← Book details Bad Boys Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 9

Sashe 6

Bad Boys Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sheikh yanda kasan ƙaramin yaro haka ya zama ,abunka da bai taɓa samun wanda ya nuna masa zalama ido biyu ba ,kuma yasan halin Rashid ba karamin ɗan duniya bane ba ,ya kwallafa rai akan mace ko ba aure sai ya nemeta .
Jikinsa na bari ya daga waya ya fara kiran Salimart .

Dammm! Ƙirjin Salima ya buga ganin kiran ya Sheikh daidai ta rufo ƙofar falon ta dawo ,gode ma Allah ta shigayi a ranta da ta sallami Dr kafin nan.

“Assalamu Alaika ya zaujiy”(Mijina)

“Waalaikis Salam ya ustaziya ,kina jina”

“Eh ya sheikh”

“Yau Inason kici ado nan da sa'o'i biyu ina dawowa zamu fita shaƙatawa”

Ras gaban Sayyada ya ɓaci ,out of joy ta daka tsalle tace da gaske kake Habibiy?”

“Kwarai kuwa ustaziya zamuje musha Ice cream muci ɗan pizza ko ya kikace,ɗan flexing din nan dai kema ki fita gari ayi dake”

“Umuuuuh😘 Ina sonka mijina ” ta manna ma wayar kiss ta kashe da sauri ta yi cilli da wayar akan kujera ta haura sama da gudu zuwa sashen ta.

Ya Sheikh waigawa yayi ya kalli Rashid cikin Murmushi
“Mata wato sudai mata'ul hayat ne(Ƙyale_ƙyalen rayuwa) sudai a kashe kudi a ji daɗi,yanzu zo kaga farinciki da murna”

Rashid lumshe ido yayi yana kora drinks din hannunsa yana sanyaya maƙoshi
“I can perceive bros”

***
“Salima
Salimaaaaa
Wai kina Ina ne?”

Ya shigo gidan hannunsa rike da Car key .

A ruɗe tace “Na'am ya Sheikh Ahlan wa sahlan”(welcome)

Sannan ta fito daga ɗakin tana biyo stairs din da takalminta mai tsini yana ƙara cakas! Cakas! Cakas!

Ya Sheikh Binta da kallo yayi ,kawai sai yayi zumbur ya mike

Ta saka wani dandatsatsen less an mata ɗinkin bubu ya fita sosai ya zauna ɗas a jikinta ta murza daurin turban gingiringin ta sagalo mayafi a kafada hannunta daure da wrist watch da zobentana gwal daya hannun na azurfa sai ƙamshi take zubawa.

“Salima meye hakan kenan?” cak taja ta tsaya ba tare da ta gangaro ba ,sai bin jikinta da ya nuna da yatsa take da kallo,tana neman abinda yayi aibu a jikinta

“Salima wannan ba shine leshin da Anty uwani ta kawo maki tsaraba daga cotonou ba?”

“Eh shine mana ya sheikh” tafa hannu ya shigayi yana salati

“Hazbinallahu waniimal wakil ,yanzu Ke Salima ɗingurugum leshin nan kika bada aka tsiyata da wannan ɗinkin? Ji leɓatu kotaina suna reto a iska ,meye amfanin dinkin nan kenan? Kinsan tsadan leshin nan kuwa? Da aka tsiyata leshin da gown kwara ɗaya jal!!!”

Marairaice murya tayi a shagwaɓe tace
“Ni Ina son style din ne”

Dafe goshi yayi

“Ohwuuuuu,Salima meyasa bazaki zama irina ba, Leshin da za ayi kaya uku dashi anyi daya.....ya salam
Ya kamatane kisa tela ya maki dinkin yadi hudu doguwar riga,sai kuma ki siya wani yadin ko satin ne dai ayi maki combination dinki a maki ko riga da siket ,ba sun zama dinki biyu ba kenan?”

Langaɓe kai tayi ta ɗaura hannu a ƙarfen benen ta masa shiru

“Yanzu dai nawa aka maki ɗinkin nan?”

