← Book details Bahagon Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 2 OF 4

Kashi daya a bani a hannu na sauran a koma dashi gida da kudin dari biyu ne da hamsin da dan kai.

Bahagon Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 117 min read

Duk da an kawoni da kayan abinci mai dan dama sai sukace mu dauka muyi amfani dashi sun kara jamin kunne a kan zaman aure mukai sallama dasu akan washe gari zasu tafi don baba yace kada su wuce kwana biyu a can.
Aka barina ni daya a gidan a garin da ban san kowa ba shiru banga shigowan shi ba gidan har bar ci ya dauke ni.
A tsorace nake sai haushin karnuka dake tashi unguwan da karan motoci jefi jefi.
Dayan dakin dake bude na shiga na rufe kaina a ciki har barci ya fara dauka na naji ana bugun gidan da karfi.
Tsoro ya kami sai da naji yana antaya min zagi na taso a tsorace daidai lokacin da aka turo kofan da karfi dama ba a rufe kofan yake ba .
Yasha yayi tatil dashi sai rangaji yake yi a tsakiyan falon na rakube gefe daya ina kallon ikon Allah yau ni safiyane a gaban dan giya.
Magana yake son yi amma layi ya hana maganan fita ya kwasa da tangadi ya shige daki da kyat ya iya bude kofan.
Shiru shiru banji ya fito ba na tashi na dan leka dakin da ya shiga kwance yake rub da ciki har takalman shi yana nasari da karfi.
Na sauke ajiyan zuciya na juya zuwa kofan na rufe da key na kashe wutan falon na dawo na takure a wuri daya a falon.
Inata tunanen wani irin zama zamuyi dashi a gidan haka a cikin maye duk jikin shi ya baci farin kayan dake jikinshi na jeans da farar tieshirt duk sun baci da laka.
Nasan yasha faduwa ba iyaka a hanya ne yafi a kirga kafin ya iso gidan cikin maye.
Washe gari da asuba na tashi ina jin kiran sallah can nesa da mu yana tashi don haka nasan asuba yayi ke nan.
Na idar da sallah gabana sai faduwa yake yi don far gaba da tsoron shi don ban san mene zai wakana ba in mun hadu.
Na mike da kyat na fito falo na fara gyan wurin koba a fada ba kin san may zai tashi gida akan warin taba.
Ina tunanen may zan girka na shiga kitchen tsaye nayi ina kallon komai a hankali don komai akwai a kitchen din na fanin girki.
Dabara ya fado min na nagirka abu maidan ruwa ruwa tun da safiya ne yanzu.
Nan na zage na dora faten dan kali da turawa sai kunun custad dana gani na dama har na gama babu motsin shi.
Na kara gyara ko ina na shiga dayan dakin da na mayar nawa wanda babu komai sai dan gado da katifa sai yan kayana dake a gefe daya.
Na gama zan fito na debi abincin da na girkana muka gwabza karo dashi zai shiga kitchien din shima.
Ya sauya kayan jikin shi zuwa dogon jellabiya mara hannu hannushi rike da taban da ta kusa kare waba.
A tsorace naja baya kadan na rabe tare da dan tsugun nawa nace dashi ina kwana.
Kallona kawai yayi ba tare da ya amsa min ba yana zukan taban shi wanda warin shi ya banbanta da wanda na sani.
Na raba shi na wuce zuwa falon sai naji yace uban wa yace ki rufe min kofa daren jiya dana fita.
Kallon shi na dan yi nace uban wa ya rufe ma kofan har ka bude ka shigo din in an rufe ne.
Ya dauki kallon na daga sama har kasa gaba daya na rufe jikina cikin hijjabi babba har kasa.
Yace dube ki yar iska kucakan baza sai iya bakar magawa wa babba zanyi maganin ki gidan nan.
Zanyi magana kenan aka buga kofa gidan har sau biyu ya nufi kofan yana fadin who's on the door tare da bude kofan kadan.
Lokacin na samu daman shigewa da abincin dake hannu na daki ashe kanin shi ne ya kawo muna abin karyawa daga wurin gwago.
Kiran da yake min ne nasan cewa shine ya shigo gidan ina daki na karba mashi na fito saye da hijjab dina ina gaida shi cikin ladabi naci yaya sa,adu ina kwana.
Da fara,a a fuskan shi ya amsa min tare ta zolayana na wasan tobasai yana cewa yau ga bakauya a lagos.
Murmushi nayi ina jin kunyan mayar mashi da mashi da magana.
Shiko gogan ya zauna ya harde kafa har ya kara kunna taba yana zuka a hankali sai naga annuri dan uwan yarage fara a a fuskan shi.
Da harshen turanci yake ce mashi baidace yana sha a cikin gida ba haka ko banza yaga ni karamar yarinya ce fa.
Mind your business please, don't boader me, is my house ina da right din abin da nake so in bata so ta fita waje.
Sai ya kada kanshi yace ni zan tafi dama mummy ne tace na kawo maku breakfast nace ai muna godiya wurin gwago amma dan tsaya in zuba maka abinci mana.
Baiki ba yake cewa tou har amarya ta fara girki ashe sai ya mike yana cewa dan uwa ai dole taga kayan banza mana.
Uhmmm uhmmm naji dan uwan yace dashi da yake fadan haka ya shige yana ce ma kanin zan dan watsa ruwa ni.
Shigewan shi na kawo mama yaya saadu abincin yace tun banci ba kamshi ya buge ni da alama amaryan namu ta iya girki.
Dan murmushi nayi kawai na juya zan tafi yace ji mana sai na dawo na zauna a kujeran dake dan nisa dashi.
Ina wasa dan yatsun hannu na a hankali yace Safiya nasan cewa ba, a kyauta maki ba don baki san ko waye Ahmed ba kosu kan su iyayyen namu basu sani ba ne.
Nai dan murmushi nace na sani yaya saadu yace kin sani fa nace eh don shi ya fada min komai kuma gashi ina gani a zahiri.
Ya ce Allah sarki safiya kiyi hakkuri karki biye mashi ku zauna lafiya duk abinda yake yi ki barshi da Allah tsakanin shi ne da mahaliccen mu.
Ke dai abinda kawai zan fada maki shi kiji ki ki jini dan ko ita mahaifiyar tamu sai hakkuri don son da take mashi yayi yawa har yakai bata iya tsayawa tai masa fada.
Don haka kar ma kice zaki dinga kai kara wurin ta don bata so, wanan zai iya kawo tsana a tsakanin ku.
Nace nagode yaya saadu yace zan dan rika lekoki jefi jefi ina duban lafiyan ki kinji ko kedai ki kula da hakkinshi da ya rataya a wuyan ki.
Godiya na kara yi mai ya mike bayan ya gama cin abincin ya tafi ya barni a cike da tunane a raina.
Ina zau ne a dakin ni daya sai gashi ya fado min kwatsan a dakin yana faman kale kalen dakin kamar bakon shi.
Hijjabi na dake gefe daya namika hannuna na dauko yace kada ki sama ki saka wanan tsunman a jiki ki yar kauye kawai.
Sai ya ja tsuki gefen gadon da na ke zaune ya samu ya zauna kadan yana may bin dakin da kallo har lokacin.
Kwata kwata na kasa sakewa a dakin don ban taba zama da namiji hana ba a rayuwana.
Sai naji yace ke baki iya gaisuwa bane ko a gidan ku ba a gaisuwa safe ne nace ai da zun na gaishe ka a falo.
Sai naji yace may kuke magana a kai da Saadu naji ya dade bai tafi ba nace abinci ya ke ci.
Ido ya kafa min bai yi magana ba na wani lokaci saidai bina da yaya da ido yana mun kallon kurulla do bai taba ganina haka babu hijjab ba sai yau.
Yace koma may ye shiya sani nida gidana ba wanda ya isa ya hanani abin da nake son yi don kawai wani yaji dadi.
Na dukar da kaina kasa idanuwa na suka kawo ruwa ya mike yana cewa common abincin ma ba a koya maki yadda zaki ba mutum shi ba.
Ya fice na sauke ajiyan zuciya a hankali tare da mikewa nabi baya shi ya zauna wurin cin abincin da aka tanadar a gidan.
Abincin da gwago ta aiko na fara budewa sai naga kosai ne da kunu mai zafi yace rufe shi wanda kika girka zaki bani nasan girki ba wani dadi sai maneji kawai.
Shi na zuba mashi na juya na dauko mashi ruwa ga kwalabe nan barkatai a cikin fridge din wanda ban san kasu ba .
Kafin wani lokaci har ya tashi da abincin a binka da mashayi dama cikin na rurin neman abin da yaci duk ya cin ye duka.
Na kwashe kayan a raina nace ka kaishi in dai gulma ne abincin da yace ba dadi gashi ya lashe duka bai bar komai a kwanon ba.
Don gatse nace ko in karo ma ne?
Ciki daka tsawa yace dani don Allah ban wuri kin ce ko dadi abincin yayi ne kawai dai don ba abin da zan ci ne shiya sa.
Kayan na kwashe na wanke na koma daki na dan kwanta do in huta saboda gajiya a jikina.
Na dan kwanta sai barci ya dauke ni ban falka ba sai wani lokaci can a cikin barci nake jin kida na tashi a gidan.
Na bude idanuwa da kyat kallon lokaci nayi idan ba ai sallah ba naga lokaci da saura don haka nace barin dan samu abin da naci don wanda na diba da safe ban ci ba sabo zuwan yaya saadu yazo gidan.
Na fito falo a zatona ya fitane yabar gidan na tashi kwatsan sai na gan shi kwace rigingine saman three seater dagashi sai gajeren wando yana busa taba sigari yana busa hayaki cike da yanga da gwanewa.
Tsoro da firgici ne suka dira min a zuciyana don ban taba ganin namiji a haka ba da sauri na juya zan koma daki naji yace ke bani son shashanci fa.
Nace may nayi kuma ?
Ya dago ya dan harareni ya koma ya kwanta yana cewa may kike nufi ne nufin ki ni zan dafa muna abinci da kika shiga daki kika kwanta.
Kallon wurin da kulla yake nayi sai naga alaman an cinye abincin nace ba akwai abinci ba a kulla.
Ba surutu na tsai da ke ki min ba abinci na ce ki dafa muna, ban tsaya magana ba na wuce zuwa kitchien din.
Tsaye nayi ina tunane yadda ya dora abincin nan shi kadai a cikin shi kuma wai yana neman kari.
Aiki nakeyi amma karan kidan da yasaka ya damay ni gashi babu hali nace ya dan rage ya sauke min kwandon balai a kaina.
Sai da na hada komai na fito zuwa sallah don lokaci yayi na a zahar na shiga bandaki na dauro alwala nafito na tayar da sallah.
Na koma kitchean di bayan na idar na karasa aiki na daya rage min kafin wani lokaci na hada abinci ko na aje mashi a falo nai shigewa na ciki.
Ina gama ci sai gashi cikin shirin shi do lokacin karfe biyar na yamma ya kusayi ko gabana ban da bugawa ba abin da yake yi.
Naji yace abincin fa nace dashi an gama ya dan harare ni tare da fadin ni kenan zan zubawa kai na ko.
Mikewa nayi nabi bayan shi zuwa falon yana zaune na zuzuba mai komai harda gaiyya nayi wurin zubawan amma duk haka sai da ya lasheshe kaf.
Ya mike ya dan shiga daki zuwa can ya fito ina jin lokacin da ya fita ya bar gidan.
Fitan shi gidan yasa ni sauke ajiyan zuciya namile nafito na fara dan gyaran gidan na murda kofan dakin shi na jita a kulle nace kai ka sani.
Naga komai na dawo falo na zauna ga tv amma inajin tsoron kunnawa yazo yace wayace in taba mai kaya.
Kewan gida ya dawo min a rai na zauna ina tunane ina kukan rashin yan uwana da nayi kusa dani.
Na saba a gidan mu in gari ya waye hayaniya kawai ya isheka tun safe har dare ihun yara ne zai tare ka a gidan.
Gashi yanzu nazo nan garin da bansan kowa ba ina zaman kadaici duk da unguwa guda muke dasu gwago na sin amma har dare yayi babu wanda ya sake zuwa wurina bayan yaya saad duk da kuwa tana da yara yan mata zasu girmay ni ga shekaru.
Ko da yake nasan wanan sana, a da takeyi bazai basu lokacin samun zuwa yawo ba ko wani lokaci.
In gari ya waye tun karfe hudu idan ta tashi bata da lokacin komawa kuma yi wanan sauke wancen har dare .
Jama, a sai shige da fice suke a gidan wanda akasarin su hausawa mazauna lagos da ke zuwa sayen kayan iri na arewa da babu shi a can.
Yaran ta mata ko wace nada aikin da zatayi nata cikin sana,a da take suna taimaka wa uwarsu dashi.
Suma mazan kakani ba a barsu a baya ba wurin bada nasu taimakon in ba haka ba yaro ya gane kuren sa ta hana mai kudi.
Yau ma kamar jiya bai dawo ba ina jin barci na ja kofan dakin da nake ciki na rufe kwantawa nayi na makure a wuri daya cikin tsoro.
Karfe biyu saura naji ya dawo gidan a cikin mayen shi da yasaba ina jin shi yana ta surutain shi da banke banken kaya ban dai fito ba balle.
Can nabar jin motsi haka yasani n yayi barci kenan Allah ya kyauta nace tare da gyara kwanciyana dakyau sai dai babu barcin kwarai gare ni.
Da asuba na fito in yi gyaran falo sai ganin shi nayi tirim kwace tsakiyan falon yayi amai da fitsari ya bata wurin dashi.
Take idanuwa na suka kawo hawaye nasihan da akai min ne yazo min a rai a hankali na juya zuwa ciki na dauko abin kwashewa na fara gyara wurin da ya bata nai nisa da gyara motsina ya tayar dashi.
Daga barcin naga ya mike kata kata zuwa ciki nan naji dadin tsabtace wurin da kyau ina yi ina kuka da addua a cikin bakina hawaye nata zuba min.
Nagama na shiga na dora girki abin da zamuci don nasan da ya tashi abinci zai nema in banyi kuma iyayyena su sha zagi.
Har nayi na gama ban ji motsin shi ba na shige nai wanka na fito bayan na gama gyaran jikina na fito do in debi abinci in ci ga dai abincin na diba sai na tasa shi a gaba na kasa cin koda cibi daya ne.
Nai zurfi ga tunane najiyo motsin shi daga dakin shi lokacin har karfe takwas da rabi saura na safe rana ya soma fitowa a gurguje ya fito yana sauri.
Ina kwana nai mashi ya amsa a dakile kamar wanda baya son amsawa bani abinci na yace dani ya nufi wurin cin abincin kai tsaye a ranan nasan wai ashe yana aiki ya makara saboda ya bugu a daren jiya.
Nidai na zuba mai na koma daki yana ci ya fice a gidan ban sake jin duriyan shiba kuma har rana ina zaune ni kadai a gidan nace barin leka waje inga yanayin uguwan.
Uguwa ne irin mai jamma, a din nan da yawa kowa na harkan gaban shi ba ruwan wani da wani kowa tashi ta fisshe shi din nan.
Na dan duba yanayin na koma ciki tare da jan kofa na rufe kwantawa nayi sai barci ban tashi ba sai biyu da rabi.
Na tashi ina salati don makaran da nayi wurin yin sallah na dade zaune ina adduoi na neman tsari da mafita ga Allah.
Na tashi nafito duk da akwai dan sauran abinci amma sai da na girka wani na rufe.
Don ina gudun ya dawo ya hauni da masifan don ni yanzu tsoranshi nake ji sosai gani nake zai zo ya samay ni da duka idan ya je ya shawo.
Na gyara gida na dawo falo na zauna can dai nace barin kuna tv in kallo ina kunnawa yana a wani tasha da aka badala iskancin filin Allah maza da mata.
Da sauri na kashe karshe ma a mike daga falon na koma daki na zauna ba wani aiki a gareni sai na tunane.
Sati na guda a kidan muna wanan zaman in ya fita run safe baya dawo gida sai dara ya raba idan zai shigo kuma a buge zai dawo gidan.
Tun ina tsoro har na fara sakin jikin na na saba da zaman kadaci ba mashigowa nima bana zuwa wurin kowa.
Duk da zaman da muke yi dashi tun ranan da yai mai da fitsari nakwashe ta rage zagina da tattara sai dai ba sakin fuska ko kadan a wurin shi.
Nima dai hakan ne a wurina daga gaisuwan safe zan ja bakina na tsuka sai kuma wata goben in Allah ya kamu lafiya.
Yau ma zai fita na gyara gidan nake rokon shi da ya kunna min tv zaman kadaici ya isheni har zai yi magana komay ya tuna sai da ya gama jan rai ya hada ya nuna min yadda zanyi.
Ya fita ina zaune ko ina zaune ni daya kallo ya dauke min hankali wani indiya ake yi mai ban tausayi kofa naji ana bugawa.
Nai mamakin jin bugun kofa a lokacin na tashi na saurara kofan ake bugu a hankali na bude kofan.
Sisters din shine su biyu tsaye a kofan na tare su da mutunci sai naga suna amsawa dakyat suna wani yamutse fuska.
Nace sai yau anty ?
Naji sadiya tace min tauuu,
Na sake cewa ina su gwago suna lafiya ?
Ta amsa da lafiya kalau.
Nace dasu ku zauna mana.
Sai naga sun kalli junna su kamar ba zasu zauna ba sai dai suka zauna din kitchean na wuce na fito da cups da goran ruwa na kawo masu.
Ita dai habiban ko magana bata son yimin nace dasu bissimillah ga ruwa sai naga sun kalli juna sun tabe fuska .
Sadiyan tace bar ruwanki dama mu hanya ya biyu damu nan muka ce bari mu biyu magani ko yaya yana gida mu gaisheshi.
Nace yana wurin aiki sai daren ya shigowa habiban tace ke sadiya mu tafi don Allah hakan haka auka fice nabisu da idanuwa cike da mamaki yan uwan nawa kenan kuma yan uwan miji na.
Da wani zanji a raina wai da nashi ko da nasu tsiyar da naga sun fara nuna min ina ce wurin su zan ji dadi ashe abin ba hakana yake ba.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , ,


🧕🏿9️⃣🧕🏿


DON ALLAH YAR UWA KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA BA DON BA A YAFE BA DON ALLAH KI YI HAKKURI DA HAKKIN WASU, , ,


