃣🧕🏿
YA ALLAH MUNA ROKON KA KABA MU IKON BAUTA MAKA BAUTA TSARKAKKEKE KA KUMA KARBA MU NA IBADUN MU, , , , ,
Lumshe idona nayi tun da muka fara tafiya ashe da haka nayi barci sai da mukai nisa sosai ni kadai a baya zaune sannan na falkafirgigi daga barcin ina kallon gaban mota inda driver keta faman sharara gudu.
Sai yamma lis muka iso makwabtan karkaranmu nan na dan fahinci ida muke don da gaba yana tafaduwa don ban fahinci komai ba.
Garin muke shiga lokacin marance yayi sosai don haka mazaje da yawa suna kofan gidan su suna dakon kiran sallah.
Kwantace hanyan gidan mu nake mai har Allah ya kawo mu lafiya na nuna mashi gidan mu ya nufi kofa yai packing a kofar gidan .
Duk hankalin mutane ya dawo kan motar suna son su ga wanda zai fito a wanan mota mai kyau haka ganin ta tsaya a kofan gidan mu ya su yaya sani tasowa da abokan shi.
Da sauri driver ya fito ya bude min mota na sagalo kafa daya dayan na a ciki na tsaya dauko hand bag dina zan fito.
Yaya sani yace ah Safiya ne fa da sauri yazo yana kokarin rike marfin motan da nake fitowa ciki daga ciki suma sauran sannu da zuwa suke man na gaishe su cikin mutunci sai na nufi cikin gida.
Nan suka fara biyo ni da kayan yar wurin mamace zata fito sai gani ta tsaya tana kallo na don bata sanni ba sai da nace da ita maimuna ina zaki sai ta dauki muryana tace Safiya ke ce nace nice maimuna.
Nan ta fara ihu lah ga Safiya ga safiya daidai lokacin da nake kutso kaina cikin gidan kenan duk hankalin su ya koma wurina suna mun kallon kurrullah.
Duk suka rufe ni suna min sannu da zuwa yayin da abokan yaya sani suke ta shigo min da kaya daga ciki ni kaina abin ya bani mamaki ko shiga daki ban yi ba bayan mun gaisa dasu mama sai na wuce dakin baba kai tsaye don in ga halin da yake ciki.
An zaunar dashi wai yai sallah amma saida ummina ta tsaya daga bayan shi na shigo dakin ina cewa sannu baba yaya jikin ?
Yadago kai zabban tausayi yace safiya kece tafe nace eh sannu baba yana fadin wai may yasa su ka fada min baida lafiya banji may yake fadi ba sai da na tambayi mama dake gefen shi take fada min.
Na juya wurin mama ina tambaya anko tafi asibitin birnin yau sai tace man wai kudin da aka samu arro baya isa don tun a daukan mota da za a tafi rabin kudin ya kara nace haba haba mama nace a kaishi ko nawa ne , gani nan tafe ai zan biya.
Na dan tsaya tsaye shiru ina kallon yadda baba yake wahala da bautar Allah sai na fita dafa daki na samu kanne na sun shiga min da kayana dakin mu .
Sai dai suna waje suna gardaman wai kwali goma ne inji yar wurin inna sai dan wurin ummi kanina yace hummumm sha biyu ne na gardama ya kaura a tsakanin su.
Inna ta kwala ma yar ta kira wai ina ruwanta ko kwali dari ne na shigo dashi tasan sanan da nake yi na samu kwalayen da na shigo dasu iyayyayena suna murna.
Kai kawai na girgiza na ce a ban buta nayi alwala daga dakin ummina ban tsaya sauraren ta ba bayan munyi sallah ne na fito na samu yaya sani nake cemai yaka mata mu tafi asibiti da baba sai yace ai maganan kudi ne da mota nace motar da na zo da ita zamu tafi.
Yace sai a bari sai da safe ina shiga dakin nace dashi yau dai zamu tafi yanzu ma zamu kama hanya dawa zamuyi tafiyan ?
Nake tambaya yaya Sani din ina dafa baba ina kai sannu yaya jiki ya gyada min kai alaman da sauki jikina ya kara yin sanyi don dai ni a yi sani na dashi ban taba ganin yayi ciwo irin haka ba.
Mama tace bari taje ta shirya don da ita za a tafi inna da ummi su zauna gida amma da inna ta samu labari sai ta tada fitina wai ita zata .
Yaya sani yace ai ba kasuwa zamu ba da kowa zaice zai tafi da mama kawai zamu sai ni da Nura yace mata.
Na fita naiwa driver magana kamar yadda Sulaiman yace in sanar dashi duk abinda nake so nasa ankai mai ruwa da maltina da abinci yana ci ne sai gani na fitinan nake fada mai tafiyan mu birni.
Sha daya na dare muka isa asibitin basu so su karbe mu ba a lokacin sai da na nuna masu kudi sannan suka fara nan nan da mu, har likita suka tayar cikin daren nan yazo ya duba baba maganin da ya rubuta.
A cikin daren nan su yaya Sani da driven nan suka fita neman magani anyi saa an samu a wani shago sai dai shi yaya sani yana ganin yawan kudin don dubu ashiri da wani abu suka kaso .
Ya dawo yana fada min nace mun yi arziki ai tunda an samu tun cikin dare akaiwa baba aluran da bashi maganin sai gashi ya samu barci sosai ranan.
Washegari nacewa driver ya wuce sai yake cewa ai sunyi waya da maigida yake cewa ya dan tsaya don zirga zirgan mu ya taimaka muna naji wani iri a raina sai dai a fili cewa driver nayi anya ayi haka bazamu takura maka ba ?
Haba madam aini a kan aiki na nake daganan har ki gama banda damuwa ko kadan Allah dai yaba baba lafiya.
Nai mashi godiya sosai yace babu damuwa hajiya ai mu aikin mu ne naga kuma oga ya damu sosai da ciwon na baba murmushi nayi kawai.
Sai na tuna ban kirashi ba tun jiya kamar yadda yace in kirshi din don ya anshi wayana yasa min nombashi da zamu wuto.
Gefe na koma saida na tattara natsuwa na wuri daya sanan nai dialing din nomban na shi ringi na uku ya daga wayan yana cewa.
Safiya yaya ai na zaci bazaki kirani ba kin ga mutanen gida kin manta da kowa.
Murmushi nayi nace wallahi ba hakana bane ya dan kwaikwayeni yace to yayane nace kawai dai jikin babane ya tsoratani jiya da na samay shi jikin ba dadi wallahi.
Amma yanzu ya samu lafiya sosai don maganin da aka rubuta mai da allurai tunda ya sha su ya samu barci jiya sosai.
Yace masha Allah haka akeso to yaya mutanen gida nace suna lafiya sai nai shiru kusan tare mukai magana ina cewa kuma har da wani dawai niya haka mai yawa.
Yace bake nai wa ba iyayyena da kanne na naiwa tsaraba ki basu godiya na fara mai yace haba na fada maki bana son haka nifa iyayyena ne yanzu koba hakana bane ?
Murmushi na danyi yake cewa yanzu dai hankalin ki ya dan kwanta ko baba ya samu lafiya sai na sauke ajiyan zuciya nace hakane amma da hankalina a tashe yake so sai.
Don mu din tallakwa ne na karshe indan baba ya kwanta wa zai dube mu shi kaga hankali na ya tashi sosai.
Yace karki manta da cewa Allah ne mai yi ba wani ba yanzu bagashi ya samu sauki cikin yardan ubangiji ba nace haka ne kuma.
Yace idan ya tashi ki gaida min shi zan shiga meeting yanzu dama don baki kirani ba ne yasa ban kiraki ba yanzu kuma naji dadi alama ya nuna na dan samu karbuwa ke nan.
Kai nace haba uncle kabar wanan magana tukun yace na bari as you wish ganin zai kashe wayan yasa nace sai kuma driver yace kace ya tsaya damu.
Yace eh haka na umurce shi don idan ya wuce ina zaku samu abin yin zirga zirga shine nace ya dan dakata har muga yadda hali yayi.
An gode na kara fadi zan shiga godiya naji ya kashe wayan shi kit na dubi wayan ina murmushu na shiga dakin da aka aje baba din har lokacin yana barci naja kujera na zauna tare da kafa mai ido.
Mama tana zaune a kasa saman tabarma tana karyawa da abincin da na sa yaya Sani ya sayo muna don bamu da kowa a garin.
Na dan dade a zaune sai ya motsa da sauri na dago ina cewa sannu baba yaya jikin ina dan gyara mashi kwaciya yace Safiya ke ce yaushe kika dawo ?
Nace a sanyayye jiya na dawo baba yaya jikin yaya jikin baba ?
Yace jiki da sauki Safiya na gyara mashi kwaciya yace baiyi sallah ba da tai makin mu nida mama muka kamashi ya kewa yayi alwala.
Bayan ya idar da sallah ne yake cewa nan ina ne mama ne ke fada mashi ai asibitin birni aka zo dashi jiya da dare da safiya ta iso.
Yace Allah sarki sannu Safiya nagode nagode ubangiji yai maki albarka yasa ki gama da duniya lafiya nace amin baba mama tace yau ga ranan diya mata mun gani a gidan.
Don badon Allah ya taimaka ba da bamu san yadda wanan alamarin zai kaya muna ba kana zaune a gida ciwo zai halaka ka babu yadda muka iya .
Gashi daga zuwan mu jiya jiya har mun ga haske gashi yau ubagiji ya nufa ka bude ido nace baba don Allah ka rage yawan tunane don likita yace tunane yai maka yawa har zuciyar ka ya kumbura.
Murmushin karfin hali yayi yace yaro yaro ne tune ne ai dole mai rai yayi shi balle ni da gidana yake batun fin karfina inda rai na kuma don may bazanyi tunane ba safiya ?
Nace baba hakkuri za a yi abar ma Allah komai ubangiji yana sane da komai da bawa ya gani yanzu dai may zaka iya ci a sawo ma ?
Yace ban jin cin komai sai barcin da nake bukatan komawa don idon nan nawa kamar asa min abu mai nauyi nake jin shi.
Nace baba ka daure kasha tea mai dan zafi ko hajin ka zai warware ka kara samun karfin jikin ka.
Yace dadai kune ne kila zan dan iya sha da sauri nida mama muke cewa ga kunu nan an sawo bari a baka yaya sani ne suka shigo shida driven nan suka shiga gaida shi.
Bai sha wani abin kirki ba ya koma barcin muka sauke ajiyan zuciya muna kallon yadda yake sauke numshi a wahale wai ma cikin yaji sauki ke nan.
Sama sama muke hira da mama ina fada mata irin zaman arzikin da muke yi da anty da yan uwanta tace Safiya haklin ki ne ya ja maki .
In dai baka dauki kan ka da fadi ba Allah yana taimakon bawan sa ta ida bai zata ba Allah ne ya kawo ta cikin rayuwan ki don ta taimaka maki.
Gashi tun yanzu muga haske badon Allah ya kawo ki ba wanan alamarin yaya zamuyi kena da haka zamuyi ta kallon shi a gida babu mai taimaka muna.
Shiyasa nake ganin haukan innar ku da bata da kalamin alheri sai na tsiya akan yayan mutane duk da wanan abin da ya cika dasu kuwa.
Murmushi nayi nace banga ranan da inna zata daina halinta ba ita haka Allah ya halicce ta da hassada don bata bar kowa ba a gidan.
Tace bata fa dainawa don dubi abinda tayi jiya Sani ne kawai mai taka mata burki don badon shi ba jiya ba karamin tashin hankali za a yi ba.
Nace niko ban ga Saadatu ba ma tace tana nan daki bata jin dadin jikin ne don duk da malam ya hana a zubar da cikin jikin ta amma bai hana uwan bata abubuwa a boye ba.
Nace na shiga uku mama karfa ta kashe ta tace in ma ta kashe ta ai ita ta sani waya ci baya ina mahaifiyar ki data rungumi kaddara ba ga abin yazo mata da sauki ba.
Mu dai fatan mu ubangiji ya baki miji ki aure ki huta da zargin cewa zaman banza kike yi a can na ce ai Allah yagani mama.
Ban yi ba da sai yanzu da lalura a jikina zanyi in cutawa mutane ko mai tace ai bata gane hakan ita don idon ta ya rufe ko.
Motsawan da baba yayi yana fadin a bashi ruwa yasa mu tashi muka ce yayi hakkuri an daura mai ruwa nace barin fita in nemo likita a fada mai.
Naje gun nurse din ward din mu na fada mashi sai yazo ya duba baban ya fita kiran likita sai gasu sun dawo tare da likitan yadan duba baba din tare da zare mai ruwan da suke kara mashi din.
Yace a barshi ya dan huta zai daina jin kishin da yake ji nan dai suka kara taruwa a kasa suna mashi gwaje gwaje irin nasu na likitoci.
Yaya Nura suka iso shi da su ummi da mama da rana nan suka samu yana barci bayan gaisawan da mukayi dasu ne mama take masu bayanin halin da baba din ke ciki yanzu.
Nan dai muka wuni dasu sai zuwa yamma sukace zasu tafi drive nan dan arziki yace in bari ya mayar dasu sukace ya bari zasu shiga motar kasuwa inna sai baza ido takeyi wirin kalle kalle a asibitin.
Ya kwashe ya wuce dasu hankalin gida zai kwanta yanzu da suka zo suka gan shi dan da basu zo ba duk wayan da muke yi dasu basu yarda a yadda muka fito dashi gida wai ya samu lafiya yanzu.
Baba yana samun kulan da ya dace sosai dashi sannu a hankali yake samun sauki na shigan shi yana dan dada murmurewa .
A kwana na uku ne driver da ya kawo ni yace zai koma gida na bashi kudi yaki karba amma sai naba yaya Sani ya bashi idan sun fita.
Ban wasa da shan maganina don dama ina dashi anty tana kaini ansa a sace bada sanin kowa ba a can lagos din don haka ban da matsala wurin amsan maganin .
A kwana na shida aka sallamay mu nan muka samu motar muka dauka ta dawo damu gida kowa na ta farin ciki yadda suka ga baba ya samu sauki.
Sai dai an bashi dokoki na ya rage tunane da abincin da ya kamata yaci don ya samu lafiya muka sayo magani wadatacce muka dawo gida dashi.
Dakin mu na shiga na cire kayan dake jikina don duk warin asibiti duke yi wanka naje nayi na shirya sai na fito zuwa dakin inna.
Saadatu na kwance duk ta kumbure nace subbahanallahi Saadatu may ke faruwa haka kina zuwa asibiti kuwa maimakon tai magana sai kuka ne yazo mata.
Zama nayi a kusa da ita nace bari kuka saadatu haka Allah ya nufa damu sai dai istigifar ga bawa nace kin je asibiti tace wa zai kaini Safiya dan jike jike dai inna ke bani ina sha.
Nace zuwa zamuyi gidan mau ta dubaki mu gani tace uhumm Safiya ai da na dauka halin innan mu yasa kin fita batuna ne dan da kika zo baki nemay ba harda kuka nayi gashi ban iya fita ko ina.
Nace haba saadatu may zai sa inyi fushi dake ke fa yar uwata ce ta jini halin inna kuma inda sabi ai na saba yanzu sai dai addua kawai.
Da taimako na ta samu ta shirya don inna na dakin baba sai fitowan mu suka gani kawai take cewa ina kuma zaku haka ?
Nace wiri mau ta duba lafiyan jikin ta don ba a barta haka ba tana wahala tace ai ita taja wa kanta ina ruwan wani saaden tace dani mutafi kin ji safiya.
Nan muka fice muka barta mashin na tare ta hau nima na hau mukaje gidan an dubata take muna bayani bata samun kulawa ne sosai an mata allurai don tace akwai maleria masu ciki a jikin ta do haka tabar bari sauro na cizon ta ta bamu magani tare da fada mata abinda ya kamata taci kuma ta dinga zuwa ana dubata akaiakai.
Bamu dawo gida ba sai da na sayo mata abin bukatun ta harda gidan sauro muka dawo gida yamma tayi a lokacin nan ina ta ke cewa .
Yanzu dai anyi kudin da bamu san asalin shi ba anzo ana muna facali a gida indai tai wari ai maji komai daren dadewa .
Ba wanda ya kulata sai dare muka samu kebewa da ummina nan muka shiga hiran yaushile rabo da ita nake fada mata duk yadda nake can.

🧕🏿4️⃣1️⃣🧕🏿
Ummi ta nisa bayan ta gama sauraren magana na tana cewa dani anya yar nan baki iya tsaga fadi ba wanan mutumin bai fi karfin mu ba.
Na ce ummi nima abinda nake tunane kenan amma ita anty bata son ina fadin haka din tace yanzun dai ki dan kara nazari kafin ki kai ga gabatar dashi nan din.
Fadan inna da mukaji shiya dakatar damu daga maganan da mukeyi din da muka saurara muka fahinci da saadatu ne take fadan akan daura gidan sauron da muka sayo.
Fada sosai suke yi a tsakanin su nice na fito nayi wa saadatu magana sai take cewa wai inna tace bata yarda ta daura gidan sauron ba a dakin ta.
Nace haba inna tana da wani daki yanzu a gidan nan bayan naki don Allah ki yi hakkuri kibarta ta daura daidai inda take kwanci.
Nayi dana sanin fitowa raba fadan nan tsakanin inna da diyar ta don abin karshe a kaina ya dawo babu irin kazafin da inna bataimun ba ranan kowa najin ta a gari.
Dole naja kafana na koma dakin mu bisa umurnin mama har lokacin bata daina fadan da take yi ba ta hade mu ta zage tas tana cewa sai dai yawon banza amma badai aure ba gare ni.
Naje nayi fasikanci na nadawo ina wa mutane sallo sai inyi wa wa yanda basu san abinda nake yi ba .
Ummi tace da na hanaki fita zakiga kamar ban son zaman lafiya ne ai gashi kin jawo wa kanki kwana da bakin ciki a ran ki.
Nidai shirin kwanciya nake yi ina kara jimamay maganan Inna datake yawan fada min a koda yau she magana ya hada ta damu.
Ya zama min dole in yarda da bukatar Sulaiman akaina kamar yadda yace bai son abin ya dauki lokaci don shi yanzu bai ga abinda zamu tsaya jira ba .
Magana ummi keyi dani amma banji ba nayi nisa sai da ta kara daga murya na ji ta nai saurin cewa ummi kanin mijin anty na ne.
Kuma su suka hada ni dashi don shima irin matsalar mu guda dashi aure yayi matar ta rufe mai tana da lalura sai da akayi abin ya bayana mata.
Bacin rai yasa ya rabu da ita duka duka watan su shidda da aure suka rabu da ita tace amma ko bai kamata ya sake ta ba tunda ya dai riga da ya kamu da ciwon.
Nace ai nima abinda nagani ke nan amma sai anty tace dani dama ba sonta yakeyi ba itace ta like mashi.
Yanzu ke baki ganin akwai matsala idan kika bashi baki akan ya fito nifa ina tsoron masu kudin nan don da wuya suke rikon aure.
Nace ummi duk wanan tunanen nayi shi kuma na fada ma anty amma sai cewa tayi nasan dai ba zata kaini inda za a cuce ni ba kin ga banda ta cewa don darajan ta a gare ni.
Amma dai ni sanin da nai mai baida wani matsala rayuwa sai dai ba a san abinda ke boye ba kwai ne.
Tace yanzu dai kafin ki koma sai ki shirya kije can gida ki ga baba da yaya Adamu ki fada masu in ma mallam ya yarda sai mu tafi tare dake mu gan su.
Nace to ummi hakan ya kamata ayi nima dai hankali na bai gama kwatawa ba dashi amma babu yadda zanyi ne kawai sai ya zama kamar na watsa ma anty kasa a ido bisa kokarin da takeyi dani.
Haka na muka kwanta kowa da tunanen da yake yi a zuciyar shi sai asuba muka tashi bayan nayi sallah na fito na share gidan na tara kwanonin da akai amfani dasu.
Ina cikin wanke wanke ne na kusa gamawa sai ga inna ta fito sai cewa tayi dama ko acan abinda ke yi ke nan anzo nan za ai muna barkadon banza.
Nace inna ina kwana bata amsa min ba ta shiga daki sai gata tafito da kwanoni masu yawa ta zube min su ashe mama na daga kofan ta tana kallon mu.
Inna ta wuce tana maganganun ta sai mama tace kai wanan balain da may yai kama don Allah ba a barin mutane suji da abinda ya damay su sai bakin fitina tun da farin safiya haka.
Wa na hana yadda yake so a gidan nan idan kuma kin saka kan ki ne sai a sayar maki ba abune mai wuya ba ehhy.
Mama tace in ma zaki iya nan da shekara sai ki tayi bama sayar ba ko kwasa ne sai ki yi gaki ga wuri ai.
Wanan abu damay yai kama kin kwana fitina kin tashi dashi duk yarinyar nan bata kula ki ba ba sai kiba kanki lafiya ba wanan ai zubar da mutunci ne gare ki.
Nan dai sukai dan cacan baki tsakanin su ba wanda ya kula ta ni dai na gama na shige dakina na barsu nan.
Wanka na fito nayi ina cikin gyara jikina sai ga Saadatu ta shigo dakin ummi din ta samay ni muka gaisa.
Nake tambayan ta yaya jikin ta sai tai murmushi tace jiya na samu barci sosai wallahi Safiya na gode kwarai wallahi banda abinda zan fada maki sai dai kuma kiyi hakkuri da halin inna don Allah.
Na yi murmushi nace ai inna uwane fadan su gare mu taki wata rana zai muna amfani a gare mu dariya ta dan yi tace kayya ke dai kiyi hakkuri kawai.
Muna nan muna dan hira sai jin muryan inna mukayi tana kwala ma saadatu kira share uwar tayi kamar bata jita ba.
Sai da ta kara kiranta tace tana zuwa ta ci gaba da maganan ta sai da nace taje taji kiran da inna ke mata ta dawo.
Bayan fitan ta ne na ci gaba da shiri na nace ma ummi gidan gwagon ta zan tafi in gaida ita tace dani aiko kin kyauta.
Nace a debi tsaraba abawa kowa har da makwabta tace kidai diba sai ki ba mutanen gidan abasu sai na makwabtan duk ki diban masu.
Dole na tsaya nayi kamar yadda tace inyi din tace haka yayi bayan na raba na dauki na fanin su gwago aka fita min dashi waje inda zan samu mashin din da zai kai mu gidan gwago din.
Mu kafito ni da kauna na da zata rakani gidajen uwayen mu muka hau mashin sai gidan gwago anan muka shiririce da ita har lokaci yayi mun fito.
Mun tashi muna batun zuwa gida maman mu bayan muyi sallah azahar ta dafa muna taliyan hausa da manja munci mun fito sai ga kani na saman keke ya biyo mu.
Nace lafiya ka biyo mu haka yace anty wai kizo wasu mutane suka zo wurin ki a wata irin katuwar mota.
Anty baki gansu ba kamar bature dayan mutumin suna nan sun shiga gida gaida baba shine ummi tace in zo in kiraki.
Na ce ni fa kace shafiu yace wallahi anty don Allah kiyi sauri don da ganin su masu kudi ne baki ga motan da suka zo da ita ba fa.
Gwago tace yi maza ki je tunda an aiko kiranki Allah dai yasa muji alheri dariya nayi kawai sai nace bari mu aje maki sakon su mama anan mi tafi.
Juyawa mukayi zuwa gida tun da muka karyo kwana na hango motan take naji gabana ya fadi nace to waye yazo har nan wuri na ?
Haka dai muka shiga gidan da fargaba ko waye yazo a kofan ummi muka hango takalman su ga awakin ina sun zo suna hawan takalmin nasu mama tana korewa muka shigo.
Wurin mama na nufa ina tambayan ta ko su waye tace haba Safiya ashe abin arziki muka samu baki sanar da kowa ba sai yanzu da bakin ki suka shigo gaida mahaifin ku suke sanar damu.
Na danji kunya nace kai mama ho baga shi kun sani ba yanzu ai sai yace cikin shake muryanta ai baki sani ba tun shigowan su mutumiyar ta shige daki bata fito ba nace wake nan mama.
Tace wa kika sani banda innar ku uwar yan hassada kuwa ake dai bari shiga dakin baban ku kiga abin arzikin da suka zo muna dashi.
Yaya sani ne ya shigo da kwalaben abinsha gidan a cikin leda yana sauri ya nufi dakin ummi dashi nace Allah sarki dan uwa ko ina ya samu kudin da ya karma min bakin dashi oho ?
Ya fito dakin ya ganni yace a, a ashema kin dawo ga baki mun samu daga abuja sin zo wurin ki kin kuma zo nan kin tsaya jin na dawo yasa ummi dake zaune a takure dakin fitowa ta bamu wuri.
Nan na shiga da kunya dakin da sallama na suna zaune saman tabarman da aka shimfida masu hankali kwance ga dan wake a gaban su da akayi gidan suna dan cokala suna ci.
Hamza ne ya amsa min sallama na yana dauko dan wake a kwano yace a a amaryan mu ina kika je bamu baki izzini ba haka.
Dan dariya nayi nace gidan kakata naje don tun da nazo ban je na gaida ita ba sai yau sai kuma akace min nayi baki.
Nan na dan dago kai na kalle shi bai ko dago kai ba sai cin dan wanken shi yakeyi kamar bai san ina wurin ba ma.
Yace dama ai ba ita mukazo gani ba mun dai ga wanda muka zo dubawa gashi har ummin mu ta bamu wanan abincin da na dade ban ciba muna ci.
Nace aiko abu yayi kyau amma sai dai kaci kadan kasan a gidan sarakkai kake yace ina nan ai yanzu nima na zama dan gida baki ganina a kuryan dakin uwana zaune.
Kara shiga dakin nayi yayin da na dan rakube a gefen dan gadon katakon ummi sai hamza ke cewa dashi a gara ki fada mai don naga yana batun mubar kwanon kawai.
Nace yaya hanya suka amsa da lafiya nace amma uncle shine da mukai waya dakai dazun baka fada min kuna haya ba a shirya ma zuwan ku.
Sai yace akwai shirin da yafi wanan ne a gare mu munzo munga mai jiki kima mun gabatar da kan mu an kuma ce ambamu abinda muke so gaya min akwai abinda yafi wanan farin ciki .
Sai ya samay hannushi daga kwanon tare da aje fork din da suke cin danwaken dashi yace naji dadin da ummi tace kin fada mata komai a kaina shi kuma baba ya amince dani albarkacin madam.
So ni yanzu banda wani shaku na neman ki don naga inda kika fito dakuma yan uwanki na kuma yaba da abinda idona ya ganan min.
Karya da rashin asalin shine ba a son a cikin zance naga komai kuma na gamsu da hakan yazu idan na koma munyi waya da madam da mijin ta za a zo a nema min auren ki kamar yadda sharia da alada ya tana da don na fada maki ban son wanan abin ya dauki lokaci mai tsawo .
Ina bukatan azumin bana inyi shi da matata a dakin ta don ban son a sakani cikin gwauraye kuma.
Kaina na kasa duk kunya da nauyi sun cika ni suka ce in kira masu ummi suyi sallama da ita don zasu kama hanya saboda nisa.
Na daga tsam zuwa kiran ummi din na samu tana dakin mama can na samayta na fada mata zasu wuce ta taso sunyi sallama da ita bayan godiya suka aje mata kudi suka mike.
Sai ta bukaci da su je su gaisa dasu mama sukace sun gode nan akai masu iso suka shiga wurin su kowacen su ya aje mata daurin yan dari biyar biyar a gaban ta.
Yaran gidan mu sai binsu suke yi suna kallo wasu na fadin wai batare ne shi saboda farin shi suma uncle bai barsu hakana ba sai da yai masu nasu alherinl.
Mun fito muka samu yaya Sani da driver a waje suna ganin mu suka taso nace yaya sani bakin ka zasu wuce don naga kaine mai ma saukin baki agidan.
Yace ai dole safiya ance min bakin kauna na ai banda zama don murna murmushi nayi don jin abinda ya fada nace yayana nakaina ke nan Allah barmin yayan mu.
Amin sukace muka karasa wurin mota sai shi hamza yace barin dan ga nan baya yaya garin yake ne sai ya wuce ya barmu mu kadai daga ni sai shi su yaya sani sin mara ma hamza baya.
Jin gina mukayi a jikin motar su yace safiya bazan boye maki ba naji dadin yadda iyayyenki suka tare mu sosai kuma mahaifinki na samay shi yadda nake so don ba masu kwadayi bane sai anbasu suke karba.
Yace shi wanan yayan naki yaya kuke dashi ne naga yana da kirki sosai sai dai alamu ya nuna min baiyi karatu mai zurfi ba ko ?
Nace yayana ne kuma mai kula dani sai na dan bashi labarin shi sama sama muna cikin hira ne hamza ya dawo yace kai muje inba son kake mu kwana garin nan ba dare fa yayi yanzu.
Yace ni ba bako bane kaine dai bako yanzu don ni in ta kama a kwana gida nazo hamza ya dan harare shi yace haka zakai min ko Safiya kin dai ji abinda ya fada murmushi nayi kawai.
Zai bani kudi nace a, a wanda ka bani da zanzo ban kashe ba duka sunanan su nake da amfani dasu yace to kara kikuma kashe su din don ki kashe wa yan uwa na baki kagin in godiya.
Ya juya wurin yaya sani sukayi magana da cewa ina fatan idan zata dawo zakai mata rakiya yaya sani ya washe bakin jin dadi yace ko yanzu ta tashi a shirye nake ni.
Sai naji yace ki tabbatar tare zaku dawo dashi don Abuja nake son ya tsaya ba sai ya biki lagos ba.
Nace angode indan kin shirya sai ku sanar dani driver zai zo ya daukeki nace mun gode baiyi magana ba suka shiga mota muna tsaye muna kallon su suka bace muna.
Sai naji wani irin ba dadi a raina nace may nake yi haka ne badai har son sulaiman ya kamani haka bane maganan yaya sani ta katse zuciyana da samo ansa da take so.
Don cewa yayi ikon Allah safiya ina kika samo wanan hadeden mutumin mai karamci diba fa kudin da ya bani bai ko kirga ba ya debo su ya jinka min.
Yaya Nura ne ya iso da sauri yace ina can wurin gina labari ya samay ni wani yazo gidan mu yana rabon kudi har da yan unguwa sun samu.
Yaya sani dake sa kudin shi a aljihu yace anshaka ai har sun tafi ko mukan muji dumus a aljhun mu naga yayi wani iri nace yaya Nura kar ka damu in kadawo sai muga juna.
Muka jera zuwa cikin gida tare inda muka samu suna ta farin ciki da zuwan bako suna ganina mama tace kaga yar albarka yar tohun lada haihuwan ki tankar da dubu .
Murmushi nayi tace Allah bai maka fada kayi hakkurin ki ya zama maki taki a rayuwa don yau mukan mun sheda kuma mun gani.
Dakin mu na shiga inda na samu ummi tayi tagumi zaune tana gani na ta wani nisawa tace sun tafi ko nace eh tace.
Kin ga irin alherin da yazo muna dashi kuwa yar nan ni abin ma na kasa gaskats shi a raina wai yau kece Allah yaiwa wanan budin haka a gidan nan.
Ga inna ku can harda ita wurin yabo ba kunya kamar ba ita ke tujara ba jiya a gidan nan nace kyale ta ummi ni bata gaba na fito mata da tulin kudin da ya bani nace gasu ya bani.
Zaro ido ummi tayi waje tace duka wanan kudin haka kodai sai tai shiru kuma sai ta kara cewa ni abin fa tsoro yake bani.
