← Book details Allah Gatan Bawa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 22

Sashe 10

Allah Gatan Bawa Complete Hausa Novel · about 7 min read

Anwar nanan tsaye ihsan tafito taganshi yana leke dariya tasoma yimishi kiranta yayi yatambayeta dady nacikin dakin aa tabashi amsa dan haka with confidence yashiga dakin guri yasamu yazauna yana sosa keya momy takalleshi tana murmushi tace Anwar kenan angon karni ko shekara ilham batayiba Sega yara amatsayinta nawacce bakaso keyarshi yaci gaba dasosawa yana. Murmushi kalle kalle yafara yanason gamin yaransa danshi bata ilham yakeyiba shide burinsa yaga yaransa tare da fatan Allah yasa shi suka biyo
Momy ce talura da yanayinshi tace babies din kake nemako kai yagyada mata suna gurun dadynka kaje dakinshi kagansu
Jiki asanyaye yamike yafuta dakin dady yashiga da sallama dan harga Allah yakosa yaga yaranshi sallamarsa dady yaamsa sannan yamasa izinin shigowa yaran n'a hannun dady har yanzu kuma dukansu suntashi amma basa kuka se wasa da kafafunsu sukeyi annadesu acikin tawul dan babu kayansu dan baasan da cikinsuba bare atanaji kayan samusu
Gaida dady yayi cike da Jin kunya dady yaamsa masa fuska asake sannan yace Anwar kaga tashin hankalin daya samemu ko ashe ilham da ciki tashigo gidannan kai amma Wanda yamata wannan abu be kyautaba ninarasa yadda zan bullowa lamarin dady yafadi yana kallonsa dan yanaso ne yaji me Anwar zece shiyasa yace haka
Kan Anwar ne yadaure ganin daranshi dady nashirin shegantamasa yara dasauri yakalli dady sannan yafara da cewa dady wlh yaranane nine mahaifinsu dady yace banganeba kana nufin kasan da cikin kenan amma baka fadawa kowaba nibansan tana da cikiba amma tabbas yaran nawane dariya dady yayi sannan yace taya bakasan da cikiba sannan daga ganin yara kace nakane kace kowama ze iya kama dan wani yace nasane
Anwar ganin dady da gaske yakeyi yasa shima yakara zage damtse wlh dady dagaske nakeyi nine mahaifinsu sabida ninafara sanin ilham yafada batare da shayin komaiba salati dady yayi sannan yace anya Anwar baka fara shayeshaye ba kuwa taya zakacemin haka bayan baku taba kwana guri dayaba. Habawa Anwar kamar jira yake yafara rantse rantse yana shifa yaranshine kuma bawanda ya Isa yahanashi yaranshi shi wlh yaransane zuwa lokacin har yamike tsaye kamar meshirin yin dambe bakaranin dariya dady yayiba sannan daga karshe yayarda da Anwar din dama kuma gwadashi yayi danko mahaukaci yaga yarannan zece Anwar ne ubansu
mika masa yaran dady yayi yace yamusu huduba bayan yagama musu huduba yaci gaba da kallonsu yana hawayen farincikin yanajin son yaransa naratsa zuciyarsa
Wayarshi yadauka da niyar daukarsu hoto seyaga ba kaya ajikinsu betsaya tambayar komaiba yamikawa dady su yajuya da sauri yafita excode dinshi namaramasa baya mota sukaga yanufa danhaka suka gane fita zeyi kankace me kowa yashige mota cikin shirin kota kwana suka fice daga gidan

jin karar jiniya ne yasa dady yagane Anwar fita yayi ko ina zashi oho momy ce tashigo dakin tsiya tasoma yiwa dady tana cewa kode shine angon karnin dariya yayi sannan yakwashe yadda sukayi da Anwar yafadamata momy dariya harda kwalla
daukar yaran momy tasake yi tana kallonsu sannan tace alhaji kaga ikon Allah ko. Wlh son yarannan nakeyi kamarni na haifesu rungumeta dady yayi gaba daya ita da yaran yana fadin mugodewa Allah shiyabamu hakane inji momy