A kwana a tashi zama yai tafiya saida babu wani jin dadin aure a gare ni kullun zaman hakkuri nake yi garama da zaman gidan mu mai wahala da wanan zaman ukuban da nake cikin sa yazu.
Ko ba komai a gidan mu ina ganin iyayyena ina jin dadi da yan uwa na nan ko haka zan wuni banyi magana da kowa ba na tsawon kwanaki.
Sai da na cika wata biyu cur a gidan ranan yace in shirya zamu tafi gidan su da farko murnan zuwa nayi sai kuma na tuna da abinda yan uwan shi sukai min sai murnan ya koma ciki.
Don yanzu ma ban san abinda zanje na sama a gidan sai dai nasa a raina cewa zan kama kaina da sha, anin su a rayuwa na.
Na shirya cikin cotton lace light green mai yan duwatsu kanana sai hijjab dina da na saka a falo na samay shi yana jiran fitowa na.
Simi simi na fito tare da cewa gani yaya mikewa yayi yana mai kare min kallon muka fita nasan kwalliya na ne bai kashi ba.
Don shi indon ta nashi ne baiki ace na fita ba hijjab a jikina ba ko na yafa dan gyale a kafada na mu fita yafi son na fito yar bariki sahihiyar ta amma ni na kasa yin hakana.
Mun shiga kwanan gidan tun daga nesa muka hango jama , a masu sayen abinci sun cika wurin sai ya dan ja ya mota ya tsaya nesa da gidan na su.
Yace cikin wani murya ke ki saurare ni kiji may zan fada maki dakyau hakan danaji yasa na natsu ina sauraren shi.
Yace bani son naga kin fito waje inda suke sana a ar su din nan kuma ki tabbatar kina saye da wanan abin har mu fito cewa hijjabin kenan.
Duk kika yarda na ganki wurin wanan sana an ran ki zai baci ki kama kan ki da dabiun wurin nan a sanyaye na amsa da to yata da mota muka karasa gidan.
Maza da mata a waje sai cin abinci suke yi tuwon shinkafa miyar ganye da agushi sai kamshi ke tashi.
Tunda muka tsayar da motar mu yan wurin suka sako muna idanuwan su da kallo maza da mata yan duniya.
Nan aka fara yi mai kirari da sunan shi na tan bariki nidai daga kafa nakeyi amma ji nake kamar zaa ce ke in sheka da gudu.
Wani rumfa muka nufa inda gwagon nawa take ciki ga yan matan ta nan gefe daya suna kidayan kudi sunci kwalliya sun kure adaka.
Duk yawan taron nan dake ciki bai hana ni zuwa gaban ta na durkusa ba in gaishe ta sai cewa tayi yau kun ga daman zuwa ku gaida ni koda yake baki da laifi ai ga mai lefin nan gaban ki.
Bai bata amsa ba wata maidan buje tazo ta run gumay shi sai yaja hannun ta sukai waje suna rike da junan su.
Nauyi da kunya suka kamani tace tashi ki zauna dan duniya ya hadu da mashiririta yan uwan shi.
Na juya inda sadiya take ina gaishe su don ko banza sun girmay ni ga shekaru.
A dakile ta amsa mim gaisuwa sai ga wata yar fara mai dan buje tazo da hausa ta gwargwari tana cewa a wanan ne amaryan tamu.
A gaskiya hardguy ya iya zabe mace Allah yasa a zauna lafiya amarya sai hakkuri da mutumin fa don naganki yarinya karama shiko gashi tsohon tazuru.
Cikin wani murya gwago tace da ita salima me i no wan dat wooo sai salima tace sorry ma.
Nace ashe su gwago tsofin bariki ne har da turancin go and come an iya a raina nake fadar hakan wata yar baka mace tazo ta katse min tunane da cewa.
Wai ki shiga ciki inji hardguy saina rashi na bi bayan ta ina jin habiba na mata magana sai dai ban fahinci may take fadi ba.
Ina nan zaune sai gata ta dawo tana cewa may za a kawo maki ne murmushi nayi nace a a barshi na gode a koshe nake ai.
Sai mamakin wanan rayuwan nake mace da auren ta tara kananan yaran mata a gida ana shar holiya wai da suna neman kudi.
Zuwa can ta dawo dauke da abinci a cikin tire tana cewa yace in kawo maki wai kin dade baki ci abincin hausawa ba ta sauke tire din naga tuwon shikafa ne da miyan alaiyahu ya ji agusi da naman shanu tace dani ko baki sin wanan akawo maki na yauki.
Murmushi nai mata nace a, a barshi kawai ko wanan ma na gode ai sai ta kashe murya tana dan waige waige tace mijin kine ya saya maki indon hajiya ne har kizo ki tafi bazakici komai ba a nan.
Kin santa da shegen son kudi koda yake ke bakuwa ne a gidan baki san komai ba tukun tun tafiyan ta ina zaune ni kadai ban kuma taba abincin ba duk da ina son ci.
Can sai gata ta dawo dauke da kwalban coke a hannuta mai sanyi ta dire min tace kina nan zaune ke kadai ba, yi hakkuri dan Allah hajiya bata tasowa yanzu sai ta rarage cinikin ta.
Ina nan zaune sai ga sadiya ta fara shigowa gidan cikim gidan daga wurin sanaar su tace a, a kina nam zaune na ashe.
Murmushi nai mata kawai sai ta dan fara rage kayan jikin ta zuwa can ta kai kallo ga abincin dake aje a wurin sai take cewa a, a baki ci abincin bane.
Aikoda kin ci abincin ki don mijiki yau yana can ya samu yan matan club suna sharholiyan su dama ya dade baizo ba sai yau.
Wani irin naji a raina amma na dake a fili cewa nayi abin da suka sabayi ne yin hankan ya zamay masu jiki ko.
Ko bata fahinci may nake nufi bane sai naji tace min bari in debo mai zafi nazo muci tare tunda naga kina jin kunyan ci.
Nace aida kin bari naci wanan din bata saurare na ba ta fita sai gata ta dawo da wani abincin wanan karon miyar danyan kubewa ne ta debo muna.
Tare muka zauna muna cin abincin muna hira sai na fahinci bata da matsala ita har take cewa dani tankan so zuwa gidan mu amma sai take tsaro kamar nace mata tsaron mai sai dai na kyale ta kawai.
Nan na taya ta sance kanta da ya tsufa da kitsu nai mata wani kitsun duk wace ta shigo ta samu muna kitsun sai ta yaba da kyan kitsun da nai mata.
Nan sukai ta fadan zasu zo in masu kitsu a gidan suma habiba dai ko kallo ban isheta ba sai
A wurin ta nake jin wai yaya saadu yai tafiya dama shi ba mazauni gida bane yana zuwa kasa ibom neman kudi ne a can.
zuwa can gwago na tashigo daka ciki lokacin ina masu shara son ko lokacin gyaran wuri basu dashi.
Kullun ana aikin naiman kudi a waje koma nasu kaca kaca a gidan yake nai ma wurin tas na kama na wanke wa na wanke.
Saida ta samu wuri ta zauna a dakin nata wanda na share kale kale take bin dakin dashi ta kwala min kira ina bakin famfo na amsa nazo.
Nazo na durkusa gabanta sai tace dani kwanaki na aika yaran nan gida ku kikai masu rashin mutunci su da gidan dan uwan su.
Ni har na aika a dibo min dana kice wai barci yake baki tashe shi ke har yaushe kika san dadin miji kega mai miji.
Sai sadiya tace mama na fada maki fa ba haka tace ba tace da sadiya ke rufa min baki yar uwar takine zatai mata karya ko may ?
In dai zurian Rabi ne wani irin tuggu ne basu iya ba matar da kullun cikin kullin sheri takewa kishiyoyin ta ta hana su shakat a gidan.
Na dago kai na kalle ta don jin kallaman da ta fadi gamay da mahaifiyana sai tace eh mana.
Ko kina nufin bansan shirin da kukayi akaina bane dashi kan cewa zaki shigo ki mallake min da sai a baninda kuka ce da ke da uwarki a kan shi.
Na dukar da kaona hawaye na tsiyayo min a fuskana ganin ina kuka tace a hasale karya na fada ke nan ko kina nufin nai maku sheri.
Nace haba gwago wallahi tallahi bansan komai ba akan haka, sai habiba tace wallahi karya kike yi an ina jin ki ranan daurim auren ku wai suna maki huduba
Ita ta fada habiban ta fada haka suka sani a gaba da zagi kamar ba yar dan uwan ta nake ba shi babana yai mata halarci ita kuma tai mai son ranta
Kwasan ya fado dakin kamar wanda aka turo ganin yadda nake nake kuka da rantsuwa a gaban mahaifiyar shi da habiba nata yanka min zagi.
Cikin mamaki yake kallon su ya kalle ni yana son jin abinda ya faru haka suke min masifa ina kwasan kuka.
Sadiyana ta fara mashi bayani sai uwar ta katse ta jikin shi yai sanyi ganin yadda nake kukan da rantsuwa sai zagi suke zubamin.
Ke tashi muje hakana yace dani ya dubi uwar yace muzamu tafi don banga amfanin yin hakan da kuke yi ba .
Simi simi na miki na jawo hijjab dina dake rataye ga igiya na saka ina fadin sai amjiman ku itako gwago sai faman fada takeyi tana cika tana batsewa.
Nan ya biyo ni baya ranshi yana mai suya yasani sarai safiya ba zatai wa yan uwan shi haka ba sheri yaran suka kulla min wurin uwar su tun ranan da yazo ta fada mai ya samani da maganan nai mashi bayanin komai ya yarda
Nika sai faman kuka nake ina tunane a raina wanan wace irin kiyayya ne haka may ne mata a rayuwan ta take shirin nakasa ni.
Har muka isa gida tunanen maganganun su nake akaina may nai mata a rayuwa na take son gani na a cikin ukuba can na nisa nace Allah ya fata duk abinda ya shirya zai samay ni babu makawa sai ya faru dani .
Na share hawaye na na mike zan shiga wanka ya shigo dakin yana fadin may ya hadaki da su habiba ne na ce babu komai nidai a rayuwa na.
Sai yai min wani kallon na sama da kasa yace zanbin cika idan kice baki da gaskiya zaki gane kuren ki.
Yana fita gidan nasu ya koma gwago najin dawowan shi ta samay ta ta cika fam har lokacin don yar ta habiba ta zugata ta zugu akaina.
Yace mummy may ke faruwa ne tsakanin ku da yarinyar nan ina ke kika hada wanan abin bai dace ba kuma ace akwai matsala a atsakanin ku yanzu.
Tace cikin fada kaga rufe min baki don wa nake wanan fadan duk mugun nufinta akan mu dakai mun sani duk sherin da aka kulla azo ai muna gashinan yana fita fili muna gani.
Mummy har wani hali ke gareta wanda baku sani ba tace kai ina zaka sani tunda a boye akeyi don a mallake ka da yan uwanka.
Niko kowaci tuwo dani miya yasha munafuka sai ta dinga yin abu simi simi da ita wai ita ta kwara mugun halin na nan tattare da ita na ta shiga dura mai akidar banza daiyi min wai mun zo da nufin raba shi da kowa kuma nu cinye dan abin hannun shi na gudu.
Tun bai dauka ba har ya fara dauka yana cewa aiko zata gamu dani dama ni ba yarda nayi da wanan yarinyar ba sam.
Sai da ya biya wurin abokan shi ya dawo gida misalin karfe tara na dare ya tarar dani na fito bandaki daure da tawul ya fado min dakin da masifa.
Ke mara mutunci dama na fada maki in na bincika naji baki da gaskitya zan dauki mumunan mataki a kanki watau kun hada baki da iyayyen ki kizo ki haince mu ko.
Idanuwa na suka kada sukayi jawur mamaki da takaici suka rufe min zuciya yace an turo ki anga kudi banza anzo aci ko har a kashe ni.
A hasale na bashi amsa da cewa kai dan Allah har ina kudin yake da za, a turoni tun daga arewa har nan ci ku kudi ya rufe wa ido kudin da ana nema kamar ba neman su akeyi ba.
Kafin in karasa magana na sai naji yakaiwa bakin nawa naushi saida naga wani wuta ya gitta min na duka tare da dafe fuska na.
Nadago nace ka dukeni akan gaskiyata ban karasa ba ya shiga duka na har tawul din dana daura yana sancewa.
Baisa ya daina ba sai da ya barni kwance a dakin ya fito yana maida numfashi daya baya daya ya nufi dakin shi.
Kuka ma kin zuwa yayi min a idona na dade duke a wurin da kyat na daga nakai bakin gado a haka na haye gadon na kwanta cikin dare zazzabi ne ya rufe ni mai karfi saboda zafin bugun da na sha.
Da safe har ya fito ban fito daga dakina ba ya leka ko na gama abin karyawa sai dai babu alaman ko fitiwa banyi ba lokacin.
Ya shigo dakin da niyar yai min fada nan ya samay ni cikin bargo ina rawan sanyi zazzabi mai karfi ya rufe ni.
Da zumar yai min fada ya shigo dakin sai ya samay ni a haka kwance cikin bargo ina makerketa yadan ja ya tsaya.
Ya dade tsaye yana kallona sai ya juya ya fita zuwa can sai gashi da paracitamal da goran ruwa ya kawo min da kyat na tashi ina sha na koma na kwanta.
Wasa wasa sai da na kai kwana uku kwance ina jiyan dukan dayai min tun wanan lakacin gaba daya zaman ya karasa jagulemuna a gidan.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , ,


🧕🏿🔟🧕🏿


NAGODE DA KUWALAWAN KU GARENI YAN UWA DA BAZAR KU MUKE RAWA

IDAN BAKI BIYA BA DON ALLAH KARKI KARANTA YAR UWA DON A KWAI NAUYI A KANKI.