Nace ummi addua zamuyi don aikin gama ya gama tunda yace baba ya basu baki ko kiran da ake min a waje ne ya katse mu na fito da sauri nabar ummi da kidin a gaban ta.
Ina fitowa akace baba na kirana dakin shi na rude na koma daki na sako hijjab dina zuwa wurin amsa kiran baba din.
Ina shiga dakin baba idona yai tozali da kayan abinci a gefe guda tare nai mamakin yadda suka dauko kaya haka a motar su.
Na shiga da sallama na na samu baba ya dan dago daga kwaciyan dayayi nace baba ya karfin jikin naka ya amsa da lafiya lau safiya sai kuma ga baki mun gani da rana tsaka yau.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , ,
🧕🏿4️⃣2️⃣🧕🏿
YAN UWA MUSULUMAI INA MAKU BARKA DA SALLAH DA FATAN ALLAH YA KARBA MUNA IBADUN MU YASA MUNA CIKIN YANTATTUN SHI ALLAH YA MAI MAITA MUNA WANAN RANAN MAI TARIN ALBAKA A RAYUWAN MU ALLAHU MA AMIN👏
Kai na dukar kasa yake cewa ai da kin sanar damu zuwan su ba sai a san shirin da za ai masu ba yanzu gashi sun zo babu komai sai dan waken da uwar ki tayi aka basu.
Nace baba ai sunci sosai sun gode yace kayya ai ina da yan kaji da su aka yanka masu amma dai na fada mashi wani zuwan ya sanar damu ida zai zo.
Safiya ina kika hadu da wanan mutumin ne bafa karamin mutum bane da ganin sa ma ba sai an fadawa mutum ba.
Na dukar da kai kasa a hankali nace baba kanin mijin maman biyu ne da nake wurin ta a can lagos.
Sai yai dan shiru sai kuma yace yasan da matsalan da kike ciki kuwa don kar ai abu a duhu a cutawa dan mutane rayuwan shi irin da sukai maki.
Kaina a duke kasa nace baba ya sani don shima matsalar mu daya dashi shiyasa anty ta hada ni dashi da sauri yace subbahanallahi.
Yanzu shima yana dauke da wanan lalurar a jikin shi nace baba yana da shi yace subbahanallahi nace shima aure yayi ashe matar nadashi ba su sani ba saida ta shigo aka sani.
Yace waiyazu billahi kai mutane basu da imani a rayuwan su mutum kamar wanan amma an cuce shi an hada shi da may ye sunan ciwon ma nace tsida don ya gane.
Yace Allah ya baku lafiya nace amin baba yana ta jijiga kanshi alaman jimamay a ran shi yace yazo da bukata auren ki nayi duk wasu kwana kwana amma yace ayi hakkuri a bashi ke yasan matsalar ashe abinda yake nufi kenan dama.
To nadai bashi baki yace zaizo da magabatan shi a tsayar da rana don bai son abin yayi nisa sosai don haka zamu iya ganin su kowani lokaci.
Nace to baba yakara dacewa Allah yasa muce gwama da akayi a raina na amsa mai da amin a fili kuma shiru nayi mashi yace
Ai na tambaya aka ce kunje gidan gwago ne nasan fitinar inna kuce yasa ki barin gida kada kije ko ina don ta nan gidan kune gidan ubanki.
Sai dai ita ta fita ta har maki gidan amma bake ba nace a a baba ai inna uwatace don haka inda sabo na saba da fadan ta akaina bani daya kowa ma bata bari ba.
Mun dade da baba muna magana akai sai yaya Nura ya kirani daga dakin baba na amsa baba ke cewa mai yake sone sai nayi dariya kawai nace baba barin ganshi yanzu in dawo yace jeki ma ki huta ai kina da gajiya a jikin ki Allah dai tai maki albarka yasa ku gama da duniya lafiya.
Na amsa amin baba na tashi na fice daga dakin zuwa wurin yaya nura nan na samay shi a dan gaba da kofan baba yana jirana.
Ina fitowa ya miko min hannu yace bani nawa duk gidan a jike suke sai ni da bana nan nace muje daki yaya biyo ni yayi zuwa dakin ummi ya tsaya daga kofa na shiga na dauko mai kudin.
Ina bashi ya washe baki yana cewa sai kin zama matar gwauna da yardan Allah sai mun je shan jar miya gidan ki.
Inna dake duke tana talgin abincin dare na semon da akazo muna dashi ta kasa kannewa da kirarin da yake min tace kuke nan da baku san ciwon kan ku ba kai da dan uwan ka.
Ku baku ko kishin zucin kanku kuyi ma kanku fada ka tsaya kanayiwa mace kirarin da yakamata aima maza.
Yace kai ina haba ai kema kin sa fadi kikayi ina mu ina kama kafan safiya ai ita tariga ta take ko sai dai bi yanzu ko mutum bai so.
Sakarai kawai Allah waddai naka ya lalace mama ta katse da da cewa a a fa ai gaskiya ya fada ke da aka baki baki karba har fa dubu hamsin aka aje maki yau a gidan nan.
Duk zaman ki a rayuwa kin taba rike dubu biyar na kanki na kan ki aiko kamar azuba mata fetur nan ta hau sai da baba ya fito duk da halin da yake ciki har yana sarkewa .
Take nasa masu kuruwa ina cewa dan Allah inna ku bari kada ku kashe muna uba da fitinan ku Saadatu ma ta saka ihu take muka sa mata kuka muna kama baba dake ta tari aiko gida ya rude da kuka yara na cewa wayyo baban mu.
Mutanen waje suka shigo gida ya cika ana tambayan may nene muke cewa babane nan maza suka kama shi zuwa daki .
Inna jikin ta yai sanyi ta koma ta rakube sai ga yaya sani da yaya nura aka ce dasu ga abinda ya faru aiko ya fito yana cewa uwar in kin kashe shi sai ki huta na tabbatar ciwon baba na da halaka dake inna.
Amma ke kulun baki saduda maimakon ki rage sai ma kara baiyana halin ki kike yi nan dai maza suka taru a kanta sukai mata tas suka fice daga gidan.
Muka taru a dakin baba kowa yayi jugun jugun baba yace idan inna ta kara kulani a gidan nan sai ya saketa.
Wanan fitinan shi yasa inna laushi sosai ta koma shiru shiru a gidan kowa ya fita batun ta bayan kwana biyu na samu saadatu a dakin su.
Tana gani na ta zauna nace ya kamata ki rage wanan zaman haka kidan rika motsa jikin ki zai fi kullun kina daki kumshe murmushi kawai tai min.
Na miko mata kudi ta karba tana cewa na may ye nace ki rike a wurin ki ki dan sai kayan baby da abin bukatan ki.
Ta fara hawaye tace Safiya halin ki na alheri ne a gare mu ko yaushe abin ki bai taba rufe maki ido ba wanan kaddaran da ya samay ni nayi kuka a zuciya na nayi a fili.
Da kina nan da haka bai samay ni ba don kudin mai man gyadan da nake daukowa a wurin shi in na sayar in kai mashi kudi sai kudin ya kare a kaina.
Kin san kudi in ana tabasu ba a kari yadda suke sai kudin ya rushe a hannu na shi kuma ya matsa min shine daga baya daya ga banda kudin ya nemi da in bashi hadin kai sai ya yafe min kudin.
Shine na diga zuwa yana amfani dani ya mayar dani kamar wata matar shi sai da cikin nan ya samu ne ya guje gare ni tare da fadin shi ba zai karbi cikin ba.
Safiya nasan inda ki na nan haka ba zai samay ni ba don zaki san hanyan da muka biya shi kudin shi ita kuma inna uwace a baki bata damu da damuwar yar ta ba.
Sai dai in kawo mata tayi bushasha shine da ya daina bani ki ka ga muna yawan samun matsalan nan da ita.
Na share hawayen da ke fuskana nace kiyi hakkuri kin san duk mai rai nada nashi kaddara a rayuwan shi.
Na fito ina hawaye dakin ranan na kasa barci ina tunanen matsalan saadatu ina neman mafita a kai.
Karshe dai na samu hanya mafi sauki na da haka na kwanta washe gari muka tashi kamar kullun a gidan kowa na ta har kokin gaban shi.
Na fita waje acan daban su yaya Sani na samay shi nan na kirashi shi da amin shi na kut da kut na kirasu gefe muka kebe dasu.
Nan na fara jero masu bukata na suna saurare na karshe dai yaya Sani ya nuna baruwan shi ga maganan sai da abokin ya kwantar mashi da hankali ya yarda.
Akan zasu je su samu mutumin nan da yai mata ciki aji hadin ta dashi sai dai zasu biya wirin kanin mahaifin mu don a samu wani babba ya tsaya muna ga maganan.
Sun yarda da hakan na shiga gida suka wuce wurin dan uwan baba sun mai bayani sai yace wanan maganan fa maganan kudi ne.
Abokin yaya sani yace adai tun kare shi aji don aiwa abinda zata haifa din gata baba baiki ta nasu ba ya tashi suka samay shi a shagon shi na kasuwa ya na tsaka da kasuwancin shi.
Sun kira shigefe da suka fito mai da maganan sai cewa yayi shi sam bai san maganan ba suka ce to za a zauna gaban hukuma.
Sai cewa yayi aje mana abu na kudi haka suka dawo da labari babu dadi daga gare su bayan sun gama magana nace haka yace suka ce eh.
Nace a hadu din babu komai nasan dai dan kudin da suke hannuna suna isana kashe maganan kauye.
Don haka washe gari muka maka shi kotu tare da ganin mai shari a saadatun tai mashi bayanin komai da zamu tafi na kawo hamsi na bashi nace ga goro.
Haba abin nema ya samu aiko take ya aika yana neman shi washe gari za a zauna kotu bai ji wani tsoro ba don yasan dubu ashirin na raba su da alkali.
Ya rigamu isa kotun don yaga alkali nan ya cin na mai dubu ashirin din ya karbe da farko sulhu ya kiramu yi don dani aka je amma nace ban san hakaba nan na dan turza har ina cewa idan sharian baiyi anan zamu tafi abuja.
Kajini fa sai alkalin ya rude nace idan mun tafi can ai akwai awon da za a yi a tabbatar idan na shi ne koba nashi ba.
Sai ga Isah mai mangyada na share gumi a fuskan shi yana cewa ai maganan bai kai can ba ciki dai nawane amma kuma ai ba wurina kadai take zuwa ba.
Saadatu tai saurin rantsewa akan bata taba zuwa wurin wani ba in ba shi ba nace tun da bai yarda ba abari kawai aje birni a hadu a can .
Daga alkali har mutumin suka fara cewa haba ki kwantar da hankali abi maganan sannu a hankali a fahinci juna.
Kowan su na gudun zuwa gaba don ba zasu ji dadi ba sai suka ce mu fito waje suyi shara muka fito wajen muka basu wuri.
Kiran abikin yaya Sani sukayi suna tambayan shi wai yanzu may na zama ne sun ga na waye da yawa idona ya bude sai yace masu kai yanzu fa ta wuce sanin ku.
Don wani hamshaki daga Abuja ne yazo neman auren ta sukace gaskiya kan na ganta haka idon ta ya bude da yawa.
Sun fito suka kiramu ankan ya yarda zai karbi cikin nace ita fa to sai ya fara shafan gumi alkali dai ya tillasta mai akan idan ta haihu za a daura masu aure.
Muka samu madafa akan ta sai da naji ta sauke wani ajiyan zuciya don a kusa da ita muke da muka fito yana yi min magana ban tsaya ba.
Muka dawo gida sai da dare na muka samu baba ni da yaya Sani mukai mashi bayani halin da ake ciki kan Saadatu din.
Bai iya magana ba sai hawayen da yake yi kawai muna bashi hakkuri har ya daina mun fita ne ya kira su mama gaba dayan su yana masu bayani abinda muka zo mashi dashi.
Nan inna ta tsaya tai tagumi ta rasa abinda zata ce sai kuka aka bata hakkuri haka dai suka watse ni har na kwanta sai ga inna dakin mu.
Ina ganin ta na mike zaune don ban san da may tazo ba wuri ta samu takai zaune sannan ta soma maga Safiya wurin ki nazo nace to inna gabana yana faduwa.
Ban san abinda zance maki ba ga kokarin da kikayi ga yar uwar ki indan bake ba da haka zama zauna da wanan bakin cikin a rayuwan mu.
Don Allah kuyi ta hakkuri damu karkubi ta namu kishin mu ba karewa zaiyi ba sai ranan da muka kare nai murmushi nace inna kudai yi hakkuri da junan ku.
Ummina tana zaune batace muna komai ba har inna ta fita tace munafuka kamar da gaske nayau ne kawai baikai ciki ba don bata san kuya ba har zatazo wai wani godiya.
Nace kai ummi baku dai barin halin ku wanda kukeyi a kan shi ma yana fama da kan shi bai son fitina wallahi.
Ummi tace tadai bari ita da ta dauki duniya da fadi yar bakin cikin mata kawai na kwanta ina mata dariya nace kishin ku dai bai karewa.
Kwana goma na kara jikin baba yayi sauki sosai na fara shirin komawa don kullun su yan biyu waya suke suna tambaya na yaushe zan dawo sai ince masu gobe.
Damuwan da sukeyi yasa nace zan koma nan muka fara shirin tsaraba abin da nasan suna so shi muka saya zan je masu dashi tsaraba.
Sai da na shirya na sa ranan tafiya mu nan yaya sani ya zake dama yana damuna yaushe zamu tafi sai gashi nace mai ranan asabar mai zuwa zamu wuce.
Ranan ina zaune na dawo sallaman uwayena ta famnin ummi na ina cire kayan jikina dana sa waya na yai kara ina dauka naga yaya Saadune.
Da murna na na dauki wayan nan na zauna a bakin gadon ummi nace yaya ina kashiga nayi kiran wayan ka yafi a kirga baka dauka ba.
Yace kedai bari wasa wasa nayi tafiya zuwa ghana sai gani har togo shiyasa ba a samu na ko an kirani.
Nai mashi sannu da zuwa yake ce min yanzu ma yazo ne matar shi zata haihu shine yadawo gida yace kin san halin gwagon ki.
Idan bani nan ba komai zasu yi ba shiyasa na dawo gida don ayi komai a gabana nace Yaya ashe zamu samu karuwa kwanan nan.
Nace idan na dawo lagos zan zo inda kuke yace zakizo lagos ne nace ai yayanan nake yanzu.
Yanzuma nazo gidanane baba baida lafiya shine nazo amma ya samu lafiya yace subbahanallahi may ya samu baban ?
Nace ya samu sauki ai amma yaji jiki sosai wallahi amma yanzu yana samun lafiya yace a gaida mashi baba insha Allahu zai shigo kafin ya koma.
Yace yaya labari safiya ina fatan komai na tafiya daidai ko nayi murmushi nace yaya komai lafiya sai dai mun hadu kawai yace akwai labari kenan ?
Dariya nayi nace ya gaida matar shi yace zataji zan fada mata kin ce zaki zo nace insha Allahu zan zo.
Mukai sallama na kashe wayan ina jin dadi a raina na yaushe rabo ina fada ma ummi ya na gaishe su wai matar shi nada ciki zata haihu.
Addu a tai masu ta na Allah ya raba lafiya nace amin muka dan taba hira da ummi akan matsalolin duniya na gidan mu dana waje.
Sai ranan jumma a inna tasan da tafiyan mu duk ta rude sai ta kira yayan a daki tana ce mashi yanzu kai don kasada binta zakayi baka san mutum ba baka san sanaar shi ba.
Baka gudun aje a yanke ma kai ko a sayar dakai kaida ganin wanan mutumin kasan kudin shi ba na kai sake bane kuma gashi yaro ina zai samo kudi irin haka ?
Da sauri ya katse uwar da cewa ke inna zaki fara ko zaki fara halin ki yanzu duk halarcin da yarinyan nan tai maki baki gani ba zaki nemi wani sheri ki lakaka mata.
To ki iya bakin kin ki kada ki je ki zauna da wani kiyishi ya fita muji kunya yarinya na bin mu da arziki ke kina binta da sheri Saadatu dake zaune tace fada mata dai ko zata ji .
Yace nidai zan bita ki min addua Allah yasa karshen zaman banza ne yazo in samu abin yi acan in dawo maki da arziki sai lokacin tace to Allah ya sa hakan ne kadai kula da kan ka don Allah.
Ya fito nikan shiri nakeyi na zabi kaya cikin wanda nazo dashi naba Saadatu na raraba masu kayana wanda naje lagos dashi don yanzu ban iya sa su naba mutanen gidan mu.
Da dare driver ya iso don sammako zamuyi tun da safe zamu bar garin ranan mun raba dare da ummi muna hira sai wani lokaci muka kwanta tun da safe muka kama haya nabar su da kewan mu muma muna kewan rabuwa dasu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , ,
🧕🏿4️⃣3️⃣🧕🏿
YAN UWA BARKAN MU DA SALLAH DA FATAN MUN WUNI LAFIYA YAYA AIKI YAYA SHAN KAMSHI ALLAH YA MAIMAITA MUNA AMIN.
Mun yi nisa ga tafiya yaya Sani da driver nata hira ina naya ina karatu a wayana har muka kai wani gari driver yace zai tsaya yasai ma iyalin shi abu.
Suka fita suka barni a cikin motan nan na dago kaina ina kalle kallen garin mutane nata hada hadan su.
Nace a raina kowa yanzu wirin nan da abinda ke damun zuciyar shi atake na tuno a yadda na bar gidan mu don dai na tabbatar da inna kiran da taiwa yaya Sani jiya da dare magana ce a kaina.
Hango su nayi sun riko ledoji ga abin saya inkai tsaraba babu hali don nasan jirgi zanbi in koma kamar yadda nazo.
Suka dawo suka shiga mota muka fara hanya sai lokacin nace wa yaya Sani mutanen gida dai na tuna.
Yace ai baba ya samu lafiya yanzu baki ga har kofan gida ya rakomu ba nasan tunda yace afito mai da tabarma anan zai zauna.
Nace ni ban san lokacin da rikicin gidan mu zai kare ba kullun ace sai makwabbata sun shigo rabon fada a gidan mu.
Yace ai ba laifin kowa bane sai inna kin ga ana shigowa raba mama da ummi fada inma har matsala ya afku a tsakani su ba mai tsawo bane kowa ya bari.
Amma ita inna da kowa tana yi a gida har baba har yaran gida kin ma san abinda ta fada min ne jiya kan tafiyan nan namu ?
Sai nace inna dai nidai Allah yasa su bari yace to amin amma da wuya su bari din don ko kowa ya bari na tabbatar inna ba zata bari ba.
Sai dai yadda kuke hakkuri kuna take halinta kucigaba dayi har Allah ya kawo muna dauki ajiyan zuciya nayi nace Allah ya kyau ta.
Karfe biyu saura muka shiga Abuja nan yaya ya dinga baza ido wurin kallo nima din ba a barni a baya ba don kallon abin mamaki da aljabi nakeyi don garin yadda yake komai a tsare.
Direct gidan Sulaiman muka nufa don daddy ya koma lagos ko tun satin da mukazo dashi sulaiman din ne ya fito ciki bayan mun shiga mun zauna a wani irin yanayi.
Da ganin sa baijin dadin jikin shi sai dai yana dauriya irin na maza cikin karfin hali yana muna sannu da hanya.
Mun gaida shi a cikin ladabi da biyayya ya samu wuri shima ya zauna yana kara yiwa yaya sani yaya hanya yaya sani daketa washe baki ya amsa da lafiya.
Ya tambayi jikin baba muka amsa mai da sauki sosai tun wanan maganan naja bakina nai shiru suke hira sama sama yayin da mai aikin shi ke ta faman jera abinci wanda nasan don zuwan mu aka girka shi.
Driven da muka zo dashi ne yashigo falon yake gaishe shi ya amsa mai cikin dakiya irin na masu gida da yaran su yake tambayan shi yaya hanya ?
Ya amsa mai Alhamdullahi ya mike zai fice sai sulaiman din yace kada kai nisa don four zaka kai madam airport zata tafi lagos yau.
Sai lokacin na sauke ajiyan zuciya na dan dago na saci kallon shi ban san shima kallon nawa yake yi ba sai ya dan murmusa yace ga abinci can an shirya maku bissimillah ko.
Dagani har yaya Sani ba wanda yake da alaman motsawa sai naji yace barin dan fita na baku wuri kunji dadin sakewa sai dai ba dadewa zanyi ba zan dawo.
Ya mike ya fita ya barmu nan sai lokacin na dago na kalli yaya sani nace yaya kaci abinci gashi can saman table anjera.
Ya juyo yace kefa nace a a yaya ban jin cin komai yace may kikaci tun fa karin safe da mukayi gida ne a cikin ki nace yaya ban iya ci ne gaskiya.
Mikewa nayi shima ya tashi ya bini zama nayi ina nuna mai yadda zaici koma duk ya rude yaga abinci kamar a banza.
Ya sake jiki yaci sosai ina kara fada mai ya rike amana da gaskiya don zai yuyu gwada ka zai yi ya ga halin ka yace .
Safiya kada kiji komai akaina insha Allahu zaki samay ni kamar yadda kike son in kasance nace nagode yaya.
Yace safiya aini keda godiya ina na taba tunanen zan zo irin wanan wirin a rayuwana gashi ta dalilin ki Allah ya kawo ni.
Yace wanan mutumin waliyi ne Safiya akwai mutunci a gare sai dai muyi fatan Allah ya sanya Alheri ga alamarin.
Kamar yadda yace ba zai dade ba haka din ne kuwa ya shigo muna da sallaman shi mukai mai sanu da dawowa yaji dadi har cikin ranshi.
Ya nasa a zuciyar shi dama ace nazo kenan ba tafiya zan yi ba don yau da ya samu masu mashi sannu da zuwa agidan shi har yaji daban.
Ya samu wuri ya zauna yana cewa i hope kunci abinci sai nace mun ci yake cewa good yaya ne yace a a Safiya nayi da ita taci bataci komai ba.
Yace a wani irin cool voice why Safiya ko kina ganin zan cuta makine da bazaki ci abincin gida na ba ba fa anan aka girka ba odan shi nasa akai maku don gidana gidan gwauro ne.
Nace ba hakana bane na koshine yaya Sani yace haka take bata son cin abinci ko a gida sai yace a a baki ko kyauta min ba.
Why kike wasa da cin abinci bayan kin san halin da muke ciki don Allah ki bar wasa da cin abinci please ?
A sanyaye nace mashi tau yace good sai yayi dan shiru can ya nisa yace zaki barmin yaya Sani anan idan mun gama abinda ya kawo shi zai koma gida.
Nace an gode yada dan harare ni ya ce ban so na fada maki ko yanzu nima basu zama yan uwa na bane ?
Nace ban ce ba.
Yace barin dan shiga na fito sai ki shirya nan ya mike ya shige ya barmu a falon yaya sani ya bishi da kallo sai ya juyo ya dube ni.
Yace Safiya kin dace kin samu miji dai dai da halinki murmushi nayi nace Allah yasa yaya don ni yanzu tsoron auren nake yi don ban san halin da zan tarar ba saboda auren Ahmed ya sani tsoron maza.
Kibar wanan maganan don Allah auren Ahmed ai auren kaddarane ga kowan mu kibar tunawa don Allah.
Kuka na fara yaya sani na bani hakkuri yana cewa ki bar kuka don Allah kada mutumin nan ya fito ya samu kina kuka bamu da abinda zamu fada mai.
Jin haka yasa na dakatar da kukan nawa nace yaya dole in kuka don in ina tuna wanan auren sai inji dama mutuwa nayi.
Yace subbahanallahi safiya kibar wanan magana don Allah hakkuri zakiyi mana gashi ubangiji na son ya musaya maki da alherin sa cikin hikima irin ta ubangiji.
Kan shi ya cuta idan yayi maki ne don ki wulakanta suka ci amanar ki Allah ya tausaya maki yaba ki wanda ya fishi ta ko ina.
Shiru kowan mu yayi zuciyar mu tana tunane kala daban daban sai ji mukayi ya fito daga dakin haka yasa mu natsuwa .
Sallah yace muyi kanfin na wuce suka fita da yaya sani zuwa yin nasu sallahn suka barni nan zaune
Da yake ba sallah zanyi ba nan na zauna naci gaba da damuwa a raina ina mai jin ba dadi a zuciya ta tare da bin gidan da kallo.
Sai gashi ya dawo nan yake cewa na shirya nace eh yace na tashi mu tafi kai yadan dafe nace sannu sai ya sake yai murmushi.
Nace kamar baka da lafiya ko kallona yayi yana girgiza kai yace yaya akayi kika sani ?
Nima murmushin nai mashi nace tun shigowan mu naga hakan a tare da kai ban dai yi magana bane kawai.
Yace don baki damu dani ba komay ?
Nace bagashi na maka sannu ba yanzu?
Yace yana kokarin tashi wallahi jikin nawa ne yadan motsa min kwana biyun nan kuma laifina ne nai tafiya ban dauki magani na ba.
Nace haba dai may yasa kai ko ?
Yace da rabon insha wahala haka ne.
Yace tashi muje kada lokacin ya wuce muna nan yau na shiga uku da madam don na fada mata azo airport a dauke ki.
Mikewa nayi yana gaba ina binshi baya zuwa wurin da mota ya ke kafin mu karasa inda su ke yace kayan na nan sutura naki ne sai tsaraban mutanen gida kuma sai na zo idan naji sauki.
Nago, , , ban saki kimin godiya ba kaina nayiwa don yanzu hakkina ne na baki duk wani kula da kike so numfashi na sauke.
Don ya hanani magana ina isowa driver ya bude min mota muka na shiga shima ya shiga yaya Sani da driver a gaba.
Ko da muka isa ban dauki lokaci ba jirgin mu ya daga sai lagos shida da rabi muka sauka inda naga anty ce da kanta tazo dauka na sai faiza.
Da murna suka tare ni bayan an dauko kaya na muka muka nufi gida yaran basu gida sun fita da daddy sai fati ce kadai a kida.
Itama ba laifi ta tareni ba yabo ba fallasa don tun da tace in andawo bata sake fadin komai ba kamar bata san jiyan mahaifina naje ba.
Ban shiga da kayana ba na ware wanda nazo masu dashi da wanda ya bayar a kawo masu murna ta shigayi tana cewa .
Safiya keda kika je jiyan kika tsaya muna tsaraba haka mai yawa ta bude naman da aka soya na zabbi wanda kaunan mama ta soya muna shi yaji hadi ta fara ci.
Tace kai Safiya mai wanan naman idan da agarin yake ai kullun ina shagon shi ke kinji nama zau da dadi ta bude kayan miya taita murna ganin na hado masu kayan miya na garkajiya ta shiga yabawa kamar nakawo masu wani daula.
Tasa funke ta kwashe kayan zuwa kitchen don su faiza sun far ma naman da ci tace su bari hakana sai ta dibawa daddy na shi.
A dakina muna like da su yan biyu da suka mane min sai hira suke so in masu na kauyen mu, suna son hiran kauye sosai sai faman tambaya na suke yi ina basu amsa sai da daddy ya dawo ya kirasu.
Na fito cikin dogon riga sai hijjab dana saka a sama yar karama don bani zuwa gaida daddy hakana sai dai idan ya girshe ni a gidan ba hijjab a jikina kuma idan ya samay ni hakana bani iya sakewa dashi.
Yana gani na ya na cin naman dana zo kasu dashi anty na gefen shi zaune itama naman take ci yace a a amarya andawo.
Kunya ya kamani na soke kaina nace daddy mun samay ku lafiya yace lafiya Safiya yaya baban naki da jikin ?
Nace yaji sauki yace a gaishe ku ai mashi godiya a wurin ku sai yace ai ba komai Allah dai yaba shi lafiya.
Nace amin tare da mikewa daga tsugunnin da nayi har na juya zan wuce sai naji yace ashe sulaiman ya samu zuwa garin naku ?
Na juyo tare da dan dukar da kaina kasa saboda kunya ya sake cewa yanzu sai batun aure don bana son a dauki wani dogon lokaci ba a yi ba .
Bandai yi magana ba na juya na wuce zuwa dakina inda ma na rufo dakin don ina son in duba kayan da ya sawo min shake a troler.
Sai da nagama komai na jawo akwatin na buda idona ya fara tozali da wasu irin dogoyen riguna masu kyau da daukan ido .
Guda guda nake fitar wa saida na fitar da kala bakwai sai kuma wasu lace da aka dinka su kamar an gwadani guda ukku suma.
Ya tashi kala goma ko wani da gyalen shi da takalman shi ido na runtse tare da sauke ajiyan zuciya nace a fili Allaj miskara ziratin .
Yau ni safiya keda wanan kayan da sai a film ko a jikin wata data kai, nake ganin su yau ni safiya gani dasu a matsayin nawa ga wa yanda ya saya min kafin in tafi gida.
Na hada suka tashi sha biyar kenan nace wanan wani irin mutum ne da baya jin kyashin kashe kudin shi haka sai naji ina son kiran shi a wanan lokacin in dada mashi godiya.
Waya na mike na dauko bayan na mayar da kayan na kirashi ringing uku ya dauka yanayin shi kamar na mai barci.
Yaya jikin na yimashi yace yaji sauki yace kin sauka lafiya kin samay su lafiya ko ?
Nace suna lafiya sai dan shiru sai naji yayi murmushi nace dama dai na bugo inji yaya jikin naka yace ashe andamu dani ke nan da har za a kirani.
Murmushi nayi kamar yana gabana sai nace yallabai kuma wani hidima akaimin haka yace yes kin san yanzu matar sulaiman kike dole ne nayi maki ko kina son a ganni cikin sutura ne ke kuma azo a ganki haka ?
Nace to na gode kwarai sai naji ya kashe wayan murmushi nayi nace har kullun idan kai min alheri baki bazai gaji dama godiya ba don kacancanci hakan.
Gidan Ahmed dana zauna har nabar gidan ko kyale bai hada ni dashi ba banda tsaraban kanjamau dana samu koma wani hali yake yanzu oho ?
Muna gama wayan dashi ya tuna da cctv din da ke gidan ya jawo ya hada ya fara kallon barin mu gidan da yayi da yaya sani.
Don yaga fuskana na sai ko ya fara ganin badakal da muka yi da yaya din tun fitar shi har shigowan shi da shiga dakin shi da yayi ya bar mu.
Lumshe ido yayi yana jin wani iri a ranshi yanayin da yaji a lokacin da haka ya samay shi har yakwanta ciwo don bakin ciki gani yake a lokacin kamar zai mutu ne a take.
Kamar ba zai yi wanan rayuwan da yake yi ba yanzu har da fadawa vikin soyayyan yarinya karama da yake jin shaukin ta akoda yaushe.
Lumshe idon shi yayi yana jin wani irin yanayi a zuciyar shi a haka barci ya dauke shi da tunane barkatai a zuciyar shi.
Washe gari da ya tashi sallah yayi bai kara kwantawa ba yayi abinda zai yi ya fito yaya Sani ma ya fito yana falo zaune shi kadai.
Yana ganin ya fito yake ce mai ina kwana yaya ce yaya sani ashe ka tashi ya gaida yaya sani din nan suka zauna suna dan hira a kaina a wurin yaya sanin ne yaji labarina tsab ba ragi ko kari.
Yace in sha Allahu karku ji komai a kaina zaku samay ni da yiwa yar wanka a dalci sai dai idan wani abu ya fito daga gare ta.
Yaya Sani yaji dadi sosai har ya kasa boye farin cikin shi sun karya yace zai fita sai ya dawo akwai maganan da zasu yi da yaya sani din.