“kyauta kawata tayi mun”

“Ehennn kinji maganar nan,ta cuce ki! Ni dama nasan ɗan jikinki bazakici 6yards ba ,ta maki wayo kamar anci ƙyalle a ɗinkin ta kwashe sauran yadin....kiyi amfani da hankali salima🧏‍♂️” ya nuna gefen kansa kamar wani super professor

Caɓe fuska tayi duk ya sattar mata da gwuiwa

“Shikenan bari inje in sauya kayan ”

“Ke😳Tare nike da Ambassador ,sai kuma ki sake ɓata wani lokacin,kiyi amfani da hankali salima🧏‍♂️” ya sake nuna mata gefen kansa 😄

“To shknn muje ,za'a kiyaye gaba”

Oum Aphnan
09065990265
*_🐹BAD BOYS🐹_*
By...
Oum Aphnan

007
___________________
“Knock knock knock”

Daga can upstairs taji ana knocking a entrance door ɗin parlourn ta ,wannan ya sata fitowa da sauri tana faɗin “Ana zuwa”

Sanye take da bugujejen jallabiyar Ya Sheikh sai hulan wanka a kanta da falkata falkatan silipas ɗin da take sakawa a ɗaki.

Murza key ɗin ƙofar tayi ta buɗe ƙofar ,cak ta ja ta tsaya ganin very tall handsome man a tsaye , kyakyawar gaske cikin ƙananun kaya ,fuskarsa kewaye da ƙasumba ya ɗan ajiye tumbin kuɗi cif cif a riga

Yana ganin ta buɗe ya saki fara'a har jajayen leɓensa da suka haskaka brown ɗin fatarsa suka sake bayyana.

“Hajiya Barkanmu da rana” yanda yayi maganar a rarrabe ya bata dariya ta lura baida Hausa sosai

“Masa'al khair” Adnan Yana jin ta iya larabci yaji kamar ta taindimashi a Aljannah ,ji yayi kamar ya kamata ya rungume

“Masha'allh A adkhul?”(In shigo)

Yanda ya ruɗe sai kawai Sayyada ta tsinci kanta cikin jin nishadi ,daga gani wannan ɗan comedy ne ,kuma duk yanda akayi mutanen Sheikh ne na wasu ƙasashen

“Tafaddal”(Shigo) ta bashi hanya ya shiga ,itama ta rufo ƙofan ta biyo bayansa .
A tsakiyar falon yaja ya tsaya ,suka gaisa sosai

“....Ammm sunana Dr Adnan Ni Likitan ƙwaƙwalwa ne ina da Asibiti a ƙasar nan ,London Specialist ,nazo ziyarar aikine So nasa a siya mun gidan da innazo zan ringa sauka Inshallah ,shine aka bani wancan gidan da yike kallon nan Compound ɗin.”

A ɗan ɗarare Sayyidah tace “Sannu sir,Ashe maƙoci mukayi”

“Na'am,to shine fa tun safe na sauka da empty stomach ,bansan koina ba ,Inason inci abinci ,amma gaba-daya water system ɗin da wutan gidan na kasa connecting ,bansani ba ko ƙauyanci ne😆Ko tsarin naku na irin na ƙasar mu bane oho”

Dariya Salima ta fashe dashi
“Hummm ɗan gayu kamar ka ai saidai ace baku saba da ganin local one irin namu ba ,na en Nigeria...Nikam yanzu me kake so inyi maka”

“Yawwa don Allah to ki ɗan haɗa mun wai cofee ne insha atleast kafin in samu a gyara mun komai nawa”

Gaban sayyada fadi yayi dam ,a take idanuwarta suka zazzago
Ta fara sosa ƙeya “Ammm eh ,dama ehhhh ,wallahi bamu da kayan shayi ” ɗaga kai yayi yana ƙarewa falon kallo ,gida har gida kudi gasunan basu magana wai ba kayan tea” bai nuna mamakinsa ba sai ma wayancewa yayi irin na gogaggun maza da suka saba hulda da mutane .

“Nop karki damu ai ma taho da nawa kawai ruwan zafi nikeso ” ya mika mata ledan hannunsa ,Plz ki hado mun a ɗan mug.

Amsa tayi a kunyace ,ta wuce Katar Katar ,ɗuwaiwuka da nonuwa suna ta rawa a Jallabiya ,bin bayanta da kallo yayi ,inner side ɗin zuciyarsa tana harbawa da ƙarfi ,a zahiri yace “Wow Original kyau please”

Sai kuma yayi saurin minding business ɗinsa ta hanyar daukan remote Yana canja channel din TV.