Nazama sha tikan duk dare yaje yawon shi ya dawo, acikin maye zai nemay ni idan nakiya kuma zai min mugun bugu ya biya bukatan shi.
Gari kuma ya waye in tashi in girka mashi abinda zai ci don ciki ya kwakware mai da ruwan giya.
Daya tashi babu abin da yake nema sai abinci mai dan nauyi da zai cika ciki dashi idan ya gama wani bi ya kara nema na koda karfin tsiya ya biya bukatan shi.
Acikin irin haka na ranan yana tsaka da buguna, sai ga yaya saadu ya shigo gidan namu yayi sallama har ya gaji amma yana jiwo ihuna daga ciki.
Kai tsaye ya fado cikin gidan ya samu ya danne ni ya ta bugu a kasa da karfi ya tire shi samana daga ni sai underwear a jikina.
Ya na ganin na haka nan ya juya baya da saurin shi shiko gogan sai mazurai yake da idon yana mai mai da numfashi .
Sai ya hau zage zage yana fadin sai ya halakani a gidan nan wani tsawa saadun ya daka ma wan nashi daidai na samu na daura zani a jikina ta dawo ciki yana cewa .
Amma bros baka kyauta ba wallahi ina yarinyar ga taga karfin ka da zaka dinga dukanta haka yace dakata mallam kada kazo min gida kace zakai min nasiha kan wanan bazan yarinyar mara mutunci.
Yace haba bros matar kace fa ta sunna kake zagi haka ya kamata ace yanzu ka daina abubuwa da daba ka kama kanka.
Ya juya wurin ina ta faman kuka yace kin ga Safiya ya isa haka shiga ciki ki kitsa kan ki kizo haka bakyau wallahi.
Nasamu naja kafana zuwa daki wanda da kyat nake dagata don wallah ina shiga naji yana cewa dan uwan nashi wanan abin baiyi ba wallahi.
Na dawo sadiya ke fada min irin sherin da habiba ta kulla mata wurin mummy a gaskiya abinda kuke yi baku rike amana ba.
Yace wani amana can dama waya ce yana son ta ko waya nemota sai dan uwan yace mummy kuma hakan da akai maka bakaji dadi ba yanzu ji yadda ka koma kaima kasan akwai banbanci da yadda ke da a watse.
Ashe ko aure dadi gare shi ko ba a fada ba yarinyan nan tana fa da hakkuri har yakai ka kure hakkurin nata ta soma mayar maka da martani kana babban kanka.
Nan dai yake cewa yarinyar baza ne kana ganin ta wurin nan munafukane ta kware bata da kunya sai na gwada mata ba irin mu akewa haka ba a tashi lafiya.
Yaya saadun yace baka ko kyauta ba wata mace zaka samu ta zauna tana hakkurin da irin halin ka nan dai sukai ta kwasan dashi.
Daga karshe ya shige dakin shi ya barshi a zaune a wurin ya kwala min kira na fito ina kuka ina share hawaye da habar zani na.
Nazp na durkusa kasa gefen kujera ina cewa gani yaya ya dago yana cewa a haba dai hau kujera ki zauna mana na girgiza kaina nace nan ma yayi min.
Yace Safiya msi yasa bakiyi wa mijin ki biyayya har kika bari yana dukan ki haka kamar wata mara gata eyeh.
Kuka yaki tsaya min nace yaya bana mashi komai haka dai ya daukan wa ran shi yai ta dukana do ban da daraja a idon shi.
Don kawai yana ikirarin da cewa bashi ni akayi ya tare ni da cewa a haba kibar fadin haka mana ke fa kaunar shine ko banza.
Yadai bani hakkuri ya lalashe ni da kuma nasiha har zuciya na tayi sanyi da zai tafi ya kawo duba goma ya ce na rike a hannuna zan samu na kashi.
Nai mai godiya ya taka har kofan dakin shi yana fadin bros ni zan tafi sai na saike lekowa kenan sai ya amsa mashi daga ciki da yaushe zaka koma.
Yace ina nan har kwana biyu sai yace sai mun hadu ke nan ya saadin yace don Allah aita hakuri yace is ok ai.
Ina shiga daki na raba kudin da yaya Saadu ya bani biyu na boye rabi kamar nasan zai karba sai ko gashi ya shigo yana ce min .
Ke bani kudin da saadu ya baki nan ashe wurin rabawa ban raba daidai ba bakwai din na boye na bashi ukun sai ya kalla yai tsaki yace munafuka kawai.
Ya fice gidan na harare shi ina cewa a fili mugu kawai ashe baiyi nisa ba ya juyo yana fadin may kika ce nace ni badakai nakeyi ba.
Yafice yana kutawa tare da gaura kofar gidan da karfi na sauke ajiyan zuciya ina mai kallon jikina inda na ji ciwo tare da dan tabawa.
Fitowa nayi na kara gyara wurin da ya bata nagama nai wanka na gyara jikina ina shirin dan kwatawa na mike naji nocking din kofan gida.
Na fito don ina ga kowa nene akofan sai ganin yarinyar aikin gwago da tai alkawarin zuwa kitso wurina a kofan nai mata sanu da zuwa tare da sake mata fuska tashigo ciki.
Baya mun gaisa da itane take cewa dani kitso tazo in mata na ji dadin koba komai zandan sake yau a gidan a wurin ta nike jin wasu halaiyan shi da ban sani ba da farko take cewa amma ke ba yar uwar su hajiya bane.
Nace may kika gani tace gani nayi dai bata kaunar ki koda yake hajiya ai da kowa zata kwasa indan ya taba mata dan lelenta.
Murmushi nayi mata kawai tace tana masifan son shi cikin yaran ta gashi dai yana aiki kuma yana samu amma bata jin kyashin kashe mai kudi.
Nace aidon su take nema ko tace wallahi yana da hanyan samu sosai amma yan matan shi basu bari ko wanan gidan da mota da ya saya sai da dabara ya saye su.
Na dauka da yai aure zai daina amma da yake dan duniya sai abin da yai gaba ga abinda yake yi.
Nan nake ji wai ai da dawata yake zaune a gidan sai da hajiyan tayi da kyat ta raba su da kamar sun rabu yanzu kuma sun dawo sun dinke wuri guda da ita.
Nan tashiga bani hiran abokiyar shashan shi din da irin rayuwan da sukayi a baya dama wanda suke yi yanzu din har nagama mata kitsa tana min hiran shi ne.
Mun gama ta ciro kudi ta bani ban karba nace ta barshi sai idan ta sake dawowa tace a, a karba wallahi idan kika soma da haka zakita aikin banzane wa mutane nan garin neman kudine ba a wasa da neman kudi.
Naimata godiya taimin alkwarin zata sake dawo idan an kwana biyu na rakata ta tafi sai da ta wuce na duba kudin nayi mamaki don har dubu daya tabani.
Ina ta murna na shiga daki naje hadawa da wanda na boye sai naga ashe dubu uku na bashi na boye bakwai.
Yanzu ga shi taban daya sun tashi takwas taban shawara na sayo kayan yin kitso don akwai wa yanda zata turo min.
Tun ranan da tazo kamar ta buda min hanyane na yin kitson na dinga samun customers mssu zuwa ganin haka ina yi a boye sai na sheda mashi don karya zo ya sani ya hauni da jidali.
Baice komai ba sai ke kika sani kardai ki bata min gidana kan wani kitso naki na banza can.
Don haka idan sun zo muke fita ta waje muyi kitson basai mace ta shigo gidana ba mun bata mai gida.
Wata rana wata mace tazo da diyan ta sai suna neman ruwa sai da aka tafi wani gu aka sayo mata sai take ban shawara na dinga saida abin sanyi mana.
Wanan shawaran yai min dadi sosai tun wanan ranan na fara sayar da ruwa sai nai shawaran ko na dinga zobo sai inayi dashi da wasu yan kakanan drinks ina sayar wa.
Aiko sai abin ya karbe ni matan hausawa harda kumshi nake masu mai zane take sunana ya fara dagawa.
Hankalina ya dan fara kwantawa koba komai dai ina samun abokan hira har ina dariya sai dai in sun tafi na koma dip.
Wata rana na gama kitso na gyara gida na dora girki gap da zan gama na shiga wanka koda nafito abinci yayi na kwashe.
Ina zaune a falo ina cin abinci sai gashi ya shigo ina gaida shi da dawowa ya amsa ciki ciki ya wuce dakin shi.
Ya fito ya zauna kenan wayan shi yai kara ya dauka zaune nake a takure a falon ina gudun in daga yace min munafuka.
Sai na dake na zauna a takure a yadda na fahinci wayan da yake da mace yake magana amma ko yaji darr dan ina zaune a wurin.
Daji lalashinta yake yi don a yadda suke magana hakkuri yake bata ita kuma sai masifa take mai a wayan.
Zuwa can ya mike zai fita sai na sasauta murya na nake cewa kayan miya sun kare a gidan na gobe ya rage kawai da zanyi.
Ya juyo a wullakance ya dube ni yana cewa ina kudin da kike samu a wurin kitson naki ki fitar ki saya mana.
Ya fice ya barni ina mai binshi da kallon mamaki don tunda kayan da nazo gidan na sama ya kare idan nai mashi magana sai ya hauni da fada.
Gashi kuma ance kudi yake samu sosai a wurin aikin shi amma baya nuna yana dashi sai yaga dama yayi.
Nidai na fahinci anyi sallah na mike zuwa yin sallah nabar falon ban fito ba ina shirin kwaciya ne naji dawo wan shi gidan.
Na dan tsaya inga da may ya dawo min a cikin mayen ne ko a birkice naji shigowan shi na mike na fito falon inda yake sai naga yana shigowa yana dariya.
A zatona waya yake yi sai naga ashe ba waya bane yana magana ne da wata da suka shigo gidan tare.
Yana dago kai ya ganin ya hade fuska tare da cewa a fusace ke kuma may kikeyi anan baki kwanta ba ?
Yarinyar da suka shigo da ita gidan tana wani taunan chewgun kas kas tana harare hararen ko ina na gidan.
Naji tace wanan ne dama matar taka ashe karamar yarinyace haka no warder kake gudun mutane yanzu
Ta kalle ni sama da kasa sai tace dashi muje don Allah karma ta kwanta mana ita ta sani tai gaba ya juya ya bita a baya.
Suka barni tsaye a wurin imani ya kashe ni may yake nufi kenan karuwa ya dauko min a gidan ko may ?
Jin sun rufo kofan daki ne nadan zabura na dawo cikin hankalina dakyat naja kafana na koma daki.
Tunane nakeyi wanan wani irin bariki ne haka karuwa har cikin gidan tazo ta wuce ni ta shige daki ita da mijina ina tsaye.
Da kyat naga safe don banyi barcin kirkiba a gidan da safe ban fitoba don haka ban dora girki ba a gida ko gyaran gida ban fito nayi ba.
Sai zuwa can ya kwala min kira daga falo saida ya kirani sau uku na amsa mai na fito falon ina saye da hijjab dina har kasa.
Ya kalle ni a wullakance yace dani ina abin karyawan mu banga kin aje min ba nace a sanyaye banyi ba.
What ya fadi da karfi nace banyi na sake fada mai saboda may zaki ce baki dafa min abinda zanci ba.
Cikin dakewa nace ita wanda ta kwana gidan bata dafa maka bane koba mace bace da baza ta dafa ma ba.
Ban san ya iso inda nake tsaye ba sai ji nayi ya buge min baki kub da nashi basan lokacin da na dafe wurin ba.
Ya daga hannu zai kara kai min wani marin sai ga ta ta fito daure da tawul a jikin ta iya cinya tace a, a marta koma ta dafa ba iya ci zanyi ba wanan kazaman yarinyar ba zan iya cin girkin ta ba.
Ta jashi zuwa cikin daki tana wani kariraya tana kwanta mai ajiki suka rufe kofa dakin garam ina wurin a tsaye.
Na sauke ajiyan zuciya a raina nace lalle yau na ga iyakar barikin da nake ji ana fada anayi a lagos na ganshi a wurin wanan bawa shine giya shine taba gashi kuma ya buga ga dauko karuwa kwana a gidan mu na sunna.
Ina jin sun gama watse war su suka fice a gidan da ihuce ihucen su da tafawa a tsakanin su.
Nace shashu banza kawai a haka zaka kare ba aga farar ka a gida ba sai gun matan bazan za suna fita sai ga yaya saadu ya shigo gida.
Natare shi da mutunci muka gaisa dashi yake tambaya na yaya gidan na amsa mai da lafiya kalau.
Sai yake tambaya na yanzu abubuwa sun yi sauki a tsakanin mu ko sai nai murmushi kawai nake cewa dashi babu komai yaya.
Ya ce a, a Safiya kada ki biye min komai ni dan uwanki ne nasan kuma halin mijin ki sarai da rashin mutunci do haka in baki fada min ba wa zaki fadawa.
Sai idanuwa na suka ciko da hawaye a lokaci guda nace yaya komai na nan a yadda ka san shi saima abinda ya karu.
Yau ma da wata mace suka kwana gidan a gaban ta yai min rashin mutunci don naki dafa masu abin karyawa.
Hakkuri ya bani ya dade yana mun na siha ina ta fada mai irin matsalolin da muke samu dashi a gidan.
Yana bani hakkuri tare da fadin sai na hada dayi mashi addua don addua baibar komai ba in kuma yi kokari in kawar da idona ga abin da yake yin don ko na ce zan fada wa iyayyen mu ba yarda zasuyi da ni ba.
Da zai tafi yakawo kudi ya bani yana cewa na rika in dinga sayen abinda zanci basai na tambaye shiba kar yaita duka na a banza.
Nace mai akwai kudi wanda na tara do yanzu kitso nake ina samun kudi yace tona kara kawai dasu.
Yai min alkawarin zai saya min fridge don sana,an zobon da nakeyi ya bunkasa sosai naji dadi ina ta zuba mai godiya mukai sallama ya wace.
Da ya tafi na kirga kudin sai naga har sha biyar ne cif din su banyi sanyi a kafa ba na shirya na shiga yar kasuwar uguwar mu na sai kayan amfani na dasu da abinda zan dan rika ci da rana.
Ashe da yabar gidan gidan su ya koma wurin mahaifiyar su ya ke fada mata duk irin abubuwan da dan uwan nashi yake min.
Sai ko ta hau fada da cewa dama tsiyan dan tallaka keman bai iya samun wuri ba ta tsamoni cikin wahala tasani ga rigan mutunci ina bidan in tona masu asiri.
Da nake cewa yana sha, shan ya hana ya kyautata min ne duka kuma in banyi mashi laifi ba ai ba zai duke ni ba , a gidan mu wani irin wahala ne bana sha nazo nan a saka ni cikin rigar mutunci shi zai ma danta sheri.
Yace mummy yarinya ga fa diyan dan uwanki ne halal malan aka dauka aka baki badon taso ba ko uwar ta taso ai kama yayi ki tsawata mashi yadaina shigo mata da maye da matan banza baki goyi bayan shi ba haka.
In tana ahan wuya a gidan su nan ai aurene ya kawo ta kamata yayi ta samu sayin rawa ta huta ba wahala irin haka ba.
Tace to ubana dama ai ka saba min fada sai kayi ita kuma ta zuba ruwa a kasa tasha tunda ta hada ni da diyana fada.
Sadiya dake gefe tana saurare tace mummy ai gaskiya yaya ya fada gaskiya abinda yayan ke wa Safiya baya kyautawa idan mu akaiwa haka bafa zaki ji dadi ba.
Harara ta watsawa Sadiya din tana cewa ai duk kuna da bakuson dan uwan ku da alheri daga yarinya taimai kake kun dauka kun haye ke nan kun yarda da abinda ta fada.
Saadun yace mainene daga ciki kake wanda ba halinsa ba cikin abinda ta fada din ina duk halin da ta fada kin sani yana yin su sarai.
Nan dai yaran suka barta tana ta fada tana fadin ai zata je gidan zamu hadu gobe bazan kara fadawa wani sirin mijina ba.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , ,


🧕🏿🧕🏿1️⃣1️⃣


INA MAI BAKU HAKKURIN RASHIN JINA KWANA BIYU WUTAN MU YA LALACE
YAR UWA IDAN KIN FITAR MIN DA NOVEL DON KAN KI KE KI SANI DON KIN SAN DAI HAKKIN WASU NE.