Ya kara da cewa idan yana son fita ya zaga gari yayi magana sai a fita dashi driver yana nan waje
Kwarai yaya sani yake jin dadin zama garin ko ba komai yaci mai kyau yasha mai kyau idan zai fita ga mota nan a fita dashi yana kallon gari
Gashi har yau sulaiman bai samu zama ba balle suyi maganan da yace zasuyi dashi shi kuma yana cikin fargaba don bai san maganan da zai mashi ba.
Ko yaushe muna waya da yaya sani din yana fada min daular da yake ciki a gidan na sulaiman din
Nakan yi mashi dari idan yace Safiya kin ko ga yadda na koma wani dan birni dani sati gudan man danayi a gidan ku.
Nakan ce kai yaya wai gidan gidan mu yana can kauye gidan sulaiman din dai sai yace gidan ku mana aini inna nake son tazo taga irin gidan da Allah ya nufa zaki zauna aciki.
Muga yadda zata yi ranan nasan bata da bakin magana nasha gayawa inna tun kina yarinya akan ta daina irin abinda take gwada maki don bata san abin da Allah zai mayar dake ba wata rana.
Amma sai inna tace min wai ni yaro ne bani sani komai ai yadda uwar ki take yar kauye basu da komai kuma diyan ta haka zaku taso baku da komai.
Yanzu gashi Allah ya gada masu shike da komai yayi ikon shi a kan ki wanda nasan har duniya ya nade gidan mu babu mai cin maki a ratuwan duniya.
Nace kai yaya banda sheri dai don kaga inna bata nan kai mata kaza fi yace safiya ke baki ganewa ne inna fa sam bata son kowa a gidan mu in ba mi diyan ta ba ni kuma wanan halin nata yana damu na sosai a raina.
Nakan yi mashi nasiha akan ya tuna fa inna uwa ce a gare shi sai yace ya sani shi dai halinta ne baya so sai nace sai hakkuri da iyayye yaya.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGO, , , , , ,
🧕🏿4️⃣4️⃣🧕🏿
DA FATAN ANYI SALLAH LAFIYA ALLAH YA MAIMAITA MUNA NA BADIN BADADADA YA BAMU CIKAWA DA IMANI A ZUCIYAR MU, , , ,
Sai bayan kwana takwas ya samu zama da yaya sani din bayan sun gaisa dashi ne yake cewa yaya sani dama maganan da zamuyi akan yadda za a gyara gidan nan naku ne kafin daurin auren mu.
Yaya Sani ya dago ya kalleshi da sauri yace kana nufin gidan baban mu ko ina yace cikin gyada kai eh nan nake nufi a gyara .
Ya ce dashi dakuna nawa ne a gidan ya fada mashi yadda tsarin ginan gidan mu yake sai yace ba a samun fili daga waje sai a kara yawan fadin filin gidan.
Yaya Sani yace daga gaban mu har bayan mu filin babane wanda yake shuka masara da damana a cikin su don haka akwai fili sosai daga bayan.
Yace abu yazo ka da sauki nan ya fitar da plan din yadda yake so a yi ginan gidan namu nan yace gobe in Allah ya kaimu nake son ka tafi amma kuma idan akwai fili a kusa daku kadan ina so don akwai abinda zanyi dashi.
Yaya sani ya rasa abinda zai ce mai sai ya kama kuka kawai don bama zai iya bude baki shi ya yi mashi godiya ba.
Ranan haka ya wuni suku suku yana tunanen wai gidan su ne za a mayar kamar na yan birni a garin mu gidan bulo da bulo wanda sai wani da wani suke ginan bulo da bulo zalla.
Gaskiya Safiya ta kasance alheri a cikin mu dan ta zama muna hasken rayuwa shi ko ma a haka aka tsaya ai ta wadatar dashi don ya samu karuwa.
Washe gari tunda safe ya gama shirya mai komai na tafiya yaya sani ya fara hanya shi wanda zai mayar dashi gida.
Sai yamma suka isa don sun tsaya hanya sun sai doya da su majan da sauran tsaraban Abuja suka kama hanya.
Mutane na zaune sunyi daba kamar yadda yanzu maza suka koyi yi a ko wani gari gungu gungu ya shigo garin sai budawa yake yi shi a dole ga dan birni ya dawo.
An bi motar da kallo har ya tsaya a kofan gidan mu abokan shi na ganin ya fito suka dauki ihu shiko sai faman washe baki yana mika masu hannu .
Da kyat ya samu ya shiga gida bayan an gama kwashe mashi kaya daga cikin mota zuwa cikin gida.
Yara na shiga gidan da kayan sai suka nufi kofan ummina da shi kamar yadda ya fada masu sai inna tace maza su kawo kayan a kofan dakin ta.
Yana shigowa ana mashi sannu da zuwa bai ko amsa ba ya hango an tara tulin doya kofan inna yace kai amma yaran jan nan suka zube kayan nan kuma bayan na fada masu inna zasu kaiwa.
Inna tafito da sauri daga dakin ta tace kamar yaya akai kofan Rabi kuma ba kai kazo da kayan ba ?
Yace kayan ummi ne don ita surikin ta yace a kawo wa don haka ku kwasa ku mayar don Allah yace ma yaran dake shirin fita daga gidan.
Bayan an gama kawarwa sai da ya tabbatar sun kwashe komai ya kara yana cewa mama, mama ga mutan Abuja sun dawo fa.
Mama tace ai naga kashigo kana ta sababi da yaran ta fada a fakaice yace wallahi fa ga inda akace sukai abu sun kwasa sun kai wurin da bashi ba.
Inna tace muma Allah ya bamu ba sai anbamu ba ta diya har ana daga muna kai a cikin gida yaya sani ya kada kai yace inna ke nan.
Kin ko san gidan da Allah yakai Safiya kuwa inna da kike fadin wanan magana haka gida ne fa gidan bene sai inna din ta katse shi tace rufa mana baki sakarai kadawo kenan da katobaran ka kamar , , ,
Tau tau baba ya fada may akai wa cirko cirko haka kuma ya fada daidai yana shigowa gidan da leda baka a hannun shi.
Mama tace umm umm mutan Abuja ne suka iso muke shan labari yace to kai haka akeyi kazo da mutum sai ka barshi a waje kuma ?
Sai lokacin ya tuna da yabar driver a waje baiko kai mashi ruwan sha ba sai inna tace ya kai kai ruwa yaya nan yana fadi ba a tambayeka ba.
Mama tace ai abinda ya gani yake fadi magana ne yakawo magana har yake fada muna yaya Sani ya fita daga gidan yana aiken yaro ya sawo mai ruwan pure water.
Bai shigo ba yana can yana nema wa bakon shi wurin kwana don haka bai samu zama su gaisa da mutanen gida ba ranan.
Sai washe gari tun da safe inna ta samu baba a dakin shi wai yaya sani yazo da tsaraba inna takama tasa shiyan ta.
Bata raba ba yace anya Rabi zatai haka kuwa a gidan nan amma barin kira ta inji dalilin ta nayin haka din ?
Da bi ar bane in magana ya kama ya kirasu dukan su don haka har da mama aka kira suka zo bayan sun zauna yace da ummi na.
Rabi yaya akayi kuma sani ya dawo da tsaraba kin kwashe kin tura dakin ki ko dan tsaraban ya fito daga gefen diyar ki ne kikai haka don yanzu Rakiya ta samay ni da maganan .
Salati ummina ta saka tace ni malam da dare fa Sani yazo da kayan kuma tun fitan shi bai dawo gidan ga ba balle inji yaya kayan suke ya dai ce ma yaya akai kayan kofana .
Sai mama ta tara tace kai ba haka zancen yake ba da yara suka shigo da kayan ita Rakiya tace su kawo kofan ta.
Sani na shigowa yace su kwashe sukai kofan Rabi surukinta ne yace a kawo shine ma ka shigo ka samay mu muna maganan dashi jiya.
Ko da dare Rabin ta samay ni da zancen kayan nace tabari har Sanin ya shigo muji yaya kayan suke sai kuma nace ta kwashe tasa daga cikin dakin ta don sata kuma da dabbobi.
Ya juya ga inna yana ce mata kinji dama na fada maki tun farko Rabi bata yin haka ke gajin hakkuri gareki Rakiya.
Ta mike zabban kuya tana cewa in ba a bayarwa ne a barshi mana doya ne mutum bai taba ci ko manja tana kokarin fita yaya Sani yana shigowa gida neman kulan da zai ba bokon shi abin karyawa a ciki.
Ummi ya nufa yana kiranta yace ummi don Allah bani kula zan sai ma boko na abin karyawa ta mike a kasalance tana cewa dashi ai nasa an mashi abin karyawa ko.
Yace da kyau ummi ashe barince mai abincin ta wuce din har na tsayar da ita baba da yaji muryan shi yace kai sani kai ka dawo baka zauna da mutane ba.
Yace baba ina zuwa akwai labari mai dadi yau a gidan nan barin ba bako abin karyawa jin haka da inna yayi sai ta shiga daki ta aika yaro ya kira yaya sani.
An samay bai ko tsaya sauraren yaron ba ya korashi ran inna yakara baci sosai dashi ta cika fam tana jiran shigowan shi gidan.
Don taso ta jamai kunne akan in alheri ya samo da kada ya fada kowa yaji a gidan subar zancen a yi su dakin su ba sai kowa yaji ba sai ga yaya sani din yaki shigowa.
Sai da ya gama da bakon ya samu shigo dakin baba ya nufa direct nan ya samu baba yana shirin fita kasuwa don yakan dan leka saboda sabo kasuwan.
Yace baba mun samay ku lafiya yaya jikin naka baba ya amsa mai da Alhamdulillahi baba yace yaya kabar su can ya gyara zama yace lafiya .
Ai ita Safiya tun ranan da muka rabu nan ta hau jirgi ta wuce lagos daka can bata kwana abujan ba don ba mace a gidan.
Baba yaji dadi yace dakyau dama tunanen da ya tsaya min acikin raina ke nan yaya yace ai baba sai kaga gidan da aka gina ma Safiya.
Wai ita zata zauna a ciki da mijin ta baba mutumin nan ba karamin mai kudi bane ko a abujan don gidan kawai zai nuna wa mutum haka a zahiri.
Baba albishirin ka yace goro sani don naga a rude kake yace ai dole ne baba kaga zuwan nan da nayi baba ya amsa mai da eh sani.
Yace baba nazo ne da shirin rushe gidan nan gaba daya a gina ma wani.
Baba yace kai sani a cikin hankalin ka kake kuwa koko dai ?
Yace wallahi baba abinda ya kawo ni ke nan yanzu yau din nan zamu je birni muzo da masu aikin da zasuyi ginan don yace bai so ya wuce wata daya ba a gama komai ba.
Ido baba ya zaro yace Allahu Akbar wai sani da gaske kake yi ko kowa wasa yace wallahi baba da gaske nake yi abin da ya kawo ni ke nan yanzu haka.
Su mama ya kwala ma kira yana fadin kuzo kuji ikon Allah da sani yazo muna dashi gidan nan.
Da yara da manya suka nufo dakin baba nan yace yaya sani ya kara maimaita abin da ya fada mashi ya mayar masu.
Gida ya dauki ihu mama tace haihuwa tai ranan ta safiya kin kai diya Rabi kin iya haihuwa tankar da dubu.
Mama na guda ummi ko ko bakin magana bata samu ba inna tace a dai yi sannu kar aje a debo muna wahala muna zaune zaman mu.
Don yan birni babu abinda basu iyawa sai ta tashi ta fita daga dakin tana maganganu tana fadin ba inda zan daga ni.
Tana fita ummi na ta nisa tare da fadin anya malam ba a bin abinga sannu ayi binciken wani irin miji yarinyar ta kwaso muna kada idon mu ya rufe.
Yace nima dai abinda nake tunane kenan yaya Sani yace zaka iya yin bincike mutumin da keda company na tayoyin mota da da gidajen mai zaku tsaya yin wani bincike.
Su wayanda take wuri su amana basu san ya kamata bane da zasu hada ta dashi basu hana ba ya mike yana fadin ni zamu shiga birni yanzu sai na dawo.
Kaunana baba yace ta lalabo ni a waya sai aka samu akasi ba layin neatwork wayan bai shiga ba lokacin.
Zuwa rana su yaya sani suka zo da mutane masu aiki har cikin gida suka shiga aka shiga aune aunen gidan da baysn gida inda filin baba ya tsaya.
Za a fara daga dakunan su inna don haka zasu fake a wani wurin sai ko inna tace bata san da hakan ba sai da baba yayi da gaske yace sai dai tabar mai gidan shi.
Mutane suka shiga tsakanin su duk wanda ya tambaya sai a fada mai mijin Safiya ne da ta samu ya aiko a rushe gidan nasu.
Karamin gari da daukan magana sai magana yabi gari washe gari suka tashi da masu aiki a gidan.
Inda suka koma gida jen yan uwa da zama suda yaran su ummi na kan gidan gwagon ta koma ita da yaranta da kayan su.
Mama ma haka inna kuma gidan yan uwanta ba wanda ya yarda ta koma can dole family house din su baba ta koma.
Ko wani gida yaya sani yakai masu abinci kamar yadda aka umurce shi yayi aiki ake yi ba dare ba rana gari duk an dauki maganan kwaaaa.
********* ********* *********
Jinya yayi so sai duk ya ramay ya fita hayacin shi karshe ma sai da ya dawo gidan gwago akai jinyan shi.
Yanzu kowa yasan abinda ya samay shi don tun a karuwan shi aka san suna dauke da cutan an kaita gida ta mutu can.
Gwago kulun kuka takeyi tana fafin Ahmed baka kyauta min ba kasa na cuci diyar mutane gashi yanzu ni da garin mu amma ina kunya zuwa.
Don ko naje ban san da wani ido zan kalle su ba kasa na rabu da dan uwana mutumin arziki da sanin ya kamata.
Yarinyar nan tana da ma bidi amma don a raya zumunci ya rufe idon shi yace sai kai kuma akayi hakan.
Ahmed dake kwace saman wani tsohon katifa yace mummy kada ki bleming dina ni kadai a cikin maganan nan ai gaban ki nake dauko mata tun ina yaro na amma baki hanani ba.
Sai yanzu da abu ya baci muna ne zaki tsamay hannu ki ciki duk waja muna saboda fitinar ki baba ya bar garin nan .
Kin hana ya zauna kusa damu ya ga halin da muke ciki ya kwabe mu tun yana zuwa har ya daina zuwa yanzu ya tare a gurin sabuwar matar shi.
Tace abinda zaka fadamin ke nan ko bayan komai a kanka ne ya faru don yana ganin yarda nake sakar maka kudi yai magana nace ina ya fito.
Nan dai sukai ta sa insa da dan nata sai da sadiya ta shiga tsakanin su taja gwago din waje kar abin yai masu yawa gashi kwance ba moriya.
Zuwan yaya Saadune ya kaishi asibiti suka karbi magani har ya fara jin saukin jikin shi ya tatara ya koma gidan shi sai dai hakan bai sa yabar halin shi ba.
Yaya saadu yazo gida kamar yadda yai alkawari ya samu ana aikin gidan mu gadan gadan ya samu baba yaji sauki sosai har yana dan fita kasuwa.
Yai masu alheri ya dawo bai tsaya lagos ba don wurin matar shi dake shirin haihuwa ya wuce direct sai da ya isa ya kirani washe gari da karfe hudu.
Ban daki na bar wayan na caji sai da na shigo ne na samu miscall din shi a nan nan nai mai kira biyu bai dauka ba ga na uku matar shi ta dauka tana cewa bai nan ne.
Nace madam yaya kike yaya tsufa ta amsa min da murmushi da lafiya tace ke haka akeyi baki lekomu ba kuma kina lagos.
Nace kada ki damu idan kin haihu zan shigo sai nayi maki one week zan koma tace kamar da gaske nace bari ki gani ko yanzu shiga daki ki haihubin banzo ba .
Ta kwashe da dariya tace to Allah ya kaimu lafiya idan ya dawo zan fada mashi kin kira baki samay shi ba.
Mukai sallama na kashe wayan na koma har kokina sai dai ban faye fita irin da ba don gidan in ba anty ke nan ba kamar suna shan kanshi.
Shiya sa ban damu da shiga harkan kowa ba a cikin su sai dai ina tunanen Ita Faiza idan fati na fushi dani ne akan dalilinta na son sulaiman .
To ita akan may take fushinta dani ni dai ban san nayi mata wani abu ba kafin in wuce gida.
Abinda ban sani ba ashe baya na ashe sunyi meeting a kaina kan nazo na samay su a gida anty ta fifitani a kan su .
Bata kallon kowa da gashi a gidan sai ni su tun yaushe suke ba a nema masu miji ba sai ni da zuwa don nazo da sihirin mu na yan kauye sai ace nice ake kokarin zuwa dani wuri.
Sai suka yanke shawaran su hade mi kai ta yadda in na dawo zan rasa gane kan su sai na raina kaina a cikin su.
Wanan dalilin yasa ban gane ma kan su sai waccan tabi can wanan tabi nan sai su watse su barni ni kuma dana ga hakan sai nima na fara share su kawai.
Gashi yanzu na dawo sai shige da fita nake yi na doke sanin su sai suka shiga gulma wai kila ba gida naje ba mun hada baki ne da anty ta turani wurin maza na samo kudi.
Tun sunayin zancen a boye har na tsura su sunayi nan nai masu tas sai suka shiga rokona wai inyi masu hakuri kada anty taji nasan korar su zatayi a gidan.
Nace amma idan na karajin wani abu makamancin haka zan fada mata dan ta dauka min mataki akansu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , ,
🧕🏿4️⃣5️⃣🧕🏿
YAR UWA KI TUNA NOVEL NA KUDI NE DON DARAJAN ANNABI KADA KI FITAR MIN DA NOVEL WAJE KE KUMA IDAN AN FITAR KIKA KARANTA BAKI BIYA HAKKINA A KAN KI, , , , , , ,
Bayan anty ta fita wurin aiki ita da yara na gama abinda zan iya taya funke na fannin aiki sai na koma daki na kwanta abina.
Can barci ya soma dauka na sai naji anturo kofan dakin alaman mutum ya shigo haka yasa na bude idona don ganin ko waye ya shigo din.
Faiza ce fuskanta dauke da murmushi tace ba dai kin kwanta ba ne nace na kwanta eh barci nake son in dan yi na wani lokaci.
Zama naga tayi a bakin gadona abinda ta dade batai min ba sai gashi yau tazo tana yi don haka nasan da wani manufa tazo.
Magana muke yi amma sai bin dakin nawa take yi da kallo kamar mai son ganin wani abu tace gida fa ya karbe ki safiya.
Kin ga yadda kika sauya gaba daya kamar bake ba sai nayi murmushi nace kin san gida dadi gare shi ai.
Tace sai kuma naji wani labari a bakin anty da nai mamakin jin shi wai Sulaiman zaki aura ba da dadewa ba ?
Faiza ke nan idan haka ne ai gida guda muke dake da a bakina zaki ji labari sai tace gaskiya kan ai na dauka da gaskiya ne sai in ce halan baki san abinda ke damuwan shi ba.
Da sauri nace may fa ?
Sai tai shiru tace kardai aji a bakina fadi ba a tambayeka.
Nace ai ya kamata na sani don kariya sai tace dama ji nayi ana fadin kila yana da cutane a jikin shi shiyasa bai son ai maganan aure dashi.
Haka naji a gida suna fada shiyasa nace barin fada maki don ki sani kada matar gidan nan ta cuta maki don kudi.
Baki ganin yadda take nan nan dashi ta kwace ma kowa shi idan ba itaba babu wanda yake shiri dashi a cikin yan uwan mu kaf.
Ita kadai ya yarda da ita yake mu,amula da ita itama din nasan don kudin shi ne take hurda dashi fiye da kowa.
Mamaki ya hana ince mata komai sai sauraren ta da nake yi rashin magana na baisa ta fasa magana ba.
Taci gaba da fadin kin gashi nan haka yake kamar bakin bature komai nashi a ka,idance yake yin shi.
Idan bai so ba sai ya nuna kamar bai sanka ba , babu dan uwan dake jin dadinsa sai wanda yaso.
Haka shima bai kula kowa yana takama da kudi a cikin dangin idan kinga gidan da ya kera a bauchi sai kin kama baki.
Babu kowa a ciki sai mahaifiyar shi da kaunar shi dake bangare guda amma duk girman gidan nan part din shi a rufe yake bai sa kowa a ciki ba.
Ni ina ma mamakin yadda idan na gaidashi anan yake amsa min a sake don a gida baka ko ganin shi balle ma ku gaisa dashi.
Nace aiko wanan halin bai kamance shi ba sai ka ganshi kamar babu ruwan sa ashe haka yake ?
Ta mike ta na cewa barin koma dama shiya kawo ni in fada maki in baki sani ba kada ai maki rifa rufa saboda kudi.
Nace amma ni sai banga wani kudin da zai rudi anty dashi ba don ko mijin ta ma yana dashi itama ba a zaune take ba.
Sai tace Safiya kenan.
Wa yaki kudi ko wa yaki kari a rayuwa balle ma ita ai ba abinda take so kamar kudi ta fadi tana kara nufar kofan fita daga daki sai ta juyo tace amma fa maganan nan ya tsaya dagani sai ke.
Nan ta fita ta barni da tunane fan a raina duk kokarin da boyar Allah nan take muna amma suna fakewa a bayanta suna zagin ta.
Nan dai nayi ta tunane kala kala har nagaji barci ya kwashe sai dai a cikin tunanen nawa ba abinda nake tunawa kamar abinda ta fada gamay da sulaiman din.
Sai kuma abin ya tsaya mun a raina nace kardai zan kara tsundumawa ne ga auren ukuba a rayuwa nace ni kuma haka rayuwa tazo min a bahaggon rayuwa komai zan gani sai akasin sa.
Karan wayan ummi na ne ya tayar dani daga barci na mika hannu na jawo wayan dake caji don na samata ringing din mamana mamana mai share hawayena.
Na yi sallama ta karba nan muka shiga gaisawa ina tambayan mutanen gida tana bani amsa da suna lafiya.
Tace yar nan shi kuma wanan bawan Allahn haka yasama kan shi lalura akan mu nace ummi wake nan fa ?
Tace mai neman ki mana ya turo yayan ki sani da abin arziki doya sai da aka shake bayan mota da shi da manja muna murna.
Ashe magana bai kare ba sai ga sani yace wai ya turo shi a rushe gidan mu a gyara a cikin wata daya anya yar nan kinyi bincike a kan sa kuwa.
Kwance nake bansan lokacin dana mike zaune ba nace ummi a rushe gidan mu fa kikace ?
Ta au ke baki ma sani ba ke nan ai yanzu duk bamu gidan kowa na gidan su sai inna ku ce a family house yan uwanta sunki yarda ta zauna masu a gida don sanin halinta.
Assha baiyi kyau ba tace halinta ya ja mata koda akazo da zancen gyaran gidan ai sai da tai halin nata mama ku ne kawai tai ta samaku albarka kedashi.
Taki kwashe kayan ta sai da mutane suka taru a kanta tonon asiri zallah abin ba dadin ji wallahi nace Allah ya kyauta.
Amma ummi ni abin ya bani maki don ko yau da safe mun gaisa dashi amma bai sanar dani zancen ba.
Watau yana son ya bani mamaki ko kuma baison godiya kamar yadda yace bai son yayi alheri a tsaya ana mashi godiya.
Sai naji ummi tace ikon Allah shine kyauta sahihi wanda ake so Allah zai saka ma mutum da alheri.
Nisawa nayi nace ummi nifa yanzu har tsoro nake ji bakiga kayan da ya saya min ba da zan dawo har akwati guda shake da kaya.
Ummi tace ikon Allah shi bai gajiya ne ?
Na amsa mata da kuma bai son godiya.
Tace Allah ya kyauta kuma ya saka da alheri ni abinda na fahinta shine bai son azo daurin aure a raina ma inda ya dauko mata ne shiyasa yace ai gyara a cikin wata guda kacal.
Nace ummi ai kowa yasan ni yar tallakane tun da ubana ba kowa bane da aka sani tace Allah ya sanmu ai nace shi kan.
Mun dade muna magana da ummi a waya har ta bani gwago buka gaisa nayi masu godiya tace akan may ai nan gidane ga ummi.
********* ********* *********
Sai da nayi sallah na fito daga daki ban dade da fitowa ba anty ta shigo gidan mun tare ta da sannu da zuwa kamar kullun.
Security din gidan yana biye da ita da kayan da ta dawo gidan dashi na mike na karbi kayan daga hannun shi zuwa ciki .
Bata zauna ba ta wuce dakin ta nasan kaya take son sauyawa tayi sallah kafin ta fito cin abinci don haka take yi idan ta dawo a wanan lokacin.
Ta sauko lokacin ta sauya kayan jikin ta tana zuwa ta zube tana fadin don Allah ku taimaka min da abinci.
Ni na mike naje hado mata sai take cewa su Faiza wai ku baku da aiki sai kwanciya ko mutum na magana bakwa dagawa.
Faiza ne tace kai madam kafin mutum ya daga safiya ta tafi hado maki sai fati dake ta faman dakalan wayan ta dago tace ba yar neman suna bane.
Komai sai tai ta nuna ita ta kamar tafi kowa alhalin bata kai kowa acikin mu ba ita ma yar kauye da ita ba a raina ta ba zata raina mutane.
Kallon ta anty keyi tace Fati ina wanan magana ya fito haka daga bakin ki har kike kokarin aibanta yar uwata a gabana.
Bari kiji ba a raina mutu idan kaga mutum baka san abin da Allah zai mai dashi ba wata rana kafinta karasa sai fati tace.
Ba dai wanan banza ba za ace wai tafini wata rana may zata iya gwada min ko ayanzu inba farin fata ba ni ma idan ina so sai in sayo a shago inyi.
Amma ke baki da hankali sha sha mara hankali ke wai sai yau shene zakiyi hankali a rayuwan ki ?
Ta mike ta shige tana guna guni na aje abincin a gaban ta don nasan bata tashi zuwa dining ci yadda take kiran yunwa take ji.
Nan muka zauna da anty tana cin abinci tana bamu labarin iri kayan da suka kama a office din su na yan smogal.
Nace anty yanzu may zakuyi da kayan tace idan sun dade basu iya kwata ba sai muyi option din shi gama su so.
Nace wai amma anty sai kuma nayi shiru tace fadi mana tana kai spoon din abinci ga bakin ta nace babu komai.
Sai tayi dariya tace haka aikin namu yake Safiya sai nayi murmushi kawai nace ai na fahinta har yamma muna wurin zaune sai sallah muka tashi zuwa yi.
Ban fito ba ko da na idar sai anty ni ta aiko kira na don haka na tashi na tafi amsa kiran nata bata falo tana dakin ta don haka na haura sama.
Tana zaune a kasa tana waya na shigo don haka na samu wuri gefe daya ina jiran ta ledan da ta shigo dashi ta nuna min da hannu alaman in dauko mata.
Na dauko na ajeye taimin alama da in bude na durkusa a gaban ta ina bude ledan ina gama budewa ta fara ciro kayan dake ciki.
Tana dubawa ina binta da kallo wanda kayane nasi yan biyun ta a ciki nace a raina ita dai bata gajiya da kwaso ma yaran ta kaya.
Na nisa tare da cewa a raina haka sulaiman yake so na dashi ya cika ni da suturu ni kuma ban saba da hakan da yake son koya min ba.
Muryan anty ne ya katse ni da cewa kayan suna da kyau Safiya na fara tanadin kayan da zasuyi bukin kune dashi don naga sulaiman bada wasa yake yi ba.
Kin san shi idan ya tashi yin abin shi bai tsaya bata lokaci naso ace kun dan kara fahintar juna dashi.
Amma kuma naga har daddy ya goya mashi baya wai ai ba bukin saurayi da budurwa zakuyi ba may za a tsaya jira kuma.
Jiya ma mahaifiyar shi ta kirani akan maganan naku nake mata bayani abinda ake ciki a zancen.
Nace anty ashe gida daya suke da mahaifiyar shi ta dago kai da sauri tace waya fada maki safiya ?
Sai nayi shiru tace don Allah a ina kikaji nai murmushi tun da ta hadani da Allah nace Faiza.
Sai naji tace munafuka yaya tayi ta sani duk wanan boyon da nake masu munafuka sai da ta gane.
Kai faiza akwai gulma wallahi.
To da suke gida guda da mshaifiyar shi ke ina ruwan ki tunda sai wani dalili yake zuwa ba tare zaku zauna.
Koma tare ne fa anty nace mata ?
Tace ai shi na gani.
Wai ma yaya akayi tazo maki da zancen ne sai na dukar da kai tace lah bazaki fada min ba ?
Ko dai ke kika fito mata da zancen ?
Nai saurin cewa a a wallahi ita dai ta samay ni da maganan wai tazo fada min gaskiya taga kamar yana sona to shine take son ta fissheni .
Don taji ana rade radin kamar baya da lafiya a jikin shi.
Salati ta saka nai sairin cewa anty tace kada in fada ma kowa don Allah abar zancen a rufe don ba zata ji dadin fada min wani ba gaba tace hakane.
Na dai kwashe yadda mukayi amma ban fada mata zaginta da tayi ba na boye wanan sai na sulaiman din na fada mata.
Tace wa yan nan yaran gulman su yayi yawa wallahi ni duk nagaji da zaman su anan don ma zuwan ki ne da duk sun koma gida.
Nace a raina don ma baki ji sauran ba aida kin rage su gaba daya sai naji tace dani gulmana fa suke yi sosai harda sakaran nan Fati da bata san ciwon kanta ba.
Naiyi saurin kawar da zancen da cewa ayyawa anty kin san ko abinda uncle yayi tace may yayi safiya ban san komai ba.
Nace dazun muke waya da ummi take fada min cewa wai ya tura a gyara gidan mu nan da wata daya a gama komai.
Ummi tace aiki akeyi ba dare ba rana sai naga ta kwashe da dariya tace namijin duniya ai tun ranan da ya tafi mukai waya dashi.
Tausaya maku yayi ya damu da yanayin da ya samu gidan ku a ciki ai ke ki godewa Allah don Allah ya kashe ya baki.
Sulaiman ban sanshi da halin banza ba sai dai mutane ne da basu fahince shi ba kawai suke gani bai son mutane ne.
Tace aiko zan kirashi in shamce shi don yasan mun sani nace anty da ki kyale shi maga gudun shi tace ai shine.
Ke har kin ma fara fahintar halin shi tun yanzu zai ce wani dan gulma ya fada min kiko ga bazan iya ce mai ummi ce ba.
Dariya na kwashe dashi nace ai sai ko ki fada tace wane ni wallahi safiya idan kin fahinci waye sulaiman shike nan kin huta.
Sai dai kinyi hakkuri da shirun shi don shi mutum ne wanda bai son magana sosai haka yasa mutane suke mashi kallon miskili.
San nan kuma dole ne in kaiki ki koya wasu abubuwa don ko shi din ba karamin dan gaye bane in dai zaki daure gaskiya kin huta safiya.
Ta tambaye ni labarin inna da za a rushe gidan yaya tayi na fada mata nan tai ta kwasan dariya tana mamakin karfin hali irin na inna.
Taci gaba da min bayani kan halin sulaiman din dana yan uwanshi da kuma halayen shi da damuwan da yake ciki.
Kaina na dukar ban iya magana ba tana ta fada min halin shi ina kara fahinta komai sai goma nabar dakin ta koda na sauko ba kowa a falon har funke ta rufe gida ko don daddy yayi tafiya kwatonu.
