Sashe 20
Alkawarin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Ahankali aka bude kofar motar Ammi, wani clean white kafane ya sauko dake sanye cikin wani hadadden sandals na Prada black, nails na kumban kafan are so fresh and white, gently yakarasa saukowa daga cikin motan yana yatsine fuska yana gyara bakin sun glasses na idanunshi na kampanin rayban, yana sanye cikin milk color yadi dayay dinkin jumper dashi daya bala’in amsan jikinshi, yanada tsayi dan wajen gabaki dayansu yafisu tsawo babu wanda baya ganin kanshi, yanada cika dakuma fadin kirji, kana ganinshi kaga Ammi kaman tai kaki ta tofar saisa yafi kannenshi kyau dansu Hafiz da Baffa suke kaman, yanada wani irin black very very dark saje dake kyalli kaman na bature, lips dinshi is so pinkish, gashin kanshi a kwance suna shinning, hannunshi ya daura agogo Rolex akai, ita kanta Ammi anytime ta kalleshi she feels proud da Allah yabata Zayn as her son, Zayn is definition na handsome guy, kyakkyawan namiji da babu macen data isa tamai yanga, ganin Baba yataho wajensu yasa ahankali yakai hannunshi yazare eye glasses na idanunshi yadan sunnar da kanshi kasa Baba nazuwa cikeda mamaki yakama hannun Baffa yace “d’ana Zayn nake gani haka” murmushi daga Baffa har Ammi da Mom sukayi, Baffa yace “da asuban nan yashigo gida” anatse Zayn yace “ina kwana Abba”? Hannu Baba yabashi ahankali yasa nashi hannun cikin na Baba, daidai sukaji muryan Maheer yana ihu. “Babaaa” Dawani irin sauri Baba yasaki hannun Zayn yay ciki Baffa da kowama suka bishi sama sukayi, dakin Mama Baba yashiga yatarar da Mu’az yarike Mama dake aman jini sosai tai lakur babu karfi kodaya ajikinta, wajenta Baba yayi yakamata daga hannun Mu’az yadau tissue yana share mata bakin ganin tadena aman, shigowa dakin Mom tayi takalli Baba tace “Alhaji bari mu chanza mata kaya” girgiza kai Mama tayi ahankali tana rike Baba gam batare datai magana ba, kallonta yayi sanan yakalli Mom yace “abarshi tukunna” karasowa gaban gadon Baffa yayi yaja kujera yazauna yana kallon Mama dabata iya bude idanunta da kyau yace “Maryam mutafi asibiti”? Girgizamai kai tayi ahankali, ajiyan zuciya yasauke yay shiru, shigowa ciki Ammi itama tayi tasami gefen gadon tazauna ahankali tana kallon Mama murya chan kasa tace “kina bukatan wani abu Maryam mezaki ci?” Girgizama Ammi kai tayi hakan yasa itama tai shiru, ahankali Baffa yajuya yakalli Zayn daya tsaya chak abakin kofa shima yana kallon Mama sanan Baffa yajuyo da kanshi ya kalli Mama yace “Maryam ga Zayn dakika ce nakira miki yazo” dan yunkurowa kadan tayi da duka karfinta, dasauri Baffa ganin haka yasa yace “Zayn come” karasowa gaban gadon Zayn yayi ahankali sanan gently ya tsugunnawa gaban gadon yana kallon Mama dake kallonshi kallon dakasan baa hayyacinta takeba yace “Mama I am here” hannunta daya tacire daga jikin Baba data rikeshi gam gam jin haka yasa Baba yatayata , kama hannun Zayn tayi hawaye yazubomata daga idanunta sanan kadan tabude bakinta dasauri Zayn da zuciyanshi ta katse yace “Mama I am here mekike so tell me” yakai kunenshi saitin bakinta, magana tashigamai a kunne wanda harta Baba dayake rikeda ita baiji abinda ta Fadima Zayn ba sanan takoma jikin Baba ta kankame shi, Maheer dataga yana kuka sosai mara sauti abakin kofan ta kalla hannu tamikamai ahankali yataso yazo kawai kankameta yayi yahau kuka sosai ahankali yace “Mama dan Allah kiwarke, Mama please karki mutu kibarmu” motsi sosai bakin Mama yafara hakan yasa Baba ya janye Maheer daga jikinta kankame Baba tasake yi takama hannunshi tarike gam gam kaman dats the only thing dake mata dadi sanan cikin wata kalan murya dabata fita da kyau dan hakoranta sun datse tace “Baffa, Ammi, Mom, dukanku yarana ina rokonku gafara ku yafeni idan nataba bata muku, idan Ummulkhair…..” wani kalan nishi tayi tana kuka sosai dabayama fitowa sosai tace “kuce