Ina duke ina wanki bansan hawa ban san sauka ba sai jin bugu nayi daga baya na sai da na kife a jikin roban da nake wanki din.
Bai hakkura ba ganin na fadi kasa ya kara kai min duka bazan iya kare kaina ba na fadi kasa gaba daya yana ta duka da zagi.
Sai da ya gaji don kanshi ya barni nayi ligis a kasa yashe ban ko motsi ruwan da nake wanki duk ya zube min a jiki na yana huce yake fadin.
Baki ga komai ba idan kin ce magana zaki dinga dauka kina kaiwa gidan mu shi wanda kika fadawa yazo yai maki maganin abin na gani mana.
Mata yanzu ma na fara shigowa dasu gidan nan gidan ubanki ne ko gidana da zaki kafa min doka akai.
Yar iska jiki matan da nake bi din basu fi min ke ba, ke har mace ce may za a samu a gare ki banda wahala.
Har ya shige ciki ya fito yace ban ga daman kawo abinci ba ki aika wa uban ki mai dakunanen hula ya kawo maki in ya mayar dake wata tsiya.
Yar iska nida gidana har kina sin kafa min doka nakawo mace ki hanani naji dadin da nake so idan kin isa.
Nikan zafin bugu sai wani gumzi nake yi kamar raina zai fita ya shige na dade wurin ko kafana bana iya dagawa a lokacin.
Da kyat naja kafa na shiga dakina ko ina sai ciwo yake min don zafi da cowo kuka nake ina tunanen rashin imani irin na yaya Ahmed.
Bai kara bi ta kaina ba sai shaye shayen shi yake a cikin falo ina jin shi warin giya da taba har dakin da nake ciki.
Sai dare naji yana rufe gida ya fita da kyat na ja kafana zuwa falo nan na samu yai baja baja da kayan da yai shaye shayen wurin.
Kitchen na nufa na dan hada ruwan liptop na don a lokacin shi kadai nake iya saqa cikina ga wani irin zazzabi ya na neman rufe ni.
Ranan tunane kala kala nayi gadai kudi a jiki ina son gudu in koma gida don dai na san motan zuwa arewa bai gagara na zuwa.
Amma kuma nasihan Ummi yana min yawo a raina da tace dani yar nan komai wuya komai dadi ki natsa kafan ki a dakin ki wuya baya kashin bawa.
To amma kuma a haka ake son na zauna cikin wanan irin ukuban babu dadin rai ko yaushe sai fitina kamar ankawo mai jaka.
Nidai tun zuwa na gida ba zan ce ga rana daya wanda naji dadin zama da shi ba daga ni har shi zamane na dole muke yi da junan mu.
Washe gari abin yafi na gare ne duk fuskana ya kumbure ga hannu da kafa ban iya daga wa ko kadan don ciwo.
Ina cikin wanan halin amma ya saka kida yana tashi ina jin sautin na shiga min har cikin rai na ba halin in magan ta.
Ganin da yayi kayan wankin da na jika ya kwana ya wuni yasa shi shigowa dakina a fusace yana cewa ke don ubanki kayan nan da kika jika suna wa mutane wari baki kwashe su wurin nan ne.
Sai ya samay ni cikin wani hali banko san ya shigo dakin ba lokacin tsayawa yayi a kaina yana kare min kallo sai kuma ya juya ya fita.
Ko ina nawa ya hakke ya kumbura dan bugu da ciwa gashi ba mataimaki yan kitso na sai zuwa suke suna tafiya.
Wata boyar Allah da nake kira mama biyu don tana da tagwaye tana kawo su kitso wuri na tai karfin halin fadowa har cikin daki na.
Sai da ta dan yi ihu don ganin halin da nake ciki tace dani amarya waya maki haka ko hatsari kika yine wai.
Na bude idona da kyat ina kallonta dishi dishi nace buguna yayi tace amma mijin nan naki baida imani ita na samu ta taimaka min har na da wanka .
Ta dan sayo min abinda zanci da dan magani na sha tai ta jamashi Allah ya isa yafi a kirga ta shirin tafiya ne sai ga yaya saadu ya shigo gidan yace yazo ya sallamay ni nao zai tafi.
Hankali yace bai kwanta ba ga yadda ya barni ranan sai kuma yazo ya tarar da abinda ya faru dani.
Matar take kara yi mashi bayanin halin da ta samay ciki aikuwa bai tsaya ba ya juya zuwa gidan su kai tsaye wurin mahaifiyar su.
Ya je ya sameta yake fada mata irin taasan da yayan nashi yai min maimakon tai fada sai cewa tayi fada kota tausaya mashi sai ta fara fada dani tana cewa.
Ai maganin ta kenan yarinya bata da kunya sam ga sa ido ga abin da bai shafe ta, gunma da yai mata dukan tsiya goma bata karawa ai.
Ya ce mummy na fada maki yarinyan nan tana cekin wani halin a yanzu idan ba zaki dauki mataki ba ni zan dauka don wallahi zanyi karashin gurin yan sanda akan zai kashe yarinyar mutane.
Da sauri tace dashi dan uwan naka zakai kara har kana fadi da bakin ka akan wata Safiyan ce ?
Yace ita din ba yar uwar mu bace mummy da zaki ce hakan wa take dashi a garin nan bayan mu ka wata sani in bamu ba.
Waya ta jawo ta kira wayan Ahmed din ya amsa mata a kadarance da cewa mummy aiki nake yi fa banson kira yanzu.
Tace kazo ga Saadu nan ya zo ya tayar min da hankali akan makiran yarinyar nan safiya wai ka mata duka har ta kwanta kuma baka kaita asibiti ba.
A cikin fada ya na daga sautin muryan shi yace wai ina ruwan shi da matana ne wai
May yasa yake son shiga harkan gidana ne matar shi ko mata na don haka babu ruwan shi ko kashe ta nayi.
Yana tsaye yana huci ya ansa a fusace da haka kace to wallahi jira kaga matakin da zan dauka a kanka ai akwai hukuma a kasan ko sai ya fita a fusace uwar na kwala mashi kira amma bai dawo ba.
Mike tayi a firgice tana fada tana shiryawa tabi bayan shi tare da kiran habiba ta raka ta.
Ina kwance bayan na samu taimakon daga maman biyu tadan bani dan ruwan tea na sha nakoma na kwanta sai dai hannu na ba dama na daga da kafa.
Tana tsaye a kaina suka shigo gidan tun daga kofa take kwala min kira a gigice tana cewa fito muna fukar banza da wufi kawai ganin ban fito ba yasa suka nufi hanyan dakin.
Sai sukai kocibis da maman biyu a kofan dakin kallon kallon sukai wa juna sai gwago din tai karfin halin fadin ina ita Safiyan take ne.
Dan jan jikinta tayi a kofan shiga dakin sai suka samu wurin shiga dakin a kwance suka samay ni sharkaf jiki ba dadi gaba daya na sundule saboda bugu.
Sai ta sasauta fadan da takeyi ta fara cewa uhmm uhmmm aishe abin yayi muni ne haka ban sani ba.
Maman biyu da bata san ko su waye suba sai tace wanan tsinanen mijin nata mara mutunci da tarbiya an baka diya amana don rashin mutunci kai mata wanan dukan kamar zaka kashe ta.
Sai habiba tadan juyo tace mata ai mijin ta ne sai dai itama tabar mai shigan tsagal ga alamarin shi.
Matar tace haba yar uwa ko ke ce ai ba zaki dauki hakan ba mace banza har cikin gidan ki don rashin tarbiya da tsoron Allah.
Tana kokarin cewa na tashi na zauna ta gani sai maman biyun tace ina ga kamar fa ta gwauce ne ko tayi tarmashe.
Don bata iya daga wa sai an kamata maman biyu din ke magana cikin tsigar tausaya wa.
Sai gwagon take cewa na daga ta gani mana.
Habiba tace in ko don taji ana karawa abin gishiri bazata daga ba yanzu.
Aiko maman biyu tai kanta da sabon fitina tana cewa amma dai ke baki da tausayi idan da yar uwar ki ce aikaiwa haka abinda zaki fada ke nan.
Wanan ai rashin tausayawa ne ke fa mace ce kin san zafin wanan abin mutum kobaida tausayi dole ya tausaya mata.
Ta neme fada mata maganan banza tace kama kanki kin kuwa san ko ni wace ce yan zan saka dake da mijin nata a kulle min ku baki daya don kashin kai ya so yi anan.
Sai da taga da gaske maman biyu keyi kuma ta kalleta taga ba raini a jikin ta da gani watace ko matar wani a garin hakan yasa taja bakin ta tai shiru, gwago sai fadi take .
Kaddarane ai ya kawo hakan fada tsakanin mata da miji ba a shiga sai mutun yayi kunya idan ya shiga.
Maman biyu tace amma dai irin wannan abin dole a tausaya wa mutum bari ai ya dawo zan tsawa ta mashi.
Tace yanzu a taimaka akaita asibiti kada yarinyar mutane ta halaka ga banza don shi na mijin kawai na ta yaya kai kaiwa yarinya sanadin haka.
Amma kana ganin ta cikin wani hali ace koda dan paracitamal wanan bazaka iya saya mata ba don tsaban iskanci wallahi ni sai nasaka a adana mun shi bawani abu bane.
Gwago tace a dai yi hakkuri a dan sawo mata dan magani tasha ko zata samu sauki.
Tace What da karfi wanan case din fa ba avin a zauna da ita gida bane.
Sai ga yaya Saadu ya shigo yana fadin a fito da ita mu tafi asibiti fa mota nan na samo a waje gwago tace har asibiti za aika bari a bata magani kawai.
Don kar aje suce sai an kira mijin nata maganan ta zama babban case kuma .
Yace ya zama mana waje ya zama don may zai duketa kuma ya kawo ido yana kallon ta haka kwance a gida.
Maman biyu dake tsaye a kaina tace asibiti kan sai an kaita don wanan bana zama gida bane mutafi tare zan san abinda na fada masu.
An kama ni an fito waje sai maman biyu taga motar hayace suke nufin a shiga tace dasu sallami mai motar ga motar na nan mutafi.
Da motar ta muka tafi ta kaimu wani asibiti na kudi da farko sunce idan duka ne sai anzo da yan sanda sai maman biyu ta dauko id card din ta ta nuna masu sai suka yarda zasu dubani.
Nan aka dubani ni ansamu nayi tarmashe da kuma raune a hakarkarina suka ce dole sai sun bani gado.
Duk maganin da aka rubuta da awo da sauran su itace ta bayar da komai aka bani gado a wani daki ni kadai a ciki.
Nan yaya saadu ya daga wayan shi ya kirashi yake sheda mai yazo an bani gado a asibiti ya fada mai sunan wurin.
Nan ya iso yana mazurai da ido yana kamay kamay sai fadi yake waya kawota asibiti nan na kudi kun san dai bazan kashe kudina ga wanan mara mutuncin ba ga banza.
Maman biyu da take gefe tana kokarin hada min maganin da aka bani insha tun shigowan shi take hararan shi.
Ta dago kai ta harare shi tace amma dai kai ka kai mara mutuncin gaske wallahi ma jin dadin naka yayi yawa da har zaka kashe yar mutane so ba a hukunta ka ba zaka zo kana muna maganan banza a nan.
Ya bita da kallon kallamin ta zuwa gare shi daidai lokacin da take dago ni daga kwance tana bani magani,
Sai faman murde murde nake yi saboda zafin da ciwo da nake ji a jikina ya tsura min ido yana kallon yadda na koma ga ciwo a fuka da hannu duk na goge wurin bugu.
Likita ma ya shigo yana dudubani sai da ya dan bata lokacin shi sosai a kaina ga dan karen tambayoyi da suke min duk yabi ya tsargu sai dai na boye wanda yai min haka don cewa nayi a duhu ne ban san su ba.
Nan nadama yazo mashi gwago ce taja shi zuwa waje ta fara yi mai fada akan ya rage wanan zafin rai don kar yaje ya kashe yar mutane yajawo masu magana.
Idan ma tai maka laifi ne ai basai kai mata mugun duka ba haka har yakai taji rauni maganar yaya Saadu ne suka ji a bayan su yana fadin.
Amma mummy bai kamata ki na haka ba fada ya kamata ki masa kin san fa girman abinda yayi badon wanan matar yau ba abinda zai hana ba adaure shi ba.
Idan ba a daure ni ba sai kai kaje kasa a daure ni mana wai may ye dalilin ka na min shishigi a gidana irin haka matar ka ce ko mata na.
Yaya Saadu yace kauna tace kaga ashe ina da right din da zanga ana cutan ta in saka baki na akai.
Ya zaburo mai shima ya zabura mashi kamar zasu buga gwago taga suna batun tara mata mutane sai ga maman biyu ta fito tace wanan wani rashin mutunci ne haka.
Wallahi in bakai hankali ba sai na sa an daure mun kai yau don baka da tausayi mutumin da ya cece matar ka har zaka zo kana son mai rashi mutunci.
Ta harare shi ta wuce zuwa wurin motar ta sai da ta dan gwauta ya juya yake tambayan su wacece wanan matar ne.
Gwago tace a tare muka samay ta da Safiya a gidan ku ya bita da kallon mamaki har ta dauko abinda zata dauka ta koma ciki koda ta dawo ta sallamay ni nayi barci.
Don haka tafito tana gyara gyalen dake jikin ta tana cewa waye zai zauna da ita a nan don ni zan tafi gida sai suka fara gardama tsakanin gwago da Habiba din.
Taja tsaki ta wuce tana mai jin haushi da Allah waddai da rayuwan su gasunan da ganin su marasa tarbiya dasu kawai ta dan tsaya tana cewa gwago kizo na maidake gida ita yarinyar sai ta zauna.
Ya zama dole subi umurnin ta don sun hango ita din wata ce shiyasa suke kyale ta suna binta a sannu.
A hanya su da gwago take dan binciken ta tana jin wani abu a gamay dani sai take lurar da gwago din nauyin amanan dake kanta na tare da fada mata cewa idan ya kara min irin dukan nan zata sa a daure mata shi.
Gwago ta tsora ta tace insha Allahu ba za a sake ba wanan ma akasi aka samu ayi hakkuri dai zata sauka takawo kudi taba ta tana ta godiya.
Yaya Saadu yace zai tafi wani wuri ya dawo sai ya bar yaya Ahmed da habiba zata fara mashi tsegumi ya katse ta da cewa ke raba ni dan Allah da anyi an ce.
Sai taja bakin ta tai shiru ta tsargu ta koma gefe daya ta rakube wuri daya tana harare harare wa mutanen dake sintiri a haraban asibitin.
Ya fita ya dawo dauke da leda da lemo da ayaba a ciki ya nufo dakin ya shigo ya samu na farka.
Ina zaune ina dan matsa kafana a hankali don haka likita yace dani nayi sai gashi ya shigo dakin babu kunya babu alamunta ya samu wuri ya aje ledan dake a hannun shi.
Yazo ya zauna a kusa dani ga mamakina sai naga ya fara wade ayaba a hankali ya miko min sai na girza kaina alaman a a yace likita yace abaki abin gina jiki saboda haka kici wanan nan.
Yayi niyar wai bani har a baki don yaudara sai na ki karba sai dai ya wade min na karba nakai a baki da kyat.
Naci kamar kwaya uku da kyat don bakina bai da dadi nace ya ishe ni sai ya mayar da ledan ya aje gefe daya ina zaune na langabe kaina a karfen gadon da nake kwance.
Sai naji ya kamo hannun da yafi mun ciwo na dan matsawa a hankali sai da nai kara, yana fadin ai sannu zai warke ya bar ciwo da yake na zugi.
Ban kai ga bashi amsa ba sai ga matar da nake cewa maman biyu mutumiyar kirki ta dawo niki niki da su flask da ledoji da wata yar budurwa bayan ta.
Suka samu wuri gefen gado na suna aje kayan da suka shigo dashi din tana cewa a she kin falka sannu yaya jikin ina sauri karki falka babu abinda zaki ci anan.
Yana zaune ya dukar da kanshi kamar maijin nauyi da kunyan ta sai can tace wanan ne mijin naki ko sai lokacin ya dago yake cewa da ita sannu da zuwa.
Yana kokarin mikewa tsaye ya fita tace dashi No zauna abinka ai tafiya zanyi don ba dadewa zanyi ba dama wanan kayan na kawo sai yarinya da zata dan zauna da ita don naga kaunar bata son zama da ita.
Ya dai mike yana cewa zan dan tafi nan bakin get ne na sayo abu sai ya fice tabishi da harara tana cewa mara mutunci kawai sai ta ja tsuki nasan haushin sa take ji har cikin ranta.
Tace wa yarinya Nafisa dan zauna anan bakin gadon barin zuba mata abincin nan kadan ta danci.
A sanyaye nace nakoshi maman biyu tace da sauri may kika ci da kyat na bude baki nace ayaba naci sai ta kalli wurin ledan ayaban da ya aje tace ina wanan bawan da nagani shi kika ci.
Na kada mata kai alaman eh,
Sai take cewa idan kika biyewa wanan mijin naki mara mutunci kina tunane sai ranki yai ta baci ga banza.
Nan ta zuba min ta jawo kujera a gabana ta zauna ta debo min zanyi gardama tai min jan ido dole na karba.
Ina ci ta jefo min tabaya akan auren mu ina bata amsa a hankali har na dan ci abincin kamar spoon biyar zata karo nace na koshi.
Bata ce dani uffan ba ta aje plate din tare da mikewa tana gyara gyalen kan ta tana cewa barin koma yara suna gida na barsu.
Sallama tai muna ina mata godiya ina share hawayen dake zuba a idanuwa don tun tana tambaya nake kuka.
Ta fice tare da jawa yarinyan kuna akan ta kula sosai idan da matsala ta kirata a waya.
Tai muna sai da safe ta fice daga dakin na dade ina kuka bayan fitan ta dakin.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , , , , ,


🧕🏿1️⃣2️⃣🧕🏿


INA MAI GODIYA GARE KU YAN UWA NA GODE DA KAUNAR KU A GARENI ALLAH YABA HAKKURIN ZAMA DA JUNA NAGODE.

YAR UWA NOVEL DAI NA KUDI NE BA YARDA KI KARANTA BA INDAN BAKI BIYA BA DON BA A YAFE BA, , , ,


Tsaye yake ya jingina jikin shi da motan shi yana busa cigari sai busar da hayaki yake sama da alaman tunane yake yi a lokacin.
Har ta tako zuwa inda yake tsaye yana shagalin shi bai farga da zuwan ta ba sai da tai magana ya dawo cikin hankalin sa.
Tace dashi wanan abinda kake yi ba dabian diyan hausawa bane komai na ba haushe ansa shi ne a cikin kawaici da alkunya.
Murmushi yayi ya jefar da taban dake hannun shi kasa yana takewa a cikin kasa.
Yace hajiya har kin fito kenan tace eh dama na kawo abinci ne da yarinya da zata zauna min da ita don na lura yan uwan nata basu san zama anan gashi tana bukatan mai taimaka mata wani fannin.
Angode yace da ita har ta juya zata fara tafiya sai kuma ta juyu tace dashi a gaskiya wanan dukan yayi muni kwarai da an kai ka ga hukuma ba abin da zai hana su kulle ka wurin su .
Ya kamata ace ka godewa Allah da yabaka mace irin wanan yarinyar dan babu macen da zaka doka a yanzu irin wanan batai karan ka ba.
Yace sherin shedan ne akasi akasamu haka bazai sake faruwa ba in Allah ya yarda.
Taima shi sallama ta yafi bayan ta bashi dan shawarwarin da ya dace na zaman takewa a tsakanin zama ta tafi sai sauke ajiyan zuciya yayi kawai koba komai dai ta rufa mai asiri.
Don irin wanan wayyayun mata ba a shansu a banza amma ita gashi ta rufa mai asiri.
Sai wani tunane yazo mashi a rai a ina safiya tasan wanan mace ne haka da har take mata irin wanan taimakon dole ya sani don gaba.
Sai da na kwashe kwaki sati a sibitin san nan suka sallamay ni kudi dai ya sha kashi sosai na dawo gida har lokacin dari dari nake dashi don nasan mai hali baya fasa halin shi.
Zaune muke a falon da Maman biyu ta wade min lemon da zan sha sai ta tambaya labarin auren mu dashi
Ban boye mata komai daga ciki ba na labarta mata sai tace barin fada maki idan sun tambaye ki ko yaya nake dake ki fada masu cewa ni yar uwan mahaifiyan ki ce tun a gida akace ki nemay ni idan kinzo nan don zan kula da almarinki kamar yar uwata ta jini kike a guri na don muna garin da dan uwa ke bukatan taimako juna.
Tace idan Allah ya hada ki zama da miji dan iska sai hakkuri don gaskiya mijin nan naki yayi nisa da harkan bariki duk na miji da zai iya dauko macen banza zuwa gidan shi tantiri ne.
Don gaskiya sai kin kwantar da hankalinki sosai kin bi halin shi a sannu ki guji duk wani abinda kika san zai jawo maku matsala a tsaka don shi zai iya yi bai zama komai ba amma idan ke kin yi zai iya komawa fitina.
Ki bishi sau da kafa ki guji saka ma alamarisa ido koda yaushe kina jina ko sai na gyada mata kai alaman eh.
Nace cikin murya mai rauni tare da hade miyau bakin cikina a wuyana nace ina iya kokarina don ganin na kyautata mashi.
Amma da yake shi wani irin mutum ne mai hali na daban duk abinda nayi baya gode min.
Sannan abun bakin ciki shine yadda yan uwanshi suka tsane ni sun sani a gaba kamar ba yar uwan su nake ba sam babu kauna a tsakani na da su .
Sanan shi ya kasa fahintar makircinsu na san ba wani abu yasa suke min haka ba sai don sun dauki iyayyena tallaka ni ban kai sa,an auren shi ba ga rayuwan da suke yi a nan don ya banbanta da namu.
Ta katse ni da cewa duk ki manta da wanan yanzu ki kama Allah Allah yana tare da mai hakkuri ko yaushe.
Za a zo ya wayi gari ya gane gaskiya ya daina su kuma zai fahinci kutungwila da suke shirya wa a kanki.
Nace mhm anty kenan sai dai don kin ce Allah ya fasan gaskiya wani abin da biyu yake min shi don kawai ya kuntata ma rayuwa na.
Tunda dagani har iyayyena babu wanda yake shakkan zagi yadda rashi yaso idan yana jin tsiyan mutumin da kullun a buge yake in baisha da safe ba da dare zai sha.
Amma nai hakkuri da hakan ina zaune shi don bin maganan iyayye in yai amai na kwashe anty in yasha giya anan inda kike zaune zai bar kofi ko kwalban in dauke.
Haka zai shigo cikin mayen shi yai ta surfa min a shar ya danne ni da karfin tsiya yayi abinda yake so dani na karasa fadi cikin kuka.
Maman biyu tai tagumi tana saurare na cikin jimamay abinda nake fadi ina kuka.
Zuwa can ta nisa tace sai hakkuri Safiya don zaman aure a yanzu hakana ya kunsa ko wani gida da tasu lalurar idan kuma kin ga zaman wasu sai ki daga hannu kiwa Allah godiya ke.
Nace a hakan maman biyu har akwai macen da tafini wahalan aure a duniyan nan tace naki kika sani safiya Allah daiya kyauta zamanin nan.
Nace ni maganan mahaifina da yace idan na neme saki a gunshi da bakina bai yafa ma haihuwan da yai min ba.
Tace to kin gani ko sai hakkuri karki gaji da hakkuri kuma ki rike ibadan ki kina yin adduoin da hannun ki bibiyu bada wasa ba.
Ina kuka ina mata godiya tace zata tafi amma zata dawo kwana biyu ta duba ni in Allah ya yarda.
Nai mata godiya ta tafi ta barni ni kadai a cikin damuwa da tunanen rayuwa mai kunci da nake ci a gidan.