Har na kwanta ina tunanen maganganun da ta fada min a kanshi nace Allah ka bani ikon yin biyyyan aure
Ina tunanen ko yaya zama zamu yi dashi har mada yan uwan shi don na fahinci sudin masu haline zurian su niko gashi iyauye na ba kowan kowa ba.
Ai so ya na hana komai idan dai shi ya kamani da mutunci ai dole yan uwan nashi su soni ko don shi tun da dai dan uwan su ne na aura
ZAINAB IDRI MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , ,
🧕🏿4️⃣6️⃣🧕🏿
AMANA YAR UWA KADA KI FITAR MIN DA NOVEL IDAN KI BA WATA BAN YAFE MAKI BA, , , , , ,
Tun karfe shida na safe na samu wayan yaya Saadu cewa matar shi ta haihu nayi murna sosai tare da kwararo mata addua yana cewa amin cikin jin dadi da adduan da nakeyiwa yarinya.
Na gama yace yaya alkawari nace yana nan daram nace so ace daya daga cikin su ummi zata zo mu tafi tare amma yanzu babu hali don gyaran gidan da ake masu yace ai ya sani.
Nace ka sani yaya yace to baki fada min ba Safiya yays zanyi ido kawai na saka maki ai nace wallahi yaya nima sai last week na sani ummi ta kirani take fada min.
Yace you are free don da har na kullace ki don yanzu bakiyi dani nace da sauri wanne ni yaya ai kaine nafarko a zuciyana.
Yace to mu bar zancen sai kinzo muyi don baiyi a waya yace zai kira su gwago ya fadamasu do nice ta farko daya fara fada mawa.
Mukai sallama ma kashe wayan ina mai farin ciki a zuciya na ranan duk wanda ya ganni yasan na tashi a cikin farin ciki.
Anty tayo shirin zuwa office bayan mun gaisa nake fada mata zamcen haihuwan matar yaya Saadu itama ta tayani farin ciki.
Nace zan tafi banda gobe don nayi mashi alkawarin zuwa sai naga antu batai farin ciki da hakan ba, bata bani amsa ba, ta dai fita tana muna sallama.
Hakan bai min dadi ba amma zanyi hakkuri in ga tafiyan ta akan zancen don ba zan saba ma yaya Saadu alkawari ba gaskiya.
Bayan na gama aiki na shiga daki na buga ma anty waya ina fada mata zancen haihuwan na matar yaya saadu.
Itama tayi murna sosai tayi ma yarinyar adduan sosai nace mata ina son zuwa kamar yadda nayi masa alkawari don wanan kawai zan mashi in iya rama mai halarcin da ya gwada man.
Tace dako kin kyauta yar nan nace sai dai ina ganin kamar anty bazata yarda da zuwa na ba tace sai ki lalashe ta kada kiyi gaban kan ki.
Nikan shiri na fara yi sai dai ban fada ma kowa ba kamar yadda ya saba kirana a ko wani rana safe da yamma yauma ya kirani da dare bayan na kwanta nan nake fada mai cewa matar yaya na ta haihu ina son zuwa Carlaba wurin suna ya taya ni murna tare da tambaya na yaushe ne suna na fada mai tare da cewa ina son in tafi suna.
Sai naji ya danyi jim sai yace yaushe ke nan kike son zuwa nace banda gobe don haka nayi ma yayana alkwari don yace yana son inzo da wuri.
Don banda kamar shi a cikin yan uwa ya taimakeni a lokacin da nake neman taimako banda wanda zai taimaka min.
Yace lallai kina ji da wanan yayan naki sai ki turo min da layin sa in mashi godiya nace angama yallabai.
Da jirgi zaki tafiya ko da mota sai nayi saurin cewa jirgi kuma zan dai bi mota in tafi yace ban faye amincewa da batun motar nan ba.
Ki dai bi jirgi ki tafi yafi tafiyan a mota sai ki kai da wuri yace zanyi magana da madam sai a san yadda za a shirya maki tafiyan dan ni bani kasan yanzu haka.
Nayi saurin duba lanban wayan nashi naga daga kasar South African yake magana tirkashi nace a raina.
Mukai sallama na kashewayan tare da kwantawa naja bargo na rufe ina mai ci gaba da tunane a zuciya na.
Anty ta fita aiki da safe bai kirani ba sai nayi tsamani aikin da yaje yi ya dauke mashi hankali ne a can.
Da ta dawo ne take ce min munyi waya da sulaiman nace a a sai tayi shiru can tace ashe kina ga zuwa Calabar din ne don naji sulaiman na fadin a sayo maki ticket din jirgi.
Nace a dake eh anty gobe nake son zuwa don hakane kawai zan iya rama ma yaya Saadu halarcin da yai min a baya.
Ta gyada kai tace shike nan da amma ni naga da kifita hanyan duk kansu baki daya har saadu din zai fi tunda sabon aure zakiyi yanzu.
Da sauri nace anty kina ganin zan iya yanke zumuncin da ke garemu da yaya Saadu shine fa dan uwa na farko da yai min tsaye na samu lafiya.
Kuma ana haihuwanan bai kira kowa ba nice ya fara kira ya fadawa idan nai haka na zama butulun a duniya har da wurin Allah.
Sai tayi shiru bata kara yi min magana ba hiran ma sama sama muke yin shi da ita taje sallah azahar nima na tashi na idar na fito bata falo.
Na samay ta a dakin ta sama nace anty ina son in dan fita in sayo wa baby tsara ba don kada naje hannu sake.
Ok ai yanzu muka gama magana da sulaiman bance da ita komai ba nace zan wuce sai naji tace dan dakata min in zo.
Na samu wuri na tsaya daga kofan daki ta mike zuwa safe din ta ta bude ta fito da kudi kashi biyu tace ga wanan sulaiman din ne yace a baki ki yi sayayya sai kuma wanan nawane asaya wa baby kaya.
Nace Lah anty ai da ku barshi ina da dan kudi hannuna da na dawo gida dasu tace kin raina kenan ko da sauri na isa wurin ta ina karban kudin.
Sai naji tace Safiya kamar maganan danayi akan saadu bai maki dadi ba ko nace ba haka bane anty ai gaskiya kika fada min.
Sai dai shi yaya Saadun ne banga laifin shi aciki ba don bai min komai ba tsakani na dashi sai alheri har gobe don ko dawowanan da yayi sai da yaje gida duba jikin baba.
Tace ai nayi tunane daga baya naga kina da gaskiya tace ki dai zabo abin kwarai don Allah kada ki kwaso shirmay.
Nace to anty na gode na juya zan wuce tace dani zan kira driver sai ya kai ki godiya na kara yi mata na fita.
Faiza tana ganina take tambayana inda zan tafi na fada mata sai tace zata rakani ta dan mike kafan ta.
Na jirata ta shirya ta tafi ta fada ma anty muka fita tare nan muka samu driver yana jiran mu a waje muka fada mota ya fice daga gidan.
Kaya na kwaso na baby da na uwa sai da na cika akwati dashi muka nufo gida Faiza take ce min tana son mu tafi tare nace sai mu fada ma anty idan zata yarda.
Bayan ta gama ganin kayan ta sauke ajiyan zuciya tace wai Safiya kaya haka kamar mai shirin bude shago ai kin fanshi uban diya.
Nake cewa anty dama ai fannin uba muke sai lokacin ne Faiza take gabatar mata da son zuwanta tayi saurin cewa da jirgi fa zatayi tafiyan.
Ba zai yuyu kuje tare ba da dai a mota zakuyi tafiyan zan barki ki tafi Faiza bataji dadin haka ba kuma gashi taji ance a jirgi zan tafi wai.
Sai yake ta mamaki wani irin asiri nayi ma anty ne haka da basu jin wuyan kashe min kudi har yaushe na dawo gida akaje airport dauko ni.
Yanzu kuma ace a jirgi zan kara tafiya kodai maganan Fati gaskiya ne da take fadin tana turani karuwanci ne wurin maza.
To amma kuma wanan uban kayan da muka sayo fa namay ye shi gashi kuma taji nace fannin uban jegon nake bukin dai zan tafi amma akwai dai daurin gindi wani wuri.
Yadda tasan anty da kudi bazata iya biya min kudin jirgi ba har Calabar in je in dawo na kwashi kayan zuwa dakina ina shiga daki kiran shi ya shigo wayana.
Ban dauka da wuri ba sai da nayi halin mata jan rai na dauka tare da sallama sai naji ya sauke ajiyan zuciya yana fadin.
Ke idan ba a kiraki ba baki kiran mutum watau nace na dauka kana uzuri ne tunda banji ka ba yace ban uzurin komai fushi dai nake yi dake.
Nace ni kuma may nayi yallabai ?
Sai yace ashe bukin dangin mijin ki na da zaki tafi ban sani ba nace kwarai dangin shi ne nima kuma dangi na ne ba gaiyan sodi zan tafi ba sai na fara bashi labaron irin halarcin da yaya Saadu yai min a lokacin.
Yace kin fini gaskiya daga baya madam ta fahintar dani ai daga baya yanzu na fahinta Allah yakai lafiya.
Nace amin yace tace girgin karfe hudu zaki bi sai ki sanar dasu can azo a dauke ki nace nagode yace ban son tsaron lafiyar matata nakeyi.
Ya kashe wayan nabi wayan da kallo tare da tunanen watau anty ta fada mashi abinda ta fada min ke nan da farko.
Idan haka ne bata kyauta min ba kuwa zuciyana ta nasa min cewa kodai abinda su Faiza ke fadi gamay da ita gaskiya ne ?
To inma gaskiya ne ni dai batai min komai ba don bazan manta da halarci ba kuma ban iya matawa da mafari.
Da dare na kira yaya nake sheda mai karfe shidda azo dauka na a airport yace bazaki zo ba kenan amma safiya baki kyauta min ba.
Gashi na sa rai kece zan gani cikin yan uwa da zaki zo ki zama min garkuwa don suna fadin ba a san yan uwana ba.
Nace yaya karfe hudu nace azo airport a dauke ni ba wasa nakeyi ba in Allah ya yarda gobe zan shigo yaya yace masu gari don Allah da gaske nace Allah yaya.
Koda gari ya waye na shirya tsab sai dai yan gyare gyaren daki da na tsaya yi don kada in dawo in samay shi ba gyara.
Wayan shi ne ya shigo min muka gaisa yace an shirya ko nayi murmushi nace kamar ka sani komai na hada tafiya kawai ya rage min yanzu yace nasan dari biyu zai ishe ki yin komai su nace ma madam ta baki jiya.
Nace ta bani na gode ubangiji ya kara rufa asiri amma dai kai baka gajiya da yi mani dawainiya haka ?
Yace idan banyi wa matata dawainiya ba in yiwa ai ke da hajiya baaba kune dole na yanzu ba zan taba dana sanin yi maku ba a rayuwa na.
Mun dan taba hira mukai sallama yake cewa idan na isa zai kirani yaji sauka na nace nagode.
Mun kashe wayan ya barni da tunanen maganan anty watau kudin da ta bani dubu goma cikin kudin da ya bani ne don dubu sittin ta bani tace inji shi.
Amma kada in zargeta zan bari in gani ko idan zan wuce zata ban sauran inma bata bani ba taci halas ai albarkacin ta nake ci da badon itaba ina zan samu wanan gatan.
Karfe uku ta dawo gidan don tafiyan nawa take cewa nayi na shirya kafin hudu driver zai kaini airport.
Nace mata tau.
Uku da ashirin na fito tafiya tana dakin ta naje mata sallama fuskan ta da fara a take ce min tau safiya Allah ya kiyayye haya agaida su ina masu barka.
Yaushe zaki dawo nayi murmushi nace sai dai idan na je can anty zamuyi waya sai in sanar dake tace to Allah ya kiyayye hanya na ce amin na fita da kayana Faiza tai min rakiya har waje sai da muka daga ta dawo ciki.
Mun fara hanya na nisa tare da fadin mutum kasan shi baka san halin shi ba yanzu ba don Allah yasa ya fada min ba ba zan taba sanin komai ba akan anty.
Bamu dade da isa airport din ba jirgi ya tashi dan wani lokaci naji ana sanarwa jirgi zai sauka mu shirya .
Mun sauka na fito tare da kaya na ina faman rabon ido ko ta ina zan ga yaya Saadu sai gashi tare da abokin shi.
Yayi murna kwarai da ganina yana ta faman washe baki yana fadin safiya ashe da gaske kike yi kin san Allah karfin hali nayi nazo airport kawai ba don na yarda ba na dauka kin fara wasan cousi ne dani.
Nayi murmushi ina gyara gyalen kaina dake kokarin walwalewa a kaina nace haba yaya ai bamu yar haka dakai.
Suka dauki kayana zuwa motar da suka zo da ita nan muka kama hanyan zuwa unguwar su sai faman zolaya na yakeyi yana fadin waiko Safiya kece nake gani a gabana ko mafarki nakeyi kin koma haka ?
Ni dai murmushi nake mashi ina bin gari da kallon mamaki abubuwan zamani irin nasu na arna da kallo.
A can wani ungwa mai kama dana hausawa muka shiga don akasarin mazau na ungwan hausawa ne amma na gari daban daban sai hausan su ya juye kamar yare.
Mun tsaya a kofan wani gida nan yace min tau Safiya yau kin zo gidana muna maki maraba da zuwa murmushi nayi nace na gode.
Mun fito suka bude bayan motar suna fito min da kayana daga ciki a tare muka shiga gidan dasu sai ga matar shi Samira ta fito da gudun ta tana min oyoyo .
Muka run gumay juna da ita tace ashe gidan gidan yawa ne mai apartment da yawa ban luraba sai naji tana fadin ku fito ga kaunar miji na tazo.
Nan naga mata na ta firfitowa daga sashen su suna zuwa yi min sannu da zuwa niko sai faman washe baki nakeyi ina karba masu.
An shiga dani dakin su dan part ne mai kumshe da ciki da falo sai wani dan daki karami da kicin a cikin part din dakin su aka kai min kayana.
Shiko yaya saadu ya rasa ina yaka saka dani don farin cikin shi baya boyuwa ranan bayan na zauna falo .
Nan ta fara gabatar min da abinci da abinsha ban wani ciba sosai don banda yunwa a tare dani aka kawo min baby a daidai lokacin da yaya ya shigo yana cewa kin ga Safiya karama ko ?
Na dago kai da sauri nace yaya sunan da aka samata kenan yace Sunan ki taci Safiya ko bai maki dadi ba na lumshe idona sai ga hawaye yazo min.
Yace kuka kuma kike yi har yanzu baki daina halin nan naki da na sanki dashi ba na saurin kuka nace yaya bansan irin godiyan da zan maka bane.
Bayan taimako gashi kuma har sunana kasa wa yarka ta fari a duniya matar shine ta fito ta samay mu zaune take cewa yaya naga kamar kina kuka.
Gaki ga yayan ki ga takwaran ki kin dauka kuma sai yaya yace wai duk farin cikin yi mata takwara takewa kuka.
Tace ai dole ina haihuwa na dauka sunan mummy zai sa kona mama na sai naji yace wai sunan yarinya safiya sai da nayi makin wanan irin shakuwa naku wallahi.
Bari kedai Samira ni duniya yaya ya gama min komai Allah dai yabar zumunci ya raya min takwara na ta famnin addinin musulunci yasa mata albarka sukace amin.
Nan muka zauna muna hira yake ce min sai yaje gida ya samu baba ya samu lafiya sosai sai dai su ummi ba kowa a gidan anata gyare gyaren gida.
Na nisa nace bari yaya nan na fara bashi labarin yadda abin ya faru da irin taimakon da yake min shi da uwar dakina.
Sai da ya gama saurare na yace Alhamdullahi Allah maji rokon bawan sa Allah ya amsa min addua na kullun ina rokon Allah akan kada rayuwan ki ya kare hakana baki more ma rayuwa ba safiya.
Don ina ganin yadda rayuwan masu wanan matsalar yake karewa a lalace saboda rashin gata da samun kulawa da basuyi.
Nacs haka abin Allah yake yaya sai dai muyi fatan dacewa da rahaman ubangijin mu yanzu.
Amma yaya inda son samu ne asamu wanda zaiyi bincike kwakwara akan Sulaiman din don kada ai abu cikin duhu a dawo ana da an sani kuma irin na farko.
Ya nisa yace insha Allahu kuwa zanyi kuma da yardan Allah sai Alheri don yadda yake kulakin nan akwai alaman nasara ga abin.
Don da akwai matsala da tun yanzu zaki dan fahinci wani abu daga gare shi sai dai zaki iya tara matsololin da ake fadi nasa ki auna ki gani .
Amma dai duk da haka zanyi kokari in bincike a kan shi don wani lokaci yin binciken yana da kyau.
Na fara hamma yace naje na kwanta mu hadu da safe sai lokacin nace dashi yanzu wani sana a yakeyi ne ?
Jeki ki huta da safe mayi magana naga kin fara hamma ni yanzu fita zanyi ya kwala ma matarshi kira tazo ta kaini daki.
Naga ta nufi dakin su dani nace ai da kun barni in kwanta a falo ma nan ya yi min yace haba dai ai kinzo taya ta aiki ne don haka ni na bar ki da ita ke nan.
Yai muna sallama cewa zai fita ya dawo na mike zuwa dakin inda na samu gadon dakin yasha gyara dakin sai kamshi yakeyi .
Na yi shirin kwanciya dukkan mu a saman gado daya muka kwanta muka sa baby a tsakiyan mu asuba ta gari yan uwa.
Idan zaki fitar min da novel na barki da raddin ubangijin mu je ki tayi tunda baki san hakkin amana ba zaki fada ranan da baki baya magana sai hali.

🧕🏿4️⃣7️⃣🧕🏿
Ni safiya ace mutum bai tsoron Allah shi dole ne karatun nan ance ba a yafe ba an hada ki/ka da Allah an hada ku da darajan annabi amma kuna wasa dashi ku sani fa hada mutum da Allah ba karamar kalma bace akwai ranan haduwa dashi ranan nadama ranan da baka da abin bayar sai ladan da ka tara ma kan ka.
Mutuna ko yanzu ko anjima koyau ko gobe ko ko ko ko zamu koma ga Allah koda ciwo ko babu ciwo may zamu fada wa Allah.
Dabara ya rage ga mai shiga rami shi kadai ni dai tun da asuba na mike batare da samira ta sani ba nayiwa gidan ta kwal ga ruwan zafi da na sa masu na wanka ya ya tafasa na sauke na fara hada mata abin karyawa.
Sai da naje daukan baby dake barci a gefen tane ta bude idanun ta tana fadin subbahanallahi gari ya waye ne ?
Murmushi nayi nace madam ki tashi ruwan zafin ki na jiran ki a bayi ban saurara mata ba na fara cirewa baby kayan jikin ta na nufi bayin da ita inda maga kayan wankan ta aje a gefe.
Wanka nayi mata na gasa mata jiki dama na iya tun ina gida idan ummina ta haihu nakan taimaka mata da wankan yara.
Na fito na fara shirya baby sai lokacin Samira ta samu ta mike zuwa wanka tana cewa yau wata rana zamuyi wanka da safe haka yadda ya dace.
Nikan naji dadin ziwan nan naki Safiya wannan kokari haka ta mike take bin dakin da kallo tace wai ko kin yi barci safiya wanan irin aikin haka ?
Kafin ta fito na saka wa yarinyar kaya cikin kayan da nazo mata dasu uwar ta fito wanka tana kallon mu da sha a wa tare da fadin aa lalai takwara tazo wanan kaya ai da ki bari sai ranan suna ki saka mata.
Murmushi nayi kawai na goya yarinyar na na fita daga dakin sai gani na dawo da cup cike da shayi mai kauri dana hado mata.
Na aje a gefen ta dago kai tayi ta kalle ni nace madam sai a sakai a shanye kafin ya huce nace za a daukan maki kaya ne ki saka ?
Tace gaskiya Safiya zaki shagwaba ni da yawa ki wuce ki barni da kewan ki nace kada ki damu madam dama shi nazo yi yanzu aiki na ne nakeyi.
Batai sanya ba ta kafa kai ta shanye shayin duka sai ga zufa ya karyo mata nan ta mike ta dauko kayanta tana sawa.
Na fito falo naji ana bude karamin dakin nan dake rufe ashe yaya ne anan ya shige ya kwana na juyo don ganin ko waye mukayi tozali dashi.
Nace yaya barka da kwana yace an tashi lafiya Safiya nace Alhamdu lillahi yaya yace yau takwaranki ne ta samu goyo haka ?
Gaskiya banji kukanta ba yau da safe don kullun itace ke tayar damu da safe da kukan ta nace yau tasan gwagon ta na gari batayi kuka ba tun da nai mata wanka takoma barci.
Yace kai har wanka ta samu yau da wuri haka nace gwago tazo fa yaya zanbar diyana takai wani lokaci bata gasa jikin ta ba.
Nan ya fara bin gidan da kallo yaga gyaran da ya sha yace keko kinyi barci kuwa nace may ka gani yaya yace wanan irin aiki haka tun da farar safiya haka ?
Nace shiya kawo ni may zan kwata wa inyi ga aikin madam a gaba na yanzu lokaci ne da take sin hutu a jikin ta don haka ta kwanta ta huta jikin ta ya watsake.
Na shige kitchen na barshi yana mamaki ya raya a ranshi da haka uwar shi ta rike zumuncin da mahaifina yaso su kulla da abin yazo da sauki.
Ya shiga daki nan ya samu samira tana ninke kayan da ta cire ta juyo tana kallon shi tace kaga aikin kanwaka ko sai yau na karkare yarda da abinda kake fadi nata.
Na shiga dakin na samay su suna magana nace yauwa bari ma in baku sakon ku tunda gaka a dakin nan na jawo akwatin kayan da nazo dashi zuwa gaban shi na juya wirin hand bag dina na ciro kudin da na ware mashi tun a gida na bashi.
Sai bina yake da kallo yana neman karin bayani nace yaya kana kallona mana yace ban fahinta bane safiya nace to kaya da na takwara nane da uwar ta gashinan akwati guda sai kudi kai kuma ka kara kai hidiman buki da su.
Tsaye yake dama zai shiga bayi sai naga ya kai zaune a wurin yayi shiru can ya dago kai yace Safiya duka wanan dawainiyar ani kika yi shi bayan zuwan da kikayi kuma ga wanan wahalar.
Ba wahala bane idan duk abinda nake dashi zanyi maka bazan taba yin da na sani ba yaya kai kaja in maka hakan da nayi.
Samira kan kallo na take da mamaki da kyat ta samu bakin magana tace wai safiya kin wanke ni ga bakin jamma a kin gama muna komai a duniyan nan.
Kin san yayan ki aikin company yake yi gashi wata uku ba a biya su jiya jiyan nan muka gama magana dashi na yaya zaiyi ko zamu daga sunan nan har zuwa gaba.
Nayi saurin cewa a uzubillahi a daga suna kuma yaya Allah ya rufa muna asiri ashe gwama da na daure nazo don da anty ta so hanani zuwa na nace nace sai nazo.
Tace Allah ne ya kawo ki yar uwa ta fara jawo kayan tana bude zip din jakkan don na karshen ne babban duka duka nazo kasu dashi.
Shiko yayi mutuwar zaune ya kasa fadin komai har lokacin tana budewa ta sake karamin ihu da fadin wai Safiya ?
Shago ke nan ta fara budan kayan tana azawa a saman gado karshe rufe akwatin tayi tai tagumi kawai sai can ta nisa tace dear ka ga ikon Allah.
Sai lokacin ya nisa a sanyaye yace na gani samira ban san may zance bane kawai imani da tsoron Allah sun cika min zuciya samira.
Kawar da zancen nayi da fadin ni kaga malam kai wanka ka shirya kazo ka karya in ka gama ka fita ka sayo muna abinci azo a aje a gidan na ciro kudi ina mika mai.
Ido ya zaro yace na may ye kuma wannan kudin nace abinci zaka sayo mana dashi wanan ba na hidimar suna na baka kayi ba sai naji yace haba kai safiya haba dai.
Tare shi nayi da fadin ka gode ma Allah adduan ku gareni ya karbu ga ubangiji shi ya wadatani da wanan niimar idan ban gode nima na na rama maku ba may zanyi da kudi.
Kudine ina samu alhamdullahi don sulaiman yana wadatar dani dasu kuma yana fada min in yiwa yan uwana alheri daga niimar da Allah ya wadatar dani.
Yace Allahu akbar haka abun Allah yake safiya shiya sa idan kaga ubangiji ya yi ikon shi akan mutum kai dai kabishi da addua don baka san hikimar ubangiji ba a kansa.
Abinda nai maki a baya har ga Allah nayi maki ne a matsayin ki na yar uwata ta jini da kuma matar yayana da hadi na musulunci banyi don zaton wata rana zaki zama wani abu har ki rama min ba.
Nace na sani yaya nima kuma ba zan taba iya rama maka abunda kai min ba har abada duk wanda yai maka abu a lokacin da kake bukatan taimako a kan shi ai baka da kamar mai shi a duniya ba don kai ba da yanzu na wullakanta.
Yai saurin cewa Allah bai yoki wullakantata ba dama safiya ki godewa niimar da Allah yai maki tun farko tunda kin samu kiyi karatun boko.
Nan dai mukai ta hira dasu har ya gaji ya mike zuwa wanka yafito ya karya ya fice daga gidan baby Safiya ta tashi na kaita wurin uwarta na dawo na ci gaba da aiki na.
Tuwo na tuka mata na Semon da na gani a kitchen din da miyar yauki ina gamawa yaya ya dawo gidan da kaya niki niki tare da abokin shi.
Wai ya kirashi yazo yaga abinda na kawo masu abinci na gabatar masu bayan sun gama gani yaya yace safiya sai kina sa ina ganin gidan yau kamar ba nawa bane.
Muna tsaka ga magana Samira ta fito daki da wayana a hannu tana mika min ana kirana a lokacin.
Na karba naga Sulaiman ne da sallama na koma gefe daya ina amsa wayan yace gida yai maki dadi kin manta da kowa ko ?
Murmushi nayi nace yallabai an tashi lafiya yaya aiki yace lafiya kalau watau ke dai baki kiran mutum ko nace tsoro nakeji kada in kira ka kana cikin uzuri.
Yace don gani agogo sarkin aiki sai ba zan tsaya na saurari kiran mata na ba ko ?
Nace tuba nakeyi katse shi nayi da fadin ga yaya na ku gaisa yace af yana kusane nace yana nan yanzu ya shigo namika ma yaya Saadu wayan.
Sun gaisa yake ma yaya barka da samun karu sai yaya yace Allah ya mayar gare ku kuma da kunyi aure a sama mana tagwaye.
Murmushi yayi kawai yaya yake mashi godiya a bisa ga kokarin da yayi masu yace na komai ai anzama daya yanzu.
Yake tambayan yaya din wani aiki yake yi sai yace mashi a wani company yake aiki yanzu kuma company tai sanyi sai dai dan buga buga da suke yi sunyi hira sosai kafin yaya ya bani wayan mu ci gaba da magana dashi har yake tambayana da yaushe ne zan dawo ?
Nace jiya fa nazo har ake batun dawowa na yanzu sai nayi a kalla wata daya ko biyu kafin in dawo sai takwara na tayi kwari zan dawo.
Yace kina hauka ne nifa in badon madam ta fada min yadda kuke dashi ba kuma yanzu a wayan da mukayi na fahinci mutumin kwarai ne don gashi har yana min fatan samun tagwaye da auren mu.
Da hankalina bai kwata da zuwan ki garin nan ba sam nace sace ni za a yi komay ?
Yace yana da wuya ne nace ni ko kofan daki ban taka ba tun zuwa ina ciki kumshe ina za a gani har a dauke ni ?
Yace ki dai bi sannu don Allah ban son yawo please zan ma fada ma yaya don ya saka maki ido sai nace ai ka hutar da kan ka ni din kifin rijiya ce fita a guna sai ya kama dole nake fita.
Yace daya fi maki ashe ba zamu samu matsala ba ban son mace mai yawo a rayuwa na ko gadan.
Yace kin san may ?
Na ce aa yallabai yace yau yayan ki ya fama min wani ciwo a zuciyata sai nayi sauri cewa subbahanallahi.
Yace dakata mana kiji ai ba wani abu yace min ba illar cewar da yayi Allah ya bamu tagwaye da munyi aure.
Sai nayi murmushi yace ban taba jin ina son haihuwa ba nima sai yau daya fada min haka naji nima ina son in ga zuria na a duniya koda kuwa bazan rayu tare da su ba.
Nace balle zamu rayu tare dasu insha Allahu ai Allah shi ya fimu sanin daidai ga rayuwan mu ni dai mu bar wanan zancen ba yanzu ba tukun.
Yace saboda may ?
Ko ba kya son haihuwa ne ke nace wai kuwa kasan sunan yarinya Safiya ?
Kin kawar da zancen ke nan ko?
Safiya yaya yasa wa babyn namu nace wallahi ina zuwa yace ga takwara nan yayi min ya ce Allah ya raya muna ita a tafarkin addinin musulunci nace amin.
Yanzu yaushe zaki dawo lagos ba wasa nake yi ba fa ina son in sani ne ?
Nace kaida baka ko kasan kake tambayana yaushe zan dawo bafa a gari daya muke zaune ba balle kuma baka ma kasar baki daya.
Murmushi yayi yace ina son in san lokacin da zaki dawo idan yayi daidai da dawowa na Nigeria don ta lagos zan sauka.
Nace gaskiya ban sani ba tukun sai dai idan anyi suna naga yadda yanayin ya ke zan saka ranan dawowa na.
Munyi sallama dashi naci gaba da aikina na fito inda na samu su yaya sun gama cin abinci sun cinye duka sai kwano.
Na kwashe zuwa kitchen tare da kokarin dora girkin yamma don inyi in gama da wuri in huta ina aiki yan barka suna shigowa jefi jefi kamar yadda ake zaune a bariki.
Na gama na gyara wurin na koma ciki nayi wanka sai lokacin na samu zama da samira muka fara hira wanda hiran namu akan yanayin garin nasu take min da kuma bani tarihin ta.
Da yadda suka hadu da yaya saadu yan uwanta suka so su hana auren su wai ba a san asalin shi ba sai da kyat aka yarda ta aure shi don suna son junar su.
Nace ai yanzu aure babu inda bai kai mace gashi ban taba zuwa bauchi ba amma aure yana shirin kaini can din.
Tace wanda zaki aura dan bauchi ne shi nace mata dan bauchi ne tace a can yake zaune nace da ita a a .
Sai nayi dariya nace shi wanan ai baida takamaimai zurin zama dan kasuwa ne baya zama sosai sai dai ina ganin abuja zai aje ni amma dai ban sani ba dai.
Waya na jawo na kira anty don nasan yanzu ta dawo gida kira uku ta daga wayan tana fadin mutanen kalaba kun sauka lafiya yaya baby da maman ta.
Nace lafiya lau anty baby safiya tana gaida ke tace a a safiya aka sama yarinyar nace eh anty .
Tace ashe gaskiya kika matsa da zaki kin san abinda kuka kulla da yayan na ki nace wallahi anty ban san safiya ya samata ba sai da nazo naji.
Tace sai yaushe zamu ganki nace anty sai anyi suna zamu zauna da yaya saadu don yanzu bai samun zama a gida.
Tace yana da buki yaushe zai zauna gida kuma Allah yasa a watse lafiya ki gyayar min dashi don Allah ina mashi barka idan ya shigo .
Mun gama ina cewa ta gyayar min dasu yan biyu tace kin sa sun zo sun damay ni da tambayan ina kika je nayi murmushi nace nasan dama zasu tambaya ai.
wayan nake aje wa sai naji samira na fadin itace wacce kike a wurin ta lagos halan ?