Minti kaɗan sai gata ta dawo da ɗan mug din shayi a saman tray ɗinsa da ɗan cokale a gefen cup ɗin.
Ta saman kansa ta miƙo masa

“Gashi ” Hannu biyu yasa ya karɓa yana bin ƙirjinta da kallo
Haka yakai cup din baki ya kurɓa “Shukran”(Nagode) ...Amma ina naki?”

Zaro ido tayi ,a ranta tana cewa shi wanann ya faye shishigi Ni ya tashi ya fita kafin ya Sheikh ya dawo.

“Ya zanyi in Sha maka abunka ? Hazha haram,ga sauran kayanka nan” cikin mamaki ya ajiye cup din shayin a saman table yana kallonta .

“Kar kice mun kina da rowa?” girgiza masa kai tayi da sauri

“To Ni kayana na kowane ,in inacin abu Naga wani bayaci gaba-daya abun gundura na ma yake yi,don haka Matsawar bazaki hada naki ba to nima na fasa sha”

Sayyada da tun asali ƙamshin shayin yake damunta ,miƙewa tayi a sanyaye ta samo cup ta ɗiba Dan kaɗan zata mike yace “Wai ku haka kuke shan tea so watery _Ba kauri?_”

“A tattala Mana in ya kare fa kaya na tsada a nan?”

Zaro ido yayi
“Topah ,Add things johhhhrrr”

Lafiyayyen Tea sayyida ta haɗa tazo falon can nesa dashi ta zauna tana sha a ɗarare duk ta ƙosa ya tafi

“Kayi hakuri ba bread ”

“Nop banashan tea da bread ,akwai kaza? Ko soyayyene?”

Zaro ido tayi harda dafe ƙirji
“Kaza? A nan?(kawai sai ma ta fashe da dariya)

“Aah baƙo babu”

“Halan su mama da baba basa nan ne wai?”

“Nan fa gida na ne”

“Oh dama ƴan mata suna iya zama a gidansu su kadai ba aure?”

“Sir I'm married” tsuriii ya kafeta da ido yanason gano asalin gaskiyar

“Hummm Saboda kin ganni baƙo shine zaki mun kora da hali?”

“Aah wlh da gske”

“Wow amma fa mijinki ya iya zaɓe,wlh kin cika duk wasu quality da nike neman mace dasu ,da na sami irinki da tuni nayi aure"

Sai yanzu ta masa kallon ƙurilla ,tabbas ya haɗo kuma tana kallonsa ba abunda ya faɗo mata a rai sai aure. Ji take tamkar ta rungumesa ko zata samu sassauci,lokaci daya bugun nunfashinta ya daɗa hauhawa

“Ƙatotonka dakai ba mata abun kunya”

A shagwaɓe yayi magana gamida langaɓe kai kamar zaiyi kuka

“Hum ban samu taste Dina bane ,nikuma gaskiya bazan iya auren macen da take not active a gado ba,saboda gaskiya Ni maciyi ne,I'm sorry kuma kinsan duk foodie dole yana buƙatar ɗumin active woman a Koda yaushe...”

Sunkuyar da kai tayi cikin jin kunya.

“Sorry na baki kunya ko? Ni namijine ke namiji... magana ake na gender equality ,kinsan komai na sani daga halittan mu aka halicceku ,dole muna da sha'awar jinsin da bamu dashi ko ba haka ba ?”
Shiru ta sake yi Tana jin wasu feelings da ta manta when last ta jishi yana taso mata,Zuciyarta tayi rauni ,hawaye a take ya fara kwanciya a idonta ,babu abunda takeso sai taji ɗumin namiji a kan gadonta,amma ina abun ba da sauki bane ba ,kullum ya Sheikh yana cikin Alwala baya son ko da wasa hannun mace ya shafi jikinsa bare ta karya masa Alwala.

Zumbur tayi ta mike tasa bayan hannunta tana goge ƙwalla
,tana tuna hadisin Manzon Allah da yike cewa duk inda mace da namiji suka kasance na ukunsu shaidan ne.

“Mijina ya kusa dawowa zanje in masa girki”

Dariyar yake yayi “Ok Nagode da karamci,meye sunan ki to”

“Salimat” ta bashi amsa tana nufar ƙofa da sauri ta buɗe masa , Murmushi yayi amma shidai psychologist ne ,ya fahimci akwai abinda ke damun Salima ,kuma ya kudiri aniyar zai bibiyeta a hankali.
Chapter 6 · 0% Book details