********* ********* *********
Na mike na shiga daki dakin duk yayi kura na rashin mutum a cikin sa duk da jikuna da dan sauran tsami amma haka na daure na gyara shi har zuwa falon gidan da duk yai kura nasan ko sau daya bai taba gyarawa da ban nan.
Sai zuwa marance na gama har da girki da na dora na shiga nai wanka na fito na gyara jiki na sai yamma lis ya dawo gidan daidai lokacin da nake fitowa cikin daki ya shigo.
Cike da girmamawa irin na macen da tasan darajan wanda take aure na gaida shi da dawowa bai takan ni ba sai umhum din da yace dani.
Nan ya zauna saman kujera yana debe takalman kafan shi da safa sai na je fridge na dauko mashi ruwan sha ban kai ga kawowa ba ya dakatar dani fuska daure yace ni bance maki ina bukatan ruwa ba.
Da sauri na kalli idanuwan shi kamar zanyi magana amma kuma sai na juyana mayar da ruwan ida na dauko da farko.
Ya na cire takalman ya shige dakin shi baiyi magana ba nidai ina tsaye daga kofan kitchen na bishi da kallo kawai.
Abinci na dauko na jera mai saman dan taburin cin abincin dake falon na juya na shige ciki abina tare da turo kofan dakin.
Can bayan kamar awa daya naji yana turo kofan dakina ya shigo yace ke nazo in maki kashedine akan fada wa Saadu sirin gidana da kike yi.
Ban taba zaton munafuncin da mummy ke fadin uwarki nadashi ya shafe ki haka ba sai yanzu.
Da sauri na dago kai don jin abinda ya fada gamay da ummina ina kallon shi cikin mamaki.
Nace ita gwago tace ummina muna fukane ita yaya akayi ta sani ko ta taba yi mata munafuncin ne .
Yace karya mummy zatai mata kike nufi komay ?
Nace wai may yasa iyayyena basu da daraja a idon ka baka jin nauyin fada min magana a gamay da su.
Ya a cikin tsawa wanan ke ya shafa kin dai ji na fada maki in ba haka ba daga ke har saadun zaiyi karanku ina ce tare kuke kuna cin amana na.
Da sauri na sake dago kai na kalle shi a cikin mamaki abinda ya fada na wai zai muna kazafi dani da yaya saadu akan muna tare .
Ya ce eh muddin baki daina jawo mani shi a gida ba abinda zanyi maku kenan a gidan nan ya juya ya fara takawa sai kuma ya juya yana cewa uhmhum dama ina son in tanbaye ki
Ina son insan wanan matar mai zuwa a inakika santa ne uta din wacece may ye alakarki da ita da take taimaka maki haka.
Nai shiru ban bashi amsa ba saida ya sake maimaitawa na ce yar uwar ummi na ce ita a kano take acan tai auri wani babban sojja ita din kuma custom ce.
Da sauri yace mayne ita din da nake gani custom ne ashe no warder take abu a gadaran ce don tasan abinda ta taka.
Nidai ban tanka shi ba sai shirun da nayi kawai yai huce ya fice daga dakin na sauke ajiyan zuciya tare da fadin Allah ya sauwa ka.
Kwana biyu ba wani fitina a gidan idan ma zaiyi shedan shi bai yi min a falo saidai ya shige daka cikin dakin shi ya dadaki giyan shi yayi talil ya lamay a wurin.
Dan kwana biyu jani shakat a raina ga maman biyu tazo ta kawomin abinci na boye a dakina duk da shima ya sayo koma amma bata yarda tuban mazuru ba tace indai boye wanan.
Na kwasa nakai dakina na boye tana shirin wacewa ne ya shigo gidan basu hadu ba tun ina aaibiti sai yau din nan suka sake haduwa dashi.
Ya shigo yana ganin ta yadan sake fuskanshi suka gaisa sai a lokacin ya samu yi mata godiyan dawainiyar da tayi damu a asibiti.
Ta katse shi da haba babu komai ai, adaiyi ta hakkuri koda yake nasan kana yi sai ka kara kasan safiya yarince karama bazaka hada hankalinta da naka ba.
Ya dan sosa kai yace ba komai komai ya wuce ai na gode kwarai ta mike tana saka hannu a jakar ta kamar yanzu ne zata sallame ni tace ke kuma karbi wanan kyadan rike karki dami mijin ki da bani bani.
Zai shige ciki tace ya tsaya shima ta debo ta bashi yana aaa amma ta matsa mashi ya karba na rakata har waje ta tafi na shigo ciki.
A falo na samay shi tsaye yana jirana ina shigowa ya miko min hannu da cewa na kawo kudin nan da ta baki nan na dago da mamaki ina kallon shi.
Ya sake fadar miko min su nan nace kuma idan kika kuskura kika fada mata cewa na karba sai na lalatsaki a gidan nan.
Jiki na rawa na mika maisu ya shiga kirgawa yaga dubu biyar ne nashi kuma goma ya hada yace sha biyar kenan.
Ya tura a aljihun ya shige dakin shi ya dade da shiga ina kitchen naji muryan shi yana cewa ni zan fita idan kinga nakai sha daya ki rufe gida bazan dawo ba a xan zan kwana.
Nace dashi to kawai ya fita ya sha kananan kaya sai kamshi yake nace a raina yau an samu kudin sheke aya ke nan.
Kamar yadda ya fada bai dawo gidan ba sai safe ko safen sai wuraren sha dayan rana shigo man har zuwa lokacin bai gama warwarewa ba daga mayen shi.
Ya shigo ido yai mai ja sai zage zage yake zubawa ni dai ina daki ban fito ba har ya gama ya fada dakin shi ya bingire sai barci.
Bashi ya falka ba sai karfe hudu na rana koshi yunwa ta tayar dashi ba ibada ba ko wani abu don daren jiyan da yake jin kudi a aljihun shi club yaje suka kwashi rawan su suka sha giya da matan banza su gama suka shiga sheda da matan a wurin.
Ya fito ya samay ni zaune ina kallon wani film din magic ya samu wuri ya zauna fuska daure yake tanbayana abinci fa.
Na dago nace dashi babu nama ya kare hakana na dafa abincin don shi baicin abinci ba abin miya a ciki.
Har zaiyi magana sai yai shiru ya ja tsuki yana fadin zubamin hakana don yunwa nake ji haka na zubo mashi ya lashe daki ya koma ya kwanta.
Babu batun cika ibada gare shi don ba zance yana cika sallah shi ba don ko da safe sai ta hantse mashi zai tashi haka kuma da rana ko yana zaune akai sallah baya tashi yayi sai jefi jefi yakan yi.
Yau ma shirin fita yake a gidan sai naji sallaman yaya saad ya shigo har na taso da yar fara a ta zan tare shi sai na tuna kashedin da yai min a kansa.
Haka na tare shi kadaran kadaham nai mashi sannu da zuwa yake cewa lalai kauna ta jiki yai dama ya zauna a saman kujera yana cewa ashe kana ciki a dadaure ya bashi amsa umhum.
Shika yaya saadu ya share shi ya shiga tambaya na yana kuma min hiran tafiyan su har kasan togo suka tafi.
Ganin ban saka ba kamar yadda ya sanni sai ya dan shiga tsarguwa a take ya fara tambayan make faruwa ne Safiya ki fada min ni yayanki ne fa.
Na share kwalla dake fuskana nace dashi ba komai yaya saadu ya mayar da duban shi a kan dan uwanshi da ya mayar da hankalin shi ga abin da yake yi da waya shi yace .
May ke faruwa ne bros.
Sai yace ai gata nan ka tamabaye ta kaji abin da ya samay ta din ya matsa min da tambaya nace don Allah yaya Saadu ka bar zuwa don yaya yace zai kulla muna sheri ni dakai wai tare muke a gidan nan.
Mikewa naga yaya saadu yayi yana huci yake fadin kaika dade baka kulla muna sheri ba.
Ban san rashin mutuncin ka ya kai hakka ba sai yanzu don ta na yar uwa nace kaga ina kula mata inda wata ne can bare ka dauko ba abin da ya damay ni da ita.
Wanan wani sallon yaudara ne ka dauko kaika dade bakai muna sheri ba cike da tsoro na ke magana a, a yaya na fada mane don kawai ka dauke kafan ka.
Na sake cewa cike da tsoro na dan kalle shi nace na fada ma a gaban shi ne don ka san gaskiya nake fada don ka kiyaye.
Ya dago jajayen idonuwan shi ya ce dani indan baibar shiga maganan ki dani ba a gidan nan zan iya mashi komai tunda bai da mutunci.
Bai kai aya ga maganan shiba saiko yaya saadun ya taso mashi kamar zai dake shi da kyat na samu suka hankura ya fice gidan a fusace.
Ranan nasha duka sosai a wurin shi sai dai bai yarda ya kaini kwance ba amma na zagu a gurin shi .
Ban damu ba don zargi da sherin da yake son muna da yaya saadu shine abin da ya tsaya min raina tun lokacin da ya fadi hakan.
Amma yau sai naji na samu sukuni akan wanan maganan na gyagije naci gaba da har kokina kamar kullan.
Na koma yin kitso idan yakawo in dafa muna kowa ya ci indan bai kawo ba kuma na dan jawo kayan abincin da maman biyu ta kawo min na hada wani abu na ci.
Wani lokaci haka zai dawo gidan da abin amfanin gida duk ranan da naga ya shigo haka nan nasan yar arzikin na a kai.
Zai zauna baisha min taba a falo ko giya ba sai dai yai ta yawan waya da matan banza ranan kuma duk matar da tazo kitsu ranan sai dai ta koma bakitso don bai bari nayi .
Yakan zauna ranan mace nake yakan wuni darza na sai ya gaji ya kyaleni don kan shi indan yai haka yakan dade bai neme ni ba kuma sai lakacin da yai mashi dadi a rashi zai kara kusanta ta.
Ranan da naje gaida gwago dakuka na dawo gidan mu don tun case din da na fada ma yaya saadu abinda ya fada ashe sun je can gabanta suyi kaca kaca da juna su a gaban ta.
Tun wanan lokacin taka nema na ta fada min kada inyi sanadin raba kan diyan ta da munafunci na dana iya a tare na gansu kuma tare zan barsu.
Idan na kara hada diyanta fada sai daukeni ta mayar dani gidan matsiyacin ubana naje can mu karata can dasu.
Zagi ta ida take shiga ba nan take fita na har cewa tayi wanan kaddararen aure nawa da ta tauye ma danta jin dadi dashi.
Ban wani dade ba don ko ruwa ban sha ba a gidan na juyo na dawo gida ina kuka a idanuwa na,
Nazo kofan gida na samu maman biyu tazo gidan bata samay ni ba tana shirin wuce wa sai gani tafe ina sharan kwalla a idona.
Ta tsaya da mamaki tana kare min kallo tare da tambaya na ke lafiya kike tafe kina kula haka .
Nan nake fada mata duk abin da ya faru a bayan ta har dukan da yai min tace wanan mijin naki ya zama abinda ya zama sai addua kawai gare shi.
Ina kuka nake cewa da ita ni gaskiya gidan mu zan koma na gaji da wannan halin baida ranan gyara halinsa sai dai gaba gaba dakeyi.
Tace kada ki fara cewa zaki gidan ku don mahaifin bazai barki ba ba kuma zai goyi bayan kiba don haka gara ki zauna kiyi hakkurri da halinsa tunda kin saba yanzu.
Mutun sai kace mara imani komai a ziciya har yanzu fa bai daina abin da yake yi ba yanzu har rashin kwana a gida ya tsiro dashi.
Tace kardai ince wurin matan banza yake kwana ta fiddo ido waje don mamaki tace wanan kuma sabon sirfan da ya dauko don mugunta fa.
Nan na soma kuka ina fadin san anty ba sona suke yi ba sin cuce ni sun cuci iyayye na, sun muna rufa rufa an hada ni da alkakai na soma kuka wiwi.
Tace meye haka kuma Safiya so kike ki tayar min da hankali nima cikin kuka nace da ita ba haka bane anty.
Wallahi ni kadai nasan halin da nake ciki yanzu haka abinci sai yaga daman bani zai kawa a gidan nan ga uwar shi har fadi tayi wai ina mashi wayo ina karbe mai kudi.
Kenan ashe tasan dan ta yadda yake amma taiwa mahaifina rufa rufa ta aura wa danta ni hakana.
Hakkuri tai ta bani kan indan kara bashi lokaci idan bai daina ba zata bani kudin mota in koma gidan iyayyena da zama.
Ranan bamu rabu ba sai da ta kaini har gidan ta na gani kamar ba a kasan nan suke zaune ba mutum zai dauka a Amerika yake don kyawon shi.
Naci na sha ta bani kyautan suturu masu kyau da tsada dama tun da nazo ko kyale bai taba hada ni dashi ba.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGO, , , , , , , ,


🧕🏿 1️⃣4️⃣ 🧕🏿


YAR UWA WANAN NOVEL NA KUDINE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , , ,


Tafiyan dare mukayi sai wajajen sha daya da wani abu na rana muka isa garin mu duk jikin yai min tsami dama yaya jikin yake balle an tabashi kuma.
Mun sauka yaya ya nema muna mashin muka hau zuwa gidan mu tare da kaya na niki niki shi yai wahalan daukan kayan da kansa.
Suna hada hadan su na safe sai jin sallama na kawai sukayi yara suka dauka ga Safiya ga safiya tazo.
Da gudu kanena suka sheko suka rungumay ni suko su mama sun fito da mamaki suna kallona mama ne tace safiya kuna tafe ashe ke daya ne take sai idanuwa suka ciko da kwalla.
Na shige dakin mu ina kuka shigowan yaya Sani da kayana niki niki ya na kokuwa dashi yasa aka samu masu taimaka mashi daukowa.
Kowa sai mamaki yakeyi sunyi tsaye cirko cirko suna mamaki Inna tace babu lafiya kan gaskiya.
Wanan tafiya da gani bana dadin rai bane sai aka fara lekowa don gulma wai ana gaishe ni da zuwa sai a fita ana dariya waje don sheri.
Inna ta koma kan yaya sani wanda ya gama aje kaya a wahalce dashi ta tsare shi da idanuwan ta tana cewa daga ina ka tsinto Safiya kai kuma.
Baiyi magana ba sai samun wuri da yayi ya zauna yana neman ruwan sha yana jin inna ta matsa tambayan shi saida ya gama kwakwadan ruwan shi ya sauke numfashi.
Ya dago kan shi yana fadan can lagos mana inna sai ya mayar da kan shi a kwanon da yake shan ruwan.
Cikin mamaki da dafe kirjin ta tace har lagos katafi ka dauko ta dakin mijin ta kana ko da hankali kuwa.
Sunyi tsaye akanshi cirko cirko suna sauraren shi maimakon ya yi magana sai ya mike kawai ya fita daga gida batare da ya tankasu ba.
Can waje ya samu yan uwanshi su yaya Nura yana basu labarin rashin mutuncinn da ya samu mijin nawakeyi don haka ya hade kan su akan suyi wa baba tawaye ga zancen.
Don gulma baba har ya fita kasuwa sai inna ta tura yaro ya kirashi a kasuwan don tasan bazasu ji komai a wurin yaya Sani din ba.
Tun shiga na dakin ummi kuka nake yi ban iya magana ba har da ruwa da kunun da ta aje mun ban iya shan ko daya ba a ciki.
Kanina ta tura ya kira mata gwagonta da sauri a gidan su don tasan ba lafiya ba wanan zuwan nawa kan.
Ta fita ta kira su mama da inna kafin gwago din ta zo nan suka sakani gaba da tambaya amma basu samu amsa komai ba ban da aukin kuka da nakeyi.
Gwago ta taso hankali a tashe tazo gidan namu cikin tashin hankali da son ganina kamar karta shigo na kara sautin kuka na ina fadin ban komawa wallahi gwago kasheni zai yi kinga duka,
Na shiga bude jikina ina nuna mashu ga tabo nan ko ina a jikin nawa ba iya ka take ummina ta fashe da kuka inna ne kawai batai kuka a wurin .
Sai ga baba da yaron da ya tafi kiranshi sun dawo tun a kofan yake fadin ina Safiyan take ne lafiya ko tare suke da mijin nata
Nan take gidan yai tsi kowa na sauraren abinda zai fito bakin na amma sai kara sautin kuka na da nakeyi kawai.
Tsawa ya dakamin tare da tambaya na dacewa ke ki ba mutane amsa kin tsaya sai kuka kike zubawa mutane, kukan ne zai fishe ki.
Daga kofa suka tsinkayo muryan yaya Nura da yaya sani suna cewa baba mijin nan ta dan iska ne wallahi da ce anan arewa yake zaune ba abinda zai hana mu casa shi wallahi.
Baba ya daka may tsawa da kai rufe muna baki don Allah yanzun dai may ya kawo nan a wani dalili tazo .
Yaya Sani ya karbe zance cikin dakewa yace a dalili na tazo don ni naje har lagos na dauko ta na zo da ita gida kar ya kashe ta ga banza kar mara galihu da gata .
Wani kallo baba yake mashi ya ci gaba da cewa diba baba ka gani yadda duka ya mayar da yariyan ga duk ta koma kamar wata ta baba wallahi.
Baba ya daka mai tsawa da kai dakata kaina ubanta ko kaine uwar ta ya girgiza kai alaman a a baba yace to kada hurumin dauko ta ka dawo gida ita .
Baba ta yaya zanje na samu yana dukanta da zagi akan taki dafa masu abinci shida karuwan shi ya doke ta yana zagi na fitan arziki.
Ina ruwan ka baba ya firfito da indo waje ya sake cewa nace ina na ruwan ka wa ya aike ka zuwa dauko ta idan ya ga dama ya kashe ta mana ai mijinta ne kuma dan uwantw.
Gwagon Ummi tace a a malam wanan ba hujja bane gaskiya kace fa ya kashe idan yaga dama da yar uwar shi ce aiba zai mata wanan tsinanen duka haka ba.
Baba yace cikin daure fuskan karki saka bakinki ga zancen nan don ba maganan ki bace diya dai diyatace kuma dan yar uwana na bawa ita.
Don haka ko yanka ta yake yi gunduwa gunduwa sai ta koma gidan nan shidin da yaje ya dauko ta shi zai mai da ita dakin ta ta zauna ai kowa hakkuri yake a dakin shi.
Mama tace bako da duka ba har da su tarmashe da sauran su sai dai wani abin kadai tsaya ai bincike kada a dauki yarinya a mayar wani abu yaje ya samay ta ta halaka fa.
Baba ya amshe zancen nata da cewa idan ta halaka aure ya halaka ta nace aure ya halakata sai ummi na ta fashe da kukan bakin ciki yace sai kiyi amma komawa sai ta koma wanan gidan ba fashi .
Ya juya ya fice gidan da banbami shiko yaya sani fadi yake yi ba inda zan tafi wallahi abar shi yaje ya kashe ta din ba shike nan ba ai yar shi ne yace.
Wanan kalamai na yaya sani suka tayar min da hankali ina ihu ina fadin yaya Sani kataimake ni bana komawa gidan nan kashe ni zaiyi wallahi.

********* ********* *********
A can lagos din bayan tafiya na bai tafi gidan su ba har tsawon kwana biyar yana hadiyan bacin rai shi kadai.
Da farko ya dauka wasa ne yana cewa in tafi mana ya huta da wahala da yar kauye maganganu dai na batacin yake fada gamay da ni din.
Sai yazo ina dan ya dawo zaiga gidan yai mashi girma ga wani irin duhu ba gyara shi kuma bashi da time din zama yai gyaran.
Don haka ya bugo waya gidan su kannen shi suje su gyara mai gida basu so zuwa ba suka tafi dole.
Sun dawo suna kwarara amai da zubar da miyau na kazantan da suka gani a gidan amai ne ragowan giya ne kai komai sun gani a gidan.
Suna fadawa uwar su kan cewa basu kara zuwa gyara mai gida sai ta hausu da fada inda take shiga ba nan take fita ba.
Idan ya rasa kudi babu mai bashi yadda yake samu ya amshe dan kudin da nake samu ga maman biyu ko wurin kitso.
Yanzu babu inda yake samu sai dai ya arro ko kuma asai mai giyan kyata don mashaya akwai su da wanan kara.
Sai ya kara sanin ashe ba karamin karya nake mashi a gidan ba gaskiya ne da aka ce mutum dan adam yana da rana.
Ga yariyar da ya raina yaga ranan ta tun ba, aje ko ina ba gashi yasan muhinmacina a gidan yasan ina hakkuri dashi to amma kuma shidin ya kasa kyautata min ne bai san dalili ba.
Ina da matukar mahinmaci sai yanzu da ban gidan ya gane hakan duk da bakwa yake dani ba sai ya ga dama amma sai tafiya ya zamay mashi yashin hankali da rashin kwaciyan hankali , ya rasa may ke kawo mai jin yawan tsana na a rashi.
Kodon yawan zagina da mahaifiyan shi keyi ne a gaban take fadin kwadayin mahaifina ya jawo min haka yana gani ita sakarai ne don kawai ya bata diya sai ta bude mashi bakin aljihun ta na kashe mai kudin ta, ba dai a kan wanan diyar tashi ba dai.
Wani yammaci sai gashi yazo gidan su dayamma nan mahaifiyar ta tare shi da zance na tana zagi tana aibanta ni tare da zagin iyayye na kamar yadda ta saba yi idan yazo.
Yai shiru yana sauraren ta sai can da abin ya isheshi yace mummy zuwa zakiyi fa, ki dawo da ita don ba zan sake taba .
Uwar dago cikin mamaki tace haka zaka ce ni ina ganin bata dace da kai ba sam,
Yace mummy idan ba ita ba da iyayyen ta wata mace ne zatai hakkuri damu gaba daya duk abinda muke mata tana zaune tana hakkuri sai zuwan dan uwata ya gudu da ita.
Ke kanki kin san cewa indan yar ki akewa hakan bazaki taba lamunta haka ba .
Don haka ki kama hanya zuwa arewa ki dauko ta kidawo da ita nan shine saukin mu bai kamata ace don ki aka dauki yarinya nan aka bani ita.
Don kwai ina danki ace baki kaunan ta ai gaskiya saadu ne da yake fadi da taimakon ki muke wani abin.
Duk ke ke kara lalatamu muke abin da muka ga dama abin da bai dace ba idan munyi sai baki iya hana mu , sai muga cewa shine daidai don bamu da masu yi muna fada a rayuwan mu.
Shi wanan tsohon ya na shagamu can yake sha a nin shi bai damu ba da halin da muke ciki a garin na babu ci babu shan shi.
Nan dai ya takewa uwa gidan wuta akan sai taje ta dawo mashi da matar shi ya zube mata kudin mota anan ya fice yabarta tana tunane akai.
Yaushe yaran nan ya fara son Safiya hakan nan ban sani ba kodai shima sun magance shine yadda suka magance yaya a gidan shi.
Yanzi ni idan naje da wani ido zan kalli mahaifin yarinya nan dashi nace na rike mai ya amana ko mai.