Nace eh wallahi mutumiyar arziki bata da matsalan komai wallahi ta rike ni tankar itace ta haife ni.
Tace kinyi dace da uwargijiya yar albarka samun irin su yanzu da duniya ya dauki zafi ai sai dace.
Yan barkan da suka shigo yasa ni tashi na basu wuri falon su na koma na kwanta ni kadai babu komai a raina sai tunanen rayuwa.
Maganar haihuwan da mukayi da shi dazun nake tunane a irin wanan halin da mutum yake ciki har zaiyi tunanen haihuwa wa a hakan.
Yaya taran zasu taso suji halin da iyayyen su ke ciki a duniya kuma ba wani dadewa zasu iya yi da iyayye su a raya sam wanan tunanen na sulaiman ban kwanta mi ba arai nikan.
Mu dai samu mu raka da rayuwan mu a hakana batare da mun jefo wasu a cikin matsalar mu ba yara su taso a wahalce babu iyayyen su a duniya.
Shigowan mahaifiyar samira da ba sai an fada ma mutum ita ta haife ta ba don kamar da sukayi da ita.
Sannu da zuwa nake masu tace a a lalai kuwa ga gwagon baby na gani sukeyi min sannu da zuwa na amsa masu a sake tare da masu jagora zuwa daki.
Bayan na gama wadatasu da abin sha saina koma falo ida nake zaune da farko na kwanta ina jiyo hiran su daga inda nake zaune samira na fada mata abin arzikin da na kawo masu.
Tunanen ummi na ya fado min a raina din haka na ja waya ina laluban ta nayi saa wayan ya shiga muka gaisa nake fada mata ai ina kabala tun jiya na iso.
Tayi ta samin albarka da na samu zuwa nake tambayan mutanen gida tace duk suna lafiya aiki dai yayi nisa jiya da yayan ki sani yazo.
Yake fada min wai yanzu window za a sa sai kuma aci gaba da sauran aiki nace yaya sani ana nan dai ana ta fama tace bari kedai.
Ai kina shan albarka a wurin shi kullun yazo maganan ke nan a bakin shi nayi dariya nace yaya sani ho yana nan dai da halin nasa
Tace may zai fasa take bani labarin harkan sana a ta nace ummi ai yanzu ya zama naki sai dai ku kula kada kudin ya karye .
Mun gama waya na sauke ajiyan zuciya ina mai ci gaba da tunanen duniya a raina har har mahaifiyar samira suka fito daga daki suka dawo wurina muka zauna muna dan fira jefi jefi basu dade ba sukai muna sallama.
Ban shiga ba anan nake zaune don akwai kawarta a dakin bata fita ba don haka na basu wuri su dan tatauna a tsakanin su.

🧕🏿4️⃣8️⃣🧕🏿
Daf da magariba yaya saadu ya shigo ya iskani zaune a falo nayi zugum cike da tunanen zucci muryan shi naji daga sama yana fadin.
Safiya haba zaki bata min rai fa idan kina zama ke kadai kina saka damuwa a ranki da tunane tunanen banza marasa amfani gare ki.
Nisawa nayi nace duk abu mace mai rai da lafiya in tana da hankali dole tayi tunane a rayuwan ta.
Zama yayi a kujera da ke fuskantana na sake cewa dashi yaya ke nan ai dole mutum yayi tunanen rayuwa din ni yanzu kaina ya daure don ban san makoma na ba.
Yace come on, wace irin magana kike fadi haka?
Wace irin magana kike fada safiya may yasa kikace hakan ?
Ta dukar dakai na kasa nai shiru da alaman tunane nakeyi abinda zan fada mashi.
Yaya wai ba za a kara ma auren nan lokaci ba don ni kwata kwata ba wai na shirya mayin aure bane yanzu.
Abu ne mai wuya yan uwanshi su yarda dani ko su soni far daya don dukkan su fa masu kudine family su cap yaya, yaya za a yi inyi daraja a wurin su.
Ya kalle ni kafin yace shi zaki aura ko yan uwan shi na ce shine yaya.
Sai naji ya kyalkyale da dariya yana mikewa yace kai amma ku mata wani lokaci sai mutum ya rasa ina tunanen ku ya tafi ne wai.
A daidai lokacin Samira ta fito daga dakin ta tana ce min tare da miko yar ta naga yamma yayi a goya ta ko ?
Karban yarinyar nayi nake mata kirari ina kokarin goya ta a bayana yaya yake cewa zai tafi masallaci yai sallah.
Yana fita Samira ta kalle ni tana cewa kin ko ci abinci safiya don ni banga kin ci komai ba tunda safe ?
Nace dazun da safe na karya ai ni dama haka nake abinci bai damay ni ba tace ko wani abin kike son ci baki magana ba.
Bari yayan ki ya dawo sai ai mashi magana ya dan samo maki wani abin marmari ko zaki iya ci amma kan kya zauna da yunwa hakana.
Nace ai banjin yunwa ne da zanci abincin baidawo ba sai taimai waya da zai dawo gida sai gashi da drinks mai sanyi da gasassan kaji biyu ya dawo dasu.
Gaba ya sani dani dashi da samira sai da yaga na ci kaza guda daya aje min amma rabi banyi ba na dan kora da drinks din na ji nauyi a cikina.
Sai dai cikan da cikina yayi ya hana ni barci da dadi da dare sai da na sha magani na samu shakkat a rayuwana.
Ana gobe suna ban zauna ba don aiki yai yawa a gidan bani na samu kaina ba sai dare shima ba wani barci na samu nayi sosai ba.
Asuban farko na tashi kafin gari ya waye na gama ayukan daya dace duk wacce tazo sai dai in debo mata abinci da abin sha in bata.
Anyi suna lafiya aka watse kuma lafiya sai mu da wasu yan uwan Samira aka bari muna gyara gida anan muka kwana tare da su.
Washe gari muka kara gyara gida sai suka fara tafiya dama su uku ne bayan tafiyan su ne na samu wuri na kwanta don duk na gaji sosai a lokacin.
Barci nayi sosai a ranan sai karfe hudu na tashi ina duban lokaci samira tace ai taki tasheni ne don taga na gaji.
Sallah nayi nazo na hada masu ruwan wanka sukai wanka muka zauna hira da ita yaya bai dawo gida ba sai da dare.
Nan ya zauna muka sha hira dashi har yaci abinci ban dade ba na basu wuri zuwa ciki nan barci ya dauke ni koda Samira ta dawo dakin ta samu har munyi barci nida safiya karama.
A kwana uku da suna muka zagaya gidanjen yan uwa da abokan arziki da suka zo mata suna da barka.
Duk gidan da muka shiga zanga sun kira samira a gefe suna tambyan ta ni wacece a gare su ?
Wasu su fadi alheri akaina wasu kuma suce tayi hankali dani tunda ba uwar mu daya uban mu daya ba zan iya aure mata miji.
Ita dai dariya take masu kawai a gidan su muka dawo muka ya da zango anan don sai dare muka koma gida don uguwar su guda sai dai da dan nisa da gidan su.
Ina cika sati daya da zuwa na fara zancen komawa don kullun na kira anty sai ta tambaye ni yaushe zan dawo ne.
Shiyasa nake son komawa yaya yaso yai min sayayya amma na hana shi sai mun komai sai cake da akai masu wanda zanje dashi a matsayin kayan buki da sauran tarkace na kwalam din yara.
Munyi waya da sulaiman na fada mashi ranan da zan taso sai yace inba yaya nombashi ya kira shi nabawa yaya ya kirashi ashe zai turo da kudi sai min ticket ne yakuma bawa yaya din wasu kudi.
Ranan monday na dawo lagos da karfe goma na safe muka sauka lagos din bansan wazai zo daukana ba don da niya ta in shiga taxi a kaini har gida.
Amma sai ganin Sulaiman nayi shida kanshi yazo dauka na ban ma san yadawo kasar ba sai dai yanzu da na ganshi.
Bayan an gama saka kaya a motar shi ya dauki hanya dagani sai shi a motan sai da ya fara tuki ya dan kalle ni a daidai lokacin da nike mashi sannu da zuwa.
Yace ai yanzu ke keda sannu da zuwa bani ba yace yaya ki ka barsu acan nace lafiya kalau suke sun ce ai masu godiya a gun ka.
Yace namay fa nace daiwaniyan da kasha na bari na in zo masu buki har kwana goma sha hudu.
Murmushi yayi yace wanan sakon yaya saadu ne ko don shine namiji dan uwana shiya san irin halin da na shiga don ba karamin hakkuri nayi ba da na barki kika tafi.
Dan kallon shi nayi nace kai uncle kamar a gidan ka nake zaune zaka fadi haka.
Ba tare da ya kalle ni ba yace in a gidana kike ai bazaki tafi ko ina ba saar ki guda yanzu baki zo gidana ba tukun.
Ban iya magana ba nayi shiru yace zan so ace kin fara koyon nisa da mutane don na fada maki matata bata yau yana daya daga cikin abinda ya dani da mata ta tafarko.
Bayan wanan magana babu wanda ya kara furta wani abu daga cikin mu har muka kawo gida ya shiga da mota ya tsaya bai barni na shiga ciki.
Mun tsaya yana kara min korafi dadewan da nayi ban dawo ba na ce in sha Allahu zan kiyayye a gaba ya lumshe ido yana bude min motar na fito da sauri kamar wacce za a kama.
Ina shiga Faiza ne kawao zaune a falo tana karyawa tana gani na ta tare ni da fara,a a fuskan ta tare da tambayana yaya gajiyan buki.
Ban dade wurin ta ba na kwashi kayana da security din gidan ya shigo min dashi zuwa dakina ba bata lokaci na fada saman gado ina tunanen tsaurin ra,ayi irin na sulaiman daya fara nuna min tun ban shiga gidan shi ba.
Barci ya dauke ni maitsawo ban falka ba sai biyu da rabi koshi don sallah na tashi bayan nayi sallah na dan gyara kayana sai na fito falin gida.
Babu kowa a falin sai tv dake aiki shikadai a falon nan na samu wuri na zauna tare da kokarin bude wayana miscall din yaya Saadune a wayan har kira biyar yai min.
Kiran shi nayi ya dauka da korafin ina na shiga tun dazun yake kiran wayana ban daga ba har hankalinshi ya tashi sai da ya kira Uncle yace mashi na iso lafiya.
Nace wallahi yaya barci ne ya dauke ni sai yanzu na tashi naga miscall din ka yace har kin daga muna hankali kin isa lafiya ?
Nace nace lafiya na isa yaya yaya safiya da mamanta yace gasu zaune suna gaida ke mun dan taba hira yace bari na barki ki huta sai mun sake waya nagode kwarai safiya da zumuncin da kika raya.
Nace ba komai yaya ai yiwa kai ne kamar yadda shima yake yawan fada min idan yayi min wani abin alheri ina mai godiya.
Bayan mun gama waya dashi ummina na kira ina sheda mata na dawo lagos yau take tambayana lafiyan su?
Mun dade muna hira nayi mata sallama na kashe wayan tare kwantawa a daya daga kujerun falon.
Sai uku da rabi anty ta dawo gidan tashigo falon ina jin muryanta na dago mukai arba tace a a mutanen kalaba ne aka dawo ?
Namike zaune ina mata sannu da zuwa bata amsa min ba takai zaune tana cewa yaya kika barsu nace lafiya anty suna gaida ke kuma suna godiya.
Tace ina sauran mutanen gidan suke bayan ta dan bi wurin da kallo, nace da ita suna dakin su bata kara magana ba sai ta mike zuwa dakin ta kawai.
Bin ta nayi da kallo ta shige na sauke ajiyan zuciya tare da komawa saman kujera na kwanta lokacin sallah yayi na shige nima ciki.
Tunda nayi sallah ban fito ba don banji kowa a falon ba don haka nima na zauna a dakina sai bayan sallah isha,i Faiza ce ta fara fitowa sai anty.
Can na fito dauke da tsaraban da na dawo dashi a hannu na su yan biyu na gani na suka nufo ni da sauri suna murnan gani na.
A gaban ta na aje kayan ina ce mata ga tsaraban suna nan anty tace cikin nuna jin dadi wanan duka namu kice dai mu muka haihu din.
Ballan cake din tayi takai a bakin ta sai yaran suka nufuta suna fadin suma a basu suci nan suka far ma cake din da ci tana fadin yayi dadi sosai wallahi.
Fira muke yi jefi jefi sai ta jefo min tambaya da cewa Sulaiman ko yazo ya ci abinci kai na kada mata tare da fadin ban sani ba anty .
Ta juya wurin Faiza tana tambayan ta ko ya zo gidan nan itama take cewa barci tayi wayan ta ta dauko tana lalaban layin shi amma bai shiga ba.
Taji tsuki tace wayan nashi ma a kashe yake tace Fati wai ba zata fito bane komay takeyi a dakin ne har yanzu ?
Aika yara tayi su kira Fatin sai gasu sun dawo wai ta koro su daga dakin basu gama fada mata ba sai gata ta fito tana wani shan kamshi ta daure fuska.
Nan take tambayan ta ko uncle ya shigo da rana tace tun dazu ina daki ban fito ba kawar da kai tayi daga gare ta.
Fati mun samay ku lafiya nace da ita bata amsa min cikin dadin rai ba wuce wa tayi kitchen ta hado abinci ta shige dakin ta dashi.
Ni dai ban dade ba na mike zan tafi daki sai take cewa da ni dan Allah kwashe min wanan kayan zuwa sama kafin in tashi.
Na kwasa nakai mata daki na dawo na gyara wirin a lokacin tana waya sai ga daya daga cin security din gidan ya shigo yana fadin oga ya kirana a waje.
Da sauri na dan juyo ina kallon anty da hankalinta yake ga wayan ta da take dakila sai ta dago take tambaya ko waye ?
Yace da ita Uncle ne daga Fati har Faiza suka kallo ni lokaci daya ban kulasu sauraren umarnin anty nakeyi a lokacin sai ta dago tace dani ba kiran ki ake a waje ba yau ban san may ya hana shi shigowa gidan ba.
Nidai na wuce daki don in shirya yayin da Fati taja dogon tsuki sai da suka kallo ta anty tace da ita wawiya kawai.
Nafito da shiri na nayi dan simple makeup sai dogon riga dana saka mai shara shara ligt green da takalma plat nace sai nadawo ban tsamani sun amsa ni ba na fita daga gidan zuwa wurin shi.
Yana cikin bai fito ba yana hango ni ya bude kofan motar ina karasowa wani kamshi ya daki hanci na a raina nace uncle ke nan badai kamshi ba kan.
Sannu da zuwa nace dashi ya sauke ajiyan zuciya tare da karasa fitowa daga cikin motar yana amsa min.
Ya gyara tsayi yana ce min yaya gajiyan hanya naga alaman baki gaji ba na katse shi da fadin yaya akayi yau baka shigo cin abinci ba ?
Ka bar anty tana tambaya yace nayi tunanen hakan sai dai idan na shiga ne ba zan samu ganin ki ba shiyasa nayi shawaran na fara kiran ki tukun.
Nace OK,
Tambayana yayi wasu kaya nafi sakawa sai kuma yace koda yake naga kin fi son irin wanan kayan da kika sa.
Murmushi kawai nayi batare da nayi magana ba yace ina son kafin nan da sati biyu a kammala komai daya kamata ayi sai a saka ranan buki.
Nidai har lokacin ban yi magana ba sai yace ko zancen bai maki dadi bane ina magana kin kyale ni ba amsa.
Uncle may zance ni yanzu duk abinda anty tayi daidai ne ni ba ruwana a zancen yace OK yanzu bari mu shiga sauran magana mukarasa a waya tunda baki iya magana a fili.
Na sake cewa uncle ba magana na bane don Allah ka bari mana na fada a tsigar shagwaba ya nuna min hanya alaman in wuce mu shiga.
Make kafada na nayi ya gane abinda nake nufi sai ya fara hanya na biyo shi a baya a tare muka shigo falon da sallama.
Tana shirin shigewa daki sai gamu ta dago tana kallon mu ba ita kadai ba duk wanda ke falon kallon mu yake yi a lokacin da muke shigowa gidan.
Ta bishi da dan hararan wasa tana cewa ai na dauka yau yajin shigowa gidan kake yi don ko da rana baka shigo ba akace.
Yace yana zama wallahi ban gama abinda nakeyi bane a bakin ruwa shi ya dauke min lokaci tace yau kuma abin yar tsayuwa kofan gida ne kawani aiko wai a kirama safiya ?
Yace No na kirata ne taimin iso in shigo kin san yanzu kin zama antyn mu ta harare shi tace waye antyn ?
Ni dai ban zauna shigewa nayi na barsu a nan suna wasan shammatan juna su ina kokarin cire gyale naji anty ta kwala min kira.
Da sauri na fito daga dakin tace ba mutumin abinci mana kin shige daki kuma kafin in juya yace No ta barshi kawai i am ok.
Yau ban jin cin komai tace yanzu naji magana amma da na dauka ko kana yajin cin abincin gidan namu ne yanzu.
Jin haka yasa najuya zan wuce tace kaga mutanen kalaba sai yau taga daman dawowa garin kallon ta kawai nayi na dan yi murmushi .
Yace na ganta har tana wani wai bata so ta dawo yanzu don ke ta dawo garin yau.
Tace ai da baki tafi kin barni ba kika je can kika zauna abinki hankali kwance.

🧕🏿4️⃣9️⃣🧕🏿
NOVEL DINA NA KUDINE IDAN KI FITAR MIN BAN YAFE BA IDAN AN FITAR KI KA KARANTA INA BINKI HAKKINA A KAN KI.
Ina kwance saman gadona da waya a hannu na na mayar da hankalina sosai a kan wayan ina duban sako naji an shigo dakin.
Na dago don ganin ko wacece sai Fati na ganj tsaye a kaina tana huci idanuwan ta sun kada sunyi jawur dasu aje wayan nayi a gefe na duk da ban karasa karanta sokon ba.
Ta harde hannayen ta saman kirjinta ta wurga min kallo mai tattare da tsana zallah a cikin shi ta fara tafa hannu ta biyu tamai kara bina da wani irin kallo na tsana.
Zama nayi da kyau ina fuskanta ta don inji abinda take shirin fadi lalai Safiya kin cika rikkan yar yaudara kin kai maciyiya amana.
Ke yanzu bakiji kunya ba don Allah to ki sani in takaman ki iya asiri da kwatar maza yau kin kai karshe don baki da wayau yanzu ina ke ina uncle ko a kafa akadaura mashi ke ai ba zai iya ja ba.
Sai lokacin nayi murmushi nace da ita balle a daurin da akewa ko wace mace da mijin ta za ai muna kuma na dauke shi kamar yadda ko wata mace take dauke mijin ta.
Hannu ta daga wai ta kai min mari kafin hannun ta ya iso gare ni na kwashe ta da mari biyu masu kyau nace kin zo har dakina ki fada min abin da yai maki dadi ki wuce kice kinci bulus.
To bari kiji uncle kamar na aure shi na gama da yardan Allah ke ce wahalala da faman dakon son wanda bai masan dake ba a duniya.
Ashe Faiza na jin mu ita ta kira anty sukazo tare daidai Fati na fadin aure fa kikace kodai karuwanci waye baisan abinda ake turaki yi wurin shi ba banza kawai ana turaki gurin shi kina samo kudi don zubar da kai dama zubun ki baiyi kama da ta mutanen kwarai ba.
Muryan anty ne ya karade dakin tana cewa wake turata karuwancin nike nan kike nufi kowa fati ?
Da sauri muka juya kofan ta karasa shigowa ita da Faiza dakin tana cewa Fati nace uban wa ke turata karuwanci tambayan ki nake yi ki fada min ?
Nace anty wanan maganan da take fada min kullun ya isheni don ba yau ne farko fada min haka da takeyi ba wai kina turani wurin maza ina samo maki kudi.
Ko zuwa gida da nayi jiyar baba sai da ta fada min ha gashi kuma yau ta sake fadin wai kin turani kalaba na samo maki kudi wurin maza dama haka kike yi.
Inna lillahi anty ke nanatawa a gigice tana kallon Fati din takeyi rai bace tace kazafin da zakiyi min ke nan Fati sakkaiyan da zaki mayar min ke nan ?
Na dauko ki cikin wahala da lalace nazo dake nan don ki zama mutum ki dogara da kanki shine zaki saka min da wanan a gidana.
Tace da kike fada a kan sulaiman ya ko san da zaman maki a duniyan nan halin ki na banza ya barki ki aikata alheri ne ne fati ?
Karshe kasa karasa magana tayi nasan takaici ya rufe ta sai juyawa tayi ta fice daga dakin rai bace.
Muka dawo da kallon mu ga juna sai gata ta juyo tace ki fice daga dakin nan tun raina bai karkare baci ba Fati.
Ta kalle ni taiyi kwafa tana cewa kin ci bashin marin da kikai min don sai na rama abina ki sani nace daga baya ke nan na nuna maki ni yar kauyen gidi ne.
Ta fice fuuu anty ta mara mata baya suka fice aka barni da gani sai Faiza tace don Allah Safiya ki boye ni kada ki fadawa anty anbin da nace hannu na daga mata nace Faiza ki fice please.
Batayi musu ba ta juya ta fita daga dakin simi simi na sauke a jiyan zuciya tare da komawa saman gado na zauna ina tunane ni may ye laifina a cikin maganan da bazata samay shi da maganan ba shi da take so.
Na dade wurin zaune na rasa amsan da zan ba kaina dole nake kwance ina ci gaba da tunane a raina sai da naji yunwa na iya fitowa don neman abinda zanci don ko karyawa banyi ba ta samayni da magana.
A falo na ga Faiza zaune wuce ta nayi zuwa kitchen batare da nayi mata magana ba na hado abinda zanci na dawo zan shige sai naji tace Safiya fushi kike yi hardani ne wai ?
Nace fushi akan may aini Allah yayi min fada akan may zan tsaya bata lokacina kuma aida ban gode masa ba.
A gaban anty ta nanata da kunnen ta taji ai hali shike nuna kansa wanan ya nuna bata da alhakin ku kuke fakewa a bayan ta kuna mata sheri har na gama na wuce bata ce dani komai ba.
Ban iya cin abincin ba don raina ya na bace har lokacin twin's na ta shigo tana ce dani maman su na kirana abinda ya sani fitowa kenan.
A falo take zaune ga Fati da Faiza a zaune suma na samu wuri na zauna in ji abinda zata ce muna.
Mun zauna shiru sai can ta nisa tace Faiza ta amsa naam Safiya nima na amsa mata da naam Fati ta amsa mata ciki ciki da naam.
Tace na koraku nan ne don in yi magana da ku baki dayan ku akan abinda ya faru dazun tsakanin Fati da Safiya a gidan nan.
Banyi mamakin jin abinda kika fada ba don nasha jin ire iren wa yan nan maganganu daga bakunan mutane dake fitowa daga bakin ku.
Amma wanan yafi min munin saurare don da kunuwa na naji ba wani ya fada min ba sai fatin tace ni may na fada anty maganan mu mukeyi kawai.
Kina rufe min bakin kin ki ko sai ranki ya baci yanzu in maki tsinanen duka anan sai ta ja bakin ta tayi shiru tare da dukar da kanta kasa tace idan da banji ba sai ince kaka tayi maki.
Ba wani ya fada min ba ni naji da kunne na abinda kika fada kenan ni ke tura ta wirin maza tana samo min kudi kike nufi.
Ta dago za tai magana ta tare ta da tsawata yana fidin tayi shiru dole ta sake kyalewa tai fada sosai a cikin bacin rai sai ta juya kan Faiza tana cewa.
Aure Safiya zatayi nan da dan wani lokaci zan iyacewa nan da dan lokaci mai zuwa bazaku ce baku san da zancen ba.
Don haka zan iya hakkurewa har lokacin da tayi aure wace taga zata iya zama dani ta zauna bazan kori kowa daga cikin ku ba don ku kuka kawo kan ku na.
Sai dai idan na sake jin wani rikici a tsakanin ku kafin wanan lokacin dukkan ku rayukan ku zai baci dani amma ke fati tun yanzu nasan matakin da zan dauka a kanki.
Gida zaki koma don ba zan yarda ki bata min suna a banza ba da abinda banji ban gani ba ki dora a kaina duk wanda yaji wanan zancen sai yace idan baki gani ba baki fadi.
To komawar ki gida shi yafi zama alheri a gare ni don haka sai ki shirya next week zan sa a kai ki gida kafin in zo muyi maganan a can.
Hakkuri ta shiga bayarwa sai ta bani tausayi ban san lokacin da nace don Allah anty kiyi hakkuri.
Ta dago kai ta kalle sai na saukar da kaina a kasa na kara fadin don Allah anty kiyi hakkuri sherin shedan ne .
Kina ji da bakin ki abinda ta fada akaina kuma kince ba yau ta fara fada maki haka ba sai fati tau sarin cewa wallahi bani na fada ba Faiza ce ta far fadi nima naji na fada.
A take Faiza tace kada kimin sheri yaushe na fada ta juya gare tana cewa wai Safiya ranan wa kiji ya fada har muka baki hakkuri akan karki bari anty taji zancen.
Murmushi nayi nace anty don Allah kiyi hakkuri da zancen in ma har suna hasashen haka ne a ransu ai Allah shiyasan gaskiya.
Haba haba kuyi min adalci mana maye laifina na ajeku a gida na danayi tare dani ?
Idan bani ba wacece zata ajeku haka a gidanta amma tunda ku kuka kawo kanku gareni na karbe ku hannu bibiyu na zauna daku may na rage ku dashi a gidan nan na jin dadin rayuwa.
Duk mukai shiru muna sauraren ta tace ke Faiza ai akwai gidan anty Ai a abuja may yasa baki je can kin zauna ke kuma akwai gidan anty mami a kaduna ai uwarku daya may yasa baki tafi wurin ta ba.
Sai nan bayan haka da halina ne hakan da ku da kuka riga Safiya zuwa nan aida daku zan fara ba Safiya da tazo daga baya ba.
Ko don ita din ta fiku kyau kuke tsamanin haka zanyi da ita toni aure na hada don raya sunnan ma,iaki SAW ba yin zina ba yadda kuke tsanmani.
Allah ne ya yanke mata wahala da zuwanta ta samu miji ku da kuka dade da zuwa aida aikinane hakan akwai maza da yawa may zai sa ban hada ku dasu ba ku samo min kudin ko ku ba mata bane yan uwanta.
Faiza tace munyi kuskure amma kiyi hakkuri ba a karawa in Allah ya yarda ta ja tsaki tare da kawar da kanta gefe.
Nan muka zauna zugun zugun damu ita dai bata sake magana ba sai duban tv da takeyi tana sauke ajiyan zuciya kawai.
Nice na fara mikewa na bar falon zuwa daki ban san lokacin da sauran suka watse ba tun wanan ranan aka rage yawan gulma a gidan.
Sai dai ban yarda na sake wa Faiza dake yawan shige min ba wai ita ala dole tana tsara yadda zamuyi buki in ya taso.
Na fito daki da safe na samu anty a falo don yau ba ranan fitanta aiki bane don haka mukan wuni da ita a gida bata fita ko ina a wanan ranan ne takanyi gyaran jikin ta.
Sai yanzi na gane hakan da nake zaune a gidan ta ina fitowa tare da gaida ita tace yauwa Safiya kin fito don Allah ki taimaka min da kan nan nawa.
Yau kitso nake so da gyaran jiki tace yan biyu ta dauko mata kayan kitson su nan na zauna muka fara banyan kai muna hira sai ga Faiza ta fito zauna nan take fada mata ai kan yayi dauda nan dai mukai ta mahara karshe dai tace zataje wankin kan.
Wayana dage gefena ne yayi kara alaman sako ya shigo min a lokacin ban dauka ba sai anty ta lura dani take cewa in diba mana ko soko ne mai muhinmanci.
Ga abinda na gani rubuce ga sakon.
Safiya badon na isa ba sai don girman Allah Safiya ki taimaka ki kashe min wutan kaunan ki dake famar kunar zuciyata har kullun, Safiya ina sonki ina kaunar ki wallahi wallahi ina son ki tsakani da Allah, Auren ki nake so don auren ki alheri ne a gareni.
Ki taimaka ki kirani a wayan ki inji muryan ki don in samu natsuwar gudanar da ayyukan dake gaba anan idan kina raayina ki kirani inji muryan ki Sulaman Habbi Bauchi.
A hankali na runtse idona bayan karanta sakon ina sauke ajiyan zuciya sai kuma gabana ya fara bugawa a hankali kamar zai tsage min.
Ganin sakon na rinkayi kamar a mafarki na shiga tambayan kaina may ya kawo wanan sakon haka har uncle ya tsaya ya rubuto min shi.
Na sake tambayan kaina may ke faruwa ne wai muryan anty naji tana cewa dani kin gama karanta sakon ki sance ma su yan biyu nasu muje a wanke muna.
Cikin dauriya na amsa mata da eh sai dai saukina kitson kan su ba wani mai yawa bane ina gamawa na shige daki don ban da kwanciyar hankali a tare dani a lokacin.
Acan kuma uncle one two ya duba wayan shi yana tsamani ko sakona zai shigo kai sai yaji shiru hakan yasa ya fara zargin ko maganan da yaji ya zama gaskiya a kaina.
Zama nayi ina kara karanta sakon sai zuciyana ta bani cewa da Allah fa ya hadani mai zai hana na kirashi inji komay ke gudana.
Yana zaune a office din shi na abuja tunane na kawai ya keyi akan don may zanyi mashi haka bayan tafiya ya nisa in nemi canza raayi a kan sa kuma.
Sai yaji kira ya shigo mai a waya da sauri ya dauko wayan don ya matsu ya dauki wayan ya tabbatar da zargin shi.
Yana dauko sunana ya baiyya na fuskan wayan sai da yaji gaban shi ya fadi don bai san may zan fada mai ba.
Ya amsa wayan da hello,
Murya kasa kasa nace mai salamu alaikum.
Ya amsa min da wa, alaikumu salam Safiya, tare da karfin halin cewa yaya naji muryan ki a sanyayye ?
Murmushi yaji nayi wanda ya fara kwantar mai da hankali nace haba uncle wanan irin sako ai sai ka tayar min da hankalina.
Bancin kasan ka riga ka gama daure zuciyana da sarkan kaunan ka kasan yadda na dauke ka da muhinmanci .
Uncle kafi kowa sanin kunya ke hanani kiran ka kan ina matukar jin nauyin ka da kunyar ka fiye da kowa yanzu.
Shine kuma zaka rubuto min sakon da ya tayar min da hankali kasa zuciyata cikin kwankwanto tun dazu.
Ajiyan zuciya naji ya sauke ya gyada kai tankar ina ganin shi yace safiya ina son ki sani yau da baki bugo min wayan nan ba sai ince abinda ake fada a kanki gaskiyane.
Da sauri nace Uncle may ake fada a kaina kuma yace forget it, bar zancen kiyi hakkuri amma ina son ki sani akwai ta inda aka fara ma zancen mu zagon kasa .
Amma ni kaina na yi tsamanin haka tun farko yanzun dai ina son ki sani ni kaina ba karamin kokari nayi ba da na iya turo maki sokon nan don in tabbatar da zargin da nakeyi maki.
Luckyly sai gashi kin kirani din kamar yadda na bukace ki kiya kin ga hakan ya tabbatar min da cewa akwai matsala kenan.
Shiru mukayi dukkan mu na dan wani lokaci kowa na tunane a ranshi kawai sai yaji na fara yi mashi kuka a wayan ina fadin ni may nayi wa wani da yake son rabani dakai ?
Safiya come on ki tsaya ki saurare ni kada wani yazo ya samu kina wanan kuka haka kuma a san abinda ake ciki.