shiko Anwar yawo yadunga yi à garin abuja har yasamu wani baby care suka shiga dakanshi yadunga zabarma yaranshi kaya kowanne iri daya motoci guda biyar yafita dasu amma bawacce boot dinta becika da kayaba yabiya kudin suka nufi gida sukansu masu shagon se mamaki sukeyi zuwan Anwar shagonsu dan ba boyayye bane kowa yasanshi

misalin shadaya darabi su momy suka ga se shigo da kaya security sukeyi kamar hauka basuyi musu mgnb
har suka gama sannan Anwar yashigo
tambayarshi momy tayi wannan kayanfa na yaranane yabata amsa mamaki sukayi daga momy har dady ihsan ce tafara bude kayan wow kawai take fadi daga karshe yashiga tayata suna shigar da ayan dakin ilham tunkafin sugama tuni inna tadauki wasu kaysn sanyi farare tashirya yaran aciki bayan ansamusu Pampers
koda Anwar yashigo yagansu bakinshi yaki rufuwa daukarsu hoto yadunga yi awayarsa gashi yaran sunbude ido gwanin shaawa gasu identical twins ko ganesu bazakayi ba sekalura dazaran da inna tadaura musu itama tabanbancesune yayinda ta daga ilham bayab ta haihu anan taga daya akasa daya asaman dayan to nan tagane nakasan shine yafara fitowa

har yanzu Anwar kotakan ilham bebiba wacce ke kwance tana sharar baccin gajiya tayaransa kawai yakeyi
kan gari yawaye gaba daya hotunan twins yagama zagaya social media waya ko kama daga Anwar dady momy ihsan Sun fara amsata tun cikin dare duk yan taya murnane

dasafe inna tayiwa ilham wankan jego dan haka ta lura ilham na yoyon fitsari duba da tayi shinfidarta tajike hankalin innane yatashi
[3/13, 07:09] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

_Zahra Muhammad mahmud_

*ayimin afuwa à page dina na farko namanta ban shida muku yayan baban ilham daya bace yanada iyaliba yanada mata daya dayaro daya namiji dan lokacin yaron shekarunsa ashirin kuyi hkr akasi aka samu*🙏🙏🙏🙏🙏

*page 43-44*

*DOCTOR MONEER*

shine likitan daya taimaki ameera aynihin sunanshi kenan
Tun watanni uku dasuka wuce yatafi kasar Amsterdam karo karatu mahaifinshi alhaji Ali kura haifaffen garin kurane ta jahar kano inda kasuwanci yamaidashi cikin garin kano da zama yana da mata daya da yara biyar hudu maza se karamarsu ta mace. Moneer shine babba se Hassan da hussaini se Abdullahi sannan auta intusar. Suna zaune a unguwar nasarawa gra dake kano. Alhaji Ali kura hamshakin me kudine a kano yaranshi kuma dukansu karatu sukeyi afanni dabandaban ita kuwa intusar tana aji biyar amatakin secondry..

Moneer zaune yake a hotel din daya sauka gaba daya tunanin ameerar sa yadameshi dan ba karamin so yakemata ba gashi yanzu shekara biyu zeyi a kasar Amsterdam kafin yakoma Nigeria abun duk yadameshi wayar shi yadauko domin yahau chatting koze ragemasa kewa gashi megari yahana yasiyawa ameera waya gashi yayi rashin hausa be amshi numbar megariba.
Instagram yahau yana kallon hotuna gabanshi yafadi yayin dayayi karo da hoton Anwar da ilham zuface ta karyomasa danshi harga Allah yadauka ameerarsace rubutun kasan Hoton yafara karantawa inda yaga ansa happy mariage life Anwar umar mutalab manumfashi and ilham bukar shettima what !!!!