********* ********* *********
Acan gida bayan baba ya kare fadan shi ya kare da cewa zai hada kudin mota da zaran sun cika bani kara kwana mashi gidan shi.
Bayan fitan shi ne gwagon ummi ta rarashe ni da mama na samu na danci abinci da aka aje mun sai dai ban iya cin komai ba ruwan kunu kawai na iya sha.
Dana dan gyagije namike naje nai wanka na fito har lokacin gwago tana nan zaune na sa kaya a jikina,
Sai lokacin na fara ciro masu tsaraban da nazo dashi da wanda na sara ina gwadawa mahaifiya ta nan dai muka cire ma kowa tsaraban shi.
Na fitar wa aka fitar ana tallata min ne diban ma maman Amina kawata aka kai mata take tambayan nazo ne yaron ke fada mata cewa nazo tun jiya ina nan gidan mu.
Nan da nan aka saye kayan don na sake su da sauki sai gulma ya fara tashi a gidan mu daga dakin inna suke fadin ai gwai dama sun san cewa yaran gwago ba su da kamun kai.
Sundai yi shiru ne naje na dan dano ai maganin mu kenan uwa cikin ukuba diya ma haka ai kadan muka gani.
Na dan samu sukuni don har na fara maida jikina da haske naje na gaida maman Amina kawata mun dade muna hira da ita na dawo gida kada baba ya dawo bai samay ni a gida ba don satan hanya nayi nazo gidan su.
Wai duk da halin da nadawo gidan mu ciki Inna sai da tai bakin ciki da gani na haka na kodan dan kayan da na saro ne ake saida min ban sani ba.
Wani lokaci taimin gori akan rashin dace miji wana sain kuma ai min habaici wai ina wa mutane takama natafi birni na waye.
Don dan kayan da nake sai daiwa yasa mutane na ribibin zuwa sayan unders na yara da yan dogon riga na mata nashan iska da sauran tarkace.
Shine dalilin da inna ta rasa sukuni a cikin zuciyar ta tace wai ai gara na koma akarasa ni can ko yaushe cikin ba babana mugun shawara take a gida.
Ina da sati uku da zuwa gida ne safiyan wata asabar sai ga gwago ta sauka a garin direct gidan mu ta yo sun tare ta kamar yadda suka saba mata idan tazo har da ummi na bata nuna mata komai ba a zuciyar ta.
Hakan yasa gwagon dan sake jiki bayan sun gama gaisawa da mama sai gwago tace dada wanan yaron haka yaje yai muna, ya dauko kaunan shi ya zoda ita gida bada sanin mu ba.
Sai mama din tai murmushi tace muma haka dai muka gansu kwatsan a gari sai dai a gaskiya abin baiyi dadi yadda suka zo muna da labari .
Anyi abu don dadin rai kuma sai abu nason ya koma tsiya haka don ma malam daya tare maganan ya hana kowa ya fadi yace yana tara kudin mota ne , ta koma dakin ta.
Gwago taji sanyi a ranta sai dai taji mama tace a gaskiya dake har wanan yaron baku rike amana ba sam abin baiyi dadi ba wallahi don ma dai anyi kawaici andubi baya .
Gwago tace to ai dada yanzu dai kuyi hakkuri kamai aka ce munyi mun dauka sai dai muba da hakkuri kawai.
Mama ta sake cewa ki sani diyar malam diyar ki ce ba sai an fada ba don in anyi laakari da irin diyaucin da ya nuna tun daga kan auren har kawo yanzu amma sai ga labari mara dadin ji ya samay mu kuma mun ga alama don ga shedan bugu nan da tazo muna.
Yadda duk akeyi mama tayi don ta fadi gaskiya yadda ya dace har da zancen kudin da suka bar ma gwago ta ja min jari sukayi tace wai mijina ya karbi kudin
Amma zatai mai magana ya dawo min da kudina na dinga juyawa da kaina zaifi tana ta ban hakkuri can dai ta tashi zuwa dakin mama ne tayo mata rakiya wurin ummina.
Nan ma hakkuri ta bayar suna cikin dakin ne baba ya shigo gidan wanda inna ta aika a kira shi yazo wai ga gwago tazo.
Yana shigowa yai dakin mama aka ce suna dakin ummi sai ya kama fada yin may ina ruwan ta da ita aiba ita taba ki dayin ba.
Nan dai yake ta sababi irin na maza da iyalin su basu da tacewa sai su kaida ke kafa dokan su a gidan yadda ransu yaso.
Bai tsaya sauren ta ba yace binta kinzo dama ina son zuwa wani sati in mayar maki da yarinyanan .
Sai hakkuri yake bata abin ya bani mamaki naidai tuna yadda take zama ta kare mashi zagi da yankar kauna .
Amma shi yana nufanta da alheri ya kuma bata go ahead akaina yace tana da iko akaina ta tsawa ta min ba sai nazo gida ba.
Hannu na sa akai ina ihu baba yace indan ban rufe masu baki ba yanzu zai debe min albarka dole mama tasani yin shiru mama tana fadin adai tsaya abin abin a sannu ba a hakana,
Tsawa ya daka ma mama tare da cewa indan bata kama mashi baki ba yanzu zai da ita dani mu bar mashi gidan shi.
Duk yadda akeyi mama tayi amma ita inna cewa tayi indan ma na zauna gidan may zan yi ai kawai gara na koma daki na, na zauna shiyafi.
Baba ka taimake ni karka mayar dani idan ka mayar dani kashe ni zasuyi wallahi wayyo baba ka taimake ni yace idan ban isa gare ki ba sai dai kibi duniya.
Ummi na saboda kawai ci kala bata ce dashi ba amma zuciyar ta kamar zai tsage take jin shi ansa rana, ranan labara zamu tafi.
Don gwago zatai dan sayayya da zata tafi dashi na sana an ta can sai wani nan nan dani takeyi don ganin idon mahaifana.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , ,


🧕🏿1️⃣3️⃣🧕🏿


IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON WANAN NOVEL DIN KUDI NE.


Ummina dake barci ta falka cikin matsanacin firgici daga barcin da takeyi wanda kwana uku kenan a jare ta mafalki dani.
Kuma mafalki mara dadin takeyi a gamay dani din wani lokaci sai taga na gwauce zan fada rami ko tagan ni a ruwa mai zurfi ina iyo.
Ina gudu ana bina zaa kashe ni da wani guduma a hannun mai shi ire iren wanan mafalkin takeyi koda yaushe hakan ya tayar mata da hankali.
Ta shiga cikin damuwa sosai ta dan saka abin a ranta don haka yau ta kudiri aniyar fadawa baba na idan ya dawo dakin ta.
Haka akayi sai da yagama sauren ta kaf yaji abinda take fada bai bari takai aya ga zancen ta ba ya ko hauta da sababi har yana daga murya sauran mutanen gidan suna jin shi.
Mama ce da taji fadan yayi yawa hakana ta tako zuwa kofan dakin tana cewa haba malam ayi hakkuri koma may nene tunda ka taba fada ai ya isa ko.
Yace a hasale bari matar nan da abin haushi auren yariyar take son kashe wa don rashin sanin ciwon kai.
Yariya na gidan mijin ta zaune lafiya hankali kwance zaki tsiro da wani tsurku wai kila ba lafiya take ba ke kina yawan mafalkin ta ke kila wani abu zai samu yar ki.
To Wallahi ahir din ki da zancen Safiya a gidan nan idan ba haka ba rayuka zasu baci sosai akan haka don sam ba zan lamunta ba.
Har yayi ya kare bata ce dashi uffan ba da safiya kuma ya tusa jidali inda yake shiga ba nan yake fita ba.
Sai inna ce ta sa mashi baki tana fadin ai kasan dan tallaka bai iya samun wuri ba in bashi ba abin farin ciki yar ki na can lagas tana aure amma ke bakin ciki ya hanaki ki gane haka ki kwantar da kai kici arziki.
Mutum mai bakin ciki da hassada ai har kanshi yake yi saboda mugun hassada daya huda jiki na sheri, har taci ta sude ummi bata tankasu ba sai share su da tayi tana aikin ta a cikin gida.
Kwana biyu hakana suke da baba sama sama sai da taga ya dan fara mantawa da zance ta roki fita unguwa gidan gwagon ta.
Bai hana ta ba illa cewa da yayi a gaishe ta ta gama abinda takeyi ta shirya ta tafi gidan nasu kamar yadda muke kiran gidan gwagon nasu.
Bayan sun gaisa da gwago tana tambayan ta yara da sauran muta ne gidan take cewa gwago dama nazo in fada maki ne kwanan duk na kwanta barci farkin yar nan nake yi ba dadi wallahi.
Nan de ta kwashe yadda take mafalkin ta fada ma ta shiru gwagon nata tayi sai zuwa can tace wuri ne bakusa ba in ba haka ba da sai a shirya aje a gane ta.
Sai dai addua duk inda take Allah ya tsare muna ita kawai zamuce wanan shawara na gwago ta dauka har tadan ji saukin abinda take ji gamay da ni a zuciyar ta.
A hanya tana dawowa tafe take tana tunanen ko a wani hali nake sai Allah kawai ya sani don yanzu kusan shekara daya ke nan da tafiya na amma babu wanda ke da labarin halin da nake ciki.
Yaya sani zaune yake gaishe ta amma bataji shi ba har sau uku yana mata magana tayi nisa a cikin tunane.
Sai da ya kara kiran sunanta da karfi taji shi ta sauke wani ajiyan zuciya da karfi take amsa mashi gaisuwan da yake mata din.
Yake tambayan ta lafiya dai na ganki a cikin damuwa tai murmushi kamar kada ta fada mai sai take cewa babu komai.
Yace wani matsalane kuma ya taso ki fada min, sai ta fara haye take fada mai yawan ma falkin da take yi dani ta kara da fadin gashi tun tafiyan ta babu wanda ya ji labarin su itama gwagon naku ta bar zuwa yanzu kamar da datake zuwa akai akai.
Shiru yayi yana tunane sai can yace lafiya take ummi mafalkine kawai ke zuwa haka na amma bari nayi maki alkwarin zan bincika inji.

********* ********* *********
Na samu masu kitso na yawan zuwa neman kitso a wurina da kuma sayen kayan sanyi da nake sayarwa a gidan.
Haka ya hana ni shiga damuwa da halin da nake ciki don yanzu takai bai bani abinci sai dai inyi dabara inci wa cikina.
Dan neman kudin da nakeyi Allah yai ma abin albarka sai gashi ina samu sosai duk abin da na taba da sunan kudi sai Allah ya sama abin albarka .
Ga anty maman biyu yanzu ta mayar dani kamar wata yar uwata na jiki nakan dauki lakaci naje nai mata gyaran gida da sauran aikin da shafi na mata dai.
Wanan ya kara kawo muna shakuwa a tsakanin mu har yakai ta tutube da zancen karo karatu tunda taga takarduna suna da kyau.
Murmushi nayi kawai nake cewa Anty nasan ko nai mashi magana ba bari zai yi ba koma ya bari ita mahaifiyar shi ba bari zatayi ba.
Don haka na hakkura da wanan zance zan tsaya inda Allah ya ajeni Allah bai manta da kowa ba ina ji ina gani na koma dani da wanda baiyi karatu ba duk daya.
Tai shiru tana kallona can ta nisa take cewa yanzu idan zaki iya sana,a sai mu duba muga yadda za a yi don dai wanan kitso Safiya bazai fishe ki ba.
Nai murshi nake cewa zan iya mana anty tunda ba wani abu nake yi ba tace to za a diba a ga binda ya dace dani.
Nai shirin komawa gida don karfe biyu ya wuce ta hada min goma na arziki kamar kullun na nufi hanyar gida ina sauri don in koma inyi abinci.
Bai bani kuma indan bayin ba fada ne idan na dafa kuma ya lashe, sai dai ashe na makara don na samu ya dawo gidan ko.
Ina kokarin shiga ne naji an shako ni ta baya sai da idanuwa suka firfito don wahala yana fadin yar iska ina kika fito kin fito wurin biyar mazan ki.
Gaba na ya fadi don jin sabon sherin da ya kulla min kuma nai karfin halin fadin Allah yai min tsari ga shiga halaka da duk wani muslimi mai imani.
Nace ni wurin maman biyu na fito don ina mata aiki tana dan bani abinda zanci yanzu can na fito zaka iya binkawa kaji gaskiyan abin.
Yana huci yakai idon shi ga dan jakar kayan da na shigo dashi gidan sai ya fisge jakar ya shiga bincike nasan dama kudi yake nema ba wani abu ba yana ganin dubu biyar ya saurin dauka yana huce yana muzurai da idanuwan shi ya hankadani gefe daya ya fice gidan.
Nakai kallona ga kayan da ya wawatsar min a kasa na duka na fara kwashewa tare da ajiya zuciya idanuwa na zubar da hawaye.
A hankali na zare hijjab din dake jikina na shiga adana kaya inda ya dace da komai a cikin shinkafa naga wani leda an dukule abu ina budewa na ga kudani da takarda a ciki da sauri na dauka ina karantawa kamar haka.
Nasan mijin ki ba zai barki da kudin motan dana baki ba shiyasa na saka maki wanan a cikin nan don in kin gani ki boye ki samu na amfani dashi.
Safiya ki ci abincin da na baki idan ya kare kada kiji kunyan dawowa ki fada min a shirye nake da in taimaki don rayuwan ki na bukatan taimako.
Ina hawaye nake karantawa nagama ina mata addua nasan Allah ne ya turo wanan matan a rayuwa na don ta taimaka min.
Idan badon Allah da ita ba da ban san yadda rayuna zai kasan ce ba a garin da bani da kowa sai Allah amma gashi ta rike ni tankar jinin ta tana taimaka min.
Da safe da wanki na tashi a gidan da gyaran gida komai na gyara na dora girki dayake ina da komai a hannu na girki nayi lafiyayye na zauna naci.
Na shiga wanka na fito ina shiryawa naji shigowan shi sai dai kamar ba shi kadai bane tashi nayi na leka tare yake da wata mace mai siffan kabila da dan riga karmi ajikin ta wata yankwamama da ita ta sa gashin doki akan ta.
Baka ce bata da wani kyau na ga ya rungumo ta yana tsotson sassan jikin ta da sauri na sake labulen ina runtse idona.
Wani irin kuna nake ji a raina har na koma na zauna sai wata zuciya tace dani na fita na yi masu magana.
Koda nafito sun shagala a cikin abinda suke yi basuji fitowa na ba daga dakin har naje gurin fridge na dauko goran ruwa mai sanyi ban tsaya jiran komai ba na bude goran na kwarara masu ruwan akai.
Wani irin zabura sukayi da karfi yace kina hauka ne zuciyana ya dake nace yanzu dai na fara haukan .
Zan kara zuba masu ruwan ya daga hannu ya sharara min mari sai da na gigice na dako nai kan yankwamaman da duka sai shi kuma ya shiga duka na sai da yai min lis .
Da kyat na kwaci kaina a hannun shi na bude kofa a gigice na fito gidan haka nabi hanya ba komai a jikina sai gidan gwagon mu.
Na isa da kukana tana gani na ta zabura tsaye tana fadin ke lafiya may ya faru da Amadun ne yayi hatsari ne komay ?
Duk suna tsaye a kaina sai faman rusa ihu nake yi da kyat na tsagaita kukan da nake yi nake cewa duka na yayi gwago don ya shigo da mace gidan nai magana.
Sai bude baki tayi tace ke mai ya kaiki yi mashi magana gidan shi ko naki har wani dadi ki yaji da zaki ce kar ya nemi matan da yake so.
Dakatar da kukan da nakeyi nayi ina kallon ta cikin mama tace kin ga bazan hana shi jin dadin rayuwan shi a kan ki ke ma in kina iyawa jiki kiyi shaanin gaban ki lagos bariki ne kazo na zo ba mai shiga shanin wani anan.
Yo wanan wani abu ne da kullun zai zama abin masifa a kanki kin hana yaro shakat a ruyuwan shi.
Habiba tace mummy ai duk laifin ki ne da kika hada shi da wanan kucakar yarin sam bata dace da zama matar shi mutum kamar doluwa gata nan.
Sukai min kaca kaca suka korani haka na fito ina kuka na nufi gidan don ban son in tafi gidan mama biyu saboda gidan zumu ba kasuwa bane.
Na dawo na samu sunyi shaye shayen su a gidan sun bar baje kwalaben giya sun shige daki sai kida ke tashi daga ciki.
Hakana na shige tare da bakin ciki a raina ranan dai yadda naga dare haka naga safiya.