mata nace tayakuri tayafema Maman ta, i hide everything sabida nasan idanda tasan banda lpy bazata dauki abin da kyau ba, Baban Manaf” tai maganan tana kankame Baba tace “ka kulamin da Khairy dan Allah, Baffa nabaku amanan Khairy da duka yarana, Khairy is fragile, and innocent please ku rikemin yarinyata amana ita nafiji araina, zanbar duniyan nan amman Khairy ce araina sabida ita kadaice diyata mace yayyinta maza ne” ajiyan zuciya Mama tasake saukewa sanan ahankali tace “idan narasu Khairy taki kwantar da hankalinta kabata Littafin nan danabaka ka ijiye mata Baban Manaf” gyadamata kai Baba yayi ahankali hawaye na taruwa a idanunshi Baffa ya bubbugamai kafa alamun karyay kuka, ahankali Mama tace “Baffa kamishi aure dazaran na rasu banson yarana su rasa uwa, Manaf kurike Matar da mahaifinku zai aura kaman ni kada kubata ciwon kai” gyadamata kai Manaf yayi, Ammi kallon Mu’az yayi dake bakin kofa tayi ya tsugunna idanunshi sunyi jajir tace “zo wajen mahaifiyar ka Mu’az” mikewa yayi tsaye da kyar shigowa yayi zuwa wajen gadon kawai yadaura kanshi kan gado yadaura hannunshi kan nata dan that’s what Maheer da Manaf duk sukayi, yanda tazo tana nishi yasa Baffa ya gyadama Baba kai ahankali Baba yasoma karanto mata kalman shahada, saukar da kanshi kasa Zayn yayi, ahankali Mama ta amshi kalman shahadan karfe 12:03 daidai tacika da imani daidai lokacin Khairy ta tashi daga kan kujera sun gama lectures zasu fita jitayi kafafunta sunyi sanyi kawai tai baya zata fadi kaman tai paralyze Rabi dake bayanta ta tareta tace “ke Khairy are u okay” ? rike Rabi tayi tana taba kirjinta tace “gabana fadi yakeyi sosai kafana ba karfi” zaunar da ita Rabi tayi tace “kinyi breakfast kuwa”? Girgiza kai tayi hakan yasa Rabi da sauran kawayenta sukai dariya tace “yunwa ce muje kici abUinci”.
2️⃣5️⃣
Almost good 10min na silent ne yacika dakin, at this point Baba jiyayi kaman shima yamutum ne dan he could feel yanda hannayenta suka sassandare ajikinshi kasa koda motsi yayi hakan yasa Baffa yay taking over, daga Baba tsaye yayi, ahankali Baba yasauke kanshi kasa yana kallonta in disbelief, yadade ahaka sanan yakai hannunshi ya kulle mata idanu kafin yaja bargon yarufeta saikawai yazauna akasa dabas baimasan mema zaiyi ba dan he’s still in shock idan ya kalli su Manaf daduk suke kuka saiyaji zuciyanshi yakara tsinkewa, kafadanshi Baffa yakama ya matsa hakan yasa ya fuzar da iska kafin ahankali yasa hannunshi yakamo su Manaf daya bayan daya duka yarikesu ajikinshi kam kam, juyawa Baffa yayi yakalli Hafiz dashima yay mutuwan zaune hakama su Hassan ahankali yace “Hafiz jeka dauko Khairy daga makaranta”
Tashi Hafiz yayi ahankali yafice daga dakin tafiya yake but jiyake kaman iska ke kadashi yana tuna all memories dinshi da Mama shikenan daba danta data haifa ba balle kuma yaranta yaya zasuji.
2️⃣5️⃣
Almost good 10min na silent ne yacika dakin, at this point Baba jiyayi kaman shima yamutum ne dan he could feel yanda hannayenta suka sassandare ajikinshi kasa koda motsi yayi hakan yasa Baffa yay taking over, daga Baba tsaye yayi, ahankali Baba yasauke kanshi kasa yana kallonta in disbelief, yadade ahaka sanan yakai hannunshi ya kulle mata idanu kafin yaja bargon yarufeta saikawai yazauna akasa dabas baimasan mema zaiyi ba dan he’s still in shock idan ya kalli su Manaf daduk suke kuka saiyaji zuciyanshi yakara tsinkewa, kafadanshi Baffa yakama ya matsa hakan yasa ya fuzar da iska kafin ahankali yasa hannunshi yakamo su Manaf daya bayan daya duka yarikesu ajikinshi kam kam, juyawa Baffa yayi yakalli Hafiz dashima yay mutuwan zaune hakama su Hassan ahankali yace “Hafiz jeka dauko Khairy daga makaranta”
Tashi Hafiz yayi ahankali yafice daga dakin tafiya yake but jiyake kaman iska ke kadashi yana tuna all memories dinshi da Mama shikenan daba danta data haifa ba balle kuma yaranta yaya zasuji.