Itace kalmar data fito abakin moneer dan yayi imani wannan itace ilham din ameerarsa data bace wacce kullum ameera kemishi kukan rashinta wani matsanancin farin cikine yaziyarshi zuciyarshi sede ameera tacemishi ilham nakasasshiyace but wannan bega alamar hakaba ko tasamu saukine tambayoyin daya dunga jerawa kanshi kenan.
Saving din hotunan yayi sannan yaci gaba da mamakin tayaya ilham har dan shugaban kasa ze aureta kuma ministan petur kai gaskiya abun da mamaki
dayayi niyar yakira wayar kannansa dan ya aykesu wudil gidan me gari sekuma yatuna suma basa kasar Nigeria duk suna kasashen dasuke karatu tsaki yayi gami da kara Jin haushin rashin waya a hannun ameera dan yasan inyayiwa ameera albishir zataji dadi rasa yadda zeyi yayi abokanshi kuma be yarda suje suis ameerarsaba dan kar amishi snaching dan ameera hasken fata kawai ilham zata nunamata dan kamarsu daya.. Dayagama tunani yaga ba mafita kawai addua yashiga yi dan itace kawai mafita gashi karatunnasa ba hutu bare yace zeje Nigeria yadawo

*BAYAN WATA HUDU*

zuwa yanzu ilham nanan apart din su momy domin koda yayiwa dady mgn kin amincewa yayi sabida momy tafadamasa abinda yayiwa ilham din dan haka dady yaki amincewa.
inna ladi yadawo itama gidan inda dady yasa akawaremusu daki ita da ilham tun zuwan inna kulawar ilham tadawo hannunta sosai take kulawa da ita.
ilham wacce ke dauke da ciki natsawon watanni hudu amma kaf gidan bawanda yalura tana da ciki domun cikin ko kadan benunaba illa jikinta dayabi zuwa yanzu takara kiba sannan ga wani fari datayi kuma cikin Allah yasa bame laulayi bane duk chanjin datayi jamaar gidan Sun Alakanta hakan da Jin dadi da kwanciyar hankalin data samu baiwar Allah kenan cikin na motsi amma ita ina ko ajikinta
tunda inna ladi tazo tsawon wata biyu kenan Anwar besake samun damar zuwa gurin ilham ba tsawon watannin kuma besata a idonshiba hakan bakaramin dadi yamasaba amma dazaran yayi mafarkinta burinshi yaje gareta amma ba hali sede yahakura

ziyara fadar shugaban kasa tashirya inda zasu kai ziyarar ayki natsawon watanni biyar à kasar amurka inda acikin tawagar shugaban kasa harda ministan petur wato Anwar dashi kanshi shugaban kasar.
ranar monday suka daga zuwa america suka bar gida cike da kewarsu zuwa yanzu momyce ce shugabar gida yayinda aykinta na office yakaru Bata samun zama agida

Koda zasu tafi seda dady yace anwar yaje yayi sallama da ilham amma yaki zuwa. Wanda shi dadyn besan bejeba

*BAYAN WATA BIYAR*

Cikin ilham yatsufa haihuwa ko yau ko gobe kuma dama tun zuwan inna takoyawa ilham wanka dakanta danhaka ita take wankanta duk da ba fita takeba amna inna tace gwara tadunga yima kanta dan tasaba dan haka har yanzu bawanda yalura dacikin jikinta amma fa tayi wata irin mahaukaciyar kiba wacce momy tace zata kira doctor yadubata anya kibar ta lafiyace kuwa dan tunaninsu ko bata da isasshen Jinine ajikinta dan gashi har wata danyacewa tayi

yau da magaruba tawagar shugaban kasa suka iso Nigeria dan haka kai tsaye gida aka fara rako shi sannan kowa yakama gabansa
Chapter 10 · 0% Book details