********* ********* *********
Yaya sani yazo ya sallami ummi da dare da cewa zai yi tafiya kamar yadda ya sallamay ta haka ma ya sallami kowa a gida ba tare da wani yasan idan zai tafi ba.
A cikin daren nan yabi mota sai garin lagos shigan safe yai wa lagos din bai sha wahala ya samu motar zuwa unguwar mu.
Gidan gwago ya nema ya samu suna cinikin safiya mutane da yawa a wurin ta masu karya wa sai ganin shi tayi kwatsan.
Da mamaki take maimaita sunan shi tana cewa sanu kaine a garin namu injin dai lafiya yace lafiya lau ta saka a kawo mai abin karyawa ya karya dama tun abincin da yaci a gida bai sake karya ba har lokacin.
Bayan ya karya ya bukaci a kaishi wuri na sai ta fara yi mai kwana kwana don tasan cewa daren jiya nasha duka wata kila ina can ina jinya jiki na.
Da dai ya matsa Sadiya tace bari ta kai shi gwagon bata so haka ba tare da Sadiyan suka zo gidan mu,
Daidai lokacin ya tsaye yana surfa min zagi wai naki fitowa in dafa masu abin karyawa yana cewa don ubanki ki fito nace dakin nan tun ban biyo ki na kara maki ba.
Aka turo kofan shigowa gidan na fito karuwan ta fito daga ita sai dan tawul iya cinyan ta tana cewa wai may ke faruwa ne sai ma a lokacin nasan wai bahausa ne ita don hausan da tayi.
Kallon kallon akeyi wa juna kamar daga sama na ga yaya sani a gidan ban san lokacin da nayi ihun murna ba na rugumay shi sai kuma na fashe da kuka don murna .
Shikan Ahmed shiru yayi don ya san duk banbamin da yake a kaina yaya Sani yaji shi ga kuma karuwan shi a tsaye da dan tawul tana cewa wai bazata dafa muna bane komay ko lalatsa muna yar iska.
Wani tsawa ya daka mata sai da ta zabura ta kama kanta tare da mashi wani irin kallon ko ta fahinci abinda yake nufi ne sai tai shiru.
Yaya Sani yace bari kuka Safiya yau Allah ya gwada min abin da ummin ki kata mafalki a kai.
Lalai ba gidan uban ta bane ashe kai baka da mutunci baka da kima ga kwalaben giyan su nan a zube da suka sha daren a jiya ba a kawar ba.
Na shiga rawan jiki da yaya na ina ce mashi ya zauna a baude nake tafiya ga kumburi a fuska na baki ya sundule min.
Shigewa yayi baya yagama hararn Sadiya da ta kawo shi gidan yaya Sani bai iya kara furta komai ba yai shiru yana bin gidan da kallo.
Nace yaya bari na hada ma abinci kaci yace ki barshi kawai na ci a wurin gwago zama nayi a kusa dashi ina tambayan mutanem gida.
Sai ga su sun fito daga dakin suka fice gidan sadiya ma tace ita zata tafi tabar aikin ta ne a gida yana jiran ta.
Bayan fitan su ne duka na fashe da kuka mai tsuma zuciya tamayoyi yake mim iin bashi amsa a hankali.
Ya nisa tare da fadi ashe dama haka yake kuma aka aura maki shi ba zan barki garin nan ba Safiya cikin wanan halin kafana kafan ki.
Naji dadi nace yaya sani ka taimake indan ka barni kashe ni zaiyi wallahi baya da imani ko kadan.
Muna nan har na gama shiri na kwatsam sai ga gwago na tashigo gidan tana wani haba haba da mutane,
Ya nuna mata ban fada mashi komao ba gamay da zama na a wurin su ta tafi tana cewa sai ya dawo akwai dakin su yaya saadu ta gyara mashi.
Yace ba zai dade ba zamu dawo gwogo na fita daga gidan ya dube ni yace akwai kudi hannunki da zai ishemu tafiya gida.
Nace eh yaya akwai yace don shima dakyat ya hada kudin da ya biyo babban mota yazo don ya ga ummi ta damu.
Mun tafi har gidan maman biyi dashi taji dadi tai murna taba lamban waya akan idan naje sai in kirata don yaji saukan mu.
Takawo kudin mota ta bamu harda na guzuri wanda zai ishemu nai mata godiya ta kaimu na dan yi tsara ba na saro lace da yan dogayen riguna takai mu garejin kananan motaci muka kama hanya sai arewa.
Tafe muke zuciya ta babu abin daka cikin sa sai yawan tunane fan ban san irin tarbon da zamu samu wurin mahaifin mu ba idan mun isa.
Can lagos shishiru gwago bata ga ya sani yazo gidan ta ba ta tayar da habiba taje tazo mata da shi.
Zuwan ta yayi daidai da dawowan shi gidan da dan ledan chefane a ciki don ya san yaya sani na gari yai wanan.
Sai dai babu kowa a gidan sai ga habiba yake tambayan ta tace bata san inda muka tafi ba itama zuanta kenan mummy ta turo ni in kira wanan bakon.
Dakyat ya bude gidan ya samu ya shiga sai bayan ya bude ne wata makwaciyar mu takawo mao key tace nace a bashi yace ni ina inane da zan bata key din gidan.
Taga dai na dauki jakkana da wasu kaya mun tafi idon ya fitar waje acikin mamaki yace What.
Eyyeh ta tafi tace damu har mun mata rakakiya yayi wani dan fito a bakin shi irin na yan daba ya shige ciki ita ko habiba komawa tayi gida ta fadawa mahaifiyar ai gwago naji tace dama ban yarda da zuwan dan iskan yaron nan ba.
Kana ganin shi kaga dan tantiri dan duniya ko ina babu mai zuwa daga ma yayi barka ya rabu da kaya gidan shi shegiya banda taulali mai aka kawo min dama su karata can.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , ,


🧕🏿1️⃣5️⃣🧕🏿


YAR UWA WANAN NOVEL NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , , , ,

Kamar yadda baba yace haka din ne ya faru gwago ta daukeni zuwa lagos ita kadai kamar mara gata ta, tafi dani.
Mama ta ance an samu wacce ta raka ni muka tafi tare amma sam baba yaki yarda da hakan yace wai ai gwago uwata kuma gwago na.
Su yaya sani sun so siyi ma baba dan banga banga amma yaki yarda yai masu tijaran tsakar gida.
Wanan abin shiya tunzura ummina tabar gidan baba yan uwanta kuma suka kama mata suna cewa su dai basu ga amfanin auren da babu yanci cikin sa ba.
Da farko baba bai damu da tafiyan ta ba sai daga baya ya damu a kan yara don yanzu dole ya bada komai na anfanin su.
Wanan abin ne ya fara damun shi taje bikon ummi mahaifinta yace badai gida shi ba yaje yayi iko da yar shi shi kuma yai iko da tashi don da baifi daba amma ummi ta gama auren gidan shi.
Ya dauka wasane sai da yaga yannen ta sun kaishi kara kotu akan ya bata takardan sakin ta yasan da gaske suke wanan karon.
Aka shiga kotu suka kora wa alkali halin da yake mata da rashin bata yancin ta alkali yace zai daure shi don sai ya fadi gaskiya indan ba sayar dani yayi ga gwago na ba yake kamay kamay.
Yai ta rantsuwa akan wallahi bai sayar dani ba zumunci dai ne tsakanin shi da gwago na Alkali yace zumuncin zamanin nan zakai wa haka.
Daga Allah ya taimake ka yar ka ta dawo gida wurin ka lafiya ba tare da wata matsala mai karfi ba don rashin sanin zafin kai zaka maida ta gidan wahala watau taje a kashe ta da kurciyan ta ko.
Yace ba haka na bane alkali yace haka ne mana sai ta zama mara anfamni zaka dawo uwar ta da ita ko yana dai ta bada hakkuri alkali yace ya basu sati biyu su shirya in ba shiri tazo ta karbi takardan ta.
Da haka suka wuce aka rabu baran baran baba hankalin shi yai matukar tashi mama tace na fada maka kabi abin nan sannu kaki .
Safiya ba irin sauran yara bane yarinya ne mai biyayya da sanin ya kama ta amma har kaga ta kasa hakkuri a wanan halin ta akwai magana da anyi bincike tare da kafa hujja mai kar fi.
Amma kaki tsayawa ai komai a hankali ka dauki yarinya kamayar da ita ba wani binciki kwakwara yanzu duk abin da ya faru da ita sai ka kuka da kan ka.
Nan suka taru da shi da Inna suka mai mama caa a kai wai tana dai su agoya mani baya ne in kashe aure yasa take fadan haka amma wani wahala nake ciki.
Nan dai itama tai masu nasu borin ta ce aidon ba diyar Inna bane a wanan halin da duk gari kowa ya gama jin wanan zancen ko.

********* ********* *********
Daga ni sai gwago da wasu mutane a bayan babban motar traller da zasu kai kaya kurmi don son mallaha ta kasa biya muna dubu hudu zuwa lagos.
Ina rakube a wuri daya a cikin mota duk inda mota ta tsaya sai ta sai abin kwalam taci bata ko kallona ni ko ta bani baya gama na ina tunanen halin da na baro ummi na ciki.
Sai wani awara data saye tun a arewa taci ta raga yai tsami ta jehomani kaina girgiza mata alamar a a bana ci har muka kai sai ruwa da nasha ina da muka sauka mukai sallah.
Anan na kulla ko sallah ba bata yi daidai irin sallah yan kasuwan kauye ne a gagauce ake yin sa ba cikawa.
Mun sauka lagos da dayan rana don motar bata sauri maimakon mu tafi gidan ta ta hada mu tai muns fada sai kawai tace a kaimu gida na bata ko shiga ba ta saukemin kayana tana ta masifa wai ban da kama jiki.
Ni dai na fita suka ja mota suka tafi suka barni nan tsaye ina mamakin ta a raina sai da motar ta bace na juyo ina kallon gida tare da sauke ajiyan zuciya na fara takawa zuciya na fal da mamaki gwago da alaman sam bata da digon amana a rayuwan ta.
A hankali na tura kofan gidan ga mamakina sai naga gidan a bude na shiga da addua na ga baki da alama akwai mutum gidan.
Warin taba da tsamin giya ne sukai min maraba ga hanci na take wani irin bakin ciki ya lulube ni na rintse idanuwa na don takai ci.
Dakina na nufa da buhun kayana ina ja don ba zan iya dauka ba don nauyi saboda nayo yan sare sare a arewa na je da shi.
Dakin yana nan kamar yadda na barshi babu sauyin komai a cikin sai dai kuran da yayi kawai na rashin mutum a cikin sa.
Zama nayi nai tagumi hannu bibiyu idanuwa na suna fitar da hawaye takaici don gwago takai katuntumar yar cin amna.
Koda yake bata da laifi duk wullancin da na gani mahaifina ne ya ja min shi don jajircewa shi a kan gwago wai shi zumunci .
Ina ga motsi suka ji ya fito kofan gidan a bude yake sai kuma ya kalli kofan dakina shima a bude yake dakin.
Da sauri ya tako zuwa kofa ya daga labulen dakin ina zaune shabe shabe sai hawayen da nake zubarwa a idanuwa na.
Kamar daga sama naji shigowan shi dakin babu annuri fuskanshi ko kadan sai dai ya dan nuna mamakin gani na a wanan lokacin.
A take na razana yayin da nai kwali dashi tsaye kofan dakin ya rike labulen dakin.
Fara takowa yayi zuwa inda nake zaune gabana ya fara faduwa da tsoro yazo daidai kaina ya tsaya na cewa.
Ciki buga tsawa yace dani tun yaushe kika dawo gidan nan ban sani ba yana ma dakin yan dube dube can ya juyo ya tsare ni da idanuwan shin jajjaye.
Ya sake maimata tambayan shi gare ni da yaushe kika dawo nace ?
Na dan kalle shi nace yanzun gwago ta sauke ni ta wuce sai ya watso min mugun kallo kamar zai make ni, yace waye ya baki izzinin wucewa garin ku.
Ban bashi amsa ba sai ma kawar da kai danayi daga kallon shi don wani irin tsanan shi nake ji da haushi yana shigata da zaran na ganshi.
Ya harare ni yana cewa wanan ya zama maki na farko da na karshe a gidan nan don ba zaki maishe ni yaro ba .
Banko san yana tsaye ba haushi da takaici sun cikani na shi caraf na jiyo muryan mace na magana daga falo ya juya da sauri ya fita zuwa falon .
Daidai wanan lokacin naja tsaki tare da fadin ai guma yaro da halin ka Allah dai ya sauwa ka gashi dai mutum a ido amma a ina halin shi na kamala baikai ba.
Can naji sun fice daga gidan na fito na kalli gidan a kazance da kyama hawaye ya zobo min na takaici da bakin ciki suka rufe min zuciya.
Yanzu ni haka zan zauna a mara gata kamar wata mara asali in zauna da mijin da bai san tsoron Allah ba a zuciyar shi.
Bazan iya zama cikin wanan jassabab in yi ibada dole na shiga aikin gidan duk da gajiyan da na dibo din a motar.
Kafin wani lakaci na gama gyaran gidan na dora girki abincin da zanci na shiga wanka daidai lokacin da na fito bandakin ne sai gashi ya dawo gidan da ledoji niki niki kamar da gaske.
Tsaye yake a tsakar falo yana kwala min kira da ke wai kina inna ne nake kira baki karba min yazo ya bankado labulen dakin ina ciki ina sallah sai ya juya yakoma dakin shi.
Sai da na idar nafito falon baya nan na taka zuwa kofan dakin nashi na tsaya daga kofa don tun ranan da yace karna kara shiga mai daki ban sake ko taka kofan shi ba.
Nace mai gani daga kofan har ya tube ya kuna taba ga kida na tashi daga cikin dakin nai magana naga kamar bai jiba na juya abina zan shige ne ga kayan da ya shigo dasu gidan.
Nasan kiran da yake min kenan don haka na tsaya ina duba kayan, kayan miya ne sai maclean da sabulun wanka dana wanki sai madara da ovaltine da sugar.
Ina duke ina cire komai ina kaiwa inda muke ajewa ya fito falon daga shi sai gajeren wando jikin shi ba rika sai hayaki da yake busawa.
Take falon ya karade da warin taban ba dadin ji, ya zama min dole na mika al, amura gaba daya ga Allah don shine kawai zaimin mafita saboda yadda naje gida baba ya wulkantani a gaban yan uwa na da su inna ummi na tana kumsan bakin ciki gaba daya naji duniyan ta fice min a rai duk kuwa da shedan da yaya sani yayi dakuma wanda suka gani a jiki na baisa baba ya sassauta min ba ga halin da nake ciki .
Ko gaida shi nayi da kwana baya karba min itama ummi na abin ya shafe ta.
Yanzu dai gani na dawo a turke na mai cabo haka zan daure in ta hakkuri don kada fushin iyayyena na hau kaina.
Dama ance sabo turken wawa inda sabo ai yanzu na saba da wahalan gidan shi musamman idan yana jin fitanan shi anan falo zai min shaye shayen shi.
Haka kuma idan yaga dama ya afka min duk rokon da zan mai bai sai ya kyale ni, har sai ya ji ya samu yadda yake so da kansa.
Na nisa tare da fadin akwai Allah sai naji yana fadin in akwai sauran abinda ban sayo ba ki fada kada kuma kice na barki da yunwa.
Dajin haka nasan ya tafi gidan gwago ta kwashe karya da gaskiya ta fada mashi kenan shine yazo da wanan sayayyan.
A sanyaya na bashi amsa da sai man miya ba a sayo ba man miya ki saye mana iyakar kudina kenan na kashe.
Na dago ina kallonshi nai karfin halin fadin ai ba hakki na bane saye da sai in saye din.
Yaci gaba da busar taban shi bai tanka min ba can naji yace tsiyan ki kenan ke ba ai maki daidai .
Na dago zanyi magana naga yana min wani irin kallo kamar tsohun maye sai nabar maganan da zan yi a lokacin na gagauta kawar da kayan don bai mashi wuya ya afka min a nan wurin mutum kamar hariji bai gajiya da kwana da mata.
Ranan dai bai barni ba tun karfe takwas da na sallame sallah insha,i yana nan yana sintiri a falon.
Ina addua ya shigo min daki muryan shi naji a tsakiyan kunne yana cewa yau ki tabbatar da cewa zaki biya bashin kwanakin da kika dauka agida .
Na dago kai na dan kalle shi naga idanuwan shi jajaye akaina babu ko alaman kuya a tare dashi nace banci bashi kowa a kaina ba don ma ko nace ai akwai masu biya da suka fini daraja da kima.
Ban gama rufe baki ba nagan shi a gaba na dauka daya yai min sai saman gadon dakin nawa .
Ba bata lokaci ya shiga kiciniyar cire min hijjabin da nai sallah ya rake daga ni sai zani Allah ya tai make ni tun da na fito daga wanka na dan kintsa jikina.
Ba ta lokaci ya shiga sinsina na wuya na da na shafe da hummura da alama yaji dadin kan shi naga yana wani shakan ko ina daga bisani ya shiga watsa min kiss irin nasu na yan duniya.
Yakai tsawon minti uku yana abu guda ajikina zuwa bakina ina kokarin janyewa ne daga gare ya da kata daga abinda yake yi yace.
Wanan abinda kike yi shi ke yawan bata min rai dake a koda yaushe mutum zaizo gare ki sai anyi rigima.
Ba tare da jin tsoron shi ba nace dole ayi rigima don ba a zuwa ma mutum ta tsigar da ya dace sai a cikin may ko najasa.
Shiru yayi na wani dan lokaci yana kallona ido da ido yace nine najasan ke nan ma ko.
Gabana ya fadi naga yadda idanuwan shi suka kara kadawa sukai ja jawur dasu a lokaci daya nai saurin dauke idona gare shi.
Yayi amfani da hannushi ya sake juyo fuskana muna fuskantan juna yace come on so nake ki kalli idanuwa ki gayamin cewa wani najasa kike magana ko ysushe.
Na dai gane yau yana son mutunci ne don ko magana da yake yi a cikin karamin murya yake yin sa tankar yana tsoron wani yaji mu ne.
Kawai sai ji nayi hawaye sun soma cika min idona na cije fatar bakina sai can nace yaya ka bani daman in fada maka abinda ke zuciyana tsakani da Allah.
Sai na ji yace ke nake saurare ai gaba daya ya tsare ni da idanuwan shi sai na dan yi shiru zuwa wani lokaci.
Sai na soma magana da cewa yaya ka yarda dani tun da nazo gidan ka na zo da shirin maka bibyaya a duk yadda kake.
Amma sai ka dauke ni daukar mace biya a gare ka yau koda ace sayoni kayi a matsayin boya baka san asalina ba ban cancanci irin abinda kake min ba.
Kadoke ni, ka zagi iyayyena, ka dauko min karuwan ka har gida uwa uba ka zauna kayi shaye shayen ka har mai na gyara wurin duk ina hakkuri da hakan don biyayya ga iyayye.
Amma hakan bai maka ba sai ka yi kokarin tozar tani a gaban karuwan ka akan dole nai mata abin karyawa.
Yaya ina zaka da wanan alhakin a kan ka kai kadai bafa ban iya dauka mataki bane ina dai hakkuri ne don daraja aure dana iyayye amma duk wana bai isa ba sai ka , , , ,
Kuka ne yaci karfina na kasa karasa abinda zan, fada mashi din , irin rikon da naji yayi min shiya tabbatar da magana na yadan shige shi a lokacin.
Anan nayi kokarin kwace jikina daga ga gare shi amma sai naji ya kara matse ni daga jikin shi, ya shiga yin wasu irin magan gannu wanda na kasa fahintar may maganan nashi ke nufi don acikin harshen turanci irin nasu na wayyayu yake yi.
Acikin wani irin yanayi naji yana kokarin shiga na a lokacin fadi nake don Allah yaya ka barni amma bai kulani ba.
Naci gaba da magiya ba tare da yasan ina yi ba har sai da yacin ma manufan sa gare ni.
Ya gama ya mike kamar wanda aka tsikara yana mai daukan wando shi yt a bar dakin ina kukan takaici na bishi da kallo har ya bace min.
Nan naci kuka na ya isheni na tashi nai wanka ina tausayin kaina ni kadai a dakin .
Washe gari koda na tashi duk jikina yai tsami haka na daure na sama muna abin karyawa na gama na jera mashi a taburi.
Kwana biyu zaka ce ya daina halin shi ne don da yadawo aiki yana gida sai dai shan giya yabar yi a falo amma taba kan sai abinda ya karu.
Na shiri ranan wani jumma a na tafi gidan maman biyu tayi mamaki kwarai data ganni take tambaya na yaushe na dawo .
Na koro mata labari duk yadda zuwana gida ya kaya da kuma dawona da gwago nan garin sai da ta gama saurare na ta nisa tana cewa.
A gaskiya mahaifin ki yana da taurin rai Safiya ya kuma tafka babban kuskure da bai tsaya binke ba ya dauki mataki yadda ya dace.
Sai ya koro ki babu wani bincike da yayi wai duk karan zumunci yake yi alhalin yanzu zamani ya canza mutane basu da gaskiya ko kadan kowa nasa ya sani.
Takare da cewa babu komai yadda kikayi kin kyauta Safiya kibar wa Allah alamarin sa Allah yana tare da mai gaskiya.
Nan take tambaya da na dawo yaya halin nasa ya sauya ko kuwa yana nan kamar kullun nake cewa da ita ya sauya halin shan giya a falo kuma tun ranan da na dawo na samay shi da mace har yau banga ya dauko wata a gidan ba.
Tace Allah yasa ya daina indai ba tuban mazuru bane yai maki amma ga yadda na fahinta yana san son ki iskan cin dai ne ya sha gaban shi.
An sauko jumma a nai shirin komawa gida ta dan hado min dan abinda ta saba yi min tasa driver gidan su ya kawoni gida.
Sanin halin shi da nayi yasa nace drivern ya sauke ni tun a farkon layin mu na karasa da kafa.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGAN, , , , , ,