Ki saurare ni kiji idan da ana iya rabamu da tun farko na dauki maganan da muhinmaci a zuciya na kwata kwata ni maganan bai tsaya min azuciya ta har da zan daukaba.
Haka kuma idan baki daina kukan nan ba mai sakon zai fahinci mun samu matsala dake .
Sanin mun rabu lafiya dake last week yasa kawai nayi tunanen in gwadaki in gani da kwata kwata ba zan taba barin ki san abinda ke zuciya ta ba to amma ba zan iya bane wallahi na kasa daurewa sai da na jerabaki yanzu share hawayen ki muyi magana na fahinta a tsakanin mu.
Share fuska nayi kamar yadda ya bukata ina fadin don Allah uncle may aka fada ma a gamay dani ne wai ?
Naga tun farko ba a boye maka komai nawa ba, nisawa yayi yace baki jin magana ko ta bari in kashe wayan tunda baki tsayawa ki saurare ni.
Na nisa nace uncle kayi hakkuri amma gaskiya maganar ne koda banji ba akwai cin rai don sheri baida kyau sam wallahi.
Kalmomin da nakeyi tuni suka jefa zuciyar shi a cikin tunane fiye da musali saboda bai taba tunanen haka ba da tun farko in yasan za a samu wanan matsalan ba zai tsaya har muyi nisa haka ba
Amma a fili cewa yayi dani come on ba nace ki manta da komai ba kiyi kamar bakiji komai dake gudana ba, idan na zo zan maki bayani yadda zaki fahinci abin
Ko kinfi son ki tadda min da hankali anan har in kasa yin aiki aiwatar da ayyukan dake gaba anan.
Shiru nayi ina sauraren maganan shi karshe na kashe waya ina mai bin lafiyan gado na tunane kuma yazo ya lulube a wirin.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , , , ,
🧕🏿5️⃣0️⃣🧕🏿
NOVEL DINA NA KUDI NE NA FADA MAKI TUN FARKO INDAN KIN FITAR BAN YAFE MAKI BA IDAN KIN KARANTA BAKI BIYA BA ALLAH YA ISAR MIN.
Yanzu ni yar uwa may zace dake tunda tun farko na fada maki kada ki fitar min ai kadan kika gani ga wanda bai tsoran Allah .
Nace tun farko kada ki fitar min da novel kin dauka kalman Allah ya isa wasa ne sai da abu ya cika dake zaki dawo kina na yafe maki.
Baki san ni ba baki kuma san inda na fito ba ina dai novel kina karantawa nace ga yadda nake son abina baji ba yanzu kizo min da wani magana ban damu ba tunda tun farko na fitar maku da hakkina na fada maku ban son a fitar min ke da sauran kadan kuka gani muje zuwa indai nice kullun ya diga bibiyar ki ke nan ai tunda kin zabi kalman Allah ya isa to ya isar min din sai may kuma ni na gama magana na ai tun shekaran jiya ku kaka rage da raddin ubangiji kuma.
Tun safe ban tashi ba ina kwance kamar mara lafiya nake jin kaina ko abinci bam iya fita na nemo ba din ban majin cin komai a raina.
Dawowan su anty da yara danaji hayaniyar su yasa ni mikewa na shiga ban daki wanka nayi na fito na shirya don ina fashin sallah a lokacin.
Bayan na gama shiri ne na nufi part din anty don in mata sannu da zuwa a hankali nake hawa steps din na kawo daidai window din ta dake bude naji ta ambaci suna na har zan wuce sai na tsamaci ita da wani ne a dakin sai daga baya na gane waya takeyi ashe.
Naji ta sake fadin anty uwa na fada maki na Safiya mai sauki ne nasan abinda zan fada mata gamay da sulaiman din ta fahince ni.
Shidai sulaiman din ne yanzu shawo kanshi abune mawuyaci da sauki don ban taba zaton zai mutu ga son yarinyar ba haka.
Shiru tayi tana sauraren maganan anty uwa din sai naji tace gaskiya anty ni safiya bata taba yi min komai ba harda zan mata korar kare a gidana.
Don yarinya nada hali mai kyau wallahi don duk tafi min wayan nan kattan bazan dana tara Fati da Faiza.
Ke dai ki bari mubi abin sannu dan Allah a samu a rabu lafiya da ita ba tare da ta fahinci komai ba.
Anty uwan ke magana ta tsaya tana sauraren ta sai naji tace ba haka bane Anty uwa wallahi wallahi sam ban kawo Nafisa a raina in ba don kinyi magana ba yanzu ai mai sauki ne tunda ba aure aka daura masu ba dashi.
Anty uwa din ke magana sai naji anty tace gaskiya ne zaman ta haka a gida kan baida amfana gaskiya zan san duk yadda zan yi ya koma ga Nafisan batare da an samu matsala ba.
Shiru tayi anty uwana magana sai naji anty din tace Safiya bata da matsala zan san yadda na raba ta da son shi ai don ba wani wayewa tayi ba sosai.
Naji tace to sai kin shigo din next week ina expecting din zuwan ku din ai kafin nan ma tun yanzu na fara aiwatar da shirina a kan su ko may tace mata naji tace ba hakana bane Allah anty yarinya ta bani tausayi ne don wahalan da tasha tun farko a gidan mijin ta.
Anty uwa din ke magana ta tsaya sauraren ta alokacin na yo baya baya tare da dafe bakina dake shirin sake kuka asirina ya tuno gaida ita da banyi ba ke nan na dawo daki na.
Sai ranan naga amfanin rashin zaman da su fati basuyi a falo don ko yau yai min rana sosai inba don haka ba da wani yana iya ganina a cikin su.
Ina shiga daki na rufe tare da fadawa kan gado na sake kuka mai tsuma zuciyan mai saurare na ina kiran sunan Allah da karfi nace ni Safiya wanan irin bahagon rayuwa da nake gani damay yai kama haka duka duka shekarana 21 amma gashi ina ta haduwa da kaddarorin rayuwan duniya.
Yanzu idan sulaiman ya kubbace min ina zan sa kaina ko sherin inna ya isheni a gidan mu ai da mutanen garin.
Zuciyana taban amsa da fadin ki rike Allah don yana sane dake mai hakkuri baya tabewa a duniya.
Haka yasa naji wani kwarin gwaiwa yazo min sai na dakatar da kukan da nake yi ina neman wa kaina mafita zancen tunane na ya tsaya akan in bar gida kawai shi mafita gare ni.
Ban tsaya yin wani shawara ba na mike na fara hada kayana a cikin trolleys dina sai da na shake su da kayan da anty da sulaiman sukai min guda biyu na saka sauran komatse na a baccon da na dawo dashi daga kalaba.
Komawa nayi na zauna a bakin gado ina tunanen abinda zan fadawa anty idan zan tafi don na fasa gudun da nayi niyar yi kada su dora min sata banji ban gani ba tunda mafita suke nema a kaina dama.
Ina nan zaune har yamma yayi min sai na fito falo don dama ina jin motsin su a falon ta kalloni fuska sake tana cewa dani ina kika shiga tun dazun muka dawo.
Nace wallahi barci ya kwashe ni daga dan kwantawa in huta sai na dauki lokaci ina barci Faiza dake gefen ta zaune tace ai da banji motsin ki ba nayi tunanen haka.
Tambayan da anty ta jefomin ya hana ni magana tace kun ko yi waya da Sulaiman yau Safiya ?
Sai na samu kaina da yi mata karya da cewa bai kirani ba anty tace nima haka kwanan nan akwai tsiyan da yake ji wata kila yaji wani magana ne yake son ya ja baya kuma.
Murmushi nayi nace in haka yafi alheri a gare mu Allah ya kawo muna saukin rabuwa tace nima shina gani dama can ba son aure yake yi ba da ayi yazo ya kawo muna wani matsala gara tun wuri dai a watse.
Nuna mata nayi maganan bai damay ni ba naci gaba da harkana tai shiru ta shiga dogon tunane sai can security din su ya shigo yace tana da baki a waje.
Ganin ta tashi yasa muka watse wurin kowa ya shige dakin shi kofana na rufo don magariba yayi a lokacin gashi kuma ina fashin sallah don haka sai na jawo tasbahana ina ja kwai.
Kiranshi ne ya shigo min na dauka a sanyaye da sallama na yayi saurin cewa dani yaya kuma naji muryan ki kamar baki da lafiya ne ?
Kodai zancen jiya kika sa a ranki yake damun ki kuka ne ya zo min shiru yayi yana saurare na tun yana fadin subbahanallahi har ya kyale ni ina tayin kukan.
Sai naji ya kashe wayan bai fi minti talatin ba ya kara kirana na dauka yace look ki tsaya ki saurare ni ban son wanan kukan da kike yi kamar ance za a kwace maki ni.
Murmushin dole yasani yi nace uncle ba haka na bane yace to yaya ne kin bi duk kin tayar min da hankali har jirgi nace a bincika min da daren nan saboda rudani da kikayi ba a samu ba.
Nace cikin dan kuka Uncle gida nake son wuce wa gobe in Allah ya kaimu da sauri naji yace saboda may zaki koma gida gobe shiru nayi kawai ina sauraren shi.
Sai da ya gama cikin kuka na fara fada mai abinda naji anty da yar uwar mijinta suna tataunawa a kaina.
Yace oho dama nufin su ke nan shiyasa tace min ba sona kikeyi ba don dan uwan tsohonijin ki dake kalaba ke kike so.
Watau gani mutumin banza zasu gara ni yadda suke so ki saurare ni kiji ni zan tsara yadda zakiyi tafiyan gobe zan kiraki in sanar dake yadda mukayi da ita kafin goben kada ki kashe wayan ki kinji ko na amsa da eh.
Naci gaba da tunanen zancen nace a raina watau anty uwa ita keson anty ta hada diyarta da Sulaiman shine suke son raba mu.
Nasan anty uwa tun zuwan mu Abuja bude company sulaiman din da mukaje yi wata yar bariki ne don idon ta ya bude sosai don ko shigan da tayi a wurin sai da nayi tir da ita da diya ta wai ita wayewa ke nan.
Yaran ta mata uku tazo dasu wajen biyu sun yi aure amma sun fito ita kuma babban ko auren batayi ba zata kai shekara talatin kila .
Itace ke nan ake son a hada ta da sulaiman nace to ke nan itama din victims ce na HIV komay don naji sunce a huta da ita.
Ban yi barci ba zuwa goma da rabi naji ya kirani yace gobe zaki kibi jirgin safe karfe bakwai za a kaiki airport na fada mata jikin baban ku ne ya tashi aka kirani kuma ina son ki koma gida har yadda hali yayi.
Ta amice don naji tace abin ma yazo da sauki don haka idan ta tambaye ki ki fada mata yadda na fada maki din nayi mashi godiya mukai sallama na kashe wayan.
Muna gama waya dashi na bi gado na lafe kamar ina barci sai gashi an turo kofan ddakin naji tana cewa kin yi barci ne Safiya ?
Na dago da sauri ina fadin yanzu na falka tun tara barci ya dauke ni daga karatu a waya na yanzu fitsari ya taddani ta samu wuri ta zauna tana cewa mutumin ya kiraki ne nace bai kirani ba anty.
Tace yanzu na samu wayan shi wai an bugo mai daga gidan ku mahaifin ki jikin shi ya tashi don haka gobe ki shirya kije gida.
Rudewa nayi ina salati tace ki kwantar da hankalin ki nace shine basu kirani ba anty tace ai sun kiraki wai basu samay ki bane tace ai nima nayi mashi wanan tambayan.
Ta mike tana cewa sai ki shirya goben karfe bakwai jirgi zai tashi yace a sayo maki ticket yau da daren nan za a kawo muna.
Ta fara tafiya sai ta juyo tace dani ina ganin zaki dauki lokaci a can don haka ki debi kaya masu yawa da zasu isheki zama nace cikin rudewa tau anty.
Tana fita na daga hannu sama inayiwa Allah godiya da ya bani mafita da saurin tun ban wulakanta ba a gare su.
Karfe shida na gama komai ban bar komai na wa ba a gidan don nasan ko na bari ba a amfani dashi katshen ta yarwa zasuyi ko su kona.
Security ya gama samin kaya a mota Faiza ce da tayo min rakiya take fadin wanan uban kaya da kika kwasa haka safiya kamar wacce bata dawo wa.
Nace zan rage kayan ne shiyasa na kwasa don in bawa mutane can a gida tace haka na da kyau kuma.
Anty dake bayan mu saye da hijjabi tace Allah dai ya kaddara saduwan mu da alheri ki gaishe sai munyi waya inji saukar ki da lafiyan baban tana magana da gani tana cikin bacin rai.
Na tako gaban ta nace anty na gode Allah ya saka da alheri ki yafe min zaman da mukayi tare idan na saba maki ki gafarce ni anty nace wa Faiza ma haka tare da yi masu sallama na shiga mota ta rufe.
Motar na fita na lumshe idona hawaye na zuba min ji nake kamar ba zamu sake haduwa ba daga nan.
Ita ko anty tun barina gidan sai maganana ya tsaya mata a rai hartayi wanka tana tunanen zancen mu da nace duk abinda nayi mata ta yafe mun.
Tana shirya wa dakina tayo bude ta shiga kallon gadon tayi dana gyara kafin in wuce tace badai tsabta ba safiya tawuce wurin wardrobe dina ta bude sai wayam babu komai a ciki sai zanin gado dana bari nasu.
Da sauri gaban ta ya fadi tace kardai yarinyar nan ta fahince ni ne ko may nake plain a kanta da sauri ta dauki wayan ta tana kiran driver ya dauka tace bani Safiya yace ai jirgin su ya daga gani hanya dawowa gida.
Zama tayi saman gadon tana magana ita kadai tace sam bata ji ba sai dai idan yadda tace ne zata rage kayan a gida.
Da wanan tunanen ta mike ta bar dakin zuciyar ta fam da tunane a ranta tana fadin haka ma yafi sauki da sai anty uwa ta zo suyi mata korar kare a gidan gashi ba mutunci je da su ba.
Tun da muka daga babu abin da nake tunane banda zama na da ita tun farkon haduwan mu da tazo tana tamnayan ko nan ake kitso wata yar wajen aikin su ce tai mata kwatance dani nakai kallo na ga ayan tagwayen ta nace nan ne anty gashi kuma yamma yayi tace ko yaran nayiwa don gobe monday nace to su zauna sai na sake kan wace nakewa kitso na shiga na dauko ma yaran abin sha na kawo masu.
Matar dake zaune tace na nuna masu banbanci su da suka dade da zama ko ruwa ban basu ba sai wanan da tazo yanzu.
Nace ai Sister dina ce ita dole in karrama su naga masu kitson harda ita kuma naki karban kudin lokacin ne Ahmed ya dawo tana jin fadan da yake min akan na tsaya kitso har dare .
Da na fito take tambyana mijinane na bata amsa a sanyayye da eh tace shine yake maki fada akan neman kudi tun wanan rana mu ka saba da ita.
Gashi yau wani matsala ya gitta a tsakanin mu har yana son raba mu da ita lumshe idanuwa na nayi ina mai ci gaba da fitar da hawaye.
Bamu dade ba muka iso abuja da sanyin safiya sai ka dauka a nan muka kwana shida kan shi yazo dauka na yana saye cikin suit irin na maza farare kayan sunyi matukar karban jikin shi sosai.
An gama sa min kaya a mota ya bude min na shiga sai lokacin yayi min magana naji yace ta gudu an iso lafiya ?
A jiyan zuciya na sauke na amsa da lafiya lau yace kin sa mun yi wa baba karyan ciwo Allah ya kara mai lafiya nace amin na gode.
Yace ina mamakin mutane yanzu son kai sai yasa mutum yayi abinda ba halin shi ba sam na rasa gane yaya akayi madam ta yarda wanan matar tayi convices din ta haka.
Hauka nakeyi ko matsuwa nayi da yin aure ai ba zan taba auren Nafisa ba a rayuwa na bayan ta gama watsewar ta a titi ace za a dauko a kawo min gida na barin ga iya gudin su ai.
Get din gidan aka bude ya shiga da mota ni dai ban yi magana ba har lokacin yace ki huta driver yana zuwa yanzu zaku tafi.
Muka fito daga cikin motar shi yayi min jagora zuwa cikin gidan a falo nan muka zube dukkan mu yace yanzu dai hankalin ki ya kwata ko kin gudo wurin antyn ki.
Murmushi nayi ina gyara gyalen kaina nace abin ne ba dadi ni tsoro na kada anty uwa su zo su samay ni a gidan don ban san abinda zasuyi min ba.
May zasu yi maki kuwa banda suyi haukan su su wuce ai ita madam tana da hankali nace haka dai yafi mun an rabu lafiya gida zan koma gidan mu ya fiye min komai zan zauna har ranan da Allah zai kawo min dauki.
Dariya yayi yana mikewa yace ko kin zo ke nan sai in bugawa baba a daura muna aure ke kin tare ko da sauri nace hai uncle abin kuma yar zolaya ne ?
Yace Allah ba wani abu bane ai sai kawai a dauro aure ke kin riga kin tare nace ba aikaina za a fara ba ni dai driver bai iso bane mu kama hanya.
Yace amma dai kya bari ki karya ko ga table can an hada muna tashi ki yi breakfast ki huta sai ku wuce.
Nace ban jin cin abinci ne Uncle yace kina wasa ne maza tashi kici abinci ko in hanaki tafiya yau da sauri na mike ban ci wani abin kirki ba sai dai na dan taba kadan sai ga driver ya shigo yana gaida shi.
Nima gaida ni yayi tare da min sannu da zuwa na karba mai fuska sake don mun saba dashi dan haduwar da mukeyi.
Key ya karasa inda suke ajewa ya dauka yana cewa zai fita yayi services din motar yace mai sai ya dawo.
Yana fita ya fuskance ni tare da cewa jinan sai na tattaro hankalina zuwa gare shi yace idan kin je gida yau ina ganin next week magaba tana zasu shigo.
Don a daidaita maganan auren mu ban son abin ya dauki lokaci mai tsawo tunda kin ga an fara samun matsala a ta inda bamu zata ba.
Don haka next Saturday in sha Allahu iyayyena zasu zo sai a saka muna rana dan naga amaryan nawa har yanzu hankalin ki bai kwanta ba.
Murmushi nayi tare da fafin Allah ya kaimu lafiya amma ni ai ban tayar da hankali na ba don nasan komai Allah ke yi .
In bashi ba ina ni ina ja da yar wurin anty uwa wa yan nan yan gaye wa yanda boko ya ratsa su ciki da bai din su ai sune suka dace dakai.
Murmushi yayi yace a naki ganin ke nan ni sam bani rayin irin su nafi son wacce zan iya controling ba tayi controling dina ba ko may kika ce ?
Nace Allah yasa mu dace yace amin mun ma dace din sai dai muyi adduan Allah ya hada hankali baki daya.
Driver ya dawo bai dauki lokaci ba muka kama hanya bayan sun gama ganawa da maigidan nashi ni kuma ya cika min jakkana da kudi wai don bukata acan .
Yace ba lalai bane mu hadu da sauri don zaiyi tafiya cikin wani sati don haka koda zasu zo yana ganin ma bai kasan.
Da haka mukai sallama dashi muka dauki hanya sai garin mu zuciya na cike da damuwa don ban san zan zo gida ba a wanan lokaci.
Mun shigo da dan sauran lokaci don sam bayi tsamanin cewa an gama ginan gidan mu ba har sun tare a ciki.
Sai driver ne naga yaja ya tsaya a kofan gidan mu nan na fara raba ido ina kallon aikin da sulaiman yayi mu agidan muna tsayawa su yaya Sani dake daban su suka taso da saurin don ganin motan da tazo kofan gidan namu.
Ina fitowa suke fadin a safiya ashe ke ne tafe yaya sani da ke kokarin kama marfin kofan ya ce safiya lafiya kuwa ?
Na kalleshi da murmushi nace lafiya yaya mun samay ku lafiya ?
Ya amsa da lafiya aka fitar min da kaya zuwa cikin gida ina biye dasu duk kan gidan ya juye min kamar ba dan kangon gidan mu ba.
Dakin ummi suka nufa da kayan nawa ana cewa Safiya duk suka firfito waje din taro na da murnan su
Sai mamakin tsarin gidan nakeyi ina mai kara bin ko ina da kallo muryan mama naji daga baya na tana fadin kina kallin ikon Allah ko.
Kin ga yadda ubanigji ke nasa ikin haihuwar mace yayi muna rana a gidan nan don gashi ta mayar damu yan birni a lokaci guda har wutan Nepa mun samu bana.
Nayi dariya nace mama mun samay ku lafiya tace aikece abin gayarwa keda kika sha hanya mai nisa.
Takalmana na cire na shiga dakin ummi tana zaune saman kujeran da aka saka masu a falon na rungumo ta sai ta ture ni tana cewa rabani da abin kunya kiji.
Nace kai ummi har yanzu kunyan ne haka takalman da na cire kanne na suka dauka suna kallo gardama ya kaure a tsakanin su wanan yace kwalba wanan yace roba ne da filawa cikin sa.
Dukawa nayi ina gaida ummi ga hasken wutan lantarki da ya haska dakin ya baiyyanar da farin da lafiyan da na kara a lokaci guda.
Daidai inna ta tunkaro dakin a take taji wani irin tsana na ya shiga zuciyar ta lokaci guda cikin yake tace Safiya ne yau gidan namu.
Da sauri nace eh inna mun samay ku lafiya ina saadatu tace ai tana tafe na barta daki ne wai kan ta ke ciwo yau nace ayya ai gani tafe in duba ta.
Kanne na suka kwashi kayana zuwa kuryan dakin ummi sai bin ko ina nakeyi da kallon mamaki acan ma da na shiga an gyara shi tsab ga gado har da sphare din kujera dogo.
Na aje jakkana na fito zuwa duba saadatu a dakun su sai muka hade da ita ta taso da kyar muka koma dakin nasu nan naga watau kowa da kalar kayan da aka saka mai a dakin shi.
Munyi yaushe rabo da saadatun inna tana kurya tana jin mu saadatun ke ce min komawa zanyi ne ko zan kwana biyu .
A nace cikin dariya a a saade na dawo kenan sai yadda hali yayi kuma tace kice muna nan ke nan dake kwana biyu nace kwarai da gaske.
Nan dai muka sha hira da ita na tashi ina cewa zan tafi in gaida mama dakin ta.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGN , , , , , , , , , ,
🧕🏿5️⃣1️⃣🧕🏿
NOVEL DI NA NA KUDI NE NA FADA TUN FARKO KARKI FITAR KARKI KADA KUMA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA BA, CIN AMANA BIBIYA TAKAI TA INDA BAKIYI TSAMANI BA, , ,
Tun farko na fada maki karki fitar min da novel don karatun ba dole bane ba kowa nake ba amma nasan Allah ya isana dama bai tafiya ga banza.
Bakiji bake kaida bane don akwai wata mai fitar wa bayan ke ke ce kika fara gani saura dayan nata sai yafi naki don ko abin ba zai zo mata da dadi ba ita.
Akan novel akan son kai tajawa kanta masifun duniya sai da na fada maku dan Allah kada ku fitar min don kada in dauki alhakin ku a kaina.
Kullun ina nanata maku kin dauka wasa ne ba abinda zai faru dake har yau kaf makaranta novel dina ba wanda zaice maki yasan makawa ko ya san ida take da idon shi hmmm muje zuwa yanzu aka fara ai ya kama binki ke nan ta hanyar dabaki zata ba yar uwa.
Ganin gidan namu nakeyi kamar bakon wuri a idona don komai ya canza min a idona sai nake jin wani irin dadi a zuciya ta.
Ranan barci dai ne barawo da ya iya dauka na safiyan fari kiran sallah masalacin da Sulaiman ya gina wa mutanen unguwar mu ya karade min kunni na dole mutun ya tashi saboda karan lasifikan da yai yawa.
Duk da bani sallah amma na tashi a lokacin na kewaya na dawo na kwanta ban iya kwaciya ba na mike zan fita don shara ummi na dake falo kwance ta dakatar dani da fadin.
Dama kin koma kin kwanta don ko dan Albarkan nan ya rabawa kowa wurin ta don haka yanzu ma ba komai akeyi a gidan gaba daya ba.
Na koma na kwanta kamar yadda ummi ta umurce sai dai ba barci nayi ba kwantawa kawai nayi zuciya ta fam da tunane.
Misalin sha daya saura na safe na fito saye cikin kayan barci na da ban cire ba a falo na samu ummi da kanne na suna karyawan safe tayi masu faten doyan da nazo masu dashi jiya.
Na fada saman kujeran da babu kowa saman shi don kasa suke zaune dukkan su tare da yin mika nace duk na gaji kamar nayi wani aiki mai yawa.
Ummi ne tace min ai tafiyan mota mai nisa gajiya yake sawa mutum ajiki na gyara kwanciya ina fuskantar su dakya nace ai rabin tafiyan a jirgi nayi ummi daga nan dai zuwa abuja ne ya saukar min da gajiyan.
Tace masu gari yau kece mai tafiya a jirgi yar nan lalai duniya abin da ya baka tausayi wata rana shi zai baka mamaki.
Kwarai da gaske ummi wallahi ni kaina ganin abin nake kamar a mafalki don nakan yi tunanen hakan a raina.
A jiuan zuciya naji ummi tayi tace mhmm ai tun dawowan mu gidan nan yau sati uku ke nan inna ku sai ta baka tausayi don zaman ta a babban gida ta raina kanta sosai a can don basu raga mata ba ko kadan.
Tace yaya wajan anty naki suna dai lafiya ko bansan adduan da zawa wanan matar ba a rayuwana sai dai fatan gamawa da duniya lafiya.
Shiru nayi ina mai ci gaba da tunane sai da naji ummi tace yanzu yaushe zaki koma naga kin kwaso uban kaya kamar baki da niyan komawa can.
Nisawa nayi na dawo daga tunanen da nakeyi nace ummi ba zan koma gidan anty ba indan ba aure nayi ba in je in gaida ita.
Da sauri ummi tace akwai matsala ke nan a tsakanin ku ganin kanne na dake zaune sun kallo ni lokaci guda yasa ni cewa babu komai haka dai na yanke a raina.
Shiru naga ummi tayi sai can tace a zubo maki faten ne kishashi da zafin sa tun baiyi sanyi ba ki kasa sha barshi ummi ban iya cin abu mai nauyi da safen nan.
Sai kaunana tace ai kin san anty Safiya bata son cin abinci ummi kina dai wahal da kankine sai zuwa rana zakiga tana neman abu mai ruwa ta sha shi ne karin kumallonta ita.
Ummi na mikewa take fadin mukan na kauye ne sai da abu mai dan nauyi muke jin dadin karin Safe don badon doyan nan da kika zo muna dashi ba da shin kafa da wake zan masu da safen nan su karya ko wanan wanan yar sa idon ne nayi aune da ita tana ferewa wai fate zasu sha da safen nan.
Muryan baba danaji ya nufo kofan mu yasani mikewa na isa kofa ina fadin baba har ka fito banje mun gaisa ba.
Yace zan fita Safiya jinki shiru yasa na dauka ko barci kikeyi yaya hanya yaya wajen su hajiyar taki nace suna lafiya sun mace agaida kai.
Yace ina karbawa yaya wajen gwagon naki kina lekasu kuwa na dukar da kai sai yace aiko baki kyauta ba Safiya ai ba a yanke zumunci tunda ita ta yanke da sai ke ki raya shi lada zaki samu a wurin Allah.
Nace baba ai zan tafi amma gaskiya ba yanzu ba yanzu ba nafi son sai ina da aure inje da mijina yafi sauki.
Yace kuma fa kinyi tunane maikyau kuma Allah yasa mu dace yaya shi Alhaji sulaiman din suna dai lafiya ko na amsa kasa kasa da lafiya yake shima yana gaida kai baba.
Ya juya yana magana da ummi da take kofan daki hakan yasani mikewa na shige uwar dakin namu ban zauna ba wanka na shiga don makewayin da ke akwai a dakin kuma da ruwa a ciki.
Na fito ina shafa mai ummi ta shigo kuryan dakin tana ce min may ke faruwa tsakanin ki da uwar dakin naki naga ganin kannen ki yasa baki fada min ba.
Nace ummi ba wani matsala sai dai akwai matsala kadan nan dai na fara bata labarin abinda naji da kunne na anty din tana fadi.
Ta nisa tare da fadin ikon Allah ai tayi kokari ko wanan da datayi Allah ya saka mata da Alheri ai an gode.
Shi son kai sone ba wanda yaki nasa ya samu bata so ki ba taki dangin mijin ta don ko sune nata don da su take zama.
Nace aini ummi banga laifin anty ba don sanin ko waye anty uwa danayi don ba karamar macen duniya bane sosai anty uwa.
Tace Allah yai muna mafi alherin sa nace amin tace yanzu shi may yace a nasa bangaren nace yace wani sati magabatan shi zasu zo sai a saka ranan aure dayani.
Tace to Allah ya kyauta muna magana kiran wayan shi ya shigo nan ta fice dakin ta barni ina karba wayan nayi sallama ya karba yace.
Watau kin ga ummi kin manta da kowa ko nace ba hakana bane yanzu na tashi ina batun kiran ka sai gashi ka kirani yanzu.
Yace yaya gajin hanya don nasan akwai gajiya nace Alhamdullahi yaya na barku can?
Ya amsa da kalau sai nace yallabai naga ka mayar muna da gida kamar bila ubangiji Allah ya saka da alheri ya dada daukaka da yalwatan arziki murmushi naji yayi yace anty ki ta kiraki kuwa ?
Ya kawar da maganan nan take nima murmushin nayi mashi nace baka son godiyan nawa ke na ko ?
Yace tambayan ki nake yi antyn ki ta kiraki da kika zo arewa?
Nace har yanzu bata kirani ba yace na san za a rina ai, kyale ta, jiya ta kirani yau ma da safen nan munyi magana da ita.
Sai naji bakina yana tambayan shi may tace ma ?
Sai yace min ina ruwan ki da maganar mu da ita.
Haba uncle dina don Allah yaya kukayi da ita yace maganan dai ne na in rabu dake in auri diyar hajiya uwa don tafi asali.
To kai may kace mata yace cewa nayi haka shine daidai don dama ke baki waye ba.
Nace to Allah ya hada kowa da rabon sa yace amin ai ya hada tunda ya hadani dake kin sace min zuciya yanzu bani jin maganan madam dina kuma.
Murmushi nayi wanda ya baiyanar mashi da jin dadi na a fili tare da sauke ajiyan zuciya tare dacewa nagode uncle dariya yayi yace aini zan gode maki da baki yarda sun hadani da ke ba.
Murmushi nayi nace ai ba zasu iya ba don hadin Allah ne bana mutum ba da zasu iya da sun raba ko tunda duk wanda aka fadawa irin kazafin da sukai min dole ya dauka gaskiya ne.
Ya katse ni da cewa ai baki san wani abu ba nace ina jinka.
Yace ai tunda ta gabatar min dake da farko hankali na ya kwanta da zancen ki don haka ma daddy su twins shima ya yaba da hankalin ki.
Banga abinda zaisa yanzu daga baya ba kuma ta kawo min zancen wata na dai ce da ita haka ne daidai sai idan lokaci yayi zata sani.
Mun dauki lokaci muna waya dashi kamar ba kudi yake kashewa ba sai da ya gaji don kanshi yai min sallama na tashi na karasa shiri na dakin mama na fara shiga muka gaisa muka dan taba hira sai na wuce dakin inna inda na samu saadatu ita kadai a dakin wai inna tafita unguwa.
Nan na sake jikina muka dauki lokaci muna hira da ita nake tabayan ta fanin Isah dayai mata ciki take fada min bata da labarin shi.
Nace baya kawo maki komai ne tace tun wanan lokacin bai kara kulata ba kuma ba wanda yai masa magana akai ana batun ginan gidan mu.
Da yaya sani ya shigo na tuntube shi da zancen sai cewa yayi min ai shi ba abinda ke gaban shi ke nan ba nace haba yaya sani idan baku tsaya muna tsaye ga alamarin mu ba wa zai tsaya muna akai yace zai duba yagani yadda za a yi.
Anan muka bar zancen ban jima da fita dakin nasu ba inna ta dawo gidan tana shigowa sai ta fara budan hancin ta tana shakan kamshina dana bari dakin tace.
Safiya ta shigo dakin nan halan sai Saade tace eh tace karuwan banza ina shigowa naji kamshin turaren ta.
Haba inna Safiyar ce kuma karuwa Saa ta fada mata haka na tace idan ba karuwa bane may nena ita uban wa take nema a birni.
Abinda kikeyi gaskiya inna baida kyau shiyasa kullun bamu ganin karuwa ga alamarin mu don bakin hassada irin naki.
Aiko tayi cikin Saade din da fitina ita kuma kamar mai jiran uwa nan suka shiga yaba ma juna bakar magana har ya jawo hankalin mutanen gida aka tsaya sauraren ta yaya Nura da yaya Sani ne suka shigo gida suke tambayan ba asin maganan.
Inna ta kama inda inda sai Saaden ne ta fada masu abinda ya hada fadan da sukeyi daidai ina fitowa daga daki kenan maganan ya daki kunne na.
Cak na tsaya raina ya baci sai yaya nura ne yace in ma karuwanci Safiya ke yi a birni ai anci albarkacin karuwancin ta a gidan nan.
Yaya Sani ya karbe da fadin wallahi fa ke yar taki mai take zaman suna takeyi maki a daki da tsohon ciki komay ba gara safiya ba kowa ya san alherin ta ne ya kaita ga haka.
Wallahi inna idan kice bazaki bar halin nan ba watarana sai kinji kunya ba kadan ba zuwan Safiya dakin ki alheri ya kawo ta ba tsiya ba.
Don zuwa tayi ai magana da Isah asan halin da Saadatu ke ciki don bai waiwaye ta ba har yau mama tace kai kedai Rakiya halin ki baiyi ba wallahi.
Safiya tayi maki kama da wacce take karuwan ci koda ba a ganin zuciyar mutum ai abin duniya baya boyuwa da muji tun tuni.
Daki na koma van iya tsayawa na saurari sauran maganan ba sai dai na sa a raina cewa ba zan sake shiga dakin inna ba komai ya faru kuwa.
Har yamma naji anty bata kirani ba don haka na dauki waya na kirata amma har wayan ya katse bata dauka ba.
Ban kara kiranta ba da dare muna zaune a dakin mu sai ga baba ya aiko a kira masa ummi ta dan dade wurin sa ta dawo muna hira da kanne na sai tambayan ta kauna tayi tace halan baba yaji zancen maganan dazu ne ummi ?
Tace ina ruwan ki sai kin san abinda naje yi gunsa nace kai kedai baki da kunya Aisha may zai kara ki idan kin ji ni ban ma son baba yaji zancen tace sai dai kada a kara don Nura ya tare shi da zancen a waje.
Ina ga ki je gun su kawun ki kafin bakin ki su iso kin dawo zaifi nace to ummi zan tafi amma ba don naso a raina ba don dai ta ce in je ne kawai ba yarda zanyi.
Kwana biyu da zuwa na na shirya dani da kani na sai kyauyen su ummi na ida mahaifanta suke da zama.
Tafiyan safe mukayi don haka muka isa da wuri mun samu karbuwa na mutunci a wurin su aka kai muna kayan mu dakin kakan mu mace .
Bayan muci mun sha daga abincin su da suka fi karfi suka gabatar muna dashi muka zauna a na gaigaisawa da yan uwa.
Sai yamma mazajen suka dawo daga gonakin su wanda dashi suka dogora suna ci suna sha daga gare shi sai kiwo da suke hadawa dashi.
Kakan mu ne na karshen shigowa gida sai da ya huta mukaje gaida shi bayan mun gaisa ya tambaye mu mutanen gida.
Yake tambayana zancen aure nace insha Allahu malam ba za a dauki lokaci ba zanyi yace ko dai anzo sallaman mu ne gaba daya nayi dariya ina ce mai a a na dai zone in duba ku.
Shekaran jiya na zo shine ummi tace in iso nan in gaida ku yace ai ta kyauta tun bayan abinda ya faru dake bamu sake ganin ki ba sai nake ji wai kin samu mane mi a can birni har yai masu abin arziki a gida.
Na soke kaina kasa din kuya yace yanzu dai ciwo ya wuce ko nace malam yadai lafa dai amma ai ciwon ba mai barin jiki bane kwata kwata.
Yace ummh ummh kar ki yarda da wanan ki sa a ranki Allah zai baki lafiya ko yana nan baya tashi har a manta cewa kina dashi a jikin ki nace Allah yasa malam.
Yace ai kin ga rakumi nace eh malam yace to komai na jikin shi magani ne bani na fada ba in ji fiyayyen halita SAW ya fadi.
Yace da zaki samo fitsarin nan nasa koyaushe ya zama maki kamar ruwan shan ki to da kan ki zaki dawo nan ki bani labari bance zaki warke ba atake amma akwai faida a gare shi.
Nace shi fitsarin rakumin yace kwarai kuwa sannan namar shi ya zama maki abin ci ko yaushe akalla a sati ki kici shi ko sau biyu.
Sai kuma nonon shi ki dinga sha akai akai shima yana da faida sosai a jikin bawa ya dan kurkure baki da ruwan butan dake gefen shi yace sannab kin ga kashin rakumi nace eh malam yace ki samu kashin ki gone shi zai ya kono sosai sai ki daka ki dinga sha da albarkan annabi zaki neme ni indan muna raye.
Ba fa wai matsalan ciwon da ke damun ki ba kawai a a koda jikin ka ne baka gane kansa ba ne mi daya daga cikin sassan jikin rakumi ka riki sahihi da yardan ubangiji zaka ga faidan shi.
Nace ikin Allah yace shiko kashin nan nasa da kika gani nace eh malam mutane ne basu gane mai ba ai da zaki samay shi.
Ki busar dashi ki samu kanufari ki hada dashi kina yin hayakin shi a jikin kin ki sai yayi murmushi yace aiko maza dake samun matsalar rashin karfin gaba gane wa ne ba sayi amma da mutum zai samay shi yayi yadda nace maki sai ya dinga hayaki a gaban shi dashi ai ba katamin taimako yake yi ba za ka iya kuma dafa gaban shi sai dai ba a faye samun shi ba don tun wurin soke shi ake sayewa.
Namiji in dai yana amfani dashi ai masa romon shi da bakin iri ban san yaya kuke kiran bakin iri ba ku.
Nace ko habbatussaudat yace sunan sa ke nan ko nace eh yace sai a hada da kanumfari da citta da masoro da tafarnuwa yace ai bashi ba gazawa ga iyalin shi don karfi ne zai taso mashi sosai yaji shi gyagyan kamar dan shekara a shirin a duniya.
Yace kaiyya ai abar gado tun baya an dauki aladun wasu mun dora wa kan mu amma kin ga mu na kauye ai bamu bar gado ba, kin ga ko mun fiku karfi da lafiya don mu ciwon nan da ake fadi duk bamu sanshi ba.
Nace hakane malam amma ai inda mutum zai samu rakumi ne aiki malam har ya tara fitsarin shi da yawa haka.
Yace kuke nan dake birni amma munan ai shi yafi komai sauki ko yanzu kafin ki tashi zan iya sa a tara maki jarka kuma samo maki sauran sassan jikin ki jeraba ki gani.
Godiya na fara yi masa yace may ye abin godiya a ciki lafiyar ki ai namu ne duka yanzu barin fita idan na dawo maci gaba don lokacin sallah yayi yanzu.
A Zuciya na fara tunabe nayi yadda mutum zai sha waban abin da ya fada min amma dai ko yaya ne zan nema un jeraba in gani nma mikewa na yi zuwa rumfar kakata inda dakin ta yake na zauna rubuta duk abinda yace min nayi a wayana.
Bayan munyi sallah aka gabatar muna da tuwon surfafen dawa da miyar danyen kuka an lema man shanu a saman shi.
Kanina yace bazai ci ba shi zai fita yasamu bread da shayi ya sha azuciya ta nace ikon Allah ashe akwai abincin da dan gidan mu zai kyamaci ci a yanzu.
Nikan naci shi sosai nayi kat tare da hamdala na wanke hannu na sai naji kawo habu ya shigo yana cewa ina bakuwar tamu ga dan tsaraban kauye nasan ba iya cin abincin namu zakiyi ba ya miko min leda na karba hannu bubiyu ina cewa ai ko naci kawu sai da na koshi.
Ledan na aje a gefe na shima ya samu wuri ya zauna muna hira kakan mu tana sa muna baki jefi jefi.
Nan dai har ya gan garo kan zancen aure na nake fada mai halinda ake ciki yanzu ga zancen nawa ban boye mai komai ba ya murmusa yace abinku ne na yan birni.
Baku neman gida sai abu ya kure maku gani kuke yi kamar mu kauyawa ne komai bamu sani ba banda noma da kiwo amma ai aiki sai kauye.
Nace kawu ba hakana bane nayi nisa ne daku ko gida sau biyu ke nan nazo tun tafiya na yace to kin ga tunda kinzo yanzu ai ba a barki haka ki koma ba ai wani dan abu ba.
Kin ga ki samu kaucin gwandan daji da kan tunkiya ki daka ai maki miya dashi kaucin zaki iya dafawa kuci har da yara in Allah ya kawo su amma fa banda mai gida wanan mallakane sahihi.
Sai na neman farin jini ga dukkan dangin miji da ma mijin kan shi zaki samu farar dawa da farin goro farin kudi kurma farar kaza sayen tunfafiya na gabas din shi ki hade ya bushe kiyi wanka dashi da hayaki bayan kin dake su wuri daya, sai naga yayi murmushi.
Don watse makircin makiya kuma zaki karanta Lah illah hailala muhammadun rasulallah, hasbunal lahu wani imal wakil kafa dari duk safe zaki ga yadda zasu kwashe da yardan Allah.
Domin tsarin jikin ki kuma zaki samu ganyen hankuwa da ganyen sabulun dawaki da ganyen geza wanda suka fadi kasa da kansu a dake ki sha.
Wanan ma na tsari ne zaki samu gero wanda ya fidda kai ya baci yayi geza da suren fatake a dake asha da kunu .
Kiran da matar shi ta aiko tana mashi ne yasa ya tashi badon ya gama bani ba sai da ya fita nace ma kakana ni ina zan samu wanan abin daya fada min tace Allah ya kaimu gobe sai in zagaya nan bayan gari in harhado maki su wanda babu in kin koma can gwagon ummin ki sai ta samo maki ban samu ganin kakana ba don ance yana waje da bamin fulani da suka zo wurin shi.
Don haka nayi shirin barci na kwanta da wuri sai barci can cikin barci na naji Shafiu ya dawo kakan mu nace mashi ya dauki ga leda nan da kawun mu ya sayo muna nama ciki.
Ban iya bude idona ba don barcin da yaci karfina a lokacin har ya gama ya fita ban tashi ba tagama abinda take yi ta rufe kofan daki ta sauke min gidan sauron da ta kafa min na gyara kwanciya na asuba ta gari yan uwa.

🧕🏿5️⃣2️⃣🧕🏿
NOVEL DINA NA KUDI NE NA FADA MAKI KADA KI FITAR MIN DA NOVEL AMANA NE GARE KI IDAN KUMA BAKI BIYA BA KIKA KARANTA ALLAH YA BI MIN HAKKINA A KAN KI DON BAN YAFE MAKI BA
Washe gari malam yayi sakon fita zuwa wani kauye da fulani da mano ma suke rikici akan gona don haka ban samu ganin shi ba ranan sai dare sosai mota ya dawo dasu har kofan gidan shi don haka ba halin in ganshi da daren nan.
Gashi washe gari zan koma don shirin taron bakin da zasu zo min anan kauyen su ummi na sayi kwan zabbi mai yawa da kuma zabbin da ransu wanda zamu gyara masu idan sunzo .
Nono har na rasa inda zan sakowa yana kawo min kyautar kwai da nono tsaraba.
Naje sallama da malam yace Allah sarki Safiya sa ar safe gashi ban samu ganin ki ba har zaku wuce nace malam ai zan dawo kafin na tare yanzu ma zan koma ne na tari bakin da zasu zo yace to ga nawa gudun mawa rago nan sai a soya masu idan sun zo Allah ya tabbatar muna da alheri yasa muce gwanma da akayi.
Nace amin a kunyace yace banyi fushi ba duk da an kasani amma in mun hadu da abokin nawa watarana zai bani kudin fansan ki a gareni.
Nayi dariya kawai na mike ina mashi sallama muka fito don mota nasa aka dauko muna shata dagani sai Shafiu kawai sai kayan mu.
Mun iso gida kafin sallah azahar aka fitar muna dakaya zuwa cikin gida na sallami driver tare da yi mashi godiya nace ya ban nombashi idan muna da sako yakai muna.
Don tunda muka kama hanya yake muna hiran yanayin kasar da sauran su shafiu ne ke bashi amsa ni sai jefi jefi nake saka masu baki ga hiran nasu.
Mun shiga gida sai bin mu akeyi da kallo Aisha ke fadin ga mutanen kauye sun dawo munko ga alama don ga tsaraban kauye nan hardasu zabbi da kwai.
Ummi ce ta buge mata baki tace kai surutu muka shiga daki na huta mama tazo ta tare mu ta tambaye mu yaya muka barsu nace lafiya suna gaida ku.
Zata juya nace mama ga nono nan da kwai da zabbi nazo dashi don bakin da zasu zo jibi sai a gyara masu.
Taji dadi tace a a baki muke dasu tafe ashe sai ta karasa shigowa dakin tana cewa yanzu yaya za ayi masu dashi don mu fara saboda akwai aiki sosai.
Nace mama yadda ya dace zakuyi dashi mana tace to yanzu bari in aika ma mamakin suzo asan abinyi kafin gobe a makara.
Ta aika kiran su mama zuwa karfe biyu sai gasu sun iso nan ta gabatar masu da komai don haka suka fara tsara abinda zasu yi na kawo kudi na basu wanda za a sai kayan aiki.
Da farko an yanka ragon da malam ya bani nan suka shiga gyara saadatu ne kawai ta fito inna cewa tayi wai ba a sata a maganan ba.
Kowa ya share ta a gidan yaya Sani yayi fada har ya gaji baba yace a kyale ta ranan asabar mi salin karfe dayan rana sai ga su kawu abu sun shigo wai babane ya aika su zo nace kai baba ho tambayan aure shine harda taso su kawu su zo kuma.
Zuwa karfe biyu saura suka iso mota biyu akai masu taron mutunci sunci sun sha sai suka gabatar da zancen neman aure da kuma suna son a yanke masu sadaki kafin su wuce.
Baba yace sadaki dubu ashirin zasu bayan ba kuma zasu wuce ba sai an daura aure don ni ba budurwa bace.
Duk yadda suka so baba yaki yarda dole suka amince za a daura kagin su wuce mu dai sai ji mukayi mai shela na sanarwa a na gaiyatan mutane kofan gidan babana.
Nan dai aka sheda daurin auren na da sulaiman akan sadaki dubu ashirin kacal ina daki kwance shafiu yazo min da labari.
Zubur na mike ina cewa yaya uncle zai min haka kuma ai ce min yayi tambaya zasu zo da kuma saka rana.
Mutane sun rage yawa sai ga bakin daya daga cikin su ya shigo na fahinci kannin Sulaiman ne don naji yana cewa ina amaryan nawa take na ganta don ban santa ba.
Nayi saurin boye sai da mama ta shigo tace in fito mu gaisa hijjab kawai na saka na fito yana zaune falin ummi yana gani na yace ba laifi shiya sa bross ya lake sai ke amma kamar na san fuskan nan taki wani wuri.
Gaida shi nayi shiko sai sheri yake min yana fadin yau ban san yadda zai ji ba idan yaji har an daura aure gaba daya akwati biyu na gani anshigo dasu yace ga sakon baaban mu nan tace a kawo maki na mun gani muna so gashi kuma har kin zama namu gaba daya.
Na dago kai da kyat nace aimin godiya wurin baaba kafin inzo yace zata ji ya mike yana fadin zamu tafi do garin naku akwai nisa sosai wallahi ai gara da aka daura gaba daya muka huta.
Mukai sallama ya fita nan aka fara fita masu da kayan da aka hada masu na ganima suka ce harda wani dawai niya haka kuma.
Nan sukai min sallama suka tafi cike da farin cikin irin karramawan da suka samu a wurin mu sun kuma yaba da halin baba da bai yi zari ba da kwadayi ya karbi kudi kadan a sadakina.
Nan aka bude akwatin mama ta fara daga dankara dankaran zannuwan dake ciki da lece har goma sha biyar dayan akwatin sauran tarkace ne a ciki aka zuba.
Baba ya shigo har dakin ummi da kudin sadakina a hannun shi yana cewa ina Safiyan ga sadakin ki nan hakkin kine ba namu ba sai dai nayi karanbanin yake masu mafi saukin sadaki don samun albarkan aure.
Na mika hannu bibiyu na karbi kudin tare da nufan ummi na dake zaune gefe dasu tace a a rike abunki Allah yasa albarka duk wanda ke dakin yace amin.
Ya fita na koma kuryan dakin na haye gado tare da lafewa kamar mai yin barci ina jin suna watsewa da guda guda.
Ya saura sai ni kadai da yan gidan mu kowa ya kama gaban shi daga inda nake kwance na jawo waya na naji ina son kiran anty in fada mata ta ida aka hau tanan ake sauka.
Amma har ya katse bata dauki wayan ba na kara kira yan biyu ta dauka tana fadin tana sallah na kira sunan ta take ta gane ni mukai ta hira dasu har tagama ta dauki wayan.
Muryan ta ba yabo ba fallasa muka gaisa tace abubuwa sukai mata yawa shiyasa bata samu kirana ba amma tasha ganin miscall dina.
Mukai sallama nai mamakin jin bata tambaye ni Sulaiman din ba nima kuma ban mata maganan shiba.
Faiza na kira tace ke yar kasa ai na dauka ki manta danine ina son in kiraki ina jin tsoron kada ki fada ma mutumiyar tamu nace haba don kin kirani sai in fada mata kuma.
Naji ta shake murya tace dama ina son kiranki in sheda maki anty uwa nan tazo ita da yaranta sai faman shuka muna tsiya suke a gida.
Nace don Allah yaushe tazo tace yau kwananta biyu da zuwa wai may ya hadaki dasune Safiya?
Nace ni kuwa ina na san su banda wurin liyafan da muka hadu a abuja.
Tace aike gara da baki gidan don ko ita anty ta gaji da su wai kuma sati daya zasuyi a gidan nace tirkashi .
Tace ke dai ai kin auna arziki da kika tafi basu samay ki ba gani nan kamar aiki zai kashe ni yan iskan yara kawai komai basa iya yiwa kansu sai dai ai masu.
Amma kamar naji ana maganan Sulaiman da suka ganin sai sukayi shiru basu san naji abinda suke fadi ba sai dai banji ba sosai kamar suna cewa inba shi ba mai zaiyi da yar kauye ga mata birjit a birni.
Nace nice yar kauyen ke nan ko tace wa yasanar masu yan bakin ciki kawai.
Mun dauki lokaci da ita muna hira ta kashe tana cewa wai ana kiranta don haka mukai sallama tace idan taji wani abu zata kirani.
Ta barni da tunane nace a raina ashe sunzo din Allah ya taimakeni dani ce zan zama masu jakar aiki harda gaiya zasu hada min ga korar karen da sukayi niyar yi min a gidan.
Da dare na yi shirin kwanciya sai ga wayan sulaiman ya shigo min ina dauka naji ya kwashe da dariya yana fadin Allah dai ya sakawa baba da alheri.
Wanan irin halarcin haka aiba kowane zai iya ba zankadedeyar kyauta haka abin yazo min da sauki da na dawo yanzu sai kawai nazo na dauki matata mu tafi.
Nace sai kace amaryan dako yace ai itace don ko baba ya hutar dani ga komai yayi yadda sunna yace ayi saura may kuma ba in daukeki ki tare a gidana ba.
Nace kana fara yi min haka aiko dan walima ka bari muyi don Allah yace kai Safiya bansan baki da tausayi ba .
Allah ya kawo min sauki kina son kuma ki kirkiro wani abu na daban kisa ai walima ko a dakin ki kaso sai ai maki.
Kara marairaicewa nayi nace don Allah uncle kada muyi haka dakai yace kedai zancewa kada muyi haka dake shekarana nawa ina zama gwauro yanzu kuma da aure na zaki mayar dani gwauro da karfi da yaji.
Kunyan zancen nake ji don haka nayi kokarin kawar da zancen da tambayan shi ka fada ma anty kuwa ?
Yace bari nayi sai taji ta kirani zamuyi maganan da ita don yanzu ban shirya abinda zan fada mata ba.
Ajiyan zuciya na sauke nace ashe su anty uwa sun tafi lagos din yau Faiza ke fada min yace itace info dinki a gidan ke nan nace a a magana ne ya kawo ta fada min.
Bayan muyi waya dashi ya sheda min a sati biyu yake son in tare gidan shi don haka na fara shirina da wuri zai dawo next week in Allah ya kaimu.
Bayan na kashe wayan ne na sauke ajiyan zuciya sai yaya Saadu ya fado min a rai don haka na kirashi don in sheda mashi.
Kira biyu ya dauka yana cewa yar halas yanzu muke maganan ki don ga takwaran kinan ta hanamu shakat sai kuka take muna nace subbahanallahi.
Kun bata magani kila cikin ta ke ciwo ina jin yana tambayan Samira ko an bata magani tace bata bata ba.
Ya juyo gareni yace yaya garin kina lafiya yaya logos nace ni ina gida yaya yace kina gida tun yaushe ?
Nace sati daya ke nan lafiya kika je gida yanzun Safiya kodai auren ya tashi ne ban sani ba ?
Nace aure sai dai ayi fatan dacewa da zaman lafiya yanzu yace may kike nufi tukun nace abinda na fada yanzu yaya.
Wai tsaya don Allah da gaske kikeyi ko wasa nace wallahi ko yau baba ya daura min aure daga zuwa tambaya sai daurin aure daya ni.
Yace don Allah ki bari ni ina nan ina cewa ni zan bada ke don asan ba zumuncin wasa ke tsakanin mu ba ashe baba ya rigani.
Nace wallahi yaya ni yanzu duk abin ma ya daure min kai wallahi duk na shiga rudu wallahi ban shirya komai ba yaya.
Yace Allah yasa haka yafi zama muna alheri nace amin yace yaushe ne tarewan naki yanzu nace ban sani ba yaya amma dai naji yace in two weeks yake son in tare.
Yace haka yayi yanzu ki bari zamuyi waya zan kiraki ansan abin yi kafin in zo nace yaya kada kace zaka wahal da kan ka don yace baison inje da ko tsintsiya gidan shi mata ya nema mata za a kai mashi.
Yace ayi haka bari dai mu gani zan kiraki da safe in nayi shawara mukayi sallama ya kashe wayan.
Na sauke ajiyan zuciya tare da kifa wayan nawa ina mai sauke numfashi tare da lumshe idona sai na mike zubur na fada ban daki tare da dauro alwala na fito.
Na dade zaune ina kai kukana ga ubangiji da ya tabbatar min da alheri ga wanan auren ya kawar da duk wani abin ki a gare mu.
Na dauki lokaci mai tsawo a zaune itama ummina tana nata a falo sai kanne na ne ke ta kwasan barcin su hankali kwance na shafa tare da mikewa na nade abin sallah.
Sai naji Ummi tace min kin idar na amsa mata tare da fitowa falon na samay ta na zauna anan.
Take cewa dani gashi dai yau Allah yayi ikon shi kina da aure a kan ki a gidan nan abinda kowa bai zata ba akan ki.
Don haka sai dai muyi fatan Allah yasa ma auren albarka Allah dai yanufa shine mijin ki kece matar shi kada kisa kowa a ranki ita ma wace tayi maki wanan dalilin aure kada ki yarda ki yashe ta komai ritse don ita din ba abin yaddawa bane a gare ki.
Ki manta da komai ku zauna lafiya don alaka ya sake hadaku dama duk wa yan da zaki samu a zurian shi ki zauna lafiya da kowa.
Kin daiga shi abin duniya bai rufe mai idon shi ba to kema ki zama haka na ga yan uwanshi da nasa sai a zauna lafiya.
Yanzu sai mu jira dawowan shi muji yaushe yake son ki tare dakin ki nayi saurin cewa ummi waifa a cikin sati biyu yake son in tare.
Sai naji ummi tace to shike nan mana Allah yakai mu lokacin nace ummi may aka shirya da za a biye mashi don yace cikin sati biyu yake son in tare ?
Tace akwai Allah shi zai hore muna abinda zamu kai masu a matsayin gara bashi kenan ba sai ki tare shike nan sai kuma a jira suna idan muna da sauran kwana.
Cike da jin kunya na sauke kaina kasa ina cewa kai ummi sai tayi dariya tace to may za a jira kuma yanzu bayan wanan sai maman ku ta shiga zuwa reno.
Kunya naji nace kai ummi tin yanzu har an fara wani maganar haihuwa can a dai samu a tare din don dazun Faiza ke fada min wai anty uwa tana lagos gidan anty kan maganan.
Sai naji ummi tace ai basuyi kamar Allah ba don aure ya riga ya dauro a tsakanin ku ko ba kuma zasu iya rabawa ba insha Allahu.
Mun dauki lokaci muna magana kafin mu kwanta barci da safe ma da muka ta shi da maganan muka tashi kuma a dakin mu.
Kiran shi ne ya shigo min na dauka da ladabi ina gaida shi bayan mun gama gaisawa yace Safiya a gidan ku wa kike ganin ta samu kebewa da Nafiu kanina da suka zo.
Gaba na ne ya fadi dam nace a gidan mu kuwa gaskiya ban sani ba don ni ina daki har suka wuce yace ki dai bincika din akwai wace ta fada masu wai.
Rufa rufa za ai min kina da cuta a jikin ki abincika kafin ki tare don kar a cuce ni da sauri nace ba kowa zai min haka ba sai inna .
Yace wacece inna nace dashi maman su yaya Sani don itace kadai zata iya yimin haka don tasha fadawa mutane hakan.
Yace subbahanallahi nan na fara bashi labarin zaman ukuban da nakeyi da ita tun tasowa na a gidan har zuwa yanzu.
Yace ok ita din ce na fada ma hajiya baaba da ta tuntube ni da zance nace ba gaskiya bane sai da mukayi gwaji dake kafin mukai ga matsaya nasan kuma ta gamsu da magana na.
Zan kuma kara yi mata bayani yadda zata fahince ni amma dai wanan matar ko bata da hali mai kyau yace zan gaya wa baba da kaina don ya dauki mataki akan ta kada yan uwa na suzo ta bata auren.
Nan dai ya kwantar min da hankalina muna gama waya na kira ummi na ina fada mata ita kuma bata tsaya ba ta kira mama tana sheda mata abinda ke faruwa.
Mama tace a bari baba ya dawo gidan ai ba kyale ta za a yi ba dole ai mata magana wanan karon.
Basu gama magana ba sai ga baba ya shigo a fusace tun daga kofan gida yake kwadawa inna kira mama tace gayacan ma shigo ko yaji ne ma ?
Inna tafito tana cewa malam wanan kira haka kamar makaho ni har gabana ya fadi ai.
Yace gaban ki ya dade bai tarwatse ba munafukan banza muna fukar wofi kawai ta Allah ba taki ba.
Munafincin ki bai ciba sai ki canza wani kafin ma ki canza badai a gida na bakan don safiya bata tarewa kina gidan.
Fadin haka yasa yaya sani dake bayan shi yana sauraren maganan baba din yace saboda may baba ?
Yace sani wanan uwar taku wani irin hali ke gareta yanzu ace duk halarcin da yarinyar nan take muna agidan nan kaf bata debe kowa ba wai amma Rakiya bata gani.
Sai tabi baya ta yi munafinci akan auren Safiya don ta kumsa muna bakinciki kawai duk a taru a lalace uwa zaune diya zaune a gida kamar yadda take da yar ta a daki.
Yaya sani ya sake fadin may ya faru ne baba may kuma innan ta sake yi ne wai ?
Yace sani wai ka diba ashe zuwan mutanen nan garin nan Rakiya ta sillace jiki ta ja daya daga cikin bakin nan ta fada masu wai ba lafiya ke ga Safiya ba ayi bincike kafin ta tare.
Sai gida ya dauki salati dama kowa ja waje cirko cirko a tsaye ana sauraren baba yaya Nura yace an ko yi haka wallahi dama nayi tunanen in ba wani abin zata fada mai ba don naga lokacin da ta fito suna alwala ta kirashi gefe ni kuma muna shagon musa mai tereda zaune wallahi na ganta.
Kai munafuki da ka ganni sai akace abinda na fada mai kenan ko may yace nidai na gan ku tsaye wallahi ba wani ya fada min ba da idona na ganki inna.
Baba yace yanzu yaron nan ya kirani yana fada min sakon da aka kaima uwarshi gida don haka ban zama da macen da bata son diyana da karuwa a gidan ki tafi gidan ku har, , ,
Yaya Sani ne yace don Allah baba kada ka karasa don Allah sai ya fashe da kuka sauran yaran suka dauki kuka gaba daya.
Ummi tace malam kayi hakkuri ko don yaran nan idan ka sallamay ta yanzu ga Saadatu da ciki ina zata yace inko ban sake ta ba yanzu bata zaka min gida sai safiya ta tare.
Nan dai gida ya dauki kuka kowa da abinda yake fada yafice yabar gidan nace gidan mu gidan danger.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON
🧕🏿5️⃣3️⃣🧕🏿
NOVEL DINA NA KUDI IDAN KIN FITAR MIN ALLAH YABI MIN HAKKINA A KAN KI IDAN KI KARATA BAKI BIYA BA BAN YAFE BA NA FADA NA SAKE FADA A KIYAYYE DON ALLAH DON CIN AMANA BALA,I NE, , , , ,
Shigana daki yayi daidai da shigowan wayan Faiza nayi saurin dauka don nasa magana ya samu ke nan ina dauka tace wai safiya may ya faru ne daga jiya zuwa safe dai surfa maki zaki ake a gidan nan babu kakautawa.
Tace bari dai zan kiraki ina zuwa sai ta kashe wayan nata na bi wayan da kallo kamar shine faiza na bashi amsa da cewa sunji zancen auren ke nan.
Shigowan gwagom Ummi na gidan ne ya dawo da kowa a cikin sai tin shi don ta shigo gidan ne da gudan ta tana fadin ayyurriri amarya Allah ya kawo mu lokaci ya kawo mu yan bakin ciki kunji kunya masu hassada kubi bango ku narke don Saifiya da Sulaiman zama daram.
Su yaya Nura ne ke fadin gwagon ummi gudan bai isa ba sai ta kara fadin ayyurriri Amarya.
Yar shagali yar biyan bukata yar galari , makulin mota ke akaba na kofan daki ke akaba sai yaya Sani ya manna mata kudi a goshi nan ta kasa karasa kirarin nata ta saike guda tana fadin Amarya bakya laifi, ina amaryan take ne.
Sai mama tace a a gwago karkizo ki sa min yarinya kuka fa munyi arziki tunda aka daura aure bata wani bata rai ba.
Gwagon ummi ta juya ta kalli mama tace kuka kuka fa kikace
Yo kukan may ina so kina so sukayi fa kinji ki da wani zancen badai yaran yanzu kuka kan.
Aiko na munafunci basa yi koda kuwa budurwace sun daina kuka tace yo Allah na tuba wanan din ma ai tayi kawaici da watace da yanzu ta kafa muna DJ a gida ta ruda unguwa da gaiyatan shedanu masu hana auren zaman lafiya.
Ummi ce ta fito fuska a daure tana yiwa gwagon sannu da zuwa ta bi yar dan uwan nata da kallo tana amsa gaisuwa nan tabar mama da sauran yara tsaye ta nufi dakin umin nawa.
Kara gaisawa sukayi ta kasa daurewa tana tambayanta make faruwa ne naga ranan farin ciki a gare ki gashi kuma kin bi fuskan ki duk kin daure ?
Ummi bata iya yin magana ba sai hawayen dake zubo mata sai nice nayi karfin halin fito ina cewa gwago an shigo tace a a kina ciki dama ?
Nace na kwanta ne dama tace may ya samu uwar taki ne haka kuma ranan farin ciki a gare ta gata tana kuka kuma ?
Nace ba wani ubu bane zancen Inna ne dai shine takema bacin rai ,
Innan taku tayi wani abune mara kyau ne kuma nace gwago takan rasa ne ai mai hali baya barin halin shi.
Zuwa tayi ta fadama ma dagin mijin antyn mu wai suyi bincike anty mu na da cuta a jikin ta amai rufarufa ne don acuce shi.
Salati gwagon ta saka tun kafin taji karshen maganan tana fadin amma dai anyi yar banza mata anan .
Da ita nufinta haka za a hada auren bai san halin da take ciki ba to mu bamu da gadon sheri a tare damu.
Yanzu may ake ciki tana sake tambayan Aisha kauna na don ta san ni da ummi ba zata gane komai a wurin mu.
Aishan tayi mata bayanin komai yadda zata fahinta tace hakan da malam din yayi yana da kyau tunda dai Rakiya bata da niyar gyaran halinta.
Nace ni gwago na rasa mai nayi wa inna a duniya tun ina karama bata kauna na haka.
Tace bazata ko kaunace ki ba don indan kika ga mutum da yafaye wanan halin yaje bakar bincike binciken ta an fada mata abinda ya tayar mata da hankali shi ne abin yake wahal da ita haka.
Kin san wasu basu da dogaro gun Allah da zaran kishiyar su ta samu ciki zasu je a bincika masu mai zata haifa da sauri nace kai haba gwago tace Allah sarki ai wanan abin abu ne da ya kewaye birni da kauye don ko ina akwai marasa imani.
To duk yadda akayi irin haka ne ke damun Rakiya taje an mata buncike an fada kata cewa abinda zaki haifa na da arziki sai ta ce a jefo mao kaddara da karshe kuma ba mai iya hana ikon Allah sai kaddaran ya juye Alheri ga bawa.
Shiru mukayi muna sauraren gwago da al,ajabin abinda take fada muna tace don yanzu an daina wasu abu saboda wayewan kai da mutane suka samu.
Amma har gobe a kwai masuyin zagon kasa don su basu bar gida ba don haka yake da kyau mutum ya nema wa kansa rigakafi tun kan rana ya baci.
Don haka kema yanzu ki saurare ni don zaki tafi cikin bakin fuska da baki san su ba baki san halin su ba .
Don haka zan baki makarin kwarce ko wani zai maki ba zai kamaki ba murshi nayi a raina nace kai gwago ho.
Zaki samu kwai na zabo guda ukku sai ki samu kayan aduwa 99 a hada su da kwanzaben nan a dafa sai ki hada bawan kwan da kayan aduwa a dakesu adinga zubawa a kunu anasha.
Maganin walwale turbuda shine turbuda kuma idan kina zargin wani na maki asiri shine,
Zaki samu ruwan tsami ko ruwan tsami da ganyen zogala wanda aka shuka iyankan gona sai ki jika da kai kayi koma kan mashekiya ki hada da ruwan tsamin da zogalan na iyakar gona kiyi wanka ki sha.
Da yardan Allah komai mutum ya dauko a kanki sai dai ya koma mai badai ya kamaki ba.
Wayana yai kara sai na mike na koma daki na bar gwagon nan falo zaune da ummi da su Aisha.
Na dauko wayan da sauri gabana ya fadi don ganin lambar anty na kira na a lokacin wada dama ina tsamanin hakan ko yaushe.
Na dauka da sallama ta, sai naji ta katseni da cewa amarya ke nan ke nan kai duniya ina zaki damu ashe tsintaciyar mage dai bata taba zama mage.
Lalai mutane sunyi gaskiya da suke fada min cewa ke din tsintaciyar mage ce a gare tabbas ko ya tabbata hakane.
Kafin in magana sai naji ta kashe wayan ta dip ajiyan zuciya na sauke tare da sake murmushin bakin ciki lokaci guda.
Na a sanyaye na fito falo inda suke na zauna ban iya cewa na fahinci hiran su alokacin sai da naji tace ai kinga idan yaro ya na dauke dauke zaki samu kaucin malge a samu kashin mai satan a hada da malgen a shaya in ya bushe a daka in ya zama gari sai a dinga sa ma mai shi a kunu ko shayi yana sha har kwana bakwai da yar da Allah zai bar satan don da yaje daukan abu warin kashin shi dayaci zai hana shi daukan abu yaji satan ya fice mashi a rai.
Sai kuma mallaka da sai abinda kika ce a gidan zaki samu kaucen gwanda na daji ki dake shi ya zama gari a samun kan tunkiya da ta kosa adafa su tare in ya dahu sosai ki zauna kici duka amma bada kashin ba.
Allah sa mu dace naji tace sai lokacin na kallo ta ina cewa ummi yanzu anty ta kirani fa.
Da sauri tace yaya kukayi da ita ta sake fadin taji ke nan dai ko ?
Na gyada mata kai da alaman eh gwago ne tace may taji auren sai ummi tace eh gwago tace dama bata sani bane Aisha dake zaune ummi ta kalla sai tayi shiru.
Na ce ummi ai yanzu ba maganan boyo bane tunda abin na ta kamari tace wai may ke faruwa ne kumbar mu a duhu haka ?
Ummi tace ummi kin san sun samu matsala da uwar rikon nata tace subbahanallahi shine baku fada muna ba asan abin yi.
Ummi tace abin ne wallahi da daure kai zaman su ba wani matsala sai daga baya ne kuma wani hali ya shigo masu.
Don ita bayan ta hada su da kanin mijin ta sai kuma daga baya bata son hadin wai tana son hada shi da wata yar yar uwar mai gidan ta.
Shine ita ta risketa tana waya suna fadin wai zasu zo suyi kata korar kare a gidan da take zaune shine shi wanda ta aura din ya bata shawaran ta dawo gida.
To shine da nake fada ma malam halin da suke ciki sai malam din ya yanke shawaran cewa da sun zo tambaya sai a daura aure da yani.
To yanzu nasan taji ne shine wai ta kirata yanzu din sai gwago tace may tace dake to ?
Nakwashe abinda ta fada min na fada mata sai tace aikin banza ai Allah ya riga yayi ikon shi ko a kan su yanzu sai dai hakkuri.
Nace ni yanzu ce min da tayi wai tsintarciyar mage bata zama mage shine abin ke damu na wallahi tana ganin nice na yaudare ta ko may gwago ?
Tace kun ga yanzu duk ba wanan ne a gaban mu ba koma may ye idan kin tare daga baya sai ki nemi shiri da ita da sannu zata fahinci ke ba tsintaciyar mage ba sai ta soki fiye da magen da aka haifar mata a gida.
Ummi tace shine kan mafita gwago don yanzu duk yadda za a fahintar da ita ta riga ta hau ba ta yarda damu ko kadan.
Gwago tace may ake ciki ne don shi ya kawo ni yau din don nasan baku shirya komai ba ga auren nan gashi kuma ba kananan mutane bane su.
Ummi tace wallahi gwago abinda muke shawara ke nan akai tun jiya da malam ya daura wanan aure don nasan ba komai zamu samu a bangaren shi ba.
Gwago tace karki yanke hukunci da sauri don baki san ajiyan shi ba nace humm gwago ai abar zancen baba kawai don yanzu baida yaushe ne ya fara fita kasuwa.
Nace akwai wasu kudi a hannu na barin dauko sai a kaima su mama asan shawaran da za a yi dasu na mike sai gwago tace dawo ki zauna zasu yanzu don na fada masu mu hadu nan ban san abin da ya tsayar dasu ba.
Sallaman su mukaji a tare suka shigo suka tsaya suna gaisawa da mama dake zaune a kofan ta tana raba abinci.
Suna shigowa suka fara gaisawa nima gaida dsu nayi da zuwa sukace amarya ke ce haka ba wani shiri da zai nuna farin ciki a gare ki?
Murmushi nayi nace kai haba mama tace ai gaskiya ne Safiya tun yanzu fa za a fara shirya ki don wanan auren ba irin wancan bane.
Tace to ai kune uwayen nata kuka tsaya nawa na fada maku mu hadu nan tun da safe amma sai yanzu kuka zo.
Yanzu dai ba wanan ba yanzu shafiu ke fada muna abin da bakar daga can tayi jiya kuma asirin ta ya tonu.
Gwago tace don Allah ku fita batun ta kuyi abinda ya kawo yanzu don ba isasshe lokaci ake dashi don tace yace a sati biyi yake son ta tare gidan shi.
Suna hada bakin wurin fadin sati biyu fa ?
Yo mai za a tsaya jira kuma aure ya dauro ba sai ta tare gidan ta ba yanzu duk wani abinda za ayi ai aladane kawai don wajibi ya auku ko tunda an daura aure may ya rage kuma ?
To yanzu gwago maye abin yi tace yanzu take fada muna akwai kudi a wirin ta sai a san abin yi nace ta bari har ku iso ne muga kudin sai a san yadda za a kasafa su.
Mikewa nayi na shiga daki tare da kirgo kudi dubu dari uku na kawo masu na mika ma mama Jummai don itace babba a cikin su.
Tana kallon kudin tace ai ina ga a dai tallakance wanan din zai isa ko sun kai dari biyu ai nake gani nace dari uku ne nan tace tirkasa.
Ta juya gun su ummi tana cewa may ye abin yi yanzu ga dai kudi sun samu gwago ta katse su da fadin akwai raguna na sai a kama biyu ku hada a laurar taku.
Nace gwago baki barin abinki tace ai don haka dama nake kiyon su yanzu ba sai ai lalura dasu ba sai dai zanso ku soya masu shi ku jefa a gara kun dai ga gidan masu shi zaku kai kayan.
Zan so ace kun tsaya kunyi abinda zai cika ido yadda ba za a raina maku ba.
Mama Suwaiba tace mu dai yi iya karfin mu amma ina zamu ita dasu nace mama may zai hana ku kira mama na nan gidan kada a kebe ta zaifi ace anyi komai da ita.
Gwago tace yanzu abin da nake shirin fadi ke nan kika riga ni fada sai ummi tace gaskiya kan kiranta aka tura Aisha da ta make dakin tana sauraren mu akayi .
Bata dauki lokaci ba sai gata nan dai akai mata bayanin ta nisa tace da son samu ne kada muyi kayan abinci mu dai tsaya ga wanda za a rabawa yan uwa da abikan arziki don shine abi magana.
Alabashi gaba in ta haihu sai ai mata wanan ko yaya kuka gani ta dago kai tana kallon su ko wayace sharan ta yayi.
Na suka fara kitasta abinda zasu inda za a kai yin cicin din a birni can wajen kaunan miji mama jummai dake zaune a birni su kuma zasu yi sauran abubuwan a nan .
Kowa ya dauki part din abinda zai yi a cikin su inda aka bar wa mama da ummi yin suyan kaji da ake so cika roba guda dashi.
Tun wanan ranan basu zauna ba kowa da abin da yakeyi don kar a girshe shi muna waya dashi ko wani rana yana kara kwantar min da hankali.
Faiza ne ke fada min cewa su anty uwa sun koma abuja a fusace wai Nafisa tana ta kuka tana fadin ba zata yarda ba.
Ita sai ta auri uncle ko ta halin kaka wai da kyat ta yarda ta bisu ta kare da cewa wai yanzu ashe an daura auren ku da uncle baki fada mu na ba sai a bakin mutane mukaji.
Nace wallahi Faiza nima ban san za a daura min aure ba a wanan lokacin kawai daga zuwa tambaya sai gashi ance daurin aure za ayi.
Tace ai dake da madam din mu ne yanzu don naji tana ta zage zage tana ta fada daga ke har uncle din wai kun munafunce ta.
Nayi murmushi kawai nace ba haka bane wallahi kowa baba bai fada wa zancen daurin auren nan ba sai da akazo yi aka sani wallahi ki yarda dani Faiza tace wallahi na yarda.
Tace yanzu yaushe ne tarewa kuma ?
Nace da ita babu rana Faiza don bamu tsaraba sai ya dawo zai saka rana tace aini abin yayi min dadi wallahi sai dai nasan yadda madam ta hau ba zata barmu mu zo wurin bukin ba.
Kin san may nace a a Faiza tace naji suna magana wai ai gidan ku ba abinda zasu kai tin anan zaiji kunya ita ko mutumiyar kullun tana daki tana kuka wai bata da lafiya.
Allah ya kyauta nace da ita ban yarda na furta wani kalma da zata kaini gaba ba don sanin halinta da nayi.
Mun gama wayan ta barni cike da tunane halin da muke ciki da anty don da ka gan ni na ramay babu walwala a tare da ni kamar wacce za ayiwa auren dole na koma.
Nasan dawowan shi Nigeria sai da ya kwana biyu ya wuce bauchi wurin mahaifiyar shi don kiran gagawa da tayi mashi akan maganan mu.
Ya iso sai dai mutane basu bari ya samu kebewa da ita ba sai da dare suka samu ganawa da mahaifiyar tashi.
Yana zaune kasa tana saman kujera ta kafa mudubin ido a fuskan ta da ke taimaka mata vurin gani.
Shiru dakin yayi kafin tace babana wata irin mace ka dauko muna don ban ji dadin labarin da ya kawo min ba.
Ko da yake mutanen duk da bamasu karfi bane amma sun san mutuncin kan su a yadda mahaifin yarinyar bai karbi sadaki mai yawa ba kuma da irin taron da sukai ma wayanda na tura daga nan.
Sun yaba kwarai da mutuncin da aka nuna masu a gidan sai da abin damuwa wanan labarin da Nafiu yazo min dashi shine banji dadin shi ba.
Nafi son kayi bincike mai karfi kafin yarinyar nan ta tare don ni ban kita ba don kaine mai zama da ita amma tunda kananan magana ya fara fitowa daga gare su sai a tsaya a bincika a hankali kada azo ai abu a cikin duhu.
Ban son ka kara auren dana sani kamar yadda kayi a baya auren da baida amfani a gare mu sai barnan suna.
Shiru yayi kafin ya dago kai yace hajiya akwai abin da nake boye maki da dadewa wanda baki sani ba har yau.
Gyara zaman tabarau ta tati dakyau ta dago kai tana sauraren shi tare da fadin baba na maye kake boye min wanda ban sani akan ka.
Ashe akwai abinda zaka iya boye min wanda ya shafi rayuwanka yace hajiya kiyi hakkuri don Allah fada maki wanan zancen tashin hankali ne a gare ki.
Nan dai ya fara bata labari tun auren shi da Samira matar shi ta farkko sai innalillahi kawai take furtawa har yakai yadda anty ta hada ni dashi dakuma yanzu da take shirin ruguza auren namu.
Innalillahi take ambata tace yanzu shi Nuhu da matar shi sun san maganan ga suka iya boye maka sirin ka ta yadda ko ni da na haife ka ban sani ba.
To amma ita maimuna may zai sa tayi haka bayan ta hada alheri kuma ta bata rawanta da tsalle a karshe.
Yanzu na gamsu da kai sannan ita wanan yarinyar itane rufin asirin ka ga kowa ta yadda ba kowa zai san abinda kake ciki ba.
Allah ya albarkaci aure ya baku zuria mai albarka ya amsa da amin tare da mata godiya ta kara kwantar mashi da hankaki tayi tare da cewa tasan yadda zata kashe maganan daga bakin kowa.

🧕🏿5️⃣4️⃣🧕🏿
NOVEL DINA NA KUDI NE WANDA YA SAN BAI IYA RIKON AMANA TA FADA MIN IN BATA KUDIN TA , , ,
Shirye shiryen buki aketayi amma ni hankalina baya gare su cike yake da damuwa don ban san yadda zai kwashe da mahaifiyar shi ba.
Na kwanta zuwa dare naji kiran wayan shi ya shigo min a sanyayye na daga wayan gami da sallama a bakina.
Yace kin fara barci ne nace ina naga barci ban san hukuncin da baaba zata yanke a kaina ba kuma ma ai yanzu barci bai ga idona ba tunda nace aure nake so.
Dariya yayi sosai har yana lyalkyatawa yace fada min may zai hana ki barci don Allah ?
Na abubuwa da yawa mana Uncle yace kamar su mai nace wayan san iyaka sai dai ranan da na tare a gidan ka.
Don kullun cikin kawo kudi ayi kaza nake yace look nafa fada maki bana son tarkace daga ke sai boxes din ki za a kawo min na fada maki .
Nace naji uncle amma dai ai za ayi abinda zan ba yan yinin buki ko ?
Yace kai mata ho wanan kuma kina son ki sawa kan ki nauyi ne nace ki bari inzo in dauke ki daga ni sai ke sai gida na amma kin ki.
Nace wani gidan uncle yace gidana na Abuja mana ba anan zaki zauna ba ?
Nace haba uncle kai ka ga haka ya dace ga hajiya baaba da ranta da lafiyan ta a dauke akaini gidan ka na Abuja ?
Ai ka bata damarta na mahaifiya ta sa muna albarkan aure dariya yayi yace Safiya wanan halin ya kara sa ina son ki wallahi yanzun dai sai an kaiki bauchi ke nan wurin hajiya baaba ko ?
Nace a wani irin murya mai sanyi shiya yafi mutunci uncle yace to shike nan hakan yayi kyau zan fada mata su shirya nan za a kawo ki direct idan an dauko ki.
Muka dan taba hira yana fada min yadda suka kwashe da mahaifiyar tashi nace uncle dama bata san halin da kake ciki ba duk wanan dadewan yace bata sani ba.
Kuma ko yanzu na fada mata ne don kada daga baya tazo ta zargeki ga abinda ba laifin ki ba ya kawar da zancen da fadin zan turo maki da sako gobe sai ki kara kiyi hidimar bukin dashi yan uwa na zasu zo ranan alhamis da kayan lefen ki wanda naso ace madam ne zata zo dashi.
Amma wanan matsalar yasa baaba tace daga wurin ta za a kawo komai yadda ya kamata nace Allah ya kaimu lafiya amma ni da an bar lefen don baaba ta riga ta aiko min da akwati biyu yace ta fada min wanan ai mun gani muna so ta hada maki wanan kuma ni na hado maki shiya kaini Dubai dama.
Mukayi sallama ina mai kara yi mashi godiya ya kashe wayan na sauke ajiyan zuciya.
Ina mai ci gaba da tinanen wanan baiwa da ubangiji yai min amma ma kuma baiwan sai yazo min a bahaggon rayuwa.
Washe gari ya shiga gaida mahaifiyar tashi nan yake fada mata yadda mukayi akan nafi son in tare anan bauchi don ta sa muna albarka.
Murmushin nuna jin dadi tayi tace mashi shiya har kullun bani dana sani da zaben ka don nasan bakayin abinda za a yi da an sani cikin sa.
Ko wanan auren kaddaran na Samira da kayi don yan uwanka ne da sukai hadin ba bincike yanzu gashi an bar mu ciki.
Daren jiya banyi barci mai dadi ba a rayuwa na amma da nai tunane sai naga bawa bai wuce kaddaran sa mutuwa kuma tana iya riskuwan bawa a ko wani lokaci.
Don haka yanzu kafin ka tafi sai a fara shiye shirye tunda buki ya dawo wurin mu don da ina dauka acan za a yi komai.
Bai baro bauchi ba sai da suka gama shirin komai da za ayi a nan ya san nan ya baro garin ina kwance naji waya alaman sako ya shigo min ina dubawa kudine wanda sai da ya sani kaduwa.
Na duba na kara dubawa naga milayan guda chur ya turo min tare da sakon da ya biyo baya na .
Nasan wanan zasu ishe ki komai da kuke son yi har da gyaran dakin ummi yadda ya dace asha buki lafiya.
Ummi na kira kurayan daki nake fada mata abinda ya turo min tsaye take sai da takai zaune tana fadin.
Yarinya wanan mutumin kuwa yasan ciwon kudi ashe nifa abin nasa yana ban tsoro wallahi.
Nace ummi samu kudin yake a lokacin su kuma nema akeyi ko yaushe wanan ai ba koma a wurin shi sai kin ga company da ya bude nasa na kan shi.
Tayi shiru tace duk dai da haka abi abin sannu dai yaya Sani na kira da ummi ta fita yazo nake neman shawara a wurin shi yace yanzu abinda za a yi shiryawa zakiyi mu samu Amina aminiyar ki can birni ita zata taimaka maki da sharan da ya dace tunda sune yan birni su suka san abinda ya dace ayi.
Banki ta nashi ba don shawara ne mai kyau ya bani ko banza ya kamata tun farko in neme ta amma na manta da ita.
Don haka shiryawa na yi muka nufi gidan su ni dashi da Rukaiya da tace zata bimu mun isa mun samu taro na arziki a wurin mummy din .
Bayan ta gabatar muna da abinsha cikin wanda takeyi na sana an ta sai na fito mata da maganan abinda ya kawo mu.
Taji dadi sosai tace bari ta kira Amin nan taji yaya za ayi nan ta buga mata waya ta dauka sun gaisa sai take fada mata gani a gidan ta ga kuma bukatan da ya kawo mu zamu zo wurin ta.
Ina jin yadda take murna tace ai ba sai na zo ba gobe ita zata shigo sai a san abin yi mun ji dadi sosai don haka muka koma gida.
Daga yaya sani har yaya Nura basu zauna ba don duk abinda ake so suke zuwa birni su sawo su dawo shafiu kani na ma ba abarshi baya ba.
Amina ta iso da kaunan mijin ta dake zawarci a wurin ta nan suka shiga shiri do ba lokaci issashe gare mu.
Komai an kamala don haka aka kai gidan gwago ana tarawa a can nima na bar gidan mu can gidan gwago din na koma.
Ranan da yan uwanshi zasu iso ana gobe zamuyi walima sai abin ya taru yai masu yawa nidai nawa ido sai dai ina kewan anty na don da yanzu itace zata shirya min komai.
Maimakon bakin da muke jira su iso yaya Saadu ne da iyalin shi suka iso da mahaifiyar Samira da yayanta mace da na miji sai Sadiyan shi da tace zata biyo su.
Nan aka shiga murnan ganin su sai dare bakin shi suka iso garin don haka aka kaisu gidan su Amina a can aka sauke su.
Su yaya Saadu kuma suka sauka wurin mama amma ita Samira da yarta dakin ummi na suka sauka don tace can ne dakin su.
Sai da safe suka gabatar da kayan lefen da suka zo dashi bisa jagorancin mahaifiyar Amina da ta zamay masu uwar daki anan don har sun saba da itako sabon mata baida wuya.
Ga ganin lefe ga shirin walima da za ayi wanda duk kusan matan karkaran mu mama ta aika masu da mintin gayyata wurin.
Inda Amina ta gyato malama khadija daga birni tazo ta wayyar ma mata da kai akan hakkin aure da na yayan su.
Tako zo din don ta wayar dakan mata a wurin da sanyaya masu zuciya da nasihohin ta daga niimar da Allah yaba mace ta gari da jin tsoron Allah a cikin rayuwan airen ta bawa yaya hakkin da ya dace na fanin kula da hakkin su daya rataya akan uwaye mata.
Alamarin ya kayatar sosai don bazaka fahinci haka ba sai kaga yadda mata suka natsu a wurin har da mazaje a can baya da suka zo don saurare.
Ko wace mace a wurin ta natsu ta kama kan ta alokacin kalaman malama na shiga jikin ta nan aka kai karshe su Amina dasu samira suna ta faman raba masu abinda aka tana don waliman buta da dabino sai abinci a cikin take away.
Taro ya watse lafiya kowa sai sam barka akewa juna inda mafi yawan mata basu koma gidajen su ba suka shigo yinin bukin da ake yi a gidan mu.
Sai da dare ne mahaifiyar Samira da su mama suka kaini wurin baba don muyi sallama saboda da safe sammako zamuyi a tafi.
Ina sungun ne a gaban baba yayi gyaran murya ya fara da fadin ikon Allah Safiya kin ga yadda rayuwa ya koma muna a dalilin ki.
Ni banda abin cewa dake sai fatan alheri da gamawa da duniya lafiya Allah ya baku zuria masu albarka.
Ki rike hakkin aure ki rike mijin ki amana don ko shi din ba makyataci bane irin wancan na farko da mukayi maki jeki ubangiji ya kara sa maki albarka.
Kuka ne yaci karfi na lokacin da naji baba yace don Allah ki gafarce ni Safiya dani da duk wani wanda ke gidan nan.
Shima baba kuka ne ya kumbce mashi don haka da sauri mahaifiyar samira ta jani mukabar dakin nashi zuwa dakin mama sai dakin inna.
Tana uwar dakan ta muka shigo Saadatu ne ta shiga kiranta tace tazo ga Safiya nan an kawo ta wurin ta neman gafara.
Muna jin ta tana cewa ni may zan mata su tafi dai Allah ya sa mu sheda sai mama Jummai da dake tare da mu ta bata amsa da cewa ai mun riga mun sheda sai dai muce gwamma da akayi ba wani abu muka kawota yi ba wurin ki don zama tare a sahirce ma junane.
Ta fito don bata dauka anji maganan ta ba sai cewa take naga dai yanzu Safiya ai ba yarinya bace don duk abinda zamu fada mata ta sanshi Allah ya bada zaman lafiya.
Suka mike dajin abinda ta fada suna fadin amin tare da ja hannu na da uwar Samira tayi muka bar dakin ina sa takalma na naji Saadatu na fadin kai Inna sai yaushe zaki ja muna farin jini gun yan uwan mu ne ?
Ni dai mun tafi banji amsan da zata ba yar nata ba don jasan ba mai dadi zataji ba ga bakin inna.
Mun koma wurin ummi na can suka tasa ta gaba wai tayi min fada nasan ba abinda ummi zata iya fadi a gaban su dama sai cewa tati Allah ya albarkaci aure ku yarinya.
Bayan shi bata ce komai ba sai sharan hawayen da takeyi nima kukan nakeyi a lokacin wanda dagani har ummi bamu san ko kukan may mukeyi ba.
Sai mahifiyar Samira ce ta iya cewa haba ai bai kamata ace kuna kuka ba don abin farin ciki ne ya samay mu bana kuka ba mama jummai tace kuka dole ne gare su ai.
Haka dai aka watse ina jin suna hiran lefen da aka kawo wanda mama tasa akai dakin baba wai akwati har set biyu babu ne kawai babu a cikin sa.
Nan suka shiryasu tun cikin daren da za a tafi na kira mama nace a rabawa yan uwa da abokan arziki da sukayi tsaye a wurin sha anin nan suka zaba daga cikin wanda baaba ta turo dashi akabawa wa yanda suka dace aba.
Mutocin tafiya sun iso da dare nan suka kwana inda yaya Saadu da yaya Sani suka zabi masu zuwa kai ni.
Don dogon luxuries aka zo da ita sai karama don daukan amarya ni dai ban san masu zuwa ba na dai san Amina da Samira da yar uwar ta ne.
Daya daga cikin kayan da hajiya baaba ta aiko dashi nasa wanda Amina ta bayar aka dinka min a birni.
Sai da akazo shiga mota na ke jin yadda suke ta hayaniya nadan bude fuska na ina kallon su nace a raina wai ni Safiya yau akema gardaman rakiya gidan miji haka abinda irun su inna basu so gani ba gare nu gashi yau Allah ya nufa anayi akaina.
Yaya saadu ne a gaban motar da na shiga sai gwagon ummi da mahaifiyar Samira matar shi su samira karamar mota suka shiga da su Amina.
inda yaya Sani da yaya Nura suka jegoranci doguwar motar da mutanen dake cikin ta don shiya bugo yace a cika motar azo da mutane.
Mun sha hanya don duk da sammakon da mukayi sai bakwai na yamma muka isa garin bauchi nan naji abinda uwar Samira take cewa shi yasa ni dan bude fuskana nima in gani.
Acan lagos kuma sai faman zage zage anty ke durawa da taji ance mahaifiyar shi ta tura akai kaya ta wurin ta don har kiranshi tayi din ta fada mai bakar magana sai bai daga kiran nata ba.
Da daren nan maigidan ta ya dawo garin nan ya samay ta tana cika tana batsewa sai da ya huta yake tambayan ta abinda da ke faruwa.
Nan ta shiga labarta mashi karya da gaskiya yana sauraren ta sai da ta gama yace amma ban taba sanin baki da wayo haka ba maimuna.
Jin ya kira sunan ta kai tsaye yasata natsuwa yaci gaba da fadin yan zu ke uwa ce zaki bari har ta saki a gaba ki yarda da bukatan ta bayan kin fi kowa sanin halin ta dana yaranta.
Waima tsaya don Allah idan uwa ta juyaki zata iya juya Sulaiman ne kai tsaye ke kin fi kowa sanin ko waye sulaiman don shi dan kaifi guda na kuma ya nuna maki koshi waye.
Ya nuna maki in dake ayi in ma babu ke zai iya gashi sunyi bukin su hankali kwance yace amma ko da labari za a bani cewa zaki iya yin haka bazan taba yarda ba.
Sai gashi keda bakin ki ba kunya ba tsoron Allah kike labarta min shirin ku na shirmay kin dauka kowa baida hankali ne irin ki.
Jikin ta yai sanyi don ganin daddy bai goyi bayan ta ba dama dashi ta dogara ya dawo suyi ma sulaiman din sheri sai gashi ya dawo bakin su daya da sulaiman din.
Bata san cewa da daddy ake kulla komai ba akan bukin nan yayi mata tas yace yanzu dabara ya rage gareta ta gyara tsakanin ta da sulaiman din da ni.
Nan ya shige ya barta tana tunane tare da yin na daman abinda ta aikata gashi anty uwa taja mata hasara da tasan ita zai ba hadin lefen da yaje da yar uwan shi suka yi.
Don ba karya ba ne anty tana da son abin duniya dama maishi akace abu bai isan shi su ko yan uwan Sulaiman sai murna sukeyi yana yi dasu yanzu.
Don dama hurda da ita ya hana shi ya kula da yan uwanshi amma yanzu gashi su yaba su aiwatar mai da komai yadda ya kamata su yi.
Gida ne mai kyau na zamani wadda ya tsaru iya tsaruwa wurin haduwa wata da gani tobashiyan shi ne ita tazo tana muna jagora zuwa ciki sai zolaya take yi.
Maman Samira ta sani karanta wasu ayoyi daga cikin kurani tare da wasu adduoi na neman tsarin ubangiji.