🧕🏿1️⃣6️⃣🧕🏿


YAR UEA WANAN NOVEL DIN NA KUDINE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , , , , ,

Yau nayi yamman yin kitso saura kadan na karasa wa wata mata kitso ta dawo daganin shi a gajiya yake lis,.
Nai mai sannu da zuwa ya amsa min ciki ciki ya shige ciki nai sauri karasa ma matan kitso na sallamayta na shiga ciki.
Na samu yana dakin shi don haka ban tsaya jiran komai ba na dauki tsintsiya na shiga gyaran gidan a gagauce ko da dai bai datti amma kaida ne nayi gyaran saubiyu nan.
Ya fito daga daki rai a bace ya wuce zuwa wurin three seater yana tsuki ya zauna nayi saurin dagowa ina duke na sake gaida shi cike da girmamawa.
Bai amsa min ba sai gyara kwanciyan da yayi rai a bace mashi yace wai ke wata irin doluwar yarinya ce .
Da mamaki nake kallon shi don basan laifin da nayi mai ba yake ce min doluwa kuma na ina kallon shi da mamaki.
Ya katse ni da cewa in ba dolewa kike ba yaushe har zaki tsaya uin wani kitso can kin san lokacin dawowa na gida yayi.
Kamar zan yi magana sai na duka naci gaba da sharana ban ce dashi uffan ba, wai ashe yin haka dana yi yaji haushi na.
Dole dama yaji haushina mana sabda tun da na dawo na hanashi shakat a gidan badai magana nake masa ba amma yana dan daga kafa ga haliyyan shi na banza a gidan.
Yau kwana uku kena da naga ya tsiri daukan zafi dani abu ba abu ba zai hauni da fada.
Kamar daga sama naji saukan mari a fuskana ina duke sai da na gigice na dago ina dafe da fuskan da har idanuwa na sun fara fitar da hawaye don zafin marin.
Fuskan shi babu annuri a cikin sa yace don ubanki ina magana zaki banza dani kici gaba da shara don kin mayar dani dan iska .
Na sake kallon fuskan shi tare da nuna razana shi kanshi sai da ya fahinci razana nawa na goge wahayen dake zubo min cikin takaici.
Nace yaya may kake son nace maka bance ba ma ka mareni har da zagin ubana balle na tsaya baka amsa.
Baiko numfasawa yake fadin na zagi ubanki ko zaki rama ne ya wani zazzaro ido waje.
Oh na zaci ai zaki rama ne yar iska kawai mara kunya banza munafuka in anyi magana kice wai ke ta Allah ce ina sanin Allah yake a nan.
Cike da tsoro nace dashi Allah ya baka hakkuri, ya buga min tsawa da fadin rufe mun baki mara kunya kawai.
Ya harare ni sama da kasa a karo na biyu kamar zai kara buguna sai dai na samu ya hakada ni gefe har ina gwauruwa da bango.
Ban sake magana ba na dadafa bango na shige kitchen ina jin shi yana dura min zagi yana fadin duk rana da ya dawo ya samay ni ina shegen kitson nan a gidan nan sai ya balbalani har da mai kitson
Ya gaji da fadan shi ya suri key din motar shi ya fita waje tare da banko min kofan gidan a fusace.
Na nisa a hankali dana ji fitar shi gidan naceai hali baya barin halin sa kwana biyu bai dake ni ba hannusa na masa kai kayi dana tanka ya samay ni yai ta jigga kamar an turo shi.
Na kamala aiki na cikin baci rai kaina namin ciwa kamar zai tsage ina ji ranan ya dawo a buge yana hauka shi ban fito ba karya hada dani.
Kwana ki muka dauka a haka a gidan yana faman daukan fushi dani a gidan da zaran ya shigo gidan zai kuna kida na tashi sama kamar kune na zai tsage.
Da zara na shigo falon idan yana ciki yanzu zai dauko taba ya kunna yana busa hayakin sama yana tashi ya gauraye falon.
Da sauri zan bar abin da nake yi na shige don jin warin nake kamar zan amaye hanjin ciki na kaina ya dinga sarawa.
Yauma bai fita ba tun safe yana gida kuma a falo yake zaune bai shiga ciki ba dole na fito hakana ina aiki na.
Na gama hada abinci na aje mashi nai wuf zan koma daki na yace ka dakata naja na tsaya.
Yana zaune yana ya mutsan fuska yana kallon abincin da na aje a gaban shi kaikace mugun abu na kawo mashi.
Ya wani harde kafa yayi kutun kutun da rai yana busa hayaki sama a zuciya ta nace dan isaka ka fada ma Allah ai.
Ina tsaye har wani lokaci a wurin amma hakan baisa ya dago ya kalle ni ba duk da cewa ni gyara tsayuwa don ya san dani a wurin tsaye.
Dole na gaji na dan yi mai magana dacewa gani yaya gani kamar bada shi nake yi ba shiru yayi yana kallon tv da ke aiki wasu fitsararu na rawa.
Na kara cewa yaya gani don Allah kafada min abinda zan wanka nake som naje nayi nai sallah don lokaci yayi.
Yayi wuf ya mike tsaye yana nunani tare da daka min tsawa ya sake nuni da hunnu yace ke yarinya baki fini sanin Allah ba don ba ke kadai bace yar musulmai.
Idan baki san abinda kike yiba nina san abinda nakeyi kada ki cika min kunnuwa da surutun ki na bashi na dakar dake inji ba.
Shiru nayi ina mamakin wanan mulkin malkan da yake min kamar ya sai boya a gidan zuwa ca na nisa nace a hankali yi hakkuri yaya.
Ya koma ya zauna yana kokarin bude abincin dake gaban shi , can ya dago yana cewa uban wa zai ci maki faten doya da rana.
Tsaye nayi kawai ina kallon shi da mamaki zuciyana yana tafarfasa zangan min uba da yake yi ba gaira ba dalili.
Yace a fusace ba tambayan ki nake ba kinyi shiru kin kyale ni, nace nafada maka bamu da koma a gidan ya kare tun kwana biyu da ya wuce..
Wani kallon sama da kasa yai min ya watsar yana cewa wanda na kawo maki kikai barna yanzu ki barnatar da wanda kika gani.
Bazan sake sayen koma a gidan nan ba sai wata ya kare don bake nake yiwa aiki ba da zaki ta cinye min kudi a banza.
Ikon Allah nace a raina amma a fili cewa nayi dashi yaya ban barnan abinci don ma karya kare ban yin dahuwar rana sai da dare nake dafawa.
Yace ke kika sani ni ba ruwa na kin dai ji abinda na fadi kuma ba zan fasa ba don haka ki bace min da gani.
Har na juya naji yace dauko min ruwa mai sanyi wanan yayi zafi ya fara cin abincin wayan shi yai kara ya dauka tare da fadin kin dawo kenan don naga nomban nigeria.
Ban san may wada yake wayan da ita ta fadi ba naga ya kalli a gogon hannun shi sai yace yau dai duk yadda za ayi zamu hadu.
Yana sauraren ta yana murmushi a fuskan shi abin da ban taba ganin yayin ba a matsayina na matar shi.
Can yace alrigt sai nazo din amma fa kada in samu baki nan ya aje wayan yana ci gaba da cin abincin sa daya gama kushewa.
Ya dago yana kallona nai kicin kicin da rai saurin dauke fuskanshi yayi ya dauki ruwan ya kora ya aje ya mike ya dauke key din shi ya fice daga gidan.
Shiru nayi ina mamaki wanan hali na shi na rashin tsoron Allah a gadarance komai yake sam bai tunawa a akwai Allah.
Kusan karfe daya dare ina kwance har nayi barci na falka naji dawowan shi gidan ya shigo yana may sai dai bai bugu sosai ba.
Don baji yana min haukashi na zagi ba ina jin yana buruntu a falo can naji ya bari nasan ya kwanta ne.
Barci bai kara dauka na ba na shiga tunanen wanan halin nashi shine giya shine taba uwa uba neman mata.
May zai je ya gayawa Allah tsiyan abin kuma baida mafadi da zai tsaya yai mashi fada da nasiha yaji.
Duk iyayyen sun watsar dasu suma suna nasu sharholiyan da muamula da yan iska ta yaya zasu gyara tarbiyan diyan su.
Gaba daya ba na gari dan dama dama yaya saadu koshi ban tabatar da halin shi ba tunda bana shedar shi.
Ina kwance naji hawaye nabin kuncina zuciya na cike da tausayin kaina ga wanan rayuwan da mahaifina ya zabar min yi .
Na tabbatar da i zuwa yanzu baba yana da labarin halin da nake ciki sai dai karfin hali ne kawai irin nasa na jajircewa.
Na nisa tare da gyara kwanciya na tsoro da fargabane ta sauka min a zuciya ta anya ko nima bazan kwashi zunibi a wanan zaman ba.
Washe gari ba abin da zan dafa mu na a gidan don komai ya kare har wurin sha daya rana can naji motsin shi yafito daga dakin shi.
Fita yayi daga gidan na dauke ya shiga gari ne zuwa wani lokaci sai gashi ya dawo da ledan take away a hannun shi.
Lokacin ina folo ina tsaka da gyaran gidan babu kunya ya samu wuri ya zauna tare da cewa in miko mashi goran ruwa.
Nabar abinda nake yi na shiga na dauko kofi tare da goran ruwan na kawo mashi daidai ya bude take away din nasa.
Tozali nayi da rabin kaza sai dan shinkafa a ciki na friderice da aka zuba yasha hadi launin kore shar.
Nan ya zauna babu tsoron Allah ta cinye tas ya wurga min roban a kasa yai zaune yana sakatan hakori da tsike yagama ya jawo taba ya aza.
Sai da na gama abinda nake yi har sha biyu ya gwauta lokacin ana neman karfe daya na rana.
Na fito saye da hijjab dina ina saka takalmi na ya juya a fusace yana fadin ina zaki ?
Ban ko numfasa ba nace neman abinda zanci tunda safe banci komai a ciki na ba yayi saurin cewa to wa ya hanaki kice barnan ki ya kaiki ga karar da abincin da na kawo maki ai.
Nace abincin da ka kawo min yaushe nake barnan shi gidan nan dudu fa kwano biyu ne na shinkafa kuma ko kazon shi baka taba gani a kasa ba.
Kwano biyun ai nayi kokari daso kikeyi na kawo maki buhu komay ai a gida ku ko kwano biyun ana cine na shinkafa.
Daya ke nan kon samu banza shine kike barnatar wa ko ta yanzu kici kuma wallahi in kika kuskura kika fita yau sai na balbala ki a gidan nan.
Alokaci guda jikina yai sanyi nace kayi ma Allah yaya kayi hakkuri in nemi abinda naci kar yunwa ya illanta ni.
Yace bazaki fita ba nace a hankali na matsa wajen shi nadan fara magana a sanyaye cikin kamala nace yaya nasan ka isa ka hana ni fita amma ka tausaya min in samo abinda naci tun da ranan jita wallahi banci komai ba a gidan nan.
Yace ke na fada maki don ba zan yarda ki rika zubar min da kima a waje ba a ganki kinje sayen abu ga hannu.
Da mamaki na dago ina kallon shi bakunya ya fadi haka kamar ince kaida ka sayo abinda kaci fa yanzu.
Nace ya kamata ka tauna maganan ka kafin ka fadi indan ban sayo naci ba may zanci a gidan nan kenan.
Yace ke kika sani gobe in na kawo abinci zaki koyi tatalin shi dakyau ya tashi ya shige dakin shi ya barni tsaye a wurin na bishi da kallon mamaki.
Ina cikin daki na idar da sallah azahar naji fitan shi daga gidan nan na fito falo na zauna sai ga makwaciyana ta shigo wurina bahausa ce akwai dan nisa a tsakanin mu.
Bayan mun gaisa take cewa dani ai tun dazu naso shigowa nasan wanan miskilin mijin naki na gida don naga motar shi a waje .
Nace yanzu ya fita bai dade da fits ba ta na bude hijjib din tace ga dan wake nayi damai da yaji nasan zaki so don nan ba arewa bane na kawo maki na karba ina godiya.
A zuciya na sai kabbara nakewa Allah da yai min mafitan abinci ts ida ban zata ba bata dade ba ta fice tare da min sallama tace tana da aiki gida.
Nai mata godiya na dan raka ta bakin kofa ts fita na koma a sukwa ne daki na hauci hannu baka hannu akushi naci sai da na cinye shi tas na kora da ruwa mai sanyi.
Nai hamdala gs Allah da ya bani abin da zanci shi mugun baiga karshe na ba na bude window dakin da sake fanka kamshin ya fita.
Bai dawo ba sai bayan karfe tara na dare yazo da ledan shi na abinci da na dan wani bussashe burodi ya wuga min daki na ya zauna nan yaci abincin shi ya koshi ya fice gidan tare kulle ni ta baya.
Bai dawo ba sai safe lis koshi don ranan aiki ne nasan zai tafi wurin aiki ya dawo da wuri don kada ya makara.
Ya fice baiko bi ta kaina ba na sauke ajiyan zuciya na mike da sauri na shirya zuwa gidan maman biyu don na samay ta gida kada ta fita office.
Nayi arziki tana shirin fita na iso gidan tana ganina ta aa Safiya yau da safe haka kika bugo sammako.
Maimakon in bata amsa sai kuka bata hanani ba ta zauna tana tare da harde hanneyen ta saman kirjin ta.
Sai da nayi mai isata ta miko min ruwa tace jeki ban daki ki wanke idon ki dashi mikewa nayi ta bini da kallo a ranta tace wake da laifi mahaifina ko mijin koko ni.
Fitowa na ya katse mata tunanen tace zauna a kawo maki abinci kici nasan baki karya ba wanan sammakon da kika bugo haka.
Mai aikin ta ta kwala wa kira tazo tace akawo min abin karyawa aka cika min gaba na da abinci fal na kasa cin komai duk da ina so din amma kincin zuciya ba zai barni naci komai a lokacin.
Ta mike zuwa ciki can ta fito ta samu ban taba komai ba daga cikin abin da aka aje min din.
Tace aa anty yan biyu bakici bama na lafiya dai zan fara kuka tace dani dakata banson yawan kukan nan ki fada min binda ke faruwa.
Dama nasan wanan mijin naka dan iska tuban mazuru yayi ba tuban Allah da annabi yayi ba.
Nace wallahi anty dama kin fada ai nace wallahi anty da yunwa yake horoa na yanzu nan na kwashe komai na fada mata .
Tace dan iska wai ashe bazan sa a kama min dan iskam mijin nan naki ba aimin maganin sa matsalan kawai mahaifin ki da idan yaji zai tsitsine ki a banza.
Anya safiya wana mijin naki kuwa yana cika sallah shi don bai abinda masu imani keyi a rayuwan su.
Nace ina fa yake cika sallah anty ibandam dai gashinan ne daga jumma, a sai jumma,a ake yinta .
Tace kin ga yanzu aiki zani bari na saka a samo maki abinda zaki ci kiyi ki koma gida don yana iya maki tako yaje ya dawo ya gani ko zaki fita.
Tace ki dai kara hakkuri mu gani indan bai daina ba wallahi ni da kaina zanyi karansa a raba wana kaddararen auren naki.
Komai aka hado min mai yawa babu abunda babu na fannin girki da ba a hada min ba niki niki na dawo gida da kayana.
Taimin alkawarin zata dinga zagayowa akai akai tana dubani nai msta godiya ina kuka tace nayi hakkuri ta kawo kudin ta kara min ta wuce zuwa wurin aikin ta.
Ban bata lokaci ba na shiga kawar da kayan kafin mugun ya dawo gidan ya tar dasu ya samu na min iya shege a kan su.
Komai na adana su tsab ba abin da na bari a fili na dawo falo na zauna can ko kamar ta san zai dawo sai gashi ya shigo gidan ina zaune a falo.
Ko kallo ban ishe shi ba ya shige dakin shi fuskan murtun kamar na yan high killer marasa imani dasu jin kadan ya fito ta sake fice wa na nisa tare da fadin macuci azzalumi kawai ta Allah bataka ba.
Chapter 2 · 